Cutarwa Hausa Novel

Cutarwa part 7

This entry is part 2 of 2 in the series Cutarwa by ayshercool

                         CUTARWA!

P7

A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi.
Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti.

Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi.

Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba.

Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida.

Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?.

“Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje”

“Saboda iskanci, me tayi masa?”

“Oho masa”

“Kema uban waye ya ce ki fita?” Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye.

Ya ce “Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi”

Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita.

Iya kuwa mita take tana “Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba” Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji.

Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa.

Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa.

Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana.

Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ƙasa a ido ne.

Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya ta ƙwace kuɗin da kawunsu ya bawa ummi, da kuɗinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaɗan.
Ummi ta ji daɗi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ƙwarin gwiwa take zuwa makaranta.
Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba baƙi ne wuluk ba.

Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ƙoƙarin da ummi take da shi, ya zama a banza, saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ƴan uwanta ɗalibai za su yi mata, koma malaman da kansu.

Wujiga-wujiga ta dawo daga makaranta, saboda azabar yunwa, koko ne kawai a cikin ta, shima tun sha ɗaya da tayi fitsari, take jin kamar an sace mata kayan ciki saboda yunwa.

Da ƙyar ta ƙarasa gida, tana zuwa iya ta ɗora mata kai niƙa, haka ta kuma kwasar rana, ta kai wa iya niƙan ta dawo, a wannan wahalen da take, wannan ya ja ya aika, wancan ya ja aika, har lokacin shiga makarantar allo yayi.

Iya ta rage mata abincin rana, bai fi loma uku ba, a loma ɗaya da kaɗan ta cinye, ta tashi ta tafi makarantar allo.

Naima ce ta hangota tana share hawaye da hijjabinta, ta ƙarasa in da take ta ce “Ummi, ya aka yi ki ka makara? Kuma kukan me ki ke yi?”.

Cikin kuka ta ce “Malam babba ne ya dake ni, na makara”

“To meyasa ki ka makara?”

“Iya ce ta aike ni”

“Shegiyar mata, mai zuciyar kafirai” Naima ta faɗa a ƙule, ummi kuma ta kalli fuskar naima tana mamakin yadda take zagin babba kamar iya.

Ta ja hannunta ajinsu, ta ɗaukko wani ɗan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ƙwarya ummi take danna abincin.

Na’ima ta dubi ummi ta ce “Ya jikin amma dai kin warke ko?” Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh.

“Gashin ya fara fitowa?”

Ummi ta saka hannu ɗaya ta buɗe mata kan, Na’ima ta rufe mata ta ce “Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke kayanki na makarantar boko?”

“A’a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko” ta faɗa cike da jin daɗi.

Na’ima ta ce “Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a ɗinka miki atamfar bikina”

Ummi ta kalleta ta ce “Biki, aure kenan?”

Na’ima ta ce “Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?”

“Eh yaya Na’ima zan biki dan Allah”

Na’ima ta ciro ɗan ƙaramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata hannu ta ce “Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki”

Ummi ta ce”Ba zaki tafi da ni ba?”

“Ki yi haƙuri ummi, ba zai yiwu ba”

“Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi taƙi dawowa”

Na’ima ta yi ajiyar zuciya ta ce “Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi” ta miƙar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu.

Naja da take ƙawar na’ima, ta ce “Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita”

Na’ima da hawaye ya taru a idonta ta ce “Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan ɗauke ta, kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar ɗakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma garinsu, Kakarta ta ƙwacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ƙarshe ba” Duk da a ƙufule Na’ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ƙarshe ta bata dariya.

Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daɗi mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski.
Na’ima ta ce “Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta haƙuri kin ji ummi, duk tsanani duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?” Maimakon ummi ta amsa sai ta ɗaga kai tana kallon na’ima.

Cikin sauri na’ima ta tsaya ta ce “Suna yi miki wasan banza ko?”

Ummi ta girgiza kai ta ce “A’a”

“Ki gaya mini gaskiya, suna taɓa ki ko?”

Ummi ta girgiza kai ta ce “A’a”

“Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko” ta jinjina mata kai alamar eh.

“Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci”

Da haka suka ƙarasa gidan mai takalmi, aka yi sa’a aka samu dai-dai ƙafar ummi.

Na’ima ta ce “Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?”

Ummi ta ɗaga kai tana murmushi, daga nan suka ƙarasa gida.

Ummi ta shiga gida hannunta riƙe da wani kara tana wasa da shi “Ke!” Idris ya kwaɗa mata kira a wulaƙance.

Ta juyo tana kallon sa.

“Zo ki sayo mini sukari a kanti” yayi maganar yana watso mata kuɗi.

Ta durƙusa ta ɗauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaɗin Na’ima na hanata zuwa ɗakin su idris.

Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito.

“Dan ubanki ina aiken da na yi miki?”

Da sauri ta miƙe tana nuna masa sukarin.

“Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?”

Tayi shiru tana kallon sa, “Ba zaki kawo mini ba” ya sake yi mata maganar cikin tsawa.

Ta ƙarasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haɗa da hannunta, ya ja ta cikin ɗakin.

Kuka ta fara yi masa iya ƙarfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daɗe, amma ta nuna masa tayi wayo yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ƙarfi, kamar yadda Na’ima ta gama gaya mata ɗazu.

Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani ɗan lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin tsuma, tana karkarwa.

Wata sharɓeɓiyar wuƙa ya nuna mata ya ce “Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki” kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wuƙar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai teɓa dan wannan dai ba nono bane.

Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ƙarfin ta.

Bankaɗo ƙofar ɗakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba.

“Idris meye haka?” Hashim yayi maganar yana kallon sa.

“Kamar yaya meye haka, abun da ka gani” a fusace ya ƙarasa ya hankaɗe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce “Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?”

Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce “Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni”.

“an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na ɗauki mummunan mataki a kan ka”

“To ka ɗauka mana kar ka fasa” ya sake jan tsaki ya fice.

Cikin ƙunar ran yadda ƙaninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye, ya fito da ita daga ɗakin, shaidar yastun idiris kwance a kan baƙar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini.

Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a tsaorace take, kuma hawayenta ya ƙi tsayawa.

“Ummi” ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka.

Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya riƙe hannunta suka nufi sashin iya, tana ta dakan fura tana waƙe-waƙe.

Tana ganinsu tare ta hau bala’in tun ɗazu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna.

Magaji ya ce “Iya”

“Ya aka yi”

“Dan Allah idan ba za a iya riƙon yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike mata a ɗakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah”

Iya ta dafe ƙirji ta ce “Shi idiris ɗin? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita ɗakin ku, ai ita ta kai kanta, amma shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba ɗan uwanka ba, ka ke ɗaga murya tona masa asiri zaka yi?”

“Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?”

“Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta bawa dabbobina”

Hashim ya ce “Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane”

“Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ƙanƙanuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji”

“Haba iya, me ummin ta sani da zaki faɗi wannan mummunar maganar a kanta?”

Iya ta ce “Zaka zo ka kai mini dusar ko ta ɗauka ta kai mini?”

Ya ƙarasa ya ɗauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai.

Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya.

Iya ta dube shi ta ce “Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba, kai gashi ba sana’a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara maka ba, na gaya maka”

Cikin fushi ya ce “Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?”

“A’a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi”

Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba.

Rashin samun biyan buƙatar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ƙara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faɗan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa ita ta gaya wa Iya.

Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ƴan uwan ubanta da suke ciki ɗaya, da wanda uba suka haɗa da matayen su, babu wanda ya taɓa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ƴar tsintuwar da ta faɗo daga sama.

Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na’ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta take jin rabuwa da ummi.

Mariya kuwa tun ƴan uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata haƙuri, har suka zubawa sarautar Allah ido suka ƙyaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum tana ɗaki, daga bacci, kuka sai shiru.
Yaya ɗan lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba.
Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba ɗaya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta.

Yaya ɗan lami kuwa da suka ga mariya taƙi sakin ranta, ya ƙare mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin ta je wurin su Iya babu su babu ita, ƴa ce idan ta girma da kanta za ta neme ta.

Watan azumin ramadana ya kama, wanda hakan ya sake jefa ummi tsaka mai wuya. Ba iya azumi take yi ba, dan haka babu mai kulawa ya bata abinci, haka za ta yi ta gararanba ta wuni a kwance, idan makaranta ta je, tana kallo yara na ciye-ciye, ita ba raɓar su take yi ba ma, balle ta yi musu kwaɗayi, ko kuɗin makaranta ba bata ake yi ba, dan haka bata saba da kashe-kashen kuɗi ba.
Sai an sha ruwa take samu ta ci abinci, sai da hashim ya fuskanci ba ta samun abun da za ta ci da rana, shi ne yake rage mata abincin sa, da safe ya bata, da rana ya sai wani abun ya bata. A haka har aka ƙare azumi.

Da salla kowane ɗa cikin kyakywar shiga mai kyau, ummi kuwa kayan bikin na’ima ta saka, da suka fara koɗewa, da takalmin makarantar da kawunsu ya saya mata, shi ta koma tana sakawa tayi yawo da shi a gari, saboda ko silifas ba ta da shi, wanda naima ta saya mata tuni ya lalace.

Yara na ta shiga su na fita, ummi kuwa na ƙofar ɗakin mamanta, ta zauna tana wasa da duwatsun wurin.

Hashim yayi sallama, ummi ta amsa cikin ƴar siriyar muryarta.

Ya ƙarasa in da take zaune, ya ce “Kin je sallar idi ne?” Ta girgiza kai alamar a’a.

“Me ki ke yi a nan wurin?”

Ta ce “Bakomai”

“Kin ci tuwon salla kuwa?”

Ta ce “A’a iya dai ta ce zata bani”

Ya miƙa mata hannu ya ce “Taso mu je”

Ta saka hannunta a nasa, ya ja ta zuwa sashin mahaifiyar sa.

Babansa ma, da ake cewa baba sagir, yana zaune yana cin abinci.

Ummi ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata babu yabo ba fallasa.

Ya ce “Yaya a zubawa ummi abincin salla dan Allah”

Ta ce “Ga maimuna nan, ya zuba mata” ta kalli ummi ta ce “Ke ummi baki da kayan salla ne, ki ka saka wannan koɗaɗɗiyar atamfar?”

Ummi tayi shiru tana kallon ta.

Aka kawo wa ummi abinci, ya saka ta wanke hannunta, ta zauna ta saka tuwon sallar nan a gaba tana ci, tana yi tana kallon yadda yara suka yi kyau sosai a sababbin kaya.

Ta gama ci ta hau tattara musu kwanukan wanke wanke, ta share musu tsakar gida.

Hashim ya dawo sashin, ya tarar da ummi ta haɗa kwanukan wanke-wanke.

“Me kuma zaki yi?”

“Wanke-wanke zan yi”.

“Ke yara na can waje suna tsalle-tsalle, suna wasanni, amma ke kina nan ki na haɗa wanke-wanke, ki je ki yi wasanki sa yi wanke-wanken da kan su”

“A’a bani da kayan salla, idan na fita tsokanata za ayi, su ce mini baƙa” tayi maganar tana ƙoƙarin jan kujera ƴar tsuguno tayi wanke-wanken.

Shiru yayi yana kallonta, cikin tausayawa.

Yana zaune yana kallonta, gata yarinya ƙarama amma ta riga ta saba da wahala, yadda yake wanke manyan kwanukan da aka ɓata da miyar abincin salla.

Wata ragowar miya da ta rage, ta zuba mata ruwa zata zubar, idirisa ya kawo kai ta watsa masa a jikinsa.

Ayshercool

   CUTARWA!

P8

Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ƙaraso kan ummi, yayi ball da ita ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa.

A cikin azama hashim ya ƙarasa, ya hankaɗe idiris, yana faɗin “Idirs meye haka?”

“Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?”

“Kai za a cewa dabba,  ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa yarinyar nan yayi yawa fa”

Ummi kuwa karo tayi da ƙafar tukunyar ƙarfe, fiƙarta ɗaya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo.

Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faɗin “Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?”

Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun  bakinta ya gauraye da jini”.

“Ita kuma wannan meya sameta?”

“Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan” Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris.

Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta ɓata da miya.

Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita.

Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani.

Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai.

*
Mariya na zaune a ɗaki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai maƙwanciyar su suke yi, wadda ƴar ta aka kai gagarawa, suka haɗu da balarabe suka yi aure.

Tana bawa mama labarin ƴar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa.

Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan ƴar jummai a kai a bawa ummi ba.
Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan ƴar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuɗi mijinta ɗan sanda ne, idan suka haɗu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta.

Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa “Ai nan asalamiyya ke bani labari, ƴar da mariya ta baro, wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ƙafarta, na ce ta ɗan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun ɗaukko yarinyar nan”

Mama ta ce “Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ƙi, shiyasa muka ƙyalesu, ba su da mutunci ko kaɗan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ƙyale su idan yarinyar ta girma ta nememu”

Jimmai ta ce “Ashsha! To Allah ya kyauta”.

Mama ta amsa da “Amin”

Mariya ta ajiye ninkin, ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka.

Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga ɗakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce “Mariya na san kin ji abun da jimmai take faɗa, amma haƙuri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini”  shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ƙona zuciya, tana ji a ranta ba zata taɓa yafe wa Iya ba.

An doshi shekaru huɗu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haɗa mata.
Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina ɗorawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa.

Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka ɓalle ƙofar ɗakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karɓe kuɗin, wai da su zata tarawa ummi kayan ɗaki, ɗakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi.

Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ƙasansa kuwa ya huje, malaman su, sun gaji sun ƙyaleta, ƙafarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa in da Iya take, ta ce “Iya laifi na yi ne?”

“Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ƙwace, kuɗina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a ɗakin”

Gaban Ummi ya faɗi, ta girgiza kai ta ce “Wallahi iya ban ɗauka ba, ki sake dubawa”.

“Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? Ƙarya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuɗina kan jikinki ya gaya miki”

Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuɗi jiya, amma ba ta san ma a ina ta ajiye su ba.

“Au saboda kin mayar da ni ƴar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuɗina ba?”

Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba ɗaya kanta ya kulle.

Iya ta saɓa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ƙarasa cikin ɗakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta ajiye kuɗin.

Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce “Ka tambayeta ina ta kai mini kuɗi, ka yi ta dukanta, har sai ta faɗa” kan ummi ta ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa riƙe da manyan reshen bishiyar darbejiya.

Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiɗa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita. Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ƙarfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ƙafa.

“Fito mini da ita daga ɗaki, ɓarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a ɗaki” a ƙasa haka ya din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida.

“Ga ɗakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuɗina”

Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a ɗakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe ɗakin bisa umarnin iya.

Ummi ta kwanta a ƙasa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ƙafarsa, tamkar ba a jikinta yake ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata.

Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin ɗakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuɗi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a ɗaki.

Hashim ya ji kamar ya ɗora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaɗon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri ɗaya, saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare.

“Ummi” ya kira sunanta, ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kai.

“Da gaske kin ɗaukar wa iya kuɗi”

Ta girgiza masa kai, ya ce “Na san ba zaki ɗauka ba ummi, yi haƙuri taso ki fito”

Ta girgiza masa kai ta ce “Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni wurin mama, wallahi zan mutu” tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana iƙirarin ta mutu, “Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun ya cije ki” Da ƙyar ya fito da ita daga ɗakin.

Iya kuwa duk ta gama barbaɗawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuɗi.

Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka.

Tana banɗaki, Hashim ya samu Iya ya ce “Iya dan Allah meyasa ba kya ƙaunar ummi ne?”

“Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ƙaunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi”

“Ba wannan ba, Iya kin duba ɗakin nan da kyau baki ga kuɗin ba? Ummi bata taɓa yi miki sata ba fa?”

“In ji uban wa? Faɗa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon ɓeranya”

Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana ɗingisa ƙafarta.

Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka.

Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi.

Iya ta watso mata ƙullin kayanta, ta ce sai dai ta koma ɗakin itace ta cigaba da zama.

Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba.

Da kansa ya share wa ummi ɗakin, ya samo buhu ya shimfiɗa mata, ya kawo tabarma ya shimfiɗa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata haƙuri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka.

Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ƙasan katifarta ya ɗaukko ɗari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce “Iya ba wannan kuɗin ki ke nema ba?”

A razane ta karɓa tana ƙifta masa ido, gaba ɗaya ta manta ina ta ajiye su.

Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuɗinta, duk wasu kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi haƙuri, saboda ƙarfin hali, har da Murmushin ta, tare da ƙoƙarin nuna bakomai.

Da daddare ya sayo gyaɗa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ƙara rarrashin ta, ya daɗe yana sake kallon ɗakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a ɗakin, kuma ba za a rasa ƙwari masu cizo a ciki ba.

Ya kalli ummi ya ce “In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaɗe ko ina, ki tabattar babu wani abu a ɗakin kan ki kwanta”.

“To yaya na gode” ya jinjina mata kai ya fice.

Iya tana kallonsa daga tagar ɗakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ƙular da ita, dan haka tayi ƙwafa, tare da aniyar ɗaukar mataki a kansa.

Sai dai can ƙasan ranta, ta ji babu daɗi ganin kuɗin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a ɗaki kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har ɗaki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta.

“Kin karya ne zaki tafi makaranta?”

Ummi ta ce “A’a”

“Ki je wurin sa’adatu ta zuba miki kunu idan ta dama” ummi ta ɗan yi shiru ta tuna yadda sa’adatun ke haɗe rai idan ta je karɓar kunun.

Ummi ta ce “Na san idan na je ya ƙare”

Iya ta bankaɗa ɗan tofinta, ta ciro naira ɗari, ta ajiye wa ummi ta ce “Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci”

Ummi ta kalli kuɗin, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma’anarsa, ta miƙe tsaye idonta fal hawaye ta ce “Ki bar shi iya, idan na dawo na ci abincin” tayi waje.

Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye.

“Ƴar ƙanƙanuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki” Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya.

Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ƙarasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuɗin jarrabawar da ƙyar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo ta, take ta yi mata tambayoyi da ƙyar ta gaya mata batun kuɗin jarrabawar.

*
Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaɗa ya raya, amma taƙi tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke.
Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huɗu kenan rabonta da aure.
Kuma shekarun nan huɗu cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba.
Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ƙara tsananta kaɗaice kanta, ga rashin barcci da ya sarƙafe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci.

Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta kasa, ta din ga burgima a ƙasa tana wayyo kanta.

Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan magani, idan ta sha ɗin ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata riƙe kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai.

Ƙarshe aka tura su ganin likitan ƙwaƙwalwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ƴan uwanta, jin an tura su ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa.

Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba ɗaya.

Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta.

Yaya magaji ya ce “Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo”

Maryam ta ce “A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daɗi ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya”

Yaya magaji ya ce “Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai.

“Zata shekara goma zuwa sha ɗaya fa yanzu, ai ta zama budurwa”

Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi.

Ummi ta daina zuwa ɗakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana.
Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta ɗurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai.

Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan.

Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa “Ina wuni?”

Jiki a sanyaye ya amsa ya ce “Ummi kin gane ni?” Ta jinjina masa kai alamar eh.

“To waye ni?”

Maimakon ta bashi amsa sai ta ce “Ina mama?”

“Haryanzu baki manta da ita ba?”

Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce “Da ita ku ka zo?”

“A’a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda”

Kawu Ilyasu ya wani haɗa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce “Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida”

Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba”

“Ba zaki tashi ba?” Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce “Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya”

“Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu’a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka”.

“Wai ba zan sake ganinta ba?”

“Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki”

Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita.

Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida.

Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa “Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!”.

Ayshercool

CUTARWA!

P9

Gaba ɗaya Ummi ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, har suna neman gaza ɗaukarta, tayi ta maza ta ja jikinta ta shiga, kai tsaye ɗakin da take ta wuce, ba ta tsaya a in da Iya ke banbaminta ba.

Wucewar ta bai sanya Iya jan baki tayi shiru ba, sai ma haƙiƙancewa da tayi, tana cigaba da masifa “Ni dai na gaji da wannan maitar da masifar, dole in miƙe in nemi tsari da bala’i da tashin hankalin wannan mutanen su daina yi mini sintiri da bibiyata, ba dole mariya ta haukace ba, hakkin ɗa na ba zai taɓa barinta ba, daga haka ma in Allah ya yarda sai ta fara yawo tsirara, ni bai dame ni ba, hakkina da na ɗa na ba zai bar ta ji daɗin rayuwa ba, hauka ma yanzu ta fara ba ta ga komai ba tukuna”.

Ummi ta ja ta tsaya a cikin ɗakin, tana ƙare masa kallo, kasancewar haddar yaro ƙarami, ba abu ne da yake gogewa cikin sauƙi ba, ya sanya take ummi ta shiga hasaso abubuwa da dama da suka faru a ɗakin nan.

Yanayin jeren ɗakin, ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaɗe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ƙoƙarin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda ɗakin ya zame mata a yanzu baƙi ƙirin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ƙawata shi.

Durƙusawa tayi ta fashe da kuka tana sheshsheƙar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka.

Ummi ba ta samu fitowa daga ɗakin nan ba, sai daf da la’asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita.

Ta yo alwala ta dawo ɗakin tayi azahar da la’sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi.

Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince.

Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya ɗan sirka, kuma su kumbura.

Ta kalli kuɗin da yaya ɗanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar ɗakin, ta ƙanƙame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta.

Ba tsammani ta ga magaji a kanta.

“Ummi” ya kira sunanta a hankali.

Ta ɗaga kai tana kallonsa. “Kukan me ki ke yi?”

“Yaya magaji”

“Na’am ummi”.

“Wai mamana ta haukace?” Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta.

“Subhanallah waye ya gaya miki haka?”

“Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuɗin”

Hashim ya ce “Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ƙwaƙwalwa aka ce”

“Likitan ƙwaƙwalwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ƙwaƙwalwa”

“Ba haka bane ba”

“To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?”.

“Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu’a Allah ya bata lafiya”

“Dan Allah yaya magaji ka kai ni wurinta, ina son in ganta dan Allah” tayi maganar tana haɗe hannayenta alamar magiya, tana kuka.

Cikin matsanancin tausayinta ya ce “Ummi Maiduguri ba nan ba ce akwai nisa, kuma ban san a ina mahaifiyarki take a Maiduguri ba, lokacin da aka aureta muna yara, kuma kin ga ba taɓa zuwa muka yi ba. Amma ki yi haƙuri ki daina kuka, zan bincika miki in sha Allah”

“Gidan uwarka zaka bincika mata, munafukin Allah ta’ala, to kar ka fasa, wallahi magaji idan ba ka kiyaye ni ba, sai na hau kujerar tsiya na ci ubanka la’ada waje a kanta, kar ka fasa kai ta inda uwarta take, zaka ga cin mutuncin da zan yi maka, dai-dai nake da kai.
Kema tsohuwar munafuka, halin uwarki haka halinki yake, duk wannan ƙoƙarin da nake yi a kanki ba kya gani, da ki ke hannunmu mutuwa ki ka yi? Kowa yazo sai ki ɓare baki, ke a kai ki wurinta, tun da namanki nake gutsura in ci, to ki cigaba kar ki fasa, amma ki sani nayi alwashin yadda mariya ta rabani da ɗa na, ke da ita har abada, sai ta ɗanɗani abun da ta ƙunsa mini, wannan kuɗin na meye?” Tayi maganar tana nuna kuɗin da ummi ta watsar a wurin.

Hashim ya ce “Yayan babarta ne ya bata”

“Tattaro mini su ki miƙo mini” ummi ta tarkata kuɗin ta miƙa mata.

Ta karɓe ta kalli Hashim ta ce “Zaka tashi ka fita ko sai na ɓata maka rai, kuma daga yau na yi maka tsakani da ita, tun da kai ne ka ke zigata, shashashai kawai”

Hashim ya tashi zuciyarsa na yi masa zafi, muddin ya buɗe bakinsa, zai iya ɗurawa Iya ashar, dan haka yayi shiru ya bar ɗakin.

“Tashi ki fice ki auni dawa ki surfa mini, tun da baki je makarantar allon ba”

Haka Ummi ta ja jiki ta fito, ta fara ƙoƙarin aikin da Iya ta saka ta, ƙasan zuciyarta tana fatan, ina ma Maiduguri babu nisa da guduwa za ta yi, ta tafi wurin mamanta.

Kayan da yaya ɗanlami ya kawowa Ummi kuwa, Iya ta tsince wanda zata tsince ta ce a fita da sauran, ba ta ƙaunar duk wani abu da ya shafi Mariya.

Duk salla sai ummi ta yi addu’ar Allah ya jiƙan babanta, ya bawa mamanta lafiya, ya sa ta dawo ta ɗauke ta.

Tun wannan tafiya da yaya ɗanlami yayi, wani daga danginsu, bai sake waiwayo in da Ummi take ba, suka mayar da hankalinsu a kan lafiyar ƴar uwar su. Dan abun na mariya gaba ya din ga yi, babu sauƙi ko sassauci, yanzu tana zaune lafiya idan aka jima, sai ta hau kuka tana burgima tare da surutai, irin na masu taɓin hankali.

Ummi kuma ta cigaba da karɓar gashi a gidansu, tsangwama da kyara a cikin yara a makaranta ko kuma a gida.

Iya ta sanya ido sosai a kan magaji, ɗan taimakon da yake yi wa ummi, ta tasaya tsyin daka ta hana shi.

BAYAN SHEKARU BIYU!.

Sauri-sauri ta kammala tulin wanke-wanken da ke tsakar gidan, ta warewa kowane sashi kwanukansu ta kai musu.
Duk in da ta faki ido ta tsaya, sai ta yi soshe-soshe, dan itakaɗai ta san me take ji.

Guntun omon da ya ragu, da shi ta wanke kayan makarantar bokonta, duk hantsar wandon ta fatattake, sun koɗe sun jeme, ƙafar wandon duk ta ɗage ta tattare, gwiwar duk a farfashe.

Kasancewar lokacin rani ne, rijiyoyi duk sun ƙafe, ta ɗau bokiti ta samo ruwan wanka, ta ɗauki ledar omon da babu komai a ciki, ta faɗa banɗaki wanka, da sosonta na buhu.

Ta daɗe a tsaye tana fargabar ta ina zata fara? Tun safe a makarantar boko take jin fitsari, ta riƙe shi bata yi ba, saboda azabar da take sha.

A hankali ta cire kayan jikinta, ta ware gashin kanta, ta nannaɗe shi ta tufke, ta kawo tsumma da take ɗaure kan da shi, ta ɗaure yadda ba zai jiƙe ba.

Ta cire wandon da yake jikinta, subhanallah, wani irin ragargazajjen wando ne, kusan da shi gara babu, duk roba-robar jiki ta zaro, har da in da aka yi ɗinkin zare da allura a jikin phant ɗin, haka ta rataye shi a jikin ƙofar banɗaki, sai tsami yake mara daɗi.

Ta koma gefe ɗaya, ba tare da ta tsuguna ba, ta fara sakin fitsarin da ya cika mata mara fam, a tunanin ta hakan zai sanya ta kaucewa faruwar abun da take gudu.

Sai dai kash! Tamkar ta zuba ruwan barkono a gabanta, wani irin raɗaɗi da azabar zafi, ya ratsata tun daga kanta har ƙafafuwanta, ta toshe bakinta tana jin zafi kamar ana kekketa mata wurin, ga mararta da ta ƙulle kan fitsarin ya fita.

Ta shafe tsawon lokaci, kan ta motsa, saboda tsananin azaba da wahalar da ta shiga.

A hankali ta motasa, ta tsuguna wani irin ƙarni mai haɗe da wari ya daki hancinta, ta ɗebo ruwan nan da sanyinsa da komai, ta zuba a wurin ta fara wankewa, wani irin ruwa mai ƙarni mara daɗi ya din ga fitowa daga jikinta. Zuba ruwan sanyin da tayi, ta ji tamkar ta zuba karara a wurin, wani irin ƙaiƙayi kamar ta kurma ihu, duk yadda ta so ta daure, ta kasa ta din ga sosawa, ƙurajen da suka feso a gabanta suka yi jawur, tun tana jin daɗin susar sai da ta koma jin zafi, dan da gask take yi iya ƙarfin ta, saboda azabar ƙaiƙayi, sai da ta yi wa kanta rauni, har da jini.

Ta yi shiru ta jingina da jikin bangon banɗakin tana tunanin haka kowa yake yi? Ko ita kaɗai ce take fama da wannan masifar da bala’in, to idan ma haka ne wa zata tambaya?

Da ƙyar ta samu ya lafa, ta zuba ruwa a cikin ledar omon nan, ta zuba a jikinta tayi wanka, sai dai a ƙarshe ta rasa yadda za ta yi ta wanke wandonta, dan babu omo, dan haka ta wanke shi a haka, da zallar ruwa, ta yarfe shi ta mayar shi jikinta a jiƙen, ta fito daga wankan tana tafiya a hankali, tana ɗan buɗe ƙafarta, saboda raɗaɗin da wurin yake yi mata.

Man kaɗanyarta da na’ima ta aiko mata, shi ta shafa abun ta, ta sanya uniform ɗin ta, ƙungun wandon saboda rashin roba, da leda take kama wani sashin ta ɗaure, hakazalika takalminta ma, kasancewar ya mutu dan a tsinke yake, ta samu leda shi ma ta yi masa cunan leda, ta ɗaure shi da shi, ta saka.
Haka ta tafi makaranta tana kaffa-kaffa da jikinta, ko yaya ta saki jiki za a iya ganin tsiraicinta, saboda yadda kayanta suka mutu. Ga wannan bala’in da take ciki, na sanyi da yayi mata mugun kamu.

Iya kuwa hankalinsu yana kan bikin Idiris da za ayi, ana ta shirin biki a gidan, shi yaƙi karatun boko yaƙi na islamiyya, ya ce shi aure yake so, Hashim ya kaɗa ya raya, ya ce shi ba zai iya wannan wahalar banzar ba.

Kawu Yahaya ma sai da yayi mitar idiris ɗin nawa yake, da har zai ce zai yi aure me yake da shi? Iya ta goya masa baya, ta ce su haɗu su yi masa aure.

Aka kama masa hayar wani gida mai ɗaki biyu da kitchen da banɗaki, ginin ƙasa ne dai, amma an yi floor, da plastar ƙasa an shafa farar ƙasa.

Wata yarinya ya nema a can gaban unguwarsu, yake ta yi musu sintiri yana son ta, babanta ya ce idan da gaske yake ya fito, shi ne ya zo ya saka Iya a gaba, lallai shi aure yake so, aka je aka nema masa auren ƴar mai suna Hindu.

Kawu yahaya ya ce lokacin auren, yayi dai-dai da lokacin zuwansa umara, ba zai samu zuwa ba sai dai matarsa za ta zo, ya kuma aika musu da gudunmawa mai tsoka.

Albarkacin bikin Idiris, Iya ta sayawa ummi atamfa, da takalmi na kayan fitar biki, ummi duk da ba shiri suke yi da idiris ba, ta ji dadin zai yi aure ya bar gidan ko ta samu ta sarara.

Ana ta shirye shiryen biki, gida ya ɗau harama, ƴan uwa na nesa tuni sun fara zuwa, ummi na ta aiki kamar jaka, ɗan wannan idan yayi kuka a bata rarrashi, ɗan wancan yayi kashi ta wanke, haka dai ba ta da sukuni.

Yau kusan tun bayan azahar, yanayi ya nuna akwai matsala, duba da yadda Iya ke ta shiga tana fita ita da mahaifin su magaji, kasancewar ba abun da ya shafi ummi bane, ya sanya ko a jikinta, ta cigaba da sabgoginta.

Shi kansa yanayin Idirs ya nuna hankalinsa a matuƙar tashe yake, alamu suka tabattar da akwai matsala.

Ba a tsaya da shirye-shiryen biki ba, dan magana ake ta bai fi saura kwana huɗu a shiga hidimar biki ba.

Da yamma hashim ya shigo, ya tarar ummi na cikin mutane ana ta aiki, yayi mata nuni da ta zo.

Ta wanke hannunta ta bi shi, ya kalleta ya ce “Ke ina naki shirin bukin, ki ke ta fama da aiki haka, ko gajiya ba kya yi?”

Murmushi ta yi masa, sai da fararen haƙoranta suka haska fuskarta, fiƙarta da ta karye tana nan a yadda take, sai ƴar siriryar wushiryarta ta ce “To yaya magaji wani shiri zan yi? Ina da atamfata sabuwa da takalmin da zan saka”

“Ke ba zaki yi ɗan lallen da ake yi na zamani ba?”

Ta kalli hannunta, ta ɗan rausayar da kai ta ce “Bana so, ba zai yi mini kyau ba”

Ya kamo hannunta ya ce “Jan nan da ake yi tafin hannunki fari ne masha Allah, ko kitson ma ba ayi miki ba, kin cukurkuɗe gashi kin ɗaure”

Yayi maganar yana kallon yadda ɗankwalin kanta yake cike fam, ko ba a gaya maka ba, ka san wannan uban gashin nata ta ɗaure.

“Ai ka san ni ba a iya yi mini kitso, duk sanda na cewa yayi mini kitso, sai ya ce wai bs zai iya ba kaina ba zai yi ba, lalle kuma ai sai an biya ɗari biyu huwaila take yi hannu da ƙafa” tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa da Iya take cewa sangarta.

Ya ce “To shikenan, da safe zan baki kuɗin lallen, kitson kuma sai na yi miki”

Tayi dariya ta ce “To mata ne kawai suke yi wa mata kitso ban da maza”

Ya ce “Shikenan, je ki sai goben in Allah ya kaimu”

Cikin murna ta tafi ta cigaba da aikin, tana matuƙar son lalle, amma rabon da ayi mata, tun kan na’ima tayi aure, da take yi musu, yanzu yaran na’ima biyu a gidan miji.

Da magariba Saminu baban su Idris ya shigo hankali a tashe ya ja hannun Iya suka fita, wata duhuwa ya ja ta ya ce “Iya muna cikin tashin hankali da masifa, Idris ya zubar mana da mutunci”

Cikin kaɗuwa ta ce “Menene? Meyafaru?”

“Ban da masifa da bala’i, saura ƴan kwanaki a ɗaura maka aure, a ganka kana watsewa da wata, saboda rashin mutunci”

Iya ta ce “To ba mun gama wannan maganar ba? Har wurin maude mai babban carbi na je, ya yi mini aiki ya ce maganar an bar ta har abada, ba zata fasu ba, ko ta fasun ne?”

“To yanzun nan ƙanin baban yarinyar da zai aura ɗin, ya dawo da kuɗin auren, sun ce aje a karɓi kayan auren gobe da safe, ba za su bawa mutumin banza ƴa ba” yayi maganar yana nuna mata kuɗin.

Iya ta dafe ƙirji ta ce “Mun shiga uku, amma mutanen nan basu da mutunci, basu san tsautsayi ba?”

“Koma menene ai shi ya janyo wa kansa, da bai yi ba wa zai ce yayi, ni wannan mutanen da muka tara ne, ban san ya zamu yi da su ba”

Iya ta ce “Ni kuma tashin hankalina, garin Allah ya waye a dawo da kayan nan, kowa ya ji abun da ya faru, da sassafe ka je da kanka ka karɓo kayan, ka kai mini gidan kuluwa”.

“Ni kuma Iya? Ni zan je ɗaukko kayan?”

“To kar ka je tsaya asirinmu ya tonu, sai ka ji daɗi, santolo kawai”.

“To Shikenan zan je in sha Allah “

“Kai ka ga idan da hali, ka tafi yanzu cikin daren nan, ka tafi da babur ba wanda ya ji balle ya gani”

“To bari sahu ya ƙara ɗaukewa, amma Iya yaya zamu yi da wannan mutanen, ta yaya zamu ce musu an fasa auren nan?”

Iya ta ce “Nima shi nake tunani, dama ga akuyarsa tayi kuka a dangi, dan ma ana tsoro na ne, ya sanya ba a magana, amma jeka na san abun yi “

“Meye abun yin to?”

“Ka tafi na ce, idan ka dawo sai ka ji” ya jinjina mata kai ya tafi.

Ɗakin samarin ta shiga, neman Idris, amma ba ta tarar da shi ba, dan haka ta juya ta tafi.

A daren saminu yayi yadda Iya ta ce, ya je ya karɓo kayan a daren.

Sosai Saminu, ya din ga yi wa idiris faɗa, a kan tashin hankalin da ya sanya su a ciki.

Washegari kamar yadda Hashim ya yi wa ummi alƙawari, ya bata kuɗi ta je aka yi mata lalle.

A ƙofar gida ta gan shi ya karɓo kayan guga, tun daga nesa take ɗaga masa hannu ta ce “Yaya ka ga lalle na?”

Yayi murmushi ya ce “Inyee an sha kyau, lalle yayi kyau, ki yi sauri ki shiga gida, Iya ta fara faɗa ana nemanki”

Cikin faɗuwar gaba ummi, ta ce “Bari na yi sauri” ta yi cikin gida da gudu.

Cikin damuwa Saminu ya kalli Iya ya ce “Iya kina ganin babu matsala, ba fa son yarinyar nan yake yi ba, kuma shekarar ta goma sha uku ne kawai”

“To yaya ka ke son mu yi? Asirinmu da nasa ya tonu, idan ba haka ba kawo wata mafitar”

Ya girgiza kai ya ce “Ba ni da wata mafitar”.

“To na yanke hukunci, ya auri ummi dan mutuncinmu ba zai zube ba, a sakamu a bakin duniya da wannan iskancin da yayi ba kamar ɗan taure”

Ayshercool

                      CUTARWA

P10

Saminu ya numfasa ya ce “To shikenan, Allah ya sanya alkhairi”

Iya ta ce “Yauwwa ka turo mini shi, ko kuma ya jira ni a ɗakinsu, zan same shi”

“To shikenan, bari na je na nemo shi”

Hashim kuwa dariya yake yi wa ummi, yana cewa ta tafi a hankali, saboda yadda ta kwasa da gudu cikin tsoro.

Da Iya tayi karo, iya ta kalleta ta ce “Daga ina ki ke?”

A tsorace ta ce “Dan Allah kiyi haƙuri, huwaila ce ba ta yi mini lallen da wuri ba”

“Yenyenyen da an yi magana, dan Allah ki yi haƙuri, ki wuce ki nemi wuri ki zauna kar ki sake fita”. Ummi ta ce “to” dan ba ta yi zaton Iya ba zata yi mata tijara ba.

Iya duk ta bi ƴaƴanta da ta haifa da na riƙonta, ta sanar musu da halin da ake ciki.

Ilyas ya ce “Amma Iya naga yarinya ce ƙarama sosai, girman jiki ne kawai ba zata iya jure ɗawainiyar aure ba”

“Yarinya kuma? Ni ma shekarata sha uku aka yi mini aure, uwarta ba sha huɗu aka auro ta ba? Da ta shiga bulunbuƙui za ta yi, yaran yanzu da sun san komai, to idan ba haka ba ya zamu yi?”

Sagir ya ce “To ai Iya ba a shirya ba, da wani kayan ɗakin za ta tare?”

“Wani shirin za ayi? A sayo mata katifa a gidan dillalai, tsohuwa ba sabuwa ba, mai biyar mai goma ku yi karo-karo, ku  haɗa a saya mata buta, murhu tukunya da ƴar tabarma, ina da tsofaffin labulaye, da abun da ba a rasa ba, a saka mata kowa da haka yake farawa ai, rufin asirin ɗan uwanta ai na ta ne”

Gaba ɗaya suka amince a kan haka, baiwar Allah ummi sam ba ta san wainar da ake toyawa ba, tamkar ba mace mai ƙananan shekaru ba, ita take ta ɗawainiyar aike da girkin abincin gidan bikin, ko nauyin jikinta ba ta ji, saboda tsabar sabo da wahala, ba ta san zama wuri ɗaya bata aikin komai ba.

Idiris kuwa tun da aka gaya masa, hukuncin da Iya ta yanke, wanda da kanta ta gaya masa, ya kada baki ya ce “Allah ya kiyaye, uban ne zan ci da wannan baƙar yarinyar mummuna ragowa, ni wallahi bana son ta”.

Mahaifinsa ya ce “Rufe mini baki, ko na mangare ka, shashasha mara hankali, kai ka isa ka yi jayayya da maganar Iya? Ba kai ka janyo koma menene ba, aure ne babu fashi sai an yi shi wallahi, dan ba zamu ji kunya a idon mutane ba”

Iya cewa take “Bi shi a hankali saminu, na sani ba son ta ka ke yi ba, muni kam akwai shi amma ka yi haƙuri, tun da kai ka janyo komai, mun riga mun tara mutane, idan muka ce an fasa dole za a so jin ba’asin abun da ya faru uban me zamu ce musu? Ko kuma gaya musu abun da ka aikata zamu yi?”.

Cike da iskanci, da rashin ɗa’a ya ke kumbura baki yana masifar, shi fa baya son ummi, hindu yake so.

Iya ta fusata ta ce “Uwar hindu ka ke so ba hindu ba, ɗan iska mara mutunci, ba gata aka yi maka ba? Ka je ka yi abun da ka ke ganin zai fishsheka”

Suka tafi suka bar shi, yana wani irin huci da takaici, yarinyar da aka gama lalubewa, wanda yana da tabbacin ba shikaɗai yake yi mata ba, ga baƙi ga muni, ace ita zai aura dan an raina masa hankali, ga hindunsa ƴar fara mai kyau, ace wai ya auri ummi, za ta ci ubanta kuwa, da ƙafarta zata gudu.

Magaji ne ya shiga ɗakin su da kayansa da ya karɓo daga guga, ya kalli idiris ya cika yayi fam, yake ta tsaki da ƙanan maganganu.

“Gunagunin me ka ke yi haka ne?”

“Ba dole in yi gunaguni ba, saboda an tsane ni, za a cuce ni a kassara rayuwata da ta yaran da zan haifa”

“Wai ka da waye ne? Me kuma aka yi maka?”

“Iya mana” ya faɗa a fusace.

“Too iya kuma? Duk kusancin naku, yau a ganku a rana?”

“Ba wani kusanci, za a zalunce ni, wai dan an fasa aurena da hindu, wai sai an ɗaura mini aure da wannan buranyar yarinyar, mummuna wai ni za a aurawa ummi, wai ba zasu ji kunya ba, wannan jakar yarinya mai kama da mayu, ita fa iyan da kanta take faɗar baƙin halin uwarta, kuma za a liƙa mini”

Sakin kayan hashim yayi, bakinsa na rawa ya ce “Wace ummin?”

Idiris yayi masa mugun kallo ya ce “Wace ummin ban da wannan baƙar yarinya, da goshi kamar tsinin jirgi, mummuna ido kamar na kyanwa wallahi ni an cuce ni, kuma wallahi ko an yi auren sakinta zan yi”

Bai bi ta kan kayan ba, ya fita da sauri, ya nufi sashin mahaifiyar su, wanda nan ma ya ɗau harama da mutane, uwar ɗakin mahaifiyarsu ya shiga, ya tarar da ita tana ƙirga kuɗi.

‘yaya” ya kira sunanta.

Ta kalleshi ta ce “Ya aka yi?”

“Wai da gaske Idris ummi, za a aura masa?”.

Ta ce “Mhmm nima haka na ji”

“Amma yaya meyasa?”

“Kafi kowa sanin ai abun da ya aikata, Iya ce ta kawo wannan shawarar, mu ma rufin asirinmu ne ai”

Kamar Hashim zai yi kuka ya ce “Amma yaya kin san yadda Idris yake da yarinyar nan, gata yarinya ƙarama,a haka zaku bari ayi auren nan?”

“To ni na isa in hana ne? Kai ka san babu mai ja da maganar Iya ai ko?”

Bai sake cewa komai ba ya fita, ya nufi sashin iya, a ƙofar ɗakinta ta hange shi, yana tsaye yana kallonta, fuskarsa babu walwala.

Cikin azama ta fito, dan kar magajin ya faɗi wata maganar banzar, a cikin mutane ya tona musu asiri.

Ta ce “Menene?”

“Iya wai kin ce a aurawa idiris ummi, saboda an fasa auren sa?”

“Eh sai yaya?”

“Amma Iya kin san ba son ummi yake yi ba…

Ta katse shi ta hanyar cewa “To ina ruwanka, ku yaran zamani ku kuka san wata soyyaya, mu duk bamu santa ba, idan ya aureta ko daga baya ya saketa, ba shikenan ba in dai asirin ya rufu, ai ba ana nufin yayi ta zama da ita bane ba din-din”

Galala yake kallon Iya, idan dai-dai ya ji, kamar ta ce ko daga baya ya saketa, wato rufin asirin kawai suke nema, ko da hakan yana nufin tarwatsa rayuwar marainiyar.

“Amma iya”

“Kai rufe mini baki, bana son ƙauli da ba’adin banza, sai in ci maka mutunci yanzun nan, fice ka bani wuri” zuciyarsa na wani irin tafasa ya bar sashin na iya.

Shikenan saboda ummi bata da gata kowa ya goyi bayan Idris, ummi ko ƴar tsintuwa ce, ya ci ta ci albarkacin ita ma ɗan adam ce a kula rayuwarta, balle ita ma cikakkiyar ƴa ce a gidan, yadda idiris yake cika yana batsewa yana masifa, ka sam babu Allah a ransa kuma babu abun da ba zai iya yi ba.

Suka cigaba da shiri, sai washegari da safe, Iya ta kira ummi, da ta sha uban wanke-wanke.
Ta hura wutar kunu, ƙanwar Iya nata yabonta tana cewa taje ta huta.

Iya ta kira Ummi, ta kalleta ta ce “Ki je ki duba a tsummokaranki masu kyau ki wanke su, an fasa auren Idris da ke za a ɗaura, ki wanke kayan da zaki tafi da su, idan ya so daga baya a ɗinka wasu daga kayan auren da aka dawo da su a kai miki, atamfarki da na saya miki ki sakata gobe ɗaurin aure”

Sai da numfashin ummi ya kusa ɗaukewa, na wucin gadi, ta haɗiye wani irin yawu da taji tamkar tana haɗiye wuta ta ce “Iy..Iya aure kuma?”

“Kurma ce ke ba ki ji me na ce ba?”

Karon farko da ummi tayi yinƙurin yin musu da Iya ta ce “Iya makarantar fa? Kuma yaya idiris dukana yake yi, dan Allah kar ayi mini aure da shi, ko da wa aka yi mini auren na yarda amma dan Allah ban da yaya Idris, wallahi dukana zai yi”

“Ke dalla rufawa mutane baki, ba taimakonki ma za ayi ba, da wannan munin uban wa ye zai aureki ya zauna da ke? Ai idiris taimaka miki zai yi, kamata yayi ki yi mana godiya, idan ma bai zauna da ke ba, ai an samu asiri ya rufu, da mu da ku baki ɗaya, ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta,  ki je ki tsami kayanki ki wanke”

Kuka ne ya ƙwacewa ummi, ta juya ta tafi ɗakinta, ta kalli viva da take zuba kaya a ciki, ina wasu kaya ma suka banda tarkacen tsummokara, kuka kawai take tare da tabattarwa da kanta kashinta ya bushe.

Karo na farko da ba ta taɓa neman taimakon kowa, wurin gaya wa wani matsalar ta ko damuwarta ba, amma ta fito cikin tashin hankali, ta tunkari sashin su Hashim tana nemansa, da ta rasa shi a gidan, ta fita waje a can ta samo shi wata majalissa da suke zama, ba kowa a wurin sai shi.

Ya miƙe tsaye ya taro ta, jikinsa ya bashi wataƙila ummi ta samu labari, cikin dakiya ya ce  “Ummi lafiya?”

“Yaya magaji”

“Na’am Ummi”

“Yaya magaji, wai iya ta ce ni yaya Idris zai aura?” ta riƙo hannunsa ta ce “Dan Allah mu je ka bata haƙuri, dukana zai din ga yi, ya ce ya tsane ni a rayuwarsa dan Allah mu je ka bawa iya haƙuri, dan Allah kar a aura mini shi”.

Hawaye take tsiyayarwa daga idonta, kamar an kunna famfo.

“Ummi ki yi haƙuri, ƙaddararki ce a haka, na yi iya yi na, sun ƙi fahimta ta, ki yi haƙuri”

Ummi ta ɗora hannu a ka ta ce “Shikenan na shiga uku, wallahi kasheni zai yi da duka, Innalillahi wa Innalillahi raji’un, na shiga uku” tayi maganar jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da kiɗimewa.

“Ki yi haƙuri ummi, ki cigaba da addu’a, babu abun da ya gagari Allah, idiris bai isa yayi miki abun da Allah bai yi miki ba”

Kasa magana tayi, sai kuka tana jin yadda fargaba da tsoron idiris ke ƙara shigar ta.

Muryar Hashim ta ji ya na cewa “Ki tafi gida, kar ki su yi ta nemanki, ki ja wa kan ki matsala”

Ummi ta jinjina kai, ta tafi hannunta a tana zubar da hawaye, gaba ta yi ta bar cikin gari, ta samu wani wuri tayi zamanta, ta din ga kuka, idanuwanta suka haye suka kumbura sosai da sosai.

Har azahar ta yi bata da niyyar tashi, sai da rana ta take sosai da sosai, sannan ta tashi ta tafi gida, daga nesa take hangen gidan, gabanta ya sake faɗuwa, tayi kwana ta tafi gidansu na’ima.

Maman na’ima ta tarar a tsakar gida tana girki, ta na yi mata magana, amma ba ta iya tankawa ba, kawai ta shige cikin ɗaki ta kwanta.

“Ummi ko ba lafiya ne?”

Ummi ta girgiza mata kai, kanta na yi mata wani irin ciwo, ta hau bacci.

Ƴan biki suka din ga tambayar Iya, ba za aje gidan su amarya kamu da suaran al’adu ba?
Iya ta ce musu ba sai an je ba, gidan su amaryar malamai ne, ba sa gabatar da al’adun aure, sai ɗaurin aure da tariya kawai.

Iya bata farga Ummi ba ta nan ba sai la’asar, hankalinta ya tashi aka shiga nemanta, nan da nan Iya ta kawowa ranta ko guduwa ummi ta yi, to ta gudu ta je ina?
Aka din ga nemanta, har tasha aka je, amma aka ce ba a ga ummi ba.

Hashim hankalinsa ya tashi sosai da sosai, saboda shi ya yi wa ummi ganin ƙarshe, dan sai da iya ta rutsa shi tana tuhumarsa a kan ko shi ne yayi wani abu, ya ɓoye ummi ko makamancin haka.

Ummi kuwa bayan ta tashi, tayi salla, maman na’ima ta bata abinci, ta ci kaɗan kanta na cigaba da sara mata.

Sai dai ƙememe ta ƙi yi wa maman su na’ima magana, balle ta gaya mata abun da yake faruwa.

Har aka yi sallar magariba tana gidan, tayi sallar magariba, sannan ta cewa maman ta tafi.

Ko da ta shiga gida, da yawan an watse, an tafi yawon nemanta, dan haka kai tsaye ta tafi ɗakinta, duk an baje itace a ɗakin, ta tutture su ta kwanta a kan buhunta.

Iya ta dawo afujajan, saboda tashin hankali, ta din ga tsinewa ummi, da mariya tare da aibata mariya da cewa duk baƙin halinta ne yake gudanawa a jinin Ummi.

Ummi na jiyo ta, tana jin wani abu mai ɗaci ya tsaya mata a ƙirjinta, da ta kasa haɗiyewa, ta sake ƙudindinewa tana kuka, tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.

“Laaa, ummi, nan ki ka zo ki ka kwanta ana ta neman ki?” Matar tayi maganar tana haske ummi da fitila.

Iya ta ce “Wace ummin? A ina?”

“Gata a nan a kwance”

Iya ta ƙarasa ta leƙa, ta ga ummi ta dunƙule wuri guda.

“Shegiya matsiyaciyar yarinya, ina ki ka tafi ki ka tayar mini da hankali?”

Ummi ta tashi zaune, amma ta kasa magana, ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“Ba magana nake yi miki ba, sai na zo na hau ruwan cikinki? Wurin wani ɗan iskan ki ka je? Wurin maza ki ka tafi ko?”

Ummi ta yi shiru tana tunanin ta je wurin maza tayi me?.

“Dan ubanki tun safe, da yake ba mutunci ne da ke ba, ki ka saka ƙafa ki ka fice, ba zaki gaya mini in da ki ka tafi ba, tsinanniya ƴar matsiyata” salati wasu suka din ga yi,  suna hana Iya tsinewa Ummi.

“Ku rabu da ni, ba ku san mugun halin yarinyar nan ba, riƙonta kawai nake yi, baƙin cikinta ya kusa kasheni, ku kalli ina yi mata magana ta yi mini banza, balle in san in da ta tafi, kuna ji ina tambayarta tayi shiru”.

Hawaye wani na bin wani a fuskar ummi, amma ta kasa magana, kawai iya ta rarumi itace, ta sauke mata shi a kafaɗarta, gantsarewa tayi saboda zafi da ciwo, amma ta kasa guduwa, aikuwa ta cigaba da kwaɗa mata duk in da ta samu, da ƙyar ƴan biki aka hanata.

Wata ƴar yayar Iya ta ce “Haba Iya, yanzu wannan ƴar yarinyar da baki ki goya ba a bayanki, ki ke rafkawa wannan itacen, wannan ai mugunta ce. Ni tun da na zo gidan nan, wallahi ban ga yarinyar nan tayi wani abun ashsha ba”.

“Bar ni marka da hatsabibiyar yarinyar nan, baƙin cikin uwarta bai kasheni ba, na ta zai kasheni, ni na fara tunanin ko dai ba jinina ba ce, dan kaf zuriyarmu babu wannan munin kamar baƙar buranya”.

Aka yi ta bawa Iya haƙuri, ummi kuwa tayi mursisi ta kwanta, ta cigaba da kuka, tana jin kamar bayanta ya karye.

Ƙaiƙayin nan ne ya cigaba ta taso mata, duk yadda ta so ta daure, kasawa tayi, ta din ga soshe-soshe, kamar za ta zaee.

Da aka yi sallar magariba, ta tafi banɗaki tayi fitsari, ba tare da wurin ya tsane ba, ta tashi ta fito da jiƙaƙƙen wando, aikuwa ƙaiƙayi ya sake tasowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin wurin da duhu, ya sanya ta kai hannu ta fara sosawa, wanda har ta shagala saboda azabar zafi da ƙaiƙayi.

“Ai dama na faɗa, na faɗa wurin maza ki ke zuwa ko ummi, wurin maza ki ka je tun safe ba kya nan” zabura ummi tayi, ta girgiza mata kai, saboda yadda Iya ta haske ta da fitila.

“Uban me ya kai hannunki gabanki, ki na  soshe-soshe a duhuwa? Na faɗa wurin maza ki ke zuwa, kina sakarci, an ƙi yadda, na ce ayi miki aure, sun ce kin yi ƙanƙanta, yanzu meye Wannan?” rasa amsar da zata bata tayi, Iya ta din ga yi mata kwarmato, a cikin mutane da duk wasu kalaman cin mutunci da muzantawa, kunya baƙin ciki duk suka cika zuciyar ummi.

Saboda azaba a zaune ta yi salla, da ta motsa sai ta ji kamar ana yayyanka naman gabanta da reza, saboda wurin duk ya kwailaye.

Ummi haka tayi kwanan baƙin ciki, ta rasa yadda za ta yi, saboda abubuwa kashi-kashi, da wasu ma ko sanin kan su ma ba ta yi ba, da yawa wasu daga maganganun Iyan ba ta san in da suka dosa ba, amma abun da ta fahimta kawai shi ne, ta san cin mutunci ne maganganun Iyan, uwa uba kamata da ta yi tana susa take yi mata kwarmato, da cewa tana zuwa wurin maza, to ta je ta yi me?.

Hashim kasa bacci yayi, tsananin tausayin ummi na cin zuciyarsa, mussaman yadda ya ji Idiris ya na alwashin cin mutuncin ummi, da kuma azabtar da ita, da duk iya ƙarfin sa.

Duk yadda ya so yi wa idiris nasiha, yayi mursisi yaƙi ganewa, ya din ga kumfar baki tare da muzantar halittar ummi.

Bayan sallar asuba, Ummi ba ta fito ba, sai da Iya ta zo ta sakata a gaba, aka ce tayi wanka, da yawa sai a lokacin suka san cewa wai Ummi ce amarya.

Da yawa akwai magana a bakin mutane, sai da ana jin tsoron Iya, babu wanda zai iya tofawa.

Sai a lokacin Iya ta bata sabon kaya ta saka, ta nemi wuri ta zauna kamar gunki, kan nan a ƙasa tana aikin kuka.

Ƴan uwan Iya suka din ga tambayar, ina dangin mariya, duk ba su zo ba?Iya ta ce “Ai auren ne ba shiri, wancan Yarinyar iyayenta sun raina ƙoƙarin idris, shiyasa aka fasa auren na ce ya auri ummi, ƙara zumunci, dan haka daga baya zasu zo”.

Ƙanwar babar idiris ta ce “Amma idiris yayi jihadi, na ji kin ce yarinyar ba ta ji, kina iƙirarin tana zuwa wurin maza”.

Kowa ya din ga faɗar albarkacin bakinsa, a kan auren, wasu suka din ga cewa idiris ya samu yarinya ƙarama mai nutsuwa da ƙoƙarin aiki, wasu kuma sun hau maganar Iya sun zauna, suna yi wa ummi hukunci da shi.

Da azahar aka ɗaurawa ummi aure da Idris, a kan sadaki naira dubu takwas, mutane aka din ga yi wa ummi nasiha, ana ta cewa ta yi haƙuri, aure ɗan haƙuri ne.
Abun da ummi ta kawo a ranta shi ne, ashe sun san halinsa dukanta zai din ga yi, amma aka aura mata shi.

Cikin matsanancin tashin hankali, babar na’ima ta shigo gidan, dan tabattar idan da gaske ummi aka yi wa aure, aikuwa ta samu dahir, an riga an ɗaura aure ma.

Galibi maƙwabtan su, sun girgiza da jin wai ummi aka yi wa aure, ummin da guda nawa take, da kuma mutum kamar idris, da ba wanda bai san shi a fagen iya rashin mutunci ba.

Tsohuwar katifar ce dai da tabarma, katifar tsirarta, babu ko zani, gefenta duk ɓera yayi kalaci da ita, domin kuwa tsohuwar katifa ce, a gidan dillalai aka sayo ta, aka sakawa ummi a ɗaki, sai tsofaffin labulaye na Iya, labulayen nan sun sha jiki, dan ita ma kwancensu aka bata, daga baya ta samu wasu ta cire su, kitchen daga tukunya babba da ƙarama, sai ƴan tasoshi, da kofunan silba kamar bazawarar ƙauye.

Bayan sallar magariba, aka bata wasu kayan, ta saka, aka tafi kai ta. Da ƙafafuwan ta, har gidan Idris!.

CUTARWA!

P11

Haka a ka kai ummi, mata suka gama surutansu, wasu daga cikin maƙwabta da suka san irin rayuwar da ummi take yi, suka din ga tsinewa iya, mussaman ganin ɗakin da aka kai budurwa, da tsohuwar katifa, ko zanin gado babu.

Aka din ga ƙananun maganganu, sai dai babu wanda ya isa ya iya tunkarar iyan, ya gaya mata hakan, saboda iya bala’inta da tashin hankali, haka kowa yayi maganganun sa ƙasa-ƙasa.

A hankali kowa ya watse aka bar ummi, ƴan matasan yaran da aka bar ta da su, suka gaji da zama, ango bai shigo ba, suka watse suka bar ummi ko fitila babu.

Wani irin tsoro ya mamaye ta, da ta ji motsi kaɗan sai ta razana, shiru-shiru babu idiris babu dalilinsa.

Ji ta din ga yi a ranta, kamar ta tashi ta koma gida, dan wani irin tsoro take ji, kamar ace kyat ta zura da gudu, saboda duhun da ya mamaye ilahirin gidan.

Dare ya cigaba da yi, duhu ya sake mamaye ko ina da ko ina, ta yadda ko tafin hannunta ba ta iya gani, tun tana jin motsin mutane sama-sama, har gari ya koma yayi tsit, sai kukan ƙanan ƙwari. Cigaba da kuka ta yi cikin firgici, ta tashi a hankali ta leƙa tsakar gida, ta hango ƙofar gidan a buɗe, tsakar gidan kuma sai ta yi ta ganin abubuwa na yi mata gizo, saboda a tsorace take, kuma ga duhu.

Da sauri ta koma can ƙuryar ɗakin ta takure, bacci take ji sosai da sosai ga gajiyar aiki, ga ta biki, ga tashin hankali ga kuma dukan da ta ci jiya da daddare a wurin Iya.

Babu tsammani ta ji rugugin hadari, da walƙiyya ko ta ko ina, fashewa tayi da kuka, tana son tashi ta fita da gudu ta koma gida, amma tsoro ya hanata.
Tana nan zaune ruwa ya kece ya din ga zuba kamar da bakin ƙwarya, ta tashi da nufin ta rufe ƙofar ɗakin, amma ƙarfin zubar ruwan, da kuma tsawar da ake yi, ya sanya ta koma ta zauna tana cigaba da kuka.

Ruwa ya din ga feshi cikin ɗakin, wani irin sanyi ya mamaye garin.

Ruwa ya shigo ɗakin sosai ya jiƙe, sai dai bai kai kan katifarta ba.

Kasancewar bacci ɓarawo ne, ya kwashe ummi a nan zaune ba tare da ta shirya hakan ba.
sai da gari ya waye ya fara haske, sannan ta tashi a razane.

Ruwan da aka yi duk ƙasa ta shanye, ta zama taɓo, wani kofi ta gani a tsakar gida, ya cika da ruwan da aka yi, tayi alwala da shi, ta koma ɗakin tayi sallar asuba.

Tana nan zaune cikin zullumi da fargaba, aka yi sallama, wasu daga cikin ƴan biki ne suka zo, hakan ya sanya ta ji daɗi.

Suka din ga rafsa guɗa, ummi dai da ido kawai take bin su.

Suka kawo mata abun karyawa, ake tambayarta ina angon? Tayi shiru ba ta ce komai ba, dan kuwa ba ta san me za ta ce ɗin ba.

Suka ƙara yi mata ƴan gyare-gyaren da zasu yi mata, suna ta hira suna yi mata nasiha, da azahar suka ce za su tafi.

Ummi ta ɗau hijjabinta ta ce za ta bi su.

“Ki bi mu ina? Ai ko ƙofar gida ki ka fita babu iznin mijinki, Allah zai ƙona ki a wuta, ki koma ki zauna, shima yana ango amma safiyar fari ya fice, har azahar bai dawo ba?” Cewar wata dattijuwa.

Ƙanwar Iya ta ce “Bar mara mutunci, ai da alama ba son auren nan yake yi ba, haɗin Iya ne kawai, kodayeke ai ma ya furta, tun da hama ta yi masa Allah ya sanya alkhairi, ya ce ba amin ba, ba ya so”

“Too ikon Allah, ai dama idiris ba mutunci ya cika ba, har ta bani tausayi, sannu kin ji ummi, Allah ya baku zaman lafiya ya baki juriya” suka gama salallaminsu suka tafi.

Ta dawo tsakar gida, ta haɗa takalmanta ta zauna, ta zubawa hanyar ƙofar gida ido, in da Allah ya taimaketa, baƙin da suka zo, sun saka yara su je gida, sun ɗaukko bokiti, an cika mata shi da ruwa, da haka ta samu na alwala.

Da la’asar aka turo ƙanin idris ya kawo wa ummi, abinci ta karɓa ta ce masa dan Allah ya tayata zama kar ya tafi, tsoro take ji.

Cikin ikon Allah bai tafin ba, ya tayata zama, har suka ci abinci tare, sai magariba ya tafi ya bar ta ita ɗaya ƙwal kamar mayya.

Hashim ya rasa in da zai sanya ransa, damuwa ta din ga sassaƙar zuciyarsa, gashi tun da aka ɗaura aure, bai saka idiris a idonsa ba, yana son zuwa gidan ummi, amma yana tsoron yaje ya tarar da abun da ba shikenan ba, da zai ɗaga masa hankali.

Baban su Idris ya samu Iya yake tambayarta, ya za ayi da dangin mahaifiyar Ummi, yakamata a sanar musu.

Iya ta ce “Rabu da su, gayyar tsiya ko an gaya musu uwar mai za su tsinana, talakawan banza, ba su ajiye komai ba sai buzu da tawwada sai allo, ai a haka aka tsaface mini ɗa, aka shanye shi ba ya moruwa sai abun da take so, yanzu idan suka sani tsaf za su yi wata ƙulla-ƙullar, a bari sai komai ya lafa, an kwana biyu sai a aika musu da goro da alewa ace na aurar da jikata, shikenan”

Saminu ya ce “Amma Iya za su ga kamar ba a kyauta musu ba fa”

“Ita abubuwan da tayi mini kyautawar ta yi? Can su ƙarata yarinya ce dai na aurar da ita”

Saminu ya jinjina kai, amma dai ya san abun da aka yi ba a kyauta ba, ko ba komai suna da hakki a kan ummi, tun da ƴar su ce ta haifeta.

Ummi haka ta sake kwana a gidan nan, ita kaɗai babu idris babu alamarsa, haka ta sake yin kwanan tsoro da tashin hankali.

Sai dai wayewar garin Allah, babu wanda ya tuna da ita balle ya aiko mata da abinci.

Babar idiris ta fara ƙorafin, tun da aka kai ummi, Idiris bai zo ya ko gaishe su ba, har maganar ta je kunnen iya, ita ma tayi maganar a ranta, amma kasancewar sai a ranar baƙi suka gama watsewa, abun ya dawo kanta.

Rai a ɓace ta aika Alhassan, ta ce ya je gidan ummi, ya ce Idris ya zo tana nemansa.

A hanyar ƙofar fita, ya tarar da ita a zaune, tana kallon masu wucewa.

“Ke ummi, kina amarya kina zama a hanyar ƙofar gida kina leƙe?”

Duk da ba shiri suke yi ba, ummi ta ce “Tsoro nake ji, nikaɗai ce a gidan”

Ya ce “Taɓ, ina yaya idiris, Iya ta ce yaje tana nemansa”

Ummi ta ce “To ai bai taɓa zuwa gidan nan ba, ni tun da aka kawo ni ban ganshi ba”

Ya waro ido ya ce “Ke da gaske!? Ke kaɗai ki ke kwana a gidan nan?”

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya ce “Sannu da ƙoƙari, kuma ki ka zauna? Kodayeke idan ma ki ka ƙi zama kin san sauran, bari na je na gaya wa Iyan”

Hankalin iya ba ƙaramin tashi yayi ba, da jin cewar wai tun da aka kai ummi bai taɓa kwana a gida ba.

Ta ɗau mayafi ta tafi gidan ummi, a nan tsakar gida suka tarar da ita a zaune.

“Ke ummi, ashe tun da aka kawo ki, Idiris bai kwana a gidan nan ba?”

Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh.

“Kuma dan ubanki ki ka ja baki ki ka yi shiru baki faɗa ba? Har sai da na aiko, ke da na nemeki na rasa haka na yi miki, ba yawon nemanki na tafi ba? Wato baki damu da shi ba ko?” Ummi dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Iya ta yi ta mata masifa, sannan ta fita, daga gidan, ta saka aka tafi kasuwa aka kirawo babansa, da sagir aka ce musu, ba a ga idiris ba.

Iya ba ta damu da tsawon kwanakin nan, ya ummi take ba, ta ci abinci ko ba ta ci ba, bata bi ta kan hakan ba.

Aka din ga yawon nemansa, wurin abokansa da sauransu, da ƙyar aka gano shi, can wurin wani abokinsa ya koma, a can yake kwana.

Iya ta same shi ta din ga zaginsa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, mahaifinsu ma kamar zai kai masa duka, saboda takaici da ɓacin rai.

Hashim kallon su Iya yake yi, yana tausaya musu ranar da hakkin ummi zai kama su baki ɗayan su, babban abun da yake ƙara bashi mamaki, irin yadda ba wanda yake iya yi wa musu a kan duk wani son zuciyarta.

Ummi ba ta san me yake faruwa ba, sai ma tunanin Allah ya sa Idris yana lafiya, tun da an ce tun ranar ɗaurin aure ba a sake ganinsa ba.

Da ƙyar tayi sallar la’asar, saboda yunwar da take ji, cikinta sai ƙugi yake yi, har wani jiri take ji idan ta tashi, ban da ruwa ba abun da ta sha, tana son fita nemawa kanta mafita, amma an ce idan ta fita ba da izinin Idris ba, Allah zai ƙonata, gashi kuma tana son komawa makaranta, amma ba ta ganshi ba balle ta tambaye shi.

Sallamar yaro ta ji, tayi sauri ta fito daga ɗakin, wani yaro ta gani da kwano, ya ce mata “Gashi in ji mamanmu” saboda ƙuruciya da yarinta, ummi ba ta tambayi daga ina ba, ta karɓa ta ce ta gode.

Dafaffen rogo ne, da ƙuli-ƙuli, ko wanke hannu ba ta yi ba, ta hau rogon nan da ci, saboda yunwar da take ji.

Ta gode wa Allah bayan ta kammala, duk da ba ƙoshi tayi ba, saboda ɗan kaɗan ne aka zubo shi a kwano.

Ta fito da kwanon tsakar gida, ta saka ruwa tana girgijewa, dan ba ta da ko omo.

Kamar wanda aka cillo, ta ga idiris ya shigo, babu ko sallama, hannunsa riƙe da jakar kayansa, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, saboda faɗuwar gaba da tsorata.

Babansa da yake bayan sa yayi sallama, ummi ta amsa ta tsuguna ƙasa ta ce “Baba ina wuni?”

“Lafiya ƙalau, ya gidan?”

Kai a ƙasa ta amsa masa da “Lafiya lau”.

“Gashi nan, duk ranar da bai kwana a gidan nan ba, da safe ki je gida ki sanar da ni, zaka ga yadda zan yi da kai, mutumin banza wanda bai san abun da yake yi masa ciwo ba, an lallaɓa abun nan a rufawa juna asiri, ka daina ɗaukko mana magana, amma kana ƙoƙarin tona mana asiri” mahaifinsa yayi masa kaca-kaca, sannan ya tafi.

Ummi ji ta yi kamar tabi bayan sa, dan ta wani fannin zamanta ita kaɗai babu Idris shi ne rufin asirin ta.

Ta ajiye kwanon da take ɗaurayewa, ta nemi wuri can a tsakar gida ta zauna, tana ta addu’a a zuciyarta.

Idris kuwa ya cika yayi fam! Kamar ya fashe saboda tsabar baƙin ciki da takaici, fuskar ummi kawai idan ya kalla, ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu, me zai yi da wata ummi, mummuna kamar ba bil’adama ba, aba kamar bayan garwa.

Tsaki yayi ya fito zai sake fita, aikuwa ta sake razana, kai tsaye inda take ya nufa, ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye, ya sanya ƙafarsa ya tankaɗata ta faɗi ƙasa.

“Shine ki ke je ki ka gaya musu bana kwana a gidan nan ko? Idan na kwana a gidan uwar me zan yi miki?”

Da sauri ta girgiza kai ta ce “A..aA’a iya ce ya aiko nemanka, wallahi ba faɗa na yi ba” tayi maganar cikin rawar murya.

“Rufe mini baki”  yayi maganar yana dukanta a ka da hannunsa.

Ta saka hannu bibbiyu ta dafe kanta, saboda jin zafin dukan da tayi, dan ma Allah ya taimaketa, tudun gashinta bai bari ta ji zafin sosai ba.

“Idan ki ka kuskura ko da wasa, ki kai ƙarata, sai na yanka ki, kuma azabar da zan gana miki, sai kin gudu da ƙafarki, ke baki san yadda na tsaneki ba ko? Zaki gani yanzu ai, banza mai kama da dabbobi”

Kame jikinta take sake yi, saboda gudun kar ya kuma dukanta, aikuwa sai da ya sake takata da ƙafarsa, sannan ya fita.

Sai da ta tabattar ya fita, sannan ta iya ɗagowa a hankali, ta bi hanyar da ya fita da kallo.

Ta kalli jikinta, da ya ɓata mata da ƙasar takalminsa, tun da tazo gidan sau ɗaya tayi wanka, shi ma ba soso babu sabulu. Kayan jikinta tun wanda ta zo da su ranar da aka kawota, Iya ta ce za a aiko mata da kaya, amma shiru.

A hankali ta saka hannu ta karkaɗe ƙasar, tana takaicin yadda ya ƙasƙantar da ita ta hanyar takata da takalminsa mai datti da taɓo.

Tayi shiru tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, ta haɗe gwiwoyinta, ta kifa kanta, ta nemi hawayen ma ta rasa, sai zafi da ƙunar zuciya.

Yaya Hashim bai zo ya ganta ba, maman na’ima ba ta zo ba, tayi ta lissafin mutanen da take sanya ran su zo su ganta, amma basu zo ba.

*
A ɓangaren mariya kuwa, tuburan depression ya zame mata hauka, ga ta dai a nutse, sai dai babu cikekken hankali, wasu lokutan sai hankalin ya dawo, ta yi ta harkokinta, amma da abun ya juyo, sai daina cin abinci, ta daina magana. Duk wanda ya shigo da ƙaramin ɗa gidan, sai ta ce sai an bata umminta, ko ta ɗauki fulo tana yi masa wasa, ta ce ummi ce.
Idan ƴan yara mata suka shigo gidan, suma sai tayi ta kiransu da sunan ummi. Ta ce “Yaya ɗanlami, kalli yadda ummina tayi wayo ta girma”.

Ya amsa mata da “Tubarkallah, ki yi ta yi mata addu’a, Allah ya ƙara rayata”

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Ba ummi ba ce, ummina baƙa ce mai kyau, bari in tashi in zuba ruwa in yi mata wanka, na goyata garin nan da sanyi”

Yayi saurin tashi, ganin da gaske tana ƙoƙarin kama ƴar mutane ta yi mata wanka, ya ce “Ki yi haƙuri in anjima sai ki yi mata wankan”.

“To ai bana son babanta ya dawo ya tarar da mu, ba mu yi wanka mun yi kwalliya ba, kaga yana son turare da lallen da nake yi masa, baban ummina har kayan kasuwa yake sayo mana” haka tayi ta gwamutsa masa zantuka.

Yayi shiru yana kallonta, ba zai manta zuwan ƙarshe da yayi gidan Iya ba, da yaje da maganar neman alfarmar ɗaukar ummi, ko na ƴan kwanaki ne, dan hankalin mariya ya kwanta, ta fara samun matsala a ƙwaƙwalwa, amma ta kada baki ta ce Allah ya ƙara, hauka yanzu ta fara da yardar Allah sai ta din ga bi bola-bola hakkin ran ɗan ta ne.

Tun daga nan yayi alwashin ummi ko ƴar gwal ce ba zai kuma zuwa da niyyar a bashi ba.

Mama ta fito ta taya shi lallaɓa mariya, suka mayar da ita ɗaki, sai surutai take, tana basu labarin baban ummi da kuma ummi, sai dai ko da wasa ba ta zancen Iya, ko sauran mutanen gidan sai ummi da babanta.

Ummi ta sakankance idiris ba zai kwana a gidan ba, dan haka har ta hau kan tsurar katifar ta kwanta, sai dai ta kasa rufe idonta tayi bacci, saboda tana jin tsoro, ga gari hadari na ta haɗuwa, sai addu’a take Allah ya sa kar ayi ruwan sama.

Sai da hadarin ya haɗo gaba ɗaya tare da iska, kawai ta ga hasken tochlight a tsakar gida, inuwar Idris ta hango, ya tunkaro ɗakin. Ta runtse idanunta, tana fatan Allah yasa ba shi bane ba, sai dai ta ji ya mayar da ƙofa ya rufe, hakan ya tsananta bugun zuciyarta.

Ba ta san me yake yi ba, saboda ta rufe idonta, ƙafafuwanta ya taka ya ce “Ke dalla tashi” yayi maganar a matuƙar kausashe cikin rawar jiki ta motsa, ta tashi zaune, me zata gani Idris a tsaye a kanta tsirara kamar mahaukaci.

Ihu ta saki, ta runtse idanunta ta dafe kanta da hannayen ta.

“Dalla malama rufe mini baki, ki tashi na ce, uban meye baki sani ba? Munafukar banza da ta wofi, maƙaryaciya an cuceni an haɗani da saura, har da zuwa ki gaya musu bana kwana a gida, ai na san kin san komai kin saba”.

Kyarma ta fara yi, taƙi motsawa, aka kece da wani irin ruwan sama mai ƙarfin gaske, ba ka jin komai, sai sautin zubarsa da ƙarfin gaske a kan kwano.

Ganin za ta ɓata masa lokaci, ya sanya ya jefar da fitilar hannunsa yayi kanta, kamar zararre.

Ayshercool

CUTARWA!

P12

Kamar mai shirin tarayya da dabba, haka yayi kan ummi, ya fara yage suturar jikinta, yana ja tana ja, tana ihu tana bashi haƙuri.

“Ba zaki rufe mini baki ba?” Yayi maganar cikin fusata.

Warin bakinsa ya daki hancin ummi, kai ka ce an buɗe masai.

Sai dai ba ta gama shaƙe warin bakinsa ba, warin gashin kanta ya daki hancinsa, gashi ne fal Allah ya bata shi, sai dai kasancewar babu gyara babu tsafta, ya sanya yake wani irin tsami mara daɗin shaƙa.

Sai da ya ware gashin ya sauka bayanta, warin ya ƙaru har wani gafi gashi gashin yake yi, saboda tururin warin dauɗa da ƙazanta.

Ƙyale gashin yayi, ya cigaba da ƙoƙarin rabata da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauɗa yake yi, da tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula.

Har ɗauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris ɗin ya hanata sukuni, yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ƙoƙarin kare kanta.

Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ƙarfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar ba, amma sai da ta gigice.

Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataɓus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ƙarni mai haɗe da zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi.

Duk yadda ya so ɗauke numfashin sa ya kasa, wani irin baƙin ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya ɗaukko fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi.

Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ƙafarsa, sannan ya janyota ya hankaɗata waje ana wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ƙarfinta, tana danna ƙofar ɗakin, amma ya saka sakata ta ciki.

Tsakar gidan ya shaƙe da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar.

Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaɗota waje cikin ruwan sama.

Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi ɗaya ɗakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan zai ɗauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ƙafafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ƙarasa zuba a kanta.
Ta din ga buga ƙofar ɗakin a hankali ta na cewa “Dan Allah yaya idiris ka buɗe mini na ɗauki kayana, sanyi nake ji dan Allah” tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin karkarwa saboda sanyi.
Ruwan, bai gama ɗaukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ƙanƙame jikinta saboda ƙyanƙyamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan.

Ɗaya ɗakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ƙofa, a buɗe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri ɗaya ta raɓe tana cigaba da kuka.

Har garin Allah ya waye ummi na tsaye, babu wurin da zata raɓa ta zauna, saboda an yi ruwa ba ɗan kaɗan ba.
Gari ya fara haske tana sanya ran ya buɗe ƙofa ta suturta jikinta, amma bai buɗe ba, ta din ga fargabar kar a zo gidan a tarar da ita jikinta babu sutura.

Sai da gari yayi haske tar, sannan ya zare sakata ya fito ya shiga banɗaki, tana hangen sa ta taga, ganin ya shiga banɗaki, ya sanya ta fita ta shiga ɗakin, ta kwashi kayanta da duk ya yayyaga, ta saka, jikinta sai wata irin tsuma yake yi, saboda sanyi, ga ciwo da jikinta yake yi mata da ƙafafuwan ta.

A gurguje ta yi alwala, ta koma ɗakin yin sallar asuba, duk a ɗarare take cikin tsoro take yin ta.

Aikuwa a raka’a ta biyu ya dawo ɗakin, bai damu da salla take yi ba, ya hankaɗeta, saboda wata irin tsanarta da yake ji a cikin zuciyarsa.

Ta miƙe ta cigaba da sallar, ya tsaya a kanta yana kallon ta yana huci, da ta idar da sallar, ta miƙe zata bar masa ɗakin, amma ya janyota ta baya, ya sake hankaɗata ƙasa.

Wata irin ashar da yayi mata sai da ta kalleshi a firgice, ya din ga ɗura mata ashar yana cin mutuncin ta da na iyayenta, har da mahaifinta da ba ya raye a duniyar, har da kiranta da ƴar iska lalatacciya.

Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta nemi hawayen ma gaba ɗaya ta rasa.

Har zai fita ya dawo, ya din ga dukanta hannu da ƙafa, cike da tsana da jin haushin ta.

Ya gama rashin mutuncinsa ya fita, ta tashi a hankali, ta koma gefe tayi zuru da ido.

Sai a lokacin kuma ta samu damar yin kuka, jikinta sai ciwo yake yi, ga yunwa tana ji, gashi haryanzu sanyi take ji, ta kwanta a wurin, ta hau bacci.

Sallamar da Iya take kwaɗawa a tsakar gida ne, ya sanya ummi farkawa, ta fito da sauri, ta ga Iya tare da yaya, mahaifiyar su Idris.

Murmushi ummi ta yi ta ce “Iya sannu da zuwa, yaya ina kwana”

“Ai kya bari mu shigo mu zauna ko”

Ta basu hanya suka shiga ɗakin, suka zauna, yaya tayi ƙuri tana kallon ummi, Iya ta ce “Ke lafiya na ga kayanki a yayyage?”

“Ba komai”

“Kamar yaya ba komai, kamar wadda ta yi dambe” hawaye ne ke shirin taruwa a idon ummi.

“Kuma dan ƙazanta tun da aka kawo ki baki canza kaya ba, yau wurin kwana biyar”.

Ummi ta buɗe baki za ta yi magana, ta kasa hawaye suka riga maganar fita.

Yaya ta ce “Menene na kuka kuma ummi?”

Iya ta ce “Sangarta mana, idan zaki yi wa kanki ƙiyamullaili ki zauna ki daina wannan kukan shikenan, idan ba zaki daina ba, sai ki yi ta yi, ga kaya nan na ɗebo miki a kayan auren da aka kaiwa waccan, abun bai yiwu ba, sauran an sayar an bashi kuɗin yayi muku cefane, sadakin ki kuma, na bayar a sayo akuya a bayar da kiwo”.

“Dan Allah iya ki mayar da ni gida, bana son zaman nan”

“Ki kiyayeni ummi, tun kan na ɓata miki rai, bana son shashanci, ki tashi ki yi wanka ki canza wannan kayan”

Tashi ummi ta yi tana kuka, ta fita tsakar gida, suma fitowar suka yi, wai har tafiya za su yi.

Ummi ta tsaya tana kallonsu, suka fice, wai wata unguwar zasu je, to da me za ta yi wankan, ko ruwa ba ta da shi? Ta koma ɗaki ta zazzage lesar vivar da Iya ta kawo mata, atamfa ce kala uku, sai sabulun wanka uku, man shafawa ɗaya da soson wanka.

Sai kuma ‘yar tsala, a ƙulle a leda, ummi ta ture kayan ta kwanta, wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta, saboda dukan ruwan sama.

Sai da ummi ta kwana biyu tana zazzaɓin nan, babu abun da ya shafi Idris, da ya dawo zai koreta daga ɗakin, bayan ya gama ci mata mutunci da zaginta, wasu lokutan sai yayi mata dukan tsiya ma, duka na cin mutunci, haka take kwana a ɗaya ɗakin da babu ko ƙofa a ciki, idan aka yi ruwan sama, haka zai sameta a ɗakin nan.

Ƙarshe ma ya watso mata kayanta da ga ɗakin da katifa take, ya ce ta koma ɗaya ɗakin.

Da ya tuna ƙarin da ya ji tana yi, da kuma yadda suka din ga lalubeta tana yarinya, sai ya ji ya ƙara tsanarta, da ganin an bashi saura.

Dama abinci ba a magana, ba bata yake yi ba, wasu lokutan ne idan yaran gidan su za su zo, babar Idiris ɗin kan zuba mata abinci a kwano a kawo mata.

Tana kwance a ɗaki tana numfarfashi,  zazzaɓi da ciwon kai sun ƙi sauka, fitsari ya dameta, ta tashi da ƙyar, ta je ta yi, tana shirin komawa ɗakin, ta ji an ce “Ummi”

Tana waiwayawa taga Na’ima, ai sai ta nemi ciwon ta rasa, cikin wani irin zafin nama, ta rungume Na’ima ta fashe da kuka.

Ita ma Na’iman kuka take yi, ta ɗago ummi ta kalleta ta ce “Ummi ba ki da lafiya ne? Na ji jikinki zafi?” Ta jinjinawa na’ima kai.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, yanzu ummi a rasa wanda za a aura miki sai wannan ɗan iskan, dukan ki yake yi kenan? Kalli shaidar yatsu a fuskarki” Ummi dai ta yi shiru, daga baya ta ce “Mu shiga ɗaki”

Saroro na’ima ta bi ɗakin da kallo.

“Ummi kar ki ce ba su yi miki kayan ɗaki ba?”

“Suna can ɗakin, koro ni yayi nan shi ne yake kwana a ɗakin”

Na’ima ta zauna tayi kuka mai isarta sannan ta kalli ummi ta ce “Wai ke ba ki san in da mamanki take ba? Anya ma kuwa sun san halin da ake ciki?”

“Yaya Na’ima nifa tun da aka tafi da mama ban sake ganinta ba, dan Allah idan kin san in da take ki kaini, na gaji, wallahi yaya Idris dukana yake yi, duk jikina ciwo yake zai kasheni”

Ta rungume ummi, ta din ga rarrashin ta, ta ce “Kiyi haƙuri ummi, ban ma san an yi miki aure ba, mama ce ta aika ƙanin mijina ya gaya mini, Allah yana sane da ke ummi, bari na je gida na kawo miki abubuwan da na kawo miki, sai na kawo miki tabarma da labule, a kafa a ɗakin, tabarmar ki din ga kwana a kai”

Ummi ta yi ta mata godiya, ta bata abinci, ta aika ƙannenta suka sayo mata magani, aka kafa labule, ta shimfiɗa tabarma, sai ɗakin ya ɗan yi kyan gani.

“Yaya na’ima, dan Allah idan Allah ya yassare miki, ki saya mini wando, nawa ya ƙarasa lalacewa, ba zai saku ba”

“Ummi meyasa ba zaki din ga zuwa wurin mama kina gaya mata ba? Ya za ayi ki rayu da wando guda ɗaya, abun da a ƙalla a rana ana so ki canza biyu”

Ummi ta yi shiru, tana wasa da yatsun hannunta, yanzu ma dan ta ƙure ne ta nemi alfarmar na’ima, dan idris ya ƙarasa shi, wandon har da in da ta kama take ƙullewa.

Ta ji daɗin zuwan na’ima, ta bata abubuwa da yawa, har da kuɗi, sai bayan la’asar ta tafi, kuma Allah ya taimake ta, Idiris bai dawo ba a lokacin.

Duk yadda ummi ta so ta yi wa naima bayanin halin da take ciki, kasawa ta yi, ta ji abun yayi mata girma ta faɗa, dan haka ta yi shiru da bakinta, ta samu ta saya mata wanduna guda huɗu, har da ribbon.

Duk in da idris ya haɗu da abokansa, suka yi masa kirarin ango, da tambayarsa yaushe za su cin girkin amarya, sai ya hau masifa yana basu labarin halin da ummi ke ciki, na mummunan ciwon sanyi da yadda take bugawa, da ƙazanta tare da ƙorafin ragowa ce aka haɗa shi da ita, su yi ta masa dariya, suna ce masa angon ɗoɗɗoya.

Tare da tabattar masa, idan bai yi da gaske ba, sai ya kwashi ciwon.

Sai dai ko sun tambaye shi dalilin fasa auren sa da Hindu, sai ya ɓoye musu gaskiyar zancen.

Haryanzu kuma bai rabu da hindu ba, yana lallaɓawa su haɗu a wani wurin na daban, duk da tarin kashedi da mahaifinta yayi mata a kan idiris.

Na’ima kuwa a ranar zata koma gidanta, suka haɗu da magaji a hanya, suka haɗu suka gaisa.

Ta ce “Yaya magaji ashe aure aka yi wa ummi babu labari?”

Hashim ya ce “Ke dai bari na’ima, abun ne yazo babu shiri, ni kaina ban san da zancen ba sai ana gobe ɗaurin aure”.

Na’ima ta gyaɗa kai ta ce “Amma, ka yi haƙuri da abun da zan ce, wallahi ku din ga gaya wa kakarku da ɗan uwanka gaskiya, ya za a katsewa ummi karatunta, kuma a haɗata aure da wanda baya ƙaunarta, dama ita ba bi ta kanta za ayi, aji ko tana son sa ba, gaba ɗaya a firgice take a cikin gidan nan, jikinta duk shaidar duka, ya korota daga ɗaki, ɗakin da na tarar da ita, ba ƙofa babu taga, babu abun zama, ba ya bata abinci, wace irin rayuwa ce haka? A gidanku ba ta huta ba, an aurar da ita, ta buɗe sabon babi na ƙalubale, sai yaushe za ta huta kenan? Meyasa Iya ta tsani ummi ne, kamar ba a cikin jikokinta take ba?”

Hashim ya numfasa, cike da damuwa da takaici ya ce “Biyayyar da iyayenmu ke yi wa Iya, ta samo asali ne ga wasiyyar mahaifinmu, na lallai su yi mata biyayya. Bayan haka ban san dalilin da ya sanya bayan biyayyar suke rufe idonsu a kan gaskiya ba, su kasa nuna mata hanyar da ta dace ba.
Nayi iya yi na a kan auren nan, sai dai sun fi ƙarfina, ni dama ba wani shiri muke yi ba, saboda bani da kuɗi, Idris kuma sunan mahaifinta ne da shi. Ƙiyayyar ummi kuma, dama ba ta son mahaifiyar ummi, saboda kawu Magaji yana matuƙar son ta, har wasu lokutan baya iya ɓoye son da yake yi mata, bugu da ƙari, baban ummi ba shi da komai, bai mutu ya bar komai ba, duk da haka dai, ban san dalilin da ya sanya ta tsananta ƙiyayyar ummi haka ba.
Zan cigaba da yi wa idiris nasiha, duk da ba jin shawara yake yi ba, zan kuma biya ta gidan yanzu, in ga halin da take ciki”.

Jiki a sanyaye na’ima ta ce “Yakamata kam, ummi na buƙatar kulawa da jaba jiki, har ga Allah ina jin tausayinta sosai da sosai, dan Allah yaya magaji ka din ga zagayata”.

“Kar ki damu, in sha Allah, ba zai gagara ba, ina godiya sosai da gudunmawar da ki ke bawa ummi”.

“Bakomai yaya magaji, ummi ƙanwata ce, ba zan manta karamcin iyayenta a gare ni ba, da yadda suke girmama iyayena ba”

“Haka ne, ki gaida gida, da maigidan”

Suka yi sallama, kowa ya tafi.

Kasa wucewa gida magaji yayi, ya wuce gidan Idris da bai taɓa zuwa ba.

Sallama yayi ya tsaya a waje, ummi ta leƙo, tana ganinsa tayi murmushi ta ce “Laa yaya magaji, shigo baka zo ba sai yau”

Ya kalleta duk da tana da duhu, amma ga shaidar mari nan a gefen idonta.

Ta yi gaba ta ce masa ya shigo, ya ce “A’a bani abun zama, na zauna a nan”

Ta shiga ta ɗaukko masa tabarma, ta shimfiɗa masa ta ce “Yaya yaya na’ima ta zo fa”

Ya ce “Haba?”

“Wallahi, duk ta sai mini kayayyaki ta bani, ita ta bani tabar nan ma”

“Masha Allah, Allah ya saka mata da alkhairi”

Ta ce “Amin”

Ya ɗan dube ta, ya ce “Ummi babu wata matsala? Komai lafiya ƙalau?”

Ta jinjina masa kai ta ce “Eh”.

“Na san ko baki faɗa ba, akwai matsala ummi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce in sha Allah”

“Yaushe zai wuce yaya? Gobe ko jibi?” Tayi maganar idanunta na tara hawaye.

“Lokaci ne ummi, zai zama tarihi”

Tuni idanuwanta suka fara zubar da hawaye.

“Ki dake ummi, ki ƙarfafi zuciyarki, na san a cikin matsala ki ke, ki yi haƙuri ummi, ki share hawayenki, zai zama murmushi wataran” goge hawaye take yi, sai dai tana gogewa wasu suna zubowa.

Idiris ne ya bankaɗo babu ko sallama, yadda ummi ta zabura kawai ya isa ya baka tausayi.

Ko kallonsu bai yi ba, ya shige ya buɗe ɗakin da yake kwana, ya shiga.

Hashim ya tashi ya bi bayansa, ummi ta karkaɗe tabarmar, ta ɗaukko tsintsiyar da na’ima ta bata, ta yi shara, hayaniyar hashim ta din ga ji, da idris.

Hashim yana ce masa “Ka ji tsoron Allah wallahi, idan ka cigaba da biye wa Iya, wallahi Allah ba zai barku ba, kuna ta azabtar da marainiyar Allah ba gaira babu dalili”.

“An azabtar da ita ɗin, ni na ce a aura mini ita? Ko na ce ina son ta ne, kai meya hana a aura maka ita? An bani saura ƙazama mummuna, Wallahi ba zan zauna da ita ba, sai ta gudu da ƙafarta”.

“Amma ita ma ai ba cewa tayi tana sonka ba, haɗin Iya ne, ita tayi haƙuri, kai me zai hana ka yi haƙurin?”

Idris ya ce “ba zan yi haƙurin ba, ka fita daga harkata, ko kai ma na karta maka rashin mutunci”

Haka suka yi baran-baran, hashim ya fito, ummi tana ce masa kai gaida gida, kai kawai ya jinjina mata ya tafi.

Yana fita, Idris ya dirar mata da duka da zagi da cin mutunci kamar yadda ya saba, yana iƙrarin ƙararsa ta kai wurin magaji.

Maƙwabciyar su da ta kasance dattijuwa, yau ta kasa jure ihun ummi, ta shigo kawo mata ɗauki, ta din ga bashi haƙuri, amma mursisi ya ce ta fita ta bar masa gida, ganin idiris bai yi kalar mutunci ba, ya sanya ta fita ta bar gidan tana tausaya wa ummi.

Tun daga ranar ya ƙara tsananta azabtarwar da yake yi mata, gashi ya tula mata wankinsa, ya ce tayi masa, idan tayi bai fita ba, ya kamata ya zane ta, ban da zagi da cin mutunci.

Abinci kuwa ko tumatir bai taɓa kawowa ba, sai dai ta aika wa iya, Wataran ta bata, wataran ta ce ba ta da shi.

Ƙarshe sai da iya tayi ta mata faɗa, wai ba zata iya rufawa Idris asiri ba, ta san dai ba wata cikakkiyar sana’a ce da shi ba, ranar da ya kawo su ci, idan ba shi da shi ta din ga haƙuri.

Dattijuwar matar nan ta fuskanci halin da ummi take ciki, ta ɗauki ragamar ciyar da ita, idan ta cewa ummi ta gudu ta je gida ta kai ƙarar abun da yake yi mata, sai ummi ta ce ko ta je dawo da ita za ayi.

Da ya kalli ummi, ya tuna a yanayin da ya sameta, sai ya ƙara ƙaimi wurin cutar da ita, haɗi da zaluntar ta.

Idan aka zo ana sallama da shi abokansa, sai ta jiyo suna kiransa da angon ɗoɗɗoya, ba ta kawo komai a ranta ba, sai ranar da ta jiyo suna tambayarsa ina amaryarsa ɗoɗɗoya, ya ce musu kar su sake haɗa shi da wannan jakar yarinyar.

Duk da ƙarancin shekarun ummi, a lokacin ta fuskanci asiri ya tona mata a wurin abokansa, hakan ya sanya ta yin kuka da har kanta ya yi ciwo.

A haka a wannan baƙar azabar, tayi wata guda cir a gidan sa, tun tana tsoronsa har ta fara dakewa da duk abun da zai yi mata yayi mata.

Yau ta tashi da wani irin zazzaɓi mai zafin gaske, wanda baya rasa nasaba da dukan ruwa da kuma azababben sauron da yake cizonta a wannan ɗakin.
Ga gudawa da take zugawa babu ƙaƙƙautawa, jikinta duk yayi weak.

Bankaɗa labulen yayi, ya tarar da ita a kwance, ya watsa mata kayansa ya ce ta wanke masa.
Shiru tayi ba ta motsa ba, ya daka mata tsawa ta ce “Yaya bani da lafiya”

“Ina ruwana, dalla fito”

Ta janyo jikinta ta kwaso kayan ta fito, ya fita sayen omo, ta kwanta a kan kayan, tana jin ɗumin ranar dake ratsata, wanda hakan ya sa zazzaɓi ƙara rufeta.

Azabar zafin dukan da yayi mata da ƙafarsa yasa ta tashi da sauri, tana riƙe hannunta.

“Bacci na ce ki yi?” Shiru tayi tana sunkuyar da kai.

Wani irin yawu ya haɗiye, yana ƙare wa ummi kallo, duk baƙin fatar nan ta ta fatar tana da ɗaukar ido.

A wurin yayi yinƙurin sake afka mata, sai dai ba ta sauya zani ba, duk da ta samu sassauci, na ciwon saboda yanzu sau biyu take sauya wando a rana, kamar yadda Na’ima ta gaya mata.

Amma duk da haka tana wannan ƙarin mara daɗi, duk da jikinta baya wari yanzu, saboda ta samu sabulun wanka.

Zura masa ido kawai tayi, saboda a galabaice take da ciwo

Wata mummunar ashar yayi mata, yana zubar da yawu, ya ɗagota ya din ga kifa mata mari.

Kukan ma ba ya iya fita, saboda azaba da masifar idiris, da yake abu kamar dabba ba ɗan adam ba.

Ya din ga tsine mata albarka, da ita da iyayenta, dan har Iya sai da ya zaga.

Ƙarshe ma ya danƙara mata saki a wurin.

Ƙafarta ko takalmi babu, ta gyara suturar jikinta ta fice daga gidan a haka, ta tafi gida ga hannunta ɗaya kamar ba a jikinta yake ba, saboda takata yayi a hannun.

Iya da ke iza wuta ta miƙe tana faɗin “Ke lafiya?”

Kan ummi ta yi magana, jiri ya ɗebe ta ta faɗi ƙasa.

Da sauri Iya ta ƙarasa kanta ta ce “Ke, menene wai?”.

“Iya zan mutu, yaya idris zai kashe ni, dan Allah kar ki mayar da ni, ya ce ya sake ni” tayi maganar cikin gunjin kuka.

Ta taɓa jikin ummi ta ji zafi, ga fuskarta shaidar yatsun Idris kwance a fuskar ta har idonta yayi taruwar jini.

“Lallaɓa ki tashi ki shiga ɗaki ki zauna, daga yin aure ba a kashe shi ba, bari dai ya zo mu ji me ki ka yi masa” Iya ta tashi ta fita.

Kuka ummi ta din ga yi, tana jin dama ta mutu ta huta, idan aka mayar da ita gidan idris ta san sai ya kashe ta.

Da ƙyar Hashim ya nemo idris, aka nemo babansu, domin jin menene yake faruwa.

Sai dai daga mugun kallon da yake yi wa ummi, ka san babu Allah a ransa.

Babu zato babu tsammani sai ga kawu yahaya ya dira a gidan, kuma bai tsaya ko ina ba sai sashin Iya.

Sai dai babu walwala ko fara’a a tare da shi, suka gaisa da Iya da ɗan uwansa, da su Hashim. Sannan ya kalli Iya ya ce “Iya dan me za a aurar da ummi, ba tare da na sani ba? Sai shekaranjiya magaji yake gaya mini?”

“Saboda kai ne ubanta? Uban waye ma ya ganka balle ya gaya maka, tangarɗa aka samu da wadda zai aura, na saka aka yi da ita dan rufuwar asirinmu”.

Ummi da baccin wahala ya ɗauka, kamar a mafarki ta ji muryar kawu yahaya, miƙa hannu ta fara yi ta ce “Kawu”

Cikin azama ya nufi ummi ya ce “Na’am mamana”

“Dan Allah ka kai ni wurin mama, idan na koma gidan Idris kashe ni zai yi” ganin tana ƙoƙarin tashi ta kasa, ya sanya ya ɗago ummi.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un” ya faɗa a razane.

Fuskar ummi ya gani a kumbure suntum, ga hannunta ɗaya ma ya kumbura ba ta iya motsa shi sosai.

“Meyafaru haka?”

“Dukana yake yi kawu, dan Allah kar ka bani a nan wallahi mutuwa zan yi, idan baka san in da mama take ba, ko gidan marayu ka kai ni, ko idan akwai makarantar almajirai ka kai ni, zan mutu wallahi ” tayi maganar tana wani irin gigitaccen kuka.

“Kar ku ce mini shi yayi mata wannan dukan?”

Iya ta ce “Ka ga Yahaya, ba abu ne na tashin hankali ba, abun da muke shirin sasantawa kenan, kai me take yi maka ne?”

Cikin fitsara da rashin kunya ya ce “Haba Iya, kin san ni ba son ta nake yi ba, yarinya da take saura ce, ai kin san komai aka liƙa mini ita, ga sanyi ya kasheta ban da wari da ɗoyi ba abun da take yi, an liƙa mini na kwashi masifa gaskiya ba zan iya ba, jikinta kamar an buɗe masai, nima ba iya zama zan yi da ita ba”.

Tsit suka yi, babu wanda ya zaci fitowar wannan maganar daga bakinsa, baƙin ciki da takaici ya rufe Hashim.

“Madalla, ka iya rubutu ai ko?” Ya jinjina kai.

Kawu yahaya ya ciro takarda da biro ya ce “Sakar mini ƴa ta”

Iya ta fara “A’a Yahaya, ai dauɗar gora ciki ka sha ta “

“Ba wata dauɗa iya, koma menene ya samu ummi laifinki ne, kina me sanyi yayi mata wannan kamun? Da dauɗar gorar ciki ke shan ta, shi ya kasa rufa mata asiri ya nema mata magani, ya tona mata asiri haka, shi mai ya hana ya sha dauɗar gorar?, laifin waye idan ba naki ba, ya saki ummi, da ita zan tafi, abun da yayi kansa ya yi wa, ƴar shekara sha uku aure wata ɗaya ya rabu, In sha Allah ba zata wulaƙanta ba, na yi imani da Allah balarabe ba zai bari iyalinmu su wulaƙanta bayan bamu ba” yayi maganar ƙasan zuciyarsa yana jinjina girman hukuncin da ya yanke, dan ya san da badaƙala idan ya je da ummi gidansa.

(Ina godiya da tarin comments da ake yi a kan litattafan bright pens, cutarwa, munafukin miji, yi wa kai, masu ƙorafi a kan littafin cutarwa, ayi haƙuri da yadda labarin yazo, ina ganin sharhi da ƙorafe-ƙorafe ina godiya sosai 🙏)

Ayshercool

CUTARWA!

P13

Iya ta ce “A’a Yahaya, kar mu yi haka da kai, wannan abu ne na cikin gida da yakamata a sasanta shi, wannan ai sai asirinmu ya tonu, duniya ta zage mu”

“Iya zagi na nawa kuma? Kalli jikin yarinyar nan fa, baiwar ubansa ce ita? A gabanki a gaban ubansa yake aibata ta yake cewa baya son ta, baya ƙaunarta, wallahi dole ya saketa, zan je da ummi ta cigaba da karatunta”.

“Gaskiya ban lamunta ba yahaya, ba zaka ɓata zumunci ba da abun da na ƙulla dan ƙarfafa zumunci ba”.

Hashim da bai yi niyyar sanya baki ba, sai da ya ga abun na iya yaƙi ci ya ƙi cinyewa ya ce “Iya wane zumunci kuma banda wanda aka ɓata?”

“Rufe mini baki dan ubanka, ai duk kai ne munafikin da ka kunno kowacce wuta, ban yadda a tafi da ummi ko ina ba, ko auren ya mutu, muna nan a bar mini ita”.

Yahaya ya kalli Iya ido cikin ido ya ce “Wallahi iya idan ki ka hana ni tafiya da ummi, zan ɗebowa idiris hukumar kare hakkin ɗan Adam, su bi mata hakkinta, kuma idan suka tashi, har ke ba zasu bari ba, da duk mutanen gidan nan, na farko ga child abuse, by forced marriage, kun mata auren dole da ƙanan shekaru, ga dukanta da ci mata mutunci, deformation of character ɓata mata suna, ta hanyar yaɗa larurar da take fama da ita a cikin mutane, wanda duk ya zo kunnena tun kan na zo nan na samu lanari, kuma mariya ma zata iya shigowa cikin lamarin nan, ƙwace mata ƴa babu dalili da ki ka yi, dan dai suma ba su san ƴancin su bane, da sun haɗa ki da hukuma, da sai kin basu ƴar su”.

Saminu ya ce “A’a yaya yahaya, ba za ayi haka ba”

Cikin rikicewa Iya ta ce “Yahaya ni zaka kai ƙara hukuma ka saka a rufe ni?”

“Ba ƙararki zan kai ba, ƙarar wannan sakaran zan kai, idan kuma na kai ƙararsa su hukuma zurfafa bincike zasu yi, ina gaya miki abun da hakan ka iya haifarwa ne, kai kuma ɗauki takarda da biro, ka sakar mini ƴa, ko daƙiƙancin naka bai bari, ka iya rubutun ba?”

Cikin kumbura baki ya ɗauki takarda da biron, ya rubutawa ummi saki biyu.

Kawu yahaya ya karɓa, ya kalli ummi ya ce “Tashi in tayaki ki haɗo kayanki mu tafi”

Magaji ya ce “Bari na tayata” a hankali ta ce “Ai kayan suna can gidan, sai kuma kayana da ke ɗakin itace”

Kawu Yahaya da kansa ya tashi, ya je ɗakin itacen, ya ɗaukko vivar kayan ummi, sai dai ya ga tsummokara ne kawai, dan haka ya ce ba za su tafi da su ba.

Iya ta din ga harar ummi, amma ummi tayi kamar bata gani ba, magaji ya kawo kayan ummi.

Jama’ar gida suka taru, suna kallon ummi za ga tafi birnin kanon dabo gidan kawu yahaya, wasu na tausaya mata, wasu kuma na yi mata murna.

“Yahaya” Iya ta kira sunansa.

Ya amsa mata, ta ce “Ka yi mini alƙawarin ba za ka kai ummi wurin mariya ba, dan idan haka ta faru, abun da zai biyo baya ba zai yi mana daɗi ba”.

“Abu ɗaya na sani, na ɗauki ummi tsakani da Allah dan inganta rayuwarta, ni ban san a in da mahaifiyar ta take ba, amma akwai lokacin da lallai dole a nemi dangin mahaifiyar ummi, ta gansu, dan babu in da shari’a ta ce a yanke alaƙa tsakanin uwa da ɗan ta, ko da kuwa kafura ce, abun da yake tsakanin ki da mahaifiyar ta daban, kuma bai kamata ya shafi ummi ba” Iya tayi muƙus, dan ba ta son yi wa kanta sagegeduwar ɗan abun duniyar da yake bata.

Sosai kawu yahaya ya yi wa ƴan uwansa ta tas, a kan abubuwan da suka faru a kan ummi, kasancewar shi ne babba suna girmama shi, duk da kaf ɗin su sun riga shi yin aure, dam su ba karatun boko suka yi ba, wasun su ma shakara sha tara suka yi aure, amma suna girmama shi sosai mussaman da yana da abun duniya.

Magaji ne ya riƙo ummi, sai layi take saboda yunwa da kuma rashin lafiya.

Magaji ya ce “Ummi shikenan sai tafiya, in Allah ya yarda wahala ta ƙare, sai jin daɗi da kwanciyar hankali, ki kula da kanki, ki yi karatu da kyau”.

Ummi ta ce “To yaya, kai ne ka gaya wa kawu halin da nake ciki?”

“Eh ummi, aron waya na samu, na kira shi, idan ba haka ba, bani da wata mafita da zan taimake ki”.

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Allah ya sa kar iya tayi ta yi maka faɗa, dan Allah idan ka ga yaya na’ima ta zo ka gaya mata bana nan, ba zan iya zuwa yi wa mama sallama ba, jikina ba ƙwari ba zan so ta ganni a haka ba”

Ya ce “To shikenan, in sha Allah”

“To zaka din ga zuwa kanon muna gaisawa?”

Yayi murmushi ya ce “Zan din ga zuwa, ai kema zaki din ga zuwa muna gaisawa ko?”

Ta yi saurin girgiza masa kai ta ce “In Allah ya yarda ni da gagarwa har abada, ba zan sake zuwa ba, dan Allah idan ka samu labarin in da mama take, ka gaya mini”

Sak yayi jikinsa yayi sanyi yana kallon ummi, jin abun da ta faɗa, sai dai bai kamata ya ga laifinta ba, an azabtar da ita azabtarwa mai munin da dan ta faɗi hakan, ba ta yi laifi ba.
Kawu yahaya ya tsaya suna magana da kawu Ilyasu da sagir, wanda yanzu suka zo riski zasu tafi.

Kawai Idris ya tsinci kansa da dawowa, dan ya tabbattar da gaske tafiya za ayi da ummin? Ko kuwa ba gaske bane ba?.

Hannun hashim ya gani a cikin na ummi, ya riƙota sun tsaya suna magana, wani zazzafan abu mai raɗaɗin gaske, tamkar sukar kibiya, ya soki ƙirjinsa.

Taɓe baki yayi tare da jan tsaki, hashim suka ƙarasa gaban motar, ummi ta shiga ta zauna tana kallon hashim da ƙofar gidan da nan ne tushenta, amma azabar cikinsa ko zamanin bayi sai haka.

Yaran gidan har da mata, da maƙwabta sun yi dandazo suna kallon tafiyar ummi.

Kawu yahaya suka gama magana, ya shiga ya kunna motar Ummi ta sauke idanuwanta masu kama da na mage a cikin na Idris, idanun da suka kumbura saboda duka ɗaya yayi taruwar jini a cikin sa, wani irin kallo take yi masa mai kama da na ka saurari dawowata, zaka girbe abun da ka shuka.

Hanyar kano suka kama, suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha tare da rarrashin ta.

Ya kalli ummi ya ce “Idan mun je, kar ki kuskura ki gaya wa wani kin taɓa aure, kin ji ko?”

Ummi ta jinjina masa kai alamar to.

Suna tafe tana amai, kasancewar baya son su yi dare a hanya, ya sanya ya tsaya ya saya mata ruwan gishiri da suga, da kuma maganin zazzaɓi, suka cigaba da tafiya, ya tanbayeta ko za ta ci wani abun ne? Duk da yunwar da take ji, cikinta babu daɗi, dan haka ta ce masa ba ta buƙatar cin komai.

Tsayawa yayi ya saya mata kankana, ya ce ta sha, kaɗan ta ci ta kashingiɗa, tana tuna wulaƙanci da cin zarafin da idiris yayi mata, da yadda ya tona mata asiri a gaban mutane.

Ko da suka isa kano, wani asibiti ya fara wuce wa da ummi, aka yi mata teses, sannan aka rubuta mata magunguna, har za su tafi, kawu yahaya ya cewa ummi, ta yi wa likitan bayanin ɗaya matsalar ta ta.

Sai dai ummi ta sunkuyar da kai, ta kasa magana saboda tsananin kunya da ganin kamar tozarci ne bayanin wannan matsalar ta ta ga wani.

Ganin taƙi magana, ya sanya likitan tura su wurin wata nurse, tun da mace ce, za ta fi iya sakin jiki tayi mata bayani.

Sai dai ba ta sauya zani ba, nan ma ummi kasa magana ta yi.

Nurse ɗin ta kalli kawu yahaya ta ce “Yallaɓai me yake damunta ne? Ta ƙi magana”.

Ya ce “Kina ji ƴa ta ce wannan, a ƙauye take hannun mahaifiyarmu, aka yi mata aure na je na tarar da matsala mijin ya ce ba ta da lafiya, sanyi yayi mata yawa, auren ma dai ya mutu”

Nurse ɗin ta kalli ummi sannan ta kalle shi ta ce “Bawan Allah kai gaka wayayye, ya zaka bari a yi wa wannan yarinyar ƙarama aure a yanzu, kalli fuskarta ma kamar shaidar duka, ni wannan yarinyar ai ba ta fi in saka zani in goye ta ba”.

Ganin za ta fara yi masa faɗa, saboda yadda ta ɗau zafi, ya sanya ya yi mata bayanin komai.

Jikinta duk yayi sanyi, tana jinjina lamarin, gaba ɗaya tausayin ummi ya kamata, wannan ƴar ƙaramar yarinyar ita ce aka yi wa aure, har ya mutu.

Ta kalli ummi ta ce “Gaya mini menene yake damunki a wurin?” Ummi ta sunkuyar da kai tare da jin ta a takure.

Ta kalli kawu yahaya ta ce “Ɗan bamu wuri” ba musu ya fita waje.

Ta haɗe rai ta kalli ummi ta ce “Ke dan gidanku ki gaya mini nan asibiti ne, idan baki warke ba haka zaki yi ta aure yana mutuwa, saboda wannan matsalar”.

Ummi murya ƙasa-ƙasa ta ce “Ƙaiƙayi yake yi mini”.

“Tun yaushe?”

“An daɗe”

“Ya aka yi aka daɗe, wasa ki ke da wurin?”

Ummi ta girgiza kai alamar a’a.

“To ya aka yi yake ƙaiƙayi, kafin ayi miki auren ya fara ko bayan an yi mikk auren?”

“Kafin ayi mini ne?”

Nurse ɗin ta numfasa ta ce “Sau nawa ki ke canza wando a rana?”

Ummi ta kalleta ta ce “Kan ayi mini?”

Auren ne ba zata iya faɗa ba, tana jin nauyin haka.

Ta ce “Eh, kan ayi auren”

“Wandona ɗaya ne, idan na wanke sai na saka”

Tayi ƙuri da ido tana kallon ummi, da ta ji ta ce wando ɗaya.

“Yaya ki ke tsarki?”

Amsar da ta bawa nurse ɗin ta girgiza ta, dan ciwon sanyin ummi, yana da alaƙa da rashin iya tsarki, da tsugunawa a banɗaki barkatai, da kuma rashin kyakywar kulawa na uwa da wurin bai samu ba.

Ta dubi ummi ta ce “Daga yanzu, wando sau uku zaki din ga canzawa a rana, kuma idan ki ka yi bayan gida, sai kin fara wanke wurin fitsarinki, sannan ki wanke wurin bayan gida, ba haɗe tsarkinsu.
Kar ki kuskura ki yi fitsari kina ɗigar da ruwan tsarkin, ki mayar da wando jikin ki, ko ki saka jiƙaƙƙen wando, ki samu ɗan tsumma mai kyau, ki din ga wankewa kina ajiyewa a banɗakin da ki ke, idan kin yi tsarki, ko kin yi wanka, ki din ga tsane wurin kan ki saka wando.
Idan fitsari ya kama ki a wani wuri daban ba gida ba, ki yi fitsarin a tsaye, idan kin gama sai ki wanke ƙafarki, da jikinki, ki daina shiga banɗaki barkatai” ta din ga yi wa ummi bayanin yadda za ta din ga kula da tsabtar wurin, dan babu wanda ya taɓa zaunar da ita yayi mata wannan bayanin.

“Kin fara al’ada ne?”

Ummi ta ce “A’a”

Nurse ɗin ta a aika ummi ta kira kawu yahaya, ta ce masa “Yallaɓai gaskiya sanyi ya yi mata yawa, kuma na lura rashin tsabta da kula ne ya haddasa mata hakan, dan haka dole ku kula, tun da yanzu ka ce ta dawo hannunka. Ku dawo ranar lahadi akwai gynea doctor ɗin da yake zama, sai ka kawota ta ganshi.
Na so ace da mace ku ka zo, sai ta fi fahimtar bayanina, amma kai ɗin ba ta ɓaci ba, ai uba ne kai. A yanzu, abu na farko a sama mata isasshen wanduna, a ƙalla shida zuwa dozen. Sai kuma a sama mata flask mussaman na ruwan zafi, na ta ne ta din ga kama ruwa da ruwan ɗumi.
Banda tsarki da sabulu, a samo mata ganyen magarya, a tafasa shi ta din ga kama ruwa da shi.
Kuma ka san shi ciwo ne mai naci, dan haka a kula sosai, sai kuma ku nemi kanumfari, tafarnuwa ba mai yawa ba, da namijin goro, a jiƙa su a robar ruwa mai murfi, ta din ga tsiyaya tana sha, ta yawaita amfani da kanumfarin nan.
Sai kuma a samo saiwar zogale a din ga tafasa mata da jar kanwa, ta yi amfani da ko guda ɗaya kafin ku zo ku ga likitan, zata samu sauƙi in sha Allah. Wannan na ɗan gaya muku ne dabarunmu na cikin gida na gargajiya, kafin Allah ya sa ku zo ganin likitan”.

Ya ce “To shikenan, na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da alkhairi”

Ummi ta bi bayansa suka fito, suna tafe a hanya yana jaddada da mata ta riƙe abubuwan da aka gaya mata, ummi kuwa gaba ɗaya jikinta sanyi yayi, wata irin kunyarsa ta rufe ta.

Shi kansa yayi mamaki da nurse ɗin ta ce masa ummi ta ce wando ɗaya ne da ita.

“Ummi”

Ta amsa da”Na’am”

“Ki kwantar da hankalinki, magnunnan nan zan saya miki zuwa gobe in Allah ya kaimu, har kayan da zaki yi amfani da su, duk zan yi miki har makaranta zan mayar da ke da yardar Allah, ke dai ki nutsu ki manta da komai, ban yi miki alƙawarin gidana babu ƙalubale ba, amma na san bai kai na ƙauye ba. Ki dage ki yi amfani da shawararin da ta baki kin ji ummana”

Ta ce “To na gode sosai”

Ya shafa kanta ya ce “Yauwwa Allah yayi miki albarka”

Can gagarawa kuwa, Hashim ya sha zagi da cin mutunci da wulaƙanci a wurin Iya, ba Iya kawai ba, har da mahaifinsa suka ƙare masa tas, a kan ya kasa rufa wa ɗan uwansa asiri, da har ya iya sanar da kawu yahaya halin da ake ciki.
Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, amma har cikin ransa yake jin wannan abun da yayi shine mafita ga rayuwar ummi, kuma hakan da yayi bai saɓawa shari’a ba.

Sirikan iya wasu sun jiye wa ummi rabata da gidan nan, saboda azaba da masifar iya ga ummi.

Iya kuwa ta ji baƙin ciki da takaicin ɗauke ummi da yahaya yayi, dan yanzu ta san abu ne mawuyaci idan asirinsu da take ta ƙoƙarin rufuwa bai tonu ba.

Shi kansa Idris tun da aka tafi da ummi, bai dawo gidan ba, dan ya san zai sha faɗa a wurin Iya da iyayensa, shi kuma har ga Allah, ya tsani yarinyar nan hakan da yayi shine dai-dai.

Horn yayi, wani matashin yaro, da zai ɗan girmi ummi ya zo ya buɗe gate ɗin, ummi ta san yaron amma da daɗewa dan wasu lokutan ya kan zo da shi gagarawa.

Ya shiga da motar harabar gidan, ba laifi harabar mai ɗan girma ce, dan aƙalla za a yi parking ɗin motoci uku a ciki.

Wasu ƴan mata ne ƙanana su biyu farare tas da su, an yi musu kitson ƙari, ɗaya tafi ɗaya girma, suka nufo motar suna faɗin oyoyo Abba.

Ya buɗe motar ya fita ya rungumo su, sannan ya juya ya buɗe wa ummi motar ta fito.

Duk da duhun magariba ya fara yi, hasken fitilar da take harabar gidan, ta basu damar tsayawa suna ƙarewa ummi kallo.

Ya buɗe bayan motarsa ya cewa yaran su ɗaukko wa ummi kayanta.

Ba laifi gidan mai kyau da shi, ummi sai kallon gidan take yi.

A falo ya kalli yaran ya ce “Intee ina maama ne?”.

“Ta fita da muka dawo daga tahfee, bamu tarar da ita ba”

Ya ce “Ok, ga sister ɗinku nan, sunan ta Salma, amma ummi ake ce mata, you can call her yaya ummi, ku nuna mata toilet ɗin ku ta yi alwala”.

Cikin ƙyama intee ta bi ummi da kallo, sannan ta yi gaba, ummi ta bita a baya.

Ummi ta yi salla ta idar, tana ta kallon ɗakin, da gani na ƴan matan ne, kowacce da gadonta, ga ƙatuwar wardrobe, ga shoe rack ɗin su ɗauke da takalmansu na makaranta da na fita, duka-duka babbar da ake kira da intee ba ta fi shekara goma ba, ɗayar kuma bakwai.

Ummi ta fito daga ɗakin, ta koma falo ta zauna a ƙasa.

Ya shiga kitchen da kansa, ya haɗowa ummi tea mai kauri, ya saka intee ta dafawa ummi noodles ta ɗora mata ƙwai uku a kai.

Duk da yanayi na rashin lafiya, ummi ta ɗan ci, dan bata taɓa cin indomie ba, duk da ta na burgeta.

Yaran suka kunna tv suna kallo tare da mahaifinsu, ummi ma kallon take yi, suna ta yi wa babansu surutu, yana ta ƙoƙarin saka ummi a hirar, ta dai yi shiru ba ta cewa komai.

Bayan magariba sosai sannan wata mata tayi sallama, ita da wata matashiyar budurwa.

Ya amsa ya ɗaga kai yana kallonsu, yaran kuma duk suka tashi suka nufeta.

Cikin iyayi ta ce “Abba ka dawo kenan?” Tayi maganar tana zama da tsohon cikinta.

“Eh” ya amsa mata a taƙaice.

Ummi ta kalleta ta ce “Ina wuni?”

Ta bi ummi da kallo, ta ce “wannan fa?”

Ya ce “Ki fara amsa mata gaisuwar mana”

“Lafiya ƙalau” ta amsa a ɗan yatsune.

Ya kalli su inteesar ya ce “Abdul, intee, shalele ku bi anty rahama maza, ummi ki bisu ki samu ki huta, a haɗa mata ruwa tayi wanka”

“Wai ban gane ba, ita wannan ɗin wacece?”

Ya ce “Kya tsaya na yi miki bayani ai, yanzu dai daga ina ki ke?”.

“Gidan gana na je, wata ƴar aikin nake so ta samo mini, saboda su intee wahala tana yi mini yawa”.

“Amma ba kwanan nan ki ka rabu da wata ba, kina ta surutun tayi miki laifuka ba, shi ne zaki sake rakito wata?”.

“To Abba yaya zan yi? Ga tsohon ciki, da na haihu zan koma school, ga ayyukan gida ba zan iya ba wallahi. Ka yi haƙuri kawai ni dai”.

“Shikenan, amma kar ki kuskura ki zo kina ce mini an yi miki kaza an yi miki kaza”

“Na ji wacece waccan yarinyar da ka haɗa mini da yara?”

“Dama na san ba saninta zaki yi ba, tun da ba zuwa ki ke yi ba, Ƴar wurin marigayi ce bashir?”

“To me zata yi a nan ɗin?”

Ya gyara zamansa ya ce “Eh, na ɗaukko riƙonta ne na dawo da shi hannuna, a nan za ta zauna da mu”

A fusace ta ce “Amma yaya zaka yi mini haka, ya zaka ɗaukko yarinya ban sani ba ba shawarata kawai ka ce in riƙe? Saboda me? Abba meye amfanin kawo bare ka haɗa a cikin iyalinka”.

“Ƴar ɗan uwan nawa ce bare kuma?”

“Bare ce mana, ki ka haifeta? Naga ai ba cikinku ɗaya da ubanta ba, gaskiya ban yarda ba, ka mayar da ita in da ta fito wallahi ba zan iya ba, dama dinginku sun tsane ni, shi ne aka haɗoka da ita ta zo ta saka mini ido, wallahi ba zan riƙe ba”.

Ya dubeta ya ce”Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ƴa ce a wurina, idan har ummi za ta bar gidan nan, ki tabattar rahama ma sai ta bar mini gida, dan bani da wata alaƙa da ita, dan ina aurenki ba dole ne na riƙe ki na riƙe ƙanwarki ba, tun da baki san mutunci ba, a gobe in Allah ya kaimu rahama ta bar mini gida na gaya miki”.

“Yahaya, ni ka ke gayawa ƙanwata ta bar gidan nan?”

“Tun da ki ka iya kallona ki ka ce, ƴa ta ta bar gidan nan, to rahama ma sai ta bar gidan nan tun da ko ban riƙeta ba, bani da laifi a wurin Allah, ummi kuwa dole ne riƙonta a kaina” ya tashi fuuu ya nufi ɗakin su intisar.

Ummi na zaune a ƙasa rungume da kayanta, tana kallonsu, suna zaune a kan gadonsu, sun sakata a gaba suna ta dariya, saboda yanayin ƙauyanci da yake tare da ita da kuma baƙar fatarta.

Sallamar babansu ce ta sanya su tashi a razane, suka daina dariyar.

“Ina ruwan wankan da na ce a bata?”

Intee ta ce “Anty rahama ba ta haɗa ba”

“Wannan ban isa da ita ba, ku na isa da ku, ki haɗa mata ruwa ki nuna mata yadda ake amfani da toilet ɗin”

Ta jinjina kai, ya juya ya fita dan tafiya masallaci sallar isha’i.

Cikin ƙyama take nunawa ummi banɗakin, ƴar ƙarama da ita, amma ta iya wulaƙanci.

Ta cewa ummi kar ta kuskura ta taɓa musu sosunan wankansu, ta je ta ɗaukkowa ummi sabulun wanki, ta bata wai tayi wankan da shi, ta kuma nuna mata iya in da zata tsaya, tayi wakan.

Ummi ta jinjina mata kai, sai dai ta tsaya tana kallon banɗakin yadda ya ƙawatu.

“Rahama kina ina, wai ni yahaya ya ɗaukkowa ƴa a ƙauye na riƙe, wai idan ba zan riƙe ba kema ki bar masa gida”

Rahama ta kalleta ta ce “In bar gidan nan wai? To me ki ka ce masa”.

“Wallahi ba zan riƙe ba, kuma ba in da zaki je, shi ya isa ma, wallahi yayi kaɗan, zai gane kuskurensa”.

Rahama ta ce “Anty ke da ki ke neman ƴar aiki? Gashi kin samu a ɓagas, ba dai gida ne ba, ta zauna mana iya ka idan bala’i ya isheta ta gaji ta bar gidan nan, ki rabu da shi, sai dai karki saurara mata wallahi, idan ma sa ido aka turo ta ki ci ubanta, ki rabu da shi kawai”

Ta ce “Kuma fa haka ne rahama, haka za ayi, ɗakin mai aiki kawai zata koma, na samu baiwa zata ci ubanta kuwa, sai ta koma in da ta fito dan ba zan zauna da ita ba wallahi. Nifa gaba ɗaya ban yarda da yarinyar nan ba, lokacin da muka je gaisuwar babanta, ina jin kakarta na ta ce mata kamar mayya, ke kin ganta baƙa ƙirin ƙwayar idonta kamar mage”.

Raham ta ce “Idan ma mayyar ce ta ci kanta, dan wallahi mun fi ƙarfinta, to ma ina uwarta da za a kawo miki ita? Gaskiya baban Abdul yana da matsala wallahi”.

“Oho masa, sai ta bar mini gida dai wallahi, amma na san yadda zan yi da shi”.

Ayshercool

CUTARWA!

P14

Har kawu yahaya ya dawo daga sallar isha’i, suna tattaunawa ita da rahama, suka gama ƙulle-ƙullensu, sannan farida ta baro ɗakin rahama.

Yahaya ya tafi ɗakin yaransa, in da suke ta tsalle-tsalle a ɗakin, ummi kuma na ta gyangyaɗi a zaune a ƙasa.

Suna ganinsa suka tsagaita da tsallen da suke yi, ya kalli babbar ya ce “Ke intee, ku yi squating da kausar a kan gadonki, yaya ummi ta kwana a kan ɗaya gadon.

Turus suka yi suna bin mahaifinsu da kallo, cikin tsawa ya ce “Ba ku ji me na ce ba ne?”.

Intee ta ce “To” ya kalli ummi da ta buɗe ido ya ce “Ummana, ga gado nan tashi ki kwanta kin ji”

Ummi ta ce “To na gode”

Ta tashi ta hau gadon nan ta kwanta, wani irin laushi, ga ƙamshin room freshner mai daɗi kayan shimfiɗar suke yi, tun kan ya bar ɗakin bacci ya fara kwasarta.

Inteesar ta kwashe wa da kausar da dariya ta ce “Shikenan bedsheet ɗin ki zai kwashi baƙi, kamar an ciro a buhun gawayi”.

Kwaɓe fuska kausar tayi za ta yi kuka, intee ta cigaba da dariya, ganin kausar ta fara kuka ya sanyata cewa “Bari idan abba ya daɗe da tafiya, sai mu tashe ta, ta saukko”.

Haka kuwa aka yi, intee har da leƙawa, ta tabattar da ya tafi, sannan ta dawo, ta hau dukan ummi a ƙafa.

Ummi ta buɗe idonta tana kallonsu.

“Saukko mana daga kan gado, kausar zata kwanta”

Kasa magana tayi ta cigaba da bin su da kallo.

“Ki saukko zata kwanta, dan ba zata kwana a gadona ta matseni ba” babu musu ummi ta saukko, ta koma ƙasa ta sake tada kai da kayanta.

Kausar ta watso kayan kan gadon nata, har bedsheet ɗin da komai, wai saboda ummi ta kwanta a kai.

Wajen ƙarfe ɗaya na dare, ummi ta ji ana haurinta da ƙafa, ta tashi firgigit, dan ji tayi kamar a gidan idris za ta buɗe ido ta ganta, dan shi yake yi mata irin wannan wulaƙancin, na haurinta da ƙafa.

“Tashi malama, in nuna miki in da zaki din ga kwana, dan ba zaki kwanar mini a cikin yara ba, ban san irinki ba”

Kai ka ce sokuwa, haka ta tashi, ta ɗaukko jakar kayanta, ta bi bayan farida.

Ɗakin ƴar aiki da yake farkon falon, ta nuna mata ta ce ta shiga a nan zata kwana. Ba ta damu da a yaya ɗakin yake ba, ta je ta kwanta, saboda yanayin jikinta ga rashin lafiya ga gajiyar tafiya, dan haka duk a gajiye take.

Washegari da safe, kowa ya fito falo, rahama ce ta haɗa breakfast, yaran duk sun shirya cikin uniform na makarantar boko.

Abba ya fito ya kallesu ɗaya bayan ɗaya babu ummi, rahama ta gaishe shi ya amsa sama-sama.

Ya kalli farida ya ce “Kawo mini abincina nan”

Haushi ne ya kama ta, yana ganin yadda take fama da ciki, amma ya sakata aiki, bayan ta kai masa kayan abincin ɗaki.

Bayan ta tafi ɗaukkowa, ya kalli intee ya ce “Kirawo mini ummana” intee tayi saroro tana kallon shi.

Ya ce “Ummi nake nufi”

Tunawa tayi da safen nan, ta ji maama da anty rahama suna zancen a ɗakin mai aiki ta kwana, har take gaya musu abun da suka yi mata jiya da daddare suka din ga dariya.

A zaune ta tarar da ummi, ita ummi ɗakin ba ƙaramin kyau yayi mata ba.

Duk da ba wani abu a ciki na burgewa, amma ɗakin ya yi mata kyau.

“Ki zo in ji abba” yarinyar ta faɗa cikin fitsara.

Ummi ta tashi ta bi bayan ta, sai dai farida na ganin ummi kamar taga kashi, ta haɗe rai.

Daga in da suka fito falon, ya fuskanci a in da ummin ta kwana.

Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce “Abba ina kwana?”

“Lafiya ƙalau ummana, ya jikin naki, ina fatan baki kwana da zazzaɓin ba?”

Ta ce “Eh da sauƙi”.

Ya ce “Masha Allah, baki gaisa da maman naki ba, gata nan sunan ta farida, yara na kiranta maama, kema zaki iya kiranta da hakan, ga ƙanwarta nan anty rahama, ga Abdurrahman Abdul, ga inteesar, ga kausar, sai kuma muna jiran unborn baby da maama zata haifa mana. Abdul, intee, kausar kamar yadda na gaya muku jiya, yayarku ce, duk da kai Abdul ka girmeta, amma ku girmamata, ku zauna lafiya. Ummina duk abun da ki ke buƙata, ki sanar da ni, ko maama gidanku ne ki yi zamanki ki kwantar da hankalinki”.

Cikin ladabi ummi ta ce “To Abba” ta kalli farida ta ce “Ina kwana” banza tayi da ummi kamar ba ta ji abun da ta ce ba, ba ta damu ba ta kalli rahama ta ce “Anty ina kwana”

Ba yabo ba fallasa rahama ta amsa mata, abun da farida tayi, ba ƙaramin ƙular da shi tayi ba, bai ce komai ba da kansa ya haɗa wa ummi abun breakfast a abincinsa, ya bata.
Wanda hakan ba ƙaramin tunzura farida yayi ba, cikin ƙulewa take tuna masa yara zasu makara a makaranta, amma ya kada baki ya ce “Ƴaƴanki ne ai ki tarar musu abun hawa ya kai su, ƴa ta zan kai asibiti”

Tsit suka yi suna kallonsa, aka rasa mai magana, ya jira ummi ta gama, ya sakata a gaba suka fice.

Sai da ta kusa kuka, abun ka da mai ciki dama ga zuciya a kusa.

“Rahama ki na kallo daga kawo yarinyar nan, ni zai yi wa wannan wulaƙancin, ya fifita bare a kan yaransa”.

“Kema anty farida you over react, a gabansa ta gaishe ki, ki ka shareta, ai kisan mummuƙe zaki yi mata”.

“Yanzu kwana ɗaya tal a gidan nan ta fara haɗa ni da shi? To wallahi da sake ba zai yiwu ba”

Ran farida yayi matuƙar ɓaci, ta din ga cin alwashi kala-kala na mugunta a kan ummi.

Ya tafi da ita wurin aikinsa, ya kulleta a office ɗin sa, ya je ya gabatar da lectures ɗin da zai yi, wajen ƙarfe sha biyu na rana, ya tafi da ummi kasuwa.

Ya sai heater da nurse ɗin nan ta ce ya saya, ya sai mata phants dozen ɗaya, ya saya mata soso sabulu, brush, manyan jakar omo. Ya saya mata sababbin kaya wasu ready made wasu kuma sai an ɗinka, kasancewar yana da yara mata, kuma shi yake sayen komai na gidan sa, dan haka duk wani abu na ɗawainiyar yara mata ya sani, hatta ɗan kunne sai da ya saiwa ummi, under wear vest duk ya saya mata.
Ya ce suje mota ta zauna ta huta, ya ƙarasa sayayyar, wani irin farinciki ummi take ji, saboda kayan nan da aka saya mata, gani take kamar a mafarki, wai duk wannan kayan nata ne, har da su ɗan kunne da ribbon, ga takalmi mai kyau, ta din ga kwarara masa addu’a a cikin zuciyarta.

Wurin masu sayar da kayan ƙamshi yaje, domin haɗa magungunan da aka gaya masa a yi wa ummi.

Sai dai wasu abubuwan duk ya manta yadda aka gaya masa, mai kayan ya tambaye shi, mai zai yi da su, yake gaya masa ai maganin sanyi za a haɗa.

Kasancewar mutumin sana’arsa ce, sai ya haɗa masa komai da yadda ake amfani shi.

(Previous page, na bayar da magungunan in breif, wasu sun biyo ni suna so, yanzu zan rubuta full yadda ake amfani da su)
_Kanumfari
_Tafarnuwa ƴar kaɗan ba mai yawa ba, saboda idan tafarnuwa ta huda jikin mace, tana sanya warin baki, na jiki har da na al’aura ma, sai dai maganin sanyi ce sosai.
_Tumeric (yellown kur-kur)
_Namijin goro
_Citta mai yatsu
_Lemon tsami

Kowanne za a zuba shi in a moderate amount, lemon tsami babba guda ɗaya mai ruwa ya isa, namijin goron ma za a iya daddatsa shi, yana da ɗaci sosai, tafarnuwa one clove, sai citta mai yatsu madaidaiciya guda ɗaya, sai 1 table spoon of tumeric, sai a zuba ruwa kamar 2cups, a dafa su a din ga sha, za a iya zuba zuma, saboda yana da ɗaci, za kuma a iya haɗe su a mazubi guda, a jiƙa su, su jiƙu sosai a din ga tsiyaya ana sha.

Idan wannan bai samu ba, ana iya jiƙa kanumfari, a din ga sha yana maganin sanyi sosai, amma sai an juri sha.

Sai kuma ana samun saiwar zogale, a ɗaurayeta da ɗan gishiri, a tafasa ta da jar kanwa, a din ga sha, salam yake babu ɗaci, amma yana maganin sanyi sosai.

Sai kuma kama ruwa da ruwan magarya da bagaruwa ba da yawa ba kaɗan a haɗa su a tafasa, ana kama ruwa da shi, ganyen magarya yana gyara jikin mace, mussaman bayan gama al’ada, ayi shaving a din ga kama ruwa da shi, kuma a din ga ɗiga farin miski a kan phant, ba a jiki ba, yana kawar da ƙarni ko wani wari mara daɗi, but mark you ba kowane wari ne yake fita a gaban mace na infection ba, akwai bacterias ɗin da suke wurin wanda ba masu cutarwa ba ne ba, suna haifar da wannan ƙarnin wasu lokutan.
Galibi na infection ko na ƙazanta ya fita daban mussman idan ya haɗa da ƙaiƙayi ko ƙuraje shi ne na infection.

Shi ma wannan warin, ana iya amfani da apple cider vinegar, ruwa kal da hausa, ana zuba tablespoon ɗin sa biyu, a ruwa cikin kofin shan shayi a din ga sha, yana magance warin gaba.

Sai dai dole a kula da abincin da ake ci, domin cin abinci mai ƙarni, ko wari kamar kifi, albasa ko tafarnuwa suna da tasiri a gumin mu da sauran fluids da muke fitarwa a jikinmu.

Kawu yahaya duk ya haɗowa ummi abubuwan da suka kamata, suna tafe yana sake yi mata bayanin yadda zata yi amfani da su.

Sai azahar suka koma gida, sai dai matar gidan bata nan, da kansa ya bi ummi ɗakin masu aikin, ya dudduba abun da babu ya ce zai sayo mata.

Tamkar yar da ya haifa a cikinsa haka yake jin ummi,kuma haka yake burin ta samu lafiya daga wannan ciwon, dan ya san illarsa da hatsarinsa, dan ya san halinsu maza bakomai suke iya jurewa su kawar wa da kai ba.

Ya nuna mata yadda za ta din ga amfani da heater, da sabon flask ɗin ruwan zafi.

Da kansa ya tafasa magungunan, ya zuba mata a jarka, na kama ruwan ya zuba mata a cikin flask ɗin shayi, ya ɗaukko tsintsiya ya taimaka mata wurin gyara ɗakin saboda an kwana biyu ba a gyara shi ba.

Ya je ɗakinsa ya duba bedsheet ɗin da shi ya saya da kuɗinsa, har da bargo ya kawowa ummi.

Ya bata babban gwangwanin turare a cikin nasa ya ce ta din ga fesawa.

Kallonsa kawai ummi take yi, cikin jin daɗi da annashuwa, yadda ya zage yake ta ɗawainiya da ita, daga jiya zuwa yau, idan ta ce ya bari tayi da kanta, sai ya ce mata ai bata da lafiya, kuma cikin barkwanci ya ce mata albarkar ummansa yake nema.

Haka nan ummi ta din ga murmushi tana yi masa godiya.

Ya ce “Yauwwa ummina, Allah yayi miki albarka, saura makaranta ita ma in sha Allah sati mai kamawa, zaki koma makaranta ki manta da duk abu da ya faru, iyaka dai kar ki sake ki gaya wa wani kin taɓa aure kin ji ko?”

Ta jinjina masa kai ya ce “Good, yi wanka ki yi salla, a cikin kayan nan akwai gurasa ki ci kiyi kwanciyarki ki huta”

Murmushin kawai da ya gani a fuskar ummi, ya sanya shi cikin farinciki, kullum yaje ƙauye sai dai ya tarar da ita cikin kuka, sai kuma Murmushin yaƙe.
Hatta yadda zata din ga amfani da banɗaki, sai da ya nuna mata komai.

Fitowa yayi daga ɗakinta, a zuciyarsa yana tawasalli da farincikin da ya saka marainiya yana addu’a Allah ya biya masa buƙatunsa na alkhairi.

Ba yau farida ta fara fita yawonta ba, tun yana faɗa har ya gaji ya daina yi.

Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daɗin jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta ɗauki sabon phanta ta canza.

Wani irin daɗi take ji da nishaɗi, ta sake bubbuɗe kayan da ya saya mata tana jin daɗin hakan.

Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga ɗakin nan ba, dan ta fuskanci ƴan gidan ba ƙaunar ganinta suke yi ba.

Ana kiran sallar la’asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a ɗakin.

Kamar an watso su, taga farida da rahama a ɗakin, hakan ya sanya ta tashi a razane.

Farida ta ce “Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba” a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido.

“Ba dai kawo ki aka yi leƙen asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ƙafarki” idonta ya sauka a kan ƙatuwar ghana must go sabuwa fil.

Ta ce “Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuɗi, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da ƴaƴana, kar ta san kar ai”.

Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants ɗin ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na’ima ta saya mata.

Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ƙullin kayan maganin da ke bayan katifar ɗakin ba, heater da flask ɗin kuma suna cikin banɗaki.

Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata ɗai ɗai.

Sannan ta sake dubanta a wulaƙance ta ce “Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaɓa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ƴar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ƙiri-ƙiri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba.
Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai”.

Rahama ta kwashe da dariya ta ce “Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan baƙi kamar a dangwala”.

“Rabu da ita tashi ki wuce” ummi kaf maganganun su babu wanda ya ɓata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi mata ba, ƙwace mata kaya yafi komai ɓata rai.
Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?.

Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya.

Ummi ko a jikinta, ta durƙusa ta fara wankin kayan nan.
Tas ummi ta wanke su, kasancewar ta riga ta saba da wahala tun a gaban Iya.

Bayan ta gama cike da mugunta, rahama ta ja ta kitchen, ta sakata sassauke kwanukan da sun fi wata shida ba a saukko su an yi amfani da su ba, ta ce ummi ta wanke.
Babu ƙyuya ko ƙosawa ummi ta wanke su.

Duk yadda suka wahalar da ummi a yammacin nan har zuwa bayan isha’i, ko da wasa bata nuna musu gazawarta ba.

Kwanaki uku da zuwanta gidan, rashin mutunci da kyara, haka babar su Abdul suke yi mata, da yaranta da ƙanwarta, kuma wasu lokutan a hana ummin abincin.

Sai dai lokaci ɗaya kawun nata ya rage bata wannan kulawar da yake bata da farko, hakan sam bai damu ummin ba, dan gani take duk wahalar da zata sha, ba zata kai ta gidan Iya da idris ba.

Ranar lahadi suka koma ganin likita, sai dai ummi ta ji daɗin amfani da magungunan nan, dan kuwa sosai yayi mata sauƙi ba kamar da ba.

Likita ya dubata, ya rubuta mata magunguna, Allah ya sa kawu yahaya bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa magungunan da take sha, likitan ya ce ta ajiye su ta gama shan na asibiti, idan suka ƙare ta cigaba da waccan.

Yayi masa godiya suka tafi gida, suna tafe yana rarrashin ummi, yana yi mata nasiha.

Sai da ummi ta yi sati biyu cif a gidan, baban su Abdul ya cewa farida zai kai ummi makarantar su Abdul, amma ta ce ba ta yadda ba, sai dai ya nemi wata mai arha ya kai ummi, dan ba zai dai-daita ta da yaranta ba.

Staff school ya saka ummi, ta nan makarantar da yake lecturing, makarantar islamiyya ma, wata daban ya saka ummi, sai dai makaranta ce mai kyau sosai ana karatu, dan akwai ƴaƴan manya a makarantar.

Duk wanda ya shigo gidan nan ya ga ummi, sai farida ta ce musu ummi sabuwar ƴar aiki ta yi, su yi ta yaba ƙoƙarin ummi, yarinya ƙarama amma ba ta jin jikinta.

Ko da ummi ta fara zuwa makaranta, a nan ɗin ma bata sauya zani ba, saboda ba ta tsira daga cin zarafi daga ɗalibai ba, saboda launin fatarta da ta idonta.
Wahala ta ƙara ƙaruwar mata a ka, ga zuwa makaranta, ga kuma aikin gida tamkar jakarsu.

Hatta rahama idan ta dawo daga makaranta, har wankin phant da brezia haka take watsowa ummi, ƙarewar wulaƙanci har da wando mai jini, sai ta cire ta bawa ummi ta wanke mata.

Iya shege da rashin kunya kuwa a wurin su intee, ba a magana, sai ta gyara wuri su ɓata, idan suka ci abinci sai ta bi ta ɗauke musu kwanuka, sai dai kawu yahaya baya iya magana, yana ji yana gani farida da ƙanwarta suka mayar da ummi baiwa, ban da cin mutunci da wulaƙanci da muzanta halittarta. Dan har haramta mata zaman kan kujerar falo aka yi, wai kar ta shafa baƙi a jikin kujerar.

Abdul ne ma ruwansa da ita, dama shi ba wani magana ya cika yi ba sosai.

Yau ma farida ta tafi gida wai suna biki, ga tsohon ciki, amma kamar akuya saboda gantali, gashi tana cikin watanta na haihuwa.

Daga ummi sai Abdul, sai kuma kawu yahaya da yake gida.

Tana ta aikace-aikace, cikin tausayawa kawu yahaya ya ce “Sannu da aiki ummina, ki samu ki je ki kwanta ki huta”.

Tayi murmushi ta ce “Kawu na kusa gamawa ai”

“Ummi kin daina kirana da Abba dai sai kawu ko?” Tayi shiru tana murmushin yaƙe.

Bayan ta koma kitchen, ya numfasa ya ce “Yaya” Abdul ya ɗago ya ce “Na’am Abba”.

“Yanzu muna tare muna rayuwarmu, gwanin sha’awa kuna rayuwa tsakaninmu cikin jin daɗi, hakan yana yi muku daɗi ko?”

Yayi murmushi ya ce “Sosai makuwa Abba”.

“Allah sarki, kamar haka idan Allah ya so, a kowane lokaci zai iya raba mu, muna raye ba tare da wani ya mutu ba, amma zai iya rabamu, kamar yadda ya ɗauke mahaifin ummi, ya rabata da mahaifiyarta, ya kawota zama a cikinmu. Ina kallon duk abun da mamanku take yi wa yarinyar nan, da ita da ƙannenka, ko ban ce komai ba, Allah yana kallon komai, dan Allah ko daga ɓangaren ka ne ta samu sassauci, ba dan Allah baya son ta ya ɗauki mahaifinta ba, ya kawota cikinmu ba, zaka so ayi treating ɗin ƙannenka kamar yadda ake treating ɗin ummi?”.

Jiki a sanyaye Abdul ya girgiza kai.

“To dan Allah ka din ga nunawa ƴan uwanka, ummi mutum ce, kuma ƴa ce kamar ku, muzanta ta da bautar da ita, ba shi da wata fa’ida” ya din ga yi wa Abdul nasiha, sai duk jikinsa yayi sanyi.

Sai dare sannan suka dawo, suna dawo gidan kamar sun dawo da dauɗa, suka cire kaya suka zubar, suka ci abinci suka baje kwanuka.

Abdul ya tarar da ita a kitchen, tana ta wanke kwanukan da suka ci abinci, ya kalli ummi ya ce “Ki je ki kwanta, yakamata ki huta”.

Ummi ta ce “Kwanukan nan zan ƙarasa wankewa”

Ya ce “Bari na tayaki”

“Maza basa wanke-wanke”

Tun da ta zo gidan nan, maganar kirki bata taɓa haɗa su ba, ba ruwansa da ita, dan haka yau tayi mamakin cewa da yayi zai taya ta aiki.

Shi dai tun da Abba yayi masa wannan nasihar ɗazu, gaba ɗaya sai tausayin ummi ya kama shi.

Kallonsa take yi tana mamaki, yadda yake kikkife mata kwanukan, ummi sai cewa take yi ka bar shi fa yaya Abdul.

“Uban me ka ke yi a kitchen ɗin nan?” Rahama tayi maganar tana shigowa hannunta riƙe da indomie.

“Aiki nake taya ta”.

Ta watsawa ummi indomie, ta ce idan ta gama, ta dafa mata guda biyu.

Ko da wasa ummi babu alamar gazawa a fuskarta, ta dafa mata indomie, Abdul yana biye da ita, ta gama yayi zaton kwanciya ummi za ta yi, amma ta kwaso uwar guga ta hau yi, kayan su na babarsu da na rahama.

Abdul ya zuba mata ido, tana ta sauri ta kammala gugar, dan tana da assignment, tana yi yana ƙoƙarin yi mata hira, amma kasancewar ba sabawa suka yi ba, ya kasa ya saukko ya ce bari ya taya ta.
Ba iya gugar yayi ba, ummi tana nuna masa yadda zai yi, sai dai bisa tsautsayi Abdul ya ƙona rigar babarsa, ta lace babban lace ba ƙarami ba.

Hakan yayi dai-dai da fitowar rahama, ta gansu a tare Abdul da dutsen guga. Ta buɗe murya ta ce “Anty farida, zo ki ga bariki, aikin da ake sakata take rabawa da ƴaƴan gida”.

Abdul ya ce “Ni ne na ce zan tayata fa”

Farida da ƙyar ta ƙaraso falon, saboda ciwon baya da mara da take yi.

“Uban me ka ke yi a nan a wannan daren?”.

Ya ce “Bakomai”.

“Tashi ka wuce ka je ka kwanta” ya tashi ya nufi hanyar ɗakinsa.

Idonta ya sauka a kan rigar leshinta, da sawarta uku an ƙona rigar.

Ashar ta lailayo, ta ɗago rigar ta ce “Rigar ta wa ki ka ƙona mini? Dan ubanki dan baki da mutunci ba ki da hankali?”

“Anty dan Allah ki yi haƙuri, tsautsayi ne, ban san zata ƙone ba”

“Wallahi sai na ƙona ki da iron ɗin nan, ke wallahi sai na fanshe rigata, kut lallai baki da hankali”

Miƙews ummi tayi, ta fara kuka tana bata haƙuri, amma rahama ta danƙota, ta danne ta farida ta sake jona iron ɗin ya ɗau zafi, ta nufo ummi.

Ayshercool

CUTARWA!

P15

Ihu ummi take yi, tana yi musu magiya su yi haƙuri, amma cike da mugunta da zalunci, rahama ta danne ummi a ƙasa, ta cusa mata ɗan kwali a baki, ta yadda sautin ihunta ba zai fita sosai ba, ta ɗage wa ummi riga, farida ta din ga nana mata iron ɗin nan a cikinta da zafinsa da komai.

Wata irin miƙa ummi take, saboda azabar da ta ratsata, take ta saki fitsari, saboda azabar zafi da ya ratsa ta.

Abdul har ya je ɗakinsa ya tuna ya ƙona rigar maama, kuma ƙila ummi zata hukunta, dan haka ya juyo da sauri, ya dawo falon.

A gigice ya ƙarasa wurin, ganin bala’i da izayar da ake yi wa ummi.

“Maama dan Allah ku bari, ba a yi wa mutum azaba da wuta”.

Fitsarin da ummi ta saki, ya sanya rahama cikata, ta rufeta da duka, saboda ta ɓata mata jiki da fitsari, ta fizge hijjabi da hular kan ummi, a take dogon gashin ta mai matuƙar santsi ya zubo har fuskarta.

Rahama ta ce “Kut, wannan gashi ko attach” tayi maganar tana jan gashin ummi da ƙarfin gaske, ummi jikinta ya din ga rawa, ta kasa ihun saboda azaba, ta riƙe gashinta da rahama ta cika hannu da shi.

Abdul ya fara ƙoƙarin ture rahama daga kan ummi, farida ta kai ƙafa zata daki ummi, ta zame da ruwan fitsarin da ummi tayi, ta faɗi.

Wani irin ihu ta kurma, rahama ta ɗaga ummi, ta nufeta a gigice, ummi ta samu ta lallaɓa ta tashi da gudu, ta tafi ɗakinta.

Banɗaki ta shiga, ta cire rigarta ta din ga zuba ruwan famfo a cikinta, tana jin tamakar wurin ci yake yi da wuta, ga wani irin azaba da kanta yake yi, har wani jiri take ji.

Kan ka ce kwabo jini ya fara zuba daga jikin faruda, jikinta ya fara kakkafewa, rahama ta ce “Abdul yi sauri ka je ka taso abbanku” Abdul ya tafi da gudu ɗakin da mahaifinsa yake ta bacci, saboda a gajiye yake sosai, duk wainar da ake toyawa bai sani ba.

“Abba, Abba ka tashi maama ta faɗi ƙasa”

Da ƙyar ya buɗe ido, ya kalli Abdul ya ce “Meyafaru?”

“Maama ce ta faɗi a falo” agogo ya kalla, ɗaya saura na dare, me ta je yi falo a yanzu?”. Ya saukko daga kan gadon, suka fito falon tare, falon sai ƙauri yake yi saboda iron da aka bari a jone.

Jini take zubarwa sosai cikin gushewar hankali, da sauri kawu yahaya ya ɗaukko mukullin motarsa, da ƙyar suka ɗaga farida, saboda nauyin cikin ta suka bar Abdul a gida suka tafi asibiti.

Ummi ba ta san abun da ake ciki ba, tana can tana jinyar cikinta da suka ƙona da dutsen guga.

Ta zauna ta yi shiru tana ta tunanin, me ta aikata da ya sanya kowa ba ya son ta ji daɗi, kowa babban burinsa shi ne ya ga ya cutar da ita ta yi kuka?

Ta ɗauki vasaline ta shafawa wurin, duk da haka sai da ya fara ɗurar ruwa, duk fatar cikin ta tashi.

*
Idiris a tunaninsa tafiyar ummi, shi ne samun sassauci a gare shi, ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda.

Hashim kuma Iya ta sako shi gaba da cin mutunci, ko gaisuwarsa ta daina amsawa, saboda haushin gayawa kawu yahaya abun da ake ciki da yayi, ya sanya yahayan yana yi musu kallon azzalumai.

Idiris ya lallaɓa ya cigaba da zuwa wurin hindu, yana son ya hilace ta su aikata alfasha, tun da iyayenta sun ƙi ya aureta.

Gulmace-gulmace suka din ga yawo, a kan azabtarwar da Iya ta yi wa ummi, da wanda idris ya yi wa ummin, tare da ƙoƙarin bankaɗa asirin dalilin da ya sanya aka fasa auren idiris da hindu, ana ta zaginsu a unguwa, aure wata ɗaya ya mutu.

Haka nan sai ummi ta din ga yi wa Idris gizo, idan ya je gidan da suka zauna.

Ko kuma yayi ta mafarkinta tana yi masa mugun kallo tana kuka. Gashi duk wannan abun da ya faru, ya kasa daina jin sha’awar ummi, ya kuma kasa manta yadda jikinta ke da matuƙar taushi kamar auduga.

Tun da yake leƙe-leƙnsa, bai taɓa taɓa mace mai laushin fatar ummi ba, gashi dai ko man shafawar kirki ba ta da shi, amma fatarta har wani irin santsi take yi.

Ya din ga tuhumar kansa, da ganin wautar sa na kasa daurewa ya sauke abun da yake damunsa game da ummin kan su rabu, amma da ya tuna annakiyar dauɗar da ke jikinta, da kuma warin da take yi sai yayi tsaki.

A rashin ummi ya cigaba da ƙoƙarin hilatar hindu, yayi lalata da ita, hindu yarinya ce ƴar shekara goma sha shida, gidan su suna da tarbiyya sosai, dan haka sai wahalar da Idiris take, taƙi bashi haɗin kai, sai dai tana matuƙar ƙaunar idiris.

*
Likitoci suka rufu a kan farida, ana ta ƙoƙarin ceto ranta, sai dai jini yaƙi tsayawa, ƙarshe aka ce tiyata za a shiga da ita da gaggawa a cire mata cikin, dan ta fara jijjiga ga jini ya ɓalle.

A daren aka shiga da ita tiyata, aka ciro ƴa mace, sai dai ba ta san in da kanta yake ba, har aka fito da ita.

Ita kanta yarinyar taƙi yin kuka, aka yi ta fama, sai dai tayi kaɗan tayi shiru, ga rashin isashiyar oxygen a jikinta sai da aka saka mata oxygen.

Rahama ta din ga kuka, tare da ɗora zargin hakan a kan ummi, sai dai ta yi shiru ba ta gaya wa baban su Abdul abun da ya faru ba.

Abdul kuwa a gida aka bar shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, mussaman yadda ya kasa manta ganin jini na zuba a jikin.

Ummi bacci sai ɓarawo ya kwasheta, shi ma a rigingine ta kwana.

Da asuba ta tashi tayi salla, fatar cikinta duk ta ɗaga tayi wani iri, saboda ƙuna.

Bayan ta idar da sallar, ta lallaɓa ta fito falon, ta tarar da wurin duk jini, ga kayan gugar duk a watse a wurin, tsaf ta gyara wurin ta kwashe kayan gugar, ta shiga kitchen, ta ɗora ruwan shayi, sai lallaɓa jikinta take yi, saboda raɗaɗin da take ji a cikinta.

Ta sake fitowa falo, ta tarar da Abdul a tsaye yana kallonta.

Ta kalleshi ta ce “Yaya Abdul”.

“Na’am, ya jikin wurin ya ƙone?”

Ta ce “Eh, amma ba sosai ba”.

Ya ce “Maama fa a asibiti ta kwana”

Zaro ido ummi tayi ta ce “Meya sameta?”.

“Faɗuwa tayi” yayi maganar cikin damuwa.

Sai a lokacin ummi ta tuna taga farida ta zame ta faɗi, ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, to yanzu ya jikinta?”.

“Nima ban sani ba, tun da suka tafi basu dawo ba”.

Ummi ta ce “Allah ya sa tana lafiya”.

Ya amsa da amin.

Suna tsaye suna jajantawa, sai ga Abba yayi sallama, duk suka zura masa ido suna yi masa sannu da zuwa.

“An yi wa mamanku aiki, an ciro baby girl, sai dai dukkannin su, they are under special care, duk basu da lafiya”

Ummi ta ce “Subhanallah, Allah ya basu lafiya”.

Ya amsa da “Amin, ummina na san kin yi breakfast, ki zuba wani a flask a kai musu asibiti, ku shirya na ajiye ku a makaranta, ina su kausar?”

“Ba su tashi ba”
“Kamar yaya, ƙarfe bakwai saura, ba zasu makaranta bane?” A fusace ya nufi ɗakinsu, ya taso su da bulala.

Ƙarshe dai sai da suka makara, jin mamansu na asibiti, ya sanya suka din ga kuka, haka ya kai su makaranta ya wuce asibiti.

Gumin da ummi take ta yi, ya din ga taɓa wurin ƙunar nan, ga kuma rigar makaranta, hakan ba ƙaramin takurata yayi ba.

Sai dai duk da abun da farida da ƙamwarta suka yi mata, tunaninta yana kan yaya jin faridan yake.

Kasancewar rahama ce a can asibiti tare da farida, sai ya zamana kusan kula da ragamar gidan yana hannun ummi, kai ba ka ce babu mace a gidan ba, duk aikin gida ita take yi, har kawunta sai da ya yabawa ƙoƙarin ta tare da jinjina mata, dan hatta abincin da za a kai asibiti ita take dafawa.

Gefe guda Abdul ne yake takawa su intee burki, dan tana yi musu wahala amma ba sa gani, dan sai suka tsiri cewa ai anty rahama ta ce musu, ummi ce ta saka mamansu ta faɗi, su yi ta yi mata rashin mutunci da wulaƙanci.

Kwanan farida biyu a asibiti, aka samo kanta da ƙyar, kawu yahaya ya ɗauki su ummi ya tafi da su asibitin dubata.

Sai dai yanayin kallon da ƴan uwan farida ke yi mata, ya sanya ta sha jinin jikinta, dan ko sannun da tayi wa faridan ba ta amsa ba. Tana kwance jaririyar a kusa da ita, ana ƙara mata jini. Sai dai kasancewar babansu Abdul yana wurin, ba su iya ce wa ummi komai ba.

Ummi fa ƙuna ta din ga jagwalewa, ga ƙaiƙayi tana yi mata, ta tuna ta taɓa ƙonewa a ƙafarta lokacin tana ƙauye, na’ima ta din ga shafa mata zuma, dan haka ta cewa baban su Abdul, ya sammata zumar da yake shan shayi.

Yayi murmushi ya ce “Zumar da gata nan kaya guda, ai ba sai kin tambayeni ba ummana” ta samu abu ta tsiyaya take amfani da ita a ƙunar, dan har wurin cibiyarta ta ƙone.

Kwanan farida biyar a asibiti aka sallamo su, babu tsammani ummi ta dawo daga makarantar boko ta dawo ta tarar an cika gidan.

Ta ƙarasa falon ta durƙusa tana gaishe su, sai dai basu amsa ba, rahama ta janyo hijjabinta har tsakiyar falon ta ce “Kun ganta nan azzaluma, ita ta kusa kashe anty farida, ita ta kayar da ita”

“To ai da farida cewa tayi mai aikinta ce”.

“Ba ƴar aiki ba ce ba, ƴar wan maigidan nan ce”.

Ƙanwar babansu farida ta ce “Kuma shi babu matakin da ya ɗauka?”

Farida na daga kwance ta ce “Wane matakin zai ɗauka, kin ga faman da nayi a kan ba zan zauna da ita ba ya dage, ni kuwa na samu ƴar aiki”

“Aikuwa idan baki yi hankali ba ta kashe ki wataran”.

Ummi tayi shiru ta sunkuyar da kai, wata yayar su ta dunƙule hannu, ta ɗirka mata duka a tsakiyar ka ta ce “Wallahi da kin kasheta, sai kin yi prison daga ke har ubanki”.

Rahama ta ce “An ce ubanta ya mutu ai”.

“Matsiyaciyar yarinya da ya bar wata tsiyar, da ba a ganki a nan ba, har ki ke ƙoƙarin kashe mana ƴa, ni wannan anya ma ba mayya bace ba, kalli ƙwayar idonta fa”.

Wata a gefe tayi caraf ta ce “Wace iri ce? Turo mini ita nan, ai ni ina gane maye”

Matar ta ja ummi kamar tana jan shara, ta dungurarwa da ɗaya matar ita, tuni ummi ta fara kuka, ga zafin duka ga na cin mutunci.

“Ke ɗago idonki na gani”

Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa ɗagowa.

“Ba zaki ɗago ba sai na mareki” ummi ta kasa ta sake fashewa da kuka.

Aikuwa matar nan babu tsoron Allah, ta sauke wa ummi yatsunta a fuska iya ƙarfinta, sai da ta hantsula gefe.

“Wallahi zata iya yiwuwa mayya ce, tun da ta kasa haɗa ido da ni, shegiya ga baƙi kamar ƴar maƙera”.

Suka ciwa ummi mutunci son ransu saboda abun kunya, da yawansu zasu haifi ummi, amma kasancewar ba ƴar su ba ce ba, suka din ga muzanta ta suna aibata ta.

Tayi kukan da tun da aka kawota gidan ba ta yi irin sa ba, har ta fara tunanin ko roƙon kawu yahaya za ta yi, ya mayar da ita ƙauye.

Sai dai gabanta ya faɗi, da tuna irin azabar da ta sha a ƙauye, da sauri ta girgiza kanta, har da istigfari, ta fara ƙoƙarin auna zaman nan da na can wanne yafi sauƙi.

Duk zaluncin iya, ba ta taɓa ƙonata da wuta ba, illa iyaka duk laifin da tayi jikinta zai gaya mata.
Nan kuma duk rintsi, ko ba a bata abinci sau uku ba, ba zata kwana da yunwa ba, kuma tana da kayan makaranta da na sawa duk da babu yawa, kuma tana da takalmi da sauran abun da ba a rasa ba.

“Mama meyasa ba so na ne? Laifin me nayi, meyasa idona yake ba kalar na mutane ba? Duk abun da nayi mutane sai sun tsaneni, ko a gida ko a makaranta?” Tayi maganar tana ganin fuskar mariya a idonta, tana jin tamkar ta ga mamanta ta bayyana.

Tayi kuka ta gaji, ta duba sabulun wankanta ya ƙare, tayi wankan a haka, ta shirya islamiyya, ta fice ba tare da kowa ya sani ba.

Dama kuɗin motar zuwa islamiyyar ma, idan kawu yahaya yana nan, yana bata ko ya bawa farida ta bata, idan ta ga dama ta bata, ko taƙi bata wanda zai ishe ta shima saboda ta na biyawa ɗaukko su intee daga ta su makarantar islamiyyar, dan Abdul ba lokaci ɗaya suke tashi ba, sai ƙarfe shida, su kuma tun huɗu da rabi ake tashin su.

Dan haka ummi tafiyar ƙafa ta sha, kan ta je makarantar, nan ma da ta je sai da aka daketa dan ta makara.

Zama tayi, tayi shiru a ajin, dan kamar yadda ta saba, bata da ƙawaye, dan ba ta son shiga cikin su su tsokane ta.

Haka kurum ta ɗan shagala da kallon yarinyar da take jin tsoro a ajin, mai suna maryam saboda hantararta da take yi tana kyararta, da nuna mata tsana ƙarara a fili.

Tubarkallah maryam fara ce sol, irin fulnin nan masu dogon hanci, sai azabar iyayi da iya gayu, da yawa ƴan ajin na tsoronta, saboda azabar masifarta da rashin son rai ni.

Ba tsammani ummi ta ji ta ce “Ke lafiya ki ke kallona kamar zaki cinye ni?”

Da sauri ummi ta ɗauke kanta tare da cewa “Yi haƙuri”

“Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ki ka bayar? Bana son kallo”

“Ai na ce kiyi haƙuri” ta faɗa a sanyaye.

A ranta ta ce ‘Dama nima fara ce, wataƙila da ba za a tsane ni ba. Amma ai akwai baƙaƙe da yawa da ake son su, ni meyasa ba a sona?’ ta tambayi kanta, wasu hawayen na rige-rigen zubowa.

Maryam ta zauna a kusa da ummi, ko a jikinta ganin ummi ta kifa kanta.

Sai da malami ya shigo ajinsu sannan ta ɗago kanta, ya yi musu karatun da zai yi musu, sannan ya basu class work.

Sai dai fa maryam ba ta iya komai ba, ta din ga rarraba ido, ga malamin ya jaddada cewar duk wanda ya faɗi sai ya zane shi.

Ganin lokaci ya kusa cika, ya sanya ummi buɗe mata takardarta ta ce “ki kwafa ya kusa karɓa” babu kunya maryam ta kwafe duk abun da ummi ta rubuta.

Lokacin sallar la’asar yayi, ɗalibai na ta ƙoƙarin fita daga ajin, ba tare da tuna alkhairin ummi ba, maryam ta hankaɗeta zata fita, bisa tsautsayi ummi ta faɗi ta fama ƙonuwar da take cikinta.

Ƙara ta saki, tana girgiza kanta, duk ɗaliban suka tsaya suna kallon ummi, ganin jini yana tsatstsafowa a rigar uniform ɗin ta.

Maryam a tsorace ta ce “Na shiga uku” ta durƙusa ta ɗago ummi, a zaton ta ko cikin ummi ne ya ɓule.

Ummi sai yarfe hannu take yi tana kuka, ɗalibai suka taru a wurin, malamin da ya fita daga ajin ya dawo ganin ɗalibai a wurin yana tambayar meyafaru, aka gaya masa maryam ce ta hankaɗeta ta faɗi.

Cikin tashin hankali ya ce a kai ummi ofishin malamai, ita ma maryam ta bisu sai an hukunta ta.

Cikin tashin hankali malamai mata suka ɗaga rigar ummi, ana ƙoƙarin gano menene yake jini a cikinta, sai dai ba kyan gani, suka tarar da ƙonuwar ta jagwale, ga ruwa ga jini ya dame da zumar da take sakawa.

Maryam na ganin haka ta fashe da kuka, ta zata duk faɗuwar ce ta janyo haka.

Shugaban makarantar ya dubi Maryam ya ce “Wato maryam ba kya ji ko? Zaki gane kuskurenki, sai kin daku yau ɗin nan, makauniya ce ke da zaki tureta ta faɗi”.

Malamin ya dubi ummi ya ce “Ke ya aka yi ki ka zo da wannan ciwon makaranta, meya sameki haka?”

“Ba maryam ce ta ji mini ciwon ba, dama na ƙone a gida”

“Da me ki ka ƙone, kuma an kai ki asibiti?”

Ta ce “Eh an kaini”

“A’a wannan da an kai ki asibiti, da ba ta jagwale haka ba, kuma da ba a bari kin saka kaya ba, ki gaya mini gaskiya da me ki ka ƙone?” Malamin yayi maganar cikin zare ido.

“Da ruwan zafi”

“Mamanki ta san kin ƙone?” Ta girgiza kai alamar a’a.

“Meyasa baki gaya mata ba?”

Cikin kuka ta ce “Ai ban san in da take ba”

“A’a to ina mutanen gidan da ki ka ƙone ɗin, ba ƴar gidan dr. Yahaya bace ne?” Ta ɗaga kai alamar eh.

“Malama zuhra, a nemo abun hawa a kai yarinyar nan asibiti a dubata, ke kuma maryam mu je office ɗina sai na hora ki”

Maryam ta fashe da kuka tana magiya, cikin ƙarfin hali ummi ta ce “Malam dan Allah kayi haƙuri, ba ta san ina da ciwo ba, na yafe mata ai”

Ya ce “To zan duba, tashi a kai ki asibiti, daga nan a mayar da ke gida”.

A asibitin ma, ma’aikaitan sun yi faɗa sosai a kan sakaci da lafiyar ummi, dan da ƙunar zata iya zama infected ta taɓa sauran sashin jikinta, bayan ta zama gyambo.

Suka ce lallai a kula da ummi, a samu ƙunar ta warke, kuma a zurfafa bincike dan wannan ƙunar ba tayi kama da ta ruwan zafi ba.

Ummi ta sha kuka, saboda yadda aka dirje ƙunar nan tas, aka saka magani, aka bata magungunan sha.

Sai dai da malama zuhra ta ce ta kwatanta musu gidansu a mayar da ita ta ce “A’a a mayar da ni makaranta, idan aka tashi zan ɗaukko ƙannena daga islamiyya”

“A haka da wannan ciwon” malamar tayi maganar tana kallon ummi.

Ummi ta jinjina mata kai.

“A’a ba zai yiwu ba, mu je gidan naku, a saka wani ya ɗaukko su”.

Kuka ummi ta fara tana yi wa malamar magiya, a kan ta ƙyaleta a tashi ta ɗaukko su daga makaranta.

Ba ta da zaɓi, suka koma islamiyyar ta gaya wa shugaban makarantar duk abun da ya faru.

Suka yi waya da kawu yahaya, suka tattauna, ya ce a mayar da ummi gida, zai yi waya makarantar yaran, su jira yayansu sai su taho tare.

Da ƙyar ta yadda da hakan, saboda tana tsoron abun da ka iya biyo bayan rashin ɗaukko su daga makarantar.

Cikin sa’a malamar ta fuskanci yanayin da ummi take ciki na tsoro, dan haka a ƙofar gida suka yi sallama ummi ta shiga.

Har ta tafi ɗakinta ba wanda ya san ta dawo, saboda ana ta hada-hada a gidan, ƴan barka na shige da fice.

Ta kasa fitowa daga ɗakin, saboda tsoron kar su kuma dukanta.

Sallamar kawu yahaya ta ji a ɗakin, ta tashi da sauri, tana gaishe shi.

“Ya jikin naki?”

“Da sauƙi”

“Mu ga ciwon” a hankali ta ɗaga masa cikinta ta ƙonu sosai da sosai, ya zubawa ƙunar ido sannan ya kalleta ya ce “ya aka yi ki ka ƙone?”

“Da ruwan zafi” ta faɗa tana ƙiƙƙifta ido, saboda ta san ƙarya tayi.

“Meyasa baki gaya mini ba?” Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Wannan ƙunar ba ta yi kama da ta ruwan zafi ba, ki gaya mini gaskiya.

“Da gaske nake…” Ba ta ƙarasa ba ya ce “Shaidar iron tayi, kalli yadda shape ɗin ƙonuwar ya tafi, ki gaya mini gaskiya”.

Ta ɗan yi jimm sannan ta ce “Idan na gaya maka ba zaka gaya wa maman su Abdul ba?”

“Ba zan gaya mata ba”

“Ina guge Abdul ya ce zai tayani, ya ƙonawa mamansu riga, ta zata nice shi ne anty rahama ta danneni, suka ɗora mini iron. Dan Allah Abba ka gaya musu bani na saka anty farida ta faɗi ba, sun ce ni na kusa kasheta wallahi ba ni ba ce, fitsari na yi da na ji zafi, shi ne ta zame ta faɗi” tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ayshercool

                         CUTARWA

P16

P16

Ƙurriii kawu yahaya ya yi wa ummi da ido, abun ya girmame shi, bai taɓa zaton mugunta da zaluncim da farida za ta yi wa ummi zai kai haka ba.

Ya sauke numfashi da ƙyar ya ce “Ya isa haka ki share hawayenki, ki daina kukan ya isa ba zan gaya mata ba, kuma na san ba zaki taɓa iya cutar da kowa ba, duk wanda ya cutar da ke, shi ma Allah ba zai bar shi ba, ki yi haƙuri ummi, in sha Allah gobe in Allah ya kaimu zamu koma asibiti, tun da yau an yi dressing ɗin.

Mun yi magana da malaman islamiyyar ku, na biya kuɗin maganinki, sannan sun ce ki zauna a gida sai kin warke”.

Ummi kamar ta ce masa gara ta cigaba da zuwa a haka, dan ta san zamanta a gidan nan ba hutawa za ta yi ba, amma ta dake ta ce “To kawu na gode sosai”

“Kar ki damu, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana ummana”

Murmushi ummi tayi, tana so ta ji ya kirata da ummana ko ummina, hakan yana yi mata daɗi, kuma yana tuna mata da maman da babanta.

Ya ce “Au, na manta ban gaya miki ba, mun kusa komawa sabon gida fa, bamu taɓa zuwa kin gani ba ko”

Ta faɗaɗa murmushin ta ta ce “Allah ya nuna mana, wannan wa za a barwa, na ga shima mai kyau ne”

“To ko in bar miki, tun da kin fi son nan?”

Murmushi ta yi ta ce “Ai ni macece ba zan iya zama a gida nikaɗai ba, amma ina son gidan nan”

“Can yafi kyau ai, idan muka koma zaki gani”

“To Allah ya sanya albarka, to nan su iya ne za su dawo su zauna?”

Sai da ya ƙara kallonta da sauri, ya ce “Su iya kuma?”

Ta ce “Eh, su baro ƙauye su shiga makarantar islamiyya, makarantar mu har da matan aure da tsofaffi suna zuwa asabar da lahadi”

Bakomai a ranta ta faɗi hakan, kawu yahaya yayi murmushi saboda magana tayi cikin magana mai ma’ana, ba zaka san ummi na magana ba, sai ka zauna da ita, a haka kamar ba ta magana.

Sai kuma ta sake cewa “Kawu, kaga da ka san in da mama take ita ma zaka ɗaukkota ka dawo da ita nan? Sai mu zauna ni da ita a gidan nan sai ku koma sabon gida”

Tausayin ummi ya kama shi, ya ce “Ki na kewarta ko?”

Ta jinjina masa kai alamar eh.

“In sha Allah zan nemo in da take, zan haɗa ki da ita, sai dai ba zan so na kawo ta nan ita ma ta din ga shan wahala kamar yadda ki ke sha ba”

“To ai ba zan bari ta sha wahala ba, ni zan din ga yin duk wani aiki, idan na iya sana’a na din ga saya mata abubuwa, idan ka gano ta dan Allah kar ka kai ta wurin Iya, Iya ta ce ba ta son ta, wai mama mayya ce…”

“Ummi ya isa haka, ki daina tuna abubuwan da suka shuɗe wanda za su dinga ɓata miki rai, ki yi karatu sosai yadda maman idan ta gan ki za ta yi alfahari da ke”

Ta gyaɗa masa kai ta ce “In sha Allah” kai da ganin yadda ta ɗan kwaɓe fuska, ka san akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta da take burin amayar da su, sai dai babu wanda zai tsaya ya saurareta, to wa ma ya damu da ya zauna da ita balle aji matsalarta.

Cikin son kawar mata da wancan tunanin, ya yi murmushi ya ce “Ki na buƙatar wani abu ne ummana?”

“A’a bana son komai”

Ya ajiye mata ɗari bibbiyu guda biyar, ya ce “Gashi idan kina buƙatar wani abun ki yi amfani da shi”.

Kallon kuɗin ummi take yi dan da yawa a wurinta, kan tayi magana ya tashi ya fita, zuciyarsa na yi masa zafi.

Ɗakin farida ya wuce kai tsaye, ya tarar da ita tana saka kaya a gaban mudubi, ta ɗago ta kalleshi ta ce “Ya dai?”

A take ya nemi karsashinsa da zafin zuciyar da ya zo da ita ya rasa, duk yadda ya so yi mata magana a kan ummi, sai ya kasa kawai ya tsaya yana kallonta.

“Kana buƙatar wani abu ne?” Kawai ya girgiza mata kai ya juya ya fice, yana jin baƙin cikin kasa yi mata magana a kan cin zarafin da ta yi wa ummi.

Duk da ƙonuwar cikin ummi, haka ta cigaba da yin aikace-aikacen gidan, kuma muddin ta fito ƴan uwan farida suka ganta, sai sun ci zalinta, ko sun aibata ta.

Hatta makarantar boko, kawu ya hanata zuwa, ya ce sai ta samu sauƙi tukuna.

Dan haka, a hakan take naɗe rigar ta, ta bar wurin ƙunar a waje tana shan iska, tana aikinta.

Abdul ne kawai yake tausaya mata yake yi mata sannu, dan shi har ga Allah yake jin matuƙar tausayinta.

Mopping kuwa a rana a gidan nan, sai tayi sama da sau sha biyar, wanke-wanke kamar gidan da ake rabon sadaka, banda ɗorawa da saukewa da kula da yaran baƙi, tana yi ana zaginta.

Wani lokacin haka zata fama ƙunar tayi ta kuka.

Kawu yahaya ya din ga kai ta dressing, Allah ya taimake ta ƙuna ta fara warkewa. Tana matuƙar son ta ɗauki jaririyar da antyn ta haifa, sai dai an ƙi bata damar hakan, daga nesa take hangen ƴar, zuciyarta har raya mata take ta ce a bata ta ɗauketa, amma da ta tuna hakan na iya haifar mata da cin mutunci, sai ta haƙura.

Farida ta je ta tarar da mijinta a bedroom ɗin sa, yana ta aikin takardu.

Ta zauna tana cika tana batsewa ta ce “Dr. Wurinka na zo”

Ba tare da ya ɗago ba ya ce “Ina jin ki”

Ta ɗan taɓe baki ta ce “Jibi in Allah ya kaimu ne fa suna, haryanzu baka ce mini komai ba, baka bayar da kuɗin hidimar suna ba, kuma wuri nake so a kama ka sani, amma ka ƙi magana”.

“A wannan karon babu suna, sauran ukun da aka yi Allah ya amfana, idan Allah ya kawo wata a gaba ayi”.

A fusace ta ce “Ban fahimta ba?”

“To ki jira daga lokacin da ki ka fahimta, sai ki tashi ki bani wuri”

Ta miƙe tsaye ta ce “Yahaya ni zaka wulaƙant, na gama gaya wa mutane da taron suna ka ce ba za ayi ba”

“Hakika kawai zan yi, za a kawo raguna biyu manya, ayi hakika na sanyawa yarinya mariya, sai ki koma ki gaya wa mutanen babu suna”

“Mariya kuma? Wace irin mariya ana zaune ƙalau, sunan uwar waye mariyar da zaka sanya wa ƴa ta, haka muka yi da kai? To ba gara Salman da na ce bana so ba, a kan wata mariya, kamar dattijuwa”

Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce “To ki koma ki bibiyi tarihin fiyayyen halitta, zaki gane suna ne mai daraja da ma’ana”.

Aikuwa ta hau ta din ga surfa bala’i, duk yadda ya yi ƙoƙarin sanar masa da cewa, hukuncin zaluncin da ta yi wa ummi ne, ya sanya ya hukunta da haka ya kasa, saboda tuni ta kai sunansa wurin malamai, a kan ko ya mayar da ummi, ko kuma duk izayar da zata yi mata ba zai iya magana ba, yarinyar ta gaji ta bar gidan.

Tun a haihuwar inteesar, ya so saka mata sunan mahaifiyarsa Salma, farida ta ce ba ta san zancen ba, ba ta so, aka saka sunan ta ta uwar, haihuwar khausar ma, ta ce sunan yayarta da ta rasu za a saka, wannan ma suna ta kai ruwa rana a kan ita gaskiya ya bari sai wani lokacin a saka Salman, tun da sanyan wa ƴaƴa sunan iyaye ba wajibi bane ba, wai Jidda za a sakawa yarinyar, tana son sunan.

Shi kuma ya sanyawa yarinyar mariya, sunan mahaifiyar ummi, wanda ita Farida sam hankalinta bai kai kan cewa sunan babar ummi bane ba.

Ya fice daga ɗakin ya bar ta tana ta sababi da kumfar baki, ya zo falo ya tarar da ƴan uwan farida na ta cin abinci da lemuka da nama zuƙu-zuƙu.

Ga ummi da ɗagaggiyar riga, tana ta mopping, tare da haɗa kwanukan da suka ɓata, sai ta kwashe zata tafi, sai a kirata a jefa mata wani kwanon.

Gyaran muryar da yayi ne ya sanya duk suka juya, mai neman gyale nayi su rufe jikinsu, masu gyara zama na yi.

“Yauwwa, ina godiya ga Allah subhanahu wata’ala, da kyautar haihuwar mace da ya bani, ina kuma godiya a gareku wurin tsayawa tsayin daka, wurin kula da ƴar uwakku, duk da hakkina ne. Ina godiya sosai, dan Allah idan kun gama cin abincin, zaku iya tafiya gida, rahama zata iya cigaba da kula da ita. Ba za a yi taron suna ba, ga yanayin rayuwa, gara a tattala kuɗin tayi jego mai kyau, kuna iya tafiya idan kun gama kan magariba dan Allah, sunan jaririya mariya, za a dinga kiranta da noor”

Gaba ɗaya turus suka yi suna kallonsa, tun da suke zuwa gidan, su yi duk hauka da rashin hankalin da suke so, bai taɓa yi musu magana ba, sai yau, dan maganar tasa ta wani fannin kamar cin fuska.

Ummi kuwa washe baki tayi, jin an sakawa jaririyar mariya, duk da ba ta san dan sunan mahaifiyarta ya saka sunan ba, amma wani irin daɗi da farinciki ya ratsa ta.

A hankali ta ce “Allah ya raya noor takwarar mama”

Daga in da yake ya hango farinciki a kan fuskar ummi, yayi murmushi ya fice, yana tawasalli da farincikin da ya sanyata yana neman biyan buƙatunsa a wurin Allah.

Farida ta sha kuka, da yin alwashi kala-kala a kan yahaya, saboda yadda ya wulaƙanta ta, ya tozarta ta a gaban ƴan uwanta.

Suka din ga rarrashinta, tare da bata shawarwari daban-daban.

Babbar yayarsu ta xe “Duk sakacinki ne, waye ya gaya miki ana barin namiji haka, kyakywar mallaka zaki nema, ta mai da ɗan gida bawa, ki juya shi yadda yake so, kar ki yi bori da yawa, ki girgiɗe auren, duk cikinmu babu wanda yake cikin rufin asiri da kwanciyar hankali kamar ke, kar ki yi mana sagegeduwa, amma dole mu zage damtse”.

Suka din ga zigata, ƙarshe kan sallar magariba suka watse daga gidan sai rahma, rahama kuma ba wani abun kirki take yi mata ba, saboda shegen son jiki ne da ita.

Bayan watsewar ƴan gidansu, ta ƙuduri aniyar ƙuntatawa dr. Ta hanyar nuna halin ko in kula ga yarinyar, gashi mutum ne mai mugun son yara, baya son ya ga ƙaramin yaro cikin damuwa.

Yarinyar shegen kuka ne da ita, ba ta taɓa ɗa mai kukanta ba, idan tana kukan sai ta yi banza da ita. Yayi ta maganar ta kula da ita amma ta share shi.

Ranar da aka yanka hakika kuwa, ummi ce ta zage ƙwanji, tsaf ta gyara hanjin nan, dan kuwa rahama ƙin fitowa tayi kan naman, ga rana na dukan kayan kitchen.

Abdul ne ma ya kama mata wasu abubuwan, ta kunna murhu ta ɗora sai ka ce babbar mace.

Sai azahar yayenta suka zo da ƙanwar babanta, suka tarar da ummi a akan aikin, suka din ga yi wa rahama da farida faɗa, wai dan me za su bar ummi ta yi aikin naman, sai ta sace ta cinye tukuna.

Abdul ne ya fusata ya ce “Yaya ummi ba ɓarauniya ba ce ba, ba ta taɓa ɗaukar abun da ba nata ba”

“Rufewa mutane baki kan in mareka, mara kunya fitsararren banza”

Ummi da jikinta yayi sanyi ta ƙyale musu aikinsu.

Suka gama aikin nama suka kwashe wanda za su kwashe, suka bar saura suka tafi, dr. Ya dawo ya tarar da farida da yaranta suna ta cin naman, ya leƙa ɗakin ummi tana zaune tana ta tilawar Alqur’ani ga gida ya buɗe da ƙamshi, ya shiga ɗakin farida ya ciko leda da nama, ya kai ya bata.

A gaban yara ta rufe shi da masifa, a kan ko dai ummin nan kishiyarta ce ba ta sani ba.

Ganin cin mutuncin da take yi masa a gabansu, ya sanya Abdul tashi ya bar wurin.
Cikin miyagun maganganun da take yi masa, har da gugar zanar ko wani abu ne tsakanin sa da ummi, da ya sanya shi bawa al’amarinta muhimmanci har haka.

Ta dire noor ta tashi ta bar masa falon.

Ummi kuwa da sauri ta wanke hannunta, ta hau naman nan da ci, dan tun ana suyarsa ƙamshin ya cika mata ciki, ranta ya biya.

Sai tayi aikin abinci  da nama ba adadi, da ta gama rahama ta shiga ta raba abincin, ta kwashe naman ta hanata, koma ta bar da ɗan kaɗan sai dai ta haɗa da ƙanzo, dan haka nama tana kallo ba za a bata ba.

Ta fito falo, dan samun tsinken sakace, ta tarar da kawunta rungume da jaririya tana ta tsala uban ihu.

Da sauri ta ƙarasa in da yake ta ce “Kawu bani ita, ban taɓa ɗaukarta ba”.

Ya miƙa wa ummi ita ya ce “Gata nan mai sunan mamanki, ina fatan ita ta so ki, kuma ta din ga ɗebe miki kewar mamanki”

Da sauri ta ce “Amin ya Allah, Allah yasa” ta karɓi yarinyar ta ce “Mamana ki daina kuka, mama tana da haƙuri, kawu ta zama kakarka kenan? Maman mama ko?”

Sai da ya ɗan dara ya ce “Tsohuwa ce kenan?”

Ummi ta ɗorata a kafaɗarta, tana jin soyayyar yarinyar a ranta, da aka saka mata sunan mamanta.

Haka ummi ta din ga zagaye da ita a falon, tun tana tsala ihun har tayi bacci.

Dr. Ya ce “Lallai ummana kin iya raino, tun da har gashi kakata tayi bacci, kawota ki je ki kwanta”

Ta bashi ita, tana kallon fuskar yarinyar, gashinta har goshi, jawur da ita.

Ya kalli ummi ya ce “Na ga ƙunarki da sauƙi, in sha Allah ranar monday zaki koma school gaba ɗaya”

Ta ce “To Allah ya kaimu”

“Amin, ki je ki kwanta sai da safe” ta juya ta nufi hanyar ɗakinta, kamar ta ce ya bata ƴar su kwana tare.

Ranar Litinin ta koma ta cigaba da zuwa makaranta, ranar da ta je islamiyya, Maryam ce ta fara ganinta, da sauri ta tashi ta nufi ummi ta ce
“ya jiki?”.

Ummi ta ce “Na ji sauƙi”

“Kin warke duka ƙonuwar ta warke?”

Ummi ta jinjina mata kai alamar eh.

Ta ce “Alhamdilillah, dan Allah ki yi haƙuri, tun ranar da abun ya faru na kasa mantawa, kuma ban san gidanku ba, na gaya wa mamanmu ta din ga yi mini faɗa, ba ina sane na tureki ba ta ce in nemi yafiyarki”.

Ummi ta yi murmushi ta ce “Ai bakomai, na samu sauƙi”.

“Amma ya aka yi ki ka ƙone a ciki da ruwan zafi?”.

Ummi ta ce “Zubo mini yayi”.

“To Allah ya ƙara afuwa”

Ummi ta amsa da “Amin”.

Maryam ta liƙewa ummi, sai dai ummi sai ɗari-ɗari take yi da ita, saboda ba ta son wani abu ya haɗa su tayi mata tijara da tashin hankali, saboda ita bata iya faɗa ba, maryam kuwa dage ce, akwai masifa.

Ga maryam da azabar kashe-kashen kuɗi, banda kayan ciye-ciye da take zuwa da su.

Komai za ta ci sai ta bawa ummi, ummi kuma ta ce ba zata ci ba.

Tun tana ɗan ɗari-ɗari da ita, har ta ɗan fara sabawa da ita kaɗan.

Can gida kuwa kawu yahaya ya sanar musu matarsa an yi mata aiki, an ciro ƴa mace, sai dai likitoci sun ce sai matar ta huta sosai za azo dubiya. Saboda yana gudun su zo barka, Iya ta faɗi wani abun, da zai yi wa ummi mummunan tabo a nan. Dama kuma gashi ba shiri suke yi da farida ba, dan ita da Iya kar ta san kar ne, iyan za ta iya zuwa ta bar ta a falo ta cigaba da sabgoginta ba tare da ta bata ko ruwa ba.

Ummi ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa jaririya noor, idan uwar ta yasar da ita, sai ta ɗauke ta ta goyata, tayi ta jijjigata tana aikin gidan da ita a bayanta, dan ko da yarinyar ta fara dariya ummi ta fara yi wa.

Duk wannan soyayyar da ummi ke nunawa ƴar farida, bai sanya ta sassauta mata daga baƙar azaba da mugunta ba, da ita da ƴaƴanta da ƙanwarta, dan ummi ba sabon abu bane a wurinta, kaiwa ƙarfe ɗaya na dare ba ta kwanta ba, saboda azabar aiki.

Ga wani sabon salon zalunci, har maƙwabta sai su aiko ummi ta je, a sakata aiki, har wankin labulaye da carfet, sai a sakata, gyaran kaji da fige su, sai a saka ummi.

Makaranta kuma maryam na ta sake shishshigewa ummi, sai dai ummi ta fuskanci maryam ɗin na ƙoƙarin mayar da ita ƙarƙashin ta ta din ga mulkata ta zama kamar ƴar korenta, ummi ta cigaba da janye jikinta, maryam ta kasa samun damar hakan, saboda ummin na da mugun gudun abun hannunta.
Wasu lokutan haka ummi za ta zo ba ta ci abinci ba, maryam ta zo da abinci na alfarma amma fafur taƙi ci.

Kusan wata uku da haihuwar noor, kawu yahaya ya ce idan suka tashi suka koma sabon gida, sai su iya su zo, su ga noor, kuma su ga sabon gida.

Dan yana tsoron Iya ta zo ta saki baki ta faɗi wani abu da zata ɓata ummi, dan ya ƙudurce a ransa sai ya je yayi mata kashedi a kan ummi kan su zo, kuma gashi ba jituwa suke yi da iyalinsa ba, duk zuwa sai Iya ta ce an yi mata laifi, duk zalamar iya da son abun duniyarta ba ta ƙaunar zuwa gidan yahaya, wannan karon ma shi kawun ne ya takura su zo, kar abun ya zama surutu, an yi mata aiki ba su zo ba, ga kuma tariya a sabon gida.

Ɓangaren ummi kuwa sumul ta samu lafiya, kamar ba ta taɓa yin larurar sanyi ba, kuma lokaci zuwa lokaci, kawu yahaya ko bai sayi abu ya bata ba saboda matarsa, ya kan ɗan bata kuɗi ta sai abun da take buƙata.

Suka fara shirin tashi daga gidan, dama ƴan kayan ummi ba su da yawa tuni ta tattare su ta ƙulle.

Hatta su intee ummi ce ta haɗa musu kayansu, sannan ta koma ta haɗa na rahama, ga yau noor sai koke-koke take yi zazzaɓi na damunta, kai ka ce ummi ce ta haifeta, ta bata magani ta haɗa madara ta bata, sannan ta cigaba da aikin da ita a bayanta.

Suka gama haɗa kaya cif, washegari tun safe mota ta zo ta kwashi kayan su, zuwa sabon gida.

Gidan da suka koma, ƙato ne yafi wancan girma da kyau, a ɗan gaban unguwar da suke da yake, ƴan uwan su farida suka cika gidan, ummi na ganinsu suna ta binne-binne.

An canza furnitures, duk ta rabawa ƴan uwanta tsofaffin, ummi kuwa da tsohuwar katifarta ta dawo gidan, sai dai hakan ko a jikinta, ɗakinta shi ne na farko, baya cikin ainihin falon da zai sadaka da sashen kowa, Abdul sashinsa daban ba a cikin falon ba, da kitchen ɗin sa da banɗaki, a can gefe ɗaya.

Gidan ya ƙawatu yayi kyau matuƙa, ko ina ya sha flowers, sai ƙamshin sabunta yake yi.

Hatta ɗakin su intee kamar ɗakin wata amaryar, dr. Yayi ƙoƙari sosai da sosai, dama mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai da sosai.

Bayan magariba ummi ta gaji matuƙa, har wani jiri take ji, ga ciwo da mararta take yi, wanda tun da take bata taɓa jin irin ciwon ba.

Tana ta ƙoƙarin gyara nata ɗakin, dan kuwa ba ta gyara komai ba, tana ta fama da aiki, da rigimar noor.

Ƴan uwan farida suna ta cewa ta karɓe ƴar ta daga hannun ummi, kar ta shafa mata baƙi da muni.

“Ke!”

Ummi ta waiwayo ta kalli rahama da ke tsaye.

Ta ce “Bani kuɗin nan da zobena”

Ummi tayi saroro ta ce “Wane kuɗin?”

“Ba ke kika haɗa mini kayana ba?”

“Eh nice” ummi ta amsa.

“Kuɗin da suke cikin wardrobe ɗina, kuɗin anty farida ne”

Ummi cikin faɗuwar gaba ta ce “A’a anty rahama, ban ga kuɗi ba wallahi, kayanki kawai na haɗa miki a cikin akwatin da sauran kayanki a cikin jakunkunan da ki ka bani, dubu biyun nan ce kawai kuma kin ɗauketa, amma ban ga kuɗinki ba”.

“Ke rufe mini baki ko na dalla miki mari, kuɗin anty farida ne dubu hamsin”

“Wallahi wallahi anty rahama ban gani ba, ki cajeni ki caje kayana, wallahi ban ɗauka ba” ummi tayi maganar jikinta yana rawa tana tuna irin tozarcin da aka yi mata lokacin da iya ta ce ta yi mata sata.

“Rahama ina kuɗin ne? Ta baki?”

“A’a fa sai kin zo da kanki, ta ce ita ba ta ɗauka ba”.

Farida ta ce “Ke, ina kuɗina?”

“Anty ban ɗauka ba” ta faɗa kamar numfashin ta zai ƙwace, saboda fargaba da tashin hankali.

Ashar ɗin da farida ta yi mata cikin tsawa ya sake gigita ta, ta ma rasa me za ta ce.

Shaƙeta rahama ta yi tana zazzaro mata ido ta ce “Zaki faɗa ko sai na kashe ki” girgiza kai kawai ummi take yi.

Farida ta ce “Rahama ƙyaleta, kar ta ja miki bala’i, ta riƙe miki kurwa kamar yadda ta yi mini, wallahi sai ya biyani kuɗina, kuma a wannan karon ko ubanta zai fito daga kabari ta din ga yawo da shi, sai ta bar mini gida ta koma in da ta fito, ba zan zauna da ɓarauniya ba, ga sata ga maita ba zai yiwu ba”.

“Antyn dan Muhammadurasulillah ki yi haƙuri, dan Allah kar ki mayar da ni ƙauye, wallahi ban taɓa sata ba, ban san menene maita ba”

“Zaki santa yau, ɗaukko ƙullin kayanki ki wuce, ba zai yiwu ba”

Suka hankaɗo ummi waje, duk attention ɗin mutanen gidan ya dawo kansu, noor da ta fara dariya, tana hango ummi ta hau dariya tana ɗaga mata hannu.

“Lallai farida an haɗaki da masifa, satar kuɗi kuma, wannan wataran sai ta ganki a makara hankalinta zai kwanta” a tsakiyar falon suka zazzage mata kayanta, sai ga dubu ɗaya sabuwa fil wadda kawunta ne ya bata.

Rahama ta ce “Anty ta fito da sauran, suna wurinta wallahi, kalli dubu ɗaya fa a ina ta samu”.

Inteesar ta ce “Tashi a caje ki, olay” kausar ta ƙyalƙyale da dariya tana maimaita olay.

Dr. Yayi sallama tare da Abdul ya tarar da ummi a durƙushe, tana ta gursheƙen kuka, noor sai zillo take ummi ta ɗauke ta.

“Lafiya kuwa?”

“Dr. Ni fa na gaji, da abun da yarinyar nan take yi mini, daga bawa rahama ajiyar kuɗi ta kwashe, ta bani kuɗi tun da girma da arziki amma taƙi”.

“Shi ne zaki ajiyeta a gaban mutane kina tozarta ta haka? Idan yaranki ne haka zaki yi handling ɗin su? Nawa ne kuɗin?”

Cikin mamaki ta ce “Au haka ma zaka ce?”

“Na ce nawa ne kuɗin?”

“Dubu hamsin” ta bashi amsa tana riƙe ƙugu.

“Sana’ar me ki ke yi da har ki ka tara dubu hamsin? Idan ma akwaita na san a jikina aka sameta, zan biya na kashe maganar nan daga yau, kuma daga yanzu. Ummi ba ɓarauniya ba ce ba halin ta bane”. Ta yinƙura za ta sake magana ya tari numfashin ta ta hanyar cewa “Na ce na kashe maganar nan”

Ya dubi ummi ya ce “Ummana, tashi kiyi tafiyarki”

Ba tare da ummi ta yi zuciya ba, ta dubi yarinyar da take ta zillo tana kuka, ta ƙarasa ta ɗauketa, ta nufi ɗaki da ita.

Abdul ya durƙusa yana kwashewa ummi kayanta.

“Farida anya maganin nan yayi kuwa? Kin ga fa abun da yayi miki”.

Farida ta kasa magana saboda takaici, yau ta ƙuduri aniyar ummi ta bar mata gida, tun da yau sun yi sababbin ayyuka a gidan.

Ummi kuwa zuruuu tayi da ido, tana kallon noor da ke ta ɓangale baki tana yi mata dariya.

Cikin kuka take yi wa noor surutai, ta ce “Mamana, kin gani ko, tun tafiyarki ban taɓa kwanan farinciki ba, dan Allah mama ki dawo, ko ina ne ki tafi da ni, mama kamar in sha guba in mutu” tayi maganar tana kifa kanta a kan ƴan ƙafafuwan noor, tana wani irin kuka mai sauti”

Ayshercool.

Ayshercool

              *CUTARWA!”

P17

Shiru noor tayi, tamkar tana jin abun da ummi take faɗa.

Sosai ummi ke kuka, tamkar za ta shiɗe, duk da ba wannan ne karon farko da aka yi mata ƙazafin sata ba, amma na yau yayi mata zafi da ciwo ba kaɗan ba.

Ji tayi an dafa ta, ta ɗago da sauri dan ba ta ji shigowar mutum ba.

Abdul ta gani a bayanta da kayanta a hannunsa, cikin damuwa ya ce “Dan Allah yaya ummi kiyi haƙuri, na san ba zaki yi sata ba, amma ki yi haƙuri dan Allah ki daina kuka, kar kanki yayi ciwo”.

“Yaya Abdul, ya aka yi kai ka yadda ba zan sata ba, amma anty farida da rahama suka ɗora mini sata? Suka ci mutuncina a gaban mutane?” ya durƙusa ya ce “Na san babu daɗi, kiyi haƙuri dai dan Allah”

Ta jinjina masa kai, dan kuwa tana ganin mutuncin Abdul sosai da sosai.

Ya ɗora da cewa “Kar ki ga ɗakinki a haka, mun yi magana da abba ne, ya ce a bari mu tare ya ga ɗakin da maama zata baki, sai ayi miki furnitures, kar a saka miki ta hanaki ɗakin”.

Ummi ta girgiza kai ta ce “Dan Allah kar ka bari yayi mini, ya kashe kuɗi da yawa, ni katifata ta isheni, duk kyan furnitures ɗin da za a saka mini, ƙarshe a tsakiyar ƙasa za a binne ni, hakan ma ya isa”

Shiru yayi yana kallon ummi, ta kwanta a kusa da noor, ta sanya hannunta ta riƙe ɗan ƙaramin hannun jaririyar.

Abdul ya tashi ya fita yana waiwayenta, duk abun da aka yi mata, bai sanya tayi zuciya taƙi kula noor ba.

Kasancewar a gajiye take, wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita, baccin da rabon da tayi makamancinsa har ta manta.

Kwanki uku da tarewarsu, aka kawo wa ummi ƙatuwar katifa, da wardrobe mai biyu, sai ɗan mudubi da stool.

Ba ƙaramar murna ummi tayi ba, tare da wani farinciki, wai duk wannan nata ne abun mamaki.

Kawu yahaya ya fara deciding zuwa ƙauye, ya gaida Iya, dan haka ya tambayi ummi ko za ta bi shi, ta je a gaggaisa.

Amma tayi shiru ba ta ce komai ba.

“Ummana baki ce komai ba”

“Kawu ka ce ina gaishe su, ba sai na je ba” tayi maganar tana addu’a a zuciyarta, kar ya matsa ya ce sai ya tafi da ita, saboda tana tsoron ya tafi da ita, Iya ta sake cewa ba zata biyo shi ba.

“Ƙauyen ne ba kya son zuwa ko ummana?”

Ummi ta gyaɗa masa kai alamar eh.

Yayi murmushi ya ce “Kwantar da hankalinki kyakywar uwa, abun da ki ke so shi za a yi, zan sanar da su saƙon gaisuwarki, ko ni ba zan so ki je ba, sai kin zama cikakkiyar mutum, da babu wanda zai tursasaki yin abun da ba kya so a rayuwarki”.

Kawu yahaya da kansa ya je ƙauye dan ya ɗaukko iya, ta zo ta ga sabon gidansa da jaririya, amma ta ce ba zata ba, saboda matarsa ba ta da mutunci.

Hashim kuwa yana ganin kawu yahaya ummi ya fara tambayarsa.

Ya ce “Ummi na nan lafiya ƙalau Alhamdilillah, tana nan tana karatunta duk ta ce a gaishe ku”

“Allah sarki ummi, muna amsawa”.

Iya ta ce “To wai yaushe zaka dawo mini da ita ne?”

Kawu yahaya yayi murmushi ya ce “Ai Ummi sai Allah ya kaimu lokacin aurenta zamu gayyace ku, ba zata sake zuwa gagarawa ba”.

A ɗan hasale ta ce “Saboda me?”

“Saboda babu abun da za ta zo tayi muku”

“Kai yahaya bana son sakarci, zumuncin fa? So kake ka raba mini kan iyali?”

Ya girgiza kai ya ce “Ba haka bane ba, na nemi iznin zuwa da ita, ta ce in gaishe ku, saboda makarantar ta”

“Innalillahi wa Innalillahi raziƙuna, ita ummun ce ta faɗi haka? Ta fifita boko a kaina?”

Magaji ya ce “Iya wa Innalillahi raji’un ake cewa ba raziƙuna ba”

“Zan ci uwarka idan na sake magana ka tsoma mini baki, tun kan a haifi uwarka haka ake faɗa, ba damar mutum ya motsa sai ka ce zaka ci gyaransa?”

Ganin Iya na son dasa faifan cin zarafin ummi da iyayenta, ya sanya shi bawa Iya abun da zai bata ya tashi ya ce zai tafi.

Har mota hashim ya raka dr., Ya ce a cewa ummi yana gaisheta, tayi karatu da kyau.

Kawu yahaya yayi alƙawarin isar da saƙonsa ga ummi.

Kasancewar fitar sassafe yayi, yana gama abun da zai yi ya dawo kano, a falo ya yada zango, ummi tuni ta gama girki tayi shirin tafiya islamiyya, ya tsareta a falon yana bata labarin saƙon ƴan gidan na gaisuwa a gareta.

Ganin yadda ummi ta ɗan sake da kawu yahaya, har tana tambayarsa wasu daga mutanen gidan, ya sanya farida yi mata tsawa, ta ce ta tashi ta tafi makaranta.

Abdul ya shigo da noor a hannunsa, ummi tayi saurin karɓarta, ta ɗan ɗagata sama ta ce “Mamana tafi ta kowa” noor kuwa ta buɗe baki tana dariya.

Wata irin zabura farida tayi, tun da ummi take kiran noor da maman wasu lokutan, ba ta taɓa kawo sunan mahaifiyar ummi bane ba sai yanzu, tayi wata irin zabura ta ce “Dr. Sunan matar ƙaninka ka saka wa noor? Babar ummi?”.

Kai tsaye ya ce “Yes”

“Saboda me? Meye alaƙata da ita? Ita tayi mini cikin? Ko ita ta haufa mini, wai tsaya meye alaƙarka da ita?”.

“Alaƙar da ki ka faɗa mana, na kawo miki amanar yarinya kina ta wulaƙanta ta, gashi tana ta yi miki bauta kamar baiwar da ki ka sayo da kuɗinki, dan haka na saka mata sunan mahaifiyarta, atleast ta samu ƴar uwa, kuma wadda zata din ga kallo tana jin daɗi”.

“Yahaya gaba ɗaya na kasa gane kanka, na rasa in da ka dosa a kan yarinyar nan yanzu saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, matar da ban sani ba kawai ka saka wa ƴa ta sunanta? Ni wai wace irin alaƙa ce tsakanin ka da ummin nan, ko zagata ka ke yi ne ban sani ba, da a duniya kullum abun da zai faranta mata kawai ka saka a gaba?”.

A fusace ya ce “Wace irin maganar banza ce haka farida”

“Ba wani maganar banza, maganar gaskiya dai, to ga noor ɗin nan na bar mata, ta je ta raine ta na bar mata, tun da sunan uwarta ne ba na uwata ba”.

Duk da ummi a tsaorace take rungume da noor, jin kawu yahaya suna faɗa, sai dai jin abun da farida ta faɗa, ya sanya cikin wauta da ƙuruciya, ta risuna ta ce “Anty na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata na gode in sha Allah zan kula da ita, a bani kayanta da abincinta na gode” a zaton ta da gaske ta bar mata noor.

Kawu yahaya duk da a fusace yake, sai da yayi dariya, aikuwa cikin ɓacin rai farida tayi kan ummi, ta fizge noor ta ce “Ai ba uwarki ce tayi mini naƙudar ba”

Kawu yahaya ya ce “Ummana, jeki makarantar ki kin ji” ta ɗauki jakarta, ta fita cikin damuwa.

Ummi ba ta cika makara ba, dan haka da wuri ta je makarantar islamiyya.

Zama tayi ita kaɗai, tayi shiru tana tunani, tana son sake yi wa kawu yahaya maganar ya gano in da mamanta take? Sai dai ta kasa tana jin nauyinsa, shi ya ce mata ta bashi lokaci, dan haka ba ta son cigaba da takura masa.

“Ummi” maryam ta kira sunanta.

“Na’am” ta amsa a taƙaice.

“Taso ga mami can ta zo, ita ta kawo mu, ta ce yau dai tana son ta ganki”

Jin mahaifiyar maryam ce ke son ganinta, ya sanya ta tashi da sauri, dan duk in da aka ce wannan babba ne mussaman sha’anin uwa, ummi na bashi girma sosai da sosai.

A ƙofar makaranta suka tarar da mamin a wata zuƙeƙiyar mota, suka ƙarasa gaban motar, ta buɗe ƙofar motar tana murmushi.

Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce “Mami ina wuni”

Matar ta ƙarewa ummi kallo, sannan ta yi murmushi dariya na neman suɓuce mata ta ce “Lafiya lau ummi, ya gida ya makaranta?”

“Lafiya ƙalau, Alhamdilillah”

“Yau Allah yayi na ga ummi, kusan kullum sai tayi zancenki a gida”

Ummi tayi murmushi tare da sunkuyar da kanta ƙasa.

“To Ubangiji Allah yayi muku albarka baki ɗaya, ina fatan wataran kuma zaki kawo mini ziyara gida”

Ummi ta ce “To, zan tambaya idan aka bar ni zan zo in sake gaishe ki”

Tayi murmushi ta ce “Masha Allah, ku koma aji to, Allah ya yi albarka”

Ummi ta amsa da “Amin ya Allah na gode, Allah ya tsare hanya”

Maryam ta ce “Bye bye mami, drive well”

Ta amsa mata da “Thank you dear”

A haƙiƙanin gaskiya maryam bata da aiki sai bayar da labarin baƙin ummi, da gidadancinta da rashin wayo, da yadda take kullum cikin kuka, abu kaɗan sai ta hau kuka, da irin yadda malamai kan yi mata ba’a, ko yadda su kan su ɗaliban ke attacking ɗin ta, amma ba ta iya cewa komai.
Babban abun da ya burge mamin da ummi, shi ne nutsuwarta, da kuma gudun duniya da ta gani yau da wanda take jin labari a wurin Maryam.

**
Yau babban burin Idris ya cika, dan kuwa ya hilato hindu shagon wani abokinsa, ya aiwatar da abun da yake muradi a kanta.

Hindu tayi kuka kamar ranta zai fita, sai dai ya zuba mata ido, a tunainsa yanzu hankalinsa zai kwanta, sai dai ina, kasancewa da ummi kawai yake burin yi.

Duk da babu abun da ya shiga tsakaninsa da ummi, yana jin kamar akwai wani abu na musamman da ummi ke da shi, da baya tunanin ya samu a tattare da hindu.

Iya taushin fatar ummi ya isa saka mutum annashuwa, ya daɗe yana jin haushin kansa, da har suka rabu da ummi, bai amfana da ita ba.

Kukan hindu ne ya dawo da shi hayyacin sa, ya din ga lallaɓata yana bata haƙuri, tare da yi mata alƙawarurruka kashi-kashi irin na yaudara.

Tun da farida ta san sunan babar ummi, aka saka mata, ya sanya ta ƙara tsananta ƙiyayyarta ga ummi, azabtarwa iri-iri.

Rayuwa ta cigaba da garawa, sai dai al’amura sun tsananta ga ummi, lokacin da dr. Ya samu canjin wurin aiki, daga Kano zuwa kaduna, wasu lokutan sai yayi wata guda bai zo gida ba, wasu lokutan kuma ya kan zo weekends.

Idan ummi ta karaya ta ji kamar ta mutu ta bar duniya ta huta, sai kuma taga wahalarta ta tashi a banza kenan, ba ta yi acheiving komai a rayuwa ba.

Ko ina babu daɗi, gida azaba da wahala, makarantar boko, ba’a, cin zarafi daga ɗalibai har ma da malamai wasu lokutan, sukan aibata ta ko su muzantata da halittarta.

Sai da ta kai ta kawo, kuɗin makaranta idan dr. Ba ya gari, idan ya turowa farida, ba zata bawa ummi nata ba, har korota ake yi daga makaranta.

A ci mata mutunci, Saboda rashin biyan school fees, sai da ta kai Maryam ta saka babansu biya wa ummi kuɗin makaranta.

Shugaban makarantar ya hana malamai korar ummi, a duk lokacin da ba ta biya kuɗin makaranta ba, sai ya yi wa kawu yahaya waya, sai a lokacin dr. ya san abun da yake faruwa game da kuɗin makarantar ummi da yake bawa farida ba ta bata, daga nan har makarantar boko, direct transfer yake yi musu.

Duk wani aiki ko aike da yakamata namiji yayi ga Abdul, ummi ce za ta yi shi, sayen fetur, cefane, refilling ɗin gas, duk ummi ce ke yin sa, intee da kausar babu abun da suke tsinanawa a gidan nan, ko ɗauke cokali kuwa a kan hanya, saboda azaba har tayar da inji sai da ummi ta iya.

ƙawayensu intee idan suka zo, su yi ta nuna musu ummi a matsayin ƴar aikin gidan su.

Allah ya taimaki ummi, aka sakawa rahama ranar aure, ta din ga murna ta san ko ba komai ta ɗan samu rangwame.

Gefe guda soyayya da shaƙuwa mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin ta da noor, noor komai ummi, kai ka ce ummin ce ta haifeta ba farida ba, dan ita ce ta yaye noor ma.

Ummi na ta aiki a kicin da safe, ta je ɗakinta ta dawo, ta zo ta tarar da ƙwai guda biyu a kan drower kitchen, ita dai ba ta ajiye ƙwai ba, dan haka ta kai hannu ta ɗau ƙwan tana duddubawa, rubutu ne a jiki, an zana wani hatimi da sunan wanda rahama za ta aura, har da zanen kan ƙwarangwal.

“Ke!” Tsawar da farida ta daka mata, ya sanya ta zabura ta saki ƙwan ya faɗi ya fashe, maimakon ruwan ƙwai ya fito, sai jini da wani baƙin abu ya tsiyaye.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wai wace irin karfa ce ke ne?”

Cikin magiya ummi ta din ga bata haƙuri, amma tsabar mugunta matar nan ta ɗauki muciya ta din ga bugawa ummi.

Abdul yana falo yana video game, ya shigo kitchen ɗin da sauri ya tarar da ita tana ta bugawa ummi muciya, tana ƙoƙarin karewa.

“Maama lafiya, meyasa ki ke dukanta da muciya”

“Dalla rabu da ni, na gaji da abubuwan da yarinyar nan take yi mini”

“Amma maama bai kamata ki dake ta da muciya ba, idan kuma ki ka ji mata ciwo fa?”

Cikin ko in kula ta ce “Na daki banza”

Tayi maganar tana sake kwaɗawa ummi muciyar iya ƙarfin ta.

“Maama dan Allah ki daina cin zalin anty ummi, wannan CUTARWA! ce, maybe tsautsayi ne ya sanya ta yi miki laifin”

A fusace ta ce “Ni ka ke gayawa ina cin zalinta?” Tayi maganar tana nufo shi.

Babu tsoro ko fargaba ya ce “Idan ba CUTARWA! ba ce dai-dai ne Allah ya sa a yi wa intee ko kausar abun da ki ke yi mata” sak tayi tana kallon Abdul, ba ta taɓa zaton wannan maganar daga bakinsa ba.
Ta ji jikin ta ya yi sanyi, ta jefar da muciyar ta fice.

Ya girgiza kai shi ma ya fita, dan kunyar ummi ma yake ji, bai san me zai ce mata ba, saboda abun da mahaifiyar su take mata.

BAYAN SHEKARU BIYU
*

Ummi na tsaye a gaban mudubin ɗakinta, tana ta aikin taje gashin ta, ta nemi wuri ta zauna tana kallon kanta a mudubi, gashin duk ya rufeta, ta sunkuya tana cire gashin da yake jikin comb ɗin, ta tare shi a gefe sannan ta nannaɗe gashin kanta ta tufke shi.

Ta sanya doguwar rigar shadda brown, ta kawo dogon hijjabi milk ta saka, ta ɗauki niƙabinta ta sanya.

Ta shashshafa turare, tafin hannunta har ɗaukar ido yake yi, saboda tafin hannunta fari ne ƙal, kamar mata jini a jiki, kuma aka ɗora mata jan lalle a kai.

Ta ɗauki ƴar ƙaramar jakarta ta fito, Abdul ya ce “Inyee ka ga amaren sauka”

Kawu yahaya ya dube ta cikin fara’a ya ce “Congratulations dear, Ubangiji Allah ya sanyawa karatunki albarka, ya ƙara hasken makaranta” ta risuna ta ce “Amin kawu, na gode sosai da sosai”

Ya kalli farida da ƴan matanta da suke ta sabgoginsu, kamar ba su san da zaman su a falon ba ya ce “To mu mun tafi wurin saukar”

“Allah ya tsare” ta faɗa a yatsune.

Kawu yahaya yaji babu daɗi, da yaransa ko mutum ɗaya babu wanda yayi saukar nan, idan baya nan sai sun ga dama suke zuwa makaranta, dan kuwa farida wurin koyon kwalliya ma ta sama musu, maimakon zuwa makarantar.

Ummi gaba ɗaya bakinta yaƙi rufuwa, kaf a ƴan saukar ita ce ƙarama, danma tana da jiki ne, dan ko Maryam shekara biyu ta bata, itakaɗai ce mai shekaru sha shida a cikinsu, maryam na da sha takwas.

Aka gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan aka fara raba musu alluna.

Ana bata nata ta nufi rumfar iyaye maza, har da gudu, wurin kawu ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa tana cewa “Kawu ka ga”

Ya karɓi allon yana murmushi ya shafa kanta ya ce
“Allah ya sanya albarka ummana”

“Amin kawu na gode” tayi maganar cikin tsantsar farinciki.

Abdul ya ce “Rufe bakin mana”

Ta kalleshi ta ce “Ta ina ka san bakina a buɗe yake a cikin niƙab”.

“Yadda ki ke magana ne ya sa na gane”

Ta ce “Bari Yaya Abdul, Alqur’ani da daɗi wallahi”.

“Wannan gaskiya ne ummana, kalli baƙin ki na waccan rumfar” ummi ta waiwaya ta ɗaga kai.

Wa zata gani? Yaya Magaji da auwwal, har da su Alhassan.

Maimakon ta yi murna sai gabanta ya faɗi, ta kasa magana, dan fatanta Allah ya sa babu Idris suka zo, dan bata ƙaunar ganinsa.

Sunanta aka din ga kira a speaker, ta zo ta karɓi kyautarta ta ɗaliba mai hazaƙa.

A hankali ta tashi ta nufi in da ake kiranta, tafiya take cikin nutsuwa, shugaban makarantar ya ce “Ƙaramar su babbar su, Salma Muhammad Bashir, kun ganta nan duk ita ce ƙarama a ƴan sauka, amma babu ɗalibar da ta kai ta cin maki lokacin screening”

Ummi ta karɓi kyaututtuka daban-daban, na hazaƙa, ladabi da biyayya da sauransu.

Mamin su maryam ummi ta hango, ta tafi wurin da take, dan jan lallen da aka yi mata ma, gidan su maryam ta je, mamin ce ta biya.

Mamin ta rungume ta tana faɗin “Allah yayi albarka ummi, Allah ya sanya wa karatunku albarka”

Ta risuna ta ce “Amin ya Allah”

Sau ɗaya ya ɗaga kai ya kalleta, ya lura da yadda ko iya haɗa ido da mamin ba ta yi, saboda tsananin tarbiyya da girmama manya, ya so ta ɗaga niƙabin ya ga ainihin fuskarta.

Ya dubi Maryam ya ce “Ke ba uban da aka baki? ba na ƙoƙarin, babu na ɗa’ar” yayi maganar yana sake gyara zaman face mask ɗin sa.

Cike da tsiwa Maryam ta ce “Ina ruwanka da ni? Ba a bani ɗin ba sai ka ƙwace allon saukar ma gaba ɗaya, mami ki rabani da shi wallahi, ai da yake ma ba gayyatarka na yi ba, waye ya ce ka zo?”

“Rufen baki kan na ɓarar da ke a wurin nan”

Ummi dai murmushi kawai take yi, duk ta san yayyen Maryam, wannan ne dai bata sani ba, kuma da alama maryam ɗin ta raina shi.

Aka tashi daga filin sauka, su yaya magaji suka nufo su, “Ummi masha Allah, kin ga yadda ki ka girma?” Magaji Yayi maganar yana kallon ta.

Alhassan ya ce “Ummi har kin yi sauka anya ba zuƙu ba ce ba?”.

Ummi ta yi murmushi ta ce “Ai makarantar nan ba a saukar zuƙu”

Suka rankaya zuwa gida, suna komawa gida ta tarar da Iya, sai da ta ɗan ci burki, domin kuwa ba ta zaci Iyan za ta zo ba.

Ta ɓoye mamakinta ta ce “Iya sannu da zuwa, dama zaki zo?”

Ta harari ummi ta ce “Eh, da ki ka ce ke ba zaki zo in da nake ba, kar na yanka ki na cinye ko?”

Ummi ta girgiza kai ta ce “A’a makaranta ce take hanani zuwa, ya gida ya kowa da kowa?”.

A ciki Iya ta amsa mata da lafiya lau.

Dai-dai gwargwado kawu ya yi wa ummi ƙoƙari, dan naman kasuwa ya sayo fal, ya bata tayi girkin da zata rarrabawa mutane da ƙawayenta.

Ita ummi ma kasancewar ba ta da ƙawaye, sai maƙwabta ta babbawa, sai su Iya da suka zo.

Sam farida ba ta bi ta kan Iya ba, ummi ce take ta ɗawainiya da su, suna ta hirar makaranta da su magaji, sai dai ko da wasa, ba ta nuna musu tana shan wahala a gidan ba ko kaɗan.

Kawu yahaya ya ji daɗin yadda ummi ta samu sakewa yau cikin ƴan uwa, tana hira ba kamar da da kullum a rakuɓe take ba.

Iya kuwa ba dalilin saukar ummi ne ya kawota ba, balli ne ya tashi, Idris ya mayar da hindu tamkar matar da ya aura, tun bata saba ba har suka saba da sheƙe ayarsu.
Kwatsam ciki ya bayyana a jikin hindu, suka rasa yadda za su yi da cikin, har sai da iyayen hindun suka farga.
Dan haka zance ya fasu a gari, sai faɗuwa ta zo dai-dai da zama, domin kuwa iyayen hindu sun ce sai ya auri hindu, shi kuma ya ce ba ya son ta.
Dan kuwa zance ya fara fasuwa, an fara zunɗensu a garin.
Baban hindun kuma ya dage ba za a zubar da ciki ba, sai an haifi wannan ɗa ya riƙe, kuma sai ya aureta.
shiyasa Iya ta lallaɓo wai kawu yahaya ya ɗauke shi ya sama masa sana’a a nan Kano, a mayar da aurensa da ummi!!!

Iya a ɗakin kawu yahaya ta same shi, ta kora masa wannan jawabin.

Yayi ƙuri da ido yana kallon Iya, har ta gama jawabinta.

Kasancewar ummi na wurin, gabanta yayi wata irin mummunar faɗuwa, kawu yahaya ya kalli Iya ya ce “Amincewar ummi zaki nema, ni ba zan yanke mata hukunci ba, abun da take so shi nake so”.

“Zancen banza kenan, wane irin sai ta yarda ko ba ta yarda ba? Ba ɗan uwanta bane ba, rufin asirinmu ba nata bane ba, idan shi ma ya baro garin, suka neme shi suka rasa ba shikenan ba, asiri ya rufu, ai rufa masa asiri za ta yi,  ai umarni nake bayarwa ba shawara ba, dauɗar gora ai ciki ka sha ta!”

Masu tambayata, littafin CUTARWA! free ne, ku karanta ku yi mini addu’a, idan kuma ummi zaku tarawa kuɗin sayen man bleaching da kayan ɗaki, sai na ajiye account number😂😂 ina godiya da tarin saƙonnin sharhi kala-kala da addu’a, Ubangiji Allah ya wuce mana gaba, ya sanya ana ɗaukar darussan cikin labarin

Ayshercool

CUTARWA!

P18

18.

Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshsheƙar kuka take yi, dan kuwa da ace ta koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa.

Iya cikin masifa ta ce “To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ƙone ƙurmus, har wani zaɓi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba”.

Kawu yahaya ya ce “Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni”.

“Ka ga ni kar ka yi mini wa’azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo ɗin, sai a ja masa kunne”

Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshsheƙar kuka ya ce “Ummana, jeki ɗaki abunki kin kwaso gajiyar sauka” ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi ɗakinta tana kuka, tare da adduo’i kala-kala a zuciyarta, tana fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faɗa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko maƙiyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris.

Noor ta bita ɗakin tana kiran sunanta.

Kawu ya kalli Iya ya ce “Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba ɗaya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci ɗan wani ba, yadda ya yi wa ƴar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba.
Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauɗar gorar ba, sai ummi?
Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan riƙe ƙato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ƙauye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi haƙuri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke ɗawainiya da shi”.

Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce “Haka ka ce?”

“Ba faɗa na yi dan na ɓata miki rai ba, amma gaskiya ce” Iya ta yi ƙwafa ta ce “Shikenan na tabattar da uwarka ce ba zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku ɗaya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba”.

Ya girgiza kai ya ce “Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya ɗebo da zafi bakinsa, kin riga kin sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaɗai ne ɗa a dangi ba”.

Ba ƙaramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ƙiri-ƙiri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaɓi tonuwar asirin su.

Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaɓa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da ita.

Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuɗin motar, ya basu kuɗin kashewa, suka tafi.

Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur’ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da aka yi.

Duk da kuɗin da yahaya ya bawa Iya sun saka ta ɗan sassauta fushinta, amam ta sha takaicin rashin amincewa ya ɗauki Idiris a mayar da aurensa da ummi, ta din ga zagin ummi tana tsine mata, tamkar ba ita ta haifi baban ummi ba, tare da janyo mata jafa’i kala-kala.

Ko da suka koma gida ta sanarwa Idris da babansa cewa yahaya ya goya wa ummi baya, yaƙi yadda da magabar da ta je masa da ita.

Hankalin Idris ya tashi, dan kuwa baban hindu ɗan bala’i ne, ya ce ba zai yadda ba, ba za a zubar da cikin jikin hindu ba, sai ta haife shi, kuma sai sun karɓa sun riƙe, hindu na da wani yaya da yake soja, kurtu nema a cikin sojojin, amma ya zamewa su Iya barazana, dan kuwa shi ma cewa yayi sai ya saka bomb a gidan su iya, ko ya kama Idris ya harbe shi, tun da aka taɓa ƙanwarsa.

Magaji ya san duk barazana ce, babu ɗaya da zai faru, amma yayi shiru da bakinsa, saboda sun cancanci koma menene ya same su, dan da idris bai taɓa ƴar mutane ba, babu mai ɗaga musu hankali, kuma ya danganta hakan da alhakin ummi

Babu yawon da Iya ba ta yi wurin malamai ba, a kan a rufe bakin baban hindu, da ita kanta hindun da yayanta, amma abu ya ci tura, dan har barzanar kai su gaban hukuma baban hindu yayi idan suka cigaba da takura masa a kan maganar cikin nan, ko kuma ya saka ɗan sa ya ɗauki duk matakin da ya ga dace a kan su.

*

Tafiyar rahama daga gidan dr., Bayan an yi mata aure bata sauya zani da komai ba, daga wahalar da ummi take yi, dan har undeas ɗin su intee ba zasu wanke ba, sai a haɗa mata a kayan wanki, duk ta haɗa ta wanke su.

Sai dai tun ba aje ko ina da tafiyar rahaman ba, ta fara sintirin kawo ƙara wurin kawu yahaya, dan dama mahaifinsu ya rasu, duk wani abu na jin daɗi da ta sanya ran samu a gidan mijin, sai ta ga akasin haka, yana da hali ba bashi da shi ba, amma hatta shinkafa da man da za ta ci, sai ya ƙulla mata, ba yadda da zuwan baƙi gidansa ba, sai an kira shi ya bayar da iznin a zo, idan bai bayar ba kuwa babu mai zuwa.

Kawu yahaya ya kira shi, dan a samu masalaha amma ya nuna shi tsarin gidansa ne a haka, dan haka dole a bar shi yayi yadda yake so.

Haka nan kawu yahaya ya ce sai dai tayi haƙuri, yace shi tsarin gidansa ne a haka.

Tun da shekaru goma sha shida, samari suka fara bin intee, hakan ba ƙaramin farantawa farida yayi ba, tana ganin intee mai goshin arziki ce, shekara goma sha shida, samari sun fara sintiri, dan ma dr. Yana korarsu ya ce yarinyarsa tayi ƙanƙanta sai ta fara karatu idan ma auren zai yi mata.

Lokacin da ummi ta fara period babu wanda ta gayawa, dama ta riga ta san shi tun a karatuttukansu na makarantar islamiyya da na boko ana gaya musu shi, sannan an koyar da su tsabta a lokacin da mutum yake cikin jinin  haili. Dan har wata ƙungiya ta je makarantar su suka wayar musu da kai, a kan jinin haila da tsafta, dan haka babu wanda ta gayawa da ya same ta.
Ta samu kayanta da suka ɗan kwana biyu, ta yayyanka ɗankwalin, take amfani da shi.
Idan kuma Allah ya sa dr. Ya bata kuɗi, babu abun da take fara saya sai pad, tana iya haƙura da kowace irin buƙata ce da ita, ta sai pad ɗin da za ta yi amfani da ita da kuma farin muski.

Sintirin samari zuwa wurin intee, ta din ga wani iyayi tana yauƙi, ya sanya aka fara yi wa ummi gori da habaici, domin kuwa babu wanda ya taɓa zuwa ƙofar gidan ya ce yana sallama da ita, ko a hanya ma babu wanda ya taɓa biyota ya ce ya na so.
Su yi ta yi wa ummi wulaƙanci, wai farar mace Alkyabbar mata, baƙar mace bolar maza.
Kodayake bolar akwai wadda ake iya recycling, wata ta riga ta zama waste gaba ɗaya bata da mamora.
Ko sai sun ga ummi su fara wankan baƙi asarar ruwa, ko yayi ma kamar bai yi ba, blaki kalar dauɗa, su din ga yi suna tuntsura dariya.
Ummi kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta cigaba da sabgoginta, duk da a ƙasan zuciyarta kalaman na su na tasiri a cikin zuciyarta, tana jin babu daɗin cin mutuncin halittar ta da suke yi.

Haka Maryam ma, kasancewar ta kyakykyawa, kullum ba ta da aiki sai bawa ummi labarin saurayinta kaza yayi mata kaza, ko ya bata abu kaza.
Ba maryam kawai ba, ƴan ajinsu ba su da aiki, sai hirar samari, ita kuwa da ta san ba ta da kowa, ta rungumi litattafanta yadda yakamata.

Idan suka so yin dariya kuwa, sai su yi ta zungurar ummi, suna tambayarta wai ita waye nata saurayin, ta gaya musu fari ne ko baƙi, dogo ko siriri.

Kawai sai tayi murmushi ta yi musu shiru, taƙi kula su.

Maryam ce ta fara bata shawara “Ummi, yakamata ko ɗan mayukan nan na zamani ki ɗan din ga shafawa, ko kema kya yi haske, maza ba sa son baƙar mace, ummi kin yi duhu da yawa, duk kwatancen baƙin da za ayi a makarantar nan da ke ake yi, idan ki ka shafa mai ki ka ɗan yi haske, ko yaya zaki samu saurayi, ko zaki ji daɗi duk mu yi aure mu bar ki? Ni fa mami ta ce ina candy aure za ayi mini, na cigaba da karatu a gidan mijina, amma ke kullum kin ƙi wayewa, ga uban hijjaban da ki ke sawa, ba kya kwalliya kamar mu, bayan hijjabi har da wani uban niƙab, to waye zai ce yana son ki, kalli ranar da muka je barkar gidan su Saratu, kowa yayi kwalliya amma ummi ke kin zunduma over size hijjab fisabilillahi. Ranar da babu school, ki zo gidanmu akwai wata mai mayukan gyaran jiki, muje ta haɗa miki mai sai na biya”

Ummi shiru tayi tana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗacin gaske, da yake yi mata kai komo tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta, wannan shawara maryam take bata ko ci mata fuska.

“Ina magana kin yi mini shiru” Maryam ta yi maganar a ɗan hasale, dan daga abun da maryam ta tsana a halin ummi bai wuce miskilanci da shariya ba.
Wanda ba wai miskilancin bane kawai, tana gudun shiga harkar mutane, kar tayi wani abun da za aci mata mutunci.

Ummi ta ɗago ta kalli maryam, hawaye har ya zagaye cikin fararen idanuwanta, ta ɗan juya brown ɗin ƙwayar idonta ta ce “Maryam, I won’t bleach my skin, ko a so ni a haka, ko a ƙyale ni, banbancin fari da baƙi a wurin Allah, wanda yafi tsoronsa mu ƴan adam mune muke ɗorawa kanmu”.

Cikin ƙuluwa maryam ta ce “Au dan na baki shawara ina nema miki mafita, shine ki ke kuka, har ki ke nema ki kafirta ni? To ki ƙarata ummi, amma zaki ce na gaya miki, wallahi babu wanda zai aureki da wannan baƙin da gidadancin”

Ummi tayi murmushi mai ciwo hawayen na zubowa ta ce “Ba ke ki ka fara faɗar haka ba maryam, an daɗe da gaya mini ba zan auru ba ni mummuna ce, dan haka ban sa aure a ka ba dama, nima na san maza farare suke so masu kyau, in dai ubangijina yana sona shikenan maryam” tayi maganar cikin sanyin halinta.

Sai kuma jikin maryam yayi sanyi, ta ce “Am sorry please, ba ina nufin na ɓata miki rai ba ummi, mafita nake nema miki”

Kawai ummi ta tashi ta bar ajin, domin kuwa an kaɗa ƙararrawar tashi.

Kai tsaye gida ta nufa, tana tafe tana hawaye ta cikin niƙabinta.

*
Babban mutum ne zaune mai cike da nutsuwa da kamala,kallo ɗaya zaka yi masa ka san a cikin hutu yake, falon da yake zaune kawai ya ƙawatu dai-dai gwargwado.
A hankali yake zuƙar tea ɗin da yake hannunsa, yana kallon ƙatuwar plasma tv da ke manne a jikin bango, sai dai kana gani ka san ba kallon yake yi ba, zancen zuci yake yi.

“Alhaji ya dai?”

Wata mata tayi maganar tana ƙoƙarin zama a kusa da shi.

“Bakomai” yayi maganar yana murmushi.

“A’a da komai mana, zancen zuci ka ke yi, shekaru sun ja, yakamata a din ga rangwatawa kai, kar wani ciwon ya kama ka”

Ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ce “Da ciwo zai shigeni saboda tunani, da tuni ya shige ni hajiya. Lokaci yayi da yakamata na huta, huta nake buƙata amma ki duba ki ga haryanzu ban huta ba, ni nake fama da harkar kasuwancina, gaba ɗaya yaran nan basu saka komai a gaba sai shashasha. Na tara dukiya, suna ta bushashasha, gaba ɗaya babu hankali ko nutsuwa a cikinsu da zai tallafe ni yanzu, su karɓi ragamar kasuwancin ni na huta.

Ko kartun kirki babu wanda ya tsaya ya kammala a cikinsu, duk da tarin kuɗin da na kashe musu da sun yi karatu, amma kalli duk shashanci suke yi, suna manya amma duk babu mai saiti a cikin su.

Matan ne kawai nutsatsu a cikin su, su kuma duk matan wasu ne, ragamar babban kasuwanci irin wannan ma ai ba na mace bane ba.

Jiki a sanyaye ta ce “Na sani Alhaji, ka yi haƙuri, ka ɗan ƙara musu lokaci, mu cigaba da addu’a, kuma a cigaba da jan su cikin harkar kasuwancin”

“Eh su ƙarasa ni ba. Wane lokaci zan ƙara musu? Salim na da shekara talatin da ku san biyar, dukkansu babu yaro a cikinsu, wane lokaci zan basu banda wanda na basu a baya. Zan yanke hukuncin da nake ganin ya dace kawai”.

Ta ɗan gyara zamanta ta dube shi ta ce “Wane hukuncin kenan?”

“Zaki gani idan na yanke” yayi maganar yana sauya channel da remote.

*
Ummi kuwa tsaye take a gaban mudubin ɗakinta, tana ɗaure da zani kasancewar daga wanka ta fito, ta shiga ƙare wa kanta kallo a jikin madubin.
Ta saki gashin nan a bayanta, ta din ga kallon ƙwayar idonta, da take brown sosai, cikin idon kuma fari ƙal, ta gangaro kan fatarta da take jiƙe da ruwa, baƙa mai ɗaukar ido.
Ta kalli gashin ta, ta ɗan shafa shi a hankali, tana tambayar kanta wace irin halitta ce ita haka. Ita kanta ta san ba ta taɓa ganin mai irin halittarta ba, a ƙasar hausa duk wanda take haɗuwa da su, ba ta taɓa ganin mai irin gashin kanta da kuma ƙwayar idonta ba.

A hankali ta murza fatar jikinta, tana tuna maganganun su kausar masu sosa rai, wai wankan baƙi asarar ruwa. Baƙar mace bolar maza, irinta kuma bolar da ko recycling ba za a iya yi ba.

“Da gaske ba zan yi aure ba, saboda maza ba sa son baƙar mace mai duhu kamar ni? To haka zan cigaba da zama a gidan kamar baiwa? Ko kuma zasu mayar da ni ƙauye daga baya, saboda ban samu miji ba? Dama Iya ta ce babu wanda zai aureni, saboda munina. Idan ma na yi aure zai iya ƙara aure ya daina kula ni, saboda ni bani da kyau, to wa ma zai ce yana so na?.

Ko dai maryam da gaske take hijjabin da nake sakawa, da kuma munina ba zai bari a aureni ba?”

Ta dubi ƙirjinta, da tudunsu ya ɗaga sosai.

Ta girgiza kai ta ce “Ni ba zan iya bari a ga jikina ba, kuma ba zan saɓawa Allah ba, idan na yi bleaching na raina halittar da yayi mini kenan. Ya bani lafiya bani da wani mummunan ciwo da yake hanani sukuni, sai jarrabawar rayuwa da tsananinta bai sanya na rabu da rai na ba”

Istigfari ta hau yi, duk hawayen idonta ya kasa daina zuba.

“Yaya ummi” ta jiyo muryar noor.

Tayi saurin share hawayenta ta ce “Na’am ƴar gidan anty ummi”

“Ki ɗora ni a kan mudubin na taɓa gashinki”

Ummi ta yi murmushi, ta ɗora noor a kan mudubinta, noor ta saka hannu biyu ta kama gashin tana dariya.

Can sai ta ƙurawa ummi ido, ta ce “Kuka ki ke yi?”

Ummi ta girgiza kai ta ce “A’a mama”.

Noor ta kai hannunta ta shafo sauran hawayen ta ce “Kuka ki ke yi, maama ce ta dake ki? Ko su anty intee ne?”

Ummi ta ce “A’a mura nake yi ne, zauna a kan katifata na saka kaya” tayi maganar tana ajiye noor a kan katifar.

Noor ta din ga tsalle a kan katifar tana waƙe-waƙenta na yarinta.

*
Iya da idris fa sun haɗu da wanda suka fi su tashanci, dan mussaman uwar hindu ta din ga tatsarsu kuɗi, wai hindu ba ta da lafiya, za a saya mata magani, yadda ake kula da kowacce mace mai ciki, dole a kula da Hindu, tun da da bai yi abun da yayi ba, da hindu ba ta samu ciki ba.
Dama akuyancin sa ne ya hana su bashi hindu, dan haka tun da ya hilaceta ya ɓata ta dole ya kula da ita, saboda sun san ƴar su ba lalatacciya ba ce ba a baya.
Yadda baban hindu yayi alƙawari, sai da ta haihu, ta haifi santaleleliyar jaririya, cibiya kawai aka yanke, aka naɗo jaririyar a zani, har da mahaifarta suka kai suka direwa Iya a tsakar ɗakinta, sai tsala ihu take yarinyar.

Mutane kuma suka taru a gidan, ƙarshen tonon asirin dai da asiri ya tonu, domin kuwa rana tsaka ƙanwar babar hindu suka zo suka kawo jaririyar, sannan suka sanar da iya cewa, sun saka yara sun kama wani ƙaton rago da iya ke kiwo a waje, an kai shi can gidan za a yankawa mai jego bayan kwana bakwai na ƙauri an sakawa jaririya sunan Iya wato Hajara.

Ayshercool

    CUTARWA!

P19

P19

Tun da Iya take, ba ta taɓa cin karo da tashin hankali irin na yau ba, gida ya cika da mutane, ana ta salallami, yayin da Idris ya kulle kansa a ɗaki ya kasa fitowa saboda kunya.

Tabbas da yana da kuɗi babu abun da zai hana shi guduwa, kodayake yayan Hindu yayi masa kashedin muddin ya gudu sai ya ɗaure babansa.

Yarinya ta din ga tsanyara ihu, a tsakiyar ɗakin Iya.

Su kuma suka wanda suka kawota suka gama tijararsu da rashin mutunci, suka fice suka bar gidan.

Iya ta ce a ɗauki ƴar a kai wa babar Idris, dan ita ba ta san ya za ta yi da jaririya ɗanyen goyo haka ba, ita ko nonon ma yanzu babu sun suɗe sai fata, dan haka sai dai uwarsa.

Babar Idiris kuwa ta ce “Iya ke yakamata ki riƙe wannan ƴa ba ni ba, tun da dama sunanki suka sawa yarinyar, ba yadda ban yi ba na bawa yarona tarbiyar da ta dace, amma ki ka ƙi saboda yana da sunan mahaifinki, kin ɗau son duniya kin ɗora masa. Ko laifi yayi na yi masa faɗa, sai ki ci mini mutunci.
Dan haka Iya ke zaki kashe wannan wutar, wallahi ki ka bani jaririya ban san yadda zan yi da ita ba”.

Cikin fusata Iya ta ce “Ni ki ke gayasa haka lami?”

“Iya ba rashin kunya ba ce gaskiya ce, da kin bari na bawa ɗa na tarbiyya da haka ba ta faru ba”.

“Rufe mini baki, har wata tarbiyya ce da ke da zaki bawa wani? Ke ɗin a yaya ki ke? Ki zo ki ɗauke yarinyar nan ki san yadda zaki yi da ita”

Lami ta ce “Ban gane ba iya, ni na yi mata cikin, wallahi ba zan ɗauka ba”

“Lami uwata ce take faɗa kina faɗa?”

Lami ta ce “Maganar gaskiya ce fa, in ɗauki ƴa in yi yaya da ita? Ta in da aka hau ta nan za a sauka ai”

Iya ta ce “Rabu da ita, na san maganinta, yanzu abun da ya fi dacewa shi ne ka je, ka ce musu mun amince a ɗaura auren nan su karɓi ƴar nan. Amma wallahi Idiris ya cuce mu, ya janyo mana masifa da abun kunya, ga ragona da nake son sayarwa lokacin sallar layya, sun tafi da shi, ku san yadda zaku yi ku karɓo mini ragona”.

Ilyasu ya ce “Iya yanzu waye yake ta rago, muntuncinmu ya gama zubewa”

Baban su Idris ya ce “Ina ga kawai mu je mu samu iyayen nata, ina sa’adatu ta zo ta yi wa yarinyar wanka, a saka mata sutura, mu je gidan su Hindun”

Sa’adatu ta ce “Taɓ ƴar gaba da fatihar? Wallahi ba zan taɓa ƙazanta ba, sai dai uwarsa ta wanketa, haka kurum in taɓa masifa”

Sakin baki Iya tayi tana cewa “Wai me yake damun matan nan ne? Ƙaddara ce fa, kowa zata iya faɗa a ka”

Sa’adatu ta ce “A’a irin wannan ƙaddarar Allah ya tsayar da ita a kan wanda ta sama”

Haka dai gida ya yamutse, kamar ayi yaƙi.

Da ƙyar babar Idris ta yi wa yarinyar wanka.

*
Yau lahadi, ummi sun yi hutun makarantar islamiyya, sai dai ta kasa zama wuri ɗaya ta hutawa ranta, dan kuwa ta san babu wanda ya bata wannan damar.
Dan haka wuni tayi tana kaiwa tare da komowa, wurin yin kwalema da tsabtace ko ina na gidan.

Tana sanye da dogon hijjabinta, da ya zame mata tamkar uniform, duk zafi ko sanyi, ko a cikin gida, da hijjbi take yawo, dan ko da ta fara ƙirgar dangi, tsananta rufe jikinta tayi, balle yanzu da take aji biyar na sakandare ta ƙara cika sosai.

Dan idan tana girki, wuta ta sha kamo mata hijjabin, ko ta yi ɓarna a kitchen, farida ta ci mata mutunci, amma hakan bai sanya ta daina sawa ba.

Hijjabin jikin nata ya sha jiki ya koɗe, sai dai kasancewar a goge yake, muninsa ya ragu.

Tana mopping noor na biye da ita suna hira, ta saki jiki tana biyewa noor, suna shiririta.

Ƙamshin turaren da ya cika falon ne, ya sanya ummi ɗaga kai, aikuwa tayi tozali da intee ta fito, sai taku take ɗaya-ɗaya.

Ta sha doguwar rigar abaya, ƙamshin kansa ummi ta kasa tantance wane iri inteesar take yi.

Tayi light make up, sai wani yatsuna fuska take yi.

Ummi a ranta ta ce “Tubarkallah masha Allah, kyau yana in da yake” ba iya kyan da inteesar tayi ne ya burge ummi ba, doguwar rigar jikinta ma ta tafi da ita, ta ji ina ma ita ma tana da ita ta saka, taga ya zata yi a ciki, dogayen riguna irin haka suna burgeta”.

“Ke! Kalli gabanta kar ki kama mini kurwar ƴa” farida tayi maganar cikin tsawa.

Ɗan zabura ummi tayi, ta cigaba da aikin gabanta.

Kausar kuwa ta kwashe da dariya, yadda ummin ta ɗan shagala da kallon yayarta kamar shashasha.

Farida ta yi murmushi ta ce “Farar mace….

Caraf kausar ta ce “Alkyabbar mata”

“Farar mace kalar kyau, kalar babban gida da manyan motoci, kalar hutu da jin daɗi farar mace mowar mata”

Inteesar kamar kanta ya fashe, saboda kirarin da mamanta ke yi mata.

Ta dubi ummi ta ce “Baƙar mace borar gida”.

Farida ta amsa da “Idan ta samu mijin ba”

“Idan ba ta samu ba kuma ta dauwwama ƴar wanke-wanke”

Ummi tayi burus, ta cigaba da hirarta da noor, tana jin zuciyarta na wani irin zafi.

Intee ta yamutsa fuska ta ce “Maama bari na je, ya kirani a waya, ya zo”.

“To shikenan, a kula sosai, a iya karairaya da jan hankali”

“Kar ki damu maama, ammm ummi kin kammala girkin da na saki?”

“Na gama”

“Ok, ki shirya mini komai a tray, in the next few minutes ki kawo mana”

Kallon ƙasan ido ummi tayi mata, ta yi mata girkin tarar saurayi, kuma ita za ta kai musu.

Tayi ajiyar zuciya, tare da ɗan girgiza kanta.

Farida ta ce “Ke ummi in tambayeki mana”

Ummi ta ɗago tana kallonta.

“Wai dan Allah ina babarki ne?”

Ummi ta ɗan yi jimm, dan ba ta zaci wannan tambayar ba.

“Ban san in da take ba”

“Kamar yaya baki san in da take ba?”

Ummi ta ce “Ai tun ranar da ta tafi, Iya ta hana a tafi da ni, ban sake ganinta ba, sau kusan uku ƴan uwanta na zuwa su tafi da ni, amma ta ƙi bayar da ni”.

“Kuma saboda rashin lissafi, ba ta sake neman in da ki ke ba, daga ita har ƴan uwanta, yau shekarar ki nawa a gidan nan, ko kare daga dangin majaifiyarki ba wanda ya nemi in da ki ke, wace irin uwa ce wannan? Ko suma ba sa buƙatar ki ne, an rasa mai riƙe ki, aka liƙa mana, anya babu lauje cikin naɗi a game da ke, ta hanyar aure aka same ki kowa yake gudunki?”

Tuni idon ummi ya fara tara hawaye, cikin ƙoƙarin kare mahaifiyarta ta ce “Ai an ce ba ta da lafiya, tun da aka ƙwace ni, ta haihu ɗan babu rai, ta samu matsalar ƙwaƙwalwa”

“Mahaukaciya ce kenan?” Kausar ta faɗa kai tsaye.

Farida ta ce “To ai mahaukaci ya san ɗan sa, jahilci kawai da rashin sanin ciwon kai, idan ita ba ta da hankali, ƴan uwanta fa?”

Ummi ta yi shiru, ta kasa magana.

Farida ta shigo falon a fusace ta ce “Wai ke ummi me ki ke taƙama da shi ne? Cewa fa na yi ki kawo mana abinci, amma dan wulaƙanci kin shanya ni, bana son rashin mutunci”

Ummi ta jingine mopper ba tare da ta ce komai ba, ta je ta ɗauki tray, ta kai wa saurayin intee.
Kallo ɗaya ummi ta yi masa ta sunkuyar da kai, gaba ɗaya bai yi kalar mutane masu ɗa’a ba.

Tunanin abun da farida ta faɗa ya ɗarsu a ran ummi, idan an ce mamanta ta samu matsalar ƙwaƙwalwa, to ƴan uwanta fa, yakamata ace sun nemeta, ta san da a hannunsu take, ba za su wahalar da ita sosai ba.

Sakawa tayi a ranta a wannan karon idan kawu ya zo gida, za ta tuna masa alƙawarin da yayi mata na binciko maata in da mamanta take, dan ita ba ta taɓa jin ko sunan garinsu wani ya faɗa ba.

*
Can gida gagarawa kuwa, an samu da ƙyar da siɗin goshi, su hindu sun karɓi jaririya, babanta ya ce idan ta yi arba’in, su zo su kawo kuɗin aure, kuma yadda ake auren budurwa komai da komai, haka za a haɗo mata, kuma shayarwa da hindu, za ta yi, sai an biyata kuɗin shayarwa ko su dawo musu da jaririyar.

Kan su dawo gida, sai da babanta ya caje su kuɗi masu yawa, sannan suka dawo, suka sanar da Iya abun da babanta ya faɗa.

Iya ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wannan wane irin matsiyatam mutane ne? Sai an yi mata komai kamar auren budurwa ba ta riga ta haihu ba, har wani kuɗin shyarwa suke nema, a gidan ubanwa aka taɓa haka, ai da an dawo da ƴar a din ga bata nonon akuya”.

“A’a iya, a samu a lallaɓa mu rabu da mutanen nan lafiya, kowa ya ɗebo da zafi ai bakinsa, gobe ba ya ƙara ba”.

Da labari ya iske idiris kuwa, masifa ya fara yi, yana baloƙoƙon shi fa ba ya son Hindu, ban da zalunci yarinyar da har haihuwa ta yi, tayaya za a ce wai ayi mata kaya kamar budurwa, saboda son zuciya.

Cikin tsananin fusata mahaifinsa ya ce “Rufe mini baki, ko na turmushe ka a wurin, mara mutunci, muna zaman zamanmu ka janyo mana masifa, ka sanya kowa a tashin hankali, kuma wallahi ko ka so, ko ka ƙi sai ka auri yarinyar nan, ka ƙarata can bayan auren” yayi masa ta tas ya tafi ya bar shi.

Magaji yayi murmushi ya ce “Allah sarki ummi, baiwar Allah yanzu idan na ce hakkinta ne ya fara bibiyarku, sai ace ƙarya ne a hayayyaƙo mini, da ka yi haƙuri da ummi, ka nema mata magani tsaf zata warke ku zauna lafiya, amma ka din ga muzanta ta, kana yamaɗiɗi da ita a kan larurar da ta same ta, har abokan ka suna ce maka angon ɗaɗɗoya saboda zunzurutun wulaƙanci da tozarci, ka saketa bayan ka gama azabtar da ita, saboda ka na taƙama da kai ɗan iska ne.
Kai ma gashi Allah ya tozarta ka, gara nata tarihi zai iya shafe shi, naka kuwa har gaban abada ba zai goge ba, kuma kaɗan ka gani, ba dai bariki ba sai ma ka auro wannan ɗin, zaka san ka yi asarar mace”.
Duk wannan faɗan da magaji yake yi masa, bai iya cewa komai ba, saboda ya san ba shi da gaskiya, kuma yanzu yana cikin tashin hankali da tunanin menene mafita.

*
Ummi tana ta dakon zuwan kawu, tare da fatan Ubangiji Allah ya sanya ya samo in da mama take, gara ta tattara ta koma can wurinta, dan da ta san in da take da ta daɗe da barin gidan nan, ko bola take bi za ta din ga bin ta.

Sai da aka shafe kusan sati uku, sannan dr. Ya zo gida, bayan yayi kwana biyu ya ɗan nutsu ya huta, ummi ta same shi shikaɗai a falo, ta gaishe ta samu wuri ta zauna.

“Ummana, ya aka yi ne?”

“Dama ba wani abu bane kawu, dama tambayarka zan yi ko ka gano in da maman take?” Tayi maganar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ɗan yi shiru yana nazarin ta, sannan ya ce “Akwai matsala ne?”

Ta girgiza masa kai alamar a’a.

“Na san ba zaki faɗa ba dama, rabonki da yi mini wannan zancen an kwana biyu, na san a takure ki ke ummi, amma ki yi haƙuri, ina nan ina ta ƙoƙari a kai, ba yadda ban yi da Iya ba, ta ce mini ita ba ta sani ba.
Ƙanin babanmu da yayi masa walicci ma ya rasu, su ilyasu sun ce basu san sunan garin ba, su dai kawai an zo da mota an kai su, na san faɗa kawai suke yi, Iya ce ta hana su faɗa.
Amma ina nan ina ta bincike, ina da hotunanta biyu, da aka yi mana bayan bikin da na je gida, ina ta bincikawa, na samo sunan garin, ainihin yankin da take a garin ne ban sani ba, ana ta bincikawa ummi, ina sane ban manta ba, ki cigaba da addu’a da kula da karatunki, komai zai warware in sha Allah”.

Ummi ta risuna ta ce “Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi”.

Ya ce “Amin ummana, baki ce Allah ya yi mini albarka ba”

Rufe fuska ummi tayi tana murmushi.

Ya ɗora da cewa “Kwanaki an ce mini ɗan uwan mamanki ya zo ganinki, Iya taƙi gaya masa in da ki ke, ta ci mutuncin sa ya tafi. Amma dai in sha Allah ina nan ina ƙoƙari a kai”.

“To kawu na gode”

Ta tashi ta nufi ɗakinta, tana sake jinjina ƙiyayyar da Iya take yi wa mahaifiyarta da ƴan uwanta.

Kasancewar maryam gaba take da ummi dama, dan haka ta riga ummi candy, tun kan ta yi candy aka kawo kuɗin aurenta, dan haka an yi candy babu daɗewa bikin ya tinkaro.

Maryam ba ta tsaya saurarar ummi ba, ta sayi anko ta bawa ummi duk kyauta, sai dai da ƙyar farida ta bar ummi ta je rana ɗaya bikin, shi ma da ta je kasa sakewa tayi, dan wareta ƴan makarantar ma suka din ga yi, dan haka nan da nan ta koma gida ta bar wurin.

Satin Maryam biyu a gidanta, mijin ya tafi da ita can wurin aikinsa, kasancewar soja ne babba.

*
Kwanci tashi asarar mai rai, iyayen hindu suka din ga tatsar su Iya kuɗi, har sai da ta yi watanni shida cif a gida, sannan aka ɗaura auren Idris da hindu, saboda babanta dagewa yayi a kan sai an kai kuɗin aure da duk wani abu na al’ada da ake yi.

Tare da cigaba da yi musu barazanar cewa, zasu dawo musu da ƴar su.

Abun kunya dai da ake gudu, ya riga ya gama watsuwa a cikin gagarawa, na abun kunyar da jikan Iya ya tabka.

Gidan da ummi ta zauna, aka sake kama haya, kansancewar ba kowa a ciki, aka ƙara gyara gidan, aka kai hindu da jaririyarta.

Ko kallo hindu ba ta ishi idris ba, haka ita ma ba ta kansa ta bi ba, ta cigaba da sabgoginta da ƴar ta, sai dai cikin dare yarinyar nan ta tashi, ta din ga tsala ihu kamar za ta shiɗe.

A fusace ya tashi ya ce “Dalla malama ki ɗauki ƴar ki saka tayi shiru, ta cika wa mutane kunne da kukan banza”.

“To kai mai zai hana ka saka tayi shirun, na ga kaima ƴar ka ce”

“Ƴar gaba da fatihar? Kar ki sake haɗani da ita”.

“Ko ƴar gaba da meye uban waye yayi cikinta, ai ba ita tayi kanta ba, ka ga wallahi ka ce zaka takura mini, ko ka ɗaga mini hankali sai na koma gida na gaya musu. Kai ba ma ka da kunya, ni ka ke gayawa ƴar gaba da fatiha ce, uban waye ya lalata ni?”.

“Iyayenki dai suka ja miki, da ba aurenki zan yi ba, suka hana ni”.

Hindu ta yi shewa ta ce “To uban wa ye zai baka auren ƴa? Kana ɗan iska?”

“Eh ina ɗan iskan amma ai gashi an liƙa mini ke”

“Oho kai ka sani dai”

Ta dubi ƴar da ke ta tsala ihu ta ce “Ke hajara tsohuwar banza, ubanki ya ce ki yi masa shiru, ƴar gaba da fatiha”

Idiris ya ce “Tsohuwar banza, kakata ki ke zagi kenan?”

“Eh to, idan ka tsargu hakan ne” haka suka din ga faɗa kamar kaji, a tsakiyar daren nan maƙwabta na jin su.

Abdul ne yayi sallama a kitchen, ummi na girki, suna ta tilawar Alqur’ani ita da noor.
Raino ummi take yi wa noor da kulawa, bacci ne kawai yake raba su, baccin ma wataran a ɗakinta take yi.
Tun kan noor ta shiga makaranta, ta iya azkar da karatun Alqur’ani, dan ba ta yi pre nursery ba, kai tsaye nursery 1 aka kaita, saboda ta har rubutu ta fara iyawa.

Sai dai noor masifaffiya ce, ba ta taɓuwa a wurin yayyenta, dan baki ne da ita sosai da sosai.
Ba ta jin maganar farida, kamar yadda take jin maganar ummi, fitsara da rashin kunya kuwa ba a magana, ummi da Abdul kawai take ɗagawa ƙafa, ƴar mitsitsiya da ita ga azabar taurin kai, ummi ce kawai take iya sarrafa ta yadda take so, dan haka ba wani shiga shirgin noor suke yi ba, tayi maka rashin kunya ka jibgeta ba za ta yi kuka ba.
Ummi tayi ta mata faɗa, dan ita kanta tana mamakin rashin kunyar noor.

“Yaya ummi” Abdul ya kira sunanta.

Cikin haɗa baki ita da noor suka ce “Na’am yaya Abdul”

Abdul ya tsuke fuska ya ce “Da ke nake?” Ta girgiza masa kai tana ɗan murguɗa baki.

Ummi ta kalli Abdul ta ce “Yaya Abdul yaya ake ciki? Ka dubo mini”

Ya miƙo mata envelope ya ce “Eh to, congratulations you got nine credits including maths and English, i know you can do it ai”

A take ummi tayi sujjadar godiya ga Allah, noor ma ta durƙusa tayi, ummi ta ɗago tana Alhamdilillah.

Noor ta ce “Wai menene? Me aka yi?”

Abdul ya ce “Yaya ummi ta ci jarrabawa, dan haka ita ma very soon zata shiga jami’a”

Tsalle noor ta din ga yi tana ihu, ba tare da ta san ma menene cikakken bayanin ba.

Kausar ta shigo kitchen ɗin tana tambayar lafiya.

Noor ta ce “Yaya ummi ta ci jarrabawa, za ta shiga jami’a”.

Tsaki kausar ta yi ta ce “Shi ne kuma ki ke yi mana ihu?”

“Eh ɗin, yeeee yaya ummi ta ci jarrabawa ” tayi maganar tana tsalle ta fita daga kitchen ɗin.

Kausar ta yi tsaki ta fice, Abdul ya ce “Yaya Ummi, kina zaune an haifi mai tare miki faɗa”

Ummi ta ce “Ni mamana saliha ce, amma mama ƙarama ta fiye tsiwa” suka yi dariya, ummi na sake godewa Allah a kan wannan gagarumar nasara da ta samu.

Takanas saboda ummi dr. Ya dawo gari, saboda shirye-shiryen nema mata admission, Abdul yana level 2 a BUK yana karantar Agric.

“Dr. Wai ya na ganka a gida a tsakiyar sati haka? Kuma na ga baka daɗe da tafiya ba”.

“Abdul yayi mini magana a kan waec ɗin ummi, ina son in ƙarasa mata abubuwan da yakamata kar ayi mini ba dai-dai ba”.

“Shi ne ba zaka wakilta wani ba, sai ka dawo da kanka?”

“Ki na da damuwa da hakan ne?”.

Haushi ne yakamata tayi masa banza, duk iya ƙoƙarin ta a kan cire hankalinsa daga kan ummi, ta kasa nasara ɗari bisa ɗari.

Ta sake kallonsa ta ce “Wai ni dr. Zuwa yaushe zan cigaba da jerawa da ummi a gidan nan, intee tana gama secondary, nake son a aurar da ita, yaron ya matsa, ita kuma tana nan shirin tafiya jami’a ma take yi, gaskiya ina son privacy a gidana, ba zan cigaba da jerawa da gandamemiyar budurwa ba”.

“Intee ke ki ka takura a karɓi kuɗin aurenta, ba dole na yi muku ba, ni kuma a ƙyale mini ƴa tayi karatu. Guda nawa ummin take da ki ke wani zancen gandamemiyar budurwa, yanzu fa za ta shiga jami’ar”.

“To wai ina uwarta, a mayar da ita wurinta mana”.

A fusace ya ce “Wai a kan ki ummin nan take ne?”.

Muryar noor ce ta katse shi, tun daga wajen ɗakin take ƙwala masa kira.

Ya ce “Na’am shalelena”

“Kalli littafina, uncle ya saka mini 10 over 10, assignment ɗin da anty ummi ta koya mini”.

Ya ce “Wow masha Allah, congratulations baby”.

“Thank you ” ta faɗa cikin iyayi sannan ta ce “To nima tunda na ci jarrabawar, zan shiga University?”

Ya kwashe da dariya ya ce “From primary one to university?”

“Eh, ba anty ummi ma ta ci jarrabawa zata shiga university ba?”

Yayi dariya, ya biye mata ta gama shirmen ta, ta tafi, sannan ya kalli farida ya ce “Farida wai zuwa yaushe zaki daina planing ɗin nan, noor tayi girma yakamata ace kin sake haihuwa, 4yrs fa”.

Farida ta yamutsa fuska ta ce “Nifa na gama haihuwa, yaushe Allah ya amfana guda huɗun”.

“Amma da bani da yadda zan yi na riƙe ne, sai ki faɗi haka, Allah ya yassare mini yadda zan kula da yarana, meyasa zaki ce kin daina haihuwa?”.

Ta miƙe tsaye ta ce “Ka auri ummi ta haifa maka!”.

Wani irin damm ƙirjinsa yayi, ya bita da kallo, saboda munin maganar da ta faɗa.

Ya girgiza kai kawai, domin ba shi da abun da zai faɗa gaba ɗaya.

Iya ƙoƙari kawu yahaya ya yi wa ummi, a kan harkar makarantar ta, dan ma farida na ta yi mata mugunta a kan wasu abubuwan.
Yayi mata komai sai dai ɓangaren sutura ummi na fuskantar barazana, domin kuwa ummi ba ta da suturar kirki, duk da ma’abociyar hijjabai ce, su kansu hijjaban nata duk sun mutu su yi haske.

Ayshercool

CUTARWA!

P20

20

Ummi ganin al’amuran take yi kamar a mafarki, duk da tsanani da matsi, haɗi da ƙalubale daban-daban yau ga ta a makarantar jami’a, lallai lokaci yana sauri.

Hakazalika ta na ta shirye-shiryen haɗa saukarta ta biyu, domin kuwa bayan ta yi sauka ta cigaba da zuwa makaranta, ƴan ajinsu galibi duk sun yi aure, dama duk sun girme mata.

Wuri ɗaya ta samu ta zauna a ajin, jikin window ne in da take, hakan ya bata damar kallon shige da ficen ɗalibai, tsofaffi wanda sun kusa fita ma, da masu rawar kai wanda yanzu suka shigo jami’a.

Shigowar wani babban mutum ajin ne ya sanya ɗaliban ajin nutsuwa, tare da gaida mutumin.

Ya amsa musu, tare da gabatar da kansa a matsayin HOD ɗin su, ya nemi da kowanne daga cikin ɗaliban, ya tashi ya gabatar da sunansa da kuma garin da yake.

Haka nan gaban ummi ya faɗi, dan kuwa ba ta son mutane, da duk wani dalili da zai sanya a takurata da kallo.

Ɗalibai suka din ga gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya, kan azo kan ummi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, sai wata irin fargaba take yi.

Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye, fuskarta sanye da facemask, malamin yayi mata alama da ta sauke facemask ɗin.

Gabanta ya sake faɗuwa a karo na biyu, hannunta har rawa yake yi, ta sauke facemask ɗin tana jiran jin ƙanan magana kamar yadda ta saba, sai dai ba ta ji hakan ba.

Sai dai ta kasa magana, sai da ta ɗan sauke numfashi, sannan ta ce “My name is…. Sai dai ta kasa ƙarasawa, saboda yadda gaba ɗaliban suka juyo suna kallonta.

Ummi na da murya mai matuƙar ɗaukar hankali, duk wanda bai santa ba, idan har tayi magana dole zai waiwaya domin ganin mai muryar.

Ko a islamiyya idan ana musaffa, Alla-Alla suke yi a zo kan ummi, saboda ta iya ƙira’a mai daɗin sauraro.

Ganin ta diririce saboda kallon da ake yi mata ne ya sanya malamin takowa zuwa gabanta, ta ko ƙara sunkuyar da kanta ƙasa, tare da wasa da yatsun hannunta a cikin hijjabinta.

“Kin manta sunan naki ne?” Ta girgiza masa kai.

Ya sake cewa “Ko ba turanci ne?” Nan ma ta sake girgiza masa kai.

“Oya ya sunanki?”

“Salma Muhammad Bashir”

Yayi murmushi ya ce “What a beautiful name, na ga duk a tsorace ki ke, but mark you, this is university idan malamai suka gane kina jin tsoron magana a public, za su yi ta takura miki da tambaya, ke kina jin tsoron amma ki ka zaɓi aikin jarida? Ai harkar jarida na masu baki ne. But you can do it when you overcome your fear”

Ta ɗago a hankali ta ce “Thank you sir”

“Ƴar wace ƙasar ce ke?”

“Jigawa” tayi maganar muryarta na ɗan rawa.

“Ƙasa fa”

Ta ce “Au Nigeria”

“Are you sure? Ko dai ta ɓarauniyar hanya ki ka shigo mana ƙasa? Kin yi kama da baƙaƙen larabawan Afrika”

Ummi a ranta ta ce ‘Amma kuwa an cuci larabawa, ko kuma ni aka cuta, maybe ba’a yake yi mini’

Ƴan ajin kuwa dariya suka hau yi, ya ce “Kalar idonta da complexion ɗin ta, ba irin na ƴan Nigeria bane, dan haka zamu bincika idan baki da lasisin zama a Nigeria mu mayar da ke ƙasarku” yayi maganar cikin zolaya.

A dole ummi ta ƙaƙalo murmushi.

Ya ce “Yi zamanki, Allah ya yi albarka” kan ta zauna ta risuna ta ce “Na gode sosai Allah ya jiƙan magabata” ya ɗan ƙurawa ummi ido, yadda take amsa masa magana ma, kawai ya isa ka gane tana da tarbiyya sosai. Ya ce “Amin” sannan ya suce gaba.

Yayi musu nasiha sosai da sosai, a kan kula da ilimi da kuma tarbiyarsu, da ba su shawarar su riƙe addinansu, kar su lalace saboda kawai sun ga sun shiga jami’a.

Kowa harkarsa yake ba ruwan wani da wani, dan haka ummi ta ji daɗin hakan, da babu wanda ya matseta balle ya takura mata.

Baki har kunne ta koma gida tana murna, duk da tana zuwa gidan ta tarar da uban kwanukan wanke-wanke, da wankin kaya, kuma an cinye abinci tas, kuma ana jiran ta ɗora na dare.

Hijjabi kawai ta canza ta hau aiki, noor ta din ga bin ta, tana tambayarta “Anty, kin yi magana a gidan radiyon?”

Ummi ta ce “A’a mamana, sai an kwana biyu tukuna”

“To ta ina zaki din ga shiga radion kiyi magana?”

Sai dare yayi kin yi bacci, zan buɗe gurin batirin in shiga ta ciki.

Noor ta buɗe baki cikin mamaki, sannan ta ce “To zaki shiga da ni nima?”

“Sai kin ƙara girma sosai tukuna, noor ta dinga tsalle tana murna.

*

“Bilki, ki kira Bauchi ki gaya musu ba fa haka muka yi da su ba, ni fa ba bar musu ɗa na na yi ba, haba sun riƙe mini ɗa ko leƙo ni baya yi”.

Ta kalleshi ta ce “Taɓ, ba ruwana kun fi kusa, ka kira su ka gaya musu mana”

Yayi murmushi ya ce “Shima zan gamu da shi ne, ko a waya baya nema na”

Ta ɗan yi murmushi ta ce “Wai ɗazu da ina bacci, da wa ka ke magana ne, ka ke ta faɗa?”

Ya ɗan ja guntun tsaki ya ce “Salim mana, wai zuwa yayi na bashi kuɗi zai yi gyaran mota”.

“To meyasa ba ka bashi ba?”

“A kan me zan bashi? Duk iya ƙoƙarin da zan yi na yi wa yaran nan, dan su zama na gari, amma abu ya gagara. Yanzu daga shi har ɗan uwansa da a nutse suke, da yanzu yaushe zan din ga wannan zirga-zirgar?”

Bilki ta ɗan yi ajiyar zuciya ta taɓe baki ta ce “Laifin babarsu ne, da ta bari suka lalace”.

Yayi saurin girgiza kai ya ce “No, Hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar yara, dan har ta fiki tsanantawa ma wasu lokutan”

Ta tsuke fuska ta ce “Eh, nice mai sake da tarbiyya kenan?”

“A’a mai gado ba haka nake nufi ba, ai kin ga matan duk lafiya ƙalau, gashi duk sun yi aurensu suna zaune lafiya, su ɗin ne dai, kuma shima na san jarrabawa ce, ba a barin ɗan Adam haka”.

“Allah ya kyauta, amma nikam ba zan bari auta ya riƙa ba yazo na kasa contrilling ɗin sa ba, aure zan yi masa yana dawowa”

“To hakan ma yana da kyau, Allah ya zaɓa abun da ya fi alkhairi mai gadon zinari” yayi maganar yana jan hancinta.

“Ba wata mai gadon zinari, ka koma wurin dattijuwar matarka”

Kwashewa yayi da dariya, ya ce “Bilkisu, hajiyan ce dattijuwa Allah ya sa ta ji ki, ai shekarunta ba sa nunawa, saboda gayunta, kuma ni bana ganin girmanta, ba ta fi fifty fihe ba, amma idan ta ɗaura ɗankwali kamar ƴar 30yrs. Ai da yake ni na mayar da ita tsohuwar, ganinta nake kamar ƴar 16 lokacin da na aurota, hajiya ba ta tsufa”

Wani irin haushi ya kama bilkisu, ta yinƙura za ta tashi ta bar masa wurin, ya riƙeta yana dariya ya ce “Danne kishin nan kar ki bari ya fito”.

Alhaji Tahir kenan, tsohon ɗan boko, kuma babban ɗan kasuwa, da yake juya naira yadda yake so.
Mutum ne mai sauƙin kai da matuƙar son iyalinsa, mussaman ƴaƴansa, dan mutum ne mai biyewa ra’ayin yaransa, duk abun da suke so muddin bai saɓawa addini ba, zai yi musu shi, yana bawa iyalansa ƴancin yin abun da suke so, ba tare da ya takaura musu ba.

*
Rashin wayar hannu, yana daga manyan abubuwan da suka zama barazana ga ummi, a harkar karatunta, gashi ita ba kowa take raɓs ba, balle idan an bayar da assignment ko class work tayi, idan assignment ne ta gwammace ta kai yamma a makaranta, ta je Library ta yi.

Gashi farida ta tsiro da sababbun hanyoyin muzguna mata, ta hanyar ƙirƙirar mata abun da za ta sanya ta makara, wataran har ma ta rasa lectures baki ɗaya.

Daga baya ne take iya roƙon Abdul aron wayarsa, tayi assignment da ita.

Abdul ne ya gaya wa dr. Yakamata a saya wa ummi waya, saboda makaranta.

Da ya tashi dawowa ya taho mata da sabuwar waya, mai kyau da tsada, amma farida ta ƙwace ta bawa kausar, kuma ya kasa magana a kai.

Ba waya kawai ba, hatta undeas ummi na fuskantar matsala a kan su, sai dai idan ta tara ƴan kuɗi da ƙyar, idan farida ta aiketa kasuwa ta sai na gwanjo.

Daga baya Abdul ya saya mata wata ƴar ƙaramar waya, gionee take amfani da ita.

Makaranta ma da nata irin ƙalubalen, domin kuwa ƴan ajinsu, akwai yaran masu kuɗi, akwai ƴan ƙarya da yaran talakawa masu jin cewa su wasu ne.

Gani suke ummi ba tsararsu ba ce da za su yi mu’amala da ita, mussaman ganinta babu suturar kirki, kullum cikin hijjabi, hijjaban nata da guda biyu ne take zuwa da su, sai takalminta ɗaya ɗan wambai.

Banda masu zunɗen halittar ta, ko tambaya za ayi a aji, idan za a tanbayeta, sai malami ya  ce dark skin girl.

Ummi ta sanya a ranta babu wani ƙalubale, da zai sanya ta kasa haƙuri ta cimma burinta.

Yunwa da tafiyar ƙafa a kan karatun nan suka zamewa ummi jiki, ko lissafasu ba ta yi a cikin wahalar rayuwa, handout kuwa ba kowanne take iya saya ba, wataran idan har zata sayi handout, sai ta yi trecking, domin samun kuɗin sayen handout.

Ta wuni a makaranta ba cin abinci, ta koma gida ta ci uban aiki, a ƙarshe ba godiya sai zagi da muzantawa.

HOD kuwa ba ƙaramin mutunta ummi yake yi ba, saboda idan ta ganshi sai ta kai ƙasa take gaishe shi, idan ta ganshi da jaka, sai ta bishi ta karɓa.

Yana jinjinawa tarbiyyar ta, da bayar da misali da ita, dan shi rabon da yaga ɗalibi mai biyayyarta tun a zamaninsu, shima zamanin na su ba kowa ba.

Ummi ta dawo daga masallacin makaranta, tana ta sauri ta ƙarasa aji, saboda malamin da zai shiga, ko da minti ɗaya ya rigaka shiga aji, ba zaka shiga ba.

Abun da kunnuwanta suka jiyo mata wani ɗan ajinsu ya faɗa ne ya tayar mata da hankali matuƙa.

“Kai ishaƙ, ka yi sauri mu tafi kar malamin nan ya rigamu shiga, ga gorillar ajinmu can na ta sauri”.

Kalmar gorilla! Ta daki ƙirjin ummi, hakan ya haifar mata da wata irin mutuwar jiki, munin nata har ya kai a kira ta da gorilla?

Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri-sauri, tamkar zata kifa ƙasa ta shiga ajinsu tana wani irin kuka, wane irin abu ne wannan?.

Ishaq ya kalli abokinsa ya ce “Kai Nura kamar fa ta ji ka”

“Ahha haba dai?”

“Tana kusa fa ka faɗa”

Nura yayi tsaki ya ce “To sai me?”.

Ishaq ya ce “A’a nura, zuciya ba ta da ƙashi, cin fuska ba shi da daɗi, tuntuni na gaya maka ka daina kamanta ta da dabba, yarinyar so silent ba ruwanta da kowa bai kamata ba wallahi”

“Ka ga kar ka isheni, jokes ne”

“Ai gaskiya ce, ba wani jokes wallahi, ko kusa yarinyar nan ba ta yi kama da abun da ka ke misalta ta ba, hidden beauty ne da ita, baƙinta da rashin gayu ke hana kyanta fitowa, amma ba ta yi kama da abun da ka ke faɗa ba”.

Suka tafi aji, yana ta yi masa faɗa, suna shiga aji kuwa, kan ummi a ƙasa da alama kuka take yi.

Gaba ɗaya jikin Ishaq yayi sanyi ya ce “Ka gani ko? Kuka take wallahi”.

Shigowar malamin ya sa kowa ya nemi wuri ya zauna, ya fara gabatar da abun da ya kawo shi.

Sai dai yana lectures yana ganin yadda ummi ke sharɓar hawaye.

“Ke are you ok? Meyake damunki ne?”

Ta kasa magana ta tashi tsaye tsam, ta ɗauki jakarta cikin kuka ta ce “Sir dan Allah ka bani iznin tafiya gida”

Duk da zafin malamin da rashin son wargi, amma kukan da ummi take yi, yana nuna akwai tsantsar damuwa a zuciyarta.

Kamar yadda ake son malami ya kasance cikin kulawa ya ce “Babu damuwa, amma zaki iya tafiya? Ko ki na da ƙawa ta raka ki gidan?” Ta girgiza masa kai ta ce “Zan iya tafiya”

“Kin tabbata?” Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce “To shikenan, ki tafi a hankali ki yi ta Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ta jinjina masa kai ta risuna masa ta yi masa godiya sannan ta fice ta tafi gida.

Ta daɗe ba ta yi kuka mai yawan na yau ba, tun noor tana rarrashinta, har ita ma ta fara kukan.

Ta rarrashi noor, ta aiketa kitchen, ta mayar da ƙofar ɗakin ta rufe, ranar ba irin bugun da farida ba ta yi ba, a kan ummi ta buɗe ta zo ta yi mata aiki, amma mursisi taƙi buɗewa abun za ba ta taɓa yi ba kenan. Ta san ƙarshen abun dai, zagi ne za ta sha shi da cin mutunci a wurin farida.

Tayi shiru tana tunani kala-kala a zuciyarta “Ko zan ji daɗi a rayuwata? Ko zan huta, ko kuma a haka zan cigaba da rayuwa, sanin gaibu sai Allah.
Idan ina da rabon hutawa da jin daɗi, Allah ka kawo mini su da wuri, ba dan na gajiya da karɓar jarrabawar ka ba, ni’imominka gareni sun ninka jarrabawar, Allah ka shiga lamarina” tayi maganar a bayyane cikin kuka

Sai da ta jera kwana biyu ba ta je makarantar nan ba, ranar da ta je, malamin da a period ɗin sa ta tafi gida, ya kirata ofishin HOD, suka din ga tambayar ta meyake damunta, dan malamai da yawa sun fuskanci kamar tana da social fear.

Kukan da ta kasa riƙewa a gaban su, ya tabbattar musu da tana da damuwa sosai da sosai.

Duk yadda suka matsa ta, ba ta gaya musu abubuwan da suke damunta ba, duk da tana da abubuwa da dama a ranta, da take son tattauna shi da wani, amma ta kasa samun wanda zuciyarta za ta nutsu da shi, su tattauna sosai, ko ba ayi mata maganin damuwar ba, atleast ta furta abun da yake damunta.

Suka nemi zasu zauna da mahaifinta, amma ta din ga yi musu magiya, a kan kar su yi hakan, dan a ganinta idan aka yi hakan tamkar ƙure babanta kawu yahaya ne, domin kuwa yana iya ƙoƙarin sa a kanta.

Nasiha suka din ga yi wa ummi, tare da bata ƙwarin gwiwa, a kan muhimmancin mayar da hankali a kan karatunta, da shanye ƙalubale, wanda ba ƙaramin jin daɗin nasihar ta su yi ba.

A ƙarshe HOD ya cigaba da tsokanar ta, da cewar ba ta da visa baƙar balarabiya ce ta shigo musu ƙasa.

Ɗaya malamin yake ce mata, tun da ƴar jarida ce ita, kuma an san su da neman suna, idan ta mutu yana son idonta zai saya da tsada, ta shiga kundin tarihi.

HOD ya ce “Allah ya kiyaye, wannan idon na larabawa ne a Nigeria Masha Allah, in dai wannan tarihin ne mun yafe, ko Salma”
Ummi ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Ummi ta ji daɗin mutuntawar da malaman da take wa kallon iyaye suka yi mata, da nuna damuwarta kamar ta su, nasihohin su, sun shige ta sosai da sosai.

HOD yaje ajin su ummi, ya yi musu jirwaye mai kamar wanka, ta hanyar gugar zana a kan wulaƙanta ɗan Adam, da muhimmancin girmama ɗan Adam.

Ta samu sassauci daga jin wani abu mai nauyi da yake damun zuciyar ta.

Sai dai ta kasa manta kalmar gorilla, noor da Abdul suna falo suna kallon film ɗin king Kong, ummi har ta wuce ta dawo, ta ce “Yaya Abdul”

Ya ɗaga kai ya ce “Na’am yaya ummi”

“Dan Allah wai ina kama da gorilla?”

Wani irin banzan kallo yayi mata ya ce “Wace irin magana ce wannan?”

Cikin son ɓoye abun da ya faru ta ce “Amm, dama kawai na tambaya ne, dan na ji ana cewa ni mummuna ce”

“Kuma sai ki haɗa kanki da biri, haba ummi, ke tsakani da Allah idan aka ce ke mummuna ce sai ki yarda? Ki ƙarewa kanki kallo, a kan me zaki yadda ke mummuna ce? A halittar Allah babu mummuna, duk wanda ya ce miki mummuna ki ce ubansa ya sassaƙo kamar ki”

Noor ta ce “Maama kenan za a gayawa, itama tana cewa yaya ummi mummuna, kuma fa yaya ummi gashinta har nan, tafi fa maama gashi”

“Tashi ki bar nan wurin kan na tatsileki, baba suda” yayi maganar yana kallon noor.

Ummi kuma ta ce “To shikenan yaya Abdul, na gode sosai “

“Dan Allah kar ki kuma faɗar haka “

“Ba zan sake ba in sha Allah” sai dai a ranta tana jin har ta mutu ba zata manta da Nura ba, ya shiga cikin jerin mutanen da take yi wa wani irin kallo a zuciyarta.

Ƴan ajinsu ummi ba su tashi mamaki ba, sai da result ya fito na first semester, ummi ta ja magana, GPA ɗin ta 4, wanda kaf ajin babu mai wannan grade ɗin.

Kasancewar ɗabi’a ce ta ɗan adam, mu’amala domin cikar muradi, ya sanya suka fara lallaɓowa, domin shiga jikin ummi, amma fafur taƙi ta cigaba da rayuwar kaɗaici.

*

Gidan Idris kuwa, kamar masu zaman bariki, saboda faɗa zagi yana zagin hindu tana ramawa, tana kiran sunan uwarsa da ubansa tana zagi, idan yayi gangancin dukanta kuwa, ta dinga wawurar abubuwa tana kwaɗa masa kenan, dambe da zage-zage har ƙofar gida kamar dabbobi, maƙwabta suna raba su.
Sulhu kuwa an yi musu shi babu adadi, amma abu ya ci tura.
Sam ba ta ganinsa da mutunci, shi ma kuma haka, taje gidansu ta gaida Iyayensa kuwa ba ta wannan, saboda ta ce ba zata je gaida tsohuwar banza ba, ta ji labarin zaman da yayi da matarsa ƴar uwassa, ita ba zata lamunci cin zarafi ba.

Ya gaji da iskancinta, ya kamata yayi mata tulus da duka, ashe tana da juna biyu, ta yanke jiki ta faɗi, ƙarshe dai sai da iyayenta suka rufe Idris a police station, aka wulaƙanta shi aka kai ruwa rana kafin a sake shi, banda kuɗin magani da aka saka ya biya.

Kwana biyu da dawowar sa daga hannun ƴan sanda, ya je ya samu hashim a kan ya bashi shawara, so yake a lallaɓa kawu yahaya da ummi, a dawo da auren su.

Hashim ya ce “Haba Idris, lokacin da na din ga ankarar da kai ai kasa ganewa kayi, ummi tafi ƙarfin ka yanzu, wace irin azaba ce ba ka yi mata ba, tun tana ƙaramar yarinya. Yanzu ta sauke Alqur’ani har sau biyu, ta shiga jami’a tana karatu, ka ce ta dawo, to tayi maka me? Kai da ko kwalin sakandare baka da shi”.

Idris ya waro ido ya ce “Ummin ce a jami’a, kai waye ya gaya maka?”.

Hashim ya ce “Muna waya da ita, bautar ƙasa nake son na gama, idan Allah ya sa na samu aiki, zan nemi auren ummi”.

Idiris yayi masa wani mugun kallo ya ce “Amma dai ka ci kai, matar da na saki zaka aura? Bazawara ce fa kai kuma baka taɓa aure ba. Haryanzu bana son ummi, ban taɓa jin ƙaunarta a raina ba, amma ina da muradi a kanta, idan har ba ta dawo mini ba, idan ina raye baka isa ka aureta ba”.

Hashim ya yi murmushi ya ce “Zamu gani ai” Idris ya tashi fuuuu ya tafi.

Idris yayi shiru yana tunani, tun da mahaifinsu ya takura masa da maganar aure, ya gaya masa ga ƙudurinsa, Iya ta ce bai isa ba, ba zai auri bazawar da ƙaninsa ya saki ba, kuma ta riga ta cire ummi daga jikokinta tun da ta ƙi yarda a rufawa Idiris asiri!.

Babansa kuma ya ce Idan ya sake ɗaga maganar nan, zai yi masa abun da bai taɓa tsammani ba.

Duk son ummi da islamiyya, haka ta haƙura, saboda yanayin makaranta, ta samu wata makarantar, a nan unguwarsu, take zuwa asabar da lahadi ɗaukar karatu.

Sai dai ganin ummi tana da ilimin addini dai-dai gwargwado, idan aka yi mata ƙarin nata karatun, sai a haɗata da aji tayi musu ƙarin Alqur’ani da wasu litatafan.

Duk da ayyuka sun ƙara yi mata yawa, hakan yayi mata, saboda tana zama busy sosai, tana hana zuciyarta tunane-tunane da sukan jefata cikin damuwa.

Ga bikin Intee ya matso kusa, sai gori take sha a gidan nan, wai ta zama guzuma, babu mashinshini a haka za ta dauwwama wanke-wanke da shara.

Kawu yahaya yayi rawar gani, ya yi wa inteesar kaya na kece raini, ya so ace ta fara makaranta kan yayi mata aure, amma ta dage soyayya ta rufe mata ido, ta ce ita fa aure take so, dan haka ba yadda ya iya ya ƙyale ta.

Sagir ya danƙaro mata uban kayan lefe, kaya ba na wasa ba, ya ciko akwatuna da kaya, sai iyayi take tana rawar kai.

Albarkacin auren inteesar, a wannan karon da kawu yahaya ya yi mata ɗinki, farida ba ta ƙwace ba, har da sabon takalmi, farida kuma ta bata tsohon mayafi, kalar kayan.

Ranar party, farida ta ce ta zauna a gida, ta kula da baƙi masu shige da fice, kuma ta tsaya a kan girke-girken da za ayi.

Ummi ta zage ana can ana party, tana gida suna aikin girki, dan ita ta jagoranci aikin abincin bikin.

Ranar wuni ya kama ranar da za’ayi ɗaurin aure, dan haka da wuri motoci suka kawo ƴan gagarawa.
Su Idris da babarsa, su magaji kafatanin ahalin Iya.

Lokacin ummi ba ta gidan, suna can tana ta hidima da ƙawayen inteesar, ana yi wa inteesar kwalliya.

Ummi ta yi wanka, ta yi wa noor, ta saka kayan ankonta da ita da noor.

Sai da inteesar ta kalli ummi ganinta babu mayafi, dan zata iya ƙirga rabonta da ta ga ummi babu hijjabi.

Tayi ture ka ga tsiya, ta kanannaɗe gashinta a ƙeyarta, ɗaurin ya zauna cas a kanta, ga ɗinkin ma dai-dai jikinta.

Ta shafa man leɓe, ta yafa mayafinta a kanta, ta rufe jikinta sosai, ta kama hannun noor, suka fice.

Wani irin farinciki ya kama ummi, ganin ƴan gida gaba ɗaya sun zo, dan rabonta da su tun da ta baro gagarawa.

Duk bin ummi suka yi da kallo, yadda ta girma ta zama budurwa.

Cikin su ummi ta shiga tana gaishe su, Iya sai wani hura hanci take yi.

Ta ce “Ina yaya magaji?”

Sa’adatu ta ce “Sun tafi wurin ɗaurin aure”.

Ummi ta karrama su da abinci, dan matar gidan ba ta ta su take yi ba, ta kai su ɗakinta, ta yi ta ɗawainiya da su.
Bayan azahar su Hashim suka dawo daga wurin ɗaurin aure, ummi baki yaƙi rufuwa saboda duk ƴan uwan mahaifinta sun zo.
Ɗaya bayan ɗaya ta din ga gaishe su, suna mamakin yadda ta girma, ta zama cikakkiyar mace, sai dai ko kusa bata kalli in da Idris yake ba.

Farida sai bin ummi take yi da kallo, dan ba ta taɓa tsayawa ta kalli ummi sosai cikakken kallo ba sai yau, rashin gyara ne ke ƙara munanta ummi, idan ka kalleta sau ɗaya sai ka sake kallonta, mussaman yadda take kokowa da mayafin, kasancewar ita ba ma’abociyar ta’amalli da shi ba ne ba.

kasancewar hashim shi ne mutumin ummi, can harabar gidan suka koma, suna ta hira.

Ya dubeta ya ce “Ummi, kawu yayi miki magana kuwa a kan batun nemo mamanki?”

Cikin sauri ta ce “A’a, ya ake ciki?”

“Subhanallah, ya ce dai kar na kuskura na gaya miki saboda wani dalilinsa, amma dai idan bai ganta ba yana daf”.

“Ya salam, bai gaya mini ba, ko maganar zan yi masa?”

“A’a, dan ya yi mini kashedin kar na gaya miki, ki kwantar da hankalinki duk abu zai haɗaku”.

Cikin karaya ta ce “Yaushe hankalina zai kwanta, tana raye amma rabona da ita kusan shekara goma sha, ina son ganinta”.

Idiris kuwa wani abu ne ya din ga yi masa zillo a maƙogwaronsa, ganin ummi tare da Hashim, gashi ta gayar da kowa, amma ko sashin in da yake ba ta kalla ba, balle ta gaishe shi.
Kasa daurewa yayi, ya nufi in da suke zaune.

Sai dai ummi na hango shi, ta miƙe tsaye ba tare da ta gama maganar da take yi da Hashim ba.

Cikin zafin nama ya sha gabanta, ya kalleta ya ce “Ina zaki je? Saboda wulaƙanci ki ka gaida kowa baki iya gaisheni ba, kuma na taho da ki ka ga nan zan zo, shine ki ka tashi”.

Cikin ƙwayar idon Idris ta kalla, wani abu mai kama da wuta yana zafi a ƙirjinta.

Tuni idanunta suka tara hawaye ta ce “Cikin abun da bana ƙaunar sake gani a nan duniya har da lahira, har da fuskarka, ka matsa ka bani hanya, ko kuma in yi maka abun da baka taɓa zato ba!”

Ayshercool.

  CUTARWA!

P21

21

Mamaki ne ya cika shi, har sai da ya bayyana a kan fuskarsa, bai taɓa tunanin ummi za ta iya furta abun da ta gaya masa ba, saboda tun fil azal tamkar sokuwa take ba ta da wani karsashi balle ta yi faɗa.

Bai gama nazarin ba, ta angije shi tayi wucewarta tana tsaki, abubuwan da suka faru a baya, suna sake dawo mata tamkar yanzu suke faruwa.

Ƙarshen cin mutunci da tozarci yayi mata a garin nan, wanda yana daga dalilan da ya sanya ba ta ƙaunar sake zuwa gagarawa, haryanzu baƙin ciki da mugun tabon da take da shi a garin, yana damunta.

Dan har cikin zuciyarta tana fatan a gidan duniya, Allah ya yi wa Idiris abun da ya yi mata kafin ya koma ga Allah, ba ta sani ba ko a gaba ta iya yafe masa, amma har zuwa wannan lokacin, ba ta ji alamar manta abun da yayi mata ba, balle ta yafe masa.

Ranar da ya fara kwana a ɗakinta, ya korota waje, ta kwana cir a tsaye ruwa yana dukanta, saboda mugunta da zalunci.

Tayi iya ƙoƙarin ta wurin danne hawayen da ke ta ƙoƙarin zubo mata, ana ta hotuna, angon inteesar sagir, da kansa ya ce ummi ta zo ayi musu hotuna.

Idiris ya jinjina kai, tare da tabattarwa da kansa zaman birni, da kuma zuwa jami’a ne ya sanya ummi lalacewa, domin kuwa an ce dama ƴan matan jami’a ba su da mutunci lalacewa suke yi.

Duk in da ummi tayi sai ya bita da kallo, tamkar wani shashasha, hindu da yake yi wa kallon wayayyiya kyakykyawa, yanzu duk ta tararraɓe, haihuwa uku tayi, har da waccan mai sunan Iyan, ƙirjints da yake ɗaukar hankalinsa, duk sun zube, kullum daga ciki sai shayarwa.

Amma yanzu ummi komai nata a tsaye kyam, dai-dai da jikinta, duk da tana ta rufe jikin nata da mayafi.

Bayan la’asar suka ce zasu yafi, dan ba su zo da niyyar kwana ba dama, saboda sanin halin farida.

Duk lalacewar naka naka ne, ummi ta ji daɗin zuwansu sosai da sosai, tayi ta yi musu fatan alkhairi har suka tafi.

Idiris kuwa kamar maye, saboda azabar kallo, har suka ɗauki hanya suka tafi.

Kallo ɗaya zaka yi wa rahama da yaronta, ka san ba a kwanciyar hankali take ba, ga dai kuɗi miji yana da shi, amma yarkace-yarkace hak take, dan hatta kayan sawa wasu lokutan farida ke bata ko ta sayawa ɗan, duk wannan ƙafafar da ikon babu shi, duk ta zama so silent.

Taro ya watse, aka kai amarya, ummi kuma ta sake cin uban aikin gyaran gida, ranar monday kuma ta tafi makaranta.

Gaba ɗaya jikinta a mace yake, da ƙyar take tafiya ma duk jikinta ciwo, saboda azabar aikin da ta sha, ba ta samu damar hutawa ba, a haka a tafe har gajiyar ta ware.

Karatun ummi yayi nisa, kuma haryanzu ba a samu wanda ya doke point ɗin ta ba, duk da ba ta fasa fuskantar ƙalubale ba.

Dan haryanzu farida da kausar ke cin ƙaniyarta.

*
Tana zaune ta duƙufa tana ta aikin shirin dutse, ɗanlami yayi masa jagora har cikin ɗakin da take zaune.
Ɗakin tsaf da shi, sai ƙamshin turare yake yi, kai ba ka ce mara lafiya ce a ɗakin ba.
Ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da aikin gabanta.

Ya ɗan ƙare mata kallo, shekaru sun ɗan ja, ta girma yanzu, amma tsaf da ita, tana samun kyakywar kulawa.

Ya dubi ɗanlami ya ce “Ɗan uwa, kuma a haka ba ta da lafiya?”

Yaya ɗanlami ya ce “Babu lafiya, wasu lokutan dai hankakin yana dawowa, wasu lokutan kuma sai ciwon ya dawo tayi ta shirme. Amma a hakan nan da take, za ta yi wanka, tayi shara tayi kwalliya ga shirin dutse nan ma gashi ka ganta tana yi, likita ne ya ce a samo mata abun da zai din ga ɗebe mata kewa.
Ka ga yanzu tafi sati ba ta yi magana ba, ba ta duka ba ta zagi, kaga daga mutuwar mijinta, ga rabata da ummi, ta zo ta haihu ɗan ba rai, tayi jijjiga depression yakamata sai kuma dai ta samu matsala gaba ɗaya.
Ban taɓa tunanin wani daga dangin baban ummi zai biyomu ba, dan mun yi alƙawarin ba zamu sake zuwa ba, irin jafa’i da mugun bakin da mahaifiyar ku tayi wa ƴar uwarmu, ya sanya muka ce gara mu yanke alaƙa da ku kawai”.

Dr. Yayi ajiyar zuciya ya ce “Tun da na ɗauki yarinyar nan, nake fafutukar neman ina ku ke, ni ban san garin nan ba, ainihin in da kuka zauna aka aureta, mun je aka ce ba kwa nan, abubuwa dai duk ba su yi daɗi ba, sai fatan Allah ya kyauta”.

Mama da yaya maryam da suke gefe suka amsa da amin, dan maryam ta zo gida yau, babu tsammani suka ga kawu yahaya.

Maryam ta ce “To ya ummin take? Ba ka zo mana da ita ba?”

Ya girgiza kai ya ce “Ba yanzu ba, ummi na nan a jami’a”.

Yaya maryam ta ce “Dan girman Allah, ummin?”

Yayi murmushi ya tashi ya ƙarasa gaban ta ya zauna yana kallonta, ba tare da ta ɗago ba tayi murmushi ta ce “Baban ummi”

Ya ce “Na’am”.

“Jigidata da ka tsinka mini nake gyarawa”

Sunkuyar da kai suka yi cike da jin kunyar abun da ta faɗa, dan tafi sati ma ba magana.

Yayi murmushi ya ɗebi dutsen da take ta shiryawa ya ce “Gaskiya ban kyauta ba, ki haɗa wata maza”.

Ta sake yin murmushi ta ce “Da na san zaka dawo, ai da na yi kitso, an yi mini lalle, kaina ba kitso, bana son kitso tun da ka tafi bana son kitso” tayi maganar tana cire hular kanta, gashin kanta baƙi wuluk ya bayyana.

Yaya maryam zata yi magana, ya ɗaga mata hannu tare da girgiza mata kai, ya ce “To tun da na dawo yanzu sai ayi ko?”.

“Ba zan yi ba, tun da ka tafi ka bar ni, ka ƙi ka dawo, Iya ta ƙwace mini ummi, ɗa na ya mutu ka ƙi ka zo ka ganni kuma bani da lafiya” tayi maganar tana kuka wiwi.

Ya ce “To ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ba zan sake tafiya naƙi dawowa ba”

Ta riƙo hannunsa ta na cigaba da kuka ta kwantar da kanta a hannunsa ta ce “Baban ummi”

Ya amsa mata da “Na’am”

Ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce “Ka je ka karɓo mini ummina, Iya ba zata din ga yi mata wanka ba, ko idan yamma ta yi ta saka mata kayan sanyi, ba ta son ummi, dan Allah baban ummi ka karɓo mini ummi, kaga katifata ta ishemu ni da ita, idan ka sai mana gida sai in dawo gagarawa ko?”

Ƙura mata ido yayi, cike da matsanancin tausayinta, lallai yana daga horon da za ka yi wa uwa, ka rabata da ɗan ta, duk da tana cikin hauka, amma ba ta manta da ƴar ta ba.

Yayi ajiyar zuciya ya ce “To shikenan, ki daina kukan ya isa haka, mayar da hularki, kiyi haƙuri” ta ɗauki hularta ta saka.

Ta ja bakinta ta sake yin shiru.

“Zan kawo miki ummi in sha Allah, amma ba yanzu ba”.

Yaya maryam ta ce “Saboda me? Abun da ta daɗe tana jira kenan, ka taimaka”.

Ya ce “Ina da dalilina, kuyi haƙuri dan Allah”

“To amma mu ai ka bari muje in da take”.

Kawu yahaya ya ce “Da ina da ƙudurin rabaku da ummi, da ba zan neme ku ba, ina da hujja mai ƙarfi sosai.
Zan cigaba da shiga lamarin nemawa mariya magani in sha Allah, komai zai daidaita kuma zai wuce”.

Ba haka suka so ba, amma ba su san takamaimai menene dalilinsa na ƙin haɗa su da ummi ba.

*
Hangen dala ba shiga birni ba, domin kuwa inteesar tayi zaton soyayyar da suka sha da sagir a waje, ita za aje a cigaba da yi a gidan, sai abun da take so shi zai din ga yi mata, amma ina.
Ya nuna mata shi namiji ne, mage mai kwanciyar ɗaukar rai, a gida ta saba ba abun da take yi, ummi ce take komai. Yanzu kuma ya ce shi ba zai ɗauki ƴar aiki ba.
Dan haka sai komai ya din ga bata wahala, asubar fari zata tashi ta haɗa masa breakfast, gashi su yi ta faɗa dan abincin nata ba daɗi, ga almubazzaranci kamar ba mace ba.
Ga rashin kunya da rashin iya magana, gashi ɗan uwan mata, yana da tarin yayye da ƙanne mata, ga uwarsa mai shegen sanya ido. Sai ƙannensa su zo gidan su fi sati, gasu manya duk sun girmeta, su yi ta yi mata rashin mutunci, idan tayi magana su ce za su yi mata dukan tsiya.

Abun duniya ya damu inteesar, ta dawo gida tana kuka, ta gayawa mamanta.

Farida a zatonta zata iya maganin abun, ta kira Sagir tana masifar dan me ba zai tsawatarwa ƙannensa ba?
Ya ce mata ba zai iya ba, baya son ya saɓawa mahaifiyarsa.

Abu kamar wasa aka fara jamb, kawu yahaya ya turawa inteesar kuɗi, ya ce taje tayi jamb, a nema mata admission.
Amma sagir ya ce ba yanzu ba, sai ta haihu, domin kuwa a lokacin ma laulayi take yi.

Kawu yahaya bai matsa ba, farida ta din ga masifar dan me ba zai dage sai inteesar ta fara makarantar yanzu ba?

Ya bata amsa da “Yanzu ya fi ni iko da ita, shiyasa tun tana ƙarƙashin ikona, na so ta fara makarantar, yadda bai isa ya hana ba, amma ku ka dage, dan haka ni ba abun da zan ce”.

*
BAYAN WANI LOKACI!.

Kasancewar tsakiyar damuna ne, an ɗan kwana biyu ba a yi ruwan sama ba, dan haka ana tafka zafi, ga uwar rana da ake ƙwalawa.

Tamkar ba ita ranar ke duka ba, haka take tafiya sannu a hankali, tana ratsa layukan unguwar, sannu a hankali take tafiyar, tamkar tana tausayin ƙasa, kamar mai rangji haka take tafiyar kamar tana tausayin ƙasa.

Ta cikin niƙabinta take kallon dogon layin, tare da lissafa sauran tafiyar da ta rage mata, ta isa in take fatan zuwan.

Layin shiru, sai lokaci lokaci, ababen hawa ke giftawa, manyan gidajen layin ko ina a rufe.

Ƙarar babur ta ji, kasancewar gefen hanya take bi, ya sanya ko a jikinta, dan ko waiwaya wa ba ta yi ba, ashe layin da yake gabanta yake ƙoƙarin shiga.

A ɗan fusace ya ce “Ke, kurma ce ne? Sai mutum ya tureku, ace bai kyauta ba, ba ki ji ina horn bane?”

Ta tsaya cak, ta ɗan ja wasu seconds, sannan ta juyo ta kalleshi ta cikin niƙab, sai dai ba ta ce komai ba.

Maimakon ya wuce ya tsaya ya ji me za ta ce, idan rashin kunya za ta yi masa, ya ƙare mata ta tas.

A hankali ta ce “Sorry, ga hanya wuce” tayi maganar tana ɗan ja baya ta bashi hanya.

Fuskar ta a rufe da niƙabi, amma muryarta ce ta saka shi ƙara kallonta.

“Malama idan zaki ware murya ki ware, da na bugeki ai ba zaki maƙale murya ba”.

Ta ce “Ikon Allah, me muryata kuma tayi maka, ai na ce ka yi haƙuri ka wuce”

Tsaki yayi ya ja babur ɗin sa ƙirar lifan, ya yi gaba.

Ita kuma ta yi ajiyar zuciya, ta cigaba da tafiya.

A ƙofar ƙaton gate ɗin gidan ta tsaya, mutum biyu ta tarar sanye da uniform na security, suka dubeta suka ce “Gurin wa zaki je?”

Ta ce “Habu baka gane ni ba?”

Jin muryarta ya sanya shi cewa “Ahha wata sabon gani, ke dama kina duniyar nan?”

Ta ce “Ina nan mana, ya aiki ya kwana biyu?”.

“Alhamdilillah, gaba ɗaya tun da ƙawarki ta bar gidan nan muka daina ganinki”

“To ai gashi na zo wanke laifina yau, ina fatan mami na nan?”.

Ya ce “Eh tana ciki”
Ta ce “Yauwwa na gode” ya buɗe mata ƙaramar ƙofar gate ɗin, ta shiga ciki.

Ɗayan ya kalleshi ya ce “Ka barta ta shiga? Baka kira hajiya bilkin ba, kuma ba ta ɗaga niƙabinta ba”.

Habu ya ce “Ai ƴar gida ce, ƙawar maryam ce, tun da tayi aure ne ta daina zuwa”.

Ya ce “Ok, na so ta ɗaga niƙabin naga fuskarta, muryarta tayi mini daɗi”.

“Ji ɗan wahala, ka sani ko yanzu tayi aure, ka shiga hankalinka”.

Ummi kuwa sashin mami ta nufa, fasalin gidan yana nan yadda yake, amma yanayin fentin da aka sassauya masa da wasu abubuwan zaka san arziki ya fi na da.

A falo ta tarar da mai aiki, duk da ƴar bata san ƴar aikin ba, suka gaisa sannan ta tanbayeta ko mami tana nan.

Mai aikin ta ce “Eh, tana falon sama”

“Ki ce mata ummi ce ta zo” mai aikin ta jinjina kai ta nufi ƙafar benen ummi kuma ta zauna.

Bai kai mintuna biyar ba, mai aikin ta saukko, ta ce wa ummi ta shiga.

Ummi ta tashi ta bi bayan ƴar aikin.

Da sallama ummi ta shiga, mami ta waiwayo tana cewa “muryar wa nake ji ne haka? Gaskiya koma nayi fushi”

“Tuba nake mami”

Sai dai tana zagayowa, ta tarar da na kan babur da ya kusa tureta da lifan, yana zaune ya barbaje ƙafa a kan centre table, sai yanzu ta gane a in da san shi.
Sai da ya ɗan sake ɗaga kai ya kalleta shi ma.

Nan suka gaisa da mami, mami nata mitar ummi ta ɗauke ƙafa ta daina zuwa tunda maryam ta bar gidan.

Ummi ta kalleshi ta ce “Ina wuni?”

Ya basar ya ce “Lafiya ƙalau”

Mami ta ce “Laaa ka amsa kuwa? Kema meyasa ki ka gaishe shi? Ƙaninku ne fa, ƙanin maryam ne Raihan ne.
Kai kuma ka amsa kamata yayi fa ka gaisheta” ya wani basar.

Ummi ta ce “Ƙyaleshi mami, ai dama su Allah ya bawa girman” tayi maganar tana ɗaga niƙabin fuskarta.

Sai yanzu shima ya ganeta, ranar saukarsu da maryam a makaranta.

Mami ta ce “Ya wani je ya tara gemu, yafi kowa girma kai ka ce wani babba ne, ni wannan gemun ina tantama idan ba mai ya shafa ya fito ba, dan ga gemun nan dai, amma hankali da saura”.

Ummi ta yi murmushi ta ce “Girma ya riga hankali kenan” sai da ya ɗan buɗe baki jin abun da ummin ta faɗa.

Mami ta ce “Eh mana, ya  makaranta ummi?”.

Ummi ta ce “Mami makaranta muna jiran result”

“Masha Allah, lokaci ba wahala har kin gama ummi, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, to ya batun aure kuma? Ko invitation ki ka kawo mini?”.

Ummi ta sunkuyar da kai, tayi murmushin yaƙe ta ce “Tukuna dai mami”

Mami ta ce “Ya salam, Allah ya kawo nagari ummi, yanzu fa maryam kusan shekarar ta bakwai da aure, ke kuma shiru duk ƴan islamiyyar ku sun yi aure, saura ke, amma kar ki damu komai lokaci ne”

Ummi ta ce “To mami, bari na yi alwala dan Allah”

Mami ta ce “To shikenan ba damuwa, je ki yi”

Ummi na tashi raihan ya kalli mami ya ce “Dan Allah mami fisabilillahi meye na tambayar invitation ta kawo miki? Da shi ta kawo miki ai ba sai kin tambaya ba, kin ce shekarar maryam bakwai da aure ita ba ta yi ba, kin dawo kin ce tayi haƙuri lokaci ne, kamar fa kin mari mutum ne kina sane sannan ki ce yayi haƙuri”.

Mami ta ce “To uban tsari, ai da tausayi yakamata ace ita ma ta tashi haka, in da take tana shan wahala, matar yayan babanta ke wahalar da ita, shiyasa nake tambayarta ko auren ne ya zo, ta huta”.

“Matsalarku kenan mata, kune maƙiyan kanku, ladan ake rubutawa mace idan ta azabtar da ɗan wani? Kuma duk tausaya matan da ki ke, tun da dai ba ki samo mata mijin nan ba, ai sai ki yi mata addu’a, is like an insult at times, ka tambayi mace maganar aure, ni idan mace ne faɗa za ayi da ni”

Mami ta ce “Kai,tashi ka je mini aike na uban tsari”.

“To ɗaukko kayan, ki haɗo da kuɗin shan mai”.

“Duk kuɗin da babanka yake baka, sai ka damfareni dan zan aikeka, to ba zan bayar ba”.

Ya kashingiɗa ya ce “Mami idan kina son aiken nan a kan lokaci, ki bayar da cin hanci ” tashi mamin tayi tana hararsa.

Hakan yayi dai-dai da fitowar ummi, fuskarta a jiƙe da ruwa, gaban gashinta duk a kwance, gashin girarta ma tamkar za su haɗe.
Fararen idanuwanta suka bawa brown ɗin ƙwayar idonta fitowa sosai da sosai.
Ƙwayar idonta yake son kalla, domin tabattar da kalarta, sai dai bata bashi damar hakan ba, dan mayar da niƙabin ta rufe fuskarta, ta tayar da salla.

Mami ta dawo falon da ATM ɗinta, tana yi wa Raihan kashedin ya je ya dawo da wuri.

Ya karɓi ATM ɗin yaƙi tashi, ummi ta idar da sallar, tayi Addu’a ta cewa mami za ta tafi, tashi yayi ya riga ummi fita.

Mami ta ce sai ta tsaya ta ci abinci, amma ummi ta ce sauri take yi.

Ta ajiye wa mami kyautar kwalbar turaren humra.

Kuɗin motar da ta bawa ummi ma, ƙin karɓa ta yi, kuma da ganinta ka san tana buƙata amma mursisi taƙi karɓa ta tafi.

A babban falo ta tarar da shi, yana taje sumar kansa.

Har zata fita ya ce “Ki tsaya mu tafi tare na ajiyeki ko a titi ne”

Ummi ta girgiza kai ta ce “A’a na gode sosai, zan ƙarasa” bai kuma ce mata komai ba ta fito daga falon.

Ta fita harabar gidan, hakan yayi dai-dai da fitowar wata babbar mace, ta sha ado da lace blue, hannunta da wuyanta duk gold.

Wani matashi yana biye da ita, kai da ganinsa ka ga ɗan shaye-shaye.

Da sauri ummi ta ƙarasa in da matar take, ta ɗaga niƙabinta ta durƙusa ta gaisheta.

Matar ta faɗaɗaɗa murmushinta ta ce “Ummi yau kece a gidan, ba dan Allah yasa na fito ba tafiya zaki yi bamu gaisa ba?”

“Ba haka bane hajiya, a gurguje na shigo ne, kusan kullum ta hanyar nan nake bi, shiyasa na ce yau dai bari na shigo”

“Eh amma zaki tafi bamu gaisa ba ummi, ya gida ya makaranta?”

Ummi ta amsa da Alhamdilillah.

Hajiya ita ce uwar gidan mami, tun lokacin maryam na nan, tana son mu’amala da ummi saboda nutsuwarta, amma ummi ta janye jikinta ta daina zuwa gidan ma, saboda ba a ga maciji, tsakanin mami da Hajiya.

Ummi ta gaida Salim da suke tare da hajiya, ya amsa mata sama-sama.

Hajiya ta ce “Ummi kin yi aure ne?” Ummi ta girgiza mata kai.

“Ai da kin yi aure ban sani ba, sai mun yi faɗa”.

Kamar an jefo shi, ya dafo kafaɗar hajiya yayi ƙasa da murya ya ce “Ku daina yi wa mutum irin wannan tambayar babu daɗi”

Hajiya ta yi murmushi ta ce “To babban mutum”.

“Biki zaki je kenan?”

Ta ce “Eh, ƴar set ɗinmu ke auran ɗa”

Raihan ya ce “Shiyasa ki ka sha kwalliya, kamar ƙawar amarya mu ga jakar” ya karɓi jakar hajiya ya zuge.

Ya girgiza kai ya ce “Allah sarki Alhaji, an ɗebi kuɗinsa za aje ayi liƙi, to nima bari na ɗebi rabona” ya zura hannunsa ya ɗebo kuɗi ya zura a aljihunsa.

“Raihan abun har da gori, sai ka gayawa duniya kuɗin babanka ne”

Yayi dariya, ya ce “A dawo lafiya”

Ummi ma ta ce “Hajiya bari na tafi, a dawo lafiya “

Hajiya ta ce “A’a ummi, shigo mu fara aniyeki, sai mu ƙarasa wurin bikin”

Ummi ba za ta iya jayayya da hajiya ba, dan haka ta ce “To na gode”

Har ummi ta juya zata bi su ya ce “Eh ba shakka, ba zaki hau babur ba sai mota shikenan ai”.

Lokacin suna Islamiyya, Maryam bata da aiki sai bayar da labarin Muhammad Raihan, barkwancinsa da kuma tsokana, tsokanar ma irin mai cika cikin nan.
Dan haka ummi ba ta waiwayo ba, tayi murmushi ta bi bayan su Hajiya.

Ayshercool

    CUTARWA!

P22

22

Raihan ya nufi in da babur ɗin sa yake, ya ɗauka ya fita daga gidan.

Suna tafe suna taɓa hira da ita da Hajiya, duk da ta kasa sakin jiki da hajiyar sosai, saboda yadda take matuƙar jin nauyinta.

Har kan layinsu suka kai ta, ummi ta yi ta musu godiya, sannan ta sauka ta nufi gida.

A harabar gidan ta tarar da Abdul hannunsa riƙe da waya. Yana ganinta ya tsaya yana jiran ƙarasowarta.

“Yaya ummi ina ki ka shiga ne?”.

“Na ɗan biya wani wuri ne, meyafaru?”

Maama sai faɗa take yi, intee ce aka dawo da ita,  wai ta kuma yin ɓari, zasu tafi asibiti zata bar miki sallahu baki dawo ba.

Ummi a ranta ta ce ‘Ga kausar a gidan, ita ba za a bar mata sallahun ba’

A zahiri ta ce “Subhanallah, ubangiji Allah ya bata lafiya”.

Ya amsa da “Amin, Allah ya taimake ki sun tafi, yanzu na dawo daga kaisu, kafin su dawo na san ta huce ba za ta yi miki faɗa ba”.

Ummi ta ce “Haka ne, bari na yi sauri na shiga ciki”

Ta ƙarasa ɗakinta, ta yi wanka a gurguje, ta canza kaya ta saka hijjabinta na zaman gida, ta nufi kitchen.

Ta tarar da noor tana wanke-wanke a kitchen.

“Mama aiki ki ke yi haka?”

Noor ta ce “Eh, rage miki aikin nake yi, na san a gajiye zaki dawo, na ɓoye miki abincinki a ƙarƙashin dining, kar a cinye ba ki ci ba” tayi maganar cikin iyayi.

Ummi ta yi murmushi ta ce “Na gode sosai mama, bari na je na ci abincin, in zo mu ɗora abincin dare”

Noor ta ce “Kije ki yi bacci ma ki huta, zan yi miki greating kayan miya, na yi miki mopping”

Murmushi ummi kawai take tana kallon noor, soyayyarta da noor gamon jini ce.

Bayan magariba Rayhan ya dawo yana zaune a falon mami, yana ta bawa ƙannensa umarni, duk barkwancinsa idan yana nan basa wani sakewa saboda akwai dealing.

Mami na zaune a gefe tana cin abinci, tana kallon citruss.

Ya kalleta ya ce “Mami kin san ina ta yi wa baƙuwar ɗazu kallon sani, sai daga baya na tuna a wurin saukar su Maryam na san muryarta, dan ban ga fuskarta ba ranar”

Mami ta ce “Auu wai ummi, yarinyar kirki”.

Ya ce “Tana da tarbiyya sosai tun ranar da na ganta a wurin saukar nan, tubarkallah idonta mai kyau, ban taɓa ganin irin idonta ba”.

Mami tayi dariya ta ce “Kaga iskancin da su maryam suka din ga yi mata suna Islamiyya, saboda fatarta da idonta, duk in da maryam ta zauna sai ta bayar da labarin baƙin ummi. Gashi uwar riƙonta na azabtar da ita, ai ainihin ƙawancensu ma, maryam ce ta ture ta, ta faɗi ashe ƙonuwa ce a cikin ta, ta dinga zubar da jini, uwar riƙon ta ƙonata da dutsen guga a ciki, shima da ƙyar ta gayawa malaman ƙunar duk ta jagwale”

A razane raihan ya tashi zaune, ya ce “Ta ƙonata da dutsen guga fa ki ka ce?”

“Wallahi kuwa, maryam ta ce kusan kullum cikin kuka ummin take, kuma bata magana sai ta ga dama, duk yadda za ayi da ita, ba zata faɗi ga abun da yake damunta ba, sai kuka”.

Ya murza goshinsa a hankali ya ce “Mami kuma babu wani abu da ki ka yi, ki taimaka mata a wannan lokacin?”

“Rufa mini asiri, ai yanzu ba a wannan shishshigin, na so dai na din ga taimaka mata financially, amma yarinyar nan ba a bata kyauta ta karɓa, halint sai ita”

Ya dinga kaɗa ƙafarsa a hankali yana tunani, gaba ɗaya kalar ummi ba mai hayaniya bace, hasali ma fuskarta kalar tausayi ce.
To wani laifi za ta yi wa mutum, har a ƙonata da iron a ciki, ita kuwa wannan wace irin azzaluma ce.

Labarin da mami ta bashi tana dariya, bai ga abun dariya ba a ciki, na cewa yara na tsokanarta saboda tana da duhu da kuma ƙwayar idonta, meye a baƙar fata duk halittar Allah ce, kuma idanunta meye aibunsu, ai abun a hukunta su ne a wancan lokacin, ga child abuse a gida, makaranta ga takura daga abokan karatunta, Allah ka ɗai ya san the hardship she goes through.
Dan bai manta yadda Maryam ke bashi labarin abun da ake yi wa ummi ba, da yadda take kwatanta masa baƙinta, sai duk iya ƙoƙarin sa wurin gano muninta shi bai gani ba.

Fuskarta kawai yake hangowa, ko ɗazu da suka yi faɗa kan ya shigo bashi da gaskiya, amma ta bashi haƙuri, komai nata simple ne.

Ya miƙe tsaye ya ce “Mami sai da safe, bacci nake ji” yana gama maganar ya fita.

*
Ko da farida ta dawo sai da ta ci wa ummi mutunci, duk da ta san ummin wurin aiki take zuwa, domin kuwa bautar ƙasa take a lokacin a wani gidan jarida, daily news.

“Maama dan Allah ki daina yi wa anty ummi faɗa, ba gashi nan duk mun gama yi miki aikin gidan ba”.

Cikin tsawa ta ce “Idan ina magana ki na saka mini baki sai na yi ball dake” tayi maganar tana nuna noor da yatsa.

Ta mayar da idonta kan ummi ta ce “Dan kan ki, gaba ɗaya kin mayar mini da yarinya fitsararriya mara ɗa’a kamar ke, zaki haifa ne kema. Sakwara zaki daka, da jar miya, kije Abdul ya kai ki asibiti ki kai wa inteesar ki kwana da ita asibiti, kausar ta dawo gida”.

Daga auren inteesar zuwa yanzu, tayi ɓari ba adadi, dan kamar har mijin nata ya fara ƙosawa da hakan.

Ummi ta je kwana da ita, ta tarar ana yi mata ƙarin jini, duk ta rame, ƙannen mijin suna zazzaune, suna ta hirarsu ko a jikinsu da halin da take ciki, kausar ce a kusa da ita a zaune, ita ma kuma danna wayarta take yi.

Ko da ta ga ummi ta wani haɗe rai ta yatsine fuska ta ce “Dan wulaƙanci, tun kan mu taho asibitin nan ake jiranki, amma ki ka ƙi dawowa kin bar mutane da yunwa, kuma kin san dai ba iya cin abincin sayarwa muke ba”

Ummi ta ja wuri ta zauna ba tare da ta kulata ba, suka gaisa da ƙannen mijin inteesar.

Babu kunya suka ja kwanon sakwarar nan suka buɗe, suka ci abin su, suka gama suka ƙara gaba.

Sai da inteesar ta yi sati a asibiti, ummi ce ke sintirin kai abinci da ɗawainiyar kwana da ita, amma duk basa gani sai rashin mutunci da hantara, gashi idan ta kwana kan wani yazo daga gida ta koma ta shirya ta tafi in da take SIWES, sai ta makara sosai da sosai.

Idan ta je wurin aiki, shima ayi ta yi mata faɗa a kan makara.

Farida ta cewa sageer ya bata inteesar su tafi gida, ta ɗan kwana biyu ta huta.

Inteesar ta ji daɗin hakan, dan kuwa azabar ƙannen mijinta sun isheta, mijin suna zaune lafiya sai abun da ba a rasa ba, amma fa ƙannensa ba sa laifi, dan akan su har zaginta yake yi, ya ci mata mutunci tayi ta musu bauta.

*

A ƙalla ummi ta shafe mintuna goma sha biyar a tsaye a bakin titi, tana ƙoƙarin tsallakawa, amma ta kasa saboda tarin ababen hawa da ke kaiwa suna komowa. Ga rana gashi ta gaji matuƙa, ta gaji da tsayuwa.

“Tsallaka titin ma sai kin yi masa yanga Yaya?” Sai da gabanta ya faɗi, dan kuwa ta tsorata sosai.

A hankali ta waiwaya tana kallon fuskar sa.

Idon da yake son gani ya samu yana kallo, dan yau ba niƙab ta saka ba, facemask ne.

Sai dai bai kalla yadda yake so ba ta janye idonta, tana ajiyar zuciya.

“Na tsorata ki ne?”

Ta ce “Na tsorata ne, ina wuni?”

Ya dawo gefenta ya tsaya ya ce “Yini yana gidan biki, Ai mami ta ce ki daina gaisheni, ni ƙaninki ne, dama kin ce girma ya riga hankali zuwa”

Murmushi ta yi ta sake cewa “Ya mamin da kowa da kowa?”

Raihan ya ce “Suna nan ƙalau, ke na hango na tsaya a tsallake, morethan 20minutes, kin kasa tsallaka titi ki na yanga”

A ɗan marairaice ta ce “Eyya ba yanga nake yi ba, kasa tsallakawa na yi ne”

Ya jinjina kai ya ce “I see”

Ya ce “Taho mu tsallaka” Gaba ya fara yi, tabi bayansa a hankali, sai da suka je tsakiyar titi, ta juya zata koma da gudu saboda motar da ta taho da gudu. Hanata hakan yayi, ta hanyar danƙo hannunta yayi suka yi gaba suka tsallaka.

Ƙoƙarin cire hannunta take daga nasa, amma ya riƙe gam ya ce “Ke haka ki ke tsallaka titi? Gaba ɗaya kin tsorata kanki? Nutsuwa ake yi idan za a tsallaka titi”

Ta sunkuyar da kai, tana cigaba da ƙoƙarin cire hannunta daga nasa.

Ya kalli hannayensu nasa fari tas, na ummi mai duhu, sai dai nata hannun yafi nasa kyau sosai da sosai, nasa da gani kaga hannun namiji, duk a murɗe ga uban jijiyoyi, nata kuma ɗan madaidaici, ɗauke da dogayen yatsu, tafin hannunta fari tas, haka faratanta farare ƙal dogwaye gwanin sha’awa, ga hannunta tamkar auduga dan taushi.

Ya zare nasa ya basar ya ce “Mu je na ajiye ki a gida”

Ta ce “A’a kar ka damu, wannan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi”

Raihan ya ce “Ai ba babur bane, yau mota ce, tun da ba kya hawa babur sai mota”.

“A’a ba haka bane wallahi, kar ka damu, yanzu zan tafi na gode sosai”.

Sai ka ce ubanta haka ya haɗe rai, ya ce “Mu je in sauke ki, bana satar mutane ai, ki daina haka”

Haka nan ummi tayi tsuru-tsuru, dan da ya haɗe rai sai yayi mata kwarjini, ya nufi tsaleliyar motar da yayi parking ɗin ta a gefen titi, glasanta baƙaƙe wuluk, sai sheƙi yake, da gani ka san ba a daɗe da fara hawanta ba.

Ya buɗe wa ummi gaban motar, gaba ɗaya ji tayi kamar zata aikata zunubi, ko da wasa bata taɓa hawa motar wani ba, idan ba ta kawu yahaya ba.

Wani sanyi ne haɗe da ƙamshi mai daɗin gaske ya baƙunceta a cikin motar.

Ya zagaya ya zauna, ya rufe motar, ya ɗaukko robar ruwa da lemo, ya miƙa mata ya ce “Ga ruwa ki sha, kin daɗe a rana”.

Fuskar sa ta kalla, ta karɓa ta ajiye a kan cinyarta.

“Ina zaki yi ne?”

“Gida”

“Gida ina?” Ta kwatanta masa, ya ja motar ya fara tafiya.

Ta gefen idonsa yake kallon yadda duk tayi tsuru-tsuru kamar ba ta da gaskiya, gaba ɗaya a takure take, kamar wadda ke zaune a kan ƙaya.

Tunani yake ta yi a zuciyarsa, this innocent looking lady, ace an azabtar da ita har haka, to wane irin laifi zata yi, da zai saka ayi maka haka?.

Ɗan satar kallon sa tayi, kamar ba shi ta gani wancan lokacin ba, yana barkwanci da wasa da dariya ba.

Ya ɗaukko wayarsa ya nemo lambar Maryam, ya saka a hansfree.

“Ke yane?”

Ta amsa da “Normal, ya aka yi?”

“Guess what?”

Ta ce “I have no idea, menene?”

“Na sake haɗuwa da ƙawar nan taki, da na ce miki tazo gida gaida mami”

Ta ce “Allah sarki, ummi?”

“Eh ita”

“Wallahi bani da numbernta, ban sani ba ko tana da waya ma?”

“Baki da kirki, maybe tun da ki ka yi aure baki sake neman ta ba”.

“To a ina zan ganta, ban son zuwa gidansu, antynta ba ta da mutunci”

Ya ce “Ai shikenan, a gaida yaran”

“Za su ji in sha Allah”.

Ya ajiye wayar, ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa.

“In da na ɗauko ki aiki ki ke ne a wurin?”.

Ummi ta ce “SIWES”

“Me ki ke karanta ne?”

Ummi ta ce “Mass communication”

“Mass communication, ai karatun masu baki ne, ke kuma kamar ba kya magana ma”

Ita dai tayi shiru ba ta ce masa komai ba.

Ya bata wayarsa ya ce “Saka mini lambar ki, sai na turawa maryam, ku dinga gaisawa, zumunci abu ne mai kyau”.

Wayar ta sa zuƙeƙiya mai kyan gaske, ta saka masa lambar ta miƙa masa.

Ya ce “Masha Allah, to nima za a din ga zumuncin da ni? Tun da ƙaninki ne ni?”

Ummi ta yi murmushi ta ce “To”

“To yaya ummi na gode sosai, sunana Muhammad Raihan”

Ta ce “Ai na sani”

“Ai tuna miki na sake yi, ranar da muka haɗu mun kusa yin faɗa, ashe kin sanni nine ban gane ki ba”

Tayi murmushi tana sake gyara zaman facemask ɗin ta.

“Ki rage saka niƙabin nan da facemask, idan ba haka tayaya mutum zai gane ki, you are lucky ina da saurin gane mutane ma, da mask ɗin na gane ki”

Ummi dai ba baki, dan dama can ba mai hayaniya ba ce, sai murmushi da take yi.

A bakin titi ta ce masa zata sauka.

Ganin ya takura mata, ya sanya ya ƙyaleta, ta buɗe motar ta waiwayo ta kalle shi ta ce “Na gode sosai”

“Nima na gode ki gaida gida” yana kallonta cikin dabara ta ajiye masa ruwa da lemon da ya bata ta fice.

Raihan ya taimaketa da ya ɗaukkota, ba dan haka ba, sai ta ci uwa tafiya, kafin ta hau mota, dan kuɗin motarta ba yawa a jakar.

Har ta shiga gida, jikinta ƙamshin turaren raihan yake yi, kasancewar gaba ɗaya motar ma ƙamshin turaren take yi.

Yana zaune a motar ya kira lambar ummi, tana sauri zata shiga gida, wayarta ta fara ringing, ta ciro wayar ta ɗaga tana hello.

Kashewa yayi jin muryarta ce, yayi saving number da brown eyes.

Ummi ta shiga gida tana fatan Allah ya sa ba wanda ya ganta ta sauka daga motar raihan.

Bayan sallar isha’i maryam ta kira ummi a waya, tare da yi mata ciwon bakin bata nemanta.

Sosai suka fara hira da ummi, sai dai hirar ta daina yi wa ummi daɗi, lokacin da maryam ta fara yi mata zancen ita yaushe za ta yi aure? Ummi ta ƙarƙare hirar suka yi sallama.

*
GAGARAWA

Masifa da bala’i a gidan idris, kamar karnuka tun maƙwabta na shiga cikin lamarin, ana ƙoƙarin sasant al’amura, abu ya gagar a gaban yaran suke faɗa, suyi ta zage-zage da ashar kamar maguzawa.
Yarinyar sa ga fari kuwa, tun da aka je da ita family house, aka yi mata gori, Hindu ta wanke ƙafa taje har gidan tayi musu tijara da rashin mutunci.
Babu wanda hindu take saurarawa a dangin Idris, tun daga kan Iya har sauran mutanen gidan.
Dan haka Idris ya fara tunanin ƙara wani auren, ko ya samu sassaka daga masifa da bala’in hindu, gashi kamar tayi masa asiri, duk tijara da bala’in da zata yi masa ba zai iya sakinta ba.

Hashim kuwa ya kasa samun nutsuwar samun matar aure, saboda gaba ɗaya hankalinsa a kan ummi yake, sai dai iya tayi masa kandagarki, dan ta riga ta ce ba ta lamunce ba, dan haka ya san ko giyar wake ya sha, tun da iya ta furta ba ta so, babu mai goya masa baya.

*
Ƙarfe kusan goma na dare, Ummi ta yi wanka tana shirin kwanciya bacci, dan washegari asabar ce, za ta je islamiyya da safe ta koyar da yara, dan haka da wuri take son kwanciya dan ta kammala aikinta da wuri ta tafi da safe.
Kallon baƙuwar lambar take yi, sannan ta ɗaga tayi sallama.

Ba ta ɗau muryarsa ba da farko, dan haka gabanta ya faɗi, ko bisa tsautsayin wrong number, wani namiji bai taɓa kiranta ba.

Sai da ya ce “Yaya ummi” sannan ta ɗau muryar.

Ta ce “Au babban mutum, yanzu na ɗau muryarka ai”.

“Ke, Alhajinmu ne fa kawai yake faɗar sunan da ki ka faɗa, sai Hajiya, waye ya gaya miki wannan sunan?”.

Ummi ta yi murmushi ta ce “A bakin maryam na ji, kuma ai sunanka babbane, ba a faɗarsa anyhow”

“To sai ki ce Raihan ai”

“To shikenan, ya mami da su Hajiya?”.

“Suna lafiya, ta kira ki kuwa?”

“Eh mun yi waya da ita, ka kyauta ai”.

Ya ce “To Allah ya haɗamu a ladan baki ɗaya”

Ta amsa da “Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum”

“Ya aikin?”

“Aiki Alhamdilillah”

Ya ce “Masha Allah, kiranki nayi na kwashi gaisuwa kawai, tun da mun yarda mu yi zumunci, tun da maryam ba ta nan, sai mu mu din ga yin zumuncin. Dama bani da abokai na yi ƙawa, ƙawar yayata ta zama ƙawata”.

Ummi ta girgiza kai ta ce “Mace da namiji ba sa ƙawance ai, ƙanina ne kai”.

Yana daga kwance ya tashi zaune ya ce “To shikenan, muje a haka yaya ummi”

Tayi murmushi ta ce “Sai da safe”.

Ya ce “Allah ya tashemu lafiya yaya, sweet dreams”.

Ummi ta ajiye wayar tana cigaba da murmushi. Ta bi wayar da kallo, ƙanne suna da daɗi, ta so ta rungumi su intee kamar ƙanneta, amma suka nuna mata ba haka ba, shima Abdul alaƙarsu farida ta saka musu ido, da ta gansu tare sai zagi da cin mutunci.

Ɓangaren Raihan ma, wayarsa ya bi da kallo, yana kallon lambar ummi da ya sakawa brown eyes, sanyin halinta ya burgeshi, abun da mami ta gaya masa game da ita, ya sanya masa tausayinta, dan haka yake jin ko na ƙanƙanin lokaci ne, zai shiga rayuwarta ya fahimci ta ina zai taimaketa, kuma zai yi mata addu’ar samun miji nagari mai ƙaunarta.

A rayuwarsa ummi ce mace ta farko da ya ji yana son shiga rayuwarta, idan ba iyayensa ba sai ƴan uwansa mata, ba ruwansa da shiga harkar kowacce yarinya, duk da suna yi masa shishshigi, saboda Raihan kyakykyawa ne kamar maryam, kamar sa ɗaya da mahaifinsu.

Washegari tana makarantar islamiyya, tana fama da ɗalibai, kusan ƙarfe goma da rabi, ta sake ganin kiran Raihan.

“Ina kwana yaya”

“Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau, ya nake jin hayaniya kina ina ne?”.

“Na je islamiyya, ne ina tare da ɗalibai” .

Ya ce “Ok, ashe sayyada ce, mu yi waya idan kun tashi, dama kira na yi idan kina lafiya”

Ta ce “To godiya nake, Allah yayi albarka”

Yayi murmushi ya ce “Dan Allah ki saki muryarki ki daina iyayi”

Dariya ce ta kamata, ta ce “Ka cuci iyayi kuwa”

“Am serious, na yi recording wayar nan, zan tura miki ta what’s app ki ji yadda ki ke magana, sai anjima take care” yayi maganar a hankali.

Ayshercool.

  CUTARWA!

P23

23

Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faɗar Raihan rigiamamme ne.

A ɓangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi. 

Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banɗaki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita.

Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka.

Ya buɗe foodflask, ya tarar da doya ce da ƙwai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai.
Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye ɓangaren mahaifinsu ya wuce.

Yana zaune yana shan tea, gefen sa ƙaton tray ne, ɗauke da kayan marmari yana kallon labarai.

Ya ɗaga kai ya kalli raihan ya ce “Dama kana gidan nan?”

Raihan ya ƙarasa kusa da shi ya risuna ya ce “Barka da safiya”

“Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?”

Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin.

Ya ce “Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ƙara fresh sosai”

Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce “Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi, haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci”.

Cikin kulawa raihan ya ce “Ka yi haƙuri, ka daina damun kanka, kai ka ce ƙuruciya ce take damunsu, za su daina”.

“Zuwa yaushe kenan? Idan ƙuruciya ce kai meyasa ba ka yi?”

Raihan ya ce “Haka ne, amma dai kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, abun da su Yaya Salim suke yi, ka ɗauka jarabta ce daga Allah.
Kalli shekarunka sun ja, ba hawan jini, ba ciwon suga, ga mu Allah ya baka, ga tarin dukiya da al’umma suke amfana ga Hajiya ga mami dukkan mu naka ne, idan ka duba wannan ni’imomin sai ka ga abun da suke yi bakomai bane ba, dan Allah kar ka saka damuwa a ranka wani ciwon ya kama mana kai”.

Kallon Raihan yake yi, cikin tsananin soyayya da kulawa, ya tsiyayo tea cup, ya bawa raihan sannan ya ce “Madalla da yaron kirki, nasiharka na ratsa mini zuciya, in sha Allah zan cigaba da yi musu Addu’a”

Raihan ya ce “Yauwwa father like no other, we are proud of you, ka cigaba da yi musu addu’a in sha Allah zai zama labari”

Alhaji Tahir ya ce “Mahaifiyarka na ganin kamar laifin Hajiya ne ya sanya su lalacewa, amma kamar hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyya”.

“Haba Alhaji, kar ka ɗorawa kowa laifi, Hajiya ba ta da sakaci ko kaɗan”.

“Haka ne, ina son na roƙeka wata alfarma ne”.

Raihan ya gyara zamansa ya ce “To Alhaji, Allah ya bani ikon yi”.

Ya ce “Yauwwa, lissafin da muke yi na shekara shekara da manager, da kai nake so ku yi, a fitar da zakka, a fitar da wanda za a biyawa umara, harajinmu na nan gida da sauran ƙasashe, da duk wasu gyare-gyare da zamu yi, idan ku ka gama sai ka kawo mini na duba”

Raihan ya ɗan yi shiru yana nazari, “Ya dai na ji ka yi shiru?”

Raihan ya ɗago ya ce “Babu damuwa in sha Allah za ayi, zan je na same shi”.

Alhaji Tahir yayi murmushi ya ce Yauwwa “Babban mutum, ka ga atleast na sake na huta sosai da sosai”

Raihan yayi murmushi yana cigaba da zuƙar shayi, nauyi ne mai girman gaske Alhajin ya haɗa shi da shi, dan aiki ne ba ƙarami ba.

Ya shanye shayin, ya miƙe tsaye ya ce “Bari na ƙarasa wurin Hajiya mu gaisa”

“To shikenan babu laifi”

A sanyaye Raihan ya tashi ya nufi sashin hajiya, ba zai iya cewa mahaifinsu a’a ba ne ba, amma wannan aikin kamar yayi masa yawa, ba zai iya jajircewa ya yi shi, kamar yadda shi Alhajin zai yi ba.

“Babban mutum ya dai, na ga kana tafiya a hankali, ko yunwa ka ke ji ne?”

Ya zauna yana faɗin “Eh, ina ɗan jin yunwa ma, me ku ka yi?”.

“Ka san halinsu, kowa dafe-dafensa yayi, ni kuma tuwo na saka a ɗumama mini na sha da tea”

“To ni ma zan ci tuwon”

Ta ce “To bari a kawo, har da man shanu kuwa da yajin daddawa, mai ɗan karen daɗi”

Yayi murmushi ya ce “Hajiya kenan, ina su Yaya Sagir?”

Ta ɗan rausayar da kai ta ce “Ba su tashi ba”.

Ya jinjina kai sannan ya ce “Yauwwa Hajiya, kin tuna yarinyar nan ummi? Ƙawar maryam?”

Ta ce “Eh, ya aka yi?”.

“Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah me ki ka sani a kanta?”

Hajiya ta ɗan yi shiru tana nazarin sa, sannan ta ce “Meyafaru da ita? Me ka ke son sani a kanta?”.

“Ba wani abu bane ba, mami ta fara faɗa mini abubuwa a kan ta, so ina son sanin if their is way, we can help her, like she’s not socially ok”

“To ai kaga ƙawar maryam ce, ni kuma ba wani son shiga harkata suke yi ba, amma dai ina ganinsu tare da maryam, yarinya ce mai matuƙar haƙuri da biyayya, kamar babanta ne ko babarta ce ɗaya daga ciki ya rasu, yayan babanta yake riƙonta, matarsa take maltreating ɗin ta, gaskiya i don’t know much about her. Na so ace a cikin yaran nan akwai nutsatstse, ai da na haɗa su aure, tarbiyyar ta na burge ni sosai da sosai”

“Kin san meya ja hankalina, har na tambayeki?”

“A’a sai ka faɗa”.

“Yadda maryam take yawan bani labarinta, da irin abubuwan da suka din ga yi mata na wulaƙanci suna makaranta, gidansu an yi maltreating ɗin ta, makaranta yara sun yi maltreating ɗin ta, wai wasu lokutan har da malamai, abun bai yi mini daɗi ba wallahi Hajiya”

Hajiya ta ce “Shiyasa nake yinka babban mutum, akwai hangen nesa da zurfafa tunani”.

Cikin damuwa ya ce “Hajiya, kowace halitta da Allah yayi, tana da muhimmanci da kuma amfani, sosai nake jin zafi idan na tuna abun da maryam ke faɗa a kan ta, gaba ɗaya yanayin ta kamar a tsorace take da mutane ma, kuma ni banga muninta ba, baƙa ce kawai, meye abun aibata mutum a kan abun da baka da ikon yin sa?”

“Babu kam”

“Amma Hajiya kina ganin zan iya taimaka mata?”

“Me zai hana? Idan har da ɓangaren da zaka iya supporting ɗin ta, go ahead nima zan yi farinciki da hakan”

Raihan ya sake gyara zaman sa ya ce “Wallahi na so maganarki ta farko ta tabbata, ina ma akwai nutsatstse a cikin su yaya salim, da ɗaya daga cikin su, ko shi ko yaya sagir da wani ya aureta”

Cikin damuwa ta ce “To ya zan yi, sun ƙi karatu, sun ƙi kasuwa sai shirme, sai addu’a kawai”

“Kar ki damu Hajiyarmu, lokaci ne, zasu daina ne in sha Allah, ayi tayi mana Addu’a”

Hajiya ta ɗora hannunta kan na Raihan ta ce “Addu’a kullum cikin yi muku ita ake ai, ubangiji Allah ya tsare mana ku”

Ya amsa da Amin.

Sai da ya ci ya cika cikinsa, sannan ya tashi ya fita.

Har ummi ta koma gida, Raihan bai sake nemanta ba, tayi ta duba wayar amma bai kira ba.

Dr. Yan gari, yana ta ƙoƙari a kan kausar ta samu admission ita ma, domin kuwa a wannan karon, Farida ta ce ba zata sake aurar da ƴa ba, sai ta fara makaranta, saboda kar a sake kwata irin yadda aka yi a kan inteesar.

Suna falo suna kallo, dr. Ya ce lallai ummi ta fito falon ita ma, dan baya son duk suna tare a falo, amma ta din ga ware kanta ita kaɗai a ɗaki.

Ummi dai ta zo gefen kujeru ta zauna a ƙasa, tana kallon, wanda a son ranta tafi son zaman kaɗaicin a ɗakinta.

Noor ta hana su yin kallon, sai tsalle take a tsakar falon, tana karanta ayar Allahu nooro samawati wal ardi.

Abdul ya ce “Noor, dan girman Allah ki zauna wuri ɗaya ki yi karatun nan a nutse”.

Sai ta koma hawa kan kujera tana dirowa.

“Ke dan ubanki ki nutsu” Kausar tayi mata tsawa.

Noor ta ce “Babanmu ɗaya”

Dr. Ya ce “Lafiya ce wannan tsalle-tsallen da take yi.

Farida ta ce “Duk ta bi ta ishi mutane da karaɗin tsiya”.

Noor ta koma kusa da dr. Ta zauna ta ce “Dr.”

Ya ce “Na’am shalelena, yau kuma a dr. Na nake”

“Ka san me? Wata a ajinmu, babansu ya auro kishiya, yanzu mamanta biyu kenan”.

Yayi dariya ya ce “Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya”.

Ta gyara zama ta ce “To Abba ni bani da wata maman sai maama, ita kuma ba ta so na”

“Tana sonki mana”.

“Abba dan Allah muma ka auro mana kishiya, nima mamana ta zama guda biyu”

Ashar ɗin da farida ta yi mata sai da duk suka razana, ta zaburo zata make noor, amma noor ta tashi da gudu, tana murguɗa kwankwasonta tana dariya, ta tsaya daga can ƙarshen falon ta ce “Wallahi Maama idan ki ka kuma dukana, sai na ce Allah ya sa Abba ya auro kishiya”

Farida ta dafe kai ta ce “Na shiga uku da wannan yarinyar, anya nikaɗai aka yi wa tiyata a ɗakin nan ba ayi mini musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba ɗaya ƴa ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata wulaƙanta ni”.

Tsam ummi ta miƙe, dan ta san ƙarshe faɗan kanta zai dawo.

Ta tarar da noor a ɗakinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiɗa.

“Mama” ta kirata kamar yadda take kiranta.

Noor ta ɗago ta kalleta.

“Meyasa ba kya jin magana ne?”

“Me nayi?” Tayi maganar cikin tura baki.

“Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?”

Noor ta ce “Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina”.

Ummi ta ce “To ai ke ɗin ce ba kya ji mama”

“Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa zan din ga yi Allah ya sa Abba ya auro kishiya”

“Au ba ki ji faɗan da nayi miki ba ko? Zaki ga a auro muku kishiya, idan aka auro wadda zata din ga hanaki abinci, tashi ki bar mini ɗaki tunda ba kya ji”

Noor ta ɗan marairaice ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri, na daina”

Can falo kuwa, ganin farida ta haƙiƙance tana ta bala’i, ya sanya dr. Bar mata falon shi ma.

Ya rufe ƙofar ɗakinsa, ya zauna ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya kara a kunnensa.

Amsa sallamar ya yi, sannan ya ce “Barka da yamma, kuna lafiya?”.

Yaya maryam ta ce “Lafiya ƙalau ya iyali?”

Ya amsa da “Lafiya lau Alhamdilillah, ya mai jikin kuma?”

“Jikinta da sauƙi Alhamdilillah, zasu sallame mu ma yau, ta warware zazzaɓin ma babu”

Ya amsa da masha Allah “Ranar monday ne appointment ɗin ta na ganin psychiatric doctor ɗin nan ko?”

“Eh in sha Allah”

“To, ko zaku bari ta ƙara warwarewa daga zazzaɓin, kafin ku je ganin likitan”

“To shikenan, ana samun cigaba sosai da sosai, domin kuwa shekranjiya take cewa ita fa kamar ka zo, kamar ta ganka ko mafarki take yi”.

Dr. Yayi murmushi ya ce “Masha Allah, da haka da haka, in sha Allah zata warware gaba ɗaya, a cikin watan nan zan shigo in ga jikin nata in Allah ya yarda”.

Yaya maryam ta ce “Ubangiji Allah ya kawo ka lafiya, muna ta godiya Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya jiƙan magabata”.

Ya amsa da Amin.

Yana ajiye wayar farida na shigowa, ta cigaba da yi masa bala’in idan ma yana da burin ƙara aure ne, to ya san abun da yake ciki, dan taga kamar ya ɗau maganar noor serious.
Gaba ɗaya ma dariya ta bashi, dan haka ya shareta ta cigaba da banbaminta

*
Haka nan ummi ta ɗan damu, kwana biyu shiru ba Raihan babu labarin sa, ya daina nemanta a wayar ma, kamar za ta damu, kuma ta basar ta manta, ta cigaba da sabgoginta.

“Hi dear” taga message ta what’s app ɗin ta, what’s app ɗin da ta fi ƙarfin sati uku ba ta buɗe shi ba saboda rashin data, sai yau da ta samu ta saka ɗari biyu.

Baƙuwar lamba ce, ba ta san waye ba, dan haka tayi replying da Assalamu alaikum.

Ta tsaya ta ƙurawa message ɗin ido, hi dear, dear kalma ce da ake iya gaya wa kowa, amma mussman wanda yake da muhimmanci.
To ita akwai wani wanda take da muhimmanci a gare shi, da har zai ce dear.

Tayi guntun tsaki da ta tuna, akwai mutanen banza a what’s app, wanda ba su sanka ba, amma su yi maka maganar banza.

Ta cigaba da shirinta na tafiya wurin aiki, ba ta taso ba sai ƙarfe huɗu da rabi, a hankali take tafiya, sai dai wata mota ta cika mata kunne da horn. Ta matsa gefe amma ya cigaba da yi mata horn.
Gefe ta koma ta bar wa motar hanyar, ta cigaba da tafiyarta.

“A wannan yangar da iyayin naki, sai kin fusata mutum ya ture ki” cak ta tsaya, ta waiwayo da mamaki ta ce “Laa raihan, yi haƙuri ban san kai ne ba”.

“Eh shi ne ki ka bar mini hanyar, wato na ci kaina, ban isheki kallo ba”

Ummi ta ce “Eyya ba haka bane ba, ban san kai bane” tayi maganar tana kallon sa, idonsa yayi ja, kamar daga wani wurin yake.

“Wucewa na zo yi, na san sai yamma ki ke tashi, na tsaya ki fito mu tafi”.

Ɗan shiru ta yi tana kallon sa, ba ta son shiga motar nan tasa, kar a fara zargin wani abu.

Ya ɗan marairaice ya ce “Nayi awa a wurin nan ina jiranki, dan Allah kar ki ce a’a”.

Ta ce “To” tabi bayansa, suka nufi motarsa.

Suna tafe a hanya, har lumshe ido take yi, saboda gajiya.

“Yaya ummi kwana biyu ko ki neme ni, anya za ayi zumuncin nan da ni kuwa? Na yi busy sosai kwana biyun nan, ko waya bamu yi ba, kuma baki nemi in da ƙanin naki yake ba”.

“Yi haƙuri ba haka bane ba, zan din ga kiranka in sha Allah”.

“Allah ya sa, ya karatu ya ɗalibai?”

Ta amsa da”lafiya ƙalau Alhamdilillah”

“Masha Allah, nima kwana biyu Alhaji ne ya sakani aiki, ya ga ina sararawa bana aikin komai, ina ga gani yayi sharholiya ta yi mini yawa, ya sani aiki ko cikakken lokaci bani da shi, duk na rame na zama baƙi”

Ummi ta ɗan yi murmushin yaƙe, cikin fargabar abun da ka iya biyo bayan maganar sa, wataƙila cin zarafin kalar fatarta.

Bai damu ba ya cigaba da maganar sa, “Ni fa yunwa ma nake ji, ko mu tsaya mu ci abinci?”

Tayi farat ta ce “A’a, na ƙoshi ma ai, a ƙoshe nake ai”

“Yaya ummi kenan, da abinci ki ke zuwa kenan? Tun safe fa kina wurin nan, to idan kin zo da abincin ki din ga ci kina rage mini, dan ni yau tun da aka kirsheni a wuri ɗaya tun ina ganewa har na daina, bari na yo takeaway a wannan wurin abincin”. Ta ce “To”.

Ta kai mintuna sha biyar a motar, sannan ya dawo da manyan ledoji, ya tarar ta sauke facemask ɗin ta.

“Sannu na bar ki kina jira ko? Tuwo na so in samu, babu sai shinkafa ni kuma damuna take yi”

Tayi murmushi ta ce “Kana cin tuwo kenan? Abdul ɗin gidanmu baya son tuwo”

“Haba dai, ai yaya tuwo abun so ne, ni a bauchi na saba, Alhajin Bauchi da shi yake karyawa, ga kwanonsa ga nawa, amma shima fa tuwon bana jera kwanaki ina ci yake isata”

Tayi dariya ta ce “Ka fi son dai a din ga ccacanzawa”

“Yauwwa, ba kullum abu ɗaya ba”

Yau dai yayi sa’a, ta ɗan saki jiki kaɗan, dan yau har da dariya.

Ya ƙarewa hijjabinta kallo, duk yayi fari takalmin ƙafarta ma ya tsufa.

“Ummi”

Ta ce “Na’am”

“Me ya fi burgeki a rayuwa? Wanda yin sa yake yi miki daɗi, ko samunsa, abun da dai yake saka ki farinciki?”

Tayi shiru tana tunani, oho, ita akwai wani abu da take jiran samuwar sa ya sanyata farinciki ne? Duk abun da ya zo mata a rayuwa kawai, karɓa take yi.

“Babu”

“Ban gane babu ba? Kawai haka ki ke rayuwa ba farinciki?”

Ta sunkuyar da kai ta yi shiru.

“No dole akwai, ki tuna sai ki gaya mini”

“Babu” ta sake bashi amsa.

Bai sake ce mata komai ba suka cigaba da tafiya, in da ya ajiyeta wancan karon, ta sake cewa ya ajiyeta.

Ya yi parking sannan ya kalleta ya ce “A nan zaki sauke, ba zaki bari na ga gidan ba?” Ta hau wasa da yatsun hannunta bata ta kula shi ba.

“Bayan ƴan uwa let’s be true friends ummi, ki tuna abun da yake saki farinciki ki gaya mini, mu zama ƴan uwa kuma abokai saboda Allah”

“To in sha Allah”

Yayi murmushi ya ɗauki leda ɗaya, ya ce “Ungo naki” ta kalleshi zata yi magana, ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce “Shhh”.

“Idan zan wuce gobe in Allah ya kaimu zan jira ki mu tafi tare” ta jinjina kai, ta fice daga motar.

Addu’a take yi, tana fatan Allah ya sa kar wani ya ganta, cikin ikon Allah babu wanda ya ganta, har security gidan yana banɗaki, ta wuce ta shiga har ɗakinta ba ta haɗu da kowa ba.

Ta sauya kaya ta fito, ta dudduba gidan babu kowa, ta koma ɗakin ta duba ledar da Raihan ya bata.

Rabin kaza ce guda a cikin ƙatuwar roba, sai shinkafa da salad.

Jikin ummi har rawa yake, duk wannan kazar ita kaɗai?.

Sai kuma ta yi shiru tana tunani, anya ba ta zura jiki ba? Kasa ci tayi ta tashi ta shiga aikin gida.

Abdul ne ya shigo yana waya, ya kammala ya tsaya yana mita.

Ummi ta ce “Yaya Abdul kana nan dama?”

“A’a yanzu na shigo, wani ɗan rainin hankali ne ya kirani, wai babansu ne ya buɗe shago a tal’udu, suna neman casheir, wanda zai din ga zauna musu da safe zuwa azahar, ko azahar zuwa magariba”.

Ummi ta ce “Dan Allah yaya Abdul zan yi, ina so”

Ya kalleta ya ce “Zaman jiran shagon, shagon furnitures ne fa da kayan kitchen”

“Eh yaya Abdul dan Allah, dama na gama SIWES, kawai dai sun buƙaci na cigaba da zuwa ne, dan Allah zan yi”

Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Zan yi magana da Abba, idan ya yarda shikenan”.

“Yauwwa zai yadda ma in sha Allah” tayi maganar tana addu’ar Allah ya sa Abba ya amince, ita ko kuɗin babu yawa tana so, atleast ta din ga samun na sayen wasu abubuwan da take buƙata.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye da kazar nan a ɗaki, dr. Gidansa ba ya rabo da nama da kaji, amma tsaf ummi za ta yi aikinsu, farida ta karɓe idan ta ga dama ta sanmata idan ba ta ga dama ba, sai ummi ta zo wanke-wanke ta ɗan tsinci sauran hanta, da diddiga ta lasa abun ka da zuciya.

Hankalinta bai kwanta ba, sai da ta saka noor a gaba, ta gaya mata yadda aka yi, kamar sa’arta.

Noor ta din ga murna ta ce “Yaya ummi kar ki gaya wa kowa mu cinye abunmu”.

Ummi da noor suka cinye takeaway tare, suna ta murna, dan kuwa ummi ba ta taɓa cin kaza mai yawan haka ba.

Ayshercool

CUTARWA!

P24

24

Ummi ta kalli noor ta ce “Dan Allah noor kar ki gayawa kowa kin ji”

Noor ta ce “Yaya ummi ina da wayona fa, ba wanda zan gayawa wallahi, kazar nan tayi daɗi sosai”

Ummi ta yi murmushi ta ce “Yauwwa maman”.

Raihan kuwa tun da yaje gida, ɗakinsa ya wuce ya samu ya kwanta ya huta, ana kiran magariba ya fice, da aka idar da sallar isha’i, ya tafi gym domin motsa jikinsa.

Bai sake komawa gida ba sai wajen ƙarfe goma, ya shiga sashin mami.

“Wai yau ina ka shiga ne, tun safe ban sake saka ka a idona ba?”

“Kasuwa na je” ya bata amsa tare da ɓoye mata aikin da Alhajinsu ya sanya shi.

“Aikuwa ka kyautawa kanka, Allah ya taimaka” ya amsa mata da “Amin”

Washegari da sassafe, raihan ko karyawa bai yi ba, ya ɗauki mota ya fita, dan yaje ya ɗauki ummi kar ta makara, dama yau zai zauna da cheif accountant na mahaifinsu su cigaba da aikin da ya saka shi.

Ƙarfe bakwai da rabi, ummi ta ga kiran raihan.

Ta ɗaga wayar tare da yin sallama.

Ya amsa mata ya ce “Ina waje, idan kin shirya ki fito mu tafi”

Ummi ta ce “Eyya, sai takwas da rabi nake fita ai, kayi tafiyarka wallahi bakomai, na gode sosai “

Raihan ya ce “No, ina jiranki, idan kin kammala sai mu tafi, na zaci da wuri ki ke fita sosai, shiyasa ko karyawa ban yi ba na fito”.

“Amma ai zaka gaji”.

“Bakomai take your time”

A gurguje ummi ta kammala duk abun da zata yi, saboda kar ta bar shi yana jira, ta juyo abincin breakfast ɗin ta, a flask, lokacin farida ko tashi ba ta yi ba, ta riƙo niƙab ɗin ta a hannu ta fice.

Yana zaune a cikin mota, ya kashingiɗa yana danna wayarsa, ta buɗe ta shiga ta zauna.

“Raihan, ka yi haƙuri dan Allah, na barka kana jira, na ce ka yi tafiyarka ka ƙi”.

Ya gyara zamansa ya ce “Ai na ce ki yi a hankali ki shirya a tsanake, shi ne ki ka fito a haka kamar an koro ki?”

“Ai bana son in barka kana jira ne, jira babu daɗi, ina kwana ya su mami?”.

“Lafiya ƙalau, duk suna lafiya, ya gida?”.

“Alhamdilillah” tayi maganar tana ƙara kintsawa, ya kalli jakarta data buɗe, kamar jakar wanzamai, duk ta tsufa, daga ƴar ƙaramar robar Vaseline sai turare ɗan ɗuri, da tarkacen kuɗin da idan ka tattare su ba su fi naira ɗari da hamsin ba.

“Me ma ki ka ce sunana?”

Ta ce “Raihan”

“Ba rayyan sunana ba fa, raihan”

A ɗan marairaice ta ce “Ai haka na ce”

Ya ce “Sake faɗa to”

Ta ce “Raihan”

“Idan na ce iyayi yayi miki yawa ki ce ba haka ba, Kamar rain kamar rayyan ki ke cewa fa”

Ummi ta yi murmushi ta ce “Ni dai bana wani iyayi”.

“To sake cewa raihan in ji”

“Ba zan faɗa ba” tayi maganar tana dariya, har dimples ɗin ta suka lotsa.

Ya sanya seat belt yana murmushi, ya ce “Meye a cikin flask ɗin nan ne, ƙamshinsa ya cika mini hanci?”

Ta ɗago idonta ta ce “Kai na zubowa abinci ka ce baka karya ba, kunun alkama ne da ƙosai, ban sani ba ko zaka iya ci?”

“Saboda me ba zan iya ci ba?”

“Abincin gargajiya ne, na ƴan ƙauye zaka iya ci?”

Juyowa yayi yana kallon idonta, “Ke ƴar ƙauyen ce da ki ke iya ci?”.

“Eh mana, ni ƴar ƙauyen gagarawa ce jihar jigawa”.

“Ban ga alama ba, na gode sosai, dan aikin nan ko cikakken abinci bana iya ci, na kasa nutsuwa sai mun kammala, Alhaji ya ga sharholiya tayi mini yawa ya haɗani da aiki, ashe aikin ja ne ba ƙarami ba”.

“Allah sarki, Allah ya baka ikon yi, ni ko a mintuna goma da zan sake ganinsa ya sakani aikin da na so, sai dai ba zan sake ganin baba ba, Allah yayi masa rahama”

Cikin kulawa raihan ya ce “Eyya, Amin ya Allah, Allah ya jiƙansa”

Ta amsa da amin na gode.

“To mama fa, tana raye?” Ta ce “Ina ga tana raye”

“Kamar yaya kina ga? Tana ina ita?”.

“Rabona da ita tun ina shekara bakwai da baba ya rasu, ban ƙara ganinta ba”.

“Amma meyasa?”.

“Bakomai” ta faɗa tare da ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗaci a ƙirjinta.

Ta ɗaga hannunta tana ƙoƙarin sanya niƙab ɗin ta.

“Wai shi wannan niƙab ɗin meye amfanin saka shi, kullum ke ko gajiya ba kya yi ne?”

Ummi ta ce “Ai saboda idona”.

“Meye da idon naki?”.

“Bana son mutane su din ga tanka mini ido, ko fatata, shiyasa idan na saka shikenan ba wanda ya gani, ana cewa idona irin na akuya, ko na mage, duk bana so shiyasa bana son a din ga gani” tayi maganar a ɗan shagwaɓe da take ɗabi’arta, wanda ita a zahiri cikin damuwa ta yi maganar.

“Ummi”

“Na’am”

“Meyasa zaki bari surutun mutane ya yi tasiri a zuciyarki? Ke ki ka yi kanki, duk wanda ya tanka ki, kice masa tubarkallah idan yana da dama ya sauya abun da Allah ya yi miki. Idanunki me kyau ne masha Allah, meye da kalar fatar ta ki, dan Allah idan dan haka ki ke saka niƙab ɗin nan ki daina”.

Murmushi kawai ta yi, irin ba zaka gane ɗin nan ba, hakan yayi dai-dai da ƙarasowarsu ƙofar gate ɗin wurin aikin su ummi.

Ummi ta ajiye masa kayan abincin, ta ce “Na gode sosai,  sai anjima”

“Idan an tashi ki jirani, saura ki tafi” ba ta ce komai ba, ta buɗe ta fita.

Ya daɗe yana nazarin, ta ina zai taimakawa ummi, babanta ya rasu, ba ta san in da mamanta take ba how? Kuma yau ta ɗan sake da shi fiye da da, lallai idan ya cigaba da lallaɓata har ya ƙara saninta sosai da sosai, dan ya fuskanci akwai abubuwa na damuwa sosai da sosai a cikin rayuwarta.

Kiran wayar accountant ne ya dawo da shi hayacinsa, ya ja motarsa ya tafi.

A motar ya gama karyawa, sannan ya tafi babban office ɗin su, in da suke aikin lissafin.

Aiki raihan suke yi, suna ta aikin lissafi, amma rabin hanakalin raihan yana kan ummi.

Da suka tashi ma daga aikin, a waje ta tarar da shi, ya zo yana jiranta ya ɗauke ta ya mayar da ita gida.

Washegari da safe ummi na ta ɗawainiyar sallamar kowa, masu tafiya makaranta su tafi, ta gama abun da take yi, ita ma ta fara nata shirin, Abdul ya sameta a kitchen hannunsa riƙe da waya.

Ya ƙarasa ya miƙa mata wayar, ta karɓa ta kara a kunnenta.

Muryar dr. Ta ji ya ce “Mamana”

“Na’am kawu ina kwana?”

“Lafiya ƙalau, ina ta kiran wayarki baki ɗaga ba”

“Caji take yi ina kitchen ne”

Ya ce “Ok babu laifi, mamana Abdul ya zo mini da wani batu, wai kina son aikin jiran shago, me zaki yi da wani aikin zaman shago ummi, idan kina da wata buƙata ai gara ki gaya mini, amma zaman shago ba mutuncin ki bane a matsayin ki na mace”

Jiki a sanyaye ta ce “To kawu”

“Dan Allah ayi haƙuri da maganar nan”

“To, in sha Allah an barta”

Abdul ya karɓe wayar ya ce “Hello Abba”.

“Na’am Abdul”

“Abba ka san ummi ba za ta ce maka a’a a kan hukuncin da ka yanke ba, amma wallahi tana so, ta gama SIWES, amma sanin ba ta da wurin zuwa ya sanya ta cigab da zuwa, wataran ko kuɗin mota sai na bata, zamanta a gidan nan ba abun da zai ƙara mata sai damuwa da rigima da maama, dan Allah Abba ka ƙyaleta tayi. Kuma ba wani abun fa zata din ga yi ba, tana zaune a wuri ɗaya, dan Allah ka bar ta tayi. Kaga ba ta iya zuwa ta ce na yi mata wani abu”.

Abba ya ce “Haka ne, to Ubangiji Allah ya yi jagora, na amince amma ka je wurin ka tabattar babu wata matsala, dan nima zan je da kaina na ga wurin, a satin nan zan shigo kanon”.

“To shikenan Allah ya kawo ka, Abbanmu maganin kukanmu”

Ya kashe wayar ya kalli ummi da jikinta yayi sanyi, ya ce “Abba ya amince, zan je na ga wurin, na ce musu zaki yi, sai mu je tare ki ga wurin kema”

Ummi ta ce “Alhamdilillah ala kulli halin, na gode yaya Abdul, Allah ya saka da alkhairi”

“Bakomai, Ubangiji Allah ya kawo miki babban rabo na alkhairi” tayi murmushi tana sake hamdala.

Gaba ɗaya ranar sallar daren da tayi, Allah take yi wa godiya, tare da roƙonsa ya kawar mata da duk wani abun ƙi a lamarin.

Washegari Saturday ce, dan haka ba su haɗu da raihan ba sai waya.

Da yamma Abdul ya ɗauketa a motar da dr. Ya saya ya ajiye musu saboda zuwa makaranta ko unguwa.

Katafaren shago ne, na kayan kitchen da furnitures, manager wurin ya yi wa ummi tambayoyi, Abdul ya sanar masa ummi degree ne da ita, yanzu suna jiran result ne ma.

Manager yayi murna ganin tayi kalar haƙuri sosai da sosai.

Ya ce mata wurin sabon buɗewa ne, dan haka salarynta dubu goma sha biyar ne.

Abdul ya raina dubu sha biyar, ya ce za su je su yi shawara, suna tafe yana mita, ya ce “Yaya ummi ki yi haƙuri, zan samo miki wani wurin in sha Allah, amma wane irin 15k kamar wasan yara”

“Dan Allah yaya Abdul ka barni ina so, ko dubu biyar ce zan yi”

Ya kalleta ya ce “Haba ummi, you are degree holder fa, kuma a cikin 15k har ki yi kuɗin mota da buƙatu?”

“Eh zan yi in sha Allah, Allah ya sanya mata albarka”

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Amin, bari sai na kira su na gaya musu, na ji yaushe zaki fara zuwa”

“Yauwwa yaya Abdul, na gode sosai da sosai”

Yayi murmushi ya ce “Sai ka ce na baki kyautar wani abun, Allah ya taimaka”.

Suka je gida tana ta tunanin da wa zata yi sharing wannan abun farincikin, na samun aiki, ita ba ƙawaye ba, kuma ba abokin hira ba, tayi tunanin ko ta gaya wa raihan, amma sai ta ga hakan kamar ta zaƙe, dan haka ta share shi bata gaya masa ba.

Ranar litinin, ta ga kiran wayar raihan ya zo su tafi, wanda ranar zata je ta yi sallama da ƴan wurin aikinsu, ta fara zuwa wancan kanti na furnitures.

Tun da ta nufo motar yake kallonta, sannu a hankali, tafiyar ma cikin nutsuwa da yanga take yin ta.
Maimakon ta shiga ta zagaya ta in da yake zaune ta ce “Ina kwana?”

“Lafiya ƙalau, ina shirin aikin?”

“Sai 9 zan je idan Allah ya kaimu, zan yi musu sallama, na samu aiki a wani sabon shago, MIKIYA GALLERY, can zan koma zuwa”

Yayi shiru yana kallon ta, ya ɗan rausayar da kai ya ce “Rashin muhimmancin nawa har ya kai abu ya faru ki ƙi gaya mini?”.

“A’a ba haka bane ba, abun ne bai tabatta da wuri ba”

“Shikenan na gode, Allah ya taimaka” yayi maganar ransa a haɗe.

“Raihan haushi ka ji, walla….

“Shhhh, na fuskanci na fiye shishshigi, am sorry” yayi maganar yana kunna motar.

Ummi ta yi saroro ta kasa magana, ba ta son ace tayi laifi a rayuwarta, mussaman raihan da yake ta ɗawainiya da ita, ba ta zaci za ji haushi ba.

“Matsa zan ja motata”

A hankali ta ja da baya, ya ja motar, yana kallonta ta mirror, ta tsaya kamar sokuwa tabi motar da kallo.

A hankali ya furta ‘Lets see, if it will works’

Jiki a sanyaye ta din ga gudanar da al’amura ranar.

Ta je sabon wurin aikinta, sai dai hankalinta baya jikinta, ta din ga kiran wayar raihan, amma yaƙi ɗagawa.

Whats app ta koma, ta yi masa message nan ma bai amsa ba, sai dare sannan ya kirata.

“Raihan dan Allah ka yi haƙuri, ban san zaka ji haushi ba, ka yi haƙuri mana”.

“Yaya ummi ba sai kin bani haƙuri ba, laifina ne da nake yi miki shishshigi, duk da yanayinki na rashin son mutane”.

“A’a ba shishshigi ka ke yi mini ba, ka yi haƙuri mana”

Ya wani hura hanci ya ce “Ok, Allah ya taimaka”.

Ta ce “Yauwwa na gode, zan din ga gaya maka abu idan ya faru”

Ya ce “Promise?”

“In sha Allah “

“To shikenan, abu na daɗi ko akasin haka, kar mu ɓoyewa juna”

Ummi ta ce “To”

“Good dear, gobe in Allah ya kaimu zan zo na ga wurin”

Tayi murmushi ta ce “To Allah ya kawo ka”

“Amin, goodnight” suka yi sallama tana jinjina daru irin na raihan.

Status take kallo, ta kai kan status ɗin raihan, yana tsaye a gym, ya tsaya a jikin mudubi yayi hoto, daga shi sai gajeren wando, ya ɗaga wani ƙarfe jijiyoyin jikinsa duk sun ɗaga, ga cikinsa ya rabu kashi shida
(six packs) ga ƙirjinsa kwance da gashi har saman cikin sa.

Tayi reply da “Babban mutum meye haka?”

“A ina?”

“Ka saka hotonka babu kaya, ba mutunci a haka, dan Allah ka cire”

Ya amsa mata da “Ai ni ba mace bane”

“Duk da haka, manya ba sa haka, a cire dan Allah 🙏”

Yana daga kwance yake murmushi, ya ce “To shikenan, an gama babbar yaya, in sha Allah ba zan sake sakawa ba”.

“Yauwwa babban mutum, Allah ya yi albarka ya kula da rayuwarka”

“Amin ya rabb yayata, godiya nake Allah ya kula mini da ke”

“Amin tare da kai” ta ajiye wayar tana murmushi.

Washegari har shagon ya je ya tarar da ummi, sai dai ya ji daɗin ganinta a kauwwame a wuri ɗaya, ba wani aiki take na wahala ba.

Ya samu wuri ya zauna suka gaisa da manager, ya hau yi wa ummi hira.

Da farko a ɗan tsorace take, ko manager zai ce tayi laifi, amma yaga bai ce musu komai ba, har lokacin tasinta yayi, yana wurin.

Da suka fito ya kalleta ya ce “Wai nawa zasu din ga biyanki ne?”

Cikin murna ta ce “Dubu sha biyar duk wata”

“Me?”yayi maganar yana yatsune fuska.

“Dubu sha biyar” ta maimaita masa.

“Share-share zaki din ga yi ne? Ki zo ki wuni a dubu sha biyar, duk girman shagon nan dan son kai”.

Ummi ta waiwaya ta ga babu wanda yake jin su ta ce “Kayi a hankali, dubu sha biyar ina laifi, da waye ya bani?”.

“Degree holder da aikin dubu sha biyar a wata, me 15k zata yi miki a wata, mussman ku mata masu tsarabe-tsarabe, ni fa a wata data da katin waya na dubu ashirin nake sawa zuwa sama” Ummi ta buɗe baki tana kallon sa, saboda abun ya ɗaure mata kai, har ya kaita gida mita yake yi, yana nanata dubu sha biyar ta yi kaɗan, tayi masa shiru taƙi kula shi. Dan in dai shariya ce ummi ta ƙware a wannan fannin.

“Ni ki ka share ko, wato idan na gaji na yi shiru?” gyara zamanta tayi tana cigaba da kallon window.

A hankali ya ce “Miskili ka fi mahaukaci ban haushi”.

*
Misalin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, raihan da mahaifinsu, chief accountant da sauran accountants mutum biyu, lawyoyin Alhaji Tahir su biyu, sai kuma manajojinsa, zaune a wani katafaren office, ko ina fitilu kamar rana, kowa gabansa da ruwa da lemo, gefe ga flask na shayi, gaba ɗayansu raihan ne kawai yaro a cikinsu.
Ɗaya bayan ɗaya kowa ya din ga gabatar da bayaninsa n shekara a kan ɓangaren da yake jagoranta.

Suka kammala tsaf, sannan raihan ya tashi, ya yi connecting system ɗin sa da projector, ya fara bayanin abubuwan da ya tattara daga bayanan su, ribar da suka samu a shekarar, ya tabbattar wa da mahaifinsu duk sun bibiyi shige da ficen kuɗi na shekarar, kuma sun yi dai-dai da bayanan da abun da kowane accountant yayi presenting.
Ya ware harajin da zasu biya, na ciki da wajen Nigeria, ya ware kuɗin zakka, kuɗin abun da ake rabawa ma’aikata na riba bayan albashinsu, abubuwan da suke buƙata, kuɗin duk wani abu da ya shafi sadaka da makamantansu, da kuma kuɗin umara na mutum goma, kamar dai yadda Alhajin ya umarce shi.

Tafa masa Alhaji Tahir ya hau yi, ya ce “Ƙaraminsu babbansu, am so much proud of you, ban zaci zaka iya ƙoƙari haka ba, saboda na san aikin ba ƙarami bane”.

Chief accountant ya ce “Ni kaina ya bani mamaki, yayi ƙoƙari sosai da sosai, na bi duk abubuwan da yayi, kamar dai yadda ka saba ne, yayi iya yin sa, kuma da alama zai kamanta adalci kamar dai kai, sai dai rigimamme ne”

Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce “Ai na san halin kayana” suka yi dariya baki ɗaya.

Suka ƙarasa tattaunawa, da bibiyar abubuwan da Raihan ya gabatar, daga bisani Alhaji Tahir ya ce kowane ɓangare su rubuto abun da suke buƙata, na gyara ko makamancin haka, raihan zai duba, shi zai je hutun taƙaitaccen lokaci.

Duk suka gamsu da abubuwan da aka tattauna, tare da yi wa Alhaji Tahir addu’a saboda mutum ne mai farantawa ma’aikatansa, dan ya ce abokan nemansa ne, bayan iyalansa ba shi da sama da su.

Dirver ya ɗauke su zuwa gida, a hanya raihan ya ce “Alhaji”

“Na’am babban mutum”

“Tsakani da Allah aikin nan da wahala, kuma ko murmurewa ban yi ba, ka ce a kawo mini duba wani abu, ni fa ban san komai ba, dan Allah a kaiwa su yaya sagir, gaba ɗaya ƴan kwanakin nan saboda aikin nan, ko bacci bana yi sosai” ranƙwashin da Alhajin yayi masa ne ya sa shi yin shiru yana kallon sa.

“Kana da nasibi a kan harkar kasuwanci raihan, amma wasa da shiririta sun yi maka yawa, da aikin kashe-kashen kuɗi, office zan baka a head branch, a din ga baka salary”

Cikin sangarta ya ce “A’a dan Allah, shagona fa da nake ta processing, ka fa bani jari rance, ka manta, kayana sun kusa zuwa fa”.

“Na sani raihan, akwai abun da nake targeting ne”

Raihan ya ce “To, Allah ya taimaka, amma ba sai na sake duba wani abun ba ko? Kuma ba sai na yi maka aikin ba ko?”.

“Sai fa ka yi, gara ma ka shirya”

Raihan ya kifa kansa ya ce “Wayyo mami, dama ban dawo kano ba”

Alhaji Tahir yayi dariya ya ce “Ko ina ka tafi, i know how to deals with you, Munnir ya sangarta ka, kashe kuɗi kawai ka iya, baka iya nema ba” yayi maganar yana murɗe masa kunne.

Raihan ya ɗago da sauri ya ce “Ka tambayeshi ka ji, na sayar da agoguna, na sayar da takalma, kuma na tara kuɗi”

Alhaji Tahir dariya kawai yake yi wa raihan, so yake dole sai ya zame, kuma ya san dalilin sa na yin haka, dan raihan akwai biyayya in dai abu zai faranta masa rai zai yi, da mamansa ne ma suke faɗa wasu lokutan ba su fiye shiri ba, idan ta zo da abu na son zuciya, ya ce ba zai yi ba.

Duk da ummi ta ɗan girmewa Raihan, sannu a hankali ya nuna mata shi namiji ne, domin kuwa yafi ummi wayo nesa ba kusa ba, dan bata ankara ba, suka yi wani irin mugun sabo da ita da shi, duk ɗari-ɗarinta da shi, ta sake jiki da shi, dan barkwancinsa kawai nishaɗi yake saka ta.

Kullum a wurinta yake karyawa, da safe sai ta tafi masa da abinci, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya sanya mata ido ya lura da shige da ficenta.

Shi kansa raihan a tarayyarsa da ummi, ya san tana da baki dan tana magana tana tsoron yi ne, saboda yanayi na yadda al’umma suke karɓar ta.

Idan suna hira, wasu lokutan manager sai ya kalleta ya ce “Wai ummi dama kina da baki haka?” Sai ta yi shiru ta daina maganar cikin jin kunya.

Gaba ɗaya ta daina jin nauyin raihan, haka kurum sai ya zame daga office, ya taho wurin aikinta, manager har tambayarsa yake “Wai kai Raihan baka sana’a ne? Kullum kana liƙe a wurin ummi?”.

Kasancewar manager matashi ne, da kaɗan zai girmewa ummi, ƙanin mai shagon ne, dan haka Raihan ya ce “Eh ni bani da sana’a, zaman banza nake a yanzu, shiyasa kullum muke tare da ita”.

“Ta ce Abdul yayanta ne, kai kuma ƙaninta, anya ba ka girmeta ba kuwa? Ka yi ta mata wayo, ta zo da ɗan abincinta, ta ajiye maka ka zo ka cinye, ka hanata sakat da surutu, ka zo in baka aiki kaima”.

Raihan ya ce “Allah ya kiyaye in yi aiki ku biyani dubu sha biyar, dan wayo, dan kun ganta saliha, ai ta kusa daina aikin nan”.

Manager ya ce “Ai tawakalli ta fika, shiyasa take aikin, kai ka raina sana’a, kullum kana liƙe da ita, ka cinye mata abinci, kuma kana jiran a biyata ka karɓe mata kuɗi”.

Raihan ya ce “Wai manager abincin nan daga gidanka ake kawo wa ne? Ina ruwanka ne ka dameni fa”

Idan suna abun su shi da manager, sai dai tayi ta dariya, kamar sako da sako manager komai sai yayi magana, shikuma raihan baƙar magana da neman tsokana.

Ummi na jin daɗin aikinta a wurin nan, ko albashin farko ba a bata ba, amma manager yana daga cikin mutanen da suke mutuntata, bai taɓa nuna mata ƙyama ba, kuma tana iya ƙoƙarin ta wurin kula da coustomers ɗin su, idan ta je da wuri ba ruwanta, har share-share yi take yi tayi mopping gaba ɗaya ba ta da damuwa.

Zamanta a wurin yana rage mata damuwoyi da yawa.

Yanzu ma tana ta bawa raihan labarin rigimar noor, ba ta da wata hira sai ta noor.

Cikin nishaɗi take hirar, Raihan yana kallonta, ya ce “Ya aka yi haƙorinki ɗaya ya ɓalle ne? Ko dai da kina yarinya kin yi rashin ji ne?”

Ta yi murmushi tana dariyar yaƙe, da tuna yadda aka yi haƙorin ya ɓalle ranar salla ta ce “A ƙaddara bana jin magana ne, na taho da gudu ranar salla, na faɗa cikin kwanuka na buge baki da tukunya, haƙorin ya ɓalle” tayi maganar tana tuna yadda idiris yayi ball da ita ranar.

Raihan yayi dariya ya ce “Ai da alama, kuma fa da ya ɓalle ɗin yafi kyau, amma dai mijinki sai ya rage sadaki, saboda ɓallewar haƙorin nan, duk da ta wani fannin sai ya ƙara, tun da kina cikin matan da malaman fiƙhu suka ce a ƙarawa sadaki”.

Basar da zancen tayi, saboda jin zai ɗaukko wani babban karatu mai nauyin gaske, ita ina ta ga ko saurayi balle ayi zancen ƙari ko ragin sadaki, ita da tun da take, ba wanda ya taɓa cewa yana sonta?.

Raihan yayi mugun sabo da abincin ummi, kusan kullum a wurinta yake karyawa, ba tare da ya san abincinta take sadaukarwa ta bashi ba.

Suna tafe a hanya ta ce “Raihan, manager ya ce a satin nan fa za a biya salary”

“Dubu sha biyar ɗin ki ke wa wannan washe bakin?”

“Eh mana, idan Allah ya saka mata albarka zaka sha mamaki”.

Ya ce “Oho dai, amma dubu sha biyar ya fi kuɗin mayukan da zaki shafa a sata” ta ware ido ta ce “Ni ɗin? To wallahi vaselin nake shafawa ko man kaɗanya”

Yayi murmushi ya ce “Amma zaki kai ƙaninki shopping ko? Muje ki yi mini sayayya”

“Me ka ke so in saya maka?”

Raihan ya ce “Sai mun je sai in zaɓi abun da nake so”

Ta ce “To shikenan, in sha Allah idan aka biya sai mu je, nima na je shopping ban taɓa zuwa ba fa, to ina zamu je?”

“Ki yi tunanin in da ki ke so mu je” ta jinjina masa kai tana ta murmushi, wai duk saboda dubu sha biyar take wannan farincikin.

“Yauwwa, ya ake ciki da aikin Alhaji kuwa?”

Ya ce “Hmm kin san ya kuma haɗa ni da wani, alhakin fitar da zakka, da mutanen da zai biyawa umara da aikin hajji”

Ummi ta ɗan yi shiru ta ce “Masha Allah, sai ka tsaya ka ji tsoron Allah, kar ka bari son rai ya shiga lamarin, wataƙila ya yi hakan ne dan ya gwadaka, ka bawa wanda suke buƙata kayi adalci”

“Haka ne ya sayyada, shiyasa ban so ya sakani ba, kin san ina da yayye, kamar ba zasu ji daɗi ba tun da su ne manya, tunda ki ka ce ina ma zaki sake ganin baba ya saki aiki, zaki yi farinciki, sai na sha jinin jikina, komai lokaci ne, wataran da kuɗi nima zan nemi na ganshi ya sakani aiki, ba zan ganshi ba”

Ummi ta ce “Wannan haka yake, Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana, ya yalwata arzikinsa”

“Amin ya Allah sayyada”

*
Kamar kullum sai da ya mayar da ita gida, sannan ya koma office ya cigaba da ayyukan sa, bayan la’asar ya koma gida.

Mami na ganinsa ta hau murmushi, wanda har hakan ya bashi mamaki, ya ce “Mami na ga kina ta fara’a”

Ta ce “Ashe kai Alhaji ya saka duba mutanen da za a bawa zakka, da wanda za a kai umara bana, har da aikin hajji mutum uku?”

Ya kalli mami ya ce “In ji wa?”.

“In ji ubanka, da baka gaya mini ba, ai ni mijina ne ya gaya mini”

Ya ɗan yi miƙa ya ce “To shikenan tun da ya gaya miki”

Mami ta ce “Ohh, Allah dai ya cika mini burina, to su wa ka zaɓa? Dan ina da vacancies”.

Ya dubi mami ya ce “Vacancies kuma, na me?”

“Ahh wanda za a bawa zakka mana da wanda za a kai umara har ma da aikin hajji”.

Raihan ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Amma ni mami, duk a gidanku su Anty Saude, ba wanda ba a kai aikin hajji ba wasu umara, ƙawayenki kuma duk suna da rufin asiri, to wa kuma za a baki? Ai gara a kai waje wasu ma su amfana”

Ta ce “Kai dalla yi mini shiru, nima na san waɗanda suke da buƙata, ka bani vacancies, da kuma kuɗin da zan bayar nima, duk shekara Alhaji yana bani, maganar ma na yi masa ya ce kai ya bawa wannan damar”.

Raihan ya ɗan ɓata fuska ya ce “Haba mami, dan Allah me zaki yi da kuɗi? Zan baku vacancies huɗu, ke biyu Hajiya biyu shikenan, kuɗin zakka kuma gaskiya ba zan iya baki ba, an ware percentage ɗin share ku fa, a ribar da aka fitar ta shekara za a baku”

Mami ta shiga tafa hannu, ta ce “Raihan, wai tsaya ni da hajiyar nan muka yi naƙudarka, da komai sai ka daidaitani da ita, kuɗin mijina ka ce ba zaka bani ba Raihan, shikenan ba zan kyauta ko sadaka ba nima?”

Ya miƙe yana zumɓura baki ya ce “Dan Allah mami kiyi haƙuri, nifa ba haka muka yi da Alhaji ba, what if gwadani yake yi, wallahi kin fi Hajiya yawan ci masa kuɗi ma, haba mami dan Allah” sai ta kasa magana ta bi shi da kallo, gashi dai ita ta haife shi, amma idan ya botsare, wasu lokutan kasa magana take yi, dan bata san dalilin da ya sa yake yi mata kwarjini ba wasu lokutan, idan ta yi ba dai-dai ba ɓaro-ɓaro yake gaya mata.

Manager ya kira ummi a waya, ya ce ta turo account number zai tura mata kuɗinta na albashi.

Bata da account number, dan haka ta kira raihan jikinta yana rawa dan farinciki ta ce “Raihan, manager ya ce na tura account number, zai turo mini salaryna, amma bani da account, ka bani naka na bashi”

Yayi dariya ya ce “Gaskiya banki za su rufe mini account ɗina idan aka saka dubu sha biyar, ni kuɗi idan bai kai dubu ɗari ba, basa shiga account ɗina”.

Ta ce “To ko kawai in bari sai da safe idan Allah ya kaimu, idan na je sai ya bani a hannu kawai ko?”.

“Ina da lambarsa zan tura masa, amma dan Allah kar ki kasa bacci saboda dubu goma sha biyar, kuma kar ki manta kin yi mini alƙawarin zaki kai ni shopping”.

Ayshercool

CUTARWA!

P25

25

Cikin murna ummi ta ce “Ban manta ba, in sha Allah zamu je, nima ina son mu je”.

“To kin zaɓi in da zaki kai ni ɗin?”.

“A’a ai ni ban san wuraren ba, ko ina ne ma kawai sai mu je”

Yayi dariya ya ce “To shikenan, amma dai dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi bacci a nutse kar ki kasa bacci saboda 15k, you are not ɗangote yet, kar ki kasa bacci saboda 15k dan Allah”

Ummi cikin halinta na yanga da ita ba ta gani ta ce “Kar ka dameni fa, ce maka aka yi ba zan iya bacci ba, kuma ko naira goma ce tunda ita ce gumina ai ita ce arzikina dole na yi murna”

“Ahaaf, ai na san ba iya bacci zaki yi ba saboda dubu sha biyar, to dai ki nutsu da ƴar 15k ɗinki kin kasa rufe baki”.

“Ai kuma sai ka yi, ba kula ka zan cigaba da yi ba”

Sosai yake yi mata dariya, noor ce ta shigo ɗakin ta ƙure ummi da take dariya da ido.
Cikin diriricewa ta ce “Raihan sai da safe”.

“Akwai matsala ne?”

Ta ce “A’a zan yi wani abu ne” ta katse wayar tana kallon noor.

Noor ta ƙarasa ta zauna ta ce “Yaya ummi da wa ki ke waya ne?”

Ummi ta ce “Amm ɗan ajinmu ne”

Noor ta waro ido ta ce “Ke fa ki ka ce ƴan ajinku ba sa kulaki, kuma ba kin daina zuwa makarantar “

“Kai maman ƙarya nake yi kenan?”

Noor ta ce “A’a, to amma me ku ke cewa na ga kina dariya, ban taɓa ganin kina waya kina dariya haka ba, ko kema saurayin ki ka yi?” Da sauri ummi ta girgiza mata kai alamar a’a.

“To me ku ka ce a wayar”

Ummi ta ce “Noor kin fa isheni, magana muke za a bani salary ne, shi ne nake dariya, ai kiwa yana son kuɗi, ko ke ba kya so?”

Noor ta ce “Ina so mana, zamu ci daɗi ashe”

“Sosai ma” ummi ta yi maganar tana murmushi.

“Kin san me yaya ummi?”

Ummi ta ce “Sai kin faɗa maman”

“Inteesar ce ta zo fa yanzu” ummi ta ɗan waro ido, ta kalli agogon wayarta ƙarfe goma da rabi na dare.

Ta basar ta ce “Inteesar kawai ko? Ba na hanaki ba, ba zaki ce mata anty inteesar ba?”

“Kema ai ummi take ce miki, kamar fa kuka take yi, sun shige ɗaki ita da maama, na je in ji meyafaru wai in fita har da ce mini munafuka”.

Ummi ta kwantar da noor ta ce “Shhh maza yi bacci, kar in sake jin bakinki, hakan gulma kenan kuma haramun ne babu kyau”

Noor zata sake magana, ummi ta riƙe mata baki, tayi murmushi ta lumshe idonta kamar zata yi baccin.

Ummi ta kashe musu fitila, ita ma ta kwanta, amma noor ta tashi ta lallaɓa kunnen ummi ta ce “Wai mijinta ne zai auro mata kishiya, uncle sagir” ta sauka daga kan katifar ummi ta fita da gudu.

Sai da gaban ummi ya faɗi, ta san akwai tashin hankali kenan, tun da aka ce za a yi wa ƴar gwal kishiya, tayi saurin kawar da tunanin daga ranta dan ba huruminta bane ba.

Maganar raihan ta tuna, wai kar ta kasa bacci, saboda dubu goma sha biyar.

Dariya abun ya bata, ta gyara kwanciyarta ta shiga karanto addu’oin kwanciya bacci.

Aikuwa da safe da ta tashi, ta ga inteesar a gida, idanuwanta sun kumbura alamar ta sha kuka, kuma ba ta samu isasshen bacci ba.

Ummi ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama.

Daga haka ummi ba ta sake shiga sabgarsu ba, dan ta ga alamar ƙiris suke jira tayi wani abu, su huce a kanta, dan haka ta kama kanta, ko sallama ba ta yi musu ba ta fice.

Ɗan halak yana in da suka saba haɗuwa yana jiranta.

“Ina kwana” ta gaishe shi, sai dai maimakon ya amsa ya ce “Inye ka ga attajirar garin nan, ke fa yau jin kanki ki ke yi daidai da kowa, saboda kina da 15K”

Ummi ta ce “Ka cigaba, tuwo ne yau a cikin flask ɗin nan, wannan kuma kunun tsamiya, ka cigaba da tsokanata ba zan baka ba”

Ya kwashe da dariya ya ce “Aikuwa sai na ci abincin nan, kuma ba zan daina tsokanar ki ba”

“Sai ka ci in gani ai”

Raihan ya kunna motar ya ce “Girmata fa ki ka yi, ba fin ƙarfina ki ka yi ba, ƙwace abincin nan ba wahala zai bani ba”.

Ummi ta ce “Idan ya zube shikenan ba”.

“Kar dai ki manta kuɗinki account ɗina za a tura su, attajirar duk duniya”.

Ummi tayi dariya tana kallon window.

Suna zuwa wurin aikin ummi, raihan ya ce a wurin zai ci abincin, idan ya tafi da shi ba zai ƙoshi ba.

Suna shiga wurin bayan sun gaisa manager ya ce “Ummi, an saka miki kuɗin nan fa”

Raihan ya ce “Eh, sun shigo sai ka ce wasu kuɗin kirki, gaskiya manager a ƙara kuɗin nan, haba 15k yafi ta sai man shafawa da cingam”.

Ummi ta kalli raihan ta girgiza masa kai ta ce “Manager na gode sosai da sosai, Allah ya ƙaro mana coustomers, dan Allah kar ka damu da abun da raihan yake faɗa, Allah ya sanya musu albarka ka san yaro ne, sai a hankali” tayi maganar tana kawar da kanta gefe tana dariya.

Manager ya kwashe da dariya ya ce “Ai shiyasa bana biye masa, baƙinciki yake yi miki, shi yana zaman banza, wallahi ko kati kar ki saka masa”.

Kallon ummi raihan yayi ya ce “Me ki ka ce mini yanzu?”

Juyawa ta yi tana dariya, ta nufi wurin da take zama, tayi aiki.

Aikuwa ya bi bayanta, yana sake cewa “Maimaita me ki ka ce mini yanzu?”

Ta ce “Na yi magana ne?”

Ya ɗan tsuke fuska ya ce “Ki maimaita”.

Ummi ta kalli raihan ta ce “Yaro, ko ba yaron bane?” ta sake maganar tana yi masa dariya.

Kyau ya ga tayi masa dariyar da take yi, haƙoran nan sun haska fuskarta sosai, ga laɓɓanta pink shar, dimples hagu da dama a kumatunta.

Yadda ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta zata, ko haushin yaron da ta ce ya ji, dan haka ta sake cewa “Lokacin da ka ke tsokanata, daɗi ka ke ji ai, nima yanzu is my turn”.

Yayi wani irin murmushi ya ce “Wai shekara nawa ki ka bani ne? Na san dai maryam ta girmeki”.

“Ba za a lissafa ba, koma dai yane kawai na girmi mutum, kuma idan kana son ka yi albarka ka din ga yi mini biyayya ka daina tsokanata”

Ya ja kujera ya zauna, har cikin ransa yake jin daɗi idan ya ga ummi ta sake da shi tana dariya, saɓanin da da kullum kamar a tsorace take da mutane, da farkon haɗuwarsu ne, ko haɗa ido ba za ta iya yi da shi ba, amma yanzu da confidence take gaya masa abu.
A ransa ya ce ‘Irin wannan confidence ɗin nake son ki samu, a cikin mutane”

Manager ya ce “Kai raihan, ka wani je ka gurfana a gabanta, zaka kalallame ta ka cinye mata kuɗi, to ahir ɗinka”

Raihan ya ce “Manager, idan na waiwayo kanka ba zaka ji daɗi ba, yau ka sa an kirani da yaro, duk girman nan nawa, the whole me aka ce mini yaro, ke kuma ai shikenan ban abincina in ci, shima dan ba zan iya fushi da abincinki ba, da yasin ba zan ci ba” yayi maganar cikin sigar shagwaɓa.

Ummi ta yi ƙasa da murya tana kallonsa ta ce “Haba kar aji kanmu ayi mana dariya, ci abincinka ko manager kar ka yi wa bisimillah”

“Dama shi ya isa?”

Ummi ta tashi tana ta  ɗawainiya da coustomers, raihan yana cin abinci, suna yi suna faɗa da manager.

A hanya ummi take yi masa faɗa kuma ta haɗe rai kamar wata babarsa “Raihan, ka ce Alhaji ya baka aiki, amma sai ka zo wurina ka yi zamanka ka ƙi yi masa aikin, ko office ɗin fa baka zuwa, meyasa?”.

“Haka aka ce miki bana zuwa?”

“To yau ka je ne? Zama fa kawai ka yi a wurin aikina, yakamata ka kammala yi masa aikin nan on time, sai shiririta ka ke yi”

Raihan ya ce “Nifa ba shiririta nake yi ba”

“To aikin ka ke yi? Banda surutun ƙwallo, me ku ka yi kai da manager? Gobe in Allah ya kaimu ka je office ka yi aiki, idan ba haka ba, ni da kai ne, ba zan kai ka shopping ɗin ba, kuma na daina bin ka mu tafi aikin tare”

Raihan ya ce “Gidanmu dai ni ne autan maza, kuka zan tayi miki, kuma ke da Alhajinmu kin saka babban mutum kuka”

Ummi ta ce “Ai bulala zan samu, na zaneka ka yi kukan da dalili, Alhaji ba zai ce komai ba”

“Wallahi ummi ina iya ƙoƙarina, Alhaji ashe aiki yake tuƙuru ba kaɗan ba, dare nake bi in yi, bana son zaman office ɗin ne saboda kowa sai ya kawo mini abun da suke buƙata, na son zuciya, na rasa yadda zan yi musu, ni ba Alhaji bane cewa nake ba zan yi ba, kuma sai su zagaye su kai ƙarata.
Sai wahalar da ni ake yi, wallaahi ji nake kamar na lallaɓa na gudu bauchi, amma kawai mun riga mun wani saba, ba zan iya tafiya na bar ki ba, ba zan din ga cin irin abincinki ba”

Ƙuri ummi ta yi da ido tana kallonsa, wai yau ita ce a rayuwa wani zai ce yayi sabo da ita, da ba zai iya nesa saboda ita ba, babu dangin iya babu na baba, Allah sarki.

“Ki ke kallona ki bani shawara mana”

Tayi ajiyar zuciya ta ce “Kamar yadda na gaya maka a baya, kar ka nuna wa Alhaji gazawarka, ka yi haƙuri ka daure, da haka zaka san zafin nema, kuma kar ka kuskura ka yi zalunci dan ka farantawa wani rai, ka yi abun da ka ke ganin ya dace, amma dan Allah ka janye maganar guduwa bauchin nan”

“Saboda me?”

Ta ce “Kawai, Alhaji ba zai ji daɗi ba”

“Shikenan, ranar da ki ka tashi da wuri, zaki rakani zagaya ƙananan branches ɗin mu, daga nan sai mu je sayayyar, kamar jibi in Allah ya kaimu ko gobe yayi?”

Ta ce “Eh, Allah ya kaimu, amma dan Allah a cikin kuɗin ka bani ko dubu ɗaya ce idan ban takura maka ba, na sai kayan miya da kaina in yi wa kawu girki, yau zai dawo na saya wa mama noor chocolate, idan ya so ranar da muka je sayayyar sai in siya wa kawu wani abun, da ƴan gidanmu ko?”

“Eh har da gori zaki yi mini, saboda kina da 15k, dan kuɗinki yana wurina, bari a samu POS na baki kuɗinki kan ki tara mini jama’a”.

“Ni ba haka nake nufi ba fa, to yi haƙuri, sonake kawai na farantawa kawu”

“Albashin naki har nawa ne da zaki yi ta rabo? Daga kawu sai noor da ni zaki sayawa abu, idan aka kuma biya sai ki sayawa sauran, kuma ni duk wata sai kin saya mini abu”.

Ba musu ta ce “To”

“Me zaki dafa wa Kawun ne?”.

“Haryanzu ban gama tsarawa ba, amma ina ga alkubus zan yi masa, da miyar ganye yana so sosai”.

“To nima zan ci”.

“To shikenan, idan na gama zan kiraka a waya, amma kar ka ƙaraso gida ka kira ni a waya, sai na kawo maka”.

“Meyasa ba zan ƙaraso gidan ba?”

“Amm, saboda kar a ganka ace wani abun”

Raihan ya ce “Saboda ni ciwo ne?”

Ummi ta ce “A’a ba haka bane ba”

“Salma” ya kira sunanta kai tsaye abun da bai taɓa yi ba” wani yarrr ta ji a jikinta yadda ya faɗi sunan.

Ta waro ido ta ce “Salma kuma?”

“Ba sunanki ba ne?”

“Kuma sai ka faɗa gatsal, ina yayan ni ka daina kirana haka, yaya ummi zaka ce”

Yayi dariya ya ce “Eh to sannu uwar son girma, ba za a faɗa ɗin ba”.

“To ba zan yi alkubus ɗin da kai ba”.

“Kuɗinki kuma suna wurina ba, in sai data da kuɗinki”

“To ai ba damuwa zan yi ba idan ka yi hakan”.

“A’a kar ki zo kina yi mini kuka”.

Sai kuma ya ce  “Amma ummi kamar akwai matsala yanayin zamanki a gidanku ko?” Bata amsa masa ba ta kalleshi.

“Ba sonake na ji sirrinki ba, mun wuce wannan zuwa yanzu, yadda wasu abubuwan suke gudana, duk da ni yaro ne ina fuskanta, dan Allah duk wani abu da zan yi idan zan janyo miki matsala ki gaya mini, kar a ɓata miki rai saboda ni ba zan ji daɗi ba”
Bai jira amsarta ba, ya canza hirar har ta ware.

Suna tafe suna hira suna dariya, suka tsaya wurin masu kayan miya, ta sayi abubuwan da take buƙata ya biya, a tunaninta a cikin kuɗinta ne.

Tana zuwa gida ta tarar da kawun a gida, ummi ta ce “Kawu, na ɗauka sai yamma fa zaka dawo, na yi cefane zan yi maka abincin dare”

Yayi murmushi ya ce “Mamana ta kaina, dawowa ce ta kamani da wuri”.

Ummi ta risuna ta ce “Kawu an biyani salary, shi ne na yi cefanen alkubus”

“Allah dai yayi miki albarka, amma cefane nawa ne ummi, ki riƙe kuɗinki ki yi buƙatunki kar ki ce zaki din ga kashewa a gidan nan”.

“Kawu ka sanya albarka” tayi maganar tana murmushi tana jin ƙwarin gwiwar yin magana kamar tana tare da raihan.

Dr. Ya ce “Allah ya yi albarka”

“Amin na gode sosai ” ta miƙe ta nufi kitchen, farida kuma sai kwaɓe fuska take yi tana hararar ummi babu dalili.

Bayan sallar magariba ta gama girkin da ta yi wa dr., Ta zubawa raihan na sa a flask, ta buɗe data ta yi masa message ya zo ya karɓa, za ta bawa maigadinsu, da ya zo ya ce masa shi ne raihan, zai bashi.

“Sai ka ce wani me ma zance ne? Idan ba ke zaki fito ki bani ba, na ƙoshi”.

“Haba raihan, ba lallai a barni na fita, kuma zan iya samun matsala, wai kai idan ba ka yi rikici da gangan ba ba ka jin daɗi?”

Ya ce “Soryy don’t cry Salamatu, zan zo in karɓa in sha Allah”

“Salamatu ko?” Ya katse wayar yana dariya

Shima bai samu zuwan ba, direba ya aika, ya karɓo masa, babu ƙarya raihan yana sarawa ummi wurin iya girki, dan sosai ya saba da abincinta ya rage yawon restaurant cin abinci, dan cewa yake ƴan aikin gidansu jagwalgwalo suke yi.
Yana cin alkubus ɗin ya kirata yana ta zuba mata santi yana koɗata.

Da safe ummi ta ji abun da ba ta taɓa tunani ba, dr. Ya kan yi faɗa wasu lokutan, duk da yana da kawaici amma yau ya ɗau zafi da yawa.

Farida yake zazzagawa bala’i, a kan lallai inteesar ta koma ɗakinta.

“Wai dan Allah dr. Meyasa ka ke haka? Ba zaka tsaya ka ƙwato wa yarinya ƴancinta ba? Ai ba haihuwa ne ba ta yi ba, ɓari take yi bayan ya hanata karatu, ga wulaƙancin danginsa kuma yanzu ace an bashi ƴa zai ƙara aure haka ake yi?”

“Shut up farida, ki daina cusa mata wannan banzar aƙidar taki, bai hanata ci da sha da muhallin zama ba, a kan useless excuse ɗinku, ba zan kira yaron nan muna musayar yawu mutuncina ya zube ba, karatu kume ku ka janyowa kanku, dan haka dole inteesar ta koma ɗakinta a yau ba sai gobe ba, ke kuma” yayi maganar yana nuna kausar da yatsa.

“Abun da ki ka aikata a makaranta kin kyauta mini kenan, kuma kin kyautawa kanki? Carryover shida a courses goma sha ɗaya, uban me ki ke yi a makarantar? Duk uban kuɗin da na kashe? Kuma baku gaya mini ba HOD ɗin su ne ya kirani ya gaya mini, haka ki ka ga ummi tayi ko Abdul? carryover shida fa, courses shida ki ka faɗi a sha biyu, ba ma ɗaya ko biyu ba balle ace tsautsayi ne, me hakan yake nufi? In cigaba da asarar kuɗina? Idan auren ki ke so kema sai ki yi mini bayani ki fidda miji”

“Kaga duk ba a kai ga wannan maganar ba, tsautsayi ne bai kuma wuce kan kowa ba, ita ummin kana da tabbacin ƙoƙarinta ne ba satar amsa”

“Ki yi mini shiru farida kan na yi miki rashin mutunci, ƴa ta tafi ƙarfin ta yi satar amsa, dan haka zaɓi biyu zan baku, ko dai in ga canji next semester ko kuma ta fitar da miji, in yi mata aure ta bar mini gida, ta daina tara mini ƙarti a ƙofar gida tun da hankalinta a kan su yake ba karatun ba”.

A harzuƙe farida ta ce “Waccan guzumar yakamata ka bawa wannan zaɓin ba kausar ba? Da ta gaji da balaga ta riƙe a gida taƙi fitar da miji, ita ma sai a saka mata wannan dokar, ai an yi na Allah, an riƙeta tayi karatu, ko ta fitar da mijin aure ko a san yadda za ayi da ita, dan wallahi nima sai ta bar mini gida ba zan cigaba da zama da zabgegiyar mace a cikin gida ba, kuma kana sakawa ƴaƴana doka ba, wallahi ita ma sai ta bar gidan nan “

Ganin da ya yi idan ya yi magana komai na iya faruwa, ya sanya ya ɗauki mukullin motarsa ya fice, ummi tana jin abun da yake faruwa ta dake, ta fito daga kitchen ta ɗaukko takalminta tana gogewa za ta fita.

“Ke ummi! Da ke nake na san kin ji komai ai” ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“Na gaji da zama da ke a gidana, ina buƙatar space nima, tun da komai ke ce ki ka iya, ƴaƴansa ba su iya ba, duk in da miji yake ki nemo shi, sai kin bar mini gida ko kuma wallahi ki koma ƙauye in da ki ka fito”

Kausar da take kuka ta ce “Wallahi maama ta bar mana gida, banza mummuna ko kuma koma waye a aura mata, ta rabamu da ubanmu ji yadda ya ci mini mutunci”

Inteesar ma ta fito falon tana faɗin “Ai wallahi maama ki tarka mata tsummokaranta baya nan, ta bar mana gida, tuntuni ki ke cewa sai ta bar gidan nan, idan ki ka cigaba da zama da ita wannan dai ba auruwa za ta yi ba, idan ba sadakarta za ayi ba, sadakin ma shi Abba ya biya ba, ko a mayar da ita can ƙauyen ta samu dai-dai da ita”.

Ummi ta saka takalmanta, ta tashi zata tafi, farida ta zabga mata wata irin ashar ta ce “Dawo nan ina magana zaki wuce, sai na tsinke ki da mari tukuna, ƴar ƙauyen banza daga zuwa cin arzki kin zaƙe, baya ganin kowa da gashi sai ke, zan yi maganinki, in dai ina numfashi wallahi sai kin bar mini gida. Ya kai ki duk in da zai kai ki, tun da su dangin mahaifiyarki da ƴan ƙauyen naku ba su da hankali, da ma neman maraba suke yi da ke”.

Ummi ta danƙe wayarta da take vibrating na kiran raihan, zuciyarta na wani irin zafi, idanunta suka cika da hawaye, yanzu meye laifinta a saɓanin da suka samu yau ɗin, da har aka huce a kanta haka da cin mutunci.

Sai da farida ta gama, sannan ta juya ta kamar hanyar fita, ta goge hawayen da suke shirin zuba, saboda kar raihan ya gane, ya matsa mata da tambayoyi.

Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kai, dan ko gaishe shi ba ta yi ba, kawai ta zauna, tana ta murza yatsunta.

Ya kunna motar sannan ya ce “Yau kin shanya ni fa, ga kuma kulolinki na abinci na gode sosai, Allah ya ƙara zaƙin miya”.

“Amin” ta faɗa a hankali.

Tsit har suka kusa zuwa ya gaji da shirun yana ta son ya tsokane ta, amma gaba ɗaya ko in da yake taƙi kallo, waje take kallo, tana fargabar kar Allah ya jarrabeta da abun da zai mayar da ita gagarawa.

Unexpected taga har sun je tana can tana tunani, ta kalli gefe ta ce masa thank you.

Ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma ta ga ya saka lock, ta waiwayo ta sanya idonta cikin nasa, bai ce komai ba ya zuba mata ido.

Idonta fal hawaye ta ce “Zan sauka”

“Are you ready to tell me?” Yayi maganar very serious.

Ta ɗan sake yin shiru, tare da sunkuyar da kanta ƙasa.

“Salma” ta saci kallonsa sannan ta sauke idonta, tana ta kokowa da hawaye kar su zubo.

“Yanayinki ya bayyana komai, kuma kin saka ni a damuwa nima, dan Allah gaya mini, idan ba haka ba zan yi ta kokwanto”.

Kawai hawaye ya fara gangarowa daga fararen idanuwanta, wani na bin wani.

Tun tana yi a hankali, har sautin kunkan nata ya fara fita sosai da sosai, ta sanya tafukan hannayenta, tana wata irin sheshsheƙar kuka mai ƙona zuciya.

Ji ya din ga yi ina ma kowace irin damuwa ce, ya ɗauke mata ita duka, idan ba zai iya ba su raba damuwar biyu.

Ya saka hannayensa ya sauke nata, ya zira hannu a aljihunsa ya ɗaukki handkerchief, ya saka mata a hannunta ya ce “Ya isa haka, goge hawayenki”

Ya kira manager a waya, ya ce masa ummi ba ta da lafiya, ba zata shiga shago ba yau.

Ummi ta kalleshi, ya ce “Mu je yau ki tayani aiki a namu office ɗin yau”

Za ta yi magana ya ce “Mata shhh” ya ja motar ya bar wurin.

Ta ɗan yi shiru tana kallon hanya, ta rasa dalilin da ya sa ba ta iya yi wa Raihan musu.

“Mu je ki ga wurin aikina, sai mu je shopping ɗin, daga nan zaki gaya mini meyasaki kukan?”

Tayi ajiyar zuciya tana kallon fuskar sa, “Ko haryanzu ban kai in san damuwarki ba?” Ta girgiza kai alamar a’a.

“To idan kin huce, sai ki gaya mini”

Suna tafe yana ta ɗan jan ta da hira, ta fara sakewa.

Ummi ta sha mamakin ganin wurin aikin su raihan, kuma nan kawai babban office ne na gudanar da ayyukan kasuwanci, ba wurin da suke gudanar da kasuwanci ba.

Yadda raihan ya wani maze, ake ta girmama shi, har mamaki ya bata, kamar ba raihan ɗin da suke hira da wasa da dariya ba, ya wani maze.

“Raihan wai me ku ke sayarwa ne?”

“Mutane, da masu kukan banza, da matsorata, da ragwaye, sai kuma mun kai sai kawunan mutane mu sayar, kin ga kamar ke ɗin nan, na ajiye ƴan china zan sayar musu da idonki ne, da ƙafafuwan ki a cire a saka mini” handkerchief ɗinsa da yake hannunta ta kwaɗa masa, yayi gaba yana dariya.

Sagir suka tarar a cikin office ɗin a zaune, yana jiran zuwan Raihan.

Ummi ta gaishe shi ya amsa, raihan ya ce “Yaya ya na ganka a nan kuma, lafiya dai ko?”

“Kai haka ka ke yi sai ka ga dama zuwa wuri kake zuwa? Ka shanya mutane suna jiranka?” Ya jefa masa takarda ya ce “Signing zaka yi mini”

Raihan ya ƙarewa takardar kallo ya ce “Wannan Alhaji yakamata ka bawa yayi maka”.

“Shi ya turo ni wurinka”

“Amma yaya meyasa zan yi Signing ka fitar da wannan kuɗin haka? Me zaka yi da su?”

Abun ka da mai shaye-shaye a kusa, ya daki tebur ya kalli raihan ya ce “Wai kuɗin nan nake ne? Ina ruwanka ne, ya gani ya ce in zo ka saka mini hannu, business zan fara, kar ka ɓata mini lokaci”

Raihan ya juya takardar ya ce “Sana’ar me?”

“Ban sani ba” ya bashi amsa.

“Ba zan saka hannu a wannan takardar ba yaya ka yi haƙuri, sai dai ka zo mu yi aiki tare a din ga biyan mu, sai ka tara kuɗin da ka ke buƙata, amma yana shan wahalar tara dukiyarsa bai kamata a din ga yi masa ɓarna ba”.

Kan kace kwabo, sagir ya shaƙe raihan, yana zazzaga masa bala’i.

Nan da nan ummi ta rikice, saboda ba ta son faɗa ko tashin hankali, take ta fara kuka, tana basu haƙuri.

Yinƙuri ɗaya Raihan yayi, ya hankaɗa Sagir, sai da ya kai ƙasa.

Ya ɗauki takardar ya yayyaga, ya watsa masa cikin kurari da zafin rai ya ce masa “Get out” ya ɗaga murya ya ce “Idan da wani a waje, ku kirawo mini security su fita da shi”.

Ummi ta ce “Raihan yayanka ne fa, ya zaka yi masa haka?” Kallon da ya yi wa ummi ne ya sanya ta jan bakinta ta tsuke, dan gaba ɗaya tsoro ya bata jikinsa har tsuma yake yi, kamar wani zaki.

Khadija ƴar gatan mama, ina gaisuwa 😂 Autar manya tamu ta gargajiya, Allah ya bar zumunci, ɗaukacin jama’a masoya littafin CUTARWA! ubangiji Allah ya bar ƙauna

Ayshercool

CUTARWA!

26

26

Sagir ya miƙe cikin zafin rai ya ce “Ni ka yi wa haka raihan?”

“Na yi maka ɗin, da na lallaɓaka meyasa ka kai ni bango? Ai sai ka bari na kammala masa aikinsa na bar office ɗin, sai ka sake rubuta masa wata takardar shi ya sanya hannu ba ni ba”.

Cikin zafin rai Sagir ya nuna kansa da yatsa, yau shi raihan ƙanin ƙaninsa ya yi wa wannan cin mutuncin.

“Zaka ga abun da zan yi maka, komai ya faru ka kuka da kanka”

Raihan ya ce “Get out from here, ko na sanya security su fitar da kai”.

Ummi ta ce “Dan Allah raihan kar ka yi haka, zaku zubarwa da mahaifinku mutunci a gaban ma’aikatansa, kuma kar hakan ya shafi zumunci da mutuncinku”

Sagir ya fice daga office ɗin rai a ɓace, Raihan ma rufa masa baya ya yi, ummi ta bishi da sauri za ta yi magana, ya ce “Ki jira ni a nan” ya fice shi ma.

Zama ta yi zuciyarta babu daɗi, tana ta tunani, yanzu ace ƴan gida ɗaya ciki ɗaya suna wannan abubuwan, abun da mamaki.
Sai kuma ta tuna ba abun mamaki bane ba, duba da yanayin na su familyn suma.

Ummi har ta fara gajiya da jiran raihan, ta kira shi a waya, amma ta ga wayar ta sa a office ɗin tana ringing.

Ta sauke hannunta a hankali, tana cigaba da kallon hanya, Raihan ya dawo office ɗin, hannunsa ɗauke da leda, ya ajiye a kan table ya kalleta ya yi murmushi ya ce “Afuwan na bar ki kina ta jira, bari mu ci wani abun”

Miƙewa ummi ta yi ta ce “Tafiya zan yi, ka rakani na samu abun hawa na tafi”

Cikin mamaki ya kalleta ya ce “Meyasa?”

“Au tambayata ma ka ke yi? kamar ba yanzu ka gama hantarata ba, daga gaya maka gaskiya, dama ina cikin wata damuwar ka ƙara mini wata” tayi maganar a shagwaɓe tana kai hannunta fuskarta, ya zata da wasa take yi, kawai ya ga ta fara zubar da hawaye.

Da sauri ya ƙarasa gaban ta, ya kai hannu zai sauke mata hannunta yana faɗin “Am sorry please, let me explain..

Ta ja da baya ta ce “Kar ka sake taɓa ni, ni tafiya zan yi”

“To shikenan, na yi kuskure amma dan Allah ki yi haƙuri”.

Ummi ta sauke hannunta ta ce “Na ji, amma ka mayar da ni”

Raihan ya ce “Dan Allah ki zauna ummi, mu yi magana ki yi haƙuri Please “

Yadda yake ta marairaicewa ne ya sanya ta ga idan ta cigaba da yi masa musu, ba ta kyauta ba, dan haka ta zauna, shima ya ja kujera ya zauna.

Ya kalleta ya ce “Am sorry ummi, this is the raihan you don’t know, ina da haƙuri amma idan aka ƙure ni bani da kyau, mutum ne ni mai zafin zuciya da fushi, amma da wuri nake sauka.

Yaya Sagir da Salim, su ne manya, kuma mahaifinmu yayi iya ƙoƙarin sa a kan inganta rayuwarmu, sai dai sun ƙi makaranta, sun ƙi sana’a kullum sai ɓarnar kuɗi a kan mata da shaye-shaye.

Ban taɓa tunanin haka mahaifinmu ke shan wahala a kan dukiyarsa ba sai yanzu, a haka ma fa aikin da ya sakani iya gida Nigeria ne, yadda yake zirga-zirga sai kin tausaya masa.

Sana’arsa ba ɗaya ba ce ba, mutum ne mai nasibi a harkar kasuwanci, muna shigo da kayan gini daga ƙasashen ƙetare, ana bamu kwangilar kayan gini, na ofisoshi, manyan ma’aikatu na gwamanti da na ƴan kasuwa, kuma muna rarraba wa kamfanoni da yawa kayanmu a Nigeria da ƙasashen maƙwabta.

Ya kunna system ɗin gabansa, ya shiga nuna mata kayayyakin da suke sayarwa, kama daga ƙofofi, furnitures, kayan banɗaki, da sauran kayan alfarma na ƙawata gini.

“Ɓangare guda, mahaifinmu babban dealer ne na shige da ficen kayan masarufi, sai dai an fi saninsa da harkar kayan gine-gine, iya kano muna da shaguna sun kai goma sha biyu a wurare daban daban ban da sauran garuruwa. Mahaifinmu duk shi yake kula da ayyukan kasuwancin sa, sai ma’aikatansa wasu lokutan a cuce shi a karkatar da kuɗaɗen sa, babu mai taimakonsa a cikinmu sai dai ya nemo mu kashe.

Wannan shi ne babban ofishinmu na ƙasa, duk da ya ce zai mayar da shi Abuja, duk da haka mukan tafka asara wasu lokutan, amma hakan ba ya sanya mahaifinmu shiga hakkin ma’aikatansa, idan an samu riba da yawa kuma, ya kan ƙara musu domin farincikin su da mu baki ɗaya, to kuma duk da wannan abun sai azo da son zuciya mu ƴaƴa cikinsa mu din ga cutarsa duk ƙoƙarin da yake yi mana?”

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Raihan, na ji duk abubuwan da ka faɗa, ka na da gaskiya, amma still ka yi kuskure, ba dan Allah ya fi sonka ya sanya ka zama shiryayye ba har Alhaji yake janka cikin al’amuransa ba.

Yayyenka na buƙatar kulawarka da tausayawa, a wannan halin suna sama da kai, amma ace sai ka yarje musu yin wani abu, ka yi tunanin yaya za su ji? Ka na da gaskiya, amma kamata yayi ace ka yi ƙoƙarin dannewa kun rabu lafiya, abun da ka yi masa bai kyautu ba gaba ɗaya.

Raihan komai lokaci ne, ina sake jaddada maka, ranar da ba sa doron duniya sai ka din ga ina ma ace, ni ba gani ba, sha’awa ku ke bani, mahaifina ya rasu, mahaifiyata ban san in da take ba, bani da wa, ba ni da ƙani, haka nan kawai dai rayuwa nake yi. Duk da ka ce yayyenka basa ji, but they are blessing to you idan ka kallesu ƴan uwanka ne, ban ce ka ƙyale su su yi abun da bai kamata ba, amma gaba suke da kai, su yakamata ace a wannan position ɗin, amma Allah ya ƙaddara kai ne ba su ba, haba Raihan, why are you kind to me, amma brother’s ɗin ka ka yi musu haka?”

Gaba ɗaya jikin raihan yayi sanyi ya ce “Haka ne, na yi kuskure kuma na fahimce ki, in sha Allah zan kiyaye gaba ba zan sake ba, raina ne ya ɓaci sosai, kuma na yi ƙoƙarin dannewa amma yayi pressing ɗin na”

“Yauwwa dan Allah ka daina, ba ka ‘ sanin muhimmancin wasu abubuwan a rayuwa, sai ranar da ka rasa su, wani rashin idan ka yi sai ya tafi ya barka da rauni mai raɗaɗin da har ka koma ga Allah ba zai goge ba, kamar dai ni da na rasa babban masoyina babana, da barinsa duniya ya yi wa rayuwata giɓi” tayi maganar hawaye na kwararowa daga idonta, har jijiyar goshinta ta tashi.

Raihan ya matsa kusa da ita ya ce “Ummi, dan Allah ki daina koke-koken nan haka, Addu’a ita ce abun da mahaifinki ya fi buƙatar mu yi masa”.

Ta jinjina masa kai tana share hawayen ta, ya ce “Ga lemo na sayo mana, na san is hardly idan kin karya, yau ba ki zo mana da abinci ba”

“Na ƙoshi, ba zan iya cin komai ba”

Cikin damuwa raihan ya ce “Ni gaya mini menene ya saka ki kuka ma tun farko, kin ce zaki gaya mini”

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “A bar wannan zancen kawai”

“Ba za a bar shi ba, sai mun yi shi, ai alƙawari ki ka yi mini”

“Ai ba zaka gane ba”.

Raihan ya ce “Zan gane, ko ta ina ne yi mini bayani, ina cin maths a aji ai” yayi maganar yana ɗan murmushi.

Ta ɗan tsura masa ido, har cikin zuciyarta take jin yardar da ta yi wa raihan, ba ƙarama ba ce ba, saboda sosai take jin sa a ranta, mutumin da yake ta ƙoƙarin fuskantar matsalolin ta.

“Ina ƙarama mahaifina ya rasu, kakata ta karɓi riƙona daga hannun babata, nikaɗai kuma suka haifa, mama ta koma garinsu, ƴan uwanta suka yi ta zuwa a basu ni, amma kakata ta hanasu ni, aka ce mamana ta haihu ɗan babu rai, ga damuwar rabamu, ta samu larurar ƙwaƙwalwa, amma aka hana su ni, har ƴan uwan mama suka yi fushi, basu sake zuwa sun ce a basu ni ba.
Abubuwa suka ɗan faffaru, har kawu yahaya, ya ɗaukkoni daga gagarawa ya dawo da ni nan, tun da ya kawo ni, ake ta samun issues da family ɗin sa, Allah dai yayi sai na zauna a gidan, yanzu ma dai wata rigimar ce ta taso, matar kawuna ta ce zan bar gidan na koma ƙauye, ni kuma bana son komawa garin nan wallahi, mamana nake son gani, wallahi ko ba ta warke ba ko bola take bi, zan bita bolar mu rayu tare da dai in koma wannan garin da ko sunansa bana son ji, Raihan aƙalla na kai shekaru goma sha takwas rabona da mama, kuma ban ji labarin ta rasu ba, kowa yaƙi gaya mini sunan garinsu abun da na sani kawai a Maiduguri take.
Ba wanda yake kulani, duk wanda na raɓa sai ya tsangwameni, an ce mini mummuna, an ce mini mayya, an aibata ni, to wai ya zan yi nema? zuciyata ta kusa fara ciwo, ban ma san ina na dosa a rayuwata ba, tun a kan cinyar mama nake ganin bala’i da tashin hankali, raihan tafiya kawai nake yi amma na san zuciyata na ciwo, ƙwaƙwalwa ta kuma kamar  na haukace nima, abubuwa suna damuna, ba wanda yake zama na gaya masa ya zan yi?” Wata irin karkarwa ummi take yi, tana magana ba comma babu full stop, wani ɓoyayyen abu ne da yake cin zuciyarta da ba ta taɓa zama ta faɗe shi ba, once in her life, yau ta samu chance.

Babu tsammani ta durƙushe a ƙasa daga kan kujerar, tana kuka mai sautin gaske.

Raihan bai san lokacin da ya durƙusa, duk da dauriya da dakiya irin ta raihan, yau da aka zo gaɓar da yake jira a zo, ya ji wacece ummi, ya ji sai dai zuciyarsa ta gaza ɗauka, zuciyarsa ta karye, ashe da ba tausayinta yake ji ba, kallonta kawai yake yi bai san meye a ƙunshe a zuciyarta ba, a hakan ma ba wai buɗa masa rayuwar ta tayi ba.

Shekara sha takwas, ba ta sanya mahaifiyarta a idonta ba, alhalin duk suna raye, bama ta san in da take ba.

Ya sanya hannun sa cikin tattausan hannunta, yana murzawa a hankali amma ya kasa magana, sai saurara sautin kukanta, da yake ƙara bugun zuciyarsa.

Danƙe hannunsa tayi sosai a cikin nata, tana ƙara pressure kukanta.

“Is ok salma, ya isa haka” ta girgiza masa kai ta ce “Allow me, idan na yi kuka ina jin sauƙi”.

Ya ɗora hannunsa ɗaya a kafaɗarta, amma ya kasa magana.

Ganin kukan nata ba mai ƙarewa bane, ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen da suke ta kwarara ya ɗan tura baki ya ce “Nima kin sani kuka, ya isa haka please” yayi maganar yana cigaba da goge mata hawayen.

Kallon raihan take yi, da girmanta ko Abdul bai taɓa kai hannu jikinta haka ba, tana da taka tsantsan da kanta, wa ma ya damu da ita balle yayi yinƙurin kai hannunsa jikinta? Amma rarrashin nan da Raihan yake yi mata, ji take yi kamar ɗan uwanta da suke ciki ɗaya ne yake yi mata.

“Waye ya ce ke mummuna ce?”

Ta ɗan ja numfashi ta ce “Mutane” tayi maganar cikin tura baki

Hannunsa a kan fuskarta, yana goge mata hawayen ya ce “Kuma kin yarda?”

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya girgiza mata kai ya ce “Kar ki sake sakawa kanki cewa ke mummuna ce, i understand that you are traumatized by what people are saying about you, this is common among us. Ke fa malama ce ummi, kin fi kowa sanin Ubangiji gwani ne, kuma ba ya kuskure. Kin manta cikin suratul mu’iminun, aya ta goma sha huɗu, bayan Allah ya yi bayanin yadda yake tsara halittar ɗan Adam da kansa ya yabi kansa ya ce fatabarakallahu ahsanul kaliƙin? Ubangiji da ya yi ki ya yabi kansa, kuma sai ki sawa ranki cewa ba haka ba saboda surutun banza na mutane, as from today duk wanda ya ce miki mummuna, ki tabattar kin gaya masa maganar da gobe ba zai ƙara ba, fight for yourself ke ba mummuna ba ce”.

“Har gorilla fa wani ɗan ajinmu ya ce mini” tayi maganar wasu hawayen na fitowa daga idonta.

Wani abu mai zafi ya soki zuciyar raihan, banda tsabar rashin mutunci ya za a haɗa mutum da biri?.

Amma ya maze ya ce “Sai kuma ki ka din ga kuka ko?”

Kamar mara wayo, ta jinjina masa kai.

Raihan ya ce “Meyasa baki tsinka masa mari ba”

Ummi ta zare ido ta ce “Haka kurum ya dake ni, ni bana faɗa”

“Ai shiyasa mutane suka rainaki ai, da kin guara masa mari, gaba ba zai ƙara ba ai”

Ta girgiza kai ta ce “Ni ban kula shi ba, muna level 3 ma aka kore shi daga makaranta ya yi satar amsa, duk abun da zan yi mutane ba za su daina ce mini mummuna ba” tayi maganar a raunane.

“Sun gano weak point ɗin ki ne, shiyasa suke amfani da hakan suna yaƙarki. Ki kwantar da hankalinki na san kawu ba zai taɓa bari ki koma ƙauye ba, and ki ƙara tuntuɓawa ko zaki samu wani information a kan in da mama take, zan yi iya ƙoƙarina na gano miki ita”.

Ummi ta zabura ta ce “Dan Allah raihan da gaske?”

“I promise you salma, wannan kukan nake son na daina gani sai farinciki a fuskar ki”

“Nifa abubuwan da suke sakani kuka da yawa, ka san alfarmar da nake so ka yi mini?”

“Sai kin faɗa”.

“Dan Allah ka manta na taɓa baka labarin nan, ban taɓa yin irin wannan hirar da wani ba, kai ne mutum na farko da na ji na nutsu da kai, na yi maka kuka, na rage abun da nake ji a raina, dan Allah kawai ka manta da labarin babu wani abu mai daɗi na tunawa a rayuwata, amma for now ka manta da shi, na gaya maka ne saboda na yi maka alƙawarin gaya maka abun da ya sani kuka”

Idanuwanta yake bi da kallo, ya kasa amsa mata maganar, muninta kawai yake so ya gani, amma har ga Allah ya kasa, kawai dai baƙa ce, kuma baƙi dai ba muni bane ba.

“Kayi magana mana” tayi maganar a ɗan shagwaɓe.

“Zan yi, amma ba yanzu ba, mu karya ko, zuwa azahar mu yi salla sai mu je siyayyarmu ko?”

Ummi ta ɗan ɓata fuska ta ce “Ko kawai mu canza rana, kaga yau duk sai godiyar Allah”.

Ya jingina da jikin tebur, ya ce “Kin sani kuka ba, marainiyar Allah, Allah ya ƙara kulawa da ke”.

“Amin amma ba na ce ka manta ba”.

Ya shafa sumar sa ya ce “Kema dai kin faɗa ne kawai, tashi in nuna miki aikin da zan kai wa Alhaji na gama”

Ta miƙe suka koma kan kujera, yadda ya rarraba bayar da zakka, da kujerun umara da na hajji da zasu bayar, da ƙarin da za a yi a ɗan bawa ma’aikatan na riba da sauransu.

Ummi a ranta ta jinjina dukiya tana nan a in da take, kuma yadda raihan ke gudanar da lamarinsa, ba zaka ce ɗan mai kuɗi ne haka ba, Maryam ce ma dai uwar jin kai, da jin ita wata ce.

Sai da suka yi sallar azahar, sannan suka nufi tafiya, a mota take tambayarsa ina za su je, ya ce mata zata gani.
Ya ja ɗan guntun tsaki ya ce haƙarƙarinsa a riƙe yake, zai fara koya mata mota, ya gaji da aikin direba ba a biyansa.

“Ai ba ni na ɗauke ka aikin ba, kai ka ɗauki kanka, amma ba faɗuwa ka yi ba ka ke ciwon haƙarƙari?”

“Ina fa, coach ɗina ne na gym, ya sakani ɗaga wani ƙarfe, haƙarƙarina ya amsa”.

Ta kalleshi ta ce “Wai sai ka ji wa kanka ciwo tukuna, meye na zuwa gym kai ba ƙiba ba?”

Ya rausyar da kai ya ce “Waye ya ce dan a rame ake motsa jiki, bari na nuna miki ƙarfen da na ɗaga a Instagram” ya buɗe mata wayarsa ya bata.

Suna tafe tana mitar ƙarfen yayi girma, daga bisani ta cigaba da yi masa taɓe-taɓe a wayar.

Suka shiga go slow, yana jiran a basu hannu, ya ɗan leƙa wayar, ya ga ta nutsu, kallon dogwayen riguna kawai take yi tana liking ɗin su, da takalma da jakunkuna.

Ya ɗan yi murmushi, aka basu hannu suka tafi.

Katafaren kantin saye da sayarwa, suka shiga, ummi kamar ƴar ƙauye, sai kalle-kalle take yi.

“Ta ina zamu fara?”

Ummi ta ce “Ko ta ina ne ma”.

Sannu a hankali suke zagayawa, suka fara zuwa wurin turarruka, ya saka hannu ya ɗauki wani, ya jefa a cikin trolley.
Ummi ta waro ido ta ce “Raihan, dubu sha takwas fa aka rubuta, ka manta kuɗin dubu sha biyar ne?” Ya kashe mata ido ɗaya ya cigaba da ɗaukar kaya.

Tayi ta magana, amma yayi mata shiru, suka je wurin kayan kwalliya ya kalleta ya ce “Me ki ke so a nan?”

“To ai kuɗin sun ƙare”

“Ke ina ruwanki ne, ɗauki abun da ki ke so kawai”

Comb ta ɗauka sai ribbon da coacoa butter, dan man yana burgeta ta ce sun isa.

“Wai ke ba kya kwalliya ne, ga su hoda da kayan mata”

“Ni bana wata kwalliya” ta bashi amsa tana ɗan kalle-kalle.

Ya ɗaukko ɗaya wayar ta sa, yana dube-dube, ya ɗaukko wasu mayuka ya koma kan mayukan gyaran gashi, suma ya ɗauka.

“Wannan me zaka yi da su?”.

“Budurwata zan saiwa lefe zan fara tarawa”.

Ummi ta yi dariya ta ce “Riga malam masallaci, za ta kwashi kayan shiririta”

“Ni ne ma shiriritar ko? Son kowa ƙin wanda ya rasa da ni ɗin nan, ɗan kyakkyawan matashi mai gemu, kin san maza masu gemu muna da tsada”.

“Ai mami ta ce mai ka shafa ya fito”

“Wallahi ban shafa mai ba, girma na yi gemu ya fito”

“Muyi sauri kar na makara komawa gida”

Ita dai ummi ta zuba wa sarautar Allah ido, ta san dai abubuwan da raihan ya ɗauka, sun fi ƙarfin kuɗinta nesa ba kusa ba.

A wurin biyan kuɗi aka yi billing ɗin sa kuɗi masu yawa, ya basu ATM suka cire.

Gaba ɗaya ummi ta manta da damuwar da ta baro a gida, jin zuciyarta take fes, yau ta faɗi abun da yake ci mata zuciya tsawon shekaru, kuma ta samu ta yi kuka, an saurareta.

“Raihan” ya ɗago ya kalleta “Na gode sosai da lokacinka, Allah ya saka da alkhairi, ya ja kwanan Alhaji da mami”

Ya ce “Da kuma Hajiya” tayi murmushi ta ce “Amin, kuma dan Allah da ka je gida, ka yi haƙuri ka danne zuciyarka, ka bawa yaya Sagir haƙuri dan Allah”

“Zan yi in sha Allah”

“Allah ya yi maka albarka”

Kasa amsa mata yayi sai murmushi, ƙasan zuciyarsa na hango masa ita tana kuka ɗazu.

Suka isa bayan layin su ummi, ta buɗe motar ta sauka har ta fara tafiya ya ce “Ke wannan alkunyar taki tayi yawa, maimakon ki ce “Malam bani kayana, ko kin bar mini  dubu sha biyar ɗin taki?” Ta waiwayo ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya fito daga motar, ya ɗaukko kayan yabi bayanta, ta tsaya cak ta waiwayo ta ce “Ina zaka ne?”

“Gidan zan biki na kai miki kayan”

A rikice ta ce “A’a dan Allah”

“To karɓi kayanki”

“To ya zan yi da su, idan aka tambayeni….

“Ki ce da salarynki ki ka saya, ba wasu kaya ne masu yawa ba fa, ya kamo hannunta ya danƙa mata ledar ya ce “Zan je gida na cika alƙawarin da na yi miki” ya juya ya koma motarsa ya tafi.

Cikin mamki ummi take kallon kayan, wai duk wannan nata ne? Amma uban kuɗin da raihan ya kashe, dubu ɗari da sha takwas, kayan mai turare da ciye-ciye.

Cikin matsananciyar fargaba ta shiga gidan, kasancewar ɗakinta ne a farko, ba ya cikin main safe contain na gidan, shiyasa ba sa sanin shige da ficenta.

Ta kalli agogo ta san noor tana makarantar islamiyya, da ta kirata ta gani.

Tayi alwala ta yi sallar la’asar, ta zauna ta din ga kallon kayan, wannan mayuka masu uban tsada, ita za ta shafa a fatarta.
Wai har da hoda, to ita mai za ta shafawa hoda ma? Ta ɗau turaren tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyi da daɗin gaske.
Ga roll on, kusan kala huɗu, wanda kullum cikin dabaru take na haɗa alumun, ko ta jiƙa gishiri bayan yi wanka ta shafe jikinta, saboda kar ta yi wari.

Wata envelope ta gani a cikin kayan, wadda ba ta san da ita ba, ta ɗauka ta buɗe taga kuɗi a ciki sai takarda.

“Assalamu alaikum, brown eyes, this is your first salary, given to you 15th April, spend it well, ga additional na 15k making 30k, ki lallaɓa na ji daɗi na kuma gode da shopping, Allah ya ƙara arziki ummita. Raihan” galala take bin takardar da kallo, Raihan ya mayar da ita sakarya ma.

Wurin Alhaji ya fara zuwa, ya tarar da mami, da kuma Hajiya tare da Alhajin.

Cikin damuwa mami ta ce “Raihan sannu da zuwa, ba abun da ya sameka dai ko?”

Ya ce “A ina?”

“An ce mini Sagir yaje har office, ya yi yinƙurin dukanka, na kira wayarka baka ɗauka ba, na zo in ji ba’asi”.

Raihan ya haɗe rai ya ce “In ji wani munafukin ne ya faɗa?”.

Alhaji ya ce “Bai yi maka komai ba dai ko?”

“To aini Alhaji ban gane yayi mini wani abu ba?”

Sagir yayi sallama, suka amsa banda mami da take sababi tana faɗin “Wallahi dole ka ɗau mataki Alhaji, kar a kassara mini ɗa a cuceni”

Cikin dakiya Hajiya ta miƙe ta ce “Sagir, uban meye ya kai ka wurin raihan, ka yi yinƙurin dukansa?” Yayi shiru yana kallon Hajiyan.

Alhaji ya ce “Yi masa a hankali, ni na tura shi wurinsa, ban san kuma haka zata faru ba, zo ka yi mini bayanin meyafaru?”

Cikin fusata hajiya ta riƙo rigar Sagir ta ce “Ba magana nake yi maka ba? Zuwa ka yi kayi rashin mutunci a gaban mutane ko sagir? Idan baku yi abun da za a ce baku kyauta ba ba kwa jin daɗi ko?”

Raihan ya cire hannun Hajiya daga jikin Sagir ya ce “Duk fa baku fuskanta ba, ya zaku ɗauki zafi a kan abun da ba a gabanku aka yi ba? Ni ne mai laifi abun da na yi wa yaya Sagir yana gaba da ni ban kyauta ba, kuma da niyyar ba shi haƙuri na dawo, bai kamata ba yadda na yi treating ɗin sa, dan Allah ka yi haƙuri yaya Sagir” wani irin mugun kallo Sagir yayi masa, tare da tunanin wata shiryayyiyar ce Raihan da babarsa suka shirya, kawai ya juya zai tafi, Hajiya ta bishi a zafafe, Raihan ya riƙeta ya girgiza mata kai, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na yi mata zafi.
“Jarrabawa ce mai buƙatar juriya Hajiya, ki daina yi masa kuka” raihan ya faɗa da sigar rarrashi.

Mami kuma sai rashin mutunci take yi, tana yaɓawa Hajiya magana, Raihan ya dafa kafaɗarta ya ja ta suka bar falon yana rarrashinta.

“Gaskiya Alhaji ka saka baki, yaranta ba za su lalace kuma ta din ga nema ta ƙwace mini ɗa ba, alhalin yaranta na barazana ga rayuwar Raihan ba.

Ummi ta yi ta kiran raihan a waya, amma sai ta ji busy, bama ta shiga gaba ɗaya, haka ta haƙura ta ajiye ta tafi kitchen dan yin sanwar dare.

Farida ta daka mata tsawa, ta ce kar ta kuskura ta shigar mata kitchen, ba ta buƙata, domin kuwa barin gidan za ta yi.

A karo na farko da ummi ta ji ko a jikinta, yau ta samu hutu.

Alhaji Tahir ya kira meeting na gaggawa na iyalansa, da manyan manajojinsa da lawyoyinsa gidansa, bayan sallar isha’i.

Suka din ga mamakin hakan, dan kuwa ba su san dalilin hakan ba, dan bai taɓa yi ba.

Raihan yana maƙale da Hajiya, dan tun ɗazu da suka bar falon, sashinta ya koma ya tare yana rarrashinta.

“Bakomai ne ya sanya na taraku a halin yanzu ba, sai dan gabatar da wani hukunci da na yanke, wanda na daɗe ina nazarinsa kafin yanke shi.

Daga yanzu Raihan zai riƙe office ɗina, na tsawon shekara guda, ni kuma zan koma gefe ina monitoring ɗin ayyukan sa, duk hukuncin da ya zartar kamar ni na yi ne, duk mai buƙatar wani abu, zai yi a rubuce ya kai masa, yana da damar sallama ko ɗaukar ma’aikata, kar wanda ya zo ya sameni ya sani in yi masa wani abu, wurinsa za aje. Aikinka tuƙuru shi zai tabattar da kai a kan wannan kujera mai nauyi, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan sabon MD na Tahir and Son’s Limited.

Wata irin razana raihan yayi yana kallon mahaifinsu, yayin da Mami ta rangaɗa guɗa tana faɗin “Ƙaraminsu babbansu, ka ga ɗan ƙaramin sauro mai hana giwa bacci”

Hajiya da yake zaune kusa da ita ta yi murmushi ta shafa sumar Raihan ta ce “Allah ya tayaka riƙo babana, Allah ya tsare mana kai”

Raihan kuwa miƙewa yayi ya bar falon, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan Allah ya gani baya so, kuma ya ƙudirci a watse ya samu Alhaji.

Ayshercool

CUTARWA!

P27

27

Mami har ta yinƙura za ta bi bayansa, amma Alhaji ya hanata, mami tamkar ta taka rawa, tana kallon fuskar Hajiya, ko zata ga damuwa ko ɓacin rai a fuskarta.

Amma sam bata ga hakan ba, sai ma fatan alkhairi da take ta yi wa raihan ɗin, su kansu su Salim ko a jikinsu, sai dai Salim ya ɓata fuska ya kalli Alhaji ya ce “Yanzu idan muna buƙatar wani abun sai mun je wannan yaron ƙanin bayanmu ya yarje mana, ni bani da matsala da koma me ka bashi, amma wallahi ba zan je wurinsa neman abu ba, a nemi wani abun kawai”

Sagir ya ce “Balle kuma ni, da yayi niyyar dukana, sai dai ace na daina morar komai a gidan nan, da dai ace in je in sake neman wani abu a wurinsa wallahi”

“Sagir….

“Shhhh” ita ma Alhaji ya hanata yi masa magana, duk ya ce su rabu da su.

Raihan wuri ya samu yayi zamansa, gaba ɗaya ransa babu daɗi, saboda sam bai yi farinciki da wannan al’amarin ba.

Har kusan sha ɗayan dare, babu wanda ya san in da raihan ya yi, Alhaji kuma yana falo yana jiransa, dan ya san a daren dole zai dawo ya neme shi.

Aikuwa sai ga shi yayi sallama ya dawo, da ya tabattar kowa ya watse.

Alhaji bai ɗago ya kalli raihan ba, har ya zo gabansa ya zauna, a hankali ya ce “Alhaji”

“Ka dawo ka ce mini ba zaka yi aikin bane ko? Ba ka so na nemi wani, kaima da nake jin daɗinka zaka fara bujure mini”

Jiki a sanyaye raihan ya girgiza kai ya ce “Ba haka bane ba Alhaji, yayi mini nauyi da yawa, ba zan iya ba wallaahi kaima ka san na yi ƙanƙanta da wannan al’amarin, kuma nine ƙarami kar yayyena su ji babu daɗi a kan hakan”

“Raihan”

“Na’am”.

“Ba lokaci ɗaya kuma kai tsaye na yi assigning ɗin ka a kan wannan matsayin ba, na yi addu’a, kuma na jarrabaka ta kowane ɓangare, kai ɗin ne dai zaka iya, yara nawa Allah yake ɗaukakawa wanda suka kai ka, da wanda basu kai ka ba ma? Wani a waje bare ka ke so na ɗaukko na danƙa masa ragamar dukiyata da kula mini da ku? Ko kuma wannan yayyen naka da ba su san ciwon kansu ba? Ka sani ko takaicin abun da na yi musun, ya sanya su shiryu? Hajiya ce ta bani wannan shawarar, kuma na ga hakan ne ya dace”

Raihan ya kalleshi da sauri, ya ce “Hajiya ce ta ce ka bani ragamar kula da harkokinka?”

Alhaji ya jinjina masa kai, raihan ya yi shiru yana tunani, ya san da mami ce sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa, da dai ta yarda ko ta bayar da irin wannan shawarar.

Maganar Alhaji ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi “Babban mutum, kar ina yabonka salla ka kasa alwala mana, kar ka watsa mini ƙasa a ido, i will always be by your side, duk abun da ba ka gane ba, ko abun da ka ke buƙata i will assist you like a ghost” yayi maganar yana dariya, wanda raihan ma yayi murmushi.

“Alhaji ka ɗaureni da jijiyoyin jikina, kana faɗar maganar nan na ji kamar ka sakani a kurkuku”.

Yayi dariya ya ce “Ba wata kurkuku, ka san babban abun da ya burgeni? Da ka yi offending ɗan uwanka, ka dawo ka bashi haƙuri, ka hana abun da ya faru yin tasiri a cikin gidan nan, da kuma tsakanin iyayenku mata”.

Raihan ya jinjina kai ya ce “Ummi ce ta bani shawarar yin hakan ai, ba idea ta ba ce”.

Alhaji ya sake dubansa ya ce “Wace ummi kuma?”

“Baka santa ba, ƙawata ce bari ne je na kwanta Alhaji, idan na yi bacci wataƙila kaina ya daina ciwon”.

“To Allah ya bamu alkhairi, zan saka ranar yi maka walima tare da abokan hulɗarmu da ma’aikata, da gabatar da kai a matsayin sabon MD”.

“Alhaji riƙon ƙwarya fa ka ce, ko dai wayo ka yi mini?”

“Tashi ka tafi sai da safe” kamar soko raihan ya tashi ya bar ɗakin ya nufi ɗakinsa.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya tsaya ya ɗaga.

“Ƙaraso sashina ina son ganinka” ya sauke hannunsa shi ko son yin wata maganar baya yi.

Ya koma ya nufi sashin mami, tana falo tana jiransa, “Mami, baki yi bacci ba?”

“Ya za ayi na yi bacci, zaka yi mana sagegeduwa, ai bacci bai kama ni ba, dole na din ga bacci da ido ɗaya. Uban me ka je ka cewa Alhaji?”.

Kai tsaye raihan ya ce “Ce masa na yi ya taimaka ya saukeni daga muƙamin nan”.

“Saboda ba ka da hankali ko? Allah ya ƙwaci abun ya baka, sai ka ce ba ka so saboda shashasha ne kai raihan?”

Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban abun da ya bashi mamaki, irin huɗubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya.
Ta kafa wa Hajiya ƙahon zuƙa, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haɗe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaɗai ne a ƴan ɗakinsu suke shiri da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba.

Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta ɓoye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi ɗaukar hankalinta.

Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya ɗagawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana sake kiran wayarsa farida ta shigo ɗakin.

Gabanta ne ya ɗan faɗi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta ƙyallin man da ta shafa, ga ƙamshi da ɗakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar da kai tana danna waya.

“Ke!” Ta daka mata tsawa, ummi ta ɗago da sauri, ta ja hijjabi ta saka.

“Dalla ki tashi ki wuce ki ɗora mana abincin dare” kallonta ummi take da mamaki, ɗazu taje tayi girkin ta koreta ta ce ba ta buƙata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi.

Da “To” ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen.

Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an ƙi ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta ɗanɗana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai male-male a kai.

Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta ƙuduri aniyar ƙuntata mata, kausar ta yi girki ya ƙi ciyuwa.

A daren ta tuƙa tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma ɗaki.

Missed calls ɗin raihan ta tarar, da message “Call me when you are available”

Ba ɓata lokaci ta kira shi, ya ɗaga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce “Ka kyauta raihan”.

“Da na yi me?”

“Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka ƙi ɗaga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi ƙarfin kuɗina, kuma ka dawo mini da kuɗina har da ƙari, kafi ƙarfin abun hannuna ko?”

“A’a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban”.

“Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karɓi kuɗin nan and am serious”

Ya gyara kwanciyarsa ya ce “Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ƙara mini damuwa”

Sai kuma ta nutsu “Wace irin damuwa kuma?”

“Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki”

Ummi ta ce “Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini”

“A’a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo”

“To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?”.

“In sha Allah, sai da safe” suka yi sallama, ta gyara shimfiɗarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, ƙamshin da yake tashi a jikinta sai nishaɗi take yi.

*
“Anty Rakiya, ai in gaya miki da ƙyar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faɗi wannan sanarwar da ƙyar na yi barci saboda murna, shi ɗan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so”

Rakiya ta ce “Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar ƴaƴan can gaba ta kai ki Bilki”.

Mami ta ce “Can gaba ma, kuma ƙoƙari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na ƙare masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruɗin kuɗi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riƙewa”

Yaya rakiya ta ce “Ke bilki”

“Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma’abocin kula mata bane ba, amma kin san kuɗi, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma”

“Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haɗa shi da Safiyya, ayi ƴar gida kawai”

Mami ta ce “Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuɓe shi da zancen idan har ya amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ƙara sanya ma’aikatan su girmama shi”

Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ƙara ziga mami, da yadda za ta ɓullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haɗa shi da Safiyya, dan ƙarafafa zumunci.

*
Ƙurii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya.

“Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, ƙarshe na rufta kuma kin zo kina dariya”

“To ai kai ɗin ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD” hararta yayi yana kallon wayarsa.

“Attention” tayi maganar tana kallon sa.

Ya juyo yana kallonta shi ma “Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka ne” ya haɗa hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido.

Ummi ta ce “Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan manta da shi ba, ina fatan Allah ya haɗa ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane.
Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuɗi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka riƙe gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka ƙasƙantar da kowa, yayyenka ƙannenka ma’aikatanka da duk wani na ƙarƙshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah.
Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaɗe-kaɗen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu’a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun ƙi.
Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinƙurin mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ƙara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan”

Jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa.

“Ummi wallahi an scared, ba zan iya ba, jagoranci abu ne mai wahala”

“Haba madubina, kai kake ƙoƙarin koya mini jajircewa, kai kuma in ga gazawarka? A’a kar ka watsawa Alhaji ƙasa a ido, zaka iya ka ji”

Yayi shiru bai ce komai ba.

Ta ce “Ka ce to mana”

“Ba zaki gane a yanayin da nake ba ne”.

Ummi ta ce “Eh ba zan gane ba kam, karɓi kuɗinka” tayi maganar tana ajiye masa envelope ɗin da ya saka mata kuɗi a kan tebur.

“Ɗauke tun kan ki fusata ni, na yi miki rashin mutunci a gaban mutane”

Da mamaki ta kalleshi ta ce “Amma raihan idan ka yi mini haka ba ka kyauta mini ba, kuma ba zan ji daɗi ba” tayi maganar muryarta na rawa, dan tuno shi tayi ranar da suka je office ɗin su, da ya burkice sai da ya bata tsoro.

Ya tashi tsaye ya ce “Bari na ƙarasa office, idan na samu kaina zan zo mu tafi gida, idan kuma aiki yayi mini yawa zamu yi waya” ko amsarta bai jira ba, yayi waje ya barta da kuɗin.

Sai da ya fita manager ya ce “Ummi, me aka yi wa mutumin ne na ga yana cika yana batsewa?”

Ummi ta ce “Rigima kawai yake ji”

“Ai nima na ga alama, shiyasa ban kula shi ba”.

Abu kamar wasa, aka yi ta shirin yi wa raihan liyafa, ya so ummi ta je, amma ta ce ba zata ba.
Abokan hulɗar Alhaji Tahir wasu sun ga wautarsa, na bawa raihan jagoranci babban business irin wannan, matashi mai shekaru 23 dan ma yana da siffar kwarjini da girman jiki, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san yaro ne.
Sai dai ko a kalamansa na godiya, da na kama aiki, sun tabattar wa da mutane ƙaraminsu babbansu ne, kamar yadda Alhaji Tahir yake faɗa, wanda wasu maganganun ummi ce ta gaya masa abun da zai ce, dan Alhaji Tahir ya sanar masa ya shirya kalaman da zai faɗa ranar liyafa.

Aka yi taro aka watse, ya turawa ummi hotunan abun da aka yi, ta ɗauki hotonsa guda ɗaya ya sha coat, ƙuruciyarsa ta fito sosai, sai dai ya tsare gida babu fara’a, ta saka shi a status da caption na “Allah ya tayaka riƙo ƙanina, MD Muhammad Raihan”

Ta kai awanni biyu da yin status ɗin, da ta buɗe what’s app ta tarar da saƙonni, na tambayar waye shi, ciki har da yaya magaji, babban wanda ya fi bata mamaki shi ne message ɗin maryam, tun da raihan ya haɗa su, suka yi magana maryam ba ta sake kulata ba, idan ta yi mata magana ma, sai ta ga tana shareta, dan haka ita ma ta daina kulata, sai yanzu taga message ɗin ta, wai ya aka yi ki ka sani?.

Ummi ta yi mata reply da “Shi ya gaya mini”.

Maryam ta ce “A ina ku ka haɗu ya gaya miki?”

“Muna gaisawa idan zai wuce ta wurin da muke aiki ne”.

Ta yi reply da “Dan Allah ki cire shi, ba kowa ya sani ba, kar azo hakan ya bashi matsala” Ummi ta daɗe tana jujjuya message ɗin, ita mutum nawa ne ma a what’s app ɗin nata. Ta ga ita kanta maryam ɗin, ta saka hotunan sun fi goma, kodayeke wata kusan ta fi wata, dan haka ummi ta goge.

Tamkar jira yake ta goge, ya ce “Meyasa ki ka goge status ɗinki?”

“Bakomai”.

“Akwai dalili mana, saboda Maryam ko?”.

Abun ya bata mamaki, kan ta yi magana ya sake turo wani saƙon ya ce “Muna tare take nuna wa mami status ɗin naki ai, ita take saka miki data da zata ce ki cire abu kuma ki cire? Ina ruwanta, ko haifarki tayi da zata bani umarni ki bi? Akwai mutane a wurin ne ya san na ƙyale maganar, ƙarewa gobe in Allah ya kaimu hira za ayi da ni a wani gidan jarida. Dan Allah ki daina bari ana raina mini ke bana so”

Karanta saƙon nasa ta din ga yi, tana ƙoƙarin bawa saƙon damar yin tasiri a zuciyarta, amma ta kasa.

“Dan Allah ki sake duba wani hoton, ki ɗora ni ki yi mini addu’a, tun da ba ki je taron ba Please”.

“Yanzu ka gama cewa a daina sani abu in yi, ai ba kai ka saka mini data ba” ta tura masa tana dariya.

Emojin dariya ya tura mata ya ce “Ta kaina zaki fara kenan? Ni ki ka raina ko?”

“Kai ka mayar da ni haka ai, ina salihata ka koya mini surutu”.

“Dama can kin iya abinki”

“To na ji, sai da safe bacci nake ji”

” ya kaimu” ya rufe data ya ajiye wayar, ya lumshe ido yana tuno moments ɗin su tare, ba zaka taɓa cewa ummi na magana ba, dama ce kawai ba ta samu ba, amma tana da baki sosai”.

*
Alhaji Tahir kallon mami yake yi, bayan ta gama kora masa bayanin abun da take so.

Ta kalleshi ta ce “Wai ya ka yi shiru kana kallona ne?”

“To ai abun ne na ji shi banbarakwai, guda nawa raihan ɗin nawa yake zaki ce ayi masa aure yanzu? Daga ɗora masa wannan ɗawainiyar sai kuma ki ce ayi masa aure?”.

“To ai shine cikar kamalarsa, ya samu matsayi ya zamana yana da iyali, dole zai nutsu ya mayar da hankalinsa, ko so ka ke na saki jiki shima ya lalace? Ni dai dan Allah ka taimaka ka amince”

Alhaji ya ce “Ai ni bani da damuwa, in dai ya amince yana so shikenan, Allah ya sanya alkhairi”

“Yauwwa, dan Allah ka tayani shawo kansa, ka san ko budurwa ba shi da ita, ko zancen na yi masa sai ya sha kunu, dan Allah ka tayani lallaɓa shi, ko da Safiyyar Anty rakiya a haɗa shi”

Ya kashingiɗa ya ce “Wannan ba hurumina bane, kin san takura wa ɗa ba ya cikin tsarina, ku tattauna kawai”

Tayi ajiyar zuciya ta jinjina kai.

Mami ta din ga fargabar tunkarar raihan da maganar, haka nan ta dake da safe ya shiga gaisheta zai fita office, ta ɗaukko masa zancen, aikuwa ya haɗe rai, ya ce “Dan mami ki daina wannan zancen, abokaina kowa ba wanda yayi aure sai ni, kawai na tsufa da wuri, kuma matar ma ki rasa wa zaki zaɓar mini sai wannan marar kunyar, ni ba zan auri matar da ba zan iya tanƙwarata ba, yarinyar da bata da kunya, ni bana so”.

“Raihan, cikar kamalar mutum iyali, ace kana da wannan matsayin baka da aure, ai sai a rainaka, kuma ganin kai baka da ko budurwa ya sanya na zaɓa maka, aure yana ƙarawa mutum kamala”

Ya ce “To mami na ji, amma dan Allah ki ƙyaleni, idan lokaci yayi zan yi miki magana zan yi auren, amma ni yanzu wallahi ban yi niyyar yin auren ba, kuma da kaina zan samo budurwa da zan aura, ummi ta ce in nutsu in samo mace ta gari”.

Cikin mamaki mami ta ce “Wacece ummi kuma?”

Ya miƙe tsaye ya ce “Kar ki damu mami, ni dai ki bar wannan maganar”

“Wallahi ba zan barta ba, dole ka yi aure dan ba zan zuba ido ka lalace a banza ba, ko wata ta lallaɓa ta lalataka ba, wato ni nake yi maka kallon salihi, har mai baka shawara ce da kai a waje?”.

“You should thank God, shawarar kirki take bani, ita ta saita ni a hanyar da na ci jarrabawar Alhaji” daga haka ya fice ya bar falon.

Abu kamar wasa, raihan har ba ya son shiga sashin mami, dan ta fara hura masa wuta, shi ko zancen ba ya so.

Yanzu Ummi haɗuwa da raihan yana bata wahala, saboda yadda aiki ya saka shi a gaba, ba shi da cikakken lokacin kansa.
Yau ya kirata a waya ya ce mata zasu fita, zai zo ya ɗau excuse a wurin manager.

Da azahar ya zo ya sameta, lokacin ta gama aiki, tana ta tsokanarsa MD, yayi mata shiru yana hararta.

Ta bashi wayarta ta ce “Raihan, dan Allah ka buɗe mini Instagram”

“Me zaki yi da shi?”

Ta ce “Kallon abubuwa zan din ga yi”

“Wai wannan wayar taki, da ke da ita waye ya girmi wani? kalli yadda ta ci ƙaniyarta”

“To sai ka bani taka ai” tayi maganar tana hararsa.

Ya ce “Kin samu, ciro mini layukana ki ɗauka”

“Ni da wasa nake yi, ka buɗe mini dan Allah na kasa buɗewa”.

Raihan ya ce “Ke Instagram ba zai hau wannan dattijuwar wayar taki ba, ai na ce ki ɗau tawa, ba abun da zaki ce na baki na hanaki”

“Da wasa nake yi maka, ka buɗe mini” tayi maganar tana miƙa masa wayar tana ɓata fuska kamar ƴar yaye.

“Da gaske na bar miki wayata ummi, kawo wayar taki mu yi exchange na layukan”.

“So kake ace na fara sata ko? Me nake sayarwa da zan mallaki wannan wayar?”

Ya ce “Sai ki ce ke ƙawar MD ce”

“A’a nice ma MDn, tun da ba zaka buɗe mini ba shikenan” ya karɓi wayar ta ta yana dubawa, ya ce.

“Tashi muje mu dawo da wuri”

“Ina zamu je?”

“Budurwata zan sai wa wasu kaya, mu je ki tayani saya, za ta yi ki a jiki, bana son na sai mata wanda zai yi mata yawa”.

Ta harare shi ta ce “Kuma saboda ka raina ni, da ni zaka gwada? Daga baka muƙami ka fara kule-kule, guda nawa ka ke da ka fara yin ƴan mata” wani irin kallo yayi mata, tayi shiru, ta zata maganar da tayi ne, ta ɓata masa rai.

Shi kuwa hoton da ya gani ne ya bashi mamaki, hotonta da noor, gashin kanta kamar aljana.

Sai dai yayi tunanin ko sakawa tayi, amma ina ummi take da wata wayewar saka gashi.

“Tashi mu je” ta tashi tabi bayansa, a ranta tana fatan Allah ya sa ba haushi ya ji ba.

Ita kanta mamakin kanta take yi, yadda take bin raihan duk in da ya ce suje, ba tare da musu ba, yanzu ta daina fargabar shiga motarsa, kodayeke zuciya na son mai kyautata mata, kuma bai taɓa yi mata wani abu na rashin ɗa’a ba.

Suna tafe a motar, ta ciro leda a jakarta ta ce “Gashi, dama ina ta jira mu haɗu, kuma saura ka ce baka so, sai ka je gida zaka duba”

Ya amsa mata da “To babbar yaya”

Wani ƙaton shagon sayar da kayan sawa suka je, suka shiga raihan suka gaisa da matar da ke shagon.

Ya nuna mata ummi ya ce “Yauwwa hajjaju, ban san size ɗin da take sakawa ba, amma ga wata mun zo tare da ita, ki bata ta gwada, idan dai ta yi mata dai-dai, ita ma za ta yi mata.

Matar ta ce “Masha Allah, bisimillah, muje to ka zaɓa sai ta gwada”.

Tarin abaya ne a wurin da suka je, kala-kala na kece raini.

Ya kalli ummi ya ce “Zaɓo ɗaya wadda za ta yi mata kyau sosai”.

“To ai ban san ya take ba, ko wanda ta fi so ba, fara ce ko baƙa?”

“Ina ruwanki da kalarta? to black beauty ce”

Ta tsaya ta kalleshi ta riƙe ƙugu ta ce “Daga baka office, ka fara kashewa ƴan mata kuɗi ko? Alhaji ya sani?”

Raihan shima ya riƙe ƙugu ya ce “Yau nake ganin ikon Allah, ke ina ruwanki ne? Wai ce miki aka yi ɗan zaman banza ne ni? Ɗauki muje akwai in da zamu je”.

Wata blueblack ta ɗaukko mai matuƙar kyau, matar ta nunawa ummi in da zata shiga ta gwada rigar.

Tsayawa ta yi a gaban mudubin ɗakin, tana ƙarewa kanta kallo sanye da rigar, yau dai sau ɗaya a tarihin rayuwarta, ta saka doguwar rigar abaya da take matuƙar burgeta.

Ta riƙe ɗan kwalin rigar a hannunta, ta zubawa mudubin ido, ta tafi tunani, ta zubawa mudubin ido, tana hango rayuwarta ta baya a ciki, cike da tozarci da ƙasƙanci, da rashin galihu kamar mara amfani, shigowar raihan rayuwarta ya bata lokacinsa, duk hankalinsa saboda kawai ya sakaya farinciki. A ranta take addu’a ‘Allah idan ina da rabon yin aure a duniya, Allah ka kawo mini miji na yi aure, kar na yi aure na kasa rabuwa da raihan’ saboda sosai take jin sa a jikinta.

Ummi bata san adadin daɗewar da ta yi a tsaye ba, saboda gaba ɗaya ta bar cikin hayyacinta.

Raihan gajiya yayi da zaman jiran ummi, kawai ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin amma shiru, kawai ya tura ƙofar da sallama.

Kamar gunki ya ganta a tsaye hannunta riƙe da ɗan kwalin rigar, hawaye ya wanke mata fuska.

Sandarewa yayi a tsaye, ta saka siririn ribbon ta ɗaure gashin, ta sake shi har tsakiyar bayanta.

Ganin raihan ta cikin mudubi daf da ita ne, ya sanya ta dawo hayyacinta a razane, kokowar rufe kanta ta fara yi.

A hankali ya saka hannu ya ɗaure zaren rigar ta baya.

Ya saka hannu ya kamo gashin da ya sauka a bayanta, tsigar jikinta ce ta tashi, ta waiwayo da sauri, ƙare mata kallo yake yi. Rigar ta yi cif a jikinta, dirarriyar mace ce ta gaske, baƙar fatarta kawai mutane suke kallo, amma daga ƙirjinta zuwa ƙugunta komai dai-dai jikinta, kasa daina kallonta yayi, karo na farko kuma da yau ta kalli raihan a wani abu daban ba ƙaninta da take yawan faɗa ba.

(Team a bamu daga farko, ku yi Allah ku din ga dubawa a watpad Please 🙏)

Ayshercool

CUTARWA!

P28

28

Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannunsa a aljihunsa, ya ciro wayarsa.

Ya shammaceta ya fara ɗaukar ta hoto ta cikin mudubi.

Haɗe rai ta yi ta ce “Meyasa zaka shigo mini ba izini? Ni ka fita”

“Na yi knocking, na kuma yi sallama, duk baki amsa ba, kin bar ni a tsaye ina ta jiranki, kin shigo kina kuka, idan ma dan in bar miki rigir ne ki ke kuka, ba zan baki ba, fito mu tafi”

Ba tare da ta saki fuska ba, ta ce “Ni ka fita na cire rigar”

Ya basar ya ce “Ki batta a jikinki, ki zo mu tafi”.

“Dan Allah ka fita na cire” tayi maganar a raunane tana ɓoye jikinta.

A hankali ya taka ya nufi hanyar fita, ya sake waiwayo wa, tana tsaye jiran ya fita ta canza kayan.

Ya fita ya koma reception.

Ba ƙaramar kunya ce ta kama ta ba, ganin da yayi mata a haka, gashi dai doguwar riga ce, amma ta kasa manta irin kallon da yayi mata, da ya sanya ta shiga wani yanayi da ba ta san menene ba, gaba ɗaya sai ya canza mata, kamar ba raihan ɗin da ta sani ba.

Ta mayar da hijjabinta, ta fito da rigar a hannunta, matar ta kallesu ta ce “Rigar ta yi?”

Ya ce “Eh, bamu wasu kalolin a haɗa da wannan, su zama biyar sai takalmi uku da zai shiga da kowacce” komai da ummi aka gwada, kuma ba ta kawo komai a ranta ba.

Ɗan nazarinta ya din ga yi, ko fushi take yi da shi, amma ya lura kawai ta tsorata ne, ta kasa sakin jiki ma tayi masa magana, dan abu ne mawuyaci ka ga ummi ta yi fushi, dan zai iya cewa bai taɓa ganin tayi ba, idan ma abu bai yi mata daɗi ba, sai dai ta yi shiru.

Suna tafe a hanya ya cigaba da yi mata hira, kamar bai ga komai ba, yana koɗa kyan da kayan suka yi.

Sai dai gaba ɗaya shima jikinsa yayi sanyi, basarwa kawai yake yi.

Wani restaurant suka je, yayi reserving VIP, aka kawo musu abinci kala-kala, amma ummi ta ce ba za ta ci ba, ya gama kawai su tafi ita hankalinta yayi gida.

“Amma mussman saboda baki je walimar nan ba na shirya mana wannan”

“Sai ka ce wani film, ni ka yi sauri mu tafi, kar na je gida na kasa kare kaina”.

“Da na san zaki watsa mini ƙasa a ido, da ban kashe kuɗina ba, i did all this because of you”

Ta ɗan kalleshi ta ce “Ni ban taɓa cin abinci a waje ba, dan Allah ka yi haƙuri”

Raihan ya ce “Zan fita na baki wuri ki ci, amma idan ki ka yi mini haka ba zan ji daɗi ba”.

Ƙarshe dan kar ya ji haushi, da ƙyar ta cakala ta ci, suka tafi gida.

A hanya yake ta ce mata tayi ƙoƙarin rarraba CV ɗin ta, ko Allah zai sanya ta samu wani aikin da ya fi wanda take yi.
Ta ce masa zata jarraba yin hakan.

Raihan ya dage sai ya mayar da ummi ƴar gayu, ta hanyar kaita wurare da zasu ɗebe mata kewa, ba tare da ƙetare iyakar addini ba.

A ɗan fitar nan da ummi suke yi, take ganin mata kala-kala, masu dressing kala-kala, ba ta sani ba ko rashin shiga cikin mutane ne ya sanya ita duk ba ta iya wannan abubuwan ba, hatta ɗaurin ɗan kwalin da ta kan gani a kan mata yana burgeta, amma ita ba yi take yi ba, daga aikin gida sai makaranta ba ta da wani hope balle tayi tunanin wata kwalliya.

Da Raihan yaje gida ya duba ledar da ummi ta bashi, sabon agogo ne kar, da links sai littafin azkar babba, da carbi counter.

Ta yi rubutu kamar haka “Allah ya taya riƙo mai girma MD, wannan ce gudunmuwata, ban san me kake buƙata ba, amma ina fatan ba zaka raina kyautar yayarka ba, Ummi”

Ya yi murmushi a hankali ya ce ‘Kin rama kenan, a taƙaice kin dawo mini da kuɗina’

Ya kirata a waya, sai dai wayar a kashe.

Ya kashingiɗa yana tuno ummin, mussaman ɗazu da ta saka doguwar rigar abaya, tayi wani irin kwwarjini da kyau, daga cikin abun da ya ɗau hankalinsa dogon gashin ta har tsakiyar bayanta, ya fara tunanin anya ummi ba ta haɗa dangi da wani ahali na yankin ƙasashen ƙetare ba? Idonta da gashinta, sun nuna hakan.

“You are beautiful fa ummi” ya faɗa a fili ba tare da ya shirya yin hakan ba.

Dubu talatin ɗin nan da ya bata, dubu biyu ce tayi saura, dan sai da ta saya wa kawunta turare, ta saya wa Abdul, sai ƴar ɗakinta wato noor, har da su farida, amma kausar ta yatsuna fuska ta ce Allah ya kiyaye ta shafa wannan abun kamar ƴar bori, suka bar ta da abun ta.

Duk da abun da suka yi mata, ummi ta ji daɗin murna da addu’a da dr. Yayi mata, hakazalika Abdul ma yayi mata addu’a sosai, mutuniyarta kuwa kasa zama wuri ɗaya tayi, dan ƴar tsana ta saya mata.

Ummi ta yi mamakin yadda aka yi kuɗin ma suka isheta, ba ta taɓa tunanin haka yi wa mutum kyauta yake da daɗi ba, ayi ta yi maka addu’a.

Kwanaki biyu da fitar su ita da raihan, tana ɗakinta tana tilawa Abdul yayi sallama, ta kaste karatun tare da amsa masa.
Ya miƙa mata ledar hannunsa, ta karɓa tana kallonsa bakinta fal tambaya.
Kan tayi masa tambayar ya ce “Wani guy ne muka haɗu a waje ya ce na baki, wani ɗan dogo mai haske” gaban ummi ya faɗi, ta san ba wani bane face raihan.
Abdul bai sake yi mata wani bayanin ba, ya fita daga ɗakin.
Jikinta na rawa ta hau duba kayan, dogwayen riguna nan ne da suka sayo, har takalman da komai.

Da sauri ta tashi ta leƙa ƙofar ɗakin, ta tabattar babu kowa, me raihan yake nufi ne? Wannan kayan idan aka tanbayeta ta ce a ina ta samu?

Layinsa ta fara kira, ya ɗaga a nutsensa tare da amsa sallamar da tayi masa.

“Raihan, shine ka bawa Yaya Abdul wannan kayan ya kawo mini, idan aka tuhume ni a ina na samu me zance? Kar ka janyo mini matsala fa”

“Kar ki ji komai ki ce ni na saya miki, saboda na fuskanci kina so, budurwa ce ke ba tsohuwa ba, dan haka mace sai da kwalliya, ni ina da yayye da ƙanne mata, duk in da mace take tana buƙatar kulawa, a kan buƙatunta na yau da kullum, kar ki ji komai yayata, ki yi kwalliyarki dai-dai da addinin musulunci, Allah ya kawo mana abokin rayuwa na gari” maganar sa ta ƙarshe, da yayi addu’ar sai ya ji wani abu mara daɗi a ƙasan zuciyarsa.

Ya kashe wayarsa, ummi ta bi kayan da kallo, ina ma zata iya amfani da kayan nan, ta tashi ta kulle ƙofar ɗakin, ta ɗauki kayan tana gwadawa ɗaya bayan ɗaya, karo na farko da ta ɗauki jambakin da yasa mata wancan karon, ta ƙara tisa shi a kan jajayen laɓɓanta, ta saka kwalli a idonta.

Ta ƙurawa kanta ido a gaban mudubin, ta din ga juyi a tsakiyar ɗakin, wai yau ita ce ta saka wannan kayan masu tsada, ta kalli takalmin ƙafarta mai tsini, ta din ga kaiwa tana komowa a ɗakin.

“Allah ya ƙaro maka arziki mara yankewa, ya yalwata maka duniya da lahira” hakanan ta ji ina ma ya ga kayan a jikinta, har da janbaki ta saka yau, abun da yake so ya mayar da ita ƴar gayu.

*

Gaba ɗaya farida ta kasa sukuni, tun da mijin inteesar ya ce zai ƙara aure, suke yawon neman asiri, amma babu abun da ya sauya, ga azabar takura daga dangin miji, da gori na cewa ita juya ce.
Da ya ce kan ya ƙara auren zai canza mata gida da furnitures, amma babarsa ta ce bata yadda ba, da wanne zai ji, kuɗin da zai kashe yayi wani auren, ko kuma wanda zai kashewa juya, da ma tana haihuwa ne da sauƙi.
Gefe ga kausar dr. Ya ƙara hura mata wuta, a kan lallai ko tayi karatu, ko sai ta fitar da miji.
Farida kuma ta yi alwashin, sai ummi ta koma ƙauye ta bar mata gida, ko kuma ta fitar da miji itama, dan ba zai yiwu ya takura wa ƴar ta ita kaɗai ba.

Ga noor wani irin rashin ji take yi, ba ta shakkar farida ko kaɗan, tsagera ce ta gaske, ummi ce kawai sai dr. Suke iya tanƙwarata, dan ko Abdul sai ta ga dama take jin maganar sa, dan ta ce faridan ba ta sonta, su inteesar kawai take so, ita kanta ummi tsagerancin da noor take yi da ƙanan shekarun nan, yana bata tsoro, amma babu yadda ta iya, tana yi mata addu’a, tare da yi mata fatan shiriya.

Gashi farida ta ɗora laifin hakan a kan ummi, wai ita take zigata, take hurewa ƴar ta kunne.

Kamar a baya da duk abun da za ayi ummin ba magana take yi ba, haka yanzun ma, ba wani abun take cewa ba, duk abun da za ayi sai dai tayi shiru.

Babban abun da ya ɗaga mata hankali, bai wuce kawu Yahaya da ya je gagarawa, ya dawo da katin bikin Yaya magaji ba, kuma ya tabbatar mata da ita za su je bikin nan, kuma a yadda yayi maganar umarni ne kawai ba wai neman yardarta ba.

Ta amsa masa da to, amma ƙasan zuciyarta wani irin lugude take yi da fargaba, da fatan Allah yasa ba da sun je za a baro ta a can ba, dan kuwa farida ta ƙara matsa lamba sosai da sosai, ta addabi ummi da gorin rashin aure da kuma ƙara tabattar mata da barin gidan.

Gefe guda kuma, abokin shawarar ta ta, ya zama very busy, wataran sai su wuni ma basu yi waya ba, ga tafiye-tafiye da suka sako shi a gaba, saboda importing na kayansu, nan da nan kuwa ya fara rama, duk ranar da zai dawo gari, sai ya yi wa ummi waya tayi masa abinci, ya aika a karɓo masa ba zai ci na gida ba.

Alhaji Tahir ya sha suka da caccaka, a kan yadda ya ɗauki ragamar babban kasuwanci kamar wannan, ya danƙawa raiha, a matsayinsa na ƙaramin yaro, Alhaji Tahir ya toshe kunnensa, dan kuwa bai ji zai canza ra’ayi ba.

Abunka da mata da miji, mami tayi ta lallaɓa Alhaji, har ya amince da maganarta a kan raihan yayi aure, amma ya ce ba ruwansa da zaɓa wa raihan ɗin matar aure, balle auren  yaƙi daɗi ace laifinsa ne.

Shima Alhajin yayi iya ƙoƙarin sa wurin fahimtar da raihan muhimmancin ace yana da iyali yanzu, tun da ya samu matsayi.

Raihan ya ce “Wai Alhaji da wanne zan ji?, tsufa zan yi da wuri, ka manta nauyin da ka ɗora mini?”

Alhaji ya ce “Ni meyasa ban tsufa da wurin ba?akwai riba a cikin yin aure da wurin babban mutum, aure ba takura bane ba, kwanciyar hankali ne da nutsuwar zuciya ka yi tunani a kai”.

Raihan ya ce “To Alhaji zan yi, zan yi shawara da hajiya”

Alhaji ya ce “Ba maminka ba?”.

“A’a Hajiya”

“Ɗan gidan Hajiya, ni ba zan bayar da shawara ba sai Hajiya kenan? Ai shikenan babban mutum”.

Gidansu ummi kuwa yau gaba ɗaya jikinta babu daɗi, ta gaji sosai da sosai, dan farida baƙi tayi, kan ummi sai ciwo yake yi, kamar za ta yi zazzaɓi da ƙyar ta lallaɓa ta yi aikace-aikace.

Sai da ta jera kwana biyu ba ta zuwa aiki, ta sanarwa manager ba ta da lafiya ne, haka islamiyya ma, kwana biyu zazzaɓi ya sakata a gaba da matsanancin ciwon kai da na ciki.

Dama Ummi ba ta saka ran wani ya bata kulawa ba, ita da noor kawai suke jinyar, noor ta yi wanke-wanke da abun da zata iya, a daddafe ummi take aikin gidan, farida ta lura da hakan, amma ko a jikinta dama da dr. Yana nan ne ya fuskanta zai kaita asibiti.

Raihan kuma ba sa iya waya, sai ta what’s app, dan kuwa baya ƙasar gaba ɗaya, dan haka bai san halin da take ciki ba.

Tun ƙarfe shida ummi ta ga farida sun  ɗauki mota da ita da kausar sun fice, Abdul kuwa aiki yaƙi samuwa, dan haka a wani kamfanin sarrafa taki, dr. Ya samar masa aiki, shima farida ta din ga kushewa, da nuna ɗanta ya fi ƙarfin wannan, amma Abdul ya ce yana so zai yi.

Ganin da noor tayi ummi babu lafiya sosai, ya sanya ta karya da buredi ta tafi tahfeez, ummi ta din ga burgima a ɗakin ta, ga amai kuma cikin ta babu komai.

Wayarta tayi vibrating ya fi sau shida, da ƙyar ta ɗaga ta yi sallama.

“Baccin safe ki ke yau kenan, ko islamiyyar baki je ba? Na shigo gari jiya da daddare, abincinki nake son ci, kuma in ganki”.

Cikin ƙarfin hali ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri, bana jin daɗi amma zuwa yamma in sha Allah idan na gama zan kira ka”.

Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba ya ce “Ummi kamar fa haki ki ke yi, kina Asibiti ne?”.

“A’a ina gida ne, zan warware in sha Allah” tayi maganar da ƙyar kanta na sarawa.

“Bani 20minutes gani nan” kan ta sake magana ya kaste kiran, ya fita da sauri.

Ummi ba ta sake sanin in da kanta yake ba ma, sai da ta ji ana buga ƙofar ɗakinta.

A hankali ta ce “Waye?”.

“Mai gadi ne, kin yi baƙo ne, yana sallama”

Ummi ta ce “To” maimakon ta tashi, sai ta cigaba da bacci na rashin lafiya, a ƙalla maigadin ya zo sau uku, kan ta iya fitowa.

Hankalin raihan ba ƙaramin tashi yayi ba, da ya ga ummi, idanuwanta duk sun yi waje.
Tana ƙarasawa ta nemi wuri zata zauna a ƙasa, ya hanata hakan ya saka ta shiga motar.
Tun da ya ja motar yake faɗa a kan wasa da lafiyarta, oho ba ta ma san takamaiman zahiri ne ko mafarki ba saboda zafin zazzaɓi.

Ba a samo kan ummi ba, sai bayan ta sha ruwa roba biyu, sai dai a halin da take ciki, hankalinta yana gida, kar wani ya dawo a tarar ba ta yi girkin rana ba.

Likita ya din ga yi mata tambayoyi cikin harshen Ingilishi, dan ba ya jin hausa, da ƙyar take iya amsawa saboda ciwo, kuma hankalinta yayi gida.

Ya ce “Akwai ciki ne?” Sai da ummi ta kalli likitan, amma ta kasa magana.

Raihan ya ce “Babu”.

“Ka tabattar? When last ta yi period?”

Maimakon raihan ya ce ba ta da aure, sai ya kalleta ya ce “Yana tambayar ki”.

Likitan ya ce “Kai baka sani ba ne? Are you not couples? Na ji ka ce babu ciki”

Raihan ya wani gyara tsayuwa ya ce “Ai da yake bana gari, shiyasa ban riƙe ba, ummi ki gaya masa” ta sunkuyar da kai ta yi shiru, kamar ta buɗe ido ta ga ta ɓace, raihan ya gama da ita gaba ɗaya.

Raihan ya ce “She can’t recall, but she’s not pregnant”

Aka yi wa ummi teses, malaria da typhoid sun yi mata mummunan kamu.

Likita ya ce a bari ta kwana ɗaya a asibitin, ummi ta ce ba ta san zance ba, ta sha faɗa a wurin raihan kan rashin kula da lafiyar ta, tare da yi mata kashedin saura ta je gidan a sakata aiki tayi. Ji yake tamkar ya samu wani kauwamammen wuri, ya ajiye ummi ya din ga kula da ita, kulawa ta musamman.

Ta so ace zata iya abun da raihan ya ce, taƙi yin aikin gidan, dan a galabaice take, amma da cin mutuncin da za ayi mata, gara aikin gidan.

Tayi ta yi wa Allah godiya, har suka dawo bayan azahar su farida ba su dawo ba, dama noor sai la’asar zata dawo.

Haka ta lallaɓa take aikin, lokaci-lokaci sai raihan ya kira ummi, ya tambaye ta ya take ji a jikinta, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa hankalinsa ya ƙi kwanciya, dan babban fatansa ace a kwance take ko ruwa za ta sha, a ɗaukko a bata.

Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern makarantar islamiyyar su ya zo dubata ba, har da kawo kayan dubiya, headmaster yana daga cikin mutanen da su kan hantari ummi, mussman idan ta je a makare, gashi ita kuɗin makaranta take biya, wurin ɗaukar nata karatun, ita kuma koyarwar da take yi, ko sisi basa bata, dan raihan har mita yake yi, a kan hakan ya ce yakamata ko ba yawa a din ga biyanta.

Amma ga mamakinta sai ga headmastern ya zo dubata, ba ta kawo komai a ranta ba, tayi masa godiya ya tafi.

Saboda rigimar raihan, ummi ta lallaɓa ta koma aiki, dan kuwa idan ba ta yi wasa ba, a sintirin da yake yi, sai an san da alaƙarsu, alaƙar da ba ta san ta yaya za ta yi bayaninta ba.

Har wurin aikin yake bin ta, ya tabbattar ta ci abinci ta sha magani.

Ta sanar masa da batun zuwa gagarawa, da yadda take cikin damuwar hakan, kar idan ta je a riƙeta a can.

Raihan ya ce “Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru sai ikon Allah, kuma babu wanda zai rabaki da garin nan, abun da nake so da ke, ki yi iya ƙoƙarinki ki sake samo information a kan mama idan kin je, zan san ƙoƙarin da zan yi a kan hakan, da wallahi suka riƙe ki a garin nan, ba abun da zai hana ni binki”

Ɗan buɗe baki ta yi tana kallon sa, da gaske har cikin zuciyarsa yayi maganar.

“Raihan wai ranar da na yi aure, yaya zaka yi ne?”

“Yaya zamu yi dai? A ƴan uwanmu zan samo miki miji nagari, ni kin san kuwa mami ta sakani a gaba, wai tun da Alhaji ya bani ragamar kasuwancin nan, wai sai na yi aure”

Ummi tayi dariya ta ce “Daɗina da mami hangen nesa, wallahi kuma da gaskiyarta”

Ya girgiza kai ya ce “Ba zaki gane bane yanzu haka kawai ganina ki ke yi, bana son yawan takura miki, amma sai kin tayani da addu’a, akwai ƙalubale sosai a harkar kasuwancin nan, kuma kamar yadda ki ka faɗa, akwai buƙatar yadda ki ka gaya mini, ina buƙatar mace ta gari to assist me, wallahi ummi ban taɓa budurwa ba, kuma bana son auren haɗi, ni ba zan auri matar da bana so ba”

Ummi ta yi dariya ta ce “Za a sha ƙiriniya, amaryar ka za ta sha fama da ƙuruciya”

Kallonta yayi ya ce “Kin rainani da yawa fa, idan na fita kin ga yadda nake tsare gida kuwa a waje, a man of 24yrs, ki ke cewa za a sha ƙuruciya”

Ummi ta waro masa idanunta ta ce “24 kuma, ka ji tsoron Allah raihan, yaushe ka kai 24yrs kuma?”

Ya ce “Wallahi na cika 24yrs”

Da suka yi lissafi, watanni goma sha huɗu ummi ta bashi.

Ya ce “Da na san ba wani girmata ki ka yi ba, ba zan bari ki raina ni ba, ashe ma sa’ata ce na ma fa fiki girma ummi, daga yanzu ma ni ne yayanki yaya zaki din ga ce mini”

Ummi ta ce “To meye a ciki Han? Ai duk in da namiji yake jagora ne, mai girma MD, sai dai ba a canzawa tuwo suna, ni yayarka ce”

Yayi dariya yana shafa sajensa, ya na bin ta da kallo, ya kasa gane a wane bugire ma ya ajiye ummin ne a yanzu.

“Me ka ke kallo ne?”

“Your eyes, masha Allah i like them, ina son idanunki”

Ummi ta rausayar da kai ta ce “Idan ka faɗi haka kana tuna mini da babana, idan na ce masa baba wai idona irin na akuya ne da mage? Sai ya ce A’a, idonki mai kyau ne, ina son idonki ummina”

Raihan ya ce “Allah sarki, Allah ya jiƙan baba da rahama”

“Amin Yaya Han, ina godiya sosai da sosai”

Yayi murmushi ya ce “Han sai ka ce sunan ƴan china, amma duk yadda ki ka faɗa zan amsa, ki kula da kanki sosai a garin idan kin je, zamu din ga waya har ku dawo”

Ummi ta ce “To, in sha Allah”

Ummi na son nunawa raihan hotunan da ta yi da rigunan nan a wayarta, amma ta kasa, shi kuma bai takurata da tambayar bai taɓa ganin ta saka kayan da ya bata ba.

Ummi ta lura kamar babu jituwa tsakanin dr. Da farida tun wancan karon da ya koma aiki, har wannan dawowar tasa, sai dai kasancewar ummi ba huruminta bane ba, ya sanya ta cigaba da sabgoginta.

Ranar tafiyarsu gagarawa na ƙaratowa, adadin tashin hankalinta, da fargaba na ƙaruwa, sai dai ta na ta addu’a a kan Allah ya kare faruwar dukkan wani abun ƙi.

Ta ɗauki ɗaya daga cikin dogwayen rigunan wurin raihan, da abun da ba a rasa ba, ta haɗa kayan da zata yi tafiyar da su.

Dr. Ya ce har da noor zasu tafi, noor ta din ga murna, tana jin daɗi.

Suna tafe a hanya, adadin fargaba da tashin hankalinta, yana ƙaruwa, tana tuna irin azabar da ta sha a gagarawa, ta din ga fatan ina ma har ta je ta dawo, ba zata haɗu da wasu mutanen ba, dan ko ambatar sunansu na sanyata cikin damuwa.

Kwantsin yaran gidan ne suka firfito, suna shelar ga kawu Yahaya ya zo, yaran da galibi duk ba ta san su ba, dan da yawansu bayan ta baro garin aka haife su.

Kallon gidan ummi take, zata iya cewa wannan gidan shi ne kurku mafi azaba a tarihin rayuwarta.

Da yawa yaran basu san ummi ba, dan haka suka din ga bin ta da kallo.

A tsakar gida sashen iya, mata nata hada-hadar shirin biki, sallamarta ce ta janyo hankalin matan.

Wanda suka santa, suka din ga zuzuta girman da tayi, ta ɗaga kai ta kalli ɗakinsu, ɗakin mai ɗauke da ɗumbin tarihi, alamu ya nuna akwai mutane a ɗakin, amma ba ta san suwaye a ɗakin ba.

Ɗakin Iya ta nufa, ta tarar da Iya zaune a tsakar ɗakin ta, tana ta bayar da umarni.

Saroro ta bi ummi da kallo, cikin ƙarfin hali ummi tayi murmushi tana gaida Iya.

“Yau Allah ya kawo ki wurin mayu kenan, wanda za su cinyeki?” Ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kai.

Noor dai ta kame tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.

Dr. Ya shigo shima yana ta gaisawa da mutane, da ya isa ɗakin iya, ko gaisawa ba su yi ba, ta fara masifar ya bar ummi ta balage ba aure, kodayeke dama ya za ayi ta auru, ai dama tun da tun farko taƙi amincewa da rufin asirin aure, ya goya mata baya, haka zata riƙe a gida ba aure.

Aikuwa kawu yahaya ya haɗe rai ya ce “Iya dan Allah ya isa haka, haba ummin guda nawa take? Ke ba ki yi farincikin ganinta tayi ilimi, a nutse a kame ba, ni na zaci wannan abubuwan duk sun wuce tun a baya?”.

Ummi ta sha mamakin yadda Iya ba ta canza ba, tsawon wannan lokacin.

Tun a daren yaya magaji ya zo wurin ummi, sun daɗe suna hira, tare da murnar ganin sauyin da ummi ta samu, ya din ga gaya mata irin yadda abubuwa suke ta kwaɓewa a cikin dangin nasu.

Abubuwan duk babu daɗin ji, mussaman gidan Idris, yarinyar su ta gaba da alfatiha, ƙalubalen da take fuskanta ya sanya ta fara fanɗarewa ita ma.

Al’amarin bai yi wa ummi daɗi ba, wanda jahilci ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanen gidan.

Washegari ɗaurin aure, bayan ummi da noor sun yi wanka sun shirya, ta ja noor suka fita gidansu na’ima, amma ta tarar maman na’ima ta rasu, ƙannenta duk sun yi aure.

Doguwar riga ummi ta saka ta wurin raihan, sai dai tana jin ta kamar ba ita ba, saboda jin ta take a takure a cikin kayan, dan ma rigar isashiya ce, sai dai fa ta zama a bar kallo a cikin gidan, duk in da tabi sai a kalleta.

Iya ta din ga nuna wa mutane ummi, ga ƴar wurin bashir, da Idiris ya aura taƙi zama, ta bi kawu yahaya gashi haryanzu ta gama balagewa ta riƙa ba aure shi yanzu yana da yara biyar.

Idiris kuwa tun da ya ga ummi kamar maye, saboda azabar kallo, sai dai ga mamakinsa ummi tayi masa kwarjinin da ko magana ya kasa yi mata, gashi dai ba wani abun ta canza ba, kamaninta suna nan, sai dai ta girma ta cika, kai ba ka ce tana fuskantar ƙalubale a in da take ba.

Ko in da Idris yake bata kalla ba, balle ya sanya ran za ta gaishe shi.

Su Alhassan ma duk sun girma, da su auwwalu, sai dai babu wani cigaba su ma, dan kuwa auwwalu ma ya zama ɗan shaye-shaye sosai da sosai, dan har prison yayi, babu sana’ar kirki ya zama criminal.

Alhassan ma babu sana’ar kirki, sai kamasho da ƴan buge-buge.

Raihan kuwa yana ta kiran ummi a waya, da jin ko komai lafiya ƙalau.

Ana dawowa daga ɗaurin aure, kawu yahaya ya ce zasu koma gida, sai dai ummi ta sha surutun mutanen gidan na rashin aure.

Suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha, a kan ta kwantar da hankalinta a kan rashin aure, saboda lokaci ne, shi aure ba gaggawa ba samun nagartaccen miji da gidan aure mai cike da farinciki shi ne abun fata.

Ita dai ummi ganin sun taho daga gagarawa ya fi komai faranta mata rai.

Tashin hankali ba a saka masa rana, bayan su ummi sun sauka a kano gida, ummi ta tarar da ɗakinta a garƙame an saka masa mukulli.

Falo ummi ta tafi, ta samu Farida ta ce “Anty ke ki ka kulle ɗakina?”

“Eh ni na kulle, saboda ba gidan ubanki bane ba? Dan mun riga mun yi da shi ba zaki dawo mini gida ba”

Saroro ummi ta yi tana kallon fareeda, dr. Ya fito yana faɗin “Wai farida bamu gama wannan maganar ba? To wallahi idan ki ka cigaba da matsawa, sai dai ke ki bar gidan, kema ki koma naku gidan”

Farida ta duba wajen dining, ta ɗaukko kaya ta watso su tsakar falon ta ce “Sai ka tambayeta a ina ta samu wannan kayan? Wallahi dole ta bar mini gida, kan ta lalace ta lalata mini yara”

Ummi tabi kayan da kallo, kayan mayukanta ne, na wurin raihan da kayan sawa.

“Wannan kayan sun fi ƙarfin na dubu ɗari, sai ka tuhumeta a ina ta samu, kuma gidanka ba zan bar shi ba, dan na ci gida”…..

Ayshercool

CUTARWA!

P29

29

Wata irin tsuma jikin ummi ya fara yi, dan ba ta san ta ina zata fara bayani ba, bata taɓa tunanin farida za ta shiga ɗakinta, tayi mata bincike ba.

Dr. Ya bi kayan ɗaya bayan ɗaya da kallo.

Cikin haƙilo farida ta ce “Sai ta yi maka bayanin in da take samun wannan kayan, idan ba wani mugun abun take aikatawa na rashin gaskiya ba”

Tsulum noor ta tsoma baki ta ce “Kai, yaya raihan ne fa ya saya ya bata, ko yaya ummi?”

Kamar gunki ummi ta sake sandarewa, dan ba ta san ta aka yi noor ta riƙe sunan raihan haka ba ma.

Dr. Ya durƙusa ya tsince kayan, ya mayar cikin ledarsu, ya miƙe tsaye ya kalli farida ya ce “Bani mukullin da ki ka rufe mata ɗaki”

“Ban gane ba, me ka ke nufi?”

“Abun da ki ka gani, ba budurwa ba ce ba? Ke abubuwan da ake kawowa kausar cikin gidan nan zama ki ke ki tuhume ta?”

“Amma tsakani da Allah ka taɓa ganin wani yayi sallama da ita da sunan yana sonta, da zai saya mata wannan kayan masu tsada?”

Ya wuce ɗakin farida, tabi bayansa tana cigaba da masifa, ya ɗaukko mukullaye, ya dubi ummi ya ce “Mu je”

Tabi bayansa hawaye na zuba daga idonta, ya buɗe ɗakin nata, duk an hargitsa shi.

Ya ajiye mata kayan, ya kalleta ya ce “Mamana, na yarda da ke ɗari bisa ɗari, na san ba zaki aikata wani abu na Allah wadai ko a bayan idona ba, goya miki baya baya nufin, ki aikata abun da bai dace ba, ba zan matsaki a kan lallai sai na san me ki ke ciki ba, ni uba ne, kuma malamin makaranta, na san yadda zan tafiyar da tarbiyar yarana.
Kin mai munzalin da bin diddigin rayuwarki, ba shi ne mafita ba, amma dai ina sake yi miki tuni, da ki ji tsoron Allah, ki kuma kare mutuncinki, amma har ga Allah ni bana zargin ki, ki goge hawayenki ki samu ki huta, ni ban gaji da zamanki da mu a gidan nan ba, saniya ba ta taɓa gazawa da ƙahonta, dan haka ki kwantar da hankalinki komai mai wucewa ne, kuma in sha Allah zaki sha mamakin abokin rayuwar da Allah zai zaɓa miki, ke dai ki cigaba da tsare mutuncinki”

Ummi ta jinjina masa kai, ya fita daga ɗakin, ta zauna a hankali tana kallon kayan, tayi shiru tana nazari, idan har zargi zai shiga zuciyar dr. Game da ita, gara ta nemi duk mai yiwuwa ta rabu da raihan. Tabbas kaya ne masu tsada da ta cancanci a tuhumeta a kansu, da kawu ya matsa ta ina zata fara yi masa bayanin wannan alaƙar ta su, da ba kowane mai hankali ne zai sanyata a gurbi mai ma’ana ba.

Ya zama dole ta nesanta kanta da raihan, duk da abu ne mai wahala a wurinta, daga haɗuwarsu zuwa yanzu, ya gina wani tarihi da ba zai rushe ba a rayuwarta, raihan na daga cikin mutane masu muhimmanci da ba zata taɓa mantawa da su ba, zuciyarta ta saba sa shi, ta shaƙu da shi, ya bata ƙarfin gwiwa daban-daban, ya sanya ta jin ita cikakkiyar mace ce ɗan Adam da zata iya gogayya da kowa, tabbas raihan ya cancanci a kira shi ƙaraminsu babbansu, domin kuwa a manyan ba kowa ne za a samu da irin qualities ɗin sa ba.

A hankali ta tattare kayan, ta gyara ɗakinta, ta rama sallolin da suka tsere mata, ta cigaba da tunani.

Ta ɗaukko wayarta ta duba, missed call ɗin sa duk a wayar, har da saƙo yana tambayarta meyafaru ba ta ɗaga wayarsa?.
Ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiye, tana son fara koyawa kanta janye wa raihan.

Ta yinƙura ta fito daga ɗakinta, amma ta jiyo hayaniyar kawu da farida, kuma duk a kanta, jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, da tana da wurin zuwa da zata bar wa farida gidanta, ko kawu ya samu sassauci daga wulaƙancin da farida ke yi masa.

*
Anty Rakiya ta cigaba da matsa lamba, da ƙarfafa mami, a kan lallai a haɗa auren nan na zumunci, ita kuma mami ta cigaba da matsawa raihan, tare da ziga Alhaji a kan lallai a takura raihan yayi aure.

Abun ya fara damun raihan, dan haka ya samu hajiya da maganar, Hajiya ta ce “Babban mutum, menene a ciki dan ka yi aure, gaskiyar maminka ne shi ne cikar kamalarka ai”.

“To hajiya sai in yi aure su yaya ba su yi ba, kuma nema ake fa a sakani na auri wadda ba na so, ni bana son yarinyar nan”

“Raihan, dan ka riga su Salim aure babu laifi a ciki, bujirewa umarnin mahaifiyarka ba shi da fa’ida, ko ba ka auri wadda take so ba, ka yi ƙoƙari kai ka kawo musu wadda ka ke so”

Yayi shiru yana nazari, sannan ya kalli hajiya ya ce “Shikenan hajiya na gode sosai da sosai”

Ya tashi ya fita, yana nazarin maganar Hajiya.

Gefe guda kuma yana mamakin kasa samun ummi a waya, har ta what’s app, ya fara tunanin ko dai wani abun ya sameta ne.

Yaje wurin aikinsu Ummi, ya tambayi mai yi musu shara, ya ce masa ba ta je ba.

Ita ma ummi a lokacin da take ƙoƙarin ƙauracewa kiran raihan, headmastern su ya kunno kai, sai ya din ga kiranta a waya, wai su gaisa, wannan satin har da bata dubu biyu wai ta hau mota, saboda ɗawainiya da take yi da ɗalibansu.

Hankalinta ba a kan wannan yake ba, kamar ta fi raihan azabtuwa da ƙauracewar da ta yi masa, gashi pressure cikin gidansu, ta ƙara yawa, dan kuwa farida kullum cikin masifa da tashin hankali take a cikin gidan nan.

Babu tsammani dr. Ya samu ummi ya ce mata “Mamana, wani mutum ya zo wurina, ya ce mini yana sonki, kuma babu daɗewa yake son ayi auren, na bashi damar ya zo ku gana, sai dai ba ina nufin lallai sai kin aure shi bane ba, bana son yi masa karambani, ganin babban mutum ne, amma duk yadda ku ka yi sai ki gaya mini”

Ummi ta amsa masa da to ne, amma ta shiga cikin fargaba da zullumi, tare da tunanin, waye wannan? Kai tsaye ya tafi wurin dr.?

Abun yayi ta bata mamaki, sai dai sam ba ta ɗokin abun, domin kuwa bayan saka wayarta a flight mode, sai ta koma tana duba messages ɗin raihan.

Gaba ɗaya ummi ta manta da dr. Ya ce za ta yi baƙo, saƙon raihan na ƙarshe ya tsaye mata a rai.

“Ummi na bincika kina lafiya, amma you are avoiding me, ban sani ba ko nayi miki laifi ne, idan na yi miki laifi ne dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, ina cikin damuwa sosai wallaahi, ban zaci shaƙuwarmu ta kai in shiga damuwa haka ba, dan Allah ki yi mini reply ummi, zan tafi italy gobe in Allah ya kaimu da asuba, dan Allah ki yi mini magana”
Ajiye wayar ummi tayi, idonta na cika da hawaye, “Ban kyauta maka ba raihan, amma yanzu ko na yi maka bayani ba zaka gane ba, buyagi zaka yi mini” tayi maganar a hankali, tana sake kallon wayarta.

“Yaya ummi, wai baƙonki ya zo” noor tayi maganar ba tare da ko sallama ta yi ba.

Ummi ta jinjina mata kai, tare da jin matsananciyar faɗuwar gaba, dan wannan ne karon farko da zata tsaya tayi zance da wani, da sunan yana sonta, gashi alamu sun nuna da gaske yake, tunda ya biyo ta wurin dr., Duk da abun da take ta addu’a a kai kenan, idan tana da rabon aure, Allah ya kawo mata miji nagari, sai dai gaba ɗaya ba ta murna da lamarin a yanzu, kuma ta rasa dalili.

Sai dai ta tsinke da al’amarin, ganin headmastern su a gareji, wai shi ya zo wurinta, kenan shi ne baƙon?

Suka gaisa suka zauna a kan fararen kujeru, tana bin sa da ido, dan ba ta gama yadda da shine baƙon ba.

Yayi gyaran murya ya ce “Wato ummi na san zaki yi mamakin ganina, da dalilin zuwana, duk da nasan mahaifinki yayi miki bayani.
To ni dai ummi ba wani abu ne ya kawo ni wurinki ba face alkhairi, na daɗe ina sonki, tun ranar da na ga kin cire hijjabi kina alwala, watannin baya baki ganni ba ke amma, to a lokacin gidana mata huɗu ne, amma yanzu Alhamdilillah mun rabu da ta ukun, dan haka akwai gurbin mutum ɗaya, ya sanya na ce tun da naga alamar babu tsayayye bari ni na tsaya, mu dai-daita mu rufawa juna asiri, dan yanzu kin san maza tsada muke yi” yayi maganar yana murmushi yana kallonta.

Ummi dai sama-sama take jin sa, ƙasan zuciyarta lissafi take yi, ta yi wa raihan reply ko ta ƙyale shi, ta san duk daɗewa idan ya dawo sai ya nemeta.

Dan haka sama-sama take jin maganganun headmastern.

“Ba zan takuraki yanzu ba, amma dai ki yi tunani, dan kuwa da wuri nake son ayi auren nan, bana son ɓata lokaci, kuma za ayi abu ne dai-dai talaka da tsarin addini, ba wani ɓarnar bidi’a, in kawo abun da Allah ya yassare ayi”

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce “To malam, idan na yi tunanin sai mu yi magana”

Ya ce “Yauwwa ummi, Allah ya wuce mana gaba ” ta amsa da Amin, ya tashi ya tafi, ita kuma ta dasa sabon zama tana nazari da tunani.

Sai da ta ji sauron wurin na neman halakata, sannan ta tashi ta koma cikin gida.

Kitchen ta nufa ta zubo abinci, zata fito farida ta tare ta ta ce “Ubanki ne ya kawo abincin?” Ummi ta girgiza kai.

“To ajiye ki fita, mayya mara zuciya, ai si ki je wurin waɗanda ki ke bi ku watse su saya miki kaya, su saya miki abincin, wallahi takura da masifa yanzu ki ka fara ganinta, sai ranar da ki ka bar mini gida, ko ki yi aure, ko ki koma in da ki ka fito ko ki bi duniya “

Salin alin ummi ta ajiye abinci, ta bar kitchen ɗin.

‘Tabbas! Tura ta kai bango, yakamata na yi wani abu na matsa daga gidan nan, na fuskanci ƙalubalen da ke gaba, zaman gidan nan yana neman fin ƙarfina” tayi maganar a zuciyarta.

Abokin kukan nata ga ƙoƙarin da take yi a kansa, ta nesanta kanta da shi.

Abubuwa suka cigaba da ɗaukar zafi, dan da kawu zai koma aiki, sai da ya gindawa farida sharaɗi, a kan muddin ya dawo ya tarar ummi ba ta nan, sai ya saketa.

Farida har mamaki take yi, yanzu asirin ya daina kama dr. Al’amari in dai ya shafi ummi, ba ya saurarawa.

Ummi ta din ga sallar dare tana kai wa Allah kukanta, amma a ƙasan zuciyarta ta ji ta amince da auren headmaster, no matter what wahala ba yanzu ta fara shigar ta ba, tarwatsewar gidan dr., Da kuma alƙarsu da raihan su ne manyan barazanar ta a yanzu, idan ta yi aure ta san ta rage kaso mafi yawa daga matsalolinta.

Raihan ya sha mamakin burus da ummi ta yi da shi, ba dan ba ta ganin saƙonninsa ba.

Gajeren saƙo ta tura masa “Baka yi mini komai ba raihan, tarayyarmu na barazana ga kwanciyar hankalina, da jefa zargi a zuciyar mariƙana, ka yi haƙuri da hukuncin da na yanke”

Message ɗin ya nuna blue tick, alamar ya ga saƙon amma yaƙi reply, tun ummi na jiran yayi reply, har ta sare, sai kuma abun ya dame ta ta rasa sukuni, ga headmaster ya matsa mata kamar maye, ita har mamaki take yi, duk lokacin da suka shafe, bai ji yana son ta ba, sai watannin baya da ya ganta tana alwala, mata huɗu sun rabu da ɗaya zai aureta, kodayeke wannan duk bai dameta ba, wutar gabanta take ƙoƙarin kashewa, dan haka ta ce masa ta amince.

Tamkar ya goya ummi, saboda murna da nishaɗi, ta amince da aurensa, ya ce mata zai zo wurin kawu su yi maganar kawo kuɗin aure, ta ce masa baya nan sai ya dawo.

Ya fara yi wa ummi huɗubar shi talaka ne, dan haka kuɗin sadaki, da na lefe da na aure, zai bayar dubu ɗari, dan Allah ta ce ta yarda a haka, ko da babanta zai ce ba yadda ba.

Ummi ta amsa masa da to, dan ba ta da burin da ya wuce ta ɗaga daga gidan nan, ita ma tana burin ta ganta a ɗakinta, ko ta samu sauƙin gorin da take sha.

Kullum cikin duba wayarta take, taga raihan yayi mata reply na message ɗin da tayi masa, amma yaƙi yin reply, wasu lokutan tana kallon sa online, amma bai yi responding ba.

Tunani ta din ga yi hanyar da ta bi tana neman maraba da raihan tayi musu tsauri daga ita har shi, amma ta san idan tayi masa bayani, ba zai taɓa tsayawa ya fuskanceta ba, dan akwai shi da kafiya wasu lokutan.

Noor tana ta gyara wa ummi kan mudubin ta, tana jera mata mayukanta tana faɗin “Ai yaya ummi ba sai kin cigaba da ɓoyewa ba, kawai ki jera abun ki, dama na san dr. Ba zai yi miki faɗa ba” ta lura hankalin ummi baya kanta, dan haka ta ce “Wai yaya ummi me ki ke jira a wayar ne, ko salary ki ke jira ne?”

“Noor raihan ya daina kulani”

Noor ta ɗan waro ido ta ce “Faɗa ku ka yi? Innalillahi yaya raihan ɗin namu?”

Ummi ta ce “Ni na fara daina kula shi, noor bana son zargi ya shiga ran kawu a kaina ne, kuma aure nake son yi, bana son na yi aure mu kasa rabuwa”.

“To yaushe zaki auren?”

“Malam ya ce idan kawu ya dawo zai zo su yi magana ya kawo kuɗin aure, sonake ya kawo kan raihan ya dawo”

Noor ta kwaɓe bakk ta ce “Wai wani malam, ni fa bana son malam ɗin nan, Astagfirullah bari dai na yi shiru, amma dan Allah kar ki auri wani malam, ki auri raihan mana” ummi ta zare ido ta ce “Ke ƙanina ne fa, kamar ɗan uwa yake a wurina, malam ya ce zai bayar da dubu ɗari kuɗin komai da komai, kar a wuce wata uku, amma ban san yadda za su yi da kawu ba”.

Kamar shashasha noor ta kalli ummi ta ce “Wai ke yaya ummi, ni na rasa me zance, shikenan ke ba za a kawo miki lefe ba? Matansa fa uku, gashi tsoho, to kina son sa ne?”

“Mama ƙyaleni, surutun nan naki ma ya fara damuna”.

“Hmm, Yaya raihan yayi fushi da ke fa, har makarantarmu ya je, bayan mun dawo daga gagarawa, ya tambayeni idan tare muka dawo kuma lafiyarki ƙalau, na ce masa eh. Ya jinjina kai ya tafi”

Cikin tsananin mamaki ta ce “Ya aka yi ya san makarantar ku har ya je? Sau biyu fa kawai kuka taɓa haɗuwa, Kin ga dalilin da yasa nake son mu rabu, raihan ya iya rigima fa”

Noor ta ce “Eh amma yana da kirki sosai ai, tun da ya taɓa bani kuɗi, wannan malam ɗin gaskiya talaka ne, ko kuma wayo, dubu ɗari fa ba ta da yawa sosai, shikenan ke ba za a kawo miki akwatuna masu yawa ba, kamar na inteesar”

Ummi kawai ta kwana ta yi wa noor shiru.
Ta cigaba da kallon wayar, a ranta ta ce ‘Haba babban mutum, manyan ba sa haka fa’ ta cigaba da duba chats ɗin su na baya.

Headmaster ya kira dr. A waya, yana tambayarsa yaushe zai dawo, so yake da ya dawo, ya kawo kuɗin, dr. Ya ce masa baya son gaggawa ya jira shi tukuna.

Wasa-wasa kusan sati uku kenan, raihan da ummi ba su yi magana ba, ba kuma dan hakan yana yi wa kowanensu daɗi ba.

Ummi ta kira direban da yake aikowa ya karɓar masa abinci, ta tambaye shi ko raihan ya dawo, ya ce mata a’a.

Yanayin sintiri da nacin da headmaster yake yi mata, abun har mamaki yake bata, kamar ya ɗauketa ya kaita gidansa ya ajiye.

In da Allah ya rufawa ummi asiri, aikin nan nata, tana ɗan samun salary, idan tayi girki ta gama farida sai ta hanata abinci, tayi ta janyo mata masifa da bala’i da miyagun alkaba’i, tare da fatan ta sha wahala a rayuwa kamar yadda ta wahalar da ita a gidan aurenta.

Ummi a ranta ta ce ‘Wahala waccece ban sha ta ba, kuma ban cutar da ke ba a zamanmu ke ki ka cutar da ni!”

Tun da dr. Ya zo gida, headmaster yake sintiri, a kan zai kawo kuɗin, dr. Ya ce ya ɗan ba shi lokaci tukuna.

Hatta wurin aiki manager ya lura yanayin ummi ya sauya, kamar wani abu na damunta, amma dai yayi shiru bai ce mata komai ba.

Dr. Ya kira ummi ya tambayeta ko tana son malam Isa, ummi ta ce eh.

“Ummi, kar takura ko damuwa ta sanya ki kai kanki ga halaka, rauwar aure ba rayuwar gida ba ce da babu nauyin kowa a kanki, kar ki kai kanki in da zaki yi dana sani, mutumin nan babban mutum ne, kar ki zo daga baya azo a samu matsala, ki dai je ki sake tunani” ummi ta amsa masa da to, ba dan ta so ba, ita fatanta kawai dr. Ya amince.

Kasancewar yau babu coustomers, ummi ta bar reception ta koma in da take zuwa ta yi salla ta ci abinci ta kwanta, tana cigaba da duba chat’s ɗin su da raihan.

Ƙamshin turaren raihan ne ya fara yi mata sallama, ta zaci hallucinating kawai take yi, sai dai ba ta gama tunanin ba, ta ganshi a tsaye a kanta.

A zabure ta tashi zaune, tana bin sa da kallo.

Wani irin kwarjini ta gani a tare da shi, wanda ba ta taɓa gani a tare da shi ba, fuskarsa a matuƙar haɗe, kamar ba ya dariya.

“Raihan” ta kira sunansa a hankali.

Ya nemi wuri ya zauna, ya ƙura mata ido sannan ya ce “Salma wannan shi ne tukuicina daga gareki ko? Ko rabuwa ki ke son mu yi, yanke alaƙa da ni kai tsaye ba tare da wani dalili ba kina ganin shi ne mafita? Bafa a rana ɗaya muka gina alaƙar nan ba, ummi dama zaki iya wulaƙanta ɗan Adam har haka kamar yadda ki ka yi mini?”

Cikin rauni ta ce “A’a raihan, ba haka bane ba, dan Allah ka fahimce ni” nan ta gaya masa bayan dawowarta gida abun da ya faru, yadda farida tayi mata bincike ta nuna wa dr.

“Raihan wulaƙanci ba halina bane ba, ina ma naga ƙarfin gwiwar da zan iya wulaƙanta wani? Raihan ba kowa zan yi wa bayanin alaƙarmu ya kalli abun da idon basira alaƙar ta yi masa ma’ana ba, bana son zargi ya shiga ran dr. Duk da ya goya mini baya, amma ban san ta yaya zan wanke kaina ba, kafi ƙarfin wulaƙanci a wurina raihan, ban yi haka dan wulaƙanta ka ba”

Ya girgiza kai ya ce “Ban yadda ba ummi, duk a ƙoƙarinki na guje mini, ki ke shirin kai kan ki ga halaka, zaki auri shugaban makarantar ku ko? Malam isa”

A zabure ta kalli raihan, ya aka yi ya san wannan maganar?

“Mamaki ki ke yi ma? Ni zaki juya baya rana tsaka ummi, har ki yi shirin aure ban sani ba? Ina bibiyar rahuwarki fiye da yadda ki ke tunani, gani nake ko yaya na kawar da kai a kanki wani abu zai faru da ke, rabuwa da ni ba mafita bane”

“Raihan haka ne kawai mafita a wurina, matar gidanmu ta matsa mini da yawa, ƙalubale ko ta ko ina, ba zaka gane a mawuyacin halin da nake ba…

Ya katseta da cewa “Kuma sai ki kai kan ki ga halaka, mutumin da ya saki mata sun kai biyar, ya saki wata ke ma zai aureki ya biya buƙatar sa ya sake ki, ba irin wannan mijin nake roƙa miki ba”

Ta ce “Raihan alkhairi nake fata”

“Yi mini shiru” yayi maganar a hasale, galala take bin sa da kallo.

“Yakamata mu daina yaudarar junanmu, daga ni har ke, idan saboda ki rabu da ni ne, ki ke ƙoƙarin yin wannan auren, kin riga kin makara, ba za ayi shi ba. Ban damu da koma me wani zai yi zargi ba, ba zaki iya rabuwa da ni ba, kin riga kin makara. Ke banda rashin lissafi ma me zaki yi da wannan dattijon, shekarunsa nawa ke naki nawa? Me zai tsinana miki, ko ke ba kya wannan lissafin, ko an ce miki ci da sha ne kawai aure? Kodayeke ai kin san me nake nufi” kai ka ce gunki haka ummi ta koma, yau raihan ya zama wani abu na daban.

“Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki”

Tamkar ya jona mata shocking ta zabura ta ja da baya tana kallon fuskar raihan, yadda farar fatarsa ta koma ja, da irin kallon da yake yi mata, ya sanya ta tabattar da ba ƙarya yake yi ba.

“Ummi ki yi tunani, wace irin alaƙa ce a tsakani na da ke?”

Kamar zata fashe da kuka ta ce “Raihan, ni fa ƙanina na ɗauke ka, ƙanin ƙawata ce kai, mutum ne kai mai muhimmanci ne a gareni, amma ba irin wannan alaƙar ba”.

Tashi yayi ya taka, ya je gabanta ya durƙusa, ya ɗan tsura mata ido ya ce “Bamu haɗa alaƙa da ke ba, ta uwa ko ta uba ba, kuma tarayyar mu da muka yi da ke ta wuce yadda ki ke tunani, ta kuma wuce gurbin da ki ka ajiyeta. Salma son juna muke yi. Lokacin nan da muka ɗauka ba ma tare, ki ka yanke alaƙarmu, kin sani a mummunan yanayin da yakamata ki ce na yafe miki, na shiga matsananciyar damuwa”

Da sauri ta girgiza kai ta ce “A’a Raihan, ina ganin mutuncinka, babu wannan maganar a tsakanin mu dan Allah a barta, kar ka sake yin ta bana so”

Ya shafi gefen fuskarsa, yana jin zafi a zuciyarsa, ya kalli ummi ya ce “Na gode Salma” ya tashi ya fice daga wurin.

Ummi ta takure tana ajiyar zuciya.

“Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki” shi ne abun da ya din ga yi mata kai kawo a zuciyarta.

Manager ne ya biyota yana tambayarta me ta yi wa ƙaninsa ya ga ya fita rai a ɓace, ummi ta ce masa babu komai.

Kwanaki biyu a tsakani, headmaster ya daina kiranta a waya gaba ɗaya, messages ɗin ma da yake tura mata ya daina.

Sai dai ko a jikinta, tunanin ya raihan yake yafi tsaya mata a rai.

Gashi ya ce halin da ta saka shi a ciki, yakamata ta nemi yafiyarsa.

Ganin ba ta da mafita, ya sanya ta neme shi a waya, amma shiru ba ya ɗagawa.

Tana cikin jimamin lamarin, dr. Yayi sallama a ƙofar ɗakinta, ta amsa sannan ya shiga.

Ya nemi wuri ya tsaya, sannan ya dube ta ya ce “Ummi, baya fa ta haihu, mutumin nan malam Isa ya kirani a waya, ya ce mini ya janye maganar aurenku, kuma hakan yayi mini dai-dai, dan kuwa ko bai janye ba, ba zan bashi aurenki ba, binciken da na yi a kansa bai yi mini daɗi ba, dan haka ki cigaba da addu’a, Allah ya kawo mafi alkhairi” har kawu yahaya ya fita, ummi na tunanin me raihan ya yi wa headmaster ya fasa aurenta, kenan da gaske yake yi sonta yake, ba zai bari kowa ya aureta ba!?

Gabanta ya faɗi tare da tabattarwa da kanta ba ta ga ta zama ba, idan ba raihan da rigima ba, ai ya san zaren ba kalar yadin bane ba, ina shi ina ita? Kyakkyawan matashi kamarsa me zai yi da ita, ga uwa uba ta girme shi, dole ta lallaɓa shi su rabu lafiya.

Sanin baya ɗaga wayarta, ya sanya washegari da ta shirya, ta tafi office ɗin su raihan.

Sai dai ba a bari ta shiga ba, sakataren shi yayi mata sannu da zuwa, tare da tambayarta raihan ya san da zuwanta?.

Ta ce “A’a, amma ace masa ummi ce”

Sakataren ya tashi ya shiga cikin office ɗin raihan, ya dawo ya ce mata ta jira, zai neme ta.

A ƙalla ta shafe awanni biyu tana jira, bai fito ba, ba kuma dan yana abun da ya fi ganinta muhimmanci ba, sai dan ya sanya ta yarda da alaƙarsu soyayya ce.

Yana office ɗin sa, ya kira waya ya saka aka kai mata ruwa da lemo da snacks.

Ya koma ta window ya tsaya yana kallonta in da take zaune, fuskarta duk ta faɗa, tana ta wasa da yatsun hannunta.

Ji yayi ya kasa jurewa, ya nufi ƙofa ya fita, tana hango shi ta tashi ta tsaye, sakataren ya fara yi masa bayanin ita ce baƙuwar da take son ganinsa, ta daɗe a wurin. Buɗar bakin raihan sai cewa ya yi ta rubuta a rubuce tana son ganinsa, idan yayi approving ya bata date da time ya fice ya bar ummi.

Ayshercool.

CUTARWA

30

Kamar a mafarki ummi ta ga abun da raihan yayi, ba ta taɓa zaton zai aikata abun da yayi mata ba.

Ƙirjinsa har wani zafi yake yi, ji yake tamkar ya koma ya saurareta, amma ya dake, ya samu wuri ya tsaya yana hangen ta, ta fito jiki a sanyaye ta bar harabar rukunin ofisoshin.

Ya din ga jin kamar ya bi bayanta, amma ya tattara dukkanin jarumtarsa yaƙi bin ta.

Ummi ta daɗe tana tunani, me raihan ya yi wa malam isa, da kai tsaye ya ce ya fara aurenta haka, duk zumuɗin da yake yi da rawar kai a kanta.

Ta tura wa raihan saƙo ta what’s app “Raihan, na zo wurinka mu yi magana shi ne ka yi mini wulaƙanci, abun har ya kai haka?” Yana online bayan gama karanta saƙon yayi blocking ɗin ta gaba ɗaya.

Ɗan ƙaramin sauro, mai hana giwa bacci, duk wata hanya da ya san zai bi ya kunna ummi, ya ɓata mata rai ya din ga bin ta.

Sai dai kusan kullum yana kan waya, yana duba hotunanta ta tare da chat’s ɗin su.

Yana sashen hajiya yayi ɗai-ɗai, ta saka an kawo masa abinci amma ko taɓawa bai yi ba, Ta ce “Babban mutum, wai sai abincin ya gama hucewa zaka ci?”

Ya sake kashingiɗa ya ce “Ba irin wannan nake so ba”

Ta zauna ta ce “To wanne ka ke so? Duk ka rame wallahi, anya ma kuwa kana cin abincin?” ya kwaɓe fuska ya ce “Ba mijinku ne duk ya ja nake ramewa ba”

Hajiya tayi dariya ta ce “Ƙaniyarka wato mijinmu”

“Eh mana”

“To tashi ka ci abincin”

“Hajiya ki ƙyale abincin nan, bana jin daɗin komai wallahi, ga gajiya ta dameni, abincin ummi nake son ci, kuma mun yi faɗa”

Hajiya ta ce “Wacece kuma ummi, da abincinta ya fi na hajiya, bani labari”

Ya tashi zaune ya ce “Ina ga hajiya auren nan fa zan yi, amma wadda nake so zan aura”

“Ahh Alhamdilillah ai haka ake so, fatanmu kawai ka kawo mana ta gari, mai tsoron Allah”

“Baku da matsala da wannan, amma dan Allah hajiya ki yi ta yi mini addu’a, Allah ya tabbattar mana da alkhairi”

“Addu’a kullum a cikinta muke ai, Allah ya shiga lamarin ku”

Ya ce “Amin ya rabb Hajiyarmu ba irin ta kowa ba” yayi maganar yana zuba ruwa a kofi.

Salim ne yayi sallama, suka amsa masa baki ɗaya, ya ƙarasa gaban hajiya ya ce “Dan Allah mukullin motarki zaki ara mini, zan je wani wuri ne”

Hajiya ta kalleshi ta ce “Ina taka?”

“Tana wurin gyara, batirinta ya samu matsala”

Hajiya ta ce “Ka je ka hau ta haya, ba zan baka mota ta, ka rugurguzo mini ita ba, ba zan iya tunkarar Alhaji canza mini wata nan kusa ba, ko ka ɗauka a sauran biyun da kuka lalata”

Raihan ya ce “Dan Allah ki bashi mana”

“Ba zan bayar ba”

“Ai Allah na ce, i will take the responsibility idan ta samu matsala”

“Iyee, ka fi son ɗan uwanka a kaina, ba zan bayar ba nace”

Raihan ya ce “A’a ba haka bane ba, amma dai a taimaka, baki san me zaki samu a sanadin hakan ba”.

“Ni fa lallaɓa mota ta nake yi, idan na bashi duk sai ya lalata ta”.

Raihan ya din ga yi mata daɗin baki, har ta bawa Salim mukullin.

Rabon da a canzawa hajiya mota, kusan shekara biyar, motocin ta uku na hawa ɗaya ce ma mai tsada, sauran duk yaran gidan sun kashe su, duk babu wata latest, mami kuwa kusan duk shekara sai ta saka Alhaji saya mata mota, ta sayar da nata, ko tayi kyautarsu, hajiya kuwa babu ruwanta, dan haka raihan yayi niyyar yin surprising ɗin ta.

Kansa har dummm yake yi, saboda tsabar gajiya da tension ɗin ummi da ya dame shi, ya tashi ya tafi sashen mami, sai dai ya tarar da Nihal ta zo gida sun yi hutu, ƴar autar mami, ga kuma Anty rakiya da Safiyya suma sun zo.

Anty Rakiya kawai ya gaisar, ya jiya zai bar falon, Safiyya ta ce “Yaya ina wuni?”

“Lafiya ƙalau” ya amsa a taƙaice.

Mami ta ce “Raihan ina zaka ne?”

“Kwanciya zan je na yi”

“Ka shigo a gaggaisa mana”

“Mami ai mun gaisa, su anty rakiya ai ba baƙina bane ba, ku gaida gida in zaku tafi” ya juya ya fice.

Jikin Anty rakiya yayi sanyi ta ce “Bilki, anya al’amarin nan zai yiwu, ni gaba ɗaya gani nayi kamar ya canza”

Mami ta ce ‘Kin san ɗan naki ne, hukuma ne sai da rarrashi, ina nan ina ta ƙoƙari dai, mu ga yadda Allah zai yi”

“To, Allah ya ji she mu alkhairi”

“Amin ya rabb”

Kwanaki biyu ciwon kai ya saka raihan a gaba, sai dai ya sha paracetamol ya ƙyale, a tsakanin kwanaki biyun, ya saka aka kawo wa Hajiya sabuwar mota dal.

Hajiya ta din ga murna, bakinta ya kasa rufuwa, tana son canza motar, amma ba ta son yawan tambayar Alhaji abu, kuma ganin ta ta motar lafiyarta ƙalau, ya sanya ba ta damu sai ya canza mata ba.

Ta din ga murna, ta yi masa godiya, har da kiran a waya Alhaji ta gaya masa, kasancewar ba ya gida, ta ce ya yi wa mami godiya.

Sai dai tun da raihan ya shiga wurin mami, ta saka shi a gaba ta din ga surfa masa zagi, kamar za ta dake shi.

“Saboda tsabar iskanci, wai ita ce tayi mini naƙudarka da zaka fifita ta a kaina, har ka canza mata mota hurumin ka ne? Saboda tsabar ka nuna mini ban isa ba, to wallahi idan wani surkullen ta yi maka, sai na warware shi, ba zai yiwu ba. Ka saya mata mota ni uwarka ina zaune kana kallona”

Ta gama masifar tsaf sannan ya ce “Mami, a shekara biyar motoci uku Alhaji ya sauya miki, ko sau ɗaya ita ba a canza mata ba, abun da ki ke karɓa a hannunsa ba ta karɓa, ai ba aibu bane ba dan an canza mata, abun alfaharinki ne fa mami an mori ɗan ki”

Ta katse shi a hasale ta ce “Rufe mini baki raihan, wallahi ba zata saɓu ba ba zai yiwu ba”

“Mami, ke uwata ce mahaifiya, wallahi tsananin haƙurin hajiya ne ya sanya nake kyautata mata ita ma, mami da ke take yi wa abubuwan da ki ke mata, ba fa zaki yadda ba, Alhaji baya jin maganar kowa sai taki, kuma ba ta nuna ta damu, duk da abun babu daɗi, tana iya ƙoƙarin ta….

“Eh lallai har ka kai ka kalleni ka na nuna mini ban isa da kai ba ko, saboda ka farantawa wata, to na mallake uban naka, idan ta isa mace tayi abun da nake yi, kuma wallahi ko ka saya mini motar da ta fi ta ta, ko kuma ka karɓe motar”

Sallamar Alhaji ce ta katse maganar da take yi, ya ƙaraso cikin fara’a yana faɗin “Ɗa ɗaya tamkar da goma, na ga an gwangwaje hajiya da mota, ta kirani a waya, ta gaya mini ta ce ayi maka godiya kai da mamanka, nima ina godiya dan ni ka kankaro, hankalina bai kai in canza mata ba, Allah ya yi maka albarka”

Raihan ya amsa da Amin, jikinsa a sanyaye ya fita, hakan ya tabattar wa da Alhaji akwai damuwa.

Ummi kasa komawa islamiyyar su tayi, dan ba ta san me raihan ya yi wa malam isa ba, duk wata kafa da za ta bi ta samu raihan ya toshe ta, duk yayi blocking ɗin ta.

Ta nemi lambar direbansa habu, ta kira shi suka gaisa.

Ta ce “Malam Habu, dan Allah raihan fa? Na kasa samun wayarsa”.

Malam habu ya ce “Raihan yana asibiti”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, meya same shi?”

“Wallahi ban sani ba, ya ce na kai shi asibiti dai jiya, ya ce likita ya bashi hutu, zai huta a asibiti kar wanda ya je wurinsa, Alhaji ne kawai ya je, ya ce a ƙyale shi hutawa zai yi”

“Kai raihan ya fiye rigima, wane irin hutawa kuma a asibiti?”

“Bashi da lafiya ne dai, aka ce ya huta aka bashi magani, ya ce a bar shi a asibitin kuma baya son kowa ya je, kwanansa biyu a can”.

Ummi ta ce “Dan Allah malam habu wane Asibitin ne?”

“Ai ya hanani faɗa ne, kuma wallaahi asibitin da nisa sosai”

“Bakomai ka gaya mini zan je”

“To ai kar yayi mini faɗa, ya hana ni ya ce kar in faɗa”.

“Ba abun da zai ce in sha Allah, dan Allah ka gaya mini”

Malam habu ya kwatanta mata, bayan sun gama wayar ya kira raihan ya gaya masa, dan kar yayi laifi.

Raihan ya ce “Ka tambayeta yaushe za ta zo, ka je ka ɗaukkota zuwan yayi mata nisa, za ta kashe kuɗin mota da yawa”

Ya amsa masa da to.

Ummi jikinta har tsuma ya din ga yi, jin bashi da lafiya, ta tuna lokacin da yayi rashin lafiya, yadda ya din ga ɗawainiya da ita.

Mami ta tashi hankalinta sosai da sosai, ta takurawa Alhaji a kan ya gaya mata in da raihan yake amma ya ce “Likita ya bashi hutu, shi kuma ya ce baya son kowa yaje in da yake. Bilki na san kina sawa yaron nan pressure a kan wasu abubuwan da ba ya so, mark you bana saurarawa abun da ya shafi yarana, na san nauyin da na ɗorawa raihan yayi masa yawa, amma so nake ya saba, because he has the spirit of good leadership, dan Allah ki bi shi a hankali”

“Ce maka yayi na yi masa wani abun?”

“Bai ce ba, amma yanayinsa ya nuna ranar da ya saya wa hajiya mota, na karanci damuwa a fuskarsa, kuma ki ƙyale shi, idan ya gama hutawar ya gaji dole zai dawo gida”

Jikinta yayi sanyi, tayi shiru ba ta kuma cewa komai ba.

*

Ummi a kitchen tayi sallar asuba, domin ta samu ta yi girkin gidan, ta haɗa da ɗan abun da za ta yi wa raihan.
Kan gari yayi haske, farida ta zo ta ritsa ta, ta kammala.

Malam habu ne ya zo ya ɗauke ta, suka tafi, asibitin yayi kyau sosai da sosai, kamar a ƙasar waje.

Can saman bene a wani rukuni ɗakin da raihan yake, tun safe yake zuba ido, ya ga ta ina za ta zo.

Fuskarsa ta faɗa sosai da sosai, ya ƙura mata ido, har ta ƙaraso, ya kalli malam habu ya ce “Jeka zan kira ka” ya jinjina masa kai ya fita.

Sai kuma ta rasa me za ta ce masa.

Ya gyara zamansa, ya sake jan lallausan bargon da ke gadonsa, yana rufe jikinsa.

Kamar an yi mata dole ta ƙarasa gaban gadon ta ce “Sannu ya jikin?”

“Da sauƙi” ya amsa mata a taƙaice.

Ta nemi wuri ta zauna ta ce “Meya sameka ne?”

“Ina ruwanki? Zuwa ki ka yi ki gani ko na mutu saboda kin ce ba kya so na?”

Ta girgiza kai ta ce “Kamar bani da zuciya ko? Ka yi mini wulaƙanci a office ɗin ka, ka yi blocking ɗina amma still na biyo ka. Raihan wulaƙanta ɗan Adam ba halina bane ba”

Ya shafi sumar kansa ya ce “Ai ke ki ka buƙaci hakan, ko kin manta so ki ke mu rabu? Dole na yi blocking ɗin ki, annoba ya fita daga rayuwarki. Kin ɗauka rabuwa da mutum irina abu ne mai sauƙi? Ai tun da muka fara game ɗin nan tare sai mun kai ƙarshen ta”.

Cikin rauni ta ce “Raihan me ka yi wa headmaster ya fasa aurena?”

“Ki tambaye shi mana”

“Ni kai nake tambaya, dan Allah me ka yi masa?”

Ya ɗan fesar da iskar bakinsa sannan ya ce “Baya sonki ne, na jarraba shi ko zai iya riƙe ki, ba zai iya ba. Ni ɗin dai ni ne mai sonki da gaskiya “

“Dan Allah ka daina wannan maganar, raihan ni ba zan iya aurenka ba, ina da dalilina dan Allah ka daina wannan maganar ka ƙyaleni na yi aurena. Na matsu na yi aure nima, baka san pressure da nake ciki ba, raihan ka ƙyaleni aurena da kai ba zai yiwu ba kai ma ka sani”

Ya tsura mata ido yadda idanunta suka cika da hawaye, ya ce “Wait, kin matsu ki yi aure to ki aure ni mana, nima na matsun da ne ban gane ba, sai da ga baya, ina da duk qualities ɗin da zan iya riƙe aure, ko ki aureni ko in hanaki sukuni kamar yadda ki ka hana zuciyata sukuni”

Hawaye ne ya fara zubo mata “Raihan, ba zaka gane me nake nufi ba, ba zan yi aure ne dan wani abu ba, domin ina da mummunan tabon aure a ƙasan zuciyata, dan Allah ka gaya mini me ka yi masa na je na bashi haƙuri”

Raihan ya haɗe rai ya ce “Arhar taki har ta kai haka? Da kina da muhimmanci a gare shi, da bai fasa aurenki ba tare da kin san dalilin hakan ba”

“Eh ni wacece? Arhar tawa ta wuce haka ma, ni dai dan Allah ka taimaka mini, zan iya durƙusa maka ma, idan ka san waceceni ko ka san halin da nake ciki, ba zaka yi mini haka ba dan Allah ka gaya mini meyafaru in san ta ina zan ɓullowa lamarin”.

Maimakon ya bata amsa, sai ya kashingiɗa yana kallonta yana lumshe idonsa.

Ta ɗaga idonta da ke zubar da hawaye, amma tas da su kamar ba kuka take yi ba.

Ya girgiza mata kai ya ce “Ki daina it hurts me, zafi nake ji a nan, idan kina kuka” yayi maganar yana nuna ƙirjinsa.

“Dan Allah idan da gaske ka ke so na, ka tayani son abun da nake ganin shine mafita a gare ni”

Raihan ya ce “No, I can’t ɗan Adam ne ni, nafi son kaina a kan kowa, ban damu da halin da zaki shiga ba, nima mafita nake nemawa kaina, ko in ce nake nema mana, duk wanda zaki aura ba zaki daina tunanin raihan ba, muna son juna sosai” yayi maganar yana miƙa hannu ya karɓe flask ɗin hannunta.

Kawai ta bishi da kallo, ya buɗe flask ya fara cin abincin sa.

“Yo hauka nake in yi missing wannan delicious food ɗin, bari na ajiye in anjima in ci, yanzu a ƙoshe nake, tun da kin zo biko na, na haƙura zan yi unblocking ɗinki, kin ji sweetheart”

Ganin yana neman ya ƙarasa tarwatsa mata zuciya, ya sanya ta tashi zata tafi ta bar masa ɗakin, cikin zafin nama ya diro daga kan gadon, ya rigata ƙarasawa ga ƙofar ya tsaya, yana bin ta da kallo.

“Zan wuce” ta faɗa tana share hawayen ta.

“Tsaurin idona yayi yawa ko? Na dame ki da yawa, kin daina yi mini kallon ƙanin ma, maybe ma kamar kin tsane ni yanzu, kin fara dana sanin sanina ko?”

Tayi saurin ɗagowa tana kallonsa.

“Ba wai ina nufin kin daina so na ba, ai ba zaki taɓa iya daina so na ba”.

Ta ce “Ni ban ce ina sonka ba”.

Ya matso da fuskarsa dai-dai tata, da sai da ta ja da baya saboda yadda yake yi mata numfashi a fuska.

“Wallahi ina sonki Salma, hubban shadidan irin son da bana tunanin akwai abun da zai canza shi, ina sonki so daga ƙasan zuciya” yayi maganar a wani marairaice, da muryar da bai taɓa yi mata magana da irin ta ba.

A take jikinta ya hau tsuma, har wani jiri ya fara ɗibarta, ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, kamar ba za su jure cigaba da ɗaukarta ba.

Ya matsa ya bata hanya ya ce “Je ki kar ki faɗi, dan zan iya rungumeki idan ki ka cigaba tsayuwa a gabana ki na kuka.

Tamkar an buɗeta daga kejin zaki, ta fita har da haɗawa da gudu, ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko wayarsa, ya kira habu a waya, ya ce ya tari ummi a ƙasan bene ya mayar da ita gida.

Ummi kuwa ta razana da abun da raihan ya yi, ya bata mamaki sosai da sosai.

Wurin aiki ta wuce, sai dai kamar wadda ta samu matsalar ƙwaƙwalwa, haka take a yau, gaba ɗaya ta kasa sukuni, wai raihan ɗin da suke tare yake mata raha da ɗebe mata kewa, ya koma mata kamar wani baƙo, gaba ɗaya ya canza halinsa.

Wallahi i love you, hubban shadidan haka kalmomin nan suka din ga kaiwa suna komowa a kanta.

Wai ita raihan yake so, ko me ya gano oho masa.

A jejjere ya turo mata saƙonni ta SMS “Ina son ki”

“I love you”

“Ana uhubbiki” har da ɓoye wayar, tana rarraba ido.

Ta kashe wayar gaba ɗaya, har ta tashi ba ta sake kunna wayar ba, sai da ta je gida ta sanya caji, tayi salla ta zauna tana lazimi, noor ta shigo hannunta riƙe da jakarta ta makaranta.

“Mama, ya ki ke yawo da jakar makaranta?”

“Saƙo aka bani na baki” tayi maganar tana zuge jakar, ta ɗaukko wata leda ja da fara ta bawa ummi.

“Waye ya ce a bani?”

“Yaya raihan mana, ko headmaster zai iya wannan ne? Buɗe mu ga meye a ciki”

Ummi ta yi sak tana kallon noor.

“Ya ki ke kallona kuma?”

“A ina ya ganki?”

Noor ta ce “Nifa na gaya miki makarantar mu yake zuwa, ɗazu ma yazo buɗe mana mu gani, Allah ya sa kayan daɗi ne”

Ummi ta ce “Na shiga uku”

“Ni bani in buɗe kan ki fito daga ukun” ta fara bubbuɗe ledar.

Wata ƴar box ce a ciki, ja da wani jan turare mai heart, hoton da yayi mata a shagon dogwayen riguna ya sako a ciki, duk ya rubuta i love you da jan maker.

Kamar wadda ta ga abun tsoro haka take bin kayan da kallo.

“Yaya ummi, yaya raihan ya zama saurayinki kenan, Innalillahi yaya ummi wallahi yaya raihan kyakykyawa ne mai kirki, kin ga shikenan an daina yi miki gori muna jin haushi, amma wallahi kar ki gaya wa maama, kar ki gaya musu, amma dai shi zai yi miki kayan lefen ko, ya kawo akwatuna tun da yana da mota ko?”

Ummi ta tanƙwashe ƙafa, sam bata fuskantar abun da noor ke faɗa, manyan kwalayen chocolate ɗin da ke ciki, ta buɗe ta fara cin abun ta.

Ummi ta janyo wayarta, ta kunna, aikuwa messages ɗin sa suka cigaba da shigowa kamar sa fasa wayar.

“Tsarabar ki ce da na je italy, domin na ƙudurce idan na dawo, zan gaya miki abun da yake raina, ga sabon product ɗin turaren da na saya mana da shi zamu din ga using as a couples, ki yanke hukunci da wuri, daga yanzu zuwa kowane lokaci zan tunkari dr.”

“Dole in taka maka burki raihan, kafin ka janyo mini masifa”.

Noor ta ce “Masifar me? Dan Allah kar ki ce ya daina kawo mana chocolate da kayan daɗi”

“Mama Allah ya shiryeki”

Kai tsaye ta amsa mata da “Amin”

Hankalin farida baya jikinta, domin kuwa wannan satin za a ɗaurawa mijin inteesar aure, kullum cikin zuwa gidan take, kusan kullum cikin kuka da damuwa, ita ma rahama tana ta fama da miji, suna zaryar police station, ta ɗauki wayarsa ta duba ta tarar da ɓarnar da yake shukawa, ta kira budurwar ta ci mata mutunci, budurwar ta kira shi ta gaya masa, ya kamata yayi mata shegen duka, ya kumbura mata ido.

An ce a kashe auren, ya ce ba zai saketa ba.

Duk wannan pressure idan ta yi mata yawa, sai ta ƙare ta a kan ummi.

Raihan ya cigaba da tura mata saƙonni, masu ɗauke da irin tsantsar son da yake yi mata, sai dai ya ƙi kiranta a waya.

Ranar da amaryar inteesar zata tare, babu kowa a gidan, daga ita sai noor, dan haka ta kira shi.

Bugu ɗaya ya ɗaga wayar tare da yin sallama.

Ta amsa masa ta ce “Ya jikin?”

“Kin daina jin haushin nawa ne? Tun da ki ka tafi baki neme ni ba sai yanzu, ko kina shirya wani abun ne?”

“Ba faɗa na kira ka mu yi ba, ya jiki?”

“Ba sauƙi sweetheart tun da ba kya so na” yayi maganar cikin sigar shagwaɓa da sai da ƙirjinta ya ɗan buga.

“An sallameka ne?”

Ya ce “Eh, na koma bakin aiki ma”

“Ina son mu haɗu yau ne”

“Me zaki yi mini? Zaki karɓi soyayyata ne, ko kuma akasin haka?”

“Ka zo gida dai, ina son mu yi magana ne”

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Shikenan, zan zo in sha Allah” ta jinjina kai sannan ta katse wayar.

“Ka yi haƙuri raihan, yau nake son na kawo ƙarshen alaƙarmu, mussman iƙrarin soyayyar nan da ka ke yi, sai dai a wannan karon rabuwar kirki nake son mu yi, ba tare da na cutar da kai ba” tayi maganar tana kallon wayar.

Da la’asar ummi ta sanya ɗaya daga cikin dogwayen rigunan ta, har da saka jan baki da kwalli, tudun gashinta ya cika ƙeyarta, ta zauna zaman jiransa.

Ƙarfe biyar ya kira ta ya ce ya zo. Sai dai shi kansa yana mamakin ƙwarin gwiwar da ta sanya ummi kiransa gidansu.

Tuni noor ta riga ummi zuwa wurinsa, suka zauna suka din ga hira, dan ba wani ne ya gaya masa batun headmaster ba face noor, duk abun da ya tambayeta gaya masa take yi a kan ummi.

Tamkar wadda za ta fita tsirara, haka ummi ta din ga ƙumbiya-ƙumbiya, ta fito.

Kamar mai kallon tv, ya ƙureta da ido, takalmin ƙafarta na ta bayar da sautin ƙwas-ƙwas.

Noor ta ce “Bana gaya maka har kwalliya ta yi ba?”

Ta ƙarasa har in da yake ta zauna, ta ce “Sannu da zuwa”

Ya ce “Yauwwa”

“Kin yi mini kyau sosai da sosai yau ɗin nan, rigar ma kamar dan ke kawai aka yi ta, tubarkallah masha Allah, kwalliyar ma tayi miki kyau” ita dai tayi shiru tana nazari.

Noor kuwa tashi ta yi ta shiga cikin gida.

Ya tsiyayi lemon da noor ta kawo yana sha.

Ya numfasa ya ce “Gani, me zaki gaya mini?” Tayi shiru tana cigaba da jujjuya maganar a zuciyarta.

“Ko kunya ki ke ji ne?”

A hankali ta ce “Raihan”

“Ki ke kiran sunana haka babu ko kara? Ai yanzu ni ba ƙaninki bane ba”

Ta ce “Keep jokes aside please”

Ya ce “Ok, ina jin ki”

“Da farko ina neman afuwarka, saboda hanyar da na bi da farko dan mu rabu. Na sani ban kyauta maka ba, dan Allah ka yafe mini. Abu na gaba kuma na kira ka ne domin gyara kuskuren da na yi. Raihan kai mutum ne mai muhimmanci a wurina, kuma ba zan manta da soyayyar da ka yi mini ba, dan haka na kiraka mu tattauna, dan Allah sonake yau ta zama ranar da zaka cireni daga ranka mu rabu gaba ɗaya, idan na bari ka cigaba da so na zan cutar da kai”

Ta ɗaga kai ta ga ya ƙure ta da ido, sai kuma ta yi shiru, “Ina jinki cigaba” yayi maganar very serious fuskarsa tuni ta fara ja, ya fara sauya mata, zuwa ɗaya raihan ɗin da take tsoro.

“Dan Allah ka fahimce ni raihan, dan Allah ka rabu da ni daga yau, mu yanke alaƙa daga yanzu”

Dukan teburin gabansu yayi da ƙarfi da sai da ta razana ya ce “Never! So you just call me to hurt my feelings salma?”

“No, ba haka bane, ba zaka iya aurena ba raihan, dan Allah ka yi haƙuri”

Cikin zafin rai ya ce “Saboda me? Meye aibuna?”.

Ta girgiza kai ta ce “Baka da aibu, babu wanda zai kushe ka, nice nake da aibun, nice mai aibun raihan, bazawara ce ni na taɓa aure”

“Duk dan saboda ki rabu da ni, shi ne har da ƙarya?”

Tuni hawaye ya fara gangarowa daga idonta ta ce “Ba ƙarya nake yi ba, sirrina ne da ba kowa ya sani ba, sai makusanta na, an yi mini auren fari a ƙauye, ƴan watanni na yi auren ya mutu, na taɓa aure. Tarihina ba shi da wani ma’ana, babu lallai mutum mai daraja da cikakkiyar kamala kamar ka ya aureni. Na yi aure na tozarta, uwata ana iƙirarin ta kashe mahaifina, ana mini iƙirarin maita, idan aka zo aure dole ayi bincike, sakamakon binciken ba zai yi maka daɗi ba, ko kai ko ƴan uwanka. Wallahi ba ƙarya nake yi maka ba raihan, na taɓa aure bazawara ce ni.
Matashi ne kai, da yake tasowa yanzu ka nemo mace budurwa dai-dai da kai, ina yi maka fatan samun mace ta gari, amma dan Allah ka manta da ni”

Ko ƙifta idonsa bai yi ba, har ta gama maganar, sai da ta kammala tsaf, ba tare da ya ce mata uffan ba, ya tashi yayi tafiyar sa.

CUTARWA

31

Har raihan ya bar harabar gidan bayansa ummi take kallo, ko sau ɗaya bai waiwayo ba, ita kuma ba ta daina zubar da hawaye ba, gani take kamar kallon ƙarshe take yi masa, ba zai sake dawowa rayuwarta da sunan yana son ta ba.

Ta tashi jiki babu ƙwari, ta tafi ɗakinta, ta rufe ɗakin ta saka sakata, saboda kar noor ta zo ta isheta da surutu.

Ta zauna ta din ga kuka, ta ma rasa kukan me take yi.

Ta yi shiru tana tuno irin rayuwar auren da ta yi a gidan idiris, ta kasa manta irin wulaƙantar da ta yi a gidan idiris, irin tozarcin da ya yi mata, tamkar ya auri mushen dabba ba ɗan Adam ba, kuma ɗan Adam ɗin ma ƴar uwarsa.

Ta tuna yadda abokansa suke zunɗensa da angon ɗoɗɗoya, ba zata manta tonon asiri da wulaƙantarwar da Idiris yayi mata ba.

‘To idan kuma haryanzu ban warke ba fa’?” Ta tambayi kanta.

Ta dafe ƙirjinta tana zancen zuci, ita dai tun da Allah ya sa kawu yahaya ɗaukkota, yayi ta ƙoƙarin saya mata magunguna, cikin ikon Allah ba ta sake jin wannan matsalar ba, ko maƙiyinta ba ta fatan Allah ya haɗa shi da bala’in da yake cikin larurar sanyi.

Tun da farida ta dawo daga gidan inteesar, tamkar ita za ayi wa kishiya, kamar za ta yi hauka, domin kuwa da ita da wasu daga ƙannenta suka dawo gidan, suna ta bata haƙuri, a kan sai ta daure ita ma, idan ba haka ba inteesar ba zata kwantar hankalinta ba.

Sun cika falo suna mayar da yadda aka yi, noor kuma na ta kokowa da remote tana ƙara volume ɗin tv.

“Wai ke noor baki da hankali ne? Ba ni san meya samu yayarki Inteesar ba ne?”

Noor ta juyo ta kalli mai maganar ta ce “Mutuwa ta yi ne?”

“Wane irin mutuwa, ke ko gidan nata ma baki je ba, balle a haɗu a rarrasheta da ke, kina kallon mahaifiyarku hankalinta a tashe, ita ma can muka baro ta tana kuka, amma ke kina nan kina ƙure wa mutane kunne da ƙarar tv”

Noor ta taɓe baki ta ce “To tun da dai ba mutuwa tayi ba ai barkanta, wanda ba shi da kunya ai dole ayi masa kishiya, haka wata malama ta ce rannan a tv, na ce ashe saura maama”

“Ke uwar taki ki ke cewa ayi wa kishiya?”

Kausar ta ce “Mama hadiza, ki ƙyale yarinyar nan kar ta saka hawan jininki ya tashi, ba isasshen kai ne da ita ba, yanzu sai ta yi miki rashin kunya, kuma ba kowa ne ke zigata yana koya mata wannan iskancin ba, ban da ummi, idan ba haka ba ta yaya ɗa zai yi fatan a yi wa uwarsa kishiya, banda shashasha mara hankali”

“Ni dai ban saka da daƙiƙi a maganata ba, mutum ya bari ya fara gane karatu” kausar ta ja bakinta tayi shiru, idan ta cigaba da tankawa noor, sai noor ta kunyata ta a gaban mutane.

Nan kuma akalar hirar ta koma kan ci wa ummi mutunci, da ziga farida a kan lallai yakamata ummi ta bar mata gida, tun da ta tsofe a gidan babu aure.

Suka gama soko burutsunsu, suka bar gidan.

Ummi kusan kwanan zaune tayi, tayi ta salloli tana kaiwa Allah kukanta, wayarta kuwa ta dubata babu adadi, amma babu saƙon raihan ɗaya da ya sake shigowa cikin wayarta.

Ƙasan zuciyarta ya shiga tabattar mata da sun rabu da raihan kenan.

Bayan ta idar da sallar asuba, message  ya shigo wayarta, wani website da raihan ya saka ta shiga, ta yi submitting cv ɗin ta, an kira su screening ciki har da ita, wani sabon gidan talabijin da ba a daɗe da fara shirye-shirye a cikin sa ba.

Yau da safe aka ce su je wurin, ba ta ga saƙon ba sai yanzu, cikin sauri ta tashi ta haɗa credentials ɗin ta, agogo ta kalla, muddin ta ce za ta jira ta yi musu girki, to fa zata makara, dan haka ta dudduba jakunkunanta, ta samu kuɗi ta fito, ta turawa Abdul message na in da ta tafi.

Ko da ta je wurin ta tarar da mutane da yawa, haka nan ta fara bin layi ita ma, ta din ga duba wayarta tana tunanin raihan, shi ne mutum na farko da yakamata ta kira, ta sanar masa da an kirata screening, sai dai ba ta da wannan damar a yanzu.

“Dama na sani, babu lallai ka dawo gareni raihan, amma duk da haka ba zan ga laifinka ba, ina yi maka fatan alkhairi a duk in da ka ke”.

Farida tamkar ita aka yi wa kishiyar, ko bacci gagararta yayi, ta taso da nufin ta tarar da abincin safe, Abdul ya shigo ya sanar da ita saƙon ummi, tana fara zage-zagenta, ya fice ya bar mata falon.

Raihan yana zaune yana ta juyi a kan kujera a office ɗin sa, ya kasa taɓuka komai, ya juya kai nan ya juya kai can, in aka jima sai ya ciro wayarsa ya duba ya mayar ya ajiye.

Ya kifa kansa a kan teburin gabansa, yana jin yadda kansa yake masa wani irin zafi.

Jin motsin an buɗe ƙofa ya sanya shi ɗaga kai ya ga me shigowar, babu tsammani ya ga safiyya, tana sanye da doguwar riga straight gown, sai mayafinta a kafaɗa da jakarta, ta shigo bakinta ɗauke da sallama.

Ya amsa mata tare da mayar da kansa ya kifa.

“Yaya raihan, barka da rana?”

“Yauwwa sannu”

Ta nemi wuri ta zauna ta ce  “Gidan su wata ƙawata na je, a nan tsukin ne, na ce bari na biyo mu gaisa”

Yayi shiru bai ce mata komai ba.

“Are you ok?” Tayi maganar tana kai hannu goshinsa, ganin yana gumi duk da akwai sanyi a office ɗin.

Rau ta ji goshin nasa ya ɗau zafi, ta ce “Subhanallah, yaya raihan baka da lafiya ne? Jikinka zafi”

Ya ɗago a hankali ya ce “Safiya, ki tafi gida Please, ki ƙyale ni”

“Amma ya zan tafi na barka a wannan halin?”

Kallonta yake yi, yana tunanin dama ummi ce a zaune a gabansa take yi masa magana yanzu.

“Ki tafi na ce” yayi maganar a ɗan hasale, tare da jin haushin yadda ya ta tsare shi da ido, saɓanin ummi da ba ta iya ƙura masa ido haka, sai tana yi tana kawar da kai.

Safiyya ba ta fi shekaru goma sha tara ba, ummi ta girmeta sosai, sai dai shegen iyayi da rawar kai, duk in da ta zauna ba ta da aiki sai hira da samari a waya, ga shegiyar kwalliya kamar ƴar tsana.

Ta razana da tsawar da yayi mata, ta tashi da sauri, har ta kusa fita ya ce “Kar ki sake biyo ni office, office wurin aikina ne ba shirme ba” tayi sauri ta fice tana waiwayensa.

Ummi kuwa ta galabaita a ranar, dan bayan screening, aka ce su jira aka tura musu waɗanda suka yi nasara a waya, ciki har da ita, aka ce su jira ayi musu interview.

Kuɗin hannun ummi ba zasu kai ta ci abinci ba, ga yunwa ta isheta, haka nan suka cigaba da jira.

Ba a zo kan ummi ba, sai kusan biyar na yamma, da farko bayan shigarta studion aka fara yi mata interview, a ɗan tsorace take, ga yunwa tana ji, ɗaya daga cikin masu interview yana cewa masha Allah muryarta mai daɗi.

Ɗayan ya ce “Jin ta ya fi ganinta, wannan da radio ce irin su ne masu sauraro ke ɗokin gani”

Shugaban wurin ne ya shigo, ma’aikatan suka din ga gaishe shi, yana hura hanci, ya dubi ummi ya ce “Wannan fa?”

“Sir tana cikin wanda suka tsallake screening, interview ake yi mata”

“Wannan ɗin?”

“Eh sir”

“Dan Allah ku zaɓo wanda za su yi attracting ɗin mutane, ba wanda sai mun yi ta faman sanya filter muna fafutuka kan mu haska su ba, wannan shirin talabijin ne, ba na gidan rediyo ba!”

Tsit mutanen wurin suka yi, ba wannan ne karo na farko ba, amma a duk lokacin da aka yi mata, jin abun take kamar sabo, sum-sum, ta tattara kayanta, tayi waje, duk suka tsaya suna kallon ummi, shi kuma ko a jikinsa ya cigaba da maganar sa.

Ita ba ta san ma yadda aka yi ta isa gida ba, abubuwa daban-daban cunkus a ranta, ta ɗaukko gajiya da baƙin ciki, tana zuwa gida farida ta dira mata nata tashin hankalin.

“Raihan ka gani ko?, ka kori wanda zai aureni, kaima ka tafi ka bar ni, komai yayi mini zafi”

Tayi kuka-kuka iya yin ta, har ta gaji tayi shiru.

Ta wuni da yunwa, haka ta kwana da wata.

Kwanaki huɗu rabon raihan da ummi, yayi ƙoƙarin sanya abun da ta gaya masa a matsayin hujjar da za ta rabu da shi, amma shi sam bai ji hakan a matsayin hujja ba, dan damuwa yake ƙara shiga na rashin ta, ya zuba mata ido ya ga iya gudun ruwan ta, ko za ta neme shi, amma ya ji shiru.

Hakan ya sanya ya fara zargin anya ba da gaske take ba ta son sa ba, tun da ta iya gaya masa cewar su rabu, kwanaki huɗu amma ba ta sake nemansa ba, dan haka tsoro ya sake shiga zuciyar sa, ummi ba ta son sa.

Ƙasan zuciyarsa yana mamakin yadda ta ce masa ta taɓa aure, shi ba auren ta ne ya dame shi ba, meya kashe auren? A yadda ummi take har ace namiji ya sake ta?.

Daurewa yayi, ya sake bawa ummi kwana ɗaya, ya zamana kwanaki biyar, amma shiru ba ta neme shi ba.

Kwana na biyar, da yamma ya koma gidansu ummi, sai dai ya kira wayarta amma ba ta shiga.

Yana tsaye sai ga motar dr. Raihan ya risuna ya gaishe shi, dr. Ya amsa masa, yayi parking a waje, ya shiga cikin gida.

Raihan ya dudduba, mai gadin gidan ma baya nan, yayi ta kiran lambarta amma shiru ba ta shiga.

Ya samu wuri ya zauna a ƙofar gidan, yana cigaba da dannan wayarsa.

Dr. Ya sake fitowa,  ya ga raihan, ya kalli raihan ya ce “Yarona wa ka ke nema ne? Ko wurin Abdul ka zo?”

Raihan ya ce “A’a Abba, wurin Ummi na zo”

Dr. Ya ce “Too, ummi kuma lafiya dai ko?”

“Eh lafiya ƙalau, wurinta dai na zo, na kira wayarta ba ta shiga ne”

“Amma wani abun tayi maka ne?”

Ya girgiza kai ya ce “A’a, ba ta yi mini komai ba”

Dr. Ya jinjina kai ya ce “Yaron kirki, ai babu lallai ummi ta tsaya ta saurareka, a yanzu mijin aure ne ya dace ya zo wurinta, ba wanda za a yi soyayya ba kawai, wannan idan ba ku yi sa’anni ba, ba zaka girmeta da yawa ba.
Ka yi haƙuri ka ji ɗana.

Cikin girmamawa raihan ya ce “Abba ummi ta sanni, akwai alaƙa tsakani na da ita, wallahi abba ba ɓata mata lokaci zan yi ba, aurenta zai yi, ina son ta wallahi”.

Dr. Yayi shiru yana kallonsa, sannan ya yi murmushi ya ce “Meye matakin karatunka?”

“Na yi degree a ɓangaren Business administration, a ATBU”

“Idan da gaske ka ke zaka aureta, ranar lahadi ka turo mini mahaifinka mu yi magana da shi”

Raihan ya washe baki ya ce “To Abba, in sha Allah zan gaya masa, na gode sosai da sosai”

Dr. Yayi murmushi yayi gaba, a tunaninsa yayi maganin raihan, dan ya zata irin yaran nan ne marasa ji, amma duk da haka nutsuwa da kamalar raihan ɗin.

Raihan tafiya yayi yana murmushi, yana ganin abun kamar a mafarki, yau ya tsinci dami a kala, abun kamar a shirin film, wai ya tura Alhajinsa a nema masa aure? Kai tsaye gida ya tafi.

Sai dai ƙasan zuciyarsa yana tunanin, ummi za ta amince ko kuwa za ta cigaba da gardama ne? Dan ya ga kamar ta raina shi ne a matsayin mijin aure, yayi mata ƙanƙanta.

Yana zuwa ya tafi sashin Alhaji, dan kwanakin nan kusan kullum Alhajin yana gida, ya daki sa’a shikaɗai ya tarar a sashin nasa.

Alhaji Tahir ya gyara zaman tabaran sa, ya ce “Ya aka yi ne? Yanayin farinciki haɗe da damuwa a fuskar babban mutum”

Raihan ya je ya zauna a kusa da shi, ya ce “Kowanne akwai Alhaji”

“Bani labari”

Ya ciro wayarsa, ya nemo hoton ummi da yayi mata, lokacin da suka sayo dogwayen riguna, ya ce “Alhaji ka ga wannan”

Alhaji ya karɓi wayar, ya ƙare wa hoton kallo ya ce “Na gani, meyafaru?”

“Alhaji tana da kyau?”

Ya ce “Masha Allah, very beautiful kuwa, da gani kuma tana da kunya”

“Ita nake son aura Alhaji, zaka nema mini aurenta?”

Alhaji Tahir ya kalli raihan yayi murmushi ya ce “Babban mutum wannan ai matar manyan ce, anya ba ka yi tsaurin ido ba kuwa?”

“A’a Alhaji, ai nima babban mutum ne, dan Allah tayi? Wallahi mutuniyar kirki ce”

Alhaji ya yi shiru ya ce “Ai ni kallon sani nake yi mata ma”

Raihan ya ce “Eh, ƙawar maryam ce, amma ita ba ta girme ni ba, shekrunmu ɗaya da ita, kuma mutuniyar kirki ce ka tambayi Hajiya ma ka ji”

Alhaji Tahir ya dafa kafaɗar raihan ya ce “Easy my dear, in dai kana son ta tayi mini, za a nemi aurenta in dai za a bamu”

Raihan ya washe baki ya ce “Babanta ya ce ranar Sunday wai ka je ku yi magana, gani yake yi kamar ba aurenta zan yi ba, Alhaji tana bani shawarari masu kyau, tana da kirki sosai”

“Allah ya kaimu lahadin, zan je in sha Allah, ko a lokacin suka ce sai a ɗaura, Ubangiji Allah ya sa abokiyar zama ta gari ce”

Raihan ya sosa kai ya ce “Alhaji saura abu ɗaya”

“Ok to ina jinka”

Raihan ya ce “Dan Allah kar ka gaya wa mami sai maganar ta faɗa, ban san yadda za ta karɓi maganar ba.
I really have to marry her, Alhaji rayuwar ummi akwai ƙalubale da ban tausayi, dan Allah ka tsaya mini”

Alhaji Tahir ya jinjina kai ya ce “In dai ni ne ka san baka da matsala da ni, ko tsohuwa ka ce kana so, zan wuce maka gaba in dai tana da tarbiyya, kuma ko a hoto, ni yarinyar ban ga aibunta ba, ko ta girmeka in dai kana son ta shikenan, ai soyayya ba ƙarya ba ce raihan, mune muke barin al’ada na rage mana jin daɗin abun da addini ya halatta mana. Allah ya sanya alkhairi ango”

Raihan ya sunkuyar da kai yana murmushi, wani irin farinciki na ratsa zuciyarsa.

Dr. Ya manta da batun haɗuwarsa da raihan, dan ko ummi ma bai nema da maganar ba, sai dai ya rage ganin gilmawarta ko a gidan, ya bar hakan a wataƙila takurar farida ce ta saka ta ƙara takura kanta.

Washegari raihan ya tafi wurin aikin Ummi, amma manager ya ce “Ai ummi yau kusan kwana uku ba ta zo ba, ni ban sani ba, ba ta da lafiya ne ko ya aka yi ban sani ba, kawai ta ce mini za ta je screening, tun ranar ba ta sake zuwa ba, na zata ma ko ba ta gama ba ne ba”.

Raihan ya yi shiru ya ce “kira ta a waya ka ce ko ta dawo aiki, ko zaka koreta”.

Manager ya zare ido ya ce “Yayarta ka za a kora? Idan ban koreta ba ni ai yayana ya kore ni, ka san yadda yake yabawa ƙoƙarin ta, da yabawa amanarta”

Raihan ya ce “Dan Allah ka bar wannan maganar, kawai ni dai taimakon da zaka yi mini kenan, ka ce lallai ta dawo aiki.

“Ba zan yi ba, ba kun fi kusa ba”

Raihan ya sassauta murya ya ce “Haba manager, dan Allah ka taimaka Please”

“Da ka ce ba ka ji? Zan yi mata magana, amma ba dan halinka ba, kuma ba zan ce zan wani koreta ba, zan dai yi ƙoƙarin ta dawo ɗin”

Raihan yayi dariya ya ce “Allah ya bar mini manager”

Manager kawai yayi murmushi, ya cigaba da aikin da yakamata ace ummi ce ta yi.

Sai dai manager bai kai ga yin hakan ba, washegari sai ga ummin ta zo aiki, sai dai ta rame sosai, kallo ɗaya zaka yi mata ka san akwai tashin hankali a fuskar ta.

Manager ya kira raihan a waya, ya gaya masa ummi ta zo.

Bai ja dogon lokaci ba, ya daidaici lokacin tashin ta ya kusa, sannan ya tafi.

Ta fito daga wurin aikin, yana nesa kaɗan da ita yana kallonta, tana tafe a hankali kamar mara lafiya.

Zuwa yayi ya sha gabanta da motar, ta tsaya tana kallon motar, ya sauke glass ɗin motar suka haɗa ido, sai da ta ɗan razana, ya buɗe mata motar ba tare da ya ce mata uffan ba.

Jikin ummi ya yi sanyi sosai da ganin raihan, dan ba ta taɓa tsammani ba, kamar mai jin tsoro haka ta ɗosana ta shiga motar.

“Ta tabatta dai ba kya so na ko ummi? Kina iya rabuwa da ni, baki damu da halin da zan shiga ba, kin ce mu rabu, ko nema na baki sake yi ba, rashin muhimmancina har ya kai haka kenan ko Salma?” Ta girgiza masa kai alamar a’a.

“Shikenan, ni gashi na sake biyo ki ai, ranar lahadi Alhaji zai zo wurin dr.”

A razane ta kalleshi, tana ƙifta ido.

“Eh, mun haɗu da dr. Shekaranjiya, na zo wurinki kin ƙi ɗaga wayata, mun yi magana ya ce Alhaji ya zo su yi magana”

“Wai da gaske aurata zaka yi?” Tayi maganar cikin matuƙar rauni.

“Gashi ina gaya miki, kin zata da wasa nake yi? Na san wataƙila ba ni ne irin mijin da ki ke so ba, na san zaki ga na yi miki yarinta da yawa, amma har cikin raina nake jin zan iya aurenki na riƙe ki da kulawa da girmamawa”.

“Raihan zaka aureni ina bazawara”

“Kar ki sake kawo mini maganar kin taɓa aure, zuciyata zata fashe, ummi kina wasa da son da nake yi miki kina ganin kamar wasa ko? Hubban shadidan na kira shi, ban taɓa jin damuwa da takura a kan son wani abu ba kamar ke, kawai in ganki a kusa da ni, shi zai kawo mini cikakkiyar nutsuwa”

Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta.

“Meya rabaku da tsohon mijinki?”

Tayi ajiyar zuciya ta ce “Kakarmu ce ta haɗa auren, ba ya so na, an kai kuɗin aurensa aka fasa, shi ne ya aure ni”

Ya ce “Ya yi wa kansa, ni ina so. Ki saka aurenmu a addu’a salma, in sha Allah zai yi albarka, wata nawa ki ke so a saka na ji kin ce a matse ki ke ko?”

“Ai wannan maganar dr. Ba tawa ba”

Ya ce “Haka ne, nima na matsun ne, in ga kin zama tawa” ummi dai ta yi shiru tana tunanin ko dai ba da gaske raihan yake ba.

“Na ga gidan tv nan sun kira screening, manager ya ce mini kin je, ya ku ka yi da su?”

Ta ɗan rausayar da kai ta ce “Kyawawa suke so, ba wanda sai an ta saka musu filter ba”

“Kamar yaya kenan?”

“Haka mai wurin ya ce”

Kawai ta ga yayi parking ɗin motar, ya kalli ummi ya ce “Ke kuma ki ka ce masa me?”

Tayi shiru tana kallon sa.

“Magana nake yi miki?”

“Ni ban ce komai ba”

Raihan ya ce “Sai ki ka tsaya kina kuka ko? Gwanar kuka”

Ta ce “A’a ai ban yi kukan ba”

Ya danƙo kunnenta ya ce “Wallahi ummi, duk wanda ya kuma kushe mini ke, ki ka tsaya kina kallonsa, baki ɗau wani mataki ba, sai na huce a kan ki, kamar na fi ki jin takaici idan aka kushe mini ke. Ke kina da baki, amma ba zaki iya magana ba? Tun da ba aikin zai ɗauke ki ba, sai ki wanke shi tas ki bar wurin, atleast ai kya ce masa Allah ya sa kyawawan su durƙusar da tashar, ko ki ce masa ya koma islamiyya a karanta masa Allah ne mahalicci”

Sosai ya riƙe mata kunne, ta kai hannu ta riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunnen cikin muryarta mai cike da iyayi da shagwaɓa ta ce “Babba ne fa”

Ya sakar mata kunnen ya ce “Babban banza ba, tun da ba shi da hankali”

Sai kuma ya kwantar da murya ya ce “My wife”

Ta ce ‘Na shiga uku”

“A’a ko ɗaya baki shiga ba, ko ba ni ki ke so ba, dan Allah ki yi haƙuri mu karɓi ƙaddara a yadda ta zo mana, bamu san dalilin da Allah ya sa ya haɗa mu ba, kar taurin kanki yayi delaying zuwan wasu bayin Allah duniya” tayi burus kamar ba da ita yake magana ba.

“A haka kamar saliha, nan kuwa taurin kai a cikin ki kamar me”.

Ranar lahadi gaba ɗaya dr. Ya manta da batun zai yi baƙi, dan ya faɗi maganar ne dan ya kori raihan, ummi ma ta kasa zaune ta kasa tsaye, dan raihan ya tabattar mata da ranar lahadin Alhajinsu zai zo.

Ƙarfe sha ɗaya na safe, Abdul ya je ya sanarwa dr. Yayi baƙi.

Ya fita ya ga manyan mutane a manyan motoci, suka gaisa, Alhaji Tahir ya ce “Ka manta zaka yi baƙi ne? Kodayake ƴan boko sai kun bawa mutum lokaci yake zuwa, Tahir ne baban sirikinka Muhammad da ka ce kana son ganina”.

Dr. Ya ce “Subhanallah, Allah sarki bisimillah ku shigo”  suka bi bayan dr. Zuwa cikin gida.

Har cikin falo, ya fita da sauri ya samu Abdul ya bashi kuɗi, ya ce ya sayo musu ruwa da lemuka.

Sun daɗe suna hira da Alhaji Tahir, da wasu mutane su biyu ɗaya ƙaninsa ɗaya abokinsa.

Dr. Ya sha mamakin jin waye raihan, tare da yi wa ummi fatan, Allah ya sa ƙarshen wahalarta ne ya zo.

Nan Alhaji Tahir yake gaya wa dr. Tuni ya saka an gama yi masa bincike a kan ummi, kuma ya ji daɗin sakamakon binciken, dan haka ko yanzu aka ce su bayar da kuɗin aure dr. Ya yanka za su biya, idan kuma shima zai yi bincike a kan su tukuna shikenan.

Dr. Ya ce “Eh to, ina son a bani damar binciken tukuna, sannan kamar nan da sati biyu zan yi magana, saboda in kira wasu daga ƴan uwana a karɓi kuɗin auren”

Alhaji Tahir ya ce “Babu laifi, Allah ya kaimu”

Ba tare da wata alkunya ba, suka ci abin da dr. Ya gabatar musu, suka yi masa godiya suka tafi.

Farida ta din ga bin sa tana tambayarsa suwaye wannan baƙin, amma yaƙi gaya mata ko suwaye.

Ummi ta sha mamaki, ba ta zaci da gaske ba, sai da ta ga su Alhaji Tahir sun zo.

Alhaji Tahir ya koma gida, ya kira mami sashinsa, Hajiya na tare da shi, sai dai bai gaya mata ba ita ma, sai da Mami ta zo, ta tarar da su ta wani haɗe rai tana harare-harare.

Alhaji Tahir ya ce “To ke fa abun arzki ya same mu, ban sani ba ko mun yi laifi”

Mami ta ce “Meyafaru?”

“Babban mutum ya zo mini da magana, ya je zance an ritsa shi an ce in je in gabatar da kaina idan da gaske yake, dan yau ma daga can nake da ni da su Alhaji Hamza, nan da sati biyu zamu koma mu kai kuɗin aure”

“Ikon Allah, kuma shi ne ba a saka ni a maganar ba sai yanzu?”

Hajiya ta ce “Masha Allah lallai babban mutum an girma, Ubangiji Allah ya sa abokiyar arziki ce, Alhaji a ina take zan yi shishshigi”

Alhaji Tahir ya ce “Au kema babbar aminiyar ta sa bai gaya miki ba? Wai wata yarinya amm.. ammi ne sunan nata ne ko ummi ne, wai ƙawar maryam ce dai”.

Hajiya ta ce “Laaa ko dai Ummi, Ummi dai da suka yi islamiyya tare?”

Ya ce “Yes of course haka ya ce mini”

Cikin tsananin mamaki da takaici mami ta ce “What! Wannan kwazgwamar yarinyar baƙa ƙirin?”

Ayshercool

                        CUTARWA

32

Alhaji ya ce “Meye kuma na wata kwazgwamemiya baƙa? Ba mutum ba ce ba?”

“Ban gane ba mutum ba ce, ta girme shi fa ƙawar maryam ce?”

Ya ce “To shi ne me? Idan har shi zuciyarsa ta nutsu da ita ba shikenan ba, ni na yaba da tarbiyyar gidansu”

“Wallahi da sake, tun wuri ma dole a janye wannan maganar. Na zaɓa masa yarinya ya ƙi sai ya jajibo wannan mummunar yarinyar? Gidan da take zaune ai ba gidansu bane ba, zaman boranci ta yi a gidan kamar ƴar aiki”

“To kin ga kya samu lada ma, idan ya aureta ya kula da ita”

Kamar zata kama da wuta dan bala’i ta ce “Wallaahi ba zan lamunta ba, shi ne dan munafunci ni bai gaya mini ba, kawai sai yau ka zo mini da wannan zancen, a’a wallahi”

Alhaji ya ce “Ni dai in kin ga na fasa zancen auren nan, sai dai in shi ne ya dawo ya ce mini ya janye ya fasa, amma ba zan zama mutumin banza ba, shima sai dai in yi masa jagora ya je ya samu ubanta ya ce masa ya fasa”

Hajiya ta ce “Banda abun ki, ai ummi yarinyar kirki ce, nutsatsiyar yarinya ce, shi kyau ba shi ne abun dubawa ba, nagarta ake da cancanta ake dubawa”

“Kin ga malama ki rufa mini baki, ban saka da ke ba, idan nutsatsiya ce, ki haɗata da makakkun yaranki mana, sai ɗa na dama na san wannan duk kitumurmurarki ce, ke ki ka shirya wannan abun aka yi ban sani ba”

Hajiya ta ce “Allah ya baki haƙuri, nima ban san zancen ba sai yanzu, kuma su makakkun ƴaƴa ba laifi na yi wa Allah ya bani ba, jarrabawa ce, kuma da da nutsatstse a cikin su na yi sha’awar sanya ɗaya ya aureta”

Har mami za ta yi magana, Alhaji ya yi mata wani mugun kallo, hakan ya sanya ta yin shiru tana huci.

Hajiya kuwa tuni hawaye ya cika mata ido, tana jin zafin gori da cin mutunci da mami ke yi mata a kan yaranta, gani take yi kamar dabarar ta ce ta sanya Allah ya bata shiryayyun yara.

Alhaji ya kalli mami ya ce “Tun da kin saka mini mata kuka, sai ki bani wuri zan kula da ita”

Maganar ta sa ba ƙaramin fusata mami tayi ba, ta tashi ta ce “Haɗiyeta ƙarewar soyayya” tayi waje fuu rai a ɓace.

Ya dubi hajiya da hawayen fuskarta suka fara zubowa, ya rungumota jikinsa a hankali ya ce “You are brave woman, kar ki karaya, ki yi haƙuri ke ce fa mai Kwantar mini da hankali da rarrashina, ki yi haƙuri in sha Allah zaki ga tanadin da Allah ya yi miki sakamakon haƙuri”

Ɗan ƙara sautin kukan nata tayi, hawayenta ya ɓata masa riga, amma bai damu ba ya cigaba da rarrashin ta.

Kira uku raihan ya yi wa ummi sannan ta ɗaga, tayi masa sallama.

“Meyasa baki ɗaga ba, missed calls uku fa na yi miki”

“Ina aiki ne a kitchen, wayar tana ɗaki”

Raihan ya gyara kwanciyarsa ya ce “To ya ki ke sweetheart” wata irin kunya ce take kama ummi, idan ya ce
sweetheart ɗin nan, wai raihan ke ce mata sweetheart abun da kunya.

“Ba zaki amsa ba?”

“Ina lafiya” ta amsa a taƙaice.

“To yaya, su Alhaji sun zo ko? Na ga ya dawo ɗazu ina jiran ya kira ni ne”

A sanyaye ta ce “Eh sun zo”

“Yauwwa masha Allah, daga nan zuwa kowane lokaci zaki zama matata baby”

Ummi ta ce “Dan Allah ka din ga ce mini ummi kawai ko salma”

Raihan yayi murmushi ya ce “Ba kya son babyn saboda me? Ba daga bakin yaro kamata ki ke son ji ba ko? Kar ki yanke mini hukunci a yanzu, ina da kyakywan tanadi a kanki da rayuwarki ummi, zaki ji daɗin zama da ni sosai da sosai ki yi ta yi mana addu’a kin ji my Salma”.

Ta amsa masa da “To” amma tunanin yadda za ta yi rayuwar aure da raihan take yi, ita yanzu gaba ɗaya ma kunya yake bata.

Faɗowar mami afujajan ɗakin ya sanya shi tashi zaune, ya ce “Zan kira ki” sai dai kan ya katse wayar ta ce “Sannu shashasha, ni zaka je ka aurowa wannan mummunar yarinyar?” Kan ya katse wayar ummi ta ji me mami ta ce.

“Mami meyafaru ne?”

“Uwarka da ubanka ne suka faru, in ce maka ga safiyya ka aura amma ka yi burus, ka je ka kwaso wannan yarinyar uwar mata ka yi yaya da ita? Ta girmeka ba sa’arka ba kawai saboda baka da hankali ko dan ba ka da mafaɗi?”.

Raihan ya ce “Mami, dan Allah ki kwantar da hankalinki, duk fa ba abun ɗaga hankali bane ba. Ke ki ka gabatar mini da ita da kyawawan halayenta, na ji ina jin tausayinta. Ki ka kawo mini maganar aure na ga ita ta dace da ra’ayina, idan kowa ya ce ba zai aureta ba mummuna ce shikena sai ta rayu a haka, ba tausayawa babu kulawa?”

Rufe mini baki kan na daki bakin naka ya fashe, kai ne ɗan sarkin taimako, wani ya taimaketa mana a waje, ta girmeka ba sa’arka ba ce ba, ita ba ƴar uban kowa ba, kawai ka jajibo mana ita, to wallahi idan ma wannan matar ce ta zigaka dai-dai nake da ku. Kuma umarni nake ba ba shawara ba, ka je ka samu mahaifinku, ka janye wannan maganar da zancen auren nan da komai, dama ai ni na kawo maganar auren to safiyya na zaɓa maka, ita kuma ummin na san yadda zan yi da ita”

Cikin sauri ya ce “Dan Allah mami kar ki yi wa ummi komai, ni zaki yi wa ni na ce ina son ta, dan Allah kar ki sakata a damuwa, dan Allah mami ki yi haƙuri”

Galala ta saki baki tana kallon sa, “Au kar in sakata a damuwa? Har abun naka ya kai haka kenan? Dole na san abun yi”

Ta juya ta fita.

Ummi kuwa a hankali ta sauke wayar hannunta, fes abun da ta ji mami ya faɗa yake dawo mata, tabbas! Ta san a rina ta san zata fuskanci wannan ƙalubalen, tayi ta ƙoƙarin ankarar da raihan, amma bai gano ba, ta san yanayin mami ƴar ƙarya ce, mace ce mai iyayi da son nuna isa, ta san dama abu ne mai wuya mamin ta amince.

Dr. Ya yi sallama a ƙofar ɗakin ummi, ta amsa masa ya shiga, ya kalleta cikin farinciki da kulawa ya ce “Ummana, ke ashe ɗan manya ki ka samo mini siriki, ai ni gatse na yi wa saurayin naki, ganin yayi yarinta da yawa, na ce ya turo mini babansa ni na ma manta, kin ga sai ga su sun zo” Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tamkar ta ce wa dr. Dan Allah ya warware maganar.

“Alhamdilillah, ina jin labarin Alhaji Tahir ashe babban mutum ne, mutumin kirki ne, kamar ba mai kuɗi ba, yayi mini bayanin komai, na ɗeba musu sati biyu, zan ne na yi bincike a kansu da yaron, in dai lafiya ƙalau nan da sati biyu za su kawo kuɗin auren, Ubangiji Allah ya kusa kawo miki ƙarshen zaman gidan nan, Allah ya baku zaman lafiya, ya kawar da fitina.
Dama wani jinkirin alkhairi ne, ki kwantar da hankalinki ummi, kar ki ga yaro ne ƙarami, ki saka a ranki Allah ne ya duba ki, ya kawo miki miji.
Ita nagarta ba a shekaru take ba ko tarin dukiya, babban fatan Allah ya tabbattar da alkhairi, dama ke mai biyayya ce, dan haka ki ƙara dan sa’anki ne kar ki ce ba zaki bi shi ba, Allah ya sanya muku dukkan alkhairi”

Ummi a ranta ta ce “Ji kawu da wata magana, har da nasiha kamar an ɗaura auren, akwai ƙura fa’ sama-sama take jin sa, ya gama nasiharsa ya fice.

Farida kuwa har Abdul ta tambaya, ko ya san suwaye baƙin dr., Amma ya ce mata shi ma bai sani ba.

Bayanin da Alhaji ya yi wa raihan ne ya rage masa damuwar abubuwan da mami ta yi masa.

Ya ɗora da cewa “Mahaifiyarka ta fara tutsu, a kan ba ta san lamarin, idan har da gaske kana son yarinyar kana son tainakonta, ka tsaya a kan hakan, ka cigaba da addu’a, ni dai yarinyar ta yi mini, ban ga aibunta ba, wani muni wani waye hotonta da ka nuna mini ban gani ba, ban sani ba ko dan kana sonta ba ka ga munin bane ya sanya nima ban gani ba.

Ka je ka cigaba da shirye shiryen ka, a duba fili ɗaya ka gina abun ka yadda ka ke so, ba wata matsala in sha Allah”

Cikin girmamawa raihan ya ce “Na gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana”

“Amin babban mutum”

Hajiya ta yi sallama hannunta ɗauke da tray, da kayan shayi a kai.

Tana ganin raihan ta ce “In fara guɗa tun yanzu ne, ko in ɗan jira?”

Murmushi raihan ya yi yana sosa ƙeya.

Hajiya ta zauna tare da faɗin “To kai raihan daga ganin ummi, har ce maka fa na yi wa ina yi wa yayanka kamu, kawai sai ka lallaɓa”

Ya ce “Wallaahi hajiya tausayi take bani a lokacin, na din ga damunta har muka fara sabawa. Hajiya ummi na da matuƙar kirki da tarbiyya”

Hajiya ta ce “Sosai kam, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, na yi maka murna raihan, in dai mace ta gari ake nema, aka samu ummi to a gode Allah.
Sannan shekarun da ke tsakanin ku ba abun damuwa bane, shekaru lambobi ne kawai, ka riƙe ta ka kula da ita, ni dai ina son ta saboda Allah, tun tana zuwa gidan nan lokacin maryam tana nan, akwai ɗa’a da ladabi”

Raihan ya ce “Kuma wallahi ta iya girki sosai hajiya, ba ki ga yadda take bani abinci ba, ban taɓa cin abinci mai daɗin nata ba”

Alhaji ya dungure masa kai ya ce “Sannu ciki muka kawo duniya ” suka yi dariya gaba ɗaya, gaba ɗaya sai ya manta da damuwar da yake ciki.

Ummi na zaune na tilawar litattafanta na addini, wayarta ta fara ringing, baƙuwar lamba ce, tayi zaton ko raihan ne, dan akwai canza lambobi.

Sai dai tana kai wayar kunneta, tayi niyyar sallama, ta gimtse sallamar jin uwar ashariyar da aka lailayo mata.

“Sannu asararriya ƴar wahala, baƙin kunurci, saboda asara da taɓewa kana da rashin kyakykyawar makoma, ummi ki rasa wa zaki ce zaki aura sai ƙanina ummi, na yi dana sanin saninki, saboda kin zama guzuma muni yayi miki katutu shi ne ki ka yi wa ƙanina asiri, saboda zalamar abun duniya, to wallahi ummi ki kuka da kanki, ko ki janye wannan maganar ta auren raihan, ko kuma in ƙasƙanta ki a idon duniya, in muzantaki kin san zan iya”

Jikin ummi yayi sanyi matuƙa, ta kasa magana, har maryam ta yi tijararta a waya ta gama, ta kashe wayar, kamar shashasha ummi ta bi wayar da kallo.

Sweetheart, ki yi bacci cikin aminci da salama, zan so kiranki in ji muryar ki, amma na san wataƙila kin yi bacci, ki kula mini da kanki, ina son ki message ɗin raihan ya shigo wayarta.

Ta miƙe ta tafi gaban mudubin ɗakinta, tana ƙarewa kanta kallo.

‘to shi raihan ya aka yi baya ganin munina ne? A wajen ina munin nawa yake da yake ɓuya a idonsa baya gani?’.

Abu kamar wasa, mami ta sako raihan a gaba, ta daina amsa gaisuwar sa, ta daina shiga sabgarsa ta ce lallai sai ya je ya cewa Alhaji ya fasa auren nan.
Duk taurin kan ɗa, fushin uwa masifa ne, hakan ya sake jefa shi cikin damuwa da wasi-wasi, idan ta ce ya rabu da ummi, sai ya ji kamar ta ce ya raba jikinsa da rai.
Gefe Hajiya da Alhaji suna ta ƙarafafa masa gwiwa a kan auren ummi.

Ga lokacin kai kuɗi na cigaba da kusantowa, ga pressure office, ga ummi gaba ɗaya ta canza ta koma masa kamar wata baƙuwa, taƙi sakin jiki da shi, kamar ma ƙara nesanta kanta da shi take yi.

Yanayin aiki ya ƙara takura raihan, dan haka ko wurin aikin bai fiye samun damar binta ba, ga yawan barin ƙasar da yake yi.

Gefe guda maryam ta saka ummi a gaba da cin mutunci da zagi na cin zarafi kala-kala, ban da saƙonni da kuma barazana da take yi mata, ummi ta rasa in da za ta saka kanta, daga kuka sai addu’a, dan ta rasa yadda za ta yi da al’amarin gaba ɗaya.

Duk da mami ba ta shiga harkarsa, hakan ba ya hana shi zuwa in da take, da la’asar bayan ya dawo daga aiki, yayi niyyar zuwa yau ya je ya ga ummi, ya nufi sashin mami ya je ya tarar da maryam ta zo gidan.

Sanin halinta ya sanya ya tsuke fuska, dan ya san ba wai zuwan Allah da annabi ba ne ta yi shi haka.

“Mami barka da yamma” banza ta yi masa, daga baya kuma ta ce “Kar ka sake zuwa gaishe ni, muddin ba ka aiwatar da umarnin da na baka ba, bana buƙatar ganinka a sashina ma gaba ɗaya”

Maryam ta kalleshi ta ce “Wallaahi ka bayar da maza raihan, me aka yi aka yi ummi? Meye da ita meye abun burgewa a tare da ita? Sannan menene aibun Safiyya, amma na lura kamar ba a hayyacinka ka ke ba, wannan annakiyar baƙin zaka ɗaukko ka kawo mana mugun iri cikin family, wannan yarinyar da mujiya…..

“Dalla malama dakata!” Ya yi wa maryam tsawa.

“Islamiyyar da ki ka yi ba ta amfane ki da komai ba, da baki san daraja karramawar da Ubangiji ya yi wa ɗan Adam ba, ki tsaya iya matsayinki, idan mami tayi matsayinta ne, ke kuwa ko kusa ko a nesa ba ki da alaƙa da aurena, dan haka ki zuba ido idan zaki iya idan ba zaki iya ba ba zan juri cin zarafin matata ba, idan kin yi mata a baya ba ta da bakin ramawa, ni dai-dai nake da ke”

A tare suke shiga karanto “Innalillahi wa Innalillahi raji’un”

Mami ta ce “Au raihan har ta zama matarka ma ashe? Yanzu a gabana ka ke gaya wa ƴar uwarka haka saboda yarinyar da ba ka aureta ba ma? A wayance kana nuna mini babu gudu ba ja da baya kenan sai ka aureta” raihan ya yi shiru yana huci.

Maryam ta ce “Taɓɗijan, akwai ƙura mami, ita ma munafuka na kirata a waya ta ƙi magana, da yake ba ta da gaskiya, munafuka uwar son abun duniya, sumi-sumi da ita garin yayime-yayime na, na yayimo mana masifa”

Cewar ta kira ummi ya fi komai ɗaga masa hankali, ya san dole sai ta yi wa ummi rashin mutunci.

Juyawa yayi da sauri ya fice, ya tafi ɗakinsa ya sauya kaya, ya ɗau babur ɗin sa ya fita.

Gidansu ummi ya tafi, ya yi sa’a security yana nan, ya ce masa ya yi masa sallama da ummi.

Jin ana sallama da ita, ya sanya farida kallon ummi da take ta aiki a falo.

Farida ta kwaɓe baki, haka ma kausar, kausar ta ce “Ohh su mujiya an yi abun arziki, kowane mai tsautsayin ne? Na ga dai wancan tsohon ya ce ya fasa”

Farida ta ce “Oho dai, ni dai ayi a tattara a bar mini gida”

A gaggauce ummi ta gama, ta je ɗakinta ta shirya, ta fito harabar gidan, ya mayar da hankali a kan wayarsa yana dannawa.

Ƙamshin turaren wurinsa da take yi, ya sanya shi ɗagowa, ya zuba mata ido.

Duk ta yi wani iri, alamu sun bayyana ƙarara a cikin damuwa take.

“Sannu da zuwa” ta faɗa a hankali.

“Yauwwa, ya ki ke ya gidan?”

“Lafiya ƙalau” ta amsa tana murza yatsunta.

“Kwana biyu ayyuka sun yi mini yawa sosai ban samu na zo na ganki ba, zuciyata duk a takure”

Ita dai ummi ta yi masa gumm, taƙi magana.

“Yaya ummi” ya kirata da sunan da ya saba a baya.

Ta ɗago ta kalleshi, ya ce “Meyafaru ne? Duk kin canza mini, kamae an canza mini ke, meyafaru ne?”

Kamar ya soso mata in da yake yi mata ƙaiƙayi, ta ce “Dan Allah, ka taimaki rayuwata ka fasa auren nan raihan, wani ƙalubalen ne yake tinkaro ni, kamar ba zan iya ɗauka ba, Astagfirullah idan ka aureni kamar sabon babin ƙaddara zan buɗe, da alama kai kaɗai ka ke so na, gidanku ba zasu karɓe ni a matsayin sirika ba”

Ya jinjina kai ya ce “Eh, thank God tun da ina son ki ni, na san akwai ƙalubale, maryam na san ta kira ki, haka zalika na san mami kin ji abun da ta ce ranar, amma duk ba matsala ba ne ba. Salma ki canza rayuwarki ki koyi tsayawa a kan ra’ayinki da abun da ki ke so duk tsanani duk ƙalubale. Ke kin san ko mata huɗu na ce ina so za a bani a garin nan, amma na tsaya kai da fata na ce sai ke, ni meyasa zaki watsa mini ƙasa a ido? Ummi ba wasa nake yi ba da nake nanata miki ina son ki, ni kaina fa a cikin ƙalubalen nake, amma na ji zan jure saboda ke. Dan Allah ummi kema ki koyi tsayuwa a kan ra’ayinki ba ra’ayin wani ba, ita maryam ɗin waye ya hanata auren wanda take so, sai ke?
Dan Allah ki manta da wani ƙalubale mu tsara rayuwar mu, jarrabawa ba ta ƙarewa a rayuwar mumini.
Ai ki na so na ko? Tayi shiru tare da haɗe rai.

“Ba kya so na saboda na yi miki yarinta ko? Headmaster ki ke so?”

Ta ɗaga kai alamar eh.

“Ko gidan tsohon mijinki ki ke son komawa” yadda ya ga ta razana ne abun ya bashi mamaki.

Ya kawar da zancen ya ce “Ni a wani bugiren ki ka ajiye ni?”

Bai yi tsammanin za ta bashi amsa ba, ya ɗora da cewa “Ƙanin ki ko, wanda ki ka raina da aure?”

Zumɓura baki ta yi, tana juya ƙwayar idonta a hankali.

“Ummi wai meyake damunki ne? To mu yi hira ta yaya da ƙanwa kamar yadda muka saba”

Ta ce “To, ya gida ya office?” murmushin yayi ya ce “Ita ce hirar da ki ka fi so take yi miki daɗi kenan?”

Ta jinjina kai alamar eh.

“Office aiki ya yi yawa ba hutu”

“Ina su Yaya sagir? Kun shirya kuwa?”

Raihan ya ce “Mun shirya, amma ba ya kulani”

“To kai ka din ga kula shi mana ai kai ne ƙarami”

Ya ɗan shafi sajensa ya ce “Gayen nan ɗan wulaƙanci ne fiye da tunaninki, yanzu sai ya yarfa ni, har gara Salim wasu lokutan”

“Ai gani za su yi kamar idan suka sakar maka fuska zaka raina su, ka cigaba da jan su a jiki, kar ka nuna musu ƙyama saboda abun da suke yi watarana sai labari, ka gayyace su cikin ayyukan kamfaninku, ko ba ka sakar musu komai ba, ka ja su a jiki sosai”.

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Gaskiya ne, sai ma kin ga hajiya, ta fi bani tausayi wallahi, tana iya yin ta a kansu, amma kullum kamar ana tura su dawa, amma zan yi ƙoƙari in yi abun da ki ka ce in sha Allah”

“To Allah ya baka iko”

Ya amsa da amin, “Bari na je, zani wani wuri zo mu je ki karɓi saƙon ki”

Ya tashi ya yi gaba ta bi bayansa, a jikin babur ɗin sa suka tsaya, ya kalleta ya ce “Alhaji ya ce na zo na fara gini, a wace unguwar ki ke son mu zauna? Sannan wane irin gida ki ke so, flat ko mai bene?”

“Kowanne ka yi shikenan, Allah ya yassare”

“Salma kenan, haryanzu kina doubting idan ni zan aure ki, kuma ko zan iya riƙe ki, abun da muke shirin yi ba zunubi bane ba, hasali ma yana da asali a addinin musulunci, dan haka ki manta da batun al’ada da surutun mutane kin ji sweetheart”

Ta jinjina masa kai, tana wasa da hannun babur ɗin.

“Salma” ya kira sunanta a hankali, ta ɗaga ido ta kalle shi.

“Ina sonki sosai saboda Allah” tsigar jikinta ta tashi, ta kawar da idonta gefe.

“Ko sau ɗaya ki gaya mini wani abu mai daɗi da zai bani ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar neman aurenki, dan nima ina fuskantar ƙalubale”

Jiki a sanyaye ta ce “Dan Allah raihan ka yi abun da zaka zo ka cutu daga baya, ka ƙara tunani a kai”.

“Ni na riga na roƙi Allah a kan lamarin nan, kuma shi so baya bayar da ƙofar tunani, ba abu ne da yake bamu damar yin shawara ba, ki tausaya mini ummi” jikinta yayi sanyi, wani irin tausayin su ya kama ta.

“Ban san me zan ce ba, zan yi mana addu’a iya yi na, Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi”

Ya ce “Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum. Gobe in Allah ya kaimu ki yi mini girki dan Allah, zan biyo ta wurinku na ci”

“Me ka ke so” tayi maganar tana murmushi.

“Ke nake so”

Ta yamutsa fuska ta ce “Ina nufin me zaka ci?”

Yayi dariya ya ce “Abinci mana, ko me ki ka dafa zan ci da yardar Allah” yayi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa ya ce “Ki koma gida ki huta, duk da ban gama ganinki ba, zamu yi waya, dan Allah kar ki kashe waya kin ji baby”

Ta karɓi ledar ta juya tana murmushi.

Sabuwar waya dalleliya raihan ya gwangwaje ummi da ita, irin wayar da ba ta taɓa zaton zata riƙe irinta ba, bakinta ya ƙi rufuwa sai da ta kira shi ta yi tayi masa godiya, ya ce shi ba godiya yake so ba, kawai ta ce masa tana son sa shi zai sa ya ji daɗi ya tabbatar da ta ji daɗin kyautar da yayi mata.

Aikuwa ta yi gumm, ta kasa magana.

Da kuɗinta tayi cefane, washegari da safe ta sheƙa masa girki, bai kira ta a waya ba, sai fita tayi ta ganshi a waje yana jiranta.

Suna tafe yana yi mata normal hira, tare da nuna mata yadda za ta yi amfani da wayar da ya saya mata.

A mota ya ci abinci, yana ci yana yi mata hira, ta buɗe ruwa ta bashi, ta duba jakarta ta ɗaukko tissue, ta warwro masa ta bashi ya goge hannu.

Yayi murmushi ya ce “Ka ga mace ta gari, ta fara aikinta tun yanzu”.

Ta haɗa kan kwanukan ta ta ce masa “Sai anjima, Allah ya kiyaye”

“Amin ya rabb, yakamata mu koma ayi siyayya, mayukan nan kamar sun karɓe ki, na ga kina ta glowing”

Da sauri ta ce “Fari na yi?”

“A’a kyau ki ka ƙara, ban sani ba ko idona ne”

“Kar ka saka mu makara, sai anjima” ta fice daga motar, ya zuba mata ido, har ta shige shagonsu, sannan ya ja motar ya tafi.

Duk wata hanya da mami za ta bi, ta rusa maganar auren raihan, abu ya gagara ta kaɗa ta raya, amma raihan ya dage, ya samu goyon baya ɗari.

Dr. Ya sanar da su kawu Ilyasu, zai karɓi kuɗin auren ummi, dan haka mutum biyu daga cikin su su zo ranar juma’a.
Hatta kayan soye-soye da zai karɓi baƙi, daga waje ya yi order abun sa, dan sai saura ƴan kwanaki, sannan ya gaya wa farida.

Farida ko a jikinta, tana ganinsa yana ta shige da ficensa shikaɗai, ya shirya komai.

Kafin sallar juma’a, su kawu Ilyasu suka zo gidan, bayan sallar juma’a, su Alhaji Tahir suka zo.

Bayan gama tattaunawar da duk yakamata, dr. Ya gabatar da su kawu Ilyasu ga su Alhaji Tahir, tare da gaya musu matakin karatun ummi, tare da tabattar musu da binciken da yayi a kan Raihan, bai samu wata matsala ba.

Alhaji Tahir ya sake gabatar da kansa ga su kawu Ilyasu.

Sannan ya kalli dr. Ya ce “Ban sani ba ko kun yanke kuɗin aurenta da sadakin?”

Dr. Ya ce “A’a, duk abun da Allah ya sa ku ka bayar, zamu karɓa fatanmu ubangiji Allah ya sanya alkhairi”

Alhaji Tahir ya jinjina kai, sannan ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye kuɗi dami guda a tsakiyar falon, ya ce “Ga su nan, dubu ɗari biyar ne, mun saka watanni huɗu idan Allah ya sa zamu gani, amma idan kuna ganin mun saka da yawa kuna iya ragewa”.

Dr. Yayi murmushi ya ce “Bamu nemi ƙari ba ma nemi ragi? Allah ya nuna mana”

Kawu Ilyasu ya ce “Amma ranka ya daɗe har naira dubu ɗari biyar, kun kuwa san yarinyar nan bazawara ce? Kuma auren da ba a tsauwwala almubazzaranci ba yafi albarka, bazawara ce ta taɓa aure shekarun baya”.

Ayshercool

CUTARWA

32

Alhaji ya ce “Meye kuma na wata kwazgwamemiya baƙa? Ba mutum ba ce ba?”

“Ban gane ba mutum ba ce, ta girme shi fa ƙawar maryam ce?”

Ya ce “To shi ne me? Idan har shi zuciyarsa ta nutsu da ita ba shikenan ba, ni na yaba da tarbiyyar gidansu”

“Wallahi da sake, tun wuri ma dole a janye wannan maganar. Na zaɓa masa yarinya ya ƙi sai ya jajibo wannan mummunar yarinyar? Gidan da take zaune ai ba gidansu bane ba, zaman boranci ta yi a gidan kamar ƴar aiki”

“To kin ga kya samu lada ma, idan ya aureta ya kula da ita”

Kamar zata kama da wuta dan bala’i ta ce “Wallaahi ba zan lamunta ba, shi ne dan munafunci ni bai gaya mini ba, kawai sai yau ka zo mini da wannan zancen, a’a wallahi”

Alhaji ya ce “Ni dai in kin ga na fasa zancen auren nan, sai dai in shi ne ya dawo ya ce mini ya janye ya fasa, amma ba zan zama mutumin banza ba, shima sai dai in yi masa jagora ya je ya samu ubanta ya ce masa ya fasa”

Hajiya ta ce “Banda abun ki, ai ummi yarinyar kirki ce, nutsatsiyar yarinya ce, shi kyau ba shi ne abun dubawa ba, nagarta ake da cancanta ake dubawa”

“Kin ga malama ki rufa mini baki, ban saka da ke ba, idan nutsatsiya ce, ki haɗata da makakkun yaranki mana, sai ɗa na dama na san wannan duk kitumurmurarki ce, ke ki ka shirya wannan abun aka yi ban sani ba”

Hajiya ta ce “Allah ya baki haƙuri, nima ban san zancen ba sai yanzu, kuma su makakkun ƴaƴa ba laifi na yi wa Allah ya bani ba, jarrabawa ce, kuma da da nutsatstse a cikin su na yi sha’awar sanya ɗaya ya aureta”

Har mami za ta yi magana, Alhaji ya yi mata wani mugun kallo, hakan ya sanya ta yin shiru tana huci.

Hajiya kuwa tuni hawaye ya cika mata ido, tana jin zafin gori da cin mutunci da mami ke yi mata a kan yaranta, gani take yi kamar dabarar ta ce ta sanya Allah ya bata shiryayyun yara.

Alhaji ya kalli mami ya ce “Tun da kin saka mini mata kuka, sai ki bani wuri zan kula da ita”

Maganar ta sa ba ƙaramin fusata mami tayi ba, ta tashi ta ce “Haɗiyeta ƙarewar soyayya” tayi waje fuu rai a ɓace.

Ya dubi hajiya da hawayen fuskarta suka fara zubowa, ya rungumota jikinsa a hankali ya ce “You are brave woman, kar ki karaya, ki yi haƙuri ke ce fa mai Kwantar mini da hankali da rarrashina, ki yi haƙuri in sha Allah zaki ga tanadin da Allah ya yi miki sakamakon haƙuri”

Ɗan ƙara sautin kukan nata tayi, hawayenta ya ɓata masa riga, amma bai damu ba ya cigaba da rarrashin ta.

Kira uku raihan ya yi wa ummi sannan ta ɗaga, tayi masa sallama.

“Meyasa baki ɗaga ba, missed calls uku fa na yi miki”

“Ina aiki ne a kitchen, wayar tana ɗaki”

Raihan ya gyara kwanciyarsa ya ce “To ya ki ke sweetheart” wata irin kunya ce take kama ummi, idan ya ce
sweetheart ɗin nan, wai raihan ke ce mata sweetheart abun da kunya.

“Ba zaki amsa ba?”

“Ina lafiya” ta amsa a taƙaice.

“To yaya, su Alhaji sun zo ko? Na ga ya dawo ɗazu ina jiran ya kira ni ne”

A sanyaye ta ce “Eh sun zo”

“Yauwwa masha Allah, daga nan zuwa kowane lokaci zaki zama matata baby”

Ummi ta ce “Dan Allah ka din ga ce mini ummi kawai ko salma”

Raihan yayi murmushi ya ce “Ba kya son babyn saboda me? Ba daga bakin yaro kamata ki ke son ji ba ko? Kar ki yanke mini hukunci a yanzu, ina da kyakywan tanadi a kanki da rayuwarki ummi, zaki ji daɗin zama da ni sosai da sosai ki yi ta yi mana addu’a kin ji my Salma”.

Ta amsa masa da “To” amma tunanin yadda za ta yi rayuwar aure da raihan take yi, ita yanzu gaba ɗaya ma kunya yake bata.

Faɗowar mami afujajan ɗakin ya sanya shi tashi zaune, ya ce “Zan kira ki” sai dai kan ya katse wayar ta ce “Sannu shashasha, ni zaka je ka aurowa wannan mummunar yarinyar?” Kan ya katse wayar ummi ta ji me mami ta ce.

“Mami meyafaru ne?”

“Uwarka da ubanka ne suka faru, in ce maka ga safiyya ka aura amma ka yi burus, ka je ka kwaso wannan yarinyar uwar mata ka yi yaya da ita? Ta girmeka ba sa’arka ba kawai saboda baka da hankali ko dan ba ka da mafaɗi?”.

Raihan ya ce “Mami, dan Allah ki kwantar da hankalinki, duk fa ba abun ɗaga hankali bane ba. Ke ki ka gabatar mini da ita da kyawawan halayenta, na ji ina jin tausayinta. Ki ka kawo mini maganar aure na ga ita ta dace da ra’ayina, idan kowa ya ce ba zai aureta ba mummuna ce shikena sai ta rayu a haka, ba tausayawa babu kulawa?”

Rufe mini baki kan na daki bakin naka ya fashe, kai ne ɗan sarkin taimako, wani ya taimaketa mana a waje, ta girmeka ba sa’arka ba ce ba, ita ba ƴar uban kowa ba, kawai ka jajibo mana ita, to wallahi idan ma wannan matar ce ta zigaka dai-dai nake da ku. Kuma umarni nake ba ba shawara ba, ka je ka samu mahaifinku, ka janye wannan maganar da zancen auren nan da komai, dama ai ni na kawo maganar auren to safiyya na zaɓa maka, ita kuma ummin na san yadda zan yi da ita”

Cikin sauri ya ce “Dan Allah mami kar ki yi wa ummi komai, ni zaki yi wa ni na ce ina son ta, dan Allah kar ki sakata a damuwa, dan Allah mami ki yi haƙuri”

Galala ta saki baki tana kallon sa, “Au kar in sakata a damuwa? Har abun naka ya kai haka kenan? Dole na san abun yi”

Ta juya ta fita.

Ummi kuwa a hankali ta sauke wayar hannunta, fes abun da ta ji mami ya faɗa yake dawo mata, tabbas! Ta san a rina ta san zata fuskanci wannan ƙalubalen, tayi ta ƙoƙarin ankarar da raihan, amma bai gano ba, ta san yanayin mami ƴar ƙarya ce, mace ce mai iyayi da son nuna isa, ta san dama abu ne mai wuya mamin ta amince.

Dr. Ya yi sallama a ƙofar ɗakin ummi, ta amsa masa ya shiga, ya kalleta cikin farinciki da kulawa ya ce “Ummana, ke ashe ɗan manya ki ka samo mini siriki, ai ni gatse na yi wa saurayin naki, ganin yayi yarinta da yawa, na ce ya turo mini babansa ni na ma manta, kin ga sai ga su sun zo” Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tamkar ta ce wa dr. Dan Allah ya warware maganar.

“Alhamdilillah, ina jin labarin Alhaji Tahir ashe babban mutum ne, mutumin kirki ne, kamar ba mai kuɗi ba, yayi mini bayanin komai, na ɗeba musu sati biyu, zan ne na yi bincike a kansu da yaron, in dai lafiya ƙalau nan da sati biyu za su kawo kuɗin auren, Ubangiji Allah ya kusa kawo miki ƙarshen zaman gidan nan, Allah ya baku zaman lafiya, ya kawar da fitina.
Dama wani jinkirin alkhairi ne, ki kwantar da hankalinki ummi, kar ki ga yaro ne ƙarami, ki saka a ranki Allah ne ya duba ki, ya kawo miki miji.
Ita nagarta ba a shekaru take ba ko tarin dukiya, babban fatan Allah ya tabbattar da alkhairi, dama ke mai biyayya ce, dan haka ki ƙara dan sa’anki ne kar ki ce ba zaki bi shi ba, Allah ya sanya muku dukkan alkhairi”

Ummi a ranta ta ce “Ji kawu da wata magana, har da nasiha kamar an ɗaura auren, akwai ƙura fa’ sama-sama take jin sa, ya gama nasiharsa ya fice.

Farida kuwa har Abdul ta tambaya, ko ya san suwaye baƙin dr., Amma ya ce mata shi ma bai sani ba.

Bayanin da Alhaji ya yi wa raihan ne ya rage masa damuwar abubuwan da mami ta yi masa.

Ya ɗora da cewa “Mahaifiyarka ta fara tutsu, a kan ba ta san lamarin, idan har da gaske kana son yarinyar kana son tainakonta, ka tsaya a kan hakan, ka cigaba da addu’a, ni dai yarinyar ta yi mini, ban ga aibunta ba, wani muni wani waye hotonta da ka nuna mini ban gani ba, ban sani ba ko dan kana sonta ba ka ga munin bane ya sanya nima ban gani ba.

Ka je ka cigaba da shirye shiryen ka, a duba fili ɗaya ka gina abun ka yadda ka ke so, ba wata matsala in sha Allah”

Cikin girmamawa raihan ya ce “Na gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana”

“Amin babban mutum”

Hajiya ta yi sallama hannunta ɗauke da tray, da kayan shayi a kai.

Tana ganin raihan ta ce “In fara guɗa tun yanzu ne, ko in ɗan jira?”

Murmushi raihan ya yi yana sosa ƙeya.

Hajiya ta zauna tare da faɗin “To kai raihan daga ganin ummi, har ce maka fa na yi wa ina yi wa yayanka kamu, kawai sai ka lallaɓa”

Ya ce “Wallaahi hajiya tausayi take bani a lokacin, na din ga damunta har muka fara sabawa. Hajiya ummi na da matuƙar kirki da tarbiyya”

Hajiya ta ce “Sosai kam, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, na yi maka murna raihan, in dai mace ta gari ake nema, aka samu ummi to a gode Allah.
Sannan shekarun da ke tsakanin ku ba abun damuwa bane, shekaru lambobi ne kawai, ka riƙe ta ka kula da ita, ni dai ina son ta saboda Allah, tun tana zuwa gidan nan lokacin maryam tana nan, akwai ɗa’a da ladabi”

Raihan ya ce “Kuma wallahi ta iya girki sosai hajiya, ba ki ga yadda take bani abinci ba, ban taɓa cin abinci mai daɗin nata ba”

Alhaji ya dungure masa kai ya ce “Sannu ciki muka kawo duniya ” suka yi dariya gaba ɗaya, gaba ɗaya sai ya manta da damuwar da yake ciki.

Ummi na zaune na tilawar litattafanta na addini, wayarta ta fara ringing, baƙuwar lamba ce, tayi zaton ko raihan ne, dan akwai canza lambobi.

Sai dai tana kai wayar kunneta, tayi niyyar sallama, ta gimtse sallamar jin uwar ashariyar da aka lailayo mata.

“Sannu asararriya ƴar wahala, baƙin kunurci, saboda asara da taɓewa kana da rashin kyakykyawar makoma, ummi ki rasa wa zaki ce zaki aura sai ƙanina ummi, na yi dana sanin saninki, saboda kin zama guzuma muni yayi miki katutu shi ne ki ka yi wa ƙanina asiri, saboda zalamar abun duniya, to wallahi ummi ki kuka da kanki, ko ki janye wannan maganar ta auren raihan, ko kuma in ƙasƙanta ki a idon duniya, in muzantaki kin san zan iya”

Jikin ummi yayi sanyi matuƙa, ta kasa magana, har maryam ta yi tijararta a waya ta gama, ta kashe wayar, kamar shashasha ummi ta bi wayar da kallo.

Sweetheart, ki yi bacci cikin aminci da salama, zan so kiranki in ji muryar ki, amma na san wataƙila kin yi bacci, ki kula mini da kanki, ina son ki message ɗin raihan ya shigo wayarta.

Ta miƙe ta tafi gaban mudubin ɗakinta, tana ƙarewa kanta kallo.

‘to shi raihan ya aka yi baya ganin munina ne? A wajen ina munin nawa yake da yake ɓuya a idonsa baya gani?’.

Abu kamar wasa, mami ta sako raihan a gaba, ta daina amsa gaisuwar sa, ta daina shiga sabgarsa ta ce lallai sai ya je ya cewa Alhaji ya fasa auren nan.
Duk taurin kan ɗa, fushin uwa masifa ne, hakan ya sake jefa shi cikin damuwa da wasi-wasi, idan ta ce ya rabu da ummi, sai ya ji kamar ta ce ya raba jikinsa da rai.
Gefe Hajiya da Alhaji suna ta ƙarafafa masa gwiwa a kan auren ummi.

Ga lokacin kai kuɗi na cigaba da kusantowa, ga pressure office, ga ummi gaba ɗaya ta canza ta koma masa kamar wata baƙuwa, taƙi sakin jiki da shi, kamar ma ƙara nesanta kanta da shi take yi.

Yanayin aiki ya ƙara takura raihan, dan haka ko wurin aikin bai fiye samun damar binta ba, ga yawan barin ƙasar da yake yi.

Gefe guda maryam ta saka ummi a gaba da cin mutunci da zagi na cin zarafi kala-kala, ban da saƙonni da kuma barazana da take yi mata, ummi ta rasa in da za ta saka kanta, daga kuka sai addu’a, dan ta rasa yadda za ta yi da al’amarin gaba ɗaya.

Duk da mami ba ta shiga harkarsa, hakan ba ya hana shi zuwa in da take, da la’asar bayan ya dawo daga aiki, yayi niyyar zuwa yau ya je ya ga ummi, ya nufi sashin mami ya je ya tarar da maryam ta zo gidan.

Sanin halinta ya sanya ya tsuke fuska, dan ya san ba wai zuwan Allah da annabi ba ne ta yi shi haka.

“Mami barka da yamma” banza ta yi masa, daga baya kuma ta ce “Kar ka sake zuwa gaishe ni, muddin ba ka aiwatar da umarnin da na baka ba, bana buƙatar ganinka a sashina ma gaba ɗaya”

Maryam ta kalleshi ta ce “Wallaahi ka bayar da maza raihan, me aka yi aka yi ummi? Meye da ita meye abun burgewa a tare da ita? Sannan menene aibun Safiyya, amma na lura kamar ba a hayyacinka ka ke ba, wannan annakiyar baƙin zaka ɗaukko ka kawo mana mugun iri cikin family, wannan yarinyar da mujiya…..

“Dalla malama dakata!” Ya yi wa maryam tsawa.

“Islamiyyar da ki ka yi ba ta amfane ki da komai ba, da baki san daraja karramawar da Ubangiji ya yi wa ɗan Adam ba, ki tsaya iya matsayinki, idan mami tayi matsayinta ne, ke kuwa ko kusa ko a nesa ba ki da alaƙa da aurena, dan haka ki zuba ido idan zaki iya idan ba zaki iya ba ba zan juri cin zarafin matata ba, idan kin yi mata a baya ba ta da bakin ramawa, ni dai-dai nake da ke”

A tare suke shiga karanto “Innalillahi wa Innalillahi raji’un”

Mami ta ce “Au raihan har ta zama matarka ma ashe? Yanzu a gabana ka ke gaya wa ƴar uwarka haka saboda yarinyar da ba ka aureta ba ma? A wayance kana nuna mini babu gudu ba ja da baya kenan sai ka aureta” raihan ya yi shiru yana huci.

Maryam ta ce “Taɓɗijan, akwai ƙura mami, ita ma munafuka na kirata a waya ta ƙi magana, da yake ba ta da gaskiya, munafuka uwar son abun duniya, sumi-sumi da ita garin yayime-yayime na, na yayimo mana masifa”

Cewar ta kira ummi ya fi komai ɗaga masa hankali, ya san dole sai ta yi wa ummi rashin mutunci.

Juyawa yayi da sauri ya fice, ya tafi ɗakinsa ya sauya kaya, ya ɗau babur ɗin sa ya fita.

Gidansu ummi ya tafi, ya yi sa’a security yana nan, ya ce masa ya yi masa sallama da ummi.

Jin ana sallama da ita, ya sanya farida kallon ummi da take ta aiki a falo.

Farida ta kwaɓe baki, haka ma kausar, kausar ta ce “Ohh su mujiya an yi abun arziki, kowane mai tsautsayin ne? Na ga dai wancan tsohon ya ce ya fasa”

Farida ta ce “Oho dai, ni dai ayi a tattara a bar mini gida”

A gaggauce ummi ta gama, ta je ɗakinta ta shirya, ta fito harabar gidan, ya mayar da hankali a kan wayarsa yana dannawa.

Ƙamshin turaren wurinsa da take yi, ya sanya shi ɗagowa, ya zuba mata ido.

Duk ta yi wani iri, alamu sun bayyana ƙarara a cikin damuwa take.

“Sannu da zuwa” ta faɗa a hankali.

“Yauwwa, ya ki ke ya gidan?”

“Lafiya ƙalau” ta amsa tana murza yatsunta.

“Kwana biyu ayyuka sun yi mini yawa sosai ban samu na zo na ganki ba, zuciyata duk a takure”

Ita dai ummi ta yi masa gumm, taƙi magana.

“Yaya ummi” ya kirata da sunan da ya saba a baya.

Ta ɗago ta kalleshi, ya ce “Meyafaru ne? Duk kin canza mini, kamae an canza mini ke, meyafaru ne?”

Kamar ya soso mata in da yake yi mata ƙaiƙayi, ta ce “Dan Allah, ka taimaki rayuwata ka fasa auren nan raihan, wani ƙalubalen ne yake tinkaro ni, kamar ba zan iya ɗauka ba, Astagfirullah idan ka aureni kamar sabon babin ƙaddara zan buɗe, da alama kai kaɗai ka ke so na, gidanku ba zasu karɓe ni a matsayin sirika ba”

Ya jinjina kai ya ce “Eh, thank God tun da ina son ki ni, na san akwai ƙalubale, maryam na san ta kira ki, haka zalika na san mami kin ji abun da ta ce ranar, amma duk ba matsala ba ne ba. Salma ki canza rayuwarki ki koyi tsayawa a kan ra’ayinki da abun da ki ke so duk tsanani duk ƙalubale. Ke kin san ko mata huɗu na ce ina so za a bani a garin nan, amma na tsaya kai da fata na ce sai ke, ni meyasa zaki watsa mini ƙasa a ido? Ummi ba wasa nake yi ba da nake nanata miki ina son ki, ni kaina fa a cikin ƙalubalen nake, amma na ji zan jure saboda ke. Dan Allah ummi kema ki koyi tsayuwa a kan ra’ayinki ba ra’ayin wani ba, ita maryam ɗin waye ya hanata auren wanda take so, sai ke?
Dan Allah ki manta da wani ƙalubale mu tsara rayuwar mu, jarrabawa ba ta ƙarewa a rayuwar mumini.
Ai ki na so na ko? Tayi shiru tare da haɗe rai.

“Ba kya so na saboda na yi miki yarinta ko? Headmaster ki ke so?”

Ta ɗaga kai alamar eh.

“Ko gidan tsohon mijinki ki ke son komawa” yadda ya ga ta razana ne abun ya bashi mamaki.

Ya kawar da zancen ya ce “Ni a wani bugiren ki ka ajiye ni?”

Bai yi tsammanin za ta bashi amsa ba, ya ɗora da cewa “Ƙanin ki ko, wanda ki ka raina da aure?”

Zumɓura baki ta yi, tana juya ƙwayar idonta a hankali.

“Ummi wai meyake damunki ne? To mu yi hira ta yaya da ƙanwa kamar yadda muka saba”

Ta ce “To, ya gida ya office?” murmushin yayi ya ce “Ita ce hirar da ki ka fi so take yi miki daɗi kenan?”

Ta jinjina kai alamar eh.

“Office aiki ya yi yawa ba hutu”

“Ina su Yaya sagir? Kun shirya kuwa?”

Raihan ya ce “Mun shirya, amma ba ya kulani”

“To kai ka din ga kula shi mana ai kai ne ƙarami”

Ya ɗan shafi sajensa ya ce “Gayen nan ɗan wulaƙanci ne fiye da tunaninki, yanzu sai ya yarfa ni, har gara Salim wasu lokutan”

“Ai gani za su yi kamar idan suka sakar maka fuska zaka raina su, ka cigaba da jan su a jiki, kar ka nuna musu ƙyama saboda abun da suke yi watarana sai labari, ka gayyace su cikin ayyukan kamfaninku, ko ba ka sakar musu komai ba, ka ja su a jiki sosai”.

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Gaskiya ne, sai ma kin ga hajiya, ta fi bani tausayi wallahi, tana iya yin ta a kansu, amma kullum kamar ana tura su dawa, amma zan yi ƙoƙari in yi abun da ki ka ce in sha Allah”

“To Allah ya baka iko”

Ya amsa da amin, “Bari na je, zani wani wuri zo mu je ki karɓi saƙon ki”

Ya tashi ya yi gaba ta bi bayansa, a jikin babur ɗin sa suka tsaya, ya kalleta ya ce “Alhaji ya ce na zo na fara gini, a wace unguwar ki ke son mu zauna? Sannan wane irin gida ki ke so, flat ko mai bene?”

“Kowanne ka yi shikenan, Allah ya yassare”

“Salma kenan, haryanzu kina doubting idan ni zan aure ki, kuma ko zan iya riƙe ki, abun da muke shirin yi ba zunubi bane ba, hasali ma yana da asali a addinin musulunci, dan haka ki manta da batun al’ada da surutun mutane kin ji sweetheart”

Ta jinjina masa kai, tana wasa da hannun babur ɗin.

“Salma” ya kira sunanta a hankali, ta ɗaga ido ta kalle shi.

“Ina sonki sosai saboda Allah” tsigar jikinta ta tashi, ta kawar da idonta gefe.

“Ko sau ɗaya ki gaya mini wani abu mai daɗi da zai bani ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar neman aurenki, dan nima ina fuskantar ƙalubale”

Jiki a sanyaye ta ce “Dan Allah raihan ka yi abun da zaka zo ka cutu daga baya, ka ƙara tunani a kai”.

“Ni na riga na roƙi Allah a kan lamarin nan, kuma shi so baya bayar da ƙofar tunani, ba abu ne da yake bamu damar yin shawara ba, ki tausaya mini ummi” jikinta yayi sanyi, wani irin tausayin su ya kama ta.

“Ban san me zan ce ba, zan yi mana addu’a iya yi na, Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi”

Ya ce “Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum. Gobe in Allah ya kaimu ki yi mini girki dan Allah, zan biyo ta wurinku na ci”

“Me ka ke so” tayi maganar tana murmushi.

“Ke nake so”

Ta yamutsa fuska ta ce “Ina nufin me zaka ci?”

Yayi dariya ya ce “Abinci mana, ko me ki ka dafa zan ci da yardar Allah” yayi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa ya ce “Ki koma gida ki huta, duk da ban gama ganinki ba, zamu yi waya, dan Allah kar ki kashe waya kin ji baby”

Ta karɓi ledar ta juya tana murmushi.

Sabuwar waya dalleliya raihan ya gwangwaje ummi da ita, irin wayar da ba ta taɓa zaton zata riƙe irinta ba, bakinta ya ƙi rufuwa sai da ta kira shi ta yi tayi masa godiya, ya ce shi ba godiya yake so ba, kawai ta ce masa tana son sa shi zai sa ya ji daɗi ya tabbatar da ta ji daɗin kyautar da yayi mata.

Aikuwa ta yi gumm, ta kasa magana.

Da kuɗinta tayi cefane, washegari da safe ta sheƙa masa girki, bai kira ta a waya ba, sai fita tayi ta ganshi a waje yana jiranta.

Suna tafe yana yi mata normal hira, tare da nuna mata yadda za ta yi amfani da wayar da ya saya mata.

A mota ya ci abinci, yana ci yana yi mata hira, ta buɗe ruwa ta bashi, ta duba jakarta ta ɗaukko tissue, ta warwro masa ta bashi ya goge hannu.

Yayi murmushi ya ce “Ka ga mace ta gari, ta fara aikinta tun yanzu”.

Ta haɗa kan kwanukan ta ta ce masa “Sai anjima, Allah ya kiyaye”

“Amin ya rabb, yakamata mu koma ayi siyayya, mayukan nan kamar sun karɓe ki, na ga kina ta glowing”

Da sauri ta ce “Fari na yi?”

“A’a kyau ki ka ƙara, ban sani ba ko idona ne”

“Kar ka saka mu makara, sai anjima” ta fice daga motar, ya zuba mata ido, har ta shige shagonsu, sannan ya ja motar ya tafi.

Duk wata hanya da mami za ta bi, ta rusa maganar auren raihan, abu ya gagara ta kaɗa ta raya, amma raihan ya dage, ya samu goyon baya ɗari.

Dr. Ya sanar da su kawu Ilyasu, zai karɓi kuɗin auren ummi, dan haka mutum biyu daga cikin su su zo ranar juma’a.
Hatta kayan soye-soye da zai karɓi baƙi, daga waje ya yi order abun sa, dan sai saura ƴan kwanaki, sannan ya gaya wa farida.

Farida ko a jikinta, tana ganinsa yana ta shige da ficensa shikaɗai, ya shirya komai.

Kafin sallar juma’a, su kawu Ilyasu suka zo gidan, bayan sallar juma’a, su Alhaji Tahir suka zo.

Bayan gama tattaunawar da duk yakamata, dr. Ya gabatar da su kawu Ilyasu ga su Alhaji Tahir, tare da gaya musu matakin karatun ummi, tare da tabattar musu da binciken da yayi a kan Raihan, bai samu wata matsala ba.

Alhaji Tahir ya sake gabatar da kansa ga su kawu Ilyasu.

Sannan ya kalli dr. Ya ce “Ban sani ba ko kun yanke kuɗin aurenta da sadakin?”

Dr. Ya ce “A’a, duk abun da Allah ya sa ku ka bayar, zamu karɓa fatanmu ubangiji Allah ya sanya alkhairi”

Alhaji Tahir ya jinjina kai, sannan ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye kuɗi dami guda a tsakiyar falon, ya ce “Ga su nan, dubu ɗari biyar ne, mun saka watanni huɗu idan Allah ya sa zamu gani, amma idan kuna ganin mun saka da yawa kuna iya ragewa”.

Dr. Yayi murmushi ya ce “Bamu nemi ƙari ba ma nemi ragi? Allah ya nuna mana”

Kawu Ilyasu ya ce “Amma ranka ya daɗe har naira dubu ɗari biyar, kun kuwa san yarinyar nan bazawara ce? Kuma auren da ba a tsauwwala almubazzaranci ba yafi albarka, bazawara ce ta taɓa aure shekarun baya”.

Ayshercool.

                          CUTARWA

33

Tsit suka yi gaba ɗaya, suna jiran abun da Alhaji Tahir zai ce, dr. tamkar ya nutse saboda takaicin abun da kawu Ilyasu ya yi.

Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce “Ɗan uwa, ita bazawara ba mutum ba ce ba da ba za a kyautata mata ba? Shi ya ga yana son ta ai, ni mutum ne mai matuƙar ƙaunar ƴaƴana duk abun da suke so, sai ya saɓa wa addini ne zan ce a’a, amma dan bazawara ce ba shi yake nufin a aureta a wulaƙance ba”

Kawu Ilyasu ya ce “Ai dama kar ku ga an rufe ku ne, ku kallemu a matsayin mutanen banza, shiyasa na bayyana komai ko ba gaskiya ba? Kar ku zo a saka yaro yayi ta kashe kuɗi, tun da an ce shi bai taɓa aure ba, kar ya narka dukiya a auren bazawara ya zata budurwa ce, amma dubu ɗari biyar sun yi yawa a kuɗin auren bazawara, kar a cutar da shi”

Alhaji Tahir ya gyara zamansa ya kalli kawu Ilyasu ya ce “Ka san da wa ka ke magana kuwa? Bana alfahari da fariya, amma ko yafi haka ya bayar in kawo zan kawo, ba bazawara ba ko da tsohuwa ce kuwa, ka kuwa san wa ƴar ku zata aura ne? Da alama dr. Shikaɗai yayi binciken nan yakamata ya faɗaɗa muku bayanin waye Muhammad Raihan Tahir, zuriyarmu mun gaji yi wa iyali hidima. Ai ni da raihan ya ce mini mahaifiyar ta ƴar maiduguri ce, na yi zaton zaku yanka mana sadaki ne da sisin gwal, dan an ce auren ƴaƴanku sai jarumi” yayi maganar cikin barkwanci.

Dr. Da kunya kamar ya nutse ya ce “Ai kamar yadda na gaya maka, mu ƴan jigawa ne gagarawa, mahaifiyarta ce ƴar maiduguri”

“Allah sarki, to ace wa sirikata ina nan ina jiran turaren wuta, dan mutanen barno akwai ƙamshi”

Kawu Ilyasu ya ce “Kuma akwai ta’addanci da surkulle ba, ai da yake ma babartata ba wanda ya san a in da take yanzu, shekarun baya aka ce mana ta haukace ma”

Alhaji Tahir ya yi masa banza ya ce “Yanzu kun amince a kan watanni huɗun?”

Dr. Ya ce “Ubangiji Allah ya nuna mana, ya sa zamu gani”

Suka kammala, suka tashi suka tafi, suna tafiya dr. Ya dirar wa Iliyasu da bala’i.

“Wane irin mutum ne kai mara mutunci, ka ke tozarta yarinya a gaban sirikanta, wannan ai ba daidai bane ba”

“A’a yaya yahaya, haka shi ne kankaro mutuncinmu da kimar mu, haka kurum su gano daga baya, su ga mun zalunce su ai gara mu faɗa”

Kawu Saminu ya ce “To yanzu da ka faɗa ɗin me ya sauya?”

Cikin takaici kawu yahaya ya ce “Auren na ta na fari, ba a gabanku Idiris ya saketa ba, ko kusantarta bai taɓa yi ba ya ce saboda larurar da take fama, ya tozarta ta da bakinsa ya faɗa, da na taho da ummi daga gagarawa na kaita asibiti a kan larurar da take damunta, shi ma da bakinta ta tabattar babu mu’amalar aure a tsakanin ta da idiris ba ta da iddarsa.
Idan ka tona wa ummi asiri meye ribar ka? Sigar yadda ka faɗi maganar salon tozarci ne kawai, In da na gode wa Allah mutumin wayayye ne, kuma magana ake ta zunzurutun ilimi, kuma wannan maganar duk mun yi ta da shi, na gaya masa ummi bazawara ce ta taɓa yin aure, ya ce mini in dai ɗan sa yana son ta, shi ba shi da matsala da ita, kuma ɗaukakace kuna raye sai ummi ta yi ta, dan yaron manyan mutane ne, in sha Allah sai yarinyar nan ta huta.

Ya ciri dubu hamsin a aljihunsa ya ce “Ga wannan, ku bawa Iya dubu goma, ku ɗau goma-goma sauran ku rabawa dangi an saka ranar ummi”

Kawu Saminu ya ce “Amma yaya, a bayar da kuɗi har dubu ɗari biyar amma ka bamu dubu hamsin, a duba lamarin nan mana”

“Da nake raye na yi auren ƴa ta nawa ku ka bani gudunmawa? Sai ummi da ba ta da gata sai Allah sai ni, yarinyar da ku ka son tozartawa zan baku kuɗin aurenta, a kuɗina ma na baku dubu hamsin ɗin nan, kuɗin aurenta sisi ba zan taɓa ba, kayan ɗaki zan yi mata na alfarma” Haka suka rabu baran-baran dutse a hannun riga.

Suna tafe a hanya kawu Saminu ya ce “Ilyasu meyasa ka yi haka? Kai ina ruwanka?”

Ilyasu ya yi tsaki ya ce “A gidanka ko a gidana meyasa ba a samu irin wannan ba, fin ƴaƴanmu kyau ta yi, kaf sirikanmu babu wani mai maiƙo, amma kalli ya kawota birni zai aura mata mai kuɗi, su haɗu su yi ta ci Allah ya isa wallahi”

“To yanzu da wa ka ke Allah ya isan?”

“Kai ba zaka gane ba, yarinyar nan idan ta samu daula, za ta iya aikata rashin mutunci, ina laifin a samo mata miji dai-dai ita, wai kuɗin aire kawai dubu ɗari biyar, wai ya zata sisin gwal za a yanke musu, a’a sisin uwarsa, sai wani baza babbar riga yake wai shi ga attajiri, shi kuma wannan banzan sai ƙaryar turanci, ƴaƴan mu ba su samu haka ba, sai wannan galmashurar yarinyar” har suka isa gagarawa bakin Ilyasu bai rufu ba yana bala’i.

Su Alhaji Tahir ma suna tafe, abokinsa Alhaji Sabo yake cewa “Tahir mutumin nan fa da gaskiyar sa, yaya za ayi ka bari raihan ya auri bazawara kuma ya kashe mata wannan kuɗin haka?”

Alhaji Tahir ya ce “Saboda ɗa na kowa ne, kuma dukiya ɗazu ce, muddin na bari yayi abun da mutuncinmu zai zube tun yanzu, to raihan ba zai taɓa kima a idonta ba, ina fatan ko bayan raina, nima Allah ya kawo masu kula da bayana, labarin nagartar yarinyar da na ji, ko tsohuwa ce ta kai a bayar da hakan”

Ƙanin Alhaji Tahir ya ce “Gaskiya ne wannan, Allah ya wuce mana gaba, amma daga yadda wannan kawun nata yake zaƙewa kawai na ji ta bani tausayi, Allah ya sanya musu albarka”

Suka amsa da Amin.

Tsananin ɓacin rai da farinciki, ya sanya dr. Gaya wa ummi abun da kawu Ilyasu ya yi, a ƙa’ida farida yakamata yayi zancen ya ji sanyi, amma ya san sai ta sake yin wani abun da zai tunzura shi, dan haka ya zaunar da ummi yana gaya mata, tare da nuna mata kuɗin, ya tambaye ta wani irin kaya take so.

Jiki a sanyaye ta ce “Duk abun da ka yi mini na gode kawu, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata”

Ya amsa da “Amin ummana, ki yi ta addu’a kina haƙuri kin ji ko? Nasara ba ta zuwar wa bawa daga kwance babu jarrabawa”ta jinjina masa kai ta ce “In sha Allah”

Iya tayi mamakin jin abun da kawu Ilya suka ce mata an kai wa ummi, ta riƙe baki ta ce “Shi kuwa wani asarren ne zai kwashi wannan mummunar yarinyar mara fasali, har da kashe mata maƙudan kuɗi haka?”

Kawu Ilyasu ya ce “Oho musu, kuma yaron ma wai bai taɓa aure ba, amma an cuce shi gaskiya”

“Ai ba zai wuce yahaya shi yake ƙuƙƙula wannan abubuwan ba, kuma zai zo ya sameni har in da nake”

Magana ta cika gagarawa, cewar ummi ta samu wani hamshaƙin attajiri a kano za ta aura, kuɗin aurenta kawai naira dubu ɗari biyar.

Aka din ga surutu da yayata zance, har da masu zuwa yi wa iya Allah ya sanya alkhairi.

Kasancewar Alhaji Sabo da suka kai wa raihan kuɗi, matarsa ƙawar mami ce sosai da sosai, bayan gama bawa matarsa labarin abun da ya faru, ta ɗauki waya tana yi wa mami mitar duk ga ƴaƴan su amma raihan ya tsallaka waje zai auri bazawara.

Mami ba ta gane zancen ba, sai da ta yi mata dalla-dalla, hakan ya ƙara tunzura mami, ta tafi sashin Alhaji kamar za ta kama da wuta.

“Alhaji Tahir” ta kira sunansa kai tsaye.

“Na’am Bilkisu ya aka yi ne?”

“Wallahi raihan ba zai auri bazawara ba, ba zai yiwu ba, wai ka san yarinyar da zai aura bazawara ce?”

“Na sani, ba shi ya ce yana so ba?”

“Kuma ka kwashi kuɗi har 500k ku ka kai, to wallahi sai dai ayi wadda za ayi, auren nan ba za ayi shi ba, ban lamunci auren fari ya auri wata bazawara ba, lallai yarinyar nan munafuka ce macuciya, har aure ma ta taɓa yi”

“A irin wannan ƙadamin, idan ɗa namiji yana son abu ba ya ji ba ya gani, ba ya ganin aibun abun, ki bi a sannu kan yaron nan ya fara bujure miki, na so ace matar Alhaji Sabo ba ta yi gaggawar gaya miki ba, da kaina zan gaya miki, amma tun da ta riga ta gaya miki shikenan “

“Ba wani baka yi niyyar gaya mini ba, to idan shi ba shi da hankali, ni ina da shi”

Ya girgiza kai ya ce “Hankalin nan dai ban ga alama ba da saura bilki, baki san rayuwa ba haryanzu “

“Ni ka ke cewa bani da hankali?”

Ya tashi tsaye ya riƙo hannunta da ƙarfi ya ce “Ni da ke duk musulmai ne, da aka haufa a cikin musulunci gaba da baya. Kuma muna koyi da rayuwar annabi sallalahu alaihi Wasallam ne, idan kuwa haka ne, sunna ce mai ƙarfi raihan zai yi koyi da ita.
Bilki yaranki Allah ne ya shirya miki su, ba wai dan kina da techniques na yadda ake tarbiyar yaran ba, mutane da yawa na ganin bai dace biye wa yarana da nake yi a kan abun da suke so ba, ina tunatar da ke zamani ya sauya, ka yi wa yaranka tarbiyya dai-dai da zamani sai a zauna lafiya. Wannan baloƙoƙon da ki ke kamar a zamanin da, ba abun da zai haifar miki, illa bijirewar yaron nan, shawara nake baki kar ki matsa da yawa, dan yana wani stage ne da ba ya ji ba ya gani, cikar muradi kawai yake fata, amma idan kin ƙi ji gaki nan ga shi” kamar ta shaƙe Alhaji Tahir haka take ji, tare da jinjina tsantsan rashin hankali da wauta irin na raihan, da ma ba ta ce za ta yi masa aure ba, ta bar shi a haka, kawai daga cewa za ta yi masa aure, ya jajubo wannan ina da munin wai ita zai aura.

Raihan ya fito daga Masallaci sallar la’asar, Ummi ta kira wayarsa, ya samu wuri ya tsaya tare da ɗagawa “Hello my love”

Cikin sassanyar muryarta da yake cewa iyayi ta ce “Barka da yamma”

“Yauwwa barka, kin wuni lafiya?”

“Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su mami?”

“Duk suna lafiya, ina noor ɗina?”

“Tana tahfiz” ta faɗa a hankali.

Ya ce “Kirana ki ka yi ki ji muryata love?”

Ta ɗan yi murmushi ta ce “Muryartaka ba gata nan a what’s app ɗina ba? Su Alhaji sun zo ɗazu”

Yayi murmushi ya ce “Shiyasa na ji bakin ki yaƙi rufuwa, zaki yi wuf da ɗan kyakykyawa yaron da ki ka raina”

Ta ce “Hmm amma kuɗin da su Alhaji suka kawo, har da kayan lefe ko?”

“Yaushe muka yi haka da ke?”

“Ba muyi ba tambayarka kawai na yi, kuɗin da yawa ka manta na taɓa aure ne?”

“Ke ki ka san kin taɓa auren ai, ni ban sani ba, kuma ke ina ruwanki da abun da zan yi, ke da ba kya so na, ina ruwanki idan zan yi lefen koma ba zan yi ba”

“Yi haƙuri” ta faɗa a sanyaye.

Ya gyara tsayuwarsa ya ce “Ummi ke malama ce, annabi Sallallahu alaihi Wasallam, mutum ne mai hidimtawa iyalinsa, kuma rayuwarsa ce abun koyi a garemu, haka zalika mahaifina mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai haka na tashi na ga yana yi, kuma babana mudubina ne, bana cikin maza masu nakasashiyar zuciya duk abun da na kashewa wadda zan aura ribata ce, kin san tsare hakkin iyali yana ƙarawa namiji kima da kwarjini a wurin iyalinsa. To balle ni da nake yaro kuma ba a so na, dole sai na yi aiki tuƙuru tukuna, dan saya wa kaina kima a wurin matata”

Ummi ta numfasa ta ce “In dai kai Allah ya ƙaddara ka zama mijina, ba ka buƙatar wahalar da kanka, zan yi maka biyayya iya yi na, ban yi wayo sosai da mahaifiyata ba, amma mama mace mai matuƙar biyayya ga babana”

Cikin yanayi na nishaɗi ya ce “Allah ya sakawa iyayenmu da mafificin alkhairi ummi, ya nuna mana auren nan lafiya” Ummi ta yi shiru ta kasa amsawa.

Hira suka yi sosai, sannan suka yi sallama.

Raihan yana zaune a ɗakinsa yana danna system yana shan lemon kwali, Salim ya yi sallama a ɗakin.

Raihan ya amsa yana mamakin ganin Yaya salim a ɗakin nasa, dan sai ya shafe shekara bai shiga ɗakin sa ba.

Kamar wanda yayi baƙo raihan ya tashi yana faɗin “Sannu da zuwa yaya”

Salim ya jinjina masa kai ya zauna, ya kalleshi ya ce “Yanzu muke magana da hajiya, ashe yau an yi maka engagement? Ubangiji Allah ya sanya alkhairi babban mutum, girma zai ƙara hawa kanka, Allah ya sanya alkhairi”

Duk in da ɗan uwa yake ɗan uwa ne, maganganun ummi suka din ga dawo masa, ya dubi Salim ya ce “Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sa ayi naka kafin ayi nawa”

Salim yayi murmushi ya ce “Sai ka ce wasan yara? Allah ya baku zaman lafiya, ace ina gaisheta” yayi maganar yana shafa sumar raihan.

Salim shi ne babba, aƙalla ya kai shekaru talatin da huɗu, ya fi Sagir sauƙin kai, ba shi da magana, sannan mutum ne mai son kaɗaici, amma akwai abokan banza, dan su suka koya masa shaye-shaye.

Raihan ya ce “Za ta ji, amma ita tana yawan cewa a gaishe ku, da kai da Yaya sagir”

Ya ɗan kalli raihan ya ce “Ta sanni ne?”

“Eh, ummi ce ai ƙawar maryam, ta sanku, sannan ina yi mata zancenku”

Ya ce “Ohh that dark lady, mai brwon eyes ko? Wow na yi maka murna she’s decent and good lady”

“Amm yaya dan Allah da gaske ummi mummuna ce? Mami tana ta complain a kan hakan”

Salim ya ce “Ita wannan mamin naka, ra’ayi idan ba nata ba, kowa bai iya ba, just go ahead, ita kuma mamin ka yi ta sakata a addu’a, Allah ya kwantar maka da hankalinta shikenan kawai”

Raihan ya riƙe hannun Salim ya ce “Na gode sosai Babban yaya, Ubangiji Allah ya baka kujerar MD Tahir and Son’s”

Salim ya ce “You are not serious, kai dai Allah ya tayaka riƙo, ya sanya maka albarka, take care” ya fice daga ɗakin.

Raihan yayi shiru, babu shaƙuwa sosai a tsakaninsu, saboda shi raihan a Bauchi ya ƙarasa girma, gidan yayar Alhajinsu Hajiya Aisha, mijinta da ita da Alhaji duk cousin’s ne, shi kuma su Salim suna nan kano, kuma mami ba ta da aiki sai gaya masa yayi a hankali da Hajiya da yaranta ba sa ƙaunar su, kuma kar su Sagir su koya masa shaye-shaye.

Sai dai shi bai ga alamar hakan ba, hasali ma ba sa wani shiga shirgin sa, dan ba sa’aninsa bane ba, har gara Sagir ma suna faɗa da raihan sosai. Hajiya kuwa kamar ɗan da ta haifa haka ta ɗauki raihan da ma duk ƴaƴan mami, amma matan duk mami ta hure musu kunne.

Farida ko a jikinta, jin an kawo kuɗin auren Ummi, dan kawai jikinta bai bata ummi wani mutumin kirki za ta aura ba, dan da an kawo abun arziki da jiki na rawa dr. Zai gaya mata, sai dai yayi mata shiru bai gaya mata me aka kawo ba, kuma wa za ta aura ba.

Noor ta kasa nutsuwa saboda murna, sai tsara yadda bikin zai kasance take yi, har da cewa sai dr. Ya ɗinka mata sababbin kaya guda hamsin har da irin na amarya da ango.

Saboda tsokana ta je ta samu kausar tana bata labarin yadda raihan yake, ta koreta amma ta ƙi tafiya ta cigaba da cewa “Kin ganshi kuwa? Wallahi duk saurayinki babu mai kyan sa, fari ne fa sosai da sosai, wallahi motarsa ta fi biyar, masu kyau ɗan bala’i, idan yana magana yana ɗage girarsa guda ɗaya, me kyau da shi” kasancewar hankalin kausar ba a kan noor yake ba, ya sanya sam ba ta fahimci me noor ɗin ke faɗa mata ba.

Mami ba ta nemi raihan ba, sai yau da safe ya je karyawa, tayi masa shiru, ya gaisheta ta amsa masa, ya kammala cin abinci, ya tashi zai fita, ta janyo hannunsa da ƙarfi ta tankaɗa shi har ɗakinta ta mayar da mukulli ta rufe, ta dawo ta ɗauke shi da mari har kashi biyu.

Sai dai ya tsaya yana kallon mami da mamaki, ba tare da kuma ya yi yinƙurin kare marin ba.

Ta ɗora da ɗura masa ashar, amma ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon tiles.

“Ashe ba ka da hankali raihan, ba ka da mutunci ba ka san abun da yake maka ciwo ba, ashe yarinyar nan bazawara ce, ka je zaka auri bazawara sauran wani, da ƙuruciyarka da komai, ashe baka san me yake yi maka ciwo ba?
To ai dama ni na ce zan yi maka aure ko? To na janye na fasa, ba zaka yi auren yanzun ba, sai ranar da ka fuskanci kai mutum ne da daraja da girma. Dan haka umarni nake baka ba shawara ba, ka je ka janye maganar auren nan. Saboda hauka tana bazawara ga muni da rashin gata, amma ka ɗauki kuɗin aure har dubu ɗari biyar, ka bayar a kai, to baka isa ba wallahi, idan har ni na haifeka ka ka je ka gaya wa mahaifinka ka fasa auren nan, ba zaka aureta ba dan kai kaɗai ne kawai zaka gaya masa haka ya yarda, idan ba haka ba zaka fuskanci abun da baka taɓa tununi daga gareni ba, na gaya maka. Ka wuce ka je ka same shi ka ce masa ka fasa yanzu ba anjima ba. Matar da na zaɓa maka ita zaka aura, duk matan garin nan masu kyau da aji, ba ka ga kowa ba sai wannan cilakowar?”

Tuni fuskar raihan ta yi jawur, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, saboda tashin hankali da ɓacin rai, ya buɗe ƙofar ya fice, yana gazgata maganar ummi da ta taɓa ce masa su mata mutane ne masu masifar son kansu, bai yi mamakin hakan daga mami ba, duba da yanayin halinta kuma gashi jiya ya ga Anty rakiya ta zo gidan, ya san ita zata sake ziga mami, amma ita bazawara ba mutum ba ce?.

Zuciyar sa na wani irin tafasa ya tafi sashin Alhaji, Alhaji tashin sa kenan, yana ta shiri za shi Abuja, ya ga raihan, bai yi wa raihan magana ba, Raihan ya ce “Na fasa auren ummi, na janye, ka karɓo kuɗin auren, amma idan aka karɓo kuɗin auren nan an karɓo kenan aure sai dai in ga ana yi, babu ƴar da za a sake kaiwa kuɗin aure da sunan zan aureta” yana gama maganar ya juya ya fice.

Alhaji bai yi niyyar dakatar da shi ba, dan ko magana bai yi masa ba, ko raihan bai yi masa bayani ba, ya san bilki ce ta kunno shi, dan raihan akwai ladabi, idan ya je bango kuma akwai taurin kai, dan haka Alhaji ya ƙyale shi, da nufin idan ya huce sai su yi maganar.

Ummi na wurin aiki tana ta shigar da sabbin price a computer, ta ga raihan ya shigo, fuskar sa babu walwala.

Bai ce mata uffan ba, ya zagaya ya zauna a kujerar kusa da ita.

“Baka gaya mini zaka zo ba, ai da na dafo maka wani abun, baka da lafiya ne?”

Ya girgiza mata kai ya ce “Bauchi zan tafi daga nan, na zo mu yi sallama ne, babu lallai na dawo nan kusa”

Da sauri ummi ta ce “Saboda me?”

Ya kalleta wani abu mai ɗaci na kaiwa na komowa a zuciyarsa, ga wani irin tausayin ummi da yake ji, idan ya fasa aurenta bai yi mata adalci ba sam.

“Ka gaya mini mana, menene meyafaru gaba ɗaya ka yi wani iri, me aka yi maka ne?” Tayi maganar cikin rauni sosai, saboda ba ta fiye ganinsa a irin wannan yanayin ba.

Kasa magana yayi, ya tashi ba tare da ya ce mata komai ba zai tafi, karo na farko ta riƙo hannunsa a nata ta ce “Ka zauna ka gaya mini menene, ka ɗaga mini hankali ka gaya mini menene?”

Ya zauna a hankali ya ce “Ummi, ban san me yake shirin faruwa ba, daga yanzu zuwa ko yaushe abu mai daɗi ko akasin haka ka iya faruwa, dan Allah ko me ye ya faru, ni dai ki saka a ranki ina son ki sosai da sosai ummi, kuma ba zan daina sonki ba, ki tsananta yi mana addu’a, ko da ke ba kya so na, ni ina sonki ummi”

“Raihan, dan Allah idan a kaina ne, kar ka samu matsala da ƴan gidanku, ahali sun fi komai daɗi, ni daga baya ka sanni, zaka iya canza ni, su kuwa fa, in dai nice babu komai zan fahimceka amma ahalinka na da muhimmanci a rayuwar ka, ni tsangwama da kyara na saba da su”

“Amma ba zaki dauwwama a cikin su ba, akwai hatsari mai girman gaske a rabani da ke, ko kin auri wani ba ni ba, ba zan iya rabuwa da ke ba, zan tafi bauci wataƙila zan shafe tsayin lokaci, amma zamu din ga waya in sha Allah, take care am going to miss you dear” yayi maganar yana shafar gefen fuskarta. Ya tashi ya fice.

Haka kurum gabanta ya tsananta faɗuwa, a duk lokacin da ya ce ko tayi aure ba zai iya rabuwa da ita ba, sai ita ma ta din ga jin irin haka a zuciyarta, kamar itama ba zata iya rabuwa da shi ɗin ba.

Jikinta duk yayi sanyi, har ta kammala aiki ta tashi, bayan ta koma gida tana ta neman layukansa, amma shiru ba ta samunsa a wayar.

Sai washegari ya kirata da wata lambar daban, ya ce mata yana bauchi cikin ƙoshin lafiya, da wannan lambar za ta din ga kiransa.

Jin muryarsa wasai ya sanya ta cewa “To amma yanzu zaka dawo ko?”

“Ko zan dawo ba yanzu ba, kewarki ce kawai take damuna”

“Dan Allah ka dawo ka ji babban mutum, manya ba sa haka, idan laifi muka yi mutanen kano, tuba muke yi kar a hora mu da yi mana yaji, ka san menene zan dafa maka abinci mai daɗin gaske, na san abun da ya saka bar garin zuwa yanzu ka huce ai ko? Zan yi maka girki”

Raihan yayi dariya ya ce “Matar raihan, kirarin nan kawai ya ƙara sanyaya mini zuciya, kar ki saka na ɗaukko mota na taho mana. Ke dai ki yi ta addu’a kamar yadda na ce miki kin ji ko?”

“To shikenan, amma dai ka yi tunani a kan lamarin nan”.

Can gida kuwa Alhaji Tahir ya saka mami a gaba da masifa, tare da cewa duk in da ɗan sa yake sai ta fita ta nemo shi, dan ba a samun sa a waya, baya gida kuma baya office.

Abu kamar wasa, hankalin mami ma ya tashi, ba ta yi zaton raihan zai yi haka ba.

kwana kusan biyar, babu raihan babu dalilinsa.

Dr. Ya samu ummi ya ce mata ta shirya kayanta, washegari za su yi tafiya ta kwanaki uku, ta sanar a wurin aikinta.

Ummi tayi ta mamakin, ina za su je haka afujajan babu cikekken shiri babu komai.

Ba ta matsa masa da tambaya ba, ta shirya kayan kamar yadda ya umarce ta.

Mami kuwa, Anty rakiya ta bata shawarar ta je har gida ta ci mutuncin ummi, kuma ta tursasata ta gaya mata in da raihan yake, dan ba zata kasa sani ba.

Alhaji Tahir ya shigo a fusace ya ce “Kin yi naki role ɗin, barkana tun da na san in da ɗa na yake, amma bari na gaya miki wani abu, idan har kin cigaba da dagewa ba za ayi auren nan ba, to ki tabattar da zan kawo yarinyar nan matsayin matata ta uku, dan ba zaki zubar mini da mutunci a idon duniya ba”

Gabanta ne yayi wata irin mummunar faɗuwa, wayarta ta fara ringing, cikin rawar jiki ta ɗaga. Saboda kura ta san gidan mai babban sanda bijirewa ɗaga wayar ka iya jefata cikin matsala.

“Bilki, ashe baki da mutunci baki da hankali? Ashe wayewar ta ki ta ƙarya ce, saboda wulaƙanci da rashin mutunci ke da ba a aure, da zamu bari Tahir ya aureki ne? Ke kin san auren zumunta muke yi, da matarsa ƴar uwassa tana son shi yana son ta, ya auro ki, mu a cikinmu waye ya hanakk zaman lafiya? Saboda rashin kunya yaro ya kawo mace yana so ki ce a’a, saboda wulaƙanci idan shima ya faɗa shaye-shayen ki ce me? Bar ganin ke ki ka haifi raihan, wallahi ba zamu lamunci son zuciya ba, ko tsohuwa ya ce yana so, zamu bashi goyon baya, ba dan Allah ya sa ya taho nan bauchin wurin mu ba, wani wurin yayi ba, to ahir ɗinki wallahi idan ba haka ba da ni ki ke zancen, kuma bauchi ya zo kenan, ku nemi wanda zai riƙe muku kasuwancin naku, tun da kin hana shi auren”.

Cikin tsuma Mami ta ce “Dan Allah Hajiya Aisha ki yi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba”

“Oho miki ta cigaba da faruwar ma, kin ce ya fasa aure, ai ke uwa ce yayi biyayya ya janye, amma ya ce a gaya miki, shi da aure har abada, sai kuma ki shirya idan ya kawo miki ɗan gaba da fatiha ki karɓa ki riƙe tun da ba ki da hankali” ta kaste wayar.

Ayshercool.

  CUTARWA

Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon.

Raihan ƙararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murɗa mata.

Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuɓe.

“Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya goɗai-goɗai da kai sai ka auri yarinyar da ɗan ka ya ce yana so?”

Alhaji Tahir ya ce “In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ƙara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya” ya ƙarasa maganar tare da ɗaukar wayarsa ya fita.

Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya.

Rakiya na ɗagawa mami ta fashe da kuka, “Anty rakiya na shiga uku na lalace”

“Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?”

“Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haɗo ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa”

Anty Rakiya ta ce “Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a matsayin sirika”

“Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana ɗaya yake yi ko ta yi maka daɗi, ko kuma akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?”

Anty Rakiya ta ce “Taɓ, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi ƙarfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa”

Mami cikin takaici ta ce “Lamarin fa ya wuce yadda ki ke tunani, kin san taurin kan raihan kuwa? To cewa tayi wai ba zai dawo ba, ya bar aikin kenan, ya kuma ce idan aka karɓo kuɗin auren nan, shi da aure har abada, ga babansa ya ce idan aka fasa zai aureta, na shiga uku ina na kama? Kin ga suna nema su haukata ni, raihan kafiya da taurin kai kamar ubansa, idan ya ƙi aure ya lalace yaya zan yi?”

Anty Rakiya ta ce “Ai kawai ki dage ki samu ya dawo tukuna, ki kira shi a waya”

“Wayoyin da duk ya kashe su, ina zan yi?”

“To ki koma ki samu babansa ki lallaɓa shi, ya dawo da shi kar a rasa wannan damar kuma ta kasuwancin nan “

Mami tayi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan, zan kira ki mayi magana anjima” ta katse wayar ta ajiye tana wani irin haki, ita ba mai asma ba.

*
Dr. suna tafe a mota da shi da ummi, ya ce “Mamana zaki ga zamu yi doguwar tafiya, ba sayar da ke zan yi ba abun alkhairi ne”

Ummi ta yi murmushi ta ce “Idan sayar da ni ɗin ma ka yi ai na saidu kawu”

Yayi murmushi ya ce “Idan na sayar da uwata ina na kama? Yakamata ace kin yi azumin farinciki kan mu yi tafiyar nan”

“To Ubangiji ya tabattar mana da dukkanin alkhairin da yake cikinta”

Ya amsa mata da “amin”

Ummi ta gaji da zaman motar nan sosai da sosai, sai dai tun da taga symbols da sunan borno, jikinta ya fara sanyi, har ta rasa tunanin me ma za ta yi ne?.

Kawu kuma ya mayar da kai sosai a kan tuƙinsa, sai lokacin salla ya tsaya suka yi salla, ya saya mata abinci.

Ta tuno lokacin da ya ɗaukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin riƙonta da yayi

A ranta ta ce “Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai da zuriyarka”.

Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita.

“Mamana tashi mun zo” a hankali ummi ta motsa tare da buɗe idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa komai ba, sai bin wurin da kallo.

Ƙofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya ɗan daddana ya kara a kunnensa ya ce “Gamu mun zo”

Wani matashin saurayi ya leƙo ya durƙusa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga.

Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Alƙur’ani bugun warshi a gabansa.

Dattijon ya miƙe tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta ɗaga niƙabin fuskarta ba, sai dai ta shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa.

Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa.

Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina kallonta.

Dr. Ya ce “Ina mutuniyar kuwa?”

“Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya ɗan motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a ɗora muku girki, ai bamu san zaku zo ba”

Dr. Ya ce “Ai alƙawarin da na ɗauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo”.

Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banɗaki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiɗa tana hutawa, saboda gajiyar da tayi.

Ummi ta ɗan jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a ɗora sanwa.

Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam.

Dr. Ya ce “Malam ba ka ganni da baƙuwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba”

Malam yayi murmushi ya ce “Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai ɗakinka ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da niƙabi”

Dr. Yayi murmushi ya ce “Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?”

Ummi ta ce “Na sanshi amma na manta a ina?”

“To ki cire niƙabin ko zai gane ki”

Ummi ta jinjina kai tana ƙoƙarin cirewa, aka  yi sallama.

Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ta ji tamkar numfashin ta zai bar ƙirjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa.

Malam ya ce “Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi baƙi tafiyayyu daga kano”

Ta ce “Baban ummi ne?”

Malam ya ce “Eh shi ne, tun da shikaɗai ki ka sani a kanon ba”

Shigowa suka yi tare, tana riƙe da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur.

Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda ƙirjinta ke lugude. Gaba ɗaya suka zuba musu ido, kai tsaye ta nufi ummi ta zauna a gabanta, tana cigaba da kallon ummi ta niƙabinta.

Ta miƙa hannu a hankali ta ɗaga niƙabin ummin, tayi tozali da fuskar ummin da a duniya bata ganin kyan komai, kamar yadda take ganin kyawun wannan fuskar.

A gigice ummi ta yi mata wata irin runguma ta fashe da matsanancin kuka, saroro mariya tayi, ta kasa taɓa ummi sai hawaye da ya fara zuba daga idonta.

Mama ta miƙa hannu tana faɗin “Ki yi mata a hankali ba ta da cikakkiyar lafiya”

Mariya ta buge hannun maman da ƙarfi, ta ruƙunƙume ummi, tana wata irin ajiyar zuciya kamar za ta fita daga hayyacinta.

Ta miƙa hannu ta warware mayafinta, ta lulluɓe da ummi da shi, ta ɗaukko mafici kuma tana yi mata fifita tana kuka.

Sai a yanzu suka gane wacece, malam ya sunkuyar da kai yana hawayen tausayin ƴar sa.

Ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukko wayarsa, ya kira Maryam a waya da kuma yaya ɗan lami.

“Ummina, kina cin abinci kuwa? Naga duk kin rame, iya tana yi miki wanka? Ko dai zazzaɓi ne a jikinki?” Tayi maganar tana ɗora hannu a goshin ummi.

Wasu irin jijiyoyi suka ɗaɗɗaga a goshin ummi, wani irin riƙo take yi wa mariya, tana jin kamar an sanyata a wata ni’ima.

Sun fi mintuna talatin a haka, sun ƙi sakin juna, mariya sai kakkare ummi take yi, kar wani ya taɓa mata ita.

Dr. Yayi gyaran murya ya ce “Yau na cika alƙawari ko?”

Ta jinjina masa kai, tana kuka ta ce “Wallahi ba zan taɓa yafe wa iya ba, Allah ya saka mini zaluncin da ta yi mini, ta ƙwace mini ummi bayan ba son ta take yi ba, ta ce ni na kashe mata ɗa, kalli yadda duk ummi ta rame, haka zan kwanta in yi ta mafarkin ummi tana kuka, tana cewa na zo na tafi da ita”

Ta ɗago ummi tana goge mata hawaye ta ce “Ki daina kuka kin ji ummana, ba zan sake bari a mayar da ke wurin iya ba, na san ba ta sonki ba ta ƙaunarki, ban san me ki ka yi mata ba, wallahi ba zan yafe mata ba, yaya ɗan lami yaƙi dagewa ya karɓo mini ƴa ta, kullum sai na yi kuka saboda ummi, yaya maryam ma ta hantare rannan wai kamar nikaɗai ce me ƴa, ki daina kuka kin ji ummina, da kaina zan din ga yi miki wanka, ina baki abinci, katifata zata ishemu mu din ga kwana tare, ba zan sake bari a kai ki wurin iya ba kin ji mamana”

Ummi ta ƙura mata ido, yadda mama ke wannan surutan daga wannan zuwa wancan tare da kasa gane ummi ta girma yanzu, ya tabbatar wa da ummi cewar mariya bata da lafiyr ƙwaƙwalwa.

Ta miƙa hannu ta ɗaukko ledar pure water, ta buɗeta ta saka wa ummi a baki tana faɗin “Na san ƙishirwa ki ke ji ummi, sha ruwa kin ji”

Babu wanda tausayin ummi da mariya bai kama a wurin ba, uwa kenan duk da ciwon ya motsa ba ta hayyacinta, amma hakan bai hanata gane ƴar ta ba, duk da shekarun da suka shafe basu haɗu ba.

Dr. Yayi gyaran murya ya ce “Alhamdilillah ala kulli halin, na gode Allah da ya sanya ummi da mahaifiyar ta suka haɗu, ba tare da ta Allah ta kasance ba. Ummi na yi miki laifi, kuma na yi muku duk da ina godiya da fahimta ta da ku ka yi.
Ummi ban ƙi sada ki da mahaifiyarki dan baƙanta miki ba, a lokacin da na ganota, tana cikin halin larura sosai, ba komai take ganewa ba, na yi fargabar haɗuwarku ba za ta yi daɗi ba, idan ku ka haɗu ta kasa gane ki, abu na gaba kuma ina tsoron halin da ki ke ciki, ya sanya ki ƙi zama ki dawo wurinta, alhalin kina tsaka da karatu, dan duk wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa zai kama, dan haka a matsin nan da ki ke, duk da kasancewar ki mai biyayya, zaki iya bujirewa ki zaɓi dawo wa gaban mahaifiyarki, ba tare da kin yi acheiving wani abu ba.
Wanda a lokacin babban burina da fatana, ki samu nagartaccen ilimi, da zaki iya tsayawa da ƙafafuwanki, ina fatan zaki yafe mini daga ke har mahaifiyar ki” yayi maganar a sanyaye.

“Ai dama kai na yafe maka, baka cuceni ba, amma iya iya iya, ban san me na yi mata ba, amma za ta maimaita a gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya ɗan lami ka ƙi dagewa ka karɓo mini ummina”

Dr. Ya ce “Haba maman ummi, ki yi haƙuri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi haƙuri dan Allah” yayi maganar yana haɗa hannayensa.

“Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya ɗan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ƙwace mini ita dan ta wulaƙanta ni”

Dr. Ya ce “Ba gani a gabanki kina kallona ba?”

“Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau” yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne.

Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu shar da ita, gashi gaba ɗaya ba sa kama, sai kaɗan, kamar ya da ƙanwa ba uwa da ƴa ba.

Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta ɓoye ummi a bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a ɗauketa a mayar da ita wurin Iya.

Ummi ta ga ƙauna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa.

*

Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaɗa ƙafa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a waya.

Falon ta shigo cikin takunta na ƙasaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce “Kai, babanka ya kasa samunka a waya, yana ta ƴar murya a lallaɓoka ka koma fa”

Raihan ya gyara zamansa ya ce “Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce taƙi tsayawa ta fuskance ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, taƙi fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata”

“Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta’adar, ya aurota daga nan kowa ya samu ƴancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?”

Raihan ya ce “Abun kuma har da gori?”

“Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata”

Yayi murmushi ya ce “Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daɗi sai na matata”

“Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak yarinyar nan, haka zaku yi ta faɗa da babarka”

Raihan ya miƙe ya ce “Ni kaina na sani, ina ƙoƙarin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki sosai”

Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage ɗin, ba a saka pressure wurin cewa lallai sai an tanƙwara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren.

Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluɓe ummin, sannan ta rungumeta.

Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan.

Aikuwa a take ya ɗaga ya ce “Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru”

Ummi ta ce “Albishirinka”

“Goro fari ƙal”

“Na haɗu da mama”

Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce “Wace maman?”

“Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ƙi zama na yi karatu ya sanya ya ɓoye mini”

Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce “Congratulations to both of us ummi, dan wallahi da al’amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah”

Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin rabuwa da suka yi, da irin so da ƙaunar da maman nata ta nuna mata.

Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ƙara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa.

A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi.

Yaya maryam ta ce “Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za a zo a ɗauketa a tausaya mana dan Allah”

Dr. Ya ce “Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daɗin zama da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huɗu, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku”

Anty maryam ta yashe baki tana faɗin “Masha Allah, Alhamdilillah”

Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka.

“To amma, akwai ɗan shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata”

Dr. Ya ce “Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake”

Yaya ɗan lami ya ce “Amma ba za a ƙara mana ko wata ɗaya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma”

“A’a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan mutane ne, idan muka ce a ƙara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara”

Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano.

Ummi taga gata da ƙauna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faɗan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen.

Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai ɗaga mata hankali ba.

*
A ka yi bikon raihan da ƙyar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake “ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne”.

Hajiya ta ce “Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka”

Raihan ya ce “Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba”

Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu’ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya tarar da sabon ɓacin rai.

A bedroom ɗin ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya durƙusa ya ce “Mami barka da gida”

Maimakon ta amsa sai ta ƙure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa.

“Ai gara in ƙare maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har ubanka? In haifi ɗa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ƙaunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ƙara ta ta kira ni ta ci mini mutunci”

“Wallahi mami ba ƙararki na kai ba”

“Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu ɗari biyar ɗin ta isa komai da komai”

Cikin damuwa raihan ke ƙoƙarin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata ɗaki.

Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ƙaunarta amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu ɗari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa.

Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata banza ya ƙyale ta.
Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daɗi idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daɗewa ba.

Ummi a gabanta aka fara haɗa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ƙasa ana tsuma su.
Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure.
Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba.

Mami ta ƙara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son wulaƙanta ɗan Adam irin na raihan, ƙarshe sai da yayi blocking ɗin ta, dan ta daina damunsa da kira.

Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta kusa dawowa.

*
Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma ɗaukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ƙwaya biyu da ta je da su, sai da aka ɗinka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haɗa kayan gyaran jiki masu haɗe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi.

Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haɗa mata.

Mariya ta kalli dr. Ta ce “Ka yi mini alƙawarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?”

Yayi murmushi ya ce “Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba”

“To ai zaka dawo da ita ko?”

“In sha Allah”

“To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka”

“In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai”

Ta kalli ummi ta ce “Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ƙyuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga dukanki kin ji ko?”

Ummi ta riƙe hannunta ta ce “To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?”

Ta ɗan yi jimm sannan ta ce “Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke ba”

Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daɗi.

Da ƙyar suka rabu suka nufo hanyar Kano.

Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta.

Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo.

Ummi ta shiga har falo, ta ce wa farida sun dawo, ta amsa mata a yatsune, sai dai fuskar inteesar kawai ta kalla ta san matsala ce ta kawota gida.

Ummi ta koma ɗakinta, suka din ga hira ita da noor tana bawa noor labarin mamanta.

Noor ta ce “Kuma ki ka yadda ki ka dawo, wallaahi idan ni ce ba zan dawo ba, amma na san saboda yaya raihan ki ka dawo ko?”

Ummi ta ce “Ban sani ba”

Suka din ga dariya, noor ta ce “In gaya miki, Inteesar mijinta ya ɗauki amaryarsa sun tafi umara, shi ne take kuka wai ba a tafi da ita ba”

“To waye ya tambaye ki?”

Noor tayi shiru tana ƙifta idanu.

Haka nan take murna, ta san yau za ta ga raihan, ta rasa dalilin da ya sanya take murna.

Haka nan ta samu kanta da yin shirin haɗuwa da shi.

Ta ɗauki kayan tsaraba da ta zo da su, har da su kayan turaren wuta ta kai wa farida, ta karɓe ba tare da godiya ba.

Bayan sallar magariba ummi ta saka rigar atamfa bubu, tana ta fama ta ɗaura ɗankwali, abu ya gagara saboda ba ta saba ba, ƙarshe noor ce ta ɗaura mata da ƙyar, shima gashin ya ƙi rufuwa, sai da ta saka hula sannan aka ɗaura ɗan kwalin.

Ta yafa mayafi, tana ta rufe-rufe tana tunanin anya za ta iya fita a haka? Kiran wayarsa ta gani, ta tashi ta kalli noor ta ce “Anya in fita a haka kuwa?”

“Wallahi kin yi kyau, kin rufe ko ina kuma”

Da ƙyar ummi ta iya fita, tana ta kare jikinta, ta ƙarasa in da yake.

“Oyoyo sweetheart, long time”

Tayi murmushi ta zauna, tana kawar da kanta gefe.

“Congratulations once again, ya ki ka baro mini maman?”

Ummi ta yi murmushi ta ce “Tana lafiya ƙalau”

“Kin bata labarina kuwa?”

Ummi ta ce “Idan na yi mata babu lallai ta gane ma”

Ya ce “Ba ki yi niyya ba dai, zan je da kaina mu gaisa ai”

“Ka gama yajin?”

Yayi murmushi ya ce “Ke ma haka zaki ce?”

Ummi ta ce “To ba yajin ka yi ba, ko kunya ba ka ji ba?” Yayi dariya ya ce “Na samu mafita ai, kin yi kyau sosai da sosai wallahi, Allah ya nuna mana ranar nan lafiya babyna” ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kanta.

Kausar ce ta nufo in da suke zaune, dan haka yayi shiru yana kallon ta.

Cikin mamaki take kallon raihan, yanzu wannan ne zai auri ummi? Wannan yaron, amma kuwa tayi asara, ko kuma shi yayi asarar kyakykyawan matashi kamar wannan ya auri ummi. Ta yi maganar a zuciyarta

Cikin gadara ta ce “Ke ki zo maama tana kiranki, wa ki ka barwa yin abincin daren da haryanzu baki ɗora ba,” tayi maganar cike da son wulaƙanta ummi a gaban raihan.

Raihan ya ce “Tana magana da mijinta ne, idan kun matsu ku ci, ku dafa, tana buƙatar hutu, tun da yau ta dawo daga tafiya, kuma ina buƙatar yin magana da ita”

Zare ido ummi tayi ta ce “Na shiga uku, raihan”

“Shhh” ya ɗora yatsansa a kan lips ɗin sa yana zare mata ido.

Ya sake kallon kausar ya ce “Ki koma ki ce ba za ta yi ba”

Ayshercool

CUTARWA

35

Galala kausar ta buɗe baki tana kallon raihan.

“Ko ba ki ji me na ce ba ne?” Yayi maganar yana kallon kausar.

Ta kalli ummi, ta ce “eh lallai, zaki shigo zaki haɗu da maama”

Raihan ya ce “Idan ta shigo kar ku bar ta da rai” kausar ta juya fuuu ta tafi.

A rikice ummi ta ce “Raihan, meyasa zaka yi haka? Ka san me zaka jan yo mini ne?”

Ya ƙare mata kallo ya ce “Idan kin koma gidan, ki tsaya ki zuba musu ido su illata ki, ummi ba fa kowanne lokaci ne haƙuri yake maka amfani ba, meyasa da ba a ce sai kin yi girkin ba sai da na zo? Dole ki rage wannan shirun naki, kuma ki shirya tsaf, domin akwai ƙalubale a zaman da zamu yi, zaki fuskanci challenge daban-daban dole ki din ga ƙoƙartawa, a yanzu dai duk abu ba zaki daku ba, dan haka kar ki bari wani abu ya baki tsoro, idan ma dukkan ne ki rama, ki daina zama ana cin kashi a kanki, tun da kin kusa bar musu gidan”

Ummi ta yi shiru tana nazarin matsalar da raihan ya jefa ta a ciki.

Ya basar ya ce “Baki bani labarin Maiduguri ba, ya ki ka ga garin, ya kuma ki ka ji da ki ga mama?”
Duk da a tashin hankali take, sai da ta yi murmushi, ta ɗan saki jiki, ta bashi labarin yadda ta ga garin, da abubuwan da suka faru.

Har ta fara mantawa da matsalar da raihan ya jefata a ciki.

Da zai tafi ya zura hannu a aljihunsa, ya ajiye mata kuɗi, ya ce “Na san ba zaki rasa buƙatunki ba, sannan ranar monday zamu je banki a buɗe miki account, zan saka miki kuɗin kayan lefenki a ciki”

Ta kalli tudun kuɗin da ɗan yawa, ta ce “Ka bar kuɗin nan mana, hidima ce a gabanka sosai”

Ya girgiza kai ya ce “Kar ki damu, ai ba wani kyautar kuɗi nake yi miki ba, kina buƙatar kuɗi kuma na san ba tambayata za ki yi ba, abu na gaba kuma shi ne, saura ki shiga cikin gidan nan, su yi miki magana ki zauna kina kuka, ina da cid na kin sani, idan ki ka bari noor ta ce mini kin zauna kin yi kuka, ni da ke ne, ki kula mini da kan ki amaryata” Ummi ta yi zuru da ido tana tunanin irin tashin hankalin da zata iya fuskanta.

Kausar kuwa jiki na tsuma ta je ta sanar wa farida abun da raihan ya ce, babu kunya a gaban ƴaƴanta ta kuza ashar ta miƙe tsaye jikinta yana tsuma.

“Wai wani ɗan iska ne ma wanda za ta aura ɗin? Wani matsiyacine ne, bari in je in ga ɗan gidan uban waye na ci mutuncin sa daga shi har ita”.

Kausar ta tare ta ta ce “Wallahi wani ɗan yaro ne, dan dai yana da jiki ne, amma wallahi ba ki ganshi ba”

“A’a bari na ƙarasa na je na ga wani shegen ne, ita ma ba ta isa ba balle shi”

Kausar ta ce “A’a maama, ba mutuncinki bane ba ba girmanki bane, ai kin fi ƙarfin haka, dan Allah kar ki je, ki jira ta shigo ki ci ubanta”

Noor ta ƙyalƙale da dariya, har da tuntsurawa, ta ce “Hmm wallahi maama baki san yaya raihan ba, ba fa matsiyaci bane da ki ka faɗa, ranar da aka kawo kuɗin auren anty ummi, kin ga motar babansu kuwa?”

“Rufe mini baki kan na zo na tatsile ki, munafuka kamar na saka da ke” noor ta tura baki tare da yin shiru.

Sai da ummi ta nufo shigowa cikin gida, ƙirjinta ya tsananta bugawa, wani irin tsoro ya shige ta, ta din ga tunanin yaya za ta yi.

Ganin har ta shiga ɗakinta babu wanda ya ganta, ya sanya ta rufe ƙofarta ta ciki, tana fargabar abun da hakan ka iya haifarwa.

Farida na zaune na jiran shigowar ummi, dan ta san dole za ta shigo ta ce za ta yi girkin, dan haka ta yi niyyar wulaƙanta ummi, sai dai shiru babu ummi babu dalilinta.

A fusace farida ta kasa jurewa, ta tafi harabar gidan, kausar tana riƙeta tana ƙoƙarin hanata.

Sai dai suka tarar da kujerun babu kowa, ta tambayi mai gadi, ya ce mata tun ɗazu suka shiga cikin gida. cikin zafin rai da zage-zage ta nufi ɗakin ummi, tana wani irin bugun ƙofar kamar za ta hau iskokai.

Noor ta fito ta ce “Maama maƙwabta fa suna jin ki, kina ta ɗaga murya”

Banza ta yi wa noor, ta cigaba da bugun ƙofar ɗakin ummi, tana ɗura mata ashar kamar bamagujiya.

Ummi kuma wani irin tsoro ya kamata, ta kasa buɗewa tsoro take ji, ba ta san me faridan za ta iya yi mata ba idan ta buɗe.

Sai da farida  ta ji ƙarar motar dr. Sannan ta saurara da bugun tana huci, dr. ya ƙaraso ya tarar da su a tsaitsaye, ya ce “Lafiya kuwa?”

Farida ta ce “Ina fa lafiya? wallahi na gaji, wai ba wurin uwarta ka kaita ba, meye na dawo da ita gidan nan, to wallaahi barin gidan nan za ta yi, ko a kan bola uwarta ta take, ta je su ƙarata”

Dr. Ya ce “Wai meyafaru ne?”

“Sai ka yi magana ta buɗe ƙofar ɗakin ka tambayeta ka ji, tun da kai ka isa da ita, ni tana ganin sa’arta ce”

Dr. Ya bubbuga ƙofar ɗakin ummi ya ce “Mamana ni ne buɗe ƙofar”

Cikin tsoro da fargaba ummi ta buɗe ƙofar, kallo ɗaya yayi mata ya san a tsorace take.

“Meyake faruwa?” Ya sake tambaya.

“Dole ka ce meyake faruwa tun da ta riga ta raina ni, wallahi ba zan cigaba da zama da yarinyar nan ba, ka mayar da ita wurin uwarta wallahi ba zan cigaba da zama da ita ba”

Cikin zafin rai ya ce “Dan Allah ki nutsu ki yi mini bayani, ummi ba ta taɓa yin haka ba, me ki ka yi mata?”

Cikin takaici farida ta ce “Au tambayata ma ka ke yi me na yi mata?”

“Dr. Maama ce fa ta aika anty kausar, wai ace ummi ta zo tayi girki alhalin yaya raihan ya zo, aikuwa ya ce ba za ta zo ba, anty kausar ta je ta yi girkin, ko su kwana da yunwa”

Gaba ɗaya suka tsaya suna kallon noor, da ke wassafa abun da aka yi.

Ummi ta yi saurin cewa “Dan Allah anty ki yi haƙuri, wallahi ba ni na faɗa ba, kuma tsoron abun da ya faru da rashin sanin abun da zan ce miki ya sa na rufe ƙofar, kunya ma nake ji, dan girman Allah ki yi haƙuri”

Dr. Ya ce “Ummi wuce ki je ki kwanta, Allah ya yi miki albarka”

Ya kalli Farida ya ce “Ai gara da ya nuna miki ɗan zamani ne shi, kuma gaskiya ya faɗa miki, idan ba zaku girka ba ku zauna haka, dan ba baiwar ku ba ce ba, banda zubar da kai da son nunawa duniya rashin sanin ciwon kanki, su ƴaƴanki haka ki ke yi musu, shikenan yarinyar nan babu damar ta huta, har a gaban mijin da ta aura sai kin yi yinƙurin tozarta ta? Meye na wani ta zo ta yi girki, a bari ta dawo mana”

Babu kunyar idon ƴaƴansu farida ta din ga zuba wa dr. Rashin mutunci a gaban yaransa.

Yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya shareta.

Har da iƙrarin ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, tun da ya fifita ummi a kan ta, sai ya ware mata kitchen ɗin ta ya raba musu kwana kuma.

Sosai ummi ta yi kuka, ba kowa ya ja wannan abun ba sai raihan.

Tun daga ranar takun saƙa mai zafin gaske ya shiga tsakanin ummi da farida, idan ta taho kausar ta taho, sai ta bangajeta, sabon wulaƙanci da tozarci iri-iri.

Farida har da iƙrarin in dai dan ta samu mijin aure ne, ta fara take-taken iskanci, sai gidan mijin ya zame mata gida mafi azaba da tashin hankali.

Ummi ta mayar da hankali a kan addu’a, tare da yaƙinin ko da raihan zai wulaƙanta ta bayan, ba zai kai yadda Idris ya ci zarafinta ba, tun da shi mutum me mai ilimi.

Can gida ma raihan Mami ta sake sako shi a gaba,  duk ta in da ya motsa idonta na kansa, gashi sai cigaba da tura masa safiyya take yi, ɓangaren anty rakiya da safiyyan ma sun riƙe wuta sosai da sosai.

Ummi kullum sai sun yi waya da mama da su yaya maryam, maryam tayi ta gaya mata shirye-shiryen biki da suke yi, ummi sai dai ta yi murmushi ba ta iya cewa komai saboda kunya.

Ana tsukin wannan tashin hankalin, jami’ar bayero suka kori kausar daga makaranta, saboda rashin kawo points ɗin da ake buƙata, ga Inteesar gidan miji ya ƙara yi mata tsanani, saboda abokiyar zamanta ta samu ciki, da mijin da danginsa duk sun juya mata baya ta amarya suke yi.

Hakan ya saka ummi ta ɗan samu sassauci, kamar yadda farida ta ce ta daina shigar mata kitchen, abinci sai ta ɗan sai abu ta ci, da ta ga babu sarki sai Allah idan an yi girki ba ya ciyuwa, sannan ta ce ai ita da yaranta ba bayin ummi ba ne, ita ce yakamata ta zama baiwa, tun da tana cin albarkacin su, dan haka dole ta fito ta yi musu girki su ci.

Duk wannan abun bai damu ummi ba, dan ko a jikinta, farida ta shiga cikin tashin hankalin yadda za su sanar da dr. An kori kausar daga makaranta.

Wani irin kyau da sheƙi fatar ummi ta din ga yi, tayi kyau sosai da sosai, ga wani irin ƙamshi na mussaman da yake ratsata.

Raihan daga ya dawo daga office, sai mami ta tsiri kirshe shi ta hana shi fita,wai dan kar ya je wurin ummi, abun da ba ta sani ba shi ne, yana tsaka da aikin ma idan ya so ganinta sai ya ajiye yayi tafiyarsa wurinta.

Ummi ta dage a kan cewar, raihan ba zai saka mata kuɗin lefe a account ba ita tsoro take ji, yayi yayi da ita taƙi yarda.

Hajiya Aisha ce ta din ga kiransa tana tambayar sa ya batun lefe, ya ce mata sai sun yi aure zai yi mata, yanzu akwai matsala.

Hajiya Aisha ba ta takura masa a kan sai ta ji matsalar ba, ta san ta mecece dan haka ta ƙyale shi.

Amma ta ce masa dole ya yi wa ummi kayan fitar biki na gani na faɗa, ya amince da hakan ya ce mata su ba zasu yi wasu bidi’oi ba, sai an ɗaura aure juma’a zai yi reception da abokansa da ƴan uwansa, ita kuma su yi taronsu Saturday a kaita.

Lokacin biki ya cigaba da ƙaratowa, dr. Shikaɗai yake faɗi tashin sa, babu mataimaki sai Allah, babu wani wanda zai ba shi shawara, shi yake ta ƙoƙarin playing both roles ɗin, ya kira raihan ya tambaye shi ya yanayin gidan da zai ajiye ummi, saboda ya san me zai saya, raihan ya ce masa kar ya takura kansa yayi iya abun da zai iya yi.

Ummi ta sanar da dr. Abun da raihan ya ce mata a kan kayan lefe, dr. Ya ce “Ummi, ba kayan lefen ba, zaman aure mai ƙarko dan dai kayan da zaki saka, ni zan yi miki kar ki damu”

Ummi ta ce “Dama ba damuwa na yi ba, gaya maka dai kawai na yi”

Ya ce “Yauwwa mamana, na san ba zaki damu ba dama, Allah ya yi miki albarka”

Ta amsa masa da amin.

Dr. Kallon farida kawai yake yi, dan tuni ya san an kori kausar daga makaranta, amma taƙi gaya masa sai gaba da take yi da shi ma, a kan abun da ya faru tsakanin ta da ummi.

Message ɗin da ummi da tayi tozali da shi a wayarta ne ya girgiza ta, ta duba lambar ba ta maryam ba ce ba, dan ta daina ɗaga kiran maryam, idan tayi mata message kuma gogewa take yi.

Ta duba lambar a Truecaller ta ga an rubuta safiyya.

Shiryayyen zagi ne na cin mutunci da cin zarafi ta shiryowa ummi mai zafin gaske, tare da tabattar wa da ummin cewa ita ce matar da aka zaɓa masaya aura, dan haka ko ta aure shi tamkar zaman haya za ta yi a gidansa.

Ran ummi yayi mummunan ɓaci, ta sake duba message ɗin, sai ga kiran wayar lambar ya shigo wayarta, kamar kar ta ɗaga, sai kuma ta ɗaga ta saka a kunnenta ta yi sallama.

“Na san zuwa yanzu kin ga message ɗina ko? To kina magana da safiyya matar da raihan zai aura, tun wuri idan ki na son kanki da arziki, ki fita harkarsa, domin kuwa babarsa ba son ki take yi ba, mummuna da ke har zaki ce zaki aure shi kin yi masa asiri dan mugunta, to wallahi raihan nawa ne kuma sai na aure shi, ke ban da mugunta ma kina bazawara ni kuwa budurwa ce, ba zaki haɗa kanki da ni ba, mummuna kawai” gaba ɗaya kalaman yarinyar ya tabattar wa da ummi yarinya ce.

Ummi ta yi murmushi ta ce “To meye a ciki safiyya? Namiji ba mijin mace huɗu bane ba? Sai ya auremu duka mu yi zamanmu, da matar so da matar shige, sai a cika bakin bazawara da budurwa, ai ni bani da damuwa ki tambaye shi ki ji, lafiya ƙalau zamu zauna da ke, in dai wannan alfarmar ki ke nema, na yi miki ƙanwata Allah ya bamu zaman lafiya”

Ta katse kiran ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri, dan ba ta tunanin daga ƙuruciyarta zuwa yanzu, ta taɓa tsaya wa ta mayar wa da wani martani ba.

Ƙasan zuciyarta kuma wani irin tafasa yake yi mata, da tuna yadda take ce mata wai ita ce matar da aka zaɓa masa, lallai akwai aiki a gabanta kamar yadda yake gaya mata, to meyasa bai gaya mini ba?’ ta tambayi kanta.

Kiran Safiyya ne ya cigaba da shigowa, amma tayi banza ta ƙi kula wayar, har magariba tayi ranta a ɓace yake, da ta tuna maganganun Safiyya sai wani irin haushi ya kama ta.

Tana kallon kiran raihan da ta yi saving lambar da MD, amma ta yi burus da shi, taƙi ɗaga kiran.

Abun ya bashi mamaki, dan haka da safe ya zo har gidan, ya duba ko bata da lafiya ne.

Amma ya ga ta fito da shirinta na zuwa aiki, har ya fara murmushi, kawai ya ga ta yi gaba, ba ta nufo in da yake ba, kan ya bita ga shige lunguna, ta ɓulla titi ta haye napep ta yi tafiyar ta.

Nan da nan raihan ya kiɗime, ya fara tunanin laifin me yayi mata? Da take share shi haka? Ya rigata isa wurin aikin na ta, ya tarar mai gadi ya buɗe wurin yayi shara.

Ya shiga ya zauna, yana jiran isowarta, da ta iso ɗin ma, tana kallonsa ta ajiye jakarta ta shiga hidimomin ta, kallon ta kawai yake yi, ya zuba mata ido yana son gano meyake damunta, ko me yayi mata, amma ya kasa gano komai.

Ana ta kirnaa a waya, ana jiransa amma yana zaune yana jiran ummi ta gama jan ajin ta saurare shi.

Shi yadda ta share shin, take abubuwan ta ma, burge shi yayi, da alama fushi take yi.

Ga wani irin kyau da ta yi kamar ya sace ya ya gudu, ta yi kyau sosai da sosai, ta ɗan washe sai sheƙi fatarta take yi.

Ta zo ta zauna, ta kunna computer ta, za ta fara aiki, ya zuba mata ido, duk da a takure take da kallon, amma ta wani maze.

Dukan teburin yayi da ɗan ƙarfi, sai da ta razana, ya ce “Yaushe zaki saurare ni ne?”

“Ba rana ta bashi amsa tana harararsa” a ransa ya ce “Wow, ta fara iya tsiwa”

Ya kwantar da murya ya ce “Ayi haƙuri dan Allah, laifin me na yi ne? Kina kallona har ki ka share ni ki ka yi tafiyarki?”

“Ai na zata ɓatan kai ka yi ai, gidansu Safiyya zaka je”

Wani irin shock ya ji da abun da ta faɗa, wani irin shu’umin kallo yayi mata, sannan ya ce “Wacece Safiyya kuma?”

“Ka fi ni sani ai, idan ka san an haɗaka da wata a gidanku, ni me zaka yi mini?”

“Ke a ina ki ka santa?”

A ɗan ƙule ta ce “Wace irin tambaya ce wannan? Kirana ta yi a waya” tayi maganar tana tura masa wayarta.

Ya ɗauki wayar yana dubawa, kawai ya kwashe da dariya.

Ta zuba masa ido tana kallon sa, ya ce “Kina da haƙuri da kawaici a kan komai, amma banda kishi kenan? Aishikenan gaskiya ne Safiyya ita ce wadda ake son haɗa ni da ita, ni kuma ke nake so, shiyasa na ce miki akwai ƙalubale, ko ba komai safiyya ta saka na gane in da ki ka dosa, yanzu zaɓi ya rage naki sweetheart, ki kula da ni sosai kar Safiyya ta ƙwace miki ni, kin san zuciya na son mai kyautata mata, ke kin ce ba kya so na, safiyya kuma tana so na, ki zage damtse kar ki bari a ƙwace ni, i so much love you baby”

Ɗaga ido tayi ta kalleshi, ya ga kamar hawaye ne yake shirin taruwa a idon ummi, ya tashi tsaye ya ce “Bari in tafi wurin safiyyan, tun da ita take so na, na san zata yi mini, idan kin tashi ki kirani”

“Idan ka je kar ka dawo, a ɗaura muku aure yau”

Gwalo yayi mata ya ce “Ki gama iyayin da tsiwar, raihan ɗin dai ki ke so”.

Ayshercool

  CUTARWA

36

Ya fice daga shagon yana murmushi, ta iya ɓoye fushinta da damuwa, amma ta gaza ɓoye kishinta.

Yana tuƙi yana tuno fuskarta, wai har da yin fushi saboda shi, fushi sosai kishinta ya fito.

Ya shafi gemunsa ya ce “Ina sonki sosai salma, in sha Allah idan na aureki ba zaki sake yin kukan damuwar rashin wani abu ba”

Ummi kuwa, tayi shiru tana tunani, tare da ganin kamar tayi wauta raihan ya gano tana kishinsa, tayi guntun tsaki za ta cigaba da aiki, kawai sai Safiyya ta faɗo mata.

Sai gabanta ya faɗi, gaskiya ne akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, amma ita babu abun da ya taɓa haɗa ta da Idiris har suka rabu, a take kuma tunaninta ya sauya da tunanin kar matsalar da ta faru da ita a farko ta sake faruwa da ita.

Tayi shiru tana tunani menene mafita? Ita ba ƙawaye ba, mamanta kuma ba lafiya ba su yaya maryam kuma ba sabawa suka yi ba, ko da sun saba ma, ba zata iya gaya musu wannan lamarin ba.

Ta din ga saƙe-saƙe a ranta, ta tuna duk da tsanar da Idiris yayi mata, larurar nan ta ƙara taka muhimmiyar rawa, wurin kashe mata aure, dan da ya samu abun da yake so, da sai ya gama moreta kan ya saketa, ta tuna yadda ya din ga ƙoƙarin haike mata tana yarinya, take ta kawar da tunanin, dan a duk lokacin da ta tuna har kuka take yi, yadda Idris ɗin yake lalubeta, ba ta jin a duniya ko zata yafewa kowa za ta iya yafewa Idiris, ba ta riƙe CUTARWA! idan an yi mata amma cutarwa irin ta iya da Idiris ba zasu goge a tarihin rayuwarta ba cikin sauƙi.

Ta cigaba da tunani a irin wa’azin da take bibiya, mussman na malamai daban-daban da sauran shirye-shiryen gidajen rediyo, domin kasancewar ta ƴar jarida, ya sanya tana yawan sauraren Radio, da bibiyar labarai, ta fuskanci cewa duk soyayyar da namiji yake yi wa mace, idan aka samu naƙasu akwai matsala, ƙila ba lallai raihan ya jure ba ya auro safiyya su juya mata baya, kamar yadda aka yi wa inteesar.

Sai kuma kawai ta ga abun banbarakwai, wai ace raihan ya aureta shi ne mijinta, ta haɗa shimfiɗa da shi, goɗai-goɗai da ita, kawai ta ji wata kunya ta sake kamata.

A ƙarshe ta yanke shawarar yin haɗin da malamar asibitin nan ta taɓa bata, na kanumfari, citta, namijin goro da tafarnuwa, tun da maganin sanyi ne sosai.

Aikin ma dai ta kasa mayar da hankali a kansa sosai, sai saƙe-saƙe, rayuwar aure rayuwa ce da ke buƙatar a zaunar da mace a karanta mata darussa daban-daban, ba kuma wai sai lokacin da aka kawo kuɗin aure aka saka mata rana ba, yakamata mace ta san wasu abubuwan, amma ummi ba ta da wani da zai zauna da ita ya buɗa mata, duk da daga ita har mijin nata ba wani mai yawan shekaru sosai.

*
Yaya maryam ta kira dr. A waya,suna yi masa tunin ya kawo musu ummi, suka cigaba da shirye shiryen su na al’ada, ga mariya ma duk ta ishesu, har da koke-koke a kan a dawo da ummi.

Ya ce mata so yake ƙarshen wata, tayi sallama da wurin aiki ya rage saura wata biyun sai ta dawo.

Ya gaya musu yadda aka tsara bikin, ta ce a matsayin su na dangin uwa, zasu gabatar da nasu bukukuwan a nan maiduguri, sai su taho da ummin kano, suma su yi nasu.

“Amma ina ganin kar ɗawainiya tayi muku yawa, ba sai kun yi ba, ku bari duk ayi a kanon”

Ta ce “Haba baban ummi, ƴar mariyar ƙwaya ɗaya tal mu kasa bajinta a bikinta, a’a ka bari zamu yi mata bikk na gani na faɗa, sai mu taho da ita, da mu da abun da Allah ya yassare mana”

Ya ce “To shikenan, in sha Allah zan kawota da kaina, amma saura sati biyu biki, zan zo na kaita gagarawa, ta je ta yi musu sallama, ta kuma basu katin bikinta”

Yaya maryam ko sunan garin ba ta ƙaunar ji, balle wani abu da zai sake haɗa su da garin, ta kasa jurewa ta ce “Amma ba a iya aika musu ba, dole sai ta je”

Dr. Ya ce “Na san abun da yake cikin zukatanku, amma ba a canzawa tuwo suna, dangin mahaifinta ne dole ku yi haƙuri”

Ta ce “To shikenan, Allah ya kaimu ƙarshen watan, sai kun zo ɗin”

Ya amsa mata da Amin.

Raihan daga shi sai Hajiya da kuma Hajiya Aisha suke ta shirin bikin, sai Alhajin sa, tausayin ɗawainiyar da yake ta yi, ya sanya Salim ɗan shiga lamarin, yake taimaka masa da shawarwari, dan shi abokansa duk sun yi aure, raihan kuwa age mate ɗin sa wasu ma ba su kammala makaranta ba.

Saura watanni biyu bikin ummi, dr. Ya ce ta haɗa kayanta, zata tafi maiduguri kamar yadda ya yi alƙawari.

Ummi murna kamar ta taka rawa, dan dama jin ta take yi a matse a gidan nan, farida ta sakata a gaba da masifa iri-iri.

Ta rubuta takarda ta kai wa manager na barin aiki, manager kamar yayi kuka, saboda sun saba da ummi sosai da sosai, kuma suna jin daɗin aikinta, ba ƙyuya babu ganin ido komai na ta tsakani da Allah, sai dai sun yi mata fatan alkhairi sosai da jin ummi za ta yi aure.

Tana ta shirin tafiya maiduguri, raihan ya kirata a waya, ya ce mata manager yana nemanta, tayi mamakin yadda aka yi manager bai kirata ba, ya kira raihan, kai ka ce shi ma ma’aikacin su ne.

Ko da suka je, manager ya ce yayansa ne yake son ganin ummi, su ɗan jira shi zai zo. Manager sai cewa yake “Shikenan tayi aurenta ta huta da nacinka, ko gidan nata zaka din ga bin ta kana takura mata?”

Raihan yayi wani irin murmushi ya ce akwai wanda ya isa ya raba ni da ummina ne? Kullum ina gidanta, ko kuma ka bani ƙanwarka na aura a haɗa mu biyu”

Manager ya harare shi ya ce “Aikuwa da mijinta ya zaneka saboda hayyatarka, in baka ƙanwata kai wa zai maka aure yanzu? Raihan da kana ganin ka fi ni girma gani ka ke kai wani babba ne ko? In sake jin ka yi maganar auren nan, sai na zaneka”

Wata irin kunya ta kama ummi, ta san da kunya idan ya bayyana raihan za ta aura, dan manager ya ɗauka kawai ɗan uwanta ne, irin sako da sakon nan.
Raihan kuwa ya din ga dariya, ya ce “Zan baka mamaki kwanan nan”

Shugaban wurin ne ya yi sallama, da yaransa suka amsa masa, ya samu wuri ya zauna suka gaggaisa, ya ɗan yi musu raha kasancewar sa mutum mai barkwanci.

Ya ce “Ummi yanzu haka zaki tafi ki barmu, mijin ba zai bari ki cigaba da zuwar mana ba?” Ummi ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Raihan ya zuba mata ido ya ji me za ta ce, amma tayi shiru.

Ya yi ta yi wa ummi nasiha a kan zaman aure, ba tare da sanin da angon a wurin ba, sai dai raihan ya fara jin haushin yadda manager ya tsare ummi da ido, yana yi mata faɗan kamar mai rarrashinta.

Bayan sun gama ya ce ya bawa ummi kyautar sabon fridge babba, da kuɗi dubu hamsin da certificate na karramawa saboda gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙoƙarin da tayi wurin cigaban wurin.

Raihan cikin girmamawa ya ce “Masha Allah, mun gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya sa afi haka”

Ummi ma godiyar take yi masa, ta san kuɗin fridge ɗin nan ba kaɗan ba ne ba, ga kuma kuɗi da ya bata.

Manager ya ce wa raihan “Ka gani, haƙuri mai tarar da rabo, da ba ta raina 15k ba, ga rabon da ta tarar nan, ka canza hali raihan. Ko kuma tun da ta tafi kai ka zo mu baka aikin”

Ya harari manager ya ce “Ba zan yi ba”

Har da masu kai fridge ɗin aka haɗa ummi, masinjojin su.

Ummi ta kira dr. Ta gaya masa, ya din ga murnda sanya albarka ya ce zai je yayi musu godiya.

Ana gobe ummi za ta tafi maiduguri, raihan kamar yayi mata kukan ba ya son ta tafi, saboda zai daina ganinta a kai-a kai, sai dai yayi mata alƙawarin zuwa ya gaida mama.
Haka zalika ya tura mata kuɗi a account ɗin ta, ya ce idan ya tashi zuwa maiduguri zai taho mata da kayan fitar biki.

Suna zane suna hirar, wayar ummi ta fara ringing, ta ɗaga wayar, sai ya ga ta yi shiru tana kallon sa, amma ba ta ce komai ba.

Kawai sai ya tsargu, ya karɓi wayar ya saka a hansfree.

Muryar Safiyya ya ji, tana ta zazzaga rashin mutunci, da kalaman muzantawa ga ummi.

Jin ummi ba ta ce komai ba ya sanya safiyya cewa “Malama ba magana nake yi miki ba?”

“Da raihan ɗin ki ke magana ba ummin ba” hankali a tashe ta kashe wayar, tana salatin Allah ya rufa mata asiri.

Ya kalli ummi ya ce “Dama haka take kiranki tana ci miki mutunci ba ki gaya mini ba?”

Ummi ta ce “To me zan ce, kullum sai in ƙare a kan ƙara, ni ba zan iya ba tun da ka ji yanzu da kanka shikenan, dan Allah idan zaka aureta ka aureta amma ni ta daina zagina”

Ya jinjina kai ya ce “Ina fatan dai ba shiru ki ke yi mata ba?”

“Ni mu bar wannan zancen bana so” tayi maganar tana zumɓura baki, ya ɗan ƙura mata ido, kishin ne yake damunta, dan haka yayi mata shiru kawai.

Daga wurin ummi da niyyarsa ya je gidan su safiyya, sai dai ya fasa ya tafi gida kawai.

Ummi ta tattara muhimman kayanta, ranar tafiya ta je yi wa farida sallama, amma ta ka da baki ta ce mata Allah ya raka taki gona.

Mami na ta sake maimaitawa raihan idan ya kuskura ya kashe kuɗi sosai a harkar auren ummi, sai ta ci masa mutunci fiye da yadda yake zato.

Kwana biyu da tafiyar ummi maiduguri, Raihan ya je gidan su safiyya, anty rakiya har ta fara yashe baki, tana cewa “Babban mutum barka da zuwa, yau kai ne a gidan namu?”

Ya ce “Eh, safiyya fa”

Ta ce “Ahh wurin mutuniyar aka zo kenan, to bari na yi mata magana”

Kasancewar Safiyya ta san abun da ta aikata, ya sanya gabanta faɗuwa ta ce ba zata ba.

“Dan ubanki abun da muke neman zaki ce ba zaki ba?”

Kamar za ta yi kuka ta ce “Ni fa tsoro nake ji, na gaya miki abun da ya faru”

“To sai ki bari kanki ya kulle, ba mace ba ce ke? Guda nawa raihan ɗin yake banda ma ya jajibo aure? Tashi ki je dalla”

Har ta shiga falon tv yake kallo, bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, sai da ta zauna ta fara gaishe shi ya amsa, ya tambayeta ya makaranta ta ce masa lafiya ƙalau, sannan ya kalleta ya ce “Safiyya na san kin san abun da ki ka aikata, to ki sani, ba zuwa na yi bin ba’asi ba, kuma ba wani ya gaya mini ba, ta gaya mini na farko na kawar da kai, ban zaci irin wannan zagin ki ke yi mata ba, to ba sa’arki ba ce ba, kuma hakan da ki ke yi ba zai canza komai na batun aurena da ummi ba, wallahi idan ki ka sake kira mini mata ki ka ci zarafinta sai na gwada miki waye raihan, ba ruwana da wani zumunci sai na ɗaureki an ci tarar ki, na gaya miki. Ni ba ƙyale-ƙyale nake bi ba, mutunci, tarbiyya da soyayyar da nake yi mata ya sa zan aureta, kalli jikinki kowa ya gama gani, ba shigar mutunci a tuninki wannan ce wayewa safiyya? Dan an ce miki matar da zan aura kidahuma ce, ni a wurina hakan ne wayewa, kar ki bari abun da ki ka yi ya taɓa zumuncinmu, dan bana magana biyu, idan kuma Anty na da kuɗin belinki ki cigaba da kiran Salma kina ci mata mutunci tun da baki da kunya” bai ko tsaya yin sallama da anty rakiya ba, ya tashi yayi tafiyarsa.

Aikuwa kan ya je gida, tuni sun sanarwa da mami, yan zuwa ta dirar masa da masifa tare da kashedi iri-iri, ciki har da barazanar sanyawa a fasa auren sa da ummi, tare da jaddada masa cewar aurensa da safiyya ba fashi.

Ummi kuwa yadda su yaya maryam suke kula da ita da gyarata, har gajiya ta fara yi, a murza mata wancan, a shafa mata wannan, gashi aka hanata aikin komai, kullum tana kauwwame a wuri ɗaya, daga ci sai sha, banda kayan magungunan gyaran da ake ta yi mata.

Tulin turarukan wutan da ake ta haɗawa kuwa, kai ka ce ci za ayi, ga uban kayan kitchen.

Ummi har hawayen daɗi tayi, saboda irin so da ƙaunar da dangin mahaifiyarta ke nuna mata, gashi dai ba wani ƙarfi ne da su ba, amma sai zuciya da ƙoƙari.

Ga isasshen lokaci da ta samu tare da mama, ga isasshen abinci mai kyau, komai na ta daban.

Saura wata guda biki, raihan yana ta shirin zuwa maiduguri, yana zaune suna shawara da hajiya, a kan yadda abubuwa zasu gudana, ya haɗa akwati guda na kayan fitar biki kawai.
Salim yana zaune sai dai bai tsoma musu baki ba.

Sai daga baya ya ce “Wannan akwatin ɗaya kawai zaka kai sai ka ce tsiya, ba zaka yi lefe ba?”

Cikin sanyin jiki ya ce “Mami ta hana, ta ce bazawara ce, wai kuɗin auren da aka kai ya isa, shi ne na ce bari na yi mata kayan fitar biki, lefen idan ta je gidana na yi mata, amma kalli kayan ka gani masu kyau ne fa” yayi maganar yana buɗe masa akwatin.

Tabbas manyan kaya ne sosai da sosai na alfarma.

Salim ya yi ajiyar zuciya ya ce “Idan ka kai musu sai dai ka yi musu bayani, na ji ka ce maiduguri zaka kai mata, ana yi wa iyaye akwati fa su ma, dole ka yi ƙoƙarin fitar da su kunya, aurensu da tsada sosai”

Hajiya ta ce “Kai a ina ka sani?”

Ya amsa mata da “Abokina umar ɗan can ne ai, kuma ƴar can ya aura, ni da shi muka din ga shirin bikin ai”

Cikin marairaicewa raihan ya ce “To ka taimaka mini mana nima”

Ya girgiza kai ya ce “Bana son babarku ta zo ta ce ba a kyauta ba”

Hajiya ta ce “Ba ƙaninka bane ba? Babu abun da za ta ce”

Haka kuwa aka yi, dan sai da suka sake sayen akwati, aka zuba atamfofi da shadda, wanda ake yi wa iyaye, sannan ya gaya masa zai bayar da kuɗin turaren wuta.

Gwiwar raihan ba ta yi sanyi ba, dan shi a ganinsa komai zai kashe wa ummi bai faɗi ba.

Yadda raihan ɗin ya din ga yi wa salim biyayya, ya sanya da Hajiya ta lallaɓa shi ta ce su tafi tare maidugurin bai yi musu ba.

Can Maidugurin ma da ummi ta ce musu raihan zai zo, aka din ga shirye-shiryen tararsa, dan bai gaya mata da Salim zai zo ba ma.

Mami ta so hana tafiyar nan, amma Alhaji ya taka mata burki, ya ce babu abun da zai hana raihan zuwa maiduguri, tun da matarsa a can take.

Kasancewar ana idar da sallar asuba suka tafi, ƙarfe sha ɗaya na safe suka sauka.

Suka bi adress ɗin da ummi ta basu har gidan suka je.

Kasancewar sun yi shigar kamala, daga shi har Salim, hakan ya ƙara musu kima a wurin ƴan uwan ummi.

Sai rarraba ido kawai yake yi ya ga ummi, aka kawo musu abinci na alfarma.

Sun kai a ƙalla awa guda, yaya maryam ta tsare ummi, ta hana ta zuwa, sai daga baya ta shirya cikin lafaya mai kyau, sai ƙamshin turare take yi, hujin hancin da suka yi mata, ta saka barimar azurfa, sai ƙyalli take yi a kan baƙar fuskarta.

Da tayi sallama tare suka ɗaga kai suka kalli ummi, babu kunya raihan ya kafe ta da ido.

Salim ya jinjina kai a ransa ya ce “Lallai yaron nan akwai tsaurin ido”

Ummi ta wani ƙara cika sosai, ga wani irin ƙamshi da ya cika ɗakin.

“Oyoyo sweetheart” yayi maganar cikin sanyin murya.

Durƙusawa tayi har ƙasa ta gaida Salim, ya amsa mata fuskarsa babu yabo ba fallasa.

Ta juya wurin raihan ma ta gaishe shi, ya amsa yana washe baki.

Ya ce “Tun da ga yaya salim, akwai kuɗi a jikina, sai a ɗaura yanzu kawai” hararsa tayi ta samu wuri ta zauna.

Salim ya mayar da hankali a kan wayarsa, kamar bai san suna wurin ba, raihan kuwa ya rasa control ya din ga zuba a gaban Salim, ummi kuma kunya kamar ta nutse.

“Baby me mama take baki ne? Kin ƙara ƙiba, kalli skin ɗinki”

“Ni fa bana son ƙibar nan” ta faɗa a hankali.

“Ni kuma ina so, baki ga kyan da ki ka ƙara ba, kin ji ƙamshin da ki ke yi kuwa? Anya zan iya jiran lokacin nan, Innalillahi kin ganki kuwa? You look take away, ko dai in yi zamana a nan”

Dukan da Salim yayi masa a ƙeyarsa ne, ya sanya shi yin shiru yana sosa kai.

Ummi ta yi masa gwalo, ta ce “Bari na je n yi wa mama magana, mu shiga ku gaisa” ta tashi ta fita.

Tana fita Salim ya ce “Kai dan ubnka a gidan sirikai fa ka ke? Wannan da bamu zo tare ba me zaka yi?”

Raihan ya ce “Bakomai”

Yayi ƙasa da murya ya ce “Zaka ƙara da kuɗin gyaran jikin da ake yi mata, kara fa aka yi maka da duk ba ta tambayeka ba, zaka saki bakin aljihu tun da ɗiyar ƴan maiduguri zaka aura”

Raihan ya ce “To ai duk ba ta gaya mini ba”

Salim ya ce “Ni yanzu na gaya maka, kuma wannan ginin da ka ke yi, ka je ka ce wa Alhaji ya saya ko ka bashi jingina, ka samu gida mai kyau ginanne ka saya”

Raihan ya ce “To ai ina son gidan sosai “

“To ka ce wa Alhaji ya baka gudunmawar bikin, ka ƙarasa”

Raihan ya yi dariya ya ce “Haka za ayi yaya”

Ya ɗaga masa gira.

Ummi ta ce “Bisimillah ku shigo”

Suka tashi suka shiga, suka din ga gaisawa da mutanen gidan, ummi tana gabatar musu da kowa.

A ɗakin mama suka yi sallama, suka zazzauna, ta din ga murmushi tana amsa musu gaisuwar.

Ta kalli yaya maryam ta ce “Yaya, wannan suwaye?”

“Sirikanki ne, wannan ne zai auri ummi”

Sai tayi dariya ta rausayar da kai ta ce “Ummin za a yi wa aure yanzu? Ai tayi ƙarama da yawa”

Maryam ta ce “Wai ke ummin haryanzu a kan cinyarki take ne tsawon shekaru ba ta girma ba?”

Ta kalli raihan ta ce “To kai ba ka ga munin na ta ba? Iya ta ce mummuna ce babu mai aurenta”

Raihan ya ce “Haba mama, ummi ba mummuna ba ce ba, kalleta fa ki gani tubarkallah masha Allah”

Ta ce “Yauwwa, da ma na faɗa, wani zai ce yana son ummi a haka, amma iya ta din ga yi wa ummi ba’a, har sauran yaran gidan, su yi ta ce mata mummuna ko wasa da yara ba ta yi, kuma duk iya ce ta janyo, da ta tsawatar ai ba za su yi mata ba ko?”

Raihan ya ce “Gaskiya ne, amma ummi ai mai kyau ce, ga ilimi da tarbiyya, ta cancanci a so ta”

Yaya maryam ta ce “Dan Allah ki daina zancen nan da ya wuce”

Salim ya ce “Kamar tana jin daɗin hirar, ki ƙyaleta”

Mariya ta sake cewa “Ka san har malaman makarantar su ummi, wai su yi ta ce mata baƙa, na yi ta kuka, ko ace idonta irin na mayu, da ta fita yara su yi ta cin zalinta, shiyasa ni da babanta mu yi ta sonta, ba ka ga yadda yake son ta ba”

Raihan ya ce “Allah sarki, mu ma muna son ta sosai”

Ta kalli Salim ta ce “Ka ga yadda kakarta ba ta son ta ko? Amma bayan mutuwar baban ummi, matar nan ta ƙwace mini ummi, ba fa iya kula da ita take yi ba, an ce sun azabtar mini da ummi sosai da sosai” tayi maganar tana share hawaye.

Salim ya ce “Ki yi haƙuri ki daina kuka dan Allah”.

Ta kalli raihan ta ce “To ka ga dai yarinya ce, dan Allah ka kula da ita sosai, ka din ga ba ta abinci, idan magariba tayi a saka mata kayan sanyi, cikin dare ma a tashe ta tayi fitsari”

Ya ce “Duk za ayi mama, ai ummi yarinya ce kyakkyawa, duk za a din ga kula da ita”

“Eh, to amma ban bar maka ita ba fa, zaka dawo mini da ita”

Mama ta din ga zuba, suna hira da raihan da Salim, duk rashin sakin jikin salim, suka din ga hira da mama, wani abun idan tana gaya musu, sai tayi kuka, wasu abubuwan ma duk ummi ba ta san sun faru ba.

Har da tambayar maryam, wai anya Salim da raihan ba su ne jaririn da suka haifa ba aka ya ce ya mutu.

Gashi dai ba ta da cikakken hankali, amma a nutse take, malam kakan ummi, ya din ga yi musu nasiha, tare da gaya musu muhimmancin riƙe addu’a.

Salim suka ba su kayan da suka zo da su, Malam ya ce ai ba su suka riƙe ummi ba, dan haka babu buƙatar kawo wannan kayan.

Malam akwai kwarjini, ya kasa magana, Salim ne ya tausasa harshe tare da nuna masa cewar ba su takura ba, duk abun da suka yi wa ummi ta cancanta.

Kuɗin turaren wuta da na gyaran jiki, suka danƙawa yaya maryam masu kauri.

Mama har bakin mota ta raka su, suna cigaba da hira.

Ummi ta ji daɗin karamcin da suka nuna wa mama, mama har da tambayar yaushe zasu kuma zuwa? Su faɗi abun da zata dafa musu.

Yaya ɗanlami ya ce “Ban da larura ma, yaushe mutum zai zauna ya yi ta zuba da sirikai”

Su raihan suka koma kano, cikin farinciki da tausaya wa mama da irin abubuwan da ta din ga faɗa game da rayuwar ummi.

Har suka je gida ummi na kiransu na jin yaya suka je gida?

Mama sai zancen su raihan take yi, ko sunansu ba ta sani ba, tun da Allah ya sa ta haɗu da ummi, bakinta ya buɗe tayi ta surutu amma da ummi take yi, sai kuma su Salim da suka zo.

Da daddare bayan su raihan sun sauka kuwa, ya takurawa ummi da waya, dan duk taka tsantsan ɗin sa sai da ya kusa kauce hanya, sai dai ummi ta yi masa shiru.

Kwana biyu da komawar raihan kano,  Salim da kansa ya samu Alhaji ya tsutsiye shi, wai me zai bawa raihan na gudunmuwa.

Alhaji ya ji daɗin kulawar da Salim ya bawa raihan a kan aurensa, kuma ya lura raihan ɗin ne bai canza masa daga biyayyar da yake yi masa ba, duk da yana da wani muƙami ba.

Alhaji ya ce “Ni za a yi wa solidarity?”

Ya ce “A’a ginin da saura ne, kuma saura wata guda biki, za a kai mahaifinta ya ga gida, kuma da kai da hajiya bamu ga gudunmawarku ba”

Alhaji ya yi murmushi ya ce “Na tsaya na ga iya gudun ruwan sa ne, kuma yayi ƙoƙari sosai da sosai, kuma babban abun da ya burgeni, duk faɗi tashin da yake yi, bai nemi taimakona ba, bai kuma ci amanar da na bashi ba, ya ɗaukar mini kuɗi babu izinina ba, dan haka za a san abun yi, kar ka damu”

Ya ce “Ok, mun gode, dan Allah a bashi da kauri sosai”

“Za a duba, Salim na ji daɗin ƙoƙarin da ka ke yi masa, ka yi playing role ɗin ka na babban wa, saura kuma kai ma ka nutsu ka yi naka auren”

Salim ya ce “Raihan, duk da wasu abubuwan da mahaifiyarsa take yi, ina kallon yadda yake ɗawainiya da mahaifiyarmu, duk da yadda muke ɓata mata rai wasu lokutan, shi sanyin idaniyarta ne, yana ƙoƙari a kan mahaifiyarmu sosai, amma a cigaba da yi mana addu’a” bai jira me Alhaji zai ce ba, ya fita.

Alhaji ya ce “Tabbas raihan babban mutum ne, amma akwai dattaku kam”

Da Alhaji ya tashi, a account ɗin Salim ya tura masa kuɗin gudunmuwar auren raihan, kuɗi masu kaurin gaske.

Nan da nan aka ƙarasa ginin raihan, suka kai Alhaji tare da Dr. Rana ɗaya suka gani.

Jikin dr. Yayi sanyi, gado biyu ya yi wa ummi, da dining da kujeru saiti ɗaya.

Sai dai falukan ummi uku, bedroom huɗu, sai kitchen da sauransu.

Alhaji ya ja dr. gefe ya ce masa “kar ka damu, ka saka abun da Allah ya yassare maka, zan ƙarasa ba tare da kowa ya sanu ba, ai ana ƙoƙari sai godiyar Allah”

Saura sati biyu biki, Raihan ya koma maiduguri ya kai wa ummi katin biki, ya ce ko akwai wanda za ta rabawa a kano ta ce ita ba wanda za ta bawa.

Raihan ya tafi da kwana ɗaya, dr. Ya je, ya ɗauki ummi zuwa gagarawa, ta kai musu katin bikin da kanta, in da ta ji daɗi, sai ya tafi da  noor.

Kamar kullum, tarbar da ta saba samu ita ta samu, sai dai sai kallon ummi suke yi, ta yi kyau sosai da sosai, a nan dr. Ya gaya wa iya cewar ya gano garin su mariya, kuma ummi tana can, sai da suka yi faɗa sosai da iya a kan hakan.

Ummi suna zaune, wata yarinya ta shigo za ta yi sa’ar noor, kallo ɗaya ummi tayi mata ta gane ta, saboda kamar da take yi da hindu matar Idris.

Iya ce ta hau zagin yarinyar tana tambayarta daga ina take?.

Cikin fitsara yarinyar ta ce “Tasha na bi sajida sayar da shinkafa da wake na tayata ta san mini”

“Saboda matsiyaciya ce ke, sai kin tona mana asiri?”

“Tun da aka bar ni da yunwa, ba a ƙaunata dole na ciyar da kaina”.

Ganin da Yarinyar ta yi ummi na kallonta, ya sanya ta ce wa ummi “Ina wuni?”

“Lafiya ƙalau ya ki ke?”

Ta ce “Lafiya ƙalau”

Ummi ta ce “Zo mana” ta ƙarasa gaban ummi ta durƙusa.

Ummi ta ciro kuɗi a jakarta ta ce “Ungo, yo cefane sai mu yi girki mu ci, amma ki daina zuwa tasha ba mutuncin ƴa mace bane, kamata yayi ace kina makaranta duk da an yi hutu”

Yarinyar ta ce “Ni da bana zuwa makaranta, ko abinci basa bani, sai idan babarmu ce ta bani, kowa ya tsane ni, ni ya zan yi ni na ce a haife ni haka?” Yarinyar tayi maganar tana kuka, duk da ba ta san ummi ba, amma ta ji hankalinta ya nutsu da ita.

Ummi ta fuskanci in da zancen ya dosa, ta ce wa noor “Rakata ku yi cefanen, sai ayi girki kowa ya ci”

Iya na kallonsu ba ta kula su ba.

Kusan mintuna talatin, ummi ta tayar da salla, ta ji sallamar su noor, sun dawo, sai dai suna shigowa ba daɗewa Idris ma yayi sallama, kuma bai yi wata-wata ba, ya hau yarinyar ta sa da duka.

Ihu take yi tana neman taimako, ummi ta yanke sallar ta fito da sauri, ya saka itace yana ta jingar yarinyar, har bakinta ya fara kumfa.

Ummi ta hankaɗe shi, ta riƙo ta, bai san wacece ba, ya kuma kawo itacen yana ƙoƙarin janye yarinyar, a fusace ummi ta tsinka masa mari, da ya sanya shi ɗaga ido ya ga wacece.

“Jahilin ina ne kai? Azzalumi mara imani, ƴar ta ka ma baka ƙyale ba, dabban ina ne kai idris?”

Ayshercool

   CUTARWA

37

A razane yake kallon ummi daga sama zuwa ƙasa, iya kuma ta miƙe tsaye da sakakken baki ta kasa magana.

Ummi ta durƙusa ta ɗago yarinyar da take zubar da wani irin yawu daga bakinta, saboda wahalar duka.

Noor kuwa na gefe tana tsuma, duk da basu saba ba, tare suka yo cefane, har noor ta bata shawarar su sayo taliya sai tafi sauri, tun da ummi ba ta gaya musu me zasu sayo ba.
Suna tafe a hanyar ta kalli noor ta ce mata “Ya sunanki?”

“Sunana mariyatul kibɗiya, ana ce mini noor”

“Masha Allah, sunanki me daɗi”

Noor ta ce “To ke ya sunanki?”

“Wai hajara, sunan kakata aka saka mini, ni kuwa na ce wallahi bana so, na canza suna ake ce mini Nana”

“To meyasa ba kya so, ba kakarku ba ce? Au kamar sunan iya ne ai ko?”

Nana ta ce “Eh mana, baki ga yadda ta tsane ni ba, ni ma kuwa na tsaneta, yauwwa idan kuɗin yayi ragowa muka sayi kifi, ba za ta ce komai ba?”

Noor ta ce “Ai idan ma kifin ki ka saya da duka kuɗin babu abun da za ta ce miki, yaya ummi fa babu ruwanta”

Nana ta ce “Na gani, kin san wani abu, wallahi ta burgeni, ga muryarta mai daɗi, a nutse take komai, sau ɗaya na taɓa ganinta sun zo da kawu yahaya, ƴar sa ce?”

Noor ta ce “Ke, ni ma fa ƴar sa ce, iya duk kakarmu ce kenan? To ya aka yi ban sanki ba”

Noor ta ce “Ni ba kakata ba ce ba, kakana ta haifa dan haka babu abun da ya yi mini zafi da ita”

Wani yaro suka haɗu da shi a hanya ya ce “Nana, ana ta nemanki a gida, wallahi ki je gida baba yana nemanki”

“Ba zani ɗin ba, in je a jibgi jaka, gidan iya zan je, tayi baƙi za a dafa abinci, sai na ci na dare zan dawo gida”

Mamaki ya kama noor, jin amsar da ta bayar, da aka ce babanta yana nemanta.

Sai dai sun shiga sashin iya sun yi sallama babu jimawa, Nana ta fara ɗaukko kwanukan da zasu yi amfani da su su yi girkin, Idris yayi sallama da itacensa a hannu, ya fara jibgar Nana.

Marin da ummi ta yi masa ba a kan sa hankalinsa yake ba, face shaiɗan da ya shiga ƙawata masa ummi, hijjabi ne a jikin na roba, dan haka ya kwanta a jikinta, gaba ɗaya tamkar ƙibarta ta koma ƙirjinta, haka da ta juya baya ma, kamar an aunata an dasa mata ƙugunta.

“Ke yanzu lalacewar taki har ta kai haka ummi, Idris ɗin ki ka mara?”
Duk da jikin ummi tsuma yake da tashin hankali da tsoro, dan ko a mafarki ita kanta ba ta taɓa zaton aikata abu makamancin haka ba.

Amma ta ji zuciyarta ta bushe, ta ce “Iya yaushe zaki bari kanmu ya haɗu a matsayin iyalanki ne? Kalli fa dukan da yake yi mata? Mutum ba dabba ba”

Cikin ƙwarin gwiwa, da son ɓoye halin da ya faɗa ya aro jarumta ya ce “Ni zaki mara? Kin san abun da ta yi ne?”

“Ina ruwana da abun da tayi maka? Barewa za ta yi gudu ɗanta yayi rarrafe ne? Abun mamakin daga haɗuwata da yarinyar yau, har ta fara faɗar irin damuwar da take ciki, look at her, just an innocent kid like me before”

Tayi maganar cikin matuƙar rauni, hawaye na zuba daga idonta, tana share wa yarinyar hawayenta da wannan yawun, da daƙalƙallen hijjabin da yake wuyan yarinyar, sautin kukan na ta ma ya kasa fita sai sheshsheƙa, santaleleliyar yarinya kai da ganinta ka san fara ce, azabar datti da rashin kula duk ya dafar da ita.

Bilhakki ummi ta rungumeta tana kuka, wanda kukan na ta yana da alaƙa da tuna irin baƙar rayuwar da ta yi a baya.

Iya kuwa ba ta taɓa zaton ummi ta yi kilewar da zata iya gaura wa Idiris mari har haka ba.

Hashim ne yayi sallama tare da matarsa, ya ji labarin ummi ta zo, ya ce bari ya zo tare da matarsa su gaisa, dan ba su taɓa haɗuwa ba.

Amma ya tarar da mutane cirko-cirko, ga Idiris a gefe yana ta huci, ummi a durƙushe da yarinya tana kuka.

Ya kalli mutanen ya ce “Lafiya kuwa? Meyafaru ne?”

“Ai magaji ba lafiya ba, ƴar daba ta zo mana gida, ashe bayan lalacewa a birnin ina ga ko dai shaye-shaye ko daba ta fara, wai ace ummi ta ɗaga hannu ta zabge Idris da mari”

Saroro yayi ya ce “Wane irin mari kuma ana zaune ƙalau?”

Iya ta ce”Au to ƙarya zan yi maka, ba gata nan a zaune ba?”

Hashim ya ƙarasa gaban su ummi, ya ce “Ummi meyafaru ne?” Ummi ta kasa magana sai kuka.

Ya ce “Nana meyafaru?”

Cikin kuka yarinyar ta ce “Ƙawata na raka tasha, na tayata sayar da abinci, da ta gama ta bani na ci, shi ne babanmu ya biyoni yana dukana da itace” tayi maganar tana kuka.

Magaji ya ce “Tabbas abun da ya baka tausayi, watarana zai iya baka tsoro, Allah ya kyauta, kuma wannan tsayuwar da ku ka yi duk ba mafita ba ce ba, dan Allah kowa ya watse ” haka sai hashim ya sallami kowa.

Suka gaisa da matarsa da ummi, ummi cikin kuka take yi wa hashim ƙorafin abun da yake faruwa a familynsu, na muzanta wanda wata ƙaddara ta same shi, ko kuma a ɗorawa mutum tsana babu dalili.

Ya ce “Ummi, wannan abun da zan iya maganinsa, da tun a kan ki na yi, lamarin yafi ƙarfina, kuma har da sakacin iyayenmu, da son zuciya irin na iyayenmu. Ba irin nasihar da ban yi masa ba a kan kula da yarinyar nan ba, amma yaƙi. Ƙarewa ba ya kula da su da uwarsu, aka korota daga makaranta, uwar ta koma ɗora mata talla, aka tasamma lalata ta, idan ma an lalata tan ban sani ba, duk in da tayi sai tsangwama, na ce ya bani ƴar ya hanani, idan aka ɗora mata tallan sai ta sayar ta kashe kuɗin su yi ta rigima, abubuwan dai duk babu daɗin ji”

Ummi ta dafe kai, tare da faɗin “Innalillahi wa Innalillahi raji’un” muddin ba a takawa wannan lamarin burki ba, ƴaƴa da yawa za su cigaba da shan wahala a gidan, idan har basu zo a yadda ake so ba.

Ummi ta bata kuɗi, ta sayo sabulu ta yi wanka, ta bata kuɗin omo ta ce idan ta je gida ta yi wanki, ta ce washegari ma kan su tafi, ta zo ta karɓi kuɗin abinci.

Nana ta din ga yi wa ummi godiya, ummi ta roƙi Hashim a kan dan Allah azo mata da Nana kano lokacin bikinta, yayi mata alƙawarin da yardar Allah za a taho da ita.

Faranti ɗaya suka ci abinci da ummi, da Nana, nana na ta basu labarin irin azabtarwar da ubanta mahaifi yake yi mata. Ummi a ranta ta ce “Mugunta idan kana yi, ba ka yi wa kanka ba, ai baka iya ba’ ta rubuta wa Nana lambar wayarta, ta ce gashi nan ta ɓoye, idan tana buƙatar wani abu, ta saka wani ya kirata.

Iya ta din ga bugun cikin ummi, sai ta ji yadda suka haɗu da raihan, da kuma sana’arsa amma ummi ta ƙi gaya mata.

Sai dai da dare yayi, Nana ta ce a wurin Ummi za ta kwana, idan ta je gida babansu zai sake zaneta, buɗar bakin Iya sai cewa tayi ba zata kwana da ƙazanta a ɗakinta ba, sai dai ta tafi gidan ubanta ta kwana.

Cikin tsiwa Nana ta ce “Sai ka ce wata tsiyar ce a ɗakin, ba dan anty ummi ba nima ba zan ce zan kwana a ɗakin nan ba, kuma in sha Allah sai ɗakin nan yayi gobara, kin ƙone a cikin sa”

Iya ta ce “Laaa, ki gani a kan uwarki, tsinanniya”

Nana ta ce “Wanda yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yake” Ummi kasa magana ta yi, jin mummunan alkaba’in da ƴar ƙaramar yarinyar da ba ta fi sa’ar noor ba, ko sha huɗu ba su cika ba, take ja wa iya.

“Oho, idan ma baki ƙone a ciki ba, ko dai ɗakin nan ya zama kabarinki, ko kina ji kina gani zaki barshi tun kina raye”

Noor ta ce “Taɓ girma ya faɗi”

Ummi ta ce “Shut up noor”

“Ai ban ce komai ni”

Ummi ta ce “Nana, iyan ki ke gaya wa haka?”

“Kina ji fa yadda take tsine mini, ni me na yi mata take ce mini ƙazanta? Ba fa yau ta fara yi mini ba, In sha Allah kina raye sai kin ga ƙazanta a jikinki kuma ba zaki iya gyarata ba” Nana ta yi maganar cikin ɗaga murya tana kuka.

Abun duniya ya ishi ummi, ta yi dana sanin zuwa gagarawa.

Idris kuwa marin da ummi tayi masa bai yi masa zafin da abun da ya bijiro masa yake damunsa a kanta ba.

Yana zuwa gida ya tarar da Hindu a zaune tana tankaɗe, ta saki nono tana shayar da yaro kamar akuya, duk sun zuɓe sun suɗe, ya ja uban tsaki ya shiga ɗaki yana zage-zage.

Sai da ya shiga ɗaki ya tsaya ya yi shiru, wai ummi ce ta mare shi a kan ƴar sa, ummin da ya din ga cin ubanta a baya, wai yau ita ce da ƙwarin gwiwar tsinka masa mari.

Hindu ba ta kula shi ba, ya hau zage-zage yana ci mata mutunci da ita da Nana.

Da abun ya isheta ta ce “Kaga ni fa ban yi maka komai ba, ba zaka din ga zagina ba, Nana kuma ka je can ka nemeta, ni ma ban san gidan uban da ta tafi ba, dan haka ba zaka huce a kaina ba”

“Ai koma menene ke ki ka ja, a can gidan Iya na sameta, ta ja mini mari shegiya watsatsiya”

Hindu ta ce “kai ne babban watstste da ka kawota duniya, kuma ko waye ya mareka, Allah ya saka masa da alkhairi” suka din ga faɗa, ba ganin mutuncin juna, balle kima.

Nana kuwa da ta je gidan, idiris ya kuma yinƙurawa zai daketa, ta fita da gudu, ba ta kwana a gidan ba.

Dama dr. Yana garin, cikin gari ya tafi ya samu hotel ya kwana, da niyyar washegari ya mayar da ummi maiduguri sannan ya koma kano, a ganinsa haka shi ne ƙa’ida duk da abun da ya faru a baya, yakamata ace da kansa ya kai ummi gagarawa su kai musu katin aurenta.

Da sassafe ummi da noor suka shirya, sai ga Nana da farar safiyar nan, dan a gidan iya tayi sallar safiya kamar yadda take cewa.

Ummi ta yi ta mata nasihar ba a salla da safe, ta ce “Ai ba a gidanmu na kwana ba, babanmu ne zai sake dukana na gudu na tafi ƙasan teburin wani mai tireda, na kwana”

Ummi ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un” tabbas idan ba a tsaya a kan yarinyar nan ba, to zata gagari kowa.

Har ƙasan zuciyarta ummi take jin damuwa a kan Nana, kyakywar bafulatanar yarinya kamarta ɗaya sak da mahaifiyarta, amma ba kula.

Tana kallon iya tana kallonta, amma ko kallo iya ba ta isheta ba.

Ummi ta dafa musu tea har da madara, ga bredi da ƙwai, duk da cin mutunci da Iya tayi musu, bai hanata cin abincin da ummin ta sayo da kuɗinta ba.

Gidan babu wanda bai san zancen marin nan ba, aka din ga surutu a kai.

Allah ya taimaki ummi, da wuri kawu ya zo, dan kuwa tuni kawu Ilyasu ya kira shi ya sanar da shi abun da ya faru.

Sai da Iya tayi ta faɗe-faɗen maganganu, tare da gaya masa ƙarya da gaskiya, amma ya basar da zancen, dan shi yanzu abun da ya dame shi, yadda zai samu sauran kuɗi, ya cika ya ƙarawa ummi kujeru.

Suna tafe a hanya, yake bata labarin gidanta da raihan ya kai shi, ummi ta ce “Kawu kar ka wahalar da kan ka, ka yi abun da Allah ya yassare maka kawai”

Ya ce “Haka ne, amma dai duk da haka dolena ne na fitar da ke kunya”

“Na gode sosai kawu, ubangiji Allah ya ƙara arziki”

Ya amsa mata da “Amin”

Aka jima ya ce “Ummina, meya haɗaki da idris har ki ka mare shi? Na dai ji zancen ne amma ban yadda ba”

Ummi ta sunkuyar da kai ta ce “Wallahi kawu ban yi tsammanin hakan za ta faru ba, ƙoƙarin ceton yarinyar nake yi, abun ya taɓa mini zuciya sosai da sosai, amma na yi dana sani sosai wallahi”

Dr. Ya jinjina kai ya ce “Na fahimce ki ummi, amma ki kula sosai”.

“In sha Allah, amma kawu shikenan kowane family suna zamansu gwanin sha’awa, mu kuma shikenan idan ka zo ba a yadda ake so ba, sai a tsangwame ka, yarinyar nan zuciyarta a bushe take fa, za ta iya lalacewa” tayi maganar idonta na tara hawaye, dan sosai take jin abun a ranta.

“Ummi, duk al’ummar da zata zauna cikin jahilci, dole a din ga samun irin wannan, bayan jahilci kuma har da son zuciya, sai dai fatan ke da nake saka ran Allah ya ɗaukaka, Allah ya sa ki zama silar gyaruwar komai” ta jinjina masa kai.

Haka kawu yahaya yayi ta ɗawainiya, dan bai koma kano ba sai cikin dare, kuɗinsa duk sun ƙare, a harkar bikin ummi, iya labulayen da zasu isa gidan ummin, sai da aka yi masa estimating kusan dubu ɗari biyar, ya dage baya son daga ɓangaren raihan ace sun ƙarasa wani abun.

Da safe yana zaune a falo, bayan ya karya yana waya, zai sayar da wani filinsa ya ƙara wa ummi kujeru, bayan ya gama wayar, Farida ta kalleshi ta ce “Wasu irin kujeru ne da sai ka sayar da filinka, ga ƴaƴa kana da su? Ba ka ce ka gama komai ba?”

Dr. Ya ce “Ke ina ruwanki? Ke ki ka saya mini filin? Falonta uku na riga na yi kujera set ɗaya, dole zan nemi yadda zan ƙara mata”
Waro ido tayi kamar za ta faɗi daga kan kujerar ta ce “Ban gane falo uku ba, ɗan wa za ta aura haka? Anya ka yi binciken sana’arsa kuwa?”

Dariya yayi, yana kallon yadda hassadar ta, ta kasa ɓuya ta fito fili, ya ce “Ai ummana, Allah ya gwangwaje ta da miji, ni na san sana’ar sa kuwa, sai fatan Allah ya sanya alkhairi”

Can maiduguri kuwa, noor ta sake sosai, tana hidimominta, gashi kasancewar mariya na son yara, kuma ta ji sunansu ɗaya, ya sanya noor da mariya jonewa, komai tare suke yi.

Raihan yana ta turawa da ummi kuɗi, a ciki ta yi wa noor ɗinkuna ita da Nana, da kayan fitar biki, shi ma raihan ya na ta samun gudunmuwar biki, duk da ba wani babban biki ya ɗaukko ba, amma ya kashe kuɗi sosai da sosai.

Ita kanta Ummi ta san ta gyaru, ta sha kulawa da gyara kala-kala daga wurin dangin mahaifiyarta.

Aka shiga satin biki, suka din ga shagulgulansu a maiduguri, har ummi ta gaji, daga wannan sai wancan, aka yi aka gama, ana gobe ɗaurin aure, ranar Alhamis, suka taho kano.

Sai dai dr. Ya aika Abdul, ya ce ya kai su tsohon gidansa, ya saka an gyara, a can za su zauna, su yi nasu taron bikin, saboda sanin halin farida.

A yammacin da suka zo, raihan ya zo, suka kuma gaisawa da su mama, kamar ya sace ummi, tana magana tana lumshe ido saboda azabar gajiya.

Ya ce “Madam, tun yanzu har kin gaji har haka?”

A ɗan raunane ta ce “Ba zaka gane ba MD, a gajiye nake sosai wallahi”

“Kar ki damu, akwai kulawa ta mussaman jibi in Allah ya kaimu da zan baki” tayi masa shiru.

“Babyna am talking fa” taƙi kula shi.

Ya sake cewa “Ina fatan da ki ka je gagarawan babu wata damuwa? Kuma ba ku haɗu da tsohon mijinki ba?”

Ta ce “To meya kawo wannan maganar kuma?”

“Saboda ina kishinki fiye da yadda ki ke tunani, duk da ɗan uwanki ne, ba zai sake saka ki a idonsa ba”

“Saboda me?”

“Saboda haka na ce” yayi maganar cikin isa, tare da tsareta da ido, sai da ta ɗan sha jinin jikinta. Ta tura baki ba tare da ta ce masa komai ba.

Ya ɗora da cewa “Gobe in Allah ya kaimu da wuri mai yi miki kwalliya za ta zo, duk in da huɗu tayi, ki kammala shirinki, zamu zo ɗaukar ki”.

“Tom Allah ya kaimu”

“Gobe in Allah ya kaimu i yanzu, kin zama matar Muhammad, inyeee babyn ba” zolayar raihan ta yi yawa, sai da ya sakata murmushi tana rufe fuska.

Ya ce “Bari na tafi, ki je ki huta, ki ci abinci sosai da sosai” ta jinjina masa kai suka yi sallama.

Washegari da sassafe ƴan gagarawa suka isa kano, sai dai babu Iya, dan cewa tayi ba zata je ba.

Ranar juma’a tun sassafe, su Yaya maryam suka je kafin kaya, sai dai sun riƙe baki da ganin gidan ummi, gida ya haɗu sosai da sosai, ya ƙawatu kai da gani ka san an kashewa gidan kuɗi ba kaɗan ba.

Ba ƙaramin murna ummi ta yi ba, ganin an zo da Nana, ƴan gagarawa a gidan dr. Suka sauka, su mama kuma suna ɗaya gidan.

Bayan sallar juma’a, aka ɗaura auren Ummi da raihan, a kan sadaki naira dubu ɗari biyar.

An sha surutu shi ma a kan sadakin nan, mussaman ƴan gagarawa, har da cewa dr. Zai aurar da ummi ga ɗan yankan kai, tana bazawara ana wannan bushashasha haka a aurenta.

Manager yayi mamakin ganin wai raihan ne mijin da ummi za ta aura, dan ko da ya ga katin ma, bai kawo shi ne ba, dan Muhammad Muhammad Tahir aka saka a katin bikin.

Duk in da ummi ta yi, noor da Nana ne ke biye da ita, su ne ƙawayen nata, can gidan su raihan Hajiya ce take hidima da jama’ar da suke ta shiga suna fita.

Wani irin danƙareren leshi da raihan ya saya mata ta saka, ɗinkin doguwar riga, da mayafi, ba wani make up aka yi mata ba, komai dai-dai kalar fatarta.

Idan ba an gaya maka ba zaka ce mama ba ta da lafiya ba, ta sha kwalliya cikin atamfa ita ma, tayi kyau sosai da sosai.

Ƙarfe huɗu da rabi raihan ya aika motocin da zasu tafi da waɗanda zasu je walimar da za ayi.

Daga baya kuma motarsa ta je ɗaukar ummi, ta yi kyau sosai da sosai, cikin tausaywa da soyayya yake kallon ummi.
Ta shiga cikin motar da sallama, tuni ƙamshin turaren ta ya cika motar, ta sunkuyar da kanta ta ce “Ina wuni?”

“My wife, legally sealed you now belongs to me Salma” yayi maganar yana riƙe hannunta.

Tayi murmushi ta ce “Ka rabani da headmaster ko…

Ba ta gama ba, ya riƙe hannunta da ƙarfi ya ce “Ki sake maganar wani a gabana ki gani, da kin aure shi in ba sai ya gaji ya sakar mini ke ba, idan na din ga sintiri a gidan ki har uwar ɗakinki” ƙunshe baki tayi tana dariya, haryanzu gani take kamar ba ita ba, wai raihan za ta aura, abun da mamaki.

Babu mutane da yawa a wurin, an ci an sha sosai, sai dai duk da mayafi ne a jikin ummi irin na amare, daga sama har ƙasa, tana ta rufe jikinta, amma sai da raihan ya ji wani abu a ransa na kishi.

Ana ta hotuna, a nan ƴan gagarawa suka ga mariya, tsaf da ita kamar ba ita ta haifi ummi ba, tsaf da ita gashi ta yi kyau sosai da sosai, shekara sha takwas rabon da a haɗu.

Suka din ga gaisawa da facalolinta, ta kalli sa’adatu ta c “Ina Alhassan mai yi mini Albishir da mutuwar mijina?” Tayi tsuru-tsuru tana basar da zancen, dan ba su zaci ganinta a haka ba, sun ɗauka hauka take yi tuburan.

Ana ƙoƙarin yin hoto, noor na ta ture Sagir, wai ya koma kusa da raihan shi ne ɗan uwansu, su kuma su ne ƴan uwan ummi, a kusa da ita za su tsaya.

Zuwa sallar isha’i aka tashi daga wurin, noor da Nana suka shige motar Salim, noor ta ce “Bawan Allah dan Allah ka mayar da mu mukaɗai gida, kar ka ɗauki kowa, motar daɗi” kallonsu yake yi, har gara Nana akwai ƙauyanci a tare da ita, amma ya lura da noor, tun a wurin bikin tana da rawar kawai sosai da sosai.

Ya kalli noor ya ce “Ke bana son surutu, ke ki shiga bayan mota, ke kuma dawo gaba” yayi maganar yana nuna Nana.

“A’a ka barmu mu zauna a baya daukkanmu”

“To ku nemi wani”

Noor ta ce “A’a yi haƙuri, Nana ki koma gaban” suna tafe suna ta surutu ita da Nana.

Nana tana magana tana fulatanci, Noor ta ce “Nana, Allah ya sa nima na auri irin yaya raihan, mai kyau kamarsa”

Sai da Salim ya waiwaya ya kalli noor, ba ya tunanin ko fitsarin kwance ta daina take zancen wani miji.

Suka yi ta surutu, ko gajiya ba sa yi, har ya kai su gida.

Washegari aka yi wunin biki, da isha’i aka kawo motocin ɗaukar ummi, da mariya da yaya maryam da wasu daga ƴan uwan su, suka tafi da ummi gidan farida, domin yi mata sallama.

Yaya maryam ta din ga yi wa farida godiya, saboda riƙe ummi da ta yi, sai wani cika take tana batsewa, ta zata za ta gan su ƴan ƙauye, sai dai ta ga sun sha dressing, sun yi kyau, tayi mamakin ganin babar ummi, ta ɗauka ita ma baƙa ce wuluk, amma ta ganta da haske kuma shar da ita.

Dressing ɗin da aka yi wa ummi, ta din ga kallo, ita kanta a ƙasan zuciyarta ta san son zuciya ne ke sanya suke ce wa ummi mummuna, tana da baƙi ne dai kawai amma ba wani muni.

Dr. Ya yi wa ummi nasiha sosai da sosai, ummi ta yi masa godiya tare da neman yafiyarsa, ya ce shi ba ta yi masa komai na laifi ba.

Ƙarfe tara na dare, aka kai ummi gidan raihan, dr. Da kansa ya kaita a motarsa bayan yi mata nasihohi masu ratsa jiki, mutane sun yi santin gidan nan sosai da sosai, dr. Sai da ya cika ko ina, kitchen ɗin ta kuma su yaya maryam sun yi rawar gani, ga uban kayan turaren wuta duk an yi mata, komai nata sai masha Allah.

Dangin mami da ta din ga ce musu ba ta da gata, sun ɗauka ba za a zuba mata kayan kirki ba, su samu na gori, amma suka sha mamakin kayan da dr. Ya zuba mata.

Kowa ya watse, ummi idonta ko kuka ba ta yi ba, saboda ita a wurinta cigaba ta samu, ta bar wa farida gidanta, sai fatan Ubangiji Allah ya sassauta mata ƙalubalen gidan raihan.

Sai sha ɗaya ya shigo, daga shi sai Salim da wasu mutum uku, da take kyautata zaton ƴan uwansa ne, suma suka yi musu nasiha, tare da addu’a zaman lafiya, suka watse suka bar su.

Ya dawo ya tarar da ummi a zaune a in da ya bar ta, ya yi gyaran murya ya ce “Yaya” ta ɗago kai ta kalleshi yayi murmushi ya ce “Kin yi kyau fiye da kullum” ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Ya zauna a kusa da ita, ya miƙa mata hannunsa ya ce “Ɓalle mini” jikinta na rawa ta ɓalle masa maɓallan hannun rigarsa, ya cire babbar rigarsa, da ta cikin, ya shiga banɗaki yayi alwala, yayi mata umarnin yi ita ma.

Bayan sun yi salla raka’a biyu, raihan ya daɗe yana yi musu addu’a, bayan ya kammala kuma, ya din ga yi wa ummi nasiha.

“Salma, bayan gwagwarmaya daban-daban, Allah ya cika mini burina a kanki, ina da yaƙinin na kawo mace ta gari, kuma uwa ta gari ga ƴaƴana, ummi duk wani aure da nasa ƙalubale, amma in sha Allah, daga gareni babu ƙalubale, sai abun da ba a rasa ba, amma zaki yi haƙuri da wanda zaki fuskanta daga ƴan uwana, mu zama masu haƙuri da riƙe sirrin junanmu, kamar yadda na yi wa mama alƙawari, zan riƙe ki amana na kula da ke, in sha Allah zan yi iya yi na, Allah ya bamu zaman lafiya. Na san ba a za a rasa ɓacin rai a harkar auratayya ba, kin san halina wasu lokutan ina da zafi, amma ki zama mai yi mini uzuri, Ubangiji Allah ya bamu ikon kula da juna” ta amsa da Amin, ya tambayeta ko ta na da abun cewa ta ce masa a’a.

Duk yadda yayi da ita ta saki jiki ta ci abinci, ummi fafur taƙi, shi yayi ciye-ciyen sa.

Ita kuwa ummi wata irin fargaba da tsoro ne ya addabwa zuciyarta, abun da ya faru a aurenta na farko ne ya din ga ya dawo mata, tana ta fargaba da addu’ar kar ta sake cin karo da matsalar da ta faru a farko.

Ya fita daga ɗakin, ya dawo da wasu kaya a hannunsa, ya ce “Ƙaraso” yayi maganar yana yi mata nuni da hannunsa.

Ta tashi tana sinnewa ta ƙarasa, ya ɗaga mata wata doguwar rigar bacci, ja mai kyau, nasa kayan ma jajaye, ya ce “Ungo naki”

Jikinta na rawa ta karɓa, wani irin girma da kwarjini ta ga raihan ɗin yayi mata.

“Ki saka naki, bari na baki wuri” yayi maganar yana ɗaukar nasa kayan, ya fice daga ɗakin.

Ta lura raihan yana son jar kala, ta din ga jujjuya rigar, a ranta ta ce “Taɓ ni zan saka wannan rigar kamar a turai, ba kunya kuma in kalle shi?’ ta zubawa rigar ido, sam ba ta ji za ta iya sakawa ba, haka ya dawo ya tarar da ita, shi har ya saka nasa, kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta, ya cika tasa rigar shirt ɗin cif, an rubuta i love you, a gaban rigar sai wandon ta ja 3quater.

“Ya baki canza ba?” Yayi tambayar yana kallon ta. Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Ya ƙarasa gabanta ya ce “I understand, bari na taimaka miki” yayi maganar yana janyo mayafinta.

“A’a dan Allah, yi haƙuri” tayi maganar kamar ta yi kuka. “Oya ki canza ina jiranki, dare yana yi” Ya juya ya sake ficewa, bayan wasu mintuna ya dawo, ta saka rigar amma ta yafa mayafin kayanta.

A ransa ya ce ‘Lallai aurenki na fari mijinki yayi fama da taurin kai’ rigar iya gwiwar ta, tayi kyau sosai, bai takura mata sai ta sauke mayafin ba, ya kama hannunta suka bar ɗakin.

Suka ratsa falo suka shiga wani ɗakin daban, an yi wa ɗakin ado na musamman, duk da a cikin fargaba take, ɗakin ya yi mata kyau sosai, ya yi wa komai adon jar kala.

“Sai ka ce ɗakin amaryar indiya” tayi maganar a hankali.

Yayi dariya ya ce “Duk wani abu na soyayya ummi, ba sai a wurin wasu ba, mu ma zamu iya idan har bai saɓawa addininmu ba, bai burge ki ba?”

Ta ce “Yayi kyau sosai” ya yi murmushi, suka ƙarasa gaban gadon ya zaunar da ita, ya tashi ya kashe fitilar ya dawo da plate ya zauna a kusa da ita ya ce “Ki na buƙatar isasshen abinci sweetheart, ba zan bari ki kwana da yunwa ba, na kashe fitilar tun da kunyata ki ke ji, dan Allah ki ci”

Sai a lokacin ummi ta tuna aurenta na fari, ko fara Idris bai shigo mata da ita ba, yau kuwa kazar da ta gani a ƙalla ta kai biyar, ban da kayan marmari da lemuka.

A hankali yake lallaɓata yana ba ta a baki, kai ka ce wani babban mutum ne mai shekaru.

Duk da ba da yawa ta ci ba, ta ji daɗin hakan, dan dama tana jin yunwa, hira ya ɗan din ga yi mata, kan ya bata damar ta kwanta.

Sai dai ummi tamkar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta, ta faso saboda tsananin tsoro da fargaba, da zunzurutun tashin hankali, duk da kulawar da ƙoƙarin kwantar mata da hankalin da yake yi. Shi har mamaki ta bashi, kamar wadda ba ta taɓa aure ba.

Raihan ya nuna mata banbancin ilimi, da zunzurutun jahilci, banbancin dattaku da tarin wauta, banbancin wayewa da kuma ƙauyanci.

Komai na shi cikin nutsuwa da aji yake gudanarwa, ba kamar yadda Idris ya yinƙurin haike mata, tamkar wani jaki ko mahaukaci ba.

Ya nuna mata ita mutum ce, mai ɗauke da zuciya mai rauni a ƙirjinta, da ke buƙatar tausasawa da kuma kulawa tare da tarin soyayya, ba abar wulaƙantawa da cin mutunci ba.

Yau ta san meye aure, ba auren Idris ba, dan auren Idris ta bar shi a matsayin wata ƙaddara da dole sai ta faru da ita.

Raihan ɗin da take yi wa kallon auren sa abun kunya, haka tana kallo ta zama cikakkiyar mallakinsa.

Babban abun da ya razana ummi, tare da ɗaga mata hankali bai wuce yadda raihan bai ce mata komai ba, hasali ma ya juya mata baya yayi shiru. Hakan ya ɗaga mata hankali, tare da tabattar mata da an samu matsala a wannan karon ma.

Ayshercool.

                       CUTARWA

38

Ƙirjin ummi ne ya cigaba da bugawa, tare da sallama cewa, a wannan karon ma an samu matsala, wataƙila shi ma raihan ya ci karo da matsalar ta, ta farko.

Ta zubawa bayansa ido, duk da ɗakin ba haske, sai dim light na kan side bed.

Ko wane hukunci zata karɓa a wannan karon a hannun raihan? Allah ne ya bar wa kansa sani.

A hankali ta ga ya motsa yayi miƙa, yana gode wa Allah, ya tashi tsam ya nufi toilet.

Duk Addu’ar da ta zo bakin ummi yi take, saboda ita sam ba ta ga al’amuran sun faru kamar yadda take karantawa ko sauraro a littatafan soyayya ba, a zaton ta tun da abun da take tsammani bai faru ba, an sake samun matsala, tun da babu wanda ya zaunar da ita a nasihar da aka yi mata, aka yi mata bayanin menene gundarin auren.

Tana tufaka da warwara, da adduo’i, ya buɗe ƙofar ya fito, ba ta iya ganin me yake yi daga in da take, amma ta ji alamar ya buɗe wardrobe ya rufe.

Bai ɗauki lokaci da yawa ba, ya kunna fitilar ɗakin, hakan ya sanya ta sake shigewa cikin bargo tana jiran irin hukuncin da zata karɓa a wannan karon.

A hankali ta ɗago kai jin shiru, ta ganshi a tsaye a kan ta, ƙugunsa ɗaure da towel jikinsa da sauran ruwan wanka, ya yi murmushi ya ce “Ya ki ke sake shigewa cikin bargo, taso mana” yayi maganar yana miƙa mata hannu yana murmushi.

Jin maganar sa ya saka ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa, ta ga me za ta iya ganowa, amma ba ta ga komai na damuwa ba, ko ɓacin rai ba.

“My love, ba fa canza miki ni aka yi ba, naga kamar wani abu ki ke son ganewa, yaron nan ne dai ki ke cewa ba zaki auri ƙaninki ba”

Ta sunkuyar da kai cikin matsananciyar kunya.

Ya ce “Ok, let me help you” yayi maganar zai ɗaga bargon amma ta riƙe ta ce “Ka bani hijjabi”

“Ai nan babu hijjabi, sai dai na baki towel sai ki yafa mayafinki” haka kuwa aka yi, ta ɗaura towel, ta yafa mayafinta, ya rakata har toilet, ya dawo kan gadon ya sake gyarawa, sai dai abubuwa na ta kai komo a ransa, duk da bai san dawan garin ba, amma ya san akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, to ita ummi mecece? Budurwa ko bazawara?.

Yana tsaka da wannan tunanin, ta fito ya tashi da sauri ya nufe ta yana jera mata sannu, kamar wadda ta yi hatsari, sai raɓe-raɓe take tana tafiya a hankali.

Ya rungumota jikinsa ya kai ta bakin gado, ya zaunar da ita, cikin dabara ya zare mayafin, ya shiga tsane mata dogon gashin ta da yake jiƙe da ruwa da shi.

“My love, gaskiya yakamata mu tambayi mama, anya asalinku ƴan Nigeria ne? Ni fa ban taɓa ganin bahaushiya mai irin gashin ki ba”

Ta ce “HOD ɗinmu ma haka ya ce, wai ƙwayar idona ba irin ta ƴan Nigeria ba ce”

“Shi kuma saboda sa ido, har ya zuba miki ido ya gano ƙwayar idonki ba irin ta ƴan Nigeria ba ce?”

Ta tura baki ta ce “To ai ana ganina ake ganewa ba baƙa ba ce”

Ya ce “Idan na tashi dole a nemo hand drier, saboda tsane gashin nan, kar yawan wanke shi ba a busar ba, ya din ga saka ki mura ko ciwon kai”

Ummi ta ce “Ai ban damu da yawan wanke shi ba ma, saboda wahalar bushewa, na yi ta fama, duk ya dame ni, sai … Sai kuma ta yi shiru.

Ya kwashe da dariya ya ce “Yanzu kuma wanke kai ya ganki, ba dare ba rana daga ɗaya zuwa sau ba adadi a rana” yayi maganar yana dariya, ta ja bakinta ta yi masa shiru.

Yadda yake ta tattalin ta, da nuna mata kulawa kawai ya ga hawaye na zubowa daga idonta, tun daga kan auren Idiris ba ta taɓa zaton zata samu miji da zai nuna mata kulawa ba, hakan ba ƙaramin tayar masa da hankali ba.

“Sweetheart na yi miki wani abu ne da ba dai-dai ba? Dan Allah ki gaya mini menene me na yi miki? Ko abum da na yi ne ya ɓata miki rai?”

Ummi ta share hawayen ta ce “Bakomai fa, wani abu na tuna ne kawai”

“Dan Allah kar ki sake tuna abun da zai saka mini ke kuka please, kar ki ɓata mana farincikin da muke ciki mana, abun da ya wuce ki bar shi a baya, yanzu sabuwar rayuwa zamu gina baby, dan Allah ki daina” yayi maganar yana share mata hawayen fuskarta, ya rungumeta suka kwanta.

Sai yanzu yake yi mata abun novel ɗin da take tunani, yana ta yi mata magana mai sanyaya zuciya, wasu maganganun ma kamar ta toshe kunneta dan kunya, dan a duk rashin jin raihan, ba ta yi zaton jin wasu maganganun daga bakinsa ba.

Can gida kuwa ƴan gagarawa na koɗa gidan ummi, dan sai da kausar ta je gidan, kuma sai da ta ɗaukko wa babr su videon komai, ta zo ta nuna mata.
Nan ɓangaren su mariya ma haka ne, ana ta santin gidan ummi, da irin maƙudan kuɗin da mijinta ya kashe a kan aurenta.

Mariya ta ce “Yaya maryam kin gani ko? Ina da kyakywan yaƙinin ummina ba za ta tozarta ba, na yaba sosai da nutsuwar mijin nan nata”

Yaya maryam ta ce “Shiyasa kullum nake cewa ki din ga yi mata addu’a, yawan damuwar ba shi ne ba, ke dan ma baki je kin ga gidan ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu kafin mu tafi, sai mu je ki gani”

Mariya ta yi murmushi ta ce “Yaya Maryam kenan, mai ɗaki shi ya san in da yake yi masa yoyo, ba zaku fahimci halin da na shiga ba a kan raba ni da ƴa ta”

“Eh dama ya za ayi mu gane mara kunya, ƴar farin ki ke wa haka” mariya ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Kiran sallar farko, Raihan ya tashi, da ƙyar ya yaƙi shaiɗan ya saukko daga kan gadon, ya je yayi alwala ya gabatar da nafiloli, sai da aka kira sallar asuba, ya tashi ummi shi kuma ya fita masallaci.

Kafin ya dawo ta yi salla, ta koma kan gado, saboda gajiya da kuma bacci da take ji.

Jin motsinsa a kan gadon ne ya sanya ta farka ta buɗe idonta da ƙyar.

“Kin yi sallar ne?” Ta jinjina masa kai tare da cewa “Good morning” cikin kasalalliyar muryar bacci.

“Morning honey, duk gajiyar ce ne, ake yi mini shagwaɓa” murmushi ta yi tana ƙoƙarin juyawa, amma ya riƙe ta ya sumbaci goshinta, ya gyara kwanciyarsa shima a gajiyen yake, dan haka bacci duk yayi awon gaba da su.

A hankali ya yi juyi, ya nemi ummi ya rasa, kamar aljana, ya daɗe a kwance yana miƙa, sannan ya saukko ya fito, can ɗaya falon ya ganota, tana ta zazzagawa tana kallon ko ina, ta saka dogon hijjabi abun ta.

Fito yayi, hakan ya ɗan razanata ta waiwaya.

“Me ki ke nema ne?”

Ta ce “Bakomai, kawai na gaji da kwanciyar ne na tashi”

Ya ƙaraso falon ya ce “Sai ki ka tashi ki kar bar ni? Ni fa yunwa ce ta taso ni ma, bari na kira hajiya a kawo mana abun karyawa kan mutane su fara zuwa”

Ta ce “Da in girka mana, kar a wahalar da su” ya girgiza kai ya ce “No, kina buƙatar hutu, kuma gidan bakomai na masarufi, ban sayo ba tukuna bari na kira ta, akwai sponge da sabulu da toothpaste a drower mudubin ɗakin da muka kwana, ki shirya kan mu fara baƙi”.

Ta ce “To”

A ƙalla ta kai awa guda, sannan ta dawo falon, yana kwance a kan doguwar kujera, yana danna wayarsa, ya ɗaga kai ya kalleta cikin dogon hijjabinta, ya girgiza kai tare da yin murmushi ya ce “Wane irin wanka ne haka fiye da awa goma?”

Ta ce “awa goma tun jiya kenan fa”

“Ai kin daɗe ne, ƙaraso mu gaisa mana amaryata”

Cikin matsananciyar kunya, ta ƙarasa gaban sa, ya tashi ya zauna, tare da zaunar da ita a kusa da shi, ya ce “Kin tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau”

“To ya jikin naki? Are you ok now?”

Ta sunkuyar da kai, tana murza yatsun hannunta, da ya zame mata ɗabi’a idan ba ta da amsar bayarwa ga tambaya.

Cikin son ƙureta ya sake cewa “To ya daren jiyan?”

Mutsu-mutsu ta hau yi, za ta tashi ta tafi, dan raihan ɗin ya wuce tunanin ta, kamar an canzo wani.

Riƙeta yayi ya ce “Ba in da zaki fa, yanzu dai bari in rama dukan da ki ka yi mini jiya, poor me kin kusa karya mini ƙashi, you even bite my tongue daga kiss”

“Zan je ɗaki in yi abu” tayi maganar cikin rauni.

Yana dariya ya ce “Koma menene yi a nan, amma sai na rama” wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga yayi sallama, daga bisani ya ce “Ok”

Ya katse wayar ya ce “Bari na karɓo mana abincin, hajiya ta aiko” ta jinjina masa kai ya tashi ya fita.

Tayi ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo.

Shiru ta yi ta tuna irin cin zarafin da idiris yayi mata, ta kwana a waje tsirara cikin ruwan sama, saboda kawai ya same ta da larura, ta girgiza kai abun kamar ba zai wuce ba.

Raihan ya yi sallama da ƙaton kwando, ta tashi ta karɓe shi, suka iso falon suka zauna.

Sai dai ita ta kasa sakewa ta ci abinci, sai cakala take yi, ya ci ya ƙoshi, ya hau kan kujera ya kwanta sai bacci.

Ummi ta lallaɓa ta bar masa falon.

Sai azahar sai ga su yaya maryam da mama, dan a washegari za su koma maiduguri, ummi ta ji daɗin zuwansu, kamar ba jiya suka rabu ba.

Suka kawo mata soyayyayiyar miya ta sha kaji, har da kayan gara, sun kai ruwa rana da dr. A kan kayan garar nan, ya ce ba addini ba ce ba, idan ma sai an yi su bari a kwana biyu shi zai yi mata da kansa, suka ce sun riga sun zo da ita, sai dai ya yi haƙuri.

A nan wasu daga dangin su raihan ma suka zo, suka tarar da su, wanda ba su samu damar zuwa ganin gida ba, ciki har da wasu daga ƙannen mamin raihan.

Kallonta suke suna zunɗen ummi, ganin yadda take tafiya a takure, kamar mara kuzari.

“Ji munafuka, kowa fa ya san bazawara ce, amma ji salon kinibibi da iskanci, wai a dole sai ta nuna wa mutane budurwa ce” suka yi ta surutun su, ummi ba ta ma san suna yi ba.

Da za su tafi, mariya ta kama hannun ummi, tayi ƙasa da muryarta ta ce “Mamana, kin shiga sabuwar rayuwa, duk da baki da wayo sosai lokacin da na yi rayuwar nawa auren, amma aure ba soyayya ba ce kawai, kowane aure da kalar jarrabawarsa, ni na samu soyayyar miji, ƙalubale na danginsa ne.
Ki riƙe Allah ki ji tsoron Allah, babu abun da ya gagari Allah, kar ki bari ki yi nesa da Allah, babu abun da zai yi galaba a kanki, sai abun da Allah ya ƙaddara. Ki riƙe mijinki domin Allah, banda yaji ko kan ƙara, matar da ta isa a ɗakinta take yi wa miji yaji, ayi haƙuri, ayi haƙuri da juna” sosai mariya ta yi wa ummi nasiha, sai dai a ƙarshe ne kuma ta koma shirme.

Da za su tafi ummi ta je ta kira shi, sai dai bai ji daɗin garar da suka kawo ba, yaya maryam ta ce masa ai su normal ne al’adar su ce.

Bayan tafiyar su ummi ta dudduba kayan da suka kawo mata, ta je kitchen ta jera wanda za ta jera, kayan miya, busasshshen kifi, man shanu da sauran su.

Kasancewar raihan ba ya ɓangaren da take, kuma duk baƙin sun tafi, ya sanya ta ɗan sake, tana ta ɗan gyara in da aka ɓata.

Tana ta gyara abun da bai yi mata ba, tana yi wa kawu addu’ar samun buɗi da alkhairi mara yankewa a duniya da lahira, kamar an ce ta ɗaga kai, ta hango raihan a tsaye yana kallonta.

Ta miƙe tsaye ta ce “In zo ne, kana buƙatar wani abu?” Ya ɗaga mata gira.

Ta nufi in da yake tana takawa a hankali, cikin tafiyarta da yake cewa yanga ce tayi mata yawa.

Ta ƙarasa ta ce “Gani”

Ya riƙo hannunta ya ce “Dama kin tambaye ni ina buƙatar wani abun ne, mu je daga ciki to, sai na gaya miki me nake buƙata” danƙarewa ta yi a wurin taƙi yin gaba.

“Ya haka kuma? Ke fa ki ka tambaye ni”

“A’a to na janye tambayar” ta yi maganar tana son ƙwace hannunta.

Raihan ya yi dariya ya riƙe hijjabin jikinta ya ce “Ummi nan fa ba muhallin hijjabi bane yanzu, aure muka yi, dan Allah ki cire shi na din ga ganin kwalliyar ke ko zafi ba kya ji”

Ummi ta ce “To, zan din ga cirewa”

“Ai yanzu nake son ki cire” yayi maganar yana cire hijjabin daga jikinta.

Doguwar rigar material ta saka, sai ƙamshi take yi, ya cire mata ribbon ɗin kanta, gashin ya sauka a jikinta, ya gyagygyara mata zaman gashin ya ce “Masha Allah, what a beautiful creature” yayi maganar yana murmushi.

Tura baki tayi tana ƙoƙarin karɓar hijjabinta daga hannunsa.

Ya riƙo ƙugunta yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, tabbas ba dan ummi ta kasance ma’abociyar suturta jikinta ba, da babu shakka mutanen banza su din ga bin ta, saboda duk in da ake fasalta mace mai diri, Allah ya yi wa ummi dirin jiki mai kyau da ɗaukar hankali.

Suka koma falon suka zauna, sai dai ya hana ummi sakat da tsokana kala-kala, kuma ya riƙeta a jikinsa.

“Komai na ki perfect baby, da headmastern nan ya yi gardama, da na yi masa abun da ban taɓa yi ba”

Ummi ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce “Wai dan Allah me ka ce masa ya fasa?”

Raihan ya yi murmushi ya ce “Dubu ɗarin da ya ce zai baki kuɗin aure, na bashi uku, na ce aje a mayar da wadda aka saka a kula da iyali na gida, ya bar mini ke, jikinsa na rawa ya bar mini ke, dama na gaya miki na fi kowa sonki” yayi maganar yana haɗa fuskar sa da ta ta yana murmushi.

“Cin hanci ka bashi dan ya bar maka ni, cin hanci ba kyau”

“A nan ya halarta” yayi maganar yana dariya.

Raihan na ƙoƙarin ɗaukar su zuwa wata duniyar, wayarsa ta fara vibrating, sunan mami ne a kan screen ɗin wayar, ya ɗaga tare da yin sallama.

“Raihan har ka fi ƙarfin ka zo in da nake ka gaishe ni ko?”

Ya san a rina, ya kwantar da ummi a jikinsa sannan ya ce “A’a ba haka bane mami, zan zo ne”

“Zaka zo sai yaushe? Har an yi ƙulle-ƙullen da zaka kasa zuwa ka gaisheni?”

“Mami, wallahi a gajiye nake ne sosai da sosai, na kira ki ma da safe baki ɗaga ba, but an ce mini gida haryanzu da mutane, na ce bari na ƙyale ki, sai da daddare, amma in sha Allah a satin nan dole na  na zo gaishe ki, na gaji ne sosai….

“Dalla rufe mini baki, nusari shashasha. Yaushe aka yi daren da gari zai waye?  Lallai lallai ka zo gida ina son ganinka, yarinyar nan safiyya ma na kwance babu lafiya duk saboda kai, kar ka bari ka fusata ni”

Raihan bai yi mamaki ba, ya san a rina, amma shi bai ga haɗin rashin lafiyar safiyya da shi ba, asibiti zai kai ta ko me zai yi mata? Kodayake ba abun mamaki bane ba idan mami na jin rigima.

“Shikenan mami, zan zo in sha Allah” sai dai tun da aka ambaci Safiyya, yana jin yadda bugun zuciyar ummi ya ƙaru a ƙirjinsa.

Ya saka hannu ya ɗagota, amma taƙi kallonsa.

“Sweetheart, an fara kiran sallar magariba, bari na yi alwala na tafi masallaci” ba ta kula shi ba, ta tashi ta nufi ɗaki, ya bi bayanta da kallo, zubin manyan mata sosai.

A hankali ya ce ‘Haba mami, is too early for that’.

Bai je kiran mami a ranar ba, dan ya san idan ya je da mutane a gidan, kuma sai ta yi wani abun da zata ci mutuncin ummi, a gaban mutane dan haka ya ƙi zuwa.

Kwanan ummi uku a gidan raihan, ta fara girkin abinci, sai dai rigimar raihan har mamaki take bata, baya zuwa ko ina sai salla, yana maƙale da ita kamar cingam, ga wani irin mugun kunyarsa da take ji, ta kasa sakewa da shi, kusan kullum cikin ƙorafin saka hijjabin nan yake, ta kasa daina yawo da hijjabi.

Kwana na ukun da daddare, Raihan ya je gida, sai da ya je wurin Hajiya yayi mata bangajiya, Alhaji dama baya nan, washegarin ɗaurin aure ya tafi umara.

Sai dai cikin fargaba ya isa sashin mamin.

Ya tarar da ita ta hakimce, gefe ga Nihal a zaune, sai Safiyya da ke kwance a kan doguwar kujera.

Yana shiga suka gaishe shi, ya amsa musu, sannan ya je gaban mami ya risuna yana gaisheta.

“Sai yau Allah ya nufe ka da zuwa? Har ka sallami kanka na yi maka waya ka zo raihan amma ka ƙi”

“Ba ƙi na yi ba mami, wallahi bana iya zuwa ko ina, zirga-zirgar bikin nan na gaji ne wallahi”

“Uwar zirga-zirgar bikin, ka fito fili ka faɗi uban abun da ya hanaka fitar, na yi dana sanin cewa zan yi maka aure ina ganin mafita ce, ashe ruwan dafa kaina ne, ka kwaso bazawara da ta tafi ƙarfin ka, wallaahi ka shiga hankalinka, ka san abun da yake yi maka ciwo”

Ta din ga yi masa faɗa na babu gaira babu dalili, ƙarshe ta rufe da cewar, watanni uku ta bashi, yazo ya nemi auren Safiyya.

Ya ji ta da kunne kawai, ta gama ya ce zai tafi, ta ce ba zai tafi a lokacin ba.

Ummi kuwa na gida na ta duba agogo, dan be gaya mata zai je wani wuri ba.

Har ƙarfe goma saura shiru bai dawo ba, ta kasa jurewa ta kira wayarsa.

Bai ji nauyin mami da ke zaune tana kaɗa ƙafa cikin isa ba, ya ɗaga wayar ya ce “Hello dear”.

“Ina ka tafi tsoro nake ji”

Yayi murmushi ya ce “Gani nan, babu dodo a gidan fa”

“Dan Allah ka yi sauri, tsoro nake ji sosai ko falo na kasa fita”.

Mantawa yayi da mami a wurin, yayi dariya ya ce “To yi ta addu’a kan na dawo? Kin ci abinci ne?”

“A’a”

Ya ce “But you are not hungry ko?”

Ummi ta ce “Eh”

“Ok ki jirani, in sha Allah yanzu zan taho”

Muryar mami ta jiyo tana cewa “Zaka ajiye wayar nan ko sai na ci ubanka mara kunya” a rikice gaban ummi ya faɗi, ta kashe wayar ba ta san gidan ya je ba da ba zata kira shi ba.

Mami ta tashi ta shiga ɗaki, raihan ya ɗau mukullin motarsa ya fice da sauri.

Abun da raihan yayi, ba ƙaramin mamaki ya bawa mami ba, dan mugunta ta shirya yi, ta zaunar da shi har sha biyun dare, daga nan ta ce dare yayi ba zai fita ba sai da safe, bisa ga miyagun shawarwarin da Anty rakiya ta bata, sai dai abun da raihan ɗin yayi ya bata mamaki.

Ta din ga kiran wayarsa amma a kashe.

A bedroom ya tarar da ummi, kai da ganin ummi ka san a tsorace take, ya ajiye kayan hannunsa ya ce “Sorry dear, yi haƙuri”

“Ban haƙura ba” ta yi maganar cikin shagwaɓa.

“Yi haƙuri, ayi mini afuwa” ba ta nuna masa ta san in da ya je ba.

Ya cika cikinsa da abinci, yana ta yabonta tare da santin abincin.

Ya koma ya hana ummi sukuni, ya gama tara mata gajiya, suna kwance babu tsammani ta ji ya ce “Salma, me ki ka yi wa mijinki na farko ku ka rabu?”

Gyara kwanciyar ta tayi, ta ce “Meyasa ka tambayeni?”

Ya kalli fuskarta ya ce “Am just curious about it”

Tayi ajiyar zuciya ta ce “Labarin babu daɗi, auren huce takaici aka yi masa da ni, saura kwana uku aurensa, ba ya so na, ranar da ango ya tare a tsakar gida na kwana cikin ruwan sama, ba ya so na, tuntuni ni mummuna ce kuma ya rasa wadda yake so yayi niyyar aure. Auren watanni biyu ne dai bai kai uku ba ma, watanni mafi tashin hankali, marasa daɗin tunawa, na tozarta sosai a aurena na fari ko tunawa bana son yi” tayi maganar tana zubar da hawaye.

Ya rungumota jikinsa yana share mata hawayen, ya ce “Is ok, you are much more than special, ke ta daban ce, kuma ya yi wa kansa, ni kuma ya taimakeni irin sosai ɗin nan fa” yayi maganar yana ƙoƙarin zolayarta.

Da safe da ya kunna wayarsa, da kiran mami ya fara cin karo, ya ɗaga ta ƙare masa zagi tsaf, amma ko a jikinsa, shi kasancewar sa da ummi, mantar da shi komai yake yi. Duk da kunyarta har ta yi yawa.

Abu kamar wasa, raihan ya shafe sati biyu cirr a gida, ummi ba ta da aiki sai ɗorawa da saukewa, abokan aikinsa su ka zo ummi ta yi musu girki, har da ƴan china.

Raihan ba ya jin duk wanda zai zo gidansa, saboda matarsa ta iya girki.

Haka zalika ga rigimarsa da ba ta ƙarewa.

Gidan farida kuwa, tun da Allah ya sa ummi ta bar gidan, komai ya taɓarɓare, kausar mugun sok jiki, ba ta iya aikata komai, noor ce ma mai ƙoƙartawa, ita ma idan ta gaji, sai ta watsar da aikin ta ce ta gaji, idan aka tursasata kuma, tayi abun da ba a so.

Uban wankin da ummi ke yi musu, babu wanda zai yi yanzu, mopping gyaran ɗaki, da kuma girki duk abubuwan sai a hankali, girkin ma ba daɗi yake yi ba.

Farida ta ce sai an samo ƴar aiki, dr. Ya ce babu mai kawo masa ƴar aiki, idan aka kawo ta kuwa sai dai ta din ga biyanta, babu yadda za ayi ga kausar a gida, ba aure ba karatu, ace an ɗaukko ƴar aiki.

Dr. Ya kira ummi ya tambaye ta me take so ayi mata da kuɗin sadakinta, ta yi tunanin wata sana’ar, ya bata jari sauran ya cika ya saya mata kadara.

Ummi ta tuntuɓi raihan, amma ya ce a wannan lokacin, ba ta buƙatar sana’a a saya mata kadara kawai.

Duk yadda mami ta so yin abun da za ta ƙure raihan, ta shiga hakkin ummi, raihan sai ya zille, ta yi masa faɗa ta zage shi, ko a jikinsa.

Babban abun da ya ba ta takaici, bai wuce tana tsaka da duba saƙonni, ta ga raihan yayi status da special whats app ɗin sa, da ba kowa ne ya san shi da shi ba, galibi family ne kawai ke da lambar.

Hoton Ummi ya saka, tana zaune a kan dining, ta naɗe kanta da mayafin doguwar rigar jikinta
“My perfect woman, khairun nisa’i, Allah ya ƙara miki lafiya”

Ya sake rubuta “Goodnight ƴar aljannata”

A fili ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, bazawarar wannan mummunar”

Hankalin Safiyya ne ya koma kan mami, dan kuwa mami ta sanya safiyyan dawowa gidan da zama.

“Mami menene?”

Ta miƙa mata wayar, bayan ta nemo status ɗin raihan.

Gaban Safiyya ya faɗi, duk yadda ake koɗa munin ummi bai kai nan ba.

Mami ta din ga zage-zage, tana cewa an asirce mata ɗa.

Sai da ta jera kwana biyu tana kiransa ya je tana nemansa, amma ya ce mata ai aiki yayi yawa a office, baya samun isasshen lokaci, alhalin rabonsa da office ɗin tun saura sati biyu bikinsa.

Asabar ce suna baccin safe, kiran Alhaji ya tashe su, raihan ya ɗauka cikin jin nauyinsa.

“Ango ka sha ƙamshi”

“Alhaji ka dawo kenan?”

“Eh na dawo, baka nema na ko?”

Raihan ya ce “Haba dai wane ni”

“To yaya ƴar tawa?”

“Gata nan tana jin ka, ta ce a gaisheka kan mu zo”

“To dan Allah ace mata ina roƙon arziki, a taimaka a bar mini kai ka koma office, ana ta kirana a waya ana nemanka”

Raihan ya ce “To za a gaya mata, amma na zata saura sati biyu sannan na koma”

Alhaji ya ce “A’a babban mutum, a duba mini lamarin nan”

Raihan ya ce “Zan shigo in anjima in sha Allah, sannu da zuwa”

Alhaji ya sauke wayar yana murmushi ya ce “Lallai babban mutum, ka ci gidanku da sati biyun”

Mami da ke kusa da shi ta ce “Kana nufin ba ya zuwa aiki dama?”

“Da sabon auren zai fita aiki? Lallai wato ni ya mayar shashasha, idan na ce ya zo sai ya ce mini wai aiki ya yi yawa”.

Alhaji ya kalleta ya ce “Ya zo yayi miki me? Ango ne fa”

A fusace ta ce ‘Angon banza, bazawarar?”

“Ba mace ba ce? Ke ina ruwanki ne, Bilkisu ki kiyayi shiga shirgin yaran nan kin ƙi ko? Zaki yi ta fama da takaici kuwa”

Haushi ne ya ishi mami, tare da yi wa kanta alwashin, dole ta san abun yi a kan raihan da ummi, tun da tun ba aje ko ina ba, kansa yana rawa.

Ummi sai magiya take yi wa raihan, ya tafi da ita ta gaida Alhaji, ya ce mata sai an kwana biyu.

Ta ja gefe ta kashingiɗa a kan kujerar da suke ta ce “To ka tashi ka je ka yi masa sannu da zuwa”

“Sai anjima” yayi maganar yana ɗora ƙafafuwan ta a kan cinyarsa yana matsa mata.

Ta buɗe datar ta, taga messages da yawa sun shigo, ta din ga mamaki dan ita wanda take chatting da su ba su da yawa.

Group ta ganta a ciki, na ƴan makarantar islamiyyar su ne, kuma ta ga ana ta tagging ɗin ta, banda messages da ta gani ta private.

Voice messages ta fara buɗewa, ta din ga jin saƙonnin zagi da ashar, wai saboda ta auri ƙanin maryam, ana ta cewa ta yi asara.

Kashewa take ƙoƙarin yi, ta ajiye wayar, ya karɓe wayar, ya cigaba da saurarar abun da suka ce, tare da duba messages ɗin duk da suka yi.

Tun tana jure jin, har ta karaya ta fara kuka, saboda cin zarafin yayi muni.

Wayarsa ya ɗaukko, ya danna ya kara a kunnensa.

“Zan turo maka wasu lambobi, ayi tracking ɗin su duk in da suke dan Allah, zan biya ko nawa, zan turo maka wani abu”

Ya ajiye wayar ya kalleta ya ce “You don’t need to cry anymore, zan yi dealing da duk wanda ya ce zai saka ki kuka ko waye shi” daga haka ya tashi ya fita.

Gaba ɗaya jikin Ummi yayi sanyi matuƙa, zagin da suka yi mata yayi mata zafi, tun da suka bar islamiyyar suka yi aure babu wadda ta sake neman ta, sai yanzu da suka sakata a group na makarantar suka ci mata mutunci, da dawo da abubuwan da suka faru a baya, wai tana yawo duk da dauɗa ga muni, dan son zuciya ta auri ƙanin ƙawarsu.

Hankali kwance raihan ya je gida, ya shige wurin Alhaji, Alhaji ya din ga ce masa yayi ƙiba ya ƙara kyau.

Nan suka tare a sashen Alhaji, har da Hajiya da Salim.

Mami ce ta kira shi hankali a tashe ta na tambayar sa yana ina. Ya bata amsar yana sashin Alhaji.

Ko mintuna uku ba ayi ba sai gata, ba ta damu da su hajiya da suke zaune ba, ta nufi raihan tana neman ta kai masa duka.

Alhaji ya miƙe ya ce “Bilki meye haka?”

“Aure hauka ne? A kan me zai sanya ƴan sanda su kama matan mutane? Maryam ta kira ni tana kuka, an kama su an kira shi a waya yaƙi ɗagawa, uban me suka yi maka?”

“Matata suka zaga babu dalili, tsakani nake so ayi musu, kar su zagar mini mata, ba tayi abun kunya ba dan ta aureni”

“Ni ka ke gaya wa haka raihan?”

“Mami ba da ke nake ba, ba kuma da wata manufa na faɗa miki ba, ni na saka ummi ta aureni, idan na zuba ido ana cin zarafin ta, ban yi mata adalci ba”.

Hajiya ta yi murmushi ta ce “Allah mai ƙudura, ɗan so ya faɗa hannun matar so, ko dai ki bi a hankali ko ki rasa shi gaba ɗaya”

Ayshercool

   CUTARWA

39

Alhaji ya ce “Jidda ya haka ne? Wace irin magana ki ke yi kuma?”

Hajiya ta ce “Kaga ƙyale ni na faɗa, ai a baya ban taɓa yi ba, sai mu gani idan dabarar mutum za ta ƙwace shi, me aka yi da maza ko sati uku ba a rufa ba fa? Baki ga komai ba”

Mami kuwa kumfar baki ta din ga yi tana cika baki, Salim ya tashi tsam ya fice, dan baya son hayaniya, hajiya ma ficewa tayi ta bar ɗakin.

“Ka gani ko ka ga abun da ka janyo mini ko?”

Kamar raihan zai fashe da kuka ya ce “Mami me kuma na yi?”

Alhaji ya ce “Raihan bai yi miki laifin komai ba, ke ki ke ƙoƙarin koya masa rashin gaskiya, da kuma raina ki, wuce ka jirani a mota, mu je a kashe wancan case ɗin da ka ɗaukko” Raihan ya fita yana satar kallon mami.

Alhaji ya sake mayar da idonsa kan mami ya ce “Gaskiya hajiya ta gaya miki, na sha gaya miki mu maza idan muna kan wannan gigin da rawar kan, ba a cewa za a tanƙwaramu ta ƙarfin tsiya, ko da kuwa iyayen da suka haifemu ne, ke meye ban yi ba a kanki?
Ko kin manta yadda na ɗauke ki, na bar ƙasar sama da wata uku na bar hajiya, na toshe kunnena, na ƙi saurara kowa sai yanzu dan abun ya zo kan ɗanki ki ce ba ki san zancen ba? Shiyasa a kowane ƙadami ake so ka zama mai adalci, ko dan gaba, baki nuna mini illar abun da na din ga yi ba, sai daga baya da na gane kuskurena dan kaina, ka kwanta da mace kawai ba shi ne aure ba, wannan abu ne na lokaci, managarciyar mace mai tsoron Allah, da kuma biyayya ita ake fata. Amma idonki ya rufe dan ɗanki ya auri bazawara, sai me qualities ake dubawa ga mutum mai hankali, ba wai abun da ku ke tunani kawai quality na mace ba” da farko faɗa yake yi mata, daga bisani kuma ya koma nasiha, ya gama ya fice daga ɗakin ya bi raihan.

Ko kaɗan mami ba ta ji nasihar Alhajin ta shige ta ba ma, babban burinta a yanzu kawai, shi ne raba ummi da raihan tun kan ta kanainaye shi gaba ɗaya.

Ba dan tare da Alhaji raihan suka je station ba, da sai raihan ya ja case ɗin, dan kuwa babbar headquarter hukumar ƴan sanda yasa aka kai su, kuma ya tafi da wayar ummi a matsayin shaida.

Alhaji ya ce wa raihan, ya kai shi gidansa, yana son yin magana da shi da ummi gaba ɗaya.

Suna tafe yana yi wa raihan nasiha.

“Babban mutum, na son kana son matarka, amma ka yi ƙoƙari ka din ga ɓoyewa saboda mahaifiyarka da bakin sauran mutane, ka san kishin mata ba lallai sai tsakanin kishiyoyi ba, su ba sa raina abun yi wa kishi, sannan ka yi ta haƙuri kana cigaba da addu’a komai zai wuce, amma matarka ka riƙe ta sosai ka kula da ita”

Raihan ya jinjina kai, suka ƙarasa gidan sa, tun da raihan ya kirata ya ce mata tare za su zo da Alhaji, ta gama girki, amma ta shiga ƙoƙarin ƙara wasu abubuwan.

Tun da ya zo kanta a ƙasa yake, saboda tsananin kunya, ko sau ɗaya ba ta yadda sun haɗa ido ba, shi duk yadda ake zuzuta muninta shi bai gani ba, sai tsantsar tarbiyya da nutsuwa, kuma tubarkallah shi bai ga wani muni ba.

Yayi musu nasiha sosai da sosai, ya ce raihan ya mayar da shi gida.

Ummi ta ce “Baba na gama abinci, bari na kawo maka”

Alhaji ya ce “Kar ki damu ƴar albarka ta, sauri nake kuma a ƙoshe nake, Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri kun san irin auren nan naku, society ɗinmu sun ɗauke shi, kamar wani zunubi, amma tun da bai saɓawa addini ba shikenan.

Da ƙyar ya sha lemo ya tashi, sai dai lemon yayi masa daɗi sosai da sosai, lemon cucumber ne da lemon tsami.

Da ƙyar wannan tarzoma ta lafa, sai dai aka saka ƴan islamiyyar su ummi ba ta haƙuri, kuma suka rubuta takardar ban haƙuri, suka yi signing ba ruwansu da ita ya taho da ita gida.

Bayan ya nuna mata takardar ta jujjuyata ta ce “You go far MD, da duk ba ka yi musu haka ba”

Ya ce “No, abun da na yi dai-dai ne, ba zai yiwu su ɗarsa miki wani abu mara kyau game da aurenmu ba, alhalin halataccen aure muka yi ba, kuma gaba ba za su sake yi wa wani hakan ba”.

Ta ce “To Allah ya kyauta. Alhaji bai ci abincina ba” tayi maganar a shagwaɓe.

“Bani in haɗa da nawa da nasa na cinye”

“Wai ba ka gajiya da cin abinci ne, ka daina zuwa gym ɗin ma, idan ba ka yi wasa ba, sai ka kasa wucewa ta ƙofar falo”

“Eh na ji bakomai, hakan ma normal ne”

Ummi ta ce “Sai na saita maka cin abincin ka, ba zan je da kai unguwa ka bani kunya ba, ace ba ka ƙoshi” ya kwashe da dariya, ya ce “Yanzu ba zan gane wannan ba, sai cikina ya cika tukuna”.

Ranar litinin kuwa, ummi ta sha fama da raihan kan ya tashi ya tafi aiki, aikuwa da ya je ya sha aiki sosai da sosai.

Tun da raihan ya koma aiki, sai gidan ya yi wa ummi girma, ba ta aikin komai, duk sai kaɗaici ya dameta.

Gashi baƙin da sukan shigo, duk sun daina zuwa.

*
Anty Rakiya ce a zaune tana kallon fuskar mami me ɗauke da zunzurutun damuwa.

“Ke yanzu Bilki har matar nan ta samu bakin yi miki rashin mutunci, yaushe ta waye?”

“Anty Rakiya ni ba wannan ne ya dame ni ba, kar bakinta ya tabatta yarinyar nan ta ƙwace raihan na shiga uku, ta ji daɗin yi mini dariya, shi ne babbar damuwata da tashin hankali”

“To wai kin bi shawararin da na baki kuwa?”

“Wallahi na bi, kin san raihan da taurin kai, ban gaya miki ranar da na kirshe shi ba, daga shiga ɗaki ya gudu ba. Ya ce mini ya koma aiki ashe duk ƙarya yake yi, yarinyar nan sumi-sumi, kar in je ta ƙwace shi, tun da sa’arsa ce kuma bazawara wayo za ta yi masa na shiga uku Anty rakiya”.

“Ba ki shiga uku ba, ai wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi, dole ki samu hanyoyin muzgunawa yarinyar nan, kuma ki fara matsa masa a kan auren safiyya”

Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan, in sha Allah zan cigaba da ƙoƙari”.

Ranar asabar raihan yana ta murna zai wuni a gida tare da ummi, tana kitchen tana shirya musu breakfast, yana ɗaki yana bacci mami ta kira shi a waya wai ya je.

Tamkar ya fashe da kuka, haka ya ji, ya ajiye wayar, yana tunanin meyasa mami take yi masa haka, lallai sai ta shiga rayuwar aurensa da ummi.

Ya lumshe idonsa, ransa babu daɗi, ummi ta shigo ta kunna turaren wuta a ɗakin.

Ta shiga banɗaki ta haɗa masa ruwan wanka, ta je kan gadon tana ɗan dukan filonsa ta ce “MD, ka tashi ka yi wanka mu karya” juya mata baya ya yi, ya ce “Wake me up in romantic way”

Ta ce “Like how? Ba gashi yanzu ka tashi ba”

Ya juyo ya kalleta ya janyota jikinsa, yayi kissing ɗin ta a goshi ya ce “Wake up sweetheart” irin haka nake so.

Ta ce “Ashe ba zaka tashi ba idan haka zan yi maka, yadda nake fama da kai ka tashi, da ƙyar ka ke tashi fa”

Ya ce “A’a idan ki ka yi mini haka sai na fi saurin tashi ai” ya ƙare mata kallo ya ce “Ni gaskiya a daina tashina da irin wannan kayan, ni dressing zaki din ga yi mini yadda ba za ace ki na jin hausa ba ma”

Ummi ta ce “Innalillahi, wai dama haka ka ke, mutum sai tsaurin ido, duk a ina ka san wannan ne?”

Wata irin dariya ta bashi, ya ce “Ai tsaurin ido ya riga ya ƙare tsakaninmu, tun da ni da ke yanzu kin san waye boss, fita fa zan yi”

Ta ɗan ɓata fuska ta ce “Cewa fa ka yi a gida zaka wuni”

“To ya zan yi fita ta kamani, ki yi haƙuri kin ji baby”

Ummi ta kalli fuskar sa ta ce “Yaushe zaka kai ni gida na gaida su mami ne? Kuma ban je na yi wa Kawu da su anty bangajiya ba”.

Ya ɗan sosa kai ya ce “Haka ne, amma for now ban ji zan iya bari ki fita ba”

Ta marairaice ta ce “Dan Allah”

“Na ji amma da sharaɗi”

Da sauri ta ce “Menene sharaɗin?”

“Sai kin ce mini baby”  tayi turus tana kallon sa.

Ya ce “Yauwwa ai na san lagonki, and ki roƙe ni in a romantic way, a guje zan barki”.

“Dan Allah baby ka bar ni na je na gaida su mami, na je gida na yi wa kawu bangajiya”

Ya girgiza kai ya ce “Ba haka ba, idan kin koyo sai ki tambaye ni, yanzu dai tashi mu je ki tayani wanka” sai da ta ɗan matsa daga kusa da shi ta ce “Wanka kuma?” Ya ɗaga mata gira.

“A’a zance maka babyn dai” sauka yayi daga kan gadon ya ce “Kina da sauran aiki Salma, ina son soyayya sosai ban sani ba ko dan ban taɓa yi ba sai a kanki, amma ina son gidana ya fi ko ina samar mini farinciki, kar ki saka na fara leƙe-leƙe” ya ƙarasa maganar yana shigewa toilet, a daidai lokacin da ƙirjin ummi ya buga da maganar sa ta ƙarshe.

Shi ya ma manta da ya faɗi maganar, ummi kuwa duk ta shiga damuwa, ya gama cin abincin sa ya fice.

Ummi ta zauna ta yi shiru tana tunani, abun duniya ya isheta, tana son yin abun da za ta faranta wa raihan rai, sai dai haryanzu tana tsananin jin kunyarsa. Ta buɗe wayarta ta shiga YouTube, tamkar sun san halin da take ciki, ta ci karo da wani video, malamar tana ta bayani a kan kula da miji.
Malamar take cewa “Ƴan mata nawa ya tsallake bai aure su ba, ke ya auro ki ya kai ki gidansa, ko da ya kasance mai kule-kule ke ɗin dai ke ya zaɓa, dan me zai kai ki gidansa ki din ga yi masa gidadanci, ba ko yaushe kunya take da muhalli a aure ba” ummi ta shagala tana kallo, malamar har da demonstration na yadda za a yi wa miji kissa.

Ji ta yi ana danna bell ɗin ƙofar falon, ta ajiye wayar ta tashi ta buɗe.

Ta faɗaɗa murmushinta, ganin wata babbar mace da wata.

Tayi musu maraba zuwa cikin falon, tana ta jera musu sannu da zuwa.

Matar ta kalleta ta ce “Kin gane ni ne?”

Ummi ta yi murmushi ta ce “Na gane ki, maman bauchi ce, ai ya nuna mini a hoto”

Hajiya Aisha tayi murmushi ta ce “Lallai kin yi kyan kai, ina can ya aike ni bana ƙasar, ban samu zuwa bikinku ba, na je umara daga nan na tafi aiken raihan”

Ummi ta yi murmushi ta kawo musu ruwa, da lemo.

Ta ce “Daga baucin ku ka taho?”

Hajiya Aisha ta ce “Daga can muke, tun safe muka taho ai”

Ummi ta ce “Be gaya mini ba, ai da na ɗora muku girki tun kan ku ƙaraso”

“Be san zamu zo ba shi ma, amma yana gida ai ko?”

Ummi ta ce “A’a ya fita tun ɗazu”

Ta kawo musu kayan tea, ta shiga kitchen ta ɗora tukunya.

Siyama ta kalli Hajiya Aisha ta ce “Mummy, ga fa kairun nisa’i in ji raihan, ki ga rashin mutuncin da yake yi mini a kan matar nan, wai duk matan ƙarshen zamani ita suka rako”

Hajiya Aisha ta yi dariya ta ce “Raihan ne fa, haka nima yake ce mini duk ranar da na zo gidansa na ci girkin ummi, wai sai na koma bauci ba yatsu saboda daɗi, hannunta akwai maggi”

Suka yi ta dariya, nan da nan ummi ta din ga yi musu hidima, ta kawo wannan ta kawo wancan.

Duk rashin son sakewa da mutane irin na ummi, ta ɗan sake da hajiya Aisha, suna ta hirar duniya.

Hajiya Aisha ta kira raihan a waya tana faɗan ina ya tafi weekends, ta zo baya nan.

Ya ce mata yana gida, ta ce ita ba zata kwana a kano ba, ya dawo za ta tafi.

Dama duk a takure yake, kiransa kawai ta yi ta zaunar da shi, Safiyya na ta kaiwa tana komowa tayi kwalliya, sai dai ko kallo ba ta ishe shi ba, hankalinsa yana kan wayarsa yana kallon hotunan ummi.

Idan ya kalli safiyya sai ya ganta wani iri, shi dai a wurinsa ya fi ganin kyan ummi nesa ba kusa ba, ita baƙinta ke hana a ga kyawunta, kuma yanzu ta washe ta ƙara kyau.

Duk da yana complain da kunyarta ta yi yawa, amma yana jin daɗin wuninsa a gida tare da ita, ya ci abinci da ita, ya shaƙi daddaɗan ƙamashin turarukan ta, uwa uba lallausar fatarta da ba ya gajiya da taɓawa, jikinta tamkar jikin tarwaɗa, ko kuma wata fulawa.
Shi komai na ta burgeshi yake yi.

Raihan ya kalli mami ya ce  “Maman bauci tazo tana gidanmu tana jirana”

“Saura ka je ka gaya mata wani abu, ta zo ta cika mini kunne da masifa”.

Mintuna arba’in sai ga raihan ya dawo.

Aikuwa hajiya Aisha ta din ga masifar weekend ya zauna a gida da matarsa, amma ya fita yawo, idan ya je wurin mamin shayar da shi take ko kuwa?.

Shi dai bai ce komai ba ya ce “Ayi haƙuri na daina, amma kar a juya mini baya a koma wurin ummi”

Ta ce “A’a ni fa na yi ƴa, ga iya girki ga mutunci, kalli yadda ka yi ƙiba fa, ummi ta iya kiwo, ya ma sunan da ka ke gaya mata”

Ba kunya raihan ya ce “Khairun nisa’i”

Ummi kuwa kamar ta nutse, ta tashi ta tafi kitchen tana wanke kwanuka.

Ya sameta a kitchen ya ce “Madam sannu da ƙoƙari, Mummy na ta yaba miki, ina godiya sosai da sosai”

Hararsa tayi ta ce “Baƙina ne ai ba naka ba”

Ya ce “To ai shikenan, zo ku yi sallama”

Ummi ta ce “Har tafiya za su yi?”

“Wallahi kuwa, ta ce ko gidanmu ba zata ba bauchi zasu koma, gashi ba su taho da direba ba, kar su yi dare”.

Ta ce “To yi gaba zan taho”

“Saboda me?”

“To kawai sai kuma a ga mun jero tare?”

Danƙo hannunta yayi suka yi waje, turus ummi ta yi ganin iyayen akwatuna a falo.

Hajiya Aisha ta ce “To ga kayanku nan, ku duba abun da bai yi miki ba, sai a canzo, ko kuma ma yi waya kawai, tafiya zamu yi”

Ummi ta ce “Mummy ki bari ki kwana mana”

Hajiya Aisha ta ce “Taɓ mijina yana gari, wa zai kula mini da shi, sai mun yi waya”

Cikin sauri ummi ta tafi ɗaki, ta ɗebo turaren wuta, na gashi da na jiki, ta din ga haɗo kaya a leda, ta bawa Siyama ta ce musu ba yawa.

Hajiya Aisha ta yi musu nasiha, tare da fatan alkhairi suka tafi.

Nan raihan ya zauna a falon, yana bubbuɗe akwatunan, ummi kawai ta zuba masa ido tana kallon uban kayan da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin mallakar su ba.

“Ki saukko ki gani mana sweetheart” ta saukko ta zauna a kusa da shi tana kallon kayan.

Ganin tayi saroro kamar sokuwa ya sanya ya ce “Ko kayan ba su yi miki bane ba?”

Kawai ya ga hawaye na bin idonta, gaba ɗaya ya rikice ya ce “Menene kuma? Ko Mummy sun yi miki wani abun da ya ɓata miki rai ne?” Ta girgiza masa kai alamar a’a.

“To menene? Bana son kukanki ummi, gaya mini”

Ta ƙara matsawa kusa da shi, ta rungume shi tana kuka.

Ya saka hannunsa ya tallafo fuskarta, cikin kulawa ya ce “Gaya mini menene?”

“Na gode” tayi maganar wasu hawayen na zubo mata.

Raihan ya ce “Haƙƙinki ne fa ummi, meyasa zaki yi kuka?”

Ta sake kwantar da kanta a jikinsa, ta ce “You mean a lot to me, na tuna lokacin da na shekara biyu babu kayan kirki, yau ka gwangwaje ni da wannan uban kayan, ni wallahi ban san ma me zan ce ba, kamar kalmar godiya ta yi kaɗan, Allah ya suturta ka duniya da lahira, ya yalwata arzikinka, na gode MD”

Jikinsa yayi sanyi sosai, duk da bai san cikakken tarihin ummi ba, amma alamu sun nuna ta sha gwagwarmaya da rayuwa.

“To ki daina kukan haka, in sha Allah in dai ina raye, sutura sai dai ki ɗauka ki bawa wani, sutura ba zamu yi ta ɗinka ta muna sawa”.

“Na gode MD, amma dan Allah kar ka takurawa kanka yi mini abun da ba ka da shi, ni dai na gode sosai”

“To ba zaki kirani da wani suna na soyayya ba, sai MD”

“MD my dear” ta faɗa tana murmushi.

“Wow ashe duk tsawon wannan lokacin, am your dear ban sani ba, barakallahu fik baby”

Ɗaɗɗaga mata kayan ya cigaba da yi, kaya sun haɗu masu tsada har da gwal.

Sai da ya zo kan akwatin ƙanan kaya, ya din ga ɗaɗɗagawa yana cewa ba ƙaramin kyau zaki yi a ciki ba.

Ummi ta ce “Ai kai a nan ka fi kauri, ni bari na je kitchen abincina kar ya kama”.

Idan ummi ta kalli raihan ta kalli kayan nan, sai ta rasa me ma za ta ce masa, ya baje yana ta aiki a system gefen sa ga biro da takarda.

Dogon matashi cikakke, dai-dai gwargwado raihan kyakkyawa ne, kuma duk kyawawan mata babu wadda ya gani ya ce yana so, sai ita kuma yake ta wahala da ita.

“Ya dai madam?”

Ta tashi ta ce “Bakomai, zan je wancan falon na gyara shi kan magariba”.

Ya ce “Yauwwa, ni kuwa na ce ko ƴar aiki za a samo miki ne? Ta din ga taya ki aikin nan, yayi miki yawa”.

Ummi ta ce “Aikin gidan nan guda nawa yake, zan iya abuna”

“Faɗi gaskiya dai, ko abun ne ya motsa, dan kar a aure ni”

“To a aurekan mana, duk wadda za ta iya zama da ni ta shigo”

Ya kwashe da dariya ya ce “Eh lallai kin yi baki baby”.

Ummi ta ɗauki hoton kayan, ta turawa su Yaya maryam, suka din ga murna tare da sanyawa raihan albarka.

Iya ƙoƙari ummi take yi, wurin rage kunyar raihan da take ji.
Dan haka a yau tayi iya yin ta tayi irin shigar da yake so.

Aikuwa daga kallon da ya din ga yi mata, ta gane ya ji daɗin hakan sosai da sosai.

Ya sha mamaki sosai da sosai, dan kuwa tayi masa kyau sosai da sosai, Allah ya taimaki ummi raihan ba shi da abokan da zai yi zaman majalisa da su.

Duk a kunyacen take, amma ta dake kar sokoncinta ya sanya shi fara kalle-kallen.

“Baby zaka kai ni gaida su mamin da su kawu”.

Ya ce “Wow, shagwaɓar nan taki tana burgeni ummi”

Maganar Iya ta tuna, da take ce mata ‘Tana shagwaɓa da fuska kamar kashi’

Ya amince da zuwanta gaida su mami, amma ya ce sai ranar juma’a da daddare. Washegari ranar asabar kuma sai ya kai ta gidansu.

Ummi ta yi ta murna, raihan ya ce “Ai in dai zaki din ga abun da nake so, zan zama mijin hajiya Salma.

Wata irin soyayya raihan yake nuna wa ummi, da take fatan ta ɗore har abada.

Ranar juma’a tun safe, ummi take aikin yin sinasir da miyar agushi, wanda za ta kai gidan su raihan.

Tun sallar magariba ta shirya take jiran raihan, ya dawo ya ƙare mata kallo ya ce “Gaskiya kin yi kyau da yawa, ba zan tafi da ke a haka ba, sai ƙamshi kuma ki ke yi, am jealous ki rage kyan nan”

“Daga ni sai kai fa zamu tafi a mota mu dawo, dan Allah ka shirya mu tafi”

Sai da ummi tayi da gaske, sannan ya shirya suka tafi.

Tambayarta ya din ga yi a kan wannan kulolin restaurant za ta buɗe ne?.

“Eh in dai zaka yi patronizing ɗina”

“To ɗan buɗe ki san mini abun da ki ka dafa ɗin”

“Aikuwa ba za ka ci ba”

“Suna tafe suna faɗansu irin na masoya”.

Karɓar da mami tayi mata kawai jikinta yayi sanyi, ko kallo ummi ba ta isheta ba.

Safiyya kuwa tun da ta ga ummi jikinta yayi sanyi, ana ta ummi mummuna ce, amma ta ga ummi dirarriyar mace, muryarta kawai idan ta yi magana sai ka so ganin waye yake yin maganar, gashi komai na ta a nutse. Duk da dare ne amma duk wanda ya ga ummi ya santa a da, ya san ta canza sosai, fatar nan ta ƙara kwanciya tayi fresh sai ƙamshi take yi.

Ko gaisuwar ummi taƙi amsawa.

Raihan ya ce “Mami zuwa muka yi ta gaishe ki, ta yi muku bangajiya”

“Na ce maka ina nemanta ne, tun a farko ban gaya maka babu yawuna a maganar aurenka ba? Ka nema mata wata sirikar bani ba. Muguwa kawai, sumi-sumi da ke na zata ta Allah ce, ashe mutuniyar banza ce, kuma da ni ki ke zancen. Ɗa na ne dai wallahi sai kin bar shi, zan yi masa irin auren da nake so, kuma ina nan dawowa kanki”

Raihan ya tashi ya ce “Ummi mu je mu gaida su Alhaji mu tafi kar dare yayi”

Ta tashi kanta a ƙasa, ta ɗauki kwandon da suka zo da shi, ta ajiye wa mami na ta food flask ɗin.

Mami  ta ce “Kwashe tsiyarki, ba abun da zan yi da abincinki”

Raihan ya durƙusa ya ɗauka ya ce “Bari a ƙarawa mami da shi”

Ta buɗe baki tana kallon raihan.

Bayan fitarsu Nihal ta ce “Taɓ mami dama haka matar yayan take? Gaskiya babu lallai ya saurari safiyya, kin san halin sa ba komai yake burge shi ba, amma idan ya ce yana son abu ya dage, canza shi sai Allah. Kalli dirarriyar mace ga iyayi”.

“Ke dalla rufe mini baki, tashi ki bar falon nan”

Can kuwa ummi jikinta yayi sanyi, amma karɓar da ta samu a wurin Alhaji da Hajiya, sai ya mantar da ita abun da mami ta yi mata.

Sai gashi sun shantake, har goma na dare suna gidan, sun sha nasiha da sanya albarka daga bakin Hajiya da kuma Alhaji.

Alhaji da kansa ya kira Salim da Sagir a waya cewa yana nemansu, bayan sun zo, ya sake gabatar musu da ummi.

Tun ummi na nan suka fara cin abincin su, suna santi ana koɗa girkin nata, wanda hakan ya yi wa ummi daɗi sosai.

Goma da rabi, sannan suka tafi gida, raihan bai yi mata maganar abun da mami ta yi ba, ita ma ba ta yi masa ba, sai dai ta damu da ganin safiyya ya ɗaga wa ummi hankali, ganinta yarinya kuma kyakykyawa.

Haka ta kwana tana wasi-wasi daban-daban, ta ƙuduri aniyar sake zage damtse a kan raihan, yadda ko zai yi wani auren, ba za ta rasa soyayyar sa ba.

Ta nemi iznin sa, tana son ɗaukar wani abu daga lefenta tayi kyauta da shi, ya ce nata ne, babu buƙatar ta tambaye shi.

Washegari  ta yi girke-girken ta, ya kaita gidan dr.

Suna hanya take ce masa “MD, yakamata ka koya mini mota, sai in din ga kai ka wurin aiki, ina ɗaukko ka”

Yayi dariya ya ce “Matata direbata”

“Eh mana, kaiman ka din ga hutawa”

“Kawai ki ce a saya miki mota”

Ta waro ido ta ce “Wace ni? Ba haka nake nufi ba da wasa nake yi maka”.

A ƙofar gidan yayi parking, ya ciro 10k ya miƙa mata ya ce “Wannan ki bawa dr. Ki ce in ji ki amma, ni idan na zo ɗaukar ki, zamu gaisa da shi”

Kissing ɗin raihan ta yi a kumatunsa ta riƙe hannunsa ta ce “Thank you baby.. ya kalli idonta ta ƙarasa babyna.

Dariya yayi yayi kissing ɗin ta a baya, yana maimaita mata i love you.

Farida kasa ɓoye mamakinta tayi, ta bi ummi da ido, ummi kuwa ta shagala suna murnar ganin juna ita da noor.

Kallo ɗaya zaka yi wa ummi, ka san hankalinta ya kwanta, leshin jikin ummi kawai take kallo, da yake wasu kayan a ɗinke a ka kawo mata, ta sha kwalliya duk da mayafinta a ka ta ɗora shi.

Dr. Ya fito yana faɗin “Oyoyo mamana, amarya ba kya laifi”

Ummi ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa.

Ya ce “Mamana, kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa? Lallai aure ya karɓe ki, kin ganki kuwa? kunya ta rufe ummi.

Da kausar ba tayi niyyar fitowa ba, amma dai ta fito ganewa idonta ikon Allah, ummi an sha to match, har da wani agogo mai ɗan karen kyau.

Noor ta bubbuɗe kwanukan da ummi ta zo da shi, miya ta sha kaji zuƙu-zuƙu ga snacks, abun da inteesar ba ta taɓa yi ba.

Sun yi hira sosai da dr. Har take gaya masa cewar raihan ya yi mata lefe.

Dr. Ya din ga sanya masa albarka.

Da azahar da zai fita, ummi ta kawo kuɗin nan ta bashi dubu bakwai, ukun kuma ta ƙara biyu ta bawa farida biyar.

Sai dai farida ba ta so yadda ta ga ummi ba, ta kasa ɓoye hassadarta baƙin ciki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta, kausar ma sai wani zumɓura baki take yi tana hura hanci.

Ummi ta ce wa noor “Yaushe zaki zo ki ga kayan da MD ya saya mini, ki zo ki ɗauki abun da ki ke so”

Noor ta ce “rana ita yau, zan diro ko ta katanga ne, zan zo ki haɗa mini akwatu guda” ummi kamar wurin noor ta zo, tare suke ta hirarsu.

Ummi ta miƙe ta hau gyare-gyaren gidan, duk gidan yayi ƙazanta saboda ba ta nan.

Tana nan Abdul ya dawo, shi ma ya yi farinciki sosai da sosai da ganin ummi, sabuwar shadda ta bashi yadi goma, ta ce ya ɗinka musu shi da dr.

Ana sallar magariba raihan ya zo tafiya da ummi, suka gaisa da dr. Yayi wa dr. Alheri, ya sha sanya albarka sosai daga wurin dr.

Ya ɗauki matarsa suka tafi.

*
Watannin ummi huɗu a gidan raihan, mami ta matsa lamba a kan lallai sai ya auri safiyya.
Sai dai juyin duniya, fafur raihan ya nuna mata ba zai iya auren Safiyya ba.

Ta je ta samu Alhaji da maganar, ya ce ta bari, za su yi maganar da Raihan.

Raihan ya amsa kiran da Alhaji yake yi masa, ba tare da sanin dalilin sa ba.

Bayan Alhaji ya sanar masa da buƙatar mami, sai ya ga ya ɓata fuska.

“Babban mutum ba ka ce komai ba”

“Alhaji me zan ce? Kwata-kwata yaushe na yi auren da zan ƙara wani? Ni wallahi ummi ta isheni, mami ba za ta iya samo mini mace mai qualities ɗin ummi ba, ni dai dan Allah ka bata haƙuri, ka san plan ɗina Alhaji wallahi ina son ummi, yayi wuri in yi mata kishiya, kuma wallahi idan na auri wata ba zan iya adalci ba, na fi son ummi”

Alhaji ya yi murmushi irin nasu na dattawa ya ce “Shikenan, jeka ba sai ka je wurinta ba, tafi gida abun ka”.

Sai da daddare da mami ta zo wurin Alhaji, tayi masa maganar ya ake ciki, yaushe za a kai kuɗin auren Safiyya”

Alhaji ya ce “Bilkisu, ina son ki fuskanci wani abu, ki ƙyale yaron nan da matarsa hankalinki da na su su kwanta, kar ki saka ƴar mutane a wahala, idan ba ki bi a hankali ba yaron nan zai iya gaya miki abun da zaki gaza haɗa ido da shi, ya ce ba zaki iya samo masa mace irin matarsa ba, ko ya auri wata ba zai yi musu adalci ba, idan kin gane shikenan idan kuma sai ranar da yayi miki hansfree shikenan.
Na manta ban gaya miki ba, this coming Friday, za su tafi China tare da matarsa maganar auren nan ki bar ta for now.

Ayshercool

Series Navigation<< Cutarwa Part 1
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *