🥚ƘWAI CIKIN ƘAYA!!🥚 Bilyn Abdull ce Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. Ya rabbi ka bani ikon faɗar abinda zai amfanar da al'ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka tsare harshena da alƙalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.😭🙏🏻 Ya ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al'ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama, ALLAH ka kawo mana ƙarshen wannan annoba ta corona virus (covid-19), domin rahamarka garemu😭🙏🏻. Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin ƙanƙantarta, inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba☹️. Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ɗina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum), alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da kuke har gadon barci.😘👌🏻 _____________________________________ BOOK ONE Shafi na ɗaya _____________________________________ ...........Ko wacce kafar yaɗa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine sace shahararren mai arziƙin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*. A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin sauka da tashi na babban birnin ƙasar. Abu mafi ɗaure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da mutumin da yay garkuwa da shi ya ƙwamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi ɗaya da Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama'a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ƴan jarida guda biyu a filin jirgin da har suka ɗauki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar da ɗaya a masu gadinsa ya buɗe masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake buɗe masa ƙofa dan ya fita sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye, a taƙaice dai Alhaji Sadi kokino yayi ɓatan dabo a hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa. Zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da buɗe kunnuwa da idanu ko za'aji wani abu da ga bakin wannan mai ƙwamushe da ba'a san ta yanda yay siddabarun sace Alhaji kokino ba... *____________________________________* A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruɗaɗɗen labari suma talakawa ƴan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu ALLAH ya ƙara suke faɗa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke ƙaryata lamarin da dangantashi da farfaganda irinta manyan ƙasa ce kawai, ƙilama yana can kwance a gidansa lafiyar ALLAH. Daga masu ƙaryatawa har waɗanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda ƙwamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami'an tsaro da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana. Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan😟. *___________________________________* Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan ɗanja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa. Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai ƙoƙari da jajircewa a aikinsa kallo ɗaya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin kasalar dake tattare da shi. Tsayuwar motar da buɗe murfin da akayine ya tilasta masa buɗe lumsassun idanunsa kaɗan tare da ɗago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun, kaɗan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaɗan kafin ya sauke hannun da maida dubansa ga ƙofar motar da aka buɗe. Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baƙar rigar sanyinsa jibgegiya dake gefe ya zura kafafunsa waje. Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya buɗe ƙofar yay azamar kai hannu zai amshi rigar sanyin yana sake ƙamewa alamar girmamawa. Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaɗan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaɗayansa yana tura ƙaramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando. Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka ƙame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinƙule kawai yay gaba ba tare da suma yace musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba. Cikin nutsuwarsa ya iso wajen da ake buƙatar ganinsa, da ganin yanayin ɗakin zaka fahimci wajene keɓantacce na jami'an tsaro da sukan tattauna akan wani case ko shawarwarinsu idan sun tado musamman ta fuskar tsaro. Ba tare da yay magana da kowa ba ya samu waje ya zauna, suma sauran waɗanda suka shigo tare wajen zama suka samu. Ɗakin yayi tsit, bakajin komai sai ƙarar AC da na fitar numfashi, sai kuma ɗan motsin da baza'a rasaba. Wanda ke tsaye jikin allon bangon yana wani ƴan zane-zane ya ɗago fuskarsa a matukar murtuke yana kallonsu. "Nasan kowa zaiyi mamakin wannan taron na gaggawa da muka kira, duk da dai dukkan tunaninmu zai iya tsayawa a waje ɗaya game da abinda muka wayi gari da shi na sace babban mutum irin Alhaji Sadi Kokino. Kamar yanda muka sani tun a daren jiya wasu a cikin jami'anmu suna a wajen domin binciko ainahin abinda ya faru, a yanzu hakama daga can muka tado ɗaya da ga cikinsu domin ya bamu bayanai dangane da lamarin, sannan musan mataki na gaba da zamu ɗauka kuma, dan yanzu dai ga agogo ya nuna ƙarfe 7:19am, na tabbata duk inda 8am tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami'ai na farko da kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama'ar gari zuwa ƴan jarida da iyalansa dama jama'ar dunaya baki ɗaya". A tare suka shiga jinjina kai alamar gamsuwa da bayaninsa. Cikin gyara tsayuwa ya ke kallonsu, ya sauke idanunsa akansa da har yanzu hannunsa ke dafe da kansa, *"Jawaad!"*. Jin sunansa da aka ambatane ya sakashi janye hannunsa tare da ɗago manyan idanunsa da ke a jajur ya sauke akan ogan nasa, cikin dakewar murya da ke tabbatar da shiɗin jarumine ma'abocin nutsuwa ya amsa da "Yes sir" tare da miƙewa tsaye yana ƙamewa. Gaban allon ogan ya nuna masa da biron dake hannunsa. Cike da kasala mai tare da nauyin jiki ya taka zuwa wajen, ya maido kallonsa gaba ɗaya zuwa ga sauran jami'an tsaron dake cikin ɗakin taron. Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara faɗin, "Duk abinda zan faɗa game da wannan lamarin a taƙaice zai iya zama gaggawa, dan har zuwa yanzu da na baro filina jirgin da gidan Alhaji Kokino babu wani bakin zare da muka samu a kai sai surutai marasa makama, a cctv cemaras na Airport kuma lafiya lau Alhaji Sadi ya shiga mota tare da masu tsaron lafiyarsa. A ɗan nazarina ta wannan gaɓar ya nuna lallai mai satar yanada matuƙar wayo, kuma ƙwararrene mai aiki da ƙwaƙwalwa..." Kowa jin jina kai ya shiga yi alamar gamsuwa da bayanin Jawaad da ke riƙe da kansa da ke ƙara ƙarfin sarawa na ciwo. Wanine cikin waɗanda ke zaune a kujeru na musamman, alamun shima babbane yay gyaran murya tare da gyara abin maganar dake gabansa. "Wato bayanan JAY abin dubawa ne kam tabbas, amma ku wace shawara ce da ku a kan hakan?". Wani ne da ga can rukunin kujerun da Jawaad ya taso ya ɗaga hannu, damar magana aka bashi. Bayan ya miƙe ya ƙame sannan ya fara magana cike da girmamawa, "Yallaɓai ƙwarai maganar jay gaskiya ce, sannan ya kamata muma muyi shiri na musamman akan wanann case ɗin, dan inhar muka kuɓutar da Alhaji kokino ba ƙaramin daraja hukumar ƴan sanda zata sake samuba a idon jama'a". Tafa masa sukai, wanima ya sake ɗaga hannu aka bashi dama, shima goyon bayansa ya nuna akan maganar Jawaad. Bayan shi mutane biyu sun sake yin mubayi'a kafin wani ya tashi shikuma bayan an bashi izini, fuska a ɗaure yana wani hura hanci da fesar da iska yace, "Sam wannan shawarar tasa bata kan tsari, ya kamata ama ƙalubalancesa, tun a daren jiya bayan faruwar abin da mintunan da basufi goma ba aka turashi wajen shida wasu jami'an tsaro, amma ace babu wani bayani na cigaba da aka samu, bayan a ƴan mintunan da sukaje wajen bai kai nisan da za'ace shi mai ƙwamishen yayi nisa ba, kawai shi dai yace bazai iyaba sai a nema wanda zai iya kawai, inba hakaba ta silar wannan case ɗin to lallai hukumar ƴan sada tana tare da babbar barazana ta zubewar kima da sake saka shakku a zukatan al'umma a kanmu". Kowa kallonsa yake kawai, yayinda manyan suke jinjina masa kai da wasu a tsirarun sauran jami'an. Jawaad kam ko motsi baiyiba balle ya kalli wanda ya gama bayanin, sai dai ya saki wani ƙasaitaccen murmushi da ya bayyana loɓar kumatunsa guda biyu kawai. Ba karamin sukar zuciyar Qaseem Ali murmushin Jawaad yayi ba, amma ta wani ɓangaren ya ɗanji sanyi a ransa ganin maganarsa taso kawo ruɗani, dan sai ya zam kawunan jami'an tsaron yana neman rabuwa, wasu suna bin bayan Jawaad Abdul'aziz yusuf, wasu kuma suna bin bayan maganar Qaseem Ali. Dan danan cece kuce ya fara yawaita a ɗakin taron har sai da aka tsawatar. Murmushi Qaseem Ali ya saki ganin Jawaad ya dafe kai, sannan fuskarsa ta kuma ɗaurewa alamar ransa ya sosu, dama babban burinsa kenan. Sai dai kuma sam tunaninsa bai sanar masa gaskiya ba, dan shi Jawaad surutun da ɗakin taron ya kaure da shine ya kuma saka kansa ƙarfin bugun ciwon da yakeyi sakamakon rashin samun isashshen barci da yay a daren jiya, ga ruwan sama da yay musu dukan tsiya jiyan da daddare, bayan dama ya koma gida a ƙurarren lokaci ne jiyan kafin ayi kiransa akan maganar sace kokino. Tsitt ɗakin yayi bayan tsawatarwar da akayi, yanzu ma ɗaya daga cikin shugabannin ne yay magana. "Duk wani kace nace bama buƙatarsa anan, kowa yasan wanene JAY akan ƙwazon aiki, ba wannan ne na farko ba da aka bashi irin wannan damar kuma ya magance ta, sai dai ko wanne irin case da ruɗanin da yake zuwa da shi, dan haka a wannan gaɓar mun naɗa Jawaad Abdul'aziz yusif matsayin wanda zai kula da wannan case ɗin, sannan mun saka Qaseem Ali matsayin mataimakinsa, kuna da damar haɗa rundinar jami'ai 30 da zasu taimaka muku, muna fatan zaku bamu gudunmawa ta haƙiƙa wajen fiddamu kunya ku kuɓutar da Alhaji Sadi cikin lokaci ƙankani da baza'a ga rauninmu ko gazawa ba". Tunda ya fara magana Qaseem yaji sunansa matsayin mataimakin JAY fara'ar fuskarsa ta ɓace ɓat, hakama magoya bayansa. Ga Jawaad kam bai ko ɗago kaiba balle musan yanayin da yake ciki. Sun ɗan cigaba da tattaunawa kusan na awa ɗaya, wandda acikin awa ɗayarnan ba ƙaramin a takure Jawaad ya tsinci kansa ba, ana kammalawa ya nema izinin zuwa gida ya ɗan huta koda na awa uku ne. Babu wani jan zance aka bashi dama, dan yanayinsa ya nuna buƙatuwa sosai na san hutun..... *___________________________________* Tunda Gimba yay fakin motar a harabar gidan ya buɗe idanunsa da suka sake masa nauyi da ƙyar, ba tare da ya jira Gimba ya buɗe masa murfinba ya buɗe da kansa ya fice, rigar sanyinsa ce kawai a hannunsa sai bindiga da ƙaramar wayarsa da ya fita da ita kawai. A yanda ya shigo ya ga falon jiya yauma haka ya sameshi, yaja siririn tsaki yana haɗiye wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maƙoshi, zuciyarsa a matuƙar cinkushe ya ƙarasa sama inda nanne ɗakin barcinsa yake. Kallo ɗaya yayma falonsa ya ɗauke kai, dan hatta da kofin da ya sha shayi a daren jiya yana a inda ya barsa, sam shi baima san wace irin mace ya aura ba, ƙazama ko ballagaza?. Takaici bai nemi shake numfashinsa ba sai da ya ƙarasa haɗaɗɗen bedroom ɗinsa ya sauke dubansa a kan lafiyayyen gadonsa da har yanzu take kwance, ta wani ƙudundune cikin lallausan bargonsa tana shaƙar barci. Tuni idanunsa sun sake kaɗawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka sake fitowa raɗa-raɗa, yasan ko rantsuwa yay baza a bisa bashin kaffara ba akan Shuhudah batai sallar asuba ba. Bai sake kallon gadonba ya jefa rigar sanyin akan sofa tare da zube wayarsa da bindigar saman tabirin dake shakanin kujerar da gado. Duk da wani jiri-jiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa hakan bai hanashi nufar bayi ba dan ya samu ya watsa ruwa ko zai samo kan jikinsa...............✍🏻 _____________________________________ Shafi na biyu (2) ____________________________________ ............Motsin ruwan wankansa ne ya farkar da Shahudah, tunda ta yaye bargon da ga fuskarta nake tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali da ya halicci wannan ƙyaƙyƙyawar baiwa tasa. Lallai Shahudah ƙyaƙyƙyawace wadda zamu iya sakata a jerin farko na ƙyawawan mutane, gata fara tas tamkar wata aljana. Har lokacin bata yaye bargon da ga jikinta ba, kamar yanda alamu suka nuna bata da niyyar tashi ma. Kusan mintuna arba'in da shigarsa bayin sai gashi ya fito ɗaure da tawul ruwan sararin samaniya, yayinda ya rataya ƙarami fari a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge gefen kumatunsa. Shahuda da har yanzu take kwanci ta a hankali ta buɗe ƙyawawan idanunta ta sauke akansa, hakan yayi dai-dai da kai nasa duban gareta shima. Kuma tamke fuska yay yana kauda idonsa a kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata ce uffanba sai binsa da kallo da takeyi. Duk da Jawaad naji a jikinsa kallonsa takeyi bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror, murya can ƙasan maƙoshi yace, "Kinyi salla?". Ɓata fuska tayi tana kuma narketa alamar son yin shagwaɓa, "Haba bb, kamun laifi maimakon ka lallasheni da ban haƙuri saika wani faramin tambaya". Duk da ya jita sarai sai ya share tamkar bai jiba, ya cigaba da shafa mansa yana lullumshe ido saboda ciwon da har yanzu ya keyi, sauƙinsa ma ruwannan da ya sakarma kan ya ji daɗinsa sosai gaskiya. Ba ƙaramin ƙunar zuciya ta kama Shahudah ba jin Jawaad ya shareta, ta turo baki gaba tana yaye bargon da take ciki. Masha ALLAH na sake ambata ganin haɗaɗɗun kayan barcin da take sanye a ciki, sun mugun mannewa da farar fatarta, tare da zama ɗam jikin surarta tamkar dan ita aka halicci figigiyar rigar barcin da kaɗan ta gota mazaunanta, siririyace sai dai jikinta a murje yake alamar hutu, ba kowa ne zai ga Shahuda ya yarda ta haɗa jini da HAUSA FULANI ba, dan komai nata yafi kama da na masu jajayen kunnuwa..... Saurin janyeta yay da ga jikinsa jin ta rungumesa ta baya yana kuma ɓata fuska, a matuƙar harzuƙe ya juyo yana sanya jajayen idanunsa cikin fararen nata masu cikar gashi da gira baƙa wulik a sama. Sam bazata iya jurar kallon cikin idonsa ba, dan haka ta wani yi farr da nata cikin salo irin na manyan yara da ke taƙama da wayewa. Hanya kawai ya nuna mata ba tare da yace uffanba. Yanzu kam ranta yakai maƙura da haushin wulaƙancin Jawaad, dan haka ta yamutse fuska cikin tsiwa ta taka gaban gadon ta saka silifas ɗinta masu taushi ta nufi hanyar fita. Sai da ta kama hannun ƙofar ne ta tsinkayo Jarumar muryarsa na faɗin, "Saura idan kinje canma ki sake kwanciya kar kiyi sallar". Harara ta watsa ma bayansa da ya juya mata ta fice tana ƙunƙunin da ita tasan mi take faɗa. Bai sake bi ta kanta ba ya kammala abinda zaiyi a gaban madubin ya nufi Wadrobe ɗinsa ya saka boxer kawai ya fito falo. Kayan tea da ke ajiye saman D/table ya nufa, ya ɗauki kofi ya haɗa komai kafin yaje ga disfensa ya matso ruwan zafi dai-dai buƙatarsa. A haka ya koma bedroom ɗinsa yana juya cokali cikin kofin shayin da keta tururi. Zama yay bakin gadon yana shan shayin a hankali, ko zafinsa baya ma damuwa da shi. A da can sam baya shan shayi sosai, ya kan sha amma ba ko yaushe ba saboda baya cikin abinda ya damesa, amma tun bayan auren sa da Shahudah suka ƙulla abota da tea, a yanzu baya da abincin da ya bama muhimmanci a rayuwarsa irin shayi, tun yana sha akan dole harya fara zame masa jiki, inma bai sha ba sam baya jinsa dai-dai, a baki sunan kawai yana da matane, amma a aikace ita da hotiho babu banbanci, dan babu wani abu na matan kirki masu daraja da Shahudah ta iya, banda tsagwaron son jiki da son hutu babu abinda ta tara, a ɓangaren gyaran jiki dai kam gwana ce, dan ƴar gayuce ta gani kasheni, sai dai sam babu tarbiyya mai birgewa da akasan ƴaƴan musulmai da ita, komai nata kwaikwayone daga jinin yahudu da nasara, salla wannan sai yayi mata jan ido take yinta, daga lokacin da yay nisan kiwo kuwa a aikinsa baisan wace wainar take toyawa ba a ɓangaren bautar ALLAH.... A hankali ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana ajiye kofin hannunsa saman durowan gefen gadon, magani ya ciro a ciki ya sha kafin ya haye gadon da ke manne da ƙamshin turarensu ya kwanta yana jan bargon ya lulluɓe har kansa. Koda Shahuda ta koma ɗakinta sam bataji gargaɗin Jawaad ba akan tayi salla, sai ma gado da ta faɗa tana ƙunƙuni wai baza tayin ba, a haukanta da gajeren tunani tunda Jawaad ya ɓata mata rai to itama saita ƙuntata zuciyarsa da ƙinyin sallar da yace tayi, dan haka tai kwanciyarta barci ya sake kwasheta saboda sanyin garin na ruwa da aka maka a daren jiya. ALLAH ya ƙyauta to, saikace kabari ɗaya za'a saki da Jawaad ɗin Shahuda?🤔 kokuma shike bada sakamako idan anyi sallar🤦🏻‍♀️?, ALLAH ka rabamu da wayewa mara amfani⛹🏻‍♀️. ★★★★★★★ Ring ɗin wayarsa ne ya farkar da shi da ga nannauyan barcin da yay nisa a ciki, ya janye bargon da ga kansa da ƙyar tare da miƙa hannu saman dirowan gefen gadon ya ɗauki ƙaramar wayarsa da ke vibration. Ba tare da ya duba wanene ba ya ɗaga kawai ya saka a kunne yana sake maida idanunsa ya lumshe. Tsawon seconds arba'in yana sauraren mai maganar da ga can, kafin ya furta "Ok sir" cikin nutsatstsiyar muryarsa da ke gauraye da barci. Ƙarƙashin filon ya tura wayar yana sake juya kwanciyarsa hankali kwance, sai faman ɓata fuska yake na jin takaicin katse masa barci da akayi. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya ture bargon yana jan dogon tsaki, ƙaramin agogon dake gefen dirowan gadon ya kalla, ⏰11:29am, numfashi ya sauke a hankali dan sam baiyi tunanin barcin nasa yayi dogon zango haka ba, tashi yay ya sauka daga gadon gaba ɗaya. Sosai ƙyanƙyamin bayin nan yakeyi, dan yakai kusan kwana huɗu kenan babu wanki, tun randa Batool tazo bai sake ganin gyara ba saboda tsabagen lalacin matar gidan. A ɗarare yay abinda zaiyi ya fito ba tare da ya sake wanka ba, baƙar jallabiyarsa mai dogon hannu ya ɗauka ya zura kawai da silifas ya fice zuwa ƙasa. Sai sha ɗaya saura Shahudah ta tashi a sabon barcin da ta sake komawa, sai faman ɓata fuska take tamkar ance ta tashi dole ne, rigar barcinta ta zame tare da sakinta a tsakkiyar ɗakin tai tsaye tsirara da ga ita sai pant wanda shi da babu duk ɗaya, hankalinta kwance ko tunanin bayan jinsinta akwai na aljanu da ido baya ganinsu a ɗakin batai ba, a haka ta nufi bathroom. Tsawon lokaci ta ɗauka a ciki kafin ta fito ɗaure da wani mitsitsin tawul kalar ruwan hoda, shima tana zuwa gaban mirror ta sakeshi ƙasa, a haka ta shafa mai kafin ta buɗe Wadrobe ta ɗauki doguwar riga ɓaƙa ta saka, tare da naɗa ɗankwalin rigar ta ɗau abin salla ta shinfiɗa. 🤥tsantsar mamaki da al'ajab sun rufeni ganin sai yanzune Shahudah zatai sallar asuba, sha ɗaya da kusan ƙwata🤦🏻‍♀️. Ina nan zaune ganin ikon ALLAH harta idar da sallar tata a cikin ƙanƙanin lokacin da bazai gaza mintuna uku ba. Rigar ta sake cirewa ta ajiye, ta ɗauki tawul ɗinta ta sake ɗaurawa tare da jan stool ta zauna aka fara tsara ƙwalliya ta garari. Kai tsaye ɗakin Shahudah Jawaad ya shiga, juyowa tai ta ɗan kallesa ta ɗauke ido ita a dole fushi takeyi da shi. Shima sai da ya fara ƙarema ɗakin kallo kafin ya kai dubansa gareta, kallon kusan seconds goma yay mata sannan ya cigaba da takowa cikin ɗakin, jikin bangon da mirror yake ya jingina tare da harɗe ƙafafunsa waje guda ya tura duka hannunsa a aljihun jallabiyar. Tsayuwar tasa sai ya zam tamkar sun fuskanci junane shi da Shahudah, hakan yasa ta sake ƙwaɓe face ɗinta tana cigaba da zana kwalliyarta. Tsawon mintuna biyu suna a haka, babu wanda ya cema ɗan uwansa ci kanka, sai zuwa can Shahudah ta ɗago manyan idanunta da gashin ya sake jin maskara ya miƙe gazar-gazar fiye da da ta kallesa, "Nikam karka cinyeni dan ALLAH bb". Idanunsa ya janye a kanta yana sakin guntun murmushi da ya saka kumatunsa loɓawa, itama Shahudah sai tayi murmushin. "Breakfast fa?" yay maganar yana sake maido kallonsa gareta. Sosai ta sake zuba masa idanunta tana narke fuska, sai dai batace komaiba. Hannayensa ya zare daga aljihu ya maida a ƙirjinsa ya harɗe, "Yanzu nan Hudah kina ganin wannan rayuwar itace ta dace da matar aure ta hausa fulani? Wata bakwai kawai da aurenmu amma matsaloli sunzo sun mana ɗaurin goro a cikin gida, wanda duk kece sanadinsu, shin ke wai bazaki taɓa canjawa bane?!....." 'Ya ƙare maganar a tsawace'. Razana tayi matuƙa, dan haka ta zabura tana jan jikinta baya tare da waro manyan idanunta waje, "Wai ni bb ya kake so in maka ne? Kaifa nace a ɗakko kuku da wanda zaike mana gyara amma kace baka yarda ba, ta yaya kake tunanin zan iya aikin gyaran wannan ƙaton gidanne saboda ALLAH, kum...." Haɗiye sauran maganar tata tayi tana ƙunƙuni saboda wani ɗan iskan kallo da yake mata, wanda ta tabbata yafara harzuƙa, idan ko ta bari ya kai ƙarshe zai iya ɓarota a kujerar ya haɗa kanta da mirror. "Shahudah baki kai matsayin sakani yin abinda ban niyyaba, dan bazan taɓa kawo wani ƙaton banza gidana ba da sunan ma'aikaci, ki kama kanki kafin na raba shi da wuyanki a gidannan wlhy, stupid girl kawai". Ya ƙare maganar da juyawa zai fita. Cikin ƙunƙuni Shahudah ke faɗin, "Karka kawo ɗin, kata zama a gida tamkar tirken akuyiyin ƙauye kuwa, dan nikam ba ƴar wahala bace, kake wani cewa kamar ba matar hausa fulani ba, ALLAH ya rabani zama irinsu waɗannan kidahuman da basusan ko yanda zama su gyara jikinsu ba balle su san miye rayuwa, da ana canja yare ma da tuni na canja nawa anbar dangantani da wasu hausa fulani can mtsowww. 🤔tab, babbar magana, Shahudah anya kinada man kai kuwa? Matan hausawan ne bamusan abinda mukeba😨🤦🏻‍♀️? Rigiji gabji☹️. Sarai Jawaad yaji abinda Shahudah ta faɗa, amma sai ya fice ko waiwayota baiyiba, bedroom ɗinsa ya koma ransa duk a jagule, ya ɗau babbar wayarsa da ke a kashe ya kunna, wata Number ya lalubo tare da danna mata kira, bugu biyu aka ɗauka. Sama-sama sukai gaisuwa da wadda ya ambaci sunanta da Hibba, kafin yace, "Cikin yarannan wace a gida?". Bansan mi aka ce masa da ga canba, ya dai sake faɗin "turomin ita" kawai ya yanke wayar ya ajiye. Tsaki yaja yana jingina da fuskar gadon tare da lumshe idanunsa ya afka duniyar tunani............✍🏻 Page 3 ..........Zaman duniya da kayan cikinta buƙatar kowacce, amma waɗanda duniya ke buƙata da amfanuwa da kayan cikinta mutanene ƙalilan. A lokacin da wasu mutane ke bushasha da wani yanki na jin daɗin cikinta wasunsu kuka suke da kwankwaɗar ɗacin cikinta. Yayinda idanun wasu ya bushe da ga kwaranyar ruwa mai amsa sunan hawaye, a lokacinne ijiyar wasu ke ambaliyar zubarwa da buƙatar abin gogewa koda ace ruwan hawayen bazai dakata daga malala ba. Zuciyoyi duk iri ɗayane a suna, amma a aiyuka kowa da irin tasa. In dai zuciya zata kasance mabanbanta a ƙirazan mutane, to lallai dolene launin halayya da ɗabi'unsu ma ya banbanta. Sai dai wanda ya halicci duniyar da kayan cikinta, ya fika sanin miyasa ya banbanta ma'abota mu'amulantar ta da shawagi a cikinta harma da gudun zukatansu. Kamar yanda duk ilimin ɗan adam bai isa ƙayyade numfashin da ke fita daga huhunsa zuwa maƙogwaro ya fita ta hanci ba, to lallai babu mai ilimin ƙa'idance ko banbance yawan jinsin ƙabilu da mutanen dake danƙare da duniyar nan sai wanda ya halicceta. A lokacin da fankama da tinƙahonka ke kwarzanta abincin tukunyar gidanka, da zaka leƙa ta gidan wani sai kaga ta fita abin kallo da kayan alfarma masu armashi. Sai dai duk wannan ba shi bane tushen zancen, ba kuma shi bane abin dubi da hange ko burin riska, tsarin shine waiwaya can bayan bayanka ka hango waɗanda ko tukunyar ɗorawar basu da ita balle tunanin hura wutar da zata dafa musu. Wani tun haihuwarsa ALLAH ya azurta tushensa ko zuri'arsa da rahamar fitowa cikin gingimemen hasken da ko baka mallaki komai ba a duniya sai shi to lallai ya gama maka komai, domin ya baka abinda ya fi komai tsadar tsada a cikin alfarmarsa. Sai dai abin mamaki da al'ajabi sai ka samu mafi yawan masu wannan damar sunyi wasarere da ita tare da mata riƙon sakainar kashi suna hange da gudun kamo wasu al'adu da ke da alaƙa da kishiyar nasu. Zancen nawa a bayyane yake, sai dai fa fahimtarsa ba kowace kwanyace hasashenta zai kai canba, ba kuma toshewar basira ce zata kawo rashin fahimtar ba, sam ko kusa ba hakan bane, ɗunbin abin tarawa ne kawai kema ƙwaƙwalen jama'a yawa su gaza warware wani ƙullun igiyar a jikin gugar da takai kimanin dogon zamani ana cuɗanya da ita a rijiyar mai bakandamiyar alfarmar ruwa buƙatar kowa. Shi wancan dama ya samu, amma rashin fahimtar hanyar da yake jefa ƙafa ta sakashi gaza fahimtar akwai waninsa da ke da buƙatar koda kwatankwacin tasa damarce shima ya shigo a dama dashi. Gashi dai a cikin duniyar irinta wadda ke da damar a tafin hannu, ga kuma gangar jiki da fitar numfashi duk ALLAH ya haliccesa da ita shima, sai dai sam ba ƙofa ɗaya ya ke shiga da fita tsakaninsa da mai damar a cikin duniyar ba. Hakan yasa yake kallon tasa duniyar da ban a cikin duniya, ba dan baya ci ko sha ba kamar kai, hatta barci da kake domin hutu da dariyar farin ciki duk ALLAH shima ya azurtashi dasu, abin lurar shine kai duniyar rungumeta kayi tsam, itama ta tallafeka tare da sake cusaka jikinta kuna kwasar ɗumin juna saboda tsantsar buƙatarka da takeyi, Shiko waninka rakaɓe yake a jikinta tamkar hawainiyar da ke ɗauke da ciki ta ke jiran ranar haihuwa. Bara dai mu ajiye duk wani dogon zance mu tsunduma cikin labarin ko mai karatu zaifi fahimtar gonar audigar da nake masa nuni da ita mai ɗauke da buɗaɗɗiyar kaɗa da gwaiduwarta ta fashe sumfut a filin gona. Ni dai sunana *Bilkeesu* ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya. A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki. A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita. Sana'ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau'in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka. Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan haka zuwa yanzu mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa. Karku ɗauka ciranine ya kawomu garin har muka samu mafaka a wannan gidan haya mai kama da hotel, sam ba haka bane, mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance naka sassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kuke tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci?. Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba. Badan bani da ƙoƙaru bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum. A yanzu haka shekaruna sha takwas, amma har yanzu ss2 nake na makaranta, saboda matsalar komawa baya da naita fuskanta. Bani kaɗaice budurwa a gidanmu ba, a ƙalla zamu iya kaiwa fin mu ashirin kuma duk yawancin sa'oin juna, sai dai kowa da gwaninsa (inji masayin taliya ƴar murji😆), dan kuwa kowaccenmu tanada abokiyar mu'amularta daga cikin ƴammatan gidan, dan haka muka kasance kusan nau'i uku zuwa huɗu a ɗaukar rayuwa. A kwai sahun farko da suke ɗaukar kansu masu matuƙar aji da jin sunfi kowa hakama iyayensu sunfi na kowa arziƙi a gidan, a group ɗin sun tasarma su kusan bakwai, sai sahu na biyu da ajinsu bai kai waɗancan sahun farkon su sakasu a cikinsu ba, sai suma sukaja tasu zugar da zama abokan takarar waɗancan ta fuskar sumafa ba bayaba, sai kaso na uku da suka ɗau rayuwar saisa-saisa saboda ƙoƙari na tsawatarwar iyaye da gudun jefa kai a halaka, sai mu da ke karshe da muka kasance ba kowan kowa ba, hasalima mune akema kallon ƙarshen ƙasƙantattu marasa gata da galihu, ta kowacce fuska bamu da wani amfani sai tarbiyyar iyaye da ke jagorantar dukkan haƙurunmu da ɗaukar duniyar wajen maƙalewa kafin wa'adin barinta ya cika. Ba wani yawane da muba gayyar ƙarshen, dan kuwa da ga ni sai Firdausi ne da take ƙawata jallin jal a gidan, dan kuwa matsayin iyayenmu kusan ɗayane, itama mahaifanta suna fama da ciwon talauci tamkar mu, sai dai su sunma ɗan ɗaramu, dan babanta nada sana'ar saida kayan miya itama anan ƙofar gidan, shinema ke taimakawa babana a tashi sana'ar idan anzo saya da idan za'a danƙa masa kuɗi, kuma ita iyayenta duk lafiyayyune, sai yazam har kwancen kayan sawa itace mai bani, dan saka sabbin kaya a gareni sai sallah, suma kala ɗaya ne da ƙyar ake ƙulla kuɗinsu saboda ƙoƙarin iyayena nason ganin sun sharemin hawaye a cikin tsarata. Haka rayuwa ta zaɓar mana, badan wanda ya haliccemu baya sonmu ba, badan mun kasance masu saɓa masa ba, sai dan kawai haka ya tsara son ganin bayinsa a cikin duniyarsa dan yazama ilimi ga jahilai, izna ga masu wauta, rahama ga masu haƙuri, sake girmama mulkin ALLAH ga masu mulki. Gidanmu wani irin gidane da bansan yanda zan fassara muku shi ku fahimta ba sam, dan duk wani mugun hali ya ƙunsa saboda jama'ar daya tara masu kalar hali iri-iri a zukata. A duk lokacin da kake barci to ka tabbata sai ka samu wanda ke maka munshari a gidan, hakama akwai masu kallo da ido ɗaya, akwai masu gani ta ƙeya kuma. Tsabar iya annamimancin gidanmu ko faɗa ba'a yawan yi, kasan kuwa duk zaman da ya haɗa jama'a irin na gidanmu kaga ba'a faɗa to lallai ka jinjina wannan zaman kuwa. Ɗakinmu shine a can ƙarshe sai na su firdausi, hakan yasa baban firdausi samun damar yimana ƙaramar baca ta katako a ɗan lungun da ke gaban ɗakinmu wanda dalilin ginin banɗakuna ya fita. wannan bacar ce ta zama ɗakinmu ni da firdausi, dan ɗakunan gidan duk falle ɗai-ɗai ne, hakan yasa mafi yawan ƴammatan gidan daina kwana a ciki sai dai suje maƙwafta kwana. Rana mafi muni da razani a rayuwata itace ranar da muka wayi gari mahaifiyata babu lafiya, tun a daren jiya amai da gudawa suka saukar mata, kafin safiya tayi ligif, lokacin da ɗaya daga cikin mazan gidanmu mai tuƙin a daidaita ke ƙoƙarin sakata a napep ɗin dan zuwa asibiti sai rai yayi halinsa. Tashin hankali ba'a sa maka rana, dan kuwa yanda na tsinci kaina a cikima ai ɓata lokacine, har aka kai gawar mahaifiyata makwancinta ban san ina hankalina ya ke ba, sai bayan komai ya dai-daita har rana ta doshi faɗuwa sannan na dawo hayyacina. Abinda ya daɗa harmutsa dukkan tunanina shine babu kowanne ɗan uwan mahaifana da ya zauna dan karɓar gaisuwa a gidan, tun bayan binneta da aka dawo sukai ɗan zaman awoyi uku zuwa huɗu sai kowa ya kama gabansa. Nayi kukan da yafi na rasuwar innata a wannan lokacin kam, hakama babana da ruɗani ya maidashi kurman gaske bai uhm baya uh-uhm, dama gashi babu ijiyar gani. Matan gidanmu sun ɗan tausaya mana a tsakanin nan, dan kuwa kullum sai an samu mai bamu abinci ni da baba, dama maman firdausi kullum saita bamu na rana da dare, dan mafi yawan jama'ar gidan basa abincin safe, kowa sai dai yaje ya siyo a waje, sai ƙalilan a ciki dake ɗanyi shima da risho a ɗaki gudun idanun masu ƙwalama. Bayan kwanaki uku na makokin mahaifiyata akai addu'ar uku, sai aranar ne naga wasu tsiraru a cikin dangin iyayena, harma sukaimin gaisuwa. Ko da aka kammala addu'a sai kowa ya sake kama gabansa aka barni da ga ni sai babana kawai. Rayuwa ta cigaba da shurawa duk muna fama da tabon rashin innata ni da mahaifina, dukda baba yana dannewa da aro jarumtar rashin inna a gabana har ya lallasheni, nasan shima yana a cikin wani hali. A haka kwanaki sukaita shuɗewa har inna ta cika watanni uku da rasuwa. Zuwa yanzu naɗan saki jikina, amma ba da kowa ba, dan dama can ni miskilace kamar yanda ake jifana da zagi a cikin gidanmu, (akance sai miskilancin tsiya tamkar ƴar wani da wata), idan naji hakan iyakata murmushi kawai, dan bani da abin faɗa. Kamar kullum na dawo da ga makaranta a gajiye yauma, dan dukda tazarar nisan da ke tsakanin makarantarmu da gidanmu kullum a ƙafa nake zuwa na dawo, idan kinga na hau napep sai dai idan baba ko innata sun sami rarar kuɗi a cikin sana'arsu, to shine za'a ɗan bani talatin na break, maimakon naci wani abun sai na maƙale kuɗin idan an tashi na hau napep, shima da ƙyar ake ɗakkoni, wataranma bana samun maimun alfarmar sai dai na taho a ƙafar dai dana saba. To yanzu ma tun bayan rasuwar innata sai komai ya sake taɓarbarewa, dan baba baya da isashshiyar lafiya, wataranma ko ƙofar gidan bai iya fita wajen sana'ar tasa sai baban firdausi ya takura masa. Tunda na shawo kwanar anguwarmu gabana ya ƙara ƙarfin faɗuwa, dama tun daren jiya nakejin girata ta haggu na rawa, ci gaba nai da takowa tamkar kazar da ke shirin sakin ƙwai zunɓutu a ƙasa, matasan anguwarmu da dattijai zagaye da wani abu a ƙofar gidanmu, ga jini faca-faca a gefen titin wajen, dan gidan mu nakan titine sosai, kuma titin irin wanda ake yawan bi ne saboda shine babban titin anguwar. Yanda wasu da ga mutanen suka zubomin idanune ya sakani sake komawa jan ƙafa, dan kallon yafi kama da na wadda ake tausaya mawa. Yayinda na iso daf da su sai naga an fara darewa ana bani hanya, mamaki ya sake kamani, dan kuwa basu tsaremin hanyar da zan shiga gidaba, suna da ga gefen jikin gidanne. Dubana nakai ga ƴar sirɗaɗen hanyar da suka ƙirkira sai karaf idanuna akan mahaifina kwance jikin jini. A hankali jina ya fara nisa, duhu ya mamaye ganina sai ga duniya na juyamin, kafin na gama fahimtar mike faruwa har na rasa komai da ga motsin jama'ar duniya, na koma wata duniya can daban mai nisan zango da ta mutane. Yau ake yinta gobe sai labari ne ya sake riskar rayuwata a karo na biyu, dan kuwa na sake rasa mahaifina da lilin bigesa da mai motar akori kura yayi yayinda yake ƙoƙarin tsallaka titi. Kowa ya shaida baiga fitowar baba ba balle ƙoƙarin ƙetara titin da ya yi, ƙararsa kawai sukaji tare da mugun jan birki da mai akori-kuran yayi. Hakan yasa kowa yayo kan baba, ganin hankalin mutane ya raja'a kansa ne ya bama mai akori-kuran ƙofar samun hanyar guduwa, baiko sakkoba balle ya ga halin da ya jefa mahaifina ciki da ni tilon ƴarsa. Bakin babana ni yaketa ambata har aka ɗakkosa aka maido gaban gidan, faɗi yake a kira masa Bilkisu, a kira masa ɗiyarsa dan ALLAH, sai dai abin tausayi da yankewar rabon sake haɗuwa numfashinsa na tsayawa ina isowa ƙofar gidan. A wannan karon nafi tsintar kaina a ruɗani fiyema da rasuwar innata, banbancin da aka samu zaman wasu a cikin dangin mahaifina tare dani har akai sadakar uku. Randa akai sadakar uku kowa ya kuma kama gabansa, babu wanda yay min tayin na bisa, sai abubuwan ɗakin masu amfani da suka tsince duk suka tafi dasu, aka barni da ga ni sai tarkacen matattun tsunmokaran iyayena da ƙwanƙwatsatstsun kwanikan cin abincinmu...............✍🏻 Page 4 Gidan Jawaad Jawaad Abdul-Azez Yuseef ɗane da ga. zuri'ar Alhaji Yuseef Tafida. Alhaji Yusif talaka ne mai rufin asirin ALLAH, domin kuwa manomine kuma makiyayi, duk da a birni yake rayuwarsa da iyalansa to dukkan wani sabgoginsa na ƙauyensu, acan yake nomansa da kiwo, hakan yasa hankalinsa rabuwa biyu, harma zamansa a ƙauyensu ya so ya rinjayi zaman birnin. Matan Alhaji Yusif uku ne cif, kuma kowacce a cikinsu ALLAH ya azurtata da haihuwa, matarsa ta farko hajiya Atika yaranta shida huɗu duk maza biyu mata, sai ta biyu badiyya yaranta huɗu itama, mata uku namiji ɗaya, sai amarya Rahina ke da uku maza biyu mace ɗaya. Zamu iya cewa a gidan Alhaji Yusif tafida akwai tsaftataccen kishi irin na matan da da suka san kansu, dan kuwa baka taɓa jinsu suna wata hayaniya a tsakaninsu, sannan kowa na da ikon tsawatarwa ɗan kowa idan yaga yayi ba dai-dai ba, so rayuwar gidan dai akwai abubuwan birgewa. Tabbas Alhaji Yusif nason ƙauyensa sosai, sannan shi mutumne mai bautawa zuminci iya iyawa, sam bashi da matsala, amma yanada zuciya idan aka kaisa maƙura. Ganin rayuwarsa ta ƙauye tana neman rinjayar zaman maraya sai ya yanke shawarar ɗauke ɗaya a cikin iyalansa ya maida ta can ƙauyen. Amma yana tara matan nasa ya ambata musu wannan batu duk sai sukai tsale suka dire akan sam bazama ta saɓu ba, kowacce tace babu yanda za'ai ta koma rayuwar ƙauye bayan ALLAH ya tsamota da ga can. Abin ya matuƙar ɗaure kan Alhaji Yusif, musamman idan yay dubi da cewar duka fa daga ƙauyen ya aurosu ya kawo birnin, dan shi bai taɓa sha'awar yin aure a bariki ba, duka matansa daga gida ya aurosu, amma gashi yanzu ƙiri da muzu sunce bazasu koma zaman tushensu ba. Da farko sai ya kwantar da murya ya shiga lallashinsu da nuna musu muhimmancin komawar wata a cikinsu can ɗin, dan babu daɗi da girmansa ace bashi da mata a inda rayuwarsa tafi ƙarfi, kullum sai dai ake kawo masa abinci da ga gidan matan ƙannensa ko ƙannensa mata. Ai sai tamkarma ya tunzurasu ne, dan kowacce sai ta sake sama akan bijirewar farko, ya kaɗa su danbu da taliya suka nuna sam bazasu yi mubayi'a ba. Ganin bazasu lanƙwasu cikin sauƙiba ya rufe ido ruf ya banbamesu da bala'i tamkar zai cinye naman jikinsu ɗanye, duk da sun razana da fusatarsa babu wadda taji zata iya sadaukarwa ta koma ƙauye da zama. Shima takalminsa ya buga yay gaba ba tare da ya sake bi ta kansu ba. Tsawon lokaci bai sake tado musu zancenba, duk sun saki jiki akan yabar ma zancen kenan, sai gashi rana tsaka yazo musu da maganar ƙara aurensa, kuma zai auri ɗiyar maƙwafcinsu ne Alhaji Sunusi na Abba, yarinyar da ke yawan shigowa gidan matsayin ƙawar ƴaƴansu. Wannan lamari ya harmutsa dukkan lissafinsu da jinsu harma da ganinsu, shiko yay tsayuwar sojan badakkare a kansu kan cewar duk wadda tai masa hauka zata ƙarasa zaman turu ne a gidansu ba da igiyar aurenta ko guda ɗaya ba a kansa. Wannan shine dalilin nutsuwarsu dan dole, kowacce ta shanye bala'in da kecin ƙahon zuciyarta zuwa maƙwallato sukabi yarima akasha kiɗa dasu. Bayan an ɗaura aure kai tsaye ɗaukar amarya maryam akai zuwa ƙauyensu Alhaji Yusif. Duk da maryam a birni ta tashi taga iyayenta, annan aka haifeta har kawo girmanta, kusanma dukkan danginsu anan suke, hakan baisa ta bijire akan bazata koma rayuwar aure a ƙauyeba, sai tayi biyayya ga mahaifanta da kuma mijinta, ta zauna lafiya cikin ƙauyen tamkarma ta saba da rayuwa a cikinsa da can, ta saki jikinta da kowa danginsa da jama'ar gari, sannan tanama mijinta biyayya sau da ƙafa, ta tsaya tsayin daka wajen taimaka masa akan dukiyarsa da yake kiwo a kanta. Shekarar maryam ɗaya cif ta haife ɗanta namiji san kowa ƙin wanda ya rasa, bakin Alhaji Yusif har kunne dan murna, sai kace yanzune akai masa haihuwar fari, ba komai ya girmama murnar tasa ba sai biyayyar maryam a garesa da ƙyautata masan da takeyi, (kunsan zuciya nason mai ƙyautata mata). Sosai maryam ke ganin gata fiye da ta farko a kan wannan haihuwa wajen dangin Alhaji Yusif, dan kuwa hidima suketa mata da bajinta irinta mutanen karkara, tunda aka kawo maryam garin matan Alhaji Yusif suka ɗauke ƙafa da ga zuwa garin, dama ƴaƴansu ba zuwa sukeba sosai, amma wannan haihuwa yace musu tilasne su halarci taron suna daga su har yaransu. Badan sunso ba suka shirya ana gobe suna suka nufi ƙauye, kai tsaye kowacce gidansu ta nufa maimakon gidan mai jego, hakama yaran babu wanda ya nemi inda take, dan duk haushinta sukeji, musamman ma ƙawayenta su Atika. Itama dukda taji sunzo sai bata kulaba, dan danginta da suka cika gidan sun share mata dukkan kukanta, ga kulawa ta dangin miji da jama'ar gari. Washe gari yaro yaci suna Abdul-Aziz. Yanda hidimar suna ta gudana ma ɓata lokacine, amma Alhmdllh komai ya tafi cikin tsari, matan Alhaji Yusif basu shigo gidan sunanba sai da dare, koda sukazo sama-sama suka gaisa da dangin maryam suka ɗauki jariri suka ƙara gaba bayan sun ajiye kayan da suka kawo. ALLAH sarki maryam ita kunyarsu ma taji sosai, domin dai kallon iyayenta take musu, gashi yanzu ta aure musu miji harda rabon ɗa tsakani, ta baza ido taga ƙawayenta su Atika sun shigo amma sai taji tsitt, bayan kuma ance dukansu sukazo, dama bata saka ran ganin su Yaya Naseer da sauransu ba, tunda su mazane. Bayan suna kowa ya kama gabansa, Maryam ta cigaba da rainon ɗanta Abdul-Aziz da kulawa da mijinta. Rayuwa ta shuɗa, dan har maryam ta yaye Abdul-aziz, gashi yana tafiyarsa ko ina ga surutu ko akku ta shafa masa lafiya, yaron akwai wayo na haƙiƙa, gashi kullum yana cikin yara idonsa na sake buɗewa. A hankali duk wasu wahalhalu da yaran ƙauyen keyi Maryam bata hana Abdul-Aziz shigaba, kiwon dabbobin babansa ma shine ya koma bin yara daji yi, ko yabi zugar yara yo ciyawa, shine zuwa gona shuka ko kwaso amfani da kaka, yana girma wahalhalu na sake hawa kansa, gashi yanata zuwa makaranta anan cikin ƙauyen, dan da farko Alhaji Yusif yayi niyyar maida Abdul-Aziz birni ya samu ilimi tamkar ƴan uwansa amma sai Maryam ta hana, cikin hikima ta nuna masa ta fison Abdul ya tashi cikin wahalhalu irinna ƙauyen, hakan zai taimakawa rayuwarsa ta gobe harma wani ya amfani jibinsa. Badan ya soba ya barsa, itako ta cigaba da sakashi duk abinda ya dace, lokacin da Abdull yakai shekara goma sha biyar tsaf zai ja maka kunyar gona sama da ashirin a nome, faskare wannan yinsa yake, ragamar kiwon dabbobin gidan kam ya koma hannunsa baki ɗaya, duk safiya da an fito sallar asubahi yana makarantar allo, zuwa takwas suke tashi sai yazo yay shirin makarantar boko ya tafi, yana tasowa abinci kawai yakeci ya ɗebo ruwa ya zuzzuba a gidan ya ɓalle dabbobin gidan ya tafi jeji kiwo, bazai dawoba sai gab da magriba, da yayi wanka zaije sallah shi da babansa idan yana gari, idan yana birni wajen sauran matansa zaije shi kaɗai, baya dawowa sai tara da rabi, dan ana gama sallar isha'i yake wucewa makarantar allo again. Sai rayuwar Abdul-Aziz tazam sam babu hutu, har wasu na ganin maryam ta cika tsauri aka sa, gashi shi kaɗai ALLAH ya azurtata da samu, tun bayan haihuwarsa bata sake koda ɓari ba, baza'a ce bata damuba kam, amma ta danne ta cigaba da harkokinta hankali kwance, tasan dai haihuwa ta ALLAH ce, kuma shine ke badawa ga wanda yaso a lokacin da yaso, guda ɗayanma ta godama ALLAH, fatanta ALLAH ya rayasa ya zama amfananne ga al'ummar musulmai da addinin musulinci. Rayuwa haka ta cigaba da shillawa, Abdul-Aziz shine autan gidansu, dan suma matansa na birni babu wadda ta sake haihuwa, abinda zai birgeka shine zuwa wannan lokacin kuma duk sun saki jiki da maryam, komai ya wuce, yaransu kan ɗanje hutu wani lokacin wajenta, itama Abdul kanje wajensu dukda dai baya jimawa sabida ya saba da ayyukansa anan ƙauye, acewarsa canko sai dai aita yawon banza da barci da kallo bayan anci an ƙoshi, shiko sam bazai iya rayuwar lalaci ba. Sauran ƴan uwansa sukan masa kallon mahaukacin da baisan ciwon kansa ba, shiko ko a kwalar rigarsa, har zuciyarsa yake faɗar abinda ke ransa ne. Yayunsa mata kusan duk sunyi aure, mazanne dai babu wanda ya yunƙuro har yanzu, dukda kuwa a cikinsu akwai waɗanda suka isa auren. Lokacin da Abdul ya kammala secondary ne wasu a cikin yayunsa sukai aure, shiko Alhaji Yusif yay masa zancen dawowa birni dole saboda cigaba da karatu, sam bayason dawowar, idan ta shine abarsa yayta harkar nomansa da kiwo yafi birgesa, secondary ɗinma da yaya ya gamata, gashi yanzu ne mahaifinsu yafi bukatarsa saboda kulawa da harkokinsa na kiwo da noma, dan ƙarfinsa ya fara karewa girma ya fara kamashi, gashi sauran yayyen Abdul babu mai son zuwa ƙauyenma bare su taimaka masa, su kawai boko suka saka gaba da burin samun daula ta birgewa suci duniyarsu da allura, kasancewar mahaifinsu manomi makiyayi ma takaici yake basu, a ganinsu ajinsu ya wuce ubansu ya ƙare a harkar noma da kiwo, bayan kuma da itace duk suka samu tallafin karatun nasu. Sosai Abdull ke lallaɓa babansa akan baison zuwa makaranta, amma sam yaƙi saurarensa, yace dolene shima ya fita haƙƙinsa akan karatu tamkar sauran ƴan uwansa. Babu yanda Abdul ya iya dole yay biyayya, amma koda yatashi karatun sai ya karanci fanin kiwo da noma, dan aganinsa yafi fahimtarnan ɗin. Ƴan uwansa dariya abun yayta basu, dan aganinsa abunfa na haukar Abdull ya fara wuce makaɗi da rawa, yaro kamar tsatson ƴan rawar banjo. Sam baya kula zancensu, abinda yasa a gaba yakeyi, ga ƙwarin gwiwa yana sake samu da ga mahaifiyarsa da babansa. Kammala karatun Abdull babu jimawa ALLAH ya ɗauke Alhaji Yusif a duniya, wannan mutuwa ta girgiza dukkan ahalinsa musamman maryam da Abdull, abin ya taɓasu masuƙa, ansha ruguntsumi da tashin hankali har komai ya lafa zukata suka dawo hankalinsu bayan haƙuri da dangana da ya riskesu bisa rahamar UBANGIJI. Ranar da akai addu'ar arba'in a ranar aka ɗakko zancen raba gado, babu wanda yay jayayya wajen amincewa akai rabo, ita dai maryam bata da abin faɗa, dan ɗaya tilo ne gareta, ita babban tashin hankakinta ma ta yadda zata bar ƙauyen, dan tasan tilas zamanta ya ƙare kenan, gashi ta saba da kowa da komai na yankin. Ilai kuwa hakance ta faru, dan a yanda rabon gadon yazoma sai da gidan sukayi, dukda Abdul yace abasa zai saya da ɗan kuɗinsa kakarsa ta wajen uwa mahaifiyar maryam sukace zasu cika masa kuɗin, amma tsabar mugunta aka hanasu saya, maryam da ta lura zamansune ba'a sonyi saita lallaɓa Abdull akan yayi hakuri yabar zancen, duk inda ALLAH ya sake ƙaddara zamansu suyi haƙuri su karɓa kawai. Da wannan nasihar taci ƙarfinsa yayi biyayya, angama raba gado tsaf, ɗan filin gonar da Abdull ya samu ma bawata mai yawa bace, dan haka yay zuciya ya saida tasa, cikin yayyun nasa da aka haɗasu ya saye suna masa dariya akan ya gama wahala amma ya tashi babu tsuntsu babu tarko. Abdul ma yanada haƙuri, amma lallai akwai zuciyar masifa idan aka kai haƙurinsa tunga, wannan kalmomi da aka jefesa da sune suka bashi ƙwarin gwiwar mikewa da ƙafafunsa ya shiga fafutukar neman na kansa, yayinda maryam ta koma gidansu ta cigaba da rayuwarta, dukda kuwa ana takura mata da batun tayi aure tunda bata wuce yinsa ba. Abdul ya zage damtse wajen neman halalinsa, ya manta ma da wasu takardun kwalin shaidar gama karatu, kai gaba ɗaya yama manta kansa matsayin ɗan boko, dukda kuwa ga yayyensa sunaci da biro cikin sauƙi, 100% kuma shima ya goyi bayan mahaifiyarsa akan tayi aure, dan shine mutuncinta. Maryam bata musaba tai aure anan ma cikin anguwar kusa da gidansu, ta auri wani bawan ALLAH da matarsa ta rasu ta bar masa ƴaƴa har huɗu duk mata. Mama maryam mace ce da ta san kanta, ta kuma yarda ɗa na kowane, dan haka ta rungumi yaran a jikinta tamkar nata, ta kuma tsaya tsayin daka akan tarbiyyarsu musamman babbar da ta zama budurwa. Wannan dalilinne ya jefa ƙaunarta mai tsanani a zukatan yaran da mahaifinsu, harma da danginsa da na mahaifiyarsu. Shima sai ya sake jan Abdull a jikinsa tamkar shine ya haifesa, ya kuma sake nuna masa hanyoyin neman na kai masu sauƙi, dan shi ɗan kasuwane. A cikin amincewar UBANGIJI sai ƙauna mai ƙarfi ta shiga tsakanin Bilkisu ɗiyar mijin mama maryam da Abdul-Azez, duk da babu burin aure kusa a ransa sai gashi ta canja masa dukkan tunani da tsarinsa, ya rikice ya fara kafa manufofinsa a gareta, koda mahaifinta ya fahimta sai yayta murna, dan shikam dama halayyar Abdul na matuƙar birgesa, hakama mama maryam taji daɗi sosai, ga yaran akwai tarbiyya dama, sannan gasu ainahin ƙyawawa abin son kowa. Abdul sam bai ɗakko maganar auren bilkisu ba sai da yasamu ɗan abin dogara wajen riƙeta, dan shima dai kudin farko da ALLAH ya albarkacesa dasu a kasuwa saiya koma ƙauyensu ya sai gona ya tsunduma harkar noma tamkar mahaifinsa, ga kuma ɗan kasuwanci yanayi na sai da dabbobi da abincinsu anan cikin binni, ganin yanada abinda zai riƙeta gwargwadon iko sai kawai aka saka biki, haya ya kama na ɗakuna biyu a wani gida, su biyune kawai suke haya a gidan, dan haka komai sai ya zam musu da sauƙi, dan matan nasu duk masu hankaline, babu mai rawar kai aciki. A Ɓangaren ƴan uwansa kuwa kowanne yana fantamawa rayuwa, dan mafi yawansu duk da biro sukeci, matan kam ba laifi suna auren masu hali, arziƙin ƴan uwansa bai taɓa kwaɗarsa ba balle ya zame masa abin rikewa wajen yimusu hassada, harkar gabansa yake da iya gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa, bai dogara su bashiba, bai kuma zauna damuwa da sunfishi ba. Suko kullum cikin kallonsa mafi ƙasƙanci a cikinsu sukeyi, suna ganin ya tashi a ƙauye, sun fishi karatun boko, sun fishi komai na rayuwa, ko tarkacen kwancen kayansu ko wani abu suka tashi saisu bashi, shiko ya amsa cikin murna da girmamawa, bai taɓaji a ransa dan ƙaskanci sukai masa ba, yasa a ransa da yarda sun fisa ɗin da gaske. ALLAH mai alkairi, harkar nomansa nata bunƙasa, hakama sana'ar saida dabbobi da abincinsu, har lokacin bilkisu bata taɓa koda ɓatan wata ba, sai da suka shekara huɗu da aure ALLAH ya bata ciki, zo kaga murna wajen Mama Maryam da shi kansa uban gayyar da ƴan uwan bilkisu, ciki na kai wata baƙwai haihuwa tazo mata, aiko tasha wahala kafin ta haifi bakwaini biyu tagwaye, ɗaya ma baizo da raiba. Sun karɓa hannu biyu kuma sunyi murna da jin tausayin kansu na rasa ɗayan, sai dai kuma hukuncin ALLAH shima ɗayan bai kai labariba ya koma. Tun da ga nan Bilkisu bata ma sake samun cikiba tsawon lokaci. *Komai na da sanadi*. Wannan magana haka take, dan kuwa sanadin dam da akajema ƙauyen su Abdul ne ya zamar masa wani gagarumin alkairi, gonarsa ta kasance ɗaya da ga cikin gonakin da dam ɗin zai cinye, hakan yasa aka biyasu makudan kuɗaɗe gwamnati ta saya, shi kuma Abdul yana da ilimi, sai yazama shine ya tsayama jama'ar ƙauyen da duk abinda ya shafa har sai da aka biyasa haƙƙinsa, ya kuma basu shawarwarin su sake sayen wasu gonakin dan ga damar yin noman rani ya sake samuwa, ɗari bisa ɗari suka amince da shawararsa da ga manyansu har matasansu. Turawan da sukazo wannan aiki sai al'amuran Abdul-aziz suka matukar birgesu, hakan yasa suka jashi jikinsu ya zama abokin hirarsu duk da kuwa ba ko yausheba, dan shima yanada harkokinsa da yakeyi. Turawan ba cikin ƙauyen suke kwana ba, zuwa yamma suke tashi su koma cikin birni inda suke da masauki, hakan yasa suka sake jan ra'ayin Abdull har yasan mazauninsu, suma kuma sukasan nasa. Kafin kace mi shaƙuwa ta shiga tsakaninsu sosai, halayensa na neman nakai da dattako na sake birgesu, gashi dai ba wani babba ba can amma akwai halayyar manya, kafin su kammala aikin ƙaton dam ɗinnan da ko Abdul baisan iyakarsa ba shakuwarsu ta wuce misali, dan har bilkisu ya kaimasu suka gaisa, sannan wani lokacin yakan sakata tayi abinci ya kai misu, acewarsu suna koyon cin abincin arewacin Najeriya. Bayan kammala aikin nasune sukai haramar komawa, dukansu sun fuskanci halin kewa na tsantsar sabo, sai kowanne ya tsinci kansa a damuwa, lokacin da zasu tafi suka damƙa gidansu kacokan ga Abdull ƙyautar ALLAH, dama saya sukai dansu zauna harsu gama aikinsu, ganin sun kammala kuma sai suka bashi da zasu tafi, rasama mizai faɗa musu yayi dan susan yaji daɗi, dan gidane mai azabar ƙyau da tsari, kowa yasan dai yanda turawa suka amince da gyaran muhalli, to shima wannan ya ɗauki tsari na musamman, gashi a anguwar manyan mutane. Duk sai da ya ɗauki ƴan uwansa ya kaisu suka sanya albarka da matan babansa, hakama dangin mahaifinsa dake ƙauye, mota biyu suka ciko sukazo suka tayasa murna. Sannan ya maida iyalansa can, harda mama maryam yaso amma mijinta da ita kanta suka ƙi, aganinsu yaya zasuje suyima ƴaƴansu zaune dukda dai gidan babbane. Dole Abdul ya haƙura amma ya ɗauke ƙannen Bilkisu biyu da suka rage ya maida gabansu, dan ɗaya a cikinsu itama tayi aure. Shekara ɗaya kacal da faruwar hakan saiga turawannan sun dawo Najeriya, ashe zuwa sukai tafiya da Abdull, dan su dai yamusu har ƙasan zuciya, bayan ɗan kace nace da aka samu akan tafiyar tasa dai da ga karshe ALLAH ya amince su mama maryam suka barshi ya bi turawannan, sai dai yabar matarsa a nan gida Nageriya. Wannan tafiya itace ta sake canja komai da ga rayuwar Abdul-Aziz Yusif Tafida, cikin ƙankanin lokaci ya bunƙasa, dan kuwa acan ƙasar turawannan ashe sun jashine akan harkar noma da kiwo irin nasu, suka sake wayar masa da kai, shima ya sake wayar musu da kai akan nasa sanin da ALLAH yay masa, dama su kunsan komansu da tsari, tamkar kamfani nasu yake, sai suka dirasa matsayin babba mai kula da komai, a duk bayan wata uku yake zuwa gida Nageriya yay wata guda ya koma can ƙasar, sannan anan Najeriya ma ya kafa jijiyoyi musamman a ƙauyensu, dan kuwa ya tallafa ma matasan ƙauyen da magidanta akan noman da kiwo, harma ya kwashi wasu acikin matasan suma sunacan turai ɗin tare dashi. Rayuwa ta matukar sauyawa, duniya ta bama Abdul-Aziz babban filin fantamawa a cikinta, abin birgewa kuma yana amfani da damarsa sosai wajen gina kowansa, tamkar ƴan uwansa da abaya suke ganin sun fisa yanzu ya zamar musu runfa, dan kuwa dukkan dukiyarsa da ke Najeriya su ya ɗaura akanta, dukkan sirrinsa sun sanshi, duk abinda kaga bai sanar musuba to lallai sai dai sirrin da ya shafi matarsa ko mahaifiyarsa, wannan kam da ga shi sai su sai ALLAH, har zuwa yanzu kuma basu haihuba, kuma bai taɓa yunƙurin sake aure ba, hakama babu wanda yace masa ya sake auren ko za'a dace. Yana son matarsa sosai, dan haka bai taɓa nuna mata ya damu da rashin samun ƴayansu ba dukda yana kwaɗayin son ganin tsatsonsa a duniya. Ba a cikin ahalinsa kawai yake taimako ba, hatta da mutanen gari ta kowanne fanni amfanuwa suke da tagomashin arziƙinsa, ya zama bango abin jinginar kowa, sannan runfa mai lulluɓe zafin rana ga kowa, dukda hakan kuma bai isa zama mai ƙyautata zukatan kowa ba, dan ko UBANGIJI daya hakicci ɗan adam baya iya masa............✍🏻 Page 5 ...........A yanda Abdul-Aziz ke bautama al'umma da hidimarsa, sai ka ɗauka bai ma san ciwon dukiyarsa ba, kokuma a banza ya sameta ba da guminsa ya taraba. Abubuwa yake na bajinta ko tunanin kuɗin zasu iya ƙarewa bayayi, kafin kace kwabo sunansa ya zauna ɗam abakin mutane, ko yaro ƙarami ka ambatama sunan Alhaji Abdul-aziz tafida da gudu zai amsa maka harma yay maka sharhi gwargwadon fahimtarsa.               Rayuwa ta ci gaba da shurawa, yayinda wasu da ga cikin jama'a suka fara kafa dandalin kiranye ga Alhaji Abdul-aziz zuwa ga siyasa. Duk da yana jinsu, kuma yana ganinsu, sai ya maida kansa makaho kuma kurma akan batun, dan shi sam siyasa bata cikin tsarin tafiyarsa ko burinsa.        A na cikin wannan yanayinne ya fara ginin wasu katafaren gidajen gona guda biyu, amma a jihohi mabanbanta. Sai wani katafaren family house da zai haɗa dikkan ahalinsa waje guda, kuma kowa da ɓangarensa babu ruwanka da shiga sabgar gidan ɗan uwanka, Wannan aikinne ya kauda hankalinsa ga nacin jama'a na son ganinsa cikin siyasa.         Lamarin kuɗi sai mai su, kafin kace wani abu gidajen gona sun kammala, hakama gidansu, matasa da yawa harma da magidanta sun samu aikinyi a ciki, abubuwan alkairi harsun fara fitowa ta gidan, sannan suma sun koma sabon gidansu shi da duk sauran ƴan uwansa da iyalansu, mama maryam ce kawai taƙi tunda dai aure takeyi, sai Alhaji Abdul-aziz ya sayi gida kusa da su suma suka koma.             Duk yanda Alhaji Abdul-aziz ya so zamewa siyasa lamarin ya faskara, dan kuwa sosai ake masa bibiko da naci harta hannun aminan mahaifinsu da mama maryam kanta da mijinta.        Rana ɗaya suka ware wajen ritsashi, dan gangami akai masa na musamman tare da manyan mutanen da zuciyarsa kejin kunyar bijiremawa. Ba da son ransa ba dole dole ya amsa da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi.    Kowa ya amsa da murna da farinciki, tare da masa addu'oin na musamman wajen bashi nasarar jagorancin al'umma cikin sauƙi.        Ƙyawawan halayensa ne yasa shi kasancewa mai kishin jama'ar sa, har suma sukeji a ransu zasu iya sakar masa ragamar rayuwarsu ya mulka, babu ɓata lokaci rana tsaka ya afka siyasa bisa jagorancin abokai da matsawar mutanen gari da suke ganin ya cancanci zama jagoran nasu.      Koda ya tuntuɓi ƴan uwansa sai suka bashi goyon baya, dan duk ya riga ya gama siye zukatansu, zuwa yanzu ƙauna ta haƙiƙa suke masa da bashi kulawa wajen jansa jikinsu, (kowa yasan ziciya da son mai ƙyautata mata), dama kuma suna cikin waɗanda aka kama ƙafa dasu harya amince da batun.       Mama maryam ma sai ta bashi goyon baya sosai, tare da binsa da addu'ar alkairi, sai dai sam Bilkisu abin bai kwanta a ranta ba, amma babu yanda ta iya tabi ayarin ƴan binsa da addu'a tunda taga kowa ya bashi goyen baya, bai kamata ita ta zama ƴar ta wareba a cikinsu.             Shekarar da Abdul'aziz ya shiga siyasa a shekarar Bilkisu ta sake samun ciki a bazata, ai farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu bashi da kwatankwaci sam.       Bilkisu tanata rainon cikinta hankali kwance, ga kulawa tana samu ga kowa, watanta tara cif da wasu kwanaki ta haife ɗanta namiji sargaɗeɗe, inda ranar suna yaci sunansa *Jawaad*.             Jawaad ya tashi cikin kulawar dangi da mahaifa, gashi yaro abin san kowa a zuciya, dan danan ya fara wayo, gashi da jikin girma masha ALLAH, shekararsa ɗaya da rabi Bilkisu ta yayesa, dan yana tafiyarsa ko ina, ga haƙora reras a baki, sai dai kumafa baya magana, dan har Jawaad ya kai shekara biyu da wasu watanni baya magana, bayama yunkurin yinta, hakan yasa kowa yake ɗauka ko bebe ne, dan sun tabbatar yanaji da kunnensa, tunda idan akai masa magana yana fahimta, bakinsa ne dai baya furtawa. Tunma Bilkisu na damuwa harta daina ta maida komai hannun ALLAH, dan koda Alhaji Abdul-aziz yace zai kaisa asibiti itace ta hana, acewarta a jira aga zuwa wani lokaci dai.      Domin farin cikinta ne kawai ya so barin zancen sai dai kuma da ga baya saiya kasa hakan, dan abin na damunsa, ga dai Jawaad da wayau harma na tsiya, amma yaro bai da maraba da dutse a fannin faɗin albarkacin baki. Kuma zama yay ya lallaɓa bilkisu akan kai Jawaad ɗin asibiti, da kyar ta yarda dai aka kaishi, sai gashi kuwa an gano yana da matsala ne a ƙasan harshensa da maƙoshinsa, nan akai masa aiki yay tsawon sati uku yana jiyya kafin ya warke su dawo gida. Ba'aja wani dogon lokaci ba Jawaad ya fara magana, zo kuga murna ga wannan ahali, kowa na sake miƙa godiyarsa ga ubangijin al'arshi buwayi gagara misali.          Babu daɗewa da samun lafiyar Jawaad, a cikin matan Alhaji Yusif ɗaya ta rasu, Wannan rasuwa ya mugun girgiza wannan ahali sosai, musamman ƴaƴanta.          Bayan wucewar komai na rasuwar jama'a suka takura ma Alhaji Abdull akan ya fito takarar shugabancin jihar, sam ki yayi, danshifa dama bai shiga siyasa dan yazama shugaba ba, ya shigane kawai dan ya zama jagora da zai tsaya kan masu mulkin su tallafi talakawa kawai, amma badan yay mulkiba.      Nanma dai caa aka sake masa, babu yanda ya iya sai ya amince kawai yabi ayarin ƴan takara.      Abin zai baku mamaki idan nace muku komai yimasa akeyi, duk da talakawa sunsan yanada kuɗin da zai iyama kansa komai haka suka tattalafa da kansu sukai komai, acewarsu ai sune sukace yayi, dan haka sune zasuyi masa komai.       Wannan lamari ya sake girgiza duniyarsa, dan yarasa miyasa jama'a suke masa irin wannan makahon soyayyar? Ni ko nace Alhaji Abdul ai masu iya magana kance (Nagari na kowa, mugu sai maishi).        Bayan kammala duk wani hatsaniya da ruguntsumi na kamfen akai zaɓe, tunma ba'ai nisa ba kowa ya fahimci Alhaji Abdul-aziza Yuseef ya bige abokin takararsa,  tunkan sakamako ya fito mutane har sun fara shagulgula, ana faɗa gari ya sake harmutsewa.      Shi Alhaji Abdul-aziz ma ana faɗan yaci kuka ya kamayi, dan haka kawai yaji zuciyarsa ta karye ya shiga share ƙwalla.       Lokacin Jawaad na jikinsa yana wasansa, sai ya tsirama mahaifin nasa ido yana kallo duk da baisan mike faruwa ba, murmushi Alhaji Abdull yayi ganin kallon kurilla da Jawaad ke masa, ya ja kumatunsa kaɗan yana faɗin “Haba ɗan sanda kallon fa na minene? Yau nauyi ya haye Abbanka mai girman gaske, kai min addu'a ALLAH ya bani ikon saukewa”.        Duk da Jawaad baisan ma'anar maganarba sai ya ƙyalkyale da dariya shima yana jan kumatun abbansa kamar yanda yay masa.      Murmushi Bilkisu da ke gefensu tayi kawai, dan batasan dalilin da yasa mijinta keson kiran ɗan nasu ɗaya tilo police ba, tun baima kai hakaba yake kiransa da suna JAY -P!, tunma bata fahimci ma'anar sunanba har dai ta tambayesa ya gaya mata.     Ko a lokacin batai masa jayayya ba sai fatan alkairi yazama ra'ayin Jawaad ɗin kenan idan ya girma shima.     Tun a lokacin ya fara amsa wayoyin taya murna har ma kansa ya nema fara ciwo.          Bayan abubuwan da suka biyo baya dai a ƙarshe aka rantsar dasu, Alhaji Abdul ya koma gidan gwamnati shi da iyalansa, sai dai su mama maryam basu bisuba, sunce zasu rayu anan gidan da ya saya musu.       Harkar mulki ta fara gudana, inda Alhaji Abdul yazoma duniyar ƴan siyasa da sabon salo mai ban mamaki, gaba ɗayan albashinsa ya sakashi a taskar gwamnati, an ware aiki na musamman za'ayi ma talakawa aiki da kuɗin, sannan ya dage tsayin daka wajen gyara jiharsa ta kowanne fanni, dandanan sunansa yay amsa kuwwa a ƙasar, komansa ya zama abin koyi da alfahari ga al'ummar da yake jagoranta, ya zama zakaran gwajin dafi sannan tauraro mai haskawa da zamaninsa.      Gashi sam bashi da girman kai, kowa nasane, babu ruwansa da wani banbancin jam'iyya ko yare, tsakaninsa da ALLAH yake aikinsa cikin ƙwarewa da jagorancin UBANGIJI.          Adadin shekaru na hawan farko suka cika ga duk waɗanda suke kan mulki, mai makon Alhaji Abdul-aziz ya koma sai jama'a suka nuna shugabancin ƙasar gaba ɗaya suke bukatar ya karɓa. Wannan lamari yaso gigitashi sosai. A fili ya nuna sam bazata yuwuba, amma ina jama'a sun tsaya kai da fata suna masa magiya da kai kukansu wajen ALLAH.      To duk abinda ALLAH ya hukunta sai ya kasance koda bawan da abin ya shafa bayaso, kana nakane ALLAH yana nashi, nashiko shine gaskiya.        ALLAH ya ƙaddara sai ya zama shugaban ƙasa, sai ga shi kuwa ya zama, dama wanda yake kai ya gamane gaba ɗaya.             Zuwa yanzu Jawaad ya girma, dan shekarunsa bakwai a duniya, yaro mai wayo da ƙyawawan ɗabi'u, kamar yanda ƴaƴan talakawa ke makarantar gwamnati sai ga Jawaad ma a ciki, dan mahaifinsa yace ita shima yayi, a ma ƙauye, to ɗansa ma can zaiyi babu tantama. Aiko hakance ta kasance, dan sai ga ɗan shugaban ƙasa a makarantar gwamnati, abin ya burge jama'a, tare da jan hankali ga sauran masu mulkin suma duk sukaita maida ƴaƴansu can.        A gefe kuwa Alhaji Abdul nata sake cusama Jawaad son aikin ɗan sanda, cikin amincin ALLAH kuwa sai gashi yayi tasiri a ran yaron, dan babu sunan da yake ƙauna a ransa kamar *JAY-P!* da Abbansa ke kiransa dashi, ma'ana *_(Jawaad Abdul-aziz Yuseef police)_*.       Ko kayan wasan Jawaad duk zaka samu suna kamanceceniya ne da kayan jami'an tsaro, abin ya riga ya shiga yaron jini da ɓargo.       Shekarar Alhaji Abdul-aziz ɗaya akan mulki ALLAH ya jarabcesa da ciwon da har ya kwanta, ashe hawan jinine bawan ALLAH, kwanansa uku kacal da wannan ciwo zuciyarsa ta buga yabar duniya😭.            Tashin hankali kenan wanda ba'a saka maka rana, wannan lamari harma bansan a yanda zan musaltashi masu karatu su fahimta ba, dan kuwa ƙasarce baki ɗaya ta harmutse tare da komai na cikinta, mutuwar Shugaban ƙasa Abdull-aziz ba batun iyalinsa kawai akeba, maganar al'umma kawai akeyi, waɗanda sukeji basu taɓa gamo da rashi mai taɓa zukata da aiyuka irin wannan ba.        Tunda wannan rasuwa ta gudana bilkisu ta rasa hankalinta, sam an kasa gane kanta, hauka take tuburan wanda ya kai ga har an rufeta a ɗaki ma.      Mama maryam tsohuwa mai tawakkali da hakuri, baka ganin hawaye saman fuskarta sai dai na zuci kawai.      Ƴan uwansa kam su kansu ka kalla abin tausayine, lamarin yay masifar ruɗasu, dan Abdul mai biyayyane a garesu tare da ƙyautata musu, suka tuna irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa da bajintar da yay musu a rayuwa sai suji hankalinsu ya kuma ƙololuwa a tashi, sunyi kuka harsun godema UBANGIJI.         ALLAH sarki Jawaad, duk da bai kai hankalin da za'ace ya fahimci komaiba ya ɗanyi kukansa ganin kowama yanayi, musamman ma halin da mahaifiyarsa take ciki na hauka, sai dai zuwa wani lokaci kuma sai ya saki ransa, yakan dai zo ya tambayi mama maryam ina Abbansa? Yaushe ne zai dawo?.     Sam bata ɓoye masa, takan ce masa Abbansa ya tafi inda ba'a dawowa.      Wani lokacin yayi kuka, wani lokacin kuma yay zugum yana tunani kafin kuma ya saki ransa ya koma wasa cikin yara sa'oin sa.        A haka aka share wasu watanni, riƙon Jawaad ya dawo hannunsu mama maryam, bilkisu kuma ana cigaba da nema mata magani, dan bata ma ƙasar an kaita asibiti.      Haka rayuwar ta cigaba da shurawa, an maido Bilkisu gida, kamar taji sauƙi sai kuma abu ya dawo sabo, lokacin har Jawaad ya fara wayo, yana shekara ta goma sha huɗu, ajin secondary js2, ranar wata juma'a sai aka wayi gari Bilkisu ta bar gida, nema iya nema anshasa amma babu ita babu dalilinta, lamarin ya girgiza mama maryam har itama ya zama sanadi a gareta.       ALLAH yayma mama Maryam rasuwa sakamakon ɓatan bilkisun itama, wannan karon kam Jawaad yaji zafi sosai na rasuwar kakarsa da ɓatan mamansa, yayi kuka har abin ba'a cewa komai.     Ƙanwar bilkisu taso riƙon Jawaad ya dawo hannunta amma dangin mahaifinsa suma suka ƙi, sai Abba Naseer babban yayansu Alhaji Abdull na farko a gaba ɗaya gidan ya amshe shi ya koma hannunsa da zama.         *★★★★★★★*       Gata sosai Jawaad yake samu a wajen ahalinsa, dan a ganinsu  lokacin da zasu nuna jin daɗin ƙyautata musu da mahaifinsa yayi kenan, ɗan gatane ta kowanne fanni, riƙonsa ake tamkar yana gaban iyayensa, ƙilama idan sune bazasu masa wani gatanba irin haka.      Kamar yanda marigayi Alhaji Abdul ya ajiye burinsa akan Jawaad na zama ɗan sanda sai ALLAH ya amince masa yasamu cikar burinsa ta hanyar cusa son aikin ƴan sanda a zuciyar Jawaad, sosai ya ke son aikin ɗan sanda, wannan shine burinsa, mafarkinsa, kuma fatansa. Lokaci ƙanƙani ya samu cikar burinsa kodan tsatson da ya fito, da dattako irin na mahaifinsa da baza'a taɓa mantawa ba. *______________________________*         Shekaru sun shuɗa, komai ya sauya, Jawaad ya zama abinda yay fata, ya girma ya zama babban mutum kamilallen saurayi mai aji da tarin cikar kamala da kwarjini na haƙiƙa, komansa na nagartattun mutane ababen koyi da dubi, gaba ɗaya halayen mahaifinsa sun dawo jikinsa, sam bashi da damuwa sai ta aikinsa tare da ƙyautatama jama'a.     Mutum ne da bai damu da abinda bai shafesa ba ko ba'a sakashiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi, idan har bakai ne ka sakashi a lamuranka ba bazai taɓa shiga ba, bashi da son hayaniya, bai da girman kai, bai da wulaƙanci, sanan sam ba miskili bane ba. Abu ɗayane yake yawo a jinin Jawaad da ke saka jama'a dangantashi da waɗancan ɗabi'un na sama, shine rashin sabo, sam baisan sabo ba, kana takashi zai shata maka dogon layi, tsautsayi ko rawar kai ya saka ka ƙetara to lallai kun ƙulla kenan, kuma ka ɗaura kanka a danja mai haɗarin gaske. Babu ruwansa da kai wanene? Ko kuma ina ka fito? Miye matsayinka a garesa duk ba'abin kallonsa bane.      Jarumi ne ta fannin aiki da rayuwa, sannan gagararrene a duniyar tsagerun mutane, idan ya ɓalle sam bai san bari ba, duk abinda ya saka a gabansa sai ya cimma manufarsa yake yankan filin hutu.       Waɗannan ɗabi'un nasane suka jawo masa abokan tsama ta fannoni daban-daban, a cikin hukumarsu da wajenta, harma da tsagerun gari.  ★★★★               Shahuda ɗiya ce ga yayar marigayi Alhaji Abdull, wato Hajiya Humaira, tuni suna ƙasar Holland ita da mijinta, yaransu biyar suma, mata uku maza biyu, asalin sunan Shahuda *Sabeerah*, dan sunan mahaifiyar Abbansu aka saka mata, amma sai suke mata alkunya da suna Shahuda, ita ce ƴa ta huɗu a gidansu, ƴan gatane na haƙiƙa, waɗanda suka tashi da ɗabi'un turawa a cikin jininsu, sam basu san bari ba, dan bama a faɗa musu.           Hajiya Humaira tana son Jawaad, shiyyasa lokuta da dama take matsa masa zuwa ƙasar Holland wajensu ya ɗan huta. To annan fa Shahuda ta ga Jawaad ta mutu a kansa, tun yana basarwa dai har shima ya zurma, dan Shahuda ƙyaƙyƙyawace ta haƙiƙa, saboda mahaifinsu bafilatanine ɗan asali mai asalin madarar ƙyawu, duk cikin yaran kuma Shahuda tafi biyosa, ga jin daɗi da suke ciki, saboda inda suka taso, wannan ya haɗu ya maida Shahudah son kowa ƙin wanda ya rasa.       Jawaad yana son Shahudah, sai dai halayenta na bashi tsoro, dan kuwa dai irin yarannane da babu kwaɓa babu harara, idonsu ya buɗe da ƙazamar wayewa mai wahalar canja ra'ayi cikin sauƙi. Dan haka sai bai wani cika sake mata fuska ba, dama can yaran Family ɗin shakkarsa suke, dan bayan gaisuwa baya basu wata fuskar shiga huruminsa, sai dai fa yana ƙyautata musu akan bukatunsu, idan abu suke buƙata kafin su tambayi sauran yayyensu sun nema da ga wajensa, kuma inhar yana da halin yimusu yakan musu gwargwado.            Aikin da ya kai mahaifin su Shahudah ƙasar Holland ya ƙare, dan haka ya tattarosu suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, tunda suka dawo Shahuda ta dawo nan Tafida Family house ɗin su Jawaad ta tare duk dan shi. Ba zamuce baya kulata ba, sake mata ne kawai bayayi, wannan kuma badan hulaƙanci yake mata haka ba, rashin sakin jiki da jama'a halinsa ne kowa ya san haka, ita kanta sanin hakanne ya sata bata damun kanta da lamarin nasa, burinta kawai ta mallakesa matsayin miji, dan badan Jawaad ba bazata taɓa dawowa zaman ƙasarba sam, duk abinda ya shafi afirika ɓata mata rai yakeyi, a haukarta bayan aurenta da Jawaad saita ja ra'ayinsa sunbar yankin afirika gaba ɗayanta sun koma turai da zama. (😂🤣Babbar magana shahudah).            *★★★★★★★★*     Hankalin Hajiya Humairah ya tashi ganin tunda suka dawo ƙasar Jawaad yaƙi yay maganar aurensa da Shahudah kusan shekara uku, hasalima yafi maida hankalinsa ga aikinsa fiye da komai, ga Shahudah kullum cikin damunsu take akan batun Jawaad.       Shiryawa hajiya humaira tayi ta nufi *Tafida family house* domin tattaunawa da ƴan uwanta akan batun auren, dama gashi lokacin meeting ɗinsu na family ya kusa. Koda takai kukanta akan zancen sai kowa ya bada goyon baya, aka kuma tuntuɓi Jawaad akan maganar.         Haushi abun ya bama Jawaad matuƙa, dan sam bai shirin wannan auren nan kusa ba, so yay sai ya maida Shahudah cikin hankalinta da aƙidar yankinta da addininta, amma sam an wani zo an masa titsiye. Cikin ƙuluwar haushi akan zancen yace suyi duk yanda ya dace kawai.           Wasunsu sun fahimci bai soba, amma sai suka watsar da fushin nasa aka hau shirin biki na ƴaƴan gata, dan dama babban burinsu suga yayi aure kamar sauran yaran gidan kodan su gujema zaginsu da jama'a keyi akan sunƙi sakashi yay aure.            Sam ƙin bama bikin muhimmanci Jawaad yayi, hasalima hankalinsa na kan aikinsa, komai sai iyayensa keyi, sai da Shahudah ta sakashi gaba da kuka sannan ne yaɗan maido hankalinsa shima ba duka ba.      Haka dai dangi sukaita lallaɓata akan ta manta da lamarinsa tunda kowa yasan halinsa ayi auren kawai, idan ta shiga zai bata kulawa insha ALLAH.       Son da take masane ya sata yarda da shawarwarinsu akai biki lafiya aka tashi, sai dai a hidimar bikinma ta mugun shaƙar baƙin ciki, dan ƙin zuwa yay taro ko guda ɗaya har dinner ɗin da suka shirya bayan ɗaurin aure ta garari ta nunawa a gidajen tv saboda tsabar haɗuwarta, sam baijeba, a ranarma tsabar iskancin Jawaad a wajen aiki ya kwana, a washe gari kuma yaƙi yarda ya hadu da kowa a gidan saboda tsiyar da ya tsula musu.         Shahuda kuma tace bazata tareba sai yazo ya bata haƙuri.      Nanma sharewa yay kamar baisan sunayiba, sai da Hajiya Ummah ƙanwar mama bilkisu mahaifiyarsa ta kirasa tai masa faɗa sannan yaje, mai makon ya bata haƙurin sai ma ya sake gaggasa mata magana, ya kuma ce inma bata tareba baida matsala da hakan.        Da yake su kaɗaine a ɗakin sai Shahudah ta ci kukanta ta share hawaye da burin sai ta rama amma a gidansa, ga sauran ƴan uwa kuwa sai ta nuna musu ai ya lallasheta ne itako tanata masa shagwaɓa (😂😝).        Kowa ya yarda da batubta, dan an tabbatar Jawaad nason Shahudah, halinsa na nuna ko in kula da abu ne yake sakashi ɓoyewa, amma yanda ma yake ɗan kulata fiye da sauran yaran gidan zai tabbatar maka da yana sonta.        Daga ƙarshe dai sai amarya ta tare a nan gidan sashin Alhaji Abdull mahaifin Jawaad, dama tun bayan tashinsu babu wanda ya shiga sashen, yanzu kam sai Jawaad yay masa gyara mai burgewa aka saka masa amaryarsa anan.       A farkon amarci abin nasu ɗoɗa-ɗoɗa, amma son jiki da shegen ɗaukar dala babu gammo na ɗabi'un Shahudah ne ya zamarma auren nasu matsalolin da baibayi da sukai ma zaman nasu ƙullin goro. Tunda gashi har Jawaad na complain a kan auren watanni bakwai kacal🤦🏻‍♀️..........✍🏻 Page 6 ..........A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take, yau ɗinkace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka. Rayuwa mataki biyu ce, kowacce ka zaɓama kanka zaka isa zuwa makomarta, saɓanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurɓatacciya.        A yau dai ga ni a matsayin marainiya, wadda babu ɗumin duka mahaifa guda biyu, sannan babu bangon jingina daga tsatson zuminci ko guda ɗaya. Rayuwata ta cigaba da tafiya a hannun mutanen kirki ahalin fiddausi, sun zamemin uwa da uba bayan ƙasa ta rufe idanun nawa, yanzu sune ci na sune shana da dukkan buƙatun rayuwa da aljihunsu sai iya ɗauka.      Zuciyata na kewar iyayena, amma jarumtata na ɓoye hakan a koda yaushe, haƙuri kuma ya zamemin sandar jagora yayin tafiya ba tare da na lalubi hanya ba saboda makantar zuci.     Tabbas rayuwar gidanmu ta canjamin ta kowanne ɓangare, dan a lokacin da iyayena na raye akanji shakkar min wani abun, amma yanzu kam ƙiri-ƙiri wasu kan nuna ƙyamata ko hantara ta ma kai tsaye, idanun maman firdausi ne kawai kan hana wasu cin zarafina koda da harara ne, amma da zaran babu ita a tsakar gidan to kare ma ya fini daraja.         Matsala ta farko dana fara cin karo da ita a gidan mai ƙona zuciya da barin tabon da ba'a mantawa shine zuwan mai gidan Alhaji lado naira, koda iyayena suka rasu bana tunanin Alhaji lado yazo gidan gaisuwa sam, amma rana tsaka sai gashi danƙyas-danƙyas yazo koramin bayanin na kwashe kayana daga ɗakinmu zai zuba ƴan haya.           Cikin ƙarfin hali da dogaro da kuɗin hayarmu na shekarar basuyi ko rabi ba na shiga kora masa bayani akan ai da sauran lokacin tashinmu.       Alhaji Lado ya bankamin harara tare da watsamin yatsun hannunsa biyar cif alamar zagi (daƙuwa) “Kinci uwarki, kujimin lalatacciyar yarinya, yo ko yau kuka biya tunda wanda yay biyan ya tafi barzahu ai kuɗinku sunyi isfaya (expire) kuma, to dan shelen uwarki ma😱, gidan tsohonki ko nawa da har zaki zauna jamin sharaɗi. Maza tashi kiyo waje da komai tafe nake da mai fenti, ki zauna wannan bacar har kuɗin su kare, dan itama zaki fara biyan kuɗin hayane tunda yanzu ƙofar ɗakin wasune”.      Kasare nai ina kallonsa tamkar wata wawuya ko sokuwa, wasu da ga jama'ar gidan ko dariya suketa tuntsurawa, ƙalilanne basu ji daɗin lamarin ba, amma babu wanda yace ma Alhaji lado baiyi dai-dai ba, dan sunajin tsoron ya shuka musu shika-shikan rashin arziƙinsa suma, kaɗanma da ga aikinsa yace kaima ka tashi ka bashi ɗakinsa. Baka da yanda zakai dashi kuma dolenka ka tashi, inba hakaba ya saka yaransa subi tsakkiyar rana ko duhun dare su naɗa maka na jaki🤦🏻‍♀️.......       Tsawar da ya dakamin ce ta sakani zabura na miƙe tsaye, ya nunamin ƙofar ɗakinmu yana haɗe fuska tamkar kashin ƙato na farar safiya.     Jikina na ɓari na nufin ɗakin, dan fuskar Alhaji lado tafi baƙin kashin shanu barazana idan ya murkite ta, ina shiga itama firdausi na shigowa, itace ta taimaka min wajen haɗe kayan muka ƙuƙƙulle ina sharar ƙwalla, sauƙina ɗaya ma kayan bawani uban yawane da suba, marasa amfanin ciki kuma sunfi masu amfanin yawa.       Bayan mun gama haɗesu ta taimaka min muka fiddosu zuwa cikin bacar da muke kwana, wadda kayan suka mamaye kusan rabinta, dan dama bawani girman azo agani bane da ita.      Alhaji Lado bai kuma bi takaina ba sai ma yaransa da suka shiga suka fara fente ɗakin da fenti mai ƙyau da ya bama kowa mamaki, dan duk ɗakunan gidan da farar ƙasa aka shafesu  maimakon fenti🤦🏻‍♀.             Da daddare munacin abinci a ɗakin su Firdausi innarsu ke bani haƙurin abinda ya faru da rana, dan ɗazun bata da sukunin nuna tausayina suma ta shafesu, shiyyasa sukai gum da ga ita har baba.      Murmushi nai mai ciwo ina faɗin, “Babu komai inna, ALLAHN da ya bashi muma bai manta da muba ai”.     “Hakane Bilkisu” inna ta faɗa tana murmushi, ta dafa kafaɗa ta tana ƙara nuna min muhimmancin haƙuri da amfaninsa.     Naji daɗin bayaninta, dan naƙara samun ƙwarin gwiwar ɗaura ɗammarar zama jaruma akan kaina. ★★★★★★        Faruwar hakan da kwanaki biyu kacal waɗanda zasu zauna a ɗakin suka tare.       Abinda ya tada hankalin dukkan jama'ar gidan, shine wanda zai tare a ɗakin da muka zauna.      Kusan sha biyun rana saiga ƙattai suna shigowa da kaya cikin gidan, waɗanda kallo ɗaya zakai musu ka fahimci addu'a kawai rayuwarsu take buƙata. Sune suka saka komai a ɗakin suka gyarashi tsaf, duk da bamu shigaba munsan dolene ya haɗu, dan kayan da akaita shiga dasu babu ma mai kwatankwacinsu a cikin gidanmu.      Mun daɗe bamu da wutar nefa a gidanmu, amma sai gashi anzo a ranar an gyara, washe gari kuma sai ga masu gyaran fanfo tunda farar safiya.      Irinmu da bamusan wanene zai tare a ɗakinba dai mamaki ya matuƙar kamamu, burinmu muga wanene zai zauna a ɗakin kawai.        Da yamma gan da magriba mun dawo islamiyya mukaci karo da baƙon lamarin da sam ada babu kwatankwacinsa a gidanmu. Kana kusanto gidan kunnenka zai fara jiyo maka sautin kiɗa da ke tashi da ƙarar Janareto (Genretor).      Kallon juna mukai ni da firdausi, dan munsan dai babu wani shagali da akeyi a gidan, koma anayi ba'a taɓa kalar wannanba.       Badai muce komaiba muka shigo da sallama a bakunanmu. Fetal tsakar gidan yake tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, gidanmu da idan ka shigo da yamma zaka ɗauka biki muke sai gashi tsitt, idanunmu suka sauka akan matasan samari da adadinsu zai kai goma sha uku acan jikin ɗakinmu da muka tashi, wanda bacar da muke kwana ni da firdausi take kallonsa, Mutum ɗaya ne zaune a kujera kawai yana zuƙar sigari, sauran kuma duk suna saman tabarna babba da aka shinfiɗa, wasu karta sukeyi, wasu kuwa zaune suke suna kallon masu kartar, sai ɗaya dake matsama na zaune saman kujerar ƙafa tamkar wani sarki.         Kallon juna muka sake yi ni da firdausi, yayinda suma matasan samarin suka zubo mana idanu su duka.       Gyaran murya da na kan kujerar yayne ya saka dukkan samarin saurin nutsuwa kowa yana sunkuyar da kai.        Baice uffanba shikam, sai zuba mana idanu da yay yana ƙare mana kallo da ga sama har ƙasa duk da sanye muke cikin hijjabai har kusan ƙasa.      Firdausi ce tai ƙarfin halin kama hannuna muka cigaba da takawa dogon tsakar gidan muna dosar inda samarin suke, dan ɗakin su firdausi shine jikin nami dama can, sannan bacarmu a tsakanin ƙofar su firdausi da ɗakinmu na da inda samarn suke yanzu take, hakan yasa samarin suke zaune har ƙofar bacarmu da gaban ɗakin iyayen firdausi.         Duk da munga a yanayin da suke da bana mutanen kirkiba, ga kuma kiɗan dake tashi da bamu da tabbacin zasujimu, hakan bai hanamu gaishesu ba. A mamakinmu sai mukaji suna amsawa kuwa, wanda ke kan kujerarne kawai bai amsaba, kuma har yanzu idanunsa na kanmu.       Wanda ke zaune saman ƙofar su firdausi ne ya matsa mana fahimtar da yay kamar nan zamu shiga, cikin sassarfa muka faɗa ɗakin kuwa da hanzarinmu ko sallama babu.       Maman firdausi dake zaune ta miƙe zumbur tana nufomu, hannunmu ta kama zuwa tabarma jikinta har rawa yake.     Mamaki ya sake kamamu, mun buɗe baki zamuyi magana tai azamar mana nuni da muyi shiru. Shirun kuwa mukayi muna cigaba da binta da kallo.          Haka mukai kwannan yau babu wani sikuni ga jama'ar gidan, kowa ya maƙure a ɗakinsa yana tsoron fitowa, mu kanmu yau a ɗaki ɗaya muka kwana da iyayen firdausi, baba ya hanamu zuwa bacarmu. MAFARIN MATSALA          Baƙon dai da ya tare a ɗakin da na taso tun ƙuruciya na ganni a ciki matsayin namu, ɗan Alhaji Lado Naira mai suna Jazuli (Jazuuuga) ne ya tare.       Jazuli ko nace Jazuuuga ɗane na huɗu ga Alhaji lado, shine namiji da aka fara haifa masa a gidansa, yana matuƙar ƙaunar yaron tun yana ƙaraminsa, hakanne yasa ya tashi a sangarce, sam Jazuuuga bayaji tun bai kai girma ba, tun yana secondary sukul ya haɗa dabarsa, yana da yara masu take masa baya da haɗarinsu ya sa ake matuƙar tsoronsa, duk yanda kuke tunanin takadaranci irinna Jazuli abin ya wuce gaban nan, bayan ya kammala sakandire dinne kuma baban nasa ya ƙarama sheɗancin nasa armashi ta hanyar fiddashi karatu can kudancin ƙasar, acewarsa zaifi samun ilimi acan.        Karku tunanin ilimin Jazuli ya nema koda yaje can ɗin, sam yama manta karatune ya kaishi, ya shige cikin manyan marasa jin magana yay kane-kane yana ɗaukar nasa karatun acan, tsawon shekara biyar iya abinda ya ƙaro ilimi a kansa kenan, idonsa ya matuƙar sake bushewa, ya zama jan wuya na sosai.       Abinda ya maido Jazuuuga gida kuwa kashe oga kwata-kwata na ƙungiyarsu da yay ne, hakanne ya sakashi gudowa ya dawo gida dan yasan dai idan yazo nan ya tsira.      Duk da hankalin Alhaji Lado ya tashi akan halin da ɗansa ya sake ƙwarewa a kai hakan baisa ya daina masa gata ba, saima ya ninka, a cewarsa ai hakanne zaisa ya shiryu.     Ɓarin kuɗin da Alhaji Lado kema Jazuli ne ya bashi damar jan ra'ayin yara takadarai irinsa, wasuma abun nasu ƙaramine, amma saiya horar dasu matsayin sojojinsa, ya haɗa ƙungiya mai matuƙar haɗari da barazana.       Akwai dalilin da yasa Jazuuga ya dawo gidan hayar na mahaifimsa, dukda gidansu kuwa yaci uban wannan sau fiye da goma, ga kayan alatu da morewar rayuwa a cikinsa, amma saboda son samun cikar burinsa shine ya cema mahaifinsa nan yakeson zama, babu ɓata lokaci kuma Alhaji Lado ya zo ya tada Bilkisu da ga ɗakinsa aka gyarama Jazuuuga............✍ Page 7 JAWAAD ............Cikin ƙunar zuciya da ɗacin da ya keji akan halayyar Shahudah yay shirin fita a gaggauce domin komawa Office. Bai bawani ɓata lokaci ba ya fito cikin shigar ƙananun kaya sai zabga ƙamshi yakeyi.         Shahudah na a falon kwance cikin kujera, ga kiɗa mai taushi ya na tashi ta cikin sifikun da aka ƙawata falon dasu, sanye take cikin wando da riga masu azabar ƙyau kalar ruwan hoda, kasancewar kayan robane sunyi mugun bin jikinta tamkar da fatarta aka haliccesu, wandon iyakarsa gwiwa, sai rigar da bata rufe mata ko cibiya ba, dan ƙyau tayi ƙyau sosai, dolene ka kalleta ka sake kallo.      Gaban ɗayan imaninta nakan waya ɗinta da take cheating, gefe ɗaya tana sauraren waƙa.         Har Jawaad ya gama sakkowa bata sani ba, sai da mayen ƙamshin turarensa ya bugi hancinta ne ta ɗan lumshe ido tana zuƙarsa kafin ta buɗe ta yunƙura ta tashi zaune, ƙyawawan fararen idanunta a kansa.          Shima idanun nasa na kanta, dan kwalliyar tata ta masa ƙyau, sai ya ji kaso mafi yawa na haushinta ya ragu a zuciyarsa, sauran cake ɗin da taci ta rage da kofin da ta sha tea ya kalla ya kauda kansa, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana sake haɗe fuska.          Murmushi Shahudah da ke kallonsa tayi, dan sam ita bata da riƙo, dama ko faɗa sukai zai ta shareta, itako mintuna kaɗan ta manta sai kuma an sake wani.     Yanzu ma dai hakan ita harta huce, hakanne ya sata tasowa ta shige jikinsa tana magana cikin shagwaɓa.          “Oh My BB kayi ƙyau sosai”.        Shiru yay mata, bai kuma rungumetanba shi.        hakan yasa ta ɗago tana kallon fuskarsa, ta kai lallausan hannunta tana shafa fuskar tana murmushi, “BB kamin murmushi mana”. ‘Ta ƙare maganar da sumbatar laɓɓansa’.         Duk da saƙonta ya shigesa hakan bai hanashi ture hannunta ba daga fuskarsa yana ƙoƙarin janyeta a jikinsa, amma sai ta ƙankamesa tana bubbuga ƙafa cikin shagwaɓa.           Iska ya ɗan huro da ga bakinsa, a daƙile yace, “Wai mikikeyi haka kamar wata tata Hudah? Ki bari karkimin Squeezing kaya”.           “Sai ka sake fuskanka to” ‘ta sake faɗa a raunane’.        Kansa ya girgiza kaɗan yana riƙota sosai jikinsa, hakan ya saka Shahudah ɗago fuskarta cike da annuri ta kallesa, shima kallonta yake cikin ido yana kuma narke idanunsa dake ƙara tsundumata a ƙaunarsa.        “Idan kinaso ki sameni yanda kike buƙata Hudah ki canja kamar yanda nima nake buƙata”.       Yay maganar a hankali tare da sauke laɓɓansa akan nata da keta walƙiyar janbaki, ya sumbata.      Kafin ta samu zarrar magana ya cireta a jikinsa ya nufi hanyar fita yana saka baƙin Eyeglasess ɗinsa a ido ba tare da ya sake koda kallonta ba.          Murmushi Shahudah tayi tana wani juya idanu, tabbas tana ƙaunar Jawaad fiye da hasashen mai tunani, dan shine namiji da ta fara so a rayuwarta, so kuma na haƙiƙa mai cike da tsagwaran sadaukarwa, kuma tana fatan ƙare rayuwarta da ƙaunarsa. Matsala ɗaya da ke tsakaninsu shine banbancin ra'ayi, Jawaad ɗan gayune mai aji da cikar haiba, duk yanda kake tunanin haɗuwarsa ya zarta nan, amma tana mamakin yanda kansa yake a tukunya game da rayuwa irinta manyan yara, ta ɗan taɓe bakinta tana komawa cikin kujera ta zauna, tasan canjawarta ta koma ra'ayinsa abune mai matuƙar wahala da iyawarsa a gareta zaiyi wuya, su dai tafi a hakan kowa da ra'ayinsa zaifi basu zaman lafiya, kan ya matsa sai ta canja ɗin dai-dai da buƙatarsa. ★★★★★★          Ya isa Office ɗinsa da ya ƙawatu da kayan more rayuwa, sai ƙamshi mai daɗine ke tashi a ciki, ya zauna cikin kujera yana mai miƙa hannunsa domin karɓar takardun hannun wanda suka shigo tare. Shafin farko da ya buɗe ya maida ya rufe yana ɗago razanannun idanunsa, “Ina na farkon?”      Ya faɗa cikin karsashi.           Cikin ɗan ruɗewa da tambayar bazata Aminu ya shiga kame-kame, “S...o...so...sorry sir!, dama Sir Qaseem ne ya karɓa, sai yace na kawo maka waɗannan”.       Gira ɗaya Jawaad ya ɗage sama, ya janye idanunsa da ke neman fara canja launi ba tare da ya tankama Aminu ba, cikin nuna halin ko in kula ya mai da hankalinsa ga Computer ɗin da ke saman desk ɗin gabansa.      Tsawon wasu mintuna da basu gaza biyar ba Aminu na tsaye, babu abinda jikinsa keyi sai tsuma, zufa ta hudo dukkan ƙofar gashin da ke jikinsa.     Jawaad dake aikinsa ya kallesa ta wutsiyar ido yana faɗin, “Tsayuwar ka zaɓa ko komawa dasu, idan ka karɓo waɗancan ka haɗa ka kawo min?”.        Sosai tsantsar firgici ya kuma bayyana a fuskar Aminu, ya sharce gumin da ya tsatstsafo masa a goshi tare da gyara tsaiwa zaiyi magana.......       Wani mugun kallo Jawaad dake ƙoƙarin miƙewa ya watsa masa, ba tare da yace uffanba ya zagayeshi ya fice da ga ma office ɗin gaba ɗaya.         Da tsantsar sassarfa ya biyo bayan Jawaad da ko kallonsa baima sake yiba.              Mutanensa biyar na amana suka take masa baya zuwa Office ɗin boss ɗinsu, yayinda Aminu ya bi hanyar da zata sadashi ga ubangidansa Qaseem Ali.            Yardar dake gareshi ga manyansa sam ta hana masa shamaki da neman izinin shiga ofisoshinsu, kansa tsaye yake shiga ba tare da jiran iso ba. Sai da yay masa sarawar girmamawa tamkar yanda al'adar jami'an tsaro take, kafin ya zauna a ɗaya da ga kujerun gaban ƙaton tabirin.            “Jay!”. “yes sir”.       “Ko kasan maganar sace Alhaji kokino tana neman  shigo da shugaba ƙasa a ciki”.       Cikin rashin fahimta Jawaad yace, “Sir! Kamar ya kenan?”.        Shiru ogan yayi na wasu sakwanni, kafin ya ɗago kansa daga wayar da yake dannawa ya maida kallonsa ga Jawaad, wayar ya miƙa masa yana faɗin, “Ɗazun  nai magana da shugaban ƙasa kai tsaye babu shamaki kowa a tsakaninmu”.      Idanu sosai Jawaad ya zaro waje, “Sir, miya ce?”. ‘Jawaad yay maganar a hankali, mai nuna alamar tsorata’.          Kaɗan Sir Ahamad barewa ya buga tebirin gabansu yana huro iskar bakinsa, ya miƙe tsaye tare da maida dukkanin hannayensa baya ya goya, sai da yay taku biyu zuwa uku kafin ya juyo ga Jawaad, “Jay! Adadin lokaci, lokaci shugaban ƙasa ya bamu na gaggauta samo Alhaji Sadi kokino, abinda ya bani mamaki annan yanda ya tsaurara, mika fahimta?”.        Jawaad dake bin ogansa da kallo kamar ya samu magiji ya sauke numfashi, tare da taɓe bakinsa yana murza yatsun hannunsa da ke bada ƙarar ɗas-ɗas a hankali, zuwa kusan sakon goma sha biyar sai kuma yaɗan zabura, cikin ƙanƙance idanu mai nuni da na tuno, yace, “Sir  sai naga kamar yana tunanin ana zarginsa da hannu a ciki....”      “Exactly my dear!, nima wannan shine tunanina, Jay kana da ƙwaƙwalwa, shiyyasa a komaina nake sonka a gaba” ‘Sir Ahmad ya ƙare maganar yana komawa a kujerarsa ya zauna’.       Jawaad dake murmushin jin daɗin yabon da ogan nasu yay masa, ya sauke numfashi yana gyara zama, “Sir inada shawara”        Sir Ahmad dake kallonsa yace, “ita mukafi buƙata ai ayanzu Jay”.       Jawaad ya lumshe idanunsa tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana jinjina kansa, “Zan turo maka a rubuce Sir”.          “Okey babu damuwa Jay, yaya maganar zaɓin haɗa runduna?”.        “Sir zanje na zauna dasu Asim yanzu insha ALLAH, zuwa yamma zamu aiko da jadawalin sunayensu”.      “Okey, amm......” Maganar Sir Ahmad ta kakare dalilin Knocking ƙofa da akayi, haɗiye maganarsa yayi ya bada izinin shigowa........ _____________________________________                 BILKEESU _____________________________________               Sakamakon tashi da hayaniyar yaran gidanmu a kowacce safiya, sai yau muka tashi da hayaƙin sigari a gidanmu.        Gashi rashin samun isashen barci ya saka mafi yawancinmu makara sallar asubahi. Hakanne ya kawo go slow ɗin shiga banɗaki. A ɗarare kowa ke komai saboda dokar rashin yawan motsi da yaran Jazuuuga suka kafa mana, a cewarsu yana barcin safe, duk wanda yay ƙwaƙwƙwaran motsin da ya tashi to lallai sai yaji a jikinsa, kuma komai tsufarsa basu ɗaga masa ƙafa.          Hakanne yasa mafi yawan mazan gidanmu ficewa da ga gidan da wuri ba tare da ko wanka sunyi ba, wasu kuma suka ɗauki kayan wankan zuwa gidan wanka.       Mukan dama maman firdausi ta mana dabara, wani tsohon bokitin ƙarfenta da hannun ya ɓalle tuni ta koma saka kayan tarkace a ciki ta ɗakko mana, a ciki mukai alwalarmu, bayan mun kammala muka fita muka zubda ruwan. Hakama da zamuyi wanka saita yi dabarar saka labule jikin murfin ƙofa da bango tace muyi cikin ƙatuwar bahonta. Muna kammalawa shirin makaranta nayi, babu zancen zaman karin kumallo, baba ya bani naira ɗari akan idan naje makaranta sai na karya, dan ita firdausi ta gama secondary tuni. Godiya nai masa na amsa na fito cikin fargabar waɗanan shaiɗanu da suka wargaza mana farin cikin gida a cikin kwana ɗaya kacal.        Sosai gabana ya faɗi, dan kuwa ina fitowa da Jazuuga na fara tozali, yana gaban fanfo tsaye, daga shi sai gajeren wando, hannunsa riƙe da brush alamar baki zai wanke, sai yaronsa ɗaya a gefensa riƙe da kofin ruwa.      Nai ƙasa da kaina, yayinda nakeji har lokacin shi nasa idanun na yawo a jikina. Tamkar munafuka naɗan risina kaɗan ina faɗin “ina kwana”.     Ban jira amsarsa ba nai ƙoƙarin wucesu.        “K zonan!” Naji an faɗa cikin wata sautin murya mai ban tsoro, sosai ƙirjina ya shiga sama da ƙasa, na rimtse idanu ina karanto *Hasbinallahu wa ni'imal wakil.*         “K dan ubanki kurma ce?!!”      Aka kuma faɗa cikin sautin da yafi na farko razanarwa.     Juyowa nai garesu, nazo gabansu na tsaya kaina a duƙe, dan bazan iya kallonsa haka babu rigaba, duk da kasancewar gidanmu gidan haya ne bamu saba ganin haka da ga mazan gidanba.      Shareni yay tsawon lokaci yana cigaba da brush ɗinsa, yayinda idonsa ke kaina ko ƙyaftawa bayayi, sai da ya gama tsaf ya raɓa ta gefena ya wuce yana faɗin, “biyoni”.       Ba ƙaramin firgici na tsinci kaina a ciki ba, dan marata wani ƙugi tayi kafin ta ɗaure tamau tamkar zata fashe. A cikin zuciyata kuwa ina tunanin na bisa nai masa mi? To. Ban gama samo amsar data dace da tambaya taba naji an fisgi hannuna, duk iya ƙoƙarin tirjewata da magiyar roƙonsa ya sakeni da nakeyi bai saurareni ba, sai da ya kaini har cikin ɗakin nasa sannan ya wurgar dani saman lallausan kafet ɗin da aka shinfiɗa yana huci.      “K kin sanni kuwa? Kinsan wanene ni? Dahar zaki ringa sakani maimaita miki magana!!”.       Jikina na rawa naja da baya dajan ɗuwawu ina girgiza masa kai, ga hawaye na gudu a fuskata tamkar fanfo, ya kuma zaromin manyan idanunsa jajaye, cikin nunani da ɗanyatsa tamkar zai tsokale idona yake faɗin, “Karki bari na tsaneki a gidannan, inba hakaba wlhy saina fatattaka rayuwarki, tashi maza ki gyaramin ɗakinnan”.       Cikin rawar jiki nake amsa masa da “to” na ajiye jakkar makarantana na fara gyara ɗakin, duk abinda nake yana tsaye a kaina tamkar wani dogari, niko sai hawaye nake zubarwa ba tare da samun zarrar gogewa ba.         Cikin mintuna ƙalilan na kammala gyaran ɗakin, dama ba wani datti yayba. Ba tare da na kallesa ba nake ƙoƙarin magana, duk da nasan shi ni yake kallo, “N...na..gama”.          “Saura shara” ya faɗa yana juyawa ya fita.      Tsintsiya na ɗauka nai sharar ina cigaba da kuka, ina gamawa na fito daga ɗakin, ALLAH ya soni ya shiga wanka, yaransa kuma wasu sun fita sai mutum uku kawai.         A gudu-gudu na fice da ga gidan, duk da naga mafi yawancin matan gidanmu na laɓe ta jikin labule suna kallona, wasu kuma ta Windown ɗakinsu.           A yau kam inhar nace na fahimci wani karatu a makaranta to nayi ƙarya, abinda ya faru tsakanina da baƙon gidanmu ya tsayamin a rai, babu abinda nake sai fargabar komawa gidan ma, malamin mu na Geography har buguna yayi akan yana darasi ina duniyar tunani. Dai-dai da yunwar cikina ban tuna da itaba har aka tashi, haka na nufo gida cike da tsoro dan bani da inda nake dashi da ya wuce gidan, kuma dama can ban saba da yawo ba, da an tashi daga makaranta gida nake nufa, shiyyasa yanzu ma naji can kawai nake buƙatar zuwa dukda kuwa tsoron dake cike fal raina................✍🏻 Page 8 ............Shigowata soron gidanmu yaɗan sakamin nutsuwa kaɗan, dan yau babu mahaukacin kiɗannan, sai da nai addu'a kafin na shiga da sanɗa tamkar wadda tazo yin sata.     Wata sassanyar ajiyar zuciya na kuma saukewa ganin ƙofarsa a rufe, sannan babu kowa a cikin irin yaransa, sai wasu a tsirarun matan gidanmu dake ƴan aiyuka a tsakar gidan.         Abinda ya bani mamaki yanda duk suka zubamin ido kamar wata baƙuwarsu, ni dai sannu nai musu na wuce ɗakin innar Firdausi kai tsaye.       Sannu Firdausi da inna dake zaune sukaimin, na amsa ina ƙirƙiro ƴar fara'a akan fuskata tare da bin tarin kayanmu da aka jibge gefe da kallo.     Kafinma na tambaya firdausi ta fara min bayani,      “Bilkeesu kayanmu ne baba yace mu kwaso da ga baca mu maido nan, dan babu dacewa zamanmu acanɗin saboda canjin da gidan ya samu”.        Murmushi nayi sosai wanda ya bayyana farin cikina yanzun kam, na zauna kusa da Firdausi ina faɗin, “Amma inna idan mun dawo nan baba fa?”.        “Karki damu kinji Bilkisu, babanku zai cigaba da kwana a bacar shi, kwananku acan babbar barazanace a garemu da mutuncinku, waɗannan yaran sam zukatansu basusan yaren tsoron ALLAH ba, abinda ransu keso kawai suke ji da gani a gaba ɗaya duniyarsu”.         “Hakane inna, babu abinda zance daku nidai a wannan duniyar, ALLAH ya yalwata rayuwarku da dukkan farin ciki har cikin aljanna, kun haska fitila a rayuwata lokacin da tsatona suka kashe domin hana kansu ganin hanyar da zasu riskeni, kuɗin masu zinariyar zuciyace mai haske fiye da ta dayimon (diamond), na.......”       Katseni inna tayi saboda kukan daya sarƙe harshena, ta jawoni jikinta tana bubbuga bayana alamar lallashi      “Ya isa haka bilkisu, kema ɗiyarmu ce tamkar Firdausi, ki daina kallonmu a waɗanda sukai miki alfarma, muna yin abinda ya dace muyine kinji”.        Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye.      Kusan tsawon mintuna uku tana lallashina, kafin na miƙe na cire Uniform ɗina naje naɗan watsa ruwa, bayan na dawone na iske Firdausi ta ajiye mana abinci.        Munacin abinci inna na zaune gefe tana ƙullin kayan sana'arta, Firdausi ta haɗiye abincin bakinta tana faɗin, “Bilki akwaifa matsala”.         “Tsayawa nai da ga ƙokarin kai abincin bakina ina kallota a tsorace”.         Inna ta harari Firdausi tana faɗin, “K Firdausi bana son ƙirƙire-ƙirkire fa, ya zaki ɓata mata zuciya? Wannan ai shirmene”.           “Kiyi haƙuri inna” Firdausi ta faɗa a sanyaye.      Kallon Inna nayi nima a raunane, “Inna dan ALLAH karki hana ta sanarmin, da inji a wani waje ai gara naji daga gareku, dama tunda na shigo naga matan gidannan namin wani kallon ƙurullah daya tsoratani”.      Murmushin takaici Inna tayi tana girgiza kanta, “Suma son zuciyane ke ɗawainiya dasu, dan abinda ya shafi kowane a gidane ai”.        “Dan ALLAH Inna miya faru?”.         “Karki tada hankalinki Bilkisu, baƙon gidanmu ne ya tara taro ɗazun bayan fitarki makaranta, ya kafa sharuɗa ne a gidan, wai bayason hayaniya, sannan kafin ya tashi barci a share tsakar gidannan a wanke tare da bayi, lokacin da zai fito kuma karyaga kowa sai.......”     Tai shiru cikin haɗiye wani takaici daya zame mata ƙululu a maƙoshi.     Cikin ƙaguwa da tsorata nace, “Inna sai me?”      Shiru tai ta kasa bani amsa, sai Firdausi dake sharar hawaye tace, “Wai sai mu ƴammatan gidan kawai, kece zaki ringa masa gyaran ɗaki, ni kuma kai masa ruwan wanka, su Aina'u ma kowa da aikinta, kinsan miya bani takaici Bilkisu?”.      Kaina na girgiza mata saboda hawayen da suka fara gudu a kumatuna. Ta goge nata itama tana cigaba da faɗin, “Bayan wannan dokokin harda sharaɗi mai barazana ga duk wanda yace zai bar gidannan ko zai sanarma hukuma, wai amma dukda wannan ruɗanin sai su Zee ke murna, harma suna ƙokarin yin kwarkwasa a gabansa”.       Kasa cewa komai nayi, sai tsame hannuna danai daga abincin da mukeci na koma gefe, hakama Inna da Firdausi kowa yay shiru yana cuɗawa da kwance abinda yakeji a ransa. ★★★★★★★         Kamar yanda Jazuga ya kafa dokoki a gidanmu haka kowa ke bi, ba komaine yasa hakanba sai tsoro, dan ba gidanmune kawai ke tsoron Jazuga ba, gaba ɗaya layinmu a tsorace suke dashi da yaransa, babu wani mai sukuni, dan yaran Jazuga sun addabi kowa a anguwar, gashi sai ƙara jan yara matasa ya keyi masu rauni cikin tawagarsa.      Abinda zai baka mamaki Police kansu tsoron shigowa anguwarmu sukeyi, ballema muyi tunanin zasu iya kamashi ko ƙwatar mana ƴanci daga mulkin mallakarsa.        Tun ina damuwa da bautar gyaran ɗakinsa har abin ya zame min jiki, ƙa'ida kullum sai na gyara sau uku, safe, rana, yamma.        Abinda kawai ke damun rayuwata dashi shine kallo, duk motsina a gidan idonsa na kaina inhar yana gida, duk da kuwa a koyaushe cikin Hijjab muke ni da Firdausi inhar zamu fito tsakar gida.      A cikin ƴammatan gidanmu kuwa wasu sai dai addu'a, dan kuwa sosai ake zargin Jazuga na lalata dasu yana basu kuɗi, hakanne ke ƙara tada hankalin iyayenmu.         Muna cikin wannan halin ne kuma saiga ɗan uwansu Firdausi wanda yake matsayin zaɓin iyayenta yazo daga can asalin garin su Firdausin, canjin daya tarar a gidanmu ne ya tayar masa da hankali, dan haka ya roƙi baba akan kawai a saka musu ranar aure.        Na taya Firdausi murna, sannan na taya kaina kuka, dan kuwa koba komai itakam ALLAH ya tsameta, niko da ko saurayi ban taɓa yibafa? Kunsan samarinma sunfi son ƴammatan masu ƙyale-ƙyale, niko bani cikin jerin masu shi, wadda suturar sakawa bata wadaceta ba ina taga kayan ƙyale-ƙyalen burge saurayi.         Saurayin Firdausi bai bar garinba sai da aka tsaida maganar aurensa da Firdausi wata biyu kacal..              Rayuwa a gidanmu ta cigaba da tafiya a ƙuntace, komai yabar mana daɗi saboda su Jazuuga, abu mafi ɗagamin hankali shine saka idonsa a kaina fiye da kowa a gidan, wani salon iskancima da ya ɓullo dashi shine danaje gyara masa ɗaki shima zai shigo ya zauna yana kallona kamar wata tv, narasa miyake kallo tare dani, ni dai sam baza'a sakani a jerin ƙyawawa ba, dan kuwa baƙace ni, bani da dogon hanci, bani da kayan ƙawa na ado da zasu fidda ƙyauna ga kowa. Shiyyasa lamarinsa ke ban mamaki da al'ajabi.           Babban abinda na riƙe shine addu'a, dan itace babban makamina a gareshi.      Yauma kamar kullum na tashi da wuri saboda zanje makaranta, dukkan abinda ya dace muyi ni da firdausi munyisa, hatta da aikinta da Jazuuga ya bata nakan tayata, saboda ni nawa saiya tashi barcinsa na ƙaddara da ko sallar asubahi bana tunanin yanayi.      Shirin makaranta nayi, na dawo ƙofar ɗakinmu na zauna tamkar yanda sauran ƴanmata gidan suka fito, wasu sunci kwalliyarsu saikace wasu matansa, sai binmu da kallon banza suke, dan a ganinsu bamukai matsayin haɗa kafaɗa dasuba.      Sukan bani dariya da mamaki, dan inda son samunanema wlhy ni namu aikinma duk ya haɗa ya basu.       Banfi mintuna goma da zamaba sai gashi ya fito, kamar yanda ya saba da ga shi sai gajeren wando, kallo ɗaya nai masa na duƙar da kaina.       Shiko inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina tamkar kullum.      Hazbilannahu wa ni'imalwakil na shiga ambatowa a kan laɓana, kamar yanda na fahimta a duk sanda nake karantata ko kallona yake saiya kauda idonsa sai naga yanzu ma yazo ta gabana ya gitta.       Inajin yanda su Aina ke masa gaisuwa cike da kwarkwasa da salo, tausayinsu ya kamani, dan kuwa ni nafi ɗaukarsu a jerin masu karancin tunani, da wannan takaicin na miƙe na nufi ɗakinsa, kamar yanda na saba a gaggauce na shiga gyarawa, dukda nasan bazai shigoba sai yay wanka, kafin lokacin kuma insha ALLAHU na gama nama fice abina zuwa majaranta.          Abinda na gani a ɗakin yauma ya tayarmin da hankali, dan haka na fice jiki na rawa ko shara banyiba, saboda tsantsar tsoro da firgici dake sake tasirantuwa a gareni game da tsagerancin Jazuga.      Ranarma dai ko'a makaranta daka ganni kasan babu nutsuwa a tare dani, haka dai aka tashi na nufo gida, ashe nabar baya da ƙura akan rashin shara da banma Jazuga ba.......😭 *____________________________________* *_JAWAAD_* *____________________________________*               Izinin shigowa aka bashi, ya turo ƙofar ya shigo, cikin risinawa irin ta girmamawa yake faɗin, “Sir! Ƴan jaridar nanne suka sake dawowa”.         Shiru Sir Ahmad barewa yay yana kallonsa na tsawon sakwanni, kafin ya sauke numfashi da masa alamar yaje.      Bayan fitarsa ya maida kallonsa ga Jawaad dake kallonsu ba tare da ya fahimci komai ba.         “Jay! Rayuwa na bani mamaki, bansan miyasa a duk lokacin da case irin wannan yazo ba  hankalin duniya yafi tashi akansa, shiyyasa talakawa har abadan bazasu daina ƙalubalantar manyan ƙasa ba komai gaskiyarsu”.        Murmushi Jawaad yayi irin na takaici, yaɗan lumshe ido yana faɗin, “Kuskuren daga mu yake Sir”.        “Jay miyasa kace haka?”.        Murmushi ya sakeyi mai ciwo, “Abun a bayyane yake muma mun sani sir, mubar wannan maganar kawai bata da muhimmanci a yanzu”.       Kai Sir Ahmad ya jinjina kawai yana cije baki, sai dai acan ƙasan ransa maganar Jawaad tai mugun sukarsa, ba komai ya sa hakanba sai sanin tsantsar gaskiyar Jawaad, amma wasu dalilai bazasu bar muryoyinsu ɗaguwa ba har suyi kururuwar da duniya zataji, ta gaskatasu cikin jerin jami'an tsaro masu gaskiya da son shinfiɗata..      Ya sauke numfashi mai zafi yana maida hankalinsa ga Jawaad, “Jay waɗanan ƴan jaridane, tun safe suke jera mana kira domin sonjin mi'ake ciki, inaga yakamata kaje garesu”.      “Okey Sir” Jawaad ya faɗa yana miƙewa, gaba ɗaya fuskarsa ta canja launi, sam babu ɗigon fara'a ko sauƙi a cikinta, sai tsumamman fushi mai gauraye da takaici irin mai zafafa zuciya.         Harya fice Sir Ahmad na binsa da kallo, yana ƙaunar yaron saboda nagartarsa, duk da mahaifinsa yay suna irin na zama wani shi sam baya alfahari da hakan, ko yaushe tunaninsa akan talaka yake, da ace yanda Jawaad keda zinariyar zuciya haka sauran jami'an tsaro suke da tuni ƙasar ta canja daga yanda take yanzu.                 Koda Jawaad ya fito sai ya samu Qaseem tare da ƴan Jarida, kallon ido cikin ido sukaima juna. Jawaad ya janye nasa yana sakin wani lallausan murmushin daya soki zuciyar Qaseem.              Office yay wucewarsa, ransa na susa akan shirmen Qaseem, baisan miyasa sam jininsu bai haɗuba.       Cikin kujera ya shige yana mai lumshe idanu da faɗawa duniyar dogon tunani.        Damuwa tai masa ɗaurin gori, saboda sabgogin aiki, ga matsalar gida na halayyar matarsa da taƙi ta zama irin kowacce mace, waje zafi, gidansa ƙunci, babu uwa ko uba da zasu fuskanci matsalarsa kai tsaye balle su taimakesa koda da shawarane.        Ina zaiga mahaifiyarsa? Shin tana raye ne kokuwa shiɗin marayane gaba ɗayansa? Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro a kumatunsa, bai damu daya sharesuba, haka ya barsu suna kwarara. (Haka yake dama, aduk lokacin daya tuno iyayensa yakanyi kukansa ya ƙoshi). Ya rabbi ka gafartama iyayenmu baki ɗaya😭🙏🏻.        Sai da yasha kukansa ya more sannan ya share hawayensa.         Nutsuwa yay ta musamman domin yin nazari akan wannan case da aka damƙa a hannunsa, dolene idan yanason aikinsa ya tafi dai-dai sai ya nemo abokansa, aminansa sun dawo kusa dashi, kuma insha ALLAH zaiyi komai da kula yanda bazai ƙara bada wata ƙofa da za'a farraƙasu ba koda na a awoyine.       Bai ɓata lokaci ba a take ya rubuta takardar neman izini tare da shawarar da yay alƙawarin badawa kamar yanda sukai da Sir Ahmad...............✍🏻 Page 9 ............Tun ƙarfe huɗu na maraice garin ya fara haɗa gagarumin hadari, wanda alamominsa suke nuna zai zubda ruwa mai yawa.         Duk da yana a office hakan bai hanashi fahimtar canjin da garin ke cikiba, miƙewa yay zuwa jikin window ɗin Office ɗin ya leƙa, tabbas hadarine mai ɗauke da alamomin iska kuma, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana huro iska a bakinsa, yana da sauran ayyuka, gashi bayason ruwannan ya samesa a waje.      Barin Window ɗin yayi ya koma gaban desk ɗinsa, wasu takardu ya haɗa waje ɗaya kafin ya fito da ga office da hanzarinsa irinna masu cikakkiyar lafiya.          Kai tsaye Office ɗin Sir Ahmad ya nufa, dan tun kusan mintuna goma baya ya aiko kiransa, bai fita bane saboda wani ɗan aiki da ya sakashi yakeson ƙarasawa ya kai masa gaba ɗaya.        Sallama yay a ƙofar Office ɗin kafin ya shiga, su uku ya iske a office ɗin, gaba ɗayansu kuma suna cikin manya-manyan ƴan sanda, gaisuwa yay irinta girmamawa a garesu, ya miƙama Sir Ahmad takardun yana faɗin, “Sir gasu na kammala, kayi haƙuri da lattin da nayi, na ƙarasa aikinne”.      “Babu damuwa Jay, dama tunanina ya bani hakan shiyyasa ban damuba, duk da kuwa jiranka muke”.          “Sorry Sir's” Jawaad ya faɗa yana maida kallonsa ga sauran mutane biyun dake zaune .          Ɗaya a cikinsu ne yay magana fuskarsa sam babu walwala, cikin tsare Jawaad da idanu yace, “Jawaad Abdul-aziz ko?”.           Cikin girmamawa Jawaad yace, “Yes Sir!”        Zama wancan ya gyara sosai yana fuskantar Jawaad, ya fara magana cikin dakiya da kuma tsuke fuska.          “Jawaad kai ɗan sandane, ɗan sandanma (SAS) ƙwazonka da ƙwarewar aiki ke ƙara maka ɗaukaka ga kowa dake a cikin hukumarnan, kamar yanda muka baka yarda a baya yanzunma munason ƙara baka a kan wannan aikin, dan tabbas inaji a jikina zaka iya, saboda kanada NAGARTA irin ta jami'an tsaro na ƙwarai, bamason wannan case ɗin ya wuce sati biyu, ya kake ganin zaka iya kuwa?”.         Jawaad dake tsaye a tsume fuska sam babu fara'a yay ajiyar zuciya yana sake tsuke fuskarsa, “Sir insha ALLAHU ina fatan hakan, sai dai bazan zama mai alƙawari akan abinda bani da ilimin sanin gaibu a kansa ba, ina dai muku albishir da koda ƙasa da kwanakin da aka banine zan iya yin hakan, alfarma ɗaya zuwa biyu nake nema a gareku, dan hakanne zai bani ƙwarin gwiwa akan nasarar da kuke fata daga gareni...”         “Wace alfarma ce wannan?”.       Ɗayan a cikin baƙin yay tambaya yana kallon Jawaad.            Gyara tsaiwa Jawaad yayi yana satar kallon Sir Ahmad, Sir Ahmad da shima ke kallonsa ya jinjina masa kai alamar ya faɗa.          Kai Jawaad yaɗan ɗaga masa, kafin ya maida hankalinsa sosai garesu yana cigaba da faɗin, “Alfarma ta farko itace inason a dawomin da abokan aikina tare dani, ina magana ne akan, Hafeez Umar, Aliyu S marwa and Jabeer Abdul-razaƙ. sai alfarma ta biyu kuma kununa ma abokan aikina cewar kun cireni da ga wannan case ɗin, a ɗora Qaseem Ali matsayin jagora, nikuma zanyi nawa aikin ne ta ƙarkashin ƙasa tare da abokan aikina ba tare da kowa yasan muna tareba”.        Shirun da yayne ya basu damar fahimtar ya kammala magana, hakan yasa su duka suka sake zuba masa ido tamkar wani baƙonsu, kusan minti ɗaya da rabi kafin ɗaya a cikinsu ya miƙe, kafaɗar Jay ya dafa yana murmushi da fadin, “Jawaad tunaninka mai ƙyaune, kuma hakan yamin ɗari bisa ɗari, abu ɗaya nake tsoro da shakku akan dukkan bayananka”.         Cikin izza da jin yakai jarumin na gaske ya ɗago kai yana kallon boss ɗin nasa, sai kuma ya sake wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa duka biyu loɓawa, “Sir! Miyasa kakejin shakku?”.         “Gudun rashin samun nasara, ina gudun yazam ba'ai nasaraba akan tsarinka Jawaad, dan rashin nasara a aikinnan tamkar zubewar mutuncinmu ne, samun nasara kuwa kimace a garemu, sannan kowannenmu kuwa ribace a gareshi, kuɗi zasu jiƙamu, sannan zamu ƙara nagarta a idon duniya harma da shugaban ƙasa”.        “Hummm” Jawaad ya faɗa a can ƙasan maƙoshi, kafin ya kallesu gaba ɗaya cikin takaici, “Insha ALLAHU zamuyi nasara, domin inaji a raina da NASARA AKE FARAUTO NASARORI a rayuwa, insha ALLAHU a karon farko da nake hangen samun damar farko zan sadaukar, badan komaiba sai dan farauto nasara ta gaske, abinda kawai nake buƙata a gareku goyon baya”.      “Mun baka kuwa Jay” Sir Ahmad ya faɗa fuska ɗauke da murmushi.       Ƙamewa Jawaad yay tare da yin Salute nasu baki ɗaya.          Sun bashi izinin tafiya, duk da kuwa maganarsa ta ƙarshe tai musu tsaye a zuciya, sam sun kasa fahimtar komai a kanta, domin dai hausace cikin hausa yayi.            Da tabbaci na dawowar abokansa uku garesa a safiyar gobe ya fita, koba komai ransa yay masa daɗi idan ALLAH ya kaimu gobe iyanzu yana tare da aminansa, ƙashin bayan jarumtarsa.           Duk bin ƙwankwantonka baka isa fuskantar yanayinsa ba, dan fuskarsa jarumar fuskace ma'abociyar adana komai, Office ya koma, cikin hanzari ya haɗa komansa.         Yana fitowa Gimba ya ƙaraso gareshi, jikkan hannunsa ya amsa suka nufi mota.          Kowa yasan Jawaad mutumin kirkine a hukumarsu, sannan jajirtacce akan aiki, sai dai sam baya ɗaukar wargi, yakanyi wasa da dariya da mutane idan yaso, amma kaɗan daga aikinsa ya birkice ka kasa gane kansa cikin ƙanƙanin lokaci.          Gimba ya buɗe masa baya ya shiga, sannan ya koma ta ɗayan ɓarin ya ajiye masa jikkarsa a gefensa, mazaunin driver ya koma  yay bismillah tare da tada motar suka fice daga station ɗin.       Luff Jawaad yay kwance jikin kujera, ƙwaƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ne kawai ke faman aiki a lokaci ɗaya, hakan yasashi barin duniyar mutane ya koma zuwa wata duniyar ta daban.                     Tun a shigowarsu farkon Layinsu ya buɗe idanunsa, da motar ɗaya da ga cikin kawunansa ya fara cin karo, ya tsurama motar ido tamkar yaune ya fara ganinta.       Har aka wangale musu ƙaton gate ɗin family House ɗin suka shiga bai daina bin motar da kalloba.            Sashin su Jawaad yana daga can ƙarshen gidan, hakan yasa saiya wuce dukkan sashin kawunansa kafin yaje nasun, umarni ya bama Gimba akan ya tsaya inda Kawu Nasiru yay fakin.         Kusan a tare suka fito da ga motocin, fuskar kawu Nasiru washe da murmushi yana kallon ɗan ɗan uwan nasa.        “A'a Jawaad har an taso aikin yau da wuri haka?”.       Guntun murmushi Jawaad yay yana ɗan shafa kai, ya rissina a gabansa yana faɗin, “Eh kawu mun dawo, ina yini”.        “Lafiya lau, Ja'iri kai dai kayi wuyar gani, muna a gida ɗaya amma sai mutum ya jera wasu kwanaki bai ganka ba”.       “Ai min afuwa kawu, aikin namune sai addu'a, a koda yaushe mutum bashi da lokacin kansa, ni kaina inason kasancewa a cikinku a koda yaushe, amma hakan bai samuwa”.         “ALLAH sarki karka damu, ai ka cancanci uziri ga kowa Jawaad, amma dai a rinƙa daurewa ana shigowa kaji, musamman ma tsofaffinnan kullum zancensu na gareka, a daure ana zagayasu akai-akai”.          “Insha ALLAHU kawu zan gyara, zuwa anjima duk zan shiga na gaishe da kowa”.       “To Alhmdllh, ka gaishe da baturiyar matar taka mai cika mana gida da kiɗa”.        Murmushin kan laɓɓa kawai Jawaad yay yana miƙewa, ya buɗe mota da kansa ya shiga, Har gaban sashensu Gimba ya tsaya da motar, yazo da sauri ya buɗema Jawaad motar ya fito.        Sai da ya rakashi da jakarsa har gaban ƙofar falonsu sannan Jawaad ya amsa yana ɗaga masa hannu ya shige.              Idanunsa ya rumtse da ƙarfi saboda su Shahudah dake baje a falo ita da ƴammatan gidan, ga mahaukacin kiɗa na tashi a sifiku, wasu na rawa wasu na zaune wasu kuma a kwance cikin kujera.       Sam babu wanda a cikinsu yaji sallamarsa balle motsin buɗe ƙofa.          Taku yake a hankali har gaban kayan kiɗan yasa hannu ya kashe, tsitt falon yayi.           Gaba ɗayansu a firgice suka maido kallonsu gareshi, kafin kace mi an fara ƴar reran gudu ta ƙofar kichin, wasu kuma ta ƙofar falon.          Shahudah da ke kwance ta ɓata fuska tana masa kallon takaici.        Koda suka gama fita baice mata uffanba, kallo ɗaya yay mata yay hayewarsa sama inda zai iske ɗakinsa.            Tundaga hawowarsa step ɗin farko ya fahimci Batool ko Nabeelah wani yazo yay gyara, hakan saiya ɗan rage masa fusatar da yayi.       Ɗakin barcinsa ya zarce kai tsaye, yana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da murza key dan karma Shahudah ta shigo.      Ɗakin yay ƙal saboda gyaran da ya samu, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi ga iskar hadari da ke bada ƙamshin ƙasa.         Tamkar jira ake ya zauna ruwa ya fara sauka a hankali.           Yana zaune a bakin gado yana zame takalminsa yakejin bugun ƙofar da Shahudah ke masa, baiko kalli ƙofarba balle tasamu darajar kulawa yay shigewarsa bayi bayan ya cire komai na jikinsa, sai ƙaramin wando da ya bari.            Gaba ɗaya yarasa wane irin mataki ya dace ya ɗauka akan Shahudah ne ta dawo hankalinta, shi yama fara tunanin ko bata da isashshen hankaline, dan sam baiga abubuwan masu hankali tattare da ɗabi'unta ba, ko ada can yasan bata da kirrki sam, amma zaman watanni bakwai da sukai a tare ya sake fahimtar dashi sanin da yay mata a baya ƙaramine ashe.          Rai a ɓace yay wankan harya gama ya fito, baiji motsinta ba, hakan yasashi gane tayi fushi, ya taɓe baki irin na rashin damuwa da hakan.        Zuwa yanzu ruwa ake zugawa sosai, hakan yasa yay sallarsa ta magriba a ɗaki, bayan ya idar mai makon ya zauna tunani sai ya ɗauki Qur'an ya hau karatu cikin nutsatstsuyar muryarsa.      Bai matsa a gunba har sai da aka kira isha'i, har sannan kuma ruwan saman ake zugawa.        Wayarsa dake ring tun yana salla ya ɗauka, ganin Umma Bara'atu ce sai yay murmushi (Umma Bara'atu ƙanwar mahaifiyar Jawaad ce, karku manta a labarinsa ya nuna mana tana da ƙanne har uku duk mata).        Cikin girmamawa ya gaisheta, da ga can ta amsa masa cike da kulawa.         Bayan sun gama gaisuwarsu take tambayarsa koya ga abinci?.        Murmushi mai sauti yayi, wanda har tana jiyosa, ya kwanta rigingine a gadon ƙafafunsa na ƙasa, “Yanzu nan Umma bazaki daina walar da kanki wajen aikomin abinciba kamar wani ɗan primary ”.       Dariya tayi daga can, cike da son tsokanarsa tace, “Yo miye banbancinka dasu Jawaad, ni a gurina ai tamkar tata kake, bama ni na aiko da abincinba, ƴar uwarka ce tayisa shine tabama Nabeelah da taga zatazo tace ta kawo maka, sai kuma Nabeelar ta iske bama ka gidan ka fice”.           “Ayya, ALLAH sarki Sister, na gode mata kuwa, ALLAH ya bata miji na gari wanda zai kulamin da ita, wlhy kiran gaggawa na samu da ga Office Umma shiyyasa na fice bata iskeniba”.         “Aini wannan aikin naka dan banda yanda zanyine, amma da ga ni har Auta da Amina bama sonsa sam, sai dai muna maka fatan alkairi a cikin, tunda kullum baba shi baya ganin laifinka”.       Guntun dariya Jawaad yayi, da gani kasan hirar ta sakashi nishaɗi, dan a ransa ji yake tamkar yana magana ne da mahaifiyarsa, “Karku damu Umma's ɗina, addu'arku ita nafi buƙata, harma kinsa na tuna da Tsoho, insha ALLAH da safe asubanci zan masa naje shan saurar furarsa”.           “Ja'iri, zaka fara ko? To sai anjima”.       Sosai Jawaad ya ƙyalƙyace da dariya, ya shiga faɗin, “Haba Ummana karmuyi haka dake, tsaya kiji......”       Ƙitt ta yanke wayar da ga can itama tana ƙyalƙyata dariya.                 Sumbatar wayar Jawaad yay a hankali yana kuma faɗaɗa murmushin fuskarsa dajin ƙarin ƙaunar ƙannen mahaifiyar tasa, masu ƙoƙarin share kukansa a koda yaushe. _______________________ BILKEESU ________________________         Naji daɗin shigowa gida na iske su Jazuga basa nan, ɗakinsa a rufe.      Firdausi kawai na iske a ɗakinmu, Inna ta fita maƙwafta yin barkar haihuwa.         Tagumin da Firdausi tayine na janye, ta ɗago a firgice tana kallona, ganin nice sai ta sauke sassanyar ajiyar zuciya.       Murmushi nayi ina faɗin, “Matsoraciya kin zata waye da?”.           “Ƴan ta'addan gidanmu mana, wlhy wannan rayuwar ta fara gundirata Bilkisu, nifa yanzu ko shakkar banzan nan banayi balle tsoro, dan nakula ibilis ne kawai ya rikiɗa a mutum ya shigo mana gida”.       Ido na zaro waje ina waige-waige, a tsorace nake magana ƙasa-ƙasa, “Firdausi bar irin maganarnan dan ALLAH kar wani yaji”.            Baki ta taɓe tana miƙewa tsaye, “Ai kunji tsiyar, wannan tsoron naku shike ƙara masa karsashi da jin ya isa, wlhy inhar a haka za'a cigaba da tafiya to lallai akwai babbar matsala, dan kuwa sai kunkoma bayinsa tamkar a ƙarnin farko”.         Tsayawa nai kawai ina kallonta, dan na fahimci ranta a ɓace yake, hakan yasa nai shiru, sam banason zancen yay tsawon da har wani zaiji, duk da Jazuga baya nan za'a iya samun wani ɗan neman gindin zaman a gidan namu ya sanar masa.          Itama jin nayi shiru sai taja tsaki ta fice ta barmin ɗakin, murmushi kawai nayi ina girgiza kaina, na cire kayana sannan na ɗauki abincinmu da nasan Firdausi bata ciba tana jirana na fita, nasan bazata wuce tana soro ba zaune.           Ilai kuwa acan na isketa, dan haka na zauna kusa da ita ina ajiye kwanon tasar abincin a gabanta.       Cikin sigar lallashi nake faɗin, “Haba dai tawan, wai fushi kikayi? To kiyi haƙuri kinji, taho muci abinci, dan da gaske da yunwa na dawo mai katse ƴan hanjin ciki”.          Hararata tayi tana ƙokarin matse dariyar dake neman kufce mata, (haka muke sam bamu iya dogon fushi da juna).           Munacin abinci muna ƴar hira jefi-jefi, sai ƙokarin kauda firar da Firdausi ke ɗakkowa ta Jazuga nakeyi gudun kar'a samu matsala, a haka har muka gama na sake ɗaukar kwanon abincin na maida cikin gida.            ★★★★★★★     Kwanaki huɗu kenan cif Jazuga baya gidan, da alama dai yayi nisan kiwo, kallo ɗaya zakaima gidanmu ka fahimci akuyoyin ɗaure sun samu sake, dan harmun fara sakin jikinmu muna rayuwarmu tamkar ta baya.           Sai dai kash a ranar cikon ta biyar murna ta koma ciki, ɓeraye suka koma wasan ɓuya da kuliya🤣, dan kuwa da yammaci kwatsam saiga Jazuga da zugarsa sun dawo, tsit kakejin gidan ya koma tamkar mala'ikan mutuwa ya shigo.           A ƙofar shigowa soro ya tsaya, sai da ya karema gidan kallon kamar yau ya fara shigowa, sannan ya tako zuwa ciki, tafiya yake kamar zai tsinke saboda rashin ƙiba          Dan sam Jazuga bashi da jiki, gaba ɗaya wiwi ta gama kalace dukkan wata tsokar jikinsa sai ƙashi data bar masa da fata            Amma a hakan akejin tsoronsa tamkar mutuwa, ga jiki duk yabi ya zane da tatu, daka gansa kaga ainahin hatsabibi mai matuƙar haɗari da rashin imani, dan tsaf zai iya tsarwatsa kwalwar kanka da bindiga ba tare da ya damu ba.................✍🏻 Page 10 ...........Wani siririn fito ya saki yana mai kallon kowacce kusurwa ta gidan.       Hakanne ya saka yaransa fahimtar jama'ar gidan ya kema kiranye.      Mai-tawaga, babban yaronsa ne yay magana cikin muryarsa mai kama da ƙattan farkon ƙarni, ga amo gata a matuƙar buɗe.       Kafin kace mi jama'ar gidanmu sun fara yo waje da gudu-gudu.         Muma dai ayari mukabi, duk da Firdausi taso yin tirjiyar ƙin zuwa, sai da inna tai mata magana sannan ta biyo bayanmu dan dole.           Kowa tsaye yay a ƙofar ɗakinsa yana jiran ƙarin bayani, abunda zaisa kaji tausayinmu kuwa hatta da mazan gidan sun koma mata maza, dan kuwa suma sunzo sun jeru a cikinmu, bayan kuma mafi yawansu sun girmi Jazugan, harma da waɗanda zasu iya haihuwarsa.           Har yanzu yana a bakin ƙofar tsaye, yana jingine a jikin bango dukkan hannayensa na cikin aljihun wando three queater ɗinsa a zube, rigace armless mai zanen tutar ƙasar Amurika a jikinsa, hakanne yasaka bayyanar ƙaton bandejin da aka naɗe damtsen hannunsa dashi, tabbacin yaji ciwo a wajen kenan.        Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonmu, sai kuma ya fara takowa yana wani rausayar layi irinta marasajin maganar gayu, fito ya fara rairawa yana cigaba da tinkaromu.            A gabana yazo ya tsaya cak.      Wata irin bugawa zuciyata tayi, tare da yin zallo tamkar zata fito, nai wuƙi-wuƙi da idanu kamar an tsamo zomo daga ruwa, addu'ar da nake ƙoƙarin haɗowa a harshena sam ta kasa haɗuwa......          hijjab ɗin dake jikina ya cikuykuye ya maidashi iya wuyana, yakamashi a hannu tamkar zai shaƙeni ya jani zuwa tsakkiyar gidan yana cigaba da fitonsa, Saikace wanda ya sayo akuya a kasuwa.      Duk da bansan warin giyaba inada tabbacin warinta ke tashi a jikinsa.       Yanda jikina ke rawa ina hawaye da ƙoƙarin bashi hakurine ya sashi kallona cikin razanarwa, ya ɗora yatsansa saman bakinsa yana faɗin “Shiiiiii”.        Duk da hawayen basu bar kwaranya ba dole haka na gumtse bakina kuwa.      Ƴan gidanmu duk sun tsorata, innar Firdausi kam ta kasa kallonmu, saima naga kamar kuka takeyi.            Ya gyara tsayuwarsa mai kama da zai ɓalle biyu yana dakama jama'ar gidan tsawa.        “Kowa ya ɗago ya kalleni, dolene yau na nuna muku real jazuuli, ina son ku ɗauki darasi akan wannan mara kunyar yarinyar, yanzu ni har nakai matsayin da zan saka wani aiki a duniyarnan yaƙi min? Wato ɗaga ƙafar da nake mukune har take bama wasu lasisin bijiremin ma........”        “Kai wanenen da baza'a bijire makaba, wawa kawai sauran giya da wiwi, mikake takama dashine shin? Da har kake tunanin sai an bika dole? Ko ka ɗauka tsoronka akeji....”      Firdausi ce a matuƙar hasale take wannan maganar tana nuna Jazuuga, takowa tai inda muke ta fisge hannun Jazuga daga hijjab ɗina a rikice..      Gaba ɗaya jama'ar dake wajen babu wanda bai zaro idanun mamaki ba, sai dai saukar ƙarar marin da ɗaya daga cikin yaran Jazuga suka saukema Firdausi ya kuma sakamu sake firgicewa.         Gaba ɗayansu sukai ribdugu akanta suka hau duka.     Hakan ya sakani fashewa da kuka ni da inna mukayo kansu, amma ni sai Jazuga ya fisgi hannuna ya nufi ɗakinsa dani.     Kuka nake ina tirjewa, shima yana jana a matuƙar fusace.        Ai sai gidan ya kuma ruɗewa da koke-koke.           Inaji ina gani ya kaini ɗakinsa, babu ko tausayi ya hankaɗani kan gadonsa, ihu na shiga kwarawa iya ƙarfina, amma babu mai ceto.     Inaji ina gani jazuga ya fara ƙoƙarin shiga mutuncina, UBANGIJI sam bai kasance azzalumin sarkiba, hakanne yasaka kawo wani haske a rayuwata, dan kuwa ina lalubawa sai ga ƙarfen da bansan kona mineneba, jawosa kawai nayi na maka masa akansa.       Wata razanannniyar ƙara mai firgitarwa ya saki, kafin yay luuu zuwa gefe, jini kuwa tuni ya ɓalle har a jikina.       Ihun Jazuga ya saka yaransa barin dukan Firdausi data gama fita hayyacinta sukayo cikin ɗakin.          Su duka kansa sukai suna kiran sunansa, da wannan damar nai amfani wajen fitowa da ga ɗakin da gudu, dukkan illahirin jikina rawa yakeyi, dan kuwa nasan tabbas na kasheshi.          Ban saurari dukkan masu min magana ba cikin ƴan gidanmu, dan kuwa hannuna da gaban ƙirjina duk jinine, nasan mafita ɗaya ta ragemin shine nabar gidan. Hakan yasa na zaɓi ficewa ba tare da nasan ina na dosaba.          Fahimtar Jazuga baya numfashi ya saka wasu a cikin yaransa biyo bayana suma a guje, ganin hakanne ya saka ƴan gidanmu suma fara guduwa zuwa wajen.          Atake anguwa ta ruɗe, wasu gudu kawai suke amma basusan akanmi bane, wasu kuma azatonsu bomb ne ma.     Ruɗewar da anguwarmu tayi baki ɗayane ta bani damar samun wajen ɓuya, dan kuwa wuuff nayi a cikin massalaci, nashige cikin mankarar dake jingine a bango taimin katanga.      Dukkan ihu da anguwar ta ɗauka inajinsa, harma da ƙarar guje-guje, taimakon da ALLAH yaymin babu wanda ya shigo massalacin, dama kuma ban iske kowa a cikiba.           Kusan mintuna talatin anguwar bata lafa ba, saima ƙarar jiniyar motar ƴan sanda danaji, ƙara tsurewa nayi da tsoro, nasan dai ni akazo kamawa ba waniba, kuka nake sosai, hannuna dafe da bakina, na jiƙe sharkaf da zufa har diga nake, duk mai imani ya ganni a wannan halin dolene hankalinsa ya tashi.     Nai wujiga-wujiga na fita hankalina gaba ɗaya.                Ɓangaren su Jazuga kuwa dai a tare dashi babu rai babu alamarsa, yaransa da sukabi Bilkisu tare da saka ƴan anguwa gudun dolene ya ankarar da ƴan sanda, hakanne ya sakasu zuwa dan suga mike faruwa.        Har cikin gidan ƴan sandan suka shiga, kowa ya fice a gidan, innar Firdausi ce kawai tsigunne gaban Firdausi dake kwance itama babu rai a tsakar gidan, sai yaran Jazuga guda uku da keta kai kawo a kansa shima, harma sun fito dashi waje da nufin kaisa asibiti saboda jinin dake malala a kansa.          Zuwan ƴan sanda yay dai-dai da zuwan Alhaji Lado naira, hankalinsa tashe ya hankaɗe ɗan sandan gabansa ya nufi wajen ɗansa yana ƙwala kiran sunansa.       Atake nanma gidan ya kuma ruɗewa, dan mutane sunɗan fara shiga hankalinsu suna shigowa gidan suga mike faruwa.           Bayan bayani da ɗaya acikin yaran jazuga ya shirya na ƙarya, da kuɗin da alhaji lado ya ɗebo a aljihu ya bama ƴan-sandan yasasu jiki na rawa suka kira Office ɗinsu, tare da shirya nasu tsarin akan Bilkisu ce tai kisan duk ita kaɗai, saboda Jazuga saurayintane, tazo ta gansa da ƙawarta Firdausi shine tayi yunƙurin kashesu ta hanyar kawo ƴan daba suka doki Firdausi, itakuma ta ƙwalama Jazuga abu a kai.            Innar Firdausi dake kuka tana faɗin ƙaryane ƴan sandan suka kaimata duka, ɗaya a cikinsu yace a fiddata daga gidan kafin manyamsu suzo.      Hakan kuwa akayi, dan an kulle innar Firdausi a ɗaki bayan an ɗaure bakinta.     Koda ƴan sandan sukazo akan bayanin ƙaryar suka zauna, dan basusan minene gaskiyarba, an ɗauki Jazuga da Firdausi zuwa asibiti, bayan ƴan sanda sun rufe gidan saboda bincike, sannan wasu aka bazasu neman Bilkisu a anguwar tako ina. 😭innalillahi wa'inna ilaihirraji'un🤦🏻‍♀️. _____________________ JAWAAD _____________________             Wani barcine mai daɗi ya sacesa take a wajen, gashi har lokacin ruwa ake zabgawa.       Kamar kullum dai yauma dai mafarkinsa akan mahaifiyarsa yake, hakanne ya sakashi farkawa a firgice, sai da ya karanto addu'a kafin ya miƙe zaune sosai hannunsa dafe da kansa.      Barcin nasama bawani nisa yayba, dan bai wuce mintuna ashirinba.      Dukda abinda ke nuƙurƙusar ransa bai barsa yay tasiriba tamkar yanda ya saba, miƙewa yay yanata sauke ajiyar zuciya a jere-jare, falonsa ya fito, inda ya hango kulolin abinci saman D/table, takawa yay ahankali zuwa garesu, dan ɗan barcin saiya saukar masa da kasala, ga kuma sanyin ruwa da garin ya ɗauka.        Kulolin yabi ɗai-ɗai yana buɗewa, yay ɗan guntun murmushi a kasalance, dan kuwa abincin da yafi sone a rayuwarsa, wato Masa, tayi ƙyau suɓu-suɓu, ga miyar taushe mai tsafta da tasamu ingantacciyar dahuwa.          Sauka yay ƙasa inda ya ɗakko filet dama duk abinda zai buƙata ya dawo.        Yana zama a kujerar dani ɗin Shahudah na fitowa daga ɗakinta saboda motsinsa da taji.       Duk da yasan itace sai yay biris ya cigaba da hidimar zuba masar sa,        Fuskarta da alamar damuwa taja kujera ta zauna kusa dashi gab, ta ɗora kanta jikin damtsen hannunsa ta kwantar tana lumshe idanu, tare da maƙalesa da hannayenta duka.      Nanma bai motsaba, bai kuma kalleta ba, saima laumar masa da ya fara kaiwa bakinsa cikin zaƙuwa.        Taunawa yakeyi a hankali yana wani luuu-luuu da idanu, ɗari bisa ɗari daɗinta yakai a yabama mai hidimar girkata.       Shahudah ta ɗago kanta tana kallonsa da mamaki, sai faman ƙyaɓe baki take tana wani yamutse fuska saikace taga kashi, itafa sosai kyankyamin abincin gargajiyar nan takeyi lokuta da dama, ji wata irin miya dan ALLAH......           “Wai dan ALLAH bb baka tsoron irin waɗanan abincin su sakaka yin nauyi da yawa?”.       Banza yay mata kamar baijiba.     Ta daki damtsen hannunsa kaɗan tana buga ƙafafu da turo baki cikin shagwaɓa.       “Kai kaji tsiyarka riƙon masifa, ba nazo na baka haƙuri ba amma dan wula ƙanci ka kulle ƙofarka dan karna shigo”.      Nanma ɗin banza yay mata.      Tagumi tayi hannu biyu ta zuba masa idanu tana hawaye.         Yi yay tamkar baisan tanaiba, yaci abincinsa yay nak, hannunsa ya wanke cikin ruwan daya ajiye, ya ciri tissue yana goge bakinsa da hannunsa. Duk dai Shahudah na kallonsa tana cigaba da kukanta.       Miƙewa yay zai bar wajen ta miƙe itama a zafafe, sai ta faɗa bayansa ta zagayo hannayenta a cikinsa ta sakar masa kuka mai sauti.             Cak ya tsaya bai motsaba, kusan mintuna biyu suna a haka, idonsa a lumshe yana sauraren sautin kukanta da saukar hawayenta a gadon bayansa.       Hannu yasa ya cire nata dake akan cikinsa, ya tureta daga jikinsa yay gaba zai bar waje.         Kuma kamo hannunsa tai da sauri tana fadin, “Haba bb, miyasa kakeson wulaƙantani ne? Kodan kaga inasonka da yawa haka? Nasan bakason a tara maka mutane a gida, amma nima ka dubi uzirina mana, kaji tausayin kaɗaicin da nake zama a ciki, ka hanani fita, dukda nasan ƴancinane na fita inda nakeso a lokacin da nakeso, amma nai haƙuri saboda kayi farin ciki, ya ka ke so na rayu dan ALLAH? ban saba da wannan rayuwar takuba, rayuwar ƴanci na taso a cik.......”       Yanda ya juyo a zafafe ne ya saka bakin Shahudah rufewa akan dole.       A tsawace tare da matsota kamar zai hadiyeta yace, “Ƴanci ko jahilci? Hudah ke wace irin daƙiƙiyace ne wai? Miyasa fitilar ƙwaƙwalwarki bata haska miki hanyar da zaki sanya ƙafa? Wlhy nayi nadamar aurenki, nadama irin wacce bama zan yafema kainaba, wawuya kawai mai koyi da toshewar basirar jahilai”.            Shahudah dake tsaye tamkar wata gunki ta bisa da kallo harya shige ɗakinsa, duk da bagama fahimtar kalaman nasa tayiba sun girgizata, dan ita hausarma bakomai take ganewa a cikiba saboda ba yimusi akeba, ɗan dawowar tasun nanmane take ƙara fahimtar wasu abubuwan🤦🏻‍♀️(kaga turawa😆😝 ).          Hawayen da suka sakko mata a farar fatarta ta goge, duk da kayan dake jikinta basu dace wani ya ganta da suba, haka ta fice daga sashen nasu, ga yayyafi har yanzu anayi ƙaɗan-kaɗan.         Da gudu ta isa sashen tsohuwa Mama atika, (wato kakarta data haifi mamanta).                  Zuciyar Jawaad a wuya take sosai, gaba ɗaya Shahudah ta sake ruguza masa dukkan farincikin da Ummansa ta bashi tare da ƴar uwarsa Batool.        Haka yay shirin barci yanata sauke ajiyar zuciya, yanayin shafa'i da wutiri ya haye gado yay kwanciyarsa.       Amma sai barcin yaƙi zuwa sam, haka yayta tunane-tunane har kusan ƙarfe uku, kafin barci ɓarawo ya sacesa.         ★★★★★★           Da safe haka ya tashi babu walwala, yana dawowa sallar asuba yay shiri ya fita wajen aiki batare da ya yarda kowa daga jama'ar gidan ya fito ya sameshi ba.               Koda suka iso gimba ya buɗe masa motar ya fito.        Da Qaseem ya fara cin karo, ya tara zaratan matasan ƴan sanda yana musu magana, da alama dai ya haɗa rundunane.         Wani mugun murmushi yayma Jawaad yana kanne masa ido ɗaya.     Waishi a haukarsa ai ya karɓi damar da Jawaad ɗin ke takama da ita.          Shima Jawaad ɗin murmushi yay masa, tare da sumbatar yatsun hannunsa biyu ya nunama Qaseem alamar saƙo.       Saikuma abin ya soki zuciyar Qaseem, tuni fara'ar fuskarsa ta bace ya koma bin bayan Jawaad da wani mugun kallo.       Baima san yanayiba, dan tuni Jawaad yama shige sashen da zai kaisa Office ɗinsa.        Yana zama da saƙo yafara cin karo.     Zumbur ya miƙe ya fice tamkar zai tashi sama dan rawar jiki.             A ƙofar Office ɗinsa yaci karo da Qaseem Ali, kallon mamaki Jawaad ke binsa dashi, amma baice komaiba.      Qaseem yay wata dariya yana watsa hannaye gefe,      “Yaya dai gwarzon ma'aikaci, yaya kaga wasan nawa? Ka shiga ruɗani ko? Aikin da kake takamar dashi an amshe cikin lokaci ƙankani an bani, nine zan jagorancesa yanzu, dama iyakar izzar taka kenan?”.              Murmushi Jawaad yayi cikin ƙokarin katse Qaseem, buso iska yay daga bakinsa yana takowa cikin tsantsar takama da izzar jarumta irinta zaratan matasan da jini ke yawo ta kowace kafar jikinsu zuwa gaban Qaseem ɗin, ya dafa kafaɗarsa da hannu,           “Na yarda kayi nasara my dear, ni kuma na faɗi, sai dai ina baka shawara akan ka kula kafin wani ya kula da kai, sannan ba'a cika baki da nasara kafin a nemota, nasara anan take Qaseem, (ya faɗa yana nuna saitin zuciyar Qaseem da ɗanyatsa), ina baka girma dalilin kaiɗin yayan matatane kuma ɗan uwana, sannan ogana a wajen aiki, karka bari zuciyata ta fara ƙoƙarin yin fito na fito da kai ko maida murtani. Nabarka lafiya, tare da fatan nasara jarumin ma'aikaci”.       Ya ƙare maganar da salute ɗinsa, tare da zagayesa ya wuce.             Harya shiga mota suka fice daga station ɗin Qaseem na tsaye kamar bishiyar giginya, zuciyarsa na tafarfasa da ƙuna, tare dajin tsanar Jawaad mai tananin gaske..................✍? https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q          *MANHA HAUSA NOVEL'S* takuce, maza garzaya domin bada gudunmawarka, danna Subscribing domin nuna ƙaunarka garemu🤩, kuyi  shiri na musamman domin samun daɗaɗan shirye-shiryenmu tare da nagartattun labaran novel's masu daɗi da ma'ana nan da lokaci ƙanƙani, MANHA HAUSA NOVEL'S ta shirya tsaf domin baku farin ciki insha ALLAHU, ku garzaya kada ƙuda ya rigaku😂, Bilynku ma har taje tayi subscribing tun farar safiya, goyon bayanku shine ƙwarin gwiwarmu🥰🥰😉🤩. MANHA HAUSA NOVEL'S (Ƙyautar ALLAH). Ku isa da hanzari domin samun ƙyautar kuma, dan ALLAH a danna subscribing, tashar tana a manhajar youtobe ne.     Page 11 .............Mama Atika tsohuwa mai ran ƙarfe dake zaune a falonta tana jan cazbaha ta ɗago tana kallon Shahudah data shigo a guje kamar an korota, ga jikinta harya fara jiƙewa da yayyafin da har yanzu akeyi, sai da ta ƙarema guntun wandon jikin Shahudah da bai gama zuwa koda rabin cinyartaba kallo da riga mara hannu, wadda inda zata ɗaga hannu sai anga cibiyarta. Janye idanunta tayi daga barin kallonta sannan ta girgiza kanta. Ƙarasowa Shahudah tayi ta zauna a jikinta tana kumbura fuska ga hawaye na kwarara. Mama Atika ta shafa addu'a tare da maida hankalinta ga Shahudah. "Kekuwa Sabirah miya jamiki fitowa a haka cikin wannan ruwan? Ko ɗankwali ma babu fa a kanki, baza dai kibar wannan shigar ta bayyana jikinki ba ko?". "Ni ki daina cemin Sabirah, idan bazakice Shahudah ba basai kin kira sunanaba, Wlhy hajiya nagaji da abinda Jawaad kemin a gidansa, ni gaskiya ku kirasa kuyi masa faɗa". Mama Atika tace, "Hummm, yauma tsiyar kuka sakeyi kenan? Waishi wannan yaron wane irine? Ni abindama ke ƙaramin takaici dashi kokin kawo ƙarar tasa an kirasa sai yace shi baki masa komaiba, narasa irin wannan rikitaccen zama naku". Kuma fashewa da kukan shagwaɓa Shahudah tayi, sai kuma lafewa jikin tsohuwar takeyi. "K yanzu yasan kin fitone?". Mama Atika ta tambayi Shahudah. "Ni ban sani masaba, dan fitowata kawai nayi bayan yamin wulaƙancin". "Hummm, to shikenan, yanzu tashi ki koma, da safen zansa iyayenku su nemeku". "Ni dai anan zan kwana, dan inason ya gane kuransa yau".. Murmushi irin na girma mama Atika tayi tana gyara zama, "Shikenan, tashi kije ki sauya waɗanan shiɗanun kayan ki kwanta muga idan zai biyoki, idan bai zoba ai iyayenki zasuzo gaisheni da Asuba zan sakasu kiransa ayi zama yau, dan bazan yarda da irin wannan halin na wulaƙanciba, sai dai yasan mai yuwuwa". Jin hakan da Shahudah tayi saiya sake kai kanta sama, ta shige bedroom din ƴar tsohuwar da aka narkama dukiya ta kwanta abunta. Tun mama Atika na zuba idon ganin ko Jawaad zai shigo a daren harta fidda, dan har tagama cin abinci da duk abinda ta saba yi kafin ta kwanta, har lokacin kuma babu Jawaad babu labarin. Da safema koda suka tashi bai zoban, harta gaƙaraci mitarta akan Shahudah da bata tashi tai sallaba tai shiru, sai kuma ta koma kan Jawaad. Da mitar Jawaad ɗin a bakinta su baba Usman suka shigo suka sameta, bayan sun gaisheta take sanarmusu komai. A take suka aika a kira musu Jawaad, amma sai akai rashin sa'a aka iske ya wuce aiki abinsa. Takaicin hakan ya hanasu motsi har saida suka fara jiyo kakarin aman Shahudah daga bedroom ɗin Mama Atika. Itace ta shiga ta isketa duƙe tanata amai cikin banɗaki, mamaki ya kamata, amma saita ajiye mamakin ta taimaketa harta gama sannan ta bata ruwa ta wanke bakinta suka fito. Sannu taketa jera mata da tambayarta komi taci haka daga tashinta?. A galabaice Shahudah ke faɗin, "Ni banci komaiba Hajiya, dan rabona da cin wani abu tunma jiya da yamma, bansan miyasaba kwana ukunnan kullum da amai nake farkawa da safe, narasa mike damuna". Tsiramata ido mama Atika tayi ba tare da ta iya cewa komaiba, tsawon wasu sakanni tana a kanta tana nazarinta, sai kuma ta fice daga ɗakin a hanzarce tare da wani irin ɗoki akan fuskarta. Shahudah kam kanta ta maida ta kwantar barci ya kuma kwasheta. Albishir ɗin da tsohuwa takaima ƴaƴan nata ne ya sakasu miƙewa zumbur a wani irin razane. Kowa na ambaton mama da gaske?. Dariyar jin daɗi tayi tana zama, "Ƴaƴannan mizaisa na muku ƙarya nikuwa, sam bakwa bina bashin rantsuwa akan wannan maganar haka take. Amma danku tabbatar a kira likita ya gwadata yanzunnan". Duk da sun yarda da batun mahaifiyar tasu haka suka nemo Doctor domin sake tabbatarwa a aikace. Jikin Shahudah rijib da zazzaɓi zuwa yanzun, haka dole Mama Atika ta tasheta, tambayoyi likitan yaymata tare da bata tsinken gwaji saboda ba'a buƙatar jan lokaci. Gwajin farko ya tabbatar akwai ciki, tuni falon ya ruɗe da wani irin murna, kowa fuskarsa a washe saɓanin ta Shahudah dake a rikice. Ciki kuma? A wannan shekarun natane zatayi ciki? Kai da sakal wai anbama mai kaza kai, sam babu tsarin ɗaukar ciki a gareta a nan kusa, yaushema sukai auren da har tagama morarsa da za'ai batun ciki a jikinta, so ake ta ragwagwgwaɓe da wurima kenan tamkar wata matar Afirika, ina wannan shirmen bamai yuwuwa bane, dolene Jawaad yazo asan abinyi, dan bazata haifi wannan cikinba koda za'a tada yaƙin duniya na ukune. 😱😱hummm ashe akwai kallo, dan inba'a tada yakin duniya na uku ba to lallai Shahudah za'a tada na ƙarshe akanki🤣🤣, yanda naga cikin yazama burin mutane da yawa aiko yagalgalaki zasuyi harma da Fans din ƙwai cikin ƙaya😆😂. ★★★★★★★★ Ya isa ƙofar kurkukun (Jail) da abokansa uku kuma aminansa suka tsinci kansu a ciki dalilin ƙaddara, dan kuwa shekarunsu na biyu kenan a wajen bisa sharri da akai musu dan a durƙusar da Jawaad ɗin, yayi iya bakin ƙokarinsa a lokacin ganin sun kuɓuta amma sai hakan ya gagara, dankuwa ƙulline mai cike da ruɗani a ka ƙulla dan kawai a dakusheshi tunda ansan abokansa suna cikin manyan abinda ke ƙara masa ƙwazo da ƙarfin gwiwa, duk yanda yaso gano wanda ya aikata masa hakan kuma bai samu nasaraba, shiyyasa ya tattara komai ya maida hannun ALLAH, sai gashi a yanzu cikin sauƙi ALLAH ya kuɓtar dasu. Shigarsa wajen ta saka ma'aikatan gidan yarin bashi girma na musamman, dan sunsan wanene shi da matsayinsa, tunda dama jail ɗin bana kowa da kowa bane, jami'an tsaro masu laifi kawai ake sakawa a ciki. Bayan shigarsa Office ɗin shugaban wajen na wasu mintuna aka kammala komai, yana nan zaune aka fito dasu. Idanu suka tsurama juna da ga shi harsu, tuni idonsa ya kaɗa yay jazur tamkar an hura barkono, jijiyoyin kansa sunyi wani irin fitowa ruɗu-ruɗu, ya miƙe ahankali yana tunkararsu tamkar yanda shima suke nufoshi cikin wani irin yanayi na kewa da farinciki, dan shekaru biyun da suka ɗauka a rufe sam an hana Jay ganinsu. Rungume juna sukai su huɗu, dukda yanda jikinsu yake baiji ƙyamarsuba, kowanne hawaye masu raɗaɗi suna kwarara a idanunsa. Su dai ma'aikatan wajen kallonsu kawai sukeyi. Kusan mintuna uku suna a haka, kafin su ɗago kowanne yana ƙokarin sharema ɗan uwansa hawayensa, sai kuma suka sake rungume juna suna dariya saikace wasu zararru. Nanma kusan sakwan arba'in suka ɗauka kafin suyi haramar fitowa ba tare da ko bakin ɗayansu ya saɓa ba wajen furtama juna magana. Gimba dake jikin mota tsaye ya hangosu suna fitowa daga cikin Jail ɗin a yanayin da yasansu a baya, jarumai kuma aminai, sannan ƴan uwan juna masu ɗaukar kansu JINI ƊAYA. Cike da wani irin ɗoki yake washe musu baki har kunne, lallai yau farin cikin boss ɗinsa sun dawo, yanzu sauyi zai sake zuwa a hukumarsu, hannunsa ya dunƙule waje ɗaya yana cigaba da washe bakinsa, yama kasa magana saboda tsabar farinciki. Suka dafashi a kusan tare suna dariya suma. Da ƙyar ya iya furta, "ALLAH mun gode maka, yau ga basawan boss sun dawo gareshi, tarkon da makiya suka kafa ya buɗe". Jawaad da fuskarsa babu walwala ya girgiza kai kawai ba tare da yace komaiba ya buɗe mota yana musu nuni dasu shiga. Basu ɓata lokaciba suka bar wajen zuwa gidan Jay ɗin dake Empty babu kowa ciki, gidan yayi ƙyau sosai, gashi anguwar da yake babu yawan hayaniya. Suna shiga gidan dukkan farin cikinsu da suka danne da kewar juna sai ya bayyana, dan sake rungume juna sukai a tare kowa na faɗo yanda yay kewar ɗan uwansa. Tsawon lokaci suka ɗauka a haka har Gimba ya dawo da ledojin abinci ba tare da sunsan zaiyi wannan ɗawainiyarba. Godiya sukai masa duk da kuwa yana ƙasansu, ya nuna musu hakan ba komai bane tare dajin daɗinsa na murna da sukai, ya jajanta musu da addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba. Wanka suka shiga su duka a mabanbanta banɗakin dake cikin gidan, sun ɗauki tsawon lokaci, dan Jawaad ma harya fice zuwa wani kiran gaggawa daya samu daga office ya barsu akan kafin ya dawo su tabbatar sunci sunsha sun huta....... ______________________ BILKEESU ______________________ .........Har dare babu labarin bilkisu a cikin anguwar, ga kuma ƴan sanda ta ko'ina an bazasu nemanta, sai kuma yaran Jazuuga dasuma ke aikinsu domin taya ƴan sandan. Ina cikin mankarar har dare, tun ina kuka da hawaye da murya harna koma na zuciya kawai nake iyawa, hankalina bai gama tashiba sai da na farajin motsin mutane masu shigowa sallar magriba, kuma nutsuwa nayi a wajen duk da ƙarfina ya ƙare, hannuna dafe da bakina gudun kar wani mai ƙarfin ji ya iya jiyo fitar numfashina. ALLAH ya aramin wannan lokacin har akai sallar magriba aka kammala. Sosai ƙarfina ya gama ƙarewa, na gaji da tsaiwar, burina kawai na zauna nahutama raina, ƙafafuna sunyi nauyi tamkar ba'a jikina sukeba, gashi wasu suna a massallacin basu gama ficewa ba, sun zauna har sai anyi sallar isha'i. Haka na cigaba da dauriya a wannan yanayi mai wahalar musaltawa har lokacin sallar isha'i yayi ya wuce, mutane sun fara barin massallacin, inda akabar tsirarun da suka koma fita ɗai-ɗai. Wani da ya fita na ƙarshe shida abokinsa naji suna faɗin ƙarfe goma da rabi na dare, bana a hayyacina zuwa lokacin sosai, amma bayan fitarsu da wasu mintuna saina leƙo kaina cikin massalacin, babu kowa sai mutum ɗaya dake barci, da gyar na tattaro ɗan sauran ƙarfina na janye mankarar na fito, tafiya nake tamkar bugaggiyar da tayi mankas da kayan maye, ni kaina bansan a ina nake jefa ƙafaba, tafiya kawai nake tamkar bahagon raƙumi. Ƙwaƙwalwar kaina sam bata aiki da zuciyata, ni kaina na fara manta wacece ni?. Ƴan sanda biyu dana hango gabana suna tunkaroni yasani firgicewa, nai saurin komawa baya na maƙale jikin bangon wani gida, ta gabana sukazo zasu wuce suna magana wadda na fahimci akainace. Ɗaya a cikinsu ke faɗin, "Oga kana ganin Alhajin nan zai bamu maƙudan kuɗinnan kuwa daya faɗa inhar aikinnan ya kammala yanda akeso?". "Hhhh bayarwa kuwa zaiyi ɗan sambo, bakaga yanda yake a firgiceba, bashi da burin daya wuce akama yarinyar, sannan ɗansa ya kuɓta, shiyyasa nima nace muyi ƙaimi, dan inada tabbacin tana cikin anguwarnan bata fitaba, sai dai idan wani munafikinne ya bata mafaka a gidansa". "Shegun ba, ai zamu kamatane, idan kuma har kuɗinan suka tabbata lallai lokacin ƙara aurena yayi kenan, dan wlhy zama da kubra kawai nafi ƙarfinsa". "Hhhhhhh!! Wato ɗan sambo shiyyasa nake sonka wlhy, kai abokin neman arziƙine, idan kana abu sainaji daɗi saboda lallai kana kan tsarina, saikace uwa ɗayace ta haifemu". Dariya suka kwashe da ita tamkar wasu mahaukata su duka biyun, da wannan mahaukaciyar dariyar suka wuceni batare da ɗayansu ya hankalta dani ba. Numfashi na sauke cikin gajiyawa, sai da na tabbatar sun ɓacema ganina sannan nacigaba da tafiya ina zirar da hawaye, wace irin ƙasa muke da ita hakane? Masu bada tsaro da kariya sune suka koma masu ɓata tsaro da zalunci?. Ta yaya har muke tunanin samun shugabanni adalai bayan muma talakawan azzaluman junane?. Nacigaba da tafiya ba tare da namasan ina nakeba, abinda na sani kawai shine nayi nesa da anguwarmu kam tabbas, sannan ina buƙatar zama na huta, sai dai tsoro da fargabar kar azo a kamani sun hanani damar samun wajen yada zango. Nayi tafiya mai nisan gaske, wadda sam banida nutsuwar ƙididdigeta koda da ƙiyasine, tun ina gamuwa da mutane da kallon motoci a titi har garin ya fara ɗaukar shiru, bakaji koda ƙarar mashin, ƙafa tafara ɗaukewa, hakama motoci, lokacin da garin ya gama ɗaukar shiru babu abinda kakeji sai haushin karnuka. Da ƙyar na iya kawo kaina wani wajen da nakeji sautin kiɗa na tashi, duk yanda naso samun dauriyar matsawa daga nan na kasa, cikin rashin kuzari da ƙarewar ƙarfi na zube jikin wata bishiyar mangwaro dake a gaban gidan, mashina ne birjik a wajen duk an faka, sai jefi-jefi na mutane dake fitowa daga wajen mace da namiji ko mata zalla. Tun ina kallonsu har na gazama hakan, idanuna da sukai nauyi jingim saboda kukan da nasha na lumshe a hankali, badai barci nakeba, bakuma ina tare da duniyar mutane bane sam. Tsawon lokaci ina a wajennan ba tare dana fargaba, sama-sama naji ana tadani, na buɗe idanu da ƙyar ina saukesu akan ƴanmata biyu da bazasu gaza sa'annina ba, sai namiji dake gefe yana faɗin, "Ƙila tasha abinda kanta ya gaza ɗaukane ko?". Ɗaya a cikin ƴanmatan da ke ƙokarin taimakamin na tashi tace, "Anya ma wannan kuwa bamma santa ananba sam, dan inaga baƙuwace". Kaɗan ɗayar ta ɗan haskani da fitilar wayarta rakani kashi, ta kautar da hasken daga fuskata tana cewa, "A gaskiya baƙuwace, dan nima bamma taɓa ganintaba a gidan wasannan". "Da wannan surutun da kuka tsaya da kamata kukai mukaje da ita gida, dan tabbas tana bukatar taimako" namijinne yay magana cikin nuna kulawa. Basuce komaiba sai taimakamin da sukayi na miƙe tsaye sosai, ni dai ban iya cemusu uffanba, suka kamani a kafaɗinsu mukabi wani lingu. Banwani damu da inda suka kawoninba, duk dama gidan tsitt yake alamar duk anyi barci, namijinne yasa key ya buɗe ɗakin suka shiga dani ciki. Sun kwantar dani a katifar ɗakin wadda halin danake ciki baisa na fahimci komai akantaba. "Ƴar daɓas kunna risho a dafa mata ruwa tasamu tai wanka, dan a halin da take ciki na fahimci bazata iya jin daɗin barciba". Da to wadda aka kira ƴar-daɓas ta amsa, cikin mintuna kalilan aka haɗamin ruwan wanka mai matsakaicin dumi, yanzuma da taimakonsu na shiga banɗakin dake a cikin ɗakin. Ban cutar da kainaba na daure nayi wankan, naji daɗin hakan sosai, bayan nagama na ɗauki doguwar rigar da aka ajiyemin na saka sanann nayo alwala na fito, dan yin wankan yasa naɗan fara dawowa a hayyacina. Zaune na iskesu sunacin nama, na ɗan kallesu na duƙar dakai ina faɗin, "Dan ALLAH ku taimakeni da abin salla da hijjab". Ganinai sun kalli juna a wani irin yanayi na shakku, ni saima na fara tunanin koba musulmai bane....... Ɗayar ta katsemin tunani da faɗin, "ƴar uwa samun abin salla a ɗakinnan lallai babban abune, ke ama gidannan gaba ɗaya zance, amma dai ga ɗankwali idan zaki iya maneji dashi, hijjab ma inaga za'a iya samun wanda nazo dashi a farkon zuwa gidanan, tunda kuma na ajiyeshi ban sake waiwayeba". Ban fahimci zancen nasuba, bankuma tambaya ba, inadai tsaye aka bani hijjab da ɗankwalin, shinfiɗawa nai na tada salla, sai da nayi sallar la'asar da banyiba da magrib sannan nai isha'i, harma da shafa'i da wutiri, hannuna na ɗaga sama ina addu'a hawaye masu zafi na kwarara saman kumatuna, nakai tsawon lokaci ina kaima ALLAH kukana, kafin na miƙe. "Wai, wannan salla taki akwai tsawo, zokici abinci muɗan kwanta, dan gari gab yake da wayewa". Yunwa nakeji, hakan yasa banyi musuba nai zaman cin naman da sukaci suka ragemin, sai fura mai sanyi wadda naji daɗinta sosai. Ina kammalawa suka nunamin wajen kwanciya. Sai a yanzune dana samu nutsuwa komai ke iya dawomin dalla-dalla, wasu hawaye ke sauka saman fuskata a gurguje, koyaya Firdausi take? Inna da baba da sauran ahalin gidanmu, na ɗago hannuna ina kallo zuciyata na wata irin suka, ni Bilkisu yau nice matsayin wadda tai kisan kai, wai ni na kashe mutum?.... Kuka mai ƙarfi ya ƙwacemin, nanfa na shiga rairashi babu mai lallashi, dan masu masaukin nawa bansan ya akai daga kwanciyarsu barcinsu yay nauyi irin hakaba, na daɗe ina kuka har aka kira sallar asubahi a kan kunnena. Tashi nai cikin layi da nauyin jiki nayo alwala, nazo ina ƙokarin tashinsu amma sam babu wadda tai motsin kirki balle na saka ran zasu tashi, haka na haƙura saboda jin zan rasa sallah. Koda na idarma na sake gwada tashinsu amma basu tashinba, nanma haka na haƙura, sai dai zuciyata na mamakin irin wannan nauyin barci haka?, nima ban fargaba barcin ya kwasheni a wajen. ★★★★★★ A daren ranar yaran jazuga suka dawo gidan da taimakon ƴan sandan nan, duk wani makami da sukasan sun ajiye gidan harda wanda Bilkisu ta gani da yawa a kwali randa ta kasa masa shara duk suka fitar dasu, kayan shaye-shayensu da duk abinda za'a iya kalubalantarsu dashi saida suka fitar dashi. Hakama innar Firdausi sun fito da ita, asibiti suka kaita inda baba yake cikin wani yanayi da baki bai iya musaltawa. Innar Firdausi ta fashe da sabon kuka saboda ganin halin ruɗani da mijinta ke a ciki, gefe yaran Jazuga sukaja baba da inna, suka shinfiɗa musu dokoki tare da gargaɗi mai tsoratarwa. A tsorace baba da inna suka amince kodan son tsira da ransu. Alhaji Lado yace, "Zamu baku ƴarku mu canjata da gawa, munaso kuyi nesa da garinanma gaba ɗaya, koda sau ɗaya naga masu kama daku na rantse saikun mutu dukanku, bayan na gama gallaza muku azaba mara musaltuwa, sannan koda wasa kuka taimaki yarinyar data kashemin ɗa wlhy kuma saikun mutu, dan daga yanzu dukkan motsinku zai cigaba da gudana ne a kan idona". Cikin kuka baba da inna suka amsa. A munafurce aka fiddo firdausi da taimakon likita da shima aka toshe bakinsa da kuɗi, tare da yaran Jazuga da ƴansandan nan. A wata mota aka sakasu harda Firdausi da har yanzuma bata farfadoba, sai dai raunikan jikinta duk sun sami kulawa. A wannan tsohon daren aka nufi asalin ƙauyen su baban Firdausi dasu, sunaji suna gani, suna kuka da ɗunbin tausayin Bilkisu da tunanin tana cikin wane haline? Wane kuma hali zata iya shiga daga nan zuwa safiyar gobe.............✍🏻 Page 12 ............Tun a farkawar da nai a wannan barcin safe da yay nasarar saceni na fahimci lallai ƙaddarar rayuwa ta sake jefoni wani rukunin ajin karatun, dan kuwa babu tantama gidan nan na karuwaine. Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro saman kumatuna, ban damu da sharewa ba na barsu suna cigaba da kwarara tamkar an buɗe fanfo.....            “Baƙuwarmu kina ganin kuwa kukan nan bai isa hakaba?”.      Ɗaya daga cikin waɗanda suka taimakeni ta faɗa tana janye hannun da nai tagumi dashi.      Idanu na ɗago na kalleta, ƙyaƙyƙyawace, sannan yarinya shakaf da shekarunta bazasu gaza kamar nawa ba, banbancina da ita kawai jikinta a murje yake alamar akwai jin daɗi tattare da ita, na sauke ajiyar zuciya ina kauda idanuna daga gareta ba tare da na ce uffanba.       Ɗayar data shigoce ta katsemu da faɗin, “Sweet gafa Laran gabas can nayi dake akan wasan jiya”.        Ƴar daɓas ta kwashe da dariya tana zama a bakin katifar, “Bar shegiya kinji Sweet, itadai ai bariki iyawace, kowa kaga yazama wane ya iya allonsa ne, idan ta isa itama ta iya wanke nata”.       “Kamar kuwa kin shiga zuciyata Sweet, dan nima haka nace mata”.         Kusan a tare suka taɓe baki, Nazy ta juyo indomie daga cikin tukunya tana ajiyewa gabana, “Sorry bakuwarmu mun barki da yunwa, kinga abincinki nan tun ɗazun tsumayen tashinki mukeyi, kinfa sha barci, saikace wadda bata samun isashen barci daga inda ta fito?”.       Murmushin yake kawai na mata, sai dai ban iya cemata komaiba itama.        Ƴar daɓas tace, “Nikam badan jiya kinyi magana ba da nace kodai ke kurmace, ki daure ki amsa mana tambayoyinmu kafin Uwargida ta shigo gidan nan, dan in bata fara samun wani bayani daga garemu ba zamu fuskanci matsalane akan kawoki, kodai kema rayuwace ta nuna miki hanyar zaɓar ƴancin kankine?”.        “Neman ƴancin kai kuma?”.       Cikin tsagwaron mamakin daya mamaye fuskata nake jefa musu tambayar tawa.        A tare suka ɗagamin kai, Nazy ta washe haƙora tana cewa, “Ai duk macen da kika gani a gidan nan tazone domin samun ƴancin kanta, sai dai kisamu banbancin dalilan da suka nuna mana hanyar hakance nasararmu”.         “Wata sabuwa kenan”. na faɗa a fili batare dana saniba.        Atare suka maimaita abinda na faɗa ɗin, suka ɗora da faɗin, “Miyasa kikace haka? Kina ganin hanyar da muke bata dace da tsarinkiba kika fito da ga gidanku?”.        Murmushi nayi ina lumshe ido, wasu hawaye suka sake ziraromin, hannu na saka na sharesu a karo na farko, na kallesu sosai cikin matuƙar tausayawa kanmu, “Ni ba wannan harkar nazo yiba, ƙaddarar rayuwace kawai ta kawoni cikin taku ƙaddarar”.      Shiru duk sukayi suna kallona, nima ban sake cewa komaiba na zame na kwanta ina cigaba da kukana, tsawon loakaci muna a haka babu wanda ya sake cewa komai, sai zuwa can ƴar daɓas tace, “To ki daure ki tashi kici abincin, sannan idan bamu shiga rayuwarkiba dan ALLAH ki bamu labarinki”.        Shiru ban motsaba, bankuma iya cewa da ita komaiba, babu abinda ke sukar zuciyata sai halin dana bar ƴar uwata Firdausi a ciki tare dasu Inna, saiko kisan Jazuga danai da hannuna, na ɗago hannuna ina kallo, wasu sabbin hawayen suka sake ziraromin, jinake inama ni Jazuga ya kashe, dana huta, koba komai zan kusantu da iyayena, na rushe da kuka mai sauti ba tare da nasan muryata tayi ƙarfi irin hakanba.        Akusan tare sukai kaina suna tambayata lafiya?, yanzunma dai basu iya samun amsaba daga gareni har wata mata ta shigo.      Barina sukai duk suka juya gareta, cikin matukar ladabi da girmamawa suka shiga gaishe ta.       Amsawa take a dake, yayinda idanunta ke a kaina ko kyaftawa batayi, batare data ce musu komaiba ta nunani da ɗan yatsa.       Nazy ce tai saurin faɗin, “Uwargida baƙuwace da jiya muka taimaka a ƙofar gidan wasa, Babu ne kuma ya bamu ƙwarin gwiwar hakan, yakuma sanar mana zai faɗa miki da safe”.          Shiru bata amsa ma Nazy ba, sai takowa da tayi zuwa gabana, da hannunta taimin alamun na miƙe zaune, babu musu na tashi danni tsoro ma ta bani, gata garjejiya da tsaho da ƙiba, kaina a ƙasa murya na rawa nace, “Ina kwana?”.      Karon farko naji muryarta ta amsa mini, sai dai kallon ƙurullar da takemin ne ya sakani jin na takura.         “Ya sunanki? Mikuma ya kawoki nan?”.      Shiru kamar bazance komaiba, wani wanda bansan dashiba ya daka min tsawa, hannu ta ɗaga masa alamar ya bari, niko da naketa rawar jiki sai ta tsugunna gabana tana cemin, “Kinga nutsu faɗamin”.         Tamkar zan haɗiyi zuciyata na mutu dan tsoro nace, “Sunana Bilkisu, ƙaddarar rayuwace kuma ta kawoni nan ɗin”.          Batace komaiba ta cigaba da kallona tsawon sakwanni, sai kuma ta miƙe tana faɗin,  “Ƴar daɓas ku bata dukkan kulawa, tana bukatar hutu koda na kwana uku ne, amma zuwa dare kuzo da ita gidan wasa”.      Da to suka amsa mata cike da ladabi, itako ta fice tana ƙara jin kanta sama.          Tun daga hakan babu wanda ya sake tambayata komai har dare, sune suka sani yin wanka tare da bani kayan sakawa, amma ganin wando da rigane nace musu bana sakawa su bani zani, Har Nazy zatai musu, sai ƴar daɓas ta hanata, siket da riga na wani yadi mai ƙyau suka bani, ba musu na amsa na saka, danni burina daga wannan fitar bazan sake dawowa ba.          Kusan ƙarfe goma na dare muka fita, tsakanin gidan wasan nasu dana kwanta a ƙofar jiya da gidan babu wani nisa, duk wanda yazo saiya saka kuɗi yake shiga, amma mu sai aka barmu muka shige bayan kawai su Nazy sun saka sunansu a wani littafi.      Ƙaton wajene da aka jerama kujeru tamkar aji ko gidan kallon wasan ball, sai ko dima-ɗiman sifiku na kiɗa, ƴammatane bila adadin cikin shiga mai tada hankalin duk wani mai aƙidar tarbiyya, sai maza dake ƙalilan a wajen,       Muma wajen zaman muka samu muka zauna, ni dai sai baza ido nake ina kallon ikon ALLAH. bamufi zaman mintuna talatinba wasa yafara gudana, ni dai sam bammaga abin birgewa a wajenba, amma su sai ihu da sowa sukeyi, wasu suna fita suna liƙa kuɗi.           Abinda yafi bani mamaki shine yanda manyan mata ƴan gayu keta shigowa ɗai-ɗai wajen suna ɗaukar ƴammata, suna fita.     “Mikenan?” Na faɗa a zuciya ba tare da nasan maganar ta fito fili ba.      Nazy dake gefena tace, “Akanmi kike magana Balki?”.      Kallonta nai da tabbacin maganata ta fito fili kenan, banyi nauyin bakiba nace, “Akan waɗanda naga ana ɗauka ɗai-ɗai ana fita dasu nake magana”.      Murmushi Nazy tayi ta ɗauke kanta tamkar bazata amsa minba, kusan mintuna uku harna fidda ran hakan sai naji tace, “Duk wanda kikaga an fita da ita tayi kasuwane, a tsarin gidan wasannan yaune ranar baje kolin haja, wasu daga wannan ɗaukar da za'ai musu sun tafi kenan, dan kuwa sunzama hajiyoyi na gaske masu ƙazaman kuɗi, duk wata hajiya dakikaga ta shigo nan mai ɗunbin dukiyace, acikin abinda zata jiƙaki dashi idan ta ɗaukeki bazai tsunkuli koda kashi ɗaya a cikin goma na dukiyartaba.......”      Maganarta ta katse sakamakon zuwan wata hamshaƙiyar hajiya wajen namu, yanda ta kafeni da ido tamkar wata mayyane ya sani jin faɗuwar gaba, saurin fara karanto “Hazbinallahu wa ni'imal wakil” nayi ina janye idona daga shashensu.       Batace komaiba tai murmushi tana maida kallonta ga ƴar daɓas da tun ɗazun na lura ranta a jagule yake, dan sam bata da walwala ko sukuni, duk wadda tazo kuma inda muke saita ɓata fuska.         Murya a yangance hajiyar ke faɗin, “ƴar daɓas wannan karonma bazaki sallama minba? Na ƙara ruɓanya kuɗin wancan karon sau biyu, harma da ƙyautar mota”.       Shiru ƴar daɓas bata ɗagoba, bakuma tace komaiba, Murmushi naga Nazy tayi tana matsawa jikin ƴar daɓas ɗin sosai, ta ɗago tana kallon hajiyar cikin fari da idanu, “Hajjaju sweetyna ba kuɗin kowa bane a gabanta, nikaɗai nasan yanda nake sarrafa kayata har take ganin babu mai iya matan sai ni, kibar ƙwaƙwa da wahal da kanki a kan kowaccenmu, ɗakin wasannan cike yake da ƴammata masu aji kuma kyawawa, kizaɓi duk wadda tai miki zaki samu da taimakonmu, dan zamu shige miki gaba wajen Uwargida”.         Ajiyar zuciya Hajiyar taɗan sauke tana sake maida kallonta gareni, ina kallonta taima Nazy nuni dani cikin wani salo.        Dariya Nazy tayi, har ƴar daɓas ta ɗago tana kallonta, nima dai kallonta nayi, taimin kallo ɗaya tana ɗauke kanta da faɗin, “Hajjaju mutan makka, banƙi zaɓinki ba, sai dai fa wannan *ƙwai cikin ƙaya* ce, sabuwar hajace da batasan kasuwar da take cikiba, tana buƙatar lokaci kafin a buɗeta Uwargida ta saka cinikinta bayan tamata sabis, kinsan duk abinda Uwargida bata ɗanɗanaba baya shiga a hajar saidawa”.       Wani shegen ƙayataccen murmushi hajiyan tayi, ta ɗaga yatsunta uku da sukasha gwala gwalai tana kaɗawa, “Zan zauna da Uwargida, sannan ku na hannun damartane, inaso ku tayani barbaza manufofi, dan inason samun sabuwa dal a leda wannan karon, a ɗaki zan sakata dindin saboda tsaro, idan har nasamu wannan hajar naimuku alƙawarin kuɗade masu nauyi da ƙyautar mota, tareda kaiku duk ƙasar da kuke buƙata Honeymoon”.           “Zamu gwada, ki bamu kwanaki bakwai kacal”.       Nanma murmushi tayi, ta zaro kuɗi masu yawa a bag ɗinta tabasu.      Sagadada nai da baki ina kallonsu, danni sam ban fahimci dukkan zaurencensu ba, jin an kamo hannuna sai nai firgigit na dawo hankalina, hajiyarce dai, bangama dai-daitaba ta kuma tsunbula tunanina a ruɗani, dan kuwa hannuna ta sumbata tare da kashemin ido ɗaya cikin wani irin salo”.      Ko motsi kasayi nayi, na bita da kallo harta fice riƙe da hannun wata yarinya.                   Dariyar su ƴar daɓas ce ta sani maida kallona garesu, Nazy tace, “Ƴar daɓas da alama fa Balki hajiya ta fara kaita network, irin wannan suman zaune haka”.      Dariya suka sake kwashewa dashi suna taɓawa.          “Dan ALLAH kumin bayani mana?”.      Cikin dariya ƴar daɓas tace, “bakya bukatarsa a yanzu Balkisu, ki kwantar da hankalinki zaki fahimci komai, mudai fatanmu ki riƙe wannan harkar, dan harkace mai cike da ƴanci, babu ruwanki da wulaƙancin wani banza shi namiji, jinsin dake kallonki a ƙasƙance, ya aureki ya kaiki gidansa yana wulaƙantawa, bakida wani muhimmanci saina haifa masa ƴaƴa da gadin gida, wannan kuwa gashin kanki zakici, sai kinso wata ta saka miki zoben mallaka ma”.        Nikam sunma ƙara ruɗar dani, hakan yasa nai shiru ban sake tambayaba.       Muna nan zaune sai da gidan kusan kashi biyu bisa ukun mutanen gidan suka fice, tsurarun mazan wajenma sun ɗauki ƴammata sun fice, muma tashi mukai muka fito domin komawa gida........ _______________________ JAWAAD _______________________     ...............A yau Jawaad bai koma gidaba, bai kuma nema Shahudah ba, dan tun fitowarsa ya fahimci bata kwana a sashen nasuba, hakan ba wani sabon abu bane a wajensa, dan abu kaɗanne zai haɗasu taje takai ƙararshi.           A wannan daren suka tsara abubuwa masu yawa shi da su Hafeez Umar akan kubutar da Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaroba), yanda tsarin nasu yazo komai ya gamsar dasu, dan haka suka kwanta cike da farinciki bayan sun gamawa Jawaad tsiya akan yatashi ya tafi wajen matarsa.      Murmushi kawai yayi, danshi mutumne mai yawan zurfin ciki, bai yarda kowa yasan matsalar gidansaba komai kusancinsa da kai, shiyyasa ko kararsa Shahudah ta kai, idan aka kirasa abinda kawai suke iyaji daga bakinsa shine (ba komai), har ƙannen mahaifiyarsa su Umma bai taɓa zama ya sanar musu matsalar Shahudah ba, sai dai ƴan gidan su Jawaad su kawo musu gulmar.          Jabeer dake gefensa yace, “Boss mufa da gaske mukeyi bazaka kwanar mana ananba, kaje wajen amarya taimaka tausar gajiyar da ka sha yau, mun yafe mata”.      Harara Jawaad ya watsa masa, yaja filo yana kwanciya saman Sofar dake cikin ɗakin tare da zungurin Jabeer da kafa, tashi Jabeer yay a kusa dashi yana dariya da riƙe gefen ƙugunsa da Jawaad ya shura.      Cikin danne abinda ke sukar ransa yace, “Waini korata kukeyine? To babu inda zanje, itace ai tace muyi hirar yaushe gamo”.          Carab Aliyu ya amshe da cewa, “A lallai Shahudah, amaryar tamu mai haƙurice wlhy, mun kwa gode mata, kuma tunda mun fito sai an sake mana sabon biki da bamu ganiba”.       Duk dariya sukayi banda Jawaad daya ɗauke kansa tamkar baisan sunayi dashi bane.....         “Alhaji kayi shiru?” cewar Jabeer yana zungurinsa da biron hannunsa da suka gama rubuce-rubuce”.       Baki Jawaad yaɗan tabe, sai kuma ya tashi zaune yana faɗin, “Kunga kubar wannan shirmen malamai, ya kamata gobe fa kowa yaje yaga iyalansa koda a ɓoyene, kafin komai ya dai-daita”.         Dukansu kallonsa suke da murmushi a fuskarsu, ƙaunarsa na sake shiga musu rai, Aliyu yay karfin halin amsa masa,        “Amma kana ganin babu damuwa Jay? Da kawai an haƙura munbi dukkan sharadin nasu yanda suka faɗa”.          Ajiyar zuciya Jawaad yayi, yace, “Aliy dokarsu ni bata wani dameniba, kawai abinda ya cancanta nake dubawa”.         Kansu duk suka jinjina masa saboda gamsuwa da maganarsa, Hafeez ya miƙe tsaye ya dawo kusa dasu, sai da ya zauna yana kallonsu kafin yace,         “Anya kuwa Jay kana ganin mahaifin Surayya zai bani damar ganinta ita da Suhail?”.          Shiru sukai su duka, kusan sakwan goma Jawaad ya ɗago kansa, guntun murmushi yayi yana dafa kafaɗar Hafeez ɗin, “Karka damu Broth, namaka alƙawarin zan kawo maka Surayya har gidannan itada Suhail, kuma Aliyu da Jabeer hakan inaga ya dace muyi”.       Bai jira amsarsu ba ya tashi ya shige bayin dake cikin ɗakin, duk binsa sukai da kallo a wani irin yanayi mai wahalar fassara.         ★★★★★★★        Kamar yanda yay alƙawari washe gari da safe sai da ya cika, dan kuwa duk sai gashi da matansu da ƴayansu, Aliyu ne kawai matarsa bata haihuba, dan aurensu da wata uku abin ya faru, Jabeer kam da yarinyarsa ɗaya Fatima, sai cikin daya barta dashi ta haifi namiji aka saka masa sunansa.        Hafeez kuma yaronsa ɗaya Suhail.     Sunyi murna sosai da ganin juna, hartakai saida Jawaad yay musu hawaye, zare jikinsa yay shima ya nufi gida wajen nasa iyalin dukda yasan ba lallai ya tarar da abu mai daɗiba. ★★★★★★          Zuwa tashin hantsi Shahudah ta koma normal kamar ba itace keta amai da safe ba, faɗan da mama Atika taimata ne ya tilastata saka doguwar rigar jallabiya baƙa a jikinta, amma sai ƙorafi take wai zafi yamata yawa.        Tun mama Atika na tanka mata har tai banza da ita, a haka gayyar ƴan gidansu suka isketa harda mamansu.     Rungume Shahudah tayi tana murna, takai hannu kan cikin Shahudah tana shafawa.     Ƙwaɓe fuska Shahudah tayi tana wani turo baki, “Momy wai kema kina nufin son cikin kikeyine?”.         Hajiya Humaira ta faɗaɗa murmushinta tana zama saman kujerar dake kallon ta mama Atika ba tare data bama Shahudah amsar maganarta ba.         Mahaifiyarsu ta shiga gaidawa, mama Atika ta amsa, tare da faɗin, “Wannan lalatacciyar ƴar taku saikun saita mata zama akan wannan cikin, inba hakaba wlhy zata ɓata komai”.       Wani guntun murmushi Hajiya Humaira tayima mama Atika, “Mama manta da batunta, zamuyi maganar daga baya, idan kuma bataso ai sai a zubar ko”.      Kafin mama Atika ta bada amsa Shahudah tai carab ta cafke maganar, “Yauwa Momy na, ashe kin gane, dama nasan kekam zaki bani goyon baya, kuma zaki saka wancan uban taurin kan Jawaad ya yarda akan hakan, danni a tsarina saina shekara goma gidan miji zan haihu, shima ƴaƴa biyu kawai nake bukata, mace ɗaya namiji sun wadatar dani, idan son samunema na haifesu ƴan biyu kawai, kunga shikenan”.      Babu wanda ya tanka mata a wajen sai Hajiya Humaira da tace, “Tsarinki mai ƙyaune mamana, kuma ni na amince dashi”.       Wannan magana ta Hajiya Humaira taima Shahudah daɗi, saitaji zuciyarta ta samu nutsuwa, tunda mahaifiyarta ta bata goyen baya ko Jawaad bai isa hanata yin yanda tasoba.       Babu wanda ya sake tada zancen har washe gari, sundai aika kiran Jawaad da daddare aka iske bai dawoba, hakan yasakasu fahimtar bazai kwana a gidaba kenan.         Yau ma Shahudah a sashen mama Atika ta kwana, duk da taso ta koma sashenta sai mama Atikar ta hana gudun kar Shahudah taje ta aikata musu ganganci akan yunkurin zubar da cikin, dan tunda ta ambata to zata aikata kuwa.       Motar Jawaad na shigowa family house ɗin ana kaima mama Atika labarin dawowarsa, hakan yasa ta aika a kira matashi, amma saiya maido ɗan aiken da saƙon yana zuwa kawai.         Sunta zuba idon ganinsa amma sukaji shiru, har kusan awa biyu da rabi sai gashi..........✍🏻 https://youtu.be/6YuGtf5lQF8 Maza garzaya domin sauraren cigaban littafin *KARAYAR ARZIƘI*  Na Bilyn Abdull a *MANHA HAUSA NOVEL'S*. Ku danna Subscribing domin nuna ƙaunarku garemu, tare da ƙararrawar sanarwa dan samun shirye-shiryenmu a duk lokacin da muka ɗora. MANHA HAUSA NOVEL'S (Ƙyautar ALLAH). *takuce, kuma natane, ta hanyar kasancewa da itane zamu sake tabbatar da wanene yafi son wani😉👌🏻😻😻😍😍🥰💃🏻 Page 13 .............“Alhaji akwai matsala fa”.        Jikin Alhaji lado na ɓari yace, “Yallaɓai matsala kuma? Akan mi? Yarinyarce ta gagareku samune ko yaya?”.        “Alhaji ba wannan bane, yarinya kam muna kan nemanta, insha ALLAHU kuma zamu sameta, matsalar danake faɗa akan ɗanka take, harbine a damtsen hannunsa, binciken likita ya tabbatar mana kuma jami'an tsarone suka harbesa a wajen, kuma da alama harbin anyisane bayan awa goma sha ɗaya kafin faruwar rigimarsa da yarinyar, lallai idan labarin nan yaje kunnen manyanmu reshe ne zai juye da mujiya, komai kuma zai iya ɓaci”.       Zufar data jiƙa alhaji lado yasa hannu ya sharce, harshensa har sarƙewa yake yace, “Yanzu miye mafita?”.         “Shine nima abinda na kasa haɗawa a raina gaskiya”.        Alhaji Lado yay shiru yana kallon ɗan sandan, sai buga hannunsa daya dunƙule yake cikin ɗayan, cikin taune leɓe yace, “Ni ga tawa shawaran”.       “Ina saurarenka Alhaji”. ‘Cewar ɗa sandan yana kallonsa’.       “Mizai hana shi likitan mu ƙara masa kuɗi ya rufe zancen da dabarunsa, dan gaskiya inason a kamo wannan yarinyan, cikin abokansa sun tabbatar min akwai abinda yarinyar tagani a ɗakin my son kwana bakwai da suka shuɗe, kwana biyar kafin faruwar wannan abun kenan, sannan rashin kamata barazanane a garemu baki ɗaya”.       “To Alhaji ka kawo shawara mai ƙyau, sai dai matsalar da nake hasashe kar yazam waɗanda suka harbi yaronka sun san fuskarsa ko wani abu dangane dashi, hakanne kawai zai kawoma shirinmu rashin tasiri”.       Nanma shiru Alhaji Lado yayi, zuwa wani lokaci ya saki wani nishi da ƙarfi, gaba ɗaya ya rasa wane irin tunani kuma zaiyi, yana ƙaunar Jazuli, sam baya buƙatar rasashi, gashi dama har yanzu baima farfaɗoba cikin hankalinsa, dan sosai bugun da Bilkisu tai masa akai ya shigesa har can cikin kansa.      Basu samo mafitaba a wannan zaman, hakan yasa Alhaji lado yace ɗan sandan ya bashi lokaci zuwa safiya zaiyi tunani akai. _________________________ JAWAAD _________________________ ............Da sallama ya shigo falon, Shahudah da mama Atika dake zaune duk suka zuba masa idanu, yana sanyene da ƙananun kaya farare tas gaba ɗaya, duk da bana kwalliya bane yayi ƙyau abinsa, ga wani annuri da cikar haibar kwarjininsa na fitowa a fuskarsa.       Babu walwala a kan fuskar tasa, ya risina yana gaida Mama Atika.     Cikin fara'a ta amsa masa tana tambayarsa ya aikin nasa, ta kuma ɗora da ƙorafin rashin zuwansa gaidasu a koda yaushe.      Haƙuri kawai ya bata yaja bakinsa yay shiru, bai ko kalli inda Shahudah takeba, ita kuma ALLAH bai bata tunanin tako gaidashiba.       Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna da basu gaza uku ba, kafin sallamar Uncle Uwaisu ta katse musu tunani.      Yana zama Uncle Bashir shima ya shigo, dan haka Jawaad yay musu gaisuwa a tare cikin girmamawa.          Sai da suka kammala gaishe-gaishen nasu, suma sukai masa ƙorafi akan rashin ganinsa akai-akai, kamar yanda ya saba dai haƙurin ya basu suma da tabbatar musu da yanayin aikinsane ya kawo hakan.        Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shiyyasa suka saki wancan zancen suka tsunduma maganar data tarasu game da ƙararsa da Shahudah ta kawo.        Hakan ba sabon abu bane a wajensa, shiyyasa baice uffanba har suka kammala, itama Shahudah aka sata ta maimaita komai daya faru.        “Jawaad kaji abinda matarka tace, shin hakane? kokuwa akwai kuskuren fahimtarta a ciki?”.         Guntun murmushi Jawaad yayi, cikin nutsuwarsa yace, “Uncle ni dai gareni babu komai, amma tunda ita na mata ba dai-daiba tayi haƙuri, akan rashin sanine”.          Dukansu sagade sukai suna kallonsa, duk da dama a koda yaushe irin wannan zaman ya haɗa amsar da yake basu kenan sai ta yau tafi ƙona ransu, a ɗan fusace Uncle Uwaisu yace, “Jawaad ka daina mana wani ɓoye-ɓoye akan abinda ke faruwa tsakaninka da matarka, mu dai iyayenkune ku duka, bamajin daɗin yawan matsalolin dake kunnowa a cikin aurenku, gashi kai kullum akazo irin wannan zaman sai kace batai maka komaiba, anya kuwa gaskiya kake faɗa?”.          “Uncle gaskiya nake faɗa, da tamin wani abu dana faɗa ɗin......”       “Wlhy ƙarya kake bb, ban maka wani abuba kake cewa kayi nadamar aurena, wai harma bazaka taɓa yafema kanka hakanba”.       Banza Jawaad yay mata bai tankaba, yayinda su Mama Atika suka zuba masa ido suga idan zaice wani abu, amma sai sukaji yaƙi cewa komai.         “To kaji abinda tace Jawaad”.      Uncle Bashir ya faɗa yana kafesa da idanu.       Kamar Jawaad bazai amsaba sai kuma ya gyara zamansa yana kallon Uncle Bashir ɗin, “Uncle wannan zancentane kawai, ita tasan a inda ta samoshi”.        Gaba ɗaya ba ƙaramin haushine ya turnuƙe zukatansu ba, musamman ma Shahudah da kamar zuciyarta zata babbake dan baƙin cikin murɗaɗɗen halin Mijin nata......       Mama Atika tai ƙarfin halin haɗiye nata ƙududun tana ƙaƙalo murmushin yaƙe, “To shikenan yanzu duk abar wannan maganar tunda yace shi babu komai, sai kuyi musu nasiha suyi haƙurin zama da juna kamar yanda kowa ke zaune a nasa gidan, ni dai zan faɗi maka albishir mai gidana Jawaad”.          Ɗago manyan idanunsa da suka sake girma saboda ɓacin rai yay ya kalli kakar tasu, sai dai baice komaiba.     Ta faɗaɗa fara'ar ta tana cewa, “Matarkace ke ɗauke da cikin wata ɗaya da wasu kwanaki”.         Kafeta da ido Jawaad yayi, sai kuma ya janye ya maida kan Shahudah, baka isa fahimtar farin ciki yayi ba kokuwa baƙin ciki.......      Shahudah ta katse masa tunani da faɗin, “Nifa kuma bar lasa masa zuma a baki Hajiya, dan wannan cikin zan zubdashine, dan yazo ne akan kuskure, sainan da shekaru tara zan sake amsar waninsa, lokacin mun cika shekara goma da aure.......”      Cikin Hanzari Uncle Uwaisu dake kusa da ita ya kai mata duka, kaucewa tai tana kumbura baki.        “Wai miyasa baki da hankaline shin Sabira?, mike damun tunaninki ne?......”          Murmushi Jawaad ya saki yana katse Uncle Uwaisu da faɗin, “Uncle barta, tanada gaskiyarta itama, haka muka tsara ba yanzune zamu haihuba saboda gudin karmu tsufa da wuri, “Hudah nawa kike buƙata dazai isheki ganin likitan da zai zubda cikin?”.        A matuƙar razani duk suka kalleshi, banda Shahudah da daɗi ya lulluɓe, babu kunya ta taso daga wajen zamanta ta faɗa masa ajiki tana ƙanƙamesa, dukda yaji kunyar hakan saiya basar shima yaɗan rungumota yana bubbuga bayanta, ɗago kanta tai ta sumbaci goshinsa da laɓɓansa, tana niyyar kissing ɗinsa ya kauda fuskarsa da ɗan tureta kaɗan a jikinsa.      Wannan abu yabama su Mama Atika matuƙar kunya, dan haka duk suka kauda kansu garesu, Shahudah kuwa ko a jikinta, neman ma ɗare cinyarsa take zata zauna yay mata gargaɗi da idanu.        Matsawa tai tana wata siririyar dariya da faɗin, “Bb har yanzu baka wayeba, ai dai matarkace ni balle ace munyi abu mara ƙyau, tunda komai ku hausawa a wajenku baida ƙyau.......”.          “Kinci gidanku Sabira”. ‘Uncle Bashir ya katse Shahudah cikin mata daƙƙuwa’ yaci gaba da faɗin, “Ke yanzu da ƙaniyarki a gabanmu kike faɗar wannan maganar?”.         A hannun kujerar da Jawaad yake ta zauna tana dariya, ta maƙale damtsen hannunsa tana ɗora kanta ta kwantar jikin hannun.      Ko motsi Jawaad baiyiba, ya kuma fuske abinsa kamar ba shi ta kwantama a jikiba.         Rashin mutuncin Shahudah ya wuce dukkan tunanin su mama Atika, dan haka suka ɗauke kansu akanta.        Mama Atika tace, “Kai yanzu nan Jawaad da hankalinka zaka biye mata ku zubda ƙyautar da ALLAH ya baku? Wane irin banzan aƙidane wannan? Ku ba'a haihuwa aka haifeku ne?”.         “Kiyi haƙuri hajiya, ni karkuga laifina, Hudah itace mai ɗauke da cikinnan, sannan itace zata haifesa, ta rainesa, ta bashi tarbiya, to taga bazata iyaba ni mizaisa na takurata, bayan kuma ƴancintane zaɓama kanta duk abinda taga ya dace da ita, inhar batason ta haihu yanzu zan goya mata baya ta zubda cikin, idan kuma zata haifesa zanfi kowa jin daɗin hakan,duk shawarar data tsaida ta sanarmin”. Ya ƙare maganarsa da ƙokarin cireta a jikinsa ya miƙe, “Kuyi haƙuri bara naje, dan nanda awa biyu zan sake fita, inason naɗan huta kafin lokacin”.       Babu wanda ya iya cewa komai sai Shahudah da tai tsigil tana faɗin, “Bb jirani mu wuce”.        Tsayatan kuwa yayi, ta shiga ɗakin Mama Atika ta ɗakko wayarta ta fito, a gabansu Uncle Uwaisu Jawaad ya kama hannun Shahudah suka fice abinsu”.        “Turƙashi”. ‘Mama Atika ta faɗa cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya’.      Daga Uncle Uwais har Uncle Bashir babu wanda ya iya cewa komai, dansu lamarin yafi ƙarfin tunaninsu.          A wannan yanayin Hajiya Humaira ta shigo ta iskesu itama..... ★★★★★★          Suna shiga Sashensu Shahudah ta maƙalƙale Jawaad tana dariya.          “Nagode ALLAH da yau ra'ayina yazo dai-dai da naka bb na, ina sonka harma babu adadi”.      Wani munafikin murmushi ya saki shima ya rungumeta, murya can ƙasan maƙoshi yake faɗin, “Duk abinda matata takeso nima shi nakeso, kuma tsarinki ya birgeni tawajena”.         Da sauri Shahudah ta ɗago kanta ta manne bakinsu waje ɗaya, babu musu Jawaad ya amsheta hannu biyu, tun a falon labari yaso fara canja salo, da ƙyar ya iya ɗaukarta ido rufe suka haura sama. 😉ni dai a falo nai zamana gudun gano abinda malam ya hana😂⛹🏻‍♀️.             Jawaad ya sumbaci goshin Shahudah dake jikinsa a lafe bayan lafawar komai, shi shaidane akan ƙoƙarinta na bashi dukkan farin ciki a makwancinsu, halayyarta da tsarintane kawai matsalarsa, dan ba mu'amular kwanciya kawai ya dace mace ta ƙware wajen mijinta ba, akwai wasu farin cikin dake girmama danƙon zaman lafiya da ƙarfafa soyayya ga ma'aurata, mafi yawancinsu a kula da gidan ma ake samunsu.        Sake matseta yay cikin jikinsa yana lumshe idanunsa alamar sonyin barci........ _______________________ BILKEESU _______________________ ...........Har muka shigo gidan zuciyata da tunanina basu gaza wajen cuɗanya game da gidan dana tsinci kainaba, kamar yanda na saba na ɗauro alwalar barci, har zan kwanta sai zuciyata ta bani ƙarfin gwiwar miƙa kukana wajen UBANGIJI, hakkane yasa na shinfiɗa ɗankwali na kabbara salla.       Ƴar daɓas da Nazy basa ɗakin, bansan ina suka maƙaleba duk da tare muka shigo cikin gidan.        Ina cikin salla naji shigowarsu, duk da hankalina ba a kansu yakeba kusan mintuna biyu da shigowar tasu sai nakeji wani nishi-nishi tamkar wasu mayu sunga nama.       Koda nai sallamar sallata ban kallesunba, saina sake miƙewa na kabbara wata sallar, kafin na idar ne abin nasu yay ƙarfin da har waswasi ya fara min kutse cikin sallata, takaitawa nai nayi sallama dan son ganin wane hali suke ciki? Ni duk tunanina ko wanine baida lafiya a cikinsu.           Cikin matuƙar razana da firgita na ƙwalla ƙara, kafin wani lokaci jina da ganina duk sun gushe.            Ƴar daɓas taɗanyi ƙoƙarin janye Nazy dake mamuƙe da ita dan bama bilkisu ɗauki, amma sai Nazy ta sake matseta tana mata wani salon sheɗancin da ya sata maida hankalinta gareta, cikin narkewar murya Nazy tace, “Barta Sweet, ta firgitane kawai saboda bata taɓa ganiba, a haka harzata saba itama ta fara sha'awar abun a ranta” bata bari ƴar daɓas ta bata amsaba ta haɗe b....... (Wa'iyazubilla) kaicon wannan mummunar rayuwa al'ummar MANZON ALLAH, yanzu waɗanan fa sune har suke iya bugar ƙirji su kira kansu cikakkun musulmai masu jiran samun aljanna😭, sune suke buƙatar addinin musulunci yay alfahari dasu matsayin al'ummarsa?😭 sune suke buƙatar ƴaƴa suyi alfahari dasu matsayin iyaye😭 ya rabbi ka wajabta mana tsoronka a zukatanmu, ka hanamu shagala da duniya da kayan cikinta, ALLAH ka rabamu da asararriyar rayuwa mara amfani😭😭😭😭🙏🏻🙏🏻. ★★★★★★           Ban tashi farkawa ba sai da zafin rana ya fara dukan fuskata, na buɗe idanu da ƙyar, inda na ganni kwance ya sani tashi zaune a firgice saboda tuna abinda ya faru jiya, waige-waige na farayi a cikin ɗakin, ganina ni kaɗai a cikine ya sakani sauke numfashi ina share hawayen da ke ziraromin, abinda na gani a daren jiya ne kawai ke dawomin cikin idanu da zuciya......        Shigowar Nazy ɗakin ya saka gabana faɗuwa, nai saurin duƙar da kaina saboda wata kunya data kamani, sukuwama da suka aikata ko a kwalar rigarta.        Ina jiyo sautin murmushinta ta zauna kusa dani, “Oh Balkisa minene damuwarki? Idan abinda kika gani jiyane karya dameki Please, wannan shine ƴancin ai, ki gwada harkarnan zakiji daɗinta, uwa uba zakiyi arziƙi, ki zama hamshaƙiyar mace abar kwatance a duniya, dan yanda ALLAH yay miki jiki mai ƙyau ɗinnan wlhy abincin manyan hajiyoyi zaki zam.......”        “Wa'iya zubillah” na faɗa a fusace ina zazzaroma Nazy idanuna da sukai jazur, ga hawaye na kwarara a cikinsu, cikin nunata da ɗanyatsa nake cigaba da faɗin, “Karki sake danganta ni da wannan shaiɗancin mai gusar da imani, ina roƙon UBANGIJI na ya shiryeku, kuma zukatanku su buɗe, tunaninku ya fara gudana akan bigiren gaskiya, kukuwa wace amsa harsunanku suka tanada wajen bama UBANGIJIN al'arshi aranar da gaɓɓai ne kawai zasu bada amsa ba bakuna ba? Wa kuke taƙama dashi da zai tsaya muku a ranar da rana take gab da ƙwakwalen mutane? Wani ƙwarin gwiwa kuke dashi na gujema makoma irinta mutanen ANNABI LUƊU da suka gushe akan wannan mummunar ɗabi'ar? Wace amsa gareku akan iyayenku da sukasha wahalar baku tarbiyya bayan ɗaukar ciki da haihuwarku zuwa ciyar daku har kuka kai wannan munzalin girman? Wace amsa gareku ga al'ummar daular musulinci da kuka fito a ciki? Tayaya kuke tunanin akan alfahari da MANZON ALLAH zaiyi daku kasancewarku al'ummarsa? Kaicon wannan Rayuwa ta dabbanci, kaicon wannan buri mara amfani, kaicon wannan duniya mara dorewa, kaicon dukiyar da zata zamewa mamallakanta dana sani, kaicon rufaffiyar zuciyar da bata banbance ƙyaƙyƙyawa da mummuna, kaicon sha'awar dake tunzura zuciya bisa ɗabi'ar aladu, inama na tsaya ƴan sanda sun kamani, da inada ilimi akan sanin tarar daku a ƙaddarata dana roƙi UBANGIJINA ya ɗauki ruhina kafin zuwana gareku.......” Ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurarenta, harshenta ya sarƙe ta kasa cigaba da magana.        Kan ƴar daɓas dake bakin ƙofa tsaye da wasu ƴammatan gidan kusan su shida duƙe saboda wani irin rawa da zucikatansu keyi akan kalaman bilkisu, ita kanta Nazy tsigar jikinta sai tashi takeyi........        Da sauri suka waiga bayansu saboda jin gyaran muryar Uwargida, babu wanda bai ruɗeba a cikinsu da ganinta, dan ɓacin ran dake fuskarta kawai ya isa tabbatar musu da taji komai akan kalaman Bilkisu, darewa sukai biyu suka bata hanya, cikin takunta na izza da bushewar zuciya ta tura kai cikin ɗakin....       Wani wawan mari ta sauke mani a fuska, na ɗago a razane ina kallonta, saukar wani na sakeji, kafin na dawo dai-dai an kuma saukemin wani, tun ina fahimtar adadin marukan har ruɗani ya sani gaza fahimta.       Jinai kawai an sungumeni anyo waje dani, ina kuka da roƙonta amma taki saurarena, ta wata ƙofa dake a cikin gidan tabi dani, ashe gidane mai ƙyau a wajen, wanda shine matsayin sashenta.      Ban damu da kawatuwar gidanba, burina kawai sauka daga jikinta na samu hanyar kuɓuta.      Wani makeken ɗaki daya jiƙu da kayan more rayuwa ta kaini, ta jefani bisa bankeken gadon ciki wanda tashin hankalin da nake ciki bazai barni lissafa muku haɗuwarsa ba..............✍🏻 Page 14 ..............Kusan a tare suka farka da ga barcin da ya kwashesu, sai dai yanda Shahudah taci karo da fuskar Jawaad sai zuciyarta ta shiga yimata wasuwasi.       Ya sauka a kan gadon ba tare da yace da ita uffanba, bayi ya shiga, ta miƙe da sauri tabi bayansa, sai dai a mamakinta ya rufe ƙofar bayin.      Ɗan bugawa tai kusan sau uku, yanajinta lokacin yana ƙoƙarin haɗa ruwan wanka amma sai ya shareta kawai tamkar bai jiba.        Dole ta haƙura saboda motsin fara wankanta da tajiyo.       “Mike damunsa kuma?” ta faɗa a fili cike da mamaki, kujerar gaban mirror ɗinta taja ta  zauna, bayan wasu mintuna kusan ashirin sai gashi ya fito yana tsane jikinsa da towel.         Yanzun ma dai fuskar babu walwala, bai kuma kalli sashen da Shahudah takeba ya wuce wajen kayansa, jallabiya ya ciro a drawer, ya juyo zai saka suka haɗa idanu da Shahudah data kafesa da idanu.         Janye nasa idon yayi  kamar bai ganta ba, saida ya saka jallabiyar a jikinsane ya ƙaraso gaban mirror ɗin yana ɗaukar turare zai fesa.      “K bazaki tashi ki wanka ba kizo kiyi salla?”.        Shiru kamar bazata tankaba, sai kuma ta sauke numfashi tana miƙewa, gabansa ta matso kamar zata shige jikinsa, ya ɗan matsa baya kaɗan yanda zasu sami tazarar data matse.      “Humm” ta faɗa cikin kafesa da ido, muryarta a raunane tace, “Bb yanaga ka canja daga tashinmu? Naga cikin farin ciki muka shigo gidannan”.       Turaren hannunsa ya ajiye, ya juya zai tafi ba tare da ya bata amsaba, saurin riƙo hannunsa tayi, bai juyoba, sai dai a hankali ya furta, “Karki ɓatan lokaci salla zanje”.      Dole ta sakar masa hannu saboda fisgar da yayi, harya fice tana binsa da kallo.          A tsakkiyar falon ƙasa ya tsaya, ba tare da ya kalli ko inaba a cikinsa yace, “K fito, idan kuma kika bari na fito dake wlhy saikin raina kanki”.             Mamaki ya kamani, dan ni dai bilynku banga alamar mutum a falonba, amma maganar Jawaad ta sakani waige-waige, a raina ina tunanin ko aljani ya gano.         kamar da wasa kuwa saiga ɗaya daga ƴammatan gidan ta fito daga ƙasan bene jiki na rawa.         Fitowarta yay dai-dai da sakkowar Shahudah da tai tunanin Jawaad ya fice.       Jikin Amrah sai ɓari yakeyi, dan batasan ta yaya Jawaad ya ganta a falon ba, tunda ta rigasu shigowa shi da Shahudah.          Juyowa yay ya kalleta da rinannun idanunsa masu firgitasu, yay mata kallon sakwan biyu ya janye yana kallon Shahudah dake tsaye jikinta sai tsuma yake dan tsoro, dan batai tunanin Jawaad zai ga Amrah ba.        Murmushin takaici ya saki launin idonsa na sake yin duhu, ya nuna kansa cikin ɗacin da yakeji a zuciyarsa yana faɗin, “Ni kika kirama wata taga yanda zanyi kwanciyar aure da ke Hudah? Saboda kawai ki burgesu akan ina miki duk abinda kikeso ko? To gata nan, saiki zauna kafin na dawo massalaci ki ida sanar mata duk abinda ya faru a cikin ɗakin da bata ganiba”.        Ya maida kallonsa ga Amrah itama, tana tsaye tamkar zatai fitsari a wajen dan firgita,  “K kuma yanzu nasan kin yarda inabin dukkan abinda takeso ko? Tunda na amince mata ta zubar da ciki, ta kuma gigitani da salonta a gabanki wanda yasa nake koma mata soko” yay murmushi irin mai nuna tsantsar takaici ɗinnan, kasa cigaba da musu magana yayi ya juya ya fita zuwa massalaci.             Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro a fuskar Amrah, lallai taji kunyar abinda ta aikata yau, takuma yi nadamarsa, bata san miyasa ta biyena Shahudah ba, yanzu da ace Yah Jawaad ɗin bai farga da itaba ya kuma biyema Shahudah a falo ɗin tamkar yanda taso da ta kasance azzaluma, dan dafa sai taga komai na sirrinsu.......        Dafa kafaɗarta da Shahudah tayine ya katse mata tunani, ta kalleta cikin takaici tana janye hannunta.      A zatonta zataga nadama a idanun Shahudah akan abinda sukaso aikatawa, amma sai taga saɓanin hakan.      Cikin dariya Shahudah tace, “Wai wannan faɗan nasa kikema kuka? Tab amma baki da wayo, mutumin da a gabanki ya komamin ƙaramin yaro shine mazuransa yanzu zasu ɗaga hankalinki, wlhy naso ya biyemin kiga abin dariya, ashe shegen idonsa ya hangoki, ni........”       A harzuƙe Amrah ta ɗagama Shahudah hannu, “Ya isheki haka malama, ni wlhy bamma san bakida wayoba sai yanzu dana dawo cikin hankalina, bansan miya lulluɓe ganina ba har na iya yarda naga abinda zan shekara dubu ina nadama, Shahudah wannan ba wayewa baceba, dan ALLAH ki dawo akan ƙyaƙyƙyawan tunani na mutanen ƙwarai masu riƙo da addinin ALLAH, yanzu dan kawaifa ki birgeni kika jawoni nazo na laɓe dan naga yanda kike maida Yaya Jawaad kamar ba shiba a shinfiɗa, sirrinku, innalillahi, na shiga uku ni Amrah, wlhy naso tafka kuskure kam yau a rayuwata” da gudu Amrah ta fice daga falon tana kuka.           Shahudah da jikinta yaso yin sanyi, amma zuciyarta dake ɗorata a shawarar banza tai saurin bijiro mata shaiɗaniyar shawarar da take bata sai tayi dariya tana taɓe baki, a fili tace, “Sun wani damu mutane da maganar sirri-sirri, uwarmiye sirri anan? Waima shegiyarnan Amrah da BF yafi talatin a cikin wayartace take faɗar kallonmu ni da Bb zaisata na dama, Mtsoooww aikin banza kawai, ni wlhy dama nayi mamakin yanda ya biyemin cikin sauƙi, mutumin da idan ina bukatarsa sai ya gama yanƙwalani kafin ya bani haɗin kai, amma ɗazun dandanan sai gashi ya miƙa wuya kamar yau ya taɓa sanina, munafiki kawai”.     Ta ƙare maganar da juyawa ta koma ɗakinta.         ...................................................             Dukkan abinda ya faru tsakanin su da Jawaad sai da suka sanarma Hajiya Humaira mahaifiyar Shahudah, ba karamin tashin hankaline ya risketa ba jin wai Jawaad ma ya bama Shahudah goyon bayan ta zubar da ciki.     To mi kenan? Mi yake nufi? Bayason ya haihu da ita ko kuwa haihuwarce gaba ɗaya baya so?.     Basu da mai basu amsa, shiyyasa suka shiga dogon tunani wajen tattaunawa da juna, harma suna tunanin ko dai Jawaad raina musu wayo kawai yakeyi, anya kuwa baisan wani abuba game da shirinsu akan sa?.       Gashi ALLAH ya basu lusarar ɗiya da bata fuskantar komai na rayuwa sai wawanci, dolene susan abinyi akan Shahudah kafin ta aikata zubar da cikin nan, su kuma sake taku akan murɗaɗɗen halin Jawaad da duk bin ƙwankwantonka baka isa gane inda ya dosa ba kai tsaye. .................................................          Bayan an idar da salla ne Jawaad ya shigo gidan, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, shirin fita yayi, bai wani jimaba ya fito riƙe da takardu guda biyu a hannunsa.      Ɗakin Shahudah ya shiga da sallama a ƙansan maƙoshi, bata amsaba, dan dama can ita bama damunta sallamar tayiba, idan kuma anyi mata bai zamar mata tilas ta amsa ba.        Tana tsaye cikin ƙananun kaya sket da riga masu ƙyau, yanda sket ɗin yake har ƙasa ne ya tabbatar masa da shirin fita takeyi, dan sam Shahudah batajin kunyar fita anguwa daduk suturar data tare gabanta, indai ka cire waɗanda tasan sunyi ƙananu da yawa, amma ita dan ta saka wando da riga ma ta yana ƙaramin gyale wannan ba damuwarta bane, a ganinta ai tayi shigar mutuntawa ma.      Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, dan haushin abinda yay mata gaban Amrah ya sata jin haushinsa.      Shima halin ko in kula ya nuna a kanta, ya ajiye takardun hannunsa saman tebirin gaban gadon tare da biro a tsakkiyarsu.     Dukda ta gani sai bata kula saba, jakkarta ta rataya a kafaɗa fuska a ɗaure tace, “Ina kuɗin zanje wajen Doctor, dan wannan cikin yau bazai kwana a jikina ba”.        Bakinsa ya taɓe yana mata wani kallon banza, yay taku biyu gira ɗaya a ɗage yana jan tsakin da ya shigar mata har ƙasan zuciya.        “A tunaninki nima wawane irinki? a haukarki na yarda a zubda cikin ne da gaske? To lallai har yanzu ke bagidajiyace inhar maganata a gabansu zaisa ki aminta da ni har haka, Hudah! gane ainahin Jawaad abune mai matuƙar wahala ga kowa, ko ke da kikai kusanci dani na kusan watanni takwas baki iya fara nazartar komai game daniba balle su, hhhh tunanin Jawaad kullum banbanta yake da na kowa, wannan takardun biyu, ɗaya ta cak ɗin kuɗi ce, ɗaya kuma babu komai cikinta tana jiran abincine. Idan har kina kan bakanki na zubarmin da ciki bazan hanaki ba, ki faɗi adadin kuɗinma da kike buƙata zan rubuta miki kije ki zubar, ammafa zaki zubar da shine bada igiyar aurena a kanki ba, idan kuma kin shirya barinsa ki haifa kinada lasisin cigaba da rayuwar aurene da Muhammad Jawad Abdul-Aziz yusif kenan. zaɓi ya rage naki, kafin na dawo sai naji bayani akai”.     Yana gama faɗa yay ficewarsa ya barta tsaye tamkar wata gunki........ _________________________ BILKEESU _________________________      ............Hanunta da ya sauka jikinane ya saka duhu mamaye ganina.            Yanda Bilkisu taja wani nannauyan numfashi lokaci ɗayane ya saka Uwargida dake a fusace kallonta, hannunta ta janye da ga ƙirjin bilkisun tana maidawa saman fuskarta, sam bata numfashi.      Uwargida taja tsaki tana sauka a gadon, ruwa mai sanyi sosai ta ciro a ƙaramin firij ɗin dake ɗakin ta ɓalle murfin ta watsama Bilkisu.        Nannauyan numfashi Bilkisu tayi.           Na buɗe idanuna da ƙyar bayan fitar numfashi na daya fara nisa daga gangar jikina, akan Uwargida dake gabana tsirara na saukesu, nai saurin maidawa na rufe jikina na wani azabar rawa, jin motsin zata sake dawowa kaina ya sani tashi cikin azama ina matse jikina da kare ƙirjina da ta yaga rigar ya fita fili.         Cikin muryarta mai razanarwa tace, “Wacece ke? Waya turoki cikinmu?”.         “Wlhy babu wanda ya turoni gareku sai ƙaddadarar rayuwa, dan ALLAH kirufamin asiri ki barni na tafi, wlhy bana buƙatar aikata wannan abun a rayuwata, na miki alƙawarin har duniya ta tashi babu maijin sirrinku a bakina hajiya”.        Wata dariya ta saki tana matsowa jikina, murya ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa take min magana, “Ƴammata waya gaya miki muna tsoron sirrinmu ya fitane? Hakan ba matsalarmu bane, kisa a ranki kamar yadda ƙaddara ta kawoki cikinmu itace zata wajabta miki zama damu, kina da sura mai ƙyau da zaki mori lokacinki, matana biyar dana aura, nakumayi alƙawarin daga su bazan sake auren kowaba, sai dai ɗanɗano, amma ganinki yasa naji alƙawarina bazaiyi tasiriba, dan tun jiya dana ganki kika kwantamin a rai, da tsantsar kwaɗayinki na kwana a daren jiya, ki kwantar da hankalinki zan jiyar dake daɗi, tare da mallaka miki dukiya mai tsoka da saikin wucema tsaranki. Sonki da nake na gaskiya zai hanani yimiki fyaɗe, duk da kuwa kin ɓatamin rai da maganganun da kike faɗama yarana, da watace bakeba yau ta aikata hakan wlhy saina kasheta, amma ke bazanyi hakanba, bakuma zanyi mu'amula dake ta ƙarfiba, zan biki a hankali harki saki jikinki dani kema ki soni, dan haka daga yanzu kin dawo zama sashena”.         Rumtse idanuna nayi da ƙarfi hawaye masu zafi dana tara a cikinsu suna rige-rigen fitowa, ta janye jikinta daga gareni tana sauka, riga mai igiya naga ta ɗauka ta sakama jikinta, ta buɗe ɗakin ta fita tana faɗin, “Ki buɗe drawer ɗinnan duk nau'in kayan da kike buƙata zaki samu a ciki, karna dawo na sameki kina wannan kukan, dan na tsani kuka, sunana Uwargidan farin ciki, burina kullum na saka duk wanda ya raɓeni farin ciki kawai”.        Harta gama ɓaɓatun ta ta fice ban kalletaba, na kwashi kusan mintuna goma ina kukan nawa tare da sambatun yanda kullum duniyata ke garawa da sabon salo mai saka ruɗani, maimakon haske kullum duhu nake sake gani, maimakon fahimta kullum toshewar basira nake sake gamo dashi, maimakon canji kullum tsanani nake sake gamo dashi, maimakon cigaba kullum ci bayane yake zoma rayuwata, shin haka rayuwata zata ƙare kenan?. Na sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, jinake tamkar nama kashe kaina kozan huta ne.               Ban sake ganinta ba, dan bata sake shigowa ɗakinba, ni kaɗai na wuni a cikinsa, nayi yunƙurin fita amma naji an kulleni ta baya, sai wajen ƙarfe biyu wani saurayi ya kawo min abinci, ni bamma taɓa ganinsa a gidanba, baimin magana ba ban masaba, ya ajiye ya juya ya fita abinsa, inaji ya sake kulleni ta bayan.        Ko kallon inda abincin yake banyiba, danni yanzu komai na gidan ƙyankyaminsa nakeyi wlhy, tunda nasan kuɗin siyen komai ta hanyar wannan ƙazantar suka sameta.       Gadonma tuni na sakko na dawo ƙasa na zauna, amma sanyin tayis dake shigata yasa na kasa jurewa na miƙe na koma saman gadon na zauna.          Yunwa da ƙishirwa duk sun gallaba mini, rabona da abinci tun jiya da safe da su ƴar daɓas suka takurani naci indomie ɗinsu.     Babu abinda ke tadani zaune sai salloli, har zuwa dare kuma ban sake jin motsin kowa ba a gidan, sai bayan isha'i saurayin ya kuma kawo min abincin dare, ya ɗauki kwanikan rana zai fita dasu sai yajisu da nauyi alamar banci abincinba.     Ya ɗan kalleni da mamaki, kamar zaiyi magana sai kuma naga ya share, ya ɗiba kwanikan ya fita abunsa..      Na darenma da ya kawo ƙin ci nayi, haka na kwanta abina da yunwa, dan harna fara sallar dare rashin ƙarfin jiki ya sani komawa na kwanta, dan nakasa tsaiwar, na komayi a zaune shina saina fara ganin jiri, dole dai na haƙura gaba ɗaya na zube a tsakar ɗakin barci yay awan gaba dani badan na shirya ba.         Da asuba dana farka da ƙyar na iya gabatar da sallar asubahi, ina zaune ina addu'a Uwargida ta shigo.     Batace dani komaiba ta wuce ciki, a gabana babu kunya ta cire kayanta ta ɗaura tawul ta nufi ban ɗaki.     Bani da damar fita a ɗakin tunda a kulle yake, hakan yasa na maida kallona ta inda bazan gantaba koda ta fito.      Ta jima a cikin bayin kafin ta fito, “Babyna kin tashi lafiya” ta faɗa cikin salon yaudara.      Ba ƙaramin ɗacine ya mamaye zuciyata ba, hakan yasa nai banza da ita ban amsaba.      A mamakina sai naji  tayi murmushi mai sauti, tace, “Karki bar wata ƙofa da zatasaka raina fara zafi a kanki kinji, ina sonkine shiyyasa kike samun sauƙi da ga wajena”.         Daga wannan maganar bata sake tankaminba, tai shirinta cikin shiga ta alfarma tanata zabga kamshi, sai kace ba itace shugabar sheɗanun nanba.      Gaban kwanikan abincin jiya taje ta buɗa, ganin banciba ne ya sata faɗin, “Kai-kai wai bayan ƙuntata kanki harma horon yunwa kikema Kanki? Rufamin asiri kar wannan ƙyaƙyƙyawan jikin dana ɗorama buri ya lalace matata”.      Babu shiri na juya na kalleta da tsagwaron mamaki akan fuskata, wannan matar lallai zuciyarta ta rigada ta gama bushewa, idanuna da sukai nauyi kawai naɗan lumshe na maida kaina na jingina da gadon.            Ƙamshin turarenta da ya yawaita a hancina da motsinta ya sani tabbatar da tana a kusa dani, hakan yasa naƙi buɗe ido, ta kama hannuna tana murzawa cikin wani salo na shaiɗanci.        “Haba gimbiyar mata, kiyi haƙuri haka nan, dan bazaki taɓa kuɓuta daga gareniba, na rufe dukkan ƙofofin da hakan zata iya faruwa ma, ki cire komai a ranki ki bada kai bori ya hau kinji, idanma tsoron shiga wuta kikeyi ai kafin tsufa yazo mana zamu bari ko”.          A hankali na buɗe idanuna saboda jin furucinta na ƙarshe, ba tare da na shiryaba na sakar mata murmushi ina kaɗa kaina a hankali, banso mata magana ba tsawon zaman da zanyi da ita, amma a wannan gaɓar sai na kasa jurewa hakan, “Hajiya waya faɗa miki anama ALLAH wayone? Wakuma ya baki albishir saikin tsufa zaki mutu?”.      Hannuna ta saki da sauri tana ƴar dariya ta mike, “Humm Ustazu sauri nake, ajiye waɗannan tambayoyin naki kinji, ki daure kici abinci zanje anguwa na dawo, dan gobe ne za'a mana baiko ni da ke, sai kuma a tsaida ranar da za'a ɗaura mana aure”.        Da kallo kawai na iya binta harta fice, inaji ta sake kulleni.     Sam na nema hawaye na rasa a idanuna, kuma ko kukan zuci ma na kasa yi, ina nan zaune niba mai tunaniba ba kuma gunkiba har hasken rana ya buɗe sosai, saurayin dake kawomin abinci ya shigo ɗauke da ture a hannunsa, yanzunma baimin magana ba ya ajiye tiren ya ɗauki abincin daren jiya ya fice abinsa.       Nima kala bance masaba, dan maganar da Uwargida ta ambatamin akan baikon nan ta toshe dukkan tunanina, ni Bilkisu mace ƴar uwata take dangatani da aurenta?.        “Hummm” na faɗa a fili ina maida kaina na kwantar a jikin gadon, yanda cikina ke murɗawar yunwa ya sani jin ya kamata naci abincin koda kaɗanne.       Tiren da saurayin ya ajiye na jawo gabana, na buɗe kular farko farfesune na naman kai, sai ɗayar kuma soyayyar doya da ƙwai, sai ruwan shayi a ƙaramin filas, an zuba kayan shayin cikin kofi da aka ɗoro a tiren.          Takarda mai rubutu da aka shinfiɗa akan tire ɗince taja hankalina.      Na ja kular da aka ɗora ta lulluɓe kusan rabinta gefe.   ALLAH YASA KIN IYA KARATU?        Kar kiyi abinda wani zai fahimta akan takardarnan, dan ɗakinnan akwai cctv a ciki      Abinda na fara cin karo da shi kenan a rubuce, hakanne ya sakani nutsuwa, naci gaba da ƙoƙarin haɗa shayi a kofin ina bin sauran rubutun ƙasan ina karantawa.             Na miki alƙawarin zan taimakeki, saboda baki dace da zama a wannan gidanba, Uwargida mahaifiya tace, inason ki saki jikinki da ita, duk abincin dana kawo miki kicisa dan wlhy bazan cutar da keba, insha ALLAHU gobe idan munkai da rai zan kuɓutar dake a wajen bikin baikon sheɗancin data ambata miki, dan inhar zaki cigaba da ƙuntata kanki bazata bari ki fito a ɗakin nanba, in kuma har kina a ciki bazaki samu damar barin gidan nanba, sakin jikin da zakiyi kamar kin amincewa buƙatartane kawai zai taimaka mana.         Bansan wani nannauyan numfashi ya suɓuce mani ba, na share hawayen da suka kwaranyomin, cikin sauri na zuba abinci naci kamar yanda ya shawarceni, nakuma tashi na shiga wanka, dirowan tata na buɗe na ɗauki doguwar riga baƙa na saka.       Ina nan zaune kusan sha biyu da rabi saurayin yazo ɗauke da wani abincin, nayi mamaki, dan ba'a irin wannan lokacin yake zuwa ba, sai dai zuciyata ta bani yanason fitar da rubutun da yayo minne, tattare kwanikan safen yayi, cikin wani dabara yaymin magana da idanu dake tabbatar min da abinda ya rubuto.      Yanzunma daya fita dai sake rufeni yayi, banci abincinba har saida nai sallar zuhur.       Zuwa yanzu naɗanji ƙarfin jikina, na gama babu jimawa Uwargida ta shigo, sosai mamaki na karanto a fuskarta gani na ba'a yanda ta barni ba.        Ta dire jakar hannunta tana faɗin, “Babie kece kuwa?”.        Cikin danne ɗacin da nakeji na kalleta da murmushi a fuskata, “Nice hajiya, bayan fitarki nayi nazari akan maganarki, sai naga ma to idan na matsawa kaina barinku ina zanje?, na amince da bukatarki kawai”.          Shiru Uwargida tayi kamar bata amince da magana ta ba, sai naga ta nufi wata ƙofa, ashe nan ma ɗakine, kusan mintunanta goma da shiga ta fito, babu tsammani naji ta rungumeni tana murna sosai. ★★★★★        Tun daga haka sai Uwargida taita nan nan dani kamar zata maidani ciki, tanayin wanka taja hannuna muka fito falon, falon nan ya haɗu, haɗuwar da idan na zauna misaltashi ma ɓata lokacine.       Zuwa dare na sake gaskata maganar saurayin, dan kuwa ta gama amincewa dani, harda zaunawa tana ƙara bani sirrikan arziki dake cikin harkar tasu, ni dai jinta kawai nake ina sake neman tsarin ALLAH da sharrinta a zuciyata..............✍🏻 Page 15 ...........Washe gari ma dai naga gata wajen Uwargida, yanda na saki jikina da ita sai itama ta sake yarda dani ɗari bisa ɗari, dan har barina tai naje wajensu ƴar daɓas.        Yanda suketa sinne kai basason mu haɗa ido sai suka bani mamaki, amma sai ban nunaba, dan na lura kunyata sukeji.      Nima dai a kunyacen nake dasu, amma sai na dake tamkar baniba, nanko ƙasan zuciyata a matuƙar tsorace nake da kowa na gidan, nakan danne zuciyata bana kukan zahiri sai na zuci, tunanin iyayena dasu Firdausi yana sake gallabar zuciyata.        Tun a yammacin ranar naga anata shigowa da drinks da wasu kayayyaki a kwalaye, tsoro ya sake kamani, danfa tabbas da gaske wannan sheɗaniyar takeyi, cigaba nai da neman tsarin ALLAH da sharrin kowannensu a zuciyata.         ★★★★★★ Washe gari aka tashi da shirin baiko kamar yanda Uwargida ta faɗa, tun da rana manyan hajiyoyi suka fara isowa gidan, abin idan ka gani zat tashin hankali, sam banyi tunanin wannan ƙazantar tayi girma da yaɗuwar haka a cikin al'ummar musulmai jinin hausa fulani ba, wanda ma baka taɓa zato ko tsammani ba saika ganshi a wajen.      Yara ƙanana ƴammata duk an tsundumasu wannan ƙazamar harka, mafi yawansu kuma saboda abin duniyane, gashi idan kana sauraren hirarrakinsu zaka fahimci sanadin waya suka haɗe da hajiyoyin a yanar gizo, bansan hawaye sun fara wanken fuskaba, sai da naji ɗigarsu akan hannuna, nai saurin gogewa ina haɗiyar rai.         Kowa ya ganni sai ya yabama ƙoƙarin Hajiya, suna kurantata wai ta more, dan inada karuwan jiki, dukda ba wata ƙyaƙyƙyawa bace a fuska kuwa.           Wasu mata kuwa su biyu sai hararata suke, ni ban saniba ashe wai matan hajiyarne, waisu nan kishina sukeyi.     Kai jama'a, ALLAH kai mana tsari da asararriyar rayuwa dai.       Anmin wankin kai saikace wata amaryar data samu miji, sannan aka kawo mai kwalliyar da zatamin, bansan yanda zan musalta muku ɗunbin tashin hankalin da nake cikiba a wannan lokaci har aka gama kwalliyar.       Duk wannan shiri da akeyi bikin zai gudana ne bayan sallar isha'i, amma abinda zai baka tsoro babu wanda naga yayi salla a cikinsu koma ambatarta a bakunansu.       An kawomin wata riga mai ƙyau da zan saka, harda takalma da sarƙa da nake zaton ta gwal ce, dan ƙyawunta a ido kawai ya isa ka shaida hakan.         Dakatar dasu nayi akan inason sai nayi sallar isha'i, da mamaki kuwa sai naga abun ya basu dariya, ni dai ban kulasu ba naje nai sallata, bayan na idarne na duba takardar da saurayinnan ya bani ɗazun da rana a ɓoye, bayanin danaga yayi a ciki ne ya sakani miƙewa da sauri, kaya na buɗe drawer ɗin Uwargida na ɗauka, na saka tare da gyara jikina tamkar ba niba, a yanda na fito inba sani kaimin na tsiyaba bazaka taɓa gane niceba, balle dama tunda akaimin kwalliyar babu wanda ya ganni a cikinsu har Uwargida.          Cikin taimakon ALLAH na fito falon cikinsu ina taku da yauƙi, na saki jikina tamkar nima irinsu ce, duk da na fahimci wasu suna min kallon rashin sani, amma  harkar ta wayewace sai kowa ya amsheni ba tare da bincikeba.         Uwargida ta miƙe akan zataje ta fito dani, hakan yasa wasu manyan mata suka bita ɗakin, suna shiga watar gidan na ɗaukewa baki ɗaya.       Jikina har rawa yake na ajiye takalma da jakka tare da sarƙar danasa ta gwal ta uwar gida na fito da lalube, dan dama a hanyar ƙofar fita na zauna kamar yanda saurayin ya shawarceni.      Ina fitowa kuwa ana kama hannuna, cikin raɗa yace, “Karki damu nine”.        Bansan inda muke jefa ƙafa ba, kasancewar gidan babban gidane, maido wutar da akayine ya saka gabana faɗuwa, ni dashi duk mukaja birki ba tare da mun shirya ma hakanba.       Surutai muka fara jiyowa wanda da alama ni suke nema, wasu na faɗin ta gudu, wasu na cewa ai da alama wata baƙuwace data shigo ta saceta kota kuɓutar da ita, dama su basu yarda da baƙuwar fuskarba.      Cikin hanzari yaja hannuna muka faɗa ɗakin mai gadi dake a bakin gate, hawaye kawai nake jikina na rawa.       Duk bidirin nemana da sukeyi muna jiyosu, wata naji tana tambayar Uwargida ko ina Sani?.       Uwargida tace tun da rana ta turashi can wani ƙauye danya bar gidan ma tace ya kwana acan da safe ya dawo.      Kallonsa nayi, dan da alama na lura shi ake nufi, kenan wasu sun fara zargin akwai saka hannunsa.     Tun suna ɗaukar neman nawa wasa har abun ya fara caja musu kai, dan haka suka rabu, akabar ƙalilan a cikin gidan, ɗaukar kowa na fice, saboda sun iske gate buɗe.      Saurayin ya ɗan leƙa ta Window, sai da ya tabbatar babu kowa kusa yay min nuni muje, hijjab ya bani na saka, ta bayan ɗakin mai gadin muka iske tsani, duk da tsahon katangar nan haka na hau tsanin nan ga tsoro na cina ga hawaye, da taimakonsa muka dira can baya, dayake ta canma ya saka tsani, kuma akwai abokinsa dake tsaye yana jiranmu.      Duk naji ciwo a jikina, amma sam tashin hankalin da nake ciki baisa na damu da ciwukanba.           Babu ɓata lokaci muka bar wajen, muna matsawa muka jiyo hayaniyar su Uwargida suna faɗin “tanan ta biyo” kugafa harda tsani, aiko tabbas akwai waɗanda suka taimaka mata ta gudu kenan. Buɗar bakin wata sai naji tace “kodai su ƴar daɓas ne”.        Bamu jiyo amsar da Uwargida ta bata ba mai adaidaitar da suka sakani ciki yaja yay gaba.       Na damƙe jakkar da saurayin ya bani a jikina sosai ina cigaba da yin hawaye, yanzu kuma ko ina zan dosa kenan?.      Wata zuciya ce tace, “Bilkisu duk kibar wannan guje-gujen, kibi shawarar zaɓi biyu, kodai ki miƙa kanki ga ƴan sanda, kokuma ki nema gidan ƴan uwan mahaifinki ko mahaifiya kije ga wani, idan sun riƙeki shikenan, idan sun nuna bazasu iyaba sai kisan mafita”.       Wannan shawara itace tai tasiri a raina, koda mai napep ya tambayeni batare da na shiryaba na faɗa masa anguwar da zai kaini.     Ganinai ya tsaya da napep ɗin yana kallona, “Hajiya kinsan kuwa mi kike faɗane? Anguwar nan gaskiya tana da nisa, nikuma wanda ya bani ke ya cemin tashar mota zan kaiki”.      Hawayen fuskata na share, murya na rawa nace ka taimakeni bawan ALLAH, kaga ni mace ce, tashar mota kuwa wajene mai haɗari musamman da daddare, amma anguwar da zaka kaini yanzu akwai wanda na sani, wajenta zanje kafin safiya idan ALLAH ya kaimu”.       “Gaskiya Hajiya bazan ɓoye mikiba, a darennan bazan iya zuwa har canba, yanzu idan mun tafi sai mukai goma na dare bamu isaba, to yaushene na ajiyeki harna juyo nikuma na dawo gida. Ki dai faɗi wani wajen bayan wannan ɗin”.          “Shikenan na gode” nai maganar cikin jan majina ina sharce hawaye, zuwa can wani tunanin ya sake faɗomin, bara naje gidan Inna zainaba, ko arziƙin kwana ɗaya tamin, da safe saina doshi gidan baba manu ɗin da nai niyyar zuwa, duk da dai bana zaton samun alfarma daga ko ɗayansu, amma zan gwada, karya zam na yanke hukunci akan gaibu.      Sake faɗa masa anguwar da zamuje nayi, dan haka ya tada napep muka cigaba da tafiya, sai yake cemin to ai shima cannema anguwarsu.      Wani daɗine ya kamani, dan dama dai bawani iya gane gidan inna zainaba ɗin zanyiba sai na haɗa da tambaya.      Shiru mukai na wasu mintuna, lokacu-lokaci ina cigaba da sharar hawayena.     Muryarsa na tsinkayo yana cewa, “Baiwar ALLAH kibar kukannan, ita rayuwa duk jarabawace, haƙuri kawai kesa a cimma buri, da alama dai wanda ya sakaki a keken nan mijinkine ko?”.        Shiru na masa ban tankaba, jin haka shima sai ya tsuke bakinsa, mun ɗan ƙara tafiya na sake jiyoshi yana faɗin, “Dai-dai ina zan ajiyeki baiwar ALLAH?”.         Muryata a dasashe saboda kukan dana sha nace, “Kace nan anguwar kake ai kaima? Dan ALLAH ko kasan gidan dogo kafinta?”.      Da sauri ya juyo ya kalleni, bakinsa har harɗewa yake wajen faɗin, “Can gidan zakije?”.       “Eh” na faɗa cikin mamakin razanar danaga yayi.      Yace, “Kai, to ai babanane dogo kafintan hajiya? Dan ALLAH kozan iya sanin ke wacece?”.       “Gidankune? To ko dai Yaya Shu'aibu ne?”.      “Ikon ALLAH, tabbas kuwa kin canka dai-dai, Shu'aibu ne kuwa, wacece ke dan ALLAH? daga ina kuma?”.       Murmushin yaƙe mai haɗe da takaici nayi, ganin yanda taɓarbarewar zuminci tasa ko juna bamu saniba dukda kusanci mai ƙarfi da muke dashi, shi kansa sunansa kawai nakeji a bakin Innata, amma ban taɓa ganinsa ba a ido, “Da wahala ka sanni, sai dai bansan ko kasan Asiya gurguwa data rasu kusan shekara ɗaya kenan?”.        “Tabbas na santa, dan gwaggona ce ma ai, tunda ƙanuwar innatace”.      Murmushi nayi mai ciwo, na maida kallona ga wata tukubar mai nama da muka tsaya dai-dai satinsa, mazane cike da wajen saboda mai shayi dake gefe, daga can kuma gabansu kaɗan mai doya da ƙwai, zaman masu wannan sana'a ne ya maida wajen dandali, harda masu suyar awara, gaddamar siyasa kawai kake jiyowa a wajen kamar zasu fara danbe, cikin share hawaye nace, “To ita mahaifiyata ce, ni kaɗaice kuma ƴarta tilo data bari a duniya”.         Jinai kawai yanata jero salati da sallalami, na maida hankalina sosai a garesa, cike da tsagwaron mamaki yace, “Yanzu nan dama Gwaggo Asiya nada ƴa amma ban saniba? Har tambaya nayi wlhy a randa mukaje zana idarta sai akace ai bata haihuba, to kodai dama baƙya tare da ita?”.       “Muna tare” kawai na iya cemasa saboda abinda ya tokaremin maƙoshi.      Saurin tada Napep ɗin yayi yana faɗin, “Kinga yi haƙuri na tsareki da tambayoyi a titi, muje gida duk a yisu............ ________________________ JAZUGA ________________________             Alhaji, ina baka shawara muyi amfani da maganat likitannan, gara ka ɗauke yaronnan ya koma yin jiyya wani waje, mukuma saimu fito mu sanarma duniya ya rasu, a ajiye wata gawar a maimakonsa kamar yanda mukai na yarinyarnan.       Wlhy wannan sabon d.p.o ɗin baida mutunci, sannan baya amsar cin hanci, kaga dai yau kwanansa uku kawai da kawowa ko? To wlhy harya lalata wasu ɓoyayun cases guda huɗu da wancan d.p.o ɗin yaci ƙuɗi a kansu, to kaga kafin yazo kan bayanan case ɗin yaronka gara dai musan mai yuwuwa. Saboda tsaf zai gano gaskiya ta tashi mana mu duka wlhy”.      Wani irin nishin damuwa Alhaji lado yaja, yace, “Zanbi shawararku, amma lallai naso ace burina ya cika an kama yarinyarnan, dan shine kawai zai kawo ƙarshen wannan case ɗin”.       “Indai dan kamatane karka damu, zamu cigaba da ƙokari har sai mun ganta, kuma bazamu bartaba, tunda kaga yanzu kowa zai ɗauka yaronka ya mutune ai”.      “To shikenan yallaɓai, nagode sosai da ƙoƙarinka, zan shirya mota a darennan abar asibitin da Jazuli, da safe kuma saiku bamu sabuwar gawar a maimakonsa”.         “Hakan yayi Alhaji, na barka lafiya”.     Bayan tafiyar ɗan sanda Alhaji Lado yata kai kawo akan zancen, tsarin likitan shima ya masa, amma fa yana burin a kama yarinyar kodan ya wulaƙantata, ya ɗaukama yaronsa fansa. Nace, “Humm”.      Duk yanda suka shirya haka aka tsara, washe gari saiga gawa a zuwan ta jazuga, mutane da yawa sunyi farin ciki, dan koba komai saji sakat, waɗanda sukaima wannan muwa kuma mutanene ƙalilan, suma na jikinsa, mutanen gari dai ko a fuska basa nuna jin kunyarsu akan gakan.      Haka akayi zana idar gawa aka kaita makwancinta, yayinda acan bayan fage Jazuga ke cigaba da jiyya. ★★★★      Haka abubuwa sukaita shuɗawa, jikin jazuga na samun sauki, sai dai da alama dukan da Bilkisu tai masa ya taɓa masa ƙwalwar kai, dan idan abun ya motsa haka zaita dukan kansa yana wata irin ƙara har sai an bashi maganin barci, idan kuma ya farka sai ka ganshi normal sai kuma ya sake motsa masa.          Sunje asibiti akan matsalar, suma dai magani suka bashi, tare da tabbacin inhar yabi soka komai zai dai-daita.       Dalilin sun sanarma duniya Jazuga ya mutu dole ya haɗa kayansa da yaransa suka bar garin akan sai komai ya lafa zai dawo.      Wannan abu ya sake masa ciwo, tare da dasa tsanar Bilkisu mai tsanani fiye da farko ma a zuciyarsa, yakuma saka a ransa duk randa suka haɗu kasheta kawai zaiyi kowa ya huta. 😱🙆🏻‍♀️. _________________________ JAWAAD _________________________                  Duk da ɓacin ran Shahudah daya fito dashi a rai, hakan bai hanashi zagewa ya maida hankali akan aikin da suke son farawa ba shi da su Aliyu abokansa.        Duk suna zaune ne a cikin falon gidan da ya kaisu, Jawaad yace,       “Tabbas a cikin satar kokino akwai lauje cikin naɗi, kuma tare dana kusa dashi akai hakan, bayanan dana samu yanzu haka sune, tare da amaryarsa suka dawo daga ƙasar Colonbia, kowa ya kasa gane yanda har aka sacesa babu wanda ya gani, hakanne yasakani ɗaura alamar tambaya akan wannan matar tasa, lallai tasan wani abu akai, dan a yanda tsarin saukarsa da baro airport ɗin ta kasance babu wani mahaluki dazai iya kutse wajen aikata hakan, kunsan a yanda tunanina da nazarina ya bani an sacesa?”.       Dukansu kai suka girgiza masa cike da mamakinsa, duk da dai dama sunsan Jay mayene akan bincike da bin ƙwanƙwanto.     Murmushi yayi yana komawa jikin kujera ya kwanta, sai kuma ya tashi zaune sosai fuska a haɗe yana tsaresu da idanu, “Tabbas lokacin da aka faɗi sacesa yana cikin gidansa ne, daga baya aka fita dashi acikin gidan”.       “Kamarya kenan Jay? ALLAH ka sakamu a duhu, danni kam wannan case ɗin ban fahimci komaiba akansa, tayaya hakan zata kasance bayan kowa ya shaida Alhaji Kokino lafiya ya fita a jirgi, agaban kowa kuma ya shiga mota direbansa yaja shi, kuma basu tsaya ko inaba sai a cikin gidansa.........”      Cikin katsesa Hafiz yace, “Ni kasan mina fahimta Jabeer, kamar Jay kanason kace mana dai babu wanda ya sace Alhaji Kokino ko? Kawai matarsa tayi ƙarya da hakanne saboda wani dalilinta ko manufa ko?”.        Kai Jawaad ya shiga girgizawa, ya miƙe tsaye hannunsa goye duka a baya, “Fahimtata tasha banban da taku, nakula kuma irin Fahimtar da sauran jama'a sukaima abin kukeyi a yanzu, “Tabbas an sace Alhaji Kokino da gaske kamar yanda zancen ya fita duniya taji”.         “To waya sacesa kenan? Miyasa kuma ka kawo matarsa cikin zancen?”.       Aliyu daya tsare Jay da idanu ya faɗa.       Murmushi Jay yayi kawai ba tare daya amsawa Aliyu tambayarsa ba, ya taka a hankali zuwa gaban Window yana leƙa harabar gidan, kusan sakwan goma kafin ya juyo gasu Jabeer da suka zuba masa idanu kamar wani magiji.        “Aliyu wannan shi nake so ku fahimta nima? Ni kaina inason nasan miyasa matarsa ta shigo cikin zargina”.      Dukansu ajiyar zuciya suka sauke.          Hafiz yace, “To yanzu dai saimu tsunduma aiki kawai, sai dai ina ganin Jay lokaci yayi da zaka yafema Rose ta dawo tare damu, kowa yasan amfaninta a cikinmu, bai kamata muyi sakaci da itaba ko a wannan lokacinma”.      Gaba ɗaya fara'ar fuskar Jawaad ta ɗauke, sai dai baice komaiba ya tako ya dawo wajen zamansa ya sake zama.      Maimakon ya taya zancen Rose da Hafiz ya ɗakko sai ya ɗakko wani maganar daban ma.      Sunsan bazai tankaba, dan wannan salonsa ne idan baya buƙatar abu, suma duk sai suka ƙyalesa kawai akan zasu cigaba da lallaɓashi har itama Rose ɗin ta dawo tare dasu su koma su biyar ɗinsu tamkar yanda suka saba a baya..... _________________________ SHAHUDAH _________________________           Tunda Jawaad ya fice tai tsaye a wajen, bata motsaba amma ta dasama takardun daya bari manyan idanunta.       A wannan yanayin Hajiya Humaira tai sallama ita da ƙanwar Shahudah ɗin mai suna Aamila.        Ko kusa bataji motsinsu ba, sai da Hajiya Humaira ta taɓata ne tai saurin juyowa a tsorace, dan tazata Jawaad ne ya dawo.      Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗawa jikin momynta ta fashe mata da kukan shagwaɓa............✍🏻 Page 16 ...........Wai nikam kukan mi kike Sister? Ni yanzufa lamarinki har mamaki yake bani, akan Brother Jawaad duk kin zama wata lusara.      Hararar Aamila Hajiya Humaira tayi, hakan yasa ta ɓame bakinta.         Ta mai da kallonta ga Shahudah dake kwance a kafaɗarta, “Babie na tashi muyi magana”.     Tashi Shuhudah tayi zaune, Hajiya Humaira tace, “miya sakaki kuka?”.         Cikin tsagwaron taɓara Shahudah ta fara magana da shashshekar kuka, “Momy wai ni yau Bb yake iya cewa na zaɓi ciki koshi? Harni yake iya furtama zai saki akan cikin da bai gama zama mutumba ma, dama ashe baya sona ban saniba....”     Ta rushe da kuka tana faɗawa jikinta.       Hajiya Humaira tai murmushi tana buga bayan Shahudah, “Ba sonkine bayayiba Shahudah, wannan abun daya ambata miki ma shine ya nuna yana tsananin sonki, duk wanda yake son haɗa jini da kai aikuwa yana sonka Shahudah”.        Shahudah ta ɗago da sauri baki a kumbure, “Wlhy Momy baya sona, tunda har bazaiso abinda nake soba, ni gaskiya ban shirya haihuwa yanzuba, salon nazo na tsufa yaje yana kallon wasu a waje ko?”.        Dariya Aamilah ta kwashe dashi tana faɗin, “Tab ashe su wata ta kusa komawa jagwal, na rantse karma ki yarda, toke ta yaya kikai sake ciki ya shiga jikinki ma?”.        “Zanci ubanki Aamila, tashi kibar ɗakinnan” Hajiya Humaira ce tai maganar a zafafe.     Hakan yasa Aamila tashi ta fita tana ƙunƙuni da buga ƙafa na rahin samun isashshiyar tarbiyya.       “Mamana karki biyema Aamila kinji, ki kwantar da hankalinki akan wannan cikin tunda yazo a kuskure, koshi kaɗai kika haifa ya isa haka, zuwa nan gaban idan kinso saiki ƙara ɗin, kinsan dai Jawaad yanada Zuciya idan aka ƙure haƙurinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya faɗa, kuma Abbanku ma yaji faɗa zai miki, insha ALLAH haihuwar wannan cikin sai dai ya ƙara miki daraja a wajen Jawaad badai ya rage mikiba, ALLAH yasa ki haifa mana little Jawaad dai mu shine babban fatanmu”.       Shahudah dai da maganar bata gama shigarta ba tace, “Yanzu kowa dai baya sona a gidannan, ni wlhy barmuku ƙasar zanyi to, dama saboda shi na dawo cikinta, tunda ya fara wulaƙantani gara nai gaba abuna”.      “Kefa wata sa'in baki da man kai Shahudah, lokacin da ake nuna miki Annabi saiki ta ƙoƙarin rimtse idonki haba, banason shashanci mana, to wlhy ki tabbata inhar kika zuba da cikinnan ba Jawaad kaɗaiba hatta ni da Abbanku mantawa zamuyi dake shasha kawai mai girman banza”.       Yanda Hajiya Humaira ta fusata sai abun ya bama Shahudah mamaki, hakane yasaka ta tsura mata ido kawai, miyasa kowa kejin haushinta akan wannan cikin? Tana kallo Hajiya Humaira ta fice ta barta, kwanciya tai ta rushe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan dabarar kiran Qaseem tazo mata.      Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cikin kuka ta sanar masa da duk abinda ke faruwa.       Da farko shima kamar zai mata masifa akan zubda cikin sai kuma yay saurin haɗiyewa ya kwantar da murya.       “Haba Shahudah na, manta kawai da batunsu, koni banso kika ɗauki ciki yanzuba, amma kuma yaya muka iya, ni badan ina tsoron akan ance idan mata sukaje zubda ciki suna mutuwa ba da dakainama zan kaiki a zubar dashi gaskiya”.         “Broth da gaske wai ana mutuwar dan ALLAH?”.       “Da gaskene fa Dear”. “Tab wlhy banson na mutu, amma kuma ai itama haihuwar wlhy ance ana mutuwa”.         “Eh amma ai kinga bakamar idan za'a zubar da cikiba, ki kwantar da hankalinki kawai kinji Sweetsister, ke dai kawai kina haihuwar wannan ki ɗauki mataki kinji”.     Haka yayta lallaɓata da kalamai masu sanyi harta aminta da zancensa.       Bayan sun ajiye wayar yay ƙwafa, wlhy badan shima yana da buri akan cikinnan na jikin Shahudah ba da sai ya sakata zubdawa koda ya baƙanta ran Jawaad, dan yasan zubda cikinnan ba ƙaramin sukar zuciyarsa zaiyiba, amma babu komai, idan yasha a wannan ai bazai sha ba anan gaba.       Itakam Shahudah shawarar Qaseem ce ta sakata yarda zata bar ciki, amma wlhy saita rama wulaƙancin da duk Jawaad yay mata a gidannan, bazata sake ɗaga masa ƙafaba daga yanzu.... _______________________ BILKEESU _______________________           Gidan nasu bawani mai ƙyau bane, ginine dai irin na masu ƙaramin ƙarfi, darene shiyyasa bazan iya ƙarar da komai ba dan gane da tsarinsa, gashi anguwar babu wuta         Mun shiga da sallama bayan ya ajiye napep ɗinsa inda yakan ajiyeta, gidan shiru kamar babu kowa, sai muryar mutum ɗaya da najiyo ta amsa, ta fito tana ƙoƙarin ɗaura zaninta, amma ganinmu sai ta tsay turus tana haɗe fuska.       “Wannan fa?” ta faɗa muryar ta na ɗaukar zafi.       Ina jinsa yay gajeren tsaki, kamar bazai bata amsaba sai kuma naji yace, “Inna tai barcine?”.       “Ni ban saniba” tai maganar tana juyawa fuska a kumbure.     Kansa kawai ya girgiza ya nufi ɗakin dake can wani ɗan lungu yana min nuni dana biyosa.      Munyi sallama amma ba'a amsaba, ya ƙarasa shiga ɗakin nima ina biye dashi a baya.       “Inna harkun kwantane?”     Tsohuwar dake kwance mai tsananin kamanni da Innata ta ɗaga masa hannu cikin yanayin barci tana faɗin, “Uhm, ka dawo da wuri haka?”.       “Eh wlhy inna, amma ina tare da baƙuwane”.      Babu shiri ta tashi zaune, takai hannu ta ƙara hasken fitilar dake ajiye saitin fuskarta ɗakin yay fayau.      “Aibo baƙuwa daga ina kuma a tsohon darenan?”.      Sai da gabana ya faɗi dajin furucinta, amma amsar da naji ɗan nata na bata ce ta sakani sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya.        “Inna zan miki bayani da safe, yanzu dai gata nan bara na samo mata abinci wajen Lawusa”.      Kamar zatai magana sai kuma ta fasa, ta kalleni fuska babu walwala tana min nuni da wajen zama, zama nayi jikina duk a sanyaye, dan banga alamun zan samu karɓuwa ananba kam.      Muna zaune shiru kaina a ƙasa saiga Shu'aibu ya dawo ɗauke kula, a gabana ya ajiye yana faɗin, “ƙanwata maza kici saiki samu ki kwanta kinji”.       Godiya nai masa, na buɗe kular dan yunwa nakeji, Taliya da wakene a ciki, ban cutama kainaba naci na ƙoshi, dan rabon da na samu nutsuwar cin abinci haka tun ranada zan buge Jazuga.       Tabarma Inna ta bani, na shimfiɗa inda nake zaune na kwanta, filoma sai da ledar da Sani ya bani wadda bansan ko minene a cikina nai filo, kafin kace kwabo barci mai nauyi yay awon gaba dani.      Ban sake sanin halin da ake cikiba sai da asuba da inna ta tasheni nayi sallah.            Ina daga inda nai sallar ne na gaisheta.     Ta amsa min cikin halin ko in kula ta fice abinta, lallai nasan akwai matsala, a yanzuma batasan koni wacce ba ban damu karɓa daga gareta ba inaga ta ji wacece ni?.       Haka na zabga tagumi ina komawa duniyar tunanin yanda rayuwa take tamkar juyawar ƙarfunan agogo, wani lokacin sai kaga komanka nata maimaici bisa ga matsalolin rayuwa, idan kai wasa tuni kake aikata saɓo koda afurucine.     Shigowa inna da Shu'aibu ta katse mani tunani, na gaida shi bayan sun zauna.        Cike da fara a ya amsa yana tambaya ta ya baƙunta?.     Nai ɗan murmushi mai sauti ba tare dana iya cewa komaiba.      Hankalinsa ya maida ga inna daketa faman taɓe baki tana kallonmu, “Inna kinsan wacece kuwa wannan?”.       “Yazan sani baka faɗaba Aibo”.      Ƴar dariya yayi yana gyara zama, yace, “Kalleta da ƙyau dawa tai miki kama?”.     Kallona Inna tayi, sai kuma taɗan taɓe baki, “Yo kai banda abinka Aibo ina nake ganin fuskarta, tunda ta shigo gidannan banda sinne kai da take kamar sabuwar amarya mi takeyi”.      Saurin ɗago kaina nai na kalleta, sai dai kuma ban jureba na janye idanuna, amma dai nasan yanzu zataga fuskar tawa kamar yanda take buƙata.        Inajin yanda idanunta ke yawo a jikina, zuwa wasu mintuna kamar biyu tace, “Ina gano kamannin Zubairu da Asiya tare da ita kuwa Aibo”.      Dandanan bakin Shu'aibu ya washe, cike da zumuɗi yace, “Masha ALLAH, ai ɗiyar Inna Asiyar ce kuwa inna”.      “Ɗiyar Asiya? Kai ina ka samota haka?” Inna ta faɗa cike da mamaki.        Murmushinsa ya faɗaɗa, tas a yanda muka haɗu jiya sai ya sanar mata, sai jinjina kan mamaki takeyi, ta juyo gareni tana tambayata daga ina nake haka har shi Shu'aibu ya ganoni?.       Da farko nayi niyyar faɗa musu gaskiya, amma yanayin Inna da naga har sannan bawani ɗokin ganina taiba saina canja zancena kawai, na faɗa musu iya abinda zasu iya amsata game da nemnsu kawai na fitoyi dan nagaji da zama ni kaɗai.     Kai inna ta jinjina, babu ko jin nauyina tace, “Amma kai Aibo kana ganin riƙon babbar budurwa kamar wannan bazai zamar mana wani tawayaba? Mu dai ba kuɗin aurar da ita ke garemu ba kaima kasan haka, ga ɗan karen kishin matarka da batason ganin wata mace ta raɓeka, inaga mu taimaka mata da wani abun ta koma inda ta fito tai haƙuri kamar yanda kowa keyi a nasa gida.           Murmushi nayi mai ciwo hawaye na taruwa cikin idona, wato sai yanzu na fahimci abinda yasa dangina ke gudun ɗaukata, ashe hidimar aurar danice damuwarsu kawai, to nida banida ko saurayi wane maganar aurena za'ayi kuma?, maganar shu'aibu ta katseni.       “Haba inna, wannan wace irin maganace haka, koba komai ai Bilkisu abar tausayice, ALLAH kuma shine zai buɗa mana mu sauke dukkan nauyinta gwargwadon iko, dan riƙe maraya ba ƙaramin alkairi bane da falala ga bawa, amma yanzu sai kowa ke gudun hakan, kifa tuna mahaifinku ɗaya da inna Asiya, na tabbata kuma da itace a raye zata riƙe naku ƴaƴan ai, sa......”        “Nikam naji gwanin iya magana, tunda kaji ka gani ta zauna ga fili nan, ni dama dai kai nake tausayi, tunda dukkan ƙarfin riƙe gidannan kaine keyi”.         Cikin jin daɗi yace, “Nagode da amincewarki inna, ALLAH ya tayamu riƙo”.       Wannan shine yazama sanadin zqmana a wannan gida, duk da bajin daɗin zaman nakeba hakan ya fiyemin akan naje naita raɓe-raɓe harna cigaba da gamo da irin gidajen su Uwargida masu dulmiyar da imanin bawa zuwa halaka.         Babu mai sakarmin fuska inba Shu'aibu ba, shi kuma ba yini yake a gidanba, a hankali dukkan aikin gidan ya dawo kaina, sam bani da wani hutu inba dareba shima sai kowa ya rigani kwanciya.      Lawusa matar Shu'aibu ta mugun tsanata, ni zan dafa abincin gidan amma idan tazo rabo ɗan kaɗan take zubamin, wani lokacinma saita gama rabon zatace ta manta dani, sai dai ace na kankare ƙanzon.     Duk da agaban Inna ake komai uffan bata ce mana balle ta nunama Lawusa batai dai-daiba, koda yake na lura Inna tsoron Lawusa takeyi, dan haka zatai ta mata rashin kunya amma bata iya cewa batai dai-daiba, sai idan taimata abinda yay mata zafine sosai zakaji ta faɗama Shu'aibu, shiko iyakarsa yace tayi haƙuri ta bar Lawusar da halinta kawai.      Wannan zama nasu na bani mamaki sosai.     Ban fahimci abinda yasa gidan yake hakaba sai da ƙanwar yaya Shu'aibu Sa'a tazo gidan yini a ranar da nake cika wata guda a cikinsa, itakam hannu biyu ta amsheni, sai murna take matsayina na ƴar uwarta.         Akan Lawusa namin masifa nazo na ɗaura abincin rana sukai faɗa da Sa'a, tace ban ɗorawa ita da take aure a gidan ta fito ta ɗaura, da yake Inna batanan sai babu wanda yace Sa'a batai dai-daiba, nicema naita bama sa'a haƙuri akan tabari kawai nayi, amma fir tace bazanyiba.     Nanne ta zauna ta bani labarin ai Yaya Shu'aibu ba son Lawusa yakeba, Inna ce ta haɗa auren saboda Lawusa ƴar ƙawartace, yanada wadda yakeso amma inna tace bazai aureta ba sai Lawusa.     A lokacin babansu na jiyya baida lafiya, shiyyasa aka rasa mai goyama Shu'aibu baya, dole ya auri Lawusa badan ya soba, bayan bikin da sati biyu kuma babansu yarasu, daga nan Lawusa ta fara ma Inna rashin mutunci a gidan, inna ko bata iya ce mata komai, yanzu haka aurensu shekara uku kenan, amma ko ɓari Lawusar bata taɓa yiba sai rashin mutunci, sai dai duk wannan tijara tata tana tsoron Shu'aibu, ita kuma Sa'a bata raga matane.         “ALLAH ya ƙyauta” kawai na iya faɗa naja bakina na tsuke.     Sai yamma lis Inna ta dawo gidan, Lawusa ta kwashe ƙarya da gaskiya ta faɗa mata a kaina, Inna ko ta rufeni da masifa hardasu gori akan daga taimakona da sukai shine zanzo na watsa musu gida.       Ran Sa'a ya ɓaci akan wannan abu, Shu'aibu na dawo ta kwashe komai itama ta sanar masa, shiko ya balbale Lawusa da masifa har takaisu ga marinta.       Kuka da ihu taita kurmawa akan mari guda ɗaya, yayinda bakinta keta danƙarama Shu'aibu zagi ta uwa ta uba, ta haɗa kaya zata tafi Inna taita roƙonta da bata haƙuri, sai da ƙyar Lawusan ta haƙura saboda tana bala'in son Shu'aibu, batason rabuwa dashi sam.     Ni daga baya ma abin nasu dariya ya koma bani dan na lura dama Lawusa bason tafiya takeba, farfaganda ce kawai.         Sam abinda akemin a gidan sai baya damuna sosai, komai kuma suka buƙata ina musu dan a zauna lafiya, ban taɓa ɗaga kai na kalli wulaƙancin da Lawusar kemainba sam, a ganina ba laifinta bane ai, haka ƙaddarar rayuwata take..... ________________________ JAWAAD _________________________           Yau ma dai Jawaad bai kwana gidanba, koda ya baro wajensu Aliyu Office ya koma, acan ya raba dare yana aiki, daga baya ya fito, amma saima ya rasa ina zai dosa, sam baya buƙatar komawa gida, dan bayason yawan ɓacin rai a yanzu, yana buƙatar nutsuwa ta musamman akan gudanar da wannan aikin da yake fatan nanda kwana biyu ya kammala shi insha ALLAHU.        Gidan dasu Jabeer suke dai ya sake komawa, ya iske har sunyi barci, dan haka ya buɗe wani ɗakin ya shiga ya kwanta, bama wani barci sosai yayiba aka kira asubahi.         Su Hafiz duk sunyi mamakin ganinsa a gidan, sai dai tunda bai basu fuskar da zasu tambayesa komaiba sai basuce ɗinba.      Suna dawowa daga salla duk da barcin dake cin idonsa bai kwantaba.     Zama sukai yana musu bayanin abinda kowa ya kamata yayi a ranar yau.       Coffee da Jabeer ya dafa musu da kansa kowa yake sha, Jawaad ya ajiye kofin hannunsa yana faɗin, “Dolene yau muyi komai da azama, dan guri na sake ƙure mana. Ni zanje gidan Alhaji kokino na gana da matarsa, Jabeer kaikuma filin jirgi ya kamata kaje ka sake mana bincike a cctv ɗinsu, Aliyu da Hafiz ku kamo mana drivern Alhaji Kokino da ƙaninsa wakili, dan hardashi akaje tarbosa filin jirgi, shima inada alamar tambaya a kansa”.      A tare duk suka jinjina masa kai, sai kuma kowa ya miƙe domin zuwa ya shirya...............✍🏻 Page 17 .............A gaggauce yay shirin cikin Suit kalar ruwan goro mai duhu, sai rigar ciki data kasance ruwan bula mai haske, yanada kaya a gidan, saboda duk randa Shahudah ta haɗa masa zafi to nan ne wajen fakewarsa ya samu nutsuwa, shiyyasa yake da abubuwan amfaninsa.      Turare ya fesa kaɗan ya fito yana ƙoƙarin ɗaurama hannunsa a gogo, rigar suit ɗin ta sama rataye a hannunsa dan bai sakaba.      Su Aliyu dake zaune a falo cikin shirin fita suma suna jiransa duk suka miƙe idonsu a kansa.         Jabeer ya kama hannun da Jawaad yake ɗaurama agogon yana ƙarasa ɗaura masa.       Bai musaba ya miƙa masa hannun yana maida hankalinsa ga Hafiz.       “Hafiz ka kulafa sosai, dan ƙaninsa ɗinnan shegen wayone dashi, duk wani motsinsa inda yake zuwa, da wanda yake mu'amula da dai komai nasa ku sani, a koda yaushe yakan nuna yanason yayan nasa fiye da kansa”.       Ya ƙarasa maganar dai-dai Jabeer na gama ɗaura masa agogon, yace, “Thanks”.      Kai kawai Jabeer ya ɗaga masa, sukai ƙoƙarin ficewa.     Jawaad na gaba suna binsa a baya su uku, dolene ka gansa su burgeka sosai, dan kallo ɗaya zakai musu ka tsinkayo tsantsar jarumtar aikinsu a fuskokinsu.        Gimba ya gaishesu cikin girmamawa, sannan ya buɗe ma Jawaad mota ya shiga.        Suma sauran kowa mota ya shiga, Jabeer shi kaɗai, Hafeez ma shi ɗaya.          Sai Aliyu da ya shiga kusa da Jawaad zasuje gidan Alhaji kokino tare.       Shiru Jawaad na kwance a bayan mota, kansa kwance jikin kujera. yayinda idanunsa ke buɗe yana kallon titi.      Dai-dai danja ta tsayar dasu idonsa ya sauka akan wata mahaukaciya dake tsaye bakin titi tanata soshe-soshe, kafeta da idanu yayi ko ƙyaftawa bayayi, Gimba da Aliyu da basusan mike faruwa ba suna ɗan magana jefi-jefi, gimba yaja motar sukai gaba.      Jawaad yasa handkherchief ya tsane hawayen da suka cika masa idanu, yanajin kewar mamansa sosai, irin yanda bakinsa ma bazai iya furtawa ba, ya lumshe idanunsa yana magana a hankali akan laɓɓa wanda inba kusa da shi kakeba bazakajiba.          “Boss mun iso” Gimba ya sake maitawa Jawaad da yay nisa cikin tunani sam baisan harma sun samu damar shigowa harabar ƙaton gidan Alhaji kokino ba, Aliyu da gimba harsun fita a motar sai shi kaɗai.         Numfashi mai nauyi Jawaad ya sauke yana kallon Gimba da idanunsa dake a rine da damuwa?.      Baice komaiba ya ziro ƙafafunsa ya fito, agogonsa ya ɗan kalla kafin ya maida kallonsa ga dogon ginin benen gidan,         “Ali muna buƙatar ai mana iso fa”.     “Yes Boss, ai mai gadin ya shiga ya sanar musu ma”.      “Ok” Jawaad ya faɗa yana tura hannayensa biyu cikin aljihun wandonsa kamar maijin sanyi.         Kusan mintina uku sai ga mai gadin ya dawo, shine yay musu jagora har ƙaton falon baƙi dake a cikin gidan, sannan yay musu sallama ya fita.         Zamansu baifi na mintina ukuba wata dattijuwa ta shigo ɗauke da ƙaton tire, ta ajiye sannan ta risina ta gaishesu, cikin kulawa Jawaad ya amsa mata.      Tana fita babban yaron Alhaji kokino ya shigo cikin kayan barci, da alama ma tasoshi akayi daga barcin, dan yanayinsa ya nuna hakan.      Hannu ya bama Jawaad suka gaisa tare da Aliyu da Gimba, sannan ya samu waje ya zauna hankalinsa akan Jawaad.         “Yallaɓai ko an samu wani ƙyaƙyƙyawan news ne haka?”.          Jawaad dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya girgiza masa kai yana gyara zamansa, “Babu wani labari mai nuni da nasara abokina, yanzu ma munzone dan inason ganawa da dukkan jama'ar gidannan idan babu damuwa”.        “Babu damuwa yallaɓai, barama kaga naje na tattarosu”.       Kai Jawaad ya jinjina masa cikin lumshe idanu, ya miƙa hannu ya amshi system ɗinsa dake a hannun Aliyu, saman cinya ya ɗorata yana ƙoƙarin kunnawa. A haka jama'ar gidan suka fara shigowa cikin sallama.        Jawaad bai ɗago ya kalli kowa ba a cikinsu, danne-dannensa kawai yake a lap-top.         Kowannensu mazauni ya samu, budurwar da tunda ta shigo idonta ke a kan Jawaad ta miƙe daga inda ta zauna tana faɗin, “A yallaɓai ko shayi ai kwasha, dan da alama kunyo sammakon barin gida”.          Ɗan murmushi Aliyu yay kawai, Jawaad kam ko motsi baiyiba balle zancen ɗagowa, zata fara ƙoƙarin haɗa shayinne Aliyu ya ɗan kalleta yana girgiza kansa, “No Please barsa kawai”.       Da sauri Uwargidan Alhaji Kokino dake ƙoƙarin zama ta katsesu da faɗin, “A'a haba dai, in kuka ƙi kuwa bazamuji daɗiba sam”.      Murmushi kawai Jawaad da ya kallesu yayi, amma baice komaiba, dan haka shema'u ta cigaba da haɗama su Jawaad shayin, cike da yanga ta kalle Jawaad kamar shi kaɗai kawai take gani a wajen tana faɗin, “Asa shuga da yawa?”.         “Spoon ɗaya ya isa” Jawaad yay magana a taƙaice ba tare daya kalleta ba.          Koda ta kammala tazo miƙa musu sai da fara bama Jawaad, saboda neman magana saida tai yanda hannunsu ya gogi juna, hakanne ya saka Jawaad ɗago idanu ya kalleta, yanda ta kafesa da natane ya sakashi yin luuu da nasa cikin salon isa irin na mazan da suka isa ya janye daga nata yana faɗin, “Thanks” a hankali.      Tai murmushi saboda jin daɗin godiyar da yay mata, wajen zamanta ta koma bayan ta bama Aliyu da Gimba suma, inda take facing ɗin Jawaad da har yanzu bai kai shayin bakinsa ba yana cigaba da danna lap-top ɗinne.      Amaryar Alhaji kokino ce ƙarshen shigowa cikin shiga ta alfarma, ta samu waje nesa da kowa ta zauna.        Sai lokacinne Jawaad ya janye system ɗin daga saman cinyarsa yana maida hankalinsa garesu.         Shayin yakai bakinsa kafin ya basu dukkan nutsuwarsa yanayin gyaran murya.          “Zakuyi mamakin cewar da nai a tattaromin ku duka, so amin afuwa idan na shiga rayuwarku da yawa. Dama dai akan maganar Alhaji ne, maganar gaskiya a koda yaushe lamarin nan sake rikitar damu yakeyi, musamman idan mukai dubi da lafiyar ALLAH suka baro filin jirgin, ku kuma gashi kunce bai shigo gidannan ba, sai labarin rashin ganinsa aka kawo muku”.       “Hakane kam yallaɓai, mu kanmu mun rasa yanda zamu kwatanta al'amarin gaskiya”.         Kai Jawaad ya jinjina yana duban Amaryar Alhaji.       “Hajiya kece kuka dawo da Alhaji daga tafiya ai?”.      Zamanta ta gyara sannan cikin isa tace, “Tabbas tare muka dawo, sai dai shi gida aka wuto da shi, ni ko gidanmu na wuce saboda uzirin san zuwa na duba mahaifiyata da bata da lafiya, mun rabu dashi akan zaije gida ya kimtsa shima sai ya zo yaga jikin nata”.         Jawaad yay murmushin gefen baki a zuciyarsa ya furta “Kamar yanda aka shirya kenan”, a fili kam sai ya jinjina kansa yana maida hankalinsa ga Uwargidan Alhaji da fuskarta kawai ta isa ta nuna maka tsagwaron damuwarta.           “Maganar gaskiya Hajiya a yanda nazarina ya nunamin Alhaji ya shigo cikin gidannan, cikin abu uku kuma tilas ɗaya ya kasance”.        Kusan gaba ɗayansu zuba masa ido sukai cikin wani irin zumuɗi, suka haɗa baki wajen faɗin, “Yana cikin gidannanfa kace yallaɓai?”.        “No, ba ayanzu nake nufiba” Jawaad ya faɗa yana miƙewa riƙe da kofin shayi a hannu, tamkar malami da ɗalibai haka ya tsaya musu ƙikam dan ya samu damar nazarin fuskar kowa a falon.         “Cikin abu uku dana ambata dolene a samu ɗaya kuwa, na farko shine, ko dai an shaƙama Alhaji wani abu an barsa a motar da aka ɗakkosa sannan aka sanar da ɓatansa gareku, da ga baya kuna cikin wannan ruɗanin aka sake fita dashi daga gidan, kokuma ba'a fitan dashiba yana cikin gidannan har yanzun, ko kuma tunma a hanya drivern sa ya bada ƙafar da akai canjin motar da aka ɗaukesa da wata, ina nufin da haɗin bakinsa a ciki, dama duk wanda suke tare a wannan lokacin        Cikin fusata Amaryar Alhaji Kokino tace, “Ban gane mi kake magana akaiba ɗan saurayi, ya zakayi jam'u akan duk wanda yake tare dashi?”.          Jawaad ya rumtse hannunsa da ƙarfi yana feso numfashi mai zafi, dan ya fara hasala da maganar hajiya Amarya, amma kasancewarsa gwanin ƙwarewa akan aikinsa sai yay azamar dai-daita kansa, “Hajiya ke ai babuke a ciki, saboda tun a filin jirgi kuka rabu kikace? To miye haɗinki ma da tawagar wanda sai da suka shigo har gida dashi?”.        “Hakane” ta faɗa aɗan daburce.        Kusan da yawansu lamarinta sai da ya basu mamaki, amma sai basuce komaiba.     Jawaad ne ya katse musu tunani da kiran sunan Gimba.     Gimba dake daga can gefe yana aikin nazarin kowansu yay saurin faɗin, “Yes Boss”.        “Kiramin mai gadin gidannan”.     Da sauri gimba ya fice, Jawaad kuma ya sake kallon budurwar ɗazun Shema'u data haɗa musu shayi yace, “Zan iya ganin ma'aikatan gidannan duka?”.       “Mizai hana boss” tai maganar da salonta na jan hankali.      Idanunsa ya janye yana faɗin, “Wannan ƴar matsalace” a saman laɓɓansa.......      A mamakinsa sai yaji tace, “Mi kace?”.      Kai ya girgiza mata alamar babu komai.       Cikin mintuna ƙalilan kowa ya hallara, Jawaad ya bisu da kallon nazari, kafin yace, “Inason ku bani haɗin kai, duk maganar da wani ya faɗa daga baya na fahimci ƙarya a cikinta sam bazan yafe masa ba”.      Duk suka amsa da cewar zasu fa ɗi gaskiya.       Kansa ya jinjina musu ya koma cikin kujera ya zauna, “Mai gadi da kai zan fara”.      “To yallaɓai”. “Kaine a gate, kuma dolene komai nisanka da inda mota tai parking a gidannan sai kaga wanda zai fito a cikinta?”.      “Ƙwarai kuwa yallaɓai”.         “A randa Alhaji ya dawo motoci nawane suka shigo gidannan?”.       “Inaga dai kamar biyarne”.      “Kanaga kokuwa ka tabbatar”.        “Ayi haƙuri yallaɓai na tabbatar”.        “Idan Alhaji zai shigo gidannan kafin ranar yana tsayawa gaisuwa da ku? Kokuwa shigewa kawai yakeyi?”.        “Eh idan aka tsaya da mota ya fito daga ciki sai muje muyi masa barka da zuwa kafin ya shige cikin gida”.       “To aranar kunyi hakan?”.       Jimm mai gadi yayi bai tankaba, sai da Aliyu yace, “Ya dai?”.      Firgigit Mai gadi ya dawo hayyacinsa, cikin in  ina yace, “Gaskiya bamu gaisa ba, dan na nufi zan gaishesa kenan bayan rufe gate da nayi sai najiyo suna taraddadin baya cikin motar ai”.       “Waye ya fara ambata baya cikin motar?”.      “Bazan iya ganewa ba, saboda ruɗanin dana tsinci kaina a ciki, kuma darene”.       Jawaad yay guntun murmushi yana lumshe idanunsa, da alama akwai ɗan ɓacin rai tattare dashi.     Da sauri ya sake kallon maigadin da har yaji daɗi an gama dashi, “A daren wace motace ta fara fita a gidannan?”.           “Da yake kasan darene yallaɓai, amma mota kusan uku suka fita, sai dai bazan ce gasuwa da suwanene a cikiba, saboda ruwan sama da ya ɓalle.........”     Da ƙarfi Jawaad ya daki tebirin gabansa a wata irin fusata yace, “Ƙaryane!! Dolene ma ka sani”.      Babu wanda bai zabura ba a falon.      Ya kallesu da jajayen idanunsa cikin matuƙar tsawa yace, “Tabbas wanda ya aikata garkuwa da Alhaji yana cikinku, a cikin gidannan yake!! Akwai haɗin bakin wanda ya sanshi, Idan kuma har ya bari na kamashi da hannuna kashinsa ya bushe!” ya ƙare maganar yana nunasu da ɗan yatsa su dukansu, ya miƙe a fusace yana fisgar rigar suit ɗinsa ya rataya a kafaɗa ba tare da ya sauke hannunsa ba ya fice abunsa.      Aliyu ya miƙe da sauri yazo ya ɗauki lap-top da wayar Jawaad da ya bari yabi bayansa da sauri shima yana faɗin, “Hajiya ku sa ido wa junanku kamar yanda ya faɗa”.        Aiko kafin kace mi, hayaniya ta ɓarke a tsakanin Jama'ar gidan babu maijin ta wani, duk ɗinsu Jawaad ya saka musu zargin junansu da bayanin Aliyu na ƙarshe.        Jawaad kam tunda ya fito a harabar gidan yay tsaye yana dube-dube tamkar mai neman wani abu, nanko nazarin komai yake a cikin ƙwarewar aiki.           Gimba da Aliyu suka ƙaraso, a bayansa suka tsaya suna binsa da kallo, ba tare da ya kallesu ba yace, “Aliyu mika fahimta game da kowansu?”.         “Boss abubuwa da yawa ai, wannan mai gadin da alama yasan wani abu, sai dai kamar yanajin tsoron faɗa, hakama amaryar Alhaji ban yarda da itaba, sai ko dattijuwar data kawo abinci kafin kowa......”         Kallonsa sosai Jawaad yayi, ya tsaresa da idanu tamkar a jikinsa ne zaiga gaskiyar abunda yake buƙatar, sai kuma ya saki lallausan murmushi yaɗan kashema Aliyu ido ya juya a hankali yana takawa cikin izza dajin lallai shi ɗinfa ya kai”.       Murmushi gimba da Aliyu sukayi, dan sunsan halin mai gidan nasu akan iya aiki, tabbas fusatar da yay harya fito ba'a banzaba, yana kan sani ya jefa zargi a zukatan jama'ar gidan baki ɗaya...... _________________________ BILKEESU _________________________           Yau gaba ɗaya tunda na tashi banajin daɗi, da ƙyar ma na iyayin sallar asubahi na koma na sake kwanciya, kowa yasan ba ɗabi'ata bace baccin safe, dan tunma ina gidanmu na haya bansamun hakan, balle yanzu da aikin gidansu inna zainaba kawai ya isheni.        Cikin barci kawai naji saukar ruwa mai azabar sanyi a kaina.     A matuƙar firgice na tashi zaune jikina na wani irin ɓari na razana da sanyin ruwan, ga zazzaɓi dake jikina daman.       Lawusa ce tsaye kaina tana hura hanci tamkar wata guguwar tsakkiyar rani.      “Sannu isassa, waye ɗan iskanki a gidannan da zai tashi ya ɗaura miki abimci ki tashi kici? K bara kiji, bakifa da maraba da ƴar aiki a gidannan, dolene ki bauta mana mu biyaki da abinci da wajen kwana, inko ba hakaba to lallai kuwa sai dai idan gidan zaki bari”.          Yau rana ta farko a rayuwata da nakejin bazan iya ragama Lawusa ba, hakan yasa na miƙe a bazata na zazzaro mata idanuna dake jajur saboda zafin ciwo, nakai hannu na cakumo mata wuya na maƙureta a bango,        “Tunda gidan Ubanki ne dan ALLAH Lawusa karki barni yau na kwana a cikinsa, ke wai shin jakar wane yankin jejice da bakisan darajar ɗan adam ba?! Ko an gaya miki tsoro kesa ɗan adam shiru-shirune?”.     Na ƙare maganar ina hankaɗata ta bugi da buhun masara dake ɗakin.        Ai kafinma na sake cewa wani abu ta fita a guje tana kururuwa wai akawo mata ɗauki zan kasheta.      Tsaki nayi na zube a ƙasa kamar mara laka a jiki, sai kawai naji hawaye masu zafi na saukamin a kumatu, ga wani irin rawa da jikina keyi tamkar mazari.      A haka naji mutum biyu matan maƙwafta sun shigo suna hayaniya, sai sannama na fahimci daga ni sai Lawusa ne a cikin gidan kenan?.          Sunyi maganar duniya nai banza dasu tamkar banajinsu, sai uhu sukemin a kai wai ban ƙyautaba, kalloma basu isheniba.     Lawusa kuwa tana daga bakin ƙofa taƙi shigowa tana kukan munafunci da danƙaramin zagi ta uwa ta uba da gori iri-iri.        A wannan yanayin inna ta shigo ta iskemu, ta tambayi ba'asi, Lawusa ta zauna ta shirya mata ƙarya da gaskiya, hakama matan da suka shigo, tsabar munafunci harda cewa da ƙyar suka ɓanɓare Lawusa a hannuna.........✍🏻 Page 18 ...........A mamakin kowa sai mukaji Inna tace, “To kukam ALLAH ya ƙyauta muku, na lura sam jininku bai haɗuba, bara Aibo yazo, ai na samo maganin wannan yawan fitinar taku mara dalili”.            Ba Lawusa kawaiba, koni kaina nayi mamakin maganar inna, danni a zatonama yau saita koreni a gidan saboda na taɓo ƴar mai ɗinta, amma ji yanda ta nunama halin ko in kula akan zancen, sai daimaganarta na ƙarshe akan mafitar data samo ta tsayan a zuciya sosai, komawa nai na kwanta ina rawar sanyina.      Lawusa kam kuka ta sanya rurus wai dama inna bata ƙaunarta ai a gidan, yau sai ta tattara ta barmusu gidansu, sai inna ta aurama Sha'aibu ni a yau da rana danta nuna ma duniya ni ƴar uwartace”.     Duk surutan nata dai inna bata kulaba, matan kuma da sukazo haɗa munafinci sai gasu suna jan ƙafa suna fita ɗai-ɗai da kunya.      Ina jiyo fitar Lawusa tana cigaba da zagin Inna.      Kaina kawai na girgiza ina mamakin irin wannan tarbiyya ta Lawusa, a hakane wannan zata zama uwar wasu, ita kanta tana buƙatar tarbiyyar balle abinda zata haifa.      A haka wahallalen barci ya kwasheni, ban tashi farkawaba sai lokacin sallar zuhur, shima dai inna ce ta tasheni akan naje nai sallah.        A mamakina kuma na fito zanyi alwala sai naga inna tayi abincin rana da kanta bata tasheni ba.        Salla nayi, ina zaune sai ga sallamar Yaya Shu'aibu ya dawo cin abincin rana kamar yanda ya saba, muryar Inna na tsinkayo tana sanar masa bani da lafiya, hakan ya sakashi faɗin “Subahanallahi, miya sameta kuma?” yay maganar yana ɗage labulen ɗakin.       Sannu nai masa sannan na gaishesa, cike da kulawa ya amsa, ya ƙarasa shigowa ɗakin yana tambayata mike damuna?.       “Yaya zazzaɓine kawai, kuma Alhmdllh yama sauka”.       “Wayyo sannu, ai ko sauron gidannan ya isa saka mutum zazzaɓi, kici abinci saina kaiki kamiz ki amshi magani”.      Nace “to” tare da masa godiya.      Nanma nazata Inna zatace a'a sai naji batace komaiba, sai ma amsar tambayarsa akan Lawusa take bashi, duk abinda ya faru tsakanina da Lawusar ta zano masa, ta ɗora da faɗin, “Ni yanzu na samo mafita akan wannan yawan rigimar tasu, fitar danai yau wani gida ƴar kande ta rakani na samowa Bilkisu aikin wanke-wanke da shara, inasha ALLAHU tananma sai kaga ta haɗa kuiɗin kayan ɗakinta har muma mu mora, kaga bama ta yini gidanba balle wannan fitinar ta cigaba da girmama a gidannan”.         Shu'aibu da fuskarsa ta ɗan nuna alamun damuwa, yace, “Amma Inna ni dai da kinyi shawara dani da ba'ayi hakaba, wane kuma aikin wanke-wanke Bilkisu zatajeyi fisabillahi, ni dai duk da sana'ata ba wata mai ƙwari bace zanyi iya bakin ƙoƙari wajen sauke haƙƙin zuminci akan komai na aurenta, indai dan zaman gidane zanma matarcan ta tsallake magana Bilkisun taje ta fara koyon ɗinkin jakka a wajenta, kinga ko aure tayi ai tasamu madogara insha ALLAHU”.       Ran inna a ɓace tace, “Nikam Aibo bansan miyasa kake nina tamkar ina zalintar yarinyarnanba, yanzu shi aikin da zataje bazai taimaketaba ne? Ko aure tayi ai dai ta samu ta iya komai”.        “Hakane Inna, nima banƙi ta takiba, muyi addu'a to ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi a ciki, idan ta samu lafiya sai muyi maganar”.      “Shike nan” Inna ta faɗa a taƙaice, da alama dai har yanzu ranta babu daɗi akan canja mata tsari da yayi.      Bayan mun gama cin abincine ya ɗaukeni a napep ɗinsa zuwa ƙyamiz, an bani magani tare da allura muka dawo gida.      Mamaki ya kamamu saboda iske jibga-jibgan motoci guda biyu da mukayi a ƙofar gidan, sai walƙiya suke.       Na kalli Yaya Shu'aibu ina faɗin, “Yaya baƙinmu ne waɗannan kokuwa?”.       Cikin jimami yace, “Wlhy ban saniba Bilkisu, amma inhar hakane to lallai inaga Kawu Ali ne kuwa yazo, dama lokaci-lokaci yakanzo su gaisa da Inna idan ya samu dama?”.        “Kawu Ali? Shikuma wanene shi?”.      Da mamaki sosai akan fuskarsa ya kalleni, “Bilkisu kina nufin wai baki san Kawu Ali ba shima? Yayansu Inna ne fa, ɗakinsu ɗaya da Inna ai”.           “Wlhy ban sanshiba Yaya, kana nufindai shima babansu ɗaya da Innata kenan?”.      “Ƙwarai kuwa Bilkisu”. “Yaya to ko shine suke cema Ɗan iya?”.        “Ƙwarai kuwa Bilkisu shine, amma nayi mamaki, na lura dai ke babuma wanda kika sani a dangin kenan?”.        Murmushin yaƙe nayi zuciyata na suka, murya na rawa nace, “Ai yaya sanda Innata nada rai babu wani ɗan uwanta dake raɓarta, nasan dai lokacin ina ƙarama takanje dani wasu wajajen gidan dangi, amma sai na lura saboda tana da nakasa kamar kowa gudunta yakeyi, Inna Zainabu ma abinda yasa ban manta da itaba ita da Kawu Manu saboda Innata na yawan ambatarsune”.        Tausayina sosai na gani a fuskar Yaya Shu'aibu, ya girgiza kansa kawai yana sauke numfashin tsantsar takaici, “Karki damu Bilkisu, komai na rayuwa da kika gani akwai ƙalu bale, watarana sai labari, irinku da kuke tashi cikin rashin gata ALLAH yafi ɗaga darajarku da ni'imomi masu yawa da komawa birge wanda suka juya muku bayan a lokacin da kuke buƙatar taimako, mu shiga ciki kinji, ALLAH ya ƙara miki haƙuri da jimirin cinye jarabawar rayuwa”.       Murmushi nayi ina share hawayen da suka zubomin a fuska, kusan a tare muka fita zuwa cikin gidan.           Ashema ba shi kaɗai bane harda iyalinsa, matarsa da ƴaƴansa namiji da mace su biyu, kallo ɗaya nai masa na gano asalin kamanninsa da Inna zainabu, yana kuma yanayi da innata itama, da yake ni sam ban biyo innata komaiba, gaba ɗaya kamannina na babana ne, dan dana biyo Innata da nazama ƙyaƙyƙyawa kuwa, dan su jinin fulanin asaline.      Inna tanata hidima da baƙinta, bakinta kam a washe tamkar gonar audiga.       Duk tsugunnawa mukai ni da Yaya Shu'aibu muka gaishesu, inna daketa faman washe haƙora tace, “To ka gantanan Ali, wannan itace ɗiyar Asiyar da nake faɗa maka”.        Idonsa a kaina yace, “ALLAHU akbar, ashema ta zama budurwa? Koda yake rabona da ganin Asiya tunfa kafin nabar ƙasarnan, lallai sheɗan ya jagoranci zukatanmu wajen raunana zuminci, yanzu ace ɗan uwanka da kuka tashi gida ɗaya dan aure ya ɗaukesa shikenan sai zuminci ya yanke? Manu ne ma wlhy yake sanarmin rasuwa lokacin bana ƙasar shiyyasa banzo ta'aziyya ba, ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata, ke kuma data bari ALLAH ya rayaki kinji”.      Hawaye na share ina amsawa da amin.       Daga nan ya koma kan Shu'aibu yana masa tambayoyi akan yanzu mi yakeyi?.      Matarsa dai da ƴaƴansa basa cewa Uffan, saima faman danne-dannen wayoyi sukeyi.      A cikin tambayoyin da yakema Yaya Shu'aibu ne yakejin ai ya kammala diploma ɗinsa, daga haka karatun ya tsaya, a take yace ya bashi takardun zai nema masa makaranta ya koma, ya juyo gareni yana tambayata nifa?.      Kaina a ƙasa nace, “Ai kawu ni koma Secondary ɗin ban kammala ba”.        Ya ɗan nuna damuwa saman fuskarsa, hakanne ya sakashi maida kallonsa ga Inna yana faɗin, “To nifa inaga wannan itace hanyar dazan gyara kuskurena akan Asiya, Zainabu zan tafi da Bilkisu ta zauna a gidana cikin ƴan uwanta, itama ta samu ilimin da zata taimaki kanta koda anan gaba babumu a raye”.      Take fuskar Inna ta canja launi, hakama matarsa da ƴaƴansa wani kallo na sukemin mai kama da wannan ƙazamar?.     Yaya Shu'aibu ne kawai ya bayyana tsantsar murnarsa a fili, kafinma inna ta bada amsa tuni Yaya Shu'aibun nata godiya.     Hakan ne ya dakatar da ita daga son hawa dokin naƙin datai niyyar yi.        Niko bammasan yazan fasalta muku yanayin dana shigaba, ɗumin hawaye kawai nakeji suna bin kumatuna, duk da naga rashin jin daɗin iyalansa hakan bai hanani ƙwaɗayin binsu ba, koba komai burina nayin karatu mai zurfi ashe zai cika a duniya, insha ALLAHU zanyi haƙuri da kowane irin halin daza fuskanta daga garesu domin samun cikar burina”.       Abu kamar wasa sai ga magana ta zama babba, dan kuwa dai Kawu Ali cayay nai shiri mu wuce, ba kuma saina ɗauki komi ba, ni kaɗi suke buƙata.       Tashi nai nayi wanka kamar yanda Yaya Shu'aibu ya umarceni, sai gani na fito tsaf cikin irin kayan da Sani ɗan gidan Uwargida ya bani kala uku.     Yanda na ɗanyi tsaf na kula ya sakasu mamaki, dan sanda nake ɗazu kam tamkar an kwatonj da ga bakin kura ne.      Kewar Yaya Shu'aibu kawai naji, amma Inna da Lawusa banji komaiba kam, Yaya Shu'aibu ya kwantarmin da hankali akan ai tunda inacan zai dinga zuwa dubani, da dai kam baya zuwa, dan sau ɗaya ma ya taɓa zuwa gidan, tunta kuma matar Kawu Alin tai masa wulaƙanci shi da inna bai sake zuwa ba koda wasa, amma yanzu darajar zan zauna a gidan zaike zuwa insha ALLAHU.       Yamin nasiha yanda zanyi ƙoƙarin zama da kowa lafiya ba tare da anyi kuka da niba, ya sake maimaitamin muhimmancin haƙuri a duk halin da zan tsinci kaina.      Godiya nai masa cikin share hawayena.            Da zamu wuce har mota suka rakomu, Kawu da matarsa suna a mota ɗaya, yaransuma motarsu daban, to nima sai akace na shiga motar yaran nasu.      Ina kallon namijin baiso hakanba, dan harda guntun tsaki yaja, macenma tanata ƙunƙuninta da ba kowa kejiba.      Suna gaba niko ina zaune a baya a maƙure tamkar wadda aka sace, a haka muka bar anguwar su Inna na ɗaga mana hannu, niko ina share hawayen sabo dana farayi dasu....... ________________________ JAWAAD ________________________                 Koda suka baro gidan Alhaji kokino station Gimba ya nufa dasu, Jawaad kawai ya fita a motar amma banda Aliyu, dan ɓoyensu akeyi ba kowa yasan da dawowar tasuba.         Gimba ya juya da mota domin maida Aliyu gida, yayinda wani ya ƙaraso da sauri ya amshi kayan hannun Jawaad bayan ya gaidashi cikin girmamawa.          Fuskarshi da ɗan murmushi ya amsa masa, yana gab da shiga Office ɗinsa ya hango Qaseem na fitowa daga Office ɗinsa cikin hanzari, da alama dai wani uzirin zaije, baki Jawaad ya taɓe ya shige abinsa.             Aiki garesa danƙam a office ɗinan, harma tunanin ta ina zai fara yakeyi, ya zauna yana sauke numfashi bayan ya rataye rigar suit ɗinsa jikin kujerar.        Yana duba sabbin files ɗin daya iske a saman tabir ɗinsa yana murmushi sai kace wani zararre, shi kaɗai yasan mi yake tufƙawa a zuciyarsa.           ★★★★★★              Saboda ayyukan da yayi sosai, ga mitin da suka zauna bai bar office da wuriba, lokacin da suka hau titi gimba ke tambayarsa ina zasuje? Sai kawai ya bashi amsa da suje gida, dan haka kawai yakejin sha'awar zuwa gidan yau kodan yaga ɗan tayin cikinsa yaji sanyi, duk da bashi da tabbacin Shahudah bata aikata abinda tai niyyaba, tunda yasanta da taurin kai.       Gidan gaba ɗaya babu wuta, hakanne ya bashi mamaki, dan koda babu wutar nepa akwai ƙaton janareto da ake kunnawa da daddare.       Ba tare da ya fita a motarba ya cema gimba yaje ya duba mike faruwa da janareton, dan yasandai ba lafiya ba, tunda dama kullum shike hidima akansa, koda baya gari jan... Ɗin ya samu matsala basajin kunyar kiransa su sanar masa duk da kuwa ALLAH ya basu arziƙi gwargwadon ikon da suma zasu gyara matsalar.       Sai dai bazasuyi hakanba, saboda ɗunbin dukiyar da aka barma Jawaad ɗin itace kawai idonsu ke gani.       Gimba da ya dawo yaɗan risino daga waje yana kallon Jawaad dake danna waya harken ya haske kamilalliyar fuskarsa.      “Boss waifa kaji yaƙi tashine, tun ɗazun ojo yake ta fama, yanzu hakama na iskesa yana ƙara dubawane koza'a dace”.       Janye idanunsa yayi daga kan wayar ya maido kan gimba, fuskarsa da ɗan alamun ɓacin rai yace, “Shine kuma dan wulaƙanci bai faɗaba tun ɗazun a ɗauki mataki?”.       “Wlhy Boss nima namasa wannan faɗan, amma sai ya nunamin ya faɗama kawu babba tun wajen 6, amma sai yace masa yaje sashenka idan ka dawo ya sanar maka, shikuma yazo madam tace bakama kwana gidaba”.          Tsaki kawai Jawaad yayi, ya buɗe motar zai fito, hakanne ya saka Gimba matsawa baya ya bashi hanya.        Yay gaba gimba kuma ya ɗauki ƙaramar jakkar dake gefen Jawaad ɗin ya bisa da ita, kafin ya ƙaraso gareshi harya shige falonsu.        Shahudah na kwance a falo tana kallon tasharta da tafi so saboda waƙoƙi da ake sakawa, sai dai yau anyi abin arziƙi sifikun can ƙasa aka sakasu babu ƙara sosai, kallo ɗaya Jawaad yay mata ya janye idonsa yana fara taka steps ɗin benan.       Tamkar sokuwa haka Shahudah ta bisa da ido, idanunta harsun fara tara ƙwalla......        Ƙwanƙwasa ƙofa da akaine ya sakata maida kallonta wajen, kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa da yes.         Jawaad na step ɗin ƙarshe yaji Gimba ya shigo falon yana gaida Shahudah da cewa ga jikkar boss, tsayawa yay cak saboda wani abu daya taso masa a maƙoshi na ɓacin rai, bakomai bane face tsantsar kishi mai gauraye da baƙin ciki, saboda kayan da yagani a jikin Shahudah, amma dan rashin mutunci ta bama Gimba damar shigowa ba tare da yunƙurin suturta jikinta ba.      Kasa jurewa yay sai da ya juyo ya kallesu, gani yay kan gimba a ƙasa ya juya zai fita, yayinda Shahudah ke tsaye zata je ta ɗauka jikkar a inda Gimba ya ajiye saboda yanda ya ganta bazai iya ƙarasawa gabanta ya bata ba.      Sosai idon Jawaad yay jajur, babu tsammani ma yaji ya cika da hawaye saboda tsabar kishi, juyawa yay kawai ya ƙarasa hayewa batare da yayi mata magana ba.         Yana tsaye gaban mirror yana saɓule rigar saman suit ɗinsa Shahudah ta shigo, baiko kalleta ba ya jefa rigar kan sofa ya fara sassauta tia ɗin wuyansa.        Itama bata tanka masanba taje ta ajiye jakkar saman tebir ɗin gaban gadon sannan ta zauna fuska a ɗaure, ita a dole yanzu tabar sakar masa fuska.      Daga inda take take hangosa ta cikin mirror yana ɓalle maɓallan rigar sa ta ciki kalar bulu, harya gama farar best ɗinsa ta bayyana bata iya janye idonta ba, ya kunce belt ɗinba da saɓe dogon wandon ya faɗi ƙasa sannan yajawo stool ɗin mirror ya zauna ya saɓile ƙafarsa daga cikin wandon, yana fara cire takalmi ne Shahudah ta fara magana cike da gadara kamar yanda ƙanuwarta Aamila ta bata shawara, dan tace inba haka takema Jawaad ba bazai dana cin tuwo akanta ba, itama dai ta yarda da hakan ɗari bisa ɗari, shiyyasa farawa tun daga yanzu.         “Ban taɓa tunanin baka ƙaunata ba sai akan wannan ɗan iskan cikin, wai yau harni kake ƙwatanta zaɓa da ciki bb,  walhy ka bani tsantsar mamaki, ni son gaskiya nake maka, dan haka bazan danganta martabarka da ciki ba, zan haifesa kamar yanda ka buƙata, sai daifa ka tabbatar tunma daga yanzu wlhy bazan shayar dashiba, dan ƙirjina bazai zube a banza ba, kaima baka samuba balle wani ɗanka, sannan lokacin da ciki yakai haihuwa sai dai amin cs bazanje wajen haihuwa na buɗe a wofi ba ka samu zarrar bin wata, danku mazan hausawa yanda kuka san bunsiraye akan mata haka kuke.....”      Ba ƙaramin sukar Jawaad maganar Shahudah ta ƙarshe tayi ba, da har zaice mata harda ubanki ma bunsurunne kenan saikuma ya haɗiye abunsa kawai yay shiru yana miƙewa bayan ya zame safar ƙafarsa, dolene ya koyama yarinyarnan ɗanyen hankalin da ƙwaƙwalwarta zata dawo aiki tamkar ta kowa, wlhy ya yarda wayewar da babu ilimin addini a ciki ba ƙaramin daƙiƙanci take kawowa mai itaba.       Ƙala bai ce mataba, baima ko kalli sashen da takeba yay shigewarsa bayi domin samu ya watsama jikinsa ruwa.............✍🏻 Page 19 ..........A wannan tsakanin kam sai abubuwa suka sake rikice musu a gidan, dan salo-salo na rashin mutunci Shahudah ta ƙaro take tsulama Jawaad, shiko sai ya watsar da ita tamkarma bai san da ita a gidanba, yama koma ba kullum yake kwana a gidanba, gara yaje gidansa da su Aliyu suke yay kwanciyarsa acan, idan suka takura masa da tambayar lafiya yace Shahudah bata nan ne.     Tun suna yarda da zancensa har suka fara zargin akwai dai wata a ƙasa, amma tunda bai basu damar saniba sai basu takura ba, sun dai ɗauki aniyar tayasa da Addu'a.          Cikin hikimar UBANGIJI sai yay ma Jawaad maganin Shahudah ta hanyar jarabtarta da laulayi mai azabar tsiya, dan takai yanzu ma sai da taimakon wani take iya wasu abubuwan, shi sai bai duba abinda take masaba, a duk lokacin da ta nema taimako yakan taimaketa inhar yana gidan.          Abu ɗayane har yanzu ta kasa samu a gareshi, shine sakin fuska, gaba ɗaya tabar ganin haƙoransa a waje, baya wata doguwar magana da ita, idanma yanaji da shariyar sai yazo gidan ya fice bai tanka mataba, tun abun baya damunta harya fara yanzu, dan kuwa tana tsananin buƙatarsa a kusa da ita kuma, sai dai dukkan damar hakan ya toshe mata ita.       Inhar a gidan ya kwana da safe zai leƙa ɗakinta yaji yaya jikinta?, zai kuma tambayeta abinda take buƙata, inhar ta faɗa zaisa a sayo mata.      Idan kuma da dare ya dawo koda ya isketa a falone zai tambayeta yaya ta yini? tana buƙatar wani abu? Iya amsar data bashi zai saurara yay wucewarsa ɗaki, yana shiga yake kullowa dan karma ta shigo masa. Ba ƙaramin zafi hakan yake mataba, harma tanaji tamkar taje ta zubar da shegen cikin taga ƙarshen iskancinsa.       Sai dai zuciyarta na tuna mata gargaɗinsa na ranar, yayi rantsuwa da inhar ta zubar ta tsinka igiyar aurensu duka uku, tasan wanenen Jawaad, tasan kuma zai iya tunda har ya hau dokin zuciya akan hakan..        Ita shaida ce akan haƙurinsa, sannan kuma tasanshi inhar yay zuciya da abu akansha fama kafin ya waiwayesa, a zahiri mutane sukaga sauƙinsa yayi yawa, amma saika nutsu dashi zaka fahimci murɗaɗɗen halinsa na ra'ayin riƙau, mahaifiyarta kace mata haka mahaifin Jawaad yake, dan haka dukkan hallayar Jawaad na ubansa ne, ya kuma kwaso wasu daga uwarsa, dan itama lumbu-lumbu take wutar ƙaiƙayi.        A yau dai kam lamarin nasa ya mata tsanani, dan ko mama Atika tabi duk hanyar da zataga Jawaad yaƙi bama kowa damar hakan hatta da kawun nansa, saima Qaseem ne ya samu damar gaggaya masa magana a kan Shahudah a office, sai kuma Jawaad ya manna masa hauka ya sharesa tamkarma bai san da shiba.       Waɗannan abubuwa suka taru akan Shahudah sukai mata yawa, dan haka ta shirya zuwa gida kozata samu sassauci dan yau tana ɗan jin jikin da sauƙi.      Dama ita babu tambayar fita a tsarinta, shirin ta tayi ba tare data nema izininsa ba, shi dama baya gidan, a office ya kwana yau.         Shirinta tayi cikin wando da riga jeans da top baƙa mai adon stones an runbuta *Beauty* da manyan baƙi da su, tayi ƙyau dan ƙyau, saboda farar fatarta na ɗaukar wankan ƙananun kaya da kalar baƙi, cikin a lafe kamar babu ɗa a cikinsa, yau dai ba'a samu damar zane fuska da kwalliya ba, fauda kawai aka shafa sai lipsgloss, ƴan arziƙin na kusa kuma, aka saka kimono tare da yafa siririn gyale akai, sai dai an saki rigar ba ɗaureba, hakan yasa taketa jan ƙasa a baya, ga glasess baƙi da aka toshe fuska dashi, ta dai fito asalin ƴar gayenta lamba ɗaya kuma shafin farko a jaridar manya.         Da kanta taja motar, yayinda kiɗa mai taushi ke tashi daga sifikun. _______________________ BILKEESU _______________________               Tun a harabar gidan nake tsarkake sunan ALLAH, dolene akira dukiya jarabawa ga bawa, yanzu mai wannan muhallinma dan yace ya manta da danginsa ai bakaga laifinsa ba, wani dai saikaga tamkar alƙalamin rubuta ƙaddarar rayuwarsa a hannunsa yazo.......         Zungurata da akaine ya sakani dawowa hayyacina babu shiri, harara ta gallamin da jan tsaki, “K dalla baƙauyar banza ki wuce muje, kin wani zauna kallon gida, halan yau kika fara ganin irinsa?”.        Bance komai ba, sai bin bayanta da nayi kawai.       A falonma dai akwai abin kallo da bakima bazai iya lissafowaba, abinda kawai zan iya faɗa hotunan masu gidan da aka ƙawata adon falon dasu, a yanda naga hotunan da alama yaran nasama sun zarta biyu, dan kuwa bayan waɗan na gani ga mutane uku kuma a hoto, namiji haɗaɗɗen saurayi maiji da kansa, sai ƙyaƙyƙyawar budurwa da tafi dukkan ƴan gidan asalin ƙyawu, saikace wata jinin larabawa, dan nikam bazan ce baturiya ba, dan ba ƙyawunsu nake ganiba, sai dai shigar tatace kam sak ta turawan ce, sai hoton namiji again da bazai wuce shekaru goma sha biyarba, hoton dai da gani tsohon hotone.      Na sake waigawa ko zanga inda yake babba sai dai babu.       Tunda muka shigo kawu saman bene ya haye, hakan ya saka hajiya binsa itama.        Suma duk sai suka shige ɗakunansu aka barni ni kaɗai a falon tamkar mayya, hakan baisa naji rashin daɗiba, koba komai nasamu damar yima falon kallon tsaf ai.      Sakkowar hajiya daga saman bene ranta a ɓace ne ya sakani kallonta, sai kuma na duƙar da kaina saboda mugun kallon data jefeni dashi, kafin tace wani abu sai ga Kawu ma ya sakko fuskarsa babu walwala.        Ni dai dama a ƙasa nake zaune, sai na ƙara ladabtuwa domin girmamawa a garesu.       Kawu yace, “Ɗiyata taso muje kiga ɗakinki kinji”.        Cikin girmamawa na amsa da “to” ina miƙewa, yana gaba ina biye har ɗan lungun dake falon, ɗakuna ne a jere guda biyu, muka isa har gaban na ƙarshen ya buɗe ya shiga, nima shigar dai nayi.      Ɗakine babba sosai, akwai komai a ciki na amfani tamkar ɗakin matar aure, matar aurenma ƴar gata ta gaske.      Da ƴar ƙura a cikinsa kaɗan, alamun dai ba amfani ake dashiba, komai na ciki kuwa kalar ja da fari ne.......       “Bilkisu nan ne zai zama ɗakin ki kinji, shi ɗin ɗakin ƴar uwarkice datai aure kusan wata tara kenan, yanzu kinga saiki maye gurbinta, inason ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki ɗauki kanki tamkar kowa na cikinsa, yanzu dai idan kin huta zuwa dare zamu zauna dan ki san kowa da sunansa kinji”.       “To kawu nagode sosai, ALLAH ya ƙara buɗi da haske na alkairi”.      Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “Amin ɗiyata, amma daga yau ba kawu ba, ki kirani Dad kamar yanda ƴan uwanki suke kirana dashi, kema yanzu baki da banbanci dasu a gareni kinji”.        kaina na ɗaga masa nima ina murmushin jin daɗin dajin tsantsar ƙaunarsa a raina, shine mutum na shida da arayuwa bazan manta da suba, domin sunji tausayina a lokacin da nake buƙatar hakan ga kowa, sun ƙyautata mani lokacin da jama'ar duniya suke guduna, na share hawayen da suka ziraromin a fuska.      Jinai kawai an kama hannuna, na ɗago na kallesa aɗan firgice, “Haba ɗiyata, banason na sake ganin waɗannan hawayen a fuskarki dan ALLAH, nasan bazan iya ɗauke miki dukkan matsalarki ba a rayuwa, amma insha ALLAHU zan kamanta kinji, ki daure ki saki jikinki, zanji daɗin hakan”.         Murmushi nai masa, “Insha ALLAHU Dad bazaka sake ganiba”.      “To Alhmdllh ƴar gidan dad” yay maganar yana rungumeni.      Duk saina rikice, miye hakan kuma kawun yay min?, nashiga ukuna.        Shima fuskantar abun yazomin wani iri ya sakashi sakina yana faɗin, “muje na nuna miki yanda zaki amfani da banɗaki”.           Komai sai da ya nuna min shi, yakuma tabbatar na fahimta sannan ya fita ya barni ina ƙara gwada fahimtar komai yanda bazan manta ba.      Daga baya kuma na zage na gyara ɗakin tsaf, sai naga ya sake ƙyau saboda gyara na musamman daya samu sosai.    ★★★★★★★★        A daren ranar wajen cin abinci na sake sanin kowa na gidan, dan kuwa duk Dad yaymin bayani a kansu da sunansu.      Duk na fahimta, duk da dai na kula shi kaɗaine ke ra'ayin zamana a gidan, dan ko babban ɗansu da alama ban cikin tsarinsa shima, sai kallon ƙurilla yake bina dashi a yatsine, wanda hakan ya tunomin da Jazuga a zuciyata, koda na koma ɗaki sai da na zubda hawaye saboda tuno firdausi da su inna da nayi, ina kewarsu sosai, inason sanin halin da suke ciki kuma.      Naci kuka a wannan daren har na rasa hawayen tsiyayarwa, dukkannin komaina na baya ya shiga dawomin daki-daki, ganin ina neman cinye daren da tunani sai na tashi na ɗauro alwala nazo naita nafilfilina ina miƙama ALLAH godiya da kukana game da sabuwar rayuwar dana sake shigowa.           Tabbas rayuwar wannan gida tasha banban da duk inda na rayu, ba'a ɓangaren jindaɗiba kawai harda yanayin zamantakewa da tarbiyya.        Gashi dai ina samun komai na buƙata, dan ko sutura kwana na ɗaya a gidan dad ya kawomin masu yawa, sai dai kumafa duk ƙananune, dan babu ko ƙyallen atanfa.      Abincin da kowa zaici nima shi nakeci, babu wani banbanci tanan ɓangarenma.       Sannan bana aikin komai a gidan, kamar yanda yaran gidan suma basa komai sai ƴan aiki, ko gyaran ɗakina ma sai da nai magana mai aikin gidan ta daina min.         Yanayin tarbiyyar gidan ce dai sai addu'a, dan kuwa na kula dai tsantsar rayuwar turaice da ɗabi'unsu ke wanzuwa ga jama'ar gidan.       Duk kayan daga gadama zaka saka babu ruwan wani da kai, babu mai maka faɗan rashin dacewarsu, rungumar juna tsakanin mazan da matan hakan ba komai bane, shima Dad ɗin dazai tsawatar rungumemu yake, rashin girmama na gaba matsayin na yayanka wannan sam babu shi, ɓangaren ibada ba damunsu tayiba idan har ka cire Dad da ba kullum yake zama gidanba, bazan ce maka arana suna cika salla biyar babu tsallake ba har Mommy ɗin, maganar Qur'an ma ban gansa a gidanba tunda na shigo, amma akwai ɗaki na musamman domin karatu, cike yake da kowanne nau'in littafin daya shafi boko harma dana labaran turanci, komai kayi a gidan sunansa ƴanci kawai, babu mai cemaka akwai kuskure a ciki.        Duk ɗabi'un nasu sunmin girma, na kasa kwaikwayon ko guda ɗaya a ciki balle na riƙesa matsayin cigaba.     Hakan yasa a kullum suke hantarata da suna baƙauya ko bagidajiya, bana damuwa dan bana samun sakewar fuska daga kowannensu dama idan ka cire Dad, idan baya gida babu maimun magana sai hantara da harara.      Iyakar nan dai tsananin ya tsaya min, shiyyasa bai cika damuna ba sosai.      A ƴan kwanakin dana samu a gidan jikina harya fara nuna alamun canji, dan kuwa fatata ta fara gogewa, sannan jikinma dai da alama ƙiba zai fara, baƙina da kullum suke zagina a kansa ya fara korewa, dan duk sanda Yah Qaseem zai hantareni yakan kirani da suna baƙar banza.       A kwai ranarda Yah Salman ke faɗin wai dama na taimaki kaina nazo ya kaini asibiti anmin allurar da zan koma fara ko nayi ƙyan gani, danshi wlhy har kunya yakeji suzo suyi baƙi aga ɓaƙar fuskata a cikinsu, ni da kwalta ta titi bamu da maraba.      Dariya Aamila da Mummy sukaita tuntsurawa akan wannan zance, harma Mummy ke faɗin, “karka damu, sonake mu fita shopping ai na haɗo mata mayukan da zata kore wannan mugun baƙin, ni kaina baƙin nan nata har tayarmin da tsigar jikina yakeyi, anya Bilkisu nama taɓa ganin mai baƙinki kuwa?”.          Murmushi kawai nayi ina haɗiye kukan da yake shirin taho mani.     Yah Qaseem yaja tsaki shima daga inda yake zaune yana cewa, “Ku baƙin kawai kuke gani, ni wlhy nafi tsanar naniƙaƙƙen hancin yarinyarnan, sai kace tana gudu aka saka mata, wannan ko farin tayi an faɗa muku fasali zatayi? Indama ALLAH ya sota ya bata jiki mai ƙyau, gashi dan jaraba kullum tana fama da wannan hijjabin sai kace akanta aka fara addini, idanma zaki sauƙaƙama kanki ki sauƙaƙa yarinya, larabawanma tushen musuluncin sha'aninsu sukesha balle ke jinin wahala”.            Nan ɗinma dariyar sukayi, hakan ya sakani kasa jurewa sai da yawayen da nake riƙewa dai suka zubo, hijjab na saka na share kawai.       “Tofa, wai kuka kikeyi dan an faɗa miki gaskiya? Tab kinada aiki wlhy” Yah Salman ne mai maganar yana miƙewa zai fice.         Haka suka cigaba da cimin fuska kowa na faɗin albarkacin bakinsa, dawowar Dad ce ta ceceni na samu sukuni, shikuma ganin yanayina ya sakashi tsareni da tambayar lafiya?.      Nace masa babu komai daga barci na tashi ★★★★            Ina sati na huɗu a gidan da safe kowa ya fice, daga ni sai Aunty Aamila da mummy ne a gidan, kuma duk suna ɗakunansu suna barci, niko bana iya dogon barcin nan hakan ya sakani fitowa falo na zauna ina kallo a tv, ɗauke wutar da sukaine ya saka ni miƙewa, ga shirin gidan kuma yasaka  naji duk kaɗaici ya taso mani, tashi nai na koma ɗaki na kwanta duk da nasan ba barcin zanyiba. ★★★★         Da ƙyar Shahudah ta iya isa gidansu saboda rashin jin ƙarfin jikinta, tai hon mai gadi ya buɗe mata, yana ma gaisheta amma bata sauraresa ba ta shige, koda tai fakin ma kanta ta kwantar a sitiyari tai shiru na wani lokaci, kusan mintunanta biyar sannan ta samu ta fito zuwa cikin gidan.        Yanda gidan yake shiru tasan su mummy basu tashi barciba, gashi tana buƙatar hutawa, tsohon ɗakinta ta wuce danta samu ta hutama ranta, dama inhar tazo gidan takan zauna acannane.      Takun takalman da najine ya sakani kallon ƙofa, har aka buɗe aka shigo.        Idanuna suka saukakan ƙyaƙyƙyawar matashiyar mace cikin ado na ainahin zubin wayewa ta shigo ɗakin babu ko sallama.        Tozali dani ya sakata zare baƙin glasess ɗin idonta da ya rufe kusan rabin fuskarta tana min kallon sama da ƙasa, nason sanin ke kuma wacece haka?.        Nikuma cire glasess ɗin natane ya bani damar ganeta duk da a hoto na taɓa ganinta, ɗiyarsu Dad da aka bani ɗakintace mai suna Shahudah kamar yanda ya sanarmin ce, yauce ranar farko dana ganta a zahiri, dan kuwa tunda nazo gidan bata zoba, dama Dad ya sanarmin batajin daɗin jikintane tana fama da ƙaramin ciki shiyyasa, amma ita bata iya sati ɗayama batazo gidanba.      Takun takalminta ya sakani dawowa hayyacina, ƙoƙarin fita take tana sake bina da kallo, sai yamushe fuska take tamkar taga wani kashi ko abin ƙyanƙyami.        Da ƙyar na iya fusgo magana a harshena nace, “Sannu da zuwa aunty”.         Banyi tunanin ta amsa mani ba, ta dai fice da ɗan gudu kamar cikin fushi ko tunanin takalmin ƙafarta zai iya kadata bataiba kuwa...... ______________________ JAWAAD ______________________              Ɓangaren Jawaad kuwa yau gidan Alhaji Kokino ya sake kai ziyara, inda ya samu damar ganawa da dattijuwar nan da wancan zuwan ta kawo musu kayan breakfast.         Wannan karon ma itace ta kawo masa ruwan sha, dan shi kaɗai ya zo sai gimba.       Koda ta ajiye ruwan bayan gaisuwa sai tai yunƙurin juyawa zata fice abinta.            “Da alama dai a ranar sha uku ga watan bakwai, dai-dai da washe garin rasa Alhaji wani abu ya faru wanda ganinsa ko jinsa ya jawo Accident ɗin faɗuwa a gareki har kika samu ciwon da har yanzu kike jinsa a jikinki, kuma tabbas wannan abun da kikaji ko kika gani yana da nasaba da Alhajin”.         Cak ta tsaya, ita bata fitaba bakuma ta dawo da baya ba, ba komai ne ya jawo hakanba sai kalaman Jawaad masu saka rikici ga duk mai alaƙa dasu.....      Jawaad dake ƙoƙarin zubama kansa ruwa a kofi ya sake katseta da faɗin, “Abin bana dogon tunani bane mama, abin kawai na sani zan cigaba da riƙe Yazeed har sai nasan dalilin faɗuwarki a wannan ranar, miya tsorataki?, abu na gaba ki taimaki kanki kije asibiti a duba ƙafarki, dan naga har yanzu kina ɗangyasata”.      Ya kai ƙarshen maganar yana takowa inda take a tsaye.     Hakanne ya sakata kallonsa ta kauda kanta da ƙoƙarin haɗiye hawayenta, tace,         “Miyasa zaka sakamin yaro cikin al'amarin da baisaniba?”.         “Mama idan har kina buƙatar na sanar masa komai a yanzu ai bamu makara ba”.      Idanunta jajur ta ɗago ta kallesa, shima kallon nata yake, amma sai ya janye nasa idanun ganin tana neman rikicewa, yay murmushi yana sake matse kofin hannunsa na glass, rashin ƙwarinsa ne ya saka kofin tarwatsewa  sauran ruwan ciki ya jiƙe masa hannu ya zuba a ƙasa, guntayen kofin kuma sukai ɗai-ɗai a ƙasan suma.       Dattijuwa ta sauke idonta akan hannun Jawaad har zuwa kofin da yaya kuci-kuci a saman tayis tamkar ba shiba, sake maida kallonta tayi gareshi a wani yanayi mai nuni da tsantsar damuwarta.         Jawaad ya zaro handkherchief a aljihunsa ya goge hannunsa tas sannan ya turasu a aljihu duka biyun yana ja da baya fuskarsa na ƙara tsukewa.         “A duk lokacin da aka zuba ruwa a glasscup yana da matuƙar ƙayatarwa, har kakanji bakason ɗauke idonka wajen kallonsa koda zaka kwana a haka, amma da tsautsayi zaisa wannan kofin fashewa a hannunka zaka iya gamo da haɗarin yanka maisa aji zafi, shi kuma ruwan dake ciki idan har ya zuba a jikinka ƙoƙarinka kawai ka goge, damshin da ya rage iskace kawai ka iya busar maka dashi, wanda yake a ƙasa kuwa sai kaga dukansa ya zama haɗarine, musamman akan abu mai santsi irin tayis. Na tabbata duk wanda zai shigo falon nan a yanzu zaiyi ƙokarin ganin bai taka wannan ruwan da glasess ɗin nanba, yaron da hankali bai gama bin jikinsa bane kawai zai maidashi abun wasa. Mama bansan yaya zaki rarraba zantukana a jujuwan da suka cancantaba, ni dai kawai abinda raina ya bani komai tsanani zansan gaskiyar zancen....”        Ya raɓata ta gefe zai fice, yana saka ƙafarsa ɗaya a waje yajiyo sautin dariyarta.       Dakatawa yay tare da juyowa yana kallonta.        Tace, “Yarona idan kwalba ta fashe a hannun mutum zafinta kawai zaiji saiko fitar jini da zai gani, amma idan zuciya ta samu suka har abadan wannan tabon baya gogewa komi adadin shekarun da aka ɗauka bayan jin wannan ciwon, ruwan da zai zuba a jiki a goge iska ta busar bashi da banbanci da hawayen dake kwarara daga idaniya zuwa fuska a goge iska ta busar da sauran, inda ake samun banbancin kawai shi wannan ruwane, daya zube labarinsa ya shuɗe, suko waɗannan hawayene koda sun bushe ba'a daina iya ƙididdige su a tsarin da sukazo na farin ciki ko akasinsa har ranarda fitar numfashi zata yanke, ka cancanci a kiraka da suna *Ƙwai cikin ƙaya* sannan kuma lallai kai *Yarone ɓata hankalin dare kayi suna*, duk abinda kake buƙata daga gareni zaka samu, amma ba'a nan gidanba, mu haɗu a gidan daka ɗauki yarona Yazeed.............✍🏻 Page 20 ............Tunda suka baro gidan Alhaji kokino maganganun tsohuwar ne kawai ke yawo a zuciyar Jawaad, gaba ɗaya ya kasa fahimtar alaƙar ɓatan Alhaji kokino da kalamanta, ya rarrabasu ajujuwa daban-daban amma basa bashi ainahin abinda ya dace, yay guntun tsoki yana cigaba da shafa gemunsa a hankali, yayinda idanunsa ke kallon hada-hadar jama'ar gari. Daga nan office ya koma, inda ya tarar da baƙuwa zaune tana jiransa. Rose da tunda Jawaad ya fito a mota ta dasa masa idanu ko ƙyaftawa batayi ta sauke nannauyan numfashi lokacin daji ƙarfin ƙamshin turarensa gab da ita. Ta bishi da kallo tana sake yabama kwarjininsa da cikar zati da ALLAH yay masa, tasan sarai ya ganta, amma jiba yanda ya basar abinsa. Murmushi tayi ta miƙe tana gyara zaman wuyan rigarta. Itama ƙyaƙyƙyawar ce ba laifi, gata doguwa masha ALLAH, yanda take tafiya cikin zafin nama tana juya dukkan illahirin jikinta zai tabbatar maka da tasamu isashen training wanda ya haɗu da ainahin halittar yanga ta ɗiya mace. Kanta tsaye ta nufi Office ɗin Jawaad, wanda kowa yasan bata da shamaki da hakan. Yana zaune a kujerarsa yayinda wani ke tsaye a kansa yana masa bayani akan aikin daya sakashi, har Rose ta zauna bai kalleta ba, dan idonsa nakan wasu takardu ne, itama batace komaiba ta dai zauna tana saurarensu. Sai da wancan yakai aya sannan Jawaad ya ɗago yana kallonsa da rikitattun idanunsa da mafi yawan lokuta ke tsorata duk wani maison kawo masa wargi. "Aikinka yayi ƙyau, sannan yana tafiya dai-dai, yanzu dai kafin dare a tababbar an kamo min Ɗan Lawan da yaransa baki ɗayansu, sannan itama kanta Kande barikin a kamomin ita tare da wiwi ɗin dasu ɗan lawan ɗin ke kai mata ajiya". "Okey sir" ya amsa yana mai sara masa, takardu biyu Jawaad ya miƙa masa, ya amsa yana ƙara sara masa sannan ya fice. Lokacinne Rose ta miƙe tai salute ɗin Jawaad dake haɗe takardun daya baza bisa tebir ɗin waje ɗaya, fuskarsa ta sake tsukewa alamar babu wasa, a dake yace, "Ban saniba yanzu ko zaki maida hankalinki ga aikinki, kokuma zaki cigaba da ɓata lokacinki akan farautar soyayya?". Ido Rose ta lumshe tana sakin murmushi mai sauti, ta kuma ƙamewa tare da sarama Jawaad a karo na biyu, "Boss duk zaɓin daka bani zan riƙe". Ɗago ido Jawaad yay ya kalleta, mikuma ya tuna sai ya saki wani guntun murmushi yana girgiza kansa. Ya jawo drawer ɗin gefensa ya fiddo bindiga ƴar ƙarama mai ƙyau, saman tebir ɗin ya ajiyeta idonsa akan Rose da itama kallonsa take ko ƙyaftawa babu, yaɗan bugi bindigar kaɗan sannan ya turata gabanta cike da salo. Itama cikin nata salon ta ɗauka ta wurwurata tare da buɗeta. Babu komai a cikinta, hakan ya sakata sake kallon Jawaad daya maida hankalinsa ga latsa Computer ɗin saman tabir ɗin. Ba tare daya kalleta ba yace, "Riƙe soyayya a wajenki tamkar riƙe bindiga ne babu bullet a cikinta, kinsan kuwa a garemu jami'an tsaro sam bindigar bata da amfani, domin ba bindigar bace ƙarfinmu harsashin cikinta ne, shima kuma yana amfanine idan an samu ƙwarewar iya harbi. Karki yarda a karo na biyu kiyi sakaci da damarki, Jawaad akwai mai shi". "Hummm" ta faɗa cikin ƙunar zuciya ba tare data iya cewa komaiba. Shima bai sake cemata komanba tsawon lokaci kafin ya miƙe zuwa ga wata kanta, yabi tarin files ɗin cikinta da kallo, da alama dai kwanan wata yake dubawa, har idonsa yakai inda yake buƙatar zuwa sannan ya zaro wata takarda, mazauninsa ya dawo fuska a tamke ya miƙa mata, "Ki samu su Jabeer da wannan file ɗin zakuyi magana". "Okey Boss" ta faɗa cikin rissinawar girmamawa gareshi tana amsar file ɗin. Sai da ta sake salute nashi sannan tai ƙoƙarin ficewa. "Ji mana" Jawaad ya faɗa yana bin Rose da kallo. Juyowa tai ta kallesa, da ido yay mata nuni da harsasai (bullets) kusan goma daya ɗora a tebir ɗin. Dawowa tai da baya ta kwashe tana faɗin, "Thanks you boss". Baice da ita komaiba, saima maida hankalinsa yay ga kallon Computer harta fice. Aikinsa ya cigaba dayi, duk da zuciyarsa na tunanin halin da yabar Shahudah jiya da dare, tana bashi tausayi saboda wahalar da cikin yake bata, amma bayason nuna mata hakan koda a fuska ne. Ƙarfe huɗu da wasu mintuna ya fito massalaci ya zarce office ɗin boss ɗinsa domin amsa kiransa. Bayan nuna girmamawarsa garesa ya zauna kamar yanda ya bashi izini. "Jay yaya dai? Na jika shiru, ko akwai matsala ne?". "A'a Sir, babu wata matsala aiki yana tafiya dai-dai, a yanzu haka zancen da nake maka insha ALLAHU ƙiris yama rage". "To Alhmdllh, banason aikinnan ya shige satinnan, dan yanzu hakama wata ta taso kuma". Kallonsa Jawaad yayi da son jin ko minene?. Ya cigaba da faɗin, "Akwai wani mai kayan miya anguwar ƴan kilishi daga can ƙasan layin, majiya mai ƙarfi ta kawo mana alamar tambaya a kansa, saboda gagarumin fashin da akayi satin baya gidan Alhaji Sulaiman, Qaseem aka ɗora akan case ɗin, sai dai naga baiyi wani serious ba sam, yamafi maida hankalinsa akan wannan case ɗin da ayanzu nasan kai kama kusa kammalashi". "Okey Sir, yanzu mikakeson nayi ni akai?". "Case ɗin nakeso ya dawo hannunka Jawaad, dan waɗannan ƴan fashin bincikenmu ya nuna sunada laifuka masu yawa, amma basu barin kowacce damar da za'a gane sune, sai yanzune muka ɗan samo bakin zaren". "Na gane sir, to amma an buɗema case ɗin file ne?". "No, nabar komai a hannunka, dan banida shakku akanka sam". Kai Jawaad ya jinjina masa, "To amma sir kozan iya sanin wanda ya kawo sirrin?". "Mizai hana Jay". Murmushi Jawaad yayi, dan har zuciyarsa yana ƙaunar ogan nasa, ALLAH ne ya ɗaga darajarsa a hukumarsu, da kuma ƙoƙarin ogan nasa, dan ƙarancin shekarunsa basukai ace yana a kujerar da yakeba a yanzu, amma saboda manyan ayyukan da sir Ahmad Barewa ke bashi yaketa samun cigaba, har takai yanzu yana cikin jami'an da hukumar ƴan sanda ta DSS ke ji dashi saboda ƙwazonsa, da salon aikinsa, duk da kuwa ta wani ɓangaren yana zagayene da maƙiya masu burin taɗosa ƙasa a kullum. Ya daɗe a Office ɗin suna tattaunawa kafin ya fito. _________________________ "Ke kuwa yaushene zakiyi hankali mamana?". Hajiya Humaira ta faɗa saboda faɗowa kanta da Shahudah tayi tana barcinta. Baki Shahudah ta zumɓura tana faɗin, "Ni Mummy inada hankalina, wai wacece a ɗakina kuma?". Baki Hajiya Humaira ta taɓe tana sakkowa daga saman gadon tare da jan tsaki, "Ƴar uwarkuce". "Ƴar uwarmu fa mommy? Waccan baƙar yarinyar?". "Ita ɗinfa, ɗiyar ƙanwar dad ɗinkj Gurguwarnan da kika taɓa ƙonawa da shayi wani zuwa data taɓayi kuna primary lokacin, koda yake dawuya dai ki tuna ma". "Tab wlhy mummy ban mantaba, shine Dad ya jajubo mana ƴarta? Itama gurguwarce halan?". "Ko ɗaya, lafiyarta ras itakam, mamar tata ta rasune ai, shine ya kawota nan wai tayi karatu". Dariya sosai Shahudah take kwasa harda kwanciya, cikin dariya take faɗar tab ɗi, "Wannan mummunar ce za'aima gatan karatu? Irin waɗannan ko a makarantar ma mi suke ganewa yo? Amma kuma shine ama rasa inda zata zauna sai ɗakina" ta ƙare maganar da kumbura baki. "Uhm, ke bakisan tsiyar da mukasha akan hakanba da shi, yanzu dai karkice komai ki bar mata ɗakin, ke sai a gyara miki na kusa dani, dan idan kikace wani abu akanta komai zai iya faruwa, ya ɗauki son duniya ya aza a kanta waishinan mai riƙon amana". Sosai lamarinnan ya zafi zuciyar Shahudah, harda ma dad ɗinsu wani maganar rashin tarbiyya, na zata Hajiya Humaira zata kwaɓeta sai naga kawai tayi dariya. Tunda ta fita sai nima na kasa daurewa na fito falo na zauna, kusan awa ɗaya ina wajen zaune duk damuwa ya rufeni, dan bansan dalilinta na fita da gudu ba. Aunty Aamila ta fito daga ɗakinta cikin figigiyar rigarta ta barci, wadda kaɗan ta zarta cinyarta. Kallo ɗaya taimin taja tsaki ta wuce tebirin cin abinci. Lamarinta baya damuna nikam, hakan yasa ko sashen da take bamma kallaba. Ina zaune a wajan Mummy da baƙuwarmu suka fito, na gaida Mummyn cikin girmmawa kamar yanda na saba. Amsawa tayi itama cikin nuna halin ko in kula, aunty Shahudah kam bamma isheta kalloba, hakan ya tabbatar min itama dai bazan samu karɓuwaba a gareta kenan, ban damuba, dan ba yaune karon farko dana fuskanci hakanba. Zuwan Aunty Shahudah gidan yaɗan sake takurani, saboda wulaƙancin da takemin yafi na kowa muni, ko abu na taɓa ita bazatayi amfani da shiba, a cewarta karna gogama ɗan cikinta Munina, nakanyi murmushi aduk lokacin da naji furucinta. Takai inhar tana falo zaune takance bazan zaunaba wlhy, banaja da ita saina tashi na fita kona koma ɗaki, kaida kazo cin arziƙi miye naka na zaƙewa?. Kwannanta uku a gidan, duk da kuwa tun a daren da tazo naji suna tafka bala'i da mijinta a waya akan kwannan nata, dan naga tanata magana a zafafe akan dan tazo gidansu zata kwana dole saita sanar masa. Da alama ma yanke mata waya yayi kafin takai zancen ƙarshe, dan kuwa sai faman faɗin, "Hello hello takeyi, daga ƙarshe cikin takaici tai jifa da wayar saman kujera tana masifa iya iyawarta akan ya kashe mata waya. Itako Aunty Aamila sai zugata take akan wulaƙancin da yake mata yayi yawa, ni dai banji ƙarshen zancenba na shige ɗaki, dama daga kicin nake na zubo abinci, suko suna a tebir zasuci nasu. ________________________ Ran Jawaad ya ɓaci da ya dawo ya iske Shahudah bata gida, hakanne ya sakashi kiranta amma saita sanar masa tana gidansu, ya tambayeta da izininwa? tahau kansa da masifa, shine kawai ya yanke wayar ba tare daya gama saurarenta ba. Sam bayason jin zafinta da yake ya cigaba da girmama cikin ransa, dan haka ya tashi yay shirin fita dukda kuwa lokacin ƙarfe tara da rabi na dare, kuma dawowarsa gidan kenan ko hutawa baiyiba. Da kansa yaja motar dan yabama gimba damar zuwa ya kwanta ya huta. Kansa tsaye gidan dattijuwarnan ya nufa, yanabin address ɗin da su Hafez suka bashi dalla-dalla. A ƙofar madaidaicin gida ya tsaida motar dajin tabbacin nanne, dankuwa duk abinda aka kwatanta masa a jikin gidan ya gansa, kashe motar yay sannan ya fito cikin nuna alamun tsantsar gajiyar dake tattare dashi. Ya kulle motar amma sai bai fitoba ya fara ƙoƙarin yin kira cikin ƙaramar wayarsa. Bugu uku aka ɗaga, "Gani a ƙofar gida" ya faɗa idonsa akan murfin gidan. Bansan amsar da aka bashiba daga can naga dai ya kashe wayar yana fitowa a motar, bindigarsa ya ɗauka ya tura a aljiyu sannan ya rufe murfin motar yana mai kulleta gaba ɗaya. Dai-dai nan dattijuwa mai aiki gidan Alhaji kokino ta fito sanye da lulluɓi. Da hannu tai masa nuni alamar su shiga, babu musu ya bita, bayan yaɗan wawwaiga bayansa yaga babu alamar kowa a wajen, dukda ma anguwar babu wani isashen haske saboda rashin wutar lantarki. Gidan bawani babba bane ammafa yasha gyara, dan fes yake sannan kuma da gani babu ƙananun yaran da zasu ɓata. Zama yay a farar kujerar roba dake ajiye a bangon yamma da yake ƙyautata zaton kicinne, itama ta zauna a ƙofar kicin ɗin bayan ta kawo masa tea tamkar tasan yana buƙatarsa a halin yanzu. Godiya yay mata kuwa ya ɗauka yana sha. "Bani da tabbas amma inaji a jikina kasan inda Alhaji yake". Jawaad dake ƙoƙarin kai kofin shayi bakinsa ya dakata yana kallonta, leɓensa na ƙasa ya tura cikin bakinsa yana tsotsa tare da kafeta da wani kallon nazari na seconds biyar, sai kuma yay murmushi yana ƙara damƙe kofin shayin da hannu biyu yakai bakinsa ya kurɓa. Itama kallonsa takeyi har yanzu, sai dai bata sake cewa komaiba. Jawaad ya cigaba da shan shayinsa kawai idonsa na kallon yanda iska ke kaɗa labulen ɗakin matar. Yasha kusan rabin kofin shayin sannan ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, idonsa akanta. "Mama shekararki nawa kina mata aiki?". Murmushi dattijuwa tayi tana kallonsa, "Yarona ai mai son kama fara sammako yakeyi" "Hakane" Jawaad ya faɗa yana shafa kansa cikin murmushi. "Miyasa take ɓoyemin kanta har yanzu?". "Bani da wannan amsar a zahiri da baɗini". Kansa ya rausayar kawai, idanunsa na sake rikiɗewa zuwa ja sosai, sai haɗiyar numfashi yake da zafi, hakan yasaka zuciyarsa gudu tare da tsitstsinkewa....... Mama ta katse masa tunani da faɗin, "Ta bani saƙo na baka". Ɗago kansa yay ya kalleta, amma baice komaiba. "Tace ka sadaukar, a cikin hakan akwai alamar tambaya? Idan kabi diddigi zaka fahimta". "Zanyi biyayya, sai dai zan cutu kuma". "Shiyyasa nazo maka da maganin hakan". Miƙewa Jawaad yay yana kallon agogon hannunsa, "Ina saurarenki, dan lokacina ƙararrene". "Karka damu nima komai inayinsa da ƙa'ida. iya ruwa fidda kai, amaryar alhajice mafitarka". Jawaad ya juyo yana kallon dattijuwa hannuwansa duka a cikin wandon jeans ɗinsa, "Mimene nata burin?". "Kisa da mallakar abinda ya tara". Kansa ya jinjina yana murmushi, ahankali ya furta "Abin birgewa". Kallonsa mama tayi tana murmushi itama. Takowa yay ya dawo gabanta yana ɗan jingina da bango, yace, "Shine kikaji a ranar da kika faɗi kenan?". Cikin sauke numfashi mama tace, "Kusan haka yarona, sai dai tsoron ya gauraya ne da cin amanar aure, kuma da makusancinsa". Hannu ɗaya Jawaad ya ciro a aljihu yana mai shafa fuskarsa, "Idan babu kuskure a hasashena auren manufa tayi da haɗinkan ƙaninsa kenan?". "Hasashenka yana kan dai-dai, kamar yanda sukuma ka ruguza musu nasu a ranar da Alhaji zai dawo daga tafiya shi da ita". "Zan samu dukkannin bayanan?". "Ƙwarai kuwa, harma da wanda baka tambaya ba" tai maganar tana kunce ƙullin haɓar zaninta ta ciro wani ɗan abu ta miƙa masa. Amsa yay yana sauke numfashi, "Nagode ƙwarai da gaske mama. A sanar mata ina buƙata matuƙa, sannan ke kuma yaushe aikinki zai ƙare a gidan?". "Eh to, inada zaɓi biyu ne, sannan dama ɗaya kacal, a koda yaushe za'a iya nemana a rasa". "Shikenan, ni zan wuce, a daren yau zan ƙulle bakin zaren". "Kariyar ALLAH ta tabbata a gareka tareda rahamarsa akowane lokaci". "Amin ya rabbi mama, nagode sosai, da safe Yazeed zai dawo gida". Murmushi kawai tai masa, shikuma ya fara taku cike da kasala ya fice daga gidan. Buɗe motarsa yay ya shiga sannan ya rufe kansa, ya buɗe hannunsa dake rumtse da abinda mama ta bashi, idanu ya tsira masa yana kallo, kusan mintuna uku sannan ya ajiye yana tada motar ya fice daga anguwar. Tuƙi yake amma hankalinsa kashi sittin baya a wajen, gefen titi ya samu jikin wani ƙyamiz yay fakin motar, ya cire babbar wayarsa a caji ya danna kiran Jabeer, bugu ɗaya ya ɗauka, sai dai yanda yaji muryarsa ya bashi tabbacin ya fara barci ne. "Barci kake?". Jawaad ya faɗa a ƙasan maƙoshi. Daga can Jabeer yace, "Wlhy kuwa barcine ya figeni a falo ma, yaya kana office ne?". "Eh to badai a cikiba, amma ina akan aikine, inasu Aliyu?". "Duk gasu muna a tare". "Yauwa ku kasance cikin shiri yanzu nima zan iso". Bai jira amsar Jabeer ba ya yanke wayar. Rose ya kira, itama bugu ɗaya ta ɗauka, ko gaisuwarta bai sauraraba ya fara faɗin, "Yanzun nan ki kira number dana baki ranar, ki kirata da wayar dana baki ki sanar mata tazo bayan kamfanin robobi na kwanar gulbi ta sameki, wannan wayar ta ƙawartace wadda da ita suke haɗa komai, dan haka zatazo da sauri". "To amma boss kana ganin zatazo a darennan?". Tsawa ya daka mata wadda ta sakata firgita har tana neman yadda wayar, ta daiyi nasarar damƙeta da sauri tana faɗin, "Sorry Boss". Tsaki mai ƙarfi Jawaad yaja yana katse kiran, dama zuciyarsa a saman maƙoshi take sosai. Motar ya tayar yaja da uban gudu zuwa gidansa dasu Aliyu ke ciki, shigowarsa falon yasasu miƙewa su duka cikin girmamawa, hannu ya ɗaga musu kawai ya wuce ɗakin da ke cikin falon, mintuna kamar uku sai gashi ya fito da mace da shekarunta ba zasu gaza talatin da biyu ba. Dukansu sunsan da zamanta, dan haka basu wani damuba, Jawaad ya ciro waya a aljihunsa yay danne-danne yana miƙa mata, karɓa tayi tana kallonsa a yanayin tsoro-tsoro bariki-bariki.... "Ki kira number nan, ki sanar masa kina tare da Alhaji Kokino, yanzunnan tazo bayan kamfanin robobi na kwanar gulbi ta sameki, kuma yanzunnan". Bakinta ta taɓe tana kallon Jawaad ɗin, "Yallaɓai to miyasa zanyi hakan? Bayan kasani na sani Alhaji baya tare dani?". Bindiga ya ɗora mata a saman kai ba tare daya ce komaiba. Take jikinta ya fara mazari, ta shiga ƙoƙarin yin abinda yace. Yace, "Ki tabbatar muryarki ta fita normal babu gargada a cikinta". Zufar data fara jiƙa goshinta ta goge tana haɗiye yawu da ƙyar ta saka wayar a kan kunnenta. Duk yanda Jawaad ya shaida mata haka tayi, su dai su Hafiz suna tsaye suna kallonsu duk da sun kasa gane kan abokin nasu ma, tunda bai musu bayanin komaiba. Bayan ta kammala wayar Jawaad ya maida bindigarsa a aljihu yana kallon su Hafeez. "Zan barta tare daku, nanda mintuna ashirin zan iya kiranku, zakuzo bayan kamfanin kuma ku sameni". A tare suka jinjina masa kawuna, ya fice da hanzarinsa.............✍🏻 Page 21 ...........Guri Jawaad ya samu yay fakin nesa da gidan Alhaji kokino, ya ɗauki ƙaramar wayarsa yay kiran Rose, bugu biyu  ta ɗaga.        Kafin yace wani abu tai saurin faɗin, “Sir komai ya tafi dai-dai, yanzu haka ina ƙyautata zaton kowane lokaci zata iya tahowa”.        “Yayi, yanzu haka ina ƙofar gidansu, zankira su Aliyu suzo da ƙawar tata, duk yanda za'ai karki bari tazo ta sameki a wajen koda ta rigasu zuwa”.        “Okey sir” Rose ta faɗa cikin girmamawa.      Wayar ya katse, ya tada motar ya ƙarasa ƙaton gate ɗin gidan Alhaji kokino.    Horn yayi, babu ɓata lokaci baba mai gadi ya buɗe dan yasan da zuwansa, yay fakin motar ya fito, a kuma dai-dai wanna lokacinne Hajiya Usaina ta fito kamar a rikice, motarta da Jawaad ya kare ta nufa, sai da ta zira key zata buɗe ta juyo da nufin yima baba maigadi magana ya buɗe mata gate idonta ya sauka akan motar Jawaad, yanayin da take cikine ya hanata fahimtar motar bata gidan bace ba.        Ranta a ɓace ta shiga kwala kiran “Baba Dauda! Baba dauda!!”     Jikin Baba mai gadi na rawa ya rugo zuwa gareta yana amsawa da “Na'am hajiya, afuwa naɗan zagaya banɗakine wlhy”.        Batako sauraresa ba ta nuna motar Jawaad, “Uban waye yay fakin mota a gurin nan? Bayan ansan ko yaushe zan iya fita tunda inada mara lafiya a asibiti”.         “Kiyi haƙuri hajiya baƙone yanzu kuma ya shigo shima” ‘Baba yay maganar yana nunamata Jawaad dake tsaye jikin motar yana waya hankalinsa kwance tamkar baisan mi sukeyiba, nanko dukkan hankalinsa na kansu’.          Kaɗan ya rage key ɗin motar data zare daga jikin motar ya faɗi, tai saurin damƙesa dan ba ƙaramin razana tai da ganin Jawaad ɗinba, fasa buɗe motar tayi ta nufo inda Jawaad yake tana ma baba maigadi alamar ya tashi da hannu.          Jawaad ya janye wayar daga kunnensa yana maida hankalinsa gareta, cikin harɗewar harshe tace, “Yallaɓai lafiya kuwa a daren nan? Ko anga Alhaji ne?”.         Fuskarsa ya kauda daga gareta tamkar baiji mi taceba, ya tura wayar tasa a aljihu yana komawa jikin motarsa ya jingina, cike da nutsuwa ya maida hankalinsa gareta, “Nazone inason magana da ɗaya a cikinku, ke ko Hajiya babba”.         “To Yallaɓai nidai amin afuwa jikin mamana ne ya motsa, shine aka kirani asibiti”.        “Okey babu damuwa, bara na bari sai da safe na dawo, ALLAH ya bata lafiya”.         “Amin ngd” tai maganar tana barin wajen cike da sauri, dukta rikice, da alama kuma ganin Jawaad ne ya kawo hakan. Cikin gida ta koma ba tare da tasan mizatayo ba kuma.        Murmushi Jay yayi yana ɗauke ido daga kanta, ya maida dubansa ga baba maigadi yana faɗin, “Buɗemin gate, ina fatan komai done?”.       “Komai dai-dai ƴallaɓai, ALLAH ya ƙara nasara”.       Murmushi Jawaad yay masa, ya buɗe motar ya shige ya bar gidan saboda baba ya buɗe masa gate ɗin.       Yana ƙoƙarin harba motar kan titi yana kiran waya, ya ajiyeta a saman cinyarsa bayan ya saka a hansfree.         “Hello Hafiz!, kuyi maza mu haɗu acan ɗin, idan kun rigani zuwa saiku jirani, inaso saina fara ajiyeshi kafin ku sauketa kuma, saboda tsarin yayi dai-dai”.         “Okey Boss” Hafez ya amsa daga can yana gimtse wayar, zuwa yanzu kam ya fahimci mi Jawaad ke shirinyi, dan haka ya kalli su Jabeer da suma sunji komai saboda a hansfree ya saka.        Dariya sukayi gaba ɗaya, dan sun fahimci inda aikin ya dosa yanzu kam.           “Daga jikin kamfanin ta baya yay fakin motar, ya fito a ɗan hanzarce bayan ya saka baƙar safar hannu a hannunsa, bayan motar ya buɗe bayan ya wawwaiga babu alamar mutun ta ko ina, yakai hannu ya jawo mutum a seat ɗin baya da ƙyar, dan babu laifi yanada jiki,  kuma da alama a sume yake ma. Da ƙyar ya iya saukeshi ƙasa, sai hakki yake, ya sake ɗagashi da ƙyar zuwa wani ƙaramar baca ta kwano dake wajen ya ajiye saman kujera, igiya ya saka ya ɗaɗɗauresa kafin ya zaro  allura a aljihun wandonsa yay masa a hannu, bai jira komaiba ya zare abinda suka rufe masa fuska ya fice da hanzari yayo waje.      Mota ya koma, da babaya yajata yaɗan koma nesa da wajen sannan ya kashe ya sake fitowa, wayar dake hannunsa ya ɗora a kunne yana fadin, “Zaku iya kaita”.       Bai jira misu Aliyu zasu ceba ya yanke wayar ya koma kiran Rose wadda tana daga can ɗan nesa da kamfanin itama, tana ɗagawa yace, “Kin ajiye wayar da kika kiratane a bacar?”.      “Yes boss, tun ɗazun ma”.        “Okey kizam cikin shiri, dan bayan awa ɗaya kacal zamu far musu kafin suyi tunanin kashesa”.       “Angama boss”.     Katse kiran yay yana lumshe jajayen idanunsa tare da dafe kai, babu abinda yake buƙata sai hutu, dan a matuƙar jigace yake.        A haka Su Jabeer suka ƙaraso inda yake, dan Aliyu ne kawai yakai matar cikin bacar da Jawaad ya ajiye Alhaji kokino.       Fitar Aliyu da kamar mintuna biyu Alhaji Kokino ya farfaɗo saboda Allurar da Jawaad yay masa, mutsu-mutsu ya fara yana ƙoƙarin buɗe idanu da ƙyar, hakan ya saka matar da Aliyu ya kawo miƙewa jiki na rawa ta nufesa, dan itama tunda Aliyun ya jefota kanta a juye yake bata fahimtar komai, ta rasa dalilinsu na aikata hakan.     Da yake kuma akwai duhu sai bata san ita da waye bane a wajen, da lalube ta isa inda yake, tana ɗora hannunsa jikinsa wayarta da Rose ta ajiye a bacar ta hau ring.      Cikin tsananin firgita ta juya ta kalli wajen, inda shima Alhaji Kokino ya sauke wani nannauyan numfashi, wayar ta nufa dan ɗan hasken screen ɗin ya haska bacar kaɗan, mamaki ya kamata ganin wayartacema ashe, kuma Hajiya Usaina ce ma ke kira, kasa ɗagawa tai harta tsinke.       Aka sake kira, cikin rashin sanin abinyi ta ɗaga, daga can Hajiya Usaina amaryar Alhaji kokino tace, “Lamcy gani a wajen kamfanin, ke kina ta inane?”.       Sosai Lamcy ta zaro idanu waje, amma sai cikin rawar baki ta amsa da cewa, “Ki duba akwai baca ta kwanon langa-langa daga gefen gabas, sai dai karkizo da mota Usaina, wannan lamarin akwai lauje cikin naɗi ba shirinmu bane”.        Katse kiran Hajiya Usaina tayi, dan tafi buƙatar su karasa ga Lamcy komaima sayi acan, fita sukai daga motar itada Abdul ƙanin Alhaji kokinon, dan tare sukazo, kuma yaji komai da Lamcy ta faɗa.        A baca kuwa ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya kama Alhaji kokino saboda ganin Lamcy aminiyar matarsa Uswina, ga kuma furucin datai a waya, wanda ya tabbatar masa cewar da Usainar tai waya, “To minene shirin nasu?” yay tambayar a zuciyarsa.      Kafin ya samo amsa ne Abdul da Usaina suka shigo cikin bacar.         Gaba ɗaya sai tunanin Alhaji kokino ya sake birkicewa, ya kafe ɗan uwan nasa da kallo yana faɗin, “Abdul!” sai dai muryar tasa bata fita sosai.         Dariya Abdul ya kwashe da ita yana maida hankalinsa kan Lamcy dake ƙokarin musu bayanin wannan fa sam ba shirinsu bane, karsu ce zasuyi wani yunƙuri a zagaye suke.        Saurin dakatar da ita Abdul yayi da faɗin, “K dalla malama a zagayenwa? Kefa kika kiramu kika kuma sanar mana komai, ni yanzu babuma maganar ɓata lokaci anan, mu aikashi kawai, dan yanzu ƙarfe biyu saura, ya kamata ace nanda uku mun kammala komai munbar wajennan” ya ƙare maganar yana buɗe jakkar da sukazo da ita.     Duk yanda Lamcy taso su fahimceta hakan ya gagara, sai ma ƙoƙarin saka Alhaji kokino suke akan dole yana saka musu hannu a takardun dake cikin jakkar, waɗanda duk na kamfanoninsa ne da kaddarorinsa dake ƙasashe daban-daban harda na nan ƙasar.          Haushi ya kume zuciyar Lamcy, dan ta kula gaba ɗaya kawunan su hajiya Usaina a toshe suke, da ƙarfi ta hankaɗe Abdul daya kama hannun  yayan nasa yana sakashi  saka hannun dolen.     Kallonta yay da mamaki mai haɗe da ɓacin rai, “Wai ke mike damunki ne? Kokinsha wani abu dayafi ƙarfin kankine?.......”       “Ba nice banda hankaliba Abdul, kune baku da hankali, to idanma barci kuke ku farka wannan shirin duk wasune da nima ban saniba suka tsarashi!!!”.         Yanda tai maganar da cikakkaiyar gaskiyane ya sakasu kallonta su duka, amma sai hajiya Usaina tai tsaki kuma, “Lamcy karki kawo mana wani ruɗani anan, indai akan maganar abinda kikace za'a bakinne munji zamu baki, ke ni harma wani kaso zan ƙara miki a cikin nawa, ai burinmu ya gama cika, dan yau dai ta Alhaji ta ƙare, kudin da muketa wahalar gadi tsahon shekara shidda gasu komai ya dawo hannunmu, nanda sati ɗaya sunayenmu zasu fito cikin manya-manyan masu arziƙin duniya, hhhhhhhhh!!, sai ni Usaina ɗiyar malam garba, mace ta farko mai arziƙin da babu kwatankwacinsa a wannan yanki, Abdul ka kawoma duniyata haske dalilin buɗamin hanyar auren ɗan uwanka, wanda toshewar basira ke sakashi kallon sonsa nake, besan ina cikin waɗanda zasu zamo ƙatshen rayuwarsa bane, hhhhhhhhhh!!!!!!”.      Ta sake kwashe da wata mahaukaciyar dariya Abdul na tayata, hannu yasa ya fisgota ta faɗo jikinsa, a gaban idon Alhaji kokino dake ɗaure suka hau sumbatar juna tare da yamutsa kansu.       Hawaye masu zafi ne suka wanke fuskar Alhaji kokino, ya duƙar da kansa domin daina kallonsu, wuƙa Abdul ya zaro a aljihunsa, babu wanda ya lura ya sokama Lamcy dake ƙokarin jan hannun Hajiya Usaina, so take ta sake fahimtar dasu ko zasu fahimta, idan sunƙi ta gudu itadai ko ranta ta tsira dashi idanma babu dukiyar.     Ƙara ta saki mai ƙarfi tana ƙanƙame Hajiya Usaina.        Da sauri Hajiya Usaina ta saki Abdul da maida kallonta ga Lamcy.      Sosai ta zaro ido ganin wuƙar dake gefen cikin Lamcy ga Abdul riƙe da ita ya ciza bakinsa yana ƙara dannama Lamcy.......      “Abdul mikakeyi haka kuma? Kasheta fa kayi?”.....        Dariya ya kwashe da ita yana jan wuƙar ya fitar daga jikin Lamcy, “Bata da wani amfani a yanzu a gareni, ta gamamin aiki mizaisa na barta? Dolene ta wuce kafin ɗan uwana da ke ku bi bayanta, ni kaɗaine na cancanta da wannan dukiyar hhhhhhhhh!!!!!!!......”        Tsagwaron tsorone ya bayyana a zuciyar Hajiya Usaina, ta zabura baya da sauri tana ƙwalalo idanun mamakin Abdul, kanta yay gadan-gadan, ya ɗaga hannu zai daɓa mata wuƙar aka riƙe masa hannu ta baya.       Juyowa yay yana huci dan duk zatonsa Lamcy ce bata mutuba ta riƙesa, amma a mamakinsa sai yaci karo da fuskar jami'in dake bincike akan ɓatar yayansa, Jawaad Abdul-aziz yusuf.      A wani irin razane ya zaro idanu yana sakin wuƙar, zaiyi magana Jabeer ya ɗora yatsansa kan bakinsa yana faɗin, “Shiiiiii!!”.       Sai kuma ya daki ƙafar Abdul ya zube ƙasa jiki na rawa.        Aliyu yay ƙoƙarin kwance Alhaji Kokino da Jawaad ya ɗaure, Hafiz kuwa nakan su Abdul da binduga, sai Rose dake ƙoƙarin bincikar Lamcy wadda da alama da wuyama takai labari.       A take suka tattaresu, ana ƙoƙarin fita dasu, tuni jiniyar motor ƴan sanda da Ambulance dasu Jawaad suka buƙata tunkan su shigo bacar har sun iso.       Alhaji Kokino da Lamcy asibiti aka wuce dasu, yayinda Abdul da hajiya karima aka nufi ofishin su Jawaad dasu. __________________________________          Da daddare duk muna zaune a falo ana hira, duk da ni a takure nake daga can gefe, ina dai saurarensune kawai, na murmushi nayi na mamaki da takaici na girgiza kaina, dukda suna tsangwamata idan na zauna cikinsu hakan bai hanani son zamanba, dan koba komai ina ƙara ilimin sanin duniya daga garesu, sannan ina rage kaɗaici da damuwa.            Aunty Shahudah da dama ita kaɗaice babu a cikinmu ta sakko daga saman bene cikin wando da riga, sai siririn gyale data yano bisa kai, ganin key ɗin mota a hannunta da bag ya saka mummy faɗin, “ke kuma ina zuwa haka mamana?”.           Tana ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai take fadin, “Mummy jirgin su my friend ya kusa sauka, kin sanshi bayason jira”.        “Okey amma ai baƙya fita ke ɗaya ba adaren nan, Salman ya tashi kuje, tun ɗazunma da driver kika tura da bai ɗakkosa ba?”.          “Mum driver kuma? To da wane yaran zai ɗakkosa?”.      Dariya duk suka sanya, banda ni dama na kasa fahimtar zancen, duk da tun ɗazun dama naji tana faɗin zuwan matafiyin dana kasa yarda a raina namijine duk da yanda take alaƙanta komai nasa da suffofin namiji.      Tashi Salman yay yana tuttura baki irin shi baiso zuwanba, ta jefa masa key ɗin hannunta tana harararsa, amma batace komaiba.        Juyawa tai ta kalleni cikin yamutse fuska tana faɗin, “K karna dawo naga wannan baƙar fuskar taki a falon nan, dan jack ya ganki wlhy zaima iya amai, dan bai saba ganin trash irinki ba”.         Murmushi nayi idona na cika da ƙwalla na miƙe na nufi ɗaki ina maimaita kalmar trash data kirani dashi, sai dai kuma abin mamaki abun baimin zafi sosai ba, dan zuwa yanzu a halayyarta kuma kaɗanne bata zubar na ganiba, gado na haye abina, na faɗa duniyar tunanin da yazamar min abokin rayuwa da ɗebe kewa.      Ban sake sanin hidimar da masu gidan keyiba har washe gari, duk da bayan kusan awa biyu da tafiyar su Aunty Shahudah na fara jiyo ƴar hayaniyarsu, sai kuma gidan ya koma tsitt.     ★★★★★★            Da safe ƙin fita nai har lokacin da nakeda tabbacin sun kammala yin breakfast, sai da naji gidan yay shiru sosai sannan na fito, babu kowa a falon hakanne ya bani ƙwarin gwiwar nufar kicin, Amina mai aiki nata ƙoƙarin gyara kicin ɗin, gefe kuma kuku na shirin ɗaura abincin rana, gaisawa mukai duk da suna bani girma kamar kowa na gidan, amma hakan baisa na ɗauki kaina sama da suba, Amina maƙwaftan suke da gidan namu, sai dai su ba masu ƙarfi bane, hakan yasa take shigowa aiki a nan duk wata ana biyanta, tacemin da can ita da mamanta sukeyi, da ciwon ƙafane ya takura mata sai ita tacigaba dayi ita kaɗai.                Itace ta nunamin abincina, dan haka saima na zauna a kujerar kicin ɗin kawai nahau karyawa muna hira da ita, inda shima kuku ke ɗan sakko nasa zancen da turanci, sai hausa ɗai-ɗai wadda sam babu daɗin ji daga harshensa.        Wani irin kuka naji a bayan Windown kicin ɗin, hakan ya sakani kallon Amina ina faɗin, “Minene haka ke kuka?”.       Ƴar dariya tayi tana bani amsa da cewar, “Jojon big Aunty ne”.     Nasan Shahudah suke cema hakan, dan haka nace, “Jojo kuma? Waye mai wannan sunan?”.      Yafitoni tai da hannu alamar nazo na gani, na ajiye dankalin dana ɗauka zansa a baki na miƙe zuwa gareta, kaɗan taja labulen Windown ta yanda zan iya leƙa wajen.         Aunty Shahudah na hango zaune cikin korayen ciyayin da aka gyara wajen da wani ɗan ƙaramin kare mai kama da jikin zaki a saman cinyarta tana shafawa, sai wani tsamurarren bature zaune gefenta daf, Aunty Aamila kwance itama a wajen kanta kamar bisa cinyar baturen suna dariya.             Labulen na saki ina sauke ajiyar zuciya, na dubi Amina sosai, “To Amina wanene jojon a ciki? Dan da alama dai wannan shine baƙon da yazo jiya kenan?”.          Tace, “Karen dake cinyarta shine Jojo, baƙon kuma Jack, a farkon fara aikina gidannan nazo na iske Big aunty da wani karenta jojo, sai dai wataran tsautsayi Boss yazo gidannan ya takashi da mota ya mutu, lokacin har a asibiti ta kwanta jiyyar saboda mutuwar karennan kuwa”.        “Tofa, ALLAH ya ƙyauta to, akan karen? wanene Boss ɗin to? Dan nasan kam ba ƙaramin fin ƙarfinta yayba da har bata ɗauki wani matakiba?”.       Dariya Amina da kuku sukayi, Amina tace, “Aikam kamar kin sani yafi ƙarfin nata, dan har yanzu batayi ko tari hakan a gabansa ba saboda mutuwar karen, ballema ayi tsammanin bin ba'asin yanda abun ya faru, ba kowa bane face mijinta”.        Kaina kawai na jinjina, na koma wajen abincina batare dana ce komaiba, nikam harma naji inason ganin wannan miji na aunty Shahudah, dan kuwa lallai yana ganin shashanci tsantsa daga gareta, inhar shima ba irinta baneba.           Ina cigaba dacin abincina ina sauraren hirar Amina da kuku harna kammala na tashi na fita.        A falo naci karo da Yaya Qaseem daya shigo ransa a matuƙar ɓace, hannu yasa ya wurgani gefe saboda na shigo masa gaba ba tare dana saniba, kaɗan ya rake fuskata bata bugi tebir din gilas dake wajenba.      Na sauke numfashin ambaton Alhmdllh ina binsa da kallon mamaki harya gama haurawa saman benen yana ƙwalama mummy kira tamkar zai tsaga gidan biyu dan azaba.       Tashi nai tsaye jikina har yanzu rawa yake, na shiga murza hannuna daya bugu da kujera yanamin zogi.          Yaya Qaseem ne ya sake sakkowa yana zage-zage da harshen turanci Mummy na biye dashi tana ƙoƙarin riƙesa da masa magana da hausa ita kuma, amma sam yaƙi saurarenta.        Saiga su Shahudah sun shigo suma daga waje da ɗan gudunsu ita da jack da Aamila.       A take falon ya hautsine da hayaniya, nidai ina daga gefe ina kallonsu, sai dai bana fahimtar komai banda wani suna *Jawaad* danaji Qaseem nata ambata, yayinda Shahudah ke masifa tana nunashi, yako kai mata duka sai da jack ya kare shi aka sameshi.       Abu kamar wasa saiga gidan ya harmutse sosai, Mummy sai fama take dasu amma sunƙi suyi shiru, ganin hakanne ya sakata fashe musu da kuka.       Tsitt falon yayi kuma, sukai kanta banda Qaseem da ya fice abinsa rai ɓace, da sauri jack yabi bayansa, Shahudah da Aamila kuma suka zagaye Mummy, Salman baya gidan dai da alama.           Wannan lamari nasu yayi matuƙar bani mamaki, har yamma kuma ban samu jin abinda zai fahimtar daniba, sai abu ɗaya kacal ne kawai na ɗan gane, da alama dai daga wajen aikine aka fusatar da Qaseem, kuma wanda ya sakashi fusatar yanada alaƙa dasu musamman ma Shahudah da haushin Qaseem yaso ƙarewa a kanta...............✍🏻 Page 22 ...............Tun shigowar Qaseem hukumar tasune ya tabbatar akwai abinda ya faru, dama kuma ya samu kirane daga sama akan yazo da gaggawa.          Shigarsa wajen da manyansu suke tare dasu Jawaad ya saka zuciyarsa tsitstsinkewa, musamman tozali da ƴan tawagar Jawaad da yay su Hafeez.          Shi Jawaad ma yana zaune ne kansa a ƙasa saboda ciwon da yake masa, baima san da shigowar Qaseem ɗinba.        Bayan shigowar Qaseem an jira mutane biyu da ake jira suma sun shigo, kafin a fara gudanar da yabo da jinjina akan namijin ƙoƙarin da su Jawaad sukai.        An kuma tabbatar da wanke su Aliyu daga laifin da ake zarginsu dashi wanda yay sanadin zamansu cikin jail.      Take wajen ya ɗauki tafi.         Abinfa zai baka mamaki ko motsi Jay baiyiba a wajen, duk da laifin abokansa da aka wankesu baisashi ya ɗago yama kalli kowa ba sam.            Qaseem ya buƙaci yin magana, dan haka aka bashi damar yi.         Duk da son danne fushinsa da yaketa ƙoƙarin yi hakan ya gagara, sai da muryarsa ta fallasashi, a kausashe yake magana akan yanda aka maida aikin ta bayan fage bayan kuma shi aka damƙawa, ya cigaba da maganganun da suke nuna sukar Jawaad kai tsaye tareda muƙarrabansa, harma yana nuna akwai shiri a cikin lamarin, sai dai idan Jawaad ɗin dama yasan inda Alhaji Kokino yake.          Jay da duk yake sauraren komai yaɗan taɓe bakinsa ba tare daya ɗago ba, ɗakin taron kuma yay tsit an rasa mai bama Qaseem amsar tambayoyinsa, kowa ya zubama Jawaad ido ana buƙatar ƙarin bayani daga garesa, amma abin mamaki tamkarma baisan sunaiba.         Hakanne ya saka Aliyu dake kusa dashi taɓashi kaɗan.       Jawaad ya ɗan ɗago ya kalli Aliyun idanunsa sunyi jajur na gajiya da barci,       “Boss kanafa jin mi yake faɗa”.        Guntun murmushi Jay yayi kawai ya maida kansa yanda yake yana lumshe idanu, sai da Qaseem ya gama ɓaɓatunsa har sir Ahmad ya dakatar dashi sannan ya dawo ya zauna yana huci, ba ƙaramin haushin ƙin kulashi da Jawaad yayba yaji.        Sir Ahmad ne yay bayanin da kowa ya gamsu a wajen bisa shakkun da Qaseem yaso jefa musu akan Jay, daga nan sukai abinda ya tarasu aka sallami kowa.      Dan Jawaad yaƙi cewa kowa komai, koda aka buƙaci jin ta bakinsa Jabeer yaba damar yin bayani, acewarsa shi kansa na ciwo, da yake kowa yasan yanada lalurar ciwon kai da sam idan ya motsa masa bayason takura sai akai masa uziri.        Wannan abunne ya sake fusata Qaseem matuƙa, koda suka fito sai ya tare Jawaad ɗin bisa hanya.         Ko kallonsa Jay bai yiba ya raɓa ta gefensa zai wuce, nanma Qaseem ya sake taresa.          A fusace Jawaad ya fisgo bindigar dake jikin Rose ya nuna Qaseem da ita, dan zuciyarsa a maƙoshi take, shiyyasa sam yaƙi kula Qaseem ɗin tun farko.           Babu wanda yay zaton da gaske Jawaad yake saida ya saki harsashin ciki gadan-gadan akan Qaseem, Aliyu ne ya hankaɗa Qaseem ɗin gefe harbin da Jawaad yayi ya sami ƙofar wani Office dake a wajen.      Nan take wajen ya hargitse da ihu, inda shima Qaseem ya fiddo bindiga wai zai harbi Jawaad, da ƙyar aka rirriƙesa.       Cikin huci Jawaad ya nuna Qaseem ɗin yana faɗin, “Wlhy idan baka fita hanyata ba duk abinda nai maka kaine ka jasa, ka kama kanka Qaseem, karkai wasa da ɗaga maka ƙafan da nakeyi.....?”        Jan Hannun Jawaad da sir Ahmad yayine ya sakashi yin shiru, sai da ya kaisa har Office ɗinsa sannan ya sakesa.         Faɗa ya shiga masa akan waya kaisa aikata wannan gangancin? Yafa tuna Qaseem a samansa yake, baya tsoron abinda zai iya biyo baya?, duk da kowa yasan Qaseem yana shiga rayuwarsa hakan bazai hana a juya abun ta wani ɓangarenba, musamman da akasan Jawaad ɗin yana aiki tuƙuru, wanda hakan yana ɓatama  wasu a cikinsu rai da ruguzasu ta hanyoyi da dama sosai.          Ganin Jawaad ɗin baice komaiba shima sir Ahmad ɗin sai yay shiru, dan yasan Jay yanada haƙuri, amma tabbas yanada zuciyar jaraba idan ka kaisa maƙura.         Ruwa ya fiddo a firij ya miƙa masa, babu musu Jawaad ya amsa ya hau sha, sai da yasha fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a gwame.      Ya tsani takura a rayuwarsa, shiyyasa shima bai san takurama kowa,  amma Qaseem yaƙi ya riƙe girmansa, ya rasa miya tare masa a wannan duniyar?, tun suna ƙanana Qaseem bayason yaga cigabansa ko farin cikinsa, baisan miyasa hakanba?.      Nannauyan numfashi ya kuma saukewa yana maijin kewar mahaifiyarsa, sosai yake bukatar ɗumi irin na uwa a kusa dashi, sai dai shi tashi ta masa nisan kiwo.........        Sir Ahmad ya katse masa tunani ya dafashi a kafaɗa, ɗago jajayen idanunsa yay yana kallonsa, cikin sigar lallashi sir Ahmad ɗin yake ma Jawaad nasiha akan yacigaba da haƙuri da lamarin mutane, haka rayuwa take, kai kana harkokinka baka damu da kowa ba amma wani shi idanunsa na bisa kanka gaba ɗaya, kowa a rayuwa da kagani akwai tasa gaddarar, maƙiya kuma sune gishirin zaman duniya.       Jawaad ya gamsu da jawaban ogan nasa, dan haka yay masa godiya sosai.         A waje kam sosai hayaniya ta ɓarke, su dai sauran waɗanda ke wajen sun zama ƴan kallo, dan kuwa dai faɗan na manyane.       Inda su kuma manyan hankalinsu ya tashi, da ƙyar aka saka Qaseem a mota aka bar wajen dashi, amma sai iƙirarin kashe Jawaad yakeyi.      Wannan shine dalilin shigowarsa gida yana banbamin masifa🤦🏻‍♀. _______________________________                Washe gari da yamma Jack da Aunty Shahudah suka fita yawo, basu dawo gidan nanba sai kusan sha ɗaya na dare, tunda yazo gidan kuma ban yarda mun haɗa hanyaba kamar yanda ƙawarsa ta buƙata, duk da ma dai na lura yau bata da walwala, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci ma bata da lafiya, dan tunda suka dawo daga yawo ita da Jack take ƙudundune a cikin kujera a falo, inaji tanama Amina masifa akan ta kashe mata ac.           Washe gari da safe kuma Abba ya dawo, kowa a gidan yayi farin cikin dawowarsa, dan ranar tare akai zaman cin abinci baki ɗaya har Yaya Qaseem da rabon dana gansa tun randa ya dawo a fusace.      Na zata Abba zaima Aunty Shahudah faɗan ganinta a gida tare da zuwan jack, amma sai naga luf, saima taɓara take zuba masa salo-salo wai ita ciki ya dameta, sannan hannu biyu ya amshi jack ɗin da shikuma yakemin kallon mamakin wannan kuma daga ina?.         Ni dai inda yakema ban kallaba, haka kuma ban saki jiki naci abincinba saboda harar da kowa ke jifana da ita a wajen, idan ka cire dad da lokaci-lokaci yakan kalleni yana maganar miyasa banason cin abinci?.       Amsa ta ɗayace kacal, “Dad inaci”.       Yanda Aunty Aamila keta faman takamin ƙafa ta ƙasan tebirin yasa na miƙe badan na ƙoshiba nace ya isheni, dad ne kawai yay min faɗan hakan, amma kowa baice uffanba.        Nidai nabar wajen ina murmushin yaƙe, ina shiga lungun ɗakinmu kuwa hawaye suka fara rige-rigen zubowa, ban sharesuba kuwa, haka na faɗa saman gado inayinsu, ban sake sanin hidimar da sukeba har washe gari da safe, inda Dad ya buƙaci ganina afalonsa.        Albishir ɗin da Dad yamin akan zanje na zana jarabawa duk sai ya mantar dani komai, bakina ya gaza rufuwa saboda tsantsar murna da farin ciki, yinin ranar da wannan abu na yini, shiyyasa duk abinda akaimin baiko ɓata raina ba.         _________________________               Har Jawaad ya baro office ya dawo gida ransa babu daɗi sam, ya kumazo ya iske Shahudah bata dawo ba, tsaki kawai yaja yay shigewarsa ɗakinsa, wanka kawai yay ya kwanta dukda masifar yunwar dake cinsa, amma gajiyar dake tare dashi har bishi-bishi yake ganin gari.       Yana kwanciya kuwa barci mai ɗan karen nauyi yay awon gaba dashi, bai sake sanin wane hali ake cikiba sai gabda sallar magriba.        A rikice ya tashi saboda salloli da suka wucesa, yay azamar yin ramuwarsu yana jero istigifari ga UBANGIJI.      Bayan ya idar yay shirinsa tsaf ya fice zuwa gidan kakansa daya haifi Mamansa, mijin kakarsa mama maryam kenan.       Ya iskesa yana da baƙi, dan haka bayan ya gaishe da baƙin yay wucewarsa cikin falon tsohon, kuloli yaci karo dasu, dan haka ya zauna yana buɗewa, yasan dai bai wuce tuwo ba, kuma daga gidan Ummansa ne ake kawoma baba, dan tunda mama maryam ta rasu bai sake aureba, shi kaɗai yake zaune a bunsa a gidan saisu idan sunzo.       Tuwonsa ya zuba yaci ya ƙoshi yanamai jin nishaɗi, yaushe rabonsa da abinci mai nagarta irin haka? Yanama zaton tun masar da umman ta aika masace.          “Kai ja'iri, tuwon nawa kake cinyewa?”. Baba dake shigowa ya faɗa yana harar Jawaad da wasa.          Dariya Jawaad ɗin yayi idonsa akan kakansa da tsufa ya kama sosai, “Haba mai ran ƙarfe kaimafa tuwon na gidan Umma nane, tunda kaƙi fita a gwaurantaka kayo mana amarya”.           Dariya sosai tsohon yayi, yasa sandarsa ya daki kafaɗar Jawaad da saida ya sosa wajen saboda zafi.        “Dan gidanku, ni da kai munada banbanci ne? Kaima da kake da matar baka da banbanci da tuzurun da baima taɓa aureba”.       Murmushi Jawaad yay yana ɗan taɓe bakinsa, saboda tsoho dai ya taɓo masa inda ke masa ƙaiƙayi, aiko bai bada amsaba ya miƙe yaje ya wanko hannunsa sannan ya dawo ya zauna.      Baba dake binsa da kallo yace, “Daga ina kake a darennan?”.          Jawaad ya zauna kusa da baba yana jingina kansa da kafaɗarsa yace, “Daga gida”.        Shafa kansa baba yayi yana maijin tausayinsa, yace, “Yau an tuna da tsoho kenan?”.         “Nikam dama kana raina, wani aikine kawai ya dabaibayeni sai yau na sauke nauyinsa”.        Murmushi baba yayi, “Naga komai ai a tv Jawaad, shiyyasa a kullum bana haufi a gareka, sai yanzu ne nake sake gaskta maganar mahaifinka da tun bakasan kanka ba yake dangantaka da aikin ƴan sanda, ashe shiya san miya hango mana”         Murmushi kawai Jawaad yay yana haɗiye abu mai ɗaci a maƙoshinsa, daga nan ya cigaba da sauraren yabo da kakansa keta jerawa akan ƙyawawan halayyar mahaifinsa, a haka barci ya sake sacesa.       Baba yakai dubansa ga fuskar Jawaad, ganin yay barci sai yay murmushi yana kai hannunsa ya shafa kumatun Jawaad ɗin.      Ido Jawaad ya buɗe a hankali ya kallesa, baba yace, “Tashi kaje ɗaki ka kwanta”.       Bai musaba ya miƙe ya shige bedroom ɗin baba, lafiyayyen ɗaki dayasha gyara tamkar bana tsohon da rayuwa taima nisa ba, lallausan gadon baba Jawaad ya haye, yaja bargo ya rufe jikinsa yana lumshe idanunsa, kafin kace mi nan nauyan barcin ya sake ɗaukesa kamar wasa. Yau dai kam Jawaad anan ya kwana tare da kakansa, sai da yay sallar asuba ya karya da breakfast ɗin da Faisal ya kawo daga gidan Umma sannan yayma baba sallama ya tafi gida akan yana nan dawowa anjima zasuyi wata magana da baba.        Baba yace “to ALLAH ya kaimu saika dawo, ALLAH ya tsareka akoda yaushe”.        “Amin” Jawaad ya amsa yana fita. _________________________        BAYAN SATI BIYU  _________________________                   Har wannan lokacin Aunty Shahudah da dai na gida, bata komaba kuma mijinta bai zoba, sannan jack na nan bai tafiba sai kace gidan tsohonsa.           Nikam tun ranar da mukaci abinci tare ban sake zama inda yakeba, saboda har ɗaki ta biyoni ta ƙaremin zagi da cin zarafi akan ko Dad ne ya kuma buƙatar na zauna dasu cib abinci nasan yanda zan zame, idan ba hakaba wlhy saita ci mutuncina.      Haƙuri kawai na bata nikam, dan yanzu ni bana ɗaukarta sahun masu isashen tunani.          Tamin wannan abun ma da kwana uku Dad yace na shirya zuwa makarantar da zanje na zana jarabawata, ranar dai kamar anmin gafara naji, har kukan daɗi nayi kuwa.     Kwana biyu na cika na tattara komai na sayayyar da Dad ya yo mani domin tafiya, dan makarantar boarding school ce, sai dai yanda naji su Aunty Aamila na faɗin wai ban dace da makarantar ba nasan babbar makarantace.      Ranar dazan wuce na lura kowama murna yake da tafiyata, dan Salman harda faɗin, “ALLAH raka taki gona, koba komai sa huta da kallon baƙar fuskata abin amai”.       Dariya mummy da aunty Aamila suka sanya, dan mu kaɗaine a wajen, Shahudah da jack suna can baya suna hira.                Har bakin mota Amina da kuku sukai min rakkiya, sai da sukaga na shiga mota mun fice a gidan sannan.       Na share ƙwallar data zubomin ina murmushin kewa da farin ciki.   😅👏🏼ALLAH ya bada nasa takwara, sai dai fa ni ƴar team Shahudah ce😆😜, bara na fece kafin naci mazga⛹‍♀. _________________________                Tunda Jack ya bata shawarar zubar da cikinnan burinta ya dawo sabi fil, dan ya tabbatar mata Jawaad burga kawai yake mata babu wani sakinta da zaiyi tunda yana masifar sonta.       Ta shafa cikinta da ayanzu haka yake mata ciwo, tabbas tana wahala akan wannan cikin da bata shiryama zuwansa ba, gashi harya fara sakata ƙiba, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, duka shekarunta nawa da za'ace ta ɗauki ciki? Kamar yanda Jack ya faɗa, ita kanta tasan dan tayi gaggawar yin aurene kawai, bakomai ya jawo hakanba kuma sai ƙaunar Jawaad data tunzurata, da shawarar Mummynta, anya kuwa bazata zubarba kawai ta huta? Iyakaci dai ayi badakalar da za'ai na ɗan lokaci ta wuce, daga baya komai zai lafa a wuce wajen.        Zama tai a bakin gado ta dafe kanta tare da cije bakinta saboda murɗawar da cikinta ke mata, kusan min tuna uku tana a haka kafin ta samu ya lafa mata, sai wani zazzaɓi da takeji wanda ya zame mata jiki a yanzu kullum yamma saita yisa.        Wayarta ta ɗauka ta kira Aamila, babu jimawa sai gata ta shigo ɗakin.        “Sisi lafiya kike kirana?”.        Miƙewa Shahudah tayi idonta akan Aamila, “Aamila na yarda da shawararku zan zubar da cikinnan kawai”.       Zaro ido Aamila tayi tana ɗan ja baya, “Wai da gaske dan ALLAH?”.        “Na taɓa miki maganar hakan?”.       “A'a, ai abunne da mamaki, keda kike mugun tsoron Brother Jawaad karya rabu dake, amma yanzu lokaci ɗaya kizo da batun amincewa”.         Tsaki Shahudah taɗanyi, “Karki damu, ni nasan barazanace kawai, son da bb kemin bazai taɓa yarda ya rabu daniba wlhy, kawai yanamin burgane dan karna zubar, idan kuma yay haƙuri nan gaba ai zan haihun, amma gaskiya ba yanzu ba”.        “Kinyi ƙyan kai gaskiya, yanzu ke mikike buƙata?”.         “Shawarar da nake buƙata kenan daga gareki, ɗazun jack yace yasan maganin da zaimin aiki ba tare da nasha wahala ba, inaga kije kufita tare kozaku samu a wani pharmacy ɗin, sai dai dan ALLAH karki bar Mummy ta sani”.        “Karki damu, insha ALLAHU babu wanda zaiji”.          Koda Aamila ta fice sai Shahudah ta koma ta zauna, wayarta ta ɗauka ta dannama Jawaad kira, sai dai harta katse bai ɗagaba.        Text massege ta tura masa kamar yanda suka shirya da jack, kodaga baya cikin ya zube wai bazai zargeta akan itace ta zubarba.         Mummy batasan mi suke shiryawa ba, a gabanta Aamila da jack suka fita a gidan.      Sun bazama neman maganai cikin manyan pharmacy's ɗin garin, amma samunsa ya gagara, saboda ba kowane ke saidawa ba, dabara ce ta faɗoma Aamila a rai ta kira number Munira cikin yaran gidan su Jawaad, dan ta taɓa bata labarin wata ƙawarta da ta raka zubar da ciki.           Sun sanar mata abinda suke buƙata sai dai basu faɗa mata gaskiyar wanda zaiyi amfani da shiba, itace ta kira likitan daya bama ƙawarta wancan maganin ta haɗasu dasu Aamila, shi kuma yay musu kwatancen inda zasu sameshi.           A asibitinsa da ya kasance privet suka samesa, babu ko ɗar suka biya kuɗin daya yanka musu ya basu allurar da za'ai amfani da ita, a cewarsa itace tafi aiki shap-shap kuma bata cutarwa.      Sai da jack ya duba sukkan bayanan allurar ya kuma tabbatar da maganar Doctor sannan ya suka amsa suka nufi gida.             Jack bashi da shamaki da shiga ɗakin Shahudah a duk sanda yaso, dan haka koda suka dawo a gaban idon Mummy ya shiga, Aamila kuma ta zauna a falon dansu ɓadda hankalin Mummy wai.     Ƙudundune ya iske Shahudah zazzaɓi ya rufeta, ya yaye bargon data rufa yana taɓa gefen wuyanta, buɗe idanunta tayi, ganin jack ne yasata miƙewa da ƙyar tana kallonsa, “Kun samo?” tambayar data fara jefa masa kenan cikin harshen turanci.      Kansa ya ɗaga mata, ya ciro allurar daga aljihunsa yana nuna mata.        Amsa tayi ta jujjuya allurar a hannunta, sai kuma ta kallesa da tambayarsa wai miyasa basu sayo maganinba? Yafasan batason allura.      Bayanin duk yanda sukai ya bata, ya kuma tabbatar mata wannan allurar tafi maganin inganci, hakan ya saka ta aminta da batunsa.        Hannu ta bashi yay mata allurar tana matse baki, can ƙasan zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai biyo baya daga Jawaad.............✍🏻 Page 23 ..........Tunda aka buɗe mana katafaren gate ɗin makarantar muka shigo nake baje idanu da hanci ina kallon wannan tsararren gini da tamkar ba makaranta ba.         Yanzu nan ni Bilkisu ɗiyar malam Ado makahoce cikin wannan makarantar? Abu kamar mafarki kamar kuma almara. Niko tayaya zan manta da Dad a rayuwata.        Ƙwallar data cikamin ido na share ina fitowa daga cikin motar, ɗalibai duk suna cikin aji, hakan yasa security kawai kake iya gani na shawagi sai malamai.           Mun samu tarba ta musamman ga wani malamin da nakeda tabbacin yazo garemune bisa umarnin Dad, na gaishesa cikin girmamawar da naga nuna jin daɗinsa saman fusakarsa.       Bisa jagorancinsa muka isa har Office ɗin shugabar makarantar, bayan an bani wani form na cike aka haɗani da malamai uku sukaimini interview, duk da karatun bai kasance ɗayaba sun yabama ƙoƙarina.          Na sauke nannauyan numfashi da naji cewar komai yayi, duk da dai ba ɗari bisa ɗari na ƙoƙartaba amma sun amsheni, to dayake kuma abun ya haɗa da harkar kuɗi sai babu wata matsala aka kammala komai tsaf.        Malamin nan dai yana tare dani muka fito, sallama mukai da driver ya tafi domin shi ya gama aikinsa, sai kuma naji hawaye sun cikamin ido, a gaban idona ya wuce.            Malamin ya kalleni yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai kinji, alkairin Alhaji a gareni bazaisa na zuba ido kiƙi nasara ba, sai dai idan ALLAH ya ƙaddaro hakan, akwai yarinyata anan makarantar insha ALLAHU zan haɗaki da ita, zata taimaka miki sosai kafin ku fara zana jarabawar, tunda akwai tazarar kusan 5weeks yanzu haka insha ALLAHU”.            Cikin girmamawa nace, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi, ya kuma bada ladan zuminci”.        “Amin” ya faɗa yana maijin daɗin addu'ar yarinyar da yaba tarbiyyarta, dan kuwa yakuma tabbatarwa ba'a gidan Alhaji ta tashiba, saboda sanin da yayma yaransa da sam tarbiyya bata gama wadatar da suba.        Security ɗin dake kusa ya kira, shine ya kwasar min kayana muka nufi inda yace min Hostel ɗinmu kenan, dan lokacin an tashi Ɗalibai duk sun shige ciki.       Mun iske hostel ɗin shiru babu wata hayaniya a cikinsa, sannan ɗalibanma ɗai-ɗai muke gani suna shawagi, kowa kuma harkar gabansa yake babu ruwan wani da wani, a ƙofar wani ɗaki mukaja birki, security ɗin ya ƙwankwasa ƙofar, babu bata lokaci aka buɗe.           Budurwa da bazata gaza sa'a taba ce ta fito, sai dai shigarta zai tabbatar maka da wahala ta kasance musulma.       Ganin malamin dake tare danine yasakata juyawa da gudu ciki tana dariya, ko minti biyu bata rufaba sai gata sun fito itada wata mai tsananin kama da malamin.        “Daddy baƙuwar harta iso?” ta faɗa cikin zumuɗi tana ɗan tsalle a gabansa.         Murmushi yayi mata, ya jinjina kansa tare da faɗin “Eh Ummie na ta iso, gata nan ma sunanta Bilkisu Adam”.       Juyowa tai gareni cikin ɗoki tace, “Barka da zuwa Bily cikin makarantarmu”.         Haɗiye hawayen farin cikin da suka cikamin ido nayi ina amsa mata, banyi zaton zanje waje a karbeni lokaci gudaba kamar yanda Ummie tai mini yau, gata dai da gani itama ƴar gatace amma sam babu fuskar wulaƙanci a tare da ita.       Ta kama hannuna cikin nata tana sauraren bayanin da daddynta ke mata a kaina cikin nuna zaƙuwa da ɗoki, ya maida dubansa gareni yana faɗin, “Bilkisu wannan itace ɗiyata kamar yanda na sanar miki, karkiji komai ki saki jikinki da ita, insha ALLAHU zakiji daɗin zama da ita kamar yanda nima nake ƙyautata mata zato a kanki, komai na tsarin makarantar zata fahimtar dake, karkuma ki cutama kanki, duk abinda ya shige miki duhu ki tambayeta kinji”.        Kaina na ɗaga masa ina risinawar girmamawa a garesa, nace, “Insha ALLAHU Daddy, ngd sosai da karamcinka a gareni”.         “Karki damu Bilkisu, Alhaji Aliyu ya wuce hakan ma a gareni, ALLAH ya bada nasara ni bara na wuce”.       Sallama yay mana Ummie nata masa shagwaɓa ya wuce ya barmu.         Itako ta rungumeni tana sake min barka da zuwa, ta shiga ƙwalama wasu kira da nake ƙyautata zaton ƙawayentane, dan kuwa daga cikin ɗakin suka fito harda wadda ta leƙo ɗazun, su uku ne, kuma duk bazasu wuce sa'anni naba.         Biyu a ciki sun amsheni hannu biyu, ɗaya kam dai sai yamutse fuska takeyi, ban damuba dan na saba ganin irinta tun shaiɗan na yawo da ɗan kanfai cikin duniya.        Sune suka kwasar min kaya har cikin ɗakin dake da gado biyar kacal a cikinsa, sannan komai tsaf tamkar ba makaranta ba.        Zaunar dani Ummie tayi a gado na ƙarshen ɗakin tana faɗin, “Wannan shine gadonki, akwai mai shi da, amma ALLAH ya mata rasuwa hutun da mukaje ɗinnan, yaya tace, tanada ciwon sikila ne.         Nace, “ALLAH sarki, ALLAH ya gafarta mata, kukuma ya baku haƙurin rashinta”.       “Amin” Ummi ta faɗa tana sharar hawaye.        Tace, “Sunana Sumayya Sadik, amma anfi sanina da Ummie saboda sunan Momy na aka saka min”.       Murmushi nayi mata, nace, “Nice name, nima zance Ummie ɗin tunda sunan Momynmu ne”.      Ƴar dariya tayi tajin daɗi, ta nuna sauran su ukun, “Waɗanan ƙawayenmu ne, mu biyarne a guruf ɗinmu kafin rasuwar ƴar uwata, mu ƙawayen junane, ajinmu ɗaya, abu ɗaya muke karanta, kuma burinmu ɗaya. Wannan sunanta Nazifa Sulaiman, wannan kuma Rebecca Emanuel, sai Zuhrah Abbas”.        “Masha ALLAH, sunayenku masu daɗi dukan ku”.     Duk Dariya sukai am ma banda Nazifa da tun farko ta Nuna bata ra'ayina, yanzunma dai tana kwance a gadonta sai latse-latsen wayama take.        Nima na faɗa musu sunana Bilkisu Adam.        Rebecca tai saurin faɗin, “Bilkisu muna fata zaki cike mana gurbin guruf ɗinmu da muka rasa a yanzun”.      Murmushi nai bance komaiba, dan bazance zanyi saurin aminta da suba tunda banga halayyarsu ba........      Zuhrah ta katse tunanina da faɗin, “Please Bily karkice a'a, muna buƙatarki a cikinmu dan mudai kin mana”.       Nanma murmushi nayi dai, a raina ina mamakin ni da kullum su aunty Shahudah ke kushe munina da ƙyamata ce kuma har suke iƙirarin na musu su kuma?.     Magiya suka shiga min da roƙon karnace a'a, dan haka kawai sainace musu su bari zanyi tunani to.       Murna sukaitayi wadda ni taita bani mamaki, sai dai ina jiyo tsakin da Nazifa tayi kaɗan.      Ban damuba, dan amsar da ƴan uwanta kawai sukaimin ta wadatar dani, da taimakonsu na kintsa kayana tsaf, daga nan muka zauna sunamin lissafin abinda makarantar ta ƙunsa.         Zakuyi mamaki idan nace muku harna kwanta barcin dare ban tuno ko ɗaya daga cikin su aunty Aamila ba bayan Dad kawai da tunda muka iso nake jerama addu'a a zuciyata. _________________________             Kamar yanda dokar allurar take sai bayan minti arba'in zata fara aiki, dan haka Jack ya fita yabar Shahudah a ɗakin ita kaɗai, kwanciya tai luf a gadon, sai kuma lokacinne wani mashahurin tsoro da fargaba suke shigarta, babu abinda ke mata kaikawo cikin rai sai Jawaad.      Tabbas ita kanta tasan ta taro match na haƙiƙa a filin da bata da ƙarfin buga ƙwallon, fatanta dai ALLAH yasa tsarin da sukai ya tafi dai-dai, shine kawai zai zama mafita a gareta daga buyagin Jawaad mai zuciyar masifa idan aka ƙuresa.       Da wannan tunanin wani barci mai daɗi ya kwasheta. ★★★★★★           Haka kawai gaban Jawaad yaketa faɗuwa, kuma sai Shahudah kezo masa cikin rai baisan dalilin hakanba, zaune suke a Office ɗinsa shi dasu Aliyu suna tsara yanda zasu fuskanci case ɗin da aka basu dangane da ƴan fashin nan a safiyar yau.        Tsayawa yay daga rubutun da yake a blackboard ya matse maker ɗin hannunsa yana dafe ƙirjinsa.        Zuba masa idanu su Hafeez sukai, Jabeer yace, “Boss lafiya kuwa?”.        Numfashi ya sauke a hankali yana musu murmushin yaƙe, yaɗan girgiza kansa sai kuma ya cigaba da abinda yakeyi.        Badan sun yardaba suka barshi, shikuma zuciyarsa na cigaba da tsitstsinkewa.        Lallai yanaji a ransa wani abu zai faru dashi kuwa, to amma minene?     Wannan amsarce baida ita, dan haka ya share abun yana cigaba da karanto addu'a cikin ransa da maida hankali gasu Aliyun....... ★★★★★★         Wani azababben ciwon marane ya farkar da Shahudah daga daddaɗan barcin daya ɗauketa, ba tare data shiryaba ta fasa ƙarar data jawo hankalin su Mummy dake falo, a matuƙar rikice suka shigo ɗakin har suna ƴar rige-rige kuwa.       Dukansu kanta sukai suna tambayar lafiya kuwa?      Cikin kuka take nuna musu cikinta, a razane Mummy tabi santaleliyar farar ƙafar Shahudah da jini kebi da kallo, har taune harshe take wajen ambaton “Jiniii!!?”.         Cikin ruɗewa Aamila itama ta maimaita “Jini kuma Mummy?”.      Shi dai jack baice komaiba, saboda da hausa su Mummy sukai magana baiji mi sukace ba, sai ƙoƙarin ɗaura kan Shahudah ma yake bisa cinyarsa yana jero mata sorry.         Gaba ɗaya Mummy ta rikice, jikinta sai rawa yake tana jerama Shahudah tambaya akan miya sameta? Miya kawo zubar wannan jinin kuma?.       Bata samu amsa ko guda ba, dan haka ta fice kamar zararriya, Dad ta kira a waya tana sanar masa yazo gida babu lafiya.        Dama yana hanya, dan haka yace mata ga shinan zuwa a rikice.       Ba Mummy ba, hatta su Aamila da sukasan tushen komai sun rikice, dan jini bana wasaba ya ɓallema Shahudah, ta jiƙe inda take kwance sharkaf cikin mintunan da basu wuce goma ba, jikinta kam harya fara saki saboda mahaukacin jinin da take ɓararwa.         A wannan halin Salman da Dad sukazo suka samesu, suma rikicewar sukai, wasu suce a kira Doctor wasu suce a tafi asibiti, daga ƙarshe dai sukabi shawarar Salman da yace akira Doctor kawai, dan kafin su isa asibiti Shahudah zata iya rasa rantama gaba ɗaya.      Kowa ya gamsu da hakan, dan haka aka dannama family Doctor ɗinsu kiran gaggawa.          Doctor ya iso akan lokaci, dan haka ya kora kowa a ɗakin ya shiga ƙoƙarin ganin ya shawo kan matsalar sai dai hakan ya faskara cikin sauƙi, dan kuwa tuni Shahudah da dai ta sanƙame masa alamar suma.       Dole Doctor ya nema taimakon wani abokin aikinsa, babu ɓata lokaci shima ya iso tare da ƙaro musu ƙarin kayan aiki.       Su Dad duk sun rasa ina zasu saka kansu, Mummy kam kuka take rurus wanda ya kasance da biyu, damuwar halin da ɗiyarta ta tsinci kanta da ɓoyayyen burinsu akan cikin da suka ƙwallafa rai.        Salman zai kira Jawaad Dad ya hanashi, acewarsa kar a tada masa da hankaki su jira suga abinda zai biyo baya tukinna.      Dole Salman ya haƙura ya ajiye wayar suka cigaba da zagayen falo, inda lokaci-lokaci Dad kan jeho musu tambaya akan miya kawo sanadin matsalar?.        Amsa ɗaya Mummy ke badawa “Ita bata saniba, wai Shahudah tana ɗakine tun ɗazun tana barci”.       Sam Dad bai gamsu da wannan maganarba, amma sai baija zancenba saboda a yanzu damuwarsu a ceto ran Shahudah tukunna. ★★★★★★         Koda su Rose suka fita suka bar Jawaad shi kaɗai a office ɗin sai zuciyarsa ta kuma ƙuntata da zungurinsa da tunanin Shahudah, abin ya ɗaure masa kai sosai, dan kuwa a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya saboda takaicinta da yakeji ko kawota a ransa bayayi ma sam.       Yanzunma dai ƙoƙarin sake ingijeta yay a zuciyarsa ya shiga wani aikin, yanayi yana jan tsaki a duk sanda ta sake faɗo masa cikin rai.          A haka dai har ya samu nasarar janyeta cikin rai baki ɗaya ya cigaba da harkokinsa kawai. ★★★★★★★        Likitocin nan sunsha wahala kafin su sami nasarar shawo kan jinin dake kwarara a jikin Shahudah, daga nan suka koma ƙoƙarin ganin numfashinta ya dawo, bayan ɗaukar kusan awa biyar a kanta suka samu komai ya dai-daita, sai dai sun zangaɗa mata allurar barci tare da ƙarin ruwa.        Suka fito kowa na yarce gumi, tare da sanarma su Dad jini da Shahudah take buƙata saboda nata data kwararar.       A nannefa aka shiga kallon kallo, dan kuwa kaf gidan jinin kowa baima Shahudah sai na Jawaad, ta taɓa samun wata matsala lokacin tana secondary, har takai ana bukatar ƙara mata jini, a time ɗin an gwada na kowa a gidan bai mataba sai Jawaad, lokacin shikuma sunje can tare da kawu Nasiru ne.          Dad yace, “To amma Doctor kafin muje ga wannan yaya maganar cikin jikinta ne?”.            “Alhaji ai muma ajiye batun ciki gefe, yanzu dai jinin muke buƙata da gaggawa domin tana matuƙar bukatarsa gaskiya, daga baya mayi maganar cikin”.        Ajiyar zuciya Dad yayi, ya ciro wayarsa a aljihu yay kiran Jawaad, kusan kira uku bai amsaba, hakanne ya saka Dad tunanin lallai Jawaad yana kan aiki, dan baya taɓa masa kira biyu a ce bai ɗaukaba inhar yana kusa.       Yana cikin yin zancen zucine sai ga kiran Jay ɗin ya shigo, jikin Dad har rawa yake ya ɗaga.       Haƙuri Jawaad ya bashi akan yay masa afuwa suna yin sallar la'asar ne.      Ajiyar zuciya Dad ya sauke, danshi ruɗewar da suka tsinci kansu a ciki bata bari sunji kiran sallarba ma.        “Babu komai My Son, wlhy wata matsalace ta taso shine nace ALLAH yasa bakan aiki kakeba zan katseka”.       Gaban Jawaad ya faɗi, dan muryar Dad kawai ta mugun tsorashi,  yay saurin faɗin, “Babu damuwa Dad, kana buƙatar ganinane?”.          “Sosaima kuwa my son”.          “Insha ALLAHU ka bani nanda mintuna talatin zan iso”.       “ALLAH ya kawoka lafiya”.      Dad ya faɗa yana sauke wayar a kunnensa.            Jawaad ya rasa mizaiyi hasashe a wannan wayar da sukai da Dad, jacket ɗinsa sky blue daya ɗoro saman baƙaƙen kayan jikinsa ya ɗauka jikin hanga ya fice cikin matuƙar hanzarinsa.       Gimba na hangosa ya taso da hanzari yazo ya buɗe masa mota ya shiga, ba tare da ya tambayi ina suka dosaba ya tada motar suka fito.        Saida suka hau kan titi Gimba yace, “Boss ina zamuje”.          “Zangina road” kawai ya iya furata masa yaja bakinsa ya tsuƙe.     Gimba daya fahimci ina suka dosa ya ɗauki hanyar da zata sadasu da gidan su Shahudah.            Tunda aka buɗe gate ɗin gidan gaban Aamila da tasan dokar ya shiga faɗuwa, jitake kamar Jawaad zai gane komai da ya faru a kan fuskarta.         Jawaad ya shigo cikin bajintarsa da jin shiɗinfa ya isa, fuskarsa sam babu walwa.           Yanda yaga duk sun nutsu waje guda sun zuba tagumine ya sakashi tsaresu da mayun idanunsa, Ya sauke akan Jack dake zaune kusa da Salman, aransa ya furta “Jack again?”.        Janyewa yay ya maida ga Dad daya miƙe tsaye yana faɗin, “Yauwa My son ka iso?”.      Kai kawai Jawaad ya iya jinjina masa yana haɗiye wani yawu mai kauri saboda ganin Jack.       Mummy ma ta miƙe ta nufoshi kamar yanda Dad yayi.       Kusan a tare suke ƙoƙarin masa bayani, dan haka ya zuba musu idanu ko ƙyaftawa bayayi.        Tunda suka ambaci jini da Shahudah ta zubar yaji tamkar an buga masa guduma a kansa, ya wani lumshe idanunsa da suka fara canja launi yana fidda numfashi da sauri-sauri.........        Maganar Dad dake cewa, “My Son yanzu haka sunce tana buƙatar jini da gaggawa, inba hakaba zamu iya rasata” ta katse tunaninsa.         Buɗe idanunsa yayi yana buso numfashinsa, ba tare daya cema su Dad ɗin komaiba ya juya ya kalli likitocin dake tsaye tsuru-tsuru suna kallonsa.      Takawa ya farayi a hankali cikin nuna halin ko in kula zuwa garesu, ya zauna cikin kujerar dake wajen yana harɗe ƙafafu tare da miƙa musu hannunsa kawai, saboda t-sheat ce jikinsa baƙa wadda ta fidda dukkan ainahin surarsa, sai jacket dake samanta itama tsawon hannun iyakarsa gwiwar hannunsa.          Yanda Doctor yaga Jawaad ɗin duk sai ya dabarbarce, a harzuƙe Jawaad ya kallesa, cikin daka tsawa yace, “Jinin zaka ɗiba kokuwa kallona zaka tsayayi malam?!”.          “A'a yallaɓai, ALLAH ya huci zuciyarka” Doctor ya faɗa jiki na ɓari.                 Su dai su Dad duk sun zuba musu ido, tsawar da yay ko ai har cikin hanjin cikin Aamila da Salman ta shiga, shi kansa Jack baisan Jawaad bane zaizo gidan da tuni yabar falon ma.           Doctor ya gama shirin ɗibar jini a jikin Jawaad, dan haka a ɗan shakku yace, “Yallaɓai ko zamu samu ɗaki mu shiga ka kwanta, saboda dokace na ɗibar maka jini a haka”.        Wani mugun kallo Jawaad ya watsama Doctor ɗin, ya ja siririn tsaki da faɗin, “Kai dokar ta dama, kana ɓatamin lokaci bayan inada abunyi kuma”.          “Sorry yallaɓai”. Uffan Jawaad baice dashiba, sannan ko gezau baiyiba dukda allurar da aka surkuɗa masa cikin jijiyar hannu, wayama ya ɗauka yana latse-latse abunsa tamkar baisan mi akeyiba.         Yana a haka har aka kammala ɗibar jinin, Doctor yace, “Yallaɓai kayi haƙuri karka tashi, dan jiri zai iya kwasarka”.         Banza Jawaad yay masa bai tankaba, duk da idanunsa na masa yam-yam sai ya dake bai nunaba.       Dad da yasan kaɗan daga taurin kan Jawaad yace zai tashin yay saurin faɗin, “My son karka tashi kaji, kaɗan dakata ɗin kamar yanda yace”.          Guntun murmushi ya ɗago yayma Dad ɗin amma baice komaiba, sai kansa daya maida jikin kujerar ya kwantar kawai ya lumshe idanunsa.       Mummy tazo kusa dashi ta zauna tana miƙa masa abu a kofi.        “Karɓa kasha wannan”.      Idanunsa ya buɗe yana kallonta, ta kamo hannunsa ta saka masa kofin, hakanne ya sakashi ɗago kansa daya kwantar yana kallon abinda ke ciki.         Kofin ya matse cikin hannunsa yana ƙankance idanu, a bazata yace, “Mummy miya kawo sanadin hakan?”.          Dukda itama Mummy batasan sanadiba sai da gabanta ya faɗi, cikin ɗan in ina tace, “Yaro na santsin ruwane ya kwasheta ta faɗi, kasan Shahudah batajin magana akan saka shegun takalman nan masu tsini”.        Karan farko daya saki wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa lotsawa, yakai kofin da Mummy ta basa kan bakinsa ya shanye abinda ke ciki gaba ɗaya ba tare da ya bama Mummy amsar maganarta ba.        Koda ya miƙa mata kofin sai ya maida kansa ya kwantar jikin kujerar yay shiru tamkar mai barci.       Gaba ɗayansu ido suka zuba masa, gaba ɗaya yanayin da Jawaad yake ya bama Dad mamaki, amma sai bai kawo komai a ransa ba ya danganta hakan da yanayin aikine maybe................✍🏻 Page 24 ..............Tabbas ran Jawaad a ɓace yake, amma baka isa fahimtar hakan a kan fuskarsa ba, kusan mintuna talatin ya ɗauka zaune kafin ya miƙe da shirin tafiya, a cewarsa zaije ya dawo.         Da kallo duk suka bishi, idon Aamila tamkar zai faɗo ƙasa kuwa, gani take tamkar abinda suka aikata zaije ya binciko.        Salman ya sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Wai miya kawo wannan matsalarne?”.        Jack da Aamilah suka kalli juna kawai, kowanne na haɗiyar yawu da sauri, dan basusan amsar da zasu bama Salman ɗinba kuwa.         Dad kam sama ya nufa yace Mummy tazo yana son ganinta.      Koda suka ƙarasa ɗakinsa sai ya turke Mummy da tambayoyi.        “Aysha mi kuke ɓoyewane?”.       “Kamarya Dadynsu?”. “Ya ina tambayarki kina tambayata? Yanayin yaron nan kawai ya tabbatarmin akwai wani abu dani ban sanshiba, sannan namiki tambayar miya kawo sanadin zubar jinin, kincemin kema baki saniba, tana ɗaki tana barci, amma gashi shi kin sanar masa faduwa tai da takalmi, minene gaskiyar zancen?”.           “Wlhy Dadynsu nima sai da na faɗa ne na fahimci nayi kuskure, amma kamar yanda na sanar maka bansan minene sanadinba, dan tana ɗaki kwance ne”.         Kai Dad ya dafe yana bubbugawa, itama Mummy zama tai ta sake zabga tagumi tana zancen zuci, babban fatanta ace kawai cikin nan bai zubeba.     Sai dai ita kanta zuciyarta na rawa akan kar dai Shahudah bataji ƙwaɓar da sukai mataba sai da ta aikata ƙudirinta kamar yanda take buri tun farko akan cikin?.      ‘Innalillahi, kai amma da yarinyarnan ta cucesu wlhy kuwa’.          Likitocin nan sai da suka samu dai-daituwar komai sannan suka fito, har lokacin Dad da Mummy basu sakkoba.         Aamilah ta matsa kusa da Doctor ɗinsu, catai yazo zasuyi magana dan ALLAH, tashi yay sukai waje, babu wanda yasan mita faɗa masa, kusan dai mintuna goma sai gasu sun dawo falon.       Itace ta haura sama ta kira su Mummy, Doctor yay musu bayani cewar cikin jikin Shahudah da dai ya zube.       Tambayar farko da suka haɗa baki wajen jefo masa shine, “Minene sanadi?”.         Jimm kaɗan yay kafin yaɗan gyara zamansa, ya ce, “Eto Alhaji matsalar dai kamar daga mahaifarta ne, dan bata da ƙwarin riƙe abu mai nauyi, yanzu kuma cikinta ya shiga wata na uku, shiyyasa ya fara nauyi kaga”.       Kai Dad ya jinjina daga shi har Mummy sun gamsu da hakan, sai yanzu yakejin zargin da yake ya bar ransa, ya gamsu da bayanin matar tasa, amma kuma tayi gangancin cema Jawaad ɗin takalmine ya kada Shahudah.      Itako Mummy dai can ƙasan zuciyarta kamar tai hauka takeji, dan gaba ɗaya kalmar zubewar cikin nan ta gama birkita mata lissafi, kallo ɗayama zakai mata ka fahimci bata a cikin nutsuwarta.         Shi dai Doctor yay musu ƙarin bayani akan idan Shahudah ta tashi, tare da cewa zaije asibiti, idan ya taso aiki zai biyo ya kawo mata magunguna. ★★★★★★            Koda Jawaad ya koma Office harkokin gabansa ya cigaba dayi tamkar babu abinda ke damunsa, sai ɗan ciwon kai da yake danganta nasabarsa da jininsa da aka ɗiba, maimakon kuma ya samu nutsuwa ya huta sai hakan ta gagara, dan bayan kamar awa biyuma Asibiti sukaje shi da Hafeez duba Alhaji Kokino da jikinsa yay ƙyau Alhmdllh.       Dukkan iyalansa na wajen, Shema'u ganin Jawaad jikinta har ɓari yake, shiko batasan yanada abinda kecin ransaba, koda ta gaishesa hannu kawai ya ɗaga mata ko kallon arziƙima bata samu daga garesa ba.     Basu wani jimaba suka baro asibitin, kasancewarsu ƴan sandan farin kaya, ba kaki suke sakawa ba sai babu ruwan kowa dasu, babuma wanda ya kawoma ransa ƴan sandane su, sai dai iyalan Alhaji Kokinon da suka sani.      Bai sake waiwayar gidansu Shahudah ba sai da ya tashi aiki, daga nan ma ɗin gida ya wuce, yay wanka ya kimtsa bayan yasha tea daya zame masa amini yanzu, ya fito cikin kayansa masu taushi farare masu tambarin Adidas, ƙamshinsa yake fitarwa a hankali.       Yauma da kansa ya tuƙa motar zai fice, a gate sukai karo da yaron Kawu Saminu Mas'ood, sauke gilas ɗinsa yayi kamar yanda Mas'ood ɗin yay shima, cikin mutuntawa suka bama juna hannu kowanne yana daga mota bai fitoba sukai musabaha, kowa na tambayar iyalan ɗan uwansa.          Daga haka Jawaad ya fice Mas'ood kuma yay ciki.          Redio ya saka yana saurare harya isa anguwar su Shahudah dake shiru babu hayaniya, duk da babu wutar lantarki ko wanne gida zaka samesa da hasken janareto tunda anguwar duk irinsune masu hannu da shuni.         Yanayin Horn mai gadi ya buɗe da hanzari, dan cayake burkutaccen nanne Qaseem.                   Salman da jack na zaune a harabar gidan can gefe, Dukansu kowa da sigari a hannunsa yana zuƙa suna fira.        Salman yay saurin jefar da tasa ya take da ƙafa saboda ganin motar Jawaad.         Nesa dasu kaɗan yay fakin, dukda ya gansu ko kallo basu ishesaba ya rufe motar yay ciki abinsa.           Babu kowa a falon gidan, amma tv nata ɓaɓatu, tsaye yay yana bin falon da kallo kamar wani baƙonsa, hannayensa dukansu na cikin aljihun wandonsa.        Aamila ta fito daga kicin hannunta ɗauke da kofin tea da kuku ya haɗama Shahudah ta amso mata.       Sosai ta firgita da ganin Jawaad, yanda tai bayama kaɗan ya rage ta zubda shayin.     Ɗauke idonsa yay daga kanta tamkar baiga halin data shigaba.         Sannu tai masa, bai amsaba sai kansa kawai ya gyaɗa mata, cikin in ina tace ya hawo sama Shahudah nacan.        Duk da yayi ɗan mamakin miya maidata sama bayan yasan ɗakinta a ƙasa yake, amma sai bai ce uffanba yabi bayan Aamilah.         Aamilah ce ta sanarma Mummy da zuwansa, Mummy taɗan ɗaga murya tana faɗin ya shigo mana.       Jawaad dake ƙofar ɗakin tsaye duk yana saurarensu tura ƙofar yay ya shiga da sallama.        Kallo ɗaya yayma Shahudah dake kwance a gadon dan bata daɗe da farkawa ba, ta daiyi wanka dan ɗaure take da tawul fari, daka ganta kasan batada lafiya dan tayi zuru-zuru, ta ƙara haske sosai ga idanuwa sun kuma yo waje.           Gaisar da Mummy data miƙe yayi, ta amsa suna ficewa ita da Aamilah daga ɗakin.      Tunda suka fita saiya shiga bin ɗakin da kallo tamkar ya ajiye wani abu a ciki, hakan ya saka itama Shahudah ta bisa da kallo ƙirjinta na wani bugawa kamar zai fito.        Kusan minti ɗaya yana kalle-kalle kafin ya koma baya. jingina yay da bango hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa, ƙafarsa ɗaya ajiye a ƙasa ya tokara ɗayar jikin bango, ya tsurama jojo karen Shahudah dake kwance kusa da ita ido ko ƙyaftawa bayayi, sai faman cizon leɓensa na ƙasa yakeyi.         Shahudah da duk jikinta babu ƙwari ta miƙe zaune da ƙyar ta jingina da filo, kofin gefenta ta ɗauka tana juya cokali cikin shayin da Aamilah ta kawo mata, ta ɗago idanu ta sake kallonsa, “Bb ka zauna mana” tai maganar a matuƙar sanyaye.      Ƙala baice mataba, sai ƙafarsa daya sauke yana cigaba da kallon jojo.        Ya tako a hankali zuwa gaban gadon ya tsaya a kanta, sai kuma ya ɗora tsaftatacciyar ƙafarsa saman gadon yana zuba mata idanunsa da suka canja launi baki ɗaya.         A bazata tajiyo muryarsa kausashe yana faɗin,        “Wane likitane yay wannan aiki?”.      Dakewa tai cikin nuna halin ko in kula tace “Wane ai kuma Bb? Kainefa ka bani jini, kuma doctor ɗinmu ne ya ɗiba, wane kuma aiki kake buƙatar sanin wanda yay bayan wannan?”        Ƙafarsa ya sauke ƙasa yana sakin wani murmushin daya saka zuciyar Shahudah harbawa da ƙarfi.       Kujera ya jawo ya zauna, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, ya kuma tsuke fuskarsa yana kafa mata rikitattun idanunsa, “Hudah kinsan sunan aikin ɗan sanda kuwa?”.      Kanta ta girgiza masa a hankali, yanayin da fuskarsa take ya sake ruɗata.        Sauke ƙafarsa yay ya ɗan ranƙwafo yanda zasu ƙara samun kusanci, cikin magana ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa ya kaɗa mata yatsun hannunsa biyu yana kuma fiddo idanu waje sosai yace, “Wasa ƙwaƙwalwa. Dan haka ki faɗa min minene gaskiyar zance akan cikina?”.             Babu shiri Shahudah ta saki kofin shayinta a ƙasa, ya zube kofin ya tarwatse, jikinta sai ɓari yake, murya na rawa tace, “Bb wace irin magana ce wannan? Kana zargina nina zubar kenan?”.           Wani murmushi ya sakar mata yana bin kofin dake tarwatse a ƙasa ga shayin ya jiƙe musu ƙafafu da kallo, ya wani wulƙita idanu luuu yana maido dubansa gareta har lokacin fuskarsa da murmushi wanda ita tasan ma'anarsa sam bana farin ciki bane, ya janye ƙafarsa daga laimar ruwan yana miƙewa tsaye.          Key ɗin hannunsa ya shiga kaɗawa yay taku ɗaya biyu kamar zai nufi hanyar fita sai kuma ya juyo gareta yana nunata da key ɗin.         “Hudah nai miki farin sanin da inaga ko iyayenki basu gama nutsuwa sun mikiba, tun muna mu biyu a ɗakin nan ki faɗamin da haɗin kan wa kika aikata?”.        Cikin son kare kanta ta aro jarumtar dole ta fara masa bayanin abinda likitansu ya faɗa.       Uffan baice da itaba ya zaro handkherchief a aljihunsa yana rissinawa ya ɗauki wani abu a ƙasa, takowa yay ya dawo gabanta, ƙafarsa ya maida a saman gadon ya nuna mata syringe ɗin daya ɗaukko.         “Ki bani amsa da gaggawa kafin nakai maƙura, Wane likitane ya bada?”.           Karon farko a rayuwar Shahudah da taso karanto wata addu'a a harshenta saboda tsagwaron tashin hankali da ruɗani, sai dai batama san miya kamata ta karantan ba tunda ba addu'oin ta saniba.        Kanta ta shiga girgiza masa tana hawaye da matsawa baya, “Bb ni bansan komaiba wlhy, wannan abun bansan wanene ya kawosaba, sai dai idan likitocin nan suka yardashi by mistake, ka yarda dani dan ALLAH”.        Cikin halin ko in kula yace,  “Ba dolema na yarda dakeba ƴammata” yay maganar yana ɗaukar leda a saman mirror ɗinta ya saka sirinjin, ko kallonta bai sake yiba ya juya ya fice daga ɗakin cike da izzar da ɓacin rai ya haddasa masa.          Da ƙarfi Shahudah tai yunƙurin miƙewa tsaye danta bisa, sai dai rashin ƙwarin jiki yasa jiri ya kwasheta ta koma saman gadon yaraf ta kwanta hawaye na gudu saman fuskarta, ita kanta a yanzu jitai tana buƙatar cikinma, kodan tashin hankali da tsagwaron bala'in data hango cikin idanun Jawaad.          Mummy da Aamilah na falon, sai dai Aamilah ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kaikawo take tsakanin kujeru, gaba ɗaya yanayin Jawaad ya kuma tsoratata.     Duk da ac dake aiki a falon ita zuface ke tsatstsafoma goshinta.      Sarai Mummy ta lura da halin da Aamilah ke a ciki, amma ta kasa tambayarta mike damunta, dan tunda aka shaida musu cikin nan ya faɗi komai ya sukukuce mata, ko mama Atika ta kasa kira ta sanarmawa balle sauran ƴan uwanta......      Sakkowar Jawaad a fusace daga sama ya katse mata tunani, daga ita har Aamilah suka zuba masa idanu kamar yau suka fara ganinsa.          Baiko kallesu ba yay ficewarsa saboda shiyasan shika-shikan rashin mutuncin daya shiryama kowa a gidan akan cikinsa.       Sosai abinda Jawaad yayi ya kuma birkita zuciyar Mummy, hakama Aamilah da tasan dokar.       A bakin ƙofa Jawaad da Qaseem sukaci karo, kallon kallo sukaima juna Jay ya ɗauke idanunsa ya raɓa Qaseem ɗin ya cigaba da tafiya tamkar baisanshi ba.      Shiko Qaseem ya bisa da kallo har sai da Jawaad ya shiga mota yabar gidan sannan ya taɓe bakinsa, cikin falon ya ƙarasa shiga inda ya samu su Mummy yanda Jawaad ya barsu.        “Mummy miya kawo wancan shashashan gidannan kuma a daren nan?”.         Mummy data maido kallonta ga Qaseem tace, “Kamin wannan tambayar bayan kasan matarsa tana a gidan”.       Zama yay yana jan tsaki, “To ba gidansu tazoba, halan zuwa yay yace su tafi taƙi dan naga yana faman haɗiyar baƙar zuciyarsa da wataran zata zama ajalin sa”.       Kai kawai Mummy ta iya girgizawa tana haɗiye yawu da ƙyar, bayanin dukkan abinda ya faru da Shahudah ta bashi.     Qaseem ya miƙe zumbur yana faɗin, “Mummy anya yarinyarnan ba ɓarar da cikin nan taiba kuwa da gangan?”.        “Wace irin magana kake haka Qaseem? Yanzufa na gama maka bayani akan abinda Doctor ya faɗa mana dangane da mahaifarta ce bata da ƙwari......”         Saurin katse Mummy yay da faɗin, “Kai Mummy impossible, a wannan fushin na Jawaad akwai magana, inkuwa har da gaskene abinda Doctor ya faɗa to lallai shi bai yarda ba, kuma zaiyi bincike”.         “Bincike kuma Broth...?”. ‘Aamilah ta faɗa tsigil cikin sarƙewar harshe’.       Kallonta Mummy da Qaseem sukayi, Mummy dai kuma rikitar da ita sukai, shiko Qaseem ya kafe Aamilah da idanu dan yanayinta ya tabbatar masa bata da gaskiya.      Kafin ya samu damar yin wata magana Salman da Jack suka shigo falon.         Wucewa Qaseem yay sama wajen Shahudah, hakan yasa suma su Mummy take masa baya su duka suka bisa.        A yanda duk suka tarar da Shahudah ne ya tabbatar musu akwai matsala, kusan duk a tare suka shiga jera mata tambayoyi, bata amsa na kowaba a cikinsu sai hawaye da take zirararwa.        Mummy ta zauna tare da jawo kan Shahudah ta ɗaura saman cinyarta, kanta ta shiga shafawa a hankali alamar lallashi.        Hakan ya saka Shahudah fara sambatu da roƙon Mummy akan Jawaad, jinfa zata ɓallo musu ruwa Aamilah ta zauna tana riƙe hannun Shahudah da faɗin, “Haba sister kiyi shiru mana, ki kwantar da hankalinki bakida lafiya fa, insha ALLAHU komai zai zama normal indai Brother Jawaad ne zai huce shima, yanzu yana cikin ruɗanin rashin cikinne da halin da take ciki, amma ki bashi kwana biyu zai sakko ya fahimta kamar yanda kowa ya fahimta”.         Ita dai Shahudah kawai tana sauraren ƙanwar tatane, amma ita tasan wanene Jawaad da abinda zai iya, ballema tun farko tariga da ta saka masa shakku akan cikin tun fil azal, tasan yanzu kam sai abinda ALLAH yayi kawai, amma tabbas akwai ƙura bata wasaba. ★★★★★               Jawaad kam koda yabar gidan gida ya koma, amma tunda yay fakin sai ya gaza fitowa daga cikin motar, kifa kansa yay saman sitiyari yay shiru tamkar mai barci.         Tun yana iyajin motsin wasu daga jama'ar gidan da hayaniyar yara har gidan ya koma yay tsit alamar dare yaja sosai, baka iya jiyo komai sai kukan karnika na gidajen makwafta, da yake akwai wuta kuma sai anguwar ta kuma samun nutsuwar yin shiru babu ƙarar Generators dake hana kunnuwansu zama lafiya.      Tashi yay zaune sosai ya kwantar da kujerar da yake ya ƙara yin Balance ɗin samun yin tunanin da ƙyau, sam baya sha'awar shiga sashen nasu saboda ƙunar da zuciyarsa ke masa.        A watannin daya ɗauka na aurensa da Shahudah bai tsinci komaiba sai takaici da ɓacin rai, kullum da salon fitinar da take kawoma rayuwarsa, ga hargitsin aiki gana cikin gidansa.      Ya tuna maganar kakansa daya taɓa faɗa masa lokacin aurensa da Shahudah.        *_“Jawaad naso ka auri irin wadda rayuwarka keda buƙata, amma tunda haka ALLAH ya tsara muna maka fatan alkairi, sai dai ka sanifa shi ubu mai ƙyau abin san kowane, sai dai ba kowanne ƙyaƙyƙyawa bane kake samunsa ciki da waje mai amfani da amfanarwa, dakamar wuya asamu cikakken farin ciki tattare dashi inhar akwai tangarɗa tun fil azal, wani lokacin daga yanayin ginin abunne a zuciya da kuma rayuwa, wani lokacin kuma tun usul akwai rashin nagarta musamman idan anci karo da sakacin iyaye wajen rashin yin ginin da addini ya koyar, bazaka fahimci komai daga zantukana ba Jawaad sai nan gaba kaɗan, irin waɗannan yaran abinda zaku haifane abin tausayi dakai kanka da za'a jefa cikin garari ba suba, amma dai ALLAH ya sanya albarka da alkairi a ciki, ALLAH yasa muce gamma da akayi”._*        Nannauyan numfashi Jawaad ya sauke yana rumtse idanu da ƙarfi, wato irin waɗannan tashin hankalin da jahilcin ne kakansa ya hango masa tattare da auren Shahudah, wanda shi a baya tunaninsa bai kawo kan hakaba, kawai yafi kallon rashin isashshiyar tarbiyyarta zai tsayane ga taɓara kawai, kuma zai iya canjata da wuri tunda tana sonsa.      A irin kima da nagartar Dad ɗinsu bai ƙyautu ace zuri'arsa ce a wannan yanayin yahudancinba da sunan wai ƴancin kai, shikenan dan ƙaddara ta shigar dakai cikin wata rayuwar da ba takaba saika mantar da kanka da zuri'arka tushensu da addininsu da al'adunsu?, ansan a shekarun da suka ɗauka cikinsu dolene a samu raunin al'adunsu, dan yau da gobe ta wuce wasa, ballema ba zuwa gidan sukeba su, to amma bai dace a duk inda ka tsinci kanka ya zam ka manta da addininka da koyarwarsa ba, dan ako ina kake ALLAH ya wajabta maka yinsa da kuma neman ilimin sani a kansa.         Lallai yana ganin anzo gaɓar da zai tunatar da Dad da Mummy abinda suka mantan kokuma son zuciya ya sakasu maidashi baya saboda son ƴaƴa ko sakacinsu.         Haka Jawaad yayta tunani bai fargaba sai kiran sallar asubahi yaji, nannauyan numfashi ya sauke tare da kallon agogon dake a tsintsiyar hannunsa.        Ya ɗan matse idanunsa da sukai masa nauyin buƙatar barci, da ƙyar ya yunƙura ya tashi zaune sosai, ya buɗe motar ya fita ya nufi ciki.      Ji yake tamkar yabar gidannan gaba ɗaya yau ɗinnan. _________________________ BILKEESU _________________________              Sosai na samu nutsuwar zuciyar zama dasu Ummie, dama can ni a rayuwata inahar zaka nunamin ni mutumce kamar kowa mai daraja tuni nake sakar maka jiki, to yanda su Ummie suka amsheni sai hakan ya dasamin ƙaunarsu.         Nazifa ce dai har yanzu muna sama-sama ne, niko halinta bai dameniba ko kusa, abinda ya kawoni ma nafi son maida hankali kansa ba matsalar wani ba.      Dan na tabbata a halin yanzu wannan ilimin dazan nutsu na samune babbar katangata kuma gatana koda anan gaba idan ALLAH yasa muna a cikin masu tsahon rai.       Su dukansu babu mugunta suke nunamin karatu, hatta da Nazifa da batayina tunda na fahimci mayyar mathematic ce sai nake raɓarta ta koyan abinda ban fahimtaba.       Zakusha mamaki yanda takan zauna ta koyamin dukda anayine ana dizgani.        Ahankali sai na fara fahimtar halin kowanne a cikinsu har ita Nazifar kuwa, tunda na fahimci yanda halin kowannensu yake saina ƙara ɗaura ɗammarar zama dashi a yanda yaken danna ribantu da hakan.         Bani da lokacin hatta tunani a yanzu, na maida dukkan hankalina ga karatun sai ko bautar ALLAH dake a gaban komai, kullum kuwa ina ƙoƙarin miƙama UBANGIJI kukana.        Abinda ya kuma sakamin nutsuwa da Nazifa sam bata wasa da salla, lokuta da dama ma ita kema su Ummie faɗa akan su tashi suyi akan lokaci, idan har zan tashi da daddare da taji motsina itama zakaga ta tashi tayo alwala tazo kusa dani ta shinfiɗa abin salla.        Hakan dasu Ummie sukaga munayi sai suma ya fara tasiri a ransu, sai suka fara cewa suma mu tashesu dan ALLAH.        Daga nan sai muke tashinsu, itama Rebecca sai take tashi taita addu'oinsu, dan bata iya barcin da muma mun tashi, fatanmu dai ALLAH ya tabbatar da nasara a garemu akan wannan jarabawa.        Kusan halin ƙuruciya, a irin wannan shekarun namu dama zakaga daga harkar makaranta saina samari ke tasiri a rayuwarmu, dan idan mun zauna hira su Zuhrah kanta hirar samarinsu, nidai bani da abin faɗa, dan ko'a mafarki ban taɓa saurayiba, na tuna sanda ina gidanmu na haya har habaici akema innata akan banda farin jinine, bata cewa komai, iyakarta murmushi kawai.       Sai zuwa yanzunne nima nake gasgata maganarsu, lallai banida farin jinin, dan nidai ba'a taɓa cewa ana sonaba, ko irin soyayyar nan ta ƙuruciya ban taɓa yiba, sai dai naga ƙawayena nayi harma a bani saƙon musayar wasiƙar soyayya na kai.............✍🏻 Page 25 .............Wanka ya samu yayi da ruwan ɗumi danya rage nauyin jikin, sannan yay alwala ya fito, jallabiya kawai ya  saka ya fito zuwa massallacin gidan dake a ƙofar kiga.       Ana idar da salla ya fice abinsa, dama yau a makare yazo, dan haka yay sallar a ƙofa-ƙofa, bai yarda tsayawa gaisuwa da kowa ba har kawunansa, ya gudo gida ya kwanta.           Duk yanda tunanin yaso masa tasiri barcin da ya keji sai yaci ƙarfinsa, kafin kace mi ya fara sauke numfashi a hankali alamar dai yayi nisa cikin barcin.         A makare ya tashi zuwa office, dan haka yayta komai cikin hanzari harya samu ya kimtsa, yayi ƙyau sosai, ya fito yanata baza ƙamshi kamar ko yaushe.         Gimba da tun ɗazun yake gewayensa da tunanin ko lafiya?, yay saurin miƙewa daga wajensu mai gadi ya nufosa.         Sam babu walwala a fuskarsa, ɗaure take tamau babu sauƙi,  kusan biyar daga matasan ƴammatan gidan da suka fito zasu wuce makaranta suka shiga gaishesa kowacce zuciyarta a narke da ƙaunarsa.        Hannu kawai ya ɗaga musu dan baijin zaima iya motsa bakin balle aje ga magana, da sauri Gimba ya buɗe masa motar saboda yau dai yasan babu wargi a wajen boss.         Shima sai da ya zagaya mazaunin direba sannan ya fara gaishesa.      Shiru Jawaad ɗin bai amsaba, Gimba ya kallesa ta mirror, yanda ya gansa kwance a jikin kujera idanu a lumshe ya tabbatar masa lallai akwai matsala.      Bai sake cewa komaiba ya tada motar suka fice daga gidan.       Sai lokacinne Jawaad ya amsa masa gaisuwar, tare da faɗa masa inda zasuje kafin Office.        Jin asibiti ya saka gimba tunanin ko baida lafiya ne?.          A ƙofar gida sukaci karo da motar yaran da aka bama Jawaad ɗin yanzu a Office saboda tsaro su huɗu, gilas ɗin motar kawai Gimba ya sauke suka matso suna gaisheda Jawaad ɗin cikin girmamawa.         Idanunsa ya buɗe yana ɗaga musu hannu, bayani ɗaya yay masa akan Sir Ahmad yace yau zasu fara gudanar da aikinsu, daga yanzu duk inda zai saka ƙafa dolene sai da su.       Numfashi kawai ya basu, yay musu nuni su shiga mota kawai.       Umarninsa sukabi, su ka rabu biyu kowacce mota mutum uku, ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta Jawaad tana a tsakkiya.     Shi sam baya buƙatar wasu securitys tare dashi, amma Sir Ahmad ya matsa sosai akan yabar barin Jawaad ɗin na yawo haka tun randa abin nan ya faru tsakaninsa da Qaseem.                Shigarsu asibitin suka samu waje sukai fakin, kasa daurewa Gimba yay ya juyo a ɗarare yace, “Boss ko baka da lafiya ne?”.      Idanu Jawaad ya buɗe a hankali kan gimba, sai kuma yay masa guntun murmushi yana girgiza kai alamar (a'a).         Duk da Gimba bai gamsu ba haka ya fito, Security ɗaya kuma ya buɗema Jawaad ɗin motar, yaja kusan seconds ashirin sannan ya zuro ƙafarsa ƙasa ya fito.          Baƙin eyeglasess ɗinsa ya ɗora saman ido alamar dai babu sassauci kenan, yana tafe suna take masa baya cikin bajinta mai nuna alamun fushi tattare dashi.         Ganinsu kawai ya isa ya baka tsoro, gasu duk sunsha baƙaƙen suits da eyeglasses, fuskoki kam ba'a cewa komai saboda ɗaurewa.         Sun samu girmamawar mutane musamman ma'aikatan asibitin, duk da fuskarsa ɓoyayyar fuskace da ba kowa yasan matsayinta ba, amma yanayinsa da kwarijininsa sun saka mutane ganin girmansa a idanunsu, sannan yanayinsa ya tabbatar da ba ƙaramin mutum bane koda a hasashe saboda mazajen dake rufe da bayansa harda masu binduga a hannu su uku.      Sai ƙalilan da ba'a rasaba da zasu iya sanin fuskar, musamman tsananin kamar da yake da mahaifinsa.             Tsaye yay dai-dai saitin matar da ke a reception ɗin, duk sai ta rikice, Jawaad ya kalli gimba dake gefensa a ƙasan maƙoshi yace, “Office ɗin Doctor Tayyeb”.        Gimba ya juya ga matar yana maimaita mata.    Kai ta shiga gyaɗa masa baki na rawa tana faɗin, “Ok ok Sir” tai maganar tana ƙoƙarin kiran wayar ogan nata Doctor Tayyeb.        Basu san mi ake cemata daga canba, tanata dai ƙoƙarin masa bayanin dazai fa himta amma da alama cewa yake bazai samu ganinsu ba....       Tsawa ɗaya daga securitys ɗin Jawaad ɗin wani ya daka mata, hakanne ya sakata sakin wayar jikinta na tsuma, Gimba yace ta haɗasu da wanda zai kaisu Office ɗin ko ita ta fito ta rakasu.       Duk fa wannan dambarwar da ake Jawaad na tsayene yana saurarensu hannayensa duka biyu a cikin aljihu, nazarin asibitin da mutanen dake kaikawo a cikinsa kawai yakeyi, duk da ma tun shigowarsu kowa ya nutsu waje guda dan yanayinsu ya nunama kowa dama ba ababen wasa bane balle a gansu a ɗauke kai.         Wata Nurse ce tai musu rakkiya har Office ɗin, tana ƙoƙarin yin knocking Jawaad ya ɗaga mata hannu alamar kar tayi.      Ja baya tai kanta a rissine alamar girmamawa a garesa.      Gimba ya tura ƙofar Jawaad ya shige kansa tsaye, yayinda yaransa suka jeru a ƙofar kamar waɗanda sukazo kama ɓarawo😂.            Takun takalman Jawaad suka saka Doctor Tayyeb saurin matsawa daga jikin budurwar daya ƙwakume a Office ɗin yana lalubewa, itama Nurse ce, sanye takema da Uniform ɗin asibitin.         Wani wawan tsaki Jawaad yaja yana ɗauke kai daga garesu, Budurwar dukta ruɗe sai duƙar da kai take cikin alamun jin kunya da firgici, shi kansa Doctor Tayyeb ɗin a firgice yake, ganin Jawaad a asibitinsa da kuma abinda yaga yanayi da ƴar mutane.          Sai faman sinne kai yake yazo ya zauna a mazauninsa yanama Jawaad ɗin barka da zuwa.       Jawaad da bai tankashiba ya jeho masa tambaya mai rikitarwa,        “Wannan shine abinda kakeyi da ƴaƴan al'umma shiyyasa ka salwantar min da ciki?!!”.       Yanda Jawaad yay maganar a matuƙar kausashe ya saka jikin Doctor Tayyeb ɓari, bakinsa na rawa yace, “Yal...Yallaɓai wl... Wlhy kaji na rantse ban san komai akan maganar nanba, matarka ba zubar da cikinta taib.....”        Da ƙarfi Jawaad ya buga tebir ɗin gaban Doctor, wasu abubuwan suka zube, wasuko tsalle sukai suka canjama kansu muhallin zama.         “Mara mutunci, zaka cigaba damin wasan kwaikwayone kokuwa zaka sanarmin gaskiyar batu kafin na fasa ƙwalwarka da bindiga?!”.          Doctor Tayyeb daya manne da bayan kujera zufa na karyo masa ya share gumin goshinsa, “Yallaɓai please Calm dawn, wlhy bansan komaiba, yanda na musu bayani shine gaskiyar magana, mahaifartace bata da ƙwarin riƙe ciki.....”         Miƙewa Jawaad yayi yana wata ƴar dariya da tafa hannayensa, ya tako zuwa gaban kujerar da Dr Tayyeb yake, a saman tebir ɗin ya zauna suna fuskantar juna, ya ajiye ƴar ƙaramar bindigarsa daya ciro a aljihu ya ajiye gefrnsa.       Wani mugun yawu Dr Tayeeb ya haɗiya idonsa akan bindigar, Jawaad ya katsesa da faɗin, “Wannan itace tambayar ƙarshe dazan maka, ya rage naka ka bani amsa dai-dai kokuma ka sakemin ƙarya. Miyasa kabi ra'ayinta ka zubarmin da ciki?”.       Doctor dake lafe jikin kujera tamkar magen datai karo da kura a daji ya haɗiye wani yawu mai kauri idonsa akan bindigar Jawaad daya ɗauka yake jujjuyata a hannu, tabbas yasan Jawaad zai iya aikata komai, shiko da baida laifi gara ya fidda kansa a cikin wannan bala'in tunkan kwaɓarsa tai ruwa, saboda kuɗin Aamilah bazai halaka kansa ba a wofi.       “Yallaɓai kayi haƙuri ka ajiye bindugar na rantse duk abinda kake buƙata zan sanar maka shi”.         Cikin wani salo da murmushin mugunta Jawaad yasa ɗanyatsa ya tura eyeglasess ɗinsa sosai yana faɗin, “Good boy, ashe kasan dokar”.       “Sosaima kuwa yallaɓai” Dr Tayyeb ya faɗa yana jinjina kai tamkar ƙadangaren jangwala gwaja yaga shinkafar manja🤪.       Ajiye bindigar Jawaad yay yana ranƙwafowa kaɗan hannayensa harɗe a cinyarsa da yake zaune da ita a tebir ɗin, ɗayar kuwa tana ƙasane a jiye, “Ina saurarenka”.        Nanma kai Doctor ya jinjina masa, “Maganar gaskiya yallaɓai lafiyar mahaifarta ƙalau, zubar da cikin akai, sai dai wlhy kaji na rantse maka bani nai mata aikinba, andai kiranine kawai na ceto rayuwarta”.        Sosai zuciyar Jawaad ke tsitstsinkewa, ya zare glasess din idonsa yana zuba ma Doctor wani hargitsatstsen kalo, “Uhmyim, wato zubarwa akai? Amma miyasa ka zaɓi faɗar abinda ba haka yakeba? Haka aikinka ya koya maka?”.        “Wlhy A'a yallaɓai, kuskurene ka gafarceni”.      Sauka Jawaad yay daga saman tebir ɗin yana taku a hankali yana faɗin, “Maybe na iya yin hakan idan na tabbatar babu saka hannunka a ciki”.          “Wlhy da gaske nake babu hannuna, bankuma san komai a kaiba”.          Komawa Jawaad yay ainahin kujerar daya fara zama ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana aza hannunsa ɗaya a tebir ɗin yace, “Doctor Tayyeb ka sanni na sanka tun lokacin daka fara aiki gidan Alhaji Ali, karka kuskura a wannan karon ka tsinci kanka a harƙallata, dan wlhy bazan maka ragiba, na kamaka da ƙaryar farko ta faɗar sakamakon abinda ba haka yakeba, kasa a ranka ba'a min ƙarya a shani a banza, yanzu zan tafi, a koda yaushe kuma zan iya nemanka a office ɗina, zaɓin kane kazo akan lokaci koka ɓatamin lokacin”.         “Insha ALLAH zanzo yallaɓai, kuma bazan sake kuskuren maka ƙaryaba akan duk abinda zaka tuhumeni a kansa”.       “Good” Jawaad ya faɗa yana miƙewa da ƙoƙarin tura bindigarsa ta baya, bai kuma tankama Doctor Tayyeb ba ya fice a office ɗin.          Bai cema su Gimba komaiba yay gaba suka sake rufa masa baya har inda suka ajiye motocinsu, buɗe masa akai yanzunma ya shiga ya zauna sannan suma duk suka shiga suka bar asibitin a sukwane.        Haɗiyar zuciya kawai Jawaad keta faman yi, shi kaɗai yasan mi yakeji da yanda ƙirjinsa ke zaɓalɓalar azabar kunar zuciya, shi Shahudah ta zubarma ciki dukda gargaɗin ta da yay akan karta aikata hakan?.          Doctor dai tunda Jawaad ya fice saiya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana share gumi, mikewa yay yaɗan leƙa kansa ta ƙofar da Jawaad bai rufe da ƙyauba, sai da ya hango sun fice sannan ya sauke numfashi yana tura ƙofar ya murza key ya koma jikinta ya lafe yana rumtse ido hannunsa dafe da ƙirjinsa.       A ransa yana ayyana tsaurin ido da tsantsar kwarjinin Jawaad, a fili ya furta, “Tabɗi, waɗannan ai sune mazajen gaskiya”. 😂🤣Su Doctor Tayyeb ashe mata mazane bamu da labari😝. ★★★★★         Ko a Office ma da suka isa kowa yau a miskile yaga Jawaad, duk da babu wani ɓacin rai a fuskarsa ko nuna damuwa.      Ya shige Office abinsa, kusan mintuna biyar ya aiko ai masa kiran Aliyu.       Babu ɓata lokaci Aliyu ya amsa kiransa da gaggawa, bayan sun gaisa cikin musabaha Jawaad ya miƙama Aliyu ledar daya ɗakko sirinjin jiya a gidansu Shahudah yana faɗin, “Inason nasan hoton yatsun wanene a jikin Syringe ɗinnan Aliyu yanzun nan”.        Cikin girmamawa Aliyu ya amsa yana faɗin, “Okey Boss, ka bani nanda mintuna Arba'in koma ƙasa da haka”.         Hannu kawai Jawaad ya ɗaga masa ba tare da yace komaiba, Aliyu ya fice shikuma ya shiga wata sabgar daban.             Kusan awa ɗaya sai ga Aliyu ya dawo, sai da ya nema afuwar Jawaad na daɗewar da yayi sannan ya zauna yana miƙa masa ledan da syringe ɗin yake ciki da sakamakon binciken, amsa Jawaad ɗin yayi da faɗin, “Thanks my Dude”.         “Babu godiya a tsakaninmu, amma akan case ɗin miye?”.      Murmushi Jawaad yay masa yana cigaba da duba takardun gabansa, yace, “Share kawai Aliy gadanga ƙusar yaƙi, su Hafiz fa?”.         Kaɗa kai kawai Aliyun yayi, bai matsa akan sai yaji ba, yace, “Hafeez da Rose inaga suna kan aikin nan, Jabeer kuma yana Office”.          “Okey, nima kam inaga zuwa yamma zan ziyarci anguwar can, dan yakamata muɗan fara motsi akan case ɗin nan, tunda ALLAH yasa munga ƙarshen wannan, saura shiga Court kawai ya rage”.           “Okey to ALLAH ya bamu nasara shima, amma wannan aikin na lura kamar zai zama na basaja ne shi?”.         Idanu Jawaad ya ɗago yana kallon Aliyu sosai, ya lashi leɓensa na ƙasa daya bushe sannan ya turasa cikin baki sai kuma ya biddosa yana janye idanunsa daga kan Aliyun murmushi kwance a fuskarsa yana faɗin, “Wani zai zama mai sana'ar kifi kenan”.       Dariya Aliyu yayi, “Kai haba boss? Wannan lokacin kuma tanan ka ɓillo?”.         Cikin taɓe baki Jawaad yace, “Mutanen duniyarne sai ka musu duniyanci kuke zama ku mori duniyar tare”.         “Hakane kam boss, kenan yau akwai zama?”.        “Eto bance a'a ba, amma da kamar wuya, dan akwai wani rami na cikin gida da nima nakeson cikewa, maybe zaku bani yau kawai na ƙarasa”.         “Ai ya zama dole Boss, ALLAH ya bada sa'ar cikosa da alkairi to”.        “Amin” kawai Jay ya faɗa yana haɗiye ɗacin daya riƙe masa maƙoshi.       Daga nan Aliyu yay masa sallama ya fita.       Kusan mintuna ashirin da fitarsa Jawaad ya ɗau ƙaramar wayarsa yay kiran Doctor Tayyeb, yana ɗagawa yace yazo ya samesa a Office.          Bai bashi damar faɗar komaiba ya yanke wayar.         Kamar yanda Jawaad yay Warning ɗinsa bai ɓata lokaciba ya iso kuwa, Gimba ne ya kawosa har Office ɗin, Jawaad daketa faman aiki da Computer baiko motsaba balle ya kallesu har Doctor Tayyeb ya zauna.         Sai da kusan mintuna biyu suka shuɗene ya fara magana ba tare da yabar aikin da yakeyiba.        “Kasan wane aiki zakai min?”.        “A'a yallaɓai sai ka faɗa”.        Jawaad yaɗan kallesa sai kuma ya maida kansa ga aikinsa yana cigaba da faɗin, “Yatsun hannun duk jama'ar gidan Alhaji Ali nake buƙata amma banda Qaseem da shi Alhaji Alin, ya rage naka kabi ta hanyar da ya dace ka aikata, kokuma kayi rawar kai ni kuma na ragargaza maka kwanya babu ruwana”.          Cikin haɗiye yawu Doctor yace, “Wannan mai sauƙine mai gida”.        “Na fika sanin sauƙinsa, dan danaso zanje kai tsayene na nema basai nabi ta hanyar kowaba, inada nawa dalilin sakoka cikin aikinne kawai”.       Ba ƙaramin faɗuwar gaba Doctor yajiba, ya hadiye yawu daƙyar yana fiddo idanu kamar kwarton da mai gida ya kama da farar magriba😑.         Jawaad yace,  “Karka tsaya kallona, lokacinka ya fara daga yanzun”.       Mikewa Doctor Tayyeb yayi yay masa sallama ya fice........ _______________________________                Idan nace muku ban fara ganin canji a rayuwata ba nayi ƙarya, dan kuwa ilimi tubaline mai ɗaga darajar kowanne mai fafutukar nemansa, idan kaga saɓanin cikagabanka a cikinsa to lallai bakabi hanyar data daceba wajen samunsa.          Kasancewar su Ummie manyan yarane wayayyu, wayewa kuma mai tsafta tuni sun fara dorani bisa layi, musamman salo-salo na tsaftace jiki dana tsara rayuwa inhar kanada ikon ribantar gobenka.       Tabbas ni baƙace, amma na yarda jin daɗi kan saka koda kai bakine baƙin ya kasance na musamman mai ɗaukar hankalin idanun mai kallonka.        A yanayin da nake ciki da sauyin iska dana fara samu tun a gidan Dad sai suka sake tasiri a yanzu a gareni, gashi dai makaranta muke, makarantarma Boarding skull, sai dai ta kasance ta musamman, dan banbancinta da rayuwar gidanma ƙalilance, anan kawai dai baka ganin iyayenka ne bakuma a ganin gari da jama'a, tunda a killace muke.       A hankali aka fara sanina saboda su Ummie ƴan babu sauƙine, guruf ɗinsu sanannen guruf ne ko a cikin ƴan mate ɗinsu, musamman saboda ƙokarinsu da kwazo da ALLAH ya basu, kowanne zakaga gwarzone a wani subject, hakan yasa har malam ma ji suke dasu ainun.      To sai shigata cikinsu nima ta kuma ƙarfafa fahimtata da tun a baya rashin gatan samun gurbin karatu mai ƙyau ya raunanashi.      Ba karatu kaɗai ba, dai-dai da yanda ake tafiya, saka sutura zuwa magana babu abinda su Ummie basa koyamin, ni wani lokacin ma har mamaki sukeba su a ina suka koyo?.       Sam bana nuna wani girmankai a garesu balle turjiya, komai sukace nayi inhar nasan bai saɓa shari'a ba ko taɓa tarbiyyar al'adata nakan amshesa hannu biyu na riƙe na kuma bada himma wajen fahimtarsa.         A hankali komaina ya cigaba da canjawa ga jarabawa nata gabatomu wadda zuwa yanzu ko fargaba banaji akan zuwanta, dan inada yakinin insha ALLAHU nima za'a goga dani a filin dagar.        Turanci kam yanda yake zama min akan harshe zakasha matuƙar mamaki da tunanin tun inada ƙuruciya dashi na tashi a baki, tsoron mutane da kuka sanni dashi zuwa yanzunkam ya fara guduwa, dan jina nake a gaban kowa zan iya fita a dama dani akan abinda ya kamata.       Sai dai kunya dake ƙara martaba kimar mace a koda yaushe tana nan daram a jikina da ayyukana bata fitaba, hatta wani abun idan su Ummie sukai nakanji nauyinsa harma na kasa saka baki ko kaina a ciki, sukan tasani da dariya sosai harsu koma tsokanata.        Bazance har yanzu Nazifa ta saki jiki daniba, amma dai bata ɗaukata da zafi kamar da.        Akwai malami da Dadyn Ummie ya ajiye mana yake zuwa duk yamma ta fannin ilimin addini, hakanne ya sakani fahimtar abinda ya zaunar da tarbiyyar su Ummie akan tsari ba tare da wayewarsu ta zarce ƙa'idar da addini ya shinfiɗaba.       Lallai ako ina inhar kanason ribantar ilimi toka ɗauki duka biyu ka riƙe, inhar da ililin addini to babu yanda za'ai ilimin boko ya dilmiyaka koyi da nasara kamar yanda naga su Aunty Shahudah sun zarma.       Wayewar mai riƙe da ilimin addini dana zamani a duk inda take dolene ta burgeka, dan zaka ganta cike da tsafta da nutsuwa babu shirme ko rawar kai a ciki.         ALLAH ka bamu ikon cin ribar ilimi a duniya da kuma lahira ba mucinye rabonmu anan duniya ba.        Zuwa yanzun kam inajin kewar gida, a duk lokacin kuma da sabbin ƙawayena suke bada labarin ahalinsu nima nakan bada labarin rayuwatane da iyayena ta gidan haya.       Sukanyi mamaki sosai, dansu sam basu taɓa tunanin ana samun makamanciyar wannan rayuwarba.      Nakanyi murmushi dan bana ganin laifinsu sam, a yanda rayuwa da duniya suka rainesu bazama su kawoma kansu tunanin akwai masu bukatar koda kwatankwacin irin tasu rayuwarba.         A koda yaushe sukan shiga damuwa da tsantsar tausayina harma da waɗanda suke da irin tawa rayuwar koma wadda ta fita, har zumuɗi suke na basu labari, sannan suna kuma ɗaukama kansu alƙawarin zamu zama masu taimakon wasunmu muma anan gaba da izinin ALLAH.       Gaskiya rayuwarsu na birgeni, dukda kasancewarsu ƴan gata iyayensu sunyi ƙoƙarin tsayawa tarbiyyarsu, ta waɗanda keda rauni a cikinsu kuma sun hadu sun daidaitata akan ƙyaƙyƙyawan bigire da shima zai amfana tun ba yanzuba, dan sun tabbatarmin tun daga js1 suke tare a makarantar, hakannema ya dasa shaƙuwa mai yawa a tsakaninsu harma da ƙulluwar zumin iyayensu, ƴar uwar Ummie data rasu na maye gurbin data bari sam basa iya mantata, kullum cikin bani labarinta da ƙyawawan dabi'unta suke, hakanne yasani fahimtarma dukta fisu zurfin ilimin addini da ƙulafucin kulawa dashi.       Wannan itace matakin na sara ta farko da ni BILKEESU ADAM MAKAHO na fara tsinta a duniyar da a baya nake kallon bata bukatar bani filin dazan zuƙi iskar cikinta a baya.............🤩✍🏻 Page 26 ............Shahudah taɗan samu sauƙi, sai dai fargabar Jawaad ta hanata sukuni sam, gashi a yau ko ƙeyarsa basu ganiba a gidan, tanason kiransa a waya tanajin tsoro.        Kusan ƙarfe uku na rana sai ga Doctor Tayyeb yazo gidan, lokacin duk suna falo, Qaseem ne kawai babu a gidan dan yana Office wajen aiki.      Shahudah na kwance ne a kujera doguwa kanta a kan cinyar Mummy, karenta na kwance daga ƙasa kusa da ita, sai Aamilah da Jack da Salma waɗanda shigowarsu gidan kenan.      Sai da Dr Tayyeb ya bama su Salman hannu suka gaisa sannan ya zauna yana gaida Mummy idonsa akan Shahudah da keta ɓata rai, dan tasan allura yazo yay mata ita kuma batason ta.       “My patient yaya jiki?” ‘Ya faɗa yana mata murmushin yaƙe’.       “Fine” kawai tace masa ta ɗauke kanta.        Bai damu ba yace, “Alhmdllh, yanzu dai babu ciwon marar ko?”.        Kanta kawai ta ɗaga masa.           Shima bai sake cewa komaiba ya shiga haɗa allurar da zai mata, ƙasan zuciyarsa yana tunanin ta yanda zai ɓilloma aikin Jawaad.        Da ƙyar Shahudah ta tsaya akai mata wannan allura, saboda tsabar taɓara harda kukanta.       Sai da ta koma dai-dai ne ya gyara zama yana mata bayanin yanda zata kula da kanta,  ya fiddo wasu ƴan kwalaben magani, ɗaya ya miƙama Salman dake kusa dashi yana faɗin, “Salman ko kasan wannan maganin?”.      Karɓa Salman yayi yana dubawa, Dr Tayyeb ya sake ɗibar biyu ya mikama Aamilah da Jack suma, “Kuma ku duba kuga ko kun sanshi”.      Suma basu musaba suka amsa, itama Mummy da Shahudah duk ya miƙa musu, da farko dai Shahudah kam taƙi amsa, a cewarta karya isheta.      Mi kuma ta tuna oho mata, sai ta miƙo hannu ta amsa.         Salman da Aamilah suka fara maido masa da kwalaben suna faɗin sudai bama su gane kan maganinba, kwalayen kwalaben ya miƙa musu duk suka saka da kansu sannan ya amsa ya maida ajikka.      Jack ya kalli Dr Tayyeb cikin nuna shiɗin ƙwararrene yace, “Wannan ai maganin hana ɗaukar cikine, macen da bata haihuwama akan bata ta gwada shi kamar na wasu wattani kafin ta dakata”.       Murmushi Dr Tayyeb yayi yana jin jina kai alamar gamsuwa da bayanin jack, ya miƙa masa kwalin shima ya saka yana faɗin, “A lallai kasan magani kam sosai”.      Jack yaji daɗin yabon da ake masa ya miƙama Doctor bayan ya saka a kwalin yana sake bajewa a kujera, suma su Shahudah duk basu yay suka saka ita da Mummy ya amshe abunsa ya maida duka a jaka, ba tare daya yi musu wani ƙarin bayani ba yay musu sallama ya tafi.         Kaf ɗinsu babu wanda ya kawo wani abu a ransa game da maganin da Doctor Tayyeb ya nuna musu, garama Mummy taji haushinsa sosai, dan ita gani take kawai Doctor ɗin nasu yayi hakanne danya nunama Shahudah hanyar ɗaukar mataki a gaba, itako yanda suka tsara yanzu nanda kwanaki kaɗan Shahudah zata koma ɗakinta ko ALLAH zaisa a dace wani cikin ya shiga.      Dan jiya dai ta daure taje gida tama Mama Atika da ƴan uwanta bayani akan matsalar Shahudah ɗin.        Dukansu sun nuna rashin jin daɗinsu da tausayin Shahudah, sai dai kuma hankalinsu ya tashi, dan a ganinsu inhar Shahudah nada wannan matsalar to kenan yaushene ciki zai fara zaman da zasu sami cikar burinsu?.       Uncle Uwaisu daya kasa haƙuri sai cewa yay, “Anya kuwa kuna ganin bazamu ɗauki matakiba?  Indai hakanefa zaman Shahudah da Jawaad bazai mana wani amfaniba kenan? Ko dai mu sake dubawa cikin yaran nan saimu aura masa wata?”.      Tsitt falon yayi kowa ya kasa magana, sai dai fuskar Mummy ta nuna alamun ɓacin rai.      Mama Atika ce ta katse shirun nasu dayin gyaran murya, cikin muryarta ta tsufa tace, “Maganar Uwaisu nakan hanya, hakama shawararsa mai ƙyau ce, sai dai akwai ruɗani a cikin hakan musamman akan ku kanku da zumincin ku”.        “Gaskiyane maganarki mama, gashi kuma bamu da damar sako wani cikin ƴan uwanmu, duk da na daɗe daji a raina kowa nada nasa burin wlhy, suna ɓoyewane kawai dan ace sunason yaron sosai,  musamman ma Yaya Nasiru da kuke ganinsa nan ko? Humm”.       Nanma duk shiru suka sake yi, sai Mummy ce a hasale tace, “Amma gaskiya idan akai haka ba aima Shahudah adalciba, ai kamata yay mu nema magani ko mafitar da cikin zaike zama ɗin bawai muyi tunanin mata kishiya ba, sannan ku kunama zaton shi yaron kansa zai yarda da wannan kwamacalar? Shahudah ma da yake so da yaya muka ƙulla auren nasu balle kuma yanzu? Mudai sake tunani amma ba wannan ba”.        Kowa ya gamsu da bayaninta, duk da dai ta nuna akwai nuna taya kishin ɗiyarta a ciki.        daga ƙarshe dai sun yanke shawarar nemawa Shahudah magani, sannan su maidota ɗakinta da wuri ko ALLAH zaisa a dace ciki ya shiga da wuri🤫🥴. ★★★★★      Dr Tayyeb da ya samu abinda yazo nema yana fita ya sauke ajiyar zuciya, mota ya shiga bai zauna wasaba ya koma Office ɗin Jawaad.          Lokacin Jay yana tare da su Jabeer akan tsara aikinsu da zasu dasama ɗanba.       Bayan saƙon zuwan Dr Tayyeb yazo masa ta hanyar Gimba, bai fitoba, sai gimban ya bama damar amsar saƙon a wajen Doctor.          Gimba na tsaye Dr Tayyeb na bashi kwalayen kwalaben da duk yasamo fingers print ɗinsu Shahudah sai ga Qaseem ya fito daga Office, da alama ma dai ya tashi aiki, aiko sai idonsa karaf akan su Gimba.       Ɗunbin mamaki ne ya kamashi ganin Family Doctor ɗinsu anan, yay saurin ciro wayarsa daga aljihu ya ɗauki Dr Tayyeb da Gimba hoto.            _____________________          Lokacin da Qaseem ya shigo gidan duk su Shahudah sun tashi, Aamilah ce kawai a falon itama tana cin abincine a dani.            Yanda Qaseem ɗin ya shigone ya saka Aamilah kallonsa ita da Amina dake gyaran falon.         Cikin tsawa-tsawa yace ma Amina, “K tattaro min kowa na gidannan”.         Da “To” Amina ta amsa cikin girmamawa.     Tasowa Aamilah tai daga falon tana tambayarsa ko lafiya?.      Bai bata amsaba sai ƙokarin danna wayarsa yake domin son nemo hoton su Dr Tayyeb daya ɗauka.        A haka duk suka fito suka samesu har Shahudah dake fama da kanta.         Kowa yazo sai ya masa tambayar lafiya?.      Ganin duk sun hallara ya bisu da kallo yana faɗin, “Jawaad yazo gidannan yau?”.       A tare suka girgiza masa kai, kowanne da mamakin tambayar akan fuskarsa.         Qaseem ya kuma cewa, “Doctor Tayyeb fa?”.          Salman yace, “Yazo har yayma Shahudah allura”.          Dariya sosai Qaseem ya sanya yana tafa hannaye, wadda tasakasu duk zuba masa idanu, Mummy ta katsesa, “Qaseem lafiyarka kuwa? Minene abin dariya to anan?”.         “Mummy bazaki ganeba, ni dama nasan Jawaad bazai taɓa bariba, da Tayyeb yazo gidannan bayan allura mi yayi?”.         Aamilah taja gajeran tsaki, “Iya allurar yayi mana, sai wani shirmensa na nuna mana wai ko maganin hana ɗaukar ciki, ni jakinma harya wuce ban fahimci manufarsa ba....”         Saurin katse Qaseem yayi, “K shashasha, aiku ya maida jakkan, to lallai akwai manufa, dan inada tabbacin aiki Jawaad ya sakashi, dan naga Dr Tayyeb a Office ɗinmu yanzunan yana bama gimba drivern Jawaad wasu kwalaye”.        Dukansu idanu suka zaro waje har Jack, dan da turanci duk suke magana saboda Jack ɗin ya fahimta.       Mummy tace, “Ni ban ganeba, kai mika fahimta to?”.      Cikin taɓe baki da ɗage kafaɗu Qaseem yace, “Cikinsa yake bin ba'asi mana, ki binciki ƴarki Mummy dan akwai abinda take ɓoye miki, kuma duk wanda yasan da hannunsa a ciki wlhy ya kuka da kansa dan Jawaad ya fiku iya birkicewa, aikin banza kawai kun jama mutane asara, ku duba nan ku gani” ya ƙare maganar yana mika musu wayarsa a hasale.         Dukansu jikinsu tsuma yake, musamman Aamilah da jack da Shahudah, ita kanta Mummy zuface ke karyo mata a kowacce ƙofar gashin jikinta, tsabar ɗumi da ƙwalwar kanta ta ɗauka tama rasa abin faɗa.          Dukansu babu wanda baiga abinda Tayyeb ke mikama Gimba ba, kwalaben daya basune fa.          Mummy da jikinta ke mazari ta juya tana kallon Shahudah dake a birkice, kasa ce mata komai tayi.      Ba Mummy da Shahudah ba kowama a birkicen yake, hatta da Salman da baisan komaiba yay wuƙi-wuƙi da idanu.          Daga nan kowa kai kawo ya shigayi a falon.       Shahudah, Aamilah, Jack, kowa yana tunanine akan a ina matsalar take?.         Yaya akai Dr Tayyeb ya je ga Jawaad? Aamilah da tasan yanda sukai da Dr Tayyeb zuciyarta sai tsitstsinkewa take, zargi biyune a ranta, kodai Doctor ya samu Jawaad da gaskiyar batu, kokuma Zaitun ce ta faɗama Jawaad, to amma ai Zaitun batasan wanene zai amfani da allurarba, ita kawai sun nema sanin likitane ta hanyarta, tayaya zata samu Jay da maganar abinda bata sani ba.            “Kenan a ina matsalar ta fito?”.     Aamilah ta faɗa a fili ba tare da ta sani ba.        Duk kallonta sukayi kuwa, Mummy tace, “Aamilah mi kike faɗane?”.         Cikin in ina Aamilah tace, “M... Mummy bance komaiba”.       Qaseem yace, “Humm yarinya zaki magantu ne, ni dama tun randa abun nan ya faru wlhy na fahimci baki da gaskiya”.          Tsaki Aamilah ta ja mai mugun ƙarfi tana harar Qaseem, tace, “To masheranci, ni kaɗai duk faɗin gidannan ka sakama idanu?, sokake ka ƙalamin sheri? Ai bani cikin ke a jikinaba balle kace....”           A harziƙe Qaseem yay kan Aamilah, ta zuba da gudu ta shige ɗaki ta kulle kanta.        Cikin matuƙar fushi Qaseem yace, “Mummy kina gani ko? Ni wannan ƴar iskar yarinyar take faɗama duk abinda yazo bakinta? Ƙanwata ta huɗu?”.          Cikin damuwa Mummy tace, “Qaseem dan ALLAH ku barni naji da abinda ya dameni, Shahudah inhar zubar da cikin nan kikai wlhy kin cutar damu kuwa”.        Sake ɓaci ran Qaseem yayi ganin Mummy ta nuna halin ko in kula da abinda Aamilah tai masa, Shahudah kam bata iya bama Mummy amsaba saboda jirin dake ɗibarta, ganinta kawai sukai zube a ƙasa wanwars. ______★______★_______★______            Bayan Jay ya koma Office ne Gimba ya je ya kai masa abinda Dr Tayyeb ya kawo.             Jawaad ya amsa yana buɗe ledar da aka zubo su a ciki, ɗaya bayan ɗaya ya fiddosu ya duba, yay guntun murmishi saboda kowanne da alamar da Dr Tayyeb yayma kwalin yanda za'a gane na kowa, maidasu yay duka a ledan ya sake miƙama gimba.        “Ka kaima Aliyu su, yanzu nake buƙatar results ɗinsu”.       “Okey boss” gimba ya faɗa cikin girmamawa yana amsar ledar..           Ba a wani ɗauki lokaci mai tsawo ba Aliyu ya shigo Office ɗin, lokacin Jawaad na tare da Rose suna magana akan wani aiki daya sakata.      Zama Aliyu yayi a kujerar dake kallon ta Rose ɗin ya miƙama Jay takardu na results ɗin, ya kuma ajiye kwalaben dake a ledar.            “Boss Result biyu fa yayi kama da na farko, dan a jikin syringe ɗin jiya yatsun hannun mutum biyu muka samu, amma ɗaya yafi fitane da ƙyau, duk da dai haka mun samu yanda mukeso.  Ka duba da Result ɗin jiya da waɗannan na saman na mutane biyune dake jikin syringe ɗin kamar yanda na faɗa maka tun farko”.         Kai Jay ya shiga jinjinawa yana ɗan lila kansa a kujera, tuni idanunsa sun canja launi sai wani munafukin murmushi dake shimfiɗe bisa fuskarsa wanda Aliyu da Rose duk suka kasa fahimta.          Cikin sauke numfashi ya ajiye takardun yana maida kallonsa ga Aliyu.        “Aliyu kiramin Jabeer”.      “Okey Boss” Aliyu ya amsa yana ƙoƙarin kiran Jabeer a waya, koda Jabeer ya ɗaga daga can  sai Aliyu ya sanar masa saƙon Jawaad.       Babu jimawa kam saiga Jabeer ɗin.        Jawaad dake rubutu a takarda ya ɗago ido ya kalli Jabeer, kafin ya miƙa masa takardar daya gama rubutun.        “Jabeer wannan Number ɗin nakeson nasan daga shekaran jiya zuwa yau da mutum nawa akai waya, sannan mutane nawa suka kira layin?”.         Amsa Jabeer yayi yana kaɗa kai, ya nufi wasu Computers guda uku dake can gefe a cikin Office ɗin Jawaad.        Hakan ne ya saka Aliyu miƙewa yabi Jabeer dan ya taimaka masa.          Rose ma mikewar tai ta koma wajen su Jabeer ɗin, shiko Jawaad ya cigaba da aikin da yake a Computer gabansa zuciyarsa na masa wani zogi da ƙuna, domin kuwa result ɗin sayin hannun Jack da Shahudah aka samu a jikin syringe ɗin, na Jack shine ya danne na Shahudah alamar shine ƙarshen riƙe sirinjin.          Kusan mintuna goma sha biyar Jabeer ya juyo yana kallon Jawaad daya maida hankalinsa ga aikinsa tamkar babu abinda ke damunsa.        “Boss ga waɗanda sukai kiran da waɗanda aka kira, sai text messages guda uku da akayi, kuma duk a jiyane kamar ma kai akaimawa”.       Miƙewa Jawaad yay zuwa inda su Jabeer suke, Aliyu yay saurin tashi ya bashi kujerar da yake zauna, jawota baya kaɗan Jay yay ya zauna, da kansa duk yabi ya duba, tabbas saƙo biyu shi Shahudah ta turomawa, sai dai babuma wanda ya duba a ciki dukda yaga shigowarsu tun ɗazun da safe, komawa yay duba Numbers uku da Shahudah ta kira randa abun ya faru, ya ƙurama Number ƙarshe ido yana nazarinta.       Kallon Rose dake tsaye yay yay mata nuni data ɗakko masa wayarsa dake tebir ba tare da yay magana ba.           Cikin hanzari taje ta ɗakko ta kawo masa.         Number Aamilah da tunda yake bai taɓa kiraba sai dai ita ta kirashi ya lalubo.         Akan laɓɓansa ya furata, “Aamilah” a hankali, Murmushi ya saki yana cizar leɓensa na ƙasa, “Jabeer bincikamin itama wannan Number ” yay maganar yana nuna masa Number Aamilah.        itama duƙufa Jabeer yay a kanta, ana cikin hakane Hafiz ya shigo hannunsa ɗauke da takardu, ganin sun haɗa kai waje guda ya nufisu yana faɗin, “Wane shagalin ake anan kuma?”.          Duk kallonsa sukayi,  banda Jawaad da Jabeer da hankulansu ke bisa Computer ɗin.         Jabeer yace, “Wannan sune ta kira a jiya, waɗan nan suka kirata, ga kuma na yau”.         Shiru Jawaad yay yana kallon Numbers ɗin, ya sauke numfashi yana girgiza kai, “Ina na shekaran jiya?”.       “Gasu nan” cewar Jabeer yanama Jawaad nuni dasu bayan ya kuma zooming ɗinsu yanda Jay zai gani sosai.          Ahankali ya ringa nazarinsu ɗaya bayan ɗaya, “Jabeer inason nasan kowacce number daga ina akai kira da ita, wanda ta kura kuma a ina yake”.          “Amma zamu ɗauki lokaci Boss, magriba kuma ta gabato........”        Kafin Jawaad yay magana Rose tace, “Bara muyi tanan kawai zaifi mana sauri”.      Duk juyawa sukai suna kallonta har Jay ɗin da yake lafe jikin kujera yana shafa ƙasumbar data ɗan taru mai a fuska kaɗan.       Sun santa mayyace itama a irin waɗannan binciken, shiyyasa suke son zamanta a tafiyarsu sosai.           Tana danne-danne tana kai kawo, hakan yasa suketa binta da kallo, shima Jabeer bai fasaba dubawar yake daga ɓangarensa.      Cikin min tunan da basu gaza biyarba, Rose tace, “Number mai ƙarshe 3434 mai ita tana a anguwar Sunusi Abdullahi stress, layi na biyu gida mai lamab 107, an kiratane da ƙarfe 10:34am, zamu iya kiran kamfanin layin idan kana bukatar jin abinda aka tattauna akanta Boss”.         Cikin kafeta da idanu  yace, “Kin tabbatar?”.       “Yes Sir, gashima ka duba da kanka” tai maganar tana miƙa masa.      Amsa yay shima yana dubawa, duk abinda ta faɗa dai-dai ya gansa, wani luuuu yay da idanunsa yana busar da huci mai azabar zafi. Kafin ya samu cewa wani abu Jabeer ya katseshi da faɗin,        “Boss ita kuma wannan daga Asibitin *NASARARMU* yanzu haka ma mai Number yana cikin asibitin, sannan Number da Rose take magana itama ta kirashi mintuna biyar kafin ita wannan ta kirasan, shima kuma ya kira waccan ɗin bayan awa ɗaya da kiran wannan.      Da ƙarfi Jawaad ya bugi tebirɗin da Computers ɗin suke kai, sai faman fidda numfashi yake da sauri-sauri.       Cikin kakkausar murya yace, “Muna idar da salla ku tababbar likitannan ya gurfanu a gabana, sannan mai wannan number itama kuje har gidan ku kamomin ita!!!”.      Ya ƙare maganar a matuƙar tsawace.      Su duka a tsorace syke kallonsa, gashi dama basu san komai game da aikinba, amma sun kula ya ɗaukesa da zafi tun jiya.       A cikin girmamawa duk suka amsa masa.           Uffan bai sake faɗaba, sai da ya ɗauki rigar suit ɗinsa yana nufar ƙofa yace, “Duk ku kaimin su Zangina road ina jiranku a can”.        Bai jira amsarsuba yay ficewarsa...............🤫✍🏻 Page 27 ............Koda motar Jawaad da ta Security's nashi suka iso ƙofar gidan nasu Shahudah basu shigaba, cayay suyi fakin a ƙofar gida.       Zamansa yay a mota bai fitaba, hakan yasa securitys nashi fitowa su zagaye motar da yake a ciki.          Yanata danne-dannensa a waya kai kace bashi bane ya fito Office ɗazun a fusace, sai dai shi yanajin zafinne a cikin zuciyarsa, yayinda fuskarsa ta shanye komai tamkar babu komai.             Har aka kira sallar isha'i suna wajen, da kansa ya buɗe ya fito daga motar dan son gabatar da salla.       Masallacin anguwar dake jikin gidan maƙwaftan su Shahudah suka shiga, tare dasu akai jam'i, suka bar waɗanda basayi a wajen.          Bayan fitowarsu daga salla ne sai ga su Hafiz sun iso tare da Zaitun da Dr Jeo, sake shiga mamaki Zaitun tayi ganin ɗan uwanta Jawaad da take mutuwar ƙauna.       Shiko kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa tamkar bai santaba ma.          Shi da rose da Hafiz, kawai suka shiga gidan, aka bar Aliyu da Jabeer a waje tare da securitys da su Zaitun da aka zubo a mota.           Amina data fito tana shirin wucewa gida tai azamar matsawa ta basu hanya jikinta na rawa, ko kallonta basu yiba kuwa, sai knocking ƙofar falon da Rose ta shigayi.        Amina da ta samu waje ta laƙe inda zata kalli komai, tace, “Ai dama tunda naji dambarwar da akeyi ɗazun a gidan nasan yau akwai kura”, dan haka tai azamar komawa ta ƙofar  kicin ta baya, dan tayi alƙawarin sai taga komai kodan ta bama Bilkisu labari idan ta dawo.          Tunda labarin zuwan Dr Tayyeb wajen Jawaad yazoma su Shahudah kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye, ga Dad baya nan yayi tafiya jiya da yamma.         Aamilah tafi kowa shiga ruɗani dan dama can ita a kwai tsoron masifa, Shahudah kam dama tanada taurin kai tun fil azal, dukda tana a tsorace da sakamakon abinda zai biyo baya wani gefen zuciyarta na nuna mata Jawaad zaiyi buyaginsa naɗan lokacine ya sakko.         Wannan gurgun tunanin natane yasa bayan ta farfaɗo daga sumar da tayi saita ragema kanta fargabar.      Sunata ƙulla mafitar da zasu kare kansu ne a wajen Jay tun bayan farfadowar Shahudah, a wannan yanayin ne motar Jawaad data security's ɗinsa suka iso gidan.         Takun takalmansu Jawaad ya sakasu Mummy zubama ƙofar falon ido, dama Shahudah da Aamilah da Mummy ne kawai a falon, duk da kiran sallar magriba da akayi Mummy ce kawai taje tayi, maimakon taima Aamilah magana tunda ita Shahudah batayi saboda jinin ɓari sai batai ba, itako Aamilah dayake bata da man kai batai ko niyyar tashinba balle tunanin yi, idanma zaka bibiya ƙila yau daga sallar asubahi bata sake wata sallaba.          Kamar yanda Qaseem ya ɗorasu a kan keken ɓera koda Jawaad yazo kar wanda ya nuna razana hakan duk suka shirya, sai dai da yake a yanzu basuyi tunanin shi bane sai Aamilah ta miƙe domin duba mai knocking ɗin ƙofar.       Sun san dai idan Jawaad ne kansa tsaye zai shigo ciki.      Cike da barbaɗa ta buɗe ƙofar tana wani yatsine-yashine, taima Rose kallon sama da ƙasa tana faɗin, “Madam ke kuma fa?”.         Rose ta nunama Aamilah ID card ɗinta tana faɗa mata suna “Sunana Rose Ayo, ƴar sandar farin kaya”.         Karaf a kunnen Mummy da Shahudah, dan haka duk suka miƙe suma suna nufo ƙofar.       Aamilah data ɗansha jinin jikinta tace, “To lafiya?”.          “Ai mu dakin gammu kinga lafiya hajiya”. ‘cewar Rose tana wani annaminin murmushi.              Ƙoƙarin fita Shahudah da Mummy sukeyi, hakanne ya saka Rose basu hanya, itama Aamilah saita take musu baya.       Dukansu idanunsu akan Jawaad dake jingine da ƙarfen da akai kwalliyar barandar suka sauka, ya harɗe ƙafafu waje guda yana danna waya tamkarma baisan mi akeba.         Mummy da jikinta ke tsumar tsoron ganin yanayin Jawaad tace, “My son lafiya kuwa....?”          Kansa ya ɗago yana wani kaɗa hannunsa ya matse wayarsa tare da miƙewa tsaye sosai, a kausashe yace, “Ba ɗaba, Jami'in tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya *_JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSUF_* ne wannan, munzo ne domin gayyatar mutane uku na gidannan zasu amsa mana wasu ƴan tambayoyi a office Hajiya”.       Idanu sosai Mummy ta zaro, Shahudah kam ai neman faɗuwa ƙasa tayi, Rose kuwa dake mata kallon tsana ta tarota tana fadin, “Madam kulafa”.        Shiko Jawaad ko kallon inda Shahudah take baimayiba dama.       Aamilah cikinta kam ya ɗuru ruwa, harta fara ƙaramin fitsari a pant ɗinta😝.             Dai-dai nan Jack da Salman suka shigo, dan yajene ya gama shirin jirgin da zai tashi a safiyar gobe dashi zuwa ƙasarsa kamar yanda Qaseem ya bashi shawara, sam basuyi zaton zuwan Jawaad gidan a daren yau ba, ko a ƙofar gida da sukaga motoci basu kawoma ransu shineba tunda shi dai Salman yasan Jawaad baida Securitys.            Mummy zata sake magana Jawaad ya daka mata tsawa yana faɗin, “Hajiya nace wannan ba ɗanki bane, jami'in tsarone a gabanki ki kama kanki”.       Ba Mummy ba hatta dasu Hafislz kansu tsawarsa ta firgitasu, dama tunda suka iso gidan mamaki ya kamasu, dan dai a saninsu wannan gidan Gwaggonsa ce, kuma gidan surukansa. Furicinsa sosai ya sakasu a ruɗani, ya kuma basu umarnin tafiya da Shahudah da jack da Aamilah.      Yana gama lissafa da waɗanda za'a tafi ya doshi hanyar barin gidan cikin takun bajinta mai ɗauke da izzar fushi.       Gaba ɗaya ji da ganin Mummy sai ya toshe ɗaf, bibiyu ma takoma ganin mutane saboda ruɗani da mamakin Jawaad.         Kukan da Aamilah ke yine saboda tafiya da za'ai dasu ya maido Mummy a hayyacinta, duk roƙo da magiyar da takema su Hafiz babu wanda ya saurareta, umarnin boss ɗinsu kawai suke ƙokarin cikawa, duk da zukatansu a ƙulle suke da wannan aiki sukam yau.         Lokacinma da suka fito dasu Shahudah tuni Jawaad ya shige mota abinsa, ya lumshe idanunsa da sukai masa nauyi, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa bisa kansa, duk yanda yaso kiyaye irin wannan ranar sai da Shahudah tai ƙoƙarin zuwanta, to lallai kam zai tabbatar musu shi *_ƘWAI cikin ƘAYA_* ne, gashi dai abinso ga kowa, sannan kuma abin haɗari ga kowa, da kayi kuskuren ɗaukarsa kasha sukar ƙaya, ƙilama kana taɓashi ya iya fashe maka.           Tsabar ya manna musu hauka cayay a kaisu a ajiye, shiko yace a wuce gida dashi yana buƙatar hutawa. ★★★★★        Ana fita dasu Shahudah Mummy ta zube ƙasa ta fashe da kuka tana ƙwala kiran sunan Jawaad.          Salman ne yazo ya ɗagata shi kansa jikinsa sai tsuma yake, gaba ɗaya Jay ya rikiɗe masa a idanu tamkar ba shiba, da ƙyar ya iya taimakawa Mummy ta miƙe suka koma cikin falo.      Shine yay ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa, sannan Qaseem daya fita, dan baya gidan komai ya faru.        Ya kira Mama Atika ya sanar mata itama.      Kafin kace mi komai ya hargitse, magana ta fara fitowa a family house ɗin su Jawaad, dama daga can kuma Maman Zaitun ta kira itama ta sanar da kama Zaitun da akazo akayi ba tare da sunsan mita aikata ba.       Lokacin da motar Jawaad ta shigo gaba ɗaya gidan ya ɗauki zafi.          Yasan abindama yafi hakan zai faru dan haka ya shiryama kowa a gidan akan wannan case ɗin, kallon wani baiyiba a cikinsu ya shige sashensa ya kulle kansa.         Sama ya haye abunsa canma ya kulle har Windows yandama bazaiji kiran waniba a cikinsu, ya kuma kashe duk wayoyinsa suma.         ********          Ana cikin haka Mummy da Salman suka iso gidan nasu Jawaad.      Yayinda shi kuma Qaseem ya zarce office a tunaninsa Jawaad yana can dasu Aamilah, sai dai ya iske kosu bama akawo canba, kenan wani waje daban yasa aka kaisu?, kuma an tabbatar masa Jawaad bai dawo office ba tun fitar da yay da yamma.        A fusace ya nufo gidansu Jawaad ɗin, inda ya iske hankulan kowa na gidan a tashe, duk da dai wasu na dariya a ƙasan rai da jinjina abinda Jawaad ɗin ya aikata a bazata.           Duk knocking ƙofar da suke masa baiko motsaba balle suyi tunanin zai buɗe su sami yanda suke buƙata, duk da yana jinsu yay kunnen uwar shegu dasu,  wankansa ma yayi, yay shirin kwanciya bayan yayi shafa'i da wutiri, duk da yasan barci da wahala ya ɗaukesa.             Ganin Jawaad yaƙi buɗe ƙofa adaren sukaje suka sanarma kakansa abinda ke faruwa, baiyi mamaki ba, dan dama sune suke ɗaukar Jawaad kamar baisan mi yakeba saboda ya zuma ƴarsu ido tana yanda ta gadama, a gabansu shima ya gwada wayar Jawaad ɗin amma switch up.           Numfashi Baba ya sauke a hankali yana faɗin, “Wayarsa a kashe take, gashi nikuma ba ƙafar kirkiba balle nace zanzo gidan a daren nan, muyi haƙuri zuwa safiya za aimasa magana insha ALLAHU zai fidsosu, wauwtace irinta Jawaad kawai”.         Duk yanda dai suka so ganin su Shahudah basu kwanaba dole suka haƙura tunda babu mafita, aiko ranar anan gidan Mummy ta kwana.           Kamar yanda ya saba yauma sai da ya fita sallar asubahi ya sami salla a cikin jam'i, duk yanda su Uncle Uwaisu sukaso ritsashi basu samu wannan damarba, dan yafisu ƙwarewa a wannan fanin.        Cikin nutsuwarsa yay shirin fita tsaf cikin baƙaƙen Suit da rigarsa ta ciki fara, yayi ƙyau dan dama mai ƙyawunne, tun daga falon sama ya hango Suraj cikin samarin gidan yaron Uncle Uwaisu ne,         Sai da ya haɗa tea ya sakko ƙasa riƙe dashi a hannu yanata turiri, tunda ya fara sakkowa daga steps ɗin benen Suraj ya zuba masa idanu, komai na Jawaad abin so ne, kodan tarin nutsuwar da ALLAH yay masa.       Suraj ya mike domin girmama wa ga Jawaad ɗin, sai da Jay ya zauna a kujera maicin mutum ɗaya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan shima Suraj ɗin ya zauna.         “Yah Jay barka da safiya”.        Jawaad dake juya cokali cikin kofin tea ɗinsa ya amsa a dakensa, “Barka dai Suraj, lafiya dai ko?”.      Murmushi Suraj yay yana risinar da kai ƙasa, “Lafiya lau Yaya, dama su Abbane sukace na kiraka, wai suna jiranka a sashen Mama”.         Shiru Jay bai amsaba, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan yace, “Tom zanzo”.      Daga haka yay gum da bakinsa.        Mikewa Suraj yay yayi masa sallama ya fita.            Jawaad yaja siririn tsaki yana kai kofin shayinsa a baki, sai da ya kammala shan tea ɗin tas cikin nutsuwa kuma sannan ya miƙe ya fita, dama ko basu kirasa ba yayi niyyar zuwa wajensu.                      Kamar yanda ya saba dakewa da shanye ɓacin rai yanzunma hakan yake, ya iso sashen Mama Atika a tsumensa alamun babu wasa ko ɗaukar abinda bai masaba ga kowa.                                Gayyar Uncle's ɗinsa ya iske a falon mama Atika, harma dasu Mummy, murmushi yayi wanda ya bayyana loɓar kumatunsa duka biyu, wato taron dangi aka shirya masa kenan?.         “Duk zan iya daku ai” ya faɗa a fili murya ƙasa-ƙasa yana kaiwa zaune a kujerar da yake ƙyautata zaton dama shi aka barwa.        Wata ƴar ƙaramar dariyar muguntar daya tanadar musu yayi a zuciya.         Suko maɗaukakin mamaki duk ya bayyana a fuskokinsu, musamman yanda sukaga shi tashi fuskar babu alamun damuwa, saima wani kwarjini da cikar haiba shinfiɗe a kanta.         Ya zauna yana ajiye wayoyinsa a ƙaramin tebirin dake gefen kujerar da yake zaune.        “ALLAH dai yasa lafiya? Na ganku haka, Barkanku da safiya?”.       Yay maganar cikin nuna halin ko in kula da kallon ƙurillar da suke binsa dashi su duka.         Sosai tambayar rainin hankalinsa ta bugi ƙirazansu, Uncle Nasir yay masa daƙƙuwa yana faɗin, “Kaci gidanku Jawaad, ya kakema nuna kamar bakasan mika aikataba?”.             Wani murmushi Jawaad ya saki yana harɗe ƙafafu ɗaya bisa ɗaya, da kwantar da bayansa a kujerar, “Uncle minayi nikam?”.        Dukansu baki suka saki suna kallonsa.        A harzuƙe Mummy tace, “Kai mara mutunci, bama kasan mi kayiba? Kaje har gida ka kama matarka ta sunna da ƴan uwanka amma kake mana wannan rainin hankalin naka?”.        Jawaad yay wani luuu da idanu da sauke numfashi, ya taɓe baki kaɗan yana ɗaukar wayarsa ɗaya ya shiga latsawa, “Mummy kenan, na dai kama waɗanda suka bada gudun mawar zubarmin ciki da wadda ta aikata zubarwar, ai matar ƙwarai ta sunna data wadatu da tarbiyya koɗan shegene bata zubar dashi balle ɗan halak na sunna. ku sanarmin kawai yanzu ku miya taraku anan?”.         Mummy data nema zaucewa da kalamun Jawaad zatai magana Uncle Nasir ya katse ta.         “Kai Jawaad ka dawo hankalinka kaji, kasan da suwa kake magana bamason takadaranci, kai yanzu kanaga ya dace ace matar aurenkace ta kwana a rufe? koda abinda kake zargi ya faru ai wannan maganace ta cikin gida, miyasa mu bazakazo ka sanar manaba muyima tufƙar hanci?”.         Shiru kamar Jawaad bazai amsaba, sai kuma ya ajiye wayar da yake dannawar ya maida hankalinsa ga Uncle Nasir yana ƙoƙarin ɗaukar takardar daya ajiye tare da wayoyinsa.           “Uncle wannan ba maganar gida bace, yanzu haka badan yinta yasa nazo nanba, dan Office zanje ana jirana, inhar akan maganar yaran canne kuka taru anan to bazaku ji komai daga gareniba, kudai nema lauya kawai, dan sai an biyani cikina, ita kuma da kuke tunanin zan raga mata saboda igiyar auren da bata amfanamin komaiba tunda aka ƙullata to ga shi nan na tsinkata, kucirema zukatanku mutuncina ne zan taɓa saboda ta kwana hannun jami'an tsaro”.         Babu wanda bai zaro ido waje ba saboda mamakin furucinsa babu ko kunyar ambaton cikinsa da yake.       Jikin Uncle Ayuba har ɓari yake wajen ɗaukar takardar da Jawaad ya ajiye ya duba.       Cikin tsagwaron tsoro da firgici yace, “Wlhy yayi sakin”.        Kusan duk a tare suka ce saki kuma?!!!.        Jawaad ya tattare wayoyinsa zai miƙe yana katse musu tunani da fadin,       “Ku gafarceni zan wuce ana jirana, kuna tunanin zan cigaba da zama da jahilar da sam bata da tarbiyyar addinin islama ne?”.          “Jawaad yaushe ka zama haka?”.     Cewar Uncle Sadiqu baki a hangame.         Babu ko gezau kuwa Jay ya bashi amsa da, “Uncle ai indai nine na wuce hakan, dama can ƙaramin sani kukaimin shiyyasa”.         Hannu mama atika da Inno suka saka aka suka fasa kuka, wai Jawaad na musu rashin kunya, ko ubansa Abdul-aziz bazai musu wannan abunba.         Haƙuri sukaita basu, Jawaad kam yay shiru uffan bai ceba.      Sai da falon ya lafane Uncle Nasir ya kalli Jawaad ɗin ransa a ɓace yace, “Wai shin ko ka fara shaye-shayene bamu saniba? Yanzu kai Jawaad duk yabon hakurinka da ake a gidannan ashe hasashen banza mukeyi?”.           Jawaad dake ta ƙoƙarin danne fushinsa yay guntun murmushi yana shafa fuskarsa, “Uncle duk yanda zan maka bayani bazaka fahimceni ba, bansan wane irin haƙuri kukeso nayi akan jahilci da rashin tarbiyyar hudah ba, ankai maƙurar da bazan iya ɗaga ƙafaba kona yafe gaskiya, karku saka kanku a wannan rigimar domin tsakanin ni da itane kawai a cikinta”.           Da yawansu maganganunsa sun shigesu, dan kuwa dai kowa yasan Shahudah kam bata da tarbiyya.        Gwaggo Nafisa mahaifiyar Zaitun tace, “To anji rigimarka ce tsakaninka da Shahudah, ita kuma Zaitun da su Aamilah miya kawosu ciki?”.        Idonsa ya lumshe nanma yana rumtse hannunsa da ƙarfi, ya buɗesu akanta sun kaɗa sunyi jazur, kamar zaiyi magana sai kuma baice komaiba ya miƙe yana kwasar wayoyinsa, dan idan har ya cigaba da zama tabbas zaiyi abinda ba tarbiyyarsa ba.          Kamar ruwa ya cinyesu haka falon yay tsitt suka bishi da kallo kawai harya fice.          Uwargidan Uncle Nasir ce ta miƙe tana faɗin, “Inhar gaskiya kuke bukata a wannan zancen to yaron nan yafiku gaskiya, mai makon wannan titsiyen da lallaɓashi kukayi yafi, tunda da dai dukanku kunsan gargaɗin da yayma Shahudah tun yunƙurin zubar da cikin nan da tayi na farko, yanzu kuma ta aikata aiko dole ku shirya karɓar abinda yamafi haka daga gareshi”.      Tana gama faɗa tabar musu falon, bata saurari yanda suka kacame da maida mata murtani ba, duk da sunsan gaskiya ta faɗa a maganarta.           Koda Jawaad suka isa Office hidimar gabansa ya cigaba dayi baiko bi takan su Shahudah ba, waɗanda shi kaɗai yasan inda yasa aka kaisu saiko su Hafiz da suka kaisun.        Yayi hakane kuma saboda Qaseem, ilai kuwa ranar Qaseem ɗin yini yay fafutukar bincike nason gano inda Jay yakai su Shahudah ɗin, sai dai ko wata alamar da zai iya samu Jawaad bai bariba.      Daga ƙarshe Office ɗin Jawaad ɗin yaje yana masa magana a gadarance.      Jawaad yay masa banza kamar baisan kurar daya kwaso Qaseem ba, sai da ya gaji da hayaniyarsa ne ya miƙe yana kallonsa a wulaƙance, “Ni bani da lokacin yin magana da kowa akan wannan batun, kuje ku nema lauya zuwa gobe zamu shiga kotu”.         Aiko jin haka Qaseem ya kuma haukacewa da surutai, sai Jawaad ɗinne ya bar masa Office ɗin.              Duk yanda sukaso zama da Jawaad akan a sasanta sam yaƙi basu hadin kai, ranarma bai kwana a gidanba, a gidansa yaje ya kwana, da yake yanzu su Aliyu kowa ya koma gidansa wajen iyalinsa.        Su kansu su Hafiz ɗin yaki sanar musu abinda ke faruwa, duk tambayar da suke masa akan kama su Shahudah sai dai yace suyi hakuri subar maganar.        Daga ƙarshe dole suka ƙyalesa saboda basa bukatar shiga haƙƙinsa.        Dai dai da kakansa yaki yarda su haɗu, hakama su Umma sunbi duk hanyar da zasu gansa akan maganar ya tosheta, yaƙi sauraren kowa, yakumaki faɗama kowa ina su Shahudah suke.       Wannan abu ba ƙaramin tada hankalin Mummy yayiba, ga Abba bai dawoba dukda shima acan hankalin nasa a tashe yake, ya gwada kiran Jawaad ɗin amma saiya iske ya sakashi a black list shima.       Kamar wasa saiga su Shahudah na neman rufa sati guda ba'asan inda sukeba, Jawaad yakumayi finfiris yanata aikin gabansa hankali kwance, dan yama cirema kansa damuwar cikin acewarsa ALLAH yasa haka shine yafi alkairi.        Lokacin da ake wannan dambarwar kam Bilkisu na makaranta abinta hankali kwance suna shirye-shiryen fara zana jarabawa.        _________________________ BILKEESU _________________________            Komai na fara zana jarabawarmu ya kammala, dan haka muka ajiye duk wani shiririta muka sake maida hankalinmu a wajen karatu.        Musamman ma ni danafi kowa buƙatar ƙarin haske akan komai, sai dai yanda su Zuhrah ke ƙaramin ƙwarin gwiwa yasa bana tare da wani tsoro ko fargaba, da ai banyi tunanin zuwa wannan matsayinba, ALLAH ya kawoni kuma ai bai kamata na sakama kaina tunanin rashin nasara ba.       A wannan yanayin muka fara zana jarabawar mu...........✍🏻 Page 28 https://youtu.be/HFjVgQVnmn0     MANHA HAUSA NOVEL'S👆🏻 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo ✍🏻ALƘALAMI TV👆🏻         Please and Please my dear fans, wannan sune chennals namu a taimaka dan ALLAH aje ai mana subscribing, zasu dinga kawo muku daɗaɗan novels namu babu ko sisinku, ga abubuwan gyaran jiki da ƙaruwa ta fannoni da dama, dan ALLAH a daure a nuna hallaci, hakan zai sake ƙaramin ƙwarin gwiwar baku ƙwai cikin ƙaya a kullum, dan zai tabbatar min kuna biye dani, kuma kuna sona har yanzu, dan ALLAH kar ayi sanya, a danna mana subscribe, idan liks ɗin baya nunawa kuyi Searching ɗinsu ta Accaunt ɗin youtobe zasu nuna muku  Please & Please😢🙏🏻🥰🥰💃🏻 __________________________ *_BAYAN SATI UKU_*          _BILKEESU_ ............Babu abinda zancema Ubangijina sai godiya, domin kuwa jarabawa na tafiya yanda ya kamata, sai dai ƴan ƙalubale da ba'a rasaba, a yanzu haka abinda ya rage mana bai wuce sati ɗaya ba kacal mu kammala, muɗanyi hutun sati biyu daga nan muyi neco.      Gaba ɗayanmu mun maida hankali, sannan muna taimakon juna, musamman ma ni da suke taimakawa ta kowanne fani.       Yau ma mun fito a gajiye, kowa sai yaƙe yake saboda yunwar dake cin hanjin cikinmu, hostel muka nufa kamar waɗanda aka zanema ƙafafu.        Ummie tace, “Ni yanzuma bama kaje ɗakinba, ka rasa abinda zakaci shine matsalar”.        Rebecca tai dariya da faɗin, “Kina nufin yau ma bazakici abincin da akai ba?”.           “Wlhy bazan ciba, nifa badan kun hananiba da tuni na daɗe da kai report ɗin abinda na gani jiyan nan, ai insha ALLAHU daga jiya harna bar skull ɗinnan bazan sake cin abincin da akai a kitchen ba”.       Dariya duk muka saka mata.       Nace, “Haba ta wajena ki ɗan sassuta, daga jiya kin gani sai kuma akace shikenan kullum za'a cigaba da gani, wannan ɗinma nasan by mistake ya shiga ALLAH”.         Nazifa dake gefena tai saurin faɗin, “Barta Bily, kartaci, wlhy yunwar cikintama ta isheta, ita ɗinnan mayyar son cin doya, duk randa akayi zamuga bazataje ta amso ba da gaske?”.           Ummie ta harari Nazifa tana faɗin, “To ƴar sa ido, duk bin ƙwaƙwƙwafinki ƙyayi ki barni, dan zan tabbatar muku da maganata”.       “ALLAH ya bada iko” cewar Zuhrah.     Duk muka amsa da amin muna dariya, da haka muka ƙarasa hostel.      Sheƙawa da gudu Zuhrah tayi ta fara shiga ɗakinmu tana faɗin, “Nizan fara wanka ehe”.           Ƙarasa shiga muma mukai, Nace, “Kai Zuhraty kin sanfa yanda nake, Please ki barni na fara”.       Shigewarta tai da sauri tana min gwalo, “Ai dama saboda ke ne zanyi fes ɗin, karda ki gogamin nima na ɓule yau”.       “Zaki sani ai, insha ALLAHU gobe sai muna tsaka da jarabawa kiji ya zubo....”        “Wlhy ke muguwace Bily” cewar Rebecca dake cire kayanta, Nazifa da Ummie kuma suka saka dariya.       Haka muke a koda yaushe cikin nishaɗi da kulawa, nakanji tamkar na ɗauki wasu shekaru masu yawa tare dasu ne, dan wanda bai saniba ya gammu zaiyi tunanin tun yarinta muke a haka, ba ƙaramin sakin jiki nayi dasuba suma kuma hakan, idan kaga faɗa a tsakaninmu sai dai rashin fahimta, mukan zauna kuma mu warware da wuri kafin abun yay mana tsamari, Nazifa ma tuni ta fara sakin jiki dani, duk da dai ba kamar su Ummie ba hakan bai dameni ba.           Sai da duk mukai wankan sannan mukaje muka amso abinci, amma banda Ummie datai alƙawarin tabarci har ta wuce.           Irin wannan farin cikin dana samu daga garesune ya sake kawoma rayuwata canji da farin ciki, jikina ya murje tamkar ba'a makaranta nakeba, duk da babu wanda ya taɓa busting ɗina hakan baisa naji ɓacin raiba, amma dai ina kewarsu su duka.      A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi mun kammala waec, a ɗan hutun da muka samu kafin fara neco ne ya sakamu sake komawa kan karatun rayuwa.      Dan kuwa ƙawayena sun sake buɗe mun wasu shafukan koyan salo-salo dake maida mace mai aji da tsaftatacciyar wayewa, niko na nutsu wajen bin komai daki-daki ina haddacewa...... _________________________ BILKEESU _________________________           Sai da su Shahudah suka cika sati uku cif sannan Jawaad yay ra'ayinma su kansu su ganshi, dan tunda ya saka aka kaisu aka ɓoye bai sake waiwayensu ba, harkokin gabansu kawai yakeyi.       Yau ɗinma dai tun safe yana office, yayi busy matuƙa saboda ayyukan dake kansa jibge.      Knocking akai dan haka ya bada izinin shigowa.         Bai ɗago ya kalli wanda ya shigo ɗinba, amma ya amsa masa gaisuwar da yake masa ta hanyar ɗaga hannu.      Ya jeho masa tambayar, “Lafiya kuwa?”.           “Lafiya lau Boss baƙine dakai”.       Jawaad dake rubutu ya dakata tare da ɗago manyan idanunsa ya zubasu a kansa, “Baƙi kuma? Maza ko mata?”.          “Boss namiji ɗaya ne dattijo sosai, sai kuma mata biyu da kamar dai budurwa”.       Shiru Jawaad bai amsaba, yadai kafeshi da idanu yana jujjuya pen ɗin hannunsa, yaɗan kaɗa hannunsa yana cigaba da rubutunsa yace, “Shigo dasu”.          Da to ya amsa masa ya juya ya fita.      Jay yaɗan tsaya da rubutu yana tunanin su wanene to? Bakinsa yaɗan motsa kaɗan kawai ya cigaba da abinda yakeyi, sai dai muryar da yaji tayi sallama ne ya sakashi ɗagowa babu shiri.       Kakansa ne da ƙannen mahaifiyarsa, ya ajiye biron da yake rubutun fuskarsa ɗauke da mamaki yace, “Baba kune anan?”.          Baba ya zauna da ƙyar yana ma Jawaad daƙƙuwa, “Kaci mai garin garinku, tunda gudunmu kake aini na biyoka har wajen ɓuyar taka ɗan jakar uba”.         Murmushi kawai Jawaad yayi ya koma ya zauna a kujerarsa yanama su Umman Batool sannu da zuwa, ya maida kallonsa ga Nabeelah datai musu rakkiya, “K miƙoma Umma ƙarama waccan kujerar ta zauna”.         Nabeelah ta amsa masa da to tana nufar kujerar dake gaban Computers ɗin office ɗin ta ɗakkoma Umma ƙarama.      Sanin halinsa da tayi ya sakata fita ta basu waje ita bata zauna ba, da kansa ya miƙe ya buɗe firijin dake office ɗin ya ɗakko musu ruwa da lemo ya ajiye yana sake musu barka da zuwa.          Su dai binsa kawai suke da kallo, dan damuwar da sukayi tunanin yana ciki sam basu ganta a tattare dashiba, sai ma ƙiba ƙamar ya ƙara da ƙyau.           Baba ne ya katse musu tunani da faɗin, “Ja'irin kaya, to yau ta gudu ta ƙare gani ga ka”.       Jawaad dake zama yace, “Haba mai ran ƙarfe ka iya rigima kaima, ni damafa ba gudu nakeba, kawai dai aikine yaymin yawa, iyayena kunajin mai ran ƙarfe fa ya sakani gaba”.          Umma babbace tace, “Ai gaskiya ya faɗa Jawaad, ka aikata laifi kuma ka koma guje-guje”.        “To Umma kema harda k? To duk laifin da ake tunanin nayi amin afuwa Please”.        “Ai ko munso yin fushin da kai bama iyawa Jawaad, amma hukuncin daka yanke akan matarka yayi tsauri da yawa duk da bata ƙyautaba” Umma ƙaramace mai maganar.         Jawaad da yay ƙasa da kai yana murmushi yace, “Baiyi tsauriba Ummana, hakan shine ya dace da Hudah tunda ita bata da hankali, lokuta da dama takan nunamin ita mai taurin kai ce, batasan nawa zafin kan ya zarce nataba, ina ɗaga ƙafane kawai bisa wasu dalilaina, bama ga itaba, su kansu waɗanda suka bata taimakon aikatawar zasuji shakkar aikata kwatan kwacin haka anan gaba”.        Baba yace, “Hakane Jawaad, dama wannan shi nake hango maka tun farko, dan Alhaji Ali yayi matuƙar sakaci da jagorancin tarbiyyar iyalansa, iyaye maza da yawa mukanyi irin wannan sakacin, ba komaine yake kawo hakanba sai ɗaukar kasuwancinmu da girma fiye da tarbiyyar yaranmu, mukan sakarma mata, bayan munsan hannu ɗaya baya ɗaukar jinka, bai zama lallai Uwar ƴaƴanka ta kasance yanda ya kamata uwa ta zamaba, saboda yanzu sam bama duba mai addini mu aura, ƙyale-ƙyalen duniya da adon jikin mace da zuri'ar data fito kawai mukafi kallo, sai kaga idan da raunin tarbiyya akan wannan zuri'ar kaima gidanka zai rayune a raunane, idanma ka samu mai addinin ka aura duk ƙoƙarinta sai kaga nauyin ya mata yawa sosai ta kasa kulawa da yaran yanda ya kamata, musamman ma da yanzu abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa, dole tana buƙatar taimakonka, kama gina yaran bisa ƙyaƙyƙyawan tsari yaka ƙare balle ka rainesu bisa al'adun yahudu da nasara, ilimin boko ba haramun bane, ka saka ɗiyarka mace ko namiji suyi zurfi a cikinsa ba ɓarna bace, matsalar kawai ya kasance babu ilimin addini a cikinsa, to lallai kaima ka tabbatar da ɓarna a gidanka bama sai an faɗa makaba. Irin wannan sakacin shine Alhaji Ali yayi tun farko, mutane nawane ke rayuwa a wajen ƙasar nan kaga yaransu kuma a nutse cikin ƙyaƙyƙyawar tarbiyya, amma shi sai yay kuskuren rashin nuna musu hanyar ALLAH da dokokin saninsa, abinda ya sani kawai ya nema musu suci, ya basu ilimin boko saboda shine mutunci a yanzu. Wannan sam ba haka bane, maiyin wannan tunaninma sam bashi da tunani shi kansa. Nasan an cuta maka ƙwarai da gaske Jawaad, amma haƙuri shine magani, sannan banso kayi gaggawar yin sakinba shi kansa, dan hakan baida amfani sam, daka ƙara haƙuri munbi wasu matakai ko zata gyara”.            Jawaad yace, “Humm, baba ban katseka ba, amma ni nasan irinsu Hudah da wahala su zam cikin Masu gyaran, dan sufa gani suke sunfi kowa sanin abinda ya dace, sunema sukeyin mai ƙyau kowa wawane kidahumi a idanunsu, abinda ya bani matuƙar takaici shine wani kafirin banzane fa ya ɗorata bisa layi bayan ta haƙura zata haifi cikin, wanda ni a ganina maybe bayan hauhuwar tata ta ɗan canja wasu abubuwan, amma yazo ya sake rikita komai”.             Umma tace, “To inma banda jahilci tanada aure miye na wani riƙe ƙaton gardi wai abokinta, ba al'adarku ɗaya ba, ba addininku ɗaya ba, ba jinsinku ɗaya ba, sukuma su Hajiya Humairan suka zuba mata idanu tsabar rashin hankali”.        “Wannan ai shine illar sakacin da baba ya faɗa Yaya, dan inba sakaci ba da girmama al'adun yahudu wlhy hakan sam bazai faruba, yanzu dai komai dai ya rigada ya faru, haƙuri shine yafi cancanta ayi, sai kuma a tari gaba, Yarona ALLAH ya azurtaka da mace ta gari darajar haƙurin da kayi”.         Dukansu da amin suka amsa banda Jawaad da ya amsa nashi a zuciya.       Baba yace, “Yanzu dai Jawaad inason kayi haƙuri ka janye maganar zuwa kotun nan, sannan ka fiddosu daga inda ka ɓoye, nasan kai mai nutsuwane bazaka kaisu station ba dama, akwai dai inda ka kaisu”.        Jawaad ya ɗanyi jimm sai kuma yay guntun murmushi yana haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi, “Shikenan baba zanyi yanda kakeso, dan babu wani sharaɗi da zaku gindayamin na tsallakesa, dama suna gidan Qaseem ne”.        A tare sukace “Gidan Qaseem kuma?”.          Murmushi Jawaad yay yana faɗin, “Eh suna can, nasan halinsa baida hankali, tunaninsa kuma bazai taɓa bashi can na kai suba tunda yasan banma san gidanba, shi kansa bama ko yaushe yake zuwaba, idanma yaje ba ko'ina yake shigaba tunda babu kowa a gidan”.           Dukansu babu wanda mamaki da al'ajab bai fito a fuskarsa ba, yanzu nan duk wannan fafutukar da akeyi akan su Shahudah ashe gidan ɗan uwansu yaje ya ajiyesu, lamarin Jawaad sai shi.       Albarka sosai baba dasu Umma suka saka masa, shiko yana amsawa cikin jin daɗi.       Baba yace, “To maganar dawo da ita ɗakinta fa, shima kayi haƙuri kaji Abdull-Jawaad”.           “Ihm-ihm mai ran ƙarfe karka sake rikitomin sabon aiki, ayi haƙuri nayi kenan, nima inason naɗanyi ƙiba kamar kai ko a fuskane”.       Dariya suka ƙyalƙyale da ita, baba ya kamo hannun Jawaad yana faɗin, “Ja'iri yaji wuju-wuju, bazamu maka tilasba, ƙila nangaba idan ka huce ka maido kayarka koda bamu saniba”.        “Ai bama za'ayi hakanba” cewar Jawaad yana dariya su Umma na tayashi.             Har mota ya rakosu baba nata masa tsiyar wai yanzu sun koma ɗaya duk gwaurayene, wannan azumin zaiba yara su kaɗama Jawaad kiɗan gwauro inhar baiyi sauri yayi aureba..       Shi dai Jawaad nasa murmushi ne, dan yasan dai duk wayo akemasa danya tashi yay aure da wuri, shiko a yanzu dai kam yanda yasha wahala wajen Shahudah tamkar kurar wasa bai yi zaton sake kallon wata ɗiya mace da sunan wani abu so ba balle akai ga aure a yanzun, Kai shi a yanzuma haushi mata yakeji. “Munga idi Shahudah ta ja mana tsiya a wajen Jay”.🤣🤣😂⛹‍♀ ★★★★★★★                Bayan tafiyarsu Jay Office ya koma ya cigaba da aikin gabansa, dan gaskiya badan su bane bama zai iya sauraren kowa a irin lokacin nanba ma, gashi yanason fita wani waje kuma.      Ya sauke numfashi a hankali yana komawa bayan kujerar ya lafe, idanunsa ya lumshe yana maijin kewar mahaifiyarsa, sosai yake buƙatar ganinta a kusa dashi, badan ya rasa kulawa bane, shi dai yana so yaga ɗa a kusa da uwa, shiyyasa idan Qaseem na wani shirman yakan ga gatane kawai yay masa yawa.         Waya ya ɗauka yay kiran Hafiz akan yazo ya sameshi a office.        Babu jimawa kuwa saiga Hafiz ya shigo, zama yay bayan sunyi musabaha yana faɗin, “Boss ta samu ne?”.          Jawaad yace, “Kanka aka samu ko?”.      Dariya Hafiz yayi sosai, “Ba komai 1-0 kenan, nima lokacina na zuwa”.        “Zaka daɗe baka isoba kuwa, kasan miya farune?”.        “A'a” cewar Hafiz yana nutsuwa.     Jawaad yay guntun tsaki yana gyara zamansa, inason muje wajen yarannan, shima mai jan kunnen can dake a cell ku fiddoshi harma da likitan, sai dai shi likitan zamu dawo dashi dan wannan asibitin nasa sai mun masa bincike”.            “Ok Boss, yanzu naje mu shirya kenan?”.        “Ai da kai kaɗaima zamuje sai rose, tunda ga Securitys ɗinnan da aka mannamin dole”.       Dariya Hafiz yayi sosai, cikin dariyar yake faɗin, “Ni bansan miyasa bakason Securitys ɗinnanba, wlhy kuma suna ƙara maka ƙyau sosai, dan idan suka dafo maka bayannan dolene maƙiyi yaji tsoro, bakaga kwana biyu Qaseem ma ya shafa maka lafiyaba”.           Baki Jawaad ya ɗan taɓe, “Ai shi wannan bashi da cikakken man kai ne kawai”. ★★★★★★          Jack da Doctor suna nan tare da Jawaad a hukumarsu ashe, su Shahudah ne kawai a gidan Qaseem, kallo ɗaya naima su Jack tausayinsu ya kamani shida Doctor, dan daka gansu kasan ba ƙaramin jigatuwa sukaiba.           An fito dasu daga cikin wani cell aka jefasu a moto.             Dai-dai lokacin da Jawaad ke fitowa daga cikin Office nashi, yau ma dai yana cikin baƙaƙen Suit da suka zauna masa a jiki tamkar danshi akayisu, duk da dai rigar saman riƙe take a hannunsa bai sakaba, yakai hannu yana gyara tie ɗin wuyansa yana taku cikin ƙasaita da jin shifa ya kai, fuskarnan sam babu walwala a cikinta, kallo ɗaya yayma su Jack ya ɗauke idonsa.       Motar da aka buɗe masa ya shiga ya zauna suka fice.           Sun isa gidan Qaseem dake a wata anguwa da ban, gidan yayi ƙyau sosai matar aure kawai yake jira tunda maishi ya tsaya ruwan ido.       Jawaad bai shigaba, baima fita a motaba  Hafiz ne kawai ya shiga shi da rose, babu jimawa sai gasu sun fito da su Shahudah.      Ba ƙaramin zare idanuba nayi akansu, Shahudah ƴar gayu ƴar ƙwalisa sati Huɗu babu wanka yay kuke tsammanin ganinta🥴? Ga tashin hankalin basusan inda sukeba, ga abubuwan da Jawaad ya shirya musu a gidan na ban tsoro babu duka babu zagi, kullum basa iya barcin kirki saboda tsoro🤣, ba kowane mai wannan aikinba kuma sai securitys nashi, su ya saka kullum dare suzo suyita abubuwan dake matuƙar firgita su Shahudah, wataran tsabar tashin hankali har fitsari sukeyi a wandunansu, ɓangaren abinci kuwa babu zancen mai daɗi, tsabar yasan Shahudah ma ta tsani tuwon dawa miyar kuka shi yake sakawa kullum batool tayo masa kuma bamai daɗiba a kawo musu, safe da rana da dare, daga ruwan Alwala kuma sai nasha kawai ake ajiye musu, hakan yasa babu damar wanka, to dama a tsare suke, duk bayan wasu awoyi kuma Rose na zuwa ta dubasu.        Tun Shahudah tana yunƙurin amai idan taga tuwon dawa har wahala ta sakata rinkaci tana toshe hanci, to taji zata mace a banza da yunwa, mutuniyarku tayi baƙi sosai kamar wadda ta taso a dokar daji, dama wajen kwanciya tabarma ne kawai aka basu, so babu dai marabar gidanma da prison, ƙilama gara jail ɗin, kowa kuma da ɗakinsa babu mai samun abokin hira ko yaji motsin dazai samu nutsuwa, dama can Rose haushin Shahudah takeji, dan a ganinta saboda Shahudah Jawaad yaƙi sonta😆, shiyyasa tafi takura mata sosai.           Har aka sakasu a mota suma baiko kalli sashen da sukeba, tun daga wajen ya sallami Rose da Hafiz akan su koma Office, shi kuma da securitys ɗinsa da motar dasu Shahudah ke a ciki suka nufi family house ɗinsu.          Da yake yammace sun sami Uncle's ɗin Jawaad ɗin duk sun dawo gida, shigowar motocin Jawaad ɗin ne ya saka mutanen gidan maida hankalinsu a kansu, ballema ya daɗe baizo gidanba.        Bai fitoba a mota ba har aka kammala fiddo su Shahudah kowanne hannusa da ankwa da yasa aka saka musu saboda son ya sake tada hankalin ƴan gidansu, su ɗauka daga wata uwa duniya aka ɗakko su Shahudah.           Aiko dabararsa yayi tasiri, dan ba ƙaramin tashin hankali kowa ya shigaba da ganin su Aamilah a wannan halin, gashi idanunsu duk a rufe.         Bai shiga sashen kowaba, koda ya fito a harabar gidan ya tsaya aka kawo masa kujera ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya su Jack durƙushe a gabansa sai kace zamanin sayen bayi😂.         Duk wanda ya fito daga sashensa ya gansu haka sai zuciyarsa ta hautsina da tsoro da mamakin tsageranci irin na Jawaad, aiko harda masu koke-koke, shiko ko a kwalar rigarsa.       Mama Atika ta nuna Jawaad tana faɗin, “Kai dai ba yaron arziƙi bane, yanzu akan zubar da ciki kawai ka wajiga rayuwar waɗannan yaran haka?”     Ko kallon inda take baiyiba, ya bama gimba Umarnin ya buɗe musu fuska.      Uncle's nashi babu wanda ya iya cewa komai saboda tsabar mamakinsa.        Mummy kam zaman dirshan kawai tayi dan tama kasa cewa uffan, ta zubama su Aamilah idanu da Jawaad ɗin tamkar ta samu majigi.        Jawaad ya katsema kowa tunani, idanusa ya kafe Doctor dasu tamkar zai cinyesa.        Kasa jurewa Doctor yayi yay ƙasa da nasa cike da ƙara jin tsoron Jawaad ɗin har cikin ransa.        Murya a kausashe Jawaad yace, “Likita bokan turai ko? To nikuma Jay bokan likita, miyasa ka zubarmin da ciki?”.        Kai likita ya shiga girgizawa, cikin muryar jigatuwa yace, “Wlhy ban zubar maka da ciki ba, hasalima bansan wanene zaiyi amfani da allurarba, ni dai Zitun ce ta kirani ta haɗani dasu, wannan da waccan sukazo na basu allura suka tafi, amma bansan wa akaimawaba a cikinsu”.         “Uhyihmgg yayi ƙyau” cewar Jawaad yana maida hankalinsa ga Zaitun.        “To ke kuma mai nuna likitan dake zubda ciki fa? Kin taɓa zubarwa ne kema kenan? Shiyyasa har kika sanshi kika kai nawa cikin aka salwantar?”.       “Wlhy yaya, wlhy kaji na rantse ban taɓa aikatawaba, sannan bansan Shahudah ce zata zubar da cikiba, nidai kawai Aamilah ce ta kirani tace na faɗa mata inda zasu sayi maganin zubar da ciki, shine na sanar mata sunan Dr Jeo”.            “Kika sanar mata sunan Dr Jeo, to ke ina kika sanshi idan har baki da alaƙa da yin ɓarnar kema?”.            Hawaye na zirara a kumatun Zaitun tace, “Yah Jawaad ku gafarceni, wlhy sanadin ƙawata na sanshi, dan ita na taɓa rakawa aka zubarma ciki, shinema har na bama Aamilah labari, ni nama manta mun taɓa maganar, ashe ita bata mantaba shine a ranar ta kirani na haɗasu”.         Jawaad yaɗan matse idonsa cikin baƙin ciki, ya maida ga Aamilah, “To ke shugabar tawaga mi cikina ya tsare miki dan uwarki?” Yay maganar da ɗauketa da marin daya gigitata matuƙa ta nema jinta da ganinta ta rasa a lokaci ɗaya.       Babu wanda bai kauda fuskarsaba a wajen, Mummy ta fashe da kuka da tasowa zata riƙe Jawaad securitys nashi suka tareta, dan dama sune suka hana kowa ƙarasowa inda Jawaad din yake balle su Aamilah.        Sai da Aamilah taja kusan mintuna uku kafin hankalinta ya dawo jikinta, sai rawar jiki take tana hawaye.        “Ba magana nake dakeba!!!”.       Jawaad yay maganar cikin matuƙar tsawa.              “Brother zan faɗa maka gaskiya wlhy”.       Jawaad ya watsa mata harara yana huci, yace, “Karma ki faɗa, ki bari nakai ƙarshe wlhy dukan mutuwa zan miki”.        Aamilah na kuka da rawar jiki ta zayyane ma Jawaad duk yanda komai ya faru, kansa kawai ya kwantar a jikin kujerar yay shiru yana kallon Shahudah da tai ƙasa da kai tana hawaye, dan harga ALLAH wani masifar son Jawaad take ƙaraji da cikin data salwantar a yanzu, dan sai yanzu ta fahimci muhimmancin zaman cikin a jikinta.          Duk jikin mutanen gidan ya ƙara sanyi, saboda inhar gaskiya za'a faɗa Jawaad ya fisu gaskiya, dama kuma da yawansu suma sunajin haushin Shahudah saboda lalata musu komai da tayi.      Uffan bai sake cewa da kowansu ba, Shahudah da jack kuwa babu wanda yacema komai sai da ya miƙe, takawa yay a hankali zuwa gaban jack, cikin harshen turanci murya a kausashe yace,        “Na baka nanda awa goma sha biyu kacal, kabar ƙasarnan, inba hakaba, saina kaika inda babu wanda zai sake jin labarinka, kuma daga yau karna sake ganin wannan fuskar taka a ƙasata, idan ra'ayin zama take da kai, sai ta bika ƙasarka can ku ƙarata”.       Yana gama faɗaya ya wuce ta gabansu yana bama securitys ɗinsa umarnin su saki su Aamilah shi kuma Doctor su maida masashi mota.        Yanda bai cema Shahudah komaiba haka bai tankama jama'ar gidansuba kaf ya koma mota suka fice a gida.         Wannan al'amari shine ya kuma jijjiga zukatan ahalin Jawaad, daga kuma wannan rana ya ɗauke kansa daga garesu kaf ɗinsu, yazo duk wani abunsa mai muhimmanci a gidan ya ɗauke ya koma gidansa da zama, yamafi zama a headquarters ɗinsu dan dama can yanada gida a wajen, kawai dai bai cika zaman baneba saboda baya ra'ayi.          Duk kuma wata kaddararsa da takardunsa dake hannun Uncle's nasa ya basu umarnin maido masa, hatta da gidajen gonar mahaifinsa guda biyu duk ya amshe, hakama gonakin dake ƙauyensu suma dukya amsa sun dawo hanunsa.       Wannan al'amari ya matuƙar tada musu hankaki, harma suka fara tunanin kodai yasan manufarsu dama sharesu yayi?..........✍🏻 Page 29 ............Ɓangaren su Shahudah ma komai ya caɓe, gashi ma tunda suka fito bata da wani isashshen lafiya, su Mummy kuma sun kasa sanar mata maganar sakin da Jay yay mata.       Jack kuwa washe gari jirgin farko dashi ya tashi.         Abu ya tsayama Dad sosai a zuciya, idan ya zauna yakan tafi dogon tunani game da kalaman Jawaad da yace jahilci na rashin ilimin addini ke ɗawainiya da Shahudah.       Maganar nan na matuƙar sukarshi, dan ya tabbata gaskiya Jawaad ya faɗa, sam a tarbiyyar yaransu babu ilimin addini a cikinta, rabon da yaransa suje islamiyya tun suna ƙananu, irin rayuwar da suka buɗa ido da ita kuma saita goge musu komai, musamman ma daba maida hankali akai ba sanda sunada ƙarancin shekarun, amma yanda yaro bai cika manta abuba dasun tsura da wani abu, koda yake masu iya magana kance duk abinda ba'a tuni a cikinsa yakan lalace ko a canja masa manufa ma baki ɗaya.        Maimakon ya ɗauki mataki akai ko ya zaunar da Shahudah harma da Aamilah yay musu faɗa, ya kuma gyara kuskuren da yay tun farko na sakaci da gidansa, sai ya yanke shawarar tura Shahudah wata ƙasa wai ta huta ko hankalinta ya kwanta.       Koda ya samu Mummy da shawarar tura Shahudah sai ta nuna masa hakan shine dai-dai,        “Wannan shawaran tayi Dadynsu, ni kaina fargabar tunkarar Mamana nake da batun sakin nan da yaron nan yayi, amma idan ta tafi ta huta hankalinta ya dawo jikinta koda tasan babu auren bazata saka kanta a damuwaba, duk da dai munama fatan kafin lokacin ya sakko ya maida auren nasu, kokuma kawai ta koma makaranta acan ɗinma”.       Numfashi mai nauyi Dad ya sauke, yay ɗan gyaran murya kaɗan yana faɗin, “Shikenan to, amma k kina ganin yaron nan zai sakko kuwa? Kigafa abinda ya aikata, yama yanke kowacce alaƙa daku ɗin kanku”.       “Humm ai saima kaga yanda ya rufe ido wlhy, ai ban taɓa sanin Jawaad haka yakeba, dukkan halin mahaifinsa shine tattare dashi, kaita musu abu suyi kamar basu damuba, rana ɗaya saisu birkice maka”.        Murmushi Dady yayi kawai bai iya cewa komaiba.         Kwana biyu dayin wannan maganar Daddy ya samu Shahudah da kansa yay mata bayanin shawarar da suka yanke, amma sun nuna mata zata tafine ta huta har lokacin da Jawaad zai sakko daga fushin zubar masa da ciki da tayi.        Shahudah batayi musuba, dan a ganinta hakan shine mafita a gareta, a yanzu komi zatayi Jawaad bazai saurareta ba, to garama taje ko makarantar ta koma ma ta ƙara karatun zaifi.       Qaseem shine yay tama Shahudah kiciniyar tafiyar har komai ya kammala, ranar da zata wuce tata kiran Number Jawaad amma bai ɗagaba, ta tura masa text message na ban haƙuri shima babu reply, ranta dai duk a jagule ta wuce, taso su haɗu da Jawaad ɗin Qaseem ya balbaleta da masifa, dole ta haƙura tadai rubuta saƙo ta barma Aamilah akan koda nan gabane ta bama Jawaad ɗin.      Ita dai Aamilah ta amsane kawai, amma bata da tabbacin iya badawar, dan ko'a mafarki yanzu bata fatan sake haɗuwa da Jawaad, itama karatun zata samu ta koma tama bar ƙasar yafi mata kwanciyar hankali. _________________________________        Duk da Jawaad yaga kiran Shahudah da saƙonta bai kulaba, kuma sarai yasan da shirin barin ƙasar da take, amma sai yay tamkarma baisan anaiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi. *_BAYAN WATANNI BIYU😹🥴_*               Zuwa yanzu komai ya lafa tsakaninsu Jawaad, duk da dai ta ciki na ciki akeyi, bai sake bi takan labarin Shahudah ba balle bibiyar inda take kokuma mi takeyi?.       Sai dai akan barin gida da share kowa a danginsa baba ya gyara wannan alaƙar, dan dakansa yaje gidan yakuma saka Jawaad zuwa dan dole.       Dukansu ya haɗasu yay musu nasiha akan zuminci da muhimmancinsa, tare da nuna musu illar wanda yazama silar rarrabewarsa. Dukansu jikinsu yayi sanyi har Jawaad ɗin, domin kuwa shima yasan hakan, tunda yanada ilimin addini sosai, har a yanzu ma bawai ya bar nema bane, take sani kawai yayi da kuma tauna aya dan tsakkuwa taji tsoro.       Da kansa ya nema gafarar Uncle's nashi ya kuma basu haƙuri.     Suma suka bashi haƙuri akan kuskuren da yake gani sun masa. Yace shi basu mashi komaiba, dama dai akan maganar cikin Shahudah ne da duk suka kasa fahimtar an cuta masa suka goyi bayanta.      Sunta baza ido da kunne suji kozai maido musu dukiyarsa daya amsa da kuma maida aurensa da Shahudah sai dai baice komaiba, da Uncle Nasir ma ya takalo masa maganar aure akan bai ƙyautu da mutuncinsa ya zauna babu mataba, cayay suyi masa afuwa akan wannan maganar, maybe zuwa nan gaba kaɗan yayi.      Sunso masa tayin ƴaƴansu sai dai bai bada fuskar hakanba, shiyyasa suka ɗaga masa ƙafa akan sai zuwa gaba.      Shi baima san sunaiba, kwana huɗu da yin wannan zaman Baba ya takura masa sai da ya dawo gidan da zama, randa ya samu dama yakanzo nan ya kwana, wataran kuma acan Barrack nasu yake kwana abinsa, kokuma gidansa, ya dai raba hankalinsa uku babu gaira babu sabar.       Sai dai shima hakan yanacin ransa, yasan da mahaifiyarsa na tare dashi wannan rashin tsayayyyen muhallin da bai samesa ba, dan duk inda take shima anan zai kasance dole.         Ga dai Jawaad ya dawo gidansu da zama, amma zaman sai ya banbanta dana fil azal da yayi, ya ɗaukarma kansa duk safiyar daya kwana a gidan zai shiga ya gaida tsoffin gidan biyu da suka rage, wato su mama Atika, idan yaga yanada isashshen time zai shiga duka sashen Uncles nasa suma, idan bai da kuma shikenan.      A ɓangarensu kuma suma duk sun saka yaransu mata farauto zuciyar Jawaad, kowa burinsa ƴarsa ta samu karɓuwa ga Jay a aura masa.       Sai dai kuma an samu matsala, shi Jawaad ma yaran gidan basu ishesa koda kalloba, yanzu hakama bazai iya kawo sunan wasuba kansa tsaye, yawancin sanda suka taso shi kuma baya gidan yana harkokin karatunsa da wasu abubuwan, amma duk waɗanda ya tashi dasu daga ƙuruciya duk ya sansu yasan sunayensu, to duk sunyi aurema matan, hakama mazan, da yawansu kuma yana gaisuwa dasu ta waya time to time idan sun kirashi. _________________________ BILKEESU _________________________          A yau muka tashi da farin cikin da baki kaɗai bazai iya furtawaba, dan kuwa mun zana jarabawa ta ƙarshe zamu koma gidajen iyayenmu, gashi dai yau ranar farin cikice ga kowacce ɗaliba, amma mu saita zamar mana ranar kuka nida ƙawayena su Ummie.     Mun haɗa kai a waje guda munata rairawa abin tausayi, Dadyn Ummie na daga gefenmu yana lallashi, duk sun bani adireshinsu, nima na basu nawa, su dama duk sun san gidajen juna iyayensuma nata zuminci.        Kowacce anzo ɗaukarta daga gidansu, niko Dad ya cema Dadyn Ummie ya kaini, bayan duk tafiyar sauran muka rage ni da Ummie kawai, sai da Dady ya gama kimtsawa muma ya ɗaukemu muka tafi, lallai zanyi kewar makarantar nan, har mukai nesa da ita ban daina kallonta ina hawaye.        Sun kaini har cikin gidanmu, wato gidan Dad, dan a yanzu shine kawai zan bigi ƙirji wajen kiransa gidanmu, tunda ƙaddara ta mallakaminshi matsayin gidan.      Amina ta fito a guje ta ƙadandaneni tana ihun murna, shima kuku sai washe haƙwara yake shi da baba mai gadi damai kula da flowers ɗin gidan, Su Dady basu shigaba suka juya akan nanda kwana biyu zai kawo mani Ummie.      Sai da naji ƙwalla ta cikan idanu, har suka fice ina ɗaga mata hannu itama tana ɗagomin, su Amina suka kwashi kayana zuwa ciki.      Duk da babu wanda ya fito domin tarbata a cikinsu ni ɗokin ganinsu nakeyi, sai dai kuma falon tsit babu motsin kowa, to yanzu dai kunsan wannan ba Bilkisun da bace da suke ɗauka bagidajiya, nima na sake ilimin rayuwa dana zamantakewa, cikin tsantsar son ganinsu na fara kwala kiran sunansu ɗaya bayan, Aunty Aamilah ce ta fara fitowa tana faɗan wake ƙwala mata kira haka? Cikin yatsine fuska.      Bamma sauraretaba na rungumeta, taso tureni a jikinta, amma sassanyan ƙamshin data shaƙo daga gareni ya sakata fasawa, nace, “Aunty Aamilah i miss you so much, irin mai zafin nan, mai hana barcin nan”.       Babu shiri tai dariya tana ƙaremin kallo sama da ƙasa, “Gaki dai kin canja kamar ba keba, sai dai shirman na nan kaɗan, ashe dama ƙazantace ta ƙara miki muni da rashin ilimi ga ƙauyanci, duk da kina nan a baƙarki ai yanzuko baƙin ya zama mai ƙyau a idon mai kallonki”.      Dariya nai mata kawai, duk da dai akwai cin fuska a zancenta sai ban ɓata rainaba, na haye sama ina dariya da ƙwala kiran sunan Mummy da Dad.        A falo naci karo da Mummy zata sakko, nako ɗareta itama ina jera mata kalaman kewa.      Dariya Dad ya shigayi shima dake bayanta yana kallonmu cike da birgewa.       Ni nasan ganin Dad ya saka Mummy amsata hannu biyu, wai har itama na faɗin tayi kewata.     Na saketa na nufi Dad, ya buɗe min hannayensa alamun nazo na shige jikinsa shima, amma sam bazan iya hakanba, sainai murmushi cikin nuna jin kunya da girmamawa a gareshi na durƙusa har ƙasa ina gaishesa.         Hakan ba ƙaramin daɗi yay masaba, dan tun a zuwana gidan idan na durƙusa gaidashi sai yakanji al'amarin da girma, dan bai saba ganiba ga yaransa.      “A tashi haka nan Yarinyar Dad, ALLAH yay miki albarka kinji, barka da arziƙi kwalin secondary ya samu, ALLAH ya kaimu randa zamuga na University haka”.        Cikin girmamawa nace, “Amin Dad, nagode sosai”.        Ban tambayi Aunty Shahudah ba, dan na zata dai ta koma gidan aurenta, Yaya Salman ko da Qaseem nasan basu dawo aikiba.     Ɗakina na nufa inda na iske Amina ta gyara minshi tsaf, sannan kuma an canjamin wasu kayayyakin cikima, ga sayayyar abubuwa dana tarar kala-kala, wanda nasan duk Dad ne, dan duk abinda ya sayama yaransa yanzu na lura bai iya mantawa dani a ciki.      Nayi wanka nai salla, Amina ta kawomin abinci, zama tai inaci muna hira tana bani labari muna dariya cikin farin ciki, mun daɗe da ita sosai a ɗakin kafin ta fita, ni kuma na kwanta danna huta kamar yanda Dad ya maido Amina ta sanar min.     Umarninsa kuwa nabi bayan nai salla na kwanta, kafin wani dogon lokaci barci yay gaba dani. ★★★★★         Wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar liyafar cin abinci Dad yasa aka shirya a gidan saboda ni, tunda na fito daga ɗakina idanun Yah Qaseem da Yah Salman na kaina, sket da rigane ƴan kanti a jikina, sket din jaa har ƙasa an masa ado da farin filawoyi, ya buɗe sosai hakan yasa sam baya nuna jikina, sai rigar fara itama mai ƙyau, ta zaunamin ɗas a jiki tamkar anyitane danni, na kawo ƙaramin hijjab na saka wanda ya rufemin ƙirjina, ga wani sassanyan ƙamshi ina fitarwa, tafiyata, maganata da komaina ni kaina nasan ya canja, dan karatun su Ummie bai tafi a banza ba.        Fiskata ɗauke da murmushi na gaida yayun nawa biyu waɗanda sai yanzune muka haɗu tun shigowata gidan, nasha mamakin yanda suka karɓamin babu hantara, saima kallon mamaki da ƙurulla da suketa bina da shi ko kunyar iyayensu dake wajen basaji.        Dad ne ya katse su dayin gyaran murya, duk suka kallesa, shiko yay ƙaramar dariya yana faɗin, “Oh kowa yaga ɗiyata ta canja shine ake kallemin ita kamar ido zai faɗo, to ƙwalelen kowa ɗiyata karatu zatayi  ko?”..      Yay maganar yana maido dubansa kaina.     Murmushi nayi daya bayyana jerarrun haƙorana farare tas, wanda ko acan baya da ake jifana da kalmar mummuna akan yaba ƙyawunsu sukam, nace, “Insha ALLAHU Dad”.         Baki Salman ya taɓe da faɗin, “Oh su o e dai an fara wayewa, kin canjafa sosai”.       Kallonsa nai ina kuma ƙayata fuskata da murmushi, nace, “To banda abunka Yah Salman ai kamar yanda ake samun cigaba a kwanaki, haka ake samu a rayuwa, kai dama tunaninka zanta zamane yanda nake?”.       Dukansu babu wanda baimin kallon mamaki ba.      Aamilah tace, “Tofa, wannan nan gaba ba ƙaramar ƴar iyayi za'aiba anan, da kinfi haka ƙyau da munsha kallo kam”.       Itama dariya nai mata ina wani juya idanu, “Banda abinki Aunty Aamilah ai ba ƙyawun fuska bane abin buƙata, ƙyawun zuciya shine cikakken ƙyawun da baya dishewa har ƙarshen numfashi, gwargwadon wannan ƙyawun da ALLAH ya bani ji nake da abuna, so abin ba'a ƙyawun fuska bane auntyna”.       Dariya Dad yayi yana cewa, “Yauwa ɗiyata, ai gara ki ringa ramawa kema”.      Nai siririyar dariya nima da nasan ta sake ƙular dasu, dan Mummy sai antayamin harara take,  niko nai mirsisi banbi takan ɗunbin mamakina da al'ajab dake shinfiɗe a fuskarsu ba.       Daga nan ban sake magana ba har muka kammala cin abincin, falo muka koma, duk da ba kowacce hira nake saka musu bakiba idan an sakkoni nakan tanka, dama Dad ne ke yawan sakko sunana a cikin firar, niko ban bashi kunyaba nake amsa masa, banayin shirun nan irin na da.       Duk ɗinsu nasan yau da mamakina zasu kwana, dan kuwa nazo musu da sabon salon da basusan ni da shiba a baya🥴😉.        Washe garima komaina kai tsaye nakeyi a gidan babu wani ɗar-ɗar na tsoron kowa kamar yanda nakeyi a da, ina kicin muna hira dasu Amina ina kallon yanda kuku ke girki dan nasa aniyar miƙewa na koya abubuwa aɗan zaman da zanyi kafin fitowar jarabarmu.       Zaune nake akan drawern kicin ɗin, hannuna riƙe da kofin shayi yanata turiri, ina sanye da kayan barci wando da riga kalar ruwan hoda masu haske, sai guntun hijjab a jikina.      Yah Qaseem ne ya shigo cikin shirin fita, dan kuwa sanye yake cikin Suit da suka ƙara fidda ƙyawunsa, dan shima dai ba daga bayaba wajen ƙyawu.      A kaina ya fara sauke idanunsa, babu zato nawa suka shige cikin nasa, janyewa nai cike da basarwa kamar bangansa ba.      Zama yay a ɗaya daga kujeru huɗun da aka ajiye a kicin ɗin da tebir tsakkiyarsu, zam Dani dai, yayma kuku Umarnin ya bashi abinci mai sauƙi.       Nace, “Yah Qaseem barka da safiya”.       Juyowa yay ya kalleni sosai fuskarsa na sake bayyana tsagwaron mamakina, niko na janye idanuna ina cigaba da shan shayina kamar banice nai maganarba.       Ganin yanda naine ya sashi sauke numfashi kaɗan yacemin, “Barkanki”.       Ban tankaba, bankuma sake kallonsa ba, har kuma ya kammala abinda yake ban gama shan nawa tea ɗinba tsabar shiririta, koda zai fice sai da ya sake kallona ina ganinsa.       Amina dake ƙumshe dariya tace, “Ƙawata, kinfa zoma jama'ar gidan nan da sabon salo alƙur'an”.      Murmushi nai mata ina taɓe baki kaɗan, “Nikam minayi Amina? Kune dai kuke ganin nazo da sabon salon kawai, amma ina nan a Bilkisu na”.       “Tab, inji wa? Wlhy kin canja sosai, kamarfa ba makaranta kikajeba yasin”.       Murmushi kawai nai musu ban sake cewa komaiba.        A ranar dai nasha labari wajen Amina, har rikicin da akasha tsakanin Aunty Shahudah da mijinta, da kuma barin ƙasar da tayi, nasha mamaki, naga kuma wautar su Dad a nan gaskiya, dan ni dai a ganina kamata yay su ɗauki hanyar gyara ɗabi'un yaransu musamman ma Shahudah da nake ganin tafi kowa nuna tsagwaron wayewar, amma gashi son zuciya ya sakasu sake dulmiyar da ita kuma,      “ALLAH ya ƙyauta” kawai na iya faɗa naja bakina na tsuke.     Da yamma Dad yace na shirya muje shopping, ban musaba kuwa nai shirina, ni da shi da Aamilah muka tafi.      Koda muka isa sai ta katsatstsare itace zata zaɓamin komai, da farko na bata dama, amma danaga duk abinda ta ɗauka baiyi dai-dai da tsatinaba saina dakatar da ita ina zaɓa, dan ko kayan kwalliya saita dinga ɗaukar mayukan da zasu sakani fari, niko batasan ba farin nake buƙataba, wannan baƙin da basaso ni shine abin sona, fatar dai ta goge tayi laushi kawai ya wadatar, banyi zariba na ɗiba komai dai-dai misali, ko kayama da yace na ɗauka nace masa atanfa nakeso to, dan naga duk kayana na gida yanzu babu suturun malam bahaushe, niko ina zan iya rayuwa babu kayan gado.      Bai hananiba yace na ɗauka, suma na ɗauki dai-dai musali mukaje Aamilah ta biya bayan ya ɗaukar mini waya shima muka fito.      Naji daɗin wayarnan sosai, dan na tsinci kaina amatuƙar farin ciki bana wasaba.      Na kumayitama Dad godiya da nuna masa farin cikina akan ɗauwainiyar da yakeyi dani, aduk sanda nake masa godiya idan ya saya min abu hakan na sakashi jin wani iri daban, yakanji daɗi kuma sosai a ransa, dan baisaba ganiba daga ƴaƴansa, basusan yay musu abuba suce sun gode, basu da laifi, dan tun farko ba'a nuna musu su godema wanda ya ƙyautata musuba koda a ƙanƙanin abune.           Kwanana huɗu da dawo gidan nacema Dad zanje gidan Inna Zainaba, baiko hanaba yace mu shirya ni da Aamilah driver ya kaimu.      Aiko wannan abu ya mata ciwo, dan masifa taitamin da muka tafi, saima tace mu sauketa a wani anguwa idan mun dawo mu biyo mu ɗauketa dan batai niyyar zuwa ko inaba, bazata wannan ƙazamar anguwar tasu Yaya Shu'aibu ba ta dawo ta kasa shan ko ruwa.        Tausayima ta bani nikam, dan kuwa arziƙin da take tunƙaho dashi wanda ya bata bai manta dasu talakawanba da take kallo ba komaiba.          Mun isa har ƙofar gidan, na shiga ciki da ɗokina ina kiran Inna.        A tsakar gida na isketa tana ɓarar gyaɗa, tunda na shigo ta ɗora idonta a kaina sai fuskarta ta canja, dan kuwa na kula bataso ganina hakaba fes, ban damuba naje na rungumeta ina hawayen farin cikin ganinta, Lawisa dake ɗaki ta bankaɗa labule ta fito, daka ganta kasan barci takeyi, “Waye haka yake mana ihu a cikin gid....”     Bata iya ƙarasawaba saboda tozali datai dani, ta wani taɓe baki tana jan tsaki ta koma cikin ɗakin.        Murmushi nayi ina muƙewa daga jikin inna, na durƙusa har ƙasa na gaisheta, sannan naja kujera na zauna ina tayata ɓarar gyaɗar.      Duk da bata sakarmin fuskaba mun ɗanyi hira, ananma ne nakejin ashe Yah Shu'aibu ya wuce ƙasar ghana karatu, na tayasa murna sosai, duk da naso muhaɗu shima yaga cigaban dana samu, amma dai inna ta bani Number sa dan Dad ya saya mata waya saboda suna waya da Yah Shu'aibun.      Banbi takan Lawisa ba har na baro gidan, bakuma ta sake fitowaba itama har na taho.      Biyawa mukai muka ɗauki Aamilah muka wuce gida, bankuma faɗama kowa ba tare mukaje ba.        Amina na tambaya ko akwai islamiyya a anguwar? Tako tabbatarmin akwaita, bazan iya zama hakaba, nako samu Dad da maganar inason shiga islamiyya tunda ta yamma sukeyi, shima bai hananiba, yace tom na binciko yaya abun yake?.      Tare da Amina mukaje, ta haɗani da yayanta da shima anan yake koyarwa, komai yay mana bayani na tsarin islamiyyar, nima nazo na sanarma Dad.    Sai cewa yay to itama Aamilah taje mu shiga tare mana da zaman banzan da takeyi.      Ai tunma Dad bai kai ƙarshen zancenba tai tsalle ta dire akan bataso, ita da zata bar ƙasar ta koma karatu miye na wahal da kanta shiga cikin kucakan yaran nan wai wani karatu kuma, ai dai ta iya na salla (Ita a nata tunaninma na salar kawai ake buƙata ta iya🤦🏻‍♀, ALLAH ka ganar damu gaskiya😢🙏🏻).         Nayi zaton Dad da Mummy zasu mata faɗa, a kuma tursasata dole ta shiga, amma sai naji babu wandama yace mata uffan, sai ƴar dariya kawai da Mummy tayi.         Nima ban tankaba, naje nai duk abinda ya dace na fara zuwa abuna ba tare dana sake bi takan Aamilah ba.       Da safe zuwa rana nakan nutsu wajen koyan girki a wajen kuku, da yamma na wuce makaranta.      Satina kusan biyu da dawo gidan saiga Nazifa, Ummie, Zuhrah, Rebecca sun kawomin ziyara, nayi matuƙar murnar wannan ziyara, dan kuwa kowama agidan ya fahimci hakan.      Ranar mun yini muna shaftarmu, sai dare suka wuce, ko islamiyya tare dasu mukajeta.      Tun daga sannan muka koma ziyarar juna akai-akai, nima Dad yasa duk aka kaini gidajensu, zuminci mai ƙarfi ya sake ƙulluwa tsakanina dasu da ahalinsu, harma yayan Zuhrah ya maƙalemin wai sona yake, ranar harda kuka nayi, dan nikam ba'a taɓa cewa ana sonaba sai ranar.     Ban dai bashi fuskaba, amma muna gaisawa ta waya lokaci-lokaci. ★★★★★★        Ba a wani ja dogon lokaci ba jarabawarmu ta fito, dukanmu mun sami sakamako mai ƙyau, ranar dai murna ai ba'a magana, dan kowa na gidan sai da ya fahimci ina tare da farin ciki kuwa.     Babu wani ɓata lokaci Dad ya fara nema min skull, da yake bakinmu ɗaya da su Zuhrah, yana tambayata zaɓin makarantar da nakeso na sanar masa wadda muka shirya.        To ashema Daddyn Ummie ne zai nema mana skull ɗin. A gurguje Please😹🥴⛹‍♀             Makaranta dai ta samu, inda cikin amincin UBANGIJI duk muka dace da cikar burinmu, dan kuwa mun sake tsintar kammu a muhalli ɗaya ni, Zuhrah, Ummie, Nazifa, Rebecca.          Komai dai an gama mana tsaf, hakama shirin tafiya nima an mani na ƴan gata, na bar gida cike da kewarsu musamman Dad da Amina dasu kuku.         Ƙaramin gida aka kama mana kusa da makarantar mu duka biyar ɗin, ɗaki biyune sai falo sai kicin kawai a gidan, duk kuma abinda zamu iya buƙata su Dad sun haɗa hannu wajen saka mana, an kuma haɗamu zama da wata dattijuwa yayar Dadyn Ummie, itace zata zauna damu saboda kula da duk wani motsinmu, kusan yaran yanzu sai ana saka mana idanu, duk ƙoƙarin tsare mutuncinka idan babu mai ƙwaɓa maka a kusa tuni kake kaucewa ko wata ƙawa ko sauriyi su sakaka a hanyar banza, hakanne yasa aka ajiye mana Gwaggo Hari danta zauna damu.        Ni da Ummie ne muka fara isa, sai ga Zuhrah, bayan magriba kuma sai ga su Rebecca, Zuhrah kam sai washe gari ta iso.      Yau kuma ga inda ƙaddara ta kawo bilynku, sai ku tayamu da addu'ar tsare mutunci da maida hankali akan abinda ya jehomu nanɗin😊...........✍🏻 Barkanku da juma'a, a sakani a addu'ar wannan rana mai albarka Please😑😥 Page 30 .............Salon rayuwa ya kuma canjawa, ga Bilkisu a matakin da zuciya bata taɓa hasasowa ba, balle sakashi a jerin burin mallaka, mun tsunduma a cikin karatu gadan-gadan babu kama hannun yaro. Sannan kamewar kai babu kula samari ko ƙawayen banza kamar yanda mukaima kammu alƙawari, inhar jerin ɗalibai masu ƙwazone, dolene ka samu sunan group ɗinmu a sahun farko, cikin lokaci ƙanƙani sunanmu yay kuwwar fita sararin subahana a makarantar.       Bawai a rashin kunyaba, ko nuna rashin tarbiyya, a'a tamu zarran mu a karatu take da kamun kai.        Ɓangaren samari akwai masu bibiyarmu akoda yaushe, sai dai sam basa samun fuska daga garemu, burinmu kawai cika alƙawarin da muka ɗaukama kawunanmu inhar muna cikin masu tsawon rai.        A haka kwanaki sukaita ja babu ko gargada a ciki, wataran a mori yini da kwana da farin ciki, wataran a riskeshi da saɓanin haka.      Kafin wani dogon nazari watanni biyar suka shuɗe mana, mukazo gida hutun sati buyu.          Bazance hutun baimun daɗi ba, sai dai babu wani farin ciki daya bani, dan na iske Mummy tayi tafiya itada Aamilah zuwa wajen aunty Shahudah, hakama Dad baya ƙasar, sai Salman da Qaseem kawai.       Tun saukata gidan na fahimci bazai zaunu a gareniba, dan kuwa ni kaɗaice mace a cikinsa, Amina ma bata zuwa kamar yanda Mummy ta bata umarni, wannan damar data samu ne ya sakata nufar ƙauyen babanta taɗan huta itama.           Ƙananun ƴan akuyancin da Salman ya fara nuna mini ne ya sakani tattara inawa-inawa tunkan abun yay nisa na fece gidan Inna zainabu kamar yanda na nema izini wajen Dad, nakuma taki sa'a babu musu ya bani dama ba tare daya bincikeni dalilina ba.          Ban wani samu gamsashahiyar tarbaba daga wajen Inna, sai dai hakan bai dameniba, dan hakan ya fimin zama cikin ƙattai.         Lawisa kam yanda ta shareni nima hakan na shareta, tadai san bata isa sakani wani aikiba a yanzu, dan wannan ba Bilkisun da bace data raina.         Nai amfani da damata kuwa, wajen ziyartar gidajen dangin mahaifina harma da sauran na mahaifiyata, duk da kuwa a baya sun nuna basa buƙatata.         Wasu a cikinsu sunji kunya sosai ganina a ƙyaƙyƙyawan yanayi, saɓanin abinda sukai mini fata, ni dai ban maida kaiba, koba komai dai na samu ladan zuminci, kuma duk duniya bani da kamarsu.               A haka na cinye nawa hutun, Dad ya turo mini kuɗin sayayyar komawata ta hannun Qaseem.         Dan haka dole na shirya na koma gida ana saura kwana biyu komawarmu, naji daɗin rashin iske Salman, sai dai shima Yaa Qaseem ɗin yawan kallo da yake bina dashi ya fara takurani, abin mamaki da zanje sayayyama shine ya kaini, sai kuma wani takalata yake da hira, ni abunma sai ya ɗaure kaina matuƙa.           Ban dai nuna masa komaiba ko a fuska, na samu muka kammala ya maidoni, tunda na samu na sheƙa ɗakina saina kulle kaina bai sake ganinaba ban sake ganinsa ba.          Sai dai bayan isha'i naji ana ƙwanƙwasa min ƙofa, koda na buɗe sai na ganshi, mamaki ya kamani, amma kafin nace wani abu sai cewa yay nazo na dafa masa shayi.             Ban masa musuba nabi umarninsa, duk da a zuciyata ƙunƙuni naketayi akan hakan, ga kuku amma ni zaizo ya saka aiki.         Abin al'ajab sai ya biyoni kitchen ɗin, yaja kujera ya zauna, ni dai inata neman tsarin ALLAH daga sharrinsa inma dashi yazo, ina gamawa kuma zan wuce ya tsaidani.            “Zauna mana, kina ganin gidan shiru babu wani abokin hira shine zaki barni ni kaɗai”.        Idanu kawai na ɗaga na kallesa, ganin ya kafeni da nasa idanun sai na sauke numfashi kaɗan, nace, “Yah Qaseem kasan ina shirine fa, gashi sammako zanyi idan ALLAH ya kaimu”.      Kamar bazai tanka minba sai kuma ya sake kallona, baice komaiba ya miƙe yana faɗin, “Muje to kina shirya kayan kina tayani hira”.        Tamkar zan fasa ihu haka naji, haka ya tasani gaba har ɗakina, ya zauna a kujerar gaban mirror ni kuma ina daga wajen gado saman kafet ɗin wajen ina kimtsa kaya, gaba ɗaya jina nake a takure, gashi ba wani hirar mukeba, ya zubamin idone kawai yana shan shayi, niko ina aiki.       Sauri-sauri na kammala nai gefe dasu, cikin kwantar da murya yanda zaiji tausayina nace masa barci nakeji.      Murmushi kawai yayi, ya miƙe ba tare da yace min uffanba ya fita.     Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi a fili ina faɗin, “Wannan takura har i...n...a...”         Na ƙare maganar da ɗai-ɗai saboda tozali danai dashi ya dawo baya, munafukin ashe ba tafiya yayba.      Kaina na sunkuyar ƙasa jikina na tsuma saboda tsoro.       Sai da ya gama ƙaremin kallo sama da ƙasa sannan ya juya ya fice abunsa.        Ai yanzu ko motsi banyiba sai da naja lokaci mai tsaho sannan, cikin sanɗa naje na rufe ƙofar tare da murza key.           Washe gari da safe, koda na idar da sallar asuba ban kwantaba, nai dukkan shirye-shiryen daya dace na fidda kayana waje, ɗaki na dawo nai wanka sannan na shirya tsaf na fito.      Nasan dai driver zai kaini, dan haka na nufi wajen motar dana kai kayana.       Cikin girmamawa yace, “Ai kayan suna can” yay maganar da nuna motar Qaseem.      Da mamaki nace masa, “Can kuma? Mikuma ya maidasu can ɗin Nura?”.          “Yallaɓai Qaseem ne yace a maida”.      Kafin na bashi amsa takun takalman Qaseem suka katseni, ba tare daya kalleni ba yace, “Malama ki zagaya mota sauri nake inada wajen zuwa”.      Tamkar na zauna naita ƙwaɗa ihu haka naji, dole nabi umarninsa naje na shiga inda ya buɗemin da kansa bayan ya shiga.        Haka muka tafi tamkar kurame, sai lokaci-lokaci yakan jani da hira, wata na amsa da baki, wata nace, “eh ko A'a”. Da haka muka iso.              Da kansa ya fito ya taimaka min muka shiga da kayan, ba tare daya zaunaba yace zai wuce.       Sake rakosa nayi wajen mota nai masa godiya.       Harya tada motar sai yace na bashi wayata.     Bashi nayi ina ƙunƙuni a zuciyata, duk da bansan miyayi da itaba naji a jikina number ta ya ɗauka, ya haɗo wayar da kuɗi ya miƙomin.      Zan zare wayar ya harareni, dole na haɗa da kudin na amsa nai masa godiya. ★★:★★:★★                   Tun daga wannan lokacin abubuwa suka fara sauyawa tsakanina da Yah Qaseem, tun yana kirana lokaci-lokaci harya fara komawa kullum.        Banaƙin ɗauka, dan koba komai matsayin yaya yake a gareni, sannan banjin zan iya tozarta zuri'ar Dad, Yah Qaseem kuma namijin da kowace mace zata iya sone, dan akwai ƙyawu, yana aikinsa, tunda nake dashi ban taɓa kamashi da wani abu mara ƙyauba, sai dai idan a ɓoye yake kayansa, wannan kuma ya rage nasa ai, matsalar sa dai rashin ilimin addini, wanda gaba ɗaya ɗiyan dad ya zama babban tawaya wa rayuwarsu, tsagwaron wayewarce kawai da duniya suka sani.           Munja kusan shekara ɗaya da rabi a haka, shi baice yan sonaba, sai dai alamomi, dan duk randa ya bushi iska zaizo busting ɗina da kaya niƙi-niƙi, zanma ce yafi kowa ziyarata a gidan, idan kuma naje hutu yata bani kulawa kenan harna taho, ko wani abu Aamilah ko Salman sukaimin sai yayi magana a yanzu.        Kulawar da Yah Qaseem ke bani a yanzu na kula tana ɓata ran Mummy, duk da dai bata magana ni nakan hasaso ɓacin rai a fuskarta.         Ni kaina take-takensa suna tsoratani, dan ni dai nasan yafi ƙarfina ta kowanne fanni, duk da canjin dana samu a rayuwa bansama raina zan samu koda wanda bai kaisaba matsayin miji, ni dai kullum addu'ata ALLAH ya bani nagari da zai zamarmin mijin marainiya.          Muna shekara ta uku a makaranta Yah Qaseem ya fiddo manufarsa fili a kaina a kaina, dan kuwa ya tabbatar min shifa sona yake.       Na shiga tsantsar ruɗani da wannan furuci, duk da na daɗe ina hasashen haka, dama a lokacin munje gida weekend ne, ALLAH ma ya soni ana gobe zan komane, aiko washe gari baisan na gudu ba.        Koda na sanarma su Ummie sai sukaita zugani akan na karɓa masa, dan Yah Qaseem ya cancanta, idan kuma bana sonshine to, amma sun daɗe su dama suna hasashen akwai wani abu a ransa game dani, sudai suna bani shawara nai amfani da damata gaskiya.          Ni dai kasa cewa komai nayi, dan idan nacema banson Yah Qaseem nayi ƙarya, ya fini komai a rayuwa, sannan ya cancanta a soshi, amma idan harna amsa to na ɗeboma kaina gagarumar rigima daga ahalinsa, musamman Mummy da tunkan ya furtama take ƙyamatar abun, inaga yanzun yace yana so.            Bai sake bi takaina akan sonjin amsar na aminceba koni ina sonsa, ya dai ƙara ninka kulawarsa kaina fiye da ta baya.         Yana cigaba da sakani sakin jiki dashi ba tare dana saniba nima.         Shi dai Dad koda ya fahimta baice komaiba, amma Mummy ƙiri-ƙiri ta nuna bazata saɓuba, hakama Aamilah da Salman.        Wannan soyayya ta Qaseem ce ta kuma ƙirƙirarmin samubawar tsangwama da tsana a gidan, a wajen Dad da yah Qaseem kawai nake samun sassauci, gashi Dad ba mazauni bane.           Cikin wannan yanayin tsangwama muka shiga shekarar ƙarshe a makaranta nida ƴan uwana guda huɗu.          ______________________            JAWAAD    ______________________         A ɓangaren Jay kuwa komai yana tafiya dai-dai, sai dai yau da gobe ba'a kiranta da nasara ko farin ciki ɗari bisa ɗari, dolene wataran tazo da daɗi, wataran saɓanin hakan.          Yana shekara ta biyu da rabuwa da Shahudah wani cigaba na musamman ya zomasa shida tawagarsa, dan kuwa wani horaswa ta musamman aka turasu zuwa ƙasar amuruka.       Duk masoyinsu dolene ya tayasu murna, inda ka cire irinsu Qaseem da suka gaza ɓoye hassadarsu akan maganar.       Dan kuwa dai kowa yasan badan matsayin kujerar Jawaad ta kai bane ya samu wannan cigaba, cancantace kawai da ƙwazonsa ya kaisa.       Da yake tafiyar gaggawace sai basu wani zaman ɓata lokaciba suka fara shiri, horarwas zata zama ta shekaru kusan biyu ce, amma bawai lallai su cika biyunba cif-cif, dan a ƙa'ida ma shekara ɗaya da rabine, sauran watannin da zasu biyo baya na wani tsarine daban.      Hakan yasaka su Aliyu duk da iyalinsu zasu wuce, Rose da Jawaad ne kaɗai babu mahaɗi🥴😂.           Ya sanarma Uncles nashi gaba ɗayansu, sun masa fatan alkairi kuma tare da addu'ar samo nasara.      Sai kuma shawarar mizai hana ya zaɓi ɗaya a yaran dangin a ɗaura musu aure ya tafi da ita, dan ba girmansa bane zama babu mace sam gashi har yana a shekara ta biyu da rabuwarsa da Shahudah, musamman a ƙasa irin wadda zaije yanzun akwai damuwa.      Bai wani jasu da nisaba ya nuna musu suyi haƙuri, maybe zuwa nan gaba idan bukatar hakan ta taso koda yana a cannne zaiyi magana.        Aiko wannan furuci nasa ya sakasu rabama ƴaƴansu lambarsa suyo farautar zuciyarsa bayan wucewarsa daya kirasu ya tabbatar musu ya sauka ƙalau.      Ko Baba ma sai da yay masa maganar auren kafin ya wuce, dan dama yana yawan masa shi dasu Umma, amma a koda yaushe yakan basu haƙurine da daɗin bakin su ƙara masa lokaci, bayason a sake tafka kuskuren baya kamar aurensa da Shahudah.        Sun masa fatan alkairi da addu'ar dacewa da mace ta ƙwarai da nasara akan abinda zashi nema................✍🏻 Page 31 ............A ɓangaren Shahudah kam taci alwashin sai Jawaad yazo ya nemeta har inda take, dan a nata hasashen gwala rayuwarsa take a haka.      Tasan ɗunbin son da yake mata dolene ya jigatu da rashinta, shekaru biyar ta ɗiba masa cif, sai ya koma ƙaramin mahaukaci a kanta sannan ta bayyana a garesa.        A shirmenta ko ganin ta cinye shekaru biyu bai nemetaba baisa taji a ranta akwai matsalaba, a'a a ganinta kawai ya rasa hanyar da zai iya ganintane, tunda Mummy ta tabbatar mata Jawaad baisan inda takeba har yanzu.        Ita kuma duk motsin Jay Mummy tana sanar mata komai harma Aamilah da Salman, wani lokacinma harda Qaseem, ko dangane da tafiyar Jawaad Qaseem ne ya sanar mata komai.         A duk sanda akai mata zancensa danne zuciyarta kawai takeyi, amma kewarsa da ɗunbin begensa kullum sake mamaye zuciyarta yakeyi, batason ya kalleta matsayin mafi arha a mata shiyyasa tai dauriyar riƙe ajinta gam tunda ta ƙetaro kasarsu tai kunnen uwar shegu dashi, sai dai a kullum hotonsa shine abin kallonta, hakama duk wata kafar yaɗa zumunta datasan yanada accaunt a wajen tana bibiyarsa da sunan da ba nataba.        Ta kasa kula kowane saurayi, ta dai yarda kuyi abota amma ba soyayyaba, to kuma dama can dai gaskiya Shahudah bata iskanci, koshi Jay shaidane akan cikakkiyar budurwa ya sameta, dama can iskancinta baya wuce shan minti, amma bata yarda tarayya da waniba, takance wannan mallakin Jay ne tunma a wancan lokacin, to a yanzunma dai da harma yanzu take ɗauka da aurensa kanta tana taka tsantsan, sai dai fa iya shege da duk wani dandali na taruwar wayayyu tana a wajen babu abinda ya dameta, tunda bawai muhimmancin auren ta saniba balle ƙa'idojinsa, a ganinta duk abinda takeyi ƴancinta ya bata damar yin hakan, balle ta dawo inda babu ruwan wani da wani. A gurguje⛹‍♀😏 _________________________        BILKEESU _________________________              Rayuwa tai nisa, sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun zama yini, yini ya rikiɗa dare, kafin wani dogon nazari daren ya haɗa kwanakin da suka bada satittikan da suka dunƙulle wattani, sai gamu da shekara ɗai-ɗai har huɗu cif a makaranta, yanzu haka jarabawa biyu kacal ta rage mana kammala jarabawar ƙarshen zangon karatunmu na.      Abubuwa da dama sun faru, wasu a iya tunawa, wasu ko zuciya ta manta saboda hidimomin yau da kullum, mun kwankwaɗi madarar ilimi wadda muke addu'a da fatan ta zamewa rayuwarmu dana ƙasa damu alkairi.      Zakusha mamaki idan kukaji a cikin baƙin al'amuran da suka zoma rayuwata ciki harda soyayyar Yah Qaseem datai ƙarfi a tsakaninmu,       Hoo duniya makarantar makaho, kai mai idonma ba ɗage masa ƙafa takeba, wai ni Bilkisu ƴar baƙa mummuna ƴan ƙwalisar samari masu ji da ƙyawu da ƴan canji a aljihu irinsu yaya Qaseem keso? To lallai dai abin da mamaki, sannan yana buƙatar alamar tambaya, shin sone na gaskiya? Kokuwa sone na sha'awa?.       A wannan kaftawar da zamu farane kawai kowa zai iya fahimtar hakan, danni dai har yanzu baiji amsa tayinsa daga bakina ba.      Dan duk wani salon rayuwa da iya zama da jama'a a yanzu Alhmdllh na san gwargwadon ilimin da UBANGIJI ya bani.           Maza da yawa surar da ALLAH ya bani ke ɗibarsu zuwa gareni, ba wai ƙyawuba, duk da ƙoƙarin killace jikina da nake ban tsiraba a wajen mayu irinsu Yah Qaseem. _________________________              Uzirin gaggawa ya sakani dawowa gida a weekend ɗinnan domin ɗaukar abinda na manta, babu wanda yasan da zuwana, dan motar haya na shigo.        Tun isowa gidan namu gabana ya faɗi, dan kuwa da motar ƴan sanda naci karo, na tura ƙaramar ƙofar gate na shi da sassarfa, dama dagani sai handbag ɗita.         Zan shigo ƴan sandan zasu fita, dan haka suka bani hanya saboda na riga na kawo jiki, koda na shigo sukuma sai suka fice, na bisu da kallo kafin na maido kan Amina dake ta faman kuka ga mamanta itama tanayi.        Sai Dad da Mummy dake tsaye sunata faman faɗa akan maza su Amina su fice musu da ga gida, inba hakaba zasu bama ƴan sandan da suka fice dama su tafi dasu.       Gaba ɗaya ban fahimci yaren kowa a cikinsuba, na sake maida dubana ga Yah Salman dake kan mota zaune yana wani munafukin murmushi, Aamilah na daga gefensa tana latse-laste a waya.          Nai saurin ƙoƙarin riƙo hannun Amina da suke ƙoƙarin fita, amma sai ta fisge a fusace harda bigemin hannu ta fice.           ‘Lallai akwai matsala’ na ambata a zuciyata ina binsu da kallo har suka fice......      Kiran da Dad ke minne ya katse tunanina, na sauke ajiyar zuciya ina nufarsu hankalina duk a tashe da tunanin mi akaima Aminar?.           Ina isowa gabansu Dad abinda ya fara faɗamin shine, “Ƴata rabu da waɗancan masherantan mutanen kinji, dan ba mutanen arziƙi bane masheranta, duk ƙyautatawar da mukaima rayuwarsu sai suka ƙare da nemanmu da sharri”.       Duk da bansan kan al'amarinba sai naji kalamun dad basumin daɗi ba, dan haka nai murmushin yaƙe kawai ina faɗin, “Wani abune ya faru Dad?”.      Kafin ya bani amsa Mummy ta katsesa da sauri, “Daga shigowarki Bilkisu, ki shiga ki huta mana koma minene zakiji daga baya”.         Kaina kawai na iya ɗaga mata, suka shiga ni kuma nabi bayansu.      Dad dake zama a kujera yay min tambayar lafiya nida nake ƙoƙarin zana jarabawa ta ƙarshe nazo gida?.         Sai da na durƙusa a gabansu na gaishesu sannan nai masa bayanin abinda ya kawoni.          Ganin ya gamsu da maganatane ya sakani miƙewa na nufi ɗakina, dan duk tunanina a dagule yake da abinda na gani, sam zuciyata ta kasa yarda su Amina ne basu da gaskiya. Akwai dai abinda tabbas shi Dad bai saniba an ɓoye masa.       Har nai wanka na fito domin cin abinci wannan lamari na sukata, babu kowa a falon na wuce kicin, a can ɗinma ban samu kowa ba, to dama wa zan gani? Amina ce dai da kuku kuma ga ayanda na iske gidan.          Babu komai a kicin ɗin, amma da alamun dai anyi abinci, fitowa nai dan na san yana Dani, ilai kuwa a can na hangosa, tunani baisa hankalina ya fara kaiwa canba.        Ɗiba nai na koma ɗaki kawai, duk da uwar yunwar da nakeji sai kuma nama kasa cin abincin, dan laumata ɗaya jal na ajiye cokalin ina sake karanto damuwar dake tattare da Amina.      Amina ta taka rawar gani a rayuwata ta gidannan, dan ta soni a lokacin da kowa ya tsaneni, ta ƙaunaceni a lokacin da kowa ke ƙyanƙyami na, to ni tayaya yanzu zan sami nutsuwa a halin da take ciki?.      Bani da ikon fita gidan a yanzu, amma nayi alwashin zuwa anjima ko a sacene sai naje gidansu Amina.       Da ƙyar naci rabin abincin dana ɗebo, na zuba tagumi ina cigaba da saƙawa da kwancewa.          Bayan sallar isha'i na fahimci gidan yayi shiru, a hankali na leƙo falon, babu kowa a ciki, yau ko tv ma ba'a kunnaba, cikin sanɗa na nufi kicin, ta ƙofar baya na fita a hanzarce zuwa harabar gidan, nanma sai da na wawwaiga na tabbatar babu mai kallona sannan na nufi gate.      Baba mai gadi ya taso yana tambayata ina zanje, saurin masa alamar yay shiru nayi, murya ƙasa-ƙasa nace, “Gidansu Amina zanje baba, dan ALLAH ko wani ya tambaya karkace na fita, duk da nasanma da wuya asan bana nan”.      Kansa ya ɗagamin, ni kuma na fice da sauri...............✍🏻 Page 32 ..............Gidansu Amina yana maƙwaftaka da gidanne, dan duk anguwar kusan shine ginin talakawa, Amina ta taɓa sanarmin Babanta ne ya saidama Dad filinsa kafin ya rasu, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH karya bar wani ya amshe gidan dasu Amina suke ciki danya lura masu hannu da shuni duk sun saye gidajen talakawan wajen sunyi gine-gine saboda ƙyawun anguwar, shiko gidansune na gado bayason yaransa su rasa.       Wannan alƙawarine da dad ya riƙe ya saka gidansu Amina zama zakka a anguwar duk da kuwa ansha ƙulla musu dan a mallaki gidan hakan bata faruba.           Da Amina na fara tozali tana kwance a ƙofar ɗakinsu lulluɓe da bargo tana rawar sanyi, na ƙarasa gareta ina ambaton sunanta.      Dai-dai nan mamansu ta fito tana ɗangyasa ƙafarta dake mata ciwo, saurin dakatar dani tai a zafafe.      Na tsaya cak ina kallonta da mamaki, dan nasan matar tana sona sosai, tana ɗaya daga cikin waɗanda suka koyamin dabarun rayuwa da mutane.        “Mi kikazo yi mana a gidan, ki fita dan ALLAH, bana buƙatar sake ganin fuskar kowa daga ahalinku, dan haka fita kona miki abinda baki taɓa tsammaniba....”         Kaina na duƙar ƙasa gabana na sake tsananta bugu, murya na rawa nace, “Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kimin uziri bansan komaiba dangane da abinda ke faruwa ba, babu kuma a wajen wanda zanji sai ku, nasan tunda naga fushi a fuskarki an miki ba dai-dai bane, dan ALLAH ki lamincemin mu raba wannan damuwar tare ko zanji sassauci a raina, da......”      Saurin dakatar dani tai da fadin, “Damuwarmu ai tafi ƙarfin mu kasaftata wani ya samu wani yanki a ciki, an rigada an cuta mana, saboda bamu da komai kuma an nuna mana fin ƙarfi, Bilkisu jin abinda ya faru bashi da amfani a gareki sam.....”       “Yana da amfani Mama, koba komai ƙila inada gudunmawar da zan iya badawa”.         “Baki da ita Bilkisu, dan haka fitar min daga gida”      Ko motsi kasawa nai, hawayen da nake riƙewa suka gangaro bisa kumatuna, juyawa nai a hankali zan fice muryar yayan Amina malamin islamiyyarmu na tsinkayo yana ma mamansu magana.        “Mama karki haka mu saurareta, dan muma munsan bata san komaiba tunda batanan, kuma koda tana nan bata da wani ƙarfin ikon sawa ko hanawa a gidan muma shaidane”.         Mama ta sauke numfashi da cewa, “Hakane, dawo Bilkisu”.        Da sassarfa na juyo garesu, na tako inda Amina take na durƙusa ina yaye bargon da take lulluɓe, ƙara ta ƙwalla, hakan ya sakani saurin ja baya a firgice.      Mama ta ƙaraso kusa damu tana mata magana, sai da ta sami nutsuwa ne maman ke cewa, “Kiyi haƙuri Bilkisu haka takeyi wanu lokacin, abu kaɗan ke sakata firgita yanzu”.        Sosai mamaki ya kamani, na kalli maman ina tambayar to minene sanadin hakan? Dan ni dai nasan Amina mace ce mai tarin nutsuwa a komanta.           Mama ta miƙomin kujera ƴar tsigunno, amsa nayi na zauna ina mai ƙarajin tausayin Amina.       Itama zama tayi daga ƙofar ɗakin, yayan Amina ma ya zauna daga ƙofar ɗakinsa.          Kallon mama nayi ina ƙara jeho mata tambayar abinda ke faruwa da Aminar.       Mama ta sauke numfashi mai ciwo tana share hawaye, tace, “Bilkisu fyaɗe akai mata a cikin gidanku, sai dai mun gaza tantance wanene yayi?, saboda abu suka bata tasha batare data saniba”.         Bansan sanda na koma ƙasa daɓas ba nai zaman ƴan bori, har taune harshena nake wajen faɗin, “Mama fyaɗe fa?”.          Kasa bani amsa tayi saboda kukan da takeyi, sai yayan Amina ne cikin takaici yace,         “Abinda ya faru kenan Bilkisu, munje mun faɗama Alhaji amma hajiya ta katsatstsare a kan sharri akaima ƴaƴanta, bayan kuma a idon mai gadi suka fiddo Amina cikin wani yanayi ita da Aamilah, munje mun ɗakko ƴan sanda shine suka basu kuɗi mukuma aka ƙaryatamu, wlhy badan mama ta hananiba da saina kaisu kotun musulinci, amma yanzu mubarsu ALLAH ya tsayar damu a kotunsa, dan yafi kowa sanin gaskiyar abinda ya faru”.       Kuka nake sosai, wanda har su mama sai da suka koma lallashina, ganin dare yayi suka lallaɓani na komo gida.         A falo naci karo da Yah Qaseem, da alama dai ɗakinama yaje bai ganniba, na share hawayen dake gudu a fuskata, ba tare dana kallesa ba nace masa “Ina yini”.         Cikin kafeni da idonun da nakeji suna yawo a kaina ya amsa mani, ya ɗora da faɗin, “Ina kikaje haka? Na leƙa ɗakinki nama zata ko kina bathroom ne?”.       Kaina kawai na girgiza masa amma na kasa magana, hakan ya sakashi takowa gabana dab, baya na matsa dan banason sunamin irin wannan abun haka.      Kafin yay magana nai saurin faɗin, “Kaina ke ciwo Yah Qaseem, ina daga baya ina shan iska dan ina tunanin zafine”.       Kamar bai gamsu ba, sai kuma cayay, “Okey to ALLAH ya ƙara sauƙi, kinsha magani ko?”.     Kaina na ɗaga masa..  Yace, “To kije ki kwanta, dama nazo naji miya dawo dake gida keda ke shirin dawowa gaba ɗaya”.       Sai da na raɓashi zan wuce sannan nace, “Babu komai, da safema idan ALLAH ya kaimu zan koma, dama abu na manta kuma ana buƙatarsa shine nazo ɗauka”.       Banji amsar daya baniba, dan tuni na shige, nakuma dannama ƙofata key dan karma yace zai biyoni.       Jingina nai da ƙofar ina kuma fashewa da sabon kuka saboda tausayin Amina, inhar zasu iya cutar da yarinyar data ɗauki tsahon shekara tara tana musu bauta to ni ta yaya zan tsira a wajensu? Miyasa zasuma Amina haka? Duk taka tsantsan ɗin yarinyarnan da riƙon addininta da martaba, Amina ko zama babu hijjab batayi a gidan, duk zafi ta gwammaci haƙuri ta zauna a hakan duk dan gujema irin wannan ƙaddarar, “Wane tsinannene ya aikata wannan aikin? Sai yaushene ƴan sandar ƙasarmu zasu ajiye kuɗi su ɗauki gaskiya? sai yaushene masu kuɗin ƙasarmu zasu fara yarda da kuskuren ƴaƴansu su ajiye son zuciya!!” na ƙare maganar da zubewa a ƙasa ina mai tauna leɓena alamar jin zafi mai yawa a zuciyata.      Ni kaina bansan tsahon lokacin dana ɗauka ina kukaba, ban taɓajin takaicin sakacin Dad ba irin yau, dan inaji a jikina koni akaima abinda akayiwa Amina bazai ɗauki matakiba, a halin yanzu kuwa ai nice a halin hau, dan kuwa zasu iya min kwatankwacin yanda sukai mata.         Kuka dai na yisa harna rasa hawayen zubarwa, rayuwar gidan haya da talauci, maraicin iyaye, matsalar Jazuga, haɗarin tsintar kai a matsayin mai kisan kai, faɗawa hannun su Uwargida, kuncin zama gidan Inna zainaba, duk sun faru, yau kuma ga jin daɗin da cigaban rayuwa amma cike take da ƙalubale kala-kala tare da firgicin rashin tabbas, shin mutanen duniyane a haka? Kokuwa duniyarce a haka?, wanene zai bani amsar wannan tambayar ko zata zamemin hasken fahimtar cuɗaɗɗun al'amuran cikinta?.           Yanda naga rana haka naga dare, sai gabannin asuba barci yaɗan saceni, hakan yasa na tashi a makare, ina yin salla nai shiri a gurguje, banama son ganin kowa a gidan har Dad ɗin kansa, dan haka na rubuta masa text message akan na wuce dan yau ina da jarabawa, naji bazan iya kwana biyun da nai niyyaba sam.           ALLAH ya soni sanda na fito ana wankema Yah Qaseem motane, bai kai ga fitowa ba.          Gidansu Amina na shiga, mama na tsakar gida tana damun kunu, na duƙa na gaidata, cikin bina da kallo da takeyi tace, “Bilkisu miya sami fuskarki haka ne?”.       Murmushi nayi ina haɗiye kukan dake shirin zomin, nace, “Babu komai mama, zan koma makarantane, amma insha ALLAHU baifi nanda kwanaki goma zamu dawo gaba ɗaya ba, akwai wani likita zaizo har gida ya sake duba jikin Amina, insha ALLAHU zai bata dukkan taimako, na kuma muku alƙawarin koba yanzuba saina binciko wanda ya aikata wannan ɓarnar kuma an hukuntashi insha ALLAHU”.       “Ah ah Bilkisu, karki saka rayuwarki a haɗari kinji, koma wanene mun barsa da ALLAH, zai saka mana, mun gode da nuna kulawarki a garemu”.        “Mama barin wanda ya aikata yaci bulus shine yake nuna na gama saka kaina a haɗari, dan abinda akaima Amina, nima zasumin kwatankwacinsa ai, ke dai kimin addu'a kawai”.          Addu'oin fatan alkairi mama ta shiga jeramin, kafin tace na zauna na karya, haƙuri na bata akan bazan iya cin komaiba, sannan inason na wucene dan banason wani yace zai kaini a gida.       Haka na wuce bayan na leƙa na duba Amina dake barci, a motarma lokaci-lokaci haka naita share hawaye, har ALLAH yasa na iso lafiya.        ★★★★★             Shigowata gidan duk sai suka taho da murnar tarata, sai dai kuma duk sai sukai turus suna kallona.       Zuhrah tace, “Bily lafiya kuwa? Kinga fuskarki a madubi safiyar yau? K..........”        Kafin takai ƙarshe Rebecca ta amshe da cewa, “Ku wannan kuka ne, Bily miya faru?”.     Duk sun rikice, Nazifa da Ummie sukazo suka kama hannuna, ni dai ban iya bama kowannensu amsaba, kallonsu kawai nake tamkar wata gunki, hakan ne ya ƙara tada musu hankali.        Dai-dai Gwaggo hari ta shigo gidan, da gani daga wani waje take, itama da mamaki take kallona, sai dai batace komaiba har muka shige.       Rufeni sukai da tambayoyi har Gwaggo Hari, sai ma na rasa nawa zan amsa.       Ganin sun matsa ne nace musu banajin daɗinefa, subar ɗaga hankalinsu.      Badan sun yardaba suka barni.............✍🏻 Page 33 ................Duk wanda ya sanni zaisan inada damuwa tun dawowata gida, a kwana na uku da dawowata mukai ɗaya a cikin jarabawar data rage mana, ranar ƴan uwana suka nunamin ɓacin rai sosai akan abinda nake ɓoye musu, dan badan taimakon Nazifa dake kusa daniba da babu abinda zan rubuta sai shirme a takardata.       Ba komai zai jawo hakanba kuma sai halin da nake ciki na ɗunbin tausayin Amina da fargabar tawa rayuwar idan na koma zaman gidan yanzu.          Ganin sunyi fushi na basu haƙuri, sannan na ɗora da faɗin,          “Ƴan uwana kuyi haƙuri, zan aikata muku babban laifi na canja burinmu nason zamowa ƴan jarida, yanzu na gane ba wan nan bane abinda nake buƙata, martaba da kare sauran ta ƴan uwana itace abar buƙatata”.        “Wace magana kikeyi haka bily, mu bamu fahimceki ba” Rebecca ce mai maganar.        Zama nai da ƙyau na shiga zayyano musu abinda na gani a gida, wanda inaji a raina cewa na manto abinda na koma ɗaukane dan na iske wannan iftila'in, dan ƙila daban ganiba babu mai bani gamsashen labari.            A take naga duk sunyi murmushi mai ciwo, Nazifa ta miƙe tabar wajen tana kuka.      Da kallo mamaki na bita, dan bansan manufar kukan nata ba, “Nazifa!”       Na ambaci sunanta, hakanne ya sakata tsayawa cak sai dai bata juyo garemu ba.      Miƙewa nai tsaye na taka zuwa gareta na dafa kafaɗarta, “Nazifa miya sakaki kuka a wannan maganar?”.          Sai da taja wasu sakanni kafin ta juyo gareni, sosai take hawaye wasu nabin wasu, ta dafa tawa kafaɗar tana sake fashewa da kuka mai ciwo. Ban hanata ba, hakama sauran ƴan uwana babu wanda yay mata magana.        Rebecca dake bayanmu tsaye tace, “Bilkisu, kukan da Nazifa keyi kukane namu mu duka, duk da dai ke mun ɓoye miki dalilin kukan tuni, sai dai maganarki ta yanzu ta sosa mana inda ke mana ƙaiƙayi harma da tuna mana abinda ya shuɗe”.         Kallonta nayi sannan na maida gasu Ummie, kukan da Ummie take har yamafi na Nazifa, dan numfashinta har sama yake tamkar zai shiɗe ta fusgosa da ƙyar.          Hankalina ya sake tashi mtuƙa fiyema da da, nace, “Ƴan uwana ku buɗemin abinda kuka rufemin ko zuciyata zata samu sukuni dan ALLAH”.         Shiru sukai kusan na mintuna biyu, kafin Zuhrah tazo ta kama hannuna dana Nazifa zuwa inda muka taso.         Duk zama mukai har Rebecca.          Zuhrah tace, “Bilkisu kinsan dai mun taɓa baki labarin ƴar uwarmu data rasu sanadin sikila ko?”.         Cikin ɗaga kai nace, “Tabbas anyi haka”.        Zuhrah ta share hawayenta yana riƙo hannuna, “Bilkisu tabbas ƴar uwarmu nada sikila amma sanadin baƙin cikin fyaɗe ta rasu”.      Cikin matuƙar razana na zabura, har taune harshe nake wajen ambaton “Fyaɗe fa kikace Zuhrah?”.         “Tabbas fyaɗe Bilkisu, ni Nazifa nida ita akaima Fyaɗe a cikin gidanmu sunje mini weekend ita da Ummie, amma abin mamaki da al'ajab sai aka rasa wanda ya aikata mana wannan ta'asa, dan kuwa kamar yanda kika bamu labarin nan sai da aka bugar da Amina muma haka akai mana wlhy. Babu kalar binciken da ba'ayiba amma har yanzu babu wani bayani, kwannamu uku a asibiti ƴar uwarmu ta rasu saboda yanayin jikinta bayason wahala, da kuma dai ƙarar kwana. Bilkisu wlhy ba ɗiyan talakawa kawai akema fyaɗe ba, sannan ba mata kawai ba, harma da maza, ƙanin Rebecca an masa fyaɗe ta hanyar luwaɗi shima kuma ya rasu”.        Kasa magana nai saboda kuka, jikina sai tsuma yake, hakan yasa na miƙe a fusace ina nunasu, “Amma duk da wannan abubuwan da suka faru da rayuwarku kuka ɓata lokacinku wajen tsara burinku akan business kawai? Rayuwa a hannun ALLAH take, amma baka yanke ƙauna daga rahamarsa, shiyyasa a kullum muke zama masu buri, kuyi haƙuri duk da ni ɗiyan talakawace, ban tashi gidanmu naga kuɗiba hakan bazaisa na cigaba da zama a cikin burinku ba gaskiya”.      Dukansu kallona sukai, bance musu komaiba naja takarda da biro nai rubutu na tura a tsakkiyarsu.        Dukansu kallon takardar sukayi, kafin su maido kallonsu gareni.           “Wannan daga yau ni Bilkisu Adam makaho shine burina, ban isa canjawa gaba ɗaya ba, amma ko alwashin dana ɗauka akan Amina da Nazifa da ƙanin Rebecca da ƴar uwarmu data rasu suka cika naci riba”.          Rebecca ta kamo hannuna ta ɗora nata, itama tace, “Daya yau nima Rebecca ina tare fake Bilkisu”.        “Nima ina tare daku” cewar Nazifa tana aza hannunta akan na Rebecca, Ummie da Zuhrah ma duk suka ɗora tare da bamu goyon baya.       Wannan shine sanadin burinmu, a haka muka ƙarasa jarabawar data rage tare da bikin karramawa da aka gudanar.       Ranar Dad da kansa yazo ɗaukata shi da Yah Qaseem.      Nayi farin cikin ganinsu, haka suma sun tayani farin ciki.       A gidanma nayi mamakin tarbar dana samu daga Mummy. *_RAYUWA SABON TAKU!_* .............Dole na kira yanayina na yanzu da suna rayuwa sabon taku, dan kuwa nazo da sabbin salon taka tsantsan a gidan, na sake komawa islamiyya, inda a kullum nake samu na leƙa Amina, duk da yanzu dai ta warke a jiki, sai dai ciwo a zuciya da kuma firgita da takeyi musamman idan taga maza kusa da ita dab. Ina tausaya mata, shiyyasa a kullum bana mantawa da ita a cikin addu'ata.           Ina fuskantar sabuwar tsangwama daga Mummy da Aamilah akan son da Yah Qaseem ke iƙirarin yanamin, wanda ni banma ɗaukesa a komaiba duk da naji zan iya zama dashi matsayin miji inhar da gaske auren nawa zaiyi, kuma bazance bana sonsaba, sai dai ban ƙwallafa rai ba, idan na samu zan amsa, idan saɓanin haka yazo zan zamto mai haƙuri.        Rashin Amina ya saka ayyuka da yawa na gidan dawowa a kaina, musamman gyaran sama ɗakin Mummy da Dad da falon saman, sai ko ɗakin Yah Qaseem daya wajabta min shima, da farko har Aamilah da Salman suma sun fara sani, amma sai Yah Qaseem yay magana akan karsu ƙara, matarsa ba ƴar aiki bace.      Harga ALLAH yaban dariyar wannan furuci, yayinda ya ƙona zuciyar Mummy harta yini bata amsa maganata tana fushi dani, Aamilah kam harda cewa wai Mummy ta bincikeni ina niyyar cinye mata kurwar ɗa, dama ta daɗe da zargin ni mayyace.      Ban damuba, danni yanzu a rayuwa mukuma ya rage ban ganiba? Sai dai zaman takewar aure da nakeji jama'a na kira da zaman haƙuri shima.        Kamar kullum yauma na tashi da wuri na kimtsa ɗakina nai wanka, na fito cikin doguwar baƙar riga zuwa kicin, kuku ne kawai keta kiciniyar ɗora breakfast, mun gaisa cikin mutuntawa na haɗa tea na fito falo.        Shi kaɗai nasha saboda sabon makaranta, yanzunma sai ban iya daurewa saina sha ɗin, dan breakfast ma saina ka sha biyu banyiba ko ƙarfe ɗaya.       Sallamar Yah Qaseem ce ta sakani ɗago idanu na, na kallesa ina amsa shi.      Yayi ƙyau cikin suit ɗin sosai, duk da baisa rigar saman ba tana riƙene a hannunsa.        Fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna a gefena dab, hakan ya sakani matsawa nikuma ina gaidashi.     Bai amsaba, sai tambaya daya jeho mani,      “K wai yaushe zakibar gidadanci ne? A zahiri dai ba Bilkisun da bace bagidajiya, amma a baɗini babu abinda ya canja na ƙauyancinta”.      Duk da maganarsa tamin zafi sai nai murmushi kawai, na cigaba da juya cokalin dake a kofin shayin ba tare dana bashi amsaba.        “Baki jinane?” ya sake min tambaya?.        Haɗiye takaicin daya tsayan a maƙoshi nayi naɗan kallesa na ɗauke ido lokaci guda saboda tsareni da yay da kallo, “Naji Yaya, sai dai kasani ni abinda nakeyi ba ƙauyanci bane ko gidadanci, hakan koyarwar addininmu ce, niba muharammarka bace, bamuda hurumin haɗuwar jikin juna a halin yanzu, kodan gujema sharrin shaiɗan mai saka wasuwasi a zukatan bayin ALLAH”.        Jikinsa ya kwantar a kujerar yana ɗan taɓe baki, yace, “Da haka ake cutarku ai dama ku kullum, shiyyasa hausawanmu sunfi kowa rashin wayewar kai, shikenan sai akace dan namiji ya zauna kusa da mace, koya kama hannunta, koya rungumeta wani abu zai faru?”.          Mamaki ya kamani jin furucinsa, sai bance komaiba na cigaba da juya cokalin a cikin shayina nidai.     Babu zato naji ya ɗora hannunsa a saman nawa yana faɗin, “Bani nasha ni”.       Ban sakar masaba, duk da jinake kamar na make hannunsa daya ɗoramin, nace, “Bari na haɗo maka wani to”.      “No barsa, wannanma ya wadatar, sai dai idan bakiso nashanye miki” Ya faɗa yana sake matsowa jikina.      Sakar masa kofin nai kawai na miƙe nabar masa kujerar, domin neman hanyar kuɓuta, ya bini da kallo harna shige kicin.           A ɗan lingun da zai sadani da kicin ɗin na tsaya ina roƙon UBANGIJI akan wannan rayuwar yahudanci, “Ya ALLAH ka kareni ka karemin martabata da mutuncina harna bar gidannan zuwa gidan aure na, ya rabbi ka hananeni saɓa maka bisa ganganci komin farin cikin da hakan zai sakani”.     Na haɗiye hawayen dake neman zubomin kafin na ida shiga kicin ɗin, na tarar kuku harya shirya masa abinci saboda shi yake fara fita a gidan kafin kowa.     Ɗauka kawai nai na kawo masa falon, na iske yana wayane yana shan tea ɗin daya amsa a hannuna.      Yanda yake wayar a zafafe yana ambatar sunan wani Jawaad ya sakani kallonsa, fuskarsa harta koma jaa saboda bala'i kasancewarsa farin mutum sosai.       Koda ya gama wayar tsaki yayta ja da ambaton sai ya kawo ƙarshen iskancin Jawaad ɗin.       Nidai bance dashi uffanba, na haɗa masa abincin na canza kujera can nesa dashi.       Bala'i na cin ransa bai wani ci abincin kirkiba ya tashi zai fice, gabana yazo ya ranƙwafo wai zaimin kiss, nai saurin kaucewa jikina har rawa yakeyi.      Wata banzar harara ya watsamin yana jan tsaki.      “K baƙauya karki ƙaramin ɓacin rai mana”.       Fuska na ɓata nima, nace, “ALLAH ya baka haƙuri Yaya, sai dai ina sake tuna maka bai daceba, kabari sai munyi aure”.      Bai tanka maniba ya fice abinsa yana sake jan wani wawan tsaki.        Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina harar bayansa, kai wlhy da sake, dolene nasan maiyuwa da wuri kafin wankin hula ya kaini dare a gidan nan.        Kayan da yaci abincin na tattare na gyara falon, na hau sama canma na gyara da ɗakin Mummy, dan tana ɗakin Dad tunda yana gari.      Sai da komai naga yamin fes sannan na fito harabar gidan tacan baya na zauna ina wani bincike ta waya.       Naja dogon lokaci a wajen kafin na shiga cikin gida saboda kiran Dad daya shigo min a waya.       A d/table na iskesu su duka, dan haka na fahimci dalilin kiran Dad.      Sai da na duƙa har ƙasa na gaishesu shi da Mummy sannan na gaida Aamilah da Salman lokacin da nake zama.         Anacin abincin ana hira, duk da dai babu bakina a ciki sai lokaci-lokaci, shima Dad ke sakoni a maganar na bashi amsa.      Bayan mun kammala ne Dad yace na sameshi sama zamuyi magana.         Duk da inata tunani akan wace magana haka na miƙe nabi bayansa.       Sai da ya zauna a kujera sannan nima na zauna a ƙasa, yace na koma kujera nima, amma saina bashi haƙuri akan nanma ya isa.      Murmushi kawai yayi yana gyara zamansa, idonsa a kaina yace, “Bilkisu nasan zakita mamakin wannan kira ko?”.        Kaina na jinjina masa ina bashi amsa da “Eh wlhy Dad, ALLAH dai yasa banyi laifi bane”.       “A'a bakiyi laifin komaiba mai gadon zinari, akan karatune dama, mizai hana da wannan zaman ki sake komawa makaranta kawai? Kinga saina turaki wajen yayarki Shahudah ko?”.           A zuciyata mamakin rayuwa irin ta Dad nake, maimakon yamin zancen aure amma kunji zancen cigaban karatu yakemin, duk da a yanzu ina cikin shekara ta ashirin da huɗu ne.......       Katsemin tunani yay da faɗin, “Karki ce zaki sakama ranki wata sakarar soyayyar Qaseem kinji, ki tsaya kiyi karatun da zaki tallafi rayuwarki koda bana raye, shi kansa zaifi ganin mutunci da kimarki, duka shekararkima nawa da har zaki sakama kanki maganar aure? Bakiga sakamakon da aure ya bama yayarki Shahudah ba, Rayuwar yau data jiya da mu mukai akwai banbanci kinji”.       Kaina na ɗaga masa ina murmushi, nace, “Dad dama ba aure nakeso ba, sai dai akwai wani buri a raina”.      Da sauri yace, “Wane burine haka ɗiyata?”............✍🏻 Page 34 ...............Murmushi na sakeyi saboda yanda yaymin tambayar cikin zumuɗi, duk yanda zaiyi ka sake dashi dad ya sani, shiyyasa akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsa da yaransa, kawai sakacine dai dashi wanda yake kallon hakan matsayin ƴancin kai.       “Dad bansan yaya zaka ɗauki zancenba, dan mutanenmu da yawa sukan ɗauki aikin matsayin bai dace da mace ba, sai dai ƙabilun nan suna shigasu, mune dai gaskiya akan daɗe babu ɗiyan bahaushe a ciki....”         “Kinga faɗamin kawai kanki tsaye, wane aikine?”.       “Dad aikin ƴan sanda, sonake na zama ƴar sanda inhar kana ganin ya dace nayi?”.        Kansa yaketa kaɗawa cikin murmushi, ya dafa kaina yana faɗin, “ALLAH yay miki albarka Bilkisu, wannan tunanine mai ƙyau kuwa, wanda ya kamata ace yaranmu mata suna irinsa koda cigabanmu, ina goyon bayanki ɗari bisa ɗari, sai dai kibari zan zaɓa miki wanda zaifi dacewa dake kinji ko?”.          Kaina na ɗaga masa ina jero masa godiya ta musamman,  dan ina ganin fatana na zama ƴar sanda maisa kaki zai cika.         Ƴan sanda masu saka kaki yafi birgeni, aikin su Yah Qaseem bai cika birgeniba, dukda su ƴan sandane sunfi yin manyan ayyuka ba irin na ƴan sandan dana saniba masu fuskantar kowacce matsala musamman ma irin tamu ta cikin gidaje, to amma babu yanda zanyi, dan kimar Dad ta wuce nai masa musu koda a mafarkine, bazan dai taɓa masa biyayya akan abinda ya kauce shari'a ba, amma duk wanda ya zaɓamin zan amshesa matsayin zaɓin UBANGIJI na.        Ina dawowa ɗaki Number Ummie na kira na sanar mata yanda mukai da Dad, taji daɗi sosai, dan haka tace zata sanarma Dadyn ta dan yazo ya samu Dad akan batun, dan suma duk sun sanar a gida kuma an barsu, Zuhrah ce kawai aka hana itama tana kan lallaɓawa. *_KANA NAKA ALLAH NA NASHI_*                   Tabbas haka wannan batu yake, sanda kake tsara wancan sai kaga ba shine a kundin ƙaddararka ba, tunda tun farko bakai ka rubuta littafinba balle kai tunanin bin tsarin daka shirya ko zuciyarka tafi so.     Kwanaki uku dayin wannan magana da Dad sai ga Dadyn Ummie yazo gidan, wanda na lura dai yaron Dad ne, dan abubuwa da dama daya shafi karatun yaran gidan shine tsaye a kansa, hatta da aiki ko wani abu shi dad ke ɗorawa akan nemawa wanda duk yaso.       Bansan mi suka tattaunaba, na dai je mun gaisa, inda kamar yanda ya saba ya sakemin nasiha akan na kula da komai karna bari nai zirmawar da zanyi dana sani anan gaba.      Na riga na gahimci hannunka mai sandarsa, dan yasha faɗamin karna yarda nai koyi da tarbiyyar gidanmu, ba ƙaramin daɗi nakejiba kuwa da wannan kulawar tasa, shiyyasa a kullum nake sake ganin kimarsa da mutunci.      Nayi zaton ko Yah Qaseem zaice shi aure yakeso muyi baison na tafi wannan aikin, amma sai naji tsitt baice komaiba, sai dama akai kusan sati sannan yakemin tambaya akan maganar.        Koda na bashi amsa murna kawai ya tayani muka cigaba da wata hirar kuma.       Hakan sai ya bani mamaki, a shekarun Yah Qaseem ya cancanci buƙatar mace a kusa da shi, kumani ban taɓa kamashi da wata maceba ko ganin wani abu daya danganci mace a ɗakinsa balle nace yana neman mata, to minene matsalarsa? Dan a yanda yake nunamin dai ai yana buƙatar jin ɗumin macen.      Na kauda wannan tunanin a raina dan bashi da wani muhimmin amfanin da zai mini.      Su Aamilah kam dariya sukaita min, inajinta har aunty Shahudah ta kira ta sanarmawa itama tana tayasu.       Mummy dai batace komai akan batunba, amma naji wani furuci nata daya tsayamin a ƙahon zuciya, wanda na lura ita gani take kamar dan neman kusanci da yah Qaseem ne ya sakani son aikin.       Ni dai na tattara dukkan lamarina a hannun mahaliccina, domin yafi kowa sanin mike raina .       Nakuma cigaba da miƙa kukana a garesa da fatan dacewa idan har aikin alkairine a garemu, idan ba alkairi bane ALLAH ya canjamana da wanda zai zama alkairi.          kusan wata guda babu wani bayani daga Dad ko dadyn Ummie, dan dad ma har yayi tafiyar sati uku yaje ya dawo.      Sai ranar kwatsam na dawo islamiyya na iske Dadyn Ummie da Ummien kanta a gidanmu. Muka rungume juna muna farin ciki, sannan naja hannunta muka shige ɗakina.         Itace ta fara gumtsamin abinda ya kawosu gidan, tuni farin ciki ya mamaye min zuciya, muka sake rungume juna, kiran Dad ya sakani sakinta muka tafi falonsa tare.       Na gaida Dadyn Ummie bayan mun zauna, Dad ya miƙomin takardun hannunsa dake tabbatar da an ɗaukemu zamuje training, harda ƴar ƙwallata ta murna tamkarma ance mun zama ƴan sandan.        Su dad nata min dariya, duk da dai ba ɗan sandan danai fatar zama bane wannan ma nayi farin ciki dashi, naji a jikina shine alkairi a gareni shiyyasa ALLAH yay min canji dashi.       Mun taso zamu fita naji Dadyn Ummie na faɗin, “Wlhy nayi mamakin hakan Alhaji, dan ban taɓa zaton Jawaad zai iya aikatawaba, kamar yanda na faɗa maka shine yayta ƙoƙarin ganin takardun yarannan sun shiga duka wlhy, musamman dayaji nace saƙon nakane.....”      Banji amsar da Dad ya bashiba muka ida ficewa, ina mamakin wanene wannan Jawaad da ake yawan faɗar sunansa a gidannan? Sai kuma labarin da Amina ta bani akan Aunty Shahudah da mijinta ya faɗomin a rai, to kodai mijin aunty Shahudah ne? To amma miyasa Yah Qaseem ya tsanesa matuƙa? Bani da mai bani amsa dan haka na kauda zancen a raina kawai muka cigaba da hirarmu da Ummie. *_INDA RAI! DA RABO_*          Lallaikam inda rai da rabo inji masu iya magana, to nima dai Bilkisu yanzu na shaida hakan, dan kuwa yau gani cikin jerin waɗanda ake horaswa na hukumar ƴan sandan farin kaya a cikin (Training center) ɗinsu, tare da ƙawayena huɗu a karo na  uku.          Duk yanda zan fasalta abun ba lallai ku fahimta ba, amma al'amarin ɗanba sauƙine, anji jiki kafin ƙashi da tsoka su saba, yayin da ƙarfin jini da karsashin zuciya ke ƙara yawaita, babu babban maicin ribar abu irin maiyinsa da yaƙini ko fushin son maida murtani.      Nayi imani da hakan ya taimakama ƙwazonmu sosai ni da ƴan uwana, dan kuwa matakin farko na nasara damu aka shallakesa, kamar wasa sai gamu a mataki na biyu, inda mataki na uku ya kasance na masu babbar nasara, dan kuwa a cikin waɗanda muka shigo wajen mu sama da dubu biyu bamu wuce mutum dubu ɗaya da ɗari uku muka shallakeba, a kuma cikin dubun muka kasance mafiya ƙwazo mu ɗari uku da ashirin, cikin 300 ɗinan aka kuma rairayemu mu saba'in, mu goma sha uku ne kawai mata a cikin saba'in ɗinan, sauran duk sun kasance mazane, cikin amincin ALLAH kuma ko ina ina tare da ƙawayena.          Mu 70 ɗinnan an waremu domin samun horo na musamman fiye da sauran ƴan uwanmu, ƙwazon da muke nunawa da juriya ya samu fita cikin ƴan rukunin farko kenan.                A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har suka rikiɗe zuwa watanni, inda cikin amincin UBANGIJI muka cika dikkan shariɗɗan zamowa cikakkun ma'aikata abin alfahari.       Tabbas wannan nasara da muka samu munyi matuƙar farin ciki da ita, ranar kuma nasha kuka saboda tunowa da iyayena da siraɗin rayuwa dana tsallake batare da hasashen kaiwa wannan matsayinba na yanzu.       Shiyyasa akace babu maraya sai rago, wannan magana tabbas haka take. ★★★★★★          Ranar data kasance ranar yayemu ta zamto rana mai daraja da zuciya bazata iya mantawaba, dukanmu muna cikin Uniform da suka ƙara mana kwarjini da cikar kamala, inda manyan baƙi da manyan wannan hukuma sukai jawabai masu nuna ƙwarin gwiwa a garemu da fatan alkairi, sai ƙyaututtukan karramawa da suka biyo baya na ɗalibai mafiya ƙwazo a cikinmu inda sunana ya fito a bazata.        Wannan abu ya sakani ɗunbin mamaki da al'ajabi, dan ban taɓa kawo hakan a rainaba koda a mafarkina, dan ni kaɗaice mace a cikin waɗanda suka samu wannan karramawa.           Dad yaji daɗi sosai, hakama Yah Qaseem, su Mummy ma dai dayake duk hardasu akazo sun tayani murna koda bata kai har cikin zukatansuba.          Daga ƙarshe kowannenmu ya samu takardar tabbatuwarsa ma'aikaci tare da inda aka turaka, matakin karatu ya matuƙar taimaka mana wajen tsintar kai ba'a matsayi mafi ƙaranci ba, dan kuwa bamu kasance matakin ƙarsheba.       Mun rungume juna mu dasu Zuhrah muna kuka, dan kuwa dai an samu matsala wajen rarrabamu bazamu kasance a waje ɗayaba, kowanne da inda aka cillashi, ni da Ummie ne kawai a waje ɗaya.       Sosai hakan ya taɓa zukatanmu, har sai da iyayenmu suka koma lallashi da nuna mana ai dama aikin kenan, wannan ba makaranta bace balle muce tilas mu kasance a zaɓinmu. ★★★★★★★          Sati guda cif da gudanar da bikin yayemu muka shiga filin daga, yau sai ga Bilkisu Adam makaho matsayin ƴar sanda ta hukumar DSS, Yah Qaseem shine ya zamemana fitila a komanmu ni da Ummie, duk da kasancewarsa babba a wannan hukuma.       Aikin farko da muka fita Ummie tayisa cike da tsoro, ni naita ƙarfafa mata Gwiwa har itama ta samu ƙarfin zuciya, a cikin kwanakin da basu gaza sittin ba, waɗanda a jimlace zasu baka wata biyu mun gama gogewa, muma munaji a ranmu mun isa karanmu yakai tsaiko.............✍🏻 Akwai sauran pages 6 a ƙasa, nima sai naga ana zabga mana ruwan subscribing sannan zan sakesu🙄😂, waɗanda sukai mana sub... Muna godiya, ALLAH yabar zuminci, kuma nayi farin ciki dan duk wanda yayi na gashi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Page 35 ............Yau safiyar Laraba muka tashi da labarin dawowar wasu manyan jami'ai na wannan hukuma tamu kamar yanda manyanmu suka sanar.        Na kasance a cikin tawagar masu zuwa tarbarsu da aka ɗiba a cikin mu ƙananun ma'aikata, akwai kuma manyanma.      Hakanne ya tabbatar mana lallai waɗanda zamuje tarar sunada muhimmanci a wannan hukuma. Haka kawai na tsinci kaina da faɗuwar gaba, zuciyata sai wani irin zallo take kamar zata faɗo ƙasa.       Ƙirjina na dafe ina lumshe idanu, dama tun jiya nakejin tamkar wani gagarumin abu na kusanto rayuwata, sai dai bansan minene ɗinba.        Mun iso airport ɗin akan lokaci, dan jirginma bai kai ga saukaba sai nan da minti arba'in kamar yanda aka sanar damu.          A yanda mutane suke kallonmu musamman ma mu matan da muka kasance mu biyu kacal yasa duk na takura, sanye muke da Uniform wanda ni kaina nasan sunma surata matuƙar ƙyau, tabbas bani da ƙyawu mai tsanani amma ALLAH ya azurtani da ƙyaƙyƙyawar  surar dake da wahalar samu ko a cikin matanma, wadda itace ke fisgar maza da yawa a gareni, akwai baby hijjab dana saka kafin na ɗora hular Uniform ɗin a saman kaina, hakan ne zai baka amsar kasancewata musulma kai tsaye.        Addu'a na rinƙayi a zuciyata, saima na saka eyeglasess a idona saboda kallon ya gundunreni.            Adadin mintuna na cika jirgin da muke tabbacin jira ya iso, saida  ya gama shawagi a sama kafin ya sauka a inda ya dace, wannan shine karon farko da nazo airport a rayuwata, hakan ya sakani tsarkake sunan UBANGIJI daya sanya fasaha ga zukatan waɗanda suka ƙera jirgi, sannan ya bashi ikon tashi sama duk da girman da yake dashi.         Bugun zuciyata ya sake sauya salon bugawa da sauri-sauri, hakan ya sakani rumtse idanu dukkan jikina na wata irin tsuma, haka kawai sai nakejin kamar na kama kuka.          Taɓanin da akaine ya sakani buɗe ido da sauri, ɗaya daga cikin ma'aikacinmu ne da yake nema takurama rayuwata, na kallesa ina ɗauke kaina dan haushi yake bani, shi a dole wai sona yake, tun a wajen training ya maƙalemin, sai kuma akai rashin sa'a muka tsinci kanmu a waje guda.         Ganin ya gyara tsayuwa zai fara magana nai gaba abuna. Dai-dai fasinjojin jirgin sun fara fitowa.      Duk wanda ya fito a jirgin idonmu a kansane, sai dai ganin babu wanda ya motsa daga jami'anmu ya tabbatarmin namu tawagar basu fitoba har lokacin.       Sai da kowa ya gama fitowa har babu alamar sauran mutane kafin wata mata da yara biyu ta fito, sai wata kuma a bayanta ita riƙe da hannun yaro namiji, sai wata na biye musu baya itama.         Suma sai da suka sauka duka sannan sannan fitowar wani sadauki da tai daidai da tsananta bugun ƙirjina ya fito.      Zaratan mazaje uku da doguwa budurwa na biye dashi a baya.        Jinai ƙafafuna na neman gaza ɗaukata, hakan yasani saurin jingina da ɗaya a cikin motocinmu gudun karna faɗi.        Jawaad dake fitowa ya sauke idanunsa akan sir Ahmad barewa, kafin yaci gaba da bin ma'aikatan tadabbaci ke nuna sunzo tarbarsu ne.      Kansa tsaye inda su sir Ahmad da wasu manya suke suka nufa, inda shima Sir Ahmad ɗin ya nufesu fuskarsa cike da fara'a da farin cikin ganinsu.         Gaba ɗaya sauran ma'aikatan sukaja layi alamar girmamawa, miƙewa nai ina sauke numfashi tamkar wadda tai gudun fanfalaƙe.       Sai da ya gama gaisawa da manyansa kafin su nufomu su dukasu.       A tare muka buga ƙafafu tare da yin salute nasu cikin nuna tsantsar girmamawa.            Jawaad dake tsaye yana ƙare musu kallo idonsa ya sauka kan matashiyar budurwa mai hijjab.      Ganin ya tsura mata idanu Jabeer da suke bayansa yay mata umarni data cire glasses ɗin idonta a ɗan kausashe.          Kawai jinai idanuna sun cika da ƙwallan da bansan dalilinsu ba, na zare eyeglasess ɗin idona kamar yanda aka umarceni tsigar jikina na wani irin tashi tamkar nai gamo da halittar ban tsoro.       Babu zato idanuna suka shige cikin nashi idanun masu wani sinadarin da baki bazai iya faɗaɗa bayani akaiba.      Kasa jurewa nai na janye nawa ina rissinar da kaina tamkar zuciyata zata faɗo ƙasa.        Shima cikin basarwa ya janye nasa idanun cikin wani salo na halin ko in kula.       Sai da ya gama ƙare mana kallo mu duka kafin yay guntun murmushin daya saka kumatunsa loɓawa.      Saitin inda nake yay mana nuni da hannu alamar mu bashi hanya, hakan ya sakamu darewa muka rabu biyu ya gittamu ya wuce, mayen ƙamshin turarensa na rige-rigen shiga ƙofofin hancinanmu.        Da sauri wasu a cikinmu suka nufi motocin suka bubbuɗe musu har manyan mu da mukazo tare wajen, ni dai bamma iya koda motsiba daga inda nake, saboda bani da wani ƙarfi sam balle samun kuzarin yin abinda ya dace.        Sai dai idona akan motar daya shiga shi kaɗai baya aka maida aka rufe masa, haka kawai naji tamkar ana kallona, kallo kuma irin na ƙurilla, sai dai iya dube-dubena banga alamun kowa da idonsa ke kainaba, saboda mutane sunata hada-hadarsu ne.     Hannu na ɗora a hankali bisa ƙirjina dai-dai saitin zuciyata ina lumshe idanu, wasu ƙananun hawaye suka silalomin a kan kumatu, saurin jan hulata nai sosai yanda zata hana kowa kallon halin da nake ciki kafin nasa handkherchief na share cikin dabara ina nufar mota nima.              Jawaad da tunda ya shiga mota idonsa ke akanta yana ƙare mata kallon da shima baisan dalilinsa ba ya lumshe idanu yana huro iska ta ƙofofin hancin, kuma buɗewa yay sai yaga wayam babu ita a wajen, cikin halin ko in kula yaɗan taɓe baki yana ɗauke idanunsa daga kallon wajen ma baki ɗaya ya maida ga wayarsa.          Tanda muka fara tafiya nake jerama kaina tambayiyin da bansan amsarsu ba.        “Miyasa nakejin tsoro? Miyasa yay min kwarjini fiye da kowa? Miya sakani kuka? Minene ma'anar halin dana shiga bayan banida wata alaƙa da wani abu daya taɓa shafar irin wannan yanayin dana tsinci kaina a ciki balle nace na tunashine?”.       Waɗanan tambayoyi su naita jerama kaina har muka iso, tarbar da muka iske an shirya musu ananma ce ta sakani samun damar zare jiki na koma can gefe na zauna ina maida numfashi da addu'ar samun daidaituwar wannan baƙon yanayi nawa da baida alaƙa da komai.        Dafanin da akayine ya sakani juyowa, Ummie ce, hakan yasa tana zama sai kawai na fashe mata da kuka.        Ɗunbin mamaki ya bayyana a fuskar Ummie, tai kasaƙe tana kallona tamkar wata sokuwa,       “Bily lafiyarki kuwa?”. Ban bata amsaba, saima ƙarfin kukana dana ƙara, tai shiru kawai ta sakamin ido, saida nayi mai isata nai shiru dan kaina sannan ta sake jefamin tambaya.        “Bilkisu mike faruwa ne wai? Ko an miki wani abune da kuka tafi?”.       Kaina na girgiza mata alamar “A'a”.     Tace, “To minene ya faru? Ko baki da lafiya ne?”.        “Lafiyata ƙƙalau kawai na tuna su babane” na samu kaina da mata ƙarya batare danasan dalilin hakanba, dan nasan bama ɓoyema juna abu sam.        Numfashi ta sauke tana dafani, cikin tausasa murya ta shiga lallashina damin nasihar addu'a su baba ke buƙata bawai kukana ba.       Kaina na ɗaga mata kafin nace, “Nagode Ummie, insha ALLAH bazan sake yiba”.      Tai murmushi tana canja akalar firar tamu zuwa wata,        “Kutt Bily basawannan namu da kuka tarofa sunji gishiri da magi, musamman mai green ɗin Suit ɗinnan”.        Gabana ya sake faɗuwa jin ta ambacesa, amma saina danne cikin ƙaƙaro murmushi nace, “Kingani ban wani tsaya ƙare musu kalloba, yanzu haka babu kamannin wanda zan iya kawowa a cikinsu”.        Tace, “Tab, amma lallai kinyi gwari dan wlhy anci kasuwar sama babuke Babie, ai har sunan mai green suit ɗinma na riƙe”.         Kallonta nayi da mamaki, tare da jin zuciyata tai zallo, kamar na tambayeta yaya sunan sai kuma na taɓe baki ina miƙewa, “Kinga dan ALLAH bar wannan shirmen tashi muje, yaushe kika fara lalacewa ne haka Ummie?”.       Dariya ta tuntsire da ita tana dukan kafaɗata, tace, “K nakai aurefa, sannan dukkan burikanmu sun cika, miya rage mana kuma? Musamu mazajen aure kawai, kodan ke kin samu Yah Qaseem a hannune”.        Kallonta nayi a wani irin yanayi jin ta ambaci yah Qaseem, sai ban iya furta komaiba nai gaba abina ina murmushin ƙarfin hali.      Itama bata sake maganaba ta biyoni da hanzari muka dai-daita tafiyarmu.            Da ɗan aiken Yah Qaseem mukai karo akan naje yanason ganina.       Haka kawai sai naji kiran yaban haushi, amma bani da damar ƙin zuwa ɗin.        Na kalli Ummie ina faɗin, “Dan ALLAH ki rakani tawan”.       Baya tai tana zaro idanu, “Wa? Rufamin asiri hajiyata, wannan fagen na masoyane ai, aidai ƙone ƙaɗan babie kar ai ƙurmus dan ALLAH”.          Harara na zuba mata kafin na wuce ina zare hular kaina na riƙe a hannu.        Koda na isa Office ɗin nasa kaina tsaye na shiga, dan ya bada sharaɗin shigata babu shamaki.          Kallo ɗaya naima fuskarsa na fahimci ransa a ɓace yake, na zauna ina gaidashi cikin girmamawa kamar yanda na saba.         Bai amsaba sai numfashi daya sauke, ya taso daga kujerarsa ya dawo inda nake shima ya zauna a ɗayar kujerar dake kallon wadda nake kai.       Idanu ya tsuramin kusan minti ɗaya, niko na gaza kallonsa saima takura da nayi, cikin son katseshi na shiga gaishesa.       Nanma numfashin ya kuma saukewa yana janye idanunsa a kaina.       Ba tare dana kallesanba nace, “Yah Qaseem lafiya dai ko?”.      Siririn tsaki yaja yana haɗawa da ƙaramar ƙwafa, “inafa lafiya wannan banzan ya dawo”.       Da mamaki nace, “Banza kuma? Wanene banza yah Qaseem?”.      Tsakin ya kuma ja yana maido kallonsa kaina, “Bazaki taɓa ganewaba, dan haka share, ina kikaje ɗazun na aika kiranki akace kun fita?”.         Zamana na gyara cikin rashin damuwa nace, “Ba inda naje, kawai tarbar waɗanan jami'an namu da suka dawone.........”       “Kina nufin dama dake akaje?”    Yay maganar cikin tare numfashina tamkar zai haɗiyi harshensa.          Da mamakinsa na ɗaga kaina kawai.       Sosai ɓacin rai ya kuma bayyana a kan fuskarsa, ya furzar da ɗacin da nakeda tabbacin yanaji tare da miƙewa.      Nidai uffan bance dashiba saima kallo dana bisa dashi kawai.      Bansan miya tunaba ya juyi yana faɗin in tashi muje muci abinci.     Tashin kuwa nayi, ya fita ina biye dashi, koda muka fito a Office ɗin sai ya tsaya muna tafiya a tare.            Bugawar da zuciyata tayine ya sakani komawa tafiya da sassarfa, ɗago idon da zanyi idona suka sauka akan mutumin ɗazun da mukaje tarba.         Da ƙyar na iya haɗiye yawun daya tsinkemin a cikin baki saboda kallon ido cikin ido da mukaima juna, amma sai ya janye nashi tamkar bani yake kalloba ya shige motar da aka buɗe masa wadda alamomi suke nuna zai tafi gidane maybe.          Nannauyan numfashi ya kufcemin wanda yay dai-dai da fitar sautin jan tsakin da Yah Qaseem yayi...........✍🏻 Page 36 .............Har muka isa wajen da kullum Yah Qaseem ke kaimu cin abinci anan kusa damu fuskarsa babu walwa, bama muba kusan duk anan manyan jami'an kecin abincin, dan wajene haɗaɗɗe da yasha gyara na musamman, sanan ake abinci mai tsafta da daɗi, sai dai kamarmu ƙananu da ƙarfinmu bai kaiba akwai wani gidan abincin daga ɗayan gefen mukanfi yawan zuwa acan muci. To nidai bamma taɓa zuwa wancan ɗinba, dan kullum nan Yah Qaseem ke kawoni, idan kuma aiki yay masa yawa yakan saka akai masa office muci acan kamar yanda wasu daga cikin manyan keyi. Kallon bawan ALLAHn can da yaymin lokacin dazai shiga mota ya mugun tsayan a ƙahon zuciya, duk yanda naso turesa hakan ya gagara, sai sauke ajiyar zuciya nake ina tsakurar abincin badan yaymin daɗiba. Shi kansa Yah Qaseem na lura bawai cin abinci yakeba sosai yau, dan ransa a ɓace yake, na kuma rasa dalilin hakan sam. Haka dai muka tsakura sama-sama muka bar wajen, kafin mu wuce na roƙesa muyima Ummie takeaway. Atm ɗin nasa ya miƙamin kawai ya fice, na bisa da kallo ni dai kafin na amsar mata abinda nasan tanaso na fito, sai dai zuciyata na mamakin miya fusata yaya Qaseem haka wai ne?. Ban iskeshiba hakan yasa na tafi ni kaɗai, dan da alama ya shige abinsa. Yau bamu bar Office ba sai kusan takwas na dare, tare da Yah Qaseem muka tafi gida, sai lokacin ne na bashi ATM card ɗinsa, inason tambayarsa mike damunsa? Amma wani gefen zuciyata na karantamin na sharesa kawai. Sharesan kuwa nayi nama maida hankali wajen cheating da Rebecca da taimin magana. Har muka isa gida ni da shi bakin juna bai saɓaba, yanata driving ɗinsa, duk da na lura akwai tuƙin ganganci a ciki, wanda na jima da fuskantarsa ya haddace gudu a titi tunba yanzuba. Amina ta taɓa bani labarin yanada driver da aka bashi na office da, sai dai rashin haƙurinsa yasa ya sallami direban, ya gwammaci ya tuƙa kansa da kansa. ★★★★★ A gidanma haka yayta tsumewa, nidai koda na gaida su Mummy dake falo ɗakina na shige, dan yanzu ganin batason sakarmin fuska sai na sake janye mata, aikin dake a gabanama ya isheni gayya basai an haɗamin da damuwa mara dalili ba. Sai da nai wanka naji daɗin jikina sannan na fito falon domin neman abinci, ganin abinda aka dafa a gidan, ni kuma ba sonshi nakeba sai kawai na haɗa tea. Ina daga dani ina shan tea ɗin nake jiyo hirar Mummy da yaranta, harda Yah Qaseem daya zama ginshiƙin hirar, shima da alama yana yin wanka fitowar yayi, jinai yana sanar mata wai Jawaad ya dawo. Da yake ban fahimci kan maganar tasuba sai bansan akan wa yake maganaba, ni dai nayima na tashi na shige ɗaki abuna dan na kwanta na hutama rayuwata. Dan tunda na fara aikinnan Yah Qaseem ke tafiya dani da dawo dani a motarsa Mummy ke haushi dani, inaji ranar tana masa faɗa akan hakan, harma da gargaɗi akan ya fita harkata, inba hakaba kuma yay kuka da kansa. Bandaiji ya tanka mataba, bai kuma fasa ɗaukata a motarba. Niko ina ruwana, tunda bani tama gargaɗinba banbi takai ba na cigaba da binsa kamar yanda Dad ya faɗamasa ya ringa tafiya dani da ɗakkoni tunda ALLAH yasa wajen aikin namu ya kasance ɗayane. _________________________ JAWAAD _________________________ Tarba maiban mamaki Jay ya samu ga ahalinsa, dan kuwa hardasu Umma duk sun taru a family house nasu. Danne mamakinsa yay shima ya nuna girmamawa ga wannan tarba tasu, bayan gama amsa sannu da zuwa suka bashi damar shiga sashensa domin watsa ruwa. Kaya yake cirewa yana jan ƙaramin tsaki shi kaɗai. “bansan miya kawo dalilin yawan tsakinba ni kaina, sai dai mucigaba da bibiyar jay ko zamu sami amsa”😉😹⛹‍♀. Yanda aka gyara sashen da ƙamshin da yakeyi ya ƙayatar dashi, sai dai yanaji a ransa aikin nan sai dai idan batool ɗin Umma ko Nabeelah wani yayisa. A wajen wankanma ya samu nishaɗi saboda yana son tsafta a rayuwarsa, ya dai gama ƙaƙale-ƙaƙalensa ya fito ɗaure da tawul yana tsane jikinsa da ƙarami. Sosai jarumin na Shahudah ya kuma canjawa, dan dai-dai da gaɓoɓin jikinsa sun sake murɗewa, ga wata gogewa da fatarsa ta sakeyi, yanda ruwa ke gudu a jikinta zai tabbatarma da mai kallonsa hakan. Komai yana yinsane a yanayin gajiya, inda son samune kwanciya zaiyi ya hutama ransa basai ya sake fita a waccan hayaniyarba. Amma yaya ya iya, dolene ya koma kamar yanda suka buƙata tunda sunce danshi suka taru. Sama-sama yay ƴan shafe-shafensa ya saka wando da riga ruwan siminti marasa nauyi, kayan sun masa ƙyau tare da fidda ainahin ƙirar da UBANGIJI yay masa, ya fesa turare kaɗan sannan ya fito harabar gidan daga can baya inda dama anyi wajenne domin hutawa, an gyarashi sosai da korayen ciyayi da filawoyi masu ƙamshi. Sam Jawaad baya zuwa wajen, saboda ƴammatan gidan sun maidashi lambun shaƙatawarsu ko ajiye samarinsu suyi hira, shi zaima iya rantsewa tun bayan daya mallaki hankalinsa baizo wajen sau ukuba, mantawama yake dashi gaba ɗaya, zuwa ukunma da yake kyautata zaton yayi shima duk mitin ne da Uncle's nashi suka shirya ya halarci wajen a wancan lokutan.. Sosai kuwa walimar cin abinci aka shirya, sai dai ya fahimci tamkar da biyu ne, danshi jami'in tsarone mai matuƙar basira da kaifin tunani, hakanne ya taimaka masa wajen gayyato ɗunbin nasarori a cikin rayuwar aikinsa. Yanda ƴammatan Family ɗin nasu kowacce taci ado na ƙure wankane ya sashi fahimtar komai a buɗe. Yay ƙwafa a zuciyarsa kawai yana sake shan toka, baisan miyasa akeson takurama rayuwarsa da awaɗanan yaranba, dan haka sukai maƙurar takura masa ta waya yanacan, kullum babu fashi sai yaga text messeges nasu ɗaya bayan ɗaya, harda masu masa a shafukansa na yanar gizo. Bai taɓa kula koda ɗayarsu ba, danshi a ganinsa hakan rainine. Ƙin cin komai yayi a wajen sai kunun aya kawai, wanda Batool ta tabbatar masa itace ta haɗa masa shi, dan dogon tabirne aka ajiye sannan aka zagayesa da kujerun da adadainsu yakai Hamsin koma fin hakan, manya maza da mata na family ɗin kowa ya samu muhallin zama, su kuma yaran an shimfiɗa musu leda mai ƙyau a ƙasa anan suke nasu shagalin bisa kulawar ma'aikatan gidan. Sai da ya gaji da harar da Umma ke masa akan cin abinci sannan ya ɗau cokali badan yaso ba ya fara cin abinda yasa aka zuba masa cikin nutsuwarsa. Sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska ya saka dukkan ƴammatan dake fama da rawar kai suka nutsu, dan dama sunsan shi baya son wargi, bakuma shiga sabgarsu yakeba tun fil azal. Sai dai sai faman satar kallonsa suke ta wutsiyoyin idanu, shiko baima san sunaiba, abincinsa yakeci yana ɗan jefa magana cikin hirar mazan gidan sa'anninsa. Dukda shine ƙarshen fara cin abincin shine kuma farkon fara ajiye cokali, babu wanda bai bisa da kallon mamakiba amma sai ya fuske cike da basarwa kamar baisan miya aikataba, sam saima yaƙi kallon sashen Ummah balle ta sake sakashi tilas akan yacin. Abubuwan da Jay yakeyi ba ƙaramin ɓata ran Uncle's nashi sukeba, amma duk sai suka danne zukatansu da addu'ar ALLAH yasa karya watsa musu ƙasa a idanunsu yadai zaɓi matar aure kamar yanda manufar taron take. Dukanin tunaninsu bai gama tsayawaba sai da Jawaad ya miƙe bayan mintuna biyar da ajiye cokalinsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yay musu sallama tare da miƙa kalamun godiya na wannan tarba daya samu daga garesu, yay addu'ar sake samun haɗin kai na wannan family mai ɗorewa, tare da jaddada musu abinda sukai masa yau din ya ƙayatar dashi kuma ya bashi farin cikin da bazai mantaba har sai ya rubutashi ya ajiye. Kowa fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallon Jawaad ɗin, kowa yaji daɗin kalamansa kuwa, dan basuyi zaton jin hakan daga gareba. Shikuma yay wani munafikin murmushin da ya kusa zautar da dukkan ƴanmatan wajen, shikuma shi kaɗai yasan ma'anar kayansa, kafin ya nema alfarmar tafiya domin ya huta saboda ciwo da kansa ke ɗan masa kaɗan-kaɗan na alamar gajiyar tafiya. Basu da yanda suka iya dashi, amma dai Uncle Nasir ya dakatar dashi har ya miƙe yay ɗan guntun bayani na sake masa sannu da zuwa, tare da roƙon Jawaad ɗin ya sake jikinsa tare da yafema duk wanda yake ganin ya masa ba dai-dai ba akan abinda ya faru wancan karo har yayma gidan yaji na kusan shekara. Nanma dai godiyar Jawaad ya sakeyi sannan ya tabbatar musu shi komai ya wuce a ransa tuni, suma yana fatan hakan daga garesu, daga ƙarshe yay musu sallama ya koma sashensa. Murmushi kawai Umma tai tana girgiza kai da bin Jawaad ɗin da kallo harya ɓacema ganinsu. Barinsa wajen ya saka taron ya fara watsewa a hankali, mafi yawansu zukatansu babu daɗi a ciki, musamman ma ƴan matan da suka ƙwallafa rai a kansa babu gaira babu sabar. Shi dai baimasan sunaiba, dan yana barin gurin ƙwafa yay yana maijin takaicin rainin da ake neman jawo masa wajen yaran gidan, zama yay a falon yana jiran shigowarsu Umma domin su gaisa kafin ya kwanta. Zaman nasa kuwa baifi da mintuna goma ba sai ga Umma dasu batool sun shigo. Dariya Batool ta fara masa tana tafa hannaye. Harara yaketa zabga dan yasan tsokanarsa zatayi, mata amma baice komaiba, dan itace kawai ke iya taɓasa kasancewar sa'anni suke dashi ta kwana lafiya, wani lokacinma har yakan biye mata, batool bata taɓa aureba, munadai tayata fatan samun miji na gari. Ɗauke idonsa yay akan Batool ɗin data zauna a kujerar gefensa tana faɗin, “Kaga mai ƴammata buhu-buhu na Shahudah bada kanka a sare kazo gida kace ya faɗi”. “Umma ALLAH kicema yarinyarnan ta kama kanta kota fita falonnan da ƙafa guda”. Jay yay maganar cikin matuƙar ɓata fuska. Murmushi Ummah dake zama tayi, yayinda Batool ta bushe da dariya, hakama su Nabeelah duk sai gyale sukasa suna kare fuska dan karya gani. “Manta da ita kaji My son, yau ba ranar ɓata fuska bace ba, ina fatan dai ka dawo cikin ƙoshin lafiya?”. Numfashi yaɗan sauke mai haɗe da ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh Ummana, sai dai kewarku kawai, yaya jikin Baba?”. “A jikinsa Alhmdllh, ai yama samu sauƙi dama murace ta canjawar wannan yanayin, sai kuma jikin tsufa da aketa rarrakawa”. Jawaad yace, “ALLAH sarki baba, ALLAH ya ƙara tsahon rai”. Da amin suka amsa su duka. Su Nabeelah suka sake gaidashi cikin girmamawa, yayinda shima yake amsawa da ƴar kulawa. Batool kam cayay bazai amsa mata gaisuwaba. Tace, “Karka amsa mana Jay, duk dai wani ɗacin ranka kayisa ka gama Aurene sai anyi makashi, danni harma na zaɓa maka waɗanda suka dace dakai a ƴammatan nan da aketa faman maka talla kana wani fuskewa, auren gata zamuyi maka, ƴammata uku zuƙa-zuƙa sai Shahudah uwar gida ran gida”. Remote dake center table ya ɗauka ya jefeta dashi, ta tashi ta fice daga falon tana dariya, shi kuma ya kuma haɗe fuska yana ƙwafa. Su Nabeelah ma dai ficewa sukai dansu bashi waje ya tattauna da Umma. Dariya Umma ma taɗanyi kaɗan tana faɗin, “Da gaskefa Fatima keyi, waɗanan yaran daka gani dansu aka shirya maka wannan tarbar, ni kuma naga bakama nuna wata alamar zaka zaɓa ɗinba”. Cikin takaici Jay yace, “Na sani Ummah, amma dan ALLAH karku biyema shirmensu, zan kuma taka musu birkine dan wannan neman jawomin rainine wajen yara kawai, bansan minene matsalarsu da aurena ba ko rashin yinsa? Nace musu ina buƙatar aurene ko yaya? Za'a wani ringa cusamin yara ƙanan kamar wani ɗan iska......” Cikin tare masa numfashi Umma tace, “Dole zaka buƙaci aure Jawaad, dan koba komai ka rigada ka ɗanɗani zama da mace, kuma koba hakaba ma cikar mutuncinka shine auren, babu wanda zaka sanarma kai kamiline ya yarda bayan mu da mukasan kai wanene, ka daure koda ba'a cikin yaran nasuba ka sami matar aure, idan kuma matarka kakeson maidawa ka maidota dan maybe ta canja zuwa yanzu, tunda na fahimci son da kake matane ya hanaka sake kallon wata mace da sigar auren, baba kansa yana damuwa sosai da rashin sake aurenka, shekarafa huɗu kenan da wasu watanni da rabuwarka da matarka, da aurenma kayi ƙila da yanzu ƴan jikokinmu na kai kawo a falonnan, sannan akwai wasu takardun dukiyarka masu matuƙar muhimmanci dake da alamar tambaya, dan sune silar komai da lokacine kawai zai buɗe kowanne sirrin da mu da kai zamu fahimta baki ɗaya....” Shiru Jawaad yay yana nazari dason ƙarin bayani akan maganarta ta ƙarshe, sai dai bata bashi wata damar masa tambaya akan hakanba, shiyyasa yay shiru yana kallonta, sai kuma ya sauke numfashi yana faɗin, “Shikenan Ummah, kuyi haƙuri indai aurene zanyi da izinin ALLAH, duk da har yanzu babu wata mace a raina, kuma ba hasashenku bane ya hanani aure na cewar son Hudah ne har yanzu, sai dai kodan farin cikinku zanyi insha ALLAH, amma ku kwantar da hankalinku ku bani lokaci, dan banason a sake komawa ƴar gidan jiya kamar aurena na baya”. Umma tace, “To ALLAH ya tabbatar mana da alkairi. ya kuma kawo mana ta gari wadda zata zo mana da alkairai”. Bai iya ce mata komaiba, dan gaba ɗaya sun dagula masa lissafi, basu san yanda yakejin haushin mata bane a ransa da sunbar ambatar aurenan da suka damu ransu akan sai ya ƙara..............✍🏻 Page 37 ............Bayan shigewar Qaseem da Bily babu daɗewa Mummy na zaune tana saƙawa da kwancewa ta yanda zasu ɓulloma zaman Shahudah da Jawaad kira ya shigowa wayarta. Ɗauka tayi babu ɓata lokaci, dan kuwa kirane mai matuƙar muhimmanci. Sama-sama sukai gaisuwa mai kiran ta fara zayyane mata abinda ya faru a family house ɗin su Jay a yau, wato dai walimar cin abincin da aka shirya masa mai taken yaɗa manufar tallar matan aure. Ran Mummy ya ɓaci ƙololuwa, dan a ganinta wannan tsagwaron munafurci ne kawai ƴan uwan nata suka shirya, taya zasu nema aikata haka?, bayan sunsan akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin Shahudah da Jawaad ɗin, saɓanine kawai da sharrin shaiɗan ya gitta har wancan matsalar ta faru, maimakon su nema hanyar da za'a sulhunta shine zasu haɗa wannan annamimancin? To lallai lokaci yayi da za'ai uwar watsi kuwa ashe, yanzu ace har mahaifiyarsu ta gaza kiranta ta sanar mata balle ƴan uwanta su Uncle Uwaisu, dan bata saka Maimuna ƙanwarta a wannan sabgar, tunda tuni ta nuna musu bata tare dasu ita dama. A wannan dare gaba ɗaya barci gagarar idanun Mummy yayi, gashi Dad baya gari, tayi kiran wayarsa yafi sau goma taƙi shiga, ta kuma kira Mama Atika ba'a ɗaukaba, ta kira Shahudah shima bai shigaba. Gaba ɗaya sai kanta ya ƙara ɗaukar zafi, sai sauke ajiyar zuciya takeyi a jere a jere. Gari na wayewa duk da uban barcin dake cin idanunta haka tai shiri tunda farar safiya ta fice a gidan, ko jiran driver bata tsaya yiba, dan aganinta kafin yazo an gama ɓata mata lokacinta. Tun shigowarta falon mama Atika dake zaune tana lazimi ke kallonta, Mummy sai sake cika take tana batsewa, ganinfa mahaifiyartasu ba ida addu'ar nan tata zataiba ya sata faɗin, “Wai nikam mama wannan addu'ar bata ƙarewa ne?, nifa a ƙage nazo”. Mama Atika batace mata komaiba, hakama bata tsaya da addu'arta ba sai da takai aya, ta shafa tana faɗin, “Ke dai Wlhy Ai'sha sam baki da ɗabi'ar ƙwarai, ba ƙaramin lalacewa rayuwarki taiba a garincan na marasa sallah, mike faruwa na ganki da wannan uwar safiyar?”. Cikin sake ɓata fuska Mummy tace, “Ba dole ake ganina da farar safiya ba, yanzu mama dan ALLAH munafurcin da ake shirin ƙullawa ya ƙyautu kenan a gidannan?, kowa yasan alaƙar dake tsakanin Shahudah da yaron nan na wajen Abdul-aziz, amma shine za'a shirya wani annamimanci ta bayan fage ba tare da nasaniba ma........” Saurin katseta mama Atika tai da faɗin, “Ke da ALLAH rufama mutane baki, waye zai sake haɗa sabgarsa da wannan shashashar ƴar taku mai kama da wadda aka yaye jiya, idan barci kike to kidawo hankalinki Ai'sha, badan wawiyar yarinyarnanba da yanzu mun gama mallakar fiyema da abinda muke buƙata, amma tazo ta ɓata mana komai saboda ita shashashar yarinyace taɓararriya, ki duba yanzu wulakancin data jawo mana ne ya saka dukkan manufofin mutan gidannan ya gama bayyana, yanzu kowama yima ƴarsa farautar yaron nan yake, dan dama can shakkatane ya sakasu haɗiye ƙwaɗayinsu a fili, dukda wasunsu na taƙamar komai yana hannunsu ne ai, maimakon kuma a shekaru huɗun nan ku nema hanyar gyara komai tunkan abunma yay nisa ta bashi haƙuri amma sai kuka ɗauketa kuka sake turawa cikin yahudawa, kekuma kika ɗauki fushi damu, yanzu har nai ciwona na gama a gidannan Ai'sha baki leƙoniba, saboda ke mai ƴa ko? To mune muka saketa? Kokuwa mune muka sakashi sakinta? Muda ta ɓatama komai mune ya dace muyi fushi ba keba? ai ko.......” “Nidai mama naji, ya isa dan ALLAH, sai faɗa kike ko haɗiyar yawu baƙyayi, naji anyi kuskure, amma kuma ai bai ƙyautu a wancan karon kowa yaƙi fahimtar ƙaddarace sanadin komai ba, ALLAH ya rubuta cikinnan bazaizo duniyaba, daga baya kuma dai ai komai ya dawo ya daidaita, amma sai babu wanda ya kirani a cikinku, ta yaya bazan ɗauki fushiba to?”. “Kedai kika sani, ai kuma fushin naki bai miki amfaniba, tunda gashi kin dawo da ƙafarki ko?, kuma a lokacin da kuka makara keda ƴar taki, dan kuwa a yanzu filin dagar ya zama na mafarauta da yawa”. “Mama ki daina faɗin mun makara, babu wata makara tunda kowa yasan Jawaad nason Shahudah, kuna insha ALLAHU a cikin watannan zata dawo ƙasarnan”. Baki mama Atika ta taɓe da yamusashshiyar fatarta ta tsufa, tace, “Kudai kuka jiyo, danni tawa tai ƙyau, dama kune masu amfana baniba, a shekaruna ni yanzu amfanin mi abinda akemawa ɗin zaimin?, komai da kukaga inayi danku nake yinsa”. Shiru itadai Mummy tayi bata tankaba, tana nan zaune har su Uncle Uwaisu suka shigo gaishe da mama Atika, annanfa suma Mummy ta balbalesu da masifa, ta inda take shiga ba tanan take fitaba. Wasa-wasa rigima ta kaure a tsakaninsu, dan kuwa yanzu suma ba ɗaga mata ƙafa zasuyiba duk da tana babbar yarsu a ɗakin, duk yanda mama Atika taso suyi shiru sunƙi, har sai da ta saka musu kuka sannan suka dawo hankalinsu sukai shiru. __________________________________ To nidai sam bansan bikin da akeba a gidan, naji dai Aunty Aamilah na magana akan Aunty Shahudah zata dawo, banji an faɗi rana ba, bakuma a faɗaminba, nima sai banbi takaiba, dan bakowace sabgar gidan nake shigaba musamman ma yanzu danasan ciwon kaina. Tsawon kwanakin da suka biyo baya a satin ban sake jin komai na faɗuwar gaba ba, hakama wanda muka taro a ranar nan ban sake ganin koda ɗaya a cikinsuba. Duk da abubuwa masu yawa game dashi sunƙi barin raina, duk kuma ƙoƙarin turesun da nakeyi hakan baisa na damu kaina da rashin ganin nasa ba, na cigaba da harkokin gabana har a yau da mukai safiyar fita aiki kasancewarta Monday tushen aiki. Kamar kullum nayi tsaf dani, tamkar ka saceni ka gudu, musamman ma data kasance a yau sanye nake da baƙaƙen suit na mata wando da riga, na kawo farin baby hijjab na saka tamkar yanda na saba a kowace rana, kayan sun zaunamin sosai a jiki tamkar dan jikin aka haliccesu, na saka siririn farin eyeglasess ɗina sannan na fito ɗauke da takalmana a hannu. Babu kowa a falon, na ajiye takalman na nufi kicin, kuku harya kammala haɗa mana breakfast ni da Yah Qaseem, tea na shiga haɗawa muna gaisawa dashi, ban fitaba na zauna a ɗaya daga kujerun huɗun dake a kicin din, tebir a tsakkiyarsu, ina fara shan shayin Yah Qaseem na shigowa shi da Salman. Nayi mamakin ganin Yah Salman da wannan farar safiyar, shi da kullum sai anyi fama dashi ma yake tashi da safen yay shirin zuwa aiki, da yake a kamfanin Dad yake aikin sai yakai goma bai fitaba ma. Hannu Yah Qaseem ya miƙomin alamar mu gaisa, amma sai na girgiza masa kai ina murmushi da faɗin, “Yaya ina kwana”. Hararata yayi sannan ya zauna, Yah Salman da shima ke zama ya taɓe baki. Shima gaishesa nayi ya amsa a ɗage kamar yanda ya saba. Ban sake bi takansuba naci gaba da shan tea ɗina nidai, suma kowanne ƙoƙarin karyawan yakeyi. Ban wani ci abincin kirkiba na tashi na koma falo na barsu a kicin ɗin, ina ɗaura takalmina sai ga Yah Qaseem ɗin ya fito yana faɗin, “Tashi muwuce mun makara”. Miƙewa nayi muka fice. ★★★★★ Yayin da muka isa office ina fitowa daga mota da shi na fara tozali. Hakanne ya saka gabana faɗuwa, ganin bamu yake kalloba na ɗauke kaina daga garesa, sai ta gefen ido nake satar kallonsa, sanye yake da jeans ruwan toka da farar shirt mai gajeren hannu, idanunsa sakaye cikin glasess da yay masa matuƙar ƙyawu. Dole inda suke tsaye shi da wani a jikin wata mota itace hanyar da zanbi ta kaini inda zanje, sai kawai na canja hanya saboda yanda nakejin gabana na cigaba da tsananta faɗuwa. Nidai nasan ba tsoro bane ba, sai dai yanamin kwarjini da zan iya rantsewa wani ɗa namiji bai taɓamin irinsa ba, bansan miyasa hakanba? Bankuma san minene dalilin hakanba?. Hanya na canja, sai dai inajin tamkar ana bina da kallo, juyowa nayi kaɗan dan inga ko zanga mai kallon nawa, sai dai banga kowaba. Na cigaba da tafiya ina karanto addu'ar duk da tazomin kan harshe. Ikon ALLAH tunda nayi nesa da wajen dana gansa sai na koma normal, harna ƙarasa wajen da nake ƙyautata zaton ganin Ummie. Ɓangaren Jawaad kam da a yau suka dawo aiki shi da tawagarsa, ya iske ayyuka da dama, musamman waɗanda suke da matuƙar haɗarin da ake buƙatar mutum mai ƙwazo da jajircewa irinsu, wasu ayyukan kuma an badasu ga wasu jami'an ne amma sunata musu tafiyar hawainiya basu ƙarasaba babuma wani bayani mai gamsarwa, hakan yasa yau aka miƙasu gaban su Jawaad ɗin. Kansa yaɗauki zafi da ganin ayyukan dake jibge a gabansu, duk da kuwa a yanzu sun sake samo dabaru na musamman shida abokan aikinsa da suka samu zuwa wannan horo na musamman a ƙasar amuruka, ya kuma dawo ne da karsashin aikin canja wani abu a ƙasarsa dan bai isa canja komaiba shi yasan wannan, irinsu masu son jajircewa ƙalilanne, tayaya kuwa suka isa canja komai? Sai dai suyi nasu ƙoƙari su koma gefe, UBANGIJI shike da sauran hanyoyin maganin sauran tunkafin nasu, rahamarsace ta saka zukatansu suma jin son gyaran. Baƙon da yayi wani abokinsa da sukai secondary tare lauya, yazone bincike akan wani case shine ya rakoshi suka tsaya a jikin motarsa suna magana. Sarai Jawaad yaga lokacin da Qaseem da Bily suka fito a motar Qaseem ɗin, amma sai ya ɗauke kansa cikin basarwa, duk da a ƙasan zuciyarsa yana tunanin minene alaƙar Qaseem da wannan yarinyar? Saboda a koda yaushe yake ganinsu tare da juna. Sai kuma akai rashin Sa'a shima abokin nasa idonsa suka hango su Bilkisun. Yace, “Woow, Jay kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta mai tsada da daraja kuwa?”. Jawaad da ras ya fahimci inda abokinsa ya dosa tsabar rainin wayo sai yay tamkar bai fahimtaba............✍🏻 Page 38 ..............Bayan wucewar abokinsa office ɗin Sir Ahmad ya wuce domin amsa kiransa, yana ƙoƙarin shiga yaci karo da Qaseem shima ya fito. Ƙoƙarin ɗauke kai Qaseem keyi, shima Jawaad ɗin har yayi niyyar hakan, sai kuma yaga rashin ƙyautuwar abun, Murmushi ya saki har kumatunsa na loɓawa, ya miƙama Qaseem hannu yana faɗin, “Assalamu alaika”. Ƙin miƙo nasa Qaseem yayi, sai dai ya amsa masa sallamar. Jawaad ya kamo hannun Qaseem cikin nasa tare da faɗin, “Haba ɗan uwana, miyay zafi shiba wutaba? Ina fatan na sameku lfy? Ya jama'ar gidan?”. Ran Qaseem ya sosu da wannan rainin hankali na Jawaad, danshi matsayin rainin hankali kawai ya kalli abun, dan haka ya kasa daurewa yace, “Da wannna salon kuma ka dawo?”. Jawaad ya murmusa yana sakin hannunsa, cikin gyara tsaiwarsa yana shafa gemu da tura hannunsa ɗaya a aljihu yace, “Minene abin salo anan Qaseem? Kaifa ɗan uwanane jinina, sannan ga alaƙar musulinci a tsakanina dakai, kuma kai yarenane, ogana a wajen aiki, shekara biyu rabon da ka ganni na ganka, da akwai ƙaddarar mutuwa tsakaninmu maybe wani zai samu saƙon mutuwar wanine a tsakaninmu, nidai tsakanina da ALLAH na gaisheka, ya rage naka ka ɗauka hakan kaima ko saɓaninsa, na barka lafiya”.. Sagade Qaseem yay yanabin Jawaad da kallo harya shige office ɗin Sir Ahmad, yayi kamar ya bisa cikin office ɗin sai kuma ya fasa, ya nufi office ɗinsa yana juya kalamun Jawaad cikin ransa. Jawaad kam koda ya shiga, bayan yayi gaisuwar girmamawa ga sir Ahmad sai ya nuna masa wajen zama. Hannu Sir Ahmad ya bashi cikin musabaha suka sake gaisawa, dukda dai Jawaad na nuna jin kunyar haka ɗin. “Jay kasan miyasa na kiraka kuwa?”. “A'a Sir”. ‘Jawaad ya faɗa cikin kaɗa kai’. Zama sosai Sir Ahmad ya gyara, ya fara magana idanunsa akan Jawaad ɗin. “Wato zakayi mamaki idan nace maka baƙin abubuwa da yawa sun sake shigoma hukumarnan, masu ban tsoro da mamaki. Akwai cases da yawa dakai kanka ka fara ka tafi kabari to ina mai tabbatar maka da yawansu ba'a ƙarasa suba har zuwa yau da nake maka maganar nan, waɗanda kuma aka ƙarasa ɗin sun canzu ga bisa salon daka barsu gaba ɗaya ma. Gashi wasu cases ɗin sun sake ƙaruwa da yawa, akwai jami'inmu mai matuƙar ƙwazo kamar kai ɗinnan, bayan tafiyarku nagartarsa ta sake fitowa, amma kamar yanda na sanar maka ranar ya fita wani aiki sai dai gawarsa aka kawo mana, kasan wani abun mamaki?”. Jawaad da idonsa ya kaɗa yay jazur ya girgiza kansa. Murmushi Sir Ahmad yayi na takaici yana cigaba da faɗin, “Abun mamakin da har yanzu yake cizon zuciyata shine bullets guda uku da aka harbi Abdallah dashi a ƙarjinsa da cikinsa dukansu bullets ne na jami'an tsaro, abi mafi al'ajab Bullets ɗin suna cikin bullets guda dubu sittin da shida da aka kawo ƙasarnan shekaru tara da suka wuce, waɗanda a zahirance bayanai sun nuna bullets ɗin sun ƙare gaba ɗaya bayan shekara ɗaya da wata bakwai da kawosu, bullets ne masu matuƙar haɗari, dan inhar akai harbi mutum dasu acikin seconds ashirin dukkanin illahirin jinin mutum ke tsinkewa, idan ba'ai gaggawar kaisa asibiti ba ya samu taimakon gaggawa zai iya rasa ransa a ƙanƙanin lokaci, sannan ba a kowacce bindiga yake aikiba. To abin tambaya anan, yaya akai bullets ɗin da suka ƙare shekara huɗu baya kuma suka kashe mana jami'inmu? Daga ina suka fito? Wasune aka sake shigowa dasu? Koko dai sune ɗin?”. Gaba ɗaya jijiyoyin Kan Jawaad sun mimmiƙe ruɗu-ruɗu, maƙoshinsa sai kaikawo yake a wuyansa saboda tsabar haɗiyar busashshen yawu mai ƙona zuciya. Ya matse idanunsa tare da rumtse hannu, muryarsa a matuƙar kausashe yace, “Sir akan wane case wannan abun ya faru?”. Sir Ahmad yay murmusa idonsa akan Jawaad, mazantakar Jay akan aiki da kishin ƙasarsa yasa ako wane lokaci yafi sha'awar ganinsa akan aiki na musamman, yaɗan ɗage kafaɗa yana buga tebir kaɗan da komawa cikin kujera ya kwanta, har lokacin idonsa akan Jawaad, “Jay ƴan bindiga daɗi ne kawai, amma ga dukkan bayanan komai anan”. ‘Ya ƙare maganar da tura masa wani file gabansa’. Ɗauka Jay yayi ba tare daya buɗeba, babu abinda zuciyarsa keyi sai tafarfasa kawai, shiru Office ɗin yayi na wasu mintoci, kafin Sir Ahmad ya katse shirun da faɗin, “A yanzu kana buƙatar runduna ta musamman Jay, fiye dasu Jabeer kawai, munada sabbin ma'aikata masu jini a jika da karsashin aiki a ransu saboda yanzune jinin jikinsu ke zagayawa cikin kowacce jijiya dalilin ƙuruciya da zafin rai mai tare da ɗokin aikin, sannan a cikinsu akwai kwararrun maharban da suka samu horo na musamman a ɓangaren harbi, wanda an daɗe ba'a yaye sabbin horaswa da wannan ƙwazonba a hukumarnan tamu, shawara kawai na baka ba umarniba, dan zuciyata ta yarda da kai, yarda irin wadda ko ɗan dana haifa ban yimawaba duk da kasan cewarsa jami'in tsaro shima, ALLAH yayi jagora haziƙi kuma jarumin yarona abin alfaharin ƙasarsa da ƴan ƙasa”. Zazzafan numfashi Jawaad ya sauke yana miƙewa idonsa a matuƙar jazur tamkar ya haɗiyi wuta, yay salute din sir Ahmad sannan ya fice tamkar wanda zaije filin daga. Koda ya isa office ma gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take, yama rasa wane kalar tunani ya dace ace yayi, dan lamarin ƙasarsa a kullum sake bashi tsoro take, tsoro irin mai firgitarwa da ban ta'ajibi, komai anayinsane saboda kuɗi, kuɗi! Dai kuɗi! Dai, sai yaushene mutane zasu ajiye son zuciya da burin mallakar kuɗaɗe su amshi gaskiya? Da wannan rayuwarne kuma kullum muke fatan ganin kayinmu cikin aljanna, a haka mukeso ALLAH yay mana rahama, a haka mukeso MANZON ALLAH yayi alfahari damu?, Ya rumtse idanunsa sosai yana cigaba da haɗiyar ɓacin ran daya tokare maƙoshinsa. Bai sake fitaba, bai kuma sake barin wani ya gansaba koda a cikin su Aliyu ne, dan kulle kansa yay a Office ɗin yanata saƙawa da kwancewa. Har sai da lokacin salla yayine sannan ya fito domin gabatarwa. ★★★★★★ Bayan sallar la'asar ya bama Rose damar tattara masa ƙananun jami'ansu sabbin ɗaukar wannan karon. Duk da tayi mamakin hakan sai bata tambayesa ba, dan bataga alamun wasa tattare da shi ba, a yandama taga fuskarsa a matuƙar murtuke sai abun ya bata tsoro, dan irin wannan fushin nasa mafi yawan lokuta sukan gansane idan aiki ya ɗauki zafi. Bamusan miya faruba mudai an taramu waje guda, inda aka nema mu rabu rukuni-rukuni akan abinda mukafi samun ƙwarewa dashi a wajen horaswa. Ina cikin jami'ai masu ƙwazo da suka samu ƙwarewa wajen harbi, dan haka banyi ƙasa a gwiwa ba wajen shiga cikinsu. Sai da duk muka gama rarrabuwa sannan wanda ya saka a taramun ya fito. Yanda sautin takun takalman ke fidda ƙara haka nake jin sautin bugun zuciyata na fidda ƙarar bugu, zuwa yanzunkam na ɗan fara jin tsoro, ba komai ya kawo tsoron nawa ba kuwa sai fahimtar da nai kasantuwar wannan mutumin a kusa dani ke kawo min wannan yanayin da bansan dalilinsa ba. “Miyasa sai a kansa kawai?” naima kaina tambayar da bani da amsarta..... Na tafi tunani sam bansan bikin da ake ba, sai da naji ƙarar sautin bugawar ƙafarsune nai firgigit, dai-dai zasu ajiye hannayensu da sukai Salutes nashi. Hakan ya sakani saurin kallon inda yake nima ina ƙoƙarin kai hannuna saman goshina. Karaf na tsinci idanunsa a kaina yana watsamin wani kallo mai kama da gargaɗi. Ƙasa na maida kaina, muka ajiye hannayenmu tare da ƴan uwana. Tsayuwarsa ya gyara har yanzu dukkan hannayensa na cikin aljihun jeans ɗinsa ruwan toka, ƙamshin turarensa na cigaba da addabama ƙofofin hancinanmu, ya ɗan furzar da huci kaɗan yana cigaba da tsatstsaremu da idanunsa masu ban tsoro, gasu yau sunyi jazur alamun yana tattare da ɓacin rai. Ganin yanda yake mana kallon ɗaɗɗayan ne yasani fahimtar nazartarmu yake ɗaya bayan ɗaya, babu zato muka tsinkayo muryarsa mai tarin nutsuwa wadda yau shine karo na farko da zan jita, sai dai kuma bamu yay ma maganarba, hakan yasa bamuji miya faɗa ɗinba duka bayan kalmomin farko na ambatar suna Rose da yayi. Rose dake gefensa ta kallemu tana matsowa kusa damu sosai da mana bayani akan abinda yace. A cikin kowane rukuni yana buƙatar mutum biyu, dan haka zai gwada ƙwazon kowa. Mun amsa da girmamawa, kafin kowane rukunu a haɗasu da waɗanda zasuyi nusu gwajin. Ni dai har muka bar wajen ban sake yarda na kallesa ba, hasalima gaba ɗaya na kasa samun sukuni, na sauke ajiyar zuciya ina dafe kaina, tare da fatan ALLAH ya kawo mani sauƙi akan wannan *Sabon al'amari* dana tsinci kaina a ciki. Mun isa wani ɓoyayyen wajen sirri na hukumar mai ban tsoro, dan kuwa yau naga abinda a films kawai nake gani, wato manya-manyan makamai masu ban tashin hankali, yanzu dama a ƙasarmu akwai irin waɗannan manyan mahaukatan makaman irin haka? Gaba ɗaya ganinsu ya saka karsashina guduwa, sai binsu muke da kallo tamkar wasu sokaye, mun daɗe munaji a labari babu jami'an da suka kai hukumar DSS mahaukatan bindigu. ban taɓa gasgata hakanba sai yau da idanuna suka ganemin zahiri...... Jin takun mutum a bayana ya sakani saurin juyawa, nai saurin matsawa gefe ƙirjina yana bugawar da bai taɓa yiba, dan sam bansan sanda ya shigo wajenba balle isowarsa kusa dani irin haka. Baiko nuna yasan dani ba a wajen ya zuge glass ɗin da nake dab, hakan ya sakani yin gaba da sauri. Jawaad dake hidimarsa cikin halin ko in kula ya ciro wata ƙaramar bindiga mai ƙyau ruwan Silver, sannan ya taka zuwa kujerar dake tare da tebir ya zauna yana ɗora bindigar da harsasai kusan guda takwas. Jabeer da suke tare ya ɗauki bindigar da Jay ya ajiye ya ɗura harsasan robar dake tare da bindigar a cikinta suna magana da Jay wadda sam su bily basajinsu. Bayan Jabeer ya kammala ya nufi su Bily dake tsaye suna jiransu. Umarni ya bamu akan mutum ɗaya yazo, dama dukanmu mu bakwaine, na rasa yanda zanyi na iya samun cikakkiyar nutsuwa a wajennan, nikam a raina nama fara zargin wannan mutumin ko yanada aljanin da baya sonane shiyyasa yake kiɗimani? Kokuma shine aljanin kansa?. Ta yaya dukkan mutane ina mu'amula dasu hankalina kwance, sai shine a duk lokacin da muka samu kusanci gabana zai keta faɗuwa? Wannan lamarin da mamaki wlhy........... Ƙarar harbin da ɗaya a cikinmu tai bisa allon gwajine ya maidoni a hayyacina babu shiri, danma harsashin robane, amma a hakan ba ƙaramar firgita nayi ba. Kallon da sukemin ya sakani yin murmushin yaƙe, shima na saci kallonsa, sai na tsinci idonsa a kaina, amma saiya janye kamar ba haka bane, ya maida ga allon da wancan yay harbin. Sai kuma mukaga ya taso zuwa garemu, hakan ya sakani sake aro nutsuwa na azama kaina, ya karɓi bindigar hannun Oga Jabeer ɗin, a wani salon kai tsaye ya harba harsashin saɓanin mu da sai ka tsaya wajen nutsuwar ina zaka harba. A tsakkiyar inda ake buƙata harsashin ya shiga anan kuwa ya shige jikin allon, ya juyo yana fuskantarmu sosai, “Wannan shine wajen da nake buƙatar kaɗai harsashi ya shiga”. Iya abinda yace kenan ya wurgama Oga Jabeer bindigar shiko ya caɓe. Na ƙagara yabar wajen, amma sai naga yama gyara tsaiwarsa alamun babu inda zaije. Ɗaya bayan ɗaya muke zuwa kowa yana gwada ƙwazonsa, amma ni na kasa tafiya, dan ji nake tamkar bazan iya komaiba a gabansa. Wanda daga shi sai ni dana rage ta ƙarshe yayi shima, hakan na nufin dai duk wayon amarya sai ansha manta, dan ta laɓe-laɓe ta ƙare kuma. Haka na taka nima na amsa, sai dai hannuna rawa yakeyi, gashi duk sun wani zubamin idanu. Cikin karanto addu'a na fara dake raina da maida hankali akan abinda ke gabana. Amma sai babu zato naji ƙamshin mayen turarensa mai daɗin shaƙa ya sake kusantoni..............✍🏻 Page 39 .............“Ki maida hankali akan abinda kikeyi”. Muryarsa mai tarin nutsuwa da amo ta daki dodon kunnena, yayinda zuciyata tai wata irin bugawa tamkar zata faɗo ƙasa, idanuna suka cika da ƙwalla. Ruɗanin dana shiga na babu zato babu tsammani ya sakani danna kunamar bindigar ba tare dana saniba..... Ji nai kawai sautin tafi na tashi, nai azamar kallonsu kafin na maida ga allon harbin, sai naga na harba ainahin inda ake buƙata. Bansan murmushi ya suɓuceminba, na saci kallonsa sai naga wayam yabar wajen ma gaba ɗaya, yana daga can gaban kantar da aka zagaye ɗakin da ita aka kuma rufeta da glasess baki ɗaya, wasu bindigu yake zubama harsasai tamkarma baisan mi akeba..... Maganar oga Jabeer ta sakani maida kallona garesa, yace, “Lallai kin cancanci a kiraki gwanar harbi”. Murmushi nayi da faɗin, “Nagode sir”. Dai-dai Jawaad ya dawo wajen kalamar godiya da Bilkisu kema Jabeer ta shiga kunnensa, yay musu kallo ɗaya yana ɗauke ido da ƙara tamke fuska ya miƙama Jabeer bindugun hannunsa. Amsa Jabeer yayi ya miƙama kowannenmu a hannunsa, sannan ya nuna mana inda kowa zai harba ba tare da ya mana bayanin dalilin hakanba. Duk jeruwa mukai, kowanne ya zam cikin shiri kafin Oga Jabeer ɗin ya irga uku sannan ya bamu umarni. Koda muka harba nidai idanuna na lumshe dan nasan dai bai zama lallai na zam cikin masu nasara tamkar ɗazunba, “Inhar zakuyi harbi ku rufe idanunku da tunanin rashin nasara to lallai wataran a filin daga wani zai fasa kayinku da nasa harsashin”. Maganarsa ta shiga kunnuwan kowannenmu babu zato, saurin buɗe idanuna nayi da mamakin jin furucinsa, musamman ma da naga ba'a kusa dani yakeba, hasalima ya nufi ƙofar fitane zai fice daga wajen. Dukanmu da kallo muka bisa harya fice. kafin sauran ƴan uwana su shiga ma juna kallon-kallo, kowa nason fahimtar wanene ya rufe idon a cikinmu?, sai dai babu wanda ya samu amsarsa. Jabeer yay murmusa yana girgiza kansa kawai, da maida kallonsa gasu Bilkisu. Shima sallamarmu yayi, dan haka duk muka fito kowa yana ƴar maganarsa da wanda halinsa ya saɓa, mu biyune mata a ciki kawai, ita kuma tunma a wajen training bama shiga sabgar juna da ita. Koda muka fito sai na shiga neman Ummie, na iske su basu fitoba, komawa nai bakin aiki, sai dai duk yanda naso ture abinda ya faru a raina yaƙi turuwa, sai kai kawo yakemin a zuciya da ƙwaƙwalwa. A wannan yanayin Ummie tazo ta sameni, tun tana kallona harta kasa jurewa ta jehomin tambaya, “Madam wai yaya dai?”. Kallonta nai da mamaki, Nace, “Kamarya?”. Dariya ta ƙyalƙyale da ita tana girgiza kanta, “Kinga bar zaromin idanu tambaya kawai nayi”. Ƙwafa nai mata ina ɗauke idanuna daga kanta da faɗin, “Gulmammiya”. ★★★★★ Kwanaki huɗu kenan da faruwar wancan gwajin wani abu bai sake tasowa ba, hasalima ban sake ganinsa ba. A ɓangarena ma nima nayi shiri tsaf na fara binciken wanda ya keta martabar Amina a cikin gidanmu, shiyyasa yau data kasance lahadi banje ko inaba na sameta a gidansu, nayi amfani da lokacin zuwa islamiyyata ne dana maida duk ranar lahadi, yau sai haƙura nayi da zuwa na yada zango a gidansu Amina. Da sallama na shiga, Amina dake zaune a ƙofar ɗakinsu tana tsintar shinkafa ta ɗago tana amsamin fuskarta ɗauke da murmushi, sai kuma ta fara tsokanata da faɗin, “Wai! Yau babbar baƙuwa garemu ashe?”. Hararta nai ina jan kujera na zauna kusa da ita, na kalli mama dake mana dariya tana ta ƙoƙarin haɗa wutar abinci nace, “Mama kina jinta ko?”. Mama tace, “Toni ai wannan faɗan bana shigarsa daga baya azo a matseni”. Dariya mukayi gaba ɗaya, sai da muka tsagaita na shiga gaida mama, ta amsa min cikin kulawa tare da tambayata yaya aikina?. Nace, “Alhmdllh mama munata gwaji, dan har yanzu ba'a gama sabawa ba”. “Karki damu Bilkisu za'a saba, harma ya zama jiki wataran kuzam kune ake ambata a ƙasar mugaye su tsorata”. Murmushi nayi kawai. Sai Amina ta amsa da “Insha ALLAHU kuwa mama” muryarta a kausashe na alamun tasowar ɓacin rai. Tausayinta ya kamani, na dafa kafaɗarta ina shafawa alamun lallashi agareta. Tai murmushi mai ban takaici ba tare data iya cemin komaiba. Shiru na mintuna kusan biyu ya biyo tsakaninmu, ita tana cigaba da tsintar shinkafarta ni kuma ina buɗe littafin da nazo dashi gidan, ɗagowa nai na kalleta, itama sai ta kallenin. “Amina nazone mu fara magana akan wancan abun da ya faru a waccan ranar, ina fata ban shiga uzirinkiba?”. Murmushi tayimin, “Kai Bilkisu, ni wane uziri gareni, kimin duk tambayar da kikeso, ni kuma zan baki amsa inhar na sani”. Kaina na jinjina mata, kafin na jeho mata tambaya, “A waccan ranar da abin ya faru, kowa yana gidan?”. Shiru Amina tayi na kusan sakanni goma, kafin tace, “Eh to, lokacin dana shiga kowa yana nan, dan kinsan da zaran nayi sallar asuba nake shiga, sai kuma azhar na dawo gida, na koma bayan sallar la'asar sai goma nake dawowa gida, sai idan Alhaji na nanne yakan ce da nayi sallar magriba naje gida na huta, to a waccan ranarma ina idar da salla na shiga gidan, bayan mun gaisa da baba mai gadi ya tsokaneni kamar yanda ya saba, sai na wuce ciki, na fara gamo driver yana wankema Yah Qaseem mota, shima muka gaisa na shige. Ban iske kowa a falonba sai motsin kuku a kicin, na shiga muka gaisa da shi, shima ya tsokaneni tamkar yanda ya saba mukai dariya kafin na fito na fara ƙoƙarin gyaran falo. Harma na kammala gyarawar ina morping Yah Qaseem ya shigo, duk da bansan lokacin daya shigoba ma dan jinai kawai tamkar kallona ake, shine na juya na gansa tsaye, a ɗan rikice na gaishesa dan bansan dalilin kallonba, shima ya amsa yana wucewa kicin ba tare da ya sake kallon nawa ba. Nai ajiyar zuciya ina cigaba da aikina, harna kammala na hau sama shima na gyaro, lokacin dana sakko na iske Yah Qaseem ya fita”. Ta sauke numfashi tana share hawaye, kafin ta cigaba da faɗin, “Kinsan sai sun tsashi nake samun damar ƙarasa aikin? To ranarma saina wuce kicin tamkar yanda na saba na zauna muna hira da kuku ina karyawa, banfi zaman mintuna gomaba Mummy ta ƙwalan kira, na amsa ina ajiye filet ɗin hannuna ina fita. Na isketa cikin shirin fita, na gaisheta cikin risinawa, tana laluben abu a jakka take amsamin, ta bani umarnin zuwa na taso mata Yah Salman. Da to na amsa ina ficewa. Nayi sallama a ƙofar ɗakinsa yafi sau biyar, sai dai babu amsa, sanin halinsa ya sani tura ƙofar na shiga kawai, yana kwance ɗai-ɗai a gado da ga shi sai guntun wando, nai ƙasa da kaina ina kiran sunansa. Kamar yanda ya saba ya tashi a fusace yana mai zagina akan ubanmi nazoyi?. Amsa na bashi da cewar Mummy ce tace na tasoshi, wawan tsaki yaja nidai na fice abina naje na sanar mata cewar gashinan”. “Bayan na sanar mata ta cemin zata fitane, idan Aunty Aamilah ta tashi na sanar mata taje can ta sameta inda sukai magana jiya, na amsa da to na nufi sama dan ƙarasa aikina”. “Bansan fitar Mummy ba, dan inacan ina aiki, bayan na kammala na sako na nufi kicin, ina ƙoƙarin shiga Yah Salman zai fito, dan jaka mukai karo da juna harna faɗa jikinsa, muguwar mamuƙar da yaymin ba ƙaramin tsoro ta baniba, dan bilhaƙƙi da gaskiya ya rungumeni tare da matseni tsam a jikinsa, nai saurin turesa ina hawaye.......” Ta kasa ƙarasawa tana sharar hawayen yanzunma, ni kaina idona ya cika da ƙwalla, handkherchief ɗin hannuna na miƙa mata, ta girgiza min kanta da cewar, “Kona goge waɗanda suka fisu zasu zubo, tuni alƙalamin ƙaddara ya fahimtar dani share hawaye a gareni bashi da wani amfani Bilkisu”. Da ƙyar na iya haɗiye yawun daya tokare min maƙoshi, nace, “Sai mi ya faru kuma bayan hakan?”. Ta ɗan taɓe bakinta tana ajiye tiren shinkafar da take tsinta, tace, “Tsaki yaymin ya fice a binsa, nima sai na samu kaina da jan tsakin ina shigewa, dama da shirin fita aiki na gansa, dan haka muna daga kicin ɗin mukaji fitar motarsa, itama Aamilah bata jimaba ta tashi a barcinta ta karya tabi bayan Mummy, ya rage gidan daga ni sai kuku da baba mai gadi”. Can baya na koma nai zamana a wajen ni kaɗai tamkar yanda na saba, da ga baya da naji na takura saima na fita a gidan na dawo gida, sai dai na iske mama bata nan itama, dama kuma ta faɗamin zataje gaisuwa, jinai nan ɗinma babu daɗi, na sake fita na koma can gidan, na kwanta a falo, anan barci ya kwasheni, ban farkaba sai ana kiran sallar zuhur”. Bayan na idar da salla ne na shiga kicin na samu abinda zanci, banga kuku ba, bankumaji motsinsa ba sam, abinci na ɗiba na zauna naci, tsautsayi ya sakani ɗaukar lemo nasha, abindama bai cika damunaba, duk da kuwa ba'aimin iyaka da dukkan wani nau'in abinci dake gidanba, duk abinda masu gidan zasuci Dad ya bani umarnin nima na ɗaukesa naci, kuma sam dukda halayar Mummy bata da ƙyau tanan ɓangaren dolene a yaba mata, ko wanene kai bata ƙyashin kaci komi zasuci, dan duk abinda sukaci shine ma'aikatan gidan keci, kuma za'a baka yanda zai isheka kaci ka ƙoshi”. “Wannan lemo shine sanadin komai, daga shansa ban sake sanin ina hankalina yake ba, sai dai tashi nai na ganni a mawuyacin hali a gidannan.....” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”, naketa maimaitawa, na share hawayen dake zubamin a ido ina riƙo hannun Amina. “Amma Amina wa kike zargi a cikin gidannan da aikata miki wannan abun?”. Hawayenta ta share tana murmushi mai ciwo, “Bilkisu ni bana zargin kowa, sannan kuma duk ina ƙyautata musu zato”. “Humm Amina su kuma basa ƙyautata miki zaton, dan da suna miki ƙyaƙyƙyawan zato da basu biyema son ƴaƴansu ba da zuciyarsu wajen kasa fahimtar an cuta miki, tabbas a wannan gaɓar abin yazo mini da ruɗani, dan zuwa yanzu hatta kuku da baba mai gadi suna cikin zargina”. Amina ta zaro idanu tana kallona, hakama mama daketa aikinta tana saurarenmu sai da ta kalleni, sai dai babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu. Nace, “Karku damu, shi laifi kowama yana iya aikatashi, musamman ma irin wannan”. Dukansu kai suka jinjinamin alamar gamsuwa, na miƙe zan tafi mama tace babu inda zanje sai naci abinci, dan yau ɗanwake takeyi. Dole nabi Umarninta na koma na zauna ina murmushi, ganin Amina tana tattare da damuwa na fama mata ciwon da nayi sai na shiga bata labarin wajen aikinmu, musamman inda na nuna ragwantaka a wajen trianing, aiko taita kwasar dariya mama na tayata. Bansan yaya akaiba har abinda ya faru dani a airport akan mutuminnan sai da na bata labari. Aiko taita kwasar dariya harda hawaye, wai mazari sunga mazaje. Ganin ta shiga cikin farin ciki nima sai naji sanyi a raina, koda mama ta kammala tare mukaci abinci mu uku a kwano ɗaya munatama mama santin ɗan waken da yaji daddaɗan yaji daketa ƙamshin tafarnuwa da kayan kamshi. Ban bar gidanba har sai da kiran yah Qaseem ya shigo wayata, ina tunanin ya dawo gidane, dan shi yau ya fita akan wani aiki da yakeyi. Sallama nai musu na tafi ina jera musu godiya suma sunamin tare da addu'ar fata alkairi...........✍🏻 Page 40 .............Ina ƙoƙarin shiga gida kiransa ya sake shigo mani, ɗagawa nai da nufin faɗa masa ganinan zuwa gidan, amma sai naji yana magana mai alamar ba'a gidan yakeba.. Ya bani umarnine akan na duba ɗakinsa akwai wasu takardu ɗaya daga cikin jami'inmu zaizo ya amsa, na amsa masa da to kafin na yanke wayar na ida shiga da hanzari. Kamar yanda ya umarta hakan nayi, ina fitowa na iske wanda aka turo ɗin yazo, shima yana sama dani, dan haka nai masa gaisuwar girmamawa kafin bashi takardun na koma ciki. Duk da na iske su Mummy a falo ban iya zama ba, gashesu kawai nayi na shige ɗaki abuna, dan ina buƙatar samun filin yin tunani akan abinda muka tattauna da Amina. Sosai komai yake neman ɗaure kaina, duk da kuwa Alhmdllh yanzu na samu ilimi sosai game da bincike, dan ko a wajen horaswa da muka samu, nafi maida hankalina anan sosai, alamu sun nuna Qaseem da Salman basa gida, shin akwai wanda ya dawo daga baya kenan s cikinsu? Ko kuwa kuku zan zarga kai tsaye ne? Baba mai gadi tsoho ne, duk da dai tsufansa bai kai ace bazai iya aikata makamancin hakanba, to amma miyasa zan zargesa ne? Lallai ya dace nama fara bincikarsa akan shiga da fitar kowa a wannan ranar. Da wannan tunanin naɗan samu nutsuwa, amma koda nai shirin barci na kwanta sai ya gagara, babu abinda nake sai saƙawa da kwancewa tare da tunanin iyayena. _______________________________ Washe gari litinin muka tashi da shirin aiki, tunda na gama shiri naga harna shiga kicin ina shan tea Yah Qaseem bai shigoba nasan bai kwana gidaba jiya kenan?. Tea ɗin kawai na iya sha na fito, babu wanda ya tashi har yanzu a mutanen gidan. Nai addu'a na fita tamkar yanda na saba. Yau kam sai driver nabi, muna isa tamkar jira na samu saƙon kira. Na nufi inda ake kiran namune na haɗu da Yah Qaseem, murmushi mukaima juna, na gaishesa cikin girmamawa tamkar yanda na saba. Shima ya amsamin da kulawa yana tambayata yaya gidan?. “Alhmdllh Yah Qaseem, yaya aikin naka? Ai ni bansan baka kwana gidaba sai yanzu da safennan?”. Yace, “Oh, wannan wace irin matace dani? Ban kwana a gidaba amma sam bama ta saniba”. Haka kawai sai maganarsa ta sakani jin kunya, naja baby hijjab ɗina na rufe muskata ina murmushi, matsowa yay kusa dani gab tamkar zai shige mini jiki, ya kai bakinsa dai-dai saitin kunnene yana faɗin, “Baƙauya”. Baya na ɗan ja saboda kusancin da muka samu yayi yawa, na janye hijjabin zan bashi amsa karaf idona akan mutumin ga, gabana yay wata masifaffiyar faɗuwa saboda cin karo da wata shegiyar harara daya watsomin, tuni fara'ar fuskata ta ɗauke baki ɗaya saboda bugun da ƙirjina yakeyi. “K lafiya?” Ƴah Qaseem ya faɗa cikin tsareni da idanu. Cikin rawar baki da hadiye yawu da ƙyar nace, “B..babu k..omai”. Idanunsa ya ɗauke da ga kaina ya maida saitin inda nake kallo, sai dai yana juyawa shi kuma yana shigewa Office. Sake juyowa yay gareni, “Wai haushi kikaji dan nace miki baƙauya?”. Murmushin ƙarfin hali nai masa ina girgiza kai, nace, “A'a yayana”. Ƙaramar dariya yayi ya dungure min kai tare da zagayeni ya wuce abinsa da faɗin, yaje gida sai ya dawo. Ko a dawo lafiyar ban iya ce masaba, na kuma kasa ɗaga koda ƙafata a wajen saboda tsabar yanayin dana tsinci kaina. “Haba Bilkisu! Ke kin cika matsala wlhy, tsayuwarmi kuma kike anan?”. Nannauyan numfashi na sauke jin muryar Ummie a kusa dani, taja hannuna ba tare da ta sake magana ba zuwa inda ake jiranmu. Sosai mamaki ya kamani ganin inda ta kawo mu, zan iya kiransa Office kai tsaye, amma mazauna cikinsa da zasuyi amfani da shi aƙalla mutane goma cif. Tunda naji zuciyata ta dai-daita nasan baya wajen, dan haka nakai dubana ga kowa, iya dai mune da aka tara ranar, tare da yallaɓai Hafiz. Ya gyara tsaiwarsa yana mana bayani yanda zamu fahimta sosai. “Wannan Office ne da zai kasance na musamman ga waɗanda boss ya aminta da ƙwazonsu, dan haka sai kowa ya duba, idan kaga sunanka to kana cikin waɗanda ya zaɓa, idan baka ganiba to ba hakan yana nufin bazai iya aiki da kai bane ko bai yabama ƙoƙarin kaba, kawai dai kasan a ranka hakanne mafi alkairi a gareka”. Duk cikin girmamawa muka amsa masa. Ni kasama dubawar nayi, sai Ummie ce tabi sauran itama tana dubawa, inajin wasunsu suna murna, alamar dai sunga sunayensu. Nima a bazata naji Ummie ta rungumeni tana faɗamin ni da ita duk muna ciki. Ban san miya saba, banji baƙin cikiba, kuma banji wani murnaba, kawai dai nayi murmushi ne dan karta zargi wani abu.. A cikin mu goma ɗinan bakwai mazane, mu uku mata, ni Ummie sai ɗayar mai suna Divine. Komai na wajen an yisane da tsari, dan an saka mana shingai da kowa bazaiga abinda ɗan uwansa keyi a sashensaba sai idan yaso hakan. Naji daɗin yanda aka saka Ummie kusa dani, duk da ba'a layi ɗaya mukeba wajen zamanta yana kallon nawa, sannan mune ƙarshen bangon wajen. Duk wanda yake cikin wannan tafiya yayi farinciki, saɓanin ni da bansan manufar zaɓin da zuciyata ta ɗauka ba. Shigowar Yah Qaseem station ɗin ya samu labari, bansan dalilinsaba naga ya fara faɗa tamkar zai cinyeni ɗanya, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba. Tun ina saurarensa da mamaki na koma al'ajab, daga al'ajabi nakoma ban haushi, har takai abin ya bani tsoro, danni bansan minene laifina a cikiba? Kuma ince nan wajen aikine, bamu da dalilin cewar sai inda muke buƙata za'a zaɓamana. A cikin masifarsa ta yau ne nakeji cikakken suna mutumin nan, wato *_Jawaad Abdul-aziz yusif_*. Ni dai bance ƙalaba har yaci jarabarsa ya tsire, daga ƙarshe yace na fitar masa a office. Na fito ina share hawayen da suka ziraromin babu shiri, sai shi kuma naci karo da shi. Tafiya yake a fusace tamkar wani ingarman doki, yana ƙoƙarin saka bindiga a aljihun wandonsa na baya, yayinda su yallaɓai Jabeer ke take masa baya suma fuskarsu babu walwala. Yana ƙoƙarin shiga motar da aka buɗe masa ne ya ɗago, sai ko idanunmu cikin na juna. Saurin janye nawa nayi ina kauda kai, a ƙasan zuciyata ina mamakin miya fusatashi har hakane?. Bani da mai bani amsa, dan haka sai ma tashin motarsu na jiyo. Har na bar Office ban kuma sakashi idona ba, hakan na nufin dai basu dawoba daga fitar da naga sunyi ɗazun kenan. Sai kuma har naje gida abin na damuna, haka kawai naji na damu da tsagwaron damuwar dana karanto a fuskarsa, ranar da wannan abun na kwana a raina. ______________________________ Washe garin safiyar talata muka tashi da dawowar aunty Shahudah ƙasar haihuwarta tamkar yanda naji a bakin su Aunty Aamilah, danni dai babu wanda ya sanarmin hakan. Ban damuba, dan nasan koba'a faɗaba bani da muhimmancin sanin irin waɗanan abubuwan tunda basu ɗaukeni dai-dai da suba har yanzu, Dad ne kawai yakemin kallon na mutum mai muhimmanci a cikinsu, sai ko Ya Qaseem da shima nake ƙyautata masa zato akaina. To ni daima aiki nai ficewata abina, dan shine mai muhimmanci a gareni a yanzu, nabar saƙon sannu da zuwa a faɗa mata wajen Aunty Aamilah, dukda dai a ɗage ta amsamin ban damuba nai wucewata driver ma yau ya ɗaukeni, dan Yah Qaseem ma yau bai kwana gidaba. Na fiskanci akwai aiki mai mihimmancin gaske da yakeyi a kwanakinnan, musamman ma yanda ya maida kansa busy ko'a Office bai cika zamaba sosai. ____________________________ Ƙarfe biyar na yamma jirgin su Shahudah zai sauka, dan haka tun ƙarfe biyu su Mummy suketa shirin tarbarta, ansa kuku ya shirya mata abinci na musamman kala-kala tamkar ba cikinta kaɗai zai ciba. Tsabar gata Mummy da kanta ta tisa ƙeyar Aamilah suke gyara ɗakin Shahudah, Aamilah sai tunzura baki take gaba dan bata saba da aikinba. Jitake tamkar taje ta kira Amina, dan ta fahimci amfaninta sosai a gidan a yau, hakama Bilkisu, dan tasan badan wannan ƙaddararran aikin da Bilkisun keyiba ai da yanzu itace zatai gyaran. Haka dai suka kammala Mummy ce ƙarfin aikinma, dan danan ɗakin ya ɗauki ƙyau da haske tamkar ba shiba, shima yau yasan maishi zata dawo garesa. Huɗu nayi Salman ya baro office ya taho gidan domin zuwa tarbar gimbiya Shahudah😝. Gudun karma a ɓata mata rai huɗu da rabi suka bar gidan, sun gwammaci su suje su jirata, amma ba ita taita jiransu ba. Zaman da baifi mintuna ashirinba kuwa jirgi ya sauka, fasijoji suka fara fita, sosai idanun su Mummy nakai. Can sai ga zillaziyya zankaɗaziyya gimbiyoyi mandiyoyin oga Jawaad ta fito cikin takun ƙasaita da gayu. Sanye take cikin wandon blue da yay masifar kama jikinta, sai riga ruwan hoda an rubuta Beauty da ado mai ƙyalƙyali a gaba, siririn gyalenta data yana a kai shima ruwan wandon, sai rigar sanyi data ɗaura a ƙugu, ta toshe fuska da eyeglasess mai nuna blue a jiki. Tabbas tayi masifar ƙyau, kuma duk wanda ya gani tilas ya ƙyasa dan ta cancanta. Aamilah ta tafi da gudu gareta, hakan yasa Shahudah sakin akwatinta da jakkarta ta hannu a ƙasa ta rungume ƴar uwarta, takalman ƙafarta masu masifar tsini badan sunada maɗauri ba babu abinda zai hana su sakata ta faɗi. Wasu daga cikin mutane sai kallonsu suke, musamman irinmu ƴan ƙauye da bamu waye ba😒, dan harda bakuna muka hangame lokacin da Salman yazo ya rungumeta shima. Yanda suka ƙanƙame juna lamarin zattakaici, ta sakeshi ta nufi Mummy ta rungume itama, sai kuma suka sake rungumeta baki ɗaya, hakan dai na nuna suna cikin tsantsar farin cikin ganinta duk da sukanje su ganta a can musamman ma Mummy da Aamilah. A sabuwar motarta da Dad ya saya mata akaje ɗaukarta ita kaɗai, ta kalli Mummy ta kalli motar cikin alamun tambaya. Dariya duk sukai mata, Aamilah ta sanar mata ƙyautar Dad ce. Wani ihu Shahudah ta saki tana ɗane Mummy, motar da kullum take nafarkin mallakarta, ta ƙiyasta kuɗinta bazasu kai ta sayaba shiyyasa ta haƙura, ashe Dad zai cika mata burinta. Yanda take matuƙar murnar ne yasa mutane suka sake maida hankalinsu a kallonsu, wasu zato suke ko daga karatu Shahudah ta dawone akai mata wanna irin tarba da ƙyauta mai tsoka, har dai suka shiga mota zuwa gida idanun mutane na kansu. Daɗi ya ishi Shahudah sosai, dan Dad yay mata bazata irin wadda bazata taɓa iya mantawa ba, sayen motarnan yay bala'in kai mata ko ina a cikin ƙoƙon ranta, har tana tunaninma wace kalar murna zatai masa yasan taji daɗi. Murnar motama ta hanata nutsuwa taci abincin kirki a cikinta, duk da tarin abincin da aka shirya matan kuwa. Wayar Aamilah ta amsa ta kira Dad ɗin, maimakon tai masa godiya da addu'ar fatan alkairi sai kawai taita masa ihun murna da faɗa masa ya cika mata burinta, shi dai yana saurarentane yana murmushi, yanataso yaji ta masa godiya tamkar yanda idan yayma Bilkisu ƙankanin abu take masa amma sai yaji tsit. Maimakon hakan ya taɓa ransa sai ya danne kawai, yama cigaba da nuna mata farin cikinsa na dawowarta, ya kuma tabbatar mata a satinnan shima zaizo ƙasar kodan ita. ★★★ Duk yanda Mummy taso tai haƙuri Shahudah ta huta sannan suyi zancen Jawaad ta kasa, haka ta zayyane mata halin da ake ciki yanzu na tallar ƴammata da ake masa a cikin family ɗinsu. Ran Shahudah ya matuƙar dugunzuma, ta shiga masifa da faɗin Jawaad natane ita kaɗai, duk yarinyar datai gigin shigar mata rayuwar miji wlhy sai ta halakata. Tai shiri akan a daren zataje family house ɗin su Jay, amma sai Mummy ta hanata, ƙin sauraren Mummy tayi, sai da ƙyar, dan ta nuna mata abinfa YAƘIN SUNƘURU yakeso yanzu, dan haka kar tayi gaggawa, ta jira taji abinda suka shirya akan al'amarin............✍🏻 Alhamdullahi ala kulli halin🙏🏻😢. Anan na kawo ƙarshen littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA na ɗaya. Abinda na rubuta daidai ya rabbi ka haɗamu a ladan baki ɗaya, wanda nayi kuskure kuma ALLAH ya yafe mani da ku da kuka karanta🙏🏻😭. Wannan shine wasa farin girki. Ga dai Bilkisu ta kafa alƙalamin bincike akan al'amarin da ya faru da Amina. Shin zata dace da gano wanda yayi? Ku fans ma to wa kuke zargine akan wannan al'amari? (Ina jiran amsarku). Ga Shahudah ta dawo, kuma da burin komawa gidan mijinta, sannan ga burin iyayenta da bamusan manufarsaba sam, shin zatayi nasara kokuwa dai iskace ke wahal da mai kayan kara?🤔🤒. Ya maganar zaɓar matar aure da family nasa keson yayi? Kuna ganin zasu haƙurane? Kokuwa zasu sake amincewa da wautar Shahudah a karo na biyu?. Ga Bilkisu alamu sun nuna zata koma tawagar Jay, yaya kuke tunanin wasan zai kayane? Faɗuwar gaba da kallon kallo da sukema juna tsakanin ita da Boss ɗin minene manufarsa?😌. Qaseem ya ɗau zafi da komawar Bilkisu tawagar Jawaad, yaya kuke ganin za'a kwashe, zai bartane? Kokuwa zai canja salon wargaza tafiyar?🤫 Ina Jazuga? Ina Firdausi da iyayenta? Ina labarin gidansu Uwargida? Ina labarin gidan hayar dasu Bilkisu suka rayu da iyayenta? Shin duk Bilkisu zata waiwayesu ne kokuwa dai sun zama labari?🙃 Mahaifiyar Jawaad babu wanda yasan inda take, akwai kuma maganar da ta taɓa shiga tsakanin Jawaad da dattijuwar dake aiki gidan Alhaji kokino ba giyar yaroba, shin kuwa babu lauje a cikin naɗi? Dan zaurancen nasu yayi kama da🤫🤭. Kenan dai akwai ƙurori da cakwakiyoyi sosai kenan, duk kuma a cikin littafin ƙwai cikin ƙaya kashi na biyu🤓🥱⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀. BILKEESU IBRAHEEM MUSA (Bilyn Abdull ce😘🤫) Inama ɗaukacin musulmai barka da shigowa sabuwar shekarar musulinci, Alkairin dake cikinta ALLAH ya tabbatar dashi a garemu, saɓanin haka ALLAH ya karemu a duk inda muka tsinci kayinmu, idan ta kasance shekararmu ta ƙarshe a duniya rabbi ka ɗauki ranmu muna cikin masu imani da soyayyar MANZON ALLAH a ruhinmu, ALLAH ka gafarta mana baki ɗaya🙏🏻😭 Duk wanda naima ba daidaiba a rayuwata ta online ya gafarceni, nima na yafema duk wanda ya cutamin, ALLAH yasa dalilin hakan nima ALLAH yay min rahama bisa nawa kurakuran🙏🏻😭 Bilyn Abdull ce🤙🏻 ALLAH ka gafartama iyayenmu da mu baki ɗaya🙏🏻😭