*_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_ _Assalamu alaikum masoya. Fatan alkairi a gareku tare da barka da salla. Ya rabbi ka amshi ibadunmu ka yafe mana kurakuran mu. Ka gafartama iyayenmu. Kafin komai dole na fara da tarin godiya a gareku musamman wanda suka sayi kayan salla a wajena. ALLAH yabar zuminci. Nagode sosai da yanda kuka nuna ƙarfafawa a gareni akan wannan kasuwanci. Ina sake albishir a gareku da in sha ALLAHU wasu kayanmu na gab da sauka musamman abayoyi da handbags na yara dana manya. Sai kowa ya ƙara zuba kuɗi a asusu 😂. Gamu mun dawo filin daga. ALLAH ya bamu ikon sauke nauyin juna mu daku, ALLAH ya haneku cin hakkinmu, muma ALLAH ya hanemu tauye hakkinku 🙏. Godiya ta musamman gareku baki ɗaya 😘😘😘🙏_. .......Kuka nayi sosai a wajen. Dan har sai da kaina ya dinga sara min tamkar zai rabe gida biyu sannan na miƙe. Cikin layi irin na rashin ƙarfin jiki na koma ɗakin dana kwana. Handbag ɗina na ɗauka tare da hijjabin danai sallar asuba. Gudun haɗuwa da shegen karensa ya sakani bi ta kitchen duk da ban san takan gidan ba. Ta bayan na bi, hakan yasa har na zagayo inda gate yake banga karen ba. Zaram maigadi dake zaune yana jin waƙa ya miƙe. Bakinsa har rawa yake wajen gaidani. Ban amsa masa ba. Face cemasa “Buɗe min!” cikin kakkausar murya da tsawa.      Cikin daburcewa da wuru-wuru ya ce, “Amma Hajiya oga baice....”    “Wlhy idan baka buɗe min ba zan haɗa kai da ogan na danna muku zagi.” nai maganar ina fisgo sandarsa dake ajiye saman bench. “Zaka buɗe min ko sai na ɗora maka ita a saman kanka”.             “ALLAH ya huci zuciyarki Hajiya bara na buɗe”. Ya faɗa cikin rawar jiki yana nufar ƙaramar ƙofar. Key yasa ya buɗe, na watsa masa harara sannan na fice. Sai da na tabbatar na fita sannan na jefa masa sandarsa nai gaba. Dogon street ɗin nabi da kallo, mai ɗauke da lafiyayyen titi. Sam ban gane a wace anguwa bane ba. Dan haka hankalina ya tashi. Amma sam banji na sare ba na cigaba da tafiya sauri-sauri duk da rashin ƙarfin jiki da nake ji. Addu'a kawai nake ALLAH ya kawo mai napep. Kai koda mota ce zan nema taimako. Na ɗan yi nisa a tafiyar inayi ina waigen bayana dan ji nake kamar makirin zai iya biyoni. Jiri ne ke ɗibata sosai, dan kaina har yafara harmutsawa. Na ɗan tsaya ina mai dafe shi da ambaton sunan UBANGIJI. Dai-dai nan wata farar mota da har ta gittani ta dawo da baya.       “Baiwar ALLAH lafiya kuwa?”. Muryar matashiyar mace ta daki kunnuwana. Hannuna na janye daga saman kaina. Cikin kallonta dishi-dishi a wahalce na furta, “Bakomai hajiya.”         “A ya zakice ba komai. Gashi kinayi kamar ma zaki faɗi”. Tai maganar tana fitowa a motar. Riƙoni tai dan jirin ne ya ɗeban zai zubar. Muryarta da damuwa sosai ta ce, “Kinga bara na sakaki a mota. Sai ki faɗamin ina zaki na kaiki”.     Ganin mace ce, kuma dama abinda nake buƙata kenan sai banyi musu ba. Da taimakonta na shiga motar. Ina zama na lumshe idanuna kaina na ƙara ƙarfin sarawa matuƙa. Koda ta shigo ta zauna tana tambayata ina zata kaini kasa bata amsa nayi, hakan yasa tai shiru ta bani ɗan lokaci da take tunanin na samu nutsuwa sannan ta sake tambayata. Da ƙyar na iya furta mata. “Yakasai”.              “Okay ba damuwa. Amma ina ganin mu fara zuwa clinic sannan. Dan kina cikin halin buƙatar taimako. Ni likitace”.        “Karki damu ki kaini gida kawai na gode”. Na faɗa a matuƙar wahale.    “Bazai yiwu ba, kiyi haƙuri na taimakeki dan ALLAH”.     (Dan ALLAH) data ambata yasa ban iya sake cemata komai ba. Daga haka ma na sulale ban sake fahimtar komai ba.     ★     Hankali tashe maigadi ya nufi cikin gidan. A dai-dai ƙofar shiga falo ya samu Maash tsaye. Rikicewa yay, musamman da yay ma fuskarsa kallo ɗaya ya ganta a tsuke kamar hadarin gabas. Cike da tashin hankali ya zube ƙasa saman gwiyawunsa yana kwaso rantsuwa. “Wlhy tallahi ranka ya daɗe ba laifina bane ba. Tace idan ban buɗe mata ba zata fasamin kai ne.”      Shiru baice masa komai ba. Maigadi ya sake rikicewa yana jera rantsuwa da magiya duk a gurbi ɗaya. Sai da ya mula dan kansa a hankali ya furta, “Jeka kan aikinka”.    Duk da a sauƙaƙe yay furucin hankalin maigadi bai kwanta ba sam. Dan gani yake akwai abinda zai iya biyo baya. So yake ya cigaba da bada haƙuri har sai yasan ainahin gaskiyar abinda ke zuciyar mai-gidan nasa, sai dai kuma baiga muhallin yin hakan ba. Dan haka sum-sum ya juya bakin gate zuciyarsa na rawa matuƙa. Cikin taraddadi da ƙaulani ya koma, kusan mintuna goma da komawarsa yana zaune ya zabga tagumi akai horn. Firgigit ya tashi domin dubawa. Sai da ya buɗe ƙaramar ƙofa yaga mai horn ɗin sannan ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya. Cikin girmamawa ya gaisar da Hayatu dake shigowa. Shi kuma ya ɗaga masa hannu yana ƙarasa shigewa cikin gidan. Yana fitowa a motar Laalah ya zaburo, inda yake yazo shi adole ya sanshi, hakan ya sakashi sakin murmushi da kai hannu ya shafa kansa yana faɗin, “Laalah how are you?”. Daga haka ya wuce zuwa cikin gidan.          Koda yay sallama a ƙofar sai da aka kwashe kusan minti ɗaya kafin a amsa masa, tare da bashi izinin shiga.  Sarakin na zaune tamkar babu abinda ke damunsa. Hasalima dukan hankalinsa naga wayar hannunsa ne. Koda Hayatun ya shigo ma bai ɗago ba. A haka ya amsa masa gaisuwar da yay masa. Sanin hali yasa Hayatu bai damu ba ya cigaba da maganarsa. “Sir Alhamdullah yanzu haka tana tare da ita. Sai dai tace akwai matsala. Dan tana shiga motar ta sume mata, a yanzu haka ma suna clinic, sun kuma tabbatar da jininta yayi matsanancin hawa da take buƙatar taimakon gaggawa saboda gudun samun matsala a zuciyarta. Amma nadai basu damar yimata dukan abinda ya dace”.        Karan farko ya ɗan ɗago ya kalla Hayatun, sai kuma ya maida kansa ga wayar batare da yace komai ba. Tsahon mintuna biyu kamar yama manta da shi sai kuma ya ajiye wayar a gefensa. Hannunsa ya ɗan matsa tare da ɗagowa ya zubama Hayatun idanunsa. Dole Hayatu yay ƙasa da nasa kan dan baya iya jure irin kallon nan na ogansa mai kama da na abokin yaƙi a filin daga..         Cikin silent voice ɗin nan nasa da janye idanunsa daga kansa ya furta, “A sanarma Hameed ya shirya zuwa 9 zamu wuce Abuja. Sai kai magana da Faisal zamu iso masa da mara lafiya ya taremu a airport”.     Sosai Hayatu ya zaro idanu waje. Duk yanda yaso haɗiye abinda ke masa kai kawo ya kasa hakan. Bai ma san sanda ya furta, “Amma Sir baka ganin tafiya da ita zai iya ɗarsama family ɗinta wani abu a rai kuwa? Jiya ne fa suka kawota nan a matsayin amarya. Kasan fa sunan arewa komai nasu na tafiya da addini da al'ada”.         Ko motsi Maash daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu baiyi ba balle Hayatu yay tunanin samun amsa. Ya kuma san shirun nasa na nufin bazai tanka ɗin ba, ya kuma gama zartar da hukunci kenan. Jiki a sanyaye Hayatu ya juya zai fita. Yayinda yake ta sake-saƙen mai fishshesa a zuciya. Dan dolene fa suyi wani abu da zai gamsar da family ɗin ta. In ba hakaba akwai babbar damuwa fa, kwaɓarsu zata iya yin ruwa batare da sun farga ba, shi komai ma sake ruɗar da shi yake. Dan yarasa dalilin ogan nasa na ƙulla igiyar aure tsakaninsa da ƴar bala'in yarinyar nan. Tunda yasan idan amsar video ɗin nan yay niyya da tuni ya amsa tako wace hanya ai, duk da dai ya fahimci itama yarinyar akwai taurin kai, sannan tana da power a cikin al'umma game da aikinta, maybe shiyyasa ogan nasa yaƙi yin komai kai tsaye a kanta ya biyo ta wannan sigar. Gashi bai sanar masa komai akan shirin nasa ba. Hasalima sai a jiya shima ya san da batun auren bayan sun baro Lagos a jirgi yake sanar masa. Ya shiga shock matuƙa, sai dai bashi da hurumin iya cewa komai tunda ya riga ya zartar da hukunci, amma ya yini ya kwana al'amarin nan na juya masa a rai. Dan duk duniya shine kaɗai kuma yasan Maash ɗin yayi wannan auren, ko su dangin yarinyar basu san shine ba, saboda baije musu a Maash ɗin ba. To koma dai miye, shi kam zaiga yaya wasan zai kaya, dan shi ɗin shaida ne, ogansa mutum ne mai tsananin taurin kai da aljananci na gaske. Ga hatsabibancin masifa da dagiya akan abu, ya tabbatar ba son yarinyar nan yake ba, dan inda hakane kai tsaye zaije yace yana sontan saboda shi bai iya ɓoye-boye ba tamkar bature yake komai nasa kai tsaye yake yinsa. Ko minene a ransa kai tsaye yake fiddashi koda bazai ma kowa daɗi ba shi babu ruwansa idan yayi dai-dai da ra'ayinsa kansa kawai yake kallo..      Kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa, dan dolene yaje ya tsara abinda ya dace gudun samun akasi.. ★★★    A gidan Abba kam sai a safiyar yau ƙananun magana suka fito sosai. Dan kuwa Mom ta titsiye Abba taji komai daya faru a wajen ɗaurin aure dama kafin ɗaurin auren. Dan haka ta shiga bazama na kusa da ita su kuma suka ɗauki zance ƙus-ƙus. Tun anayin abin a gwargwaɗe har dai komai ya fito cewar bada Mansoor aka ɗaurama Samraah aure ba da wani ne daban. Dan mahaifiyarsa ta shata layi akan auren nasu, duk da dai shi Mansoor ɗin yaso bijirewa amma su Kawu Musa suka ce bazasu bashi ba saboda abinda mahaifiyar tasa tazo tayi a jiyan har gida batare da matan cikin gida sun sani ba sai su Gwaggo Gudidi kawai. Tun dai zance na iya cikin gida har maƙwafta suka fara shigowa jin gulma da kawo wadda suka jiyo a waje. Yanda Mom ta nuna farin cikinta a fili akan abinda ya farun ya ƙona zukatan su Gwaggo Gudidi da ƴan Gwarzo. Sai ga faɗa ya kaure tsakaninta da Aunty Jimmai babbar ɗiyar Kawu Musa. Kafin kace mi gida hargitse. Suka haɗu sukama Mom tatas, dan babu abinda suka manta basu faɗa mata ba har sai da tai kuka. Kuma Gwaggo Gudidi ta tabbatar mata indai tana raye sai Abba ya ƙara aure. Da ƙyar da ƙyar dai Musaddiq ya kwantar da wannan tarzoma. A kusan kuma dai-dai lokacin Hayatu ya iso gidan. Inda ma ALLAH ya taimaka Musaddiq da Abba da su Kawu Musa na ƙofar gida a lokacin da ya iso ɗin, dan haka ya samu tarba ta mutunci. Cikin ɗar-ɗar da addu'a a ƙasan ransa bayan sun gaisa ya sanar da su abinda ke tafe da shi kamar yanda ya tsara domin bama ogansa kariya. Hankalinsu ya tashi da jin Samraah babu lafiya. A take babu ɓata lokaci suka muƙe domin binsa asibiti dubata. Bai hanasu ba, dan bashi da wani zaɓi, sannan hakanne ma zai taimaka masa tsarin nasa ya tafi dai-dai yanda yake buƙata batare da Maash ya rufta ba ko shi dake ɗan kore ba.........✍️ Hummmm🥱 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_ .......Hankalinsu ya tashi matuƙa da ganin yanayin Samraah a asibiti. Yayinda Dr Su'adah ta sake ruɗar da su da bayanin haɗarin da Samraah ke ciki. Tare da tabbatar musu idan ba'a sadata da ƙwararren likitansu dake birnin tarayya Abuja da zama ba za'a iya rasata, dan zuciyarta na gab da bugawa saboda yanda jininta yay tsananin hawa sama. Sam babu wanda yay musu akan yarda da hakan. Sai dai sun nema alfarmar Hayatu akan Musaddiq zai bisu zuwa Abuja ɗin. Rasa abincewa Hayatu yayi, dan ya tabbatar tafiya da Musaddiq bazai yiwu ba. Amma rashin mafita sai ya amsa musu da to su jira suji daga likitar yaya za'ai tafiyar. Sun gamsu da hakan, dan haka ya lallaɓa ya koma gefe ya sake samun Dr Su'adah akan ta taimakesa ya fita a tarkon mutanen nan, dan yana da dalilin da yasa baya so kowa ya bisu. Ita dai Dr Su'adah bata san ainahin mike faruwa ba, dan Hayatu ɗan uwanta ne na jini, abinda ya gaya mata kuma bashi ne ainahin alaƙar dake tsakanin Samraah da Maash ba. Dan haka babu musu ta taimaka masan. Ita ce ta tsara su Kawu Musa ta hanyar da dole suka gamsu akan za'a fara tafiya da Samraah ta jirgi ne, masu son bin bayanta sai suyi hakuri subi a baya ta mota nan da kwana biyu haka. Haka kawai sai hankalin Musaddiq ya kasa kwanciya, sai dai babu yanda zai yi tunda su Kawu Musa sun yarda. Haka dai yana ji yana gani aka shiga yima Samraah shirye-shirye dan wai za'a wuce da ita ne a jirgin ƙarfe takwas na dare...         ★✓★✓★✓★✓     *_ABUJA AIRPORT_*         Ƙarfe tara dai-dai jirgin daya taso daga Kano zuwa Abuja ya sauka a filin jirgin na birnin tarayya. Maash da tawagarsa na ɗaya daga cikin passinges ɗin wannan jirgi. Hakama Samraah da likitan da take tare da ita suna a jirgin. Sai dai a tsarin tafiyar sam babu abinda ya alaƙantasu da Maash. Hasalima shi yana a private section ne. Yayinda ita da likita suke a sashen kowa da kowa, koda yake ita bama ta a hayyacinta balle ta fahimta. Dan an shigo da ita ne a yanayin wadda take bisa umarnin likita da zataje gani a Anuja. Ko'a airport ɗin ma tuni Maash ya shige ɗaya daga cikin tawagar jerin motocin da suka zo ɗaukarsu. Yayinda ita kuma ambulance ta ɗauketa ta wani babban private asibiti da ake matuƙar ji da shi anan birnin Abuja ɗin.. *_KANO_*          Anan Kano an wuce da Samraah an bar danginta da jimamami. Musamman ma Musaddiq da sam zuciyarsa ta kasa zama waje ɗaya. Kai shi tunma jiya hankalinsa a tashe yake da wannan aure. Sai dai babu yanda ya iya tunda su Kawu Musa sun bama mijin da suka aura matan yarda ɗari bisa ɗari. An ƙarasa dai wannan dare cike da jajantama juna bisa ga halin da Samraah ɗin ke a ciki. Daga ƙarshe dai a washe gari kowa ya shirya ya kama gabansa saboda wayar da akai da mijin na Samraah akan jikin da sauƙi suka ganta ta hanyar video call. Taro dai ya tashi an bar Mom da mijinta sai auta da Musaddiq da Hafizzullah kawai a gidan dan su Baby basa nan. Sai a washe gari suka dawo gidan. Hafizzullah ma dai shirin komawa makaranta yayi, duk da yaso zuwa wajen Samraah Musaddiq ya lallashesa akan yayi haƙuri tunda an kusa musu hutu, yanzu zuwa Abuja dubata ba nashi bane, shima ɗin da akace zai je su Kawu since ya dakata kada mijin yaga kamar ana nuna ya gaza ne. Badan yaso ba ya shirya ya wuce zuciyarsa duk babu daɗi. Dan duk wani masoyin Samraah ɗin zuciyarsa a ƙuntace take da abinda ya faru akan wannan aure da kuma halin ciwo da take a ciki yanzu. Dan idan ta shine ma baza'a ɗaura mata aure da wani da bata sani ba tun farko. Amma dai su Kawu Musa sun bada goyon baya babu abinda su zasu iya musamman ma shi dake amsa sunan ƙani a wajenta. Amma zai cigaba da binta da addu'a kamar yanda Yaya Musaddiq yace yayi. Musaddiq ɗin ne ya kaisa har Katsina da kansa. Ya sake masa nasiha sosai sannan ya juyo gida.....           *_MANSOOR_*      Kowa ka kalla a ahalin gidan hankalinsa a tashe yake. Dan kusan duk manyan suna a sashen su Mansoor da aketa ƙoƙarin gaggaɓe ƙofar ɗakinsa. Yau kwanaki uku kenan yana a kulle a ciki yaƙi ya fito. Lallashin duniya da roƙo yay biris da kowa. Tun ana ɗaukar abin nasa a fushi na ɗan lokaci har abin ya wuce makaɗi da rawa, dan zuwa yau ko motsinsa an bar ji a ɗakin, dole fa aka nemo mai gyara domin gaggaɓe ƙofar. Kuka sosai Mamynsu keyi tun jiya, dan ita kanta har sai da hawan jininta ya motsa. A yanzu haka a nane take da ƙofar ji take mai aikin ma kamar baya sauri ne.         Ana ɓalle ƙofar mafi yawansu duk suka afka ciki, tsakanin Attahir da Mamy har turereniyar rige-rigen isa ake kan Mansoor dake kwance samɓal a ƙasa babu alamar rai a tare da shi. A tare suka ɗagosa, sai dai me yaraf ya koma alamar babu rai. Wani mahaukacin ƙara Mamy ta fasa mai firgitarwa, tamkar ƙiftawar ido sai gata ƙasa wanwar itama ta sume musu. Sake harmutsewa ɗakin yayi, dole aka kwashesu zuwa asibiti kamar yanda wasu suka bada shawara.....                 *_ABUJA_*     Kaifin hasken rana da nake ji mai ƙarfi a saman fatar idanuna ya sani motsasu a hankali. Sosai sun min nauyi, dan illahirin jijiyoyinsu a takure suke waje guda. Hannuna da nake ji kamar an ɗaure nai ƙoƙarin motsawa domin kaiwa saman idanun, sai naji an sake damƙesa da ƙyau, tare da jin saukar wata murya cikin kunnena. “Bi a hankali akwai abu a hannunki. Sannu kin farka bari nai kiran likita”.         Sosai naji gabana ta faɗi. A can ƙasan zuciyata na ayyana (likita) a fili kam babu abinda nake iya motsawa a jikina saboda illahirinsa yay min nauyi. Amma sai na shiga ƙoƙarin buɗe idanuna. Dishi-dishi nake gani, sai dai hakan bai hanasu sauka akan mutumin daya shigo bayansa da wasu mata guda biyu ba saboda yanda hayaniyar maganar da suke taja hankalina. Duk da ba ihu suke ba ko fidda sautin maganar tasu da ƙarfi. Ƙarasa buɗe idanun nayi da ƙyar sakamakon jin inuwar mutum a kaina. Wani irin faɗuwar gaba naji ta sake riskata, dan kuwa tabbas a asibiti nake, dan shigar wanda ke kaina tsaye kawai ta tabbatar min da shi ɗin likita ne. Sannu suka shiga jeramin, sai dai na gagara amsawa kowa a cikinsu, na dai zuba musu ido ne kawai ina binsu da kallon ƙurilla. Ko tambayoyin da likitan ke jeromin game da jikina na gagara amsa masa ko ɗaya. Fahimtar kamar a rikice nake da yanda nake bin ɗakin da kallo ya sakashi ƙyaleni shima. Sai cikin matan da ya shigo da su ne ke ƙoƙarin cire min allurar drip dake a hannuna. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya sake juyowa ya fuskanceni. Cikin harshen turanci ya furta. “I understand that you are confused. This is a hospital, you are under the care of a doctor. Alhamdulillah, your body is very easy.”         A hankali na kai hannuna saman kaina da har yanzu nake jinsa da nauyi, kafin na sake ɗagowa na dubesu murya a karye na ce, “Who brought me? Which hospital is this? Since when have I been?”.     Da alama yanda na jera tambayoyin sun bashi mamaki, dan sai da ya ɗan waro idanunsa, sai kuma yay murmushi da faɗin, "Oh relax! You will all know. Now they will help you to fix your body, eat something and I will come back and answer your questions". Ya ƙare maganar yana nuna min Nurses ɗin. Fuska na ɗan ɓata, sai dai bance komai ba. Shi kuma ya juya ya fita da Nurse ɗaya ya barni da biyu. Da farko naso naƙi yarda, dan nafi son na fara sanin a ina nake. Sai dai yanda suka nuna damuwarsu da tabbatar min ƙin yardata zai iya taɓa aikinsu yasa na amince. Amma zuciyata taƙi gajiya da daina kai-kawon ganin ɗakin da naken matsayin wai asibiti. Saboda sam bai kama da asibiti ba fa, duk da gado da tarkacen ɗakin duk irin na asibitin ne, sai dai da gani na musamman ne su. Ga television ga freight, sannan toilet da suka kamani suka kaini a cikin ɗakin dai yake shima sam bai kama da asibi ba. Ciwon da jikina kemin ya sakani bin umarninsu nayi wanka da ruwan da suka tara min mai ɗumi. Nako ji daɗin wankan, na saka doguwar riga irin wadda na cire pitch color da alama ta asibitin ce. Bata sauka min har ƙasa can ba sosai, amma dai banyi tsirara ba. Gashi tana da faɗi babu wani takura. Alwala na ɗauro na daddafa bango na fito. Da sauri suka iso gareni suka taimaka min muka ƙarasa, a saman lallausar sofa ɗin ɗakin nace su zaunar dani, sannan na buƙaci hijjab na salla da sallaya. Sai dai da alama babu, sai ɗaya ce tace bari ta sanarma doctor a kawo min. Komai bance ba, na jingina kaina da kujerar na lumshe idanuna. Bata fi mintuna biyar ba sai gata ta dawo da sallaya da sabon hijjab a ledarsa. Ita ta ciromin shi, sannan ta shinfiɗa min sallayar. Har ƙasa hijjab ɗin ya sauka min sosai dan ko ƙafafuna ba'a gani, hakan yasa naji nutsuwa dan dama rigar bai gama sauka ba. Juyawa nai na tambayesa "What day is today?". A tare suka amsa min da, “Today is Monday”.       (Litinin) na maimaita a zuciyata. A zahiri kam sai na sake tambayarsu alƙibla. Ɗayarce mai kama da musulma duk da shigarta zata iya saka kace ba musulmar bace amma akwai ƙaton tabon salla a goshinta ta nuna min tare da bayani, bance komai ba na kabbara sallata. Tun inayi a tsaye har hakan ya nema gagara. Dan dole na koma a zaune kasancewar duk sallolin da nasan suna kaina sai da na ramasu na kwanaki biyun nan da bana a hayyacina.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......Tun ina sallan shigowar doctor biyu. Sai dai ganin ban idar ba yana komawa. A na ƙarshe suka shigo su biyu dai-dai na idar ina zaune kawai nayi tagumi cikin dogon nazari da son sanin a ina nake wai. Jin muryar da banyi zato ba kasancewar nasan na kuɓuta daga garesu yasa na ɗago da sauri. Shi ɗinne kuwa. Wato yaron mugun nan Maash. Ganin yanda ina ɗagowa ya duƙar da nasa kan ƙasa kamar wani munafuki ya sani cigaba da kallon nasa kawai. Doctor ne ya katseni da tambayar yaya nake jin jikina yanzu. Cikin janye idanuna na amsa masa da Alhamdullah. Ya nuna jin daɗinsa kafin yay min nuna da mutumin nan. “Now you will get all the answers to your questions from him. I will send a nurse with your medicine. If you eat, she will give you.” daga haka ya juya ya fita. Shiru ɗakin ya ɗauka kusan na minti ɗaya, kafin a ƙufule cikin dasashjiyar muryata mai nuni da banda lafiya na furta, “Ya akayi na dawo gareku? Ina ne nan kuka kawoni?”.         Sake duƙar da kai yayi kamar mai tsoron bani amsa, sai kuma a hankali ya furta, “Kiyi haƙuri nan asibiti ne. Yaya jiki?”.      Wani irin takaici ne ya ƙuleni, dan haka cikin sake zafafa harshe na amsa shi da, “Ba ruwanka da jikina. Kaje ka sanar ma wanda ya aikoka yasa likitan nan ya sallaman. Sannan ku fita a sabgata. Idan ba haka ba zan sakaku nadama da dana sanin sani na. In ba hakaba zan tabbatar muku TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na yunƙura a hankali na miƙe, ko inda yake ban sake kallo ba na koma saman gadon. Dai-dai nan Nurse ɗin nan ta dawo... *_KANO_*.   A matuƙar tashin hankali zuciyar Mamyn su Mansoor ta gama shiga. Dan suna isowa asibitin ta farfaɗo ita. Amma Mansoor kusan awani uku kenan likitoci na tare da shi ba kuma su musu bayanin komai ba. Sai dai faman kaiwa da komawa suke a tsakanin ɗakinsa zuwa ofisoshinsu. Tun tana hawaye har ma sun ƙafe ta koma na zuci. Nadama take ji na sake shigarta akan abinda ta aikata. Lallai tayi dana sanin biyema shawarar ƴar uwarta. Inama zata iya maida hannun agogo baya. Data goge komai da yake a yanzu da maida baya data shuɗe. Dan har ga ALLAH Mansoor shine ɗa mafi soyuwa a zuciyarta. Kodan tasha matuƙar wahala ne a yayin haihuwarsa, ko kuwa dan kamanin da yake da mahaifinsa. Sam bazata iya jure rasashi ba. Dan bazata taɓa yafema kanta ba.        “Mamy dan ALLAH ki zauna ki huta, in sha ALLAHU ɗan uwana zai tashi. Kinga kema fa ba lafiyar ne da ke ba”. Attahir ne mai maganar cikin tsantsar damuwa ganin yanda Mamyn tasu ke faman kai kawo ga hannunta dafe da kanta. Yasan komai zai iya faruwa da ita, dan bata gama dawowa dai-dai ba ta fito a ɗakin da aka kwantar da ita. Anyi-anyi kuma taƙi ta koma dole aka haƙura aka barta. Dan Dad ɗin su ma haushin dagiyar tata ya sashi komawa can gefe ya zauna kawai bai sake kulata ba.          “Attahiru bazaka gane ba. Nasan bazaka fahimta ba. Barni kawai kaji. Barni da abinda ya dameni. Ni da kaina na jefa rayuwar yarona a bala'i. Da nasan haka zata kasance da ban aikata ba. Da ban hanashi aurenta ba. Attahiru idan na rasa Mansoor nima zaku rasani ne wlhy”.      “Dan ALLAH Mamy ki daina faɗa. In sha ALLAHU bazamu rasaki ba. Ki kuma daina zargin kanki kowa baya wuce kuskure ai. Mansoor zai samu sauƙi. Ki masa addu'a”.      Kuka mai nauyi ta sakar masa tana ƙoƙarin dafe bango saboda jirin dake neman yaddata taji ya kwasheta. Da sauri yayi kanta ya riƙota. Da taimakonsa suka zauna yana jera mata sannu. Dai-dai nan shima Dad ɗin su ya taso, hakama ƙannensu da suka haɗe kai gefe suna kuka. A ruɗe duk suke tambayar miya faru, sai da ta ɗago ta ce musu ba komai sannan suka shiga sauke ajiyar zuciya. Hakan sai yay dai-dai da fitowar amintaccen likitansu Dr Gana. Kamar waɗanda aka zabura duk suka miƙe garesa har Mamy. Har rige-rigen tambayarsa yaya Mansoor suke yi. Shiko ya ɗan bisu da kallo cikin damuwa. Sai kuma a hankali ya furta, “Alhaji idan babu damuwa na ganka a office mana. Amma Hajiya tai zamanta Please”.        Tsantsar tashin hankali ne ya bayyana a fuskokinsu. Yayinda Mamy ta fashe da kuka sauran ƙanensu na tayata. Shi kansa Dad ji yay ƙafafunsa sun masa matuƙar nauyi. Haka shima Attahir ya gagara tashi har sai da doctor ya sake musu magana sannan. Attahir ne ya fara jarumtar miƙewa, sannan shima Abban ya tashi suka nufi office ɗin su biyu kowanne na jin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirazansu ta fito waje.....        _Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba😭😭🙆._ *_ABUJA_*        ★Sosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL.       “Abuja?!”.     Kansa ya jinjina min da sauri. “Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down”     Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ɓaɓatunsa ya fita. Ɗauke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ɗina da ƙarfi. Na fahimci waɗan nan mutanen so suke sai mun kai matakin ƙarshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ƙaraso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara na ɗago zan watsa masa sai idanuna suka sauka akan fuskar wayar. Tamkar waccan ranar yanzun ma tar-tar nake ganinsa. Yanda ya kafeni da shegun idanunsa kaifafa kalar na maguna ya sakani sake ɗaure fuska tare da ƙarasa antayawa PA ɗin nasa hararar da nayi niyya. Sai dai ashe shi harma ya fice ya barni da wayar. Wani irin takaici ne ya sake ruƙunƙumeni. Dan haka na rumtse idanuna da ƙarfi ina jin matuƙar zafi a raina. Kafin na buɗesu gaba ɗaya a fusace kan wayar. Shiko shiru yay kawai yana kallona da kaifafan idanunsa da nake jin tasiri su har a cikin jinina. Duk da yanda nake jin tasirinsu ban janye nawa dake masa kallon tsana da takaici ba. Cikin kaushin harshe da disashiyar muryata ta marasa lafiya na furta, “Kai ko akwai zuciya a ƙirjinka?”.         Shiru babu alamar zai tanka min, sai ma janye idanunsa da yay a wani kalar slowly ya maida kan laptop dake gabansa. Dan alamu ya nuna kamar a study table yake zaune. Cikin sake jin wani sabon baƙin cikin na kai hannu saman kaina dake sara min. Fahimtar bazai amsa min ba ya sani cigaba da faɗin, “Anya kai Musulmi ne?”.       Cak ya tsaya daga barin abinda yake yi, dan haka ya ɗago muna kallon juna cikin ido, idanunsa sun wani kaɗa blue ɗin gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama siririya like mage sak. Zamansa ya gyara na ƙasaita da isa da ke tabbatar da shi matsayin ingarman namiji, ga wani irin shegen kwarjini da nake ji ya mamaye ɗakin har kamar na matsu kai kace a gabana yake mayen. Ganin haka ya sakani cigaba da maganata batare da na damu da duk abubuwan dake tattare da shi ɗin ba.        “Idan har kai musulmi ne bana jin kasan HARAMCI da HALLACIN dake cikin dokokin addinin musulunci. Idan kuma har da zuciya a ƙirjinka tabbas bata masu IMANI bace. Ina mai baka shawara kada kai wasa da wuta a tafin hannunka, dan wutar da UBANGIJI zai ladabtar da ma'abota bijirewa ta ninka wadda ake girka maka shinkafa a duniya kaci sau dubu bisa dubu. Idan baka sani bane zan faɗa maka a yanzu ni ɗin MATAR WANI CE. igiyoyin AURE ne a kaina ba igiyoyin ɗaure dabba a turken turka ba. Kaji tausayin kanka, da gujema saɓama UBANGIJI ka maidani inda ka ɗakkoni gidan aurena hannun MIJINA da IYAYENA.”           “Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN kuma fa?”. Ya faɗa cikin wata iriyar muryar dakiya da gizago mai tsarga zuciya. Dan yanda sautin amon muryar tasa da kaifinta ya tasirantar da furucin nasa a tsakkiyar kaina kaɗan ya rage zuciyata bata ɓullo ta bakina ta fito ba. Amma duk da hakan sai ga tari mai ƙarfi ya sarƙe min numfashi. Gaf-gaf jikina dake a cikin yanayin rashin ƙarfi ya fara rawa. Bamma san lokacin da bakina ba ya furta “MIJI?!”. Sai kuma kaina yay wani irin masifar sarawa da ban taɓa ji ko tsinkayen irinsa ba. Ga nauyi da idanuna sukamin har inajin jijiyarsu na ja kamar za'a fincike min su. In dai har wannan ake kira hawan jini to tabbas ya sameni kuwa a yanzun nan. Dan ƙirjina kansa yay wani irin nauyi. A karo na biyu hankalina ya sake neman barina. Nai yaƙin maidosa jikina tare da ɗagowa ina kallonsa domin son tabbatarwa. Amma a maimakon amsa ma da nake buƙata garesa hankalinsa kwance yake cigaba da aikin gabansa. Wani irin kallo nake masa mai kama da firgici, yayinda shima ya zuba min nasa cat eyes ɗin cikin yanayin i don't care tamkar zai cinyeni da su. Cike da salon izza da ƙasaita ya wani sake tsuke fuska da yamutseta sannan ya furta, “Har yanzu kina da sauran dama. Domin guri bai ƙure miki ba na komawa inda kika fito. Ki bama yarona video ko fadar inda yake a ɗakko gobe ki koma garinku. Saɓanin hakan cigaba da dawwama ƙarƙashin mulkin mallakar Maashhhh. Ke baki mori rayuwar taki ba. Ba kuma ki iya yin komai akan abinda kike tunanin iyawa ba”.........✍️ Yayanmu Barka da salla, ban sani ba ko a duniyarku kunyi azumin kuma🥱👩🏻‍🦯. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Wani irin sake sarawa kaina yayi, dole na kai hannu na sake dafesa tare da saurin dafe ƙarfen gadon dan ji nake zan zube ƙasa, hasalima sam bana fahimtar maganganunsa a yanzu. Sai kalamansa ne na farko ke faman maimaita kansu a cikin kaina cikin matuƙar amsa kuwwar data zarce ƙarfin muryar daya sanar min su. (Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN fa?) Kalamansa suka shiga min amsa kuwwa a cikin kunne tamkar wadda akema shelarsu. Gaba ɗaya ma brain ɗina ta toshe, sai nake jin kamar na kasa fahimta ko fassara su a bigiren daya dace. (Kai ina wannan gangan ne) wani gefe na zuciyata ya ambata. (Samraah dawo cikin hankalinki mana) sashen zuciyar tawa dai ya sake maimaitawa. Hannuna dake a saman kaina na sauke tare da kaisa saman kumatuna na ɗan bubbuga, dan nafi tunanin mafarkine kawai. (Kai amma wannn mummunan mafarki da muni yake) na sake faɗa ina bubbuga fuskar sosai da ƙarfin gaske kozan farka. Zafin daya ratsata ya sakani rumtse idanun da ƙarfi. A masifar jigace da ƙoƙarin haɗiye hawayena na ce, “Wai kai minene alaƙarka da ni ne? Mi kaje ka ƙulla? Miye matsalarka dani?”.        Idanunsa ya ɗauke da ga kaina gaba ɗaya. Sai kuma ya ɗan taɓe baki alamar yanzun ma bazai tanka min ba. Rainin wayonsa ya gama zuwa min ko ina. Dan haka na fisgi ɗan ƙarfen dake cikin tasar asibiti a gefena na ɗago ina kaisa saman cikina cikin soyewar ido data zuciya. “Dana zauna da kai a matsayin miji gara na kashe kaina na san ban mori komai a rayuwata ba.”        Idanunsa dake min wani kallon ƙasa-ƙasa ya sake ja luuu kamar zai rufesu gaba ɗaya. Sai kuma ya buɗesu warr cikin yanayin i don't care manners ya furta, “So! Ai ba hanaki zan ba. Abinda kawai nake buƙata kafin ki mutum ki bani video”.       Wani irin sakartaccen kallon tsana da takaici nake masa. Na cije lips ɗina da masifar ƙarfi. “Har abada kuwa buƙatar taka bazata biya ba. Dan wannan videon bazai taɓa zuwa hannunka ba har gaban abada.”      “Ashe kuwa ko kin mutu gawarki zata cigaba da zama a gareni. Ahalinki kuma zasu cigaba da amsar hukuncin laifinki”.           “Idan kuma kai na kashe fa?”. Na faɗa ina jefar da ƙarfen cike da tsantsar fusata da tafi ta ɗazun. Idanunsa ya ɗan zuba min, sai kuma cikin nuna rashin damuwa ya janyesu yana wani shegen annamimin murmushi daya ƙona min rai.       “Oh are you threatening me? Ai game dani ba wasan yara bane ba. Har yanzu bamu fara wasan ba, balle ki tunanin samun game over. Zan iya baki damar kwanaki domin shiryawa. Ba kince kinfi ƙarfin laɓewa bayan wani domin faɗan sunƙuru ba. To gana gaba-da-gaba nan kin samun bissmillah. Matsoraciya kawai. Kwana uku kacal har kin fara banbance tsakanin aya da tsakkuwa”.       Bamma san lokacin da wani irin ƙarfin zuciya yazo min ba. Cikin tsantsagwaron ɗaukar alwashi da tsawa na ce, “Har abada nafi ƙarfin yin laushi a hannun matsoraci irin ka. Dan ni har yanzu banga MAZANTAKA ba anan tunda sai da ka laɓe a bayan aure yanzun ma. Kasaka a ranka daga yau ni Samraah bint Abdul-wahab Gwarzo, sai na sakaka lissafin lissafa kwanakin rugujewarka daga yau har zuwa ranar dana ɗeba maka da zan kuma koma ga masoyina. Ni nan sai na sakaka gudu, gudu irin wanda babu wajen zuwa a tsakkiyar sahara mai tsananin zafi rana da ƙarancin ruwa. Wlhy sai kasan ka ɗakko KARA DA KIYASHI. zakuma kasan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na ture wayar ƙasa batare da na jira jin abinda zaice ba. Sai ma wani irin izza da ƙarfin iko da naji yana ratsa gaɓɓaina, duk da sara min da kaina yake tamkar zai rabe biyu. Sai kuma hawaye sharr suka shiga kwaranyomin masu zafin gaske....        (🥱🥱tofa irin wannan alwashi haka Sam-G).          💦💞💦💞💦💞    “Magana ta gaskiya Alhaji yaronka Mansoor na cikin haɗari. Sai dai akwai mafitar da in na baku shawara kuka gamsu da ita ina fatan za'a dace......”       Cikin tarar numfashi da taune harshe Dad ya furta, “Ka faɗi ko minene mu masu baka goyon bayane Doctor. Bama son rasa Mansoor dan ALLAH ka taimaka mana”.     “Wannan duk na ALLAH ne Alhaji. Idan kuma muka cigaba da roƙonsa shi mai amsawa ne. Shawarar dama itace ai gaggawar barin ƙasar nan da shi zuwa India. Akwai ƙwararren likita dana sani game da ciwonsa. Kuma inada yaƙinin in sha ALLAHU zai basa dukan kulawar da muke buƙata koma fiye da ita. Sannan ku shirya yaƙi na gaskiya game da nisanta komansa da abinda ya sake jawo wannan matsalar tasa da mukai tunanin ta barsa tun a shekarun ƙuruciya. In ba hakaba akoda yaushe komai zai iya faruwa magana ta gaskiya”.        Sosai zukatansu suka ƙara raunana da zancen Doctor. Dan duk dakiyar Attahir sai gashi yana share hawaye. Basu wani yi ja'inja ba dan basa fatan rasashi, tun ma yana yaro sanda matsalar ke da zafinta basu nutsu ba balle yanzu. A take aka fara shirye-shiryen fita da Mansoor zuwa India. Abinka da masu hannu da maiƙo, cikin kwana ɗaya da yini komai ya gama kammala. A cikar kwana na biyar da ɗaura auren Samraah da Maash aka wuce da Mansoor. Da ga shi sai doctor da Attahir ne suka wuce. Su Dad kuwa sai nan da kwanaki biyar saboda tsaiko da aka ɗan samu game da visa ɗin Amal. Duk wani masoyinsu ya bisu da fatan alkairi. Yayinda tausayin Mansoor ya sake cika zukatan wasu. Wasu ko nama iyayen nasa ALLAH ya ƙara kasancewar koma a wane hali yake sune suka jaza masa. Dolene kuma sakayyar Samraah ya bisa. Dan gashi itama ance babu lafiya har an wuce da ita asibiti. Dan tun a randa aka wuce da ita Abuja labari ya shiga kunnuwan mutane sakamakon shegen surutun Mom da ita take faɗa cike da nuna jin daɗi. Dan itafa jinta take fes uwa ya zuciyar sabon jariri haihuwar yanzu. Har faɗama mutane take ai mijin Samraah ɗin dama irin kwatakwalin yaren nan ne shiyyasa ma ya wuce da ita Abuja ɗin dan ya kaita ga danginsa a bata jiƙe-jiƙensu amma babu wani asibiti duk joni ne dan kar ai mata dariya. Wasu dai sun hau sun zauna, yayinda wasu ke fassara al'amarin nata da hassada kawai. Duk da dai mutane ba ganin mijin Samraah ɗin sukayi ba. Kowa dai batun an ɗaura aure da sunan wanda aka ɗaura ɗin mai suna Muhammad Mu'azz kawai sukaji. Sai kuma waliyayyansa da kowa ya gani ƙuru-ƙuru da ido dan wasu ma harda video sun ɗauka domin yaɗawa a media kasancewar Sam-G ɗin cele ce, yanda auren nata ya canja akala cikin ƙanƙanin lokaci sun san zai jawo magana. Ya kuwa jawo ɗin, dan har a yau da yake cika kwana biyar cif da ɗaurawa ba'a daina yawo da hotunanta da ƙananun magana ba harma dana Mansoor. Sai dai duk bin ƙwaƙwƙwafin mutane na son ganin sabon ango da iyayenta sukai mata auren huce haushi da shi har yanzu babu wanda ya gani. Duk da anata editing hotonta da maza daban-daban matsayin ita da angon nata. Masu ƙarancin hange sun yarda, masana da hangen nesa sun ƙaryata. Daga baya ma dai abokan aikinta da yawa sun fito sun ƙaryata ba ita bace editing ne.. ★★★★ Gwaggo dan ALLAH ki daina kukan nan hakanan. Ni wlhy ba wai ba zanji shawararki bane ko maganar ki. Ba kuma ina tsoron Jalilah bane da har zan gagara ƙara aure. Kawai dai ni ra'ayina kenan zama da mace ɗaya.”       “Ra'ayinka ɗin banza da wofi Imamu. Har ni zaka gayama wani ra'ayinka can na yahudanci. Mika rasa ko wane sharaɗine baka cika ba na ajiye mace fiye da ɗaya? Kaje bazan sake magana ba. Amma ka sani wlhy in dai na haifu cikin Balkisu da Usama bazan sake shiga sabgar zuri'arka ba. Sannan ina so daga yau ka saɓe hannunka daga ƴaƴan ƴar uwarka. Dan ba sai gobe ba a yau ɗin nan Musaddiq zai dawo wajena da zama. Shima Hafizun yana gama makarantar nan zai dawo. Kaje ka cigaba da rayuwarka da naka ƴaƴan da matarka tunda dama haka take so kai ma kake so ku rayu daga ku sai ku batare da wani ya raɓeku ba saboda kada mu rage muku jin daɗin duniyarku..”         “Amma Gwaggo dan ALLAH k.....”    “Na gama magana ta Imamu, tashi kaban waje. Ka dai tabbatar min bani na haifeka ba kuma na amince da hakan. Sai dai Alhamdullah bakai kaɗai bane ɗa balle hakan ya dameni, gasu nan bila'adadin harda jikoki duk mun godema UBANGIJI”. Daga haka ta miƙe ta bar masa falon. Da kallo kawai Abba ya bita zuciyarsa na kai-kawo tamkar zata fito. Babu abinda ke dawo masa a rai sai furucin mahaifiyarsu a lokacin da take gargarar barin duniya dan jinya tayi mai tsanani, kuma Gwaggo Gudidi itace ta kula da ita har ta koma ga ALLAH. (Imamu kona bar duniya nayi imanin baku rasa uwa ba kai da ƴar uwarka. Dan haka in har kuka bijirema umarnin ƴar uwata ban yafe muku ba. Kuma in har ina da hakki a kanku a matsayina na mahaifiya nasan bazaku taɓa ganin dadai ba. Ku ƙyautata mata, ku bita tamkar yanda zaku bini in sha ALLAHU zaku ribantu da hakan ba kuma zakuyi kukan rashina ba). Sosai tsigar jikinsa yaji ta tashi da tuno wannan magana. Dan tamkar a yanzu ne mahaifiyarsu ke faɗa masa shi da ƴar uwarsa mahaifiyar su Musaddiq. Bayan rasuwar ta kuma Gwaggo Gudidi itace ta cigaba da riƙe su. Itace tai musu aure da ga shi har ƴar uwarsa. Bata taɓa kuma gazawa ba a ɗawainiyarsu data ƴaƴansu har zuwa yanzu da tsufa ya risketa. Anya kuwa idan ya butulcewa wannan baiwar zai ga dai-dai? Bakin mahaifiyarsu kuwa bazai kamashi ba? Dan yana ƙyautata zaton shine ma ya taɓashi a yanzu abubuwa ke masa gangal-tangal uwa ya motar tirela mai ɗauke da siminti akan gadar icce dake tsakkiyar teku, dan yasan wasu kaso na rashin mutuncin da Jalilah ta dinga ma Gwaggo nasa a baya. Sai dai baisan miyasa baya iya tsawatar mata ba duk da abin na masa matuƙar ciwo a zuciya. Sannan yana matuƙar ƙaunar Gwaggo Gudidi, yana kallon fuskar mahaifiyarsu ne akan tata fuskar saboda tsananin kamannin da sukeyi. ya rabba yana a cikin tsaka mai wuya, dan baya jin zai iya ma Jalilah kishiya, yana kuma tsananin tsoron bijirema Gwaggo Gudidi bakin mahaifiyarsu ya kamashi.........✍️       _🥱To Abba adai sake tunani._        _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ____________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 _____________ .......“Alhamdulillah, I am very happy today we will send you off. I am very happy with the way you calmed down and gave us your cooperation. May God give you good health and protect the future”.       Murmushi na saki kaɗan ina jinjina kaina. Kafin a hankali na furta. “Thanks you doctor”.       “Ni ya kamata nayi godiya”. Dariya yanda ya haɗa hausar  da yanayin fitar kalaman ya bani, amma sai banyi ba nai murmushi kawai. A ƙasan raina ina jinjina karamcinsa gareni duk da kasancewarsa ba ƙabilata ba, sai dai ya nuna min kusancin musulunci dake tsakaninmu yafi na ƙabilancin. A kusan tare muka miƙe ni da shi, a dai-dai nan akai knocking ƙofar ɗakin jiyyar tawa. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Cikin gurɓatacciyar hausa hamshaƙiyar mace fara tas ƴar duma-duma tayi sallama ta shigo. Kallon cikin ido mukaima juna. Sai kuma matar ta janye nata tana maidawa kan doctor tare da rissinawa tana gaisheshi irin dai girmamawar ƙabilu. Ya amsa mata da kulawa. Sai kuma ya nuna mata ni. Hankalinta ta sake maidowa gareni tana murmushi. Sai kuma cike da kulawa ta gaidani da jiki. Amsa mata nayi a ɗarare, dan haka kawai naji matar batai min ba. Sai dai me bayani naji doctor na mata akan ya gama komai daya dace sai ta wuce dani. Kallonsa nayi a firgice zanyi magana sai kuma zuciyata ta ƙwaɓeni dan na tuna aljananci da hatsabibancin mai asibitin. A take na canja yanayi kawai na fara masa godiya.            Nurse ɗin da suka kula da ni ne sukai min rakkiya har inda motar matar take. Babu abinda zuciyata take face luguden daka da saƙawa da kwancewa. Dole fa a wannan karon na kuɓutar da kaina dan wannan ce kawai dama ta ta ƙarshe ta ƙuɓuta a hannun mutumin nan. Saboda zuciyata ta gama tabbatar min shine ya turo matar nan, idan kuma bashi bane to tabbas zai iya min wani tarkon da ita kamar yanda akai min a Kano sanda na baro gidansa.       “Ya rabba aiko nayi mantuwa”. Na faɗa dai-dai ina ƙoƙarin shiga motar da Semi ta buɗe min. Su duka kallona sukai, amma sai na sake zabura cikin hanasu damar min tambaya ina faɗin su jirani zan ɗakko na dawo yanzun nan. Yanda naga babu wacce tai yunƙurin bina nasan sun fahimceni, daga haka nai gaba cikin ɗan sauri-sauri da sassarfa irin ta mai gaggawa. Ina tabbatar da na ɓacema ganinsu na canja hanya. Duk da a rikice nake hakan bai hanani nemawa kaina dakiya ba na fara tafiyar nutsuwa. Da ƙyar nake iya gane inda nake jefa ƙafa har ALLAH ya fito da ni wajen wasu fanfuna da igiyoyin shanya. Akwai mutane tsiraru a wajen suna wanki, da alama wajen an tanadesa ne domin haka. Caraf idona akan hijjab dake shaye a igiya, tuni na tuɓe na jikina na ja wancan na saka, ɗan kwalin abayar jikina na naɗa a fuska tamkar niƙab. Daga haka na fito a wajen. Tambaya na dingayi har ALLAH yasa na fito a cikin asibitin gaba ɗaya dan babu laifi babbane sosai. Ajiyar zuciya mai haɗe da hawaye ne ya kufce min ganina akan titi, sai dai babban tashin hankalin banda ko sisi a jikina banda kuma abin siyarwa sisi. Ba kuma zan yarda kowa yaban lift ba dan an koyan hankali a baya. Haka na shari titi ina addu'a, ganin nayi nisa sosai da Asibitin zuciyata ta tabbatar min da zafa su iya biyo bayana su ganni duk da na canja hijjab. Ai tuni na kauce a titi na shiga wani street da naga an rubuta a ƙaramin symbol dake farkon shiga. Ganin an rubuta street nasan komai nisa zan fita, dan haka na zage damtse sosai naita tafiya duk da rashin ƙarfin jiki ga kuma rana mai zafi dake dukana ban damuba.....          ★★★....   Tun su Semi na irga mintuna har suka kusan haɗa ashirin. Mamaki ne ya kamasu, dan haka ɗayar nurse ɗin tace Bara ta duba Samraah ko ta ɓata hanya ne. Mintuna uku da wasu sakanni ta dawo a hargitse tana sanar musu itafa bata ganta ba. Sannan mutanen dake ata wajen sun tabbatar da bata dawo ba. Su dukansu har matar da doctor da aka je aka sanar mawa rikicewa sukayi. A take kuma doctor yay kiran Hayatu a waya...         Tako ina an bincike asibiti babu Samraah. Har cctv footage aka bincika, sai dai ta iya gaba kawai aka ga shigarta wajen inda ake wanki, kasancewar ta wajen babu camaras ɗin sai ba'a fahimci komai ba. Saboda ta canja hijjab sannan ta fita, ta inda ta fitan ma camara na wajen yana da matsala. Matuƙa Hayatu ya tada musu da hankali, gashi yayi kiran Maash ya sanar masa amma sai yaƙi ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ɗaukar Samraah ɗin. Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan...         💦💞💦💞💦    Ƙuuuuu!! Razanannen taka birkin ya karaɗe illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba hamshaƙiyar matar dake cikin danƙarereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a street ɗin tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa kaɗewar ta matuƙar razana, dan durƙushe tai ta cusa kanta a cikin ƙafafunta nuna alamar sadaƙarwa kawai. Haushi da takaici ya saka mutane yimata caa da faɗa, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ƙoƙarin kai mata duka ma adalilin yanda har yanzu taƙi motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar riƙota ta miƙar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata faɗi. Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen daketa faman hargowar zagin Samraahn haƙuri tare da jan hannunta ta buɗe motar a gefen mai zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun kasa barin wajen..        “Kowa yayi haƙuri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba”.      Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ƙyaƙyƙyawar zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ɗin. Daga haka kowa ya fara watsewa itama ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ɗan kalli Samraah ta sauke numfashi mai kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ƙwarewa ta harbawa saman titi da ƙyau. Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da niƙaff a fuska. A yanzu ma dai yarinyar kanta ƙudundune yake a cikin ƙafafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke fita kaɗan-kaɗan.       “Ɗiyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi haƙuri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa ko”. Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ɗaya kuma sai ta ɗago, Samraah ƙyaƙyƙyawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar hakan ba.       Idanu na tsira mata mai haɗe da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda kai na, a hankali na furta, “Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan baƙin cikin rashin tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin kaɗeni na huta da wannan rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ƙunci da baƙin ciki da ruɗani. Inama ace kin kaɗeni na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain.....”          Cikin sauri ta katseni da faɗin, “Haba haba ɗiyata wace magana kenan! Miyay zafi haka da irin waɗannan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ƙarancin shekarun naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara buƙatar ta? Idan ban shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani abu....”             “Ba taimako nake buƙata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da ƙawatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai.” na ƙare maganar da yunƙurin ɓalle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta riƙoni tana girgiza kai. “A'a ɗiyata yi haƙuri ki saurareni”. Juyowa nai na ɗan kalleta, sai dai bance komai ba........✍️ _Kuyi haƙuri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ƙaro muku. Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ƙarfina😘😘_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_ ........A hankali ta ɗan sakar min murmushi da faɗin, “Ko zaki iya mun alfarma”.       Cikin ƙosawa nace, “Tami?”.    “Ta sanin inda zakije yanzu?”. “Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma ajalina”.       Ɗan jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana wani juya idanu cike da salo, “Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ƙarshe muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda kike fata”.       Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tankaɗe gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan minti ɗaya na ɗan kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na laɓe a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu haɗari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ɗago na ɗan kalleta da faɗin, “Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya”.     Da sauri ta dakatar da in da faɗin, “Ko ɗaya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki ni kuwa, dama kawai nake buƙata daga gareki zaki tabbatar da abinda na faɗa ɗin in sha ALLAHU”.         Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin faɗin, “Ki yarda dani koda na sati guda ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ɗaukar mataki kowane iri”.      Shiru na sake yi na wasu ƴan sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ƙofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ɗan kalleni, sai dai batace komai ba. Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin, ALLAH kuma yasa ba daga ƙarƙashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba.           ★(✷✷✷‿✷✷✷)★      Tunda Hayatu yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ɗin yayi wata ƴar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu, amma a wannan gaɓar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi suka sani.        Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har harɗewa takeyi wajen sake faɗin. “Wlhy nayi duk yanda kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba laifina bane, ba daga ɓangarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin sanarma ƴan sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba”. Shiru nan ma Maash yaƙi ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ɗin dai tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu faɗa masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar shirunsa a yanzu na ɓacin rai ne, kuma bazai tanka masa ɗin ba har sai idan shine yaso hakan. Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya haƙura akaita ɗibar masa kuɗi har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ɗazun ko zaman ya kasa yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da huɗu. Idan ba hakaba yasan akwai matsala.....          💞💞💞💞    Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda ƙyaƙyƙyewa. Cikin ƙuluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya yunƙura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya riƙosa yana faɗin. “Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ɗan yaro bai mai garjejen saurayin ɗa kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka buɗe bakin aljihu kawai malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da mace ɗaya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da ana yin fin huɗu da ba tuni nayi ba”.         “Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin Jalilah tunda na gwada son ƙara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa yaran mutane.”     “Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama namiji kaji, tun farko kai ne kake ɓata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka yanzu har sai ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda tsoronta kake ji”.            “Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ɓoye matan. In kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano.”     “Wannan duk mai sauƙine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara inda amarya zata zauna nan da sati ɗaya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda inda zan kaika wlhy”.     Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ƙara auren na sake masa tasiri a zuciya....        🥱Hummm Abba cin amana ko. _________★        Gida ne mai ƙyawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani a symbol, dan komai najin daɗin rayuwar gani da ido a kwaishi. Ƙamshi da tsarin gidan yafi komai ɗaukar hankalina, dan haka nake ta ɗan kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi Hajiya da tuni takai zaune cikin ɗaya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, “Ƙaraso ciki mana ɗiyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro, wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk ƙarshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ɗaya biyu har ma zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce”. A hankali na haɗiye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ɗin Hajiya ta katseni ta hanyar ƙwala kiran sunan “Janny!”.       “Yes Ma'am”.   Wata murya ta amsa daga can gefen wata ƙofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin na gama nazarin tsarin da kujerun dining ɗin sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny ta sake gaida Hajiya tana ɗan satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da faɗin, “Kije da ita ciki, tai wanka a bata abinci”.     Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni. “Sannunka”. Abinda Janny ta faɗa kenan tana mai riƙo hannuna. Ban amsa mata ba, sai ma ƙoƙarin turjewa da nayi alamar bazanje ba. Hajiya dake kallonmu ta sake sakin murmushi. “Kinga ɗiyata nasan mike a ranki, karki damu shi komai na rayuwa mataki-mataki ne tamkar ajin makaranta. Ki kwantar da hankalinki zamuje gaɓar da kike buƙata. Bani nai miki alƙawari ba”.       “Amma Hajiya.....”   “Shiiii!! Kar kice komai bita kawai”. Hajiya ta faɗa cikin katseni tana tsuke fuska a karo na farko. Canjawar fuskar Hajiyar ya ɗan firgitani, dan haka nabi Janny kamar yanda aka bata umarni tun farko....      Cikin dauriya da danne duk abinda ke mun kai-kawo a cikin rai nayi wanka na fito fes dani cikin doguwar riga mara nauyi ƴar kanti da Hajiya ta bani na saka. Ga wani ƙamshi mai daɗi na tashi a jikina. Hatta da dunƙulallen gashina da zaman asibiti yasa baya samun gyara sai da na wanke na busar da hair dryer dana gani a toilet ɗin. Yanda na fito da shi ne a buɗe yasa Janny sakin baki tana kallona. Fuska na ɗan tsuke amma sai hakan bai sata yin shiru ba sai da tayi magana. Da ga ƙarshe ta laƙemin wai zata tayani gyarawa. Mai sosai Janny ta saka min masu daɗin ƙamshi da ma wasu abubuwan da suka sake miƙar da tsahon gashin nawa daya fara dankwafewa tsaff, sannan ta fake min shi a ribbons. Ni a karan kaina sai da naji daɗin kan nawa dama a kwanakin nan ya isheni da ƙaiƙayi. Shiru nayi kawai zaune ina ƙarema kaina kallo, a take naji tausayin kaina ya kamani. Wasu hawaye masu zafi da ɗaci suka shiga sakko min. Hannu nakai na sharesu da sauri, saboda tuna nayi alƙawarin bazan sake kuka ba akan halin da nake ciki. Plate ɗin da aka kawo min na abinci na ɗan tsurama ido, sai kuma na tureshi gefe dan bana buƙatarsa a yanzu duk da uban ƙamshin dake tashi mai tabbatar da abincin zaiyi daɗi koda banga minene ba. Zamewa nai kwance a saman lallausan carpet ɗin da shima ke ta tashin wani irin ƙamshi mai daɗi, gashi tsaf babu datti. Gajiya da wahalar dana sha ya sa barci yin awon gaba da ni cikin ƙanƙanin lokaci..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......“Madam bafa taci abincin nan ba, ko buɗe plate ɗin ma batai ba kuma tayi barci.” Janny ta faɗa cikin nuna damuwa.      Ƙaramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta buɗesu akan Janny cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. “Barta yunwar ai ba ƴar  gidansu bace, dan kanta ma zata ɗauka taci”.       Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. “Hakane Madam. Amma yarinyar yana da ƙyau fa sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?”.          “Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara. Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take buƙata”.       Sosai Janny ta washe haƙwara, dan duk hausar da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ƙaru da yarinyar sosai...       ★Washe gari kamar yanda Hajiya ta faɗa suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau ɗaya tayi shiru basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana ɗaki kwance sai dai akai mata abinci a ɗakko kwano.. Janny ce mai ƙoƙarin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan tafiyar yamma zasuyi.      Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira zata gani. Badai tace ita ƴar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta gagara cewa da Hajiya komai. Hasalima jinta take jikinta duk ya gama mutuwa ga bakinta ya mata nauyi. Sannan bata jin zata iya tsallake umarnin Hajiya sam koda cewa tai ta shiga wuta ta ƙone ko ruwan teku.        Tunda suka fito Janny taga Samraah na faman laɓe-laɓe a bayanta, Idanu Hajiya ta zuba musu kawai. Sosai ƙyawun yarinyar ya ɗauki hankalinta, sai taga tama ɗara yanda Jannyn keta kurantawa tun jiya. Baki ta buɗe zatai magana Samraah tai saurin faɗin, “Ina yini” cikin risinawa. Murmushi Hajiya ta ɗan yi tare da ɗauke kai, sai kuma ta sake maidawa ga Janny. “Wai nikam ashe amarya na kawo gidan nan ban sani ba. Irin wannan ɓoyo haka”.       Dariya Janny takeyi sosai itama idonta akan Samraah dake ta faman sinne kanta, da alama dai itama taji kunya, tunda koba komai ya kamata ta fito ta gaida Hajiyar da safe amma taƙi yin hakan. Duk sun fahimci taji kunyar ne suma, dan haka Hajiya ta kamo hanunta tana murmushi. “Daughter ai ko gaisuwa a fito muyi tunda dai naga baki son musan sunanki. Da alama dai yana da tsadar gaske, ko sai mun saya ne?”.          Karan farko na ɗago dara-daran idanuna masu shegen haske na sauke akan Hajiyar ina mai girgiza kaina da sauri, idanuna cike da ƙwalla alamar ina gab da shirin sakin kuka, dan haka kawai naji wani irin tsoro da shakkar matar ya shigeni mai tsananin gaske..    “A'a da alama dai ɗiyar tawa shagwaɓaɓɓiya ce, to mun haƙura tunda dai ba'a son mu sani. Mu sai mu saka miki namu sunan ai kawai kinga an huta canki canka ko”. Hajiya ta sake faɗa cike da salo tana murza hannuna a hankali.     Janny dai dariya take, yayinda ni kuma na duƙar da kai kawai, sai dai abinda Hajiyar ke min a hannu sam bana so, amma tsoron janye hannuna nakeyi.. “Baby zata shiga gaba koni Hajiya?”. Janny ta faɗa dai-dai muna isowa gaban hamshaƙiyar motar Hajiya data sha wanki take ta ƙyalli. Kallon Janny Hajiya tayi, yayinda ni kuma na ɗan ɓata fuska, a raina ina ayyana (baby kamar wata ƴar tsanar wasan yara) a fili kam sai na girgiza kaina a hankali na ce, “Sunana *_Samraah_*”.        A kusan tare Hajiya da Janny suka kalleni, Hajiya ta saki murmushi, Janny ta ce, “Woow nice name dear. Dole ki mana yanga irin wannan golden name haka”. Ta ƙare maganar tana ɗan rungumoni. Jikina na ɗan jaye daga nata batare dana sake cewa komai ba. Hakan yasa Hajiya ɗan harararta akaikaice alamar ta sakeni. Jayewa Janny tai tana faɗin, “I'm sorry maa”. Bata tanka mata ba ta kama hannuna muka shiga baya, dan tuni driver ya buɗe mana. Gaba Janny ta shiga, daga haka driver ya harba mota zuwa gate. Mun ɗan tsaya a bakin gate Hajiya tai magana da maigadinta, tare da bashi kuɗi masu yawa da suka bani mamaki. Shiko sai faman godiya yake bakinsa a washe har motar tai nisa da gate ɗin bai bar ɗaga mana hannu ba....       ★ A cikin tafiyar ƙanƙanin lokaci muka iso airport, hakan sai yay matuƙar bani mamaki. Dan na fahimci airport ne muka zo, sai dai na gagara iya cewa komai dan ji nake tamkar an ɗaureni ne da sarƙa, bakina kamar an saka masa padlock. Wani irin sarawa naji kaina namin da tunani barkatai akan inda zasu kaini, a wane rami kuma na sake jefa rayuwata ni Samraah, kamar fa batun Lagos naji mutanen nan nayi, sai kuma zancen Hajiya ya sake tabbatar min da hakan. Dan bayan fitarmu a motar take sanarma drivern ta yay ƙoƙarin wucewa Lagos da sassafe gobe, bata son ya kwana a hanya bai iso ba. Shiko yana tabbatar mata da in sha ALLAHU cikin girmamawa. Daga haka Janny ta gungura akwatinansu ita kuma Hajiya taja hannuna muka shige ciki. Mun ɗan yi zaman mintuna goma a wasu kujeru kafin mu miƙe lokacin da ake sanar da parssinges ɗin Lagos suyi himma. Cikin kasa haƙuri da suɓutar baki saboda sunayen ALLAH da naketa ambato a ƙasan zuciyata na ce, “Muma wai jirgin zamu hau Hajiya?”. Kusan lokaci guda Janny da Hajiya suka saki ƙaramar dariya, kafin Hajiya ta kamo hannuna cike da kulawa. “Eh Samraah muma jirgin zamu hau zuwa Lagos, dan yafi sauƙin tafiya sai kiga nanda wani ƙanƙanin lokaci mun isa. Idan kuma baƙya son zuwa ne bazamu takuraki ba, tunkan driver yay nisa sai na dakatar da shi ya koma da ke, amma fa ba can gidan zaki koma ba, dole garinku zaki faɗa ya maidaki gidanku”.         A take batare da nasan dalili ba na ruɗe, na shiga girgiza kai idanuna na cika da ƙwalla. Cikin rawar murya na ce, “Hajiya kiyimun rai. Wlhy dana koma gida gara ma ki kasheni kawai. Sannan kuma shima ya tabbatar min zai iya salwantar da dangi.....” sai kuma nai shiru tamkar wadda aka tsawatarwa har ina kai hannu saman bakina na dafe. Ganin kallon tuhumar da Hajiya ke bina da shi da Janny ya sani sakin hawayen suka zubo. “Na yarda Hajiya ki kaini koma inane, amma banda maidani gida, zaki sameni a mai yi miki biyayya ɗari bisa ɗari...”         “Miya samu dangin naki?”.     Hajiya ta katseni tana mai tsatstsareni da idanu. Ruɗewa nayi jikina ya fara rawa da lips ɗina. Saina fara ƙoƙarin jan jikinna baya daga kusa da su. Dai-dai nan aka sake shelanta neman passinges na flight Lagos. Hajiya ta ɗan ja numfashi ta fesar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da kamo hannuna. “Ok ok kiyi haƙuri ba sai naji ba. Muje kawai kar jirgin ya wuce ya barmu”. Ƙoƙarin tirjewa nayi Hajiya ta sake damƙoni da ƙyau tana min magana a hankali mai nuna alamar lallashi, sai dai nauyinta ya wuce duk yanda mai karatu ke hasashe....         Sosai jikina ke maƙyarƙyata a cikin jirgi saboda zantukan Hajiya. Sai faman maƙurewa nake a waje ɗaya alamar dai a firgice nake. Hajiya kam na riƙe da hannuna katamau tamkar zan tsere mata ne. Janny dake daga can ɗayan gefenmu kam kallonmu kawai take tana danne dariya. Dan duk wanda ya kalleni zai ɗauka ƙauyanci ne cike taf a kaina ba wai tsoro ba. A haka dai jirgi ya lula sama  harda yunƙurin amai na amma na danne, bayan ya gama dai-daita dole sai da Hajiya ta rakani restroom nayi sa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga zazzaɓi ya rufeni ruff abinka da wadda bata gama murmurewa ba dama. Koda muka sauka a Lagos kaina a juye yake ma gaba ɗaya. Dan bana iya gane komai yanda ya kamata har muka shiga mota zuwa anguwar da Hajiya take....           Babbar anguwace mara yawan cinkoson jama'a kamar ba'a cikin Lagos da nake jin ana faɗa ba. Duk da kuwa kafin mu iso cikinta mun shiga cinkoson matuƙa wani gurin ma da ƙyar muka fita, dan tafiyarmu daga filin jirgi zuwa gida yafi tafiyarmu daga Kano  zuwa Katsina nisa, duk da dai shi wancan gari da gari ne, wannan kuma cikin gari dole akwai banbanci. Iya ƙagara na ƙagu a zo gida, dan a yanzu ma amai ne keta faman taso min tunda muka shiga motar. Da alama Hajiya ta fahimci halin da nake ciki ne ya sata siya min lemon zaƙi a hanya tace na dinga shanshana ɓawon, sai goro da shi kuma na dinga ɗan ci kaɗan-kaɗan. Wannan ne ya riƙeni zuwa gidan Hajiya.        Anan ɗin ma dai maigadi ya buɗe mana gate, sai faman washe baki yake da jerama Hajiya sannu da zuwa. Da taimakonsa mai taxi ɗin daya ɗakkomu ya fidda mana akwatinansu biyu madaidaita. Janny ta tsaya biyan mai taxi ɗin, yayinda ita kuma Hajiya ta kama hannuna muka nufi wata ƙyaƙyƙywar ƙofa fara da adon golden. Wannan gidan yafi gidan Abuja girma, lokacin da muke shiga falon kuma ya sake tabbatar min da yafi wancan ɗin kayan alatun more rayuwa ma. Dan falon ƙato ne na gaske, ga wasu manya-manyan hotunan Hajiya da wani mutum a jiki tamkar zasuyi magana dan girma. Sai ƴammata biyu masu tsananin kama da juna sannan suna kama da mutumin. Fitowar wasu ƴammata biyu da dattijuwa ya katse min kalle-kallen hotunan da nakeyi. Nai tsai ina kallon dattijuwar da ƴammatan da suka zube gwiwa bibbiyu suna gaida Hajiya da jera mata sannu da zuwa. Itako amsawa take cike da nuna isa da gadara tamkar ba Hajiyar dana sani daga jiya zuwa yau ba. Dan bayan ta gama amsa su a taƙaice tai musu nuni da ni. “Kuje da ita sashenku kafin na nemeta, duk kuma wanda ya mata wata any magana sai na wulaƙantasa ta yanda sai yayi dana sanin sani na a gidan nan. Ina sauran suke?”.         Da sauri dattijuwar ta amsa mata da “Madam Oyinka ta ɗauki Surayya da Umayyah, dan tare sukazo da wata baƙuwa tun jiya da yamma kamar yanda na sanar miki a waya”.      Kaɗan Hajiya ta yamutse fuska tana kallon agogo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, dai-dai nan Janny ta shigo maigadi biye da ita jaye da akwatuna. Hannu kawai Hajiya ta ɗagama Dattijuwar alamar suje. Miƙewa duk sukayi suna min nuni da ƙofa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ _______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ ......Wani irin yamutsawa kaina ya shiga yi, dan gaba ɗaya suffar ƴammatan nan da dattijuwar batai kama data mutanen kirki ba, sai irin gogaggun matan barikin nan da idanunsu ya gama gogewa. Juyowa nai a karan farko na dubi Hajiya, itako ta ɗauke kanta gefe fuskarta babu alamar wasa a yanzu. Kamar ba itace keta faman min murmushi ba a Abuja da lallaɓani. Kallona na maida ga Janny da itama take kallon Hajiyar, a karo na farko na ce, “Dan ALLAH Hajiya ku barni a wajenku”.         Wata irin tsawar data gigitani Hajiya ta daka min. “Ka jimin shegiyar yarinya, su ɗin sama suka ce miki suna da gida bayan wannan da suke ciki?!! Zaki wuce ko sai na banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa ku gammin yarinya da tsurku. Kin fini sanin abinda ya dace ne!”.             Rawa jikina ya cigaba dayi har ina neman kifewa ƙasa. Bamma san sanda nabi wanda akace nabin ba. Da harara Hajiya ta raka bayansu, sai dai suna ficewa taja tsaki da fincike gyalen abayar data naɗe kanta da shi. Tuni gashin dokin kanta ya bayyana, ta jefar da ɗan vail ɗin tana magana cikin yare, sai kuma ta miƙe ta fincike abayar ma. Anan ɗin ma wani wandon bomshot ne na jeans ya bayyana a jikinta da riga best....         “Hajiya ya haka?”.     Cewar Janny tana dariyar shaƙiyanci. Da sauri ta harari Jannyn da zagaya hannunta saman kai ta ce, “God for bed yoo, sunana Jannifer Can hajiyansu su ƙarata da shi bani ba Mtsowww!!. Yanzu ma zanyi shirin Church pastor yay min addu'a akan hakan. I beg, give me wine na ɗan sha ma ko zandawo hankalina da ƙyau”. Tai maganar tana komawa saman kujerar ta zube. Wucewa Janny tai hanyar kitchen, babu jimawa ta dawo da kwalban giya mai tsadar gaske da cups guda biyu. Ita ta ɓalle ta zuba musu tare da miƙamata itama ta ɗauki ɗaya, sai da suka ɗan haɗa kofunan alamar chess sannan kowa ya kai bakinsa yana murmushin samun nasara. Dan kuwa dai sun samo nasarar da suke buƙata a wannan tafiyar.       (Tofa abin mamaki, idan na fahimta dai wannan Hajiya ta bogi ce, hasalima ba musulma bace, ba kuma bahaushiya ba. Ko kuma dai bahaushiyar ce musulma ada tayi ridda? Tirƙashi, muje zuwa wai maƙwafcin mai akuya ya sai kura).. _______★         “Duk yanda na lissafa miki kayan nan haka zatai amfani da su Jalilah. Sannan wannan da za'a dafa abincin da shi ki tashi da kanki kiyi girkin bawai kiba wannan shegiyar mai aikin da kika kwaso ba. Ni wlhy haka kawai yarinyar sai bata min ba, dan kawai kinƙi jin shawara ne”.       “Wai Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Mai aikin nan fa dolece. Sanin kanki ne da ga Baby har Bibaa babu abinda suka iya na aikin gida, ni kuma wlhy yanzu na riga na sangarce tunda shegiyar yarinyar can ke komai tun tana ƙanƙanuwarta. Da nasan haka abin zai ƙwaɓe min ALLAH da auren zan hanata gaba ɗaya a rayuwarta”.       Dariya Umman tata tayi da faɗin, “Daga baya kenan. Ni dai muyi abinda ke gabanmu nata kuma ya zama labari ai tunda kin ɗebi rabonki. Yanzu babban burina Bibalo da takwarata su auri mazan kere sa'a. Dan haka bana son wasa. Awakina na sayar har Niger naje amso kayan nan kema kin sani, dan haka kiyi yanda nace ni zan wuce bana son mijinki yazo ya sameni anan. Magana ta gaba kiyi duk yanda zakiyi waɗan nan samarin biyu ƴan uwan yarinyar nan suma su bar miki gida dan nafi son na cigaba da ganin daga ke sai ƴan ƴaƴanki a cikinsa.”       “Banƙi na naki ba Umma, sai dai fa yaron nan yanzu shine komai na gidan nan, ina mora a jikinsa wlhy bazan so yabar gidan ba. Shiko ƙaramin dama yana makaranta sai lokaci-lokaci yake zuwa. Mudai sake shawara yanzu ne lokacin cin amfaninsu su dama macen ce nauyi ai”.          “Eh to da kuma wannan dan wannan. To wai tsaya ma, idan yaron nan kinga yana samun wasu manyan kuɗi ne mizai hana mu haɗa shi aure da Bibaa”.      “Bibaa kuma Umma?”.   “Ƙwarai da gaske. Ga gida bai ƙoshi ba sai a kaima dawa. Ke dai ki nutsu ki sake tabbatar da nauyin aljihunsa. Dan ni dama hidimar da yay a bikin ƙanwar nan tasa da wadda yake a baya tana firgitani”.          “Amma Umma iyakar yaron nan fa Sakandire”.     “Ina ruwanmu da wani Sankandire ɗinsa ko digiri. Shi namiji ai aljihunsa adonsa. Yo ko besan (A) ba indai akwai babbar (N) a aljihunsa miya damemu. Kidai yi nazari nima zan sake tunani”.      Cikin jimamami Mom ta ce, “To shikenan Umma ALLAH yasa mu dace, sai na jiki ko kin jini.”       “To mu huta gajiya. Amma ki tabbatar sunzo sun gaisheni fa ita da shi idan ya iso”.      “Zasu zo Umma kar ki damu”. Tofa ban ganeba wai anyi gabas da kare🤔🥱 ★★★★ Gaba ɗaya a firgice nake da komai, dan wani irin juyewa ƙwaƙwalwar kaina ke neman yi. Musamman ma da naga inda ƴammatan nan suka nufa da ni. Tacan bayan gidanne alamar Bq. Sai dai an raba tsakaninsu da inda su Hajiyan suke da katanga harda ƙofa. Akwai ɗan filin tsakar gida, wanda ke da ƴan kayayyakin ajiya kamar su drum na ruwa guda uku, sai botikai da yan tarkace na aiki. Sai murhun gawayi guda biyu da wasu tukunya masu girma guda biyu. Duk da gidan a share yake tsaff ko kusa bai kama ƙafar ƙyawun inda muka baro ba. Lokacin da muke ƙoƙarin shiga ƙofar da nake ƙyautata zaton ɗaki ne na kusa cin tuntuɓe da tarin takalman dake a wajen, sai da ɗaya daga cikin ƴammatan ta taroni. Sannu tai min cike da nuna alamar tausayawa, na gyaɗa mata kai kawai ina mai haɗiye abinda ke min kaikawo a maƙoshi. Ƙaton falone sosai, sai dai babu komai a cikinsa sai carpet blue da aka malale ƙasa da shi. Sai ƙofofin ɗakuna a jajjere a kowanne bango akwai biyar. Shima falon dai babu datti, sai dai carpet ɗin yay masifar tsufa har a wasu wajajen ya yage wani gurin kuma ya gurje alamar yawan takawa, duk naga hakane saboda hasken wutar lantarki dake haske dako ina. A hankali nakai zaune kamar yanda suka umarceni, na takure jikina waje guda ina ɗan kalle-kalle. Kusan minti uku dattijuwar nan ta kawo min abinci a plate ɗin roba. Shinkafa ce da wake da mai da yaji. Sai ruwan ƙwara ɗaya.       “Bissmillah kici abinci ƴar nan. Sai kije kiyi wanka kizo ki kwanta”.      Kasa cema tsohuwar komai nai, sai binta da kallo kawai nake. Babu alamar ta damu da hakan itako tai gaba abinta ta sake fita. So nake na danne komai a raina karna sakama kaina wata damuwa ko tsoron inda na tsinta kaina. Dan haka na shiga turereniyar ture komai na fara cin abincin. Kaɗan naci abincin dan bakina sam babu daɗi har yanzu, hakama jikina babu ƙarfi sosai. Ruwanne na shanye gaba ɗaya, cikin sauke numfashi nai hamdala ga UBANGIJI. Ƙoƙarin miƙewa nake dattijuwar nan ta shigo, kallonna tai ni da plate ɗin abincin, da yanayin mamaki da gurɓatacciyar hausarta da zaman Lagos ya ɓata ta ce, “Ƴar nan badai har kin ƙoshi ba?”.             A hankali na gyaɗa mata kai alamar hakane. Mama tai ɗan jimm kamar mai tunani, sai kuma ta amshi plate ɗin ta ajiye tana faɗin, “Shikenan muje kiyi wankan sai ki kwanta ko?”.     Kai na girgiza mata, cikin yanayin dana tsinta kaina na sanyi da rashin ƙarfin zuciya kamar wadda aka jefa na ce, “Mama zan kwanta kawai basai nayi wankan ba, dan in har nayi zan iya samun matsala koda da ruwan zafi ne”.       Jimm mama tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Cikin sauke ajiyar zuciya tai min nuni da hanyar ɗaya daga cikin ƙofofin dana gani. “Ba damuwa muje ciki to”. Ɗaki ne ƙarami sosai. Amma duk da haka akwai katifu ƙanana irin na ƴan makaranta har guda biyar jere reras. Kowace katifa akwai filo da bargo. “Nan shine zai zama ɗakin ki. Ba kuma ke ɗaya bace za'a iya sake kawo wasu kuna kwana a tare. Sai dai a yanzu babu kowa sai ke kaɗai dan ankwashe wanda suke ɗakin gaba ɗaya”.        “Mama saboda mi to?”.    Na faɗa cikin suɓucewar baki da jin wani irin ƙarfin zuciya a lokaci ɗaya. Komai mama batace da ni ba. Sai ma juyawa da tai abinta ta fita kawai tana faɗin “Sai da safe”. Sosai mamaki ya saka ni ƙurama ƙofar ido na tsawon lokaci. Sai kuma zuwa can na taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar oho muku nai kwanciyarta. Amma a can ƙasan raina aikin jaridancin ne ke faman yinƙuromin, dan haka kawai nake ji a raina a wannan gidan akwai abinda ake ƙullawa. Abin mamaki na farko canjawar Hajiyar nan da mai aikinta a lokaci ɗaya, ita da suketa tattalinna tun daga jiya kamar wata ƙwai amma muna shigowa gidannan kamar basu ba. Na biyu wannan ƴammatan dana gani anan da kuma shi kansa wannan part ɗin da alamu suka nuna mutanene da yawa ke mu'amala da shi. Na uku ganin kusan ƴammatan duk hausawa ne musulmai haihuwar arewa. Lallai ina buƙatar nasan wani abu kam. Sai dai ta yaya? A wajen wa?. Wannan shine babban tsallen baɗaken....       Washe gari kiran sallar farko Maman nan ta tadamu, salla muka farayi, muna idarwa ta tattaramu zuwa ainhin cikin gidan. Babu motsin kowa alamar mutanen gidan basu tashi a barci ba. Aiki Mama ta rarraba mana, ta kuma tsaya a kanmu sai da kowa ya kama nashi yanda ya kamata. Kafin kace mi cikin abinda baifi awa ɗaya da rabi ba mun kammala ko ina ƙal, sai ƙamshin fresheners ke tashi da girkin da Mama keyi a kitchen. Can sashen nasu muka koma, yayinda muka bar mama na ƙarasa girkin, a can ɗin ma ba zaman mukai ba, gyara ko'ina muka shigayi, wasu kuma na haɗa wutar gawayi domin ɗora abincin kari. Ni dai duk abinda akace nayi yinsa nake yi, yayinda nake faman bin kowa da komai da idanu cike da nazari. Babu wanda ya tambayi sunana nima kuma ban tambayi sunan kowa ba, sannan ko'a junansu bana jin suna hira balle ambatar sunayen juna, kowa aikin gabansa kawai yake baki ruff. Kafin goma na safe mun kammala komai, masu shiga wanka nata ƙoƙarin yi duk da banɗaki biyune kacal a sashen na toilet dana wanka, amma haka suke bin layi kamar wasu ƴan makaranta. Kasancewar basu da yawa sosai basuja wani dogon lokaci ba suka kammala wanka. Zuwa sannan mama ta dawo, ita ta rarraba mana abincin kowa yazo ya ɗauki nasa yaja gefe yana ci, sai a sannan wasu ke ƴar hira ƙasa-ƙasa. Ni dai nama gagara cin abincin sai kallonsa kawai nake har sai da Mama tai min magana akan na maida hankali naci dan Madam na buƙatar ganinmu.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Wanke-wankenta take hankali kwance, yayinda bakinta ke faman raira waƙar Ado gwanja ta Chass. Sosai zazzaƙar muryarta siririya ke faman ratsa zuciyar Abba dake falo zaune yana waya. Shi kaɗai ne a gidan sai ita. Dan tun ɗazun Mom da Baby da Bibaa suka fita kasuwa wai yi cefane Baby zata yi baƙo. Sai Auta dake ɗaki yana barci saboda zazzaɓi da yake yi kwana biyu. Abbas kam ma yanzu sai ya gadama yake kwana a gidan. Shiko Nabeel yana hostel ne. Ya Musaddiq ma ganinsa yayi wuya a gidan yanzu.        Halime kenan sabuwar mai aikin Mom da ta saka wata ƙawarta ta nemo mata tun bayan wucewar baƙi ƴan biki da kwana biyu. Dan kuwa daga ita har su Baby sun gagara gyaran gidan ga hargitsewar da yayi na hidimar biki. Da gaggawa ta buƙaci samun mai aikin dan haka ƙawar tata ta kawo mata Halime da itama ta samo wajen wata mata mai kawo ƴan aiki daga ƙauye. Da farko Mom taso ƙin amsar Halime, saboda ƙyaƙyƙyawar yarinya ce ga ƙirar jiki irin ta manyan mata ALLAH ya bata. Rashin gyara ne kawai da rashin suturar kirki ya ɓoye baiwar da ALLAH ya matan. Sai kuma ɗan shirme na rashin ilimi. Har tace ƙawar tata ta koma da ita a samo mata wata su Baby suka shiga roƙonta dan su kam aikin suke gudu, dole ta haƙura ta amshi Halime akan nan da wani lokaci za'a sake samo mata wata sai ta sallameta. Sai dai duk da haka ta kafama Halime dokoki sosai a gidan musamman akan Abba. Dan tunda tazo gidan ma kusan sati uku da wasu kwanaki kenan bai taɓa ganinta ba, itama bata taɓa ganinsa ba. Yau ma Abban har ya fita kasuwa mantuwa tasa ya dawo gidan, kiran wayarsa da akayi ya sakashi zama a falon yana amsawa. Gaba ɗaya wayar ta gundiri Abba, dan sosai muryar take sake tasiri a zuciyarsa. Sallama yay ya miƙe zuwa ɗakin barcinsa yana ƙwala ma Mom kira dan bai san basa gidan ba tunda ba gaya masa tayi zata fita ba. Cak Halime ta tsaya daga raira waƙar da take yi, tai ɗan jimmm alamar saurare. Jin da gaske dai muryar namiji take ji na kiran hajiyarta yasata ɗauraye hannunta a fanfo ta fito a kitchen ɗin. Dai-dai lokacin Abba na ƙoƙarin shigewa bedroom ɗin da cigaba da ƙwala kiran sunan Mom. Cike da rashin wayo da gaɓanci Halime ta ce, “Ikon ALLAH kai kuma waye haka kake kiran mafarauta sanƙamemen ƙato har ɗakin kwanan mutane?”.      A bazata furucin nata ya shiga kunnen Abba, dan shaf yama manta da wata batun mai aiki da Mom tace masa zata kawo, tunda shi dai bai taɓa ganinta na tunda tazo gidan, dan haka ya juyo gaba ɗayansa. Idanu sosai ya tsira mata, ganin yanda ta riƙe ƙugu tana hura siririn dogon hancinta da tura madaidaicin bakinta ya bashi dariya. Amma sai baiyi ba cikin suɓutar baki ya furta, “Aljani ne”.       “Na higa uku ni Halime aljani kuma? Ita dama Hajiya tasan da aljanu a gidanta ta kawoni nai mata aikatau”.      Murmushi Abba ya saki a karo na farko, yayinda a kaikaice yake sake ƙarema yarinyar kallo. A fuska dai bazata wuce sha bakwai zuwa kaɗan ba. Amma a jiki akwai ƙira ta manyan mata, dan tako ina a cike take. Ganin tana neman zurawa da gudu yay gyaran murya. “Kinga kwantar da hankalinki ba aljani bane. Mai gidan ne. Ina hajiyar taki?”.     Da mamaki Halime ta waro idanu waje sosai, sai kuma ta dafe baki tana juyawa ta kalla makeken hoton dake falon, wanda tunda tazo gidan Ita dai bata gajiya da kallonsa saboda ƙyawun da sukayi a jiki shi da Mom da su Baby. Su Samraah dai babu su daga ita har su Yaya Musaddiq. Tabbas mutumin dake zaune kusa da Hajiya ne. Amma duk da haka sai da ta sake juyowa ta kalla Abba. Kamar wadda aka tsikara ta zube ƙasa tana faɗin, “Na shiga uku wlhy kuwa kaine ɗin. Alhaji dan ALLAH ai min aikin gafara”.        Murmushi Abba ya sake yi, sai kuma a hankali ya furta, “Ba damuwa tashi abinki. Ina hajiyar taki?”.      Miƙewa Halime tayi, sai dai yanzu kanta a ƙasa alamar jin kunya. Cikin ƙanƙan da kai ta furta, “Sun fita da Aunty Baby da aunty Bibaa”.     Ɗan jimm yay yana kallonta. Sai kuma bai ce komai ba ya kaɗa kansa zai shige bedroom ɗin. Sai da ya juyo zai rufe ƙofar suka sake haɗa ido da Halime dake kallonsa itama. Da sauri ta juya masa baya har jikinta na kaɗawa. Numfashi ya ɗan furzar da cewa, “Je ki cigaba da aikin ki”. Bai ma kai ƙarshe ba ta zura da gudu hanyar kitchen. Kansa kawai ya girgiza yana murmushi shima ya ƙarasa shigewa ciki....        💦★💦★💦★💦   Washe garin da nake cika kwana biyu a gidan bayan kammala aikin dana fahimci wajibine a garemu a gidan muna dawowa wanka nayi na shige inda ke matsayin ɗakina batare dana shiga aikin namu sashen ba. Kwanciya nayi wasu hawaye masu zafi na sauka min batare dana sani ba. Gaba ɗaya na rasa mike damuna. Koda tunani nai ƙoƙarin yi akan kaina da zaman wannan gidan sai kaina ya fara ciwo. A yanzu haka har ya fara saramin. Dole na tattara komai na watsar na cigaba da kwanciya shiru a wajen har suka kammala aikinsu Mama tazo tai kirana dan a zatonta banda lafiya ne. Da ƙyar na iya faɗa mata na ƙoshi. Jimm tai tana kallona, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya ma ta fita. Kusan mintun talatin da fitar tata sai gata ta dawo. Wai na taso Hajiya na kiranmu. Babu musu na miƙe dan bama zan iya musun ba. Hasalima sai wani irin tsoron Hajiyar ne naji ya sake shigata har zuciyata na rawa. Haka dai muka fito duk a ɗarare.       Mun kai tsahon mintuna goma a tsaye bayan shigar Mama cikin falon kafin a bamu izinin shiga ciki. Hamshaƙan mata muka samu har guda uku zaune cikin shiga ta alfarma. Basai an faɗa ba, a kallo ɗaya da zakai musu zai baka tabbacin daloli sun zauna musu bama naira kawai ba. Hajiya na zaune itama cikin tata shigar alfarmar tamkar mai shirin fita ma. Gefenta Janny ce ke tausa mata ƙafafu a hankali. Gaishesu mukai a tare, duk suka bimu da kallon ƙurulla batare da sun amsa ba.      “K fita anan banda ke”. Furucin Hajiya ya samu ɗagowa gaba ɗaya dan bamu san dawa ake ba a cikinmu. Sai dai ganin kai tsaye ni ta nuna yasa sauran maida kawunansu ƙasa. Cikin dokawar ƙirji na yunƙura zan fita a cikinsu kamar yanda ta umarceni. Amma sai ɗaya a cikin matan ta katseni da faɗin, “Kamar ya banda ita? Ai ni gaba ɗaya ma hankalina a kanta yake Madam”.     Kai Hajiya ta girgiza mata. “No Alajah ita wannan sabuwa ce. Babu abinda ma ta koya balle nai cinikinta. Sannan ba aikatau ne aikinta ba”.         “Babu wani damuwa a hakan ni tamun. Dan dama irinsu nake so sunfi daɗin sha'ani ya zama komai kaine ka koya musu. Nima zayi gift da itane kar ki damu”.     “Amma Alaja.....” “Basai kince komai ba zan ninka kuɗinta sau uku. Domin zanyi ƙyauyar girma ne”.         “Uku?”. Madam ta faɗa cikin waro idanuwa da sakin murmushi. Amsa Alaja ta bata da, “Yes nan gaba ma idan aikinta yay ƙyau har ƙyauta ta musamman zaki iya samu. Dan gidan girma za'a kaita dake kanki sai kin san kin zama mai sa'a a wannan gaɓar”.        A take kuwa Madam ta sallama. Babu ɓata lokaci matar tai kiran waya driver ɗinta ya shigo da jakkar da bamu san minene a cikinta ba. Daga ganin yanda yayma Hajiya gaisuwa kasan shima ɗan gida ne. Suma sauran duk sun zaɓi ƴammatan ɗaɗɗaya. Bayan suma an kawo tasu jakar da bata kai ta Alaja girma ba Mama ta umarcemu da mu fito. Ni gaba ɗaya ma sai naji kamar an ƙara ɗaureni da sarƙa. Sannan yanda nake jina ko wuta Hajiya tace na faɗa zan iya hakan. Sabbin kaya Mama ta bamu mu ukun nan wai mu saka. Bayan mun kammala tace muyi sallama da sauran ƴan uwanmu dan zata iya yiwuwa rabuwar kenan, idan iyayen gidanmu sunji daɗin zama damu ba lallai mu sake waiwayen nan ɗin ba. Mu dukanmu tamkar waɗanda ake sarrafawa da remote mukai sallama da su. Sai dai ƙasan zukatanmu mu kaɗai muka san halin da muke a ciki sai UBANGIJINMU. Haka muna ji muna gani aka fiddomu harabar gidan inda hamshaƙan motoci suke har guda uku. A ta farko da tafi kowacce ƙyau da tsaruwa akace na shiga gaba. Yayinda aka buɗema Alaja baya ita kuma ta shiga. Sauran ma duk shiga sukai motocin suka fice.      Haka kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga sakkomin. Duƙar da kaina kawai nayi na cigaba da kukana batare da na bar sautin ya fita ba. Haka kawai nake jin takaicin kaina da sauyawata. Jina nake tamkar bani Samraah Abdul-wahab Gwarzo ba. Gaba ɗaya tamkar an kashemin zuciya da kuzari. Abinda kawai nake ganewa shine bin umarni. Munyi tafiya mai nisa kafin na share hawayena na ɗago. Bansan lokacin dana furta (Masha ALLAH) ba a zuciyata ganin wata irin ginanniyar anguwa da muka shigo. Sam tsarin anguwar baiyi kama da a cikin ƙasata Nigeria ba. Victoria island na gani rubuce a babban symbol. Hakan na nufin sunan anguwar kenan. Tun a farkon shiga street da shima aka rubuta a symbol sai dai banga farkon sunan ba securitys suka tsaidamu. Sai dai ganin Alaja yasa suka bamu damar shigewa alamar dai sun riga sun santa.......✍️       _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏_ _______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Su Alaja na ficewa a gidan dasu Samraah Madam tai wani ƙasaitaccen murmushi da cije lips ɗinta. Wayarta ta shiga daddanawa tana tafiya har ta shige ciki. Dai-dai tana kai wayar kunnenta takai cikin kujera. Cikin wani salon gogaggun matan bariki ta shiga jera kirari ma wadda tai kira a maimakon gaisuwa. Bamu ji abinda aka faɗa mata daga can ba. Sai dai yanda ta saki siririyar dariya zai baka tabbacin mai daɗi ne. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗaura da faɗin, “Ina godiya da wannan ƙyauta hajjaju masu Lagos da wajenta. Kai Africa ɗin ma duka taku ce. Na kiraki ne domin wani babban albishir da nai imanin zai faranta miki ranki matuƙa”. Ta ɗan yi jimm alamar saurare. Wani murmushin mai faɗi ta sake saki da cigaba da faɗin, “Godiya nake hajjaju. Dama akwai babbar haja da a yanzu akai cinikinta zuwa gidanku. Na tabbatar irin kalarki ce shiyyasa ma na sayar babu ja'inja bayan na gane daga ina masu sayen suka fito. Na tabbata idan kikaga wannan hajar sai kin sake min sabon biya dan ni kaina buƙatar kuɗi kawai ta sakani sallanawa amma raina ya biya sosai.”       Amsar da Hajiyar ta bata daga can ya sata sake sakin dariya. “Ayyah! Hajjaju Ayya. Ai ku manyanmu ne. Kodan girmamawa ma kauda kai ga abinda ya dace daku. Sai dai kinga kayan dan na tabbatar yanzu suna gab da zuwa gidan naku. Duk da dai tace zata bada as gift ne. Kuna wani shagali ne a gidan naku babu gayyata Hajjaju?”.      Shiru alamar saurare, sai kuma ta tashi zaune da ƙyau tana furta, “Woow fantastic Hajjaju. Ai dolene muzo wannan birthday party kuwa kodan ke. Dan haka sai kin gammu”.     Daga haka sukayi sallama ta yanke wayar tare da ajiyeta gefe tana wata kalar shaƙiyyar dariya. A ranta tana ayyana (lallai yarinyar nan tazo da arziƙi. Ai tun da na ganta nasan mabuɗin arziƙina ce ita, dan zoben da babalawo ya bani yay wani irin haske da bai taɓa yi akan sauran yaran da nasarata ke samowa ba. Sai dai fa nima yawuna ya biya, dan komai yaji a jikin yarinyar nan, ga wani shegen fata kamar na dorinar ruwa. Dan haka sai na ɗanɗana koba yanzu ba) ta saki wata dariya a zahiri. Hakan yay dai-dai da shigowar Janny. Ko kaɗan batai mamakin gani da jin dariyar da Madam ɗin tata keyi ba. Sai ma takowa da tai cike da yauƙi jiki na girgiza ta faɗa mata a jiki...... (Hummm🥱)         💥💥💥💥       *_MAASH MANSION_* Shine rubuce da manyan baƙi da akai da kalar ruwan gold a jikin babban makeken baƙin gate ɗin gidan da ya mamaye kaso mai yawa na street ɗin. Ƙirjina yay wata irin masifar harbawa, ba sai an min bayani ba, hakan na nufin wannan katafaren gini shine gidan su Maash ko gidan Maash. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un) to yaya hakan ta faru? Maash ɗin dana sani ne a Lagos ko kuwa wani ne mai irin sunansa?. Bani da mai bani amsa sai jikina dake rawa sosai amma babu wani yinƙuri da zan iya yi. Dan tuni wasu garɗa-garɗan securitys dake tsaren ƙofar sun miƙe, sai da suka gama kallemu ɗaya bayan ɗaya da gaida Alaja cikin girmamawa sannan ɗaya daga cikinsu ya danna remote da ke hannunsa, a hankali gate ɗin ya shiga zuge kansa. A jere motocin uku duk suka shiga makeken compaund ɗin da sam baida iyaka ga mai kallo, kowacce ta tsaya a muhalin da ake son ganinta. Dolene ka shigo wannan gida ka tsarkake sunan UBANGIJI mai rahama mai jinƙai, dan shike samarwa ga wanda ya so a lokacin da yaso. Gini ne daya ginu karkashin mahaukatan maƙudan kuɗaɗe da sam zaka iya rantsuwa da ALLAH ba'a Nigeria kake ba idan kana a cikinsa. Dan a iya compaund kawai da abinda ke zagaye da gidan, da kallon ginin a tsaye ya isa tabbatar maka da naira tayi kuka. Wani irin ɗunƙulallen gini ne mai matuƙar armashi da ƙayatarwa. Ga wasu irin korayen ciyayi da furanni masu azabar ƙamshi da sanyaya gida da ƙawatashi da sukaima ko'ina ado. Ga jibga-jibgan motoci jere a cikin rumfuna kusan biyar a tsare acan nesa sosai, wasu ma rufe suke da tempol. Sosai ma'aikata ne ke kai-kawo, dan dole irin wannan gidan yana da masu kulawa ta kowanne fanni. Driver ne ya fara fita a motar ya buɗema Alaja. Kafin ita kuma tai min nunin na fito. Jikina a matuƙar sanyaye na fito ina mai bin katafaren harabar gidan da kallo. Brain ɗina gaba ɗaya ta gama kwancewa, dan tunanina ya rabu biyu ne tsakanin haɗuwar gidan da sunan dana gani rubuce ɓaro-ɓaro matsayin mamallakin gidan.       “Oya muje”.    Furicin Alaja ya katse min tunani. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki na fara takawa a hankali ina bin bayansu. Drivern ta ne yay saurin buɗe dankareriyar ƙofar mai wani irin zubin ƙyau da ɗaukar hankali da duk mai kallo zai iya tabbatar da an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi. Alaja ce ta fara shiga da sallama, yayinda ni kuma ke biye da ita kamar bindi. Sai sauran abokan tafiyarmu biye damu. Sai dai babu sauran yaran da aka ɗakkomu tare da alama an barsu a mota. A haɗaɗɗen falo dake matsayin main perlor muka fara ratsawa. Komai na cikinsa a tsaftace yake ga ƙamshi da sanyin ac kamar ka ɓingire barci. Sai dai babu kowa a cikinsa ko television ma a kashe yake. Bamu tsaya anan ba, mun shiga falo na biyu daya kasance katafaren gaske. Haɗuwar falon ba'a magana. Dan ya ƙawatu da ƙawatuwa ta musamman. Komai sai ƙyalli da ɗaukar ido yake tamkar ba'a talauci a duniya. Shima dai ƙamshin ke tashi mai nutsuwa, sai ƙafar bene da suka zama mahaɗar sassan gidan guda uku. Gashi ƙaton gaske bana wasa ba, dan duk da set na kujeru kusan biyar da ke cikinsa group-group zama a iya kawo wasu set goma sha biyar duk ya ɗauka batare da wasu sun matsi wasu ba.       Anan kam akwai mutane. A hankali dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 1sitter da laptop a gabanta tana sarrafawa a group na set ɗin kujerun dake farkon shigowa ta ɗago fuskarta ƙawace da murmushi, laptop ɗin da tun shigowarmu ta dakata da sarrafawa ta ture gefe, cikin ƙasaitacciyar muryarta ta furta, “Idanu na ne kemin gizo ko kuwa mafarki nakeyi? Da ganin Auta”.       Dariya Alajah tayi tare da nufarta ta rungumeta. Dai-dai nan wasu ƙyawawan ƴammata uku dake can ɗayan rukunin kujerun suka taso suma a guje suna faɗin, “Oyoyo Aunty Mamah. Juyowa tai ta rungumesu suma cike da kulawa da farin ciki. Sai da suka gama murnarsu suka nutsu kafin su maida hankalinsu garemu. Ni suka fara zubama idanu, kafin su maida ga sauran hajiyoyin fuskokinsu a washe da murmushi suna musu barka da zuwa cikin nuna girmamawa. Ni dai ina daga tsaye gefe dan haka kawai naji shakkar ƙarasawa garesu har sai da Alajah tai kirana tare da nuna min na zauna. Inda ta nuna min ɗin nakai zaune ƙasan carpet. Kaina a ƙasa batare dana kallesu ba na shiga gaishesu. Hajiyarce kawai ta amsa, amma ƴammatan nan ko kallo ban ishesu ba. Musamman ma babbar ciki wani kallon tsana data wurgamin tun farko sai da najisa har a ƙasan raina. Dan haka nima sai banbi takansu ba...        Munyi zama na kusan mintuna talatin a wajen kafin hajiyoyin nan biyu da muke tare da su su miƙe alamar zasu wuce. Hajiya da Alajah ne sukai musu rakkiya. Yayinda ni kuma aka barni nan maƙure waje guda ƴammatan nan na bina da kallon banza. Kusan mintuna biyar sai gasu sun dawo. Basu zauna anan ba, sai umarni da suka bama ƴammatan cewar ai kiran Mama Bilki shugabar masu aikin gidan taje dani sashensu zasu nemeta. Hakan kuwa akayi, dan atake babbar cikin ƴammatan ta ɗaga telephone tai kira, cikin gadara da izza ta isar da saƙon Alajah da tuni sun haye upstairs ta ɗaya daga cikin ƙafar bene ukun data ƙawata makeken falon na alfarma. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsaho ba sai ga wadda nake ƙyautata zaton Mama Bilki tazo. Babbar mace ce sai dai baza'a kirata tsohuwa ba. Abin mamaki kuma jikinta fes kamar bamai aiki ba, amma tabbas zata iya haihuwar kamata. Cikin fara'a da kulawa ta bani umarnin tasowa na bita. Nima sai na miƙe jiki a sanyaye nabi bayanta ina mai sakin ajiyar zuciya. Dan dama zama a tsakiyar shegun yammatan duk ya gundireni. Ina jin wata a cikinsu na sakin tsaki amma sai nan juyoba balle naga wacece.          Tafiya mukai mai tsaho sosai data bani mamaki dan kamar bama a cikin gidan muke ba. Kasancewar bata hanyar da muka shigo dasu Alaja bane yasa ban iya na fahimci komai ba. Sai ma sake zama wata baƙauya nayi dan kalle-kalle nakeyi iya iyawata. Sosai nake sake girmama girma da ƙudira ta UBANGIJI. Dan wannan gida sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba saboda ƙawatuwa da ɓannar dukiya da akai wajen saka masa kayan alatu. Ban sake tabbatar da gidan ƙaton gaske bane sai da muka ɓullo wata hanya data fiddomu wajen ginin tanan ma. Ashe ta gaban girmansa ba komai bane. Ta can baya da ginin apartment na masu aiki yake ɓangaren maza daban na mata daban shine ainahin ƙaton gaske. Dan shi ta can gefe akwai ƙaton garden da ko ba'a faɗa maka ba kasan shi ɗin ne. Sannan daga hannun dama akwai wani ƙaton wajen wasanni na yara da manya. Akwai wajen ƙwallo, wajen..... Kai dama wasu daban da ban gama tantancewa ba dan iya abinda idona ya hango kawai nake sanar miki Bily. Shi kansa sashen masu aikin da muka shiga sai da notikan kaina suka nema kwancewa. Dan tamkar ba na masu aiki ba. Komai fes akwai kuma kayan ƙawar suma duk da basu kai na sashen masu gidan ba ko kusa ko kaɗan. Amma dai duk mai hankali ya kalla yasan an girmamasu an mutuntasu. A tare ƴammata kusan takwas da muka samu a falon zaune suna kallo suka zuba min ido fuskokin wasunsu da fara'a, wasu ko kallo ɗaya sukai min suka ɗauke kawunansu. Sannu wanda suka nuna kulawar su suka shiga yi min, hakan yasa nima na amsa musu da kulawa tare da gaishesu duk da sukansu bazasu wuce sa'anni na ba har ma da waɗan da zan iya girma..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_ __________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ ......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta nuna wata dake gab da inda nake tana faɗin, “Sayyada kawo ma baƙuwarmu ruwa da abinci ko”. Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana miƙewa. Wata ƙofa dake a falon can inda ƙaton dining table yake na katako ta nufa, mintina ƙalilan kuwa sai gata da tire madaidaici a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da faɗin, “Sister ga abinci ko.”          “Nagode”.        Na faɗa a hankali nima ina murmushin yaƙe. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa murya nace, “Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna”.      Cike da fara'a tace min, “Lah ai babu komai ɗiyata. Kinga A'i tashi ki rakata ɗakinku sai tayi a can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. Ɗan tsuke fuska wadda aka kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta miƙe. Nima miƙewar nayi nabi bayanta ɗan lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ɗauke da ƙofifin ɗakuna kusan goma. Hannun dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ɗaki na biyu a hannun dama ta nuna min ƙofar bayi. “Ki shiga nan”. Daga haka ta juya ta fita. Komai bance da ita ba nima, face cikowa da idona yayi da ƙwalla. Ji nake komai ya ƙwace min, gaba ɗaya nama gagara hasashe balle tunanin komai akan wannan rayuwa dana jefa kaina. Dan a yanzu kaina nake zargi ba kowa ba. Ina ma kaina kaico akan bin hajiyar nan da nayi, sai naji inama tashar na nufa koda roƙo na samu kuɗin motar zuwa Kano. To amma bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ni bama wannan ne tashin hankalina ba. Son sanin wanene mai wannan gidan shine tashin hankalina. Karfa ya zamto ANYI GUDUN GARA ne AN FAƊA GIDAN ZAGO. Kai amma da nayima kaina kaico. In sha ALLAHU ma bazai kasance hakan ba.       Bayan na idar da salla na jima zaune a wajen shiru, dan har sai da A'i ya biyo bayana sannan na miƙe na bita. Kamar yanda na barsu haka na samesu. Sai dai an sake samun ƙarin mutum uku suma duk manyan mata dan da kaɗan Mama Balki zata iya girmarsu. Gaishesu nayi a ladabce, duk suka amsa min babu yabo babu fallasa. Na ɗan ji jikina yay sanyi, sai dai ban bari al'amarin nasu yayi tasiri a raina ba na fara cin abincina. Ka ɗan na tsakura nace na ƙoshi, Mama Balki tai murmushi da faɗin, “Ƴar nan baƙunta zakiyi mana?”.       Murmushi kawai nayi kaina a ƙasa batare da nace komai ba. Itama sai tayi ƴar dariya da cigaba da faɗin, “To ai shikenan. Bara nayi wani karanbani duk da Aunty Mama bata sanar min ke wacece ba ko matsayinki. Amma dai duk wanda aka kawo nan mun san namu ne ai. Minene sunanki?“.        Shiru nayi jimmm kamar bazance komai ba. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta Kandala”.     Su dukansu sai da naga alamar shock a fuskokinsu game da jin sunan nawa. Amma ganin yanda na fiske abuna ya sasu basarwa. Wasu a cikinsu suka furta Masha ALLAH. Yayinda wasu suke taɓe bakuna a yamutse. Mama Balki ce ta katse yanayin da nuna kanta. “Ni sunana Balkisu, amma suna kirana da Mama Balki kamar yanda kika ji. Ni ce shugabar duk wani ma'aikacin wannan gida musamman mata. Mijina kuma shugaban ma'aikata maza. Wannan kuma ta kusa dake Sayyada, sai Afrah, sai Sumayya, sai A'i, sai Asiya, sai Bintu, sai Mansura, sai Kairat, sai Bahijja, sai Sadiya suna kiranta Aunty Sadiy, itama tana da miji. Ta nuna ɗaya daga cikin manyan matan nan uku da suka shigo daga baya. Sai Aunty Kubrah itama tana da miji, sai aunty Falilah. Dukanmu muna aiki ne a wannan gida. Kowa kuma da fannin sa. Wasu gyara, wasu wanke-wanke. Kowa kuma da sashen da yakema aiki dan komai a ƙa'idarsa yake. Idan har kema tamuce zamuji fannin da aka kawoki ki kasance”.        Sosai ƙirjina ke wani kalar luguden daka tunda ta fara. Sai dai inata dauriyar danne yanayin nawa. A rain kuwa komai ya dagule min, babu abinda nake ambato sai kalmar (Na shiga uku. Yanzu kuma boyi-boyi na koma kenan? Mike shirin faruwa dani ne haka?). Bani da mai bani amsa, dan haka na maida hankalina ga Mama Balki dake cigaba da min bayani. Sai dai sam bana fahimta har tayi ta gama. Mun cigaba da zama har akai kiran sallar la'asar. Sai a sannan dukanmu muka miƙe. Ɗakin dai ɗazun naje tare da wadda ta rakani A'i sai abokiyar kwananta Bahijja. Bahijjar akwai fara'a, dan sai jana take jikinta cike da kulawa. Muna idar da salla ta kwashe tarkacen kaya da suka jibge a ɗayan gadon ɗakin dan uku ne ta ce, “Nan shine gadonki Kandala”. Yanda tayi maganar da murmushi ya sani nima mayar mata da murtani ina jinjina kai, kafin na ɗora da mata godiya. A'i dai na jinmu amma tai kamar bata ɗakin. Bahijja dake ƙoƙarin saka uniform ta sake kallona da faɗin, “Kiyi kwanciyarki ki huta mu zamu je can sashen yin aikin yamma. Idan kuma zakiyi kallone to muje falo”.       Da sauri na girgiza mata kaina. Sai kuma na murmusa da faɗin, “A'a bari na kwanta ɗin, ai bazaku jimaba ko?”.      Tsaki akaja kafin ta bamu amsa, atare muka kalla A'i dake ƙoƙarin ficewa alamar itace tayi tsakin. Murmushi Bahijja tayi da maido idonta gareni. “Karki damu da ita haka take kamar mai aljanu. Nima farkon zuwana haka ta dinga min kamar mai jin haushin mutane. Amma bari kiga nan da kwana biyu zata fara kulaki. A'in ce kamar mai aljanu wlhy”.          Murmushi nayi yayinda ita kuma ta ƙare maganar da sakin ƙaramar dariya. Daga haka ta cigaba da faɗin, “Ya danganta da yanayin aikin da zamu tarar. Musamman ma ni, dan iyayen gidan nawa mutuncinsu ragaggene bare ma idan akace miki Aunty Azizat. Tana abu kamar mai jin warin mutane. Bari naje dan in nayi latti zan sha maruka gashi ƙa'idarta ne iyanzu take wankan yamma”.        Kasa cewa komai nayi, sai kaina dana ɗaga mata kawai sunan wadda ta kira na min kai-kawo a rai batare dana san dalili ba. Bayan ficewarta na saki nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma na miƙe cikin kasalar jiki zuwa gadon da tace nawa dake a farkon shigowa. Na can ƙarshen bango na A'i, na tsakkiya nata. Sai ni a bangon ƙarshe na farkon shigowa.....       ❤️★★★❤️    Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake haɗawa ba. Dan washe gari uban aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi kuma gyaran gidan musamman falon tarar baƙi da Mom ta sakata ƙalƙalewa kamar za'a canja bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai Baby ce tayi baƙo. An kuma ce ta saka hijjab da niƙab takai masa abinci falon baƙi. Bata da yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ɗunbin mamaki ta fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ɗakinta. Bata tsaya a tsakar ɗakin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara kwasar dariya harda hawaye. “Kambu taƙashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi sanƙameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ɗi jan, daga dai ganin wannan kasan sai dai a so shi dan kuɗi duk da dai ƙyaƙyƙyawa ne a fuska.” kiran da Mom ke ƙwala mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta.       Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da alƙawarin kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma  su Bibaa da Auta da Nabil yay musu ƙyautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta yaɓe ta cigaba da aikinta. Daga haka bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ƙyautar kuɗi yay ma yaran gidanta itama wai naira miliyan ɗaya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje gidanta kuma ya bata waya mai ƙyau ƴar dubu ɗari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai Halime ta jinjina kwaɗayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa. Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi suka ƙarasa tattaunawa ba. WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira waƙarta cikin zazzaƙar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. Ɗan jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai kuma ta cigaba da shararta amma ta daina waƙar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ƙarewa a gidanmu zan tafi ɗakina. A gidan mijina zan rayu zaman kaɗaici ya kusa yankewa).       Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin daɗin daina raira waƙar tata Abba ya ƙarasa fitowa daga jikin ƙofar ɗakin barcinsa da yake maƙale.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ __________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Ƙamshin turarensa mai armashi daya bigi hancin Halime ya sata ɗagowa a zabure. Hakan yay dai-dai da isowar Abba inda take. Aiko suka kusa cin karo. Tsalle tayi baya jikinta na rawa. Tako tafi zata zube ƙasa yay saurin riƙota. Rawar jikinta ce ta ƙaru sosai sai faman zazzare idanu take tamkar bazazzage a hannun kanawa (😂😜lol).         “Please kinga calm down nutsu”. Abba ya faɗa da sauri ganin yanda duk ta gigice. Kasa nutsuwar tai, sai ma mutsu-mutsun son ƙwacewa da take kawai daga hannunsa. Sakinta yay, aiko ta kwashi tsintsiyarta ta zura da gudu hanyar kitchen dan nan ne kawai takema kallon wajen ɓuya. Murmushi Abba ya saki mai haɗe da ƙaramar dariya yana girgiza kansa da jinjina wawtarta. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai kauri zuciyarsa na sake tabbatar masa da yanayin dake son hawa kansa batare daya shirya ba. Dan duk yanda yake son ƙaryata zuciyar tasa hakan ya gagara. Dole ya haƙura a yau tare da tabbatar da da gaske fa son yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba yake. Lallai yasan shima ya taro match babba, mai aikin gidansa fa. Randa Jalilah tasan wannan sirrin nasa sai abinda ALLAH yayi ai. Maybe yankan raguna zata musu shi da yarinyar nan....        📯📯📯📯📯        Zancen Bahijja ya tabbata. Dan kuwa bata dawo ba sai bayan sallar magrib. Haka ta shigo idanunta balo-balo alamar taci kuka. A take zuciyata ta motsa. Sai dai bance da ita komai ba ganin itama ta dake tana min murmushi. Dan cike da kulawa ta shiga faɗin, “Lah baki je falo ba bayan gasu A'i can duk sun dawo su tun ɗazun. Su Mama Balki ne kawai su sai anjima saboda girkin masu gidan kowa da abinda yake so. Balle ma Uncle Boss yana gida aikin yafi tsamari kodan gayyar yaransa”.      Dariya sunan data faɗa ya bani, wai Uncle Boss. Amma sai haka kawai naji gabana ya faɗi, cikin ƴar in ina nace, “Waye Uncle Boss kuma?”.        Numfashi ta sauke mai nauyin gaske. Sai kuma tai murmushi da faɗin, “Uncle boss shine gidan dama ƙarfin ikon kidan baki ɗaya. Shine babban ɗa a gidan kuma. Bari dai kada na shagala da yawa banyi sallar magriba ba, har an kusa isha'i. Kuma Malam da anyi isha'i idan ka makara zuwa makarantar dare duka yake yi”.     Da kallo kawai na bita dan babu abinda na fahimta a zancen nata. Sai kawai na cigaba da lazimina harta fito ta kabbara salla ban sake cewa komai ba. Tana idarwa ana kiran sallar isha'i. Dan haka muka tashi a tare muka kawota. Muna idarwa ta miƙe ɗauke da Alkur'ani tace na taso muje wajen karatu. Ban musa mata ba na tashi na bita kuwa. Mun samu duk kusan ƴammatan nan sa'anninta suma sun fito, a tare muka rankaya waje. Can muka nufa cikin wajen wasannin nan dake ƙwanyar da hasken lantarki tamkar rana. Hakama tsakar gidan yake tako ina. Ga hasken ya sake ƙawata gidan tamkar ba'a duniya ake ba. Mun samu malam har ya iso, dan haka babu wani ɓata lokaci muka zazzauna a ƙatuwar dardumar dake shimfiɗe a wajen. Yayinda shi kuma yake zaune a saman kujera abinsa. Kamilun mutum dattijo. Dan shekarunsa da gashin fuskarsa zuwa kansa dake fari fat ya isa tabbatar maka da shi ɗin ba yaro bane ba. Mun gaishesa a tare, ya amsa mana da kulawa kafin a fara karatu babu ɓata lokaci dan kowa ya riga yazo. Naji daɗin karatun, duk da kuwa nayi sauka tuni. Kusan awarmu ɗaya da rabi dan sai takwas da kusan arba'in muka tashi. Sai dai yanata kallona amma baiyi magana ba balle tambayar dalilin shigowar baƙuwar fuska ajin karatunsa. Can sashen muka koma, sai dai wasu basu zauna ba suka shiga canja uniform wai zasu koma can sashen su ƙarasa ayyukansu, ciki kuwa harda Bahijja da tafi kowa rawar jikin komawa. Sun bani matuƙar tausayi, amma dai bance komai ba dan bani da abin cewar. Shiru babu wanda ya dawo a cikinsu ni dai har na fara hamma saboda sabon barcin wuri da nayi tun fil azal. Mama Balki data rigasu dawowace tace naje na kwanta. Babu musu na miƙe na wuce ɗaki kuwa, dan ni kaina nasan ina buƙatar barcin, amma ba lallai tunanin dake danƙare a zuciyata ya barni yinsa ba. Koma dai yaya ne zanyi yaƙi da zuciyata wajen ganin na yisa kodan na samu nutsuwar fuskantar abinda ke gabana. Dan Alhmdllh, ɗan zuwa islamiyyar nan ta ɗazun da nayi sai nake jin kamar yanayin da nake jin kaina sanda nake a gidan Hajiya ya fara sakina...        A hankali na buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi irin na mai barci. Akan Bahijja na sauke su. Da mamaki nake kallonta. Ta sakar min murmushi da nuna min agogon ɗakin. Sosai na waro idanun waje mamaki fal raina na ganin asubahi. Kenan nayi barci sosai yau. Tab ɗi, abinda na daɗe banyi ba a rayuwata. Dan ko kwanciya asibitin da nayi ni shaida ce akan allurar da suke min ke bugar da ni bawai normal barcina ba.     Bayan mun idar da sallar asuba muka gaisa da Bahijja. Itama A'i dake faman ɗauke min kai gaisheta nayi. A mamakina sai naga ta amsa da sauri har ma abin nata ya bani dariya. Amma sai na danne banyi ba sai dai guntun murmushi kawai. Alkur'ani na ɗauka na fara karatu, yayinda A'i ta shiga wanka, ita kuma Bahijja ta fara ƙoƙarin gyara mana gadajenmu. Ina nan zaune harta kammala tace na koma saman gado zatai shara. Hakan kuwa nayi, tana kammala shara A'i ta fito, a gurguje ta ƙarasa morping itama ta shiga wanka. Bata jima ba kamar A'i ta fito. Su dukansu shiri sukayi a cikin Uniform ɗinsu wankakku harda guga dan na fahimci suna dasu ne da yawa ba ɗaya bane. Suna kammalawa harda fesa turare, na fahimci hakan kamar yana cikin dokar aikinsu a gidan zama cikin tsaftar jiki. Fuskar Bahijja da murmushi ta kalleni. “Sis.. mu zamu wuce aiki. Ki kwanta ki hutama ranki kafin a kawo break fast. Tunda kinga har yanzu ba'a sanar da aikin da zakiyi ba, ALLAH dai yasa ba tafiya dake aunty Mama zatayi ba”.        “Waye aunty Mama?”. Na tambayeta cikin sanyin murya. Kai tsaye ta bani amsa da, “Itace wadda kukazo tare. Ita ba'a Nigeria take zaune ba. Yanzu ma nasan bikin birthday ɗin Hajiya Babba ne ya kawota. Dan ana yinsa ne tamkar bikin aure duk shekara. Ana gamawa kuma zata koma ita da nan sai babbar salla”.     Kai na jinjina mata cikin nuna gamsuwa. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya ganin itama ta nufi hanyar fita dan tuni A'i ta fice dama...      *_10:30am_*     Ina kwance a ɗaki da littafi a hannuna ina dubawa na Hadith nasu Bahijja ɗaya daga cikin ƴammatan jiya da ban gama tantancewa ba duk da an faɗa min sunansu ta shigo tai kira na. Tare muka dawo falon. Na rissina cikin girmamawa na gaida Mama Balki da muka samu ita kaɗai zaune. Ta amsa min da kulawa tana murmushi. Sai kuma ta nuna min dining table tana faɗin, “Kije kiyi break fast gashi can kar ya huce. Dan Ban sani ba ko'a buƙaci ganinki yanzu da safe. Ina fatan dai kinyi wanka?”.       Murmushi nayi mata, dan haka kawai naji ƙaunar matar na shigata. Kaina a ƙasa na amsa mata da, “Eh mama nayi wanka, kayane dai ban canja ba”.      “Karki damu da wannan. Nasan Hajiya Mama na sane da ke zata kawo kayanki in sha ALLAHU. Yanzu dai ki karya sai ki dawo nan ki zauna kisha iska ni zan koma bakin aiki kada yaran suyi shirme”.     “Na gode mama ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”.          “Amin ya rabbi ɗiyata ALLAH yayi miki albarka kinji”.     Yanda ta faɗa ɗin ya bani tabbacin taji daɗin girmamawar da nake bata. Zama nayi naci abincina, duk da dai bawani na kirki bane naji yamun daɗi. Bayan na kammala falon na dawo kamar yanda Mama ta umarceni. Ina zama sai ga Mama ta dawo. Cike da kulawa ta ce, “Yauwa to taso ɗiyata, dama nace miki Aunty Mama zata iya buƙatar ganinki”. Da girmamawa na amsa mata da to ina miƙewa nabi bayanta. Sosai nake ƙara tsarkake sunan UBANGIJI daya bama waɗanda suka tsara ginin wannan gida fiƙrah da fasahar yinsa tamkar an ɗakko an dasa ne ba hannu yayisa ba. Ashe jiya kallon tsoro nayi masa. Lallai na yarda masu arziƙi na inda suke. Ashe su Mom iyayen alfahari da kuɗin Abba basu wuce ƴan aiki ba a wani wajen. Ashe duk kuɗin da take kallon iyayen Mansoor suna da shi ba komai bane ba. Zuciyata tai  wata irin jijjiga dalilin tuna masoyina Mansoor. A take naji hawaye sun cika min ido. Amma ban bari sun zubo ba na haɗiyesu.         Mayataccen ƙamshi da sanyin ac ke fara maka sallama tamkar ba safiya ba. Ga wani irin shiru da gidan ya bada tamkar babu wani rai mai motsi a cikinsa. Wata irin ajiyar zuciya ce ta kufce min batare da nasan dalilin hakan ba. A cikin takun nan nawa na nutsuwa da rashin hayaniya na cigaba da bin bayan Mama. (Ya Al-malik) na furta a zuciyata lokacin da muke gama haurowa upstairs ɗin tsakkiya. Ashe saman ma wasu shegun faluka ne da sukafi na ƙasan ƙawatuwa da barazana tamkar ba duniya za'a mutu a barsu ba. Rasama ina zan nutsu na kalla nayi nikam. Tako ina na gama diriricewa. Sai dai a zahiri baka isa tabbatar da yanayin nawa ba dan na shanye komai a raina ni da zuciyata mukeya bidirinmu kawai a baɗini.......✍️ _😂Ku cigaba da haƙuri dai, ni kaɗai nasan yanayin da nake ciki😞._     _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ _____________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _____________ ......Daga ni har Mama Balki ƙasa muka zube gaban Alaja dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana daƙilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ɗago ba ta amsa min. Kusan mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ɗago tana cire eyeglasses ɗin idonta da bana raba ɗayan biyu na ƙara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ɗan saki murmushi. “Ƴammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne da yawa.”         “Ba komai Mama”.     Na faɗa kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab.     “Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya gwadata a ɗinka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya buƙata kuma sai ki shirya zuwa anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi”.          “To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ƙara nisan kwana da rayuwa mai albarka”.     A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa wani irin abune mai masifar nauyi ke neman riƙe min ƙirji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita kalmar “Miji”. (Kai ina ai bazan taɓa zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda)..         “K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!”. Muryar dana tabbata naji irinta a jiya ta faɗa cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ƙarshe. Ganin yanda Mama Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta furta “ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan itace ta buƙaci ganinmu”.        Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. “K kuma uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!”. Ta sake faɗa a fusace tana wani ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi  a shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma tsareta nai da idanu ina ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa....       Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu tsammani. A take ta rashin jin ya yunƙuro, bamma san lokacin dana ɗaga nawa hannun ba na sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma. Daga gani kasan akwai ƙarin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ɗaura hannuwa duka a saman kai bakinta buɗe. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar banga komai ba na raɓa zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar tsohuwar dodanniya ta damƙo min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an shaƙureni tare da jawoni baya. Tabbas da banyi azamar damƙe hijjab ɗin ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai hanata kaini ƙasa a wajen. Idan kuwa na faɗi zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa rayuwata. Gaba nayi gaba ɗaya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an hankaɗoni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan gaɓar sai na kai ƙasan mayen marbles ɗin nan mai tsananin sheƙi da ɗaukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan haka na runtse idanuna gaba ɗaya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki ɗayana......                 ★★★★     Cikin mintuna ƙalilan Halime ta dawo ɗauke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ɗakinta tasan ta ƙetare umarninta. A hankali ta dire tray ɗin a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta gefen ido tamkar zai cinyeta. Ƙoƙari barin wajen take yi tamkar mai raɗa ya furta, “Baza'a zuba min ba?”.       Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama Abba abincin. Ta kammala tana ƙoƙarin barin wajen ya katseta da faɗin, “Uhhm Kinga zo mana”. Nan ma ƙiri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa. Amma sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake faɗuwa. Tai masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. Ƙyaleta yay, cikin gyara yanayinsa ya ce, “Minene sunanki?”. Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama. Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, “Halime”.      “Halimatussa'adiyya kenan?”.    “Eh ta faɗa a hankali”. “Ina ne garinku?”. “Ƴan tumaki”. Ta bashi amsa kai tsaye.       “Ƴan tumaki?”. Ya maimaita da ɗan waro idanu a kanta a tunaninsa shaƙiyanci ne. Amma sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa haƙuri yayi sai da ya furta “A wane state ne?”. Girgiza masa kai tayi da faɗin, “Katsina ne. Amma dai muna kusa da Musawa”. Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ɗin dai da gaske. Humm mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata jiha. Cigaba yay da faɗin, “Miyasa kike aikatau?”.       Idanunta ne suka ciko da ƙwalla. cikin rawar murya ta ce, “Inna ce tace Baba ya turani na samo kuɗin kayan ɗakin aurena”.        “Ita Innar mamanki ce?”.   “A'a gwaggona ta rasu tun ina ƙarama. Matar Babana ce, amma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta riƙemu ni da ƙanina. Sai dai kuma ta tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma”.    Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar walƙiya hoton Maman su Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da faɗin, “ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun kuɗin kayan ɗaki?”.        Ƙasa ta ƙara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in ina ta ce, “Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ɗan shege ko zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren”.       Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ƙyar ya iya furta, ”Wacece ita Lami ɗin?”.     “Ƙanwata ce ita ta haifeta da su Lailah”. Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta. Shima sai ya miƙe dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ɗaki. Shirin fita yayi zuciyarsa na masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime ba.... Duk yanda Abba ke son yaƙar zuciyarsa game da abinda take ƙwaɗaita masa hakan ya gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ƙarfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro. Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ɗan nutsuwa a waje guda. Yayinda shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime baya gani saboda yanda take jin tsoron saɓa umarninta. A haka da ƙyar akai kwana huɗu. A daren cikar na biyar ya gagara haƙuri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da yaga ya ƙulu sannan ya bashi haƙuri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki....              ★★★       Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin na faɗa kan abu mai taushi saɓanin inda na gama sadaƙarwa zan faɗi. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ƙanƙame abinda na faɗawar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa ƙitjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmiƙewa. Gabana ya sake faɗuwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ɗayan numfashina ne ya ɗauke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya taban mamaki. Sake ƙanƙame abinda na faɗawar dai na sake yi. Wani irin jifff!! Ƙirjina ya sake bugawa a karo na biyu jin tabbacin mutum ne, mutum ɗin kuma daga ji ba jikin mace bane, sannan ƙamshin dana shaƙa na neman jirkice min tunani gaba ɗaya. Ga tsitt ɗin da wajen ya ɗauka lokaci ɗaya tamkar an tsaida numfashin kowa da komai na gidan. Sassauta riƙon da naima koma minene na fara yi, sai kuma na shiga ɗago kaina a hankali ina ƙoƙarin buɗe idanuna. Akan farin riga armless ta sport wear fara tas na fara saukewa. Sai ƙaton damtsen hannu dake a murɗe sosai fari mai ɗan duhu kaɗan dan fatar batai irin tas ɗin nan na mahaukacin fari ba. (Jikin namiji) zuciyata ta ayyana min, dai-dai da bugar hancina da ƙamshin turarensa ya sake yi. Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na ɗago gaba ɗayana na sauke idanuna akan fuskarsa.........✍️ _🥺🥺Hukumar tawada da alƙalami tace a tafi yajin aiki.🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Cak numfashina ya tsaya, illahirin jikina ya saki gaba ɗaya. Da ga ni har shi muka zubama juna ido. Yamutsawa kaina ya farayi saboda wani sinadari mai ƙarfi dake fitowa daga cikin cat ayes ɗinsa yana shiga cikin nawa. Wani irin kallo yake min mai kama da gargaɗi koma tsanace ban sani ba. Dan duk yanda naso dakewa hakan ya gagara. Tuni naji wani irin kwarjininsa ya gama mamayeni da cikani tamkar mu kaɗaine a wani matsatsen lungu. Hatta da iska ma ta fara min wuyar shaƙa neman komawa fisgar numfashi nake yi. Wani matsiyacin kallo daya dalla min tare da ƙoƙari janye jikinsa daga nawa ya sani tafiya gaba ɗayana baya zan faɗi. Bamma san na fasa ƙara ba da komawa gaba ɗaya jikin nashi na ƙanƙamesa tamkar zan huda shi na shige ciki...         Kusan kowa dake a wajen sai da ya sake waro idanu. Yayinda tuƙuƙin baƙin ciki da kishi mai tsanani ya gama mamaye zuciya da ruhin Azizat. A yanda take jin bawan ALLAHn nan a ranta ko macen sauro ta tsani ta taɓa mata shi, ai tuni idanunta sun sake rufewa. Batama san lokacin data isa gabansu ba. “Wlhy sai na kasheki ƴar iska. Bayan maita ma harda bin mazan mutane”. ta faɗa cikin ihu mai ƙaraji tana damƙo hannun Samraah da ƙoƙarin janta baya daga jikin Maash. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kawai ta fashe da kuka tare da sakar min hannun tana ƙoƙarin kaimin mari. Nima tamkar wadda aka farkar a barci dai-dai nan na dawowa a hayyacina, Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na sakesa gaba ɗaya tare da turashi. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar wanda ba'ai komai ba ma. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin ya taɓa sanin mai kama dani a rayuwarsa. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga ƙololuwar baƙin ciki, ruɗani da mamakin makirci da mugun halin mutumin nan, kenan da gaske shi MAASH ɗin ake nufi da sunan gidan nan?. Tayaya ma to hakan ta kasance?, farkon labarin a kano, cigabansa a Abuja, ƙarashensa a Lagos. Duka a ƙarƙashin ikonsa, kenan da gaske yayi winning kamar yanda yake iƙirari da cika bakin shi ba'a game da shi baiyi winning ba. Kai impossible...       Mugun zagin da Azizat ta lailayo min da sake yo kaina ya maidoni a hayyacina, raina a dugunzume na janye idanuna a kansa na dawo da shi gareta, dan wlhy tana sake taɓani duk haushi da takaicin mugun nan saina juyesu a kanta yanzun nan. Tana gab da kai hannunta jikina aka kira sunanta da ɗan faɗa-faɗa. “Azizat minene haka wai?!”. Mu dukanmu kalon Aunty Mama da tayi maganar mukayi, yayinda itama ta dakata tana hararata da famar huci sai kace wata kububuwa. Cikin sake bada umarni daga inda take tsaye ta dubi Mama Balki. “Kuje inda na turaku”.        “Godiya muke ranki ya daɗe, ALLAH ya ƙara girma”. Mama Balki ta faɗa tana risinawa tare da kama hannuna. Tamkar wadda aka zarema illahirin lakar jiki na shiga binta zuciyata na wata kalar suya da raɗaɗi mai zafi. Yayinda idanuna ya kasa daina kallonsa, nama rasa wana kalar tunani kuma ya dace nayi. Muna gab da fita muka haɗa ido, wani irin lumshe nasa yay da yamutse fuska ya motsa lips ɗinsa a hankali, (First Game) sai kuma ya cije gefen lips ɗin da wani salo ya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garemu.       Da ƙarfi na rumtse idanuna dake cikowa da ƙwalla. Cikin ɓacin rai na shiga ƙoƙarin son fisge hannuna daga na Mama Balki. Dan bazan iya haƙuri ba sai na maida masa murtani. Kai yau ma duk abinda za'ayi sai dai ayi wlhy. Sake damƙe min hannu Mama Balki tayi tare da jawoni gaba ɗaya daga cikin falon muka fito cikin main falo, sai da muka fito anan ma gaba ɗaya wajen compaund sannan. Cikin lallashi da ɗan faɗa ta furta, “Ya isa mana. Ki ƙyaleta. Banda abinki ina ke ina faɗa da ƴar masu gida. Kin san kuwa fitinar Azizat musamman akan bawan ALLAHn nan. Zuciya ba taki bace ba ɗiyata, anan a ƙarƙashinsu muke dole muyi haƙuri da koma mi zamu gani. Kima godema ALLAH Alhaji ƙarami yazo wajen da wlhy abinda zai faru ALLAH kaɗai ya sanshi. A hakan ma ALLAH ya taƙaita duk barci jama'ar gidan suke. Ita kuma Aunty Mama tana da sauƙi a cikinsu da ko gidan nan bazaki sake kwana ba. Kema dai na lura akwai ƙarfin hali, ki daure ki sauke wannan zuciyar taki kada ki sake kwatanta abinda kikayi yau”.        Zantukan Mama Balki sake ƙona min rai suke. Dan haka na sakar mata kuka kawai tare da faɗawa a jikinta na ƙanƙameta. Itama sai ta riƙeni hannu bibbiyu tana lallashi na.....      Su Samraah na gama ficewa a falon Azizat tayo kansa. “Yaya Please kace afitar mana da ita a gida. ALLAH yarinyar nan mayya ce. Tun jiya da aka shigo da ita gidan nan naji na tsaneta, jinake kamar ma na kashe banza. Dan bazan taɓa yafe mata rungumar da tayi maka b.....”       Ko kallon inda take baiyi ba, sai ma motsa lips ɗinsa da yay a hankali cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Good Morning Aunt” yay wucewarsa. Wani irin tsayawa tayi cak jikinta na tsuma. Duk da ba yau ne farau ɗin hakan ba a tsakaninsu sai take jin na yau ɗin ya mata zafi. Da kallo ta bisa idanunta nayin narai-narai alamar gab take da sakin kuka. Murmushi Aunty Mama tayi da ɗan girgiza kanta tana binsa da kallo. Har sai da ya ɓacema ganinsu ta janye idanun, ganin Azizat ta zabura zata bisa ta sakko ta kama hannunta batare da tace komai ba ta jata suka koma saman dan tasan bin nasa bazai haifar da ɗa mai ido ba. Dama ga wata wutar dake neman tasowa akan matsalarsun....            ★★★ Cike da nishaɗi Abba ya koma gida. Sai dai me, yana shiga ya samu Mom na jibgar Halime har Bibaa na tayata. Yayinda Baby ke kwance a kujera wanwar alamar tasha kayan nata. Tuni yay wata irin zabura batare daya sani ba ya hankaɗesu su duka. Sannan ya ɗauke fuskar Bibaa da mari. “Kinci gidanku Habiba. Dan uwarki wannan ɗin sa'arki ce?”.      Kafin Habiba dake kuka ta bada amsa Mom data sake shiga cikin matsanancin ɓacin rai ta hayayyaƙo masa. “Mitai maka zaka daketa. Akan ƴar aiki wulaƙantacciya da iyayenta ma suka sallama ma duniya saboda baƙin talauci”.       Wani irin ɓacin rai ne ya tasoma Abba. Cikin rufewar ido ya furta, “Jalilah! Halimatussa'adiyyar ce wulaƙantacciya?”.           “Kuturun ubancan! Imamu harma sunanta ka sani? Harda ƙara masa wani ƙaimi. To ko dai kana zagayowa ne ban sani ba ta zama karuwarka. No wander yanzu kullum sai ka dawo gida da rana. Idan ka zauna kuma kata waige-waige kenan...”       “You are vary stupid Jalilah! Ni kike dangantawa da fasiƙanci?”.     “Yo in ba fasiƙin ba minene kai? Taya akai kasan wannan tsinanniyar yariyar anan gidan ma? Bayan na mata gargaɗi kaima kuma nayi maka. To wlhy kuwa zaku mutu yau ku duka...” ta ƙare maganar da rarumo flower base tai kan Halime dake maƙure gefe tana kuka. Damƙota Abba yayi da masifar ƙarfi, aiko ta juyo gaba ɗayanta ta buga masa abin a kai. Lokaci ɗaya Bibaa da Halime da Baby da hayaniyarsu ta sakata buɗe ido suka ƙwalla wata irin masifaffiyar ƙara da duk maƙwaftansu sai da suka jiyo. Yayinda fuskar Abba ta gama wankewa da jini. A take ya faɗi wanwar ƙasa. Ai sai su Bibaa suka sake ƙwala wata ƙarar da tafi ta farko. Itama Mom ta yadda guntun flawer base ɗin daya rage a hannunta tayi wani uban tsalle gefe tana ware idanu. Halime kuwa tuni ta gigice tazura waje a guje.......        💦❤️💦❤️       Komai na daina ganewa. Komai ya tsaya min cak. Ba brain kawai ba, hatta zuciyata da gangar jikina komai dake taimaka musu ya tsaya cak. har muka baro inda Alajah ta sakamu zuwa anan cikin gidan bana iya gane komai. Bin kowa kawai nake da kallo tankar wadda ke a duniyar mafarki. Koda muka koma can sashen Mama Balki bata shiga ba. Tace na shige ciki ita zata koma kan aikinta. Shiru sashen babu kowa, hatta tv a kashe take. Ban zauna a falon ba na shige ciki, saman gadon dana kwana na kai zaune, cikin gushewar tunani na dafe kaina tare da fasa wata irin ƙara illahirin jikina na rawa har ta kaini da faɗowa ƙasa....         Da gudu Bahijja data shigo sashen domin shiga toilet ta ƙaraso ɗakin, dan da farko ma ita tsorata tayi, sai da tajiyo ihun kamar daga ɗakinsu ne sannan cikin ɗari-ɗari ta nufi can. Sosai ta waro idanu, sai kuma ta zabura kan Samraah tana faɗin, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!. Kandala! Kandala! Miya farune haka?...”       Ƙanƙameta Samraah tayi sosai tana cigaba da kuka mai tsuma rai da zuciya. Sai kawai itama Bahijjar ta sanya kuka. Dan yanzu su Sumayya ke bata labarin abinda ya faru tsakanin Samraah ɗin da Azizat. Sun kai kusan mintuna biyu a haka kafin su sassauta kukan nasu. Cikin lallashi Bahijja dake rungume da ita ta fara faɗin, “Kiyi haƙuri Kandala kinji. Haka take sam bata da mutunci. Bata ɗauki ɗan adam komai ba sai abin wulaƙantawarta. Sai kace itama ba cin arziƙi tazo yi gidan ba. Tunda ba gidan ubanta bane ba. Ai wlhy naji daɗin abinda Uncle Boss yay mata, azzaluma. Nima kullum sai ta mareni ga bautar gyara mata ɗaki da nake kamar jaka, hatta da pants ɗinta nike wankewa. Amma sam bata gani, komai akai mata ba'a iya ba, bayan ita ɗin ma babu abinda ta iya sai barcin tsiya da gantali. In sha ALLAHU Uncle Boss bazai aureta ba zamu gani”.         A hankali na ɗago ina kallon Bahijja, haka kawai kalamanta sukai wani irin tasiri a zuciyata. Har ban san sanda na furta kamar ya ba ƴar nan gidan bace Bahijja?”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_ 💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥 *_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327 *_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Hadin amarya budurwa ko zawara* *Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)* *Maijego package (virgin gain)* 📦 *Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji* *Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci* *Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa* *Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji* *Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa* *Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,* *Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327 *Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace* *Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327 *Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto* ============= .......Zama Bahijja ta gyara fuskarta cike da gulma. Sai kuma ta miƙe ta leƙa waje sannan ta dawo ta rufe ƙofar. Hannuna ta kama muka koma saman gadon A'i dake can ciki. Cikin sake sauke murya can ƙasa tace, “Eh mana ba ƴar gidan nan bace ba. Uncle Boss shi da ƙaninsa kawai aka haifa a gidan nan. Ita ɗin da ƙanwarta Hindu mahaifiyarsu yayar Baban su Uncle Boss ce. Ni na rasa gane musu, ko bata da mijine yanzu oho mata, dan nidai tunda nazo anan gidan nake ganinta zaune ita da ƴaƴan nata. Sai Ashna, ita kuma agola ce. Matar Baban Uncle Boss ta yanzu itace mahaifiyarta. Bata nan sunyi tafiya ne ita da Baban Uncle boss ɗin amma nasan yau zasu dawo. Itama wadda tazo dake Aunty Mama ƙanwar Baban Uncle Boss ce ba'a Nigeria take aure ba. Ƙanin baban dai da shima yake da nasa iyalan anan gidan basa nan sunje Niger biki suma yau zasu dawo yaransu uku. Suma duk basu da kirki musamman babbar su da suke takara da Azizat akan Uncle Boss dan itama sonshi take kamar zata mutu. Shiko ko kallo basu ishesa ba....”         “A'a, to shi ina mahaifiyar Boss ɗin ko ta rasu ne?”. Na faɗa cikin tare numfashinta. A take naga jikinta gaba ɗaya yayi sanyi, sai kuma idanunta suka ciko da ƙwalla. Cikin raunin murya irin ta tausayi ta ce, “Tana nan raye bata rasu ba. Amma bata da lafiya....”     Sagade nayi kawai ina kallonta. Sai kuma cikin ƙarfin hali na furta, “Tana asibiti kenan tana jiyya?”.       Nan ma idanunta ne suka sake cika da kwalla. Sai kuma ta girgiza kanta. “Tana a cikin gidan nan kulle a sashenta. Babu mai shiga inda take sai masu kula da ita, suma basa haɗa wata a gidan nan suke guduwa duk da ɗunbin kuɗin da ake biyansu na albashi, mun rasa miyasa basa zaman. Idan kinga masu gidan sun shiga su kuma to sai dai an ɗaureta ne ko an mata allurar barci mai ƙarfi”.            “Ɗaurewa kuma? Sai kace wata dabba?”.      Shiru tayi dan hawaye ne sosai ke ɓulɓulowa daga idanunta. Har tana jan ajiyar zuciya kamar zata shiɗe. Sosai hankalina ya sake tashi, sai dai ban iya cemata komai ba na dai riƙe mata hannu alamar lallashi. Kusan mintuna biyu ta haɗiye kukan da ƙyar. Sannan ta cigaba da faɗin, “Humm bazaki ganeba Aunty Kandala. Amma ni dai zuciyata na ayyana min abubuwa da yawa a gidan nan wlhy, sai dai bamu da wani ƙarfin iko ne shiyyasa kawai na zama cikin masu kallo. Mahaifiyar Uncle Boss tana da ciwon hauka ne, shiyyasa suka killaceta ba'a bari kowa ya shiga inda take sai masu kula da ita. Sai kuma likiticin dake dubata duk bayan sati biyu. Duk randa kikaga masu gidan sun shiga inda take to an ɗauretane, dan sunce duka take yi.....”        “Har su ƴaƴan nata?”.     Yanda nai maganar a ɗan tsawace yasa ta zabura. “I'm sorrry”. Nace mata dan na fahimci na fara rasa nutsuwata. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, alamar samun nutsuwa. “Ai Uncle Boss ne kawai. Shi ɗayan baya ƙasar, nima tunda nazo ban gansa ba sai a hoto kawai.....”      “Shi ɗin baya shiga kenan?!”.   “Yana shiga, sai dai ba koda yaushe ba. Saboda shigar tasa bata haifar da ɗa mai ido ne. Yau ma bakiga abu a gefen girarsa ba. Shekaran jiya ne daya shiga dubata bayan ya dawo ta jimasa wannan ciwon. Da ƙyar aka fiddosa a ɗakin ma”. Ta kare maganar tana hawaye. Cikin kukan ta cigaba da faɗin, “Wlhy yana bani tausayi aunty Kandala. Dan abubuwa da yawa idan yanayi zai tabbatar maka da yanda yake matuƙar son mahaifiyarsa. Itama kuma zakiji tana kuka duk dare tana kiran sunansa. Amma al'amarin nasu kamar wani abun sihiri basu isa haɗuwa a waje ɗaya ba kamar maƙiya. Wlhy da ace inada abinda zan taimaka masa koda da duk abinda na tara ne zanyi aunty Kandala. Ki duba fa kiga yanda ya inganta rayuwarmu a gidan nan tamkar ba ƴan aiki ba. Muhalli mai ƙyau, ilimin addini dana zamani kullum akwai malaman dake zuwa karantar damu. Ga albashi mai tsokar gaske. Rayuwarmu a killace ta yanda wani bazai taɓa ganinmu a ƙasƙance ya wulaƙantamu ba. Cimmu, shan mu, sutura, magani idan muna ciwo bai taɓa gazawa ba. Dan ALLAH dami zamu sakankama wannan bawan ALLAH?. Har sonake naga wace mai sa'a ce zata dace da samunsa matsayin mijin aure? ALLAH zan tayata murna harda azumin godiya ga UBANGIJI. Nasan bazaki gane duk abinda nake nufi ba. Amma nan da wata ɗaya kacal duk zaki maimaita abinda na faɗa, dan ma ba zama yake ba sosai saboda harkokin kasuwancinsa dana mahaifiyar tasa ance duk sun koma hannunsa, dan itace mai kuɗin fa. Ko wannan katafaren gidan ance ita ta fara gina shi sannan Uncle Boss ɗin yana ƙarami, sai da ya girma shi kuma ya ƙarasa saboda ita ciwo bai barta ba”. Tana kaiwa nan ta miƙe zaram idanunta akan agogon ɗakin. “Tabɗi na shiga tara, Aunty Kandala bari na koma wlhy minti biyar ta bani, nasan zansha mari”.      Kafin nace wani abu ta fice a guje. Shiru kawai nayi ina kallon ƙofa tamkar zan zuƙota da idanu. Akaf labarin data bani wanda ya shafi mahaifiyarsa ne kawai ya tsaya min a rai. To dama tana a haukan ta haifesu? Kokuwa daga baya ne haukan ya sameta? Bani da mai bani amsa dan haka na zabga tagumi kawai. A karo na farko naji ina kwaɗayin jin labarinsa. Ko shiyyasa baya son a tambayesa tarihinsa? Randa nai hira da shi ya shiga dawo min a rai. Tabbas a ranar bai amsa koda kalma ɗaya data shafi privet life ɗinsa ba. Na sake tuna ranar taron buɗe kamfaninsa. gargaɗinsa akan ƴan jarida baya buƙatar kowace tambaya sai akan kasuwanci. Hakan na nufin akwai abinda yake ɓoyewa ko baya son a sani dangane da shi. Kai dolene nasan komai, to amma ta yaya? Wannan shine tsallen baɗaken a gareni. Gashi ba wani jituwa muke ba, to wannan ma jiji da kansa zai barsa huɗɗar arziƙi da mutane....               ★★★   Tunda Samraah tabar gidan ya sake zama sukuku. Wani lokacin ma ya gwammace ya kwana a gareji kawai. Yakan yi kwana biyu bai shiga cikin gidan ba. Duk da kuwa bai fasa musu dukkan abinda yake musu na hidimar yau da kullum ba mussaman cefane da ya dawo bisa kansa. Idan har bazai zo ba yakan bama wani almajiri dake a garejinsu ya kawo cefanen. Duk da asha ruwan tsuntsaye da yakema zuwa gidan Abba bai taɓa tambayarsa ko cigiyarsa ba. Sai hakan ya sake ƙona masa zuciya da jin komai yama fice a ransa. Yakan ɗan ji sanyi ne kawai idan ya kira Hafizzullah ko mijin Samraah yaji yaya jikinta. Yakan so a bata su gaisa, sai dai hakan baya faruwa kasancewar duk sanda zai kira tana barci. Amma dai mijin kan kirasa video call ya ganta a wasu lokutan. Harga ALLAH yana son zuwa ya ganta, sai dai ta bakin su Kawu Musa baya son mijin nata ya ga kamar an nuna ya gaza ne shiyyasa ya haƙura yake kawaici. A kwanakin nan kuma sai ya koma baya samunsa duk sai hankalinsa ya tashi, yana shirin zuwa Abujan sai ga shi ya kiransa yana mai bashi haƙuri akan jinsa shiru wai yayi wata ƴar tafiya ne, amma yana gab da komawa gida idan ya koma zai haɗashi da Samraah. To tun daga ranar kuma basu sake waya ba dai har yanzu...         Yana cikin damuwar rashin ji daga mijin Samraah ɗin sai ga ogansa yazo masa da wani batu. Wai Companyn Maash na ƙera motoci da aka buɗe kwanaki sunzo garesa suna buƙatar matasan kanikawa masu kwalin secondary. Shi kuma ya bada sunansa dan yasan yana da su. A yanzu haka kuma sunce zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suna buƙatar ganinsa interview. Rasama abin faɗa yay, sai hawaye da suka cika masa ido yana kallon ogan nasa kawai. Bai san mizai sakankama bawan nan da shi ba a rayuwa saboda ɗunbin ƙaunar da yake nuna masa da alkairan da yay masa...       “Wai namiji da kuka Musaddiq?”.    Ogan nasa ya katse masa tunani cikin nuna damuwa. Hannu yasa ya share hawayen da shi kansa bai ma san sun zubo ba. Sai kuma yay murmushi tare da buɗe baki zaiyi magana. Da sauri ogan nasa ya dakatar da shi da faɗin, “Basai kace komai ba Musaddiq. Ka cancanci fiye da haka a wajen nan domin kai ɗin ɗan hakal ne wlhy. Da ace inada abinda yafi hakan zan maka a rayuwa. Fatana dai ALLAH yasa wannan canjin da zaka samu ya zama sanadin alkairin ka a rayuwa kai da zuri'ata. Kuma ina mai farin cikin sanar maka nima basu barni haka ba. Akwai aikin dazan dinga musu, dan haka zasuzo su gyara wannan wajen ya koma na zamani kamar yanda suka faɗa”.       A take farin ciki ya sake mamaye Musaddiq. Sujidar shikur ya farayi kafin yaje ya rungume ogan nasa. Dariya ya shiga yimasa, dan har ga ALLAH yana matuƙar ƙaunar Musaddiq saboda gaskiyarsa da riƙon amana. Ga biyayya da kwazon aiki, da wahala kaga fushi a fuskarsa koda kuwa faɗa yay masa. Mutum ne mai juriya da shanye komai koda bai masa daɗi ba....     Rasa inda Musaddiq zai kai wannan farin ciki yayi, har ya danna Number Abba sai kuma ya fasa sakamakon tsoratar da shi da zuciyarsa tayi kodan halin Mom. Haƙura yayi, sai da yamma ana tashi daga aiki ya wuce Dawanau wajen Gwaggo Gudidi. Ita ya kaima wannan labarin farin cikin, ai ko baiwar ALLAH harda kukanta tana ƙara godema ALLAH. Daga ƙarshe ta gargaɗesa akan kada ya sanarma Abba yanzu kodan mugun halin matarsa zata iya shiga ta fita ta jefesa da wani sharrin. Yana dai ganin halin da aka shiga game da auren Samraah abu kamar a film ko a labaran hikayiyin marubuta. Ya yarda da shawarar Gwaggo ɗari bisa ɗari. Daga haka suka koma hirar Samraah. Itama Gwaggo ta shiga damuwa sosai hankalinta kuma ya fara tashi, anya kuwa basuyi gangancin aurama Samraah mutumin nan ba? Duk da dai a fuska yazo musu da suffar mutanen kirki. Amma dai zatai magana da Kawu Musa domin a tuntuɓi magabatansa da sukai masa waliccin auren.........✍️              _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ______________ ......Sosai hirarmu da Bahijja ya tsaya min ƙyam a rai da zuciya. Duk yanda nake yaƙin son turesa hakan ya gagara. Gashi tun ranar ban sake ganin makirin ba. Hakama cikin gidan ban sake shiga ba. Bahijja dai ta sanar min Babansa da matar babansa sun dawo daga tafiya, hakama ƙanin baban nasa da iyalinsa sun dawo suma dai. Sannan yau gaba ɗaya sunyi busy wai ana aiki ne acan sashin saboda bikin birthday da za'ayi wai na mahaifiyar tasa. Ni al'amarin ma sai na ɗaukesa hauka. Yo inba hauka ba, koma nace sunfi ita mai ciwon haukan zama mahaukata mara lafiya dake buƙatar addu'a ce wai za'ama wani shegen birthday party. Kai yawudanci ma baiyi ba. Ko kuwa dukiyar tasu ce ke neman zauta musu ƙwaƙwale ma oho musu. Sosai takaici ya kumeni, ji nake kamar na buɗe ido na gansa a gabana. Wlhy da ko zai tsireni sai na faɗa masa gaskiya sai dai ya mutu shiya sani. Ina nan kwance ina ƙullawa da kwancewa wajen ƙarfe biyu su Mama balki suka fara dawowa. Hayaniyarsu tasa na fito falo nima. Sannu na shiga musu, wasu su amsa wasu su shareni batare dana san mina musu ba. Mama Balki ce ta dubeni da murmushi, cikin kulawa ta ce, “Ai kema daga gobe za'a fara miki sannun. Dan Aunty Mama tace zaki fara aikinki. Kinga sai ki shirya idan mun gama zamu wuce dake tare wajenta kamar yanda ta bada umarni”.        Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo. Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo.....        _Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta🥱🥱🚴_       ❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”.       Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu. Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....”       Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu..          “Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”.       “Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.”       Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu tarr da su”.      Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece....       Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu. Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa...       “Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”.       Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba. Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”.       Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”.       “Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”.        “Mama saboda mi?.     “Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”. Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”.     Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai ga Mama Balki ta dawo kirana.        Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da shi a madadin  mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya.        “Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta. Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala. Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”.       Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina. Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili ba nima..........✍️       _Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri da asha ruwan tsuntsayen nan nawa na yanzu🙏_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas. Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan biyar, cikkune dan haka ɗaure yake a tsakkiya ƙarshen kitson kuma gashin a warware ba'a kitseba dan haka ya sakesa kawai a baya yana lilo. Wani irin takaici da haushi ya sakani kallon fuskarsa duk da nasan tabbas yayi ƙyau. Karaf kuwa idanuna a cikin nasa. Bamma san lokacin dana balla masa harara da murguɗa nawa bakin ba. A mamakina sai kawai naga ya lumshe nasa idanun tare da buɗesu a lokaci guda yana cije gefen lips ɗinsa ya ɗauke kansa. nima ɗauke nawan nayi kamar zan fasa kuka, ji nake tamkar naje gareshi yanzu na zazzage masa abinda ke a raina. Amma dai na dake, sai harara dana sake jefama jelar PA ɗinsa dana fahimci tunda idonsa ya sauka a kaina yay suman tsaye. Niko na ɗauke kaina tamkar ban san da zamansa a wajen ba. Tunda nasan dai duk abinda mugun ogansa ya ƙulla tare da shine makirin shima. Addu'ar da aka fara gabatarwa ya saka kowa a wajen sake nutsuwa. Mu dai marasa gata duk muna a tsaye kan ƙafafunmu, yayinda suko ke zaune a kujerun da aka ƙawata wajen. Sosai yanda akai addu'ar wa kowa harda iyayenmu ya sake saka min nutsuwa har idanuna na tara ƙwalla. (ALLAH sarki rayuwa, da ace muma namu iyayen na raye babu yanda za'ai mu tsinta kammu a cikin wannan gararin rayuwar. Amma ko yanzu ma alhmdllh, koba komai mun rayu cikin aminci tunda gallazawar rayuwa batasa mun lalace ba). Kewar su Yaya Musaddiq ce ta sake taso min sabuwa har na zurfafa a tunani batare dana farga ba. Taɓanin da Bahijja tayi ne ya maidoni a hayyacina. A hankali na sauke ajiyar zuciya da nannauyan numfashi. Cikin raɗa-raɗa a saitin kunnena ta ce, “Aunty Kandala muje zamu fara bada drinks”. Kaina kawai na iya jinjina mata, dan gaba ɗaya babu wani ƙarfi a tattare da ni. Ta wajen babban table ɗin da aka shirya nau'ikan abinci dana lemuka da ruwa muka nufa. Bahijja ta zari handglob guda biyu ta miƙamin tare da mun nunin na saka. Itama ta zara ta saka a nata hannun sannan ta buɗe ƙatuwar kular da kayan ruwan ke ciki ta ɗiba lemunan da ruwa duk ta loda a babban tray data jawo guda biyu. Sai da ta gama zuba nata da nawa sannan ta ce, “Yauwa to muje. Kowa a gabansa zaki fara ajiye ruwa sannan ni kuma na ajiye lemon da suka buƙata”.        “Kamar ya?”.    Na tambaya cikin rashin fahimta. Ƴar dariya tayi. Kafin ta ce, “Na zuba miki ruwa ne dan kar su baki wahala. Shi ruwa zaka ajiye ne kawai. Amma lemo dole sai mutum ya zaɓa sannan”.        Kaina na jinjina mata alamar gamsuwa, sannan na kama tray ɗin na ɗaga ina ɗan taɓe baki. Ai da sauri na maida na ajiye ina waro idanu. Ai wlhy bazan iya ɗauka ba yamun nauyi. Ragewa na fara yi, hakan ya sata zaro idanu waje alamar nuna mamaki. “Lafiya kike ragewa?”.       “Yamun nauyi wlhy Bahijja bazan iya ɗauka ba”.     Sake waro idanu tayi, niko ban sake kulata ba na rage fin rabi sannan na ɗauka. Kallo take mun na tama rasa abin faɗa. Ni ko na sake ɗauke kaina gefe kamar ban ganta ba. Dole itama ta barni muka bar wajen tana gaba ina biye da ita. Suma sauran kowa ya fara aikinsa dan komai a tsare yake. Mun fara da table ɗin farko. Mai ɗauke da mutane huɗu kamar ko ina. Maza biyu masu tsananin kammani, a fisge kuma suna kama da mutumin can Maash. Sai dai kawai su baƙaƙe ne. Tabbas nasan mai irin fuskar nan amma na manta a ina. Sai mata guda biyu ƙyawawa suma, ɗaya fara tas ɗaya black beauty. Su duka sunci ado sosai mai tsananin ƙawa. Ganin kallon da suke min na rashin sani yasa naji kamar duk na daburce. Amma sai na dake kaina a ƙasa na shiga haishesu ƙirjina na bugawa da sauri-sauri. Mazan ne kawai suka amsa min, yayinda baƙar matar ta dubi Bahijja a gadarance ta furta, “Wannan fa?”.           Jikin Bahijja har ɓari yake. Cikin in-ina ta amsa da, “Au...aun..Aunty Mama ce tazo da ita randa ta iso”.     Su dukansu ɗan kafeni sukai da kallo, sai kuma duk suka janye cike da basarwa. Jiki a sanyaye na bar wajen, batare da ina kallon gabana ba saboda zancen zuci na iso table na gaba. Ganin nayi tsaye kawai Bahijja ta ɗan zungureni, firgigit na kawo numfashi, ɗagowar da zanyi na sauke idanuna a kansa. Zaunensa yake a harɗe fuskar nan kicin-kicin tamkar ba wanda ya tara jama'a ba. Gaba ɗaya hankalinsa na akan tab dake a hannunsa ne. Yanda yay serious a kanta zai baka tabbacin abinda yake yi mai muhimmanci ne. Ga uban ƙamshin turarensa da ya mamaye wajen gaba ɗaya. Fuska na yamutse tare da ɗauke kaina. Harara na ballama ɗan koren PA ɗinsa dake table ɗin bayansu. Ƙasa naga yayi da kansa yana murmushi. Jinai zuciyata ta ƙulu da murmushin nasa, amma sai na danne tare da cije lips ɗina kawai....         “Woow! fine girl ko ana mana rowan ruwan ne?”.      Ɗaya daga cikin waɗan da ke zaune a table ɗin tare da shi ya dawo dani a hayyacina. Ni sai ma yanzu na lura da sauran dake zaunen a tare da shi. Su duka su nasan fuskokinsu a wajen taron buɗe Companyn sa na Kano. Dan ALLAH ya bani baiwar da dawahala nai maka gani ko ɗaya ne na manta fuskarka koda ace ban riƙe suna ba ko a inda na sanka ba. A hankali na ɗan yamutse fuska ta. Batare da nace komai ba na fara ajiye musu ruwan. Uku na ajiye abina batare da nashi ba, dan kowa a gabansa na ajiye amma shi banda shi. Na ɗaga tray ɗin zan bar wajen wannan dai da yay maganar ya ɗan waro idanunsa yana nuna min shi. “Beauty baki ajiyema boss ba fa”. Yi nai tamkar ban jisa ba sai da Bahijja tasa hannu ta ɗauka ruwan ta ajiye masa jikinta har yana ɗan rawa. Harararta nayi batare dana san dalili ba. Itako ta waro idanunta na nuna mamakina. Tray ɗin na sake ɗagawa da nufin barin wajen ina dallamasa harara ta gefen ido dan tunda mukazo wajen ko sau ɗaya bai motsa ba balle kai tunanin yama san da zuwan namu, batare da nasan yanda akai ba, ta yaya kawai tray ɗin ya suɓuce min na tafi gaba ɗaya na. Idanu kawai na runtse tare da sallamawa, amma sai na jini zaune jikin mutum, yayinda shi kuma tray ɗin ya suɓuce a ƙasa sauran ruwan suka tarwatse. Wani irin zuƙa da nayima mayataccen ƙamshin turarensa ya saka gabana faɗuwa. Da sauri na buɗe idanuna dake a rufe. Sai kawai na waro su tare da yunƙurawa da sauri zan miƙe amma hakan ya gagara. Dan sake zamewa nayi na koma jikin nasa gaba ɗayana har ma fiye da farko.        “Sai kice son hawa kike ba sai kinyi pretending ba”.     Naji saukar muryarsa a cikin kunnena. A wani irin zafafe na sake yunƙurawa gaba ɗaya na na miƙe jikina har tsuma yake, sai da Bahijja data gama firgita ta riƙoni. Jinai bazan iya daurewa ba, idanuna na tara ƙwalla na watsa masa harara, sai dai ina motsa lips ɗin na nufin juye masa abinda ke raina naji na gagara hakan. Sakamakon wani shegen kallo daya tsatstsareni da shi tare motsa lips ɗinsa a hankali, “Kina cewa tak sai kowa yasan ke MATAR MAASH ce”.     Da masifar ƙarfi na cije lips ɗina hawaye na sake ciko min idanu. Badan na samu horo akan aikina game da salon da yay maganar ba da bazan fahimta ba. Amma gamu ƴan jarida yaren magana da ido ma an karantar da mu balle na motsa lips. Da wani irin salon rainin hankali ya kai yatsarsa manunuya saman goshinsa tamkar zai gyara silin gashi yay salute tare da sakin wani matsiyacin murmushi gefen baki ya kanne ido ɗaya.      “Sai na tarwatsa rayuwarka”.   Na faɗa nima a saman lips ɗin ina haɗiye hawayen da suka ciko min idanu. Sanin zasu iya zubowa na kai durƙushe nima ina taya Bahijja tsinci ruwan daya tarwatse. Sai faman haɗiyar zuciya kawai nakeyi dan ni kaɗai nasan abinda nake ji a cikinta, nu mutumin nan zai cema ina son hawa masa jiki ne dama. Ƙasa-ƙasa Bahijja ta furta, “Aunty Kandala kice masa yayi haƙur....” ruff ta rufe bakinta tare da haɗiye sauran abinda ke bakin nata saboda hararar dana balla mata. A fusace na miƙe tare da sunkutar tray ɗin nabar wajen. Mama Balki ce tai min nuni da nazo inda take. Dole na nufi inda muka ɗebo ruwan. Amsar tray ɗin tayi tana faɗin, “Badai kiji ciwo ba ko ɗiyata? Alhamdullah ma Alhaji ƙarami na kusa ya taimaka miki da kinyi muguwar faɗuwa ai. Sai naci ƙaniyar Bahijja kuwa, tunda bance harda ke za'ayi aikin nan ba amma ta jaki”.           Sosai naji raina ya ƙara zafafa. Wato su abinda suka fahimta kenan nazo zan faɗi ya taimakeni, alhalin ina zargin taɗeni akayi da ƙafa, tunda karo naci da abu a bazata, kuma babu wani dutsi ko ƙarfe balle ace shine. Ko rantsu nayi ba'a bina bashin kaffara mutumin nan shine silar faruwar komai, dan shine ya taɗeni da ƙafarsa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏 _*_Assalamu alaikum. Gaisuwa a gareku da fatan alkairi bayin ALLAH. Dan ALLAH kuyi haƙuri! kuyi haƙuri! kuyi haƙuri!!. Ba haka naso al'amarin ya kasance ba. Sai dai kana naka ne ALLAH na nashi. Nashi kuma shine gaskiya. Saboda ku na tsara kwanaki biyar, amma suka koma kwana tara. Amma in sha ALLAHU gamu mun dawo filin daga. Zakumin haƙuri na dinga baku ko 2pages ne dan na samu na rage nawa aikin nima daga nan ko zuwa kwana uku ne. Ngd Ngd sosai da haƙurinku gareni da uzirin da kukayi min. Wanda suka kirani kuma, kuma nagode, wanda sukai ma amarya da mai rasuwa addu'a a group duk na gode ALLAH ya bada ladan zuminci😘😘🙏._ ........“Kinga maza jeki ki zauna dan baƙya cikin wannan aikin”. Mama Balki ta katse min tunani. Kaina kawoi na iya ɗaga mata da faɗin, “Nagode” a taƙaice na wuce ina haɗiyar zuciya. Inda muke tsaye da da Bahijja na koma na tsaya, sai dai duk bayan sakan sai na harari inda yake. Haka dai taron ya cigaba da gudana. An ƙara gabatar da addu'a musamman akan wadda aka tara taron da fatan ALLAH ya bata lafiya, na fahimci ba kowa yasan ainahin ciwon da take tare da shi ba, dan ina jin wasu mata biyu na gulma ƙasa-ƙasa game da hakan. Wai shekara da shekaru anata ciwo-ciwo amma anƙi sanarma duniya wane kalar ciwo ne. Sosai suka bani mamaki, a raina nace duniya kenan, mutum na jikinka amma baya maka so dan ALLAH.      Natsuwar fara addu'ar na samu damar fara bin kowa dake a wajen da kallo daki-daki. A hankali Bahijja da duk hankalinta ke a kaina dan tuni sun kammala raba lemon da ruwa sun dawo inda muke ta furta, “Aunty Kandala kinga waɗanda ke a table ɗin kusa da nasu Uncle Boss ta hannun dama da muka fara bama ruwa da drinks mai milk shadda shine mahaifinsa. *_El-mu'azz Mashi_ kenan. Sosai na tsurama wanda ta faɗa ɗin ido ta gefe dan ɗazun ban iya musu wani kallon kirki ba. Eh tabbas da gani babu tambaya, dan ya ɗebo wasu a cikin kamanninsa. Kamar tsaho, dogon hanci da makamantansu. Sai dai shi baƙine sannan alamun girma ya bayyana kaɗan a tare da shi. Musamman akan gashinsa akwai furfuta tsilli-tsilli. Haka kawai nake sake jin tabbas nasan fuskar, sai dai a ina? Na manta sam dan na kasa tunawa. Cikin katse min tunani Bahijja ta cigaba da faɗin, “Sai matar dake kusa da shi. Hajiya ƙarama kenan. Itace matarsa ta biyu kuma amaryarsa. Itace mahaifiyar Arwa. Ance ta taɓa haihuwa da shi sau ɗaya tagwaye duk maza a shekarar farkon aurensu amma duk sun rasu, ba kuma ta sake ba. Arwa dai da ita tazo. Matar bata da damuwa sosai, sai dai akwai miskilanci da mulki tamkar itace ma uwar Maash ɗin. Sai dai abubuwa nata da yawa na matuƙar birgeni, duk da dai wasu na bani haushi musamman yanda Hajiya Mammah ke takata yanda take so amma bata iya cewa komai ko nuna ikon ta na matsayin matar gida, wani lokacin ma sai ka ɗauka itace matar gidan ba Hajiya ƙarama ɗin ba”.         Sosai na tsurama matar idanu itama. Ƙyaƙyƙyawar mace kam ga suffar kamala black beauty da ita. Amma da gani kasan miskilar ce dan sam babu fara'a a fuskarta kamar dai ɗazun da tai tambayar ni wacece a daƙile.       Bahijja ta cigaba da faɗin, “Na kusa da shi kuma Alhaji Abdullahi Mashi, ƙani wajen Alhaji El-Mu'azz kenan. Uwa ɗaya uba ɗaya. Ta kusa da shi Hajiya Mubeena matarsa uwar ƴaƴansa uku. Itama dai tana da ƙarancin damuwa, sai dai ta hannun damar Hajiya Mammah ce dan ƙiri-ƙiri take nuna banbanci tsakaninta da Ummi ɗin (Hajiya ƙarama) na taɓa jin su Aunty Falila suna gulma wai ai dama ƙawarta ce acan ƙasar Niger da tayi aure, kin san mahaifin su Azizat buzu ne, shiyyasa kike ganinsu da shegen gadarar nan da masifa duk da dai shima wannan family ɗin masifa kamar a jininsu take, fitinannun mutane ne na bugawa a jarida, Uncle Boss ne kawai nake gani ma shiru-shiru a cikinsa ko magana da wahala kaji yana yinta, in ma yayi ɗin ba lallai kaji sautin muryarsa ba, sai ko Aunty Mama itama tana da sauƙi sosai, idan kinga tana faɗa an ɓata bata rai ne matuƙa. Daga table ɗin gefensu akwai Azizat ita kam kin haddaceta” tai maganar da shaƙiyanci, sai kuma ta cigaba da faɗin, “Sai Mabrukah autar Hajiya Mubeena, sai....”      Da sauri tayi shiru saboda yafito ta da Azizat ɗin tayi, jikinta har rawa yake ta nufeta. Wani takaici ne naji ya ƙwaƙume min zuciya. Bamma san na saki sirrin tsaki ba da taɓe bakina na ɗauke kaina daga sashensu ma gaba ɗaya. A bazata suka sauka akan Hajiya data ɗakkoni daga Abuja. A mamakina sai naga ta sakar min murmushi harda kashe ido ɗaya. Ɗan tsira mata idanu nayi cikin nazartar yanayin nata dan haka kawai komai daya faru a tsakaninmu tun daga Abuja ya shiga dawo min. Yanda take wani bina da kallon ƙurilla ya sani balla mata harara na bar wajen gaba ɗaya dan muna facing juna. Dai-dai nan mc yay kiran sunan uban taro cike da girmamawa. A tunani na Alhaji El-Mu'azz ɗin ne zai tashi, amma sai naga makirin nan ne ya miƙe cike da ƙasaita bayan ya gama shan ƙamshi da busar iska da fesarwa. Taku yake tamkar mai tafiya a kan gilashi, dan sai ka ɗauka ma bazai ƙarasa inda mc ɗin yake ba dan jiji da kai. Mic ɗin ya amsa, sai kuma yay ɗan shiru kamar wanda ya rasa abin faɗa. Baki na taɓe tare da watsa masa harara sai idona a cikin nashi. Da sauri na ɗauke ina mai murguɗa bakina kawai....        “Hummm!!” ya faɗa cikin mic ɗin ta yanda kowa dake a wajen sai da ya ji sa. Amma a mamakin kowa ya sake ɗinke fuska kamar bashi ne yace hummm ɗin ba. Sai ma cigaba da maganarsa da yay cikin harshen turanci mai haɗe da faransanci, yau dai ALLAH ya taimake mu ba'ai Hausa ba balle a ɓaga mana yare. Godiya ce kawai yayi a taƙaice  tare da roƙon cigaba da tayashi addu'a ALLAH ya bama Ummiensa lafiya. Sai kuma yay shiru kansa a ƙasa fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Kusan minti ɗaya kafin ya ɗago yana mai kai handkerchief saman fuskar sa ya goge. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci guda ya saukesu akan mahaifinsa. Murmushi ya sakar masa, sai kuma ya miƙe tare da nufosa shima. Yana isowa ya rungumesa yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Daga haka ya amshi mic ɗin hannunsa shima ya fara magana. Kusan abinda dai ɗan nasa ya faɗa shima ya maimaita, sai abubuwa kaɗan daya ƙara a kai sannan suka yanka cake a tare. Baban ne ya fara ɗibowa ya kai bakinsa. Cikin wani yanayin narke fuska ya motsa ƙananun lips ɗinsa kaɗan, sai dai baban na zuwa gab da bakin nasa sai ya juya hannunsa zuwa nasa bakin ya cinye cake ɗin tare da lakata masa sauran na hannunsa a saman hanci. A take wajen ya ɗauki tafi da dariya. Shima murmushi yayi yana kauda kansa. Sai baban ya rungumosa yana dariya.         Haka kawai na tsinta kaina da yin murmushi akan wasan nasu, sai kuma na haɗiye da sauri dan tuna akan wa akeyi. Bayan sun je sun zauna Hajiya Mammah, Aunty Mama, Hajiya ƙarama, Hajiya Mubeena, Alhaji Abdullahi duk sun fito sunyi bayani tare da addu'a ga Hajiya Ummu-Hidaya kamar yanda naji suna ambata dama rubutawa da akai jikin ƙaton cake da wani irin golden color mai sheƙi tamkar ba cake ba. Gaba ɗaya zaman wajen bai wuce na awa biyu da mintuna arba'in ba. Aka raba ƙyauta har da mu daga haka taro ya tashi. Bayan tsirarun baƙin da aka gayyato irin su Hajiya sun wuce Aunty Mama ta bama Mama Bilki umarnin zuwa dani garesu bayan sallar isha'i. Ta amsa mata da girmamawa yayinda ni kuma nai kamar ban jisu ba dan hankalina gaba ɗaya ya tafi wani waje daban.....                🌜🌟🌛         Matuƙar tashin hankali Musaddiq da Halime tai gudu ta kira ya shiga ganin Abba cikin jini. Rasama abinda zai yi yay har sai da maƙota suka shigo. Sune suka ambaci asibiti sannan hankalinsa ya dawo jikinsa. Ga Bibaa da Auta na famar darzar kuka. Baby kuwa sai surutai takeyi. Duk wanda ya shigo kuma sai ta nuna Mom data maƙure gefe jikinta na maƙyarƙyata.          “Kun ganta nan itace ta kashe mana Abba. Kawai itama a kasheta dan nice alƙali na yanke hukunci”. Abinda Babyn ke faɗa kenan cikin Muryar ƴan maye da surkulle. Duk da kowa kanji shock da abinda ta faɗa ɗin da kuma yanayin da take ciki babu mai bi takanta. Burin kowa dai a kai Abba asibiti kada ya rasa ransa....      Koda suka isa asibitin da ƙyar aka amshi Abba, dan sai da Yaya Musaddiq yay ƙaryar faɗuwa yay a banɗaki sannan. Da gaggawa suka shiga bashi kulawa, yayinda aka bar su Musaddiq kai-kawo a waje kowa na addu'a a zuciyarsa. Sun kwashe tsahon lokaci kafin doctor ya fito. Bayanin da yay musu na cewa yaji ciwo sosai a kan nasa kuma bai farfaɗo ba har lokacin ya sake tada hankalin Musaddiq. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Dan harga ALLAH duk abinda Abban ke musu shi da ƴan uwansa bai taɓa jin ya tsani ƙanin mahaifiyar tasu ba. Saboda yana kallon fuskarta ne akan ta kawun nasu. Tun a daren yay kiran ƴan Gwarzo da Gwaggo Gudidi. Sai dai suma bai faɗa musu gaskiyar al'amarin ba dai. Hankalinsu ya tashi, washe gari kuwa tunda sassafe sai ga Gwaggo Gudidi. Wajen tara sai ga ƴan Gwarzo suma har da su Kawu Musa saboda kara. Dan su ta ɓangaren mahaifinsu suke bata ɓangaren Abban ba. Har Azhar Abba bai farfaɗo ba, asibiti ya ciga da dangi amma babu Mom. Sai su Bibaa da Baby. Abbas ma sai kusan azhar ya iso hankali tashe. Dan bai san mike faruwa ba sai da yaje gida yake ji a anguwa. Koda ya shiga cikin gidansu ya samu Mom nata darzar kuka gefenta mahaifiyarta Inna zaune jigum ta zuba tagumi da hannu biyu. Bai iya cewa da su komai ba dan yanayinsu da sambatun da Mom keyi ya tabbatar masa da abinda mutanen suka faɗa. Kiran Musaddiq yay a waya ya sanar masa asibitin da suke. Sai ko gashi ya iso. Hankalinsa ya sake tashi da jin Abba fa yaƙi farfaɗowa, harma likitocin na maganar ya tafi doguwar suma........✍️ _Wayyo Abbanmu kada ka tafi ka bar Halime😌😌_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_ .........“Wlhy sai na kashe yarinyar nan da hannuna na jefar da gawarta inda ko angulu basa gittawa!!”.      Yanda take maganar cikin fushi ga idanunta cike da hawaye jikinta na rawa ya tsorata Arwa. Riƙota tayi tana mai danne abinda ke cin tata zuciyar itama kamar yanda ta saba. A take zuciyarta ta hasko mata nasararta, dan tabbas wannan dama ce da zatai amfani da Azizat game da yarinyar nan taci nasarar samun cikar burinta itq. Cikin dakewa tamkar bata ga komai daya faru ba ta ce, “Aunty Azizat cool down mana. Wai mike faruwa? Mi akai miki? ki faɗa min ko ina da taimakon da zan miki. Shin waccan ƴar shishigin ce Malikah ko?”.         Ɗari bisa ɗari Azizat ta yarda da Arwa. Dan ƴar team ɗinta ce, duk da iyayensu basa jituwa hakan bai hanasu aminci ba su. Ta kuma sha bata shawara akan Malikah taci nasara. Hawayen da suka gama wanke mata fuska ta share. A matuƙar zafafe ta furta, “Malikah ɗin banza. Ita har ta isa nai mata kuka Arwa, kada kema ki ɓata min dan ALLAH. Idan baki san abinda zaki faɗa ba fita ki bani waje...”      “Kiyi hakuri to ba yanda kike nufi bane. Faɗa min mike faruwa?”.    Shiru ta sake yi kamar ba zata ce komai ba har sai da Arwa ta sake zingurarta. “Arwa ki ƙyaleni dan ALLAH. Har zaki ce bakiga sanda waccan karuwar sabuwar mai aikin yarinyar da Aunty Mama ta kawo mana gida yau ma ta sake faɗawa a jikin Yaya Awwab ba?”.        “What?!! Jikin Yaya Awwab fa? Bayan na waccan ranar da tayi kuma yau ma ta sake again? Eh lallai kam na yarda dake wlhy yarinyar nan karuwa ce Aunty Azizat. Kuma tabbas ba haka nan ta shigo gidan nan ba akwai asiri tare da ita, sannan akwai manufa, ni dama wlhy tun kallo ɗaya da nai mata nake ji a raina batai kama da masu aiki ba. Idan ba hakaba taya za'ace ranar tayi yau ma ta sake aikatawa kuma? Koda yake babu mamaki ai ba'ai mata gargaɗi ba ne a waccan ranar. Ke kuma da alama ta danne miki baki tunda na ga ko Mammah baki sanar mawa ba”.      Sosai kalaman Arwa suke tasiri a zuciyar Azizat. Zuciyarta ta shiga tabbatar mata lallai akwai asiri a al'amarin kam. In ba hakaba yama za'ai hakan ta kasance. Kuma wai abin ƙarin mamakin ma yanda abin ya faru kowa ya nuna tamkar bai gani ba. Koda yake komai ya faru ne tamkar ƙiftawar idanu dan bai wuce cikin minti biyu ba, tun daga faɗawar tata har tashinta daga jikin nasa. Sannan a yanda shegiyar tayi sai ka ɗauka accident ne bada sani ta aikata ba...     Ganin yanda ta sake tafiya duniyar tunani Arwa ta sake taɓota. Cigaba tayi da fanfata har sai da ta hau ta zauna. Sannan ta tsara mata abinda ya kamata suyi domin ɗaukar mataki. Sosai kuwa Azizat ta yarda, dan a take ta jawo kan wayar telephone tayi kiran sashen masu aiki. Ana ɗagawa ta miƙama Arwa kan wayar, itako dama ALLAH ya bata iya canja murya, a take ta koma muryar Aunty Mama. Tana gama faɗar abinda suka tsara ɗin ta yanke kiran, kallon juna sukai ita da Azizat ɗin suka saki murmushi. Sai kuma suka tafa alamar nasara ta samu....        ✨💞✨💞✨       Wajen la'asar ana ƙoƙarin maida Abba wani ɗakin sai ga Mom da Inna da ƙawarta wadda ta kawo mata Halime. Kallon inda take kowa baiyi ba, dan zuwa yanzu kowa a wajen yasan sanadin al'amarin sakamakon Baby data zazzage musu zance. Har an canjama Abba kaya za'a wuce da shi sai ga Nurse a guje yana ƙwala kiran doctor. Kusan dukansu suka afka ɗakin dan azatonsu Abba ya cika, koda Nurse ɗin da doctor suka shigo sun cika ɗakin tare da rufuwa a kansa. Da ƙyar doctor ya samu duk suka fice su kuma suka fara aikinsu.         Kowa ka gani yana cikin farin ciki da farfaɗowar Abba. Sai kuma fatan ALLAH ya bashi lafiya. Bayan kamar mintuna Talatin kuwa Doctor ya sake musu albishir ɗin farfaɗowar Abban. Sai dai ba'a bar kowa ya shiga wajensa ba sai a washe gari. Alhamdullah jikin nasa da sauƙi sosai, sai dai kansa yasha bandage abin tausayi. Babu wanda yace ma Mom komai duk wani rawar kan dafo abinci da take tana kawowa safe da rana da dare. Shima Abban kuma baya ko kallon inda take duk maganar da zata masa bai amsawa. Dama jiyyarsa Kawu Isuhu ne keyi. Ƙani yake a gurinsa dan ɗan wan mahaifinsu ne. Kwanansa uku aka sallamesa. Ya samu rakkiyar dangi data abokai irin su Alhaji Sadisu.      Tun isowarsu ya fahimci Halime bata gidan, bai dai ce komai ba har sai da yay wanka ya samu nutsuwa. Falo ya dawo ya kwanta saboda masu shigowa dubasa ƴan nan cikin anguwa. Su Gwaggo Gudidi na zagaye da shi anan ɗin ma. Basu sami lafawar mutane ba sai kusan goma na dare, alokacin ne fa Gwaggo Gudidi ta fara tsiya saboda tayin shiga ɗaki ya kwanta da Mom ta masa. Gwaggo tace babu inda zaije a ƙarasa hakalashi, Musaddiq ya kaisa ɗakinsa yaje can ya kwana. Sosai Mom ta shiga shock, dan batai zaton sun san ainahin abinda ya farun ba, amma sai ta dake ta shiga bama Gwaggo haƙuri da shi kansa Abban wai sharrin shaiɗan ne bazata sake ba. Harda ƴar ƙwallarta kamar yanda Ummanta tace tayi. Fata-fata Gwaggo ta mata a gaban su Musaddiq, sai da ƙyar aka samu tayi haƙuri. Ita dai Mom yau babu bakin magana kuma sai haɗiyar zuciya.....                  💥❤️💥❤️💥    Bayan sallar isha'i dole na haƙura da batun bin su Bahijja Islamiyya domin amsa kiran Alajah. Muna gaba da shiga sashen Mama Balki ta dakatar dani, cikin nuna kulawa da kwantar da murya ta furta, “Ɗiyata dan ALLAH yau ki danne zuciyarki. Kar ki kula Azizat komi zata miki. Mutanen nan da kike gani sunada rigima sosai, idan aka zo fagen faɗa da bare kansu haɗe yake wajen ɗaukar mataki. Ki ringa haƙuri mu neman arziƙi ya kawo mu. Fatanmu mu samu abin rufama kammu asiri shike nan kawai. Kina ƴar ƙaramarki da ke kar ki biyema wanda suka fi ƙarfin ki kinji”.           Duk da zantukanta sun tunzurani sai ban nuna ba a zahiri na haɗiye, sai ma jinjina mata kaina da nayi, a hankali na amsa da “In sha ALLAHU Mama komai ya wuce. Ranar ɗin ma akasi kawai aka samu”.        Cikin nuna gamsuwa da sake lallashina ta sanya min albarka. Daga haka taja hannuna muka ƙarasa shiga ciki. Duk da nasan banjin shakka ko tsoron kowa a raina sai da nayi addu'a sannan na shiga. Da hayaniyar surutunsu yau muka fara cin karo. Kasancewar ta inda muka shigo duk suke a ƙatoton dining yasa sukai min wani farrr cikin ido. A hankali naja numfashi na fesar ina mai karanto (Hasbinallahu wa-ni'imal wakil) a cikin zuciyata. Da farko ba kowa ya maido hankalinsa kammu ba, dan koda mukai gaisuwa bai fi mutane uku suka amsa ba. Ciki harda Alajah data furta, “A'a Mama Balki ba nace sai mun kammala cin abinci ba?”.       Cike da mamaki Mama Balki ta ce, “Eh da haka kikace Hajiya, amma kuma yanzu da kika kira sai kikace kada mu wuce mintuna talatin shiyyasa kuka taho”. Sosai mamaki ya bayyana a fuskar Aunty Mama. Harma ta gagara daurewa ta ce, “Ni ɗin?”. Da girmamawa Mama Balki ta amsa mata da, “Eh” tana murmushi. Kai Alajah ɗin ta jinjina, sai kuma ta furta, “Kuɗan jirani na kammala dinner to please, dan ina son mu ƙarƙare komai a yau tasan aikinta ni zuwa gobe zan koma”.     Kallon juna Azizat da Arwa suka yi, sai kuma suka saki murmushi suna kashema juna ido ɗaya. “Aunty Mama! Wai waye ake nufin za'a ɗauka aiki anan gidan? Badai wannan mai suffar mamiyo na ruwan ba?”. Kafin ni ko Mama Balki wani yace wani abu Azizat ta faɗa a zafafe har tana wancakalar da spoon ɗin dake hannunta. Kusan atare duk wanda ke'a wajen ya ɗago, a dai-dai nan mayen sirrintaccen ƙamshin turaren Maash kuma ya mamaye wajen. Dan haka hankalinsu ya rabu biyu. Yaran suka shiga gaishesa. Ban ji ya amsa musu ba, dan ban ɗago ba kaina a ƙasa ina ƙoƙarin danne abinda ke taso min akan wannan shegiyar Azizat ɗin. Zungurin da Mama Balki tai min ya sakani kawo nunfashi, na ɗan kalleta. Nuni tai min na gaishesa. Ban musa mata ba a taƙaice na furta, “Barka da dare” a hankali.       Kamar yanda bai amsawa ƙannen nasa ba nima bai amsa min ba. Dan haka na ɗago kaina cikin takaici, dai-dai yana kaiwa zaune a kujerar da ƙyaƙyƙyawar budurwar da zasu iya sa'anni da Azizat tai saurin gyara masa. Kasancewar kujerar itace ta kamar a ƙarshen table ɗin mu kuma muna daga farko tsaye yasa mukai facing juna. Wani kallon tsana naga Azizat na jefama budurwar, sai kuma ta cije lips ɗinta alamar dai akwai abin faɗa a bakinta amma babu dama. Sai daga baya na fahimci agolar gidan dake kusa da itace ta hanata magana ta hanyar riƙe mata hannu. Alajah ce ta katse yanayin da faɗin, “Azizat wai ina ruwanki da yarinyar nan ne? A kanki zata zauna idan ma anan ɗin zata zauna?”.      Baki sosai ta tura gaba. Cikin nuna jin haushi sosai ta ce, “Ni dai bana sonta Aunty Mama. Ba kuma nason ganinta dan na tsaneta. Idan kuma har akace a gidan nan zata zauna wataran sai na kasheta. Ta kwana da sanin marin da taimin wlhy sai ta biya bashinsa da fansar ranta....”           “K! K! Azizat ban gane ba. Mari? Wa ɗin aka mara? Waye kuma yay marin?”. Hajiyar nan da muka samu a falo randa muka zo wadda kuma Bahijja ta tabbatar min itace mahaifiyar Azizat ɗin kuma Yaya ga mahaifin Maash, sannan mai mulkin komai da kowa na gidan ta faɗa a wani irin fusace.         Kallon Alajah Azizat ɗin tayi, sai kuma ta ɓata fuska tana fiki-fiki da idanu. Da alama dai Aunty Mama ce tai mata gargaɗi. Tsawa mahaifiyar tata ta daka mata. Ba ita ba hatta ni sai da naji hanjin cikina sun wakita. A take kuwa Azizat ta fara rattafo bayanin komai daya faru a ranar da safen dalla-dalla harma da ƙarin gishiri da magi..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_ ........Wani irin huci Mahahaifiyar tata take tana kallon Alajah. Idanu Alajah ta rumtse tana ɗan dafe kanta. Sai kuma ta ɗago idanunta akanta. “Please Aunty Nafee relax. Bafa yanda kike tunanin al'amarin b....”      “Kamar ya ba yanda nake tunani bane Mashi'a! Ƴar aiki ta mari mun yarinya a gabanki amma ki gagara ɗaukar mataki sai ma ki hanata sanar min. Wai ke bazaki taɓa canjawa bane ba. Shike nan nagode, ai kin tabbatar min bake kika haifi Azizat ba. Da Imran ko Sahla ta mara ai da kin ɗauki mataki ko. K!! Kuma zaki ci ubanki. Zan sauke miki rawar kan da kika shigo da shi. Ai dama tun randa tazo dake na fahimci idanunki a buɗe suke irin na marasa mutunci.”      Idanu na na runtse sosai dan har cikin ƙwaƙwalwar kaina nake jin hargagin nata. Na tabbatar da ace ta kusa da inda take nake tsaye babu abinda zai hanata kai min duka. Abinda ya matuƙar sake bani mamaki shine babu wanda ya iya tanka mata a wajen hatta shi Alhaji El-Mu'azz ɗin. Balle kuma ƙanin nasa ma. Matansu kuwa kawunansu duk a ƙasa kai kace mala'ika ke kansu. Karo na farko na kai idamuna a kansa. Fruit salad ɗinsa yake sha hankali kwance. Sai ka rantse ma baya wajen dan ko sau ɗaya bai kalli kowa ba duk wannan hargagin da akeyi. Hasali ma a dai-dai sanda Hajiya Mammar ko nace Aunty Nafee kamar yanda Alajah ta ambaci sunanta ke faɗin, “Na soke maganar aikinta na farko. Daga gobe zata fara aiki a sashena. Ke kuma Azizat tashi ki rama marinki”. A kusan tare duk wanda ke a wajen ya ɗago yana kallon ta. Yayinda Azizat ta miƙe zaram cike da farin ciki ta nufo inda nake alamar dai zata zo rama marin kenan. Idanu duk suka zuba min musamman Aalaja da ranta yake a ɓace. Amma shi sai ya ma miƙe abinsa tamkar baiji mima ake faɗar ba. Cike da takun nan nasa mai cike da ƙasaita ya ratsa ta bayansu yazo ta gabana ya gitta kamar ɗazun zai wuce. Wani kalar kallo dana kasa fassarawa ya jefa min....         “Muhammad!”.     Alhaji El-Mu'azz ya faɗa dai-dai zai raɓani ya wuce gaba ɗaya.. Amamakina sai naga ya tsaya cak. Tamkar bazai juyo ba sai kuma ya koma da baya tamkar wanda akama dole a hankali ya amsa da, “Yess Paah”.      Idanu mahaifin nasa ya ɗan tsira masa. Sai kuma yay ɗan murmushi cike da kulawa ya ce, “Ba zaka ci abincin ba kuma? Naga fruit salad ɗin ma kaɗan kasha fa”.      A daƙile, sai dai cikin sanyin Muryar nan tasa ya ce, “I'm okay Paah. Kaina namun ciwo ina son na ɗan kwanta”.      Sosai fuskarsa ta nuna damuwa. Hakama sauran duk sai kowa ya maida hankalinsa a kansa musamman Azizat da budurwar nan data gyara masa wajen zama sanda yazo. Dan har wata ƴar zabura sukayi a kusan tare. Cikin jimantawa da kulawa sosai suka shiga masa addu'a. Kansa kawai ya jinjina musu yay wucewarsa ya fice. Sosai zuciyata ke ƙara jinjina rashin mutuncin mutumin nan. Ashe bamu ƴan waje kawai ba hatta family ɗinsa basu tsira da wannan baƙin halin nashi ba. Lallai sai a jinjina masa. Ganin yanda duk suka maida hankalinsu a kansa nasa ƙafa na taɗe Azizat dake ta leƙensa kamar mai son binsa. Razananniyar ƙarar data fasa ya saka kowa zabura sukayo kanta.      Da wannan damar Mama Balki taja hannuna da sauri hankalinta tashe muka sulale muka fice. Ashe ita taga abinda nayi, suko sai suke tambayar miya faru? Yaya akai ta faɗi. Oho mudai tuni mun ware bamu san yanda suka ƙare ba kuma.... 🤣🤣ALLAH ya shiryeki Sam-G. ❤️★❤️★❤️      “Gwaggo maganar auren nan dama nake son mu tattauna kafin ki wuce. Dan ina son ayi komai a gaggauce cikin watan nan”.      Cike da ɗunbin farin ciki Gwaggo Gudidi ke kallon Abba dake maganar, ta saki dariya tare da yin guɗa. “Kai kai da ace na iya ghuɗa babu abinda zai hanani tsallarata sama har sai duk ƴan anguwa sunji Imamu. Ka daɗe baka sakani a farin ciki irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Amma ince dai ƴar mutunci ka sama mana ba irin wannan matar taka ba dan bana son a sake yin jifar gaffiyar ɓaidu”.       Kai Abba ya girgiza yana ɗan murmushi, “A'a Gwaggo in sha ALLAHU sam ba halinsu ɗaya ba. Yarinyar da suka doka ɗin ce dama.”      “Kai kai to Masha ALLAH. Aiko kayi ƙyan kai, dan hakan da zakayi shine babban murtani da zaka maidawa matarka tasan ka haifu cikin uwa da uba. Amma kuma ai naji yaran na faɗin ta gudu tun a ranar da abin ya faru? Ko kasan inda take ne?”.            “A'a Gwaggo ban sani ba. Amma dai ta sanar min da garinsu. Nasan kuma insha ALLAHU can ɗin zata nufa tunda Alhaji Sadisu ya bincika daga inda Jalilahn ta ɗakkota ance bata koma can ba. Dan haka nake son muyi azamar bin bayanta tun kafin abin yayi nisa”.       “Eh to hakan ma dabara ce ai. ALLAH ya bada sa'a da nasara. Yaushe zaku je ɗin?”.      “Da dai gobe idan ALLAH ya kaimu ne. Sai shi Musaddiq ya jamu dan ni bazan iya tuƙi ba. Alhaji Sadisu ko baida jimirin yin tuƙi a doguwar tafiya sam”.      Ɗan jimm Gwaggo tayi alamar tunani, dan in bata manta ba Musaddiq ya sanar mata gobe ne zai je gwaji da akace za'a musu a inda aka ɗaukesa aiki. Da ɗan sauri ta girgiza kanta. “A'a inaga shi Jafaru sai ya jaku kawai dan yasan ƴan tumaki sosai tunda shima matarsa ƴar wajen garin ce. Kaga ko ai faɗuwa tazo dai-dai da zama ba sai anta faɗi tashin tambaya ba”.        Cikin nuna farin ciki da gamsuwa Abba ya shiga tabbatar mata da hakan yayi, ya ɗora da godiya. A take kuma babu ɓata lokaci yay kiran Jafaru ɗin. (Jafaru shine ɗa na biyu a wajen Gwaggo Gudidi. Kusan sa'anni suke ma da Abba dan komai na rayuwarsu tare sukayi. A dalilin Mom tarayyar tasu ta samu rauni. Dan yanda take nuna bata ƙaunar ƴan uwansa su raɓesa duk wanda yazo sai ya tafi da tabon rashin mutuncinta yasa Jafaru janyewa daga jikin Abba. Saboda akwai wani zuwa da yayi Mom ta cimasa mutunci harda ƙwallarsa. Daga lokacin ya tattara Abba ya ajiye gefe sai dai su gaisa sama-sama ta waya ko idan wata sabgar ta haɗasu ta dangi ko in sun haɗu a gidan Gwaggon. Abin na damun Gwaggo amma ta gagara sasantasu, sau yanzu ga dama ta samu kuma)....          ✨💫✨💫✨💫     Ko kaɗan Mama Balki batai min faɗa game da abinda naima Azizat ba. Sai ma Sosai yanda ta nuna tashin hankalinta ita da su Bahijja game da batun komawata aiki sashen Hajiya Mammah ya bani mamaki. Dan na sake fahimtar al'amarin babba ne. Duk da kuwa Bahijja ta ɗan bani labarinta a ƙaice ni banga wani abun tsoro tattare da ita ba, idan masifa ce na saba data Mom da ƴaƴanta ai. Sambatu suke sosai da nuna jimantawa har Mama Balki na faɗin na gudu kawai tun ma kafin komai ya faru. Zata saka mijinta ya taimaka min na fita a daren yau.         Murmushi na saki a hankali duk da kuwa nima ina jin shakkun al'amarin a zuciyata. Sai dai wani sashe na ƙarfafani dan koba komai zan samo labarai. Haka kawai kuma ina son sanin gaskiyar labarin tushen komai. Atake naga fuskokin masu dariya da nuna farin ciki a kaikaice a cikinsu na sauyawa a dalilin murmushin nawa. Nima sai kawai na basar da canja yanayina. Ƙwallar ƙarya nayi ƙoƙarin tarama idanuna. Tare da nuna tashin hankali ina mai roƙon Mama Balki data taimaka min na gudu ɗin... A bazata mukaji an saki tsaƙi, kusan mu dukanmu muka kalli mai tsakin. Ba kowa bace face aunty Kubra. Yanayin shock na gani a fuskar Mama Balki, da alama dai ta fahimci tayi ɓaranɓaramar sakin zancen gaban kowa. Sai dai bata iya cewa komai ba       Cike da taɓe baki Aunty Kubra ta cigaba da faɗin, “Mama ina baki shawarar ki rufama kanki asiri. Ke dai kinfi kowa sanin halin Hajiya Mammah a gidan nan. Sannan ita ɗin ba ita ta jama kanta ba. Banda kauɗi da rawar kai uwarwa ya kaita marin ƴar masu gida. Jarumta tafi wani a cikinmu da muke haƙurin shekara da shekaru da su ko mi? Kinga yanzu ai ya rage nata ta ajiye kauɗinta da iyayi gefe ta nemawa tsoffinta kuɗin cin tuwo cikin sallama. Idan ba hakaba wataran ba sashen Hajiya Mammah ba Sashen Hajiya Babba zasu kaifafa ko kuma da karnukan gidan nan wlhy zasu haɗata”. Daga haka ta miƙe tai ficewarta tana wani rausaya da girgiza jiki.       Shiru kowa ya gagara cewa komai, sai shashshekar kukana kawai kake ji. Kusan mintuna biyar Mama Balki tayi ƙarfin halin bama Bahijja umarnin tafiya dani ɗaki na kwanta. Babu musu Bahijja ta miƙe ta kama hannuna. Sai naga itama A'i ta miƙe fuskarta cike da tsantsar damuwa itama ya kama ɗayan hannuna....        Duk yanda naso rintsawa barci a wannan daren kasawa nayi. Dan komai ya tsaya min arai ne. Duk yanda nake jin rashin damuwa game da yin aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin wani sashi na zuciyata na tsoratar dani da nuna min illar hakan, dan na fahimci matar bata da mutunci sosai. Dan duk mai hankali ya auna yanda kowa ke nuna damuwarsa akan batun zai sake tabbatar da bada wasan yara bane al'amarin. Ganin yanda zancen yaƙi barin raina sai kawai na tashi na ɗauro alwala na fara nafilfili. Har asuba ban runtsa ba sai da nayi salla..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .......Ina idarwa na ɓingire a wajen sai barci. Ban tashi farkawa ba sai da A'i ta tasheni wai Hajiya Mammah na kira na. Yanda take maganar cikin nuna tsoro da damuwa ya sakani tsira mata ido. Sai dai bata bani damar mata tambaya ba ta juya sukuku ta fice tana faɗin, “Kiyi sauri ki shirya muje kar mu sake wani laifin kuma. Dan ga Mama Balki can tasha maruka akan guduwar da kukayi jiya da dare duk da ƙaryar kareki da tayi kan baki da lafiya ne shiyyasa”.      Sosai naji wani irin masifaffen ɓacin rai. A take ta bududdugin ta motsa (zuciya) na shiga taunar lips da ƙarfi-ƙarfi tamkar zan hudashi. Gaba ɗaya wata irin tsanar matar mai tsananin gaske ta shiga zuciyata. Yanzu dan ALLAH babbar mace kamar Mama Balki ce za'a mara wai. Kai wannan wane irin gidane haka na marasa tarbiyya da girmama mutane. Dan kawai mutum nada dukiya sai akace zai iya taka kowa a yanda yake. Kaicon wannan rayuwa mara fasali da rashin sanin daraja da kimar ɗan Adam.       A gurguje nayi wanka na shirya cikin Uniform ɗin da A'i ta ajiye min. Koda na fito a falo na sameta tsaye tana jirana. Kallon juna mukayi. Ta ɗan kafeni da kallo sai dai batace komai ba tayi gaba na bita a baya... 💞👉💞👉💞     “Alhamdullah su Abba sun isa ƴan tumaki lafiya. Tafiyar da Mom bata da masaniya a kanta, dan har yanzu Abba baya shiga harkarta. Ita kuma ta tada hankalinta sunata bibiyar teachers domin sabunta ayyuka akan Abban dan ta lura komai fa na neman canjawa. Kullum cikin ƙaryar fita take duk da kuwa yana gida yana jinya. Bai taɓa hanata ba, kamar yanda Gwaggo Gudidi bata taɓa tanka musu ba. Da tambaya da kwatance suka gano gidan su Halime da ƙyar kasancewar sun sami cikakken address wajen mai kawosu aikatau daga ƙauyen. Wadda da ƙyar suka samu ƙawar Mom ta sanar musu bayan sun danƙa mata kuɗaɗe. Tako kai su amma ta roƙi Abban da kar ya sanarma Mom ita ta faɗa, duk da kuwa ita bata san manufar Abban ba. Ya sanar mata ne kawai zasu bincika idan Halime taje gida kar a samu kuskure tayi wani wajen daban. Ta gamsu ɗari bisa ɗari dan tanama Abban kallon girmamawa duk da tasan aminiyarta ta daɗe da gamawa da shi. Koda yake itama ɗin ta gama da nata mijin ai duk da basu taɓa tarayya da Mom wajen zuwa gidan teachers ba. Kowa nayin al'amarinsa ne a bayan fage..         Sun ɗauki kusan mintuna talatin a gidan mai anguwa da sukai dabarar fara zuwa kafin Baba da aka aika kira ya ƙaraso. Tun shigowarsa Abba keta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, dan ko makaho ya laluba yasan shine mahaifin Halime saboda kama da sukeyi matuƙa tamkar yayi kaki ya ajiyeta. Sake gyara nutsuwa Abba yayi, hakan har ya saka Alhaji Sadisu sakin murmushi. Bayan Baba ya gaisa da mai anguwa ya juyi gasu ba. Kafin ma ya gaishesu su sun shiga gaida shi. Dan ko babu batun abinda ya kawosu zai girmesu gaskiya. Bayan an kammala gaggaisawar mai anguwa ya nunama baba su Abba.        “Malam Yusufa baƙine dama suke neman gidanka. Naso saka yaro ya rakasu sai suka buƙaci haɗuwa da kai anan shiyyasa na aika akayi kiranka”.     Da ɗan nuna alamun mamaki Baba ke kallon su Abba. Ganin yanda Abba ya duƙar da kansa Alhaji Jafaru ya fara magana a nutsensa. “Ni sunana Jafaru, wannan sai ƴan uwana Alhaji Sadisu da Alhaji Imam. Baba baka Sammu ba gaskiya. Wannan ɗan uwan nawa Alhaji Imam shine mai gidan da ƴarka Halimatu take zaune acan birni.....”       Sosai Baba ya waro idanu, tare da sakin salati ya ce, “Kai kai Masha ALLAH. Bawan ALLAH ashe baka rasuba Sa'adiyya duk ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tunda ta iso garin nan kwana biyar kenan kullum bata da aikin daya wuce kuka. ALLAH mun gode maka”.            Murmushi Abba yayi cike da jin sanyi a ransa Halimensa ta damu da shi. Murya a sanyaye ya ce, “ALLAH kam shine abin godiya Baba. Nima kuma ina ƙara gode masa da ya zamto gida tayo ba wani wajen ba. Dan muna can hankalinmu duk a tashe da ƙyar aka samo wadda ta ɗauketa daga nan ta bamu address.”      Sosai Baba ya nuna jin daɗinsa da wannan kulawa. Fuskarsa washe da murmushi shima ya ce, “Ai dama duk tsanani Sa'adiyya bazata nufi ko ina ba sai gida. Nima Nagode sosai da wannan kulawa taku, lallai na yarda da gaske yarinyata tana a hannun mutanen kirki. ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara lafiya”.     A tare duk suka amsa da Amin. Kafin Alhaji Sadisu ya ɗora da bayani bayan sun ɗan yi jimm na wani lokaci. “Baba dan ALLAH idan bazaka damu ba muna neman wata alfarma ne”.       “Ku faɗi komi kuke buƙata a gareni kai tsaye in dai baifi ƙarfina ba zan muku shi in sha ALLAHU”.    Cike da jin daɗin furucin nasa Alhaji Sadisu ya cigaba da faɗin, “Muna neman alfarmar ka bamu auren Halimatu”.        Ba baba kawai ba hatta da mai anguwa sai da ya waro idanu sosai cikin nuna ƴar tsorata......        🌛🌟🌜     Kallo ɗaya nayima Mama Balki dake gurfane gaban Hajiya na ɗauke idanuna zuciyata na suya. Da ƙyar na iya control ɗin kaina nima na kai durƙushe. Latse-latsenta take a laptop tamkar batama san da zuwan namu ba. Gefenta Azizat ce kwance itama tana latsa wayar fuskarta mamaye da fara'a. Sai da ta mula dan kanta sannan ta ɗago bayan ta rufe laptop ɗin. Fuska a yatsine kamar taga kashi ta daka min tsawa. Dakewa nayi batare da nuna razana ba. Sai cemata da nayi “Ina kwana”.         “Daban kwana ba ƙya ganni firiritacciya. Ke mai ido a tsakar kai kinzo cin arziƙi gidan mutane har da marin ƴar masu gida ko?”.      “Ko kuma ƴar cin arziƙin itama ba”. Na faɗa ƙasa-ƙasa.      “What! Mi kikace?”.    Ta faɗa a matuƙar tsawace. Idanuna na ɗago na kalleta fuska a shagwaɓe. “Nifa bance komai ba Mamma. Please ki daina faɗan firgitani kike sake yi”.       Ba ita ba hatta Azizat ɗin Tata sai da ta juyo tana kallona da mamaki ƙarara a fuskarta. Balle su Bahijja da suka waro idanu da wangale bakuna. Niko yi nai tamkar ban gansu ba na sake shagwaɓe fuskata da taɓeta. Sai kuma na ɗauka ruwan dake a cikin kofi a gabanta na miƙa mata. “Kisha ruwan sanyi Mamma zuciyarki zatayi sanyi. Ba'a son masu shekaru irin naku da yawan faɗa za'a iya samun matsalar hawan jini daga nan ta zama ta zuniya”.       Galala ta sake yi tana kallona. Niko na tsatstsareta da idanu ina sake tura baki da marairaice face. Da wani irin masifar ƙarfi ta cije lips ɗinta tamkar zata hudasu. Sai kuma tasa hannu ta kaɓar da kofin hannun nawa. A take ruwan ya tarwatse mana a jiki har ita. Cikin masifar ƙaraji da wutar bala'i ta ce, “Balki!!!”. A razane Mama Balki ta amsa tana miƙewa daga durƙuson da tayi zaram. “Na.. na... Na'am Hajiya”.      “Ɗauki yarinyar nan ku ɓace min anan kafin na haukata jikunan ku da duka ku duka. Na kuma fasa aikin nata a sashena ki kaita sashen Hajiya Babba ta gyaro shi kafin nan kafin azhar”.           Wani irin waro idanu na masifa Mama Balki tayi, cike da tashin hankali da suɓutar baki ta furta, “Sashen Hajiya Babba kuma Hajiya?”.       “Ko bazaki kaitan ba ne?!!”.    Cikin rawar jiki mama Balki ta shiga girgiza kanta da faɗin, “To to to Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki, za..zan kaita mana.” mama Balki ta faɗa tana kama hannuna jikinta na rawa sosai. Da ƙyar na iya danne dariyar dake cina har muka baro wajen, dan tana ambaton Hajiya babban naji tamkar na dirga tsalle dan daɗi. Muna kammala hawa upstairs ɗin a stairs ɗin ƙarshe na ɗan kallo ƙasan, sai da na haɗiye dariyar dake cina sannan na kwaɓe fuska kamar zan fasa kuka. “Mammah dan ALLAH ni dai ina neman alfarma. In dai akwai matsala da zarar kunji na banka ihu a kawo min ɗauki koda sassaƙa-sassaƙan garadan nan na bakin ƙofar gida ne a turamin idan ma ku bazaku iya ba”.        A matuƙar fusace ta watso min muguwar harara da gwala-gwalan idanunta “Sai dai a turo miki Ubanki. Ƴar iskar yarinya sheɗaniya. Da alama kema dai mahaukaciyar ce get out of my side kafin na canja miki kamanni”.      Baki na tura mata cikin sake narke fuska da yamutseta na ce, “Ai dai ubana yana aljanna in sha ALLAHU badai shi b....”          Kafin ma na kai ƙarshe Mama Balki ta fisga hannuna jikinta na rawa. Duk yanda naso ta sakan taƙi yin hakan har sai da muka ɓacema ganinsu. Kamar zata saki kuka ta ce, “Kandala baki da hankali ko? Yanzu wannan hukuncin da suka zartar a kanki bai isheki ishara ba ki koya kimtsa bakinki? Dan ALLAH ƴar nan kada ki sakamu a masifa mutanen gidan nan sun wuce fiye da yanda kike tsammani a fitina wlhy. Kiyi fatan Alhaji ƙarami bai bar gidan nan ba yazo ya fiddaki a wajen nan da wuri, zanje na samesa yanzun nan”.       Da sauri na ce, “A'a mama dan ALLAH kada ki kirashi. Miye dan tace nazo nayi aikin anan?”.      “Yarinyar nan baki da hankali, wautarki tayi yawa wlhy. Kandala wannan sashen da kike gani baida maraba da rami mai kwazazzabo da in ka faɗa a cikinsa sai abinda ALLAH yayi. Gara kiyi aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin dan ita masifa ce kawai da takura, amma nan ranki ma zaki iya rasawa. Ni dai ki jirani anan zan je na duba Alhaji ƙaramin ALLAH yasa bai fita ba”.       Ƙasa kawai nayi da kaina batare da nace mata komai ba.. Ita ma sai bata sake magana ba tai gaba.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ___________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ ......Riƙota nayi ina girgiza kaina. Ta tsaya tana kallona. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Kiyi haƙuri Mama ki buɗe min zan gwada na gani. Koba komai itama mutum ce kamar mu. Muma kuma bamu san ya rayuwa zatai damu ba anan gaba. Dan ALLAH ki buɗe min kawai ALLAH yana tare da ni”.       Sosai alamar sanyayar jiki ya bayyana a gareta na jin kalamai na. Dan haka ta nufi ƙofar dake a falon batare da ta sake cemin komai ba. Bayanta nabi ina mai jin tausayinta. Babbar mace kamila yanayin rayuwa yasa tana gurfana a gaban wadda bata wuce sa'arta ba. Lips ɗina na ciza. Kafin na furzar da iska nabi bayanta nima. Sosai tsaruwar falon farko na sashen yay matuƙar ɗaukar hankalina. Fes yake yana ɗaukar ido saboda kayan alatun da yasha. Da alama ana gyarashi kullum. Kamar zanyi magana sai kuma nayi shiru dan ganin yanda Mama Balki ke ɗari-ɗarin buɗe ƙofa ta biyu. Sai da ta runtse ido da karanto addu'a sannan ta murɗa handle ɗin. Da sauri tayo baya tamkar mai shirin zurawa a guje. Kallonta na tsaya yi kawai cike da nazari, sai kuma na sauke numfashi. “Uhhh mama, inaga kije kawai daga nan babu damuwa zan ƙarasa ni kaɗai.”       Waro idanu Mama tayi, sai kuma ta marairaice fuska idanunta na cika da ƙwalla. Ƴar nan dan ALLAH kiyi addu'a kinji, ko ki zauna a wannan falon sai zuwa anjima ta tashi ki gudo, Kinga shike nan an rabu lafiya”.       Murmushi mai kama da yaƙe kawai na mata ina jinjina kaina alamar to zanyi. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma ta haɗiyi yawu jiki a sanyaye ta juya ta fita tana waigena. Ni dai kallonta kawai nake har sai da ta maida ƙofar falon ta rufe a hankali. Sai kuma ta sake buɗewa. “Karki sake ko kulle kowacce ƙofa dan ALLAH Kandala. Ki barsu a buɗe yanda zaki samu damar gudowa koda an sami akasi”.     Kaina na jinjina mata nan ma ina murmushi. Ta sake ɗan jan ƙofar batare data rufe duka ba ta barta. Shiru nayi kawai a wajen tsaye har zuwa wani lokaci. Ni kaina a tsoracen nake. Amma inata ƙoƙarin dakewa kun dai san ɗan jarida da jarumtar wahala. Shiru sashen yake babu alamar motsin mai rai, sai ɗan yanayin kamar bashi-bashi dake bugowa daga ƙofar da Mama ta buɗe. Ƙofar na tsurama idanu na wani lokaci, kafin nayi ƙundun balar nufarta cikin sanɗa da ambaton sunan UBANGIJI...... 📯📯📯📯     Farin cikin da Musaddiq yake a wannan rana bazai taɓa musaltuwa ba a zahiri. Sai dai ya barma UBANGIJI komai. Tsaff ya fito cikin shirinsa na shadda ruwan ƙasa mai haske harda hula. Sai ƙamshin turarensa yake mai sanyin daɗi. Hannunsa riƙe da takardunsa yake ƙoƙarin kulle ƙofar. Juyowa yay da sauri jin kamar mutum ata bayansa yana kallonsa. Ilai kuwa ido huɗu sukai da Umma mahaifiyar Mom da alama isowarta gidan kenan. Kauda tsarguwar kallon ƙurillar da take binsa da shi yayi, tare da sakin nutsatstsen murmushinsa ya ƙaraso inda take. Cike da girmamawa ya ce, “Sannu da zuwa Umma. Ina kwana? Anzo lafiya?”.       Cikin ɗan daburcewa da dawowa a hayyaci ta shiga amsawa bakinta a washe. Dan harga ALLAH yaron ya gama firgita mata zuciya da guntun lissafin ta. Wani kalar mahaukacin sirrintaccen ƙyawu fa taga yayi mata da ƙiba harda haske. Ga arziƙi muraran ya nuna a jikinsa kai kace ma shine ɗan masu gidan ba ɗan riƙo ba. Dan ko mahaukaci ya kallesa ya kalla Abbas yasan akwai banbanci da tazara mai yawa ta cigaban rayuwa....      “Ki shiga Umma ai su Mom ɗin suna nan ciki”. Ya faɗa cikin katse mata tunanin data lula. Firgigit kuwa ta dawo a hayyacinta. Sai kuma ta washe baki cikin in ina ta ce, “T... t.. to ɗan nan nagode kaji, ALLAH ya muku albarka ya ƙara arziƙi. Bari na shiga ɗin dai to”. Ta ƙare maganar tana tafiya da waiwayensa a lokaci guda har taci tuntuɓe tana neman faɗuwa. Ta dai samu ta dafe gini idonta a kansa har lokacin ga baki a washe kamar sakara.       Shi dai Musaddiq cike da al'ajabinta yay ficewarsa. Kaɗan-kaɗan sai ya kalla kansa ko zaiga abinda takema kallon ƙurulla a jikin nashi. Amma sai baiga komai ba. Haka dai ya tare napep ya shiga komai na masa kai-kawo a rai da zuciya. Koda ya iso gate ɗin companyn sai da ya nuna ɗan katin da ogansa ya bashi sannan aka barshi ya shiga. Sosai yake jinjina ƙudira da rahama ta UBANGIJI. Dan gaskiya wannan Company ya matuƙar tafiya da imaninsa. Gini ne iya gini da baka iya ƙuresa da idanu. Ga ma'aikata nata faman kai-kawo da securitys. Ga kayan aikin tako ina da zai tabbatar maka da komai fa da gaske ake babu wasa. Da taimakon wani security akai masa rakiya office ɗin Manager.....          💦✨💦✨💦    Ji Abba yay tamkar ya tashi ya buga ihu da tsalle dan farin cikin hukuncin Baba. Domin ya tabbatar musu in dai Halime na son Abban zai bashi ita. Hakan yasa aka aika aka kira Halime. Koda tazo taci karo da su Abba sai da ta nuna ƙololuwar mamakinta har ta gagara yin magana sai da Babanta yay mata magana ma ta iya gaishesu muryarta na rawa. Zata ɗora da zance Abba daya san mi zata iya faɗa yay saurin katseta. Dan baya fatan ta tona asirin komai musamman akan abinda ya faru a randa ta gudo ɗin, saboda ya fahimci bata sanarma su Baban komai ba. Shirun kuwa tayi kamar ta fahimci abinda yake buƙata, daga haka mai anguwa ya sanar mata abinda ya kawo su Abba. Sake diriricewa kuwa tayi tana faman zare idanu. Da ƙyar Abba ya iya danne dariyarsa. Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu kuwa sai da suka dara kaɗan. Mai anguwa ma dai yayi kaɗan kafin ya ɗora da tambayarta ko tana son Abba ɗin.... Ai baima rufe baki ba suka tsinceta can ta zura a guje cikin gidan mai anguwar.         Basu Abba ba hatta da Babanta yanzu kam sai da ya dara. Fuskarsa da sauran dariyar ya dubi Abba. “Imamu kaga fa shirmen mutuniyar taka. Anya zaka iya da ita? Dan Sa'adiyya akwai wauta a tattare da ita ta ƴaƴan fari. Ni kaina wani abun idan tayi a wasu lokutan ƙuleni sukeyi. Sai dai kuma akwai himma ga biyayya. Duk abinda kaso daga Sa'adiyya zaka samesa. Gwargwado na bata ilimin addini, na zamanin ma ta fara wasu dalilai yasa dole aka yankesa....”           Fuskar Abba da murmushi kansa a ƙasa ya ce, “Karka damu Baba, ni ɗin ita nake so ba shirmen ba. Sannan nagartattun halayen nata da tarbiyyar ta suka jani gareta. Dan wauta wataran zata daina in sha ALLAHU yanzu ma akwai ƙuruciya ne”.       “To Alhamdullah Imamu, naji daɗin jin wannan batu daga gareka. Dan haka ina sake maka albishir da baka auren Sa'adiyya. Kuma bana son kubar garin nan sai an ɗaura, in har da sadaki a tare da kai da anyi sallar zuhur yanzu kawai sai ayi”.      Wannan furuci shi ya sake rikita Abba. Dan baba bai kammala rufe baki ba ko ya zaro kuɗi masu yawa a aljihunsa ya dire gaban Baban. Dariya su Alhaji Sadisu suka sanya masa. Cike da tsokana Jafaru ya ce, “Ai ka bari dai ni na biya maka Alhaji zumuɗinka”.      Dariya su mai anguwa suka saka da Baba. Yayinda kunya ta kama Abba ya kaima Alhaji Jafaru harara yana ɗauke kansa gefe. Da ga haka suka miƙe domin haramar masallaci....       Al'amarin tamkar almara bayan idar da sallar azhar aka dakatar da mutane. Mata dake cikin gida sai shelanta ɗaura auran Halimatussa'asuyya Yousufa da angonta Imam Gwarzo suka jiyo. Bakin Abba kamar zai taɓa kunne. Sai faman gaisawa yake da mutane cike da farin ciki. Kafin kace minene har labari ya fara yawo a gari. Gidan mai anguwa aka koma da su Abba. Sai da sukaci abinci sukai nak sannan Baba yay musu jagora zuwa gidansa kamar yanda ƙannensa biyu da akai komai da su suka bada shawara....         💢💦💢💦💢          A hankali na tura ƙofar idanuna a rufe na shiga cikin sanɗa. Yayinda zuciyata ke wani irin harmutsawa saboda ƙarni da tsamin dake tashi sosai a falon. Abin mamaki da al'ajabi shima ƙaton falone da aka zubama komai na more rayuwa da ƙawa. Sai dai mafi yawan abinda ke a cikin nasa an gama faffasashi. Dan hatta da television dake a jikin bango an mata rugu-rugu. Ta saman farin Mable's ɗin kuwa mai tsananin sheƙi tako ina fitsari ne har da su katsi, abinci ruwa da wasu nau'in kayan ciye-ciye kamar su fruit duk sun ruɓe. Hatta a saman carpet ɗin ma da ya gama fita a hayyacinsa al'amarin ba'a magana. Kai labuloli kansu wasu an fincikosu wasu kuma an goge datti da su. Sai ɗigo-ɗigon jini a wajaje daban-daban shima har a jikin bango. Bamma san sanda zuciyata ta karye ba sai ɗumin saukar hawaye da naji a saman kumatu na. Sosai nayi kuka a wajen kafin na cigaba da ƙarema falon kallon. Akwai dining table ta can gefe da aka ƙawata a cikin glass da ya raba tsakaninsa da falon. Sai dai shima an gama hargitsashi wasu kujerun ma a karye suke. Table ɗin ma kansa tuni an maida sama a ƙasa. Ta ɓangaren damata akwai ƙofofi guda huɗu, sai tsakkiyarsu ƙafar bene da akai ma wani kalar style mai ɗaukar hankali da birgewa. Numfashi na sauke a hankali nan ma tare da yunƙurawa na nufi ƙofifin, har na kusa sai kuma na tsaya cak saboda shawarar da zuciyata ta bani akan fara gyara wannan falon koda ma zan shiga cikin tunda ban san mizan tarar ba ko tarbar da zan samu daga mai sashen......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ .......Komawa nayi baya ta hanayar dining ɗin nan ina mai addu'ar samun kayan shara. Ƙofar kitchen ɗin akwai key a jiki, dan haka na murɗa a hankali, sai da na leƙa cikinsa sannan na shiga gaba ɗayana ina sauke numfashi. Babu komai a cikinsa shima. Sai dai shi ɗin fes yake babu wani datti sai ƙura ta rashin gyarawa. Sosai kitchen cabinet ɗin da aka ƙawatashi da shi yay matuƙar ƙyau kamar ka zauna kayita kallo. Ganin ina neman shagala a kallon cabinet na zabura neman kayan shara. Cikin Sa'a kuwa sai gasu na samo a store dake cikin kitchen ɗin duk masu aiki da wuta. Cike da ɗoki da zumuɗi na kwaso duk abinda zan buƙata. Tun daga store ɗin da shima babu tarkace sosai na fara gyarawa har zuwa kitchen, sannan na fito dining ɗin. A nan kam na jigatu kafin na dawo falon mai gayya da aiki. Tun ina yin aikin da marmari har na fara jigata. Amma haka na dinga dauriya. Sau biyu ina jima hannuna ciwo. Na maida abinda zai iya maiduwa. Wanda suka tashi a aiki na tattarasu na fitar can barandar da aka ƙawata ta waje bayan na zuge labule na ganta. Ashe wajen glass ne amma an rufesa da wani irin abu mai taushi nasan duk dan kar taji ciwo ne. Kaf labulolin data jeho na tattaresu dan duk abincine da fitsari a jikinsu. Hakama carpet ɗin na cireshi shima. Hatta wanda sukai min nauyi da yawa haka na dinga turasu, sai santsin Mable's ɗin ya dinga taimaka min har na kaisu balcony ɗin duka.      Ni kaina yanda falon ya dawo a hayyacinsa sai da nayi murmushi. Na baɗe ko ina da freshiners masu ƙamshin daɗi dana gani a wata drawer. Ac na kunna kaɗan dan falon ya sake samun nutsuwa. Ganin lokacin salla na neman ƙuremin na dawo falon farko nayi salla ganin akwai toilet a cikinsa shima. Duk da matuƙar gajiyar da nayi da buƙatar hutu da nake da shi haka na sake miƙewa na koma. Yanzu kam ina ƙara ƙarfin addu'a a bakina na tunkari ƙofofin ɗakunan nan biyu. Ta farko na murɗa amma sai na jita a kulle. Na koma kan ta biyu sai naji ta buɗe ita. Da sauri nayi baya saboda wani irin wari dake fitowa a cikinsa mai ban tashin hankali. Take zuciyata da cikina suka shiga yamutsawa, dole na fito a guje zuwa bayin dake a falon farko. Amai sosai na shiga yi kamar zan amayar da kayan cikina. Tun ina amaryar da ruwa dana sha kawai har na koma yunƙuri kawai babu komai, da ƙyar na samu nutsuwa na wanke bakina na fito ina hakki. Har na yanke shawarar fita na haƙura zuciyata ta zabureni akan muhimmancin aikin lada. Hawaye naji sun cika min ido dan zuciyata na ayyana min idan Umminmu ce a wannan halin kenan zanji ƙyanƙyamin kasa tsaftace mata wajen kwananta? Da sauri na shiga girgiza kaina tamkar mai magana da mutum. Bamma san lokacin dana zabura na koma ba. Sai dai ina zuwa ƙofar na zame vail ɗin kaina na nannaɗe fuskata gaba ɗaya har zuwa hancina sosai. Amma duk da haka ina ɗan jin warin kaɗan-kaɗan. Haka dai na dake ina karanto addu'a a bakina ga hawaye na ɓulɓulo min cikin idanu saboda tausayi da tashin hankali. Yanzu nan ɗan adam mai rai, mai gata ne a irin wannan ɗakin? Bily ban san yaya zan musalta miki ba. Amma duk yanda kike hasashe abin ya wuce nan, ƙazantace sosai a ɗakin mara daɗin misali. Amma haka na duƙa na fara tattarewa ina kuka. Dole naje na kwaso labulolin dana cire a falo da burin wankesu na dinga naɗe ƙazantar a ciki. Sai da na tattare komai tare da fito da katifar ɗakin da ƙyar dan itace kawai anan sai labuloli da wadrobe ta jikin bango. Ina jin mutanen gidan sun fara hayaniyar wari-wari, dan da gayya na kaita falon can na farko da zaka iya hanga ta dawn stairs. Juyawa nayi na koma ciki ina ayyana kowa yau dan ubansa sai ya shaƙa shima. Shine punishment ɗin ku. Sam ban kawo cewa tana a cikin ɗakin ba, dan ganin ban ganta ba a farko kuma har nayi kusan kashi ɗaya bisa ukun gyarashi yasa nai zaton tana ɗayan ɗakin ne ko can sama hawan ƙarshe. Toilet na nufa, cike da tsantseni na buɗesa. Bamma san na daka uban tsalle ba nayo baya cikin matuƙar razani jikina na karkarwa. Gurnani da nishin dake fitowa a toilet ɗin yasa hankalina ya sake tashi, a take hoton abinda na gani ya shiga dawo min da kansa. Mutum zaune sarƙa a ƙafa da hannayenta an saƙalo jikin fanfo. Gaba ɗaya hannunta da ƙafafun sunyi jina-jina alamar son ƙwace kanta ya kaita ga jin ciwon. Kanta a duƙe yake shiyyasa banga fuskarta ba, sai gashinta dake a wani irin cirkuɗe danƙare a kanta mahaukaciya dai cikakkiya. Tausayi da tashin hankali ya sakani durƙushewa a wajen ina kuka. Nafi minti uku sannan na miƙe na sake komawa toilet ɗin. Sosai idanuna sun gama rufewa, nama bar tunanin zata iya cutar dani kamar yanda Bahijja ta faɗa tana duka. A gabanta na zube zuciyata a dake na shiga kwance sarƙar ƙafafunta da suka kumbura suntum sukayi jina-jina. Har na kammala kwancewa bata ɗago ba, sai nishin nan dai mai ban tausayi da tashin hankali kamar wadda numfashi ke shirin barin gangar jikinta. Da ƙyar na iya kammala kwance sarƙar ƙafafun, na shiga shafa ƙafar hawaye na cigaba da zararo min. Wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ta sauke. Sai kuma ta ɗago a hankali. Wani irin bugawa da sauri-sauri zuciyata ta shiga yi saboda ganin yanda fuskarta tayi kaca-kaca da tabbunan raunuka, sai sabbin da har sun fara bushewa suma kusan uku. Gaba ɗaya baka iya shaida kamaninta saboda dauɗa data gama mamayeta. Dan kayan jikinta ma duk a yayyage suke fata-fata. Rawa jikina ya cigaba dayi, hawaye masu zafi na sake gudu a cikin idanuna. Bamma san lokacin da na kai hannuna saman fuskar tata ba ina shafawa. “Kiyi haƙuri Ummi, dan ALLAH kiyi haƙuri, ALLAH ya gaggauta saka miki, ALLAH ya baki lafiy.....” kuka ya sarƙeni na gagara ƙarasawa. Ƙara ta saki a hankali sai kuma ta shiga fisgar hannunta a galabaice. Zaram na miƙe cikin karkarwar jiki. “I'm sorry Ummu, I'm so sorry bari na cire miki. In sha ALLAHU koda fansar raina ne zan bada wajen taimakonki. Sai na ƙwato miki hakkinki, sai na san gaskiyar mafarin lalurarki. In har da saka hannun wani sai na tarwatsa masa tanadi”. Sambatu nake da kuka ina kwance mata hannayen suma. Suma dai sun kumbura sosai duk taji ciwo. Ga tabbuna nan da sayin sarƙar alamar ba yau ne aka fara ɗaureta hakan ba. Ina gama kwancewa ta saki ƙara mai ban tausayi da alama hannun ya mata nauyi, durƙushewa nayi a gabanta nai ƙoƙarin kamo hannuwan nata ra riƙe. Sosai kuka mai ƙarfi ya sake kuɓuce min harda shashsheka. Ɗago idanuna nayi ina kallonta, sai naga itama ni ta tsurama ido tana kallo kamar mai lafiya. Murmushi na saki mai haɗe da kuka. Sai kuma na buɗe baki da nufin bata haƙuri a bazata naji an damƙi wuyana. Sosai na waro ido waje dan azaba. Sai kuma na saki wahalalliyar ƙara jikina na rawa dan shaƙa ce bata wasa ba. Tamkar wulgawar walƙiya aka jehoni cikin ɗakin. Razanannen ihu na ƙwala na azabar buguwa da kaina yayi da bayana. Kafin na yunƙura na tashi domin ceton kaina har ta iso gareni, sake kai hannu tayi a wuyana ta shaƙoni...... 💦💫💦💫💦      Sosai Musaddiq ke a cikin farin cikin da baki bazai iya musaltashi ba duk da bai samu tabbacin samuwar aikin ba. Sai dai yanda interview ta kasance ya matuƙar bashi ƙwarin gwiwa. Ga karramashi da akayi sosai a wajen har abin yaso bashi mamaki. Sai dai ganin harda wani da ya samu da nasa takardun shima ya cirema kansa shakku. An sallamesu akan kowa zaiga massage daga nan zuwa safiya.      Cike da ɗoki kuwa ya dawo gida, ga wani irin farin ciki daya gama mamaye masa rai, sai dai wani fanni na zuciyarsa na matuƙar jin kewar Kandalarsa, da yanzu ita zai fara sanarma albishir ɗin komai da bata labari. Amma ba komai ko yanzu ma bata ɓaci ba. Waya ya jawo ya shiga laluben layin mijin nata. Sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kira yay har sau uku nan ma shiru. Hankalinsa ya nema fara tashi sai ga shi an kirasa back da number ɗin. Cike da zumuɗi ya ɗaga. Suka gaida da mutunta juna. Mijin ya ɗora da bashi haƙuri akan ba'a kusa yake ba sanda yay kiran. Cikin mutuntawa Musaddiq yace babu komai. Sun ɗan yi shiru kowa da tunanin da yake yi, sai kuma suka yunƙuro kusan atare zasuyi magana. Dariya abin ya basu, dan haka Musaddiq ya dara, da ga can kuma mijin na Samraah ya murmusa har Musaddiq ɗin najin sautin murmushin nasa.        “Afuwan ina jinka”.      Da sauri Musaddiq ya ce, “Ni zan nema afuwa ai ina jinka”. “Okay, dama zance ma bana gida ne, amma in sha ALLAHU dana koma zan haɗa ku. Sannan in babu damuwa tsoffin numbers nata ka ɗan turamin dan a mata welcome back ɗin su”.       Cikin jin daɗi Musaddiq yay masa godiya. Daga haka sukayi sallama. Dole ya haƙura yay kiran Hafizzullah dake makaranta yay masa albishir ɗin shi, murna suka dingayi, daga ƙarshe suka koma hirar Samraah ɗin dan da gaske kowa a cikinsu yayi kewarta sosai........✍️        _Humm, ni dai inada tambaya anan😂. Yayanmu Maash ne ko kuwa🥱🥱Bara dai bayi hiru to._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Zuwa yanzu labari ya gama shiga kunnen mutane da dama game da wannan aure na baƙo daga Kano da Halime. Ciki kuwa harda innarta da sauran matan gidansu kasancewar family house ne part-part. Dan har ƙannen mahaifinta da matansu duk a gidan suke suma. Koda su Abba suke isowa sun samu gida a matuƙar hargitse innarta nata tsiya da bori ana rirriƙeta. Abin nata zabban takaici. Dan suna shigowa ta dire tsalle ta shaƙe wuyan rigar Baba tana surutai da girgiza, ga zagi manya-manya. Da ƙyar ƙannensa da matansu suka ɓanbareta. ALLAH sarki Baba duk sai ya daburce. Fahimtar yanayin nasa yasa su Abba dakewa su. Tare da nuna masa cewar hakan ba komai bane daga halin banza irin na wasu mata kamar su Inna. Abba kuma ya sake ƙarfafawa Baba gwiwa akan in sha ALLAHU zai riƙe Halime da daraja ta yanda sai Inna ta yi kuka da idanunta. Baba yaji sanyi a ransa, hakan yasa yayma Abba alƙawarin nan da sati guda Halime zata tare kawai. Yanzu ɗin ma dan yana son sanarma dangin su Innar (dangin mahaifiyarta kenan) shiyyasa bazai basu ita ba. Sun gamsu da hakan, saboda suma suna buƙatar komawa su ɗan kimtsa. Gidan mai-anguwa suka koma aka kira musu Halime. Sai dai da ƙyar ta fito fiskarta a ƙunshe cikin Hijjab. Duk yanda Abba yaso ya ganta taƙi yarda ta buɗe fuskar. Aiko Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu nata ƙumshe dariya. Abba ko nata balla musu harara. Da ga ƙarshe ya korasu waje. Suna fita yay kan Halime yana lallashi, kamar almara yana kai hannu kan hijjab ɗin nata da nufin ɗagewa ta zungura da gudu cikin gida ta barsa da hannu a sage. Duk da yanda yaso dannewa ya gagara, tuni ya shiga ƙyalƙyala dariya yana mai jinjina wautar ta. Lallai akwai aiki gabansa tuƙuru kenan....         ★•★•★•★    Duk yanda mama Balki taso samun nutsuwa ta gagara hakan. Sai faman kaiwa da komawa take yi hankalinta gaba ɗaya na akan Samraah. Tun tana irga sakanni har ta koma mintuna, amamakinta sai ga awa ta shuɗe. Awa ɗaya, biyu, uku itama ta shuɗe. Tsaye take akan kula da girkin rana dasu Kubrah keyi amma kaɗan-kaɗan sai ta fito daga kitchen ɗin, tun ma basu fahimtaba suma har suka fara tsarguwa. Cikin gulma suka dinga nunama junansu ita da ido da baki. Sam Mama Balki bata san ma sunayi ba, saboda hankalinta a rabe yake. Ƴar hayaniyar su Arwa dake falo da zagin da taji sunayi ya sata fitowa zumut daga kitchen ɗin. Hannu taga duk sun saka suna famar toshe hancina. Yayinda tuni Muhsin ya fara kakarin amai. Dai-dai nan itama mahaukacin warin ya daki hancinta, da sauri takai hannu ta toshe hanci, sai kuma ga jama'ar gidan suma sun fara fitowa daga sassansu kowa na tambayar warin minene haka?.      Rasa mai bama wani amsa akai sai nuni da sama saitin sashen Hajiya Babba kawai akeyi. A dai-dai nan katifar da Samraah ta jingina jikin ƙarfen da aka ƙawata adon wajen da shi da bata zauna dai-dai ba ta sulmiyo downstairs ɗin gaba ɗaya. Ihu yaran suka buga a tare suna tarwatsewa. Sai kuma yunƙurin amai dan gaba ɗaya falon ya ƙarasa gumamewa. Cike da fusata Hajiya Mammah ta koma upstairs ɗin tana ƙwala kiran Samraah da “K!! K!! K!!” dan ko sunanta bata sani na. Ihun nata yaja hankalin sauran iyayen dama su Azizat ɗin suma suka bita. Hakama su Falilah ba'a barsu a baya ba. Mama Balki ce ƙarshen bin bayansu.        Isowarsu ƙofar dai-dai da ƙwalla ƙarar azaba da Samraah tayi, a take kowa ya tsaya cak. Ƙarar da Samraah ta sake fasawa kuma duk sai suka ja da baya. Dan basa buƙatar ƙarin bayani ta ƙwaɓe ne tsakaninta da mai sashen. A matuƙar tashin hankali Mama Balki ta juya da gudu ta sauka downstairs ɗin jikinta na ɓari. Bama tasan sanda takai kanta sashen Maash ba. Kawai tsintar kanta tayi a gabansa durƙushe cikin kuka da roƙo ta kama ƙafafunsa....          “Alhaji ƙarami dan ALLAH ka taimake mu. Kandala. Kandala ce gata can a sashen Hajiya Babba...” numfashinta ya nema ɗaukewa gaba ɗaya saboda yanda take a kiɗime. Shiko Maash da tun shigowar tata a guje da tsawar da Hayatu yay mata na son ta dakata ya tsaya cak daga duba abinda Hayatun ke nuna masa a tab sai dai bai ɗago ba sai da ta ambaci Hajiya Babba dan shi bai ma san waye wani Kandala ba. Idan ka cire ita a gidan da mijinta sai wasu tsiraru a masu aikin da suka daɗe a tare da su kawai zai iya cewa ya sani har ma ya shaidasu koda a wajen gidan ya gansu. Amma daga basu ɗin ba babu wanda zai iya shaidawa a cikinsu.      Cak Hayatu shima ya dakata da ga yunƙurin maganar da yake, dan sai a lokacin yama fahimci wacece ɗin. Shine yay ƙarfin halin faɗin, “Mama waye Kandala? Mi kuma ya faru da Hajiya Babba?”.         So take tai magana amma ta kasa, sai nuna ƙofa kawai take ga hawaye na kwaranya mata. Ƙarasowa Hayatun yay da sauri inda take. Ya kama hannunta ya miƙar daga gaban Maash da take durƙushe. “Kinga relax. Calm down kiyi magana yanda za'a fahimta. Rufe idonki ki shaƙi iska ki fesar Mama”.      Kai mama Balki ta shiga jinjinawa tana haɗiyar kukan da sauri-sauri. Yanda duk Hayatun yace tayi tayi, ya miƙa mata ruwan gabansa ta sha maƙwarwa biyu sannan ta sauke nannauyan numfashi. Shi dai Maash kallonsu kawai yake amma ya gagara cewa komai. Cikin ƴar nutsuwar data samu ta sake faɗin, “Kan...kandala ce sabuwar mai aikin da Aunty Mama ta kawo. Ta..ta tafi sashen Hajiya Babba gata can tana ihu da alama....” sai kuma ta kasa ƙarasawa. Sosai Hayatu ya waro idanu a firgice. Yayinda Maash yayi wani masifar runtse nashi da ƙarfi, sai kuma ya ajiye tab ɗin hannun nasa ya miƙe. Baima tsaya ƙarasa jin zancen ba ya nufi ƙofar da kan sadashi da sashen mahaifiyar tasa kai tsaye daga sashensa. Sai dai kuma a kulle take. Jikinsa ya shiga shafawa neman key, amma da alama baya tare da shi, har ya kalla Hayatu zai yi magana sai kuma ya fasa. Komawa yay da baya ya fito, da sauri Hayatu da Mama Balki suka take masa baya. Ta babban falon gidan da ya gama gumamewa da warin katifar nan ya ratsa, da bibbiyu ya dinga haɗa stairs ɗin tsabar tashin hankalin da yake a ciki. Dan duk duniya bai haɗa al'amarin mahaifiyar tasa da komai ba. Cikin rufewar ido da ɗimuwa yake sa hannu ya ture duk wanda ya tare masa gaba. A haka har ya shige ciki gaba ɗaya dan su mutanen gidan suna a falon farko ne cirko-cirko sun gagara shiga ciki dan tsoro. Sai hayaniya da suka cika wajen da shi. Yana shiga securitys ɗin da sukai kira na cikin gidan na isowa. Suma takema Maash ɗin da Hayatu baya sukayi...         Sosai nake kakarin mutuwa. Idanuna kam sun gama firfitowa. A wannan gaɓar na sallama da rayuwa. Ta ALLAH kawai nake jira ta kasance. Wata irin bugawa da tama kaina a bango ya sani fasa wahalalliyar ƙara da ko sautin kirki babu yanzu saboda galabaita dana gama yi. Daga haka ban sake sanin mi kuma duniya ke'a ciki ba...             Shigowar Maash dai-dai da wancakalo Samraah da Hajiya Babba tayi kai kace irin an yadda magen nan. Baya yay taga-taga zai faɗi, sai da Hayatu ya riƙesa. Da sauri ya kai dubansa kan abinda ta wurgo ɗin, a kuma dai-dai nan itama ta sake wawuro abin morpping irin na wutar nan da Samraah ta ajiye tare da sauran kayan shara. Ji kake bummm!! Akan goshinsa. Kamar ƙyaftawar ido ta sake rarumo wani abun, jifan kan mai uwa da wabi ta shiga musu kamar yanda take yi a duk sanda take a irin wannan yanayin. Dole su Hayatu suka shiga fita a guje. Yayinda Maash ya kasa yin hakan shi. Dan shi damuwarsa ba ciwon data jimasan bane. Kar ita ta jima kanta ciwon. Ƙoƙarin nufarta yayi da son kwashe sauran kayan sharan. Amma ina jifa kawai take kai masa dasu tako ina... Cikin wani irin karyewar murya ya shiga ƙoƙarin kai hannu gareta yana faɗin, “Please Ummie na kar kiji ciwo, dan ALLAH ki ajiye zai ji miki ciwo. Hannunki Ummie hannunki.”      Ina ita bama tasan yanayi ba. Jifan kawai take kai masa har sai da taga kayan sun ƙare, sai kuma ta koma kai masa duka da hannu. Cikin sa'a shima ta shaƙuro wuyarsa. Dai-dai nan masu kula da lafiyarta da akai kira a waya suka iso. Da ƙyar aka ɓanɓare Maash a hannunta bayan sun mata allura mai ƙarfin gaske. Zama yay ƙasa batare da jin ƙyanƙyamin komai ba ya riƙeta a jikinsa ya zubama fiskarta idanunsa da suka rikiɗe gaba ɗaya. Yanda Adams apple ɗin sa ke kai da kawo zai tabbatar maka da kukan zuci yake yi. Yafi mintuna goma zaune a haka shiru, duk maganar da su Hajiya Mammah suke masa bai ko motsa ba. Sai da Paah ya shigo ya kai duƙe kusa da shi, hannu ya fara kaiwa ya riƙo na Ummie dake kwance ka shirɓan allamar barcin nata yay nisa matuƙa, idanu ya zubama hannun cike da tausayawa shima nasa na cika da hawaye, dan har yanzu har gobe yana matuƙar ƙaunar matar tasa rufin asirinsa kuma. Hawayensa ya share kafin ya sauke ajiyar zuciya tare da kiran sunan Maash da bai ko motsa ba.       “Muhammad”.    A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Paah ɗin nasa batare da ya iya cewa komai ba, sai kuma ya ɗauke ya maida kan (Ummi) Hajiya ƙarama da ke tare da sauran masu kula da lafiyarta dan itama likita ce. Sake ɗaukewa yay ya maida kan Samraah dake kwance gefe a sume babu wanda yabi takanta. Yanda ya tsurama wajen ido na tsahon mintina kusan biyu ya saka kowa maida kanhalinsa ga kallon abinda yake kallon. Shima kansa Paah sai a lokacin ya lura da Samraah ɗin.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Cikin tashin hankali ya miƙe yana ambaton, “Subahanallahi. Ita kuma wannan mike faruwa haka?”.         Idanun Muneef cike da hawaye ya ce, “Paah ai itace ta fara shigowa yima Hajiya Babba shara shine sai....” ya gagara ƙarasawa saboda hararar da Hajiya Mammah ta wurga masa. Duk da kowa ya fahimci Hajiya Mammah ɗin ce ta kwaɓi yaron babu wanda ya iya tankawa. Shi dama Maash kansa a duƙe yake kawai yana duban mahaifiyarsa kamar bai san mi sukeyi ba. Yanda bai kallesu ba bai tanka musu ba ya miƙe ɗauke da Ummiensa. Fita yay daga ɗakin gaba ɗaya da ita. Dole suka shiga darewa suna bashi hanya. Can falon da Samraah ta gyara yaje ya kwantar da ita. Anan ɗin ma sai dai ya tsira mata ido na kusan minti ɗaya kafin ya juya ya koma ɗakin. Yanzu kam ya samu Azizat na ƙoƙarin sheƙa ma Samraah ruwa a jiki cike da mugunta da wulaƙanci, wani irin kallo daya wurga mata ya sakata daburcewa taja da baya tana faman sinne kai. Yanzun ma baice da kowa komai ba ya ƙara da inda Samraah ɗin ke kwance. Sunkuyawa yay gaba ɗayanta ya ɗauka. Dukansu sai da kowa ta waro idanu waje musamman Malika da Azizat da Arwa, yayinda ran Hajiya Mammah ya gama ɓaci amma bata ce komai ba. Kamar ɗazun darewa sukai suka bashi hanya, cike da takun nan nasa na bajinta da ƙarfin jini ya fice ɗauke da Sam-G dake a sume batama san inda kanta yake ba. Kallon kallo aka fara yi, kafin Paah da shi dama komai bai canja ba daga garesa ba sai ma daɗin kulawar da Maash ɗin ya bada akan yarinyar yaji ya bi bayansa. Dan shi dai abinda kawai ya sama ransa dole Maash ya taimaka ma yarinyar, amma yana mamakin ma yaya akai tazo har nan ɗin tunda yasan babu mai shiga sashen Hajiya Mammah ɗin kai tsaye haka sai masu kulawa da ita, tunda kuma waccan ta gudu kusan wata guda kenan ba'a sake kawo wata ba. Ganin Paah ya fita duk suka zabura suma suka bi bayansa. A falon ƙasa suka samu Maash na ƙoƙarin sauke Samraah saman kujerar falon tare da kaiwa zaune shima ya kwantar da kanta a jikinsa. Dai-dai nan Hayatu ya iso gabansa da first eld box. A gabansa ya dire, jikinsa har rawa yake wajen fara fiddo abinda za'a fara buƙata. Maash ɗin ya miƙawa auduga, da farko zubama audigar idanu kawai yayi kamar bazai amsa ba. Sai kuma miya gani oho masa ya kai hannu ya amsa. Jinin goshinta da har lokacin ke fita ya fara ƙoƙarin gogewa, ganin kamar kaɗar bata masa yanda yake so sai kawai ya jawo handkerchief dake jikinsa fari tass ya shiga kwashe jinin da duk ya gama ɓata mata fuska. Sai da ya goge shi tass sannan ya saka ƙaramin bandage dan ciwon ba wani ƙato bane can sosai amma ba laifi da ɗan girmansa. Ganin ya kammala komai Hayatu ya miƙo masa goran ruwa. Karɓa yay ya zuba kaɗan a cikin hannunsa ya shafa mata a fuskar zuwa wuyanta. Numfashi mai nauyi sosai ta kawo, sai kuma ta zabura cikin yanayin firgita ta ƙanƙamesa jikinta na rawa. A hankali ya lumshe idanunsa batare daya ko motsa daga yanda yake ba.. kusan mintuna biyu suna a haka kowa ya zuba musu ido kowai, yayinda zukatan wasu suka gama hasala, wasu ko na tausaya mata...        Shigar ƙamshin turarensa a cikin hancina ya sakani tsayawa cak, wani irin bugawa ƙirjina yayi, ga zuciyata na tafiya da sauri-sauri a cikin ƙirjina, komai daya faru ya shiga dawo min daki-daki. Fara sassauta riƙon da naima koma wanene nayi, sai kuma na sakesa gaba ɗaya na yunƙura zan tashi, sarawar da kaina yayi ya sani kai hannu na dafesa tare da faɗin, “Wash ALLAH na” na koma na kwanta a inda naken. A bazata naji saukar tattausan hannu mai zafi sosai a saman nawa hannun, janye nawan akayi a hankali, hakan ya sani sake buɗe nauyayyun idanuna. Harga ALLAH sai da zuciyata ta harba da ƙarfi Bily saboda saukarsu a cikin na wanda banyi zaton gani ba. Duk kuma yanda naso janyewa hakan ya gagara, kallonsa nake a tsakkiyar ido kamar yanda nima yake kallona. Ga hannunsa riƙe da nawa shi bai sakar min ba, bai kuma ajiye ba....          “Are you okay?!”.      Ya faɗa cikin yanayin motsa lips batare da fitar sautin murya ba, gaba ɗaya naji wata irin kasala ta saukar min, sanyi ya shiga ratsani a cikin ƙashi da ɓargon jikina. A maimakon bashi amsa sai kawai na lumshe nawa idanun a hankali nima, wasu hawaye ne da suka jima maƙale a cikin idanun nawa suka sami damar silalowa batare da nasan dalilin hakan ba...       “Hayat muje hospital”.    Furicin sa cikin sauƙaƙa harshe ya sani buɗesu da sauri. Kaina na girgiza masa da sauri ina ɓata fuska da tura baki, sai kuma na yunƙura zan tashi a jikin nasa ina faɗin, “Ni dai bance ina son zuwa asibiti ba ai”.      Bai tanka min ba, sai maidani da yay a yanda nake ya sake kwantarwa a jikin nasa. Jinai kamar na fasa kuka, amma dole na haƙura dan nasan koma sake yunƙurin tashi bazan iya ba. Saboda wani irin sarawa kaina keyi da juya min.         Azizat ce ta fara jan sirrin tsaki ranta a ɓace tabar wajen duk da bajin abinda suke faɗa sukai ba, sai Maleeka da hawaye suka gama wankema fuska dan tsabar takaici. Dan lokaci ɗaya taji tsanar yarinyar ta gama baibaye rayuwarta. Wata mace kwance a jikin Awwab ɗinta ba ita ba...      Dawowar Hayatu ya katsema kowa zancen zucinsa. Cike da girmamawa ya sanar masa ga Doctor nan a hanyar zuwa. Kamar ko yaushe bai amsa ba. Sai Hajiya Mammah ce cikin ɗan faɗa-faɗa ta furta, “Yanzu ga Hajiya ƙarama a gida matsayin doctor sai an kira wani likita dubata kuma dan ɗigimi?”.      Hayatu rasa abinda zaice mata yay, sai kallon ogan nasa da ya ɗan yi. Da gaske bashi da alamar bama Hajiya Mammah ɗin amsa, dan kansa ma na a ƙasa ne yana faman latsa waya. Sai da Hajiya Ƙarama ta furta, “Ciwon nata ma kamar bamai tsanani bane, magani kawai zata sha in sha ALLAH jikin zai mata sauƙi.” ta ƙare maganar da ƙarasowa ta duba magungunan first eld box dake gefensa. Duk maganin daya kamata nasha ta ware, sannan ta nunama Mama Balki duk yanda zan sha su. Tana kammalawa Hajiya Mammah tace su kamani su tafi dani can sashen masu aiki. Batama rufe baki ba na yunƙura na tashi daga jikinsa hannuna dafe da kaina. Mama Balki da A'i ne suka kamani. Muna ƙoƙarin barin wajen na ɗan ɗago na kallesa, idanu muka haɗa, sai kawai na tura masa baki. Dan luuu yay da idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya ɗauke kansa gaba ɗaya...       ❤️★❤️★❤️   Kwanaki huɗu kenan da ɗaura auren Abba da Halime. Har zuwa yanzu kuma bai sanarma Mom ba. Dan bama shiga sabgarta yake ba har yanzu. Itace dai take son su shirya saboda ko abincin gidan baya ci. Ga abubuwa teacher ya bata amma ta rasa yanda zatai da su. Yau ne ma da saurayin Baby ya sake zuwa Abban ya ɗan sake a gidan har suka ga haƙoransa a waje. Kai tsaye kuma batare da kwana-kwana ba ya bashi damar turo magabatansa har hakan yaso bama Mom ɗin mamaki. Amma dai batace komai ba sai da ta kira Ummanta take sanar mata sai tace mata aikin malamin ne ya fara cinsa. Tunda dama yace zai musu wani a bayan fage bayan na abincin da aka basu a saka masa. Wannan ne ya sanyaya zuciyar Mom ta samu nutsuwar cigaba da warisarta akan kuɗin da saurayin Baby ɗin ya danƙara musu yau ma.         Kwana ɗaya da zuwan saurayin Baby kwana biyar da ɗaura auren Abba ya fara gyaran gidansa. A haukar Mom dama kowa dake gidan shine Abba ya ƙirƙiri gyaran ne domin auren Baby ɗin. Shiko baicewa kowa komai ba. Garama kwana biyu da fara aikin ya zauna da Musaddiq ya buƙaci ya bashi aron kuɗi. Babu musu kuwa Musaddiq ɗin ya bashi kuɗin, jin daɗin hakan ne ya saka Abba kwancemasa abinda ke faruwa game da auren nasa. Duk da zuciyar Musaddiq ta girgiza sai da ya saki murmushin da har ya so bama Abba mamaki.       “ALLAH ya sanya alkairi Abba. Amma baka ganin akwai damuwa a haɗa Mom da Auntyn a gida ɗaya kuwa?”.     Murmushi shima Abba yayi a karo na farko, sai kuma ya dafa kafaɗar Musaddiq ɗin. “Gaskiya ka faɗa Musaddiq, sai dai hakan da zanyi zai fi bani kwanciyar hankali ni kuma. Dan Maman nan taku zata iya aikata komai saboda bata ƙaunar kishiya. Amma kaga idan suna a tare waje guda koyaya zamu dinga sani wani motsinta ai ko”.             “Hakane kuma Abba. ALLAH ya sanya alkairi to. Ya kuma kauda fitina”.      “Amin ya rabbi Musaddiq. ALLAH yay maka albarka. Ku ƙara haƙuri dani kunji”.     Murmushi Musaddiq yay kawai amma baice komai ba.      An kammala gyaran gida tsaff a cikin kwanaki uku, duk wanda ya kalla fa sai ya yaba. Yayinda kan Mom ya sake girma ta fara hurama ƴan anguwa kai. Daɗin wannan gyara ya sata sake sauke kai ƙasa ta sake bama Abba haƙuri. Shi kuma bai ja ba yace mata komai ya wuce. Cikin farin ciki ta rungumesa ana sakar masa kisses. Shi dai komai baice mata ba, sai ma zame jikinsa yay cikin dabara. Bata damu ba ta gyara zama tana tsara masa yanda zasu gyara gidan. Dan ita a haukarta sashen da Abba ya gyara ɗin nasu Bibaa ne zasu koma. Saboda ta daɗe dama tana masa nacin ayi hakan ba'ayi ɗin ba, yanzu kuma a tunaninta yayi gyaran ne dan su shirya.......✍️      _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .......Wani ɗan iskan Murmushi Abban ya sake mata da cewa to kawai. Hakan ya sakata sake shiga cikin farin ciki da tabbatar da lallai aikinsu ya ci Abban. Washe gari kuwa sai ga kaya ana kawowa danƙara-danƙara. Sosai farin cikin Mom ya kasa ɓoyuwa a wannan yini, dan har sai da ta kira Ummanta ta sanar mata. Da yamma kuwa masu aikin na gab da kammalawa sai gata ta isa gidan. Har sashen suka shiga ita da Mom ɗin, sunata faman santin kayan da yaba aikin malamin. Tun a ranar Mom ta fara haɗa ƴan kayanta, dan a bata haukar itace zata koma can abarwa yaran inda take. Da Abba ya dawo gida da yamma ya sami tarba ta mutunci daga Mom ɗin, hatta da abincinsa ranar da kanta ma tayisa bata saka sabuwar mai aikin ta ba. Shi dai komai baice mata ba, duk abinda tace shi yake yi, a can ƙasan ransa kuwa dariya take bashi...         ★★★....       Bayan wucewar su Samraah ya jima zaune a wajen batare daya tankama duk surutun su Hajiya Mammah dake a falon ba. Sai da Paah ya kira sunansa sannan ya ɗago ya ɗan kallesa sai kuma ya sake maida kan nasa ya duƙar ba tare data amsa masa ba shima. Shiru falon yayi dan kowa zuwa yanzu ya fahimci ransa a ɓace yake har shi Paah ɗin. Ilai kuwa basu gama zancen zucin nasu ba ya sake ɗagowa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya tamkar mai lissafa yawansu. Da sauri yaran suka shiga rige-rigen barin wajen, hakama Hayatu saurin fita yayi hankalinsa a tashe, dan dama duk a ɗari-ɗari yake da yanayin ogan nasa. Suna gama fita Maash daya tsare iyayen nasa da kallo cikin daƙilallen yanayin nan nasa dake sake fiddo tsantsar ɓacin ransa ya furta, “Paah sayin mi na gani a hannu da ƙafar Ummie? Ina masu kula da ita da har yarinyar nan ta shiga inda take?”.           Kai Paah ya shiga girgizawa, kafin cikin nuna damuwa shima ya furta, “Muhammad tare da kai muka bar gidan nan a shekaran jiya. Na dawo jiya da dare ka dawo yau da safe. Ban san komai ba kamar yanda kaima baka sani ba”.      “Har yanzu baka shiga duba Ummie kenan?”. Ya faɗa a zafafe.     Dabircewa Paah ɗin yayi, zai fara kare kansa Maash ya katsesa ta hanyar maida kallonsa ga Hajiya Mammah. Sosai ta fara mazurai. Sai dai shi ko'a kwalar rigarsa dan itama tasan baya tsoron duk wani hargaginta. Kame-kame ta fara tunma kafin yace da ita komai.         “Ko yau da safen nan na shiga duba ta ni dai, kuma banga wani ciwo a jikinta ba Awwab. Sai dai idan munafukar yarinyar nan ce ta aikata mata wani abun. Shiyyasa sam yarinyar bata min ba tun randa Mashi'a ta kawota. Ni inama zargin wani ne ya aikota dan ta cutar damu, yarinyar fa sam bata shakkar gasawa mutane magana, kai ma shaida ne ai tunda a gabanka ance ta mari Azizat....”        Idanunsa ya runtse da ƙarfi yana mai masifar cije lips ɗinsa. A take jijiyoyin kansa duk suka firfito ruɗu-ruɗu. Idanunsa suka kaɗa gwaiduwar tsakkiya ta koma siririya. A matuƙar zafafe da akan daɗe ba'a gansa a yanayin ba ya miƙe. Gashin jikinsa har mimmiƙewa suke saboda masifar dake cin zuciyar ƴan maza. Cikin daka tsawa ya ce, “Mammah!! Idan itace ta jimata ciwo shi kuma dattin dake a sashen itace ta zuba shi kenan?! Dama wannan dalilin ne yasa a duk lokacin da nake gari ake maido Ummie falon sashenta na farko!!!”.         “Muhammad!!”.    Paah ya kira sunansa a tsawace shima. “Kana cikin hankalinka kuwa? Addata kake ma tsawa haka kamar kana magana da wata sa'arka?!!”.           “Ni kuma ina magana ne akan mahaifiyata idan ita ɗin Addarka ce Paah! Idan kuma kana son tuna min kana nan baka canja ba to nima fa akan Ummie ban canja ba. Ba kuma zan taɓa canjawar ba. Kaf ɗinsu har kai ɗin ban ma kowa tilas a zaman gidan nan ba, tunda dama ban gayyaci kowa yazo ya zauna da mu ba a cikinku kune kuka kawo kanku. Ku gaya min na taɓa tsallake dai-dai da rana guda wajen biyan masu kula da Ummie ne? Ko na taɓa tauye wani likita a cikin masu duba lafiyarta. Kai da Baba kuka tirsasani wannan kai da kawon kasuwancin badan ina so ba. Kuka kuma min alƙawarin kulawa da mahaifiyata bakin rai bakin fama har takai da an tattaro wannan gayyar an zube a gidan nan. Idan kun manta bari na tuna muku wannan gidan mallakin wadda kuke wulaƙantawar ne. Amma ku kuna zaune cikin salama da tsafta ita tana cikin ƙazanta. Saboda son zuciya kuma kuna lulluɓe duk wata hanya dazan fahimci haka. Shin dama kun tirsasani barin kulawa da itane dan ku tozarta min it...” ya kasa ƙarasawa saboda hawayen dake neman kufce masa. Ga wani irin masifar sarawa da kansa yayi cikin ƙanƙanin lokaci falon ya shiga juya masa. Hannu ya kai da ƙyar yana ƙoƙarin dafe kan amma hakan ya gagara, sai ma layi daya fara. Gaba ɗayansu sukai kansa hankali a tashe. Dai-dai ƙarasowar Paah inda yake ya tafi gaba ɗayansa zai zube ƙasa babu alamar numfashi tattare da shi. Da ƙyar Paah da Hajiya Mammah da Mummy suka iya tallabesa. Dan Maash tsayayyen mutum ne ƙaƙƙarfa a tsayensa. Ihun Azizat dake laɓe daga upstairs tana sauraren komai ya jawo hankalin su Hayatu dake main perlor. Da gudu ya shigo hankalinsa a tashe. Dama abinda yake gudu kenan tun farko. Tunda ya fahimci ran ogansa a ɓace yake yasan akwai matsala. Ba shi ba ko shi kansa ransa ya ɓaci da ganin yanda sashen Ummie ɗin yake. Yana ji a ransa kuma an jima ana wannan ha'incin sai yau ne ALLAH yayi asiri zai tonu. Dan a watan nan zai iya cewa ko sau ɗaya basu shiga ainahin sashen Ummie ba. A falon farko suke isketa a duk sanda suka dawo suka shiga dubata, kuma Hajiya Mammah ce kan tsatstsare ta babbake komai ta hanasu shiga can cikin. Ashe akwai abinda ake ɓoyewa.            ★★★★...        Da taimakon Mama Balki na gasa jikina da ruwa mai zafi, dan duka dai kowa yasan na sha shi. Ina fitowa daga bayin zazzaɓi mai zafi ya rufeni, sai rawar sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan ciwo sosai har washe gari ina kwance, ban san abinda ke faruwa ba a gidan sai da safe bayan su Bahijja sunje sunyi aikinsu sun dawo kowa ya dawo sai naga ya dawo jiki a sanyaye. Hankali tashe na shiga tambayar Bahijja mike faruwa? Kuka ta fashe min da shi, kafin ta sanar min ai gidan ne babu lafiya ciwon Uncle Boss ya tashi. Da mamaki nake kallonta, kafin na ce, “Ciwonsa? Dama yana da wani ciwo ne?”.      Kai ta shiga jinjina min tare da sake fashewa da kuka. Cikin sarƙewar harshe da jan ajiyar zuciya irin ta mai kuka ta ce, “Eh, sai dai nima tunda nazo gidan nan sau ɗaya ya taɓa tashi masa. Amma yau naga hankalin kowa a tashe yake sosai alamar abin babbane. Dan naga har Baba prof ma yazo shi da akan daɗe ba'a gansa a gidan nan ba sai idan yazo duba Hajiya Babba ne ko wani babban dalili.”        Idanu kawai na zuba mata cike da nazari, kafin na ce, “Wane irin ciwo ne ke damunsa?”.      “Nima ban sani ba aunty Kandala. Yakan dai yanke jiki ya faɗi ne, daga nan yakanta ciwon kai mai tsanani har sai wani bawan ALLAH babban masani yazo ya bashi magani daga ƙasar Togo. Dan ance ya taɓa bama Hajiya Babba ma magani harta samu sauƙi sai kuma abin ya sake dawowa sab......” ta kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Mama Balki. Sai ma miƙewa da tai cikin wayancewa ta fice wai tana zuwa. Da kallo kawai na bita kamar yanda itama Mama Balkin ta bita da kallo. Sai da ta fice na sauke ajiyar zuciya mai nauyi ina maida kallona ga Mama. Itama ni take kallo yanzu. Sannu tai min da tambayata yaya jikina. A hankali na amsa mata, sai kuma na tashi zaune sosai dai-dai itama tana ƙarasowa inda nake ta ajiye kwanon hannunta. Hannun nata na kamo dan haka ta juyo tana kallona. Hawayen da nake ta riƙewa ne suka ziraro min.         “Ya salam Kandala miya faru kuma? Jikin ne?”      Kaina na shiga girgiza mata ina ƙoƙarin share hawayena. Itama sai kawai ta riƙoni jikinta tana lallashi. Tsawon lokaci muna a haka har sai da na daina kukan sannan ta ɗagoni, cike da kulawa ta ajiye abinci a gabana. Kaina na girgiza mata. Cikin damuwa na ce, “Mama na ƙoshi, sai dai ina son kimin wata alfarma”.         “Alfatma kuma Kandala? Ta mi?”.     “Ta bani tarihin wannan gida. Dan ALLAH mama ina son sani. Idan har kema kin sani badan ni ba dan rahamar da UBANGIJI yay mana.”     Jimmm tai alamar tunani, kusan mintuna biyu sannan ta nisa a hankali. “Kanda kin roƙeni tare da haɗani da wanda bazan iya bijirewa ba. Sai dai abinda kike buƙatar sani jinsa a bakina zai iya zama haɗari idan har wani ya jimu. Amma ina mai baki haƙuri da in sha ALLAHU watarana zan gaya miki duk abinda na sani. Dan ina aiki a ƙarƙashin wannan ahali tun ina da ƙarancin shekaru koma nace miki iyayena ma sun hidimta musu suma. Wannan baiwar ALLAHr da kika gani a halin jarabawar rayuwa yau itace ta suturtani da ilimin addini dana zamani dan kusan tare muka tashi da ita amma ta girme min. Ta kuma yimini aure da mutumin kirkin da ƙaddara ta rabamu badan mun shirya ba. Bayan rasuwarsa ne na sake auren Malam Umaru dake koyar daku karatun addini a yanzu. Abinda kawai nake so dake ki kula, gidan nan ya wuce duk yanda kike zatonsa. Ki bi komai a hankali kinji. Muma badan bazamu iya bane muka zuba ido sai dan anfi ƙarfinmu ne kawai.”       Ajiyar zuciya na sauke ina jinjina mata kaina. “Shike nan na gode Mama. Amma dan ALLAH ki amsa min tambaya ɗaya”.     “Ina jinki”.   “Dama haka ake ɗaureta?”. Sai da ta ɗan waiga ta kalla ƙofa kafin ta juyi tana ƙara sauke murya ƙasa cikin raɗa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......“Sai idan Alhaji Ƙarami baya nan suke mata hakan. Da sunga zai dawo suke kwanceta su dawo da ita falon nan na farko shiyyasa bai sani ba. Yau ɗin ma ALLAH ne yayi da rabon zai gani kuma akai sa'a sarƙar taci mata jiki dan kwana biyu kenan da ɗauretan randa yay tafiya. Da alama kuma basu san yau zai dawo gidan ba ne shammatarsu yayi. Ban kuma san yaya akai yaransu basu sanar musu da shigowarsa ba dan mafi yawan masu aikin gidan nan su sukema aiki”.       Kasa daurewa nayi a zafafe na ce, “Mama dan ALLAH su waye wai?, Nasan dai harda Hajiya Mammah ɗin nan ko?”.      Kai ta girgiza min tana miƙewa. “Duk yanda kike tunanin al'amarin ya wuce haka kandala. Ke dai kawai kar ki saka kanki a masifa”. Daga haka ta nufi hanyar fita abinta.        Badan naso ba na yarda na haƙura. Sai dai maganganunta sun sake ruɗar dani matuƙa. Har takai damuwar dana sakama raina ta sake assasa zazzaɓina. Dan yinin ranar gaba ɗaya a kwance na yisa rijif cikin ciwo har washe gari ma. Sai a cikar kwanaki uku da faruwar al'amarin zuwa yamma ya ɗan sakeni naji dama-dama. Amma a haka Hajiya Mammah ta aiko a kirani a wannan ranar. Cikin dauriya da ƙarfin hali na isa sashen nasu. A falon ƙasa na samu su Azizat zaune kowa na harkar gabansa. Ko kallon inda suke banyi ba nai nufin wucewata. Amma sai kawai gani nayi ansha gabana. Ban yi niyar ko kallon ma wanene ba, na raɓa zan wuce aka sake shan gabana. A hakan ma ɗauke kaina nayi na koma damana nan ma aka sha gabana. Runtse idanuna nayi da ƙarfi tare da cije lips ɗina ina ƙoƙarin controlling kaina. Kafin na ɗago gaba ɗayana babu alamar wasa a tattare dani.        “Oh da kika ɗago a fusace kamar wata zakanya zaki dakeni ne?”. Maleeka ta faɗa a wulaƙance cikin huci. Maimakon amsa murmushi na sakar mata mai sanyi. Sai kuma na lumshe idanun na buɗe cikin yanayin isa da ƙasaita. A hankali na motsa lips ɗina na furta, “Karki fara abinda bazaki iya ba. Dan wannan kogin ko manyan jirage da takatsantsan suke gittashi balle ke da baki wuce matsayin jirgi mai saukar angulu ba”. Daga haka na raɓata na wuce abina. Da alama hausar tawa take ƙullawa da kwancewar fassarawa. A falon sama na sami Hajiya Mammah ɗin da Alaja. Cikin girmamawa na gaishesu, Hajiya ƙarama ta tambayi yaya jikina. Na amsa mata cikin nuna jin daɗi da kulawarta. Baki Hajiya Mammah ta taɓe, kafin ta kalleni a wulaƙance ta jefo min tambaya. “K kin iya girki?”. Ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sannan na amsa mata da, “Eh na iya Mammah.”        Sai da ta ɗan ƙara taɓe bakin ta cigaba da faɗin, “Kije ki mun abu mara nauyi yanzun nan. Ba kuma nason ɓata lokaci”. Kaina na jinjina mata ina miƙewa. Dai-dai zan bar wajen muka haɗa ido. Sosai zuciyata ta harba da ganin wani irin shegen kallo da take bina da shi na ƙwaf-ƙwaf. Sai dai ban kawo komai ba nai tafiyata ina mai karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta gareni. Inda nabar ƴammatan gidan anan na sake samunsu. Sai dai a yanzu hankalinsu baya kaina, amma da alama cecekuce da zagin da suke duk a kaina ne, dan haka har na wuce basu sani ba. Karo na farko na fara shiga kitchen ɗin gidan. Da mamaki su Aunty Kubrah duk suka watso min idanu, cikin dakiya na gaishesu tare da sanar musu abinda ya kawoni kitchen ɗin. Sai gani nai Aunty Falilah da Aunty Kubrah ɗin sun kalla juna suna yamutse fuska. Kafin Falilah taja tsaki ta cigaba da aikinta. Hakan da sukai min yay min ciwo, dan haka nima na watsar da su na ƙarasa shiga kitchen ɗin ina kallon tsarinsa da haɗuwarsa tamkar ba'a Nigeria ba. Dai-dai nan sai ga Mama Balki tamkar an jehota...        “Kandala miya kawoki nan keda baki da lafiya?”.     A shagwaɓe nace mata “Mama an sani aiki ne?”.    Cikin nuna mamaki tace, “Aiki kuma? Waye ya sakaki ke da baki da isashen lafiya? Kuma banan bane sashen aikin ki”.        “Nice ko ban isa ba?”.    Aka amsa mata daga bayanmu. A tare duk muka juya, jikin Mama Balki na rawa ta ce, “A'a Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki ai ban san kece ba.”    Tsaki taja tana ɗauke kanta ta dawo da shi gareni. Cikin isa da bada umarni ta lissafo min duk abinda take buƙata. Kafin ta kalla Aunty Kubrah tace ta sameta da black tea bedroom ɗinta tai ficewarta. Ina kallon Aunty Kubrahn ta bita da uwar harara, ni dai sai na fara ƙoƙarin neman tukunya hannuna dafe da kaina dan bana jin daɗin jikina da har yanzu. ALLAH sarki da taimakon Mama Balki nayi girkin, yanda take ta nuna damuwarta akan sakani aikin da Hajiya Mammah ɗin tayi sai ya dinga bani mamaki. Amma sai ban ce da ita komai ba ni dai dan bama fahimtar inda ta dosa ɗin nayi ba, na dai dinga ƙarfafa kaina dan na rage mata damuwa. Mun kammala da ƙyar ina faman dafe kai sai ga Hajiya Mammah ɗin ta dawo. Tsaf take cikin sabuwar kwalliya da alama wanka ta sake. Abubuwan dana zuba abincin ta shiga buɗewa a yamutse. Sai da ta gama tsaff sannan ta kalleni.        “Kije kiyi wanka ki sameni da kayan abincin bedroom ɗina”.    Karan farko na ɗan kalleta. Kamar zanyi magana sai kuma na fasa ganin harta juya abinta ta fice. Side ɗin da Mama Balki take na duba. Ganin yanda fuskarta duk ta nuna damuwa ya sani sakar mata murmushin ƙarfin hali. Itama murmushin ta ɗan sakar min. Fuska na ɗan ɓata cikin marairaicewa na ce, “Amma Mama matar nan ta cika mulkin mallaka da iyayin tsiya. Yanzu kai abincin ne sai nayi wanka? ALLAH kaina ke ciwo ina son naje na kwanta”.         Cikin yanayin damuwa ta amsa min da, “To yaya zamuyi Kandala. A ƙarƙashinsu muke ai. Sannu kinji ALLAH ya sawwaƙe. Kije kiyi wankan sai ki sameni na tayaki ɗauka kinji. Ni dai bana fatan a dinga yawan kuka da ke a gidan nan balle har a fara kaima Alhaji ƙarami ƙararki.”      Zuwa yanzu na fahimci wa take cema Alhaji ƙarami a gidan, dan haka bance komai ba na fita hannuna dafe da kaina. Kai tsaye sashenmu na wuce, na samesu duk sun koma dan yanzun lokacin hutunsu ne. Bedroom na wuce na shiga wanka. Bayan na fito na gyara jikina da ƙyau kamar yanda na saba sannan na fito. A'i ce ke tambayata ina zanje. Kai tsaye na bata amsa aikin da zanyi na dawo. Babu wanda yace komai face a dawo lafiya da Bahijja tai min. Nayi mamakin samun Hajiya Mammah a kitchen ɗin yanzu ma, sai dai ban nuna ba face gaisheta da nayi na fara ƙoƙarin haɗa kayan abincin. Ita kaɗaice a ciki babu Mama Balki. Ina gab da kammalawa akai kiran wayarta, sam ban maida hankali a kanta ba balle nasan da wanda take wayar, sai da ta ajiye kan wayar ta kirani da “K!” sannan na juyo.       Cikin yanayin kafeni da idanu tamkar zata cinyeni da su ta ce, “Ki haɗa abincin nan a wani tray ki kaima Awwab sashensa ki dawo yanzu ina jiranki.” ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sai da ta daka min tsawa sannan na amsa mata da to. Yanda ta bada umarni haka nayi, na haɗa komai a wani tray ɗin daban sannan nace mata, “Mammah ban san sashensa ba ai”. Shiru babu amsa, na ɗago na kalleta sai naga ta zuba min idanu ne kawai kamar ɗazun. Jinai raina ya fara ɓaci da kallon ƙurillar nan nata. Amma sai na dake na sake maimaita mata tambayar tawa. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tana mai ɗauke kanta daga gareni, sai kuma ta fice tana faɗin na biyo ta....       💢🌟💢🌟💢    💢✨💢✨💢         Cike da kulawa da tattali bayan Abba ya kammala cin abinci Mom ta kwanto jikinsa. Sai da ta saka hannunta cikin nasa murya a narke ta fara magana da kissa. “Nagode sosai Abban Abbas. Dan ALLAH ina sake roƙonka ka yafemin kuskuren da nayi, wlhy sharrin shaiɗanne amma bazan sake ba. Ni nasan kai mutumin kirki ne, dan gashi ka tabbatar min da hakan ta hanyar gyaran gidan nan da kayi. Kaga zamuyi bikin nan cikin mutunci batare da muma anga raggarmu an rainamu ba”.       Shiru Abba baice mata komai ba. Sai wani murmushin da ya saki mai faɗi da akwanakin nan baya barin fuskarsa. Ganin haka itama sai ta sake lafe masa a jiki da kai hannunta saman fuskarsa tana shafawa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata ba dan shima yana buƙatar hakan duk da gobe in sha ALLAHU amaryarsa zata iso gidansa. Amma yasan cakwakiyar da gobe zatazo da shi ba lallai ne ya kai ga hutawar ba. Dan haka ya biyema Mom ɗin. Sosai kuwa ya sami nutsuwa dan an bi da shi ta hanyoyin da shi a karan kansa sai da ya manta kan nasa.........✍️ _Hummmmm Abba adai bi a sannu ehe🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama       _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Washe gari Mom ta tashi da shirin komawa sashen da akaima gyara. Sai dai tsabar wuce wuri batayi hakan kai tsaye ba ta shiga gayyato ƙawayenta da maƙwafta ta waya wai zata shirya walimar komawar tare da bikin baikon Baby. Aiko zuwa sha biyu sai ga gida cike da ƙawayenta da maƙwafta da take ɗan gaisawa da su. Gida fa yaci decorretion harda su dj. Ana gab da fara shagali Gwaggo Gudidi da yaranta da wasu a dangi suka fara isowa da kulolin abinci. Duk da al'amarin ya bama Mom matuƙar mamaki sai tayi ƙoƙarin ajiye komai gefe tai tunanin ko Abba ne ya sasu suzo dan su tayata murnar baikon Baby ɗin. A take kuwa ta hau musu gwalangwaso har da habaici ƙawayenta ke jefa musu. Isowar su Gwaggo Gudidi baifi da mintuna talatin ba sai ga mata har mota guda daga Gwarzo. Sai ga Musaddiq da ruwa da drinks masu yawa. Anan ne fa al'amarin ya fara girmar kan Mom, ta tare Musaddiq da tambaya. Rasa amsar da zai bata ya sashi faɗin, “Mom kuyi magana da Gwaggo kamar zaifi”. Daga haka ya juya yay ficewarsa ya barta da kallon kallo tsakaninta da ƙawayenta. Zabura tayi hankalinta a tashe zata fice a ɗakin dan dama kwalliya ake mata ƙawayen nata suka dakatar da ita. Sune suka tausheta kan ta dakata dai Abban ya shigo taji mike faruwa a bakinsa kamar zaifi. Badan taso hakan ba ta dakata sai dai ta shiga dokama Abba kira ta waya dan rabonsa da gidan tun da safe. Shiru bai ɗauka ba har kusan kira biyar, sai da wata ƙawar tata dai ta fargar da ita lokacin salla ne maybe yana massalaci sannan ta dakata. Bayan kamar mintuna biyar dan ita ko sallar ma bata nema yi ba, dama can ba damunta tai ɗin ba balle yanzu da aka zuba kwalliya. Bugu ɗaya kuwa Abba ya ɗauka, sai dai tana fara magana ya dakatar da ita da cewar gashi nan tafe gidan. Wayar ta cillar tana kaiwa zaune wutar bala'i na cin zuciyarta. Ko mintina ashirin kuwa ba'a cika ba su Abba suka iso. Tsaiwar motoci da jin buɗe-buɗe ya saka zuciyar Mom harbawa da masifar ƙarfi. Hakama ƙawayenta gaba ɗaya sukai tsitt da surutun da sukeyi dan tabbatar da inda ghuɗa ke fitowa....        💞✨💞✨💞         Muna fitowa mukaci karo da mama Balki. Ita ta bama umarnin rakani sashen ita kuma tayi gaba. Gani nayi Mama Balki ta sauke ajiyar zuciya. Kamar ba itace duk na ga cikin damuwa ba yanzu. Har ƙofar da zata sadani da sashen nasa dake ta cikin main perlor ta nuna min. Nai mata godiya na shige kaina tsaye dan naji farin cikin sakani wannan aiki da akayi. Hanyace mai ɗan tsayi daga main perlor ɗin kafin akai ainahin sashensa. Tun daga cikin dogon corridor ɗin zaka iya shaida mayataccen ƙamshin turarensa da baya ɓoyuwa a duk inda yake. Baki na taɓe tare da yamutse fuskar takaici. Dan ni kaɗai nasan kalar rashin mutuncin da yau zan zazzage masa tunda na samu damar ganinsa matsoraci kawai, ba ruwana da rashin lafiyarsa ba raga masa zan ba. A rufe ƙofar da zata sadaka da sashen nasa take. Dan haka na danna bell da ɗan ƙarfi ina hararar ƙofar. Shiru babu alamar za'a buɗe min har cikar minti ɗaya. Sake dannawa nayi nan ma shiru, na bada wasu sakanni babu dai alamar za'a buɗe ɗin. Cikin fusata na danna bell ɗin da ƙarfin tsiya batare da na ɗaga yatsana a kai ba harda su cije baki. Sai gashi kuwa an buɗe ƙofar kamar a fusace. Baki na taɓe da ɗaga ido dan ganin wanene ya buɗe ɗin, sai a cikin mayun cat eyes ɗinsa kuwa. Yanda yay wani masifar yin kicin-kicin da fuska gashi ya tsatstsareni da idanu ya sani sake tamke tawa nima ina laɓe baki. Ɗauke nasa yayi tare da juyawa ya bar wajen. Da kallo kawai na bisa cikin yanayin harara. Sosai ya zube a tsaye cikin ƙanƙanin lokaci, sai dai a zahirance bazaka taɓa ma yarda baida lafiya ba dan yana nan a dakensa. Kamar bazanbi bayansa ba sai kuma dai nabi shawarar da zuciyata ta bani, dan haka na sunkuya na ɗauki basket ɗin nabi bayan nasa ina kwaikwayon yanda yake tafiya. Ina saka ƙafata a katafaren falon da ya haɗu ya gama haɗuwa shegen karen nan nasa dana taɓa gani a Kano ya taso a zabure. Ai bamma san na fasa ƙara da ƙoƙarin sakin tray ɗin ba. Sai dai jin ban faɗi ba ni da tray ɗin ya sani buɗe idanun nawa a hankali ina mai sauke ajiyar zuciya. Kallon cikin ido mukaima juna. Ban san lokacin da numfashina ya fisga ba alamar neman barin ƙirjina da gangar jikina, da ƙyar na fisgoshi na maidoshi cikin ƙirjina ina sake waro idanun nawa waje gaba ɗaya. Shima sake tsatstsareni yay da nasa tamkar zai cinyeni da su duk yanda naso haɗiye razanata ta ganin karen nasa tsaye a kusa damu na kasa hakan. Illahirin jikina da duk wata gaɓa da jini ke gudana ta cikinta sun bar aiki. “K! Baki gajiya da pretending ɗin faɗuwa dan a tare ki”. Ya faɗa a daƙile cike da rainin wayo. Har cikin tsakkiyar kaina naji haushin furucin nasa. Da sauri na sakesa gaba ɗaya tare da ƙoƙarin turashi nima nai baya. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar bai fahimci abinda na jima haushin ba. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin yayi maganar ne dan raha. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga mamakin mutumin nan da rashin mutuncinsa ga shegen sonma mutane sheri. Kamar ko yasan mi nake tunani akan nasa ya raɓani ya wuce yana mai kiran sunan shegen karen nasa acan ƙasan maƙoshi. Da gudu kuwa ya bisa yana wani kaɗa bindi. Da harara ba rakasu su duka tare da ajiye basket ɗin hannun nawa ina bin falon da kallo. Dan babu ƙarya ya haɗu iya haɗuwa. Karaf kuwa sai idanuna suka sauka akan wayoyinsa dake a saman Centre table ɗin har uku, sai laptop a gefensu. A take wani tunani yazo min. Cike da rawar jiki da zumuɗi na ɗauka ina addu'ar ALLAH yasa babu password. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da shiga loda number ɗin Mansoor. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba. Kamar zan sake kira sai kuma na fasa na saka ta Yaya Musaddiq.       “Mr M” ya fito ɓaro-ɓaro. Da mamaki nake kallon sunan da sake duba numbers ɗin. Number ɗin Yaya Musaddiq ɗin ce dai. To miya kawota cikin wayar wannan mutumin? Bani da mai bani amsa, dan haka nai dialing kawai dan tabbatar wa. Bugu biyu kuwa aka ɗaga, na ɗan yi shiru. Sai ko ga muryar Yaya Musaddiq tar-tar yana sallama. Sai dai muryar tasa a ɗashe alamar barci ya tashi ko yake son yi. Maimakon amsa sai hawaye suka cika min ido. Muryata na rawa na furta, “Yaya!”.      Ina jin alamar yanda ya zabura. Sai kuma cikin rawar harshe ya furta, “Samraah ke ce?”.       Kuka na sakar masa kawai maimakon amsawa. Sai naji duk ya sake rikicewa. Kukan na sake fashe masa da shi da faɗin, “Yaya anya kana sona har yanzu kuwa?. Tsahon wata guda mutumin nan ya sace ni ya sace min Mansoor ɗina amma babu ku babu labarin ku. Yaya ina Mansoor ɗina kada ya halakar min da shi.....”          Cikin wata irin sautin sauke ajiyar zuciya Yaya Musaddiq ya tari numfashina. “Samraah relax. Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya ɗauki Mansoor yana gidansu. Shi kuma wannan ɗin shine mijinki yanzu ba Mansoor ba. Yayanki kuma na sonki har gobe da jibi da gatan gata ma”.       “Yaya!!!”.     Na faɗa a matuƙar razane jikina na rawa, dan duk da shi ɗin ya sanar min shi mijina ne jin tabbaci a bakin Yaya Musaddiq ɗin sai ya sake sakani a matsanancin ruɗani. Sake tareni yay da faɗin, “Nace ki kwantar da hankalinki dan ALLAH Samraah. Yanzu yaya jikin naki kuma?”.      “Yaya taya kake son na kwantar da hankalina? Ta yaya kake son kaji naji sauƙi? Bayan an ɗaura min aure da Mansoor na ganni kuma tare da wani ace na kwantar da hankakina”.          “Samraah dama ba'a ɗaura miki aure da Mansoor ba. Da shi ɗin dai wannan mai suna Muhammad aka ɗaura miki aure. A yanzu kuma shine mijinki. Ki manta da Mansoor da duk abinda ya shafesa dan ALLAH ki fuskanci sabuwar rayuwarki da in sha ALLAHU muna fatan bazamuyi nadamar kaiki cikinta ba. Haba Samraah kefa mai ilimice. Har kin manta da wannan rayuwar izayar ta gidan Abba da kika sha ne?”.     Baki na buɗe zanyi magana hawaye na rige-rigen sakko min kawai naji an zare wayar. Gaba ɗayana na juyo, dai-dai yana yanke kiran da jefa wayar cikin aljihun wandonsa. Afusace nake kallonsa, shima ɗin kallona yake tsakiyar ido. Tsahon minti ɗaya muna a haka batare da ɗayanmu yayi yunƙurin janye nasa ba wayar daya ƙwace a hannun nawa kira ya shigo cikinta. Nasa idanun ya janye tare da zaro wayar daga aljihun daya sakata, ya ɗan tsira mata idanu na sakani kafin naga ya kaita kunnensa tare da barin wajen ya nema kujera ya zauna. Da farko ban fahimci dawa yake wayar ba, sai da ya ɗago ya kalleni cikin yanayin ɗage gira da amsar da naji ya bada sannan. Da sauri na nufesa, babu zato yaji na zare wayar nima kamar yanda yay min. Kafin yay wani yunƙuri na nufi ƙofar dana shigo da gudu. Sai da naje jikinta sannan na juyo na masa gwalo nai ficewata.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ___________ .......Ba Mom kawai ba hatta ƙawayen nata sumar tsaye duk sukayi. Sai da suka sake jinfa tabbas a cikin gidanne sannan suka fara rige-rigen fitowa. Tamkar Mom zata tashi sama tai dirar mikiya a gaban wanda ke riƙe da amarya Halime. Cikin huci da fara birkicewa ta furta, “Kai lafiya? Daga ina haka? Su wanene ku?”.      Murmushi Hajiya Asabe uwargidan mai anguwa ta saki. Cikin dattako da cikar kamala ta bata amsa da, “Baƙi ne na alkairi da ga jihar Katsinan dikko ɗakin kara, kunya garemu tsoro babu”.        Duk da har cikin rai Mom taji shakkar matar, dan duk da mazauniyar ƙauye ce irin matan nan ne da aji a cikin jikinsu yake. Duk da dama can ita ba haihuwa da girman ƴan tumakin bace aurene ya kaita ƴar asalin cikin birnin Katsina ce. “Ke matsayinku ya dama, ni ba wannan ne matsalata ba. Wannan abar da aka lulluɓo nake son sanin matsayinta da dalilin shigowarku gidana”. Tai maganar tana nuna Halime da ke lulluɓe lafe a jikin Innarta Suwaiba. Duk abinda Mom ɗin keyi kuma tana jinta. Dan murmushi ma take yi ta cikin gyalen.      Kai tsaye Hajiya Asabe ta sake bama Mom ɗin amsa da, “Wannan ba huruminmu bane ba, inaga mijinki ne ya cancanci baki amsar kamar”. Daga haka ta sake jan hannun Halime zasu wuce. Idon Mom ya fara rufewa kuwa. Tana shirin sake magana Gwaggo Gudidi ta iso wajen, dama tana sallane shiyyasa bata fito a ƴan tarbar amaryar ba. Ko kallon inda Mom take batai ba ta shiga yima baƙi lalale marhaban, tare da isa inda Halime take ta kama hannunta tana faɗin, “Sannu da zuwa ɗiyata sannu kinji ƴar albarka”.        Yunƙurawa Mom ta sake yi a fusace zatayi magana wata maƙociyarta ta riƙeta. Cikin raɗa-raɗa ta ce, “Maman Baby kwantar da hankalinki, inagafa mutanen nan so suke kawai suyi yawo da hankalinki. Anya ba matar ɗanku bace Musaddiq”.        Da dauri Mom ta dubeta da idanunta da sukai jazur, cikin ɓacin rai da tashin hankalin daya gagara ɓoyuwa gareta ta ce, “Maman Nana Musaddiq kuma? Shine dan Musaddiq zaiyi aure sai a munafunceni? Sannan tayaya ma shi Imam zaiyi gangancin kawo min matar Musaddiq mu rayu a gida ɗaya. Kenan ma su ƴaƴana sun rako na wasu ne duniya”.      Ɗan jimm Maman Nana tayi, sai kuma ta jinjina kanta cike da gamsuwa. “To amma Maman Baby idan fa har ba hakan bane to tabbas Abban Abbas ne yayo aure batare da kin sani b....”      Wata muguwar ashariya Mom ta lailayima Maman Nana tare da wanke fuskarta da mari. Tuni hankalin kowa ya fara dawowa kansu. Dan kafin Mom ta sauke hannunta itama Maman Nana ta sauke mata marin. Su kam dangin amarya tuni sun gama shigewa cikin ɗaki da amaryarsu batare da sunbi takan hayaniyar data kaure tsakanin Mom ɗin da Maman Nana ba. Zaburar Mom da nufar sashen amaryar ya saka Gwaggo Gudidi cimmata ta tare ƙofar. Ƙoƙarin tureta Mom keyi cike da raini Aunty Na'ima ta janyeta rai ɓace. “Wai ke Jalilah miyasa baki da isashiyar tarbiyya ne? Ke yanzu sai ki ture Gwaggon kike nufi?”.         “Yo mizai hana nayi hakan, ai ni idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba, nima bazan ji kunyar kado shi ƙasa ba kuwa wlhy.”      “K Jalilah ki shiga hankalinki wlhy dan yanzu ba da bace. Kin kuma san ko ada ɗin ma ana ƙyaleki ne darajar wanda ya kwasoki cikinmu amma badan ana jin tsoronki ba. Hauka kuma dama kin saita kanki kafin ɗan sauran mutuncinki daya rage ya ƙarasa zubewa. Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys”.        Cak numfashin Mom ya tsaya tare da harbawar zuciyarta. (Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys) kalaman suka shiga maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarta cikin amsa kuwwa. A hankali ta ɗago tana kallon Aunty Ni'ima, sai kawai idanunta suka sauka akan Abba daya shigo. Rawa jikinta ya farayi, cikin ɗimuwa da sassarfa ta nufesa. Cak ya tsaya yana kallonta harta ƙaraso inda yaken. Yanda ta cakumo hannunsa zai tabbatar maka da bata a cikin hayyacinta, dan harshenta har sarƙewa yake wajen faɗin, “Abban Abbas wacece wannan aka kawo min gida? Matar wacece? Dan ALLAH kace min Abbas kaima aure”.        A hankali ya girgiza mata kansa tare da riƙo hannunta. “Jalilah Please relax mana..”    “Naƙi nayi relax ɗin Imamu ka faɗa min wacece ita?”.       “Zan faɗa miki amma ki muje daga ciki”.     “Wlhy babu inda zanje sai ka faɗa min anan. Kuma kaima ɗin baka isa kabar wajen nan ba....”     Gwaggo Gudidi ce ta ƙaraso wajen. Idonta akan Abba ta ce, “Miye kake wani zazzame mata Imamu, ka fito fili ka faɗa matan tunda ita ta nema da kanta. Ai shiyyasa ake son mace ta zama matar ƙwarai kodan irin wannan ranar. Idan ka zama ɗan arziƙi mai tarbiyya taya har miji zai ɗakko maka abokiyar zama batare da saninka ba. Ai dama halinka sabulun wankanka. Mata dai taka ce muma duk mun shaida. Hargowarta ko shirmenta bai isa sakawa a goge hakan ba. Dan in har kai gigin sakin wannan baiwar ALLAHr daka auro koda bayan raina ne wlhy kaf mu ahalinka bazamu yafe maka ba. Ballema nasan bazaka fara kwatanta hakan ba dan kaima kana ƙaunar matarka. Dan haka ka fito ka sanar mata aure ka ƙara dan bazaka cigaba da zama daga kai sai ita a cikin gida ba ta kasheka watarana kamar yanda ta rabaka da duk danginka damu iyayenk.....”         Babu wanda ya san ta yanda akai kawai hannun Mom aka gani a wuyan Abba ta cakumosa. So take tayi magana amma hakan ya gagara saboda numfashinta ma fisga yake. A mamakin kowa sai gani sukai tayi baya gaba ɗayanta alamar suma. Ƙasa take neman zubewa sai da Abban ya riƙota..... 🌜🥱🌛      Tunda tabar falon bai iya ya motsa daga inda yake zaune ba. Sai ma tsurama ƙofar da tabi idanunsa yay tamkar tana a wajen har yanzu. Yana nan zaune kusan mintuna goma shigowar Hayatu ta katse tunanin nasa. Koda Hayatun ya gaisheshi ma hannu kawai ya ɗaga masa. Shi dai Hayatu ya riga ya saba shiyyasa bai damu ba. Sai ma kaiwa da yay zaune bayan yaje gabansa ya ajiye takardun dake a hannunsa dan yau shi bai fita office ba sakamakon yini da sukai akan Hajiya Babba da likitocinta, tare da tsaftar sashenta aka fidda duk kayan da Samraah ta tattara dama sauran duk na sashen aka canja mata katifa kafin a kawo wasu. Shiyyasa Hayatun ya kawo masa duk wani document mai muhimmanci da zai duba ya saka hannu...           Ina fita na saki murmushin farin ciki. Yau dai na samu wayar yin magana da ƴan uwana. Duk da ko a da da nayi niyya zanyi hakan dan su Bahijja duk akwai waya a hannunsu. Abinda yasa ban taɓa ara ba saboda bana buƙatar kowa yasan sirrina. Farin cikin waya ya mantar dani wani batun aikin Hajiya Mammah. Dan amaimakon kitchen daya kamata na koma ficewata nayi daga sashen baki ɗaya ko su Azizat dake zaune acan rukunin ƙarshe na kujeru bana tunanin sun ma ganni. Ban nufi sashen mu ba na wuce garden ɗin gidan. Tsabar wuce wuri kuma maimakon babban garden sai na shige ƙaramin da akace nasa dan na samesa a buɗe da'alama aikin gyarashi akayi saboda kayan aiki dana gani an tule. Can na shige kusan ƙarshe duk dan dai na samu wajen ɓuya nai wayar a tsanake. Kaina tsaye na sake danna kiran layin Yaya Musaddiq. Sai dai harta katse bai ɗaga ba sai da na sake kira na biyu. Hayaniyar da naji ya sani faɗin, “Yaya ya nake jin hayaniya ko kana kasuwa ne?”.       Maimakon amsa ƴar dariya yayi da cewa, “Har kin gama darun?”.     “Kai Yaya ni har wani daru ne da ni?”.    “Sosai kuwa Kandalata. Ai ke naki ma na musamman ne.”    Karon farko na saki dariya, sai kuma na shiga gaishesa da girmamawa. Ya amsa min da kulawa tare da tambayar lafiyata da kuma jiyyar da nayi. Na amsa masa da Alhamdullah, tare da tambayarsa mi ake a gidan naji hayaniya. Kansa tsaye ya ce, “Mamarki akema kishiya”.     Da mamaki nace, “Mamata kuma Yaya? Wa kenan?”.        “Mom mana. Abba ne ya ƙara aure”.    Tuni na miƙe daga zaunen da nake dan mamaki, sai kuma na shiga ƙyalƙyala dariya. “Wai dan ALLAH yaya da gaske kake ko wasa? Mom fa akaima kishiya? Ta yaya Abba ya samu wannan ƙwarin gwiwar haka? A ina kuma ya samo matar?”.        Tsaf Yaya Musaddiq ya kwashe labari ya bani, tun daga zuwan Halime gidan har kawo yau da suke jiran isowar amarya batare da Mom ta sani ba. Tsabar farin ciki bamma san lokacin dana rangaɗa ghuɗa ba. Sai da Yaya yace min, “Ƙaniyarki kandala” sannan na bari ina dariya. Haka kawai nake jin raina fes da wannan al'amari. Dai-dai nan sautin muryar aunty Zakiyya data rangaɗa sallama ya ratsa kunnuwana. Bayan sun gama magana da Yaya Musaddiq yake cemata gani a waya. Amsa tayi cike da zumuɗi muka gaisa, kafin cikin raunin murya da lallashi ta ce, “Samraah shike nan kuma babu kira duk kinsa hankalinmu ya kasa kwanciya?”.      Murmushi nayi hawaye na cika min ido. Muryata na rawa na ce, “Aunty bani da waya ne. Kuma kuma kun sallamani ga wanda ban ko sani ba kamar bani da kowa a duniya”.       “Haba Samraah, shin bazamu iya haƙuri da karɓar ƙaddara ba a duk lokacin da tazo mana? A maimakon tada hankali a ganina godiya ya kamata muyima UBANGIJI dan a maimakon tozarcin da akaso ganinmu a ciki alkairi ne ke lulluɓe da mutuncin mu. Samraah kiyi haƙuri dan ALLAH, ki karɓa da hannu biyu sai ALLAH ya sauƙaƙa komai a yanda ba kowa yay zato ba. A kowace daƙiƙa ta rayuwa kuma kina ranmu. Kawai dan bamu san ta yanda zamu sameki bane ba”.      Babu daɗi kalamanta suke sake saka ni. Dan haka na sake raunana murya, “Aunty kina nufin maganar da wannan mutumin ya faɗa da Yaya gaskiya ce? Da shi aka ɗaura min aure, kuma aka kawo ni garesa? Shike nan kuma kun barmasa ni?”.         Ƴar dariya tayi, cikin wasa ta ce,.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_ _________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _____________ ........“Ya zamu bar masa ke. Sai dai ya ɗauki rabi ya bar mana rabi. Ke dai ki kwantar da hankalinki kinji. In sha ALLAHU ni da Musaddiq muna nan tafe har inda kike. Dama a tunaninmu idan kinji sauƙi zai dawo mana dake gida ne shiyyasa. To amma uzirin daya kawo akan zaman naku anan yanzu dole a haƙura har sanda ya kawoki da kansa ɗin. Ni dai kawai roƙona ki kwantar mana da hankalinki, ki mance da Mansoor kamar yanda mahaifiyarsa ta buƙata, ALLAH shine shaidar mu ba laifinmu bane sune sukaƙimu. Dan a ranar ɗaurin aurenku mahaifiyarsa da kanta tazo tace sun fasa ɗanta bazai aureki ba saboda ba'a san mi aka aikata miki ba da akai kidnapping ɗinki. Babu yanda su Kawu Musa basu lallasheta ba har gwaji sukace aje ai miki amma fir matar nan taƙi sai ma cin mutunci da gori data shiga musu. Suko sun san mutuncin kansu ai, dan haka suka janye suka bama wannan bawan ALLAHn ke dan su mutuntaki da mu kammu. Dan inba hakaba wannan mugun baƙin fentin da sukai miki zaita bibiyar rayuwarki ne harma mijin ya gagara gareki a gaba”.          Sosai maganganun aunty Zakiyya suka ratsa min jiki. Mamaki da al'ajabin mahaifiyar Mansoor ya tsaya min a zuciyata. Harna kasa daurewa na ce, “Amma Aunty shi yaya akai yasanni yazo neman aurena? Ko su kawun sun sanshi ne su?”. “To ni dai bazance ba gaskiya. Amma dai kamar naji ance shine yazo yace yana son aurenkin da kansa. Ki dai tambayi Gwaggo tasan komai kuma nasan zata sanar miki. Ko kuma shi mijin naki ki tambayesa ai bazai ƙi sanar miki ba”. Shiru nai tsahon lokaci na kasa cewa komai. Sai kuma can na ce, “Okay Aunty in sha ALLAHU zan tambayesa”. Nasiha suma suka min cikin lallashi ita da Yaya Musaddiq. Bayan munyi sallama na jima zaune a garden ɗin ina tunani kafin na miƙe na koma sashenmu bayan na kashe wayar na sakata a jikina. Ina shiga Aunty Sadiy ta shigo wai naje Hajiya Mammah na kirana. Idanu na ɗan waro dan harga ALLAH nama manta da batunta... A ɗarare na tafi amsa kiran nata, sai dai cikin sa'a ina zuwa na samu wai tana da baƙuwa sun ma fita yanzun nan. Ajiyar zuciya na sauke na juya na koma ina godema ALLAH. Dan dana sameta ban san mi zance ba wajen kare kaina. ✨★✨★✨     Da ƙyar aka samu Mom ta farfaɗo. Tana kuwa farfaɗowar wasan ya koma sabo. Dan tuni Ummanta da su Baby da basa gidan sun dawo harma da wasu ƴan uwanta. Faɗa ne mai ƙarfin gaske ya ɓarke tsakanin dangin Mom da ita kanta da dangin Abba. Dan dangin amarya su dai ƴan kallo suka zama. Sai dai kuma ransu ko ɗar balle gezau akan ƴarsu bazata iya zama ba. Sai ma murna suke da rahamar da UBANGIJI yay mata na samun wannan danƙareren gida a matsayin gidan aurenta. Itama ɗin dai Halimen ko'a kwalar rigarta. Yo ita wane kalar masifa da bala'i ne bata gani a wajen Innarta ba. Sannan faɗan kishi babu irin wanda ba'ayi a gidansu. Dan kaf matan kawunanta ba su ɗaɗɗaya bane Innace ma kawai ita kaɗai a wajen Baba. Amma sauran daga mai mata uku sai mai biyu harma da mai huɗu. Kuma haka ake shan cakwakiya a gidansu gashi gidan yawa. Ita dariya ma abinda ke faruwa ke bata. Sai da Hajiya Asabe ta ƙwaɓeta daga yanda take kwasar dariya tana leƙe ta window sannan ta nutsu.      Shi dai Abba ma tuni ya fita ya bar musu gidan bisa umarnin Gwaggo Gudidi. Haka aka ci uwar sabada mata anguwa nata shigowa. Masu yima Mom dariya da ALLAH ya ƙara sunfi yawa. Dan har a cikin ƙawayen nata wasu abin ya musu daɗi. Ummanta ce data fahimci al'amarin fa shiryayye ne dan dangin Abba sun kafa sun tsare yasa ta janye Mom ɗin suka shige ɗaki. Ba'a sake ganinta ba har kusan goma na dare sai ga likita wai yazo zai dubata hawan jininta ya tashi. Babu wanda yabi takan batun kowa ya cigaba da sabgarsa. Sai ita da ƴaƴanta da Ummanta ke ƙulle-ƙullensu can a sashenta su kaɗai.       Har washe gari daga ɓangaren Mom dai babu daɗi, gashi Abba yaƙi shiga inda take tun dubatan da yaje yay na farko bai sake zuwa ba, dan yana shiga ta sake birkicewa harda shaƙeshi tana kuka da faɗin sai ta kasheshi sai dai duk su rasa. Har ita  zai tozarta yama kishiya, to wlhy ya sani ya ɗakko bala'i da masifar da bazata taɓa ƙarewa ba har sai cikin abu uku ɗaya ya faru. Kodai ta kashesa, ko kuma ya saki yarinyar a yau danginta su koma inda suka fito da ita, ko kuma idan ita ta mutu. Kuma koda ta mutu yace zai sake aure sai ta dinga masa fatalwa. Abin nata kamar wasa ya nema zama babba, dan da ƙyar aka fiddo Abba a ɗakin tana neman murɗe masa jikinsa ALLAH dai ya taƙaita masa wahala akwai babbar riga tare da shi.         Su dai ƴan uwansa da dangin amarya sabgar gabansu suke hankali kwance dan basu san mike faruwa a cikin ba sai da su Gwaggo Gudidi suka fito da Abba ne suke jin komai. Aiko fa kowa ya shiga ALLAH wadarai da wannan baƙin hali na Mom, daga nan kowa ya sake ɗaura ɗammara a kanta. Dan a ranar dangin amarya sukai walima tare da rabon kayan gararsu cikin bajinta da aka san katsinawa da ita a wajen rabo. Al'amarin ya ƙayatar da kowa a dangin Abban, sun kuma yaba da ƙoƙarin mutanen. Ana yin sallar azhar motocin da zasu maidasu gida suka kwashesu aka bar amarya Halime na kwasar kuka. Sai da su Aunty Zakiyya suka jata ɗaki suna lallashi. Daga ƙarshe ma dai su suka cigaba da zama da ita suna ɗebe mata kewa har washe gari da suma kowa yay haramar kama gabansa bayan sun kimtsa gidan. Har kuma sannan babu wanda yaga idon Mom. Sai dai duk sun fahimci akwai abinda suke ƙullawa ita da uwarta dan sai shigi da fici Ummar tata keyi a kwana biyun nan, saboda rashin sanin ciwon kai a gidan take kwana itama har a yau da bikin ya tashi. Ƴan Gwarzo ma sun rigata wucewa. Ganin bata ma da niyyar tafiya ne yasa Gwaggo Gudidi itama ta fasa tafiya a yau duk da dai dama wasu a dangin sun kawo shawarar Gwaggon ta ɗan zauna har gidan ya dai-daita gudun kar'a cutar da yarinyar mutane. Kowa kuma ya gamsu da shawarar dan haka Gwaggon tai zamanta. Sai hakan kuma yayima Abban daɗi shima. Dan dama yana tunanin ta yanda zai fita yabar Halime daga ita sai Mom ɗin a gidan har sai ya gama saita gidan...      💦💥💦💥💦     Kwanaki biyar kenan da faruwar dukan da naci a sashen Hajiya Babba. Alhamdullah jikina yayi sauki, dan hatta ciwon da taji min ma ya warke sarai sai tabo. Tun wannan ranar ban sake gigin komawa ba duk da hankalina na'a kanta. Haka shima uban gayyar ban sake ganinsa a gidan ba. Sai ma a bakin Mama Balki nake jin wai yayi tafiya ai tun a washe garin faruwar al'amarin da dare. Ranar da Hajiya Mammah ta aikani sashensa kai masa coffee kenan harna taho masa da waya. Bakina kawai na taɓe na cigaba da harkar gabana, dan damuwar data daman daban, duk da kuwa tana da alaƙa da shi. Sosai ina buƙatar zama dashi a wannan gaɓar, dan ina son jin yanda akai har ya je gidanmu ya nema aurena. Ai abin da mamaki, dan Mansoor mahaifiyarsa ta hanashi aurena shi kuma ace yaje ya auran bayan babu wata alaƙa data alaƙanta tsakanina da shi bayan ta kidnapping ɗina da yayi da hira da nai da shi a station ɗinmu...             Zuwa yanzu aikina ya koma sashen Hajiya Mammah, nice kullum mai mata gyaran sashenta safe da yamma. Da farko dai abinda na fara fahimta ga halayyar matar shine nuna isa da mulki. Na biyu shegen kallon raini na ƙurillar tsiya kamar zata cinyeka da idanu. Sai masifa komai kayi sai ta maka jaraba kamar itace ta halicceka. Shiyyasa idan na tashi kafin ma ta tashi a barci na gama gyara ko'ina nabar sashen, sai kamar 11 sai na koma na gyara mata bedroom lokacin ta fito. Yau ma kamar kullum da wuri na kammala aikin nawa, sai dai ina ƙoƙarin sauka dawn stairs na jiyo kamar sautin kuka na fitowa ta sashen Hajiya Babba. Tsamm nayi da raina kusan mintuna uku, jin dai da gaske tanan ɗin ne bamma san lokacin dana juya cikin sauri da sassarfa ba. Idanuna a rufe na faɗa sashen batare dana tuna da wahalar dana sha a hannunta kwana biyar da suka wuce ba. Ganin key a ƙofar ya sani murɗawa na afka ido rufe, jikina har rawa yake jin sautin kukanta da yanda take ambaton kiran sunan “Muhammad” dan zuwa yanzu na fahimci Maash kadai suke kira Muhammad a gidan ita da Paah. Zubewa nai a inda take zaune can karƙashin ƙafar bene ta cure jikinta waje guda fuskarta cikin ƙafafunta.          “Ummi miya sameki? Baki da lafiya?”. Na faɗa cikin rawar murya ina kamo hannayenta dake ɗauke da sayin ɗauri har yanzu amma duk ciwukan sun warke. A mamakina sai naga ta ɗago a hankali. Yanda idanunta suka kumbura sukai jaa sosai ya sake tayar min da hankali. Ga hawaye face-face da fuskar tata. Sai kawai nima na fashe da kuka tare da faɗawa a jikinta. Tsamm ta rungumeni itama tana ƙara fashewa da kukan da cigaba da magana cikin sambatu. “Muhammad ciwo, kaina ciwo zai fashe Muhammad. Ga jikina ƙaiƙayi yake min. Muhammad ina jin yunwa”.        Kuka na sake fashewa da shi ina mai ɗagowa a jikin nata. Amma sai ta hanani tashi ta sake matseni sosai. Duk da zafin da nake ji ban sake yinƙurin tashin ba. Tsahon mintuna biyar muna a haka har na fara numfashi da ƙyar. Sai kuma ta sakeni ta dafe kanta da riƙe cikinta. Zumbur na miƙe jikina na rawa, ga hawaye sun kasa tsaya min, “Kiyi haƙuri Ummie ki daina kuka dan ALLAH, yunwa kike ji ko?, Zakici abinci na kawo miki?”.      A mamakina kai ta ɗaga min tare da kamo hannuna ta ɗaura a saman cikinta hawaye na sharara ta shiga jujjuya min kanta. Ta ce, “Yunwa Muhammad yunwa”.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .......Da sauri na jinjina mata kai ina ƙoƙarin miƙewa. “To Ummie in sha ALLAHU yanzu zan kawo miki abinci bani ɗan lokaci ƙalilan.” ban jira amsawarta ba na tashi na fita a guje dan nasan bama amsawar zatai ba. A falonta na farko naci karo da wasu mata guda uku sabbin fuska daban sani ba a gidan. Nayi mamaki dan ɗazun ban gansu ba, ko kuma ban lura dasu bane oho. Takan kowa banbi ba a cikinsu nafice zuwa downstairs na afka kitchen, ganin an gama komai har an gyara kitchen ɗin ma fito dining, komai an shirya na breakfast, sai dai babu kowa a kai dan sai sun gama barcin safensu suke fitowa karyawar. Hajiya Ƙarama ce kawai bata a gidan ta wuce wajen aiki. Komai sai da na ɗiba tare da haɗa shayi mai ƙauri na ɗauka ruwa. Da gudu na koma saman, inda na barta nan na sameta, sai dai yanzu tana kwance ta naɗe a waje guda sai nishi take alamar yunwar tacita ta cinye matan nan na tsaitsaye a kanta kamar a tsorace. Ina shigowa duk suka zabura kanta. Tsawa na daka musu tare da nuna musu ƙofa alamar su fita. Har rige-rigen fitar kuwa sukeyi. Basket ɗin hannuna na ajiye, sannan na durƙusa gabanta na ɗagota. A jikina na sanyata ina kuka da bata haƙuri, shayin dana haɗa dai-dai zafi na ɗauka na kai bakinta, jikinta har rawa yake wajen damƙe kofin, tsam ta dafesa tare da hannayena kamar mai lafiya, kwal-kwal ta shiga kwankwaɗar shayin tamkar ta samu ruwa. Kafin wani dogon lokaci ta shanyesa gaba ɗaya, sai ga zufa na karyo mata tako ina ta fara sauke ajiyar zuciya jikinta na saki. Jinai hawaye sun ƙara ziraro min, na kwantar da kanta sosai a saman cinyata ina shafa cuɗaɗɗen gashinta daya danƙare saboda datti. Tabbas ɗiya mace daban ce, da ace baiwar ALLAHr nan nada ƴa mace a cikin ƴaƴanta duk tsanani bazata dinga barinta a cikin wannan dattin ba. Amma kalla yanda aka saketa kamar mara gata. Dukiyar tatace, gidan ma nata ne, ɗan da suke taƙamar da shi a yanzu haka nata ne. Amma ita bata san daɗin ko ɗaya a ciki ba, sai wasu banzaye da sukazo suka cika gidan badan su amfana mata da komai ba. In sha ALLAHU na ɗauki alƙawarin daga yau koda baiwar ALLAHr nan zata halakani sai na ƙwato mata ƴancin rayuwarta a gidan nan, tun daga kula da ita har zuwa sanin tushen wannan ciwo nata da nake ji a raina ba banza ba. Kai harma ɗan nata da alama ba haka suka barsa ba shima. Sai da na tabbatar shayin da tasha ya faɗa mata sosai sannan na jawo abinci, ban tasheta a jikin nawa ba, a haka na dinga bata da kaina kuma tana amsa. Sai kallona take dan har ta kauda kanta alamar ta ƙoshi idonta a kaina ƙyam. Lemo na ɗakko zan bata ta kauda kai, sai na ajiye na ɗauki ruwa. Ina saka mata a baki kuwa ta hau sha. Sosai tasha tana sauke numfashi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikina, mintuna bai fi biyu ba barci mai nauyi ya dauketa. Ganin barcin nata yay nisa na fara kwance mata kitson kanta da yay bala'in danƙarewa, da naga ta motsa sai na ɗan dakata, sai ta koma barcin sai na cigaba. A haka na kwance gashin tana barci a jikina. Sosai take da gashi, da alama shima a wajenta ya gaji wannan gashin nashin da yakema mutane iyayi da shi. Ganin barcin nata yayi nisa na lallaɓa na kwantar da ita, gyaran sashen na fara, harda wancan ɗakin da naci duka a ciki wancan karon. Da yake na saka aikin a raina kuma an rage dattin da yay wancan karon sosai koma nace an gyara komai ƙal sai dai ban san wanda ya gyara ba kafin wani dogon lokaci na kammala tsaff, amma ina zargin matan nan dana gani sabbin ma'aikata ne aka kawo mata, maybe kuma sune sukai aikin. Ko'ina sai ƙamshi yake kamar ba shi ba, ruwa na haɗa inata tunanin ta yanda zatai wanka, dan harga ALLAH jikinta na buƙatar wanka, saboda alamu sun nuna an ɗan rage dattin jikinta ba kamar a ranar farko dana sameta na, harma kayan bana waccan ranar bane ba, sai dai kamar kuma ba'a sake mata ba tun waccan ranar ɗin. Ni kuma bamma san ta yanda zan iya cewa zan mata ba dan ina jin kunya. Dabara ce ta faɗo min, na fita zuwa kitchen dan nasan yanzu sun dawo aikin rana. Babu kowa a falon kuwa, cikin sa'a kuma na samu Mama Balki a dining tsaye tana waya. Tana ganina ta yanke kiran. Sai da ta wawwaiga ta tabbatar babu kowa a wajen sannan ta kama hannuna. Can ƙarƙashin stairs muka je, fuskarta cike da damuwa ta ce, “Ina kika shiga Kandala? Tun ɗazun ake nemanki a gidan nan amma babu ke”.     Kaina tsaye nace mata, “Mama ina sashen Hajiya Babba fa. Yanzu ma kiranki nazo yi ki taimakeni”.       Sosai fuskarta ta nuna mamaki, ta ce, “Sashen Hajiya Babba fa?”.     “Eh wlhy Mama. Dan ALLAH kizo ma muje kiga taimakon da zaki min kafin wani ya gammu anan a hanamu. Bata musa ba muka hau upstairs. Ni kaina tsaye nake tafiya, yayinda ita kuma take ta faman waige-waige da gani duk a tsarge take. Ita kanta sai da tayi mamakin yanda na ƙara gyara sashen, Hajiya Babba dake kwance na nuna mata. “Mama ki taimakeni jikinta na buƙatar wanka ne. Idan akai mata zataji sanyi. Ga kanta na buƙatar wanki ma, sannan matan can dake zaune a falon farko wai su wanene?”.        Ɗan jimm tai alamar tunani, sai kuma ta amsa min da, “To yanzu yaya za'ayi kenan? Kin san fa dole aka saka mata ruwa a jiki dole ta farka. Kuma hakan akwai matsala shiyyasa ma Alhaji ƙarami ya hana a jika mata kai ranar. Waɗan can matan kuma sune sabbin masu aiki da Baba ya kawo tun ranar da abin can ya faru tsakaninku”.      “Mama in sha ALLAHU baza'a samu matsala ba. Dan yanzu da kanta taci abinci. Kota farka kuma da izinin UBANGIJI babu abinda zai faru mama. Su kuma ki gargaɗesu dan ALLAH ko kuma suje waje idan anjima sa dawo”.     Badan ta gamsu ba ta yarda da magana ta, da taimakona muka kamata zuwa bathroom. Sannan ta fita ban san yaya tayi da matan ba ta dawo. Sake ɗaukar ta mukayi zuwa toilet. Ganin ta buɗe idanunta alamar ta farka cikin ruwan dana haɗa a bathtub muka sakata. Da farko taso zabura, sai da na dafe mata hannu da sauri cikin lallashi da roƙo ga hawaye a fuskata ina tofa mata addu'a sannan ta haƙura ta koma ta zauna. Kanta muka fara ƙoƙarin wankewa, sai faman sauke ajiyar zuciya take a jajjere. Yanda wata muguwar dauɗa ke fita ban san lokacin dana ƙara ƙarfin kukana ba dan tausayi. Kai da kaga wannan baiwa kasan kafin lalurar na anyi manyan hamshaƙan mata. Amma jiba yanda ƙaddara ta maidata, ɗan adam kenan ba'a bakin komai yake ba. Bamu bar kan ba sai da ya koma fidda farar kumfa sol da ruwa mai ƙyau, baiwar ALLAH sai sauke ajiyar zuciya take, barci ma ɗibarta yake. Fitowa nayi nabar Mama Balki tai mata wanka, duk da na fahimci ita tana komai a tsorace ne. Sai dai Alhamdullah ta daure ta mata wanka na gaske duk da ni na fito duba kaya kozan samu. Anan dai ɗakin da muke babu, sai da na duba ɗayan kusa da ita dake a kulle sai nayi sa'an samu, ashe ɗakin duk kayan sawarta ne da duk wani abun buƙata na gyaran jiki. Da alama tana ɓatawa ne shiyyasa ake rufesa abar key ɗin a jiki, sai dai kuma babu tabbacin ana mata amfani da su, dan da jikinta baiyi wannan masifar dattin ba ai. Komai da za'a iya buƙata na ɗauka harda towel sannan na koma inda suke. Har lokacin basu fito ba, dan haka na miƙama Mama Balki towel guda biyu, na ajiye duk abinda zasu buƙata na fita dan ta samu damar shiryata. Ina daga falo zaune kusan mintinan talatin sai ga Mama Balki ta fito tana sharar hawaye ga murmushi akan fuskarta. Zumbur na miƙe ina tambayarta ko lafiya. Maimakon amsa saita jawoni jikinta ta rungume tana mai fashewa da kuka mai ƙarfi da sanya min albarka. Ban iya kwace jikina ba har sai da tayi mai isarta ta ɗagoni dan kanta. Hawayen nima na share kafin na sake tambayarta abinda ke faruwa.         “Babu abinda ya faru Kandala. Ke dai ALLAH yay miki albarka. Kin kwatanta abinda wani bai taɓaba a gidan nan. Ashe baiwar ALLAHr nan ba kowane lokaci bane take a yanayin da ake gudunta. Dama ƙyaƙyƙyawar mace ce mai ƙyawun siffa da cikar haiba amma ƙaddara ta maidata haka. Zo ki ganta Kandala zo kiga cikar zati da asalin kwarjinin manyan mata dan ALLAH”.     Jiki na rawa nabi Mama Balki. Muna shiga ciki sai da na kusa faɗuwa dan mamakin abinda naci karo da shi. Lallai anan Awwab ya gado cikakken ƙyawu da asalin kwarjini. Hatta da idanun magen nan nasa irin nata ne. Bamma san lokacin dana ƙarasa gareta cikin sassarfa ba na durƙushe, hannayenta duka na kamo a cikin nawa na runtse, tamkar wadda ke cikin hankalinta sai ta sakar min wani guntun murmushi tare da lumshe idanunta a lokaci guda ta buɗe sai kuma ta sake maidasu ta lumshe. Bamma san lokacin da ƙaunar matar ya ƙara mamaye jini da ɓargona ba. Nai zaman dirshan a gabanta na cigaba da kallonta tamkar na samu television. Tsahon lokaci ina a haka har sai da mama Balki ta fargar dani muyi mu fita kafin mutanen gidan su farga da zamanmu a ashen. Gashi su kansu wadancan matan bamu san a ƙarƙashin ikon wa suke ba. Kaina tsaye nace “To mama minene dan sun san muna anan? Dama ba so suke su sami mai kulawa da ita ba? Nifa waɗan nan matan bazasu cigaba da zama da ita ba sai dai su koma inda suka fito”.      “Hummm” kawai Mama Balki tace dani batare da fashin baƙi ba. Daga haka ta fita tana mai tabbatar min nayi sauri na kammala tunda tayi barci na fito ita zata koma akan bakin aikinta. Da to kawai na amsa mata badan zanyi yanda tace ɗin ba, dan tana fitar ma kayan gyaran gashi na jawo tare da gyara zama na hau gyara gashin Ummie. Gashine mai uban yawa ga tsayi shiyyasa nasha wahala sosai. Ban bar mata shi a haka ba nai zaman kitsa mata shi. Nan ɗin ma dai ansha cakwakiya kafin a kammala, dan takan farka ta dafe hannuna tana yamutsa fuska. Har sai na tsaya ta huta ina tofa mata addu'a sannan nake cigaba. Sanda muka gama barcinta yayi nisa sosai, dan haka na miƙe na tattare kayan dana kawo mata abinci ɗazun da wanda nai gyaran gashinta na maida inda suke na fita da sauran samo mata wani abincin. Kusan cin karo mukai da yarinyar da Bahijja tace min agola ce a gidan, tana ƙoƙarin hawowa upstairs ina ƙoƙarin sauka ni kuma. A ɗan yamutse da kallon raini tace min nazo ana nemana........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ .......Uffan bance da ita ba na cigaba da sauka ƙasan. Tunkan na ƙarasa nake jiyo hargowa da ihun Hajiya Mammah. Nadai dake na cigaba da sauka ina kallon Mama Balki dake durƙushe gabanta kamar ma kuka take yi, sai matan nan guda uku suma durƙushe a gefenta, ai kafin ma na ƙarasa gabanta nima naji saukar mari. A take azaba ta sakani watsar da kayan hannuna suka tarwatse a wajen. Ban gama dawowa a hayyacina ba ta shaƙure min wuya da faɗin, “K wai wacece? Ƴar uban wacece a ƙasar nan dazan ce ga abinda zakiyi ki canja da naki tsarin?”.      Sam bana ma fahimtar mi take faɗa, sai kakari neman fitar rai kawai nake ga idanuna sun gama firfitowa waje. Wani marin ta sake yarfa min sannan ta hankaɗani baya. Buguwa nayi da kujera da Azizat dake ta wajen, sai itama kawai ta sake hankaɗoni na dawo. Na gama sallamawa sai na kai ƙasa, amma a mamakina sai na jini a jikin mutum babu zato...       Tun faɗowarta jikinsa a bazata ya tsaya cak tamkar bishiyar kuka. Bai kalleta ba, bai kuma motsa ba, bai kuma janyeta a jikinsa ba. Sai dai fuskar ta sake wani irin tsukewa mai tsanani dake sake fidda ɓacin ransa muraran ga duk wanda zai iya kallonsa. Duk da shi dama ba abin wasan kowa bane a gidan yanayin fuskar yasa ta sake saka kowa firgita. Hakan yasa numfashinsu ɗaukewa gaba ɗayansu a lokaci guda. Daga masu ɗora hannaye duka a saman kai, sai masu wage baki, sai masu waro idanu waje. Hatta da ita kanta Hajiya Mammah ɗin ta shiga shock da ganinsa dan babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon. Amma da yake macece data goge a iya barikanci sai ta zaburo inda suke tana cigaba da masifa.          Har isowarta inda muke na gagara tashi a jikinsa. Saima ƙanƙamesa dana sake yi ganin takai hannu zata finciko ni. Jin bata fincikonin ba na buɗe idanuna dana rumtse. Sosai na warosu waje dan mamakin ganin shine ashe ya tare hannun nata da nasa. Ai zumbur na miƙe kan ƙafafuna na. Cikin ƙara zaburowa ta ce, “Barni Awwab naci uban yarinyar nan da bata da kunya da mutunci. Ni ban san a ina Auta ta kwaso mana ita ba. Baka san abinda tai ba da baka tare ni ba. Abinci na bada a kai sashen Hajiya Babba da magungunanta kafin naje na bata shine na tadda shegiyar yarinyar nan ta amsa a hannu masu kuka da ita tana floshing ɗin tables ɗin a cikin toilet saboda ita cikakkiyar ƴar iska ce. Kai dole ne ma musan miya kawota gidan nan yau”. Ta ƙara kai min duka. Kasa motsawa nayi a yanzu. Dan sumar tsaye nayi a wajen da jin kalaman makirci da sharrin da take min. A take idanuna suka ciko da hawaye. Na cije lips ɗina sannan na kallesa. Kansa a ƙasa yake bashi da alamar cewa komai. Sai da na share hawayen da suka ziraro min sannan na ce, “Wlhy ba haka ban...”     Bamm ta buge min baki da ƙarfi har sai da ya fashe. “Dan ubanki kina nufin ƙarya na miki ke nan. Lallai yau kam zanci ubanki a gidan nan. Anya kuwa yarinyar nan keba ƴar leƙen asirinmu bace ba ma? Ba wani ya turoki ba dan ki cutar da mu. Dan Ni ba'a taɓa fitsararriyar ƴar aiki tsagera mara kunya irinki ba anan gidan.”         Cikin tura baki gaba na ce, “To ni dai Mammah ai bamma kowa rashin kunya ba sai wanda ya shiga harkarta. Ni kuma bana son ana min sharri akan abinda banyi ba. Kuma manya idan suna ƙarya mutuncinsu zubewa yake yi”.      Ɗauu naji saukar wani marin mai azabar zafi da yafi na ɗazun a saman fuskata. Tsabar yanda ya shigeni har sai da jina ya ɗauke na wucin gadi. Ina ɗagowa ta sake ɗaga hannu zata ƙara min ya shiga tsakkiyar mu. Cikin silent voice ɗin nan tasa mai cike da ƙasaita ya furta, “Mammah it's enough.”       Babu wanda mamakin jin abinda ya fito a bakinsa bai bayyana a fuskarsa ba. Duk da mafi yawansu sun san ba sabon abun bane gatsa magana kai tsaye daga garesa musamman idan yana a ɓacin rai, sai dai dalilin yin ta yau ɗin ce ta Bama kowa mamaki. Irin wannan tsawa haka. Cike da azabar masifa itama Hajiya Mammah ta daka masa tsawa. “Awwab!! Kana fa jin abinda shegiyar yarinyar nan ke faɗa har kake iya cemin ya isa. Ka barni na dawo da ita a hankalinta idan bata san matsayina a gidan nan ba ta sani da ga yau!”.      Maimakon bata amsa ko barinta dani ɗin sai jinai kawai ya kama hannuna ya fara tafiya. Bani da zaɓin daya wuce bin bayansa. Tsitt falon babu wanda ya sake yin koda tari har muka shige ta hanyar nan data nuna min ranar na kai masa shayi....        ⭐💞⭐💞⭐      Rashin wucewar Gwaggo ya ɓata shirinsu Mom. Duk da dai ita dama Ummanta ce ke tausarta. Saboda tafi ganewa ta fito ayima duk wacce za'ayi amma Umman tace a'a subi komai a sannu suma fara sanin wacece yarinyar tukunna. Gefe kuma rashin jin daɗin jikinta ya hanata iya komai. Dan da gaske jinin nata ya hau ga ciwon kai da ƙirji mai tsanani dake damunta...        A ɓangaren Halime amarya sai da aunty Zakiyya ta sakata gyara jikinta tsaff ta kuma ƙara tsaftace mata sashenta sannan ta wuce. Dan haka daga ita har sashen nata banda bulbula ƙamshi babu abinda sukeyi. Tayi fes da ita ƙyawunta da rashin kula ya ɓoye ya sake fitowa sosai. Duk wanda ya kalleta yasan tana cikin farin ciki da walwalar sabuwar rayuwar data tsinta kanta a ciki. Sai dai ta wani sashen zuciyarta rashin ganin Abba tunda aka kawota gidan na ɗan sosa ranta. Dan tun jiyan da suka iso bata sake ganinsa ba. Sai da safen nan da taji muryarsa yana gaida iyayenta dake falo. Tayi zaton zai nemeta amma sai taji shiru. Lokacin da ƴan uwan nata ma zasu wuce taji muryarsa a tsakar gida, sai dai kukan da take yasa batai yunƙurin kallon sashen da yake ba. Tunda kuma suka wuce bata sake jin motsinsa a cikin gidan ba. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke a hankali, sai kuma ta taɓe bakinta dan tasan zama ta iya ganin fiye da hakan kodan matar nan tasa a zababbiya. Jifa yanda aketa cin uwar sabada a gidan tun isowarsu jiya, a hakan ma tasan dan bata san itace matar da aka auro ɗin ba ma...      Yanda take ta faman yamutse fuska da taɓe baki ya saka Abba dake tsaye a kanta tun ɗazun kasa daurewa ya saki murmushi. Sai kuma a hankali ya kai zaune kusa da ita yana mai kai hannu ya shafi fiskarta. Tsorata tayi, dan harga ALLAH bataji koda ƙamshin turarensa ba balle motsinsa. Dan haka ta miƙe a firgice zata ƙwala ihu. Da sauri shima ya riƙota yana mai ɗora hannunsa saman bakin nata tare da jawota gaba ɗayanta cikin jikinsa yana faɗin, “Calm dawn Halimatussa'adiyya please calm down ni ne”.       Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da numfashi a jajjere. Sai kuma taji duk kunya ta baibayeta. Ƙoƙarin zamewa tayi daga jikin nasa ya hana hakan ta hanyar sake matseta da ƙyau a cikin jikin nasa. A cikin kunnenta ya shiga raɗa mata, “Amin afuwa na tsorata amarya ko.”      Halime babu bakin magana dan gaba ɗaya a kunyace take. Sai ma mutsu-mutsu da takeyi na son tashi shiko yaƙi barinta. Dole ta haƙura ta nutsu ganin bafa barin nata zaiyi ɗin ba dai. Sun kai tsahon mintuna goma a haka sannan Abban ya sassauta mata yana sauke tagwayen ajiyar zuciya tare da mannama goshinta da kan hancinta kisses. Ina ma ƙasa ta tsage Halime ta shige ciki dan kunya. Sai dai babu damar hakan dole ta haƙura tana faman cikuykuye kanta a jikinsa.       Yanda take yi ɗin yay matuƙar saka Abba dariya. Dan haka ya shiga tsokanarta da raɗa mata wasu kalamai a cikin kunne da suka sake birkita mata lissafi... 💦★💦★💦       Muna shiga ya sakar min hannu. Ganin yana neman raɓani ya wuce nasha gabansa wani irin kuka mai ƙarfi na suɓuce min. Ƙin kallona yayi, ya sake raɓawa zai wuce ta side ɗin dama ta. Nan ma taresa nayi hannayena duka riƙe da ƙuguna. Tuni na cire duk wani tsoronsa da shakkarsa cike da tsiwa na ce, “Malam wai mi kake nufi da ni ne? Ka maidani gaban iyayena daka ɗakkoni bazan iya rayuwa a wannan gidan da ba'a san darajar ɗan adam ba”.      Tamkar bazai kallan ba sai kuma ya yamutse fuska tare da sake tsuketa. Cikin gadara ya furta, “Ki gayama wanda ya kawoki. Sannan bana son rashin kunya”. Daga haka yay wucewarsa. Wani irin takaici da bakin ciki ne suka sake turniƙe ni. Tuni na shiga kokawar maida hawayen dake neman zubomin. Dole ne fa ayita yau ta ƙare dan bazan iya wannan zaman ƙasƙancin ba saboda ni ba jaka bace ba. Bazan taɓa zama a maidani yanda aka maida mahaifiyarsa ba. Kaina tsaye na nufi hanyar da yabi dan idanuna sun gama rufewa da masifa. Babu ko gezau a tare dani na bankaɗa ƙofar farko dana gani a wajen. Sai da zuciyata ta jijjiga saboda karo da abinda banyi zato ba. Da sauri na juya masa baya ina mai rumtsewa da ƙarfi, jikina har rawa yake dan tunda nasan kaina ban taɓa ganin namiji babba a yanda yake yanzu ba. Su Yaya Musaddiq ko da boxer da singlet basa zama a gida. Balle kuma ace daga su sai pant kamar yanda yake. Gashi a tsaye ƙyam da suffar ƙarfi dogo masha ALLAH. Bazan iya kallon wannan abin kunya ba, dan haka na fara laluben hanyar komawa inda na fito cikin sassarfa, amma sai hakan ya gagara. Maimakon kama handle ɗin ƙofa da nake lalube sai na damƙi lallausar fata mai santsin tsiya. Da sauri na cire hannun nawa tare da daka tsalle baya ina buɗe rumtsatstsun idanun nawa. Idanu huɗu mukai da shi, tsabar rashin kunya kuma yana a yanda na gansan. Sake juya baya nayi da sauri jikina na rawa. (Wannan wane irin fitsararren mutum ne haka wai) na faɗa a zuciyata ina ƙoƙarin riƙe numfashina da tsumar da jikina keyi........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......A bazata naji saukar muryarsa cikin kunnena.      “Ba abinda kika zo gani ba kenan?”. Ya faɗa a hankali cikin daƙilalliyar muryar nan tasa. Bamma san lokacin dana juyo a fusace na ce, “ALLAH ya kiyaye sai kace wata ƴar iska. Kuma ni ka bani hanya na wuce”.        Maimakon bani hanyar ko tanka min sai ya shiga matso ni. Baya na farayi hankalina a tashe, idanuna na fitowa gaba ɗaya waje. Shi kuma bai fasa biyonin ba har sai da muka dangane da ƙaton gadonsa dake a dunƙule tamkar zero. Ganin baida alamar dakatawa na faɗa saman gadon idanuna cike da ƙwalla. Gaba ɗayansa ya ranƙwafo kaina yay min runfa hannayensa duka biyu dafe da gadon ta gefe da gefe na. Kaina na shiga girgiza masa idanuna cike da hawaye. Kafin na buɗe baki da ƙyar cikin ƙarfin hali na ce, “ALLAH zan maka ihun da kowa na gidan nan sai yazo sashen nan”.         Wani lalataccen murmushi ya saki da ɗage gira ɗaya sama. A hankali ya sake matso da furkarsa gab da tawa. Ai babu shiri na ƙanƙame jikina tare da rumtse idanuna na kauda fuskata gefe. Amma duk da haka ina jin saukar dumin numfashinsa akan fuskar tawa. Kafin cikin maganar raɗa a cikin kunnena ya furta, “Da kuwa kowa a yau yasan ke ɗin *_MATAR AWWAB EL-MU'AZZ MAASH_* ce. Idan kuma kin cika matsiwaciya dan ALLAH ki gwada ki mana”.        Hannu nasa na ture fuskarsa batare dana buɗe idanun ba, sai kuma na yunƙura zan tashi dan ji nake tamkar an sakani a kuttun man shanu tsabar yanda kusancinmu ya dabaibaye ni. Da sauri na koma ina mai dafe kaina daya bugu da nasa. Tare da buɗe idanuna ina ɓata fuska tamkar zanyi kuka. Shima tashi fuskar a yamutse take hannunsa dafe da goshinsa alamar yaji zafi, ban san sanda na bushe da dariya ba tsabar jin daɗi. Ganin yanda ya zuba min idanu ya sani haɗiye dariyar na ɓata fuska da harararsa na ɗauke kaina gefe.          “Baki da kunya ko?”.      Ya faɗa cikin wani yanayi dana kasa fassarawa. Baki na sake murguɗawa fuskata a gefe a tunanina bai gani ba. Sai jinai ya furta, “Humm harara a duhu ai na mai tsoro ne. Idan kin isa kiyi ido cikin ido ni kuma zan banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa. Bani phone ɗina”.       Da sauri na juyo na kallesa danni nama manta da wani batun wayarsa a hannuna. Sai kuma na maida kaina gefe nace, “Ta ƙarfi ce. Kuma ni ka tashi min a kai, wannan ai rashin kun.....” na kasa ƙarasawa.     Bai tashin ba bai kuma tanka min ba. Kusan tsahon mintuna biyu sai da ya mula dan kansa sannan ya miƙe kamar wanda akai ma ishara da hakan, dan da ƴar sassarfa ya bar wajen haƙoransa cije da lips ɗinsa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, har ina kai hannuna na fara ma kaina fifita da shi dan sam ko sanyin acn dake ɗakin baya wani ratsani. Jin rufe ƙofa ya sani zabura, sai naga bathroom ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sosai tare da miƙewa. Dan gwara nabar masa ɗakin kafin ya fito min a tsirara kuma tunda naga idanunsa ba kunyace a cikinsu ba. Turus na tsaya tamkar zan fasa ihu jin ƙofar a garƙame, a take naji sabon tashin hankali da hajijiya na neman kwasata, dan na fahimci ƙofar ya rufe kenan....        ⭐💞⭐💞⭐       Yanda take safa da marwa cikin ɗimuwa a ɗakin zai tabbatar maka da ranta a ɓace yake. Tabbas kuwa ran nata a ɓacen yake. Dan tunda take ba'a taɓa raina mata hankali irin na kwanakin nan ba. Musamman ma yau. Ranar Awwab ya gasa musu magana harda gorin gidan uwarsa ta tursasa kanta shanyewa batace komai ba saboda wani dalili. Yau kuma yarinya ƙarama tai mata rashin kunya da tsallake dokarta shi kuma ya mata tsawa ya kuma hana ta hukuntata. Kowa fa a gidan nan tsoronta yake ji, amma har yau a samu yarinyar da zata ƙaryatata a gaban ƴan aiki da ƴaƴanta. Lallai sai ta ajiye lesson mai ƙarfin gaske akan yarinyar nan. Kai hatta da Awwab bazata ƙyale ba saboda goyan bayan yarinyar ta fahimci yake yi. Ai ba yau ta fara cin uban ƴan aiki a gidan ba. Kuma ko yana zaune a wajen take yi ɗin ko ɗaga kai ya kalla baya yi ma. Amma ta kula akan yarinyar nan yana neman kawo musu wani sabon salo. Jiba randa Hajiya Babba ta daketa, ɗaukartafa ya dinga yi harda ɗorata a jikinsa yay treating nata da kansa. Kai ita fa gaba ɗaya ma kanta ya kulle.         Waya ta jawo tai kira. Ana ɗagawa ko sallama bata tsaya yi ba ta fara magana cikin damuwar dake tabbatar da ɓacin ranta. Abinda ya faru tun daga randa aka kawo Samraah gidan take sanarma wadda ta kira har zuwa yau ɗin nan. Sai kuma tai ɗan jimm alamar sauraren abinda na can ɓangaren ke cewa. Tsawon kusan mintuna uku kafin ta saki murmushi mai ƙayatarwa, tare da furta, “Kai amma na gode Hajiya Rubayya, Please kiyi maza ki shigo ina saurarenki. Dan wannan shawarar taki na fara jinta a jikina ƙwarai da gaske.” ajiye wayar tai tana sakin dariyar nasara. Sai kuma ta miƙe tamkar ba itaba ta fara zame kayan jikinta cike da nishaɗi. Tana kammalawa tiɓi-tiɓi ko kunyar kanta bata ji ba ta nufi bathroom ɗinta a haka da alama wanka zatayi.....         💞💞💞💞   *_INDIA_*          Kuka take sosai da ƙoƙarin riƙe hannunsa daga haɗa kayan da yake tayi. Sai dai ko kallon inda take baiyi ba balle ya dakata da abinda yake ɗin. Cikin matsanancin takaici da fusata Attahir da ya gama harzuƙa da abinda ke faruwa ya fisge jakar yana mai dakama ƙanin nasa tsawa.     “Mansoor are you mad ne wai?”.            “Yes! I'm. Na ce I'm!. Ba haka kuke son ku ganni ba. Ko ba haka kukafi buƙatar ganina ba?. Nace muku ga wadda nake so, kun rabani da ita batare data ma wani cikinku laifin komai ba. Duk da abin yana min ciwo har yau har gobe ban taɓa ce muku komai ba. Amma hakan bai muku ba kuma sai ace min wai ga mata an ɗaura min aure da ita. Tunda nake da ku na taɓa ce muku ina son wannan yarinyar ne? Wlhy da nayi rayuwar aure da wannan yarinyar gara na shiga duniya. Na gaji da wannan rayuwar haka nan haba. Sai kace ba jininku bane ni, yaya kuke so na cigaba da rayuwa cikin salama ns wa....” kuka ya sarƙesa ya kasa cigaba da magana. Sai ma zubewa da yay a saman gadon yana mai dafe kansa dake sara masa da duka hannayensa biyu, tare da cusa hannunsa cikin sumarsa ya yamutsata.        Sosai jikinsu ya sake yin sanyi. Musamman Mamy da tafi kowa kasancewa a cikin ɗimuwa. Itama zubewa tayi a gaban Mansoor ɗin tare da kamo hannayensa cikin nata tana sake fashewa da kuka. Dad ne da tun ɗazun baice komai ba ya furzar da iska mai kauri daga bakinsa, tare da kai hannu saman kansa ya shafo. Sosai kukan Mamy da Mansoor ke cizon zuciyarsa. Sai dai shi baima san ta inda zai fara ba game da wannan hargitsi daya rasa tushensa balle iyaka.....        Kakarin da Mansoor ya fara ne ya maidosa a hayyacinsa. Kusan a tare shi da Attahir suka zabura kansa. Yayinda Mamy ta sake ɗimaucewa. Yunƙurin amai ya fara sai ga jini bula. Ihu Mamy ta fasa, yayinda Attahir ya fita a guje yana faɗin bari yay kiran asibiti...        Kafin cikar mintuna goma ambulance ta iso. Lokacin da aka fito da Mansoor daga ɗakin hotel ɗin da suke ya gama fita a hayyacinsa. Dama yau kwana uku kenan da sallamosa baya kwanakin kusan wata guda daya kwashe yana jiyya. Samun lafiyar tasa ya saka walwala da farin cikin kowa dawowa a cikin ahalin nasa. Dan nan da kwanaki biyu ma suke shirin komawa gida Nigeria. Sai kuma aka samu akasi Husnah yarinyar Auntynsa da aka ɗaura masa aure da ita a randa aka fasa da Samraah dake Dubai ta ɓaro musu aiki tai kiransa a waya. Kalaman da tayi amfani da su a wajen gaisawar tasu ya sakashi neman fashin baƙi a wajen yayansa Attahir. Shi kuma batare da tunanin komai ba ya buɗe masa zancen cewar ai da gaske Husnah ɗin take an ɗaura mata aure da shi a randa aka fasa da Samraah. Wannan shine dalilin rikicin na yanzu, ga shi kuma da alama aiki ya koma baya.....    🌜🌟🌛     Ina nan tsaye abin duniya duk ya isheni ya buɗe ƙofar bathroom ɗin alamar zai fito. Koda gigi ban yarda na kalla wajen ba balle ma na saka kaina a uku. Har tsawon mintuna uku ina ɗan jin motsinsa cikin yanayin rashin hayaniya. Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya na ce, “Ni ka buɗe min ƙofa na fita bana son taɓara”.      Shiru babu alamar zai amsa min, daurewa nai na sake maimaitawa cike da tsiwa. Nan ma banji alamar zai kulani ɗin ba. Sai kawai na taune lips ɗina ina jin kamar naje na rufesa da duka. Tsahon mintuna goma ina dai wajen a tsaye ban juya ba ban kuma gusa ba. A bazata naji sautin muryarsa a bayana.          “Bani phone ɗina”.      Da sauri na juyo har ina buge hannu da ƙofa. A tsayen kuwa yake ƙyam a bayan nawa shantali guda dashi, dan duk nawa tsawon sai na ganni ɗis a gabansa. Ga fuskarsa a tsuke babu alamar wasa tattare da shi. Duk da yanda naji zuciyata ta motsa na tsorata sai na dake nima ina mai tsuke tawa fuskar tamau harda su hura hanci.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Matsawa nayi baya ina kumbura fuska. “To ka buɗe min mana ba tana sashen Ummie ba. Oh Hajiya Babba”. Nai saurin gyarawa saboda kallon da naga ya wani kafeni da shi. Kamar bazai tanka min ba sai kuma a daƙile kamar an masa tilas ya ce, “Miya kaita can?”.        “To ina ruwanka, kai dai ka matsa naje na ɗakko maka”.      Shiru bai matsa ba ya dai zuba min ido kawai. Sai da ya mula dan kansa sannan ya sake furta, “Da gaske abinda Mammah ɗin ta faɗa kenan?”.     Karon farko na ɗago na kallesa. Dan yanda yay maganar a dakensa ba ƙaramin tsargani yay ba. Idanuna cike da ƙwalla har muryata na rawa ma na ce, “Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”         “Your are vary stupid!!”.     Ya faɗa cikin katseni da daka tsawa. A take kuma idanunsa suka jirkice ƙwayar tsakkiya ta koma siririya, zaibar ta sake duhu exactly na maguna dai musamman idan suna a cikin hasken rana. Har cikin raina naji tsawar tashi ta ratsa ni, a take kwarjininsa da shakkarsa suka sake dabaibaye ni har na gagara sake magana. Sai da ya buɗe ƙofar a fusace ya fice sannan na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna. Lallai wannan mutumin yayi nisan da bai jin kira. Sannan akwai abinda ya kamata na sani dan na fahimci sam baya son abinda zai taɓa ahalinsa kenan. To lallai babbar magana. Dan ni inaji a jikina lallai akwai ɓoyayyen al'amari mai cike da darasi a ƙarƙashin ciwon mahaifiyar nan tasa. Amma in sha ALLAHU koma minene ni *_SAMRAAH ABDULL-WAHAB GWARZO_* nayi alƙawarin sai na bankaɗosa. Uban kowa sai ya kwashi kashinsa a tafin hannunasa cikin MAASH MANSION..        (Tofa babbar magana. ALLAH ya bada nasara Kandala🥱).      Cikin cije baki da tabbatar da alwashina na nufi ƙofar nima. Dan nayi alƙawarin bazan sake bari mutumin nan yaga gazawata ba duk da ina jin shakkar tasa. Abincin rana dana tuna shine dalilin fitowata na ɗibama Ummie yasa hankalina tashi. Harna nufi hanyar barin sashen na fasa, dan sama-sama na ke jiyo magana ata falo. Falon na nufa, acan ɗin kuwa na samesa tare da ɗan kaɗafin PA ɗinsa. Yana zaune hannayensa duka dafe da kansa alamar akwai abinda ke damunsa ko kuma kan nasa na masa ciwo ne oho masa, PA ɗinsa tsaye ata gefensa cikin tsaiwar nuna girmamawa da alama magana yake masa. Ina fitowa yay shiru. Harara na watsa masa dai-dai muna haɗa ido.        “Barka da rana ranki ya daɗe”. Ya faɗa dai-dai ina isowa inda suken. Wani ƙululun takaici ne naji ya shaƙuremin maƙoshi. Sai dai na danne na watsar da banza tamkar ma banjisa ba. Ledojin dana gani a gaban ogan nasa da bana raba ɗayan biyu abincine na ɗauka. Harna ɗauka ɗaya na sake tattaro sauran biyun ma na kwashe. Dai-dai na ɗago zan bar wajen PA ɗin nasa ya ce, “Ranki ya daɗe ɗaya ne extra, sauran na Boss ne”.        “Ko zaka ƙwatar masa?”.    Na faɗa a kausashe ina watsa masa wani shegen kallo. Da sauri ya girgiza kansa da faɗin, “A'a ayi haƙuri”.      Tsaki naja mai ƙarfi, ina sake balla musu harara su duka biyun. Sai dai har yanzu kan ogan nasa na ƙasa bai ɗago ba, tamkar ma bai san mike faruwa a falon ba. Nima ba shine a gabana ba, dan haka nai gaba abina ina jan tsaki mai ƙarfi..     ★Tana shigewa Hayatu dake kallon ogan nasa da tunanin zaice wani abu amma babu alamar hakan ya sauke ajiyar zuciya. Cike da kulawa da girmamawa ya ce, “Sir bari to na samo maka wani abincin tunda ta ɗauke wannan ɗin duka ko?”.    Shiru kamar Maash ɗin bazai tanka ba. Dan har Hayatu ya fidda rai da samun amsa sai kuma ya ga ya ɗago ya kalla hanayar da tabi, ɗauke idanunsa yay ya maida ga Hayatun. Cikin yanayin nan nasa a daƙile ya furta. “Barshi kawai. Kaje ku ƙarasa abinda zakuyi. Ina sake gargaɗin ko su Juliet kar su san ina ƙasar nan yau.”          “In sha ALLAHU zan kiyaye Sir. Amma idan mun tafi yau wazai dinga samo maka abinci? Ko dai nayi magana da gidan abincin kullum su dinga kawo order sau uku har cikar sati ɗayan”.      Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma miya tuna oho. A hankali ya furta, “Kayi hakan”. Cikin jin daɗi Hayatu ya ce, “A huta kafiya”. Duk da yana mamakin ogan nasa akan daina cin abincin gidan a ɗan tsakanin nan bazai iya tambayar dalili ba. Dan tun washe garin birthday party ɗin Ummie ya sallami kukunsa dake masa girgiki, duk da ma dai ba ko yaushe bane yake cin abincin nasa yana cin na can cikin gidan a wasu lokutan musamman idan Aunty Mama na gari...        💞⭐💞⭐💞     Tunda suka idar da sallar kanta ke a ƙasa ta gagara ɗagowa ta kallesa. Yayinda shi kuma ya kafeta da idanunsa cike da nazari. Ganin yanda ta takure kanta waje ɗaya ya sashi ɗan sauke ajiyar zuciya. Kafin a hankali yay kiran sunanta..       “Halimatussa'adiyya”.    Da ƙyar ta iya ɗagowa tana amsa masa da, “Na'am”. Dai-dai suna haɗa ido. Saurin maida kanta tai ta sunkuyar. Murmushi ya saki da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya gyara yanayinsa cikin kame kai ya ce, “Wanene ni a wajenki?!”.        Kasa cewa komai tayi, sai da ya sake maimaitawa. Muryarta na rawa tana sake sunkuyar da kai a hankali ta ce, “Baba!”.       Murmushi yay mai faɗi tare da girgiza kansa. “Halimatussa'adiyya ni ba babanki bane. Mijinki ne ni, nasan kuma kin sani.”          Kanta ta sake sunkuyarwa alamar dai ta san haka ɗin ne. Shima sai ya cigaba da faɗin, “Halimatu nasan ke mai tarbiyya ce da ilimin addini gwargwado. Dan naje har tushenki naga gidan da kika fito. Kema a karan kanki a ɗan zamanki cikinmu gidan nan na tabbatar da hakan. Fatana dai ALLAH yasa abinda na gani yasa ya ɗore har abada. Zuwa yanzu kema nasan kin san gidan da kika shigo. Kin kuma san wanda kika aura. Ni ba yaro bane ba, inada ƴaƴa biyu maza Musaddiq da Abbas da suka girme miki, inada ƴaƴa biyu mata Samraah da Sakina (Baby) da zaku iya sa'anni, inada waɗanda zaki iya girma Hafiz, Nabil, Habiba auta Jamal. Ina roƙonki dan ALLAH ki zauna lafiya da su, ki jasu jikinki matsayin uwa. Kada kiyi dubi da matsayin wadda suka girma ko kuke sa'anni. Mahaifiyarsu karki damu da abinda ke tsakanina da ita. Ki zauna da ita lafiya ki bata girmanta. Dan ALLAH duk wata hanya da zata zama ta raini a tsakaninku kada ki buɗeta. Ni kuma na miki alƙawarin in sha ALLAHU zan ƙare miki mutuncinki tako wane ɓangare. Nima na baki amanar kaina. Ki riƙeni da hannu biyu Please Halimatussa'adiyya. Dan ni da ke duk marayune”. Cike da mamakin jin kalmar Maraya daya kira kansa yadata ɗagowa ta kallesa. Cikin lumshe ido ya jinjina mata kansa. “Hakane Halimatu, nima maraya ne da babu uwa babu uba sai Gwaggo na kawai da ku da ALLAH ya bani matsayin iyali, sai ahalina na Gwarzo da sai a hankali zaki san kowa da kowa”.       Kanta ta jinjina masa, sai kuma takai hannu ta share hawayen da suka zubo mata. Murmushi ya saki tare da mika mata hannunsa na dama yana faɗin, “Zo nan”.          Da ƙyar ta iya motsawa zuwa gabansa, sai dai tabar ƴar tazara a tsakaninsu. Dan haka ya kamo hannayenta ya jawota sosai ya manna da jikinsa. Zata noƙe ya sake mannata da jikin nasa tare da zame hijjab ɗinta ya ajiye gefe. Ledar takeaway daya shigo da ita ya jawo gabansu. Ta gefen ido Halime take satar kallon dankareriyar kazar da ƙamshinta ya gama cika ɗakin. Yawu ta haɗiya zuciyarta na zallo, sai dai kunya ta hanata yin ƙwaƙwƙwaran motsi.        Cike da kulawa Abba ya ɗiba naman ya kai bakinta. Babu musu ko kwana-kwana ta amsa sai dai idanunta a rufe dan kunya. Shi dai Abba dariyama ta bashi, amma ya danne abarsa. Sai da Halime tai nak da naman kaji da yogurt sannan ta kauda kanta.......✍️        🥱Gara da kikaci abinki Aunty Halime😂😜. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Rashin kowa a falon ya bani damar haurawa saman hankalina a kwance. Sai da na sauke ajiyar zuciyar jin daɗi saboda samun Ummie a yanda na barta tana barci. Ledojin abincin na ajiye gefe, na nufi bathroom nayo alwala. Sai da na gabatar da sallar la'asar sannan nai zaman yin karatun Alqur'ani da ka dan babu Alkur'anin a sashen. Tun ina karatun naji shigowar saƙo a wayarsa dake a hannuna. Ban maida hankali ba har sai da na kammala surar da nakeyi ta Baƙara. Kammalawa ta dai-dai da farkawar Ummie, dan haka na nufeta da sauri ganin tana fisge-fisge tamkar wadda ta farka a firgice. Riƙota nayi a jikina ina karanta mata addu'oi, a hankali-ahankali sai ta fara lafawa. Shiru kusan mintuna biyar kuma ta buɗe idanunta tana kallona. Murmushi na sakar mata, kafin a hankali na ce, “Ummie zaki ci abinci?”. Sai da tai ɗan jimm kamar bazata amsa min ba, sai kuma a hankali ta motsa lips ɗin ta ta ce, “Muhammad yunwa”. Murmushi na ƙara mata idanuna cike da ƙwallar tausayinta. Da taimakona ta ɗan tashi zaune, kamar ɗazun na jinginata a jikina da kaina na dinga bata abincin. Abin tausayi yanzun ma sai taci sosai, hakan ya sakani jin farin ciki, na bata ruwa ta sha, batare da tace min komai ba ta koma ta kwanta kanta a saman cinyata, cikin lokaci ƙanƙani barci ya sake kwasheta. Murmushi na saki ina mai rungumo kan nata a jikina, tsawon lokaci ina hawaye kafin na barta saboda sake shigowar saƙo a wayarsa dake hannuna. Wayar na ɗauka, fuskata a taɓe na buɗe saƙon. _(Ko zan ƙare rayuwata a bibiyar taka rayuwar bazan taɓa gazawa ba ko ƙosawa da hakan tauraron duniya. Zan kuma cigaba da roƙonka ka taimaki rayuwata ka aureni koda na wata ɗaya ne. Wlhy na maka alƙawarin maka hidima tamkar baiwa da uwargijiyarta. Kuma koda kullum kake dukana da zagina bazan taɓa daina sonka da maka biyayya ba Gwarzona.)_ wannan shine saƙon farko da aka turo tun ɗazun. Baki na taɓe tare da jan tsaki sannan na buɗe na biyu. _(Ka taimaki rayuwata Tauraron duniya. In ma bazaka aureni ba ko kwanciya kayi dani koda sau ɗaya dan ALLAH kozan rage ƙishirwarka)_        “Kitttumelecy kice ɗan iska ne ashe shima, shiyyasa yayta wani fiki-fiki da idanu uwa na kifi tarwaɗa, kamar wani ustazun ƙwarai hummm” na faɗa a fili bayan na ƙare karanta saƙo na biyu. Ai tini na shiga komawa sama ina karanto na tun daga farko, kaɗanne da alama ana gogewa, ko sau ɗaya kuma bai taɓa bada amsa ba. Koda yake munafukin maybe gogewa yake. Fitowa nayi na shiga masa bincike a messages ɗin nasa, sai gashi na ci karo da wanda sukafi nama farkon ƙazanta daga ƴammata da ban da ban. Ina cikin karanta wani daya firgitani matuƙa dan har na gagara daurewa ina surutai fittt naji an fige wayar. Da sauri na juyo nima a firgice. Sai kawai na gansa tsaye a kaina ƙiƙam yana faman mazurai, fuskar nan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa. Sai da ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa yana watsa min wani kallon dana kasa bama fassara. Baki na murguɗa masa tare da gallara masa harara nima na ɗauke kaina na maida kan Ummie dake kwance kanta a saman cinyata. Ya daɗe tsaye a kammu batare dana san mi yake yi ba dan ban sake ɗagowa na kallesan ba nima. Kafin ya kai durƙushe gaban mahaifiyarsa ya ɗan ranƙwafo kanta yana mai kai ƙyaƙyƙyawan hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen akaifa saman fuskarta ya shafa. Ɗan ɗagowa nayi na kallesa, a mamakina sai naga kamar ƙwalla a cikin idanunsa. Jinai tsigar jikina ta tashi, da sauri nai azamar ɗauke kaina ina sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Saukar hannunsa akan nawa dake a saman kanta ya sani juyowa na sake kallonsa, dai-dai nan ya ture min hannu ya maye nasa a gurbin nawan yana shafa kitson da nayi mata. Baki na tura nima na ture nasa hannun ina harararsa. Ɗagowa yay ya kalleni cikin yanayin kamar harara shima. Sai kuma ya sake ture nawan, ban bar masa ba na sake ture nasan nima ina hararar tashi.         “K baki da kunya ko!”.   Ya faɗa a dakensa a daƙile kuma. Sai da na taɓe baki sannan na ce, “Yo ni rashin kunyar mina maka. Bana rigaka ba kazo kana nemana da faɗa alhalin ban kulaka ba. Kaje kaji da ƴan iskan ƴanmatanka kwartaye ma ya isheka tunda ba'a gayyaceka ba anan ɗin”         Wani irin kallo yake min da ya saka tsigar jikina tashi gaba ɗaya. Bamma san sanda na murguɗa masa baki da gatsinawa ba na janye nawa idanun da ƙyar. “I will teach you to be smart”.     Ya faɗa a lalace yana ɗauke kansa. “Ka fara koyama kanka da ƴan iskan ƴammatanka”. Na bashi amsa nima ina ɗauke nawa kan gefe. Daga haka shima ya miƙe tsaye batare daya sake kulani ba. Nima sai ban sake kulashin ba har ya gama dube-dubensa a ɗakin ya fita...            💫💫💫💫💫      Baƙuwar Hajiya Mammah ta iso. Kasancewar kowa yasan ita dama baƙinta ba'a saukarsu a falon ƙasa yasa Mama Balki mata rakkiya har can sama na part ɗin Hajiya Mammah ɗin. Sannan ta koma ta kawo kayan motsa baki. Ta ajiye tana ƙoƙarin fita cike da isa Hajiya Mammah ɗin tace ta turo mata yarinyar nan. Ɗan jimm Mama Balki tayi na shakku, sai kuma dai a ɗarare ta ce, “Tana a sashen Hajiya Babba Alhaji ƙarami ya sakata aiki”. Dan gara ta faɗi haka ɗin kafin wani yazo mata da gulmar sake ganin Samraah a sama abin ya zama babbar matsala.        Shiru Hajiya Mammah bata amsa ba. Sai dai fiskarta ta nuna tsantsar ɓacin ranta. Fahimtar hakan yasa baƙuwarta sallamar Mama Balkin. Tana fita ta kamo hannun Hajiya Mammah ɗin cikin nata.      “Relax mana Hajiya Nafee. Ina gaya miki a koda yaushe ki ɗan dinga controlling fishinki akan al'amarin gidan nan. Ki daina barin ana gane miki haka da wuri musamman ma masu aikin nan naku munafukai. Yanzu dai ina son kimin bayanin mike faruwa?”.     Shiru kamar Hajiya Mammah bazatayi magana ba. Sai kuma cikin ƙunar rai ta shiga ma aminiyar tata bayani tun daga farkon zuwan Samraah gidan har kawo yau ɗin nan kamar yanda dai ta sanar mata ta waya. Ƙawar tata ta jima batace komai ba alamar nazari, kafin ta saki murmushi da kallon Hajiya Mammah.          “Ni ina ganin mafitace tazo mana ai akan yarinyar nan. Za muyi amfani da ita dan ta zame mana zaren ƙulla auren Awwab da Azizat. Kinga cikin sauƙi kema zaki samu cikar burinki”.     “Ban fahimceki ba Rubayya. Ita wannan abar har wacece ita da zata zama zaren cimma burukana? Sai dai burin kore ƙishi”.   “Yamzu kuwa zaki ji. Badai kince yarinyar na shishshige masa ba? Sannan tana shigema uwarsa duk da wahalar da taci a hannunta?”.        “Hakane”.     “Wannan salon nata shine ai makamin namu. Dan dashi zamuyi amfani da ita mu sarƙo wuyan shegen yaron nan mai taurin kai da rashin mutunci. Yanda yake nuna shi mata basa gabansa da ita zamu tabbatar ma duniya munafunci ne.”     “Kinfa san bana son kwana-kwana a zance Rubayya. Fito fili ki faɗa min inda kika nufa dan ni ban fahimci komai ba”.          Dariya sosai Hajiya Rubayya ta saki harda ƙyaƙyƙyewa. Kafin ta ce, “Daɗina dake rashin haƙuri Aminiya. Bari to na kaiki. Fyaɗe zamu saka ya mata na rashin imani. Mu kuma mu dinga masa barazanar yaɗa zancen ta yanda sai ya tsani kansa. A cikin tsakiyar rikicin muyi duk yanda zamuyi ya auri Azizat. Inada tabbacin bazai mana jayayya ba a lokacin dan bashi da wata mafita neman ma wajen tsira yake yi..”         “Humm to idan kuma yarinyar ta samu ciki fa? Ko kuma shi ya ce zai aureta saboda faruwar al'amarin?”.      “Mu dama ai cikin muke buƙatar ma ace ya matan. Dan aikinmu zai fi tafiya dai-dai. Idan kuma yace ma zai auretan mu dai-dai ne. Hakan kuma zai sake ƙarfafa aikinmu.”         “Ta yaya?”.    “Idan yace zai aureta kuma ga ciki ai dole dai zai bari ta haihu. Ku kuma ai ba yarda zakuyi ba matsayin iyaye musamman ma ke. Mu kuma zamuyi amfani da hakan mu zubar da cikin, a wajen zubar da shi zata bar duniyar. Sabon zance zai tashi akan shine ya kasheta, dama zuwa lokacin Azizat na tare da shi. Sai muyi amfani da wannan rikicin da yanayin da zai shiga shi da sauran mutanen gidan naku kema ki samu cikar burinki, fatanmu dai ace lokacin Azizat nada ciki ko ƙarami ne. Amma kidai zauna kiyi tunani. Sai dai fa dole ki rage wasu abubuwan ki sake jawosa jikinki fiye da kowa a gidan nan. Ta yanda idan komai ya ƙwaɓe ke kaɗai zai dinga tunkara ko tattauna damuwarsa. Itama yarinyar haka. Amma ɗan ALLAH ki shanye maitarki a kanta nasanki da ƙananun yara baki da haƙuri”.           Sosai Hajiya Mammah ta sauke ajiyar zuciya. Sai kuma tayi ɗan murmushi da faɗin, “Tabbas shawarar nan taki tayi Rubayya. Sai dai kuma kin san dai akwai matsala. Dan halin Awwab ba ɓoyayye bane akan duk wanda ke mu'amala da gidan nan. Tayaya muke tunanin zai yima yarinyar nan fyaɗe cikin sauƙi yana a hankalinsa. Kai ƙo wata ƙwaya muka bashi bazai yiba kema kin sani tunda mun taɓa gwada hakan. Ni wlhy zuwa yanzu ma gani nake kamar yaron baida isashen lafiyar mazantaka”.        Dariya sosai Hajiya Rubayya ta sheƙe da shi harda ƙyaƙyƙyewa. “Kina bani dariya Aminiyata. To wlhy bari kiji lafiya garas yake. Matsiyacin taurin zuciyane kawai ke ɗawainiya da shi. Kin san fa yaron namiji ne ɗan gaske. Akwai aji da girman kai ga miskilancin jaraba. Ai irinsu koda sha'awar mace zai kashesu wlhy ko'a fuskarsu bazaki taɓa ganewa ba sai idan sune suka so. Tabbas desire tablets bazasu biya mana bukata ba. Wajen mutumina kawai zamuje ya banko masa yasin da manya-manyan aljanuns.....”          “Nifa kin san bana son wannan sabgar Rubayya ko”. Hajiya Mammah ta faɗa cikin katseta da sauri. Baki Hajiya Rubayya ta taɓe da faɗin, “Okay to nikam na barki lafiya. Sai ki nema wata hanyar dan kin san dai wanene wannan yaron. Kuma badan munje inda kike gudunmawa ɗin ba ai da baki samu biyan buƙatar farko akansa ba da waccan shegiyar matar yayan naki”.       Riƙota Hajiya Mammah tai tana bata haƙuri, da ƙyar ta haƙura ta dawo suka cigaba da tattaunawa. Daga ƙarshe suka ɗauki hanyar data zama sanadin alaƙantasu har suka zama aminan juna.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .......Bayan fitowarsa ya jima tsaye a ƙofar ɗakin yana kallonta batare da ta sani ba, kamar ɗazun ma sai da ya jima tsaye tun tana bama Ummie abinci batare data sani ba sannan ya shigo. Dan yana fita ta cigaba da karatun Alqur'ani tana tofama Ummie. Wata irin bahaguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kai yatsarsa babba ta wutsiyar idonsa alamar ɗauke hawaye. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da sakin wani mitsitsin murmushi da ba lallai ka fahimci yayi ɗin ba sai in ka kasance mai lura. Juyawa yay a hankali cikin yanayin mutuwar jiki yabi ta hanyar daya shigo. Koda ya shiga sashen nasa kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce. Yay tsaye gaban dressing mirror ɗinsa yana ƙarema kansa kallo kawai. Tamkar abin almara ya dinga ganinta tana masa gizo ta cikin mirror ɗin. Kasa motsawa yayi, sai ma sautin muryarta da amsa kuwwar kalamanta ke maimaita kansu cikin kunnensa tamkar yanzu take zano masa su da mitsitsin bakinta na rashin kunya. _(“Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”)_ Da ƙarfi ya rumtse idanunsa cikin wani irin yanayi. Sai kuma ya kai hannunsa saman kwantaccen gashin fuskarsa ya shafa, hoton Ummiensa a yau cikin tsafta da cikar kamala na dawo masa. Wata sassanyar ajiyar zuciya ta kufce masa, sake tuno lokacin da take bama Ummie abinci yayi. Sosai tsigar jikinsa ta shiga mimmiƙewa tuna yanda Ummien ke amsa a yanayin buƙata. Kalamanta ne suka shiga sake dawo masa. Da ƙarfi ya kai hannunsa ya harbar da kayan saman mirrorn tare da faɗin, “I hate myself Ummie! I hate myself!!”. Yanda yay maganar cikin ƙaraji jikinsa har rawa yake yi. Tunda yake ba'a taɓa faɗa masa kalaman da suka tada masa hankali irin na yau ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duk suka miƙe. Tuni idanunsa sun jirkice sun koma golden maimakon blue. Sake dunƙule hannunsa yay ya kaima mirror ɗin naushi. A take ya shiga tsagewa. Sake kai masa naushin yayi. Sai ga jini ta gaba ɗaya bayan yatsun alamar yaji ciwo. Bai damu ba, sai ma hannuwan da ya kai gaba ɗaya saman kansa dake wani kalar mahaukacin sara masa ya dafesa gaba ɗaya, jiyay gaba ɗaya ɗakin na juya masa. (Wannan ba sabon abu bane a garesa. Aduk sanda zai zurfafa tunani ko damuwa da al'amarin mahaifiyarsa ko san ɗaukar mataki akan wani abu da bai masa ba game da ita tofa sai ciwon kai. Sai kuma hankalinsa ya gushe gaba ɗaya. Idan kuma ya farko shike nan ya manta komai bazai sake tunawa ba ko magana ko maida hankali akan wani abinda ya shafeta). Yanzun ma dai zubewa yay a kan gadon, tare da cure jikinsa waje guda wani kalar masifaffen sanyi na ratsa illahirin ƙasusuwansa, sai zazzaɓi mai masifar zafi da nuƙurƙusar ɓargon jiki.... 💥💥💥💥💥 Nutsuwar data samu game da shawarar Hajiya Rubayya ya sata ajiye batun hukunta Samraah. Sai ma zuciyarta data gama tsara mata fara shirinta a yanzu. Zuciyarta fes ta fito falon. Arwa da Muhsin kawai ta samu a falon suna kallo. Sai masu aiki dake ɗan kai kawo na tsaftace sa duk da babu wani datti. Komawa tayi da baya zuwa ɗakin Azizat. Kwance ta sameta da waya a hannu tana charting, sai Bahijja dake cikin closet ɗinta tana maida kayan data watso ƙasa. Batare data kalla uwar tata ba ta ce, “Mammah any problems?”. Maimakon taji haushin yanda Azizat ɗin tai magana a tsaitsaye sai ma tai murmushi. Cike da kulawa takai zaune a kusa da ita tana shafa kanta. “Babu komai Baby na. Aikenki dai zanyi sashen Yayanku”. Da sauri Azizat ta ɗago fuskarta da murmushi. Sai kuma ta tura baki tana mai haɗiyewa. “Mammah bayan Yayan ya sake fita shi da tawagarsa. Ina kuma ƙyautata zaton wata tafiyar ma ya sake yi”. Da mamaki Hajiya Mammah ke kallonta ta ce, “Tafiya kuma? Bayan yau ya dawo?”. Sai kuma ta dauki wayarta ta shiga daddanawa batare data jira amsa ba. Kunnenta ta kai. Batare da yin ko sallama ba ta ce, “Kuna ina?”. Cikin girmamawa da ga can aka bata amsa da, “Gamu a airport zamu wuce Chaina”. “What! Shine ba labari?”. “I'am sorry Maa. Da alama tafiyar gaggawace ta tasoma Boss ne.” Ƙwafa tayi, tare da yanke kiran. Batare da tace komai ba kuma ta miƙe tai ficewarta. Da kallo Azizat ta bita sai kuma ta taɓe baki itama ta cigaba da charting ɗin ta..... ✨✨✨✨     A ɓangaren Paah shima hankalinsa ba'a kwance yake ba. Dan tun randa abin nan ya faru bai sake saka samun ko kallon arziƙi daga ɗan nasa ba. Ko jiyyar kwanaki uku da yay a gidan idan ya shiga dubasa sai ya ƙirƙiri barcin ƙarya. Yana samun sauƙi kuma ya tattara ya bar musu gidan. Sai yau ne matarsa ke sanar masa Awwab ɗin ya dawo gida. Shine dalilin barowarsa inda yake a gaggauce yazo gidan. Kai tsaye sashen Awwab ɗin ya nufa, amma tun kafin ma ya shiga Hayatu daya samu a compaund ke sanar masa Awwab ɗin na sashen Hajiya Babba.          Sashen Hajiya Babban yaso nufa shima. Sai dai hakan ya gagara saboda shakkar haɗuwar tasu. Dan yasan a rayuwa Awwab bai haɗa al'amarinsa dana mahaifiyarsa da komai ba. Taɓashin da Hajiya ƙarama tayi ne ya sashi dawowa a hayyacinsa firgigit. Cike da mamaki ta ce, “Lafiya kuwa Abban Awwab?”.      Numfashi ya sauke mai ƙarfi, sai kuma cikin damuwa ya amsa mata da, “Ba komai” yana miƙewa. Da sauri ta riƙo hannunsa. “Ya zakace babu komai bayan ga damuwa ƙarara a fuskarka? Nasan dai bazai wuce akan fushin da Awwab yake ba. Ni a ganina mizai hana kaje ka samesa. Sai ka lallashesa dan yaron nan ya fimu gaskiya, shiyyasa kullum nake nusar da kai illar biyema Addah a gidan nan. Dan koba komai Hajiya Babba uwar ƴaƴanka ce”.        Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kuma ya fisge hannunsa batare da ya tanka mata ba yaja tsaki. Fuuu ya fice abinsa batare da ko waiwayenta ba. Da kallo kawai ta bisa itama. Sai kuma ta girgiza kanta ranta duk a dagule....        💕💕💕💕     *_INDIA_*     Kai kawo take kawai tana kuka ita kaɗai a ɗakin, a kallo ɗaya zaka fahimci tana a cikin matsanancin tashin hankali da bai da misali. Kanta ta shiga girgizawa cike da sakin zantukan da suka zame mata sirrinta cikin sambatu. “Kai ina bazai yiwu ba. Bazan halaka yarona da hannuna ba wlhy. Saimah bazai yiwu ba. Na tafka kuskuren farko bazan bari na sake aikata na biyu ba”. Ta ƙare maganar tana rarumar wayarta. Number ƙanwarta Saimah dake Dubai ta shiga lalubowa. Cikin sa'a kuwa ta sameta a sama-sama dan ko a jiya sunyi waya. Kira ta danna mata, sai dai harta fidda rai da za'a ɗauka tana gab da tsinkewa aka ɗaga.        Mamy da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri tamkar zata fito ko sallama bata tsaya yi ba ta ambaci sunan yar uwar tata kai tsaye.    “Saimah!”.   Cike da mamaki da shiga tashin hankali ta amsa mata daga can. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Lafiya kuwa Aunty najiki cikin tashin hankali? Kar dai kice min mun rasa Mansoor ne?”.      Wani irin suka ƙarshen zancen Saimah yayiwa Mamy a zuciya. Dan haka a fusace ta bata amsa da, “Oh haka kuke zaman jiran ji kenan shiyyasa kika saka ƴarki ta kirasa a waya ta tada masa da hankali da yake bata da isashiyar tarbiyya. To bai mutu ba, ba kuma zai mutu a sanadin auren shashashar ɗiyarki ba in sha ALLAHU....”         A fusace Saimah ta ce, “Wace irin magana ce wannan kuma daga tambaya Sadiyya?”.     “Kin fini sani Saimah. Nace kin fini sani. Duk wata masifa kece ummul ana isin sakamu cikinta. Kai haba nagaji bazan iya jurewaba gaskiya. Maganar auren Mansoor da Husnah babu shi tunda baya so”.     Wata shegiyar dariya Saimah ta sanya daga can. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗora da faɗin, “Wannan shine kuskure mafi muni da zakiyi a rayuwarki kuwa Sadiya. Dan in har Mansoor zai ce bazai zauna da Husnah ba to kemafa ki shirya tsaff dan auren shekara talatin da takwas zai guntule shima. Zan sanarma mijinki da ɗanki abinda kika aikata game da auren Mansoor na farko. Na kuma sanarma duniya komai. Ya rage naki yanke hukunci. Kin san kuma shima Maash ɗin ba kanwar lasa bane dan ya tabbatar miki da hakan”. Ɗit-ɗit ta yanke wayarta.          A matuƙar fusace Mamy tai wani irin masifar yin cilli da wayarta. Sai kuma ta zube a saman gadon ɗakin hotel ɗin tana fashewa da kuka mai masifar ƙarfi...        “Mi kike ɓoyewa Halimatu?”.    Firgigit ta juyo tana kallonsa. Sai kuma ta mike zumbur tana goge hawayenta jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya da kaƙaro murmushi take girgiza masa kanta. “Abban Attahir yaushe ka shigo? Dama kana ɗakin nan? Ai ban san kana nan ba wlhy....”      Hannu ya ɗaga mata. Dole tai shiru. Cikin ɓacin rai ya sake maimaita mata tambayar farko. Sake daburcewa tayi. Harshenta na sarƙewa ta ce, “Ba komai. ALLAH ba komai. Ko kaji wani abu ne?”.      Maimakon amsa mata idanunsa kawai ya dasa mata. Sai kuma ya jinjina kansa batare daya sake tanka mata ba ya juya ya fice abinsa. Gaba ɗaya ji Mamy tai ɗakin na juya mata tsabar tashin hankali. Birkicewa ta sake yi tamkar sabon kamun hauka. Itako idan har Abban Attahiru yaji wayar nan tata ta shiga uku. Wannan wace kalar rayuwa ce ta jefa kanta da ɗanta a ciki saboda kwaɗayin abin duniya. Wane irin son zuciya ne? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un...      Da ƙyar likitoci suka iya controlling sabon yanayin da Mansoor ya shiga. Dan a baya baya aman jini sam. Gashi yanzu iyayensa sun sake jangwaɓo abinda yafi na farko. Bayan dawowa a hayyacinsa hana kowa akai shiga ganinsa har na tsawon kwanaki uku. Sai da suka tabbatar komai ya dawo normal sannan suka barsu ganinsa bayan anja musu dogon gargaɗi.      Sunji farin cikin samun lafiyar tasa. Sai dai bai kula kowa a cikinsu ba har suka gaji da zama suka fito saboda adadin lokacin da aka basu ya cika. Suna fitowa Dad yay wucewarsa, dan har yanzu babu jituwa tsakaninsa da Mamy. Ya tattarata ya watsar da al'amarin ta. Bai kuma sake mata magana akan komai ba. Itako duk wanda ya kalleta yasan bata a cikin hayyacinta a kwanakin nan. Dan komai ya gama ƙwace mata. Ta rasa ina zata kama danta mafi soyuwa a ranta da mijinta na neman kuɓuce mata a dalilin son zuciyarta........✍️ _Humm Mamy wai mi kika aikata ne haka? Miya kuma alakantaki da Maash??🤔_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......A kunyace ta fito daga banɗakin bayan kammala canja kayan da Abba ya bata na barci. Tana fitowa suka haɗa ido da Abba dake zaune a bakin gado saitin ƙofar toilet ɗin. Ƙara cikuykuye Hijjab ɗin nata tayi da saurin duƙar da kanta ta koma jikin bango ta lafe. Murmushi ya saki tare da miƙa mata hannu alamar tazo. Sai dai ta gagara yin hakan sai ma idanunta ne da sukai ƙwalƙwal kamar zata fasa kuka. Murmushi Abban ya sake yi da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya miƙe ya nufeta. Hannunta ya kamo ya jawota jikinsa ya rungume. Kafin a hankali cikin dabara ya zane Hijjab ɗin nata ya cilla saman kujera ƙwara ɗaya dake ɗakin. Ƙoƙarin raba jikinsa da nata yayi amma taƙi yarda da hakan. Sai ma sake ƙanƙamesa da tai tana jujjuya kan nata alamar dai bata son ya ganta a kayan barcin.          A hankali ya ranƙwafa saitin kunnenta ya raɗa mata, “Mu kwana a haka kenan bazaki gaji ba?”.      Kafaɗa ta noƙe masa alamar a'a. Sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Dan ALLAH zan saka hijjab ɗin dai”.          “Kin taɓa ganin amarya da hijjabi a gaban angonta?”. Ya sake raɗa mata cikin kasala. Kasa iya cemasa komai tayi, sai ma cusa kanta da ta sake yi cikin jikinsa. Shima sai bai sake magana ba ya ɗagata cak sai tsintar kanta tayi a gado. Yanda tai wani mugun duƙunƙunewa waje guda kamar ƴar mage ya bashi dariya. Gadon ya hau shima tare da rage wutar ɗakin ya sake jawota jikinsa ya rungume....      ★“Umma ki buɗe min, na rantse da ALLAH Imamu bai isa ya kwana ɗakin tsinanniyar yarinyar can ba.”        “Jalilah bazan buɗe ba. Wai miyasa ke baƙya jin nasiha ne a rayuwarki. Wannan shirmen naki wai kina tunanin zai haifar mana da ɗa mai ido ne? A gabana a gaban ƴaƴanki fa ya rantse ya maya akan in har kika cigaba da ɗaga masa hankali sai ya sake ki babu ko shakka balle kunyata. Amma har kike kasa maida hankalinki jikinki ki nutsu mubi hanyar mai ɓullewa. Imamun yanzu fa ba irin na da bane ba. Ko so kike ya sake kin ki tafi ki bar mata gidan ne shike nan taci nasara a kanki?”.        Kuka mai ƙarfi Mom ta saki. Batare data amsawa Umman tata ba ta zube a wajen tana kara ƙarfin kukanta har numfashinta na seizing tamkar zai rabu da gangar jikinta. Duƙawa Umma dake cikin matsanancin damuwa tayi itama tana cigaba da lallashinta...       ★Zumbur Halime ta miƙe tana zare idanu jin hannun Abba akan jikinta. Shima Abba sai ya miƙe cikin mamakinta ya kunna fitilar ɗakin. “Lafiya kuwa Halimatu?”.     Kai ta girgiza masa tan ƙoƙarin sauka a gadon, riƙota ya sake yi, sai kawai ta fisge hannun ta sauka gaba ɗaya har tana haɗawa da kamar gudu. Zuba mata ido kawai Abba yay mamaki na neman kasheshi. Itako tana lafe jikin bango sai zare idanu takeyi. Murmushi Abba yayi da girgiza kansa. Sai kuma cikin ɗan rage murya ya furta, “Kina son wani abu ne?”.     Kanta ta girgiza masa. Shima sai ya sake jinjina kan. “Okay miya faru to?”.     “Zan je falo na kwanta?”. “Saboda me?”. “Naga zaka kwana anan ne”. “Ai nan ne ya dace dana kwanta Halimatussa'adiyya”.          Da sauri ta ce, “Hu'imm tabb”.    (Badaƙala) Abba ya faɗa a zuciyarsa yana cizon lips ɗinsa. Sai kuma yay ƙoƙarin sakkowa a gadon. Tana ganin zai nufota ta kwasa a guje zatai falo. Ai baima san lokacin daya buga tsalle ya cafkota ba. Kuka ta fashe masa da shi. “Dan ALLAH kayi haƙuri Alhaji. Ni wlhy babu ruwana bana so. Kai fa babba ne”.       Hankalin Abba tashi ya nema yi, a zuciyarsa ya ayyana (Haba Halimatu taya zan iya haƙuri da wannan baiwar taki) a fili kuwa sai ya jawota ya matse a jikinsa. Duk yanda take mutsu-mutsu yaƙi ya saketa. Dan ya tabbatar tana samun sa'a wlhy sai dai yaji a salansa. Shiko yanda ya samu ya killafa Mom ai gara dai ya angwance dan ganin Halime matsayin amarya zuwa gobe sabon show ne yasan zai tashi. Gara ya mora yasan ya mora duk ma wadda za'ayi sai ayi kawai ko.       Cak ya ɗaga Halime zuwa saman gadon. Aiko ta ƙwalla ƙara tana ƙoƙarin turesa. Duk da su Abba an girma ai ƙarfin ba ɗaya ba. Ganin ma tana neman tona mas asiri gida cike da ƴaƴa ga suruka ga Gwaggo sai kawai yay maganin bakin ta hanyar rufesa da nashi. Daga haka ya shiga tabbatar ma Halime shima ɗin da duk da shekaru sun ja da sauransa....       Wani masifaffen ihu da Halime ta fasa tuni ya gama karaɗe gidan. Sai ko a kunnen kowa musamman Mom data gagara rintsawa ita da Ummanta. Dan Gwaggo Gudidi tuni tayi barcinta hankali kwance. Wani irin masifar yankawa zuciyar Mom tayi. Sai ko gata ta ɓaro daga saman gado jikinta na masifar rawa da karkarwa. Ƙofa ta nufa cikin rufewar ido tana dannama Abba zagi da tsinuwa. Tana buɗe ƙofar tayo baya da sauri tare da saka duka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tana mai fashewa da kuka.. Cikin sauri Ummanta ta miƙe. Kanta tayo da sassarfa. Sai dai me, itama tana zuwa jikin ƙofar ta jiyo kukan Halime da roƙon da takema Abba. Tare da surutan Abba cikin sakin layi...         “A'uzubillahi minnashshaiɗanirrajim. La'ilaha illalahu Muhammadurrasulillahi Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Imamu ka gama tambaɗewa. Imamu kayi asara kayi girman kwabo. Wlhy ka gama watsewa Imamu gagararre mara mutunci” ta danna ƙofar da ƙarfi cikin sambatu da ruɗewa. Tuni tsohuwa ta rikice taji abinda yafi ƙarfin rashin kunyarta🥱. Yayinda Mom ta sake gigicewa dalilin salatin Ummanta. Sai kawai ta dinga numfashi da ƙyar kamar zata shiɗe.....       😒Mom ƙyale Abba kinji, ai zai dawo ne zaici mutanen garinsu gwarzo 🥱🤥.   💢💢💢💢 *_INDIA_*    A India kam sama da ƙasa an nema Mansoor an rasa. Dan a daren jiya ya gudu daga asibiti. Matuƙar ƙololuwar tashin hankali iyayensa da ƴan uwansa sun gama shiga. A take suka shiga bincike. Sai gashi an gano cewar yabi jirgin zuwa Abu-dabi a daren jiya. A yanzu hakama awanni biyu kenan da saukar jirgin.         Hankalin Mamy ne yafi na kowa tashi a wannan karon. Dan haka ta azalzalesu akan su bishi. Da farko Dad yaƙi bata goyon baya, sai da Attahir yayta roƙonsa dan shi baisan mike faruwa ba sannan ya amince bisa shawarar da tashi zuciyar ta bashi shima na bari suje ɗin yaga ƙarshen abinda Mamyn ke shiryawa. A ranar basu sami jirgin wucewa Dubai ɗin ba. Sai kuma hakan ma ya zame musu alkairi dan Mamy a daren ta samu labarin zuwan ƙanwar tata Nigeria, dan haka ta sauya akalar tafiyar tasu suma zuwa Nigeria. Dan ta tabbatar in har Mansoor yaje Dubai bai samu Sakinar ba shima Nigeria ɗin zai nufa.      Hakan kuwa ce ta faru, sai dai a washe garin ma basu sami jirgin Nigeria kai tsaye ba sai na Dubai ɗin. Hukuncin UBANGIJI a Dubai ɗin kuma sai jirgi ya haɗasu da Mansoor da shima zai wuce Nigeria ɗin. Nunawa yay ma kamar bai gansu ba, sai da Attahir yaje har inda yake ya masa magana cikin tsokana da lallashi sannan ya kulashi. Suma su Dad ya gaidasu a ciccinkushe. Shi dai Dad ɗin bai kulashi ba. Sai Mamy ce keta nan nan da shi.        Koda suka iso Nigeria tun a airport suka sake nema Mansoor suka rasa. Tashi hankalin Mamy ya sake yi, bata ko saurari Dad ba ta shiga taxi tace ya kaita anguwar su Sakina. Dan suna da gida anan Kano da in sunzo suke sauka. Attahir ne cikin damuwa yay ƙoƙarin tsaidata, amma sai bata ko sauraresa ba dan haka yay zuguy yana kallon motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Dad da shima yake tsaye cikin matsanancin ɓacin rai bai ce komai ba. Rasa abin cewa Attahir ɗin yayi, sai kawai ya duƙar da kansa yay shiru zuciyarsa duk a dagule dan shi kam ya rasa mike faruwa haka kuma a tsakanin iyayen nasu cikin kwanakin nan.....   💞⭐💞⭐💞 MAASH   Har dare bai san inda hankalinsa yake ba. Sai gabannin asubahi zazzaɓin ya sakesa. Ajiyar zuciya ya ringa saukewa a jajjere. Kafin ya miƙe zaune cikin dauriya saboda kiraye-kirayen sallar asubahi da ake tayi tako ina. Cikin nauyin jiki da rashin ƙwari ya nufi bathroom yana haɗa hanya. Ruwa mai zafi ya samu ya shiga. Sai da ya tabbatar ya ratsashi tare da watsakke masa jiki sannan yay wankan da alwala ya fito. Dukkanin sallolin daya rasa jiya saboda yanayin da yake ya fara ramawa. Bayan ya idar da sallar asubahi har zai kwanta sai kuma zuciyarsa ta gargaɗesa akan hakan. Alkur'ani ya ɗauka ya fara karatu, tun yanayi da ƙyar har jikinsa ya fara sakewa nutsuwa ta fara riskarsa. A jajjere ya dinga sauke ajiyar zuciya nan ma. Sai da ya kai har inda yake buƙata kafin ya miƙe ya hau gadon ya kwanta. Shi ba ma'abocin yawan kwanciya barci bane musamman ma na safe saboda yawan uziri. Amma rashin samun na dare yana kwanciya barci mai nauyin gaske yay awon gaba da shi...      A lokacin da Maash ke a sashensa yana fama da ciwo a ɓangaren Samraah tsaye take ƙyam akan ƙafafunta tana miƙama UBANGIJI kukanta. Kaso biyu bisa ukun daren ta rayashine da ƙiyamullail. Kafin ta ɗora da karatun Alqur'ani har asubahi. Tana idarwa duk da barcin dake a cikin idanunta haka ta ɗora shi ta cigaba dayi. Tanayi tana tofama a ruwan data ajiye botiki guda. Da yake tasa himma kafin goma tayi taci kusan izifi ashirin da wani abu. Motse-motsen da Ummie keyi ya fargar da ita, (yunwa) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin miƙewa. Ilai kuwa sai gashi tana farkawa da kiran sunan “Muhammad yunwa. Yunwa Muhammad” ta fara cin karo. Zumut ta miƙa ta nufeta har tana tuntuɓe da katifa............✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ........Sosai mamaki ya kama Paah jin wai Maash ya sake barin gidan. A take ya ɗaga waya yay kiran Hayatu dan yasan ko kiran Maash ɗin yay a yanzu ba lallai ya ɗaga ba. Dan a ganinsa har yanzu fushi yake akan abinda ya faru. Amsar da Hayatun ya bashi na tabbacin sun wuce ya sake tsaya masa a rai. Sai kawai yaji duk yana ƙara zargin kansa da kansa. Da sauri ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Babba. Sai dai me ya samu sashen a kulle. Kai tsaye zargin Maash ne ya kulle yazo masa. Jiki a sanyaye ya sakko yana jin lallai dole shima ya nufi Chaina a yau ko gobe su haɗu da Maash ɗin. 🌟🌟🌟 Cikin barci ya farka da matsanancin ciwon kai. Duk da yanda yaso samun nutsuwa hakan ya gagara. Har magani yasha duk da tsanar da yay masa amma ina. Ya jima yana tsintar kansa a irin wannan halin a mabanbanta lokuta. Sai dai na yau ya tsananta sosai. Dan duk yanda yaso sake komawa ya duba Ummie ya gagara hakan. Har dare yana cikin mawuyacin hali. Salla kawai ke tada shi. Ai kusan ƙarfe ɗaya babu shiri dole yabar gidan. Dan ji ya dinga yi tamkar ana masa yayyafi da garwashin wuta. Ya tsani gidan da komai na cikinsa matuƙa. Kasancewar cikin dare sosai ya fita a gidan babu wanda ya sani da ga ALLAH sai shi sai mijin Mama Balki da ya kira ta waya. Hatta da securitys ɗin gate sanin matsayin Malam Baba agidan yasa koda zai fita da baƙo babu wanda ya iya cewa komai. Azatonsu ma ko mai magani ne tunda yau ciwon Hajiya Babba ya tashi sosai tun safe aketa fama..      Can wani gidansa ƙarami dake a wata anguwa daban dole Malam Baba ya kaisa, anan yay jiyyar kwanaki uku ya dawo ragal, sai sannan yake ji a bakin Malam Baba ai jikin Ummie ya motsa sosai amma itama dai da sauƙi. Dan baƙuwar yarinyar nan na tsaye akan al'amarin dan ma taji mata ciwo. Kasa cewa komai Maash ɗin yayi, sai guri ɗaya daya zubama idanu kawai a yanayin da baka isa tantancewa a kansa ba....    ★★★★    Sam gidan babu kwanciyar hankali. Dan tun washe garin da naima Ummie kitso jikinta ya birkice. Sai ma abin ya nema fin na baya. Dan a ranar naci ɗan karan dukan da kowa sai da ya tausaya min. Dan har asibiti sai da aka kaini. Duk da azabar wahalar da naci a hannunta hankalina nakanta. Sam na kasa samun nutsuwa. Akoda yaushe cikin nazari da aune-aunen abubuwa nake. Dan motsawar ciwon nata ya tsaya min a rai. Ga duk wannan abun da akeyi banga ko giccin ɗanta ba a gida. Alamu kuma sun tabbatar da baya nan kenan. Sosai naji takaicinsa ya mamayeni. Har inaji a raina anya mutumin nan da curin hankali a brain ɗinsa kuwa. Rashin man kan yayi yawa matuƙa. Mahaifiya ai tafi gaban wasa. Amma shi duk motsinsa dai a neman kuɗi yake kawai baya tuna gabansa da bayansa. Kai dolene na saita masa layi ko zai tsireni, tunda na fahimci maganata ta ranar bata dawo dashi a hayyacinsa ba.       Bayan kwanaki uku jikinta yayi sauƙi Alhamdullah. Haka na sake komawa gareta. Ranar kuka nayi sosai ganin sun ɗaureta. Haka na kwanceta ina zubda hawaye. Na rungumeta a jikina duk da nasan komai zai iya faruwa. Sai dai alhmdllh babu abinda tai min face kukan yunwa-yunwa. Yau ma kamar ranar haka na fita na nemo mata abinci, ina bata ta ɓingire barci. Gyaran sashen na shiga yi bayan nayi kiran Mama Bilki ita kuma ta taimaka ta mata wanka. Dan sabbin masu aikin nan da aka kawo fa sun gudu tun daren da abin ya faru ta fashema ɗaya kai. Bayan Mama Balki ta mata wanka da taimakonta na ƙarasa gyaran sashen. Sai ko gashi ita da shi duk sun dawo a hayyacinsu. Duk wanda ya shigo ma sai yayi sha'awa. Nata yima Mama Balki tambayoyi akan wannan al'amari sai dai bata ce da ni komai ba. Dan haka nima na haƙura na duƙufa kula da al'amarin Ummie ɗin tare da ƙara ƙaimi. Dan yanzu ruwa na samu na ajiye na gorori a cikin kowane kwana biyu saina sauke Alkur'ani a ɗakin da tofawa cikin ruwan. Sam na hana kaina isashen barci. Nama daina fita a sashen gaba ɗaya sai neman abinci. Da farko Hajiya ƙarama taso taka min birki akan abinda nake yi ɗin, sai Hajiya Mammah tace ta barni. Duk da abin ya bani mamaki dan ita ma nai zaton zata hanani sai bance dai komai ba. Sai daga baya nakema Mama Balki zancen, shine tace ai Paah ne yace a barni na cigaba da kula da Ummie ɗin, sai dai bata san dalilin Hajiya ƙarama na son hanani ba. Kodan ita likitace tana ganin kamar Ummie zata iya cutar dani ne oho.        Na gamsu da hakan, dan haka na cigaba da sabgata. Sai dai na sakama kowa na gidan ido dan ina son sanin wanda ke ɗaure Ummie ɗin a duk lokacin da ciwonta ya motsa....            ✨✨✨💫     Tun asubar fari Mom ke bugama su Abba ƙofa. Amma babu alamar ma ya jita balle amaryar tashi. Sai dai abinda bata sani ba duk zagi da bugun da take musu yana jinta. Bashi da lokacinta ne kawai dan hankalinsa nakan Hamile dake faman masa kuka har yanzu. Babu irin taimakon da bai bata ba harda su magani amma yarinyar nan ta tasashi da kukan iya shege da duk ya hargitsashi. ALLAH ya soshi ma har kayan shayi ya shigo mata da su, akwai kuma kettle a ɗakin nata kasancewar ba'a haɗa mata hitter ɗinta ba na toilet yasa yayi dabarar ajiye mata kettle ɗin.        Tsabar iya shege irin na Halime Mom na buga ƙofar ɗakin tana zaginsu sai ta sake sakama Abba sabon kuka. A rikice ya riƙota jikinsa yana tambayarta mi take so. Baki ta laɓe tana sake saka kukan da turza ƙafafunta. “Ai dai Abba kai kace na girmamata. Amma gashi can tana zagar Innata da Babana bayan kuma Innata ta rasu. Ni wlhy bazan yarda ba.”        Cike da lallashi Abba ya sake sakata a jikinsa yana faɗin, “Kinga yi haƙuri barta, haba Halimatussa'adiyya na. Keda kike tare da mijinki ina ruwanki da duk abinda take. Ko kina so nima nayi miki kukan ne. Jibafa jikinki zazzaɓi ne ki kwanta ki huta ko na sake sakaki a ruwan ɗumin”.      “Uhm uhm” ta faɗa tana maƙe kafada da tura masa baki. Murmushi yayi da sake sakata sosai jikin nasa. Komai yarinyar tayi sake shiga masa rai take. Ga alkairin data kawo masa har gadon barcinsa na ƙara sakashi jin ƙaunarta mai tsanani da kimarta harma da mutuncin iyayenta. Shagala a lallashin Halime yasa bai san lokacin da Mom ta bar buga ƙofar ba ma. Yana samu tayi barci ya tashi yayi shirin massalaci ya fita sallar asuba. Da yakan bari gari yay haske sannan ya dawo gida. Amma yau ana idarwa ya dawo gidan. Wajen Halime ya koma sai da ya tadata tayi salla ya bata shayi tasha da magani tana masa taɓara yana lallashi, bayan ta koma barci sannan ya sauke ajiyar zuciya ya fito. Ɗakin ya rufe mata ya nufi ɗakin da Gwaggo Gudidi ta kwana suka gaisa. Acan ya samu Musaddiq wajen Gwaggo suna hirarsu hankali kwance. Dan haka ya zauna ana hirar da shi. Anan ne yake jin wai Musaddiq ɗin ya samu aiki a companyn Maash na ƙera motoci. Kusan satinsa uku kenan ma yana zuwa. A yanzu haka ma company ya masa alƙawarin turashi ƙarin karatu ƙasar Chaina. Gaba ɗaya sai yaji kunya ta rufesa. Yay ƙasa da kansa kawai yanata jinjinawa.       Daga Musaddiq har Gwaggo Gudidi sun fahimci kunya ta rufe Abba, dan haka Musaddiq ya saki zancen ya kama wani. Itama sai Gwaggon ta koma masa nasiha akan kada ya biyema Mom duk haukan da take a gidan kodan darajarsa matsayin namiji uba da kuma yaƴansu. Ya mata alƙawarin in sha ALLAHU bazai biye mata ba. Daga nan suka ɗan ƙara taɓa hira ya tashi ya fita zuwa ɗakin Mom ɗin.           A falo ya sami Auta da Bibaa. Auta yazo garesa da gudu yana murnar ganinsa. Bibaa kuwa sai ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba sai da shi da kansa ya kira sunanta sannan ta gaishesa tana faman fushi. Murmushi kawai yayi ya wuce dan ya fahimci kishi take taya uwarta. Hannunsa riƙe dana Auta ya shiga bedroom ɗin Mom. Dai-dai lokacin take fitowa daga wankan da Umma ta sakata yi dole. Sosai ya ƙura mata udanu yana kallon yanda idonta suka kumbura sunyi jazur je dama fuskarta. Itama wani mugun kallo take watsa masa mai cike da tsana da takaicinsa. Dan wani irin ƙyau da kwarjini taga ya ƙara mata. Daka gansa kaga sabon ango shar daya sha sharafinsa. A take abinda ya ringa musu a gida jiya ya shiga dawo mata. Fashewa da kuka tayi tana rarumar kwalbar turare ta jefesa. Da sauri ya kauce yana tura Auta bayansa. Cigaba da rarumo duk abinda ya tare mata gaba tayi tana jeho masa. Tun yana kaucewa har dai ta samesa. Dole ya fito yana dariyar data sake kular da ita. Dan harga ALLAH shifa dariya borin nata ke bashi yanzu. Da Ummanta yaci karo tana ƙoƙarin shigowa da shayi a hannunta. Haɗiye dariyar yayi ya rissina yana gaisheta. Da ƙyar ta iya amsa masa tana wucewa ko kallonsa batai ba dan itama dai al'amarin nasa na jiya ne ya shiga dawo mata a rai tamkar yanzu komai ke faruwa.......✍️ _🤣Maganin mai zama gidan suruki kenan ai Umma._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Alhamdullah sati biyu kenan da fara maida akalar al'amurana sashen Hajiya Babba. Tun ina ɗari-ɗari har na fara sakin jikina. Nayi tunanin Hajiya Mammah ko sauran matan gidan wani zai hana amma sai naji shiru. Sai ma jana da Hajiya Mammah ɗin ta farayi jikinta yanzu. Dan ta daina min faɗa sosai. Aikin sashenta ma idan naje yi iya bedroom take cewa na gyara kawai. Tun al'amarin nata naɗan bani mamaki har dai na tattara na watsar da tunanin ALLAH ne ya amsa addu'ata na fara samun sauƙi daga kowa.          Abinda na fara fahimta ga lalurar Ummie shine tana ƙarfafa ne a duk sanda Awwab ya shigo inda take ko kuma yama zo gidan zance. Dan a kwanki ukun nan da yake a gidan gaba ɗaya mun kasa gane kanta. Yau da safe har ciwo ta jimin da ƙyar aka fito dani a wajenta. Dalilin hakanne ma na yini a sashenmu da zazzaɓi shine nake kwance har yanzu. Ban samu ɗagawar jikin ba sai dare. Kwanciyar ce ta isheni na tashi na fito. Shiru sashen dan kowa har ya kwanta. Harna zauna a falo sai kuma na tashi na fita gaba ɗaya. Ko'ina akwai haske a gidan kai kace rana ce, sai dai babu hayaniya mai ƙarfi dan wanda ma basuyi barci ba duk sun nutsu a ɗakunansu. Tsamin da jikina yay ya sani ɗan fara tattakawa ko zai sake min, duk da ina kwaɗayin zuwa na duba Ummie sai dai babu yanda zanyi dan yau ɗin kam zuwa kusa da ita haɗari ne babba. Cinkushewar zuciya da son mantar da kaina damuwata ya sani nufar garden ɗin gidan. Shi kam akwai ƙarancin haske a cikinsa, amma ko ɗar banji tsiro ba na samu kujera na zauna ina mai ƙurama korayen gayyakin cikinsa da ƙarancin haske ya sakasu yin duhu ido. Kamar da ga sama naji ana wata ƙara mara daɗin ji, gabana ne ya faɗi. Sai kuma na fara jin sambatu dake fita da wasu irin kalamai marasa daɗin saurare. Neman rikicewa nayi, da sauri na kai hannu na toshe kunnuwana. Ban san adadin mintinan dana ɗauka ba a haka kafin na buɗe kunnen. Yanzu kam shiru babu ihun, sai magana ƙasa-ƙasa da akeyi cikin raɗa. Miƙewa nayi cikin sanɗa na nufi inda nake jin maganar. Hango mutane tsaye mace da namiji, namijin na ƙoƙarin sakama macen kaya a jikinta ya sani lafewa jikin fulawoyi.       Cikin shagwaɓa macen ke faɗin, “Wlhy ni na faɗama ban gaji ba. Miyasa yau duk baka son kasancewa da ni ne? Ko dai ka samu wata ne a cikin sabbin masu aikin nan?”.           Da ɗan kaushin murya namijin ya bata amsa da, “Miyasa kike da zargi ne wai? Kin san fa minene matsalar. Muhammad na gidan nan ke miyasa baƙya lissafi ne! Kije sai da safe bana son damuwa”.     Magana ta yunƙura zata sake masa ya ɗaga mata hannu. Sai naga ta faɗa jikinsa ta rungumesa. Niko tunda ya ambaci Muhammad zuciyata ke wani irin rawa. Dan kuwa a bakin mutum ɗaya ne nake jin sunan nan. Kuma ɗansa kawai yake kira da shi wato Awwab. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” na faɗa cikin rawar baki sakamakon ganin wanda zuciyar tawa ke ayyana min. Paah tare da Siyama a garden suna aikata z... kasa ƙarasawa nayi, sai ma wani irin kuka daya kufce min. Dole nakai hannuna na toshe bakina har sai da suka fice sannan na durƙushe a wajen nayisa. Wannan wane irin zubar da mutunci ne. Mutum mai daraja da kima kamar Paah ace yana bin masu aiki. Kai ya Arrahaman. Gaskiya ya kamata nasan tarihin wannan gida, ko hakan zai taimakeni wajen fara rarrabe ƙarya da gaskiya. Tare da kallon kowa na gidan nan da siffarsa.       Bayan kamar tazarar mintuna ashirin da fitarsu sannan na fita. Sashenmu nayi nufin komawa, amma sai naci karo da Mama balki da alama daga sashen namu ta fito. Idanu ta waro sosai a kaina. Sai kuma ta kama hannuna cikin sauke ajiyar zuciya tana tambayata “Daga ina haka? Yaya jikin naki? Badai sashen Hajiya Babba kika koma ba?”.      Kaina na shiga girgiza mata. Hawayen da nake makalewa na kufcemin. Sake tashin hankalin ta yayi. Babu shiri taja hannuna. Siririyar hanyar sashensu da mijinta tabi dani. Sai gamu a madaidaicin falonsu da yau ne shigowata cikinsa na farko. A saman kujera ta zaunar dani itama ta zauna. Sai da ta bani ruwa nasha sannan ta fara jeramin sabuwar tambaya.           Kaina na girgiza mata kawai. Tare da faɗin, “Mama babu komai. Amma dan ALLAH idan bazaki damu ba ki bani tarihin wannan gida a yau”.     Ɗan jimm tayi kamar mai nazari. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wani abune ya sake faruwa kuma?”.      Kamar zan faɗa mata sai kuma na fasa saboda kwaɓar da zuciyata tayi min. “Babu komai Mama. Kawai dai ina son jine saboda nasan ta hanyar dazan ɓullo wajen taimakon Ummie game da wannan ciwon nata.”      Nan ma shiru tayi kamar bazata tanka min ba. Kafin ta nisa tana mai jinjina kanta. “Zan sanar miki duk abinda na sani Kandala. Saboda harga ALLAH tun randa na fara ganinki a gidan nan zuciyata ta sami nutsuwa dake. A kuma kwanakin nan da kikayi na gwadaki ta hanyoyi da dama banga wata alamar cin amana ko kasancewarki ba mutuniyar kirki ba. Amma duk da haka ina roƙonki ki riƙe min dukkan abinda zan faɗa miki amana dan ALLAH. Sannan zan taimakeki da abinda zan iya domin ganin munyi wani yunƙuri akan Hajiya Babba ko ALLAH zaisa mu dace.”        “Nagode Mama.”      *_Alonso_* aƙon haure daga ƙasar Spain zuwa Nigeria. Kwara-kwara, bature-batture, balarabe-balarabe gashi nan dai bamu san takamaimai ɗan wane ƙabila bane ko yare, kawai dai daga ƙasar Spain yazo. Abinda kawai kowa yake kallo a tattare da shi shine bashi da alaƙa da Africa sam.  Alonso ba musulmi bane ba, baya kuma jin hausa ko zo na kasheka, daga turanci sai yaren Spanish. Da farko harkar kasuwanci ce ta shigo da shi ƙasar Nigeria. Dan yana kawo irin dish ɗin nan na kwanika kala-kala da mutanen da ke jere da su. Kafin a hankali ya samar da wajen yinsu anan cikin garin Lagos ya ɗauki yaranmu aiki yana kuma koyar dasu. Sannu a hankali kamfani ya fara bunƙasa kafin cikar shekara biyu duk yaran daya hora sun gama ƙwarewa har suma suna koyar da wasu. Adams shine kusan babban yaron Alonso saboda ƙwazonsa, ga biyayya da ya kema uban gidan nasa tamkar yaya da ƙane duk da kuwa Adams nada mata acan ƙauyensu dake Kano mai suna kwanar-mashi harda ƴaƴa biyu. Dan neman kuɗi ne ya kaisa garin na Lagos. Ƙyaƙyƙyawan halin Adams yasa Alonso yanke hukuncin kaisa ya ƙaro ilimi acan ƙasarsu ta Spain tunda ya faɗa masa yayi sakandire, sai dai bai kammala duka ba saboda matsala ta rashin kuɗi ga nauyin iyayensa da matarsa da duk ke a kansa. Alonso shine ya saka Adams dawowa da iyalinsa da mahaifiyarsa nan Lagos da zama. Tare da saka yaransa biyu mace da namiji a makaranta. Nafisa da Mu'azz, sai ciki da matar tasa ke da shi tsoho. Ganin a yanayin da take Alonso ya bama Adams shawarar tafiya da ita amma sai mahaifiyarsa ta hana. Ganin haka yasa Alonso neman wadda zata kula da ita matsayin mai aiki saboda mahaifiyar Adams bata da wani ƙarfin yin hakan saboda tsufa. Sai dai duk wadda aka kawo sai a samu matsala saboda masifar matar Adams. Dan mace ce azababbiya matuƙa...           Rabi'atu yarinya ce budurwa da bazata wuce shekaru goma sha shida ba. Ɗiyace wajen mai abinci dake gab da kamfanin Alonso Kuma duk a wajensu suke cin abinci. Tayi matuƙar sabo da Adams harma wasu na ganin ko son juna suke. Sai dai sam ba haka bane ba. ALLAH dai ya haɗa jininsu ne kawai kasancewarta yarinya nutsatstsiya mai hankali ga ilimin addini da girmama na gaba da ita. Ba Adams kawai ba kowa a gurin Rabi'ah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da shi har shi kansa oga kwata-kwatan wato Alonso. Ganin tafiyar Adams na matsowa ga matarsa taƙi kwantar da hankalinta ta zauna lafiya da masu aikin da ake ɗauka mata sai Adams ya roƙa Rabi'ah akan ta dinga zuwa tana ɗan mata gyare-gyaren kafin a samu wata. Babu musu Rabi'ah ta amince, dan akwai ƴar ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da matar Adams ɗin a dalilin kai musu abinci da take kullum gida saboda basu fara girki ba. Fara aikin Rabi'ah baifi da sati guda ba Adams ya wuce ƙasar Spain bisa ƙoƙarin uban gidansa Alonso. Bayan wucewar Adams Rabi'ah ta cigaba da ɗawainiya da matarsa Uwani har ALLAH ya sauketa lafiya. Bawai bata mata masifar bane ita, kawai dai tanada haƙuri ne sosai shiyyasa kowa ke ganin babu matsala. Bayan haihuwar matar Adams da wata biyu wani rikici ya taso, dan zuwa yanzu kanta ya ƙara wayewa tayi sabbin ƙawaye. Duk wahalar da Rabi'ah kemata da jaririnta da sauran yaranta biyu ta rufe idanunta ta mata rashin mutunci wai tana soyayya da mijintane. Rantsuwa sosai Rabi'ah ta shiga mata tana kuka akan ita bata da wata alaƙa da Adams face ta mutunci kamar kowa. Amma sam sai taƙi saurarenta har ta kaita da fusata ta watsa mata ruwan zafi dake akan risho da Rabi'ah ɗin ta ɗora zata mata girki. Hankali tashe aka kwashi Rabi'ah zuwa asibiti.       Alhamdullah anyi sa'a ƙunar batai nisa ba. Dan ta iya hannunta zuwa gefen ciki ce kawai ta tashi. Ta fuska ALLAH ya taƙaita mata wahala. Hankalin Alonso ya tashi, dan haka ya shirya matar Adams da yaransa biyu suma ya turasu ƙasar Spain inda mijinta ke karatu. Shi kuma ya maido tsohuwa mahaifiyar Adams ɗin gidansa dan yayi alƙawarin kula da ita har su Adams su dawo. Ƴar shaƙuwar da Rabi'ah tayi da tsohuwa yasa bayan warkewarta ta cigaba da zuwa gidan Alonso tana mata hidima duk da kuwa an ɗauka mata masu aiki. Rayuwar yarinyar da ƙyawawan ɗabi'unta ya fara jan hankalin Alonso kanta. A hankali sai ya fara sanyama duk motsinta ido idan tazo gidan. Tun tsohuwa bata lura ba harta fuskanta. Tausayi ya bata sosai, dan tasan da kamar wuya a bashi auren Rabi'ah tunda shi ba musulmi bane. Amma dai tana kan masa addu'a itama na ALLAH ya shiryesa kodan kyawawan ɗabi'un da ALLAH ya zurtashi da su. Zamu iya cewa ALLAH ya amshi addu'ar tsohuwa akan gaɓa. Dan kuwa randa Alonso ya gagara daurewa ya amayarma Rabi'ah sirrin dake a ransa ta tabbatar masa bazai yiwuba saboda addini ya bambantasu a ranar ya musulunta. Wannan al'amari yay matuƙar yima tsohuwa daɗi, dan haka ta sanar da Adams ta hanyar telephone da ake amfani da ita a lokacin kuma sai a gidan ma wane da wane. Shima sosai ya tsinta kansa a farin ciki mara musaltuwa dan dama burinsa kenan.........✍️        _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_ What you need to start making $500 from PromptEarn Dollar Affiliate 👇. 📍A smartphone 📱. 📍 Internet Connection. 📍Access to your AIM Course. 📍 Atleast 2 hrs of your daily time. If you still don’t know what this is, click the link below to know how you can start 👉https://wa.link/6f3908 ________ .....Musuluntar Alonso daya koma Ibrahim Khalil bai sa Rabi'ah ta amince da shi ba har sai da ta tabbatar yayi tubane domin ALLAH badan soyayyarta ba. Biki akayi na bajinta duk da kuwa kowa bai san iyayen Alonso (Ibrahim Khalil) ba. Sai Adams dake acan yana karatu. Shedar daya bada akan asalin Alonso (Ibrahim) yasa ba'a zurfafa bincike ba aka bashi kodan musulunci daya amsa ai ya zama ɗan uwa. Rayuwar Rabi'ah da Ibrahim rayuwace mai sauƙi da ƙayatarwa. Ga tsohuwa a gefe na ƙara ɗorasu kan ƙyaƙyƙyawar tirba. Shekararsu ɗaya da aure ya ɗuketa sukaje ƙasarsa. Acan suka iske Adams da iyalansa. Sosai Adams ya nuna farin cikinsa, sai dai ga matarsa sam ba haka bane ba. Banda harara da kallon banza babu abinda take bin Rabi'ah da shi har sai da Rabi'ahr ta tattarata ta watsar itama sannan tasha jinin jikinta. Satinsu biyu suka dawo Nigeria dan Ibrahim ya riga ya saba da rayuwar sabuwar ƙasarsa. Dawowarsu da watanni biyu iyayensa suka samu iftila'in gobara suka ƙone ƙurmus. Dole ya sake tattara Rabi'ah suka koma cikin tashin hankali. Sai dai zuwan nasu bai canja komai ba dan anyita ta ƙare Ibrahim ya rasa ahalinsa.            Wannan shine dalilin dawowarsa Nigeria gaba ɗaya. Adams ma ya dawo shi da iyalansa. Har lokacin kuma Rabi'ah bata taɓa ko ɓatan wata ba. Hakama matar Adams bata sake haihuwa ba tun Abdullahi. Dawowar Adams yasa Ibrahim sake sakar masa ragamar kamfani sosai. Aiko cikin amincin ALLAH sai sake bunƙasa yake har sun fara buɗe wasu reshikan a jahohi. Kwatsam sai ga Rabi'ah da ciki. Musalta farin cikin Ibrahim da su Adams da suka zama ahalinsa a yanzu ma ɓata lokaci ne. Haka aka shiga jelar tattalin cikin nan har ALLAH ya sauketa lafiya aka haifo ɗiya mace ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kamanni da mahaifinta. Yarinya taci suna Ummu-Hidaya kamar yanda Rabi'ah ta buƙaci a sanya mata. Duk wani gata Ummu-Hidaya na samunsa ga kowa. Sai dai hakan bai hana Rabi'ah tsayawa akan tarbiyyarta ba. Dan haka ta tashi yarinya mara kwaramniya ga kuma gatan iyaye da na yayu su Mu'azz da a yanzu su take kallo matsayin zuri'ar iyayenta. Tana da shekara huɗu Rabi'ah ta sake samun ciki. Nan ma anyi farin ciki matuƙa. Cikin nada watanni biyar tsohuwa mahaifiyar Adams ta rasu. Ibrahim yaci kuka dan sai ma ka ɗauka itace ta haifesa shima. Hakama Rabi'ah ta shiga ɗimuwa. Ba'a gama kukan mutuwar tsohuwa ba mahaifiyar Rabi'ah itama tai accident ta rasu. Ai sai Rabi'ah ta ƙarasa birkicewa. Dan bata san kowa ba a danginta a duniya sai mahaifiyarta. Tun bata da wayo take mata nacin sanin ina babanta da ƴan uwansu dan daga ita sai ita ta buɗe ido ta sani a Lagos sai masu tayasu aikin abinci amma bata sanar mata ba gashi har rayuwa ta ƙare. Sam lafiya taƙi samuwa ga Rabi'ah. Ga cikin na matuƙar bata wahala ƙwarai da gaske. A haka dai aka kai watan haihuwa da ƙyar. Sai dai kuma ranar haihuwa anta shan fama haihuwar tazo da gardama. Ganin za'a iya rasata ita da abinda ke cikinta aka yanke shawarar yimata cs. ALLAH sarki rayuwa, kana naka ne ALLAH na nashi, dan kuwa ana fiddo ɗan Rabi'ah daga ciki tace ga garinku nan itama. Ɗimaucewa Ibrahim yayi gaba ɗaya, dan takai sai da aka kwantar da shi asibiti shima. Kwanan jinjiri biyar a duniya shima ALLAH ya amsa abinsa...             Shike nan komai ya ƙare komai kuma ya tsaya ga Ibrahim. Dai-dai da harkar Companyn ma ya tattara ya watsar sai Adams ne ke kula da komai. Gaba ɗaya rayuwarsa ya tattara akan Ummu-Hidaya ne. Shike mata komai, sai mahaifiyata da aka ɗakko aiki domin kulawa da ita a lokacin, amma hatta barci a tare sukeyi har sai da takai shekaru goma sannan ya raba musu wajen kwanciya. Zuwa yanzu ya ɗan fara haƙura, sai dai babu abinda ke saka rayuwarsa a farin ciki sai Ummu-Hidaya, musamman idan ya ganta a farin cikin itama, itako indai tana cikinmu yaran masu aiki tana wasa zaka sameta cikin walwala da yawan fara'a. Gata yake mata da cikakkiyar tarbiyya mai ƙayatarwa. Tare da fara koya mata harkokin kasuwanci daban-daban. Tun ma bata fahimtar komai a kasuwancin harta fara ganewa. Tana da shekara goma sha bakwai a duniya ta kammala secondary. Zuwa yanzu ta zama budurwa. Sai dai yanayinta da suffarta da bai kama da na baƙar fata ba yasa sam bata da wani jikin girma. Sai dai akwai ilimi ga tarbiyya da nutsuwa. Bata da yawan magana sam. Idan kaganta tana surutu sai da Babanta ko Mu'azz ɗan Adams na biyu ko Drivern Ibrahim Abdul-wahab da muke kira Jirgin mota a gidan. Amma Mu'azz shine abokinta a gidan sosai, sai kuma autar Adams ɗin da matarsa ta sake haifa masa bayan rasuwar Rabi'a mai suna Mashi'a, Nafisa yayarsu gaba ɗaya kuwa masifarta tasa ko harkarta Ummu-Hidaya bata shiga, sai dai tana girmamata. Tun ana kallon rayuwar Ummu-Hidaya da Mu'azz a matsayin shaƙuwa har kowa ya fahimci akwai soyayya mai ƙarfi a tsakaninsu. Sosai Adams da Ibrahim sukayi farin ciki da hakan. Dan koba komai zasu hada alaƙar jini a tsakaninsu bayan ta zuminci da ALLAH ya riga ya haɗa musu. Dan zuwa yanzu idan baka sani ba sai ka ɗauka Ibrahim da Adams yan uwane uwa ɗaya uba ɗaya. Sai dai kawai siffar jiki data banbantasu. Shi Ibrahim daka gansa zaka san dan ƙetare ne. Shiko Adams baƙine kuma ƙyaƙyƙyawa. Gogewa da ilimi da ya sake yi ga dukiya ta zauna gwargwado yasa idan ka gansa bazaka taɓa tunanin shi ɗin nan ne ba na ƙauyen k/Mashi da yazo leburanci garin Lagos. Saboda tuni Ibrahim ya bashi wani abu mai kauri a dukiyarsa shima ya kafa kansa. Shi kuma ya maida komai nasa daya mallaka matsayin na Ummu-Hidaya tare da tsayawa akanta ta koya harkar kasuwanci tun tana ƙaramarta. ALLAH kuma ya sanya albarka a tare da ita dan komai sai sake bunƙasa yake tamkar ba yarinya ƙarama ba.       Bayan ta kammala secondary Ibrahim da Adams suka yanke shawarar aurama Mu'azz ita. Haka kuwa akayi aka musu auren gata. Bayan auren babu jimawa Ibrahim ya nema musu makaranta su duka. Dan shima Mu'azz ɗin zai sake ƙaro karatu duk da ya kammala degree dinsa na farko tun kusan shekara biyu kenan shima yana aiki a companyn Ibrahim.....       Next please 🚦🚴         💕💕💕💕            Mahaukacin bugun da akema gate ɗin gidan ya saka maigadi tahowa da sauri ya buɗe. Zai yi magana Mansoor yasa hannu ya ingijesa ya danna kai ciki. A ƙofar falo suka kusan cin karo da Hajiya Sakina da bugun itama ya fiddota. Kallon kallo suka tsaya yima juna. Kasancewarta gogagguyar mace da idanunta suka gama buɗewa sai ta saki murmushi. “A'a masha ALLAH Son kai ne a gidan namu? Alhamdullah jiki yayi sauƙi kai barka-barka ALLAH mun gode maka”.        Abinda ya tokare maƙoshinsa da ƙyar ya haɗiye, kafin ya kalleta a ɗage ya ce, “Ina ƴarki?”.     Murmushi ta sake yi da faɗin, “Son ƴata ko matarka dai? Ina fatan dai ba zuwa kai kace a yau zata tare ba?”.     Tsaki yaja mai ƙarfi da watsa mata kallon raini. “Ai bana tunanin ta cika macen da har zata tare a gidana. Ballema ni Bamma san da aurenta ba”.      Cikin sosuwar zuciya Hajiya Sakeena ta ce, “Idan kai baka sani ba ai uwarka da ubanka sun sani Mansoor. Kai karfa kaga ina lallaɓaka ka nema gayamin magana. Ƙanwar uwarka ce ni idan ka manta na tuna maka”.         “Na gode da kika fahimci sunanki ƙanwarta ba ita ɗin ba. A tunaninki munafuncin da kika ƙulla aka rabani da wadda nake so zai sa na auri ƴar iskar ƴarki sauran mazan Dubai ne. To kinyi kuskure, dan ko mata sun ƙare ballagazar ƴarki bata cikin matan da zan kalla matsayin mace dan bata da suffar matan. Dan haka na saketa saki ɗaya biyu uku”. Ya ƙare maganar da jefa mata takarda akan fuska ya juya abinsa. Mutuwar tsaye Hajiya Sakeena tayi a wajen, yayinda Husnah ta ƙwalla ƙara ta zube a wajen gaba ɗayanta. Sai a lokacin uwar ta dawo hankalinta. Itama ƙwala ƙarar kiran sunanta tayi da zabura kanta.......    💢✨💢✨💢 💢🌟💢🌟💢                  A shekarar farkon aurensu ALLAH ya azurtasu da samun ƙaruwar ciki. Tunda labarin ciki ya iso kowa ke farin ciki, musamman Ibrahim (Abbie) daya kasa zaune ya kasa tsaye. Ƙarshe ma sai ya shirya shi da Adams (Baba prof... sukaje duba Ummu-Hidaya ɗin. Satinsu biyu sai gasu sun dawo, sai dai yanayinsu na komawa sanyi-sanyi duk ya bama kowa mamaki, sai daga ƙarshe muke jin labarin ai cikin ne ya zube ashe. Daga lokacin Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Ba kuma su dawo Nigeria ba sai da ta kammala karatun ta. Irin farin cikin da kowa ya tsinta kansa na dawowar tata bashi da misali. Daga ita har mijinta sun ƙara wani irin ƙyau da cikar haiba. Kai da ka gansu kasan hutu ya zauna a jikinsu. Musamman ita dake mace. Tunda suka dawo ta fara jana a jikinta, yayinda kuma taita faɗan miyasa ban cigaba da karatu ba. Mamana ce ta sanar mata ai Babana ya hana, yace boko kafurci ne. Murmushi kawai tayi bata sake cewa komai akan karatun nawa ba, sai ma maida akalarta da tayi akan batun ya kamata nayi aure. Ganin ta damu nan ma Mamana ta sanar mata ai babu tsayayye. Dariya mukaga tayi, tare da juyawa ta fuskanci mahaifinta dake zaune a gefe yana duba wasu takardu. Cikin nutsuwarta ta ce, “Abbie niko mizai hana ka bama Yaya Abdull auren Bilkisu ne?”.      Mu duka sai da muka kalleta da mamaki, dan kowa yasan wa take cema Yaya Abdull a gidan. Wato dai drivern Mahaifin nata da muke kira jirgin mota. Girmama sunan duk ma'aikatan gidan tarbiyyar Ummu-Hidaya ce haka. Dan kowa bata faɗar sunansa kai tsaye sai ta haɗa da Yaya ko Baba ko Mama ko Aunty. Yanda take daraja mu masu aiki yasa kowa yake ƙaunarta sosai, babu mai son ganin ɓacin ranta sam hatta mu ƙanana.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .......A mamakinmu sai mukaga Abbien nata yayi murmushi mai ƙayatarwa da birgewa. Cike da kulawa ya ce, “To Ummuna kin tambayesu suna son juna? Ko kina ganin ya dace ai musu auren dole?”.         “Lah a'a Abbie ba haka nake nufi ba. Nifa na jima da sanin suna son juna. Kawai dai sunƙi bayyanawa ne kasan duk matsorata aka tara daga Yaya Abdull ɗin har Balkisun”.       Dariya kowa ya sanya, yayinda na miƙe da gudu nabar falon. Daga haka ban san yaya aka ƙare ba sai jin ana shirye-shiryen bikinmu kawai. Abdul-wahab mutum ne mai kunya dan haka shima ya gagara mun magana. Duk sanda ma muka haɗu sai dai yayi murmushi kawai ya sunkuyar da kansa. Nima hakan take a gareni. Cikin kwanaki kaɗan aka dasa hidimar biki, zakisha mamakin yanda akai bikin aurena tamkar yarinyar gida ba ƴar masu aiki da drivern gida ba. Bayan kammala bikin anan dai cikin gidan muka cigaba da zama. Sai dai mahaifiyata Ummu-Hidaya ta buƙaci tayi ritaya ta huta hakanan. Hakan kuwa akayi, ta ajiye aikinta suka bata ƙyautar ƙaramin gida ta koma can. Sun buƙaci shima Abdul-wahab ya ajiye aikinsa amma yaƙi, acewarsa bazai taɓa iya rabuwa da mutumin kirki irin Abbie ba. Haka dole suka barsa badan sun so ba. Da a ganinsu shima yanzu ya kamata a martabashi kafin matarsa ta fara haihuwa.. Watan aurenmu biyar da Abdul-wahab sai ga ciki ya bayyana a jikin Ummu-Hidaya. Kowa yasha mamaki dan ciki har kusan wata biyar amma babu wanda ya san da shi. Sai daga baya na fahimci ita fa tasan da abinta tana ɓoyewa ne kawai. Na shiga mamaki ƙwarai da gaske akan ɓoyewar tata. Dan nasan yanda kowa ke fata da zumuɗin samun cikin amma har ta iya ɓoyesa na tsawon lokaci haka. Rashin mai bani amsa yasa na tattara komai na watsar. Kulawar Ummu-Hidaya gaba ɗaya ta dawo kaina. Dan ta tabbatar min na sanya mata ido akan komai da zataci a gidan. Hatta da abinci idan tana so sai tace mu shiga kitchen ɗin tare, tana zaune zan dafa na bata taci abinta anan sannan mu fito. Hatta da ruwan shanta Abdul-wahab kawai ta aminta ya kawo mata daga Company. Ko wani abu take son ci shi kaɗai take aika ya saya mata. In ba shi ba ko an kawo bata ci. Abubuwan suna bani mamaki da ɗaure kaina sosai. Gashi ta gargaɗeni akan kada kowa yasan wannan tsarin nata hatta da mahaifinta. Dole kuwa na haɗiye duk wani abinda ke'a raina da damuwata, na dai cigaba da bada ƙaimi wajen kulawa da ita. Sauƙin ma cikin nata bamai laulayi bane sosai. Dan hatta company bai hanata zuwa ba. Tana gab da haihuwa suka sake buɗe katafaren companyn yin kayan gine-gine da kwalliyar gida. Ummu-Hidaya kuma ce ta samar dashi bisa fiƙirar da UBANGIJI yay mata. A randa akai shagali buɗe Company a ranar naƙudar ta tashi mata. Batare da kowa ya sani ba tasa na kira mata Mamana, ni da ita muka karɓi Haihuwar a gida batare da kowa ya sani ba. Sai wata Nurse ƙawarta da sukai secondary tare mai suna Lawisa (Hajiya ƙarama ina fatan kin gane). Alhamdullah ta sauka lafiya, yaronta santalele namiji mai tsananin kamanni da ita. Dan tsayin mahaifinsa kawai ya ɗakko amma kamanni tako ina na Ummu-Hidaya ne. Hatta da idanunta irin na maguna da gashin kai mai yalwa bai bar komai ba. Sai da ta haihu da kusan awa uku zuwa huɗu sannan tace mu sanar da mutanen gida, dan Abbie baya nan yayi tafiya. Da alama kuma ta sanar da shi, dan zuwa dare sai gashi ya dawo gida. Hakama Mu'azz baya nan a lokacin, shima washe gari ya dawo. Faɗa miki yanda ahalin biyu dama duk mai alaƙa dasu ke farin ciki ba'a magana. Dan hatta fitinanniyar surukarta a wannan rana cikin farin ciki da walwala take. Kafin wani dogon lokaci labarin wannan haihuwa ya zagaye jama'arsu na nesa dana kusa. Dan danan fa shagali ya tashi, abinka da akwai kuɗi, tako ina facaka ake da su tamkar ba'a san ciwonsu ba. Ranar suna yaro yaci suna *_Muhammad Awwab”_*. Yanda akai wasa da kuɗi a wannan shagalin suna al'amarin har ba'a magana. Sai dai abinda zai baki mamaki duk wani motsi Ummu-Hidaya na kaffa-kaffa da ɗanta ne. Daga ni sai Mamana ta yarda mu ɗauke sa. Sai ko Abbienta da Mu'azz. Sai surukanta Adams da mahaifiyar Mu'azz. Bayan bikin suna ya tashi kulawa da Awwab ya dawo kaina. Sai kuma ita Ummu-Hidaya ɗin idan tana gida. Dan tana gyagijewa ta koma harkar kasuwancinta. Kafin Awwab ya cika shekara biyu sun sake buɗe sabon kamfani na yin lass da atamfa da yadika. Sun kuma saka resunansu a jihohi ukku na kudancin ƙasar bayan Lagos.       Muhammad Awwab yaro mai masifar wayon tsiya. Ga ƙyau da shiga ran mutane Masha ALLAH. Sai dai miskilancin tsiya. Baya yarda da kowa sai ni sai Ummien sa sai ko kakansa Abbie da Abdul-wahab. Hatta da mahaifinsa ƙiwa yake masa. Yaro ne mai zafin naman tsiya, dan haka ɓarna sam bata masa wahala. Yayi kuma ya cisgune fuska tamkar bai aikata ba. Yana da shekara huɗu aka sakashi a makaranta, a lokacin ne kuma aka sake kawo mana wata mai aikin, dan acewarta ni ba mai aiki bace ƙanwarta ce. Har kuka nayi kuwa da jin wannan furuci nata, dan haka na ƙara ƙaimi wajen kula da Awwab fiye da komai a gidan. Shekarar sabuwar mai aikin nan ɗaya a gidan itama ta aurar da ita ga drivernta. Shima mutumin kirki ne dan baida hayaniya, ƙani ne ga kai bayin bulawoyi a gidan shima. Shekararsu guda suma ALLAH ya azurtasu da samun haihuwa yaro. Lokacin Awwab nada shekara biyar cur a duniya. Yaronsu yaci suna Hayatu. Tunda aka haifi Hayatu Awwab ya ɗauki son duniya ya ɗora masa. Koda yaushe yana nanne da jinjirin nan. Makaranta ma da ƙyar ake samu ya tafi, yata fitina kenan sai da Hayatu. Tun abin na bamu mamaki har ya koma bamu dariya da birgemu. Shaƙuwar Awwab da Hayatu yasa shima rainonsa ya dawo hannuna dan har lokacin ni ko ɓatan wata ban taɓa yi ba. Hakama Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Tama maida hankalinta akan kasuwancinta sai mijinta da shima dai harkokin kasuwancin da suke yi taren yasa ba wani zama yake ba sosai. Dan haka har lokacin Ummu-Hidaya dai na a gidansu ne tare da mahaifinta da bai taɓa ko kwatanta sake yin aure ba. Zuwa yanzu ma shi ya ajiye komai na harkoki ya damƙa a hannun ɗiyar tasa. Yini yake damu a gida da Awwab da Hayatu. Sai idan Adams da ayanzu ake kira Baba prof.. a gidan yazo sunsha hirarsu ko sun fita wata sabgar. Awwab nada shekara bakwai cikin ta takwas Ummu-Hidaya ta sake samun ciki, abin mamaki nima sai ga ciki a jikina. Musalta miki irin farin cikin da muka tsinta kammu a ciki ma ɓata lokaci ne. Mun cigaba da rainon ciki a tare har zuwa watan haihuwa. Itace ta fara haifo ɗanta namiji mai kama da Mu'azz da a yanzu Awwab ke kira Paah matuƙa. Dan tamkar yayi kaki ya ajiye shi kuma. Idanun Ummu-Hidaya kawai jaririn nan ya ɗakko shi kuma. Ranar suna anyi shagali sosai, yaro yaci suna Fahad. Washe garin sunan Fahad nima na haihu mace. Sosai Ummu-Hidaya ta nuna farin cikinta dana duk wanda yake gidan. Ranar suna yarinya taci Ummu-Hidaya. Wannan abu yama Ummu-Hidaya daɗi, dan haka ta ɗauki son duniya ta ɗorama yarinya. Saboda sunata aka sakaya ake kiranta da Falak. Bayan sunan Falak suka tilasta Abdul-wahab ajiye aikinsa. Acewarsu shi yanzu uba ne. Alkairi suka masa mai yawan gaske da zai iya kafa kasuwanci mai ƙarfi, amma duk da haka ya roƙa Abbie akan shi dai zai cigaba da tuƙashi koda zai koma wani kasuwancin ne. Hakan kuwa akayi, duk da ma yanzu shi Abbie ba wani fita yake ba sai idan ta kama dole. Kusan rainon Falak da Fahad ya tashi ne a hannun Ummie da su Awwab, sai da ya shiga primary 5 sannan ya sakarma su Hayatu. A shekarar da Awwab ya shiga jss 2 a secondary ranar wata alhamis Abbie da Abdul-wahab sukai accident a hanyarsu ta zuwa Katsina daga Kaduna duba sabon companyn da Abbie ɗin ke ginawa na sarrafa karfe. Jirgi zasu bi sai aka tashi da hazo, dan daga nan Lagos ta jirgi suka je Kadunar. Mun shiga matsanancin tashin hankali a wannan rana da bazai taɓa musaltuwa ba. A daren ranar ALLAH ya amshi rayuwar Abdul-wahab yayinda Abbie ke cikin mawuyacin hali. Anso yima Abdul-wahab sutura anan Lagos sai dai bai yiwuba, dan yan uwansa tun daga kano sukaje can Kadunar suka ɗaukesa, shi kuma Abbie aka wuto da shi nan Lagos. Ina son tafiya Kano hakan ya gagara, dan ban san irin tarbar da ƴan uwansa zasu min ba saboda basa son auren tun fil azal. Shiyyasama bai taɓa kaini garinsu ba. Ina dai jin sunan a bakinsa. Sai matarsa da mukan ma juna aike idan zai je ko zai dawo. Sai bayan sati ɗaya da rasuwar bisa tirsasawar mahaifiyata muka shirya muka je. Da ƙyar muka iya gano garin Gwarzo. Hakan yasa muka isa a wahalce. Sai dai me duk da azabar tafiya da mukaci bamu sami tarba daga ahalin Abdul-wahab ba. Sai ma kaca-kaca da sukai mana, tare da tabbatar min su basu san Abdul-wahab nada wata mata ba bayan matarsa da suke tare anan gida da ƴaƴansa uku. Dan haka naje can na nemawa ɗiyata ubanta su bazasu karɓa ba tunda tun farko sun tabbatar min basa buƙatata a cikinsu amma na nace sai da na auri musu yaronsu.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ........Raina yayi matuƙar ɓaci, hakama na mahaifiyata. Dan haka a daren muka baro gwarzon rai ɓace, har ƙaddara ta samu mahaifiyata aka faɗi da ita a mashin. Ciwon da taji ne ya zama sanadin ajalinta. Dan mun dawo Lagos da kusan kwana tara ALLAH yay mata rasuwa ashe ciwo ya shigeta ba'a sani ba. Wannan al'amari ya sani yin alƙawarin tattara dangin Abdul-wahab na watsar, na cigaba da takaba ta. Ga tashin hankalin Ummie akan ciwon Abbie. Duk da nawa tashin hankalin nima sai na danne na shiga bata kulawa da shawarwari. Watan Abbie kusan uku a asibiti yana jiyya jikinsa yaƙi daɗi, a wani daren lahadi yay ganawar sirri da ƴarsa ɗaya tilo da lauyiyinsa da Baba prof.. sai Awwab dake da shekaru goma sha uku a duniya. Wannan zama da su kaɗai suka san mi suka tattauna sai ALLAH kuma shine zama na ƙarshe. A washe gari Abbie shima yace ga garinku nan. Tashin hankali da ba'a saka masa rana kenan. Dan baki labarin yanda Ummu-Hidaya da Baba prof... Suka kasance a wannan rana ba'a magana. Awwab kam kulle kansa yay a ɗaki tsahon kwana uku. Duk da yarone ƙarami dan shekaru sha uku fa amma a kallo ɗaya zaka san mutuwar nan ta bugesa. Saboda akwai shaƙuwar mai ƙarfi tsakaninsa da Kakan nasa, sannan yarone da ALLAH ya bama wayo sosai da nutsuwa..         Rasuwar Abbie ya fara canja al'amurra Ummie. Office ma ta daina fita kusan wata guda. Sai dai tayi zaune shiru tana kallon yaranta kawai Awwab da Fahad. Sam idanunta basa ƙafewa da zubar hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci ta rame sosai tai duhu. Tun kowa na ɗaukar al'amarinta a matsayin damuwar rashin mahaifi saboda shaƙuwarsu har muka fara fahimtar akwai matsala. Ƙawarta data zama likita a yanzu Hajiya Lawusa (Hajiya ƙarama) naje na sanar mawa. Dan bazan iya tunkarar Abban su Awwab ba ko Baba prof.. itace ta fara tabbatar mana da Ummie na cikin halin depression ne. Kowa ya tausaya mata matuƙa, yayinda Baba prof.. da Mijinta (Paah) suka maido hankalinsu kan bata kulawa sosai. Muma ba'a barmu a baya ba, kowa tattalinta da tattalin lafiyarta yake. Sai dai me al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta koma babba. Dan daga depression sai muka tsinci baiwar ALLAH a halin hauka tuburan. Gaba ɗaya komai ya ƙwace mata. Tun ana ɓoyema yaranta musamman Awwab har ya fahimci halin da take a ciki. Tuni ya tattara karatunsa ya ajiye, ya maida hankalinsa gaba ɗaya gareta  duk da ƙarancin shekarunsa shike mata komai hatta da bata abinci da tsaftar muhalinta. Sai ya zama bata aminta da kowa ma sai shi kawai. Babu kalar likitocin da basu ganta ba amma da an fara ɗorata akan magani sauƙi ya fara samuwa sai kuma abu ya rikice. Sunsha bin yawon ƙasashe daban-daban akan matsalarta. Amma kamar dai baya. Da lafiya ta samu sai kuma jiki ya sake rikicewa.        Wani bawan ALLAH ne ya bada shawarar gwada mata maganin Islamic da namu na gargajiya, dan acewarsa babu wani ciwon damuwa manyan aljanu ne ke damunta, basuyi jayayya ba kuwa suka sa aka fara kawo musu masana akan hakan. Kamar dai yanda kika sani, magani dace ne, kowa nata gwada tashi sa'ar, sai dai tsahon lokaci ba'a dace ba. Amma dai ana ganin ɗan sauƙi a wasu lokutan. Gaba ɗaya ragamar kula da Ummie a hannun Awwab take, dan tun bai iya wasu abubuwan ba har ya iya. Hatta da kitso zama yake yay mata kiga tamkar mace tayi mata shi. Sai dai me yana da shekara goma sha bakwai komai ya fara sassautawa. A hankali ya fara ja baya da al'amuran mahaifiyar tasa. Takai ma idan yaje gareta sai ta hausa da duka da jifa har saita jimasa ciwo. Idan ya matsama kansa da damuwa sai shi kuma ya hau ciwon kai koya yanke jiki ya faɗi babu rai. Tun kowa na ɗaukar abin wasa dai har ta tabbatar zamansu waje ɗaya bazai yuwuba. Sosai hankalinmu ya tashi da wannan al'amari nasu, musamman ma ni da sukafi shaƙuwa da ni.      Canjawar al'amuran ya saka mijina na yanzu bama Awwab shawarar komawa makaranta ya cigaba da karatunsa. Amma sai ya nuna mana shi babu inda zaije. Ya haƙura da komai na rayuwa zai cigaba da kula da Ummiensa. Munta lallashinsa harda Yayar Mahaifinsa Hajiya Nafisa. (Hajiya Mammah). Kunyarmu da yake ji da addu'ar da muka duƙufa a kansa ta sanya ya amince zai koma. Dan haka da kansa ma yayma Baba prof.. da mahaifinsa maganar komawa makarantar. Sun nuna farin cikinsu suma, a take kuma suka shiga suka fita ya zana ssce ɗinsa. Cikin amincin UBANGIJI aka dace ya samu result mai ƙyau. Awwab ya shiga jami'a, kuma har lokacin yana nacin taimakon mahaifiyarsa amma dai babu daɗi dan wahala kawai yake sha. Yayinda Fahad ƙaninsa da shima a lokacin ya ke gab da kammala secondary. Hakama Hayatu suke ƙarƙashin kulawarsa. A farkon fara karatun Awwab ya ɗan fara kula da Companys ɗin mahaifiyarsa da ke neman durƙushewa duk da mahaifinsa tsaye yake akan komai, sai dai aikin ya masa yawa matuƙa dole sai da Awwab ɗin ya fara taimaka masa abubuwan suka fara dai-daita da dawowa fiye ma da yanda ya kamata. Dan shima UBANGIJI ya saka nasibi a hannunsa komai ya taɓa sai ya zama kuɗi. Yanda al'amuran nasa ke haɓaka sai ma ya fara danne na mahaifiyarsa. A haka ya kammala jami'a, yayinda ƙaninsa da Hayatu suke can ƙasar turai suna nasu karatun. Anan ɓangaren kuma Falak na nata a gida Nigeria, dan yanda Paah ya tsaya akan karatunsu itama bai banbanta da ita ba. A hankali ragamar kasuwancin ya koma hannun Awwab, yayinda yake kuma cigaba da karatunsa. Cikin amincin UBANGIJI a wannan lokaci kuma sai aka dace ta hanyar wani bawan ALLAH daga ƙasar Togo Ummie ta fara samun lafiya. Hakama al'amarin Awwab ya fara dai'daita.. Alhamdullah komai ya dawo dai-dai, farin cikinmu da duk zuri'ar Baba prof.. ma haka. Dan samun lafiyar Ummie ba ƙaramin kwanciyar hankali ya kawoma kowa ba. A lokacinne Hayatu ya kammala karatunsa ya dawo gida Nigeria. Saura Fahad da zai ƙara shekara ɗaya. Sai dai yana zuwa hutu musamman ma yanzu da Ummie ta samu sauƙi. Wannan gidan da kike gani itace da kanta ta fara ginashi a lokacin data samu lafiya. Acewarta tana fatan haɗa kan iyalinta waje guda idan su Awwab sunyi aure duk nan zasu zauna da matansu. Muma ta ware mana sashenmu tana mai tabbatar mana mune zuri'arta na ɓangaren mahaifa. Jin daɗin samun lafiyarta yasa Awwab sake maida hankakinsa akan harkar kasuwancin sosai. Yayinda itama take ƙara masa ƙarfin gwiwa. Sai dai me, ana murna ɓarawo ya tafi ashe yana laɓe a bakin ƙofa. Dan kuwa a wani dare labari ya koma baya. Jikin Ummie ya sake hargitsewar da yafi na baya muni da tashin hankali. A wannan lokacin ma dai Awwab sake tattara komai da komai yayi ya dawo da gaba ɗaya hankalinsa da ƙarfinsa akan mahaifiyarsa. Anyi-anyi ya koma kan harkokinsa yayi biris da kowa da komai. Bashi da aiki sai addu'oi da karatun Alqur'ani ga mahaifiyarsa. Da farko lafiya lau yake mata komai, sai dai zuwa wani lokaci matsalar baya ta sake dawowa ta rashin jituwa a tsakaninsu. Ya matuƙar tada hankalinsa akan hakan amma an rasa mafita. Manyan likitocin babu irin waɗanda ba'a gani, hakama masu maganin gargajiya dana Islamic duk inda aka jisu sai an kawasu.  Shima na ƙasar Togon anje nemansa aka samu babu shi, wai dama zuwaune a wajen ba'a san takamaimai ɗan wane yanki bane ba. Shekara guda ana cikin wannan zaune tsaye aka bama Paah shawarar yin aure. Amma yaƙi firr sai da aka tsaya a kansa sannan da ƙyar ya amince. Sai dai kuma babu wacce zai aura kamar yanda ya faɗa. Yawan kulawa da Hajiya Lawusa (Hajiya Ƙarama) ke bama Ummie yasa Baba prof.. bada shawarar aurenta. Dan itama a lokacin mijinta ya rasu tanada ƴa ƙarama wadda ita kaɗai ta haifa.         Sosai akasha fama kafin Hajiya ƙarama ta amince. Sai dai duk abinda ake Awwab bai sani ba sai daga baya. Sosai ya nuna ɓacin ransa da kishin mahaifiyarsa. Hakanne dalilin tada wannan ginin gidan ya cigaba da yinsa. Abinka da maganar kuɗi, cikin abinda baifi watanni uku ba komai an kammala. Shine ya dawo da mahaifiyarsa nan acewarsa ya bama Paah spiece da matar tasa su ƙarata, duk kuwa da can ɗin ma gidan mallakin Ummie ne. Dan gidan da mahaifinta ya gina da guminsa ya kuma rayu a cikinsa. Hakan yayima Paah zafi, dan Awwab ya tattara kowansu ya watsar, baya shiga sabgar Hajiya ƙarama duk da kuwa a baya kowa yasan aminiyar mahaifiyarsa ce, harma da mahaifin nasa ya tattarashi ya ajiyesa gefe.      A ƙalla mun kusa shekara guda a gidan nan da dawowa muketa ɗawainiya da Ummie, dan Awwab dai ya ajiye zancen kasuwanci gaba ɗaya sai kula da mahaifiyarsa. Kullum cikin jimasa ciwo take amma hakan baya hanashi zuwa gareta. Baba prof.. ne akoda yaushe baya gajiya da kawo masu magani, zuwan wani da ga Niger ya bada shawarar Awwab ya rage zaman gidan, dan in har suna a muhalli guda da mahaifiyarsa to lallai lafiyarta zatayi wahalar samuwa. Dan an riga an saka rashin jituwa a tsakaninsu. A samar da masu kula da ita har ALLAH ya bata lafiya. Sam Awwab yaƙi aminta da wannan shawara. Kowa ya buga sai yace babu inda zaije. Hatta da mahaifinsa da basa jituwa a yanzu sai da yazo yana bashi haƙuri da lallashinsa amma ina firr yaƙi amincewa. Mu kammu duk yanda yake girmamamu da jin kunyarmu yaƙi sauraren mu. Hakama Baba prof da kakarsa ta wajen uba matar Baba prof... Ɗin. Ana cikin haka ɗan uwansa Fahad ya dawo ya kammala karatun, ana murnar dawowarsa sai kuma murna ta koma ciki. Dan kuwa sam babu jituwa tsakaninsa da Awwab. Sosai suke nunama juna tsana. Zama inuwa ɗaya ya gagaresu. Akwai randa babu wanda yasan abinda ya haɗosu kawai Awwab ya kama zanesa. Da ƙyar aka amshi yaron a hannunsa sai da ya kwanta asibiti kuwa saboda jigata. Yana samun sauƙi ko hanyar gidan nan bai dawo ba ya tattara inasa inasa ya koma inda ya fito. Daga ranar bai sake leƙo ƙasar nan ba har yanzu. Shima kuma Awwab ɗin bana jin ya sake waiwayar inda yake. Sai su Baba prof.. da Paah.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ....Abinda ya fara dai-daita tsakanin Awwab da Hajiya ƙarama kulawar da take bama Ummie. Wanda dama tun kan ta auri Paah tanayin hakan, shima kuma Awwab ɗin ya sani, shi dai auren ne yake ganin kamar akwai cin amanar mahaifiyarsa sai kuma kishi da yake tayata. Amma daga baya daya fahimci Hajiya ƙaramar bata canja daga duk abinda takema ummien ba sai ya sakko. Wannan dalili na shiryawarsu ya saka Hajiya Ƙarama da Paah dawowa gidan nan. Basufi watanni uku ba Hajiya Nafisa da suke kira (Hajiya Mammah) a yanzu yayar Paah da akai aurenta bayan haihuwar Awwab dan ta jima batai aure ba mijinta suka samu saɓani. A Niger take auren, koda tazo sai Ba prof.. yace bazata zauna masa gida ba, dan a yanda muke jin labari fitinarta ta hanata zama lafiya da mutane kamar yanda ta hanata aure da farko, ba kuma a wannan karon bane ta fara tahowa gida yaji, sai dai na wannan karon yayi tsamari sosai dan harda dukanta mijin yayi. Koda Baba prof.. ya bibiyi al'amarin sai ya gano itace bata da gaskiya, shine ya hanata zaman gidansa. Kakarsu Awwab ɗin ce tace ta dawo nan gidan ta zauna. Itama da farko Awwab yaso borema zamanta, sai dai bamusan yaya akayi ba kuma daga baya yayi shiru. Dawowarta gidan nan komai ya fara canjawa. Ta maidani sashen masu aiki ni da iyayen Hayatu wai matsayin data sammu da shi kenan. Bayan hakan bata sammu a cikin danginsu kona Ummie ba. Ba muji komai ba muka koma. Sai dai muna ji muna gani kulawa da Ummie ya fara gagararmu, an kawo sabbin masu aiki, tare da saka Awwab komawa kan kasuwancinsa. Yaranta biyu ƴammata sun baro Niger sun dawo nan suma. Gasu basu da tarbiyya sam, basa shakkar taka kowa da wulaƙanta kowa. Gasu malalata basu iya komai ba. Dan dalilin zaman nasu yasa Awwab saka a samo masu aiki ganin suna neman ƙazanta gidan. Hajiya Mammah bata wuce wata biyar a gidan ba ALLAH yay ma mahaifiyar Hayatu rasuwa, sosai na shiga kiɗimuwa hakama mahaifinsa da shi kansa Hayatun. Shima Awwab rasuwar ta girgizashi sosai. A dalilin wannan zaman gaisuwa Alhaji Abdullahi ƙanin Paah ya dawo gidan nan da zama shi da iyalinsa, matarsa ɗaya da yara biyu Malika da Muhsin. Dan koda aka gama komai sai suka ƙi komawa nasu gidan suma. Abin nan ya bani mamaki ya kuma ɗauremin kai, sai dai banda tacewa. Ashe basu kaɗai bane, sai ga mahaifiyarsu itama (Kakar su Awwab ɗin matar Baba prof..) wai itama ta dawo nan saboda sun samu saɓani da Baba prof ɗin akan ƙin komawar Hajiya Mammah gidan mijinta. Shikenan duk sun dawo, Baba prof.. da autarta Mashi'a ne kawai babu, dan ita ba'a Nigeria take aure ba. Sai dai duk ƙarshen shekara tana zuwa bikin ƙara shekara na Ummie da Paah ke shiryawa.           Da farko su dukansu kulawa suke bama Ummie. Dan ko sashenta kaje sai ka san ita ɗin ƴar gatan dangi ce. Komai tsaff kamar ba wadda ke'a halin ciwo ba. Idan ba abin ne ya motsa ba ma bazaka taɓa cewa ga lalurar dake damun nata ba. Sosai Awwab ya samu nutsuwa a ɗan tsakanin. Hankalinsa ya kwanta har wata ƙiba yayi ya ƙara haske. Mu kammamu mun samu nutsuwa. Dan a lokacinne akai auren Hayatu da Falak ɗina. Bayan bikin shima Awwab ya bamu shawarar yin aure ni da mahaifin Hayatun. Da farko munso turjewa, amma suka dage shi da Hayatu dole muka amince. Watanni biyu zuwa uku tsakani kakarsu Awwab ta kwanta jiyya. Bata wani jima ba ALLAH yay mata rasuwa a ƙasar Egypt Cairo. Rasuwar ta girgiza kowa na family ɗin, musamman ma Baba prof.. da sai ya baka tausayi. Bayan gama jimami komai ya koma normal. ALLAH ya cigaba da riƙo da hannayen Awwab komai ya taɓa na kasuwanci sai yayi albarka. A cikin abinda bai wuce shekara ɗaya ba ya sake zama wani mahaukacin mai arziƙi da sunansa ke yawo tako ina ama duniya ba ƙasarsa kawai ba. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai ƙarancin shekarunsa da mutane ke gani amma ya tara irin wannan dukiya. Sannan mahaifinsa ba wani shahararren mai arziki bane balle ace ya gada ne. Sanda kakansa da mahaifiyarsa sukai nasu tashen basu ko kama ƙafar nashi arziƙin ba, ansan sunansu ne a iya wani yanki na garin Lagos, shiko duniya ce ke kallonsa a yanzu.         Tun Awwab na ƙarami dama ba mutum bane mai yawan magana sai idan shi yaso. Sai dai akwai tausayi da girmama duk wanda ya girme masa. Bai san wulaƙanta mutane ba koda kuwa ƴan aikine wannan tarbiyyar mahaifiyarsa ce da kakansa Abbie. Babu abinda ya damesa da sabgar kowa tashi kawai yake yi. Tun bayan rasuwar Abbie Baba prof.. ne kawai amininsa. Dan da shi kawai zakaga yana dogon hira. Sai ko mu idan yaso wani lokacin zakiga yazo har nan sashen ya zauna koda ba zaiyi magana ba. Dan alokacin da mahaifiyata ta tarasu zaki ɗauka yanada alaƙar zuminci mai ƙarfine da ita. Sosai ya nuna damuwarsa.         Tunda ayyuka da harkokinsa suka sha masa kai sai abubuwan gidan suka fara canjawa. Kulawar da ake bama Ummie ta fara ja baya. Ciwonta ya sake tsananta. Idan kinga ana kula da al'amarinta ya shigo gari ne, kuma a lokacin zakiga ciwonta ya tsananta. Duk yanda muka so mu kula da ita mu an hanamu, sashenta ma an mana iyaka da shi, duk randa kuma na shiga koda a sace ne al'amarin baya daɗi tsakanina da Hajiya Mammah. Hajiya ƙarama ce kawai ke nata ƙoƙarin bata taɓa fasawa ba dan hargagin Hajiya Mammah baya damunta. Sau biyu ana korarmu ni da Abban Hayatu saboda nacewa akan kulawa da Ummie, Awwab ne ke dawo damu. Dole muka tsaya matsayinmu na masu aiki dan mu zauna lafiya. Amma neman hanyar kuɓutar da Ummie da son gano bakin zaren kullum cikin yi muke. Masu aiki kullum cikin kawowa ake domin kulawa da Ummie, sai dai basa zarta wata ɗaya suke guduwa. Kowa ɗauka yake saboda ciwon Ummien suke guduwa. Ni kuma a raina inajin ba hakan bane ba akwai abinda ke korarsu.      “Wannan shine tarihin wannan gida a taƙaice Kandala. Dan na yanke miki abubuwa da yawa ne a cikinsa saboda wasu dalilai. Sannan ina fata ki fahimci wasu da kanki kuma”.     Hawayen da suka kasa tsaya min tun ɗazun na ƙara sharcewa. Cikin rawar murya data gama dasashewa na ce, “Amma mama miyyasa duk kika faɗa min wannan? Bayan baki sanni ba? Baki san koni muguwa bace, ko nama shigo gidan ne dan wata manufa”.     Ɗan murmushi tayi itama tana share hawayenta. Kafin ta kamo hannuna cikin nata. “Nasan ke ba muguwa bace Kandala. Duk da dai da farko haka kawai naji ƙaunarki a cikin zuciyata. Sai kuma wata fuska da nake gani akan fuskarki da bansan dalilin hakan ba. Da ga baya Hayatu ya sanar mana alaƙar dake tsakaninki da Awwab....”       Wani mugun zaro idanu nayi ina zabura gefe da fincike hannayena dake a cikin nata. Magana nake son yi amma na kasa. Sai lips ɗina dake rawa kawai. Murmushi ta saki tare da sake kamo hannun nawa ta ce, “Kwantar fa hankalinki Samraah. Kar kuma ki fasa aikin ladar da kika fara. Daga Ummie har Awwab da ɗan uwansa abin tausayi ne, suna buƙatar mai tallafama rayuwarsu. Mu kuma da muke da damar yin hakan bamu da wani ƙarfin iko. Dama fatan da muke masa yay aure ya samu mace ta gari da zata juya mulki da tsarin wannan gida ta inda kowa baiyi zato ba. Alhamdullah kuma muna fatan an samu, dan ko yanzu Awwab yaso nunama duniya matsayinki a gurinsa dole kowa ya girgiza, duk da ina tsoron kar su cutar dake dan mutanen nan hatsabiban kansu ne suma, dan ma taurin kan Awwab na rage musu tasiri a wasu lokuta. Sai dai duk abinka baka isa gane wanene na kirkin ba idan kika cire Baba prof..  Dan kowa da tasa illar da manufa da kike gani. Amma ke yarinya ce mai wayo da ilimin addini, dan har na zamani na fahimci kina da shi, ɓoyewa kawai kike kamar yadda kika ɓoye mana ainahin kanki da sunanki. Dan ALLAH ki daure ki taimaki waɗan nan bayin ALLAHn. Awwab mutumin kirki ne, yana iya ƙoƙarin sa wajen tsare mutuncin kansa ta hanyoyi da dama da samarin zamanin nan sukan kasa musamman idan kudaɗe na yawo a hannayensu. Kisa a ranki aikin lada kike yi sakamakon ki naga UBANGIJI. Kisa a ranki ceto zakiyi na Uwa da yaƴanta a cikin gobarar da bata da iyaka. Nasan bake zaki bama Ummie lafiya ba, amma zaki zama wani tsanin taimakawa mukai ga samuwar lafiyar tata. Dan in har kina a tare da ita duk maganin da mu kuma zamu nemo mun san zaki bata. Za ki kuma dinga mata addu'a har shi Awwab ɗin dan bana raba ɗayan biyu akwai sihiri mai ƙarfi shima a jikinsa. Fatanmu shima Fahad ya dawo gida su dai-daita da ɗan uwansa. Sannan waɗan nan mutanen da suka cika gidan nan kowa ya koma inda ya fito..”        Karo na farko na saki murmushi mai ciwo. Sai kuma na girgiza kaina. “Mama zan iya tsayawa dai akan samun lafiyar Ummie in sha ALLAHU da kuma batun dawowar ɗan uwansa gida. Amma shi babu abinda ya shafeni da shi ko halin da yake a ciki. Yaje can ya nemo mai taimakonsa. Ai shi ba yaro bane kuma yana cikin hankalinsa. Miyasa bazai dinga ma kansa addu'a ba. Ko sai neman dukiya kawai ya iya. Su kuma dake zaune Mama ai banga amfanin subar gidan ba yanzu, gara suna a cikinsa ta samu lafiya suma su koma kwasar kashinsu a cikin hannayensu. Ai ni baki sani ba. Aduk lokacin da maƙiyi ke tare dani bana son yay nesa da ni, na fison ya cigaba da rayuwa a jikina dan ya cigaba da kallon cigabana da nasarorina zuciyarsa na zafi. Koba komai shi zai ƙare rayuwarsa da lokacinsa ne wajen ganin ya cimmani. A bayyane shike da asara. Bai ƙaru da komai a duniya ba, ya je lahira ya tadda bai ajiye komai a taskarsa ba. Mi yafi wannan daɗi dan ALLAH”.      Murmushi Mama Balki tayi tana mai kai hannu ta shafa fuskata. Sai kuma tace, “ALLAH yayi miki albarka Samraah. Hakan ma Nagode. Amma dan ALLAH ayi haƙuri dai a haɗa da Alhaji Ƙarami. Yaron na cikin jarabawa mai ban tausayi. Karki damu da murɗaɗɗun halayensa abubuwane sukai masa yawa a cikin kai. Sannan da kike ganinsa nan mutum ne mai ibada da tarin ilimin addini. Kawai dai ana gusar masa da kulawa ne saboda kada yay ma kansa addu'ar. Amma a hakan ma azumin Litinin da Alhamis baya taɓa wucesa. Salla a cikin jam'i komi yake. Hayatu ya rantse min ya maya komai girman kasuwanci da abinda zai samu a cikinsa ko muhimmancinsa idan lokacin salla yayi sai ya barsa. Komai girman mai mulki ko wani muƙami ko dukiya dan Awwab na zaman meeting dasu baya hana da an kira salla ya miƙe ya barsu yaje yayi sallarsa. Sam bai haɗa bautama UBANGIJINSA da komai ba. Sadaka da taimakon marasa ƙarfi bazasu musaltu ba. Yasha yin ƙyautar gidajen zama da motoci batare da ya ko damu ba. Ɗaukar nauyin karatun yara da gyara makarantun addini da masallatai da asibitici ba'a magana. Idan zan ta lissafo miki alkairan Awwab zamu kwana nan, hatta samar da ruwa ga masu ƙarancinsa bai gaza ba, sai dai hakan bazai hana kuma ace yana da wasu halaye marasa ƙyau ba. Dan ɗan adam tara yake a komai na rayuwa bai cika goma ba. Ladanki naga UBANGIJIN talikai idan kinyi hakan”.        Ban iya cemata komai ba face duƙar da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma a hankali na furta, “Mama kinada hoton mijinki da ya rasu?”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Ɗan jimm Mama Balki tayi alamar tunani, kafin ta jinjina kanta. “Za'a samu hotonsa, amma sai dai a wajen Alhaji ƙarami. Dan lokacin da muka dawo rai a ɓace daga garinsu abinda danginsa sukai mana ya sakani a damuwa sosai harna kwanta ciwo. Bani da aiki sai kallon hotonsa ina kuka. Ga kuma halin da Ummie take ciki itama duk na haɗu na ƙara hargitsewa. Shine Ummie ta saka Alhaji Ƙarami ya tattare hotunan duka daga wajena, ni kuma ban sake amsa ba bayan komai ya lafa na samu nutsuwa. Amma ina ganin zan tambayesa yanzu, ko kuma na saka Hayatu ya amso”. Kai na jinjina mata cikin gamsuwa. ✨❤️✨ Yau kwanaki biyu kenan Mom bata saka Abba a idanunta ba. Dan tun jifar da tai masa a washe garin angwancinsa bai sake shiga inda take ba. Hakama amaryar tasa taƙi fitowa. A tunaninta dana yaƴanta harma da Ummanta ai tsoro ya hana amarya fitowa. Dan haka suka fara jin alfahari a ransu musamman ma Mom. Haka zata fito tsakar gida tana habaici da yada magana. Daga Gwaggo Gudidi har Halime da Gwaggon ce ta kwaɓeta babu mai kulata. Hakama Abba yayi watsin ruwan tsarki da ita shan shagalinsa kawai yake da amaryarsa. Gaba ɗaya ya ajiye shekarun girmansa gefe yana koyama Halime salo-salo da tabbatar mata ita ɗin ma fa mace ce. Itako banda raki da taɓara babu abinda take ɓarar masa. Gaba ɗaya ta susuce bawan ALLAH baya ganin komai da tuna kowa a gabansa sai ita. Hatta kasuwa a kwani biyun nan babu inda yake zuwa a gidan yake yini salla kawai ke fidda shi. Dole kuma akayi abinci Gwaggo Gudidi taje ta ɗiba musu tasa Bibaa na kumbure-kumbure takai musu har falo.      Yau dai zaman ɗaki ya ishi Halime. Tana ganin Abba ya fita sallar la'asar ta fito. Tsaff take cikin kwalliya, duk kwalliyar ba'a yi ta yanda ya kamata ba kaya data saka sun fiddo jikinta tsaff da yi mata ƙyau. Ga uban turare ta bulbula. Tun a gaban mirror ake gwada tafiyar da za'ayi, dan haka koda aka fito taku ake ɗaɗɗaya ana juya jiki su adole amare. Nan ko a cikin ɗaki raki takema Abba😂. Gwaggo Gudidi tai shirin fara gaidawa. Dan haka kai tsaye ɗakin da take ta shiga. Ta samu Gwaggon na haɗa kayan tafiya, dan magana ta gaskiya taɓarar da Abba ke zuba musu a gidan na kasa kimtsa bakinsa ya fara isarta itama. Bata ji na daren farko ba amma jiya da rana da yau gabannin asuba fes a kunnenta. Wannan taɓara da rashin sanin ciwon kai har ina. Gara dai ta gusa taɗan basu waje ai ita uwa ce. Maybe ma idan ta wuce ɗin waccan mahaukaciyar surukar tashi itama tayima kanta faɗa ta shirya ta tafi, dan har yanzu Umma na gidan ta fake da jiyyar Mom duk da itama fa abinda Abban keyi na damunta.        Cike da farin cikin ganin Halime Gwaggo ke faɗin, “Oyoyo oyoyo ɗiyata amarya”.    Kunya ce sosai ta kama Halime. Tai ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. A ran Gwaggo tace (ashe ke da sauranki Imamu bai ida kakkaɓe sauran taki kunyar ba). A fili kam sai ta riƙo hannun Halime cikin nata. Durƙusawa Halimen tayi ƙasa cike da girmamawa da kunya tana gaida Gwaggo. Sai Gwaggo taji hawaye sun ciko mata. Dan abune da bata taɓa gani ga Mom ba. Ko sanda tana amarya fingai-fingai tazo musu babu alamar kunya tattare da ita. Amma ita wannan jiba dai yarinya ƙarama amma Alhamdullah. Bayan sun gaisa Gwaggo taita jan Halime da ƴar hira. Wani ta amsa wani tayi murmushi kawai cikin kunya. Sunfi mintuna ashirin a haka suka fara jin hayaniya na tashi. A tare suka fita, dan muryar Umman Mom suke jiyowa. Cak bakin Mom dake ƙoƙarin yin magana ya maƙale, tun daga bakinta da hanci da idanu duk akan Halime. Kasa haƙuri tayi ta nufo inda suke da sauri. Gaban Halime ta tsaya sai kuma ta nunata da yatsa lips ɗinta na rawa. Amma mi a mamakin kowa sai gani sukai Halimen ta saki murmushi tare da rissinawa a girmame ta ce, “Yaya ina yini? Fatan duk kuna lahiya ke da yara? Ya gajiyar bik.....”        “Wacece ke? Miya dawo dake gidana dan ubanki?”. Mom ta katse Halime jikinta har ɓari yake. Murmushi Halime ta sake saki da ɗan bin Mom da kallo daga sama zuwa ƙasa. Sai kuma ta sake murmusawa da yin fari da ido tana wani watsa hannuwa gaba da baya cikin iyayi ta ce, “Halime mana nasan kin gane ai. Na dawo matsayin da kema kike a gidan, wato MATAR ABBA IMAM”.       Wani shegen tsalle Mom tayi gefe tamkar wadda taci karo da baƙin maciji. Yayinda Gwaggo Gudidi da abin ya bama dariya ta saki murmushi da gyara tsaiwar ta. Wani irin zaburowa Mom tayi kan Halime tana faɗin, “Shegiya munafuka algunguma ƙarya kike wlhy, mi mijina zaiyi da kucaka ƴar aiki irin ki. Dan ubanki faɗa min miya kawo ki?”.      Murmushi Halime ta saki, tare da ja baya kaɗan ta kaucewa cakumar da Mom ke ƙoƙarin kawo mata. Cike da fari da sake yarfar da hannu. Sai kuma ta ɗan duƙo cikin raɗa-raɗa ta furta, “Abinda mijin naki yake yi dake nima shi yake yi dani a cikin ɗaki” ta ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya cike da son sake bata haushi ta gittata ta wuce cikin takun da aka gama kowa a gaban mirror.     Gaba ɗaya Mom tai baya zata zube bakinta a hangane sai da Ummanta da itama tayi sumar tsaye ta tarota....     ❤️❤️❤️❤️❤️          Sosai abubuwan da naji a bakin Mama Balki suka sakani a cikin damuwa da ɗimuwa musamman akan mijinta daya rasu, dan gaba ɗaya suffofin data ambacesa dasu kama suke dana Babbanmu. Idan kuma ban manta ba Mom ta taɓa min gugar zana da cewar ai ubanmu har karuwa garesa a Lagos. Lallai tabbas ina buƙatar ganin hoton nan nashi. Damuwa tamun yawa sai dai ina matuƙar daurewa dan kada kowa ya gane min. Musamman Bahijja sarkin tambaya. Data ganni shiru tata nacin son jin mike damuna. Har cikin rai nima ina ƙaunar yarinyar, sai yanayinta ke ɗauke min kewar Auta. Kwanki biyun nan jikin Ummie da sauƙi sosai, dan na duƙufa addu'a. Yanzu hatta a ruwan wankanta da Mama Balki ke shiga a ɓoye tai mata safe da yamma sai nayi addu'a. Abincin ta da ruwan shanta duka. Dan na daina bata abinci gidan sai wanda nasan ni na girka ko Mama Balki. Damuwa da yawan tunani ya sani ɗan fitowa yau ina zagaya gidan ko zan rage nauyin zuciya da kewar ahalina, dan ina son kiran Yaya Musaddiq akan abinda naji amma na kwaɓi kaina har sai na tabbatar sannan. Wayar Bahijja ce a hannuna na gama magana da Yaya Musaddiq dake sanar min a wajen aikinsu sunce zasu turashi ƙasar waje ya ƙaro karatu. Farin cikin wannan magana ta sani cigaba da tsaiwa a wajen ina kallon kai kawon masu aiki maza dake sabgoginsu a garabar gidan.      A dai-dai nan naga ana ƙoƙarin buɗe ƙaton gate ɗin gidan. Ban kawo komai a raina ba na ɗauke kaina ina cigaba da game a wayar. Har motocin suka gama shigowa ban ɗago ba, dan na ɗauka normal baƙine tunda gidan baya rabo da shiga da fitar motoci. Sai da naji tsaiwar mota a inda nake sannan na ɗago, dan dama a jikin wata motar nake a rumfar ajiyesu. Haka kawai sai da naji ƙirjina ya motsa da ganin wanda banyi tsammani ba. Dan rabonsa da gidan kusan sati ɗaya kenan dama wasu kwanaki.        A hankali ya ziro ƙafafunsa dake cikin takalma boot brown masu laushi da ɗaukar idanu tamkar wani miski, gasu da ɗan tsaho ta sama dan har akan wandonsa sosai suka hau. Ko maƙiyi ya kallesa daga sama har ƙasa yasan yayi ƙyau matuƙa cikin shigar tasa. Ga mayen ƙamshin turarensa da tuni ya mamaye wajen kamar anyi ɓarinsa. Cike da matuƙar girmamawa duk masu aikin suka zube suna gaishesa, cikin lumshe idanu da sake dai-daita nutsuwarsa ya ɗaga musu hannayensa alamar amsawa. Kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Kuna lafiya?”.        Cike da jin daɗi da girmamawa duk suka amsa masa. Shima sai bai sake cewa komai ba ya juyo gareni. Kallon cikin ido mukaima juna, na kauda nawa da sauri ina ɗan tura baki. Ganin yanda duk yaransa suka samun ido musamman Hayatu ciki-ciki na ce “Ina yini”.     Bai amsa min ba, bai kuma daina kallona ba. Sai da ya mula dan kansa ya ɗaga ƙafafunsa zai bar wajen. A bazata naji shigar furucinsa cikin kunnena. “Karna sake ganinki a anan wajen”. Da sauri na ɗago, sai dai kafin na iya cewa wani abu yabar wajen yaran nasa na take masa baya. Sai Hayatu ne a hankali ya ce, “Good afternoon maa”. Harara na ɗago na watsa masa. Ya wuce yana murmushi.       Masu aiki dake durƙushe har yanzu kansu a ƙasa duk miƙewa sukayi tare da darewa suka bashi hanya. Shiko ya ratsasu cike da takun nan nasa na mazantaka da tsantsar kamala da nutsuwa. Hayatu da wanda ban san sunansa ba da ƙyamusashiyar baturiyar nan Juliet suka take masa baya. Baki na taɓe tare da raka bayansu da harara. Sai kuma naji duk tsaiwar ta gundireni. Haka na koma ciki ina ƙunƙuni.      Ban sake jin labarinsa ba dan ina sashenmu ina wanke kayan Ummie har yamma. Na kwaso kayan zanje na kai ciki aunty Zakiyya ta kirani a wayar Bahijja. Shine na ajiye na fito domin amsa wayar dan bana son su fahimci komai. Ina fara wayar ƙamshin turarensa ya mamaye wajen. Ɗagowa nai da sauri, sai na hangesa ɗan nesa da ni kaɗan ya nufi gate ɗayan mutumin nan daban san sunansa ba (TJ) biye da shi. Da alama masallaci zasu je dan sanye yake cikin blue jallabiya data fiddo da shi tamkar wani balaraben yankin sudani. Ɗauke idanuna nayi da sauri saboda hararar daya watsomin da ban san ta miye ba. Wayata na cigaba dayi da aunty Zakiyya ina dariya har sai da na kammala sannan na koma na ɗauki kayan Ummie na shiga ciki. Labarin data bani na ɗirkama Halime kayan mata dan ta rikita Abba yasa na kasa daina murmushi. Na samu ummie tana barci, dan yanzu abinda tafi yi kenan. Sai uban ƙamshin turarensa daya tabbatar min daya shigo sashen. Baki na taɓe na ajiye kayan na fita........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Wajen ƙarfe tara na fito nemawa Ummie abinci, dan nasan tana farkawa shi take fara nema. Ina shiga Hajiya Mammah dake kitchen ɗin ban san mi take yi ba ta aikeni sashensa. Cike da jin haushi na shigo ɗauke da abincin da Hajiya Mammah ɗin ta sani kawo masa. Ko sallamar ma ciki-ciki nayita. Tsaff katafaren falon nasa yake kamar ko yaushe, ga ƙamshin nan dana rasa daga ina yake samunsa dan ya bambanta da duk wani ƙamshi dana taɓa sani ko shaƙa a wajen mutane. Komai nasa dabbane dana saura. Sallama na sake yi a ƙuntace dai-dai isowata tsakkiyar falon sosai. Dan naga alamar basu ji ta farkon ba, inda dan shi kadai ne bazan damu ba. Dan koda yaji zai iya shareni wannan ƙaramin aikinsa ne, amma Hayatu bazaiyi hakan ba duk da takaicinsa da nake, shima kuma ƙwallon kansa ne.        Yanzun ma dai Hayatun ne ya ɗago da sauri alamar dai basu san da shigowar tawa ba da gaske. Cike da kulawa ya amsa min yana wani ɗan rissinar da kansa. Harararsa nayi kawai na ɗauke kai, dan wannan girmamawar da yake min na baƙanta min zuciya. Shiko gogan baima nuna alamar yasan da shigowar tawa ba. Gaba ɗaya idanunsa da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa na kan screen ɗin laptop ɗin cinyarsa da takardun hannunsa. Fuskar nan ciɗin-ciɗin babu alamar sassauci kamar wanda ma ke cikin ɓacin rai. Cikin i don't care na laɓe bakinna da dangwarar da tray ɗin saman Centre table ɗin daya ajiye ƙafafunsa masu tsananin tsafta da haske. Gashi cas babu wani girma sosai irin na maza. Dan wata macen ma sai ta fishi girman ƙafa. Da alama dungurarsa da tray ɗin ya ɗanyi ya saka shi ɗan ɗagowa a karo na farko ya ɗan kalleni. Sai kuma ya ɗauke idanun yuuu ya maida ga laptop ɗin. Nima nawa na ɗauke ina sake tsuke tawa fuskar na juya abina da nufin komawa inda na fito.          “Bani ruwa marasa sanyi”. Ya faɗa a dake babu alamar wasa a cikin silent voice ɗinsa. To amma tunda ba suna ya ambata ba bai shafen ba tunda bani kaɗai bace a falon ai. Cigaba da tafiyata nayi dai-dai da yunƙurawar Hayatu alamar zai bashi ruwan.     “Da ita nake”. Ya katse hanzarin Hayatun cikin gizagonsa. Duk da naji abinda yace ɗin ban kula ba. Ganin na cigaba da tafiyata cike da girmamawa Hayatu ya ce, “Aunt yace da ke yake fa”. Wani irin ɓacin rai ne naji ya ziyarcen. Dan haka na juyo a fusace ina watsama Hayatun mummunan kallo. “Wai malam banace maka ka daina kirana da wannan sunan ba. In ce dai kasan sunana Samraah ai”.       Murmushi kawai Hayatun yayi yana mai rissinar da kansa ƙasa. Sai kuma yace, “Kiyi haƙuri bazan iya faɗa bane. Dan kina da kima da matsayin fiye ma da hakan a wajena”.        Cikin gatse na ce, “Saboda a gida ɗaya aka haifemu?”.     “A'a saboda kina tare da auren boss”.      Duk da furucin nasa yay masaifar tsargani sai na dake. Cike da masifa na ce, “Kaima kasan wani auren boss ai, kar kuma ka sake jinginani da abinda ku ya shafa bani ba”.     Baki ya sake buɗewa zai yi magana, sai dai hakan bai yiwu ba, dan kamar a ɗan fusace silent voice ɗin boss ɗin nashi ta daki kumnuwanmu.          “Hayat! Kaje zan nemeka”.       Abinda yay niyar faɗar ya haɗiye. Batare da wata jayayya ba ya miƙe zumbur. Takardun jikinsa ya tattara ya kai gabansa. Hakan yasa na watsa musu harara su duka na cigaba da tafiyata. Sai dai kafin nakai ƙofar har Hayatu yazo ya wuceni, yana fita ya wani rufo ƙofar. Ban damu ba na kama handle ɗin nima zan buɗe na jita gam. Wani irin takaici ne ya ratsa zuciyata. Dan na fahimci mutanen nan neman maida min rayuwa suke wata sha katafi. Shiru nayi tsaye a wajen har kusan minti ɗaya. Sanin banda wata mafita saita wajensa ɗin ya sani nufar dining room ɗin sa. A cikin haɗaɗɗen freight ɗin dake a wajen na buɗe na ɗakko goran ruwa masu sanyi sosai saɓanin wanda yace marasa sanyi. Batare dana ɗora a saman tray ba ko ɗaukar kofi na fito. Har yanzu yana a yanda yake hankalinsa a laptop ɗin. Ruwan na dangwarar masa kawai ina tura baki. Ganin yaƙi nuna yasan dani ma a wajen ya sani faɗin, “Ga ruwan nan zan tafi”. Shiru bai kulani ba. Baima ko motsa ba. Takaici ya sake riƙemin maƙoshi, sai dai nasan fushi na bazai haifar min da komai ba sai ma sake tunzurashi. Sassauta muryata nayi a hankali na ce, “Please ka bani key na fita”.     Nan ma shiru bai da niyyar kulani, tuni idanuna sun fara cika da ƙwalla. Kusan minti ɗaya sannan ya magantu ciki-ciki.           “Ban hanaki shiga cikinsu ba?”.      Da farko ban fahimci abinda ya faɗa ɗin ba. Sai daga baya na fahimci akan ma'aikatan gidan nan ne maza da ɗazun a compaund. Dan haka cikin son manna masa rainin wayo na ɗan duƙo kansa kaɗan duk da yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri cikin dakewa na furta, “A matsayinka na wa?”.       Wani irin lumshe idanunsa dake yawo a fuskata yayi, yayinda ni kuma na yunƙura da nufin barin wajen kawai naji an bugi ƙafafuna. Gaba ɗayana na tafi, duk yanda nai ƙoƙarin son riƙe wani abu hakan bai yiwu ba sai da na faɗa kansa na zauna daram a cinyar tasa. Yanda na faɗo ɗin fuskokinmu suka kasance gab-gab da juna. Wani irin kallo yake min cikin tsakkiyar ido daya hanani iya koda motsi, kafin a hankali ya sake matso fuskar tasa gab da tawa. A take gaba ɗaya tsigar jikina ta mimmiƙe. Sai kawai na lumshe idanuna a hankali dan nagama sadaƙarwa akan nawa lips ɗin zai sauke nashin. Amma a maimakon hakan sai jin saukar yatsarsa nayi a saman lips ɗina ya shiga zagayawa a hankali, tare da sassanyar muryarsa cikin kunnena ya furta, “I'm not interested”.         Da sauri na buɗe idanun tare buge hannunsa dan har yanzu yana zagaya yatsarsa akan lips ɗin nawa. Bamma san sanda na watsa masa harara ba da ɗora hannayena akan ƙirjinsa na turashi baya. Ni kuma nai yunkurin tashi zumut. Amma tsabar mungunta sai ya sake taɗeni da ƙafar na sake komawa kan jikin nasa. Hannun na sake kaiwa jikin nasa zan turashi naji saukar nasa a bayana. Matsoni yay gaba ɗaya sai gani kwance a ƙirjinsa. A fusace na buɗe baki zanyi magana ya rufesa rufff da mitsitsin nashi. Waro idanun nawa waje nayi gaba ɗaya cikin tashin hankali da rikicewa, shima ya ɗan waro nasa kaɗan sai kuma ya kashe min ido ɗaya cike da salon iskanci. Ai ruff na sake rufe nawa idanun jikina na rawa.       Duk yanda naso ƙwace jikina hakan ya gagara, dan yayi masifar min irin riƙon da ban isa ƙwatar kan nawa ba. Da wani irin kalar salo yake sarrafa halshena cikin bakinsa. Duk mintsinin da nake masa babu alamar yana jina ma. Sai da yay mai isarsa dan ko kiran wayarsa da ake faman yi bai kula ba, gaba ɗaya jikina ya gama saki. Koda ya sakan sai kawai na duƙunƙune a jikin nasa ina sauke numfashi a gwagwgwame jikina sai rawa yake. Shima cikin furzar da nasa numfashi da shaƙaƙƙiyar murya har tana siezing a hankali ya furta, “Na miki abinda kike buƙatar ai. Sai yaushe za'a ɗaga ni”.      Bai ma gama rufe baki ba na miƙe zumbur. Batare dana kallesa ba na fisgi ɗan kwalina dake a jikinsa. Cikin haɗa hanya na nufi barin wajen, dan duk masifar da nake ji zan masa akan abinda ya faɗa min ɗin yanzu bazan iya furtawa ba.         “Ribbon”.    Ya faɗa ƙasa-ƙasa muryar tasa a shaƙe har yanzun. Kamar zan sharesa sai kuma dai na Juyo dan bana buƙatar barin komai nawa a sashen, ribbon ɗin nawa na hanga akan jikinsa. Sai da na runtse ido sannan na nufesa, hannu na kai zan ɗauka amma sai ya gyara zama ta yanda ribbon ɗin ta koma tsakkiyar ƙafafunsa. Kauda kaina nayi da sauri, tare da juyawa cikin sassarfa nabar wajen dan ni kaɗai nasan abinda idanuna suka gane min. A mamakina ina kaiwa ƙofa na murɗa handle ɗin sai gashi ta buɗe. Ƙoƙarin juyowa nayi na kallesa sai naga yana ajiye remote alamar shine ya buɗe ɗin kenan. Harara na watsa masa dayin ƙwafa cike da tsiwa na ce, “Kuma ALLAH ya isa na, sai na gayama Ummie”. Na ƙarasa fita da sauri har ina bugewa da ƙaton flowers base dake gefen ƙofar anyi decorretion da su.......✍️ _🤣Koba ALLAH ya isa ba. Muma to ALLAH ya isanmu jikinmu da aka hau🥱😜. Bara na ware kafin danginta su caskala ni🚴🚴🚴._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .....Tana fita ya runtse idanunsa da karfi, sai kuma ya fisgi gorar ruwan data ajiye masa ya ɓalle murfin tare da kafa bakinsa ya hau kwankwaɗa. Tass ya shanye ruwan yay jifa da robar tamkar itace tai masa abinda ya harmutsasan, sai kuma ya miƙe da hanzarinsa ya nufi side ɗin da bedroom ɗinsa yake yana famar haɗa hanya da furzar da huci a jajjere da taunar lips kamar zai huda su da haƙori.     ★Kai tsaye nima side ɗinmu na nufa maimakon komawa ƙarasa abincin Ummie. Ko kallon waɗanda ke a falo banyi ba na afka bedroom. Karo mukaci da Bahijja, dan haka ta riƙeni gam cikin kiɗima da ganin yanayina ta ke furta, “Aunty Kandala lafiya kuwa? Mike faruwa dake na gankai haka a birkice? Ko hajiya babba ce?.”      Hannunta na ture daga jikina batare dana iya magana ba. Cikin sassarfa na nufi bathroom ɗinmu dan bana fatan taji ƙamshin turarensa daba ɓoyayye ba a gidan a jikina. Ina shiga kai tsaye ƙarƙashin shower na shige na sakarma kaina ruwa kawai. Dan bani da wani zaɓin daya wuce hakan. A jajjere na dinga sauke ajiyar numfashi sai ga hawaye sharrr-sharrr kamar an buɗe fanfo....       💦💦💦💦   Tun fitowar Samraah da ga sashen Maash Hajiya Mammah dake laɓe ta bita da kallo. Duk da ƙamshin turarensa da yanda Samraahn ta fito ya sata farin ciki dan ta tabbatar akwai abinda ya faru koda ba wanda sukayi fata bane. Amma dai ba haka taso ba. Taso a yau komai da suka shirya ya faru kawai dan itafa tafi son idan ta saka abu a gaba kawai tayisa a wuce wajen. Har ta nufi barin wajen sai kuma ta fasa. Part ɗin Maash ɗin ta nufa, kanta tsaye ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama. Babu kowa a falon sai uban ƙamshinsa da sanyin ac. Sai television dake aiki sai dai babu ƙara sosai. Idanunta ne suka sauka akan tray ɗin abincinta. Trayn ta zubama ido na tsawon sakanni, sai kuma ta nufi inda yake. Tana gab da kaiwa ta tsaya cak, tabbacin jin motsi ya sata komawa da baya da sauri ta fita a sashen gaba ɗaya.        Sai kuma abinda tayi ɗin ya sakata dariya. Kaɗan ta dara tana nufar nata part ɗin.      Da kallo Hajiya ƙarama da komai ya faru akan idonta ta bita. Lips ɗinta ta cije da ƙarfi sai kuma ta saki ƙwafa. A zuciyarta tana ayyana lokaci fa yayi da zata amshi kayanta kafin wannan matar ta mata shigar sauri. Amma dolene ta bincika mi take ƙullawa akan Maash ɗin haka ne. Gaba tayi da yanzu bata da wannan lokacin asibiti ta nufa. Tanada aikin da zatayi na kuɗaɗe masu nauyin gaske. Dan haka tai ficewarta cike da takun kasaita irin na manyan mata gogaggun kuma ƴan boko...        Hajiya ƙarama ke kuma....🤔 (To Bara dai nayi hiru.🥱    ✨💫✨💫         A ƙofar gate Mansoor yaci karo da Mamy. Ɗauke kansa yay tamkar bai ganta ba zai wuce. Amma sai ta riƙo masa hannu cikin tashin hankali. “Mansoor mika aikata?”.      Kansa tsaye ya bata amsa da, “Sakinta nayi. Dan bazan iya koda zaman minti ɗaya da ita ba Mamy”.         “Baka da hankali Mansoor. Kasan muhimmancin auren nan a garemu baki ɗaya?”.      “Bana son na sani Mamy kiyi haƙuri”.    Daga haka ya zare hannunsa yay gaba abinsa yana ƙoƙarin shiga taxi ɗin da yazo. Dan dama bai sallamesa ba. Binsa kawai Mamy keyi da kallo komai ya ƙwace mata. Har motar tabar wajen bata iya taɓuka komai ba. Sai da motar su Hajiya Sakeena da zasu wuce asibiti ta fito sannan ta dawo firgigit. Ƙoƙarin isa ga motar tai tana tambayar mike faruwa. Dan taga Hajiya Sakeenar na kuka. Cikin masifa da hayayyaƙowa tamkar ba yayarta ba ta ce, “Koma miya faru ba huruminki bane ba. Kije ki zauna gida ki jirani. Dan wlhy in har yarinyata ta mutu kota nakasa sai ke da ɗanki kunyi dana sani” daga haka ta dakama driver tsawa akan su je. Nan ɗin ma sake sumar wucin gadi Mamy tayi, ba kuma ta dawo a hayyacinta ba har sai da sukai nisa.        Mansoor kam kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa. Ya ɗan jima tsaye a ƙofar gidan sai ga wata mata ta fito tana ƴar dariya. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Jikin gate ɗin ya matsa zaiyi knocking sai ya jiyo kamar hayaniya. Fasawa yay yayi ɗan jimm alamar saurare. Masifa wata mata keyi harda zagi, sai kuma wata siririyar murya na dariya cikin shaƙiyanci. Mamaki hakan ya basa, sai dai yaji nutsuwa a cikin muryoyin babu na Samraah. Amma kuma bai taɓa zuwa gidan nan yaji haka ba. Yana tsaye a wajen sai ga matar ɗazun ta dawo. Daurewa yay ya gaisheta ta amsa masa da ɗan kallon mamaki. Dan kuwa dai ta ganeshi sosai. Ai Mansoor ɗin Samraah ba ɓoyayye bane a layin nasu kodan aikin gidan tv da sukeyi tare.      “Ihmm niko kamar Mansoor?”. Cikin jin daɗin ta ganesa ya amsa mata da cewar shine. Tare da roƙonta ta turo masa Samraah dan ALLAH”.    Murmushi tayi tana ɗan girgiza kai. Sai kuma ta amsa masa da, “Ayya Mansoor ai Samraah bata nan tana Lagos ne ko Abuja naji ance. Amma dai kamar Lagos ɗin”.       Da mamaki yace, “Lagos? To yin me?”.     Ɗan jimm tayi alamar tunani. Sai kuma ta kaɗa kanta da faɗin, “Tare da mijinta mana. Amma dai ka nema Abban nasu ko ƴaƴanta Musaddiq mana”. Daga haka tayi shigewarta tabar Mansoor da sakakken baki....             ❤️💦❤️💦❤️     A ciki kam Mom ce ke fitina akan Halime bata isa yin girki a gidan ba yau. Dan tun randa ta tabbatar itace sukai uwar fitina da Abba har takai ya shashsheka mata maruka tare da gargaɗi mai ƙarfi akan iskancin kai hannu jikinsa da take sonyi a kwanakin nan, zata shaƙe masa kwala, ko zata cutar da shi. Acewarta gara ta murɗe kowa ya huta. Wannan mari ya girgiza Mom har ma da Ummanta. Yayinda Halime take ɗaki tana kwasar dariya. Bawai marin bane ya bata dariya itafa. Firgicewar Mom da ganinta matsayin matar mijinta ne kawai ke bata nishaɗi. Dan a take abubuwa data ɗan sani a gidan na ƙarfin Mom ya shiga dawo mata. Tana ji Abba zai shigo ta haɗiye dariyar ta.       Umma itace ta killafa Mom ta ƙarfi, ta kuma tabbatar mata idan fa bata kwantar da hankalinta ba har aurenta ya mutu to gaskiya kada tazo mata gida. Wannan hauka har ina aita tarota tana ƙwacewa kamar wata ƙaramar yarinya. Su nutsu su fuskanci abinda ya dace suyi amma ta zauna yin hauka akan wanda shi sam hankalinsa ma baya a kanta yanzu. Wannan faɗa ya sakata nutsuwa. Har Abba ya gama kwanakin angwanci a ɗakin Halime bata sake kula kowa ba. Da ya dawo ɗakinta kuma yaso nuna ɗaukar fishi da ita. Sai dai roƙon da Musaddiq yay masa ya sassauta abun. Dan haka ya haɗasu su duka gidan har Nabil dake makaranta yay musu nasiha tare da tabbatar musu da Halime itama yanzu ɗaya daga cikin family ɗinsu ce, sannan baya buƙatar damuwa daga kowa.      Abbas da Musaddiq da Nabil ne kawai sukai magana da amsar Halime. Amma Baby da Bibaa ko kallon uban ma basuyi ba. Watsar dasu Abba yayi, sai ma maganar bikin Baby daya tabbatar musu ya gama tsayar wa nan da wata biyu, tare da sanar musu alkairin daya samu Musaddiq dan nan da sati biyu shi kuma zai wuce ƙasar Chaina. Yaso ayi bikin Baby da Musaddiq ɗin, sai dai hakan bazai yiwu ba saboda komai na tafiyarsa ya gama kammala. Wannan magana itace ta hargitsa Mom matuƙa har ta danne mata al'amarin Halime a kwanaki biyun nan.        Ummanta ce ta bazama wajen teachers ɗin su. Shine jiya da dare aka kawo abinda zatai amfani da shi akan Musaddiq dan daƙile wannan batun tafiya. Yau kuma ake son yaci a cikin abinci. Da rana baya gida, dan haka ta gama shiryama girkin dare gashi ba itace da girkin ba. Sai kuma ga Halime ta shiga domin ɗorawa saboda kowa yasan ita ya kamata tayi girkin daren. Ga kuma Abba yay kiranta da sake tabbatar mata dan har ma ya aiko yaro da cefane. Shine Mom tace bata isa ba itace zatai girkin. A lokacin makwafciyarsu da sukai magana da Mansoor na gidan. Shine ta raba gardamar ta sake tabbatarma Mom cewar Halime dai ya kamata tayi girkin daren. Kawai sai Mom ta fara tura mata ashariya. Shine ta fito tana Murmushi yayinda Halime ke dariya. Dan ita al'amarin Mom ɗin yanzu dariya ma ya koma bata. Mace kamar mai mutsukku a cikin kai. Murhun gawayi makwafciyar tasu ta kawo ma Halime tunda dama abin girkin kawai take buƙata komai na ma'aikaci itama tana da shi. Harda ƙullin gawayi biyu... 💕🌟💕       Bluetooth ɗin dake cikin kunnensa ya zare yana mai sakin wani kalar lalataccen murmushi. Sai kuma ya sake maida fuskarsa ya tsuke tamkar bashi ba. Tamkar ba wanda ake jira ba ya shiga zare kayan jikinsa a nutse dan babu alamar wani gaggawa a tare da shi. Dogon wandon jikinsa kawai ya bari batare da ya cire ba ya nufi closet ɗinsa. Daga can kusurwar bango Ya danna wani maɓalli, a take adon wutsiyar wadrobe ɗin dake ta dai-dai kona ɗin ya shiga naɗe kansa. Zallar gilashi garai-garai da haskensa kesa a iya ganin komai dake a cikin wajen ya bayyana. Nan ɗin ma dai wani abu ya danna, a take gilashin yaja kansa ya shige cikin wadrobe ɗin. Zallar adon golden ya bayyana da bindigu har guda uku da aka manna a bangon wajen tamkar an zana sune. Hannunsa duk biyu ya tura a cikin aljihun wandon, tare da gyara tsaiwarsa ya zubama bindugun ido. Biyu ƙananu ne, ɗaya ƴar babba hakannan daka ganta kasan zatai haɗari da tsada. Cike da wani salon taƙadaranci ya cije lips ɗinsa tare da zare hannunsa ɗaya ya maida gashinsa daya sakko masa a fuska kaɗan saboda salon gyaran dayay masa ɗazun da yamma. Sauke hannun yay a hankali ya kai yatsarsa ɗaya saman bindigar farko, tamkar mai zana abu sannu-sannu ya dinga sakkoshi ƙasa har ya dire akan ta tsakkiya, nanma bai tsaya ba yay ƙasa har sai da yaje ta ƙarshe. Zagaya kan bindigar ya cigaba dayi da yatsar tasa kusan sakan biyu sai kuma ya sake maidashi sama ya ɗora akan ta tsakkiyar. Nan ma yaja kusan sakanni biyar ma tamkar mai nazari sai kuma ya laɓe baki cike da salon ɗage kafaɗu ya ciro bindigar alamar zuciyarsa tafi aminta da ɗaukar tata. Sauran mahaɗanta dake gefenta suma kowanne a mahallinsa ya cicciro harda bullet kusan biyar sannan ya maida komai a yanda yake ya fito. Cikin bedroom ɗin nasa ya dawo, ya zauna a katafaren bakin gadonsa ya haɗa bindigar tsaff cike da ƙwarewa ya ajiye, sai dai bai saka bullets ɗin ba ya jawo side drawer ɗinsa ta gado ya zuba su ciki. Bathroom ɗin ya nufa abinsa cike da takunsa na mazantaka da nutsuwa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......Ina kitchen ina ƙoƙarin haɗama Ummie madara kamar yanda na saba a kowanne dare yanzu saboda naga tana sonta sosai Hajiya Mammah ta shigo. Kamar ko yaushe tsaff take cikin kwalliya mai ɗaukar ido da ke nuna ita ɗin wacece. Sosai take matuƙar bani mamaki matar nan. Itafa dare baya hanata kwalliya kamar jikanyar ifiritai, musamman idan akace tana da baƙuwa da zata kwana a gidan. Gaisheta nai a ɗarare da ƙoƙarin kauda kai daga kallon ƙurillar da take bina da shi daga sama har ƙasa. Kadaran kadahan ta amsa min sai dai fuskarta a sake. Juice ta ɗauka ta ɗaura a samar tray tare da glass cup, sai ƙaramin bowl da aka yanka fruit yay ƙyau sosai musamman yanda kalolinsu suka fito a farin glass bowl ɗin kamar an zana, sai kuma wani haɗaɗɗen kula shima mai ƙyau duk ta ɗora, har zata ɗauka sai kuma ta dakata. Kallona tai tare da tukunyar da nake dafa madarar.          “Kandala mi kike dafawa anan?”.     Fuskata a ɗan cinkushe, na ce, “Hajiya madarar Ummie ce”.    Kanta ta jinjina tare da faɗin, “Okay Masha ALLAH. Ta kusa kammaluwa ne?”.         “A'a yanzu na ɗora ai babu jimawa”.      “Okay! To kinga zonan kimin wani aiki sai na jire miki. Awwab zaki miƙama wannan part ɗinsa. Azizat ya saka Paah ɗinsu kuma ya sakata aiki, Awwab kuma baya son jira zai iya fasa sha kuma nasan ba wani abu yaci ba”.     Ji nai kamar na fasa ihu, sai dai nasan ban isa cewa bazanyi ba. Amma a cikin raina na ɗan yi mamaki, to amma ina ruwana ba yayar babansa bace. Cikin haɗiye yawu da ƙyar na amsa tray ɗin, ɗauke juice ɗin tayi da glass cup ɗin tana faɗin, “Banda wannan nawane. Kiyi maza zan koma sama ne”.         “Okay maa”. Na amsa mata cike da jin haushi. Acan ƙasan raina kuwa jinake kamar na haɗiyi zuciyata na huta. Amma dai ba komai, dan nima kai fruit salad ɗin zai min amfani, dan dama ina son ganinsa. Dan akwai bashina a kansa, bazan taɓa barin maganar daya gasamin ɗazun da safe ba sai na maida murtani, idan ba hakaba zan iya kasa barci ma wlhy. Kamar koyaushe a nutsena nake tafiyata. Jikina da hijjab iya gwiwa mai hannu kamar kullum. Duk fa amatsayin ƴar aiki nake gidan kamar yanda shaiɗanin ya ƙalabamin akoda yaushe zaka sameni cikin tsaftata, dan inada ƙyanƙyami, ga son wanka kamar ƴar agwagwa. Komai a gidan free ne har gamu masu aiki, banbancin kawai komai zakayi kai da kanka ne masu gidan kuwa mune ke musu. A hankalin ƙamshin turaren da Ummie ta fesamin ɗazun har a cikin gashina ke tashi, sosai turaren ya kwanta min a zuciya. dan yana fidda wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa harma da kai daka saka. Na ɗakko ne zan saka mata ta fisge ta hau min feshi da shi a jikina tana dariya, bata kuwa barsa ba sai da nayi dabarar amshewa. Koba'a faɗa ba nasan an sayesa ne da kuɗaɗe masu nauyi. Murmushi na saki mai sanyi, dan yanda yake bama Ummien kulawa a gidan da kowanne nau'in abubuwan more rayuwa duk da lalurar dake tare da ita na ƙayatar dani. Sau kusan uku ina knocking amma babu alamar za'a buɗe min. “Ɗan wulaƙanci fitinanne mai girman kai”. Na faɗa a hankali ina murguɗa baki da hararar ƙofar. Cikin jin zafi na murɗa handle ɗin ƙofar na shiga falon. Kamar kullum babu yawaitar haske. Sai uban sanyin ac da mayataccen ƙamshinsa daya gama mamaye komai. Hatta kusa da mutum idan ya tsaya ko wani dalili yasa ya taɓaka koya zauna guri ya tashi ka zauna sai ka ɗeba mayen ƙamshin nan nashi. Narasa da wane shegen turare yake amfani haka. Koda yake ya wuce na tsafi. Na bama kaina amsa ina murguɗa baki. Ƙoƙarin ajiyewa nake a Centre table ɗin falon aka shigo da sallama bayan anyi knocking. Bakowa bane face Hayatu, dan haka na amsa sallamar tasa a zuciyata kawai batare dana kallesa ba na ƙarasa ajiye tray ɗin.        “Barka da dare Maa”.   Ya faɗa cikin girmamawa kamar yanda yake min yanzu musamman idan babu kowa a waje. Harara na ɗago na balla masa ina mai jan sirrin tsaki. Shiko yay ƙasa da kansa. Ƙafa na ɗaga zan bar wajen da sauri ya ce, “Dan ALLAH kiyi haƙuri. Ki kai masa bedroom inba hakaba bazai shasa anan ba. Dan muna uzirin fitane, Ummie kuma bata ƙaunar zamansa da yunwa duk yau babu abinda yaci kuma sai chocolate.”       Wata hararar na sake balla masa. Shiko ya sake marairaicewa da faɗin, “Dan ALLAH dan ƙaunar da kike ma Ummie”.            Idanuna na rumtse da ƙarfi. Kamar kar nayin sai kuma dai na ɗauka dan ni shaidace, duk randa Ummie ta cika fitina a gidan to dan gudan jinin nata ne. Sai dai kuma daya raɓeta babu sauran zaman lafiya musamman ace ya shiga ɗakin da take ko yazo kusa da ita sosai. Sai dai ya kasance a nesa da itane yanzu zata fa zuba masa ido kamar mai son tuna wani abu a kansa kosan sanin wanene shi har hotonsa haka take masa. Cikin ƴar fusatar da Hayatun ya sake saka min nai knocking ƙofar bedroom ɗin nasa da ƙaddara tasa zan masa shiga ta biyu. Nasan latsin rainin wayonsa. Zai ma iya kasancewa yana jina yay shiru, niko ina son komawa na kaima Ummie madararta tasha magani. Agadarance na murɗa ƙofar na shiga ina mai sake tsuke fuskasta da haɗa baƙar maganar dazan gasa masa da nake fatan ta hanashi barci. Wayam babu kowa a ɗakin, sai dai anan ɗin ma hasken akwai ƙaranci, sai dai yafi na falon dan anan ana iya ganin komai. Kayansa daya watsar a kan lallausan milk carpet ɗin dake a gaban gadon na ballama harara da taɓe baki. A bayyane na furta, “Ƙazami kawai sai iyayi da feleƙe, amma ba'a iya yima kai komai.” a saman bed side drawer na nufi ajiye tray ɗin, sai idona ya sauka akan bindiga. Sosai na waro idanu, jikina har tsuma yake wajen ajiye tray ɗin hannuna kaɗan ya rage ban zubar da shi ba na dai gyara masa zama ina ɗaukar bindigar. (Ta tabbata dai guy ɗin nan ɗan ta'addane. Yo anya ma ba ɗan fashi da makami bane? Kambu aiko yau zan tona asiri, zai ko tabbatar ya kawo ƴar jarida gidan nan) na ƙare zancen a zuciyata ina sakin ƙwafa a fili. Ƙofa na zabura zan nufa ina ƙoƙarin soke bindigar a cikin jikina. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar bathroom. Naji firgici, dan yanayina ma ya nuna hakan sakamakon a yanda na jiyo na kalla wajen. Ganin shine ɗaure da towel iya ƙugu zuwa gwiwa yana riƙe da ƙarami a hannunsa zai kai shi fuskarsa amma ya tsaya yana kallona nai saurin ɗauke idanun nawa tare da zaburar son nabar ɗakin kafin ya farga da abinda na ɗauka. Sai dai me ina isa jikin ƙofar naji ta bada ƙitt alamar rufewa, duk da kuwa a rufen take dama. Ban fasa kai hannuna jikin handle ɗin ba, na murɗa na murɗa amma ko gezau tabbacin dai an kulle. (To ta yaya?) Zuciyata ta tambaya, rashin amsa da makama ya sani juyowa, sai ko idanunsu suka sauka akan ƙaramin black & golden remote dake hannunsa alamar da shi ya kulle ƙofar. Dan yanda ya ɗauke kansa tamkar baiyi komai ba ya sake tabbatar min da hakan. A ɗan zamana gidan na fara haddace mugayen halayensa a cikin kaina. Dan babu ubanda yake ragamawa da wannan murɗaɗɗen halin nasa na rashin mutunci. Ko kallona bai sake yi ba ya nufi gaban mirror ɗinsa hankali kwance. Saurin kauda idona nayi daga kansa dan dama dai a gaba ɗaya cikin sakanni da baifi goma bane komai ya faru, ban kuma iya masa ko kallon sakan ɗaya cikakke ba saboda yanayin da yake ciki, dan ma babu yawaitar haske a ɗakin ne shiyyasa.        A bazata cikin dakewarsa da daƙilallen yanayi irin na mugayen muskilan mutane a silent voice ɗin nan nashi ya furta, “K idonki bazai daina gane-gane ba ko?”.    Sam da farko bammayi zaton shine yay maganar ba. Sai da nai ɗan jimmm sannan na fahimta. Baki na murguɗa batare dana kallesa ba cike da tsiwa nima na furta, “In dai masu mugun halin ta'addanci na a inda nake gane-gane ma yanzu ya fara ai. Kuma in kere na yawo zabo na yawo wataran za'a gamu. Adai juri zuwa rafi. Saboda wataran tulu zai fashe a tsakkiyar kasuwa. Dan in ma an binne wani abun wani bazai binnu ba. Musamman ma Samraah Abdul-wahab Gwarzo”.       Shiru bai tanka min ba. Ni kuma na kasa iya ɗaga ido na kallesa saboda a yanda yake samandagari guda babu riga ƙaton kawai. A bazata matuƙar bazata naji tsaiwar mutum a kaina daf, ai bamma san sanda na ɗago ba a harmutse. Ƙamshin turarensa ne yay mugun rige-rigen shiga min hanci saboda iskar razana dana shaƙa da ƙarfi. Kusancin namu yayi yawa dan haka nai matuƙar zabura baya ina ƙyaƙyƙyafta idanu uwa ya na namijin biranya. Hannu ya miƙomin alamar na bashi. Nasan bindigarsa yake nufi, amma sai na balla masa harara na ɗauke kaina. Dan ya kafeni da muggan idanunsan nan na maguna. Sai dai yanda nake a tsorace yasa a ankare nake karya shammaceni. Ina kuwa ganin ya motsa na sake zabura baya. Ganin kaina yayo na ɗage zan falla da gudu koda cikin bathroom ɗinsa ne tunda ya kulle nan mugun yasa ƙafa ya taɗoni, sai gani zube a saman gadonsa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Da wani kalar sauri da rawar jiki na motsa zan tashi, zuciyata na wani kalar masifaffen gudu a cikin ƙirjina tamkar zata fito ta baki ya hana hakan ta hanyar ɗora ƙafarsa ɗaya a saman gadon ɗaya a ƙasa ya ranƙwafo yay mun rumfa. Hakan ya saka kammu gwaruwa waje ɗaya saboda na riga na ɗago. Wani azabane ya ratsa min goshina, da sauri na koma tare da dafewa da hannayena duka biyun ina faɗin “Wayyo ALLAH mai kan rodi ya fasan kai na”. Nayi kusan minti ɗaya a haka raɗaɗi na ratsani dan da gaske naji zafi kafin na janye hannun ina ƙoƙarin hana hawayen da suka cika min ido zubowa, bindigar na ciro daga hijjab ɗin na nunasa da ita, cike da masifa na buɗe baki zanyi magana amma a mamakina sai naji bakin ya gagara motsawa, sai rawa lips ɗina kemun kar-kar da motsi a hankali. Dan wani irin masifar jinai ya cika min ko'ina. Hatta ɗakin jina nake a matse matuƙa a cikinsa. Idanuna na rumtse da ƙarfi ina sake wayancewa na maida hannuna saman goshin na dafe, ɗayan kuma dai na nunasa da bindigar. A cikin zuciyata nake jera masa ALLAH ya isa. Jin kamar ana ƙoƙarin saka min abu a jikin tsintsiyar hannuna ya sani saurin ƙoƙarin janye hannun. Bamma san sanda na sake zaburowar ba ganin ya saka min handcuffs. Hannun nai ƙoƙarin fisga shi kuma ya cire key ɗin daya kulle handcuffs ɗin dai-dai nan. Bindigar hannuna ce ta faɗi.         “Malam minene haka kayi?”.   Na faɗa cikin gigita da ruɗewa. Bai tanka min ba, sai ma ƙoƙarin sauke ƙafarsa yake yi, cikin ƙunar rai da rufewar ido na sake buɗe baki zan yi magana tare da kai ɗayan hannuna zan damƙoshi batare dana san mi nake shirin yi ba ya wani kalar juyowa. Farin yatsarsa mai ɗauke da dogon farin farce ƙal-ƙal masu sheƙi ya ɗaura saman pink ɗan ƙaramin lips ɗinsa. “Shiii!!!” ya faɗa yana wani waro min cat eyes ɗinsa masu girma da cikar gashi. A take tsigar jikina tai bala'in tashi. Bamma san sanda nai saurin kauda kaina ba bakin nawa na rufewa bamm batare dana iya furta ko a ba. Ga hannuna da nakai zan riƙosa na tsaye ƙyam, ban sauke ba ban kuma ƙarasa kaisa jikinsa ba, dan sai yanzu nama fahimci taɓargazar da naso yi...      Maash dake bin fuskarta da wani ɗan iskan kallo zuciyarsa na wani masifar hanƙoron mamakinta a cikin ƙirjinsa ya janye idanun ya saukesu akan hannunta. Sake tsuke fuskar yayi, a kausashe ya furta, “Idan wannan small hand ɗin ya sauka jikina You will regret it har wayewar garin yau”. Ya ƙare maganar yana kaɓar da hannun tare da ƙoƙarin ɗaukar bindigar nai saurin ɗaukewa kafin ya kai nasa hannun na tura cikin skirt ɗina.        “Humm” ya faɗa yana wani shanye girman idanunsa da jan sirrin tsaki da yay matukar zafata. Sake rumtse idanuna nayi ina mai sake tsuke fuskata nima, cikin nuna alamar ɓacin rai, batare dana buɗe idanuna ba cike da tsiwa na furta, “ALLAH ma ya tsari ɗiyar Abdul-wahab da taɓa trash body irin naka, jiki duk ta'addanci da jinin mutane ma. Sannan ma ni ba ƴar iska bace dazan taɓa jikin maza. Kuma wlhy ka tashi min a kai tun kafin kai na saka kai regretting ɗin yanzun nan terror kawai an saba bin na hotels”.      Ban gama rufe baki ba naji saukar yatsunsa a saman lips ɗina. Wata irin masifar azaba ce ta ratsani saboda yanda ya haɗesu ya matse a waje guda, tsabar iya mugunta da baƙin hali ya dinga murzawa. Kusan sakan talatin sannan ya daina murzawar tuni idanuna sun cika da ƙwalla. Yayinda ɗayan hannuna ya shiga kai masa duka akan ƙatoton damtsen hannunsa amma mugun ko gezau. A wata sabuwar bazatar da ruɗani da tashin hankali na sake jin saukar hannunsa a saman cikina. Ihu nake son ƙwalawa amma babu dama ya riƙe bakin. Da bala'i-bala'in ƙarfi na gimtse idanuna da ƙanƙame jikina saboda yanda ya damƙi bindigarsa dana tura a wajen tare da fatar shafaffen cikina. Ai da azabar ƙarfi na dunƙule hannuna na buga masa a damtsensa ina fisge kaina amma yaƙi sakin lips ɗin nawa saima sake matsesu yake. Ɗayan hannuna kuma dana dakesa da shi ya sake zuramin wata handcuffs ɗin itama ya ratayo jikin ƙarfen net ɗin da akai kwalliyar gadon da shi, dan ƙarfene a wajen. Fisge-fisge na farayi, amma ko'a jikinsa saima ya ɗakko salataf ya nane min bakin da shi bam. Tashi yay tsaye sosai akan ƙafafunsa, na fahimci hakan ne a dalilin jin iskar ac na ratsani dan rankwafowar da yay ɗazun a kaina koma jinta banayi sam. Idanuna a rumtse suke dan bazan iya kallonsa ba. Fisge-fisgen na cigaba da yi ina uhum-uhum! Na ƙoƙarin yin magana amma ko uhum banji yayi ba. Hakan ya sakani buɗe idanuna kadan, sai na hangosa can ya nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton closet ɗinsa ne saboda labulen da aka saka a wajen fari ne shara-shara kuma ƙofar wajen an yita da girma sosai. Hawaye naji suna ƙoƙarin sakko min, amma nayi ƙoƙarin hana hakan dan bazan taɓa yarda yaga gazawata ba. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito. Cikin ƙananun kaya baƙaƙe yana ƙoƙarin ɗora baƙar jacket milk mai ƙyalli a samansu. Ko kallon inda nake baiyi ba, ya ƙarasa gaban mirror ya fesa turare da ƙara kwantar da kwantaccen gashin fuskarsa dama nakan nasa da ya ɗaure waje guda. Boot takalman daya fiddo baƙaƙe masu ƙyau daga sama ya zauna bakin gadon ta kusa dani ya saka. Matsar da jikina nayi baya ina ƙunƙunin da ba'a ji tunda bakin a rufe yake. Sai da ya gama saka takalminsa batare da ya kallan ba ya miƙa hannu ya ɗauka tray ɗin dana shigo da shi, ƙaramin stool yaja gabansa ya ɗora, hankalinsa kwance ya fara kai fruit ɗin bakinsa a nutse tamkar baya so. Ɗauke idanuna nai daga kansa ina ƙwafar da ba'a ji sosai, amma nasan zai iya yajin shi. Sai dai mugun ko a jikinsa yama ƙi nuna yasan dani. Baifi cokali biyar yayi ba ya ture gefe, tissue ya ɗiba ya goge bakinsa yana miƙewa. Yanzun ma ko kallona baiyi ba ya nufi ƙofar fita ya buɗe ya fita duk da buge-bugen da nake uhhhum-uhhhum ɗin dai bai kulanin ba. Fitarsa da minti baifi biyu ba har na fara hawaye sai gashi an sake buɗe ƙofar. Shegen karen nan nasa ne ya shigo. Shi kuma biye da shi, ya tsaya daga bakin ƙofa idonsa akan karen cikin bada umari yay masa nuni da ni yana faɗin, “Ko yinƙurin cire abinda ke bakinta tayi Laalah ka gutsire lips ɗin na bar maka su ƙyauta”.        Shegen karen kuwa kamar wani mutum ya wani kaɗa bindi yana nufo ta gefen gadon ta inda zai iya ganina ya kwanta ya zubamin ido. Yanzun kama rawa jikina ke min, dan wlhy tsoron makirin karen nan nake ji over. Ya riga ya masa wani azzalumin training da in akace maka yay wani abun saika ɗauka ma ƙarya ne. Wlhy da ace bakina a buɗe yake haƙuri zan bashi, amma ina zalumin ya rufeshi. A hankali ya tako cike da ƙasaita inda nake, ya ɗan hawo gadon tare da kwanciya yana facing ɗina. Fuskata na kauda. Amma sai ya saka hannunsa ya maidota ta inda yake. Gira ɗaya ya ɗage cikin ƙanƙance idanun da ƙara maida muryarsa low ya furta, “Kwantar da hankalinki kema yau zaki samu abinda nake bama na hotels ɗin, Ba sai kin nuna jealous ba, ke dai kawai jirani na dawo”. Baki na cije da matuƙar ƙarfi ina jin kamar na shaƙosa amma babu dama. Haka ina ji ina gani ya tashi bayan ya sumbaci gefen fuskata cike da shaƙiyanci ya rufe ƙofar ya fice abinsa. Sai kawai na sake fashewa da kuka dan bani da zaɓin daya wuce hakan.        Hayatu da ƙin fitowar Samraah ta sakashi yawaita kallon ƙofar jin motsi ya sashi ɗagowa. Akan ogan nasa da sam bama shi yake kalloba shi ya zuba su. Sai dai kwarjininsa da cikar haiba ta cika masa idanun, janyewa yay tare da miƙewa cikin nuna girmamawa ya furta, “Barka da fitowa Yaya”.           Kai kawai Maash ɗin ya jinjina masa yana mai cigaba da kalle-kallensa, can kuwa idanun nasa suka sauka akan abinda yake nema wato Laalah. A can ƙasan maƙoshi da silent voice ɗin nan nasa mai fita a daƙile lips ɗin na motsawa da ƙyar ya furta, “Laalah!”. Azabure karen ya miƙe da ga inda yake ya nufosa da gudu-gudu. Bai masa magana ba yay gaba shiko ya bisa. Da kallo Hayatu ya bisu da ga shi har karen ta ƙasan ido. Yana nan tsaye cikin mamaki sai gashi ya sake fitowa dan bai wuce mintuna biyu da wasu sakanni ba. Yanzun ma bai kallesa ba face nufar ƙofa da yay yana faɗin, “Let's go”.      Da sauri Hayatu ya kwashi kayan daya zube a Centre table wanda duk takardu ne yabi bayansa. A maimakon ƙofar baya da sukafi bi yau ta babban falo suka bi. Duk da abin ya ɗan bama Hayatu mamaki sai baice komai ba, dan yasan ogan nasa yakan iya haɗa shekara ma baibi ta babban falon ba da sunan fita a gidan. Sai dai in zaije duba Ummie, ita ɗin ma sashenta na a jikin nashi ne shiyyasa akwai ƙofar da yake bi basai ya fito tanan ɗin ba, dan wannan kullum ne safe da yamma, idan ma ya yini a gidan zai iya zuwa biyar bai gaji ba.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Babu kowa a falon sai television dake aiki kasancewar dare ya fara duk al'ummar gidan sun shige ciki, hatta uwar dabar gidan Hajiya Mammah da alama yau bata kusa. Dan dama dai itace zaka zo ka iske a falon koda yaushe saboda sa idon masifa da son nuna ita a dole boss ce. Tuni guards ɗinsa da TJ sun gama shirya motocin fita. Fitowar tasa ta sakasu duk miƙewa da barin abinda suke yi. Gaishesa suka shiga yi da girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan yau sosai ƴan miskilancin ne a kusa, ga abinda ya faru tsakaninsa da Samraah yanzu. Da sauri Hayatu ya buɗe masa bayan farar zananniyar motar da TJ ya fiddo, wadda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kuɗi yay aiki wajen sayen ta. Dan sai wani irin sheƙi take da ƙyalli mai ɗaukar ido. Gata nan wata ƴar ƙumbula bata cika hayaniya ba, ba kuma ta cika mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa da ke gara kan kuɗi ta yanda suke so saboda amincewar UBANGIJI garesu. Sai da ya zauna Hayatu ya maida ƙofar ya rufe sannan kowa ya zabura ya shiga mazauninsa. Hayatu da TJ na gaba kamar koyaushe. Securitys ɗin sa na'a wata motar kamar ko yaushe suma. Da dasu uku ma kawai zaiyi fitar. TJ na ƙoƙarin tada mota ta fito da ɗan saurinta. Kamar kullum tana a cikin kwalliya dake ƙara fidda mata ƙyawunta da bayyana wayewarta. Hayatu ne yay ma TJ nuni daya dakata, dan haka ya tsaya ɗin harta ƙaraso, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, dan direct bayan ta nufa saitin inda Maash da bai san ma da fitowar tata ba yake. Dan hankalinsa nakan takardun daya ɗauka a gefensa da Hayatu ne ya ajiye masa su dan ya duba. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryata data haɗe da gayu ta furta, “My bro.. please zan bika, nasan dai club zaka je”.      Idan kujerar motar nan ta motsa shima ya motsa duk da kuwa muryar tata tazo masa a bazata tunda shi bai san da fitowar tasu ba. Ƙara narke murya tayi cikin nuna damuwa da shirun nasa ta sake cewa, “Please mana Yaya Awwab na shigo?”.         “Kai kana jiran miye?!”.     Ya faɗa cikin yanayin fusata batare daya ɗago ba. Ai jikin Tj har rawa yake wajen murzama motar key dan ko kallonsu ogansu yayi sun san mi yake nufi balle magana da baki. Da wani kalar mayen kallo Azizat tabi motar, ga wani irin sanyi ƙalau da jikinta ke komawa kamar an zubama bread ruwa. Dai-dai motocin na isa katafaren golden an black gate ɗin gidan da aka wangale musu wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen sakkowa saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Bata motsasu ba, bata kuma yi yinƙurin barin wajen ba. Ashe turaren da Mammah ta bata duk na ƙarya ne tunda gashi tazo gabansa amma bai kulatan ba. Arwa dake ta bayansu ce laɓe ta tako zuwa inda take bayan ta gama cin dariya, dan tun fitowar Azizat daga ɗaki tabiyo bayanta, dama kuma itace ta ɗauke turaren da Mammah ɗin bama Azizat ɗin dan a kunnenta komai ya faru sanda take bata batare da su sun sani ba. Hannunta ta kama kawai tare da janyota ta faɗa jikinta. Rungumeta tayi cikin sigar nuna lallashi batare da tace mata komai ba, sai dai shafa bayanta kawai da takeyi dan babu wani abu da zata faɗa mata kuma wanda ita bata sanshi ba. Sai dai kawai taƙi yarda ne kamar yanda kowa ya sani. Dan tunda yayansu yaface bayayi tofa babu ubanda ya isa cewa yayin sai Umminesa, itako batama da cikakkiyar lafiyar hankalin fahimtar abinda ake a gidan, a shi kansa ma bata masa kallo irin na mutum face ojujun dake sake hargitse lissafin brain ɗinta. Bata ganin laifin Azizat wani lokacin, dan wlhy ko ita da suke kamar uba ɗaya da Yaa Awwab ɗin a lokuta da dama takan ji inama-inama. Amma yanda tasan yana mata kallon ƙawa uba ɗaya yasa take dannewa kawai. Sun ɗan jima a wajen kafin ta kama hannunta su koma ciki...            🌜❤️🌛      A yanayin da ya shigo duk yanda Dad ke ɗauke kansa akan al'amarin nan sai da ya zuba masa ido cikin tashin hankali. Hakama Attahir da ke zaune jigum zaram ya miƙe akan Mansoor. Sai dai yana kamo hannunsa da ya dafe kansa da shi Mansoor ɗin ya kaɓe. Sai kuma ya zube cikin kujera. Amamkinsu ji kawai sukai ya fashe musu da kuka. Dole Dad ya miƙe shima. Su duka biyun sukai kansa da tambaya. Bai iya ya amsa musu ba, face kukan da yake yi da sambatun faɗin, “Shike nan na rasata. Ta auri wani bani ba. Kun cutar dani. Da kunsan irin son da nake mata da baku aitaka abinda kuka aikata ba”.         Hannu Dad ya sanya a bakinsa ya rufe, kafin cikin kulawa da tausayawa da lallashi ya shafa kansa. “Please Mansoor cool down. Nasan an maka badaidai ba. Nima kuma ina ji a raina mun cuta maka. Amma yanzu in sha ALLAHU a shirye nake na gyara kuskurenmu”.        “Taya zaku iya gyarashi Dad? Ta yaya? Bayan wadda kuka rabani da ita ta min nisa?. Iyayenta sun mata aure Dad, Samraah tayi aure, ta auri wani bani ba. Wlhy Dad ina sonta so na gaskiya da ban taɓa kwatanta yima wata ɗiya mace irinsa ba”.     Gaba ɗaya jikin Dad sanyi ya ƙara yi, sai ma ya rasa abinda zai sake faɗa. Kusan mintuna biyu kowa yay shiru a falon sai kai-kawon zuciyoyi kawai sukaji an faɗo musu babu ko sallama balle excuses. Hajiya Sakeena ce ke faman huci da cika da batsewa. Ta watsa musu wani mummunan kallo su duka sannan ta dire idanun nata akan Mansoor. “To mara mutunci haƙarka bata cimma ruwa ba. ALLAH bai karɓi rayuwar Husnah ba kamar yanda kaso kayi fata. Kaje ka gaggaya min magana son ranka har gidan mijin aurena. To yanzu ko zakaji amsa...”        Kamar an jeho Mamy itama sai gata. Kai tsaye kan Hajiya Sakina tayi. Cikin tashin hankali da mamaki ta zube a gabanta tana kuka da roƙonta ta rufa mata asiri. In sha ALLAHU indai batun auren Husnah ne zata saka Attahir ya aureta. Wata shegiyar dariyar rainin hankali Hajiya Sakina ta sanya. Kafin ta tafa hannaye da faɗin, “Iye nanaye caras-cass. Ai daga baya kenan, kema kin sanni bana manta bashin gaba ai Aunty. Ɗanki yaci zarafina ga ɗiyata ɗaya can tilo kwance a asibiti rai a hannun ALLAH. Dama na faɗa miki, in har Mansoor ya saki Husnah wlhy kema sai kin rasa naki igiyar auren dan sai na fallasa abinda kike binnewa”.        “K!! Sakeena!!”.   Attahiru daya gama kaiwa maƙoshi da abinda ke faruwa ya dakama Hajiya Sakina tsawa tare da yunƙurowa kamar zai mareta. Cike da rainin wayo tai wani irin ja baya tana ɗaga duka hannayenta sama alamar surrender. Sai kuma ta kwashe da dariya tana tafasu. Tsitt falon yayi kowa na kallonta har Mamy. Sai da tai Mai isarta kafin ta nuna Attahir ɗin tana haɗe fuska. “Oh lallai ashe kaima ka girma Attahiru? Ai ban sani. Sai ka saurara bada kai nake yi ba yanzu da tsoffinku nake”. Ta wani ɗauke kanta ta maida kan Dad da ya zuba mata ido kawai. Sai kuma takai zaune zama irin na ƙasaita da ƙularwa.        “Kayi haƙuri Yaya idan kaga an ɗaure alƙali a kotu tofa ɗaurowa tayi. Nasan zaka so sanin yanda akayi matarka ta dage dan hana yiwuwar aure tsakanin ɗan ka da budurwarsa. Da kuma ƙullawa tsakanin Husnah da ɗanka.”    Cikin ɓacin rai Dad ya tareta da faɗin, “Sakeena ki tafi maganarki kai tsaye kin san bana son shashanci”.      “Uhhm hakane Yaya kayi hakuri”. Ta faɗa tana maida kanta kan Mansoor da Attahir da suka gama cika da batsewa. Kamar bataga a yanayin da suke ba ta fara bayaninta. “Idan Mansoor da Attahir basu manta ba a ranar da matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ya shahara a ƙasar nan dama duniya yay bikin buɗe Companynsa a garin kano wato *_Awwab El-Mu'azz Adams_* da akafi sani da *_MAASH_* kun tattauna wani batu akansa da daddare daya shafi video recording da budurwar Mansoor tai masa”.     Da wani irin sauri Mansoor ya ɗago yana kallon Attahir. Saurin girgiza kai shima Attahir ɗin yayi zai fara rantsuwa Hajiya Sakina ta dakatar da shi. “Kwantar da hankalinka Mansoor ba Attahir bane ba. A sanda kuke tattauna batun wannan video Aunty ta shigo sashen naku saboda damuwar rashin cin abincin kirki da Mansoor yayi. Ta kawo masa kunun tsamiya data dama masa akan ko zai sha tunda tasan yana sonshi sosai. Sai dai tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar ta tsinkayi Mansoor yana sanar ma Attahiru batun video tare da nuna masa shi, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH ya rufe wannan sirrin har sai sun gano gaskiya. Ya kuma taimaka musu akan tabbatar da gaskiyar saboda shi yana da abokai ƴaƴan manyan ƙasar nan da sukayi karatu tare a us masu alaƙa da Maash. Cikin jimami Attahir yay masa alƙawarin bincikawa. Sai dai ya tabbatar masa da sam baya jin Maash zai aikata wannan al'amari da gangan in ma harfa ya aikata ɗin. Dan ya ɗan san Maash ɗin shima sama-sama duk da ba wata mu'amala mai ƙarfi bace ta haɗasu face zaman makaranta ɗaya a us. Ya kuma gargaɗi Mansoor ɗin akan ya gargaɗi budurwarsa ta adana video ɗin da ƙyau gudun kada wani ya gansa har yayi tunanin yin wani abu na cutarwa ga Maash. Dan yanzu mutane sun lalace. Ganin Maash mutum mai tarin dukiya za'a iya amfani da video dan yimishi barazana. Ɗari bisa ɗari Mansoor yaji wannan shawara ta ɗan uwansa, ya kuma tabbatar masa da zai nema itama Samraah ya gargaɗeta a daren nan ma basai gari ya waye ba.      Da baya da baya Aunty ta bari sashen, ta samu kai kanta falon, ta samu ka shige sai su Amal kawai na kallo, dan haka ta samu damar shigewa ɗakinta da sauri itama. Kai kawo ta shiga yi zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa akan abinda ta jiyo. Kaima dai Yaya kasan aunty akan batun kuɗi. Mace ce mai son ace ita itace. Shiyyasa ko'a sutura bata saka ƙarama. Koda bazaka saya mata ba tasan buga-bugar da zatayi ta samarwa kanta. Hakan yasa ma kuke yawan samun matsala da ita. Dan idan ban manta ba har ƙararta kasha kaiwa gida akan wannan halin nata na idan taga abu a wajen wane sai da tayisa itama hankalinta ke kwanciya tun ma baka da komai. To awannan gaɓar ma bikin Mansoor take hari. Ta riga ta gayyato ƙawayenta ƴan ƙarya irinta da matan oganninka na wajen aiki, gashi kai kuma ka kwafsa mata kaƙi yarda da duk tsare-tsaren sharholiyar da muka tsara, ka kuma ce bazaka bata ko sisi ba. Haka shima Mansoor yaƙi. Attahir ne ma ya ɗan biye mata ya bata 1mil yace ta ƙara dana wajenta tayi haƙuri. Dan haka jin wannan batun video da maganar Attahir ta kawo mata wuta a cikin kai.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_ .......A ranar daƙyar ta iya barci kamar yanda ta faɗa min, washe gari tunda farar safiya tai kirana. Da farko kwana-kwana nima ta dinga min, sai da na nuna mata ta fito kawai a mutum muyi magana tasan dai ni mai rufa mata asiri ce sannan ta buɗe min komai. Koni zancen nata ya girgizani gaskiya. Bakomai yasa hakan ba sai jin batun Maash. Dan ni nasan wani abu kaɗan daga Maash ɗin sakamakon mijina yaronsa ne. Saboda a Companynin sa na Abayoyi dake anan Dubai yake aiki. Na buƙaci nima ta ɗan bani lokaci nayi tunani, ta roƙeni karna wuce yinin yau to.       Banko wuce yinin ba, dan ta hanyar mijina na ɗan ƙara bincika halin Maash da ƙarfin ikonsa. Amsar daya bani akan cewa Maash mutum ne murɗaɗɗe, sannan yana da zafi sosai. Amma da wahala ka masa abu a farko ya maida hankali a kanka. Sai idan ka cigaba da aikatawar ne, idan har fa ya maka gargaɗi na farko baya sake na biyu sai hukunci. Wannan amsa tashi ta bani ƙwarin gwiwa, dan koba komai dai mu ai bama fata bayan na farko mu sake, yo inama zamu sake ganinsa. Wannan ɗin ma rabonmu ne ALLAH ya kawo mana har gida. Husnah ta jima tana son Mansoor amma yaƙi saurarenta, aunty kuma taƙi ƙarfafa al'amarin duk da ta sani, dan haka kawai naga ai wannan wata hanya ce ta samun cikar burina, sannan nima dai dani za'a ci kuɗin. Kai tsaye nai kiran aunty muka tattauna da tsara yanda komai ya kamata ya tafi, tare da bada sharaɗin in fa har akaci nasara a 500mil inada kaso biyu. Ma'ana inada 200mil kenan. Aunty ta nuna min bazai yiwu ba, sai dai na amshi 100mil nayi haƙuri, tunda nasan abinda ke gabanta ai. Kai tsaye na fito mata a mutum. (Aunty ke tayaya kike tunanin auren Mansoor da yarinyar nan zai kuma kasance? Mufa zamu amshi kuɗin nan ne a hannun Maash da sunanta, idan ma har ya bibiya ita zai saka a kama. Sai dai auren Mansoor ya koma kan Husnah tunda dama ba'ayi invetion ba wai ko baki gane ba). Da sauri ta amsa min da hakane fa Sakeena. Wlhy kaina duk ya cure. Yanzu dai a daren nan zan samo video daga wayar Mansoor. Ke kuma sai ki samo mana Number Maash a wayarki. Na amsa mata da karta damu, kafin ma na samar da Number zan saka a fara aika masa saƙon barazana gidansa dan akwai wani yaron mijina dake tare da Maash ɗin kuma ya san sabon gidan nasa... 🌛❤️🌜          Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso guesthouse ɗinsa. Gidane daya amsa suna gida sai dai bashi da girma sosai. Amma a ƙyau da tsaruwa ba'a magana. Dan yanda akai kusan rabin gidan da gilashi dolene ya ɗauki hankalin mai kallo. Ga wata green ciyawa da aka malala a harabar gidan aka ratsa lafiyayyen baƙin kwalta da mota zata iya bi kawai kota tsaya. Sai furanni da ƙamshinsu ya cika gidan da kukan tsuntsaye. Babu wani hayaniya, dan anguwar ma shiru ce sai uban karunuka ata waje duk da kuwa akwai securitys da baka isa ka shigoba sai da izininsu. Cikin girmamawa security ɗin daya wangale musu gate da remote ke ɗaga musu hannu, koda ya maida ya rufe motocin ya biyo. Dai-dai Hayatu na buɗema Maash mota ya iso wajen. Sannu da zuwa da gaisuwar girmamawa yake jerama ubangidan nasa. Maash dake ƙoƙarin fitowa hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan ya gama fitowa a motar a taƙaice ya furta, “How are you Semuel?”.       “I am fine Sir”. Samuel ya faɗa cike da zumuɗi. Ga bakinsa washe kamar gonar auduga. Dan ya jima baiga boss ɗin ba kasancewar kwana biyu bai shigo nan ɗin ba. Tamkar wani mai mulki haka yake tafe cikin takun mazantaka da rashin hayaniya guards ɗin nasa da su Hayatu harma da TJ da Samuel biye da shi. Hayatu ne ta ɗan gefensa amma ya zartashi a taku ke masa magana ƙasa-ƙasa. Shiko yana tafiya tamkar bada shi ɗin yake ba. Dan inda yake ajiye ƙafa kawai yake kallo. Da sauri wanda ke tsaye a bakin ƙofar shiga wajen ya wangale musu ƙofar shima tare da risinawa kwasar gaisuwa wajen boss. Hannu shima kawai ya ɗaga masa. Babu alamar damuwa a tare da shi alamar dai duk wanda ke tare da shi yasan ɗabi'unsa, da girmamawa ya cigaba da faɗin, “Sir ya iso tun kusan awa ɗaya. Kamar yanda ka bada umarni securitys basu barshi ya shigo da mota ba. Kuma da yaronsa biyu aka barshi ya shigo kawai.”          “Good job” ya faɗa a taƙaice yana tura kai ciki. Dan shima tun shigowarsu anguwar yaga motocin Minister ɗin tare da yaransa da aka dinkare a waje. Da ga shi sai Hayatu da TJ sai amintaccen guard ɗinsa Shu'aibu suka shiga. Kallo ɗaya yayima Minister da ya gama cika da takaici ya ɗauke kansa. Babu wani alamun damuwa ko nadamar shanyasa da yayi ya ƙarasa kujera ɗaya tal data banbanta da duk kujerun dake a haɗaɗɗen falon ya zauna. Wani shegen zaman ƙasaita da gadara yayi, yayinda Shu'aibu ya koma bayansa ya tsaya kamar saƙago. TJ ya ajiye kayan dake hannunsa a stool ɗin gefen kujerar na sashen damarsa. Hayatu kuma yakai zaune a ɗaya daga kujerun falon ta gefen kusa da shi. Bakin Minister daya miƙe domin girmamawa a washe kamar bashine ke faman tsinema Maash ɗin ba a zuciya. Amma kuma dama birgar ta bayan idoce kawai. A kallon ido cikin ido ko ganawar fuska da fuska Maash tamkar lu'u-lu'un narkakken ɗanyen zinare yake a cikin idanunsu. Duk da ƙarancin shekarun nan nasa shi fa takalmin ƙarfe ne baya takuwa a yanda kaso. To kaɗan daga aikinsa yace bazaiyi business ɗin da kai ba. Kuma babu ubanda ya isa yace komai, idan kuma kace zaka kona wajen wani saboda ka saɓa da Maash, to ka tabbata kuwa babu mai saurarenka kuma koda a ƙetaren ƙasar ne. Sai da ya tabbatar Maash ɗin ya gama zama sannan ya miƙa masa hannu cikin murmushi. Amma mi, sai Maash ɗin yaƙi bashi nasa, a maimakon hakan ma sai ya haɗe hannayensa biyu a daƙile alamar ya amsa masa. Shiko minister sai faman murmushin yaƙe yake dan abinda Maash ɗin yayi ya baƙanta masa zuciya, dan gaisuwar ma shine yayi Maash ya amsa a taƙaice. Bai nuna ya damu ba, dan lallaɓawa yake kasancewar ya jima yana neman alfarmar wannan zaman amma abin ya gagara, dan kusan wata biyu kenan. Yanzun ma da ƙyar sai da ya biyo ta wasu hanyoyin yaran Maash ɗin sannan ya dace. “Ranka ya daɗe ai kusan 1hour kenan da isowarmu”. Ya faɗa cikin son nuna an shanyasu a wayance. Kamar Maash ɗin bazai tanka ba dan hankalinsa nakan wayar hannunsa da yake daƙila, kusan minti ɗaya har ma Minister ya fidda rai da samun amsa sai tsine mar yake a zuciya a daƙilen nan ya furta, “10:30 ne ƙa'idar zuwana nan dama”.       Yawu mai nauyi Minister ya haɗiye yana jinjina kai da washe baki, “Hakane kuma gaskiya. Hakan ma na gode.”      Maash ɗin baice komai ba, sai ajiye wayar yay gefensa ya ɗan ɗago ya zubama Minister cat eyes ɗinsa masu kaifi da ƙarfin gani. “Zamu iya fara abinda ya zaunar damu dan banda lokaci”. Ya furta ƙasa-ƙasa batare daya janye idanun ba kuma. Ji Minister yay duk kamar ya daburce. Cikin sarƙewar harshe da in inar da bai san daga ina tazo masa ba ya fara magana yana kaɗa kai kamar tsohon jandala gwaja na ƙadangare. “Yes! Yes mizai hana. Bussines ne dama nake son mu ƙulla ranka ya daɗe, na turoma PA ɗinka kuma dukkan bayanai na. Motoci nake son a shigo min dasu kamar guda dubu biyu, idan babu damuwa bana son su wuce wata biyar. Dan nayima yarona alƙawari bana son na saɓa. Sai dai za'amin alfarmar biyan kaso ɗaya bisa biyun kuɗin daga nan zuwa ƙarshen shekara zan sake bada kaso ɗaya kasan al'amarin namu harkar gwamnati tasa fidda kuɗi kai tsaye zai iya jawo mana matsala, next shekara a wata biyar ɗin farko sai na ƙarasa biya harma da ƙarin wasu kuɗaɗe a sama. Amin alfarmar nan dan ALLAH badan ni ba badan na isa ba. Idan kuma kana buƙatar kaya sai muyi gishiri na baka manda a shirye nake”         Shiru babu alamar Maash zai amsa saima cigaba da kallonsa yake wani ƙasa-ƙasa batare da yasan kallon na hargitsa jinin minister ɗin bane. Hayatu daya fahimci Maash bazaice komai bane ya fuskanci ministar a karo na farko. Kansa tsaye ya furta, “Sir amma na gaya maka akwai ƙa'idoji sosai, sannan mu bama bada bashi kai tsaye sai kabi dukan ƙa'ijin mu. Bazai kuma yiwu ka bamu kuɗi ɗaya bisa biyu ba mu kawo maka kaya. Ƙa'idarmu zaka bada biyu bisa uku ne, tare da takardun kadarorinka na adadin sauran kuɗinmu dake kanka, lauyanka da namu su saka hannu muma mu saka. Mune kuma zamu baka lokacin biya, sannan bama buƙatar kuɗin ruwanka, zamu sakama kayanmu iya ribar da muke buƙata ta cinikayya kawai wannan kuma sirrinmu ne. A sunayen motocin daka bada kuma akwai waɗanda dokar ƙasa ta hana shigo da su kwata-kwata. Mu kuma bama ƙimma doka biyayya saboda duk wanda zai mu'amalance mu dolene muma yabi tamu dokar, idan ya kauce kuma ya rage nasa. Da farko dai fara karanta wannan sune dokokinmu da sharɗin ƙulla kasuwanci damu first. Ƙa'idarmu kuma gani ɗaya ake mana, dan daga wannan zaman boss bazai sake zama da kai ba face to face. Idan ka shirya daga nan har zuwa 3 lokcinka ne”.         Tuni fuskar ministar na ƙoƙarin canja yanayi, amma dai yana ƙoƙarin hana bayyanar hakan. Takardar da Hayatun ya taso ya ajiye masa a saman table ɗin gabansa ya ɗauka. Da sauri ya ɗago ya kalla Maash ɗin da yay biris da su, dan idanunsa ma a lumshe suke kamar namai barci. Sai dai makirin tsaff yake kallon Minister da su har yanzu. “Amma ranka ya daɗe yaya haka? Sannan nace inada kaya a hannu ko yanzu zan iya baku su muyi ciniki nima”.         “Tsarin kenan?”. Ya faɗa a yanda yake alamar kunnesa dai na'a kansu.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .....Baki Minister ya buɗe zai sake magana Hayatu ya taresa da faɗin, “Ranka ya daɗe bama canjawa a yanda muke. Zaɓi biyune kawai yarda matsayin amincewa, ko haƙura ka nema wasu kuyi business ɗin kawai mu bamu da damuwa, sannan bama buƙatar wasu kayanka mu nan dan duk abinda muke nema mun san inda muke samunsa”.      Wani mugun yawu minister ya sake haɗiyewa. Ji yake kamar ya zaro bindigar jikinsa ya fasa kan Maash ɗin da shegen PA ɗin nasa ma kowa ya huta. Sai dai hakan bashi yiwuwa, dan Maash na zama ya zaro tasa bindigar ya ajiye ta yanda kowa yake ganinta ƙuru-ƙuru, idan girma ne da cika aiki kuma tafi tashi a komai. Ashe girman kai da wulaƙancin yaron nan da ake faɗa masa ma ya wuce duk hakan. Yaro ƙarami da bai wuce sa'an ƴaƴan cikinsu ba sai gara rayukansu yake akan tituna saboda ya tara dukiyar da ba'asan tayaya tai tashin hauhawar gwauron zabi cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Gashi ya mamaye komai sai da shi a manyan Business ɗin ƙasar da ada sune masu juyasu a yanda suka so. Dolene ma suyi maganin terror ɗin yaron nan da sam babu tsoro ko shakkar kowa a cikin idanunsa shege mai ido a tsakar kai. Wata fitinar zasu ƙullo masa ta yanda ko allura bai isa sake sarrafawa ya siyar a ƙasar ba cikin daɗin rai. Dan tsalle target ɗin su na farko akan ƙin ko ganin Bussines ɗin daya zo masa da shi bashi ke nuna zasu barsa bane, akwai plan A har zuwa Z da suka tsara a kansa....        Kallon agogo da Maash yayi ya saka Hayatu daya san abinda yake nufi faɗin, “Sir kowane irin lokaci boss zai iya barin wajen nan mi ka yanke?”.      Firgigit Minister ya dawo hayyacinsa. Murmushi danne ɓacin rai ya saki da faɗin, “Shike nan na amince ɗin”.       “Okay zamu iya fara ciniki, lawyer ɗin mu na hanyar zuwa nan ɗin. Muna fatan tare kake da naka kai ma?”.       “Eh muna tare, yana can waje inda securitys suka ce su tsaya.”    Kai hayatu ya jinjina kawai yana rubuce-rubuce a file ɗin hannunsa. Kafin ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyi huɗu daya zube a gefensa, danne-danne yayi tare da miƙewa cikin girmamawa zuwa gaban Maash. Amsa Maash ɗin yayi batare da yace komai ba. Sai da ya kai wayar kunnensa cikin bada umarni ya furta “Lawyer ɗinsa ya ƙaraso”. Daga haka ya miƙama Hayatu wayar. Amsa Hayatu yayi shi kuma ya ajiye masa file ɗin hannunsa a stool ɗin gefensa....         Ƙarfe kusan uku suka dawo gidan, a matuƙar gajiye ya shigo, ga kansa na masa ciwo sosai na hargagin da surutun da Minister ya sashi yi. Dama sun sauke Hayatu gida, shi da TJ ne kawai da guards ɗinsa suka ƙaraso nan. Kai tsaye ya wuce bedroom, ya bar Tj na ƙoƙarin kashe sauran abubuwan dake kunne a falon. Kamar yanda ya saba kansa tsaye ya buɗe ƙofar ɗakin nasa ya shiga da sallama ciki-ciki yana ƙoƙarin zame jacket ɗinsa. A kan Laalah idonsa ya fara sauka. Har zai fara fusata tunda ba barinsa yake ya shigo masa nan ya kwanta ba sai kuma idonsa ya sauka a kanta. (Ya ALLAH) ya faɗa acan ƙasan ransa. Dan wlhy shaf yama manta ya barta anan ɗin. Sosai ta wani lafe can jikin fuskar gadon alamar a tsorace tai barcin saboda Laalah. Saletaf da handcuffs daya saka mata kuma na nan duka. Wani irin murza goshin yayi. Sai kuma yaja sirrin tsaki a ɗan kausashe da nuna harzuƙa ya furta, “Laalah get up!”. Zumbur kuwa karen ya miƙe shege da kunnen maciji dan barci yake fa. Amma tun motsa ƙofar ya wani tada kunnuwa sama alamar saurare, da alama kuma tunda bai miƙe ba tun farko ya gane ubangidan nasa ne ya dawo. Ƙofar ya buɗe masa kawai ya ce, “Go and sleep, goodnight  thanks”. Bindi karen ya kaɗa masa ya fita abinsa shi kuma ya maida ƙofar ya rufe tare da ƙarasa cillar da jacket ɗin daya cire ɗin saman sofa. Gaban gadon ya ƙarasa tare da lalubar aljihunsa ya ciro keys ɗin Handcuffs ɗin ya cire mata daga hannayenta, dama bai wani matse ba, sai dai hannunta bazai iya fita ba. Kamar wadda ke a ido biyu kuwa ta wani sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sosai da ya saka shi ɗan kallonta. Idanun ya zuba mata kusan sakan goma kafin ya kai hannun a hankali ya shiga ɗaye saletaf ɗin a hankali, da yaga zata motsa sai ya dakata. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta koma sai ya cigaba. A haka ya gama cirewa duka. Aiko ta wani turo lips dinta gaba da suka sake zama jazur suka tsuke sosai kamar an gyara mata su ne da gayya. Sai lokacin yaga sawun hawaye da suka bushe alamar an dai ci kuka.         (Trouble Maker ). Ya faɗa a ransa yana kauda kansa da barin wajen. Ta riga ta juya kwanciyar tata zuwa jikin fuskar gado, dole ya koma ta can side ɗin hannunsa ɗauke da blanket ɗin dake a gadon ya lulluɓa mata dan yanda ta takure waje ɗaya yasan sanyin acn nan ne ya takurata. Shi kuma harga ALLAH bama zai iya zubar da kansa ya tashe ta ta koma side ɗinsu ba. Tunda zuwa yanzu ya gane a side ɗin Ummien sa take kwana. Dan baya ma jin ta cika sati a biyu tabar kwana a side ɗin masu aiki......         💞✨💞      Duk yanda Mom taso amfani da maganin nan hakan ya gagara, dan Halime ta kafa ta tsare kamar ta fahimci mi take shiryawa. Gashi koda ta kira Abba akan itafa sai dai a raba abinci Halime tayi nata ita tayi nasu ita da yara kai tsaye yace bai amince ba. Daga ƙarshe ma sai gashi ya dawo gidan. A gabansa Halime ta gama girki ta ɗibar musu ita da shi ta samo kula mai ƙyau kuma a kayanta ta zuba wani. Koda Abba ya tambayeta na waye, kai tsaye ta sanar masa na “Yaya Musaddiq ne. Yana babba a gida amma aita bashi abinci a wulaƙantaccen kwano bayan shike cefanen. Ni ba haka naga su Gwaggo nama su Yaya Buhari ba a gidanmu”.      Shiru Abba yay yana kallonta dan ya gagara yin magana. Sai ma wani nauyi ne yaji kansa ya masa tamkar Musaddiq ɗin na gabansa. Wannan abu ya ƙonama Mom zuciya. Tako shiga surfama Halime zagi, amma ko tari ƙinyi tai, sai da taga zagin na neman zama na fitar hankali ta fashe da kuka. Hankali tashe Abba yay kanta yana tambayar ta lafiya. Kukan ta sake fashewa da shi sosai. “Innata na tuna, tana cikin kabari amma ana zaginta. Kaicon wannan rayuwa, ban ja mata addu'a ba sai zagi, gaskiya bazan iya zaman gidan nan ana zagarmin mahaifiya ba”.     Rikicewa Abba ya sake yi, tuni ya manta da wata Mom a wajen ya kama Halime ya rungume. “Haba Halimatussa'adiyya na, ke da barin gidan nan ai sai dai in mutuwa. Kiyi haƙuri ai duk wanda ya zagi wani iyayensa ya zaga. Karki sake faɗar haka kinji, ALLAH yay miki albarka”.         “Amin nagode _my Rabon alkairi_. Na kuma yarda da kai bazan sake damuwa ba. Ai lobiyu irin kamar kainuwar tafkin bayan gidanmu ɗin nan”. Ta ƙare maganar da fakar idon Abba tai ma Mom da tai mutuwar tsaye sagale tana kallonsu. Sai kuma ta wani sake narkewa jikin Abban tana shashashar kukan ƙarya. Ai tuni Abba ya sake rikicewa, hannunta ya kama tare da ɗaukar kular abincin Musaddiq data zuba ɗin suka shige ɗaki yana sanarma Mom ga nasu nan a tukunya ta ɗauke su sun shige. Rasa ma abinyi Mom tayi, sai kawai taji hawaye na rige-rigen sakko mata. Shiru tai tsaye a wajen hawayen na tarara, tana ɗagowa suka haɗa ido da Halime na leƙenta ta window tana dariya. Gwalo tai mata dayin fari da ido ta saki labulen.      Yuuu Mom taji jiri na neman ɗibarta, har sai da ta kaita da dafe bango zuciyarta na mata zafi kamar zata buga. Wai ita Jalilah dake juya gidanta yanda take so, idan ta bama Imam umarni har rawa jikinsa yake don ganin ya cika mata akan lokaci. Amma yau a gabanta yake rawar jiki akan yarinya ƙarama sa'ar ƴarta har yana faɗa mata magana a kaikaice wai wanda yay zagi iyayensa ya zaga. Kai wane irin juya baya duniya ke son yimata ita kuwa a rayuwar nan....     To bari na tayaki tambaya momcy🤣🥱       💞⭐💞⭐💞        A ranar ni na samar da Number, na kuma tura saƙo ga Maash ta hanyar yaron mijina, amma ita har tsawon sati tana fakon wayar Mansoor, randa ta samu kuma tace bataga video awayar Mansoor ɗin ba iya bincikenta. Hankalinta duk ya tashi, amma sai na kwantar mata da shi ta hanyar tunatar da ita ai in shi babu a wayar tasa ya goge ko ya kwashe yarinyar nada shi. Bai kuma zama lallai ace an rasashi ta wajenta ba. Ta gamsu da zancena, dan haka tace nabar komai a hannunta zata samo video ɗin. Amma ya kamata a fara turama Maash saƙo fa kafin samuwar video dan guri nata ƙurewa kada wani ya rigamu. Ta bani dariya sosai, dan son kuɗin Aunty mai lasisi ne. Na yarda da shawarartata duk da ban gaya mata na fara turawa ba, dan haka a ranar muka fara turama PA ɗin Maash saƙo. Munyi hakane saboda saƙon zaifi isa garesa fiye da mu tura a wayarsa. Koda muka tura dai shiru babu wani reply har tsawon kwanaki, dan haka muka sake turawa. Anan ma babu amsa ga video ya gagara samuwa a hannun budurwar Mansoor. Sai kawai wani tunani yazo min. Munfa riga mun danganta video da ita yarinyar, Maash kuma ba sakarai bane zai iya bibiyarta. Gashi mu kuma babu video ma a hannunmu. Sai kawai muka yanke shawarar kidnapping ɗinta. Komai kuwa yazo mana cikin sauƙi da taimakon maigadi na dana bama dubu ɗari. Sai dai abin takaici babu video a wayar Samraah. Munyi-munyi kuma ta bada shi amma taurin kan yarinyar taƙi badawa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ......Muna akan haka sai kawai ga reply PA ɗin Maash a randa muka aika saƙo na uku. Akan an amince za'a bamu 500m, amma da sharaɗin sai mun bada footage ɗin nan sannan a cika mana. Munta nazari akan hakan da tunanin akwai talala a batun, daga baya aunty tace babu abinda zai faru in sha ALLAH. Wannan ƙwarin gwiwa ya sakamu zuwa muka buɗe sabon account da sunan mai gadina, kai komai ma da nashi akai amfani har account ya samu muka turama Maash. Kuɗi kuwa a ranar suka shigo. Munta murna da ganin madarar kuɗin nan ziryan, sai hakan ya ƙara mana ƙaimi sosai.      Cikin abinda bai fi mintuna talatin ba muka cire kudin zuwa account ɗin aunty, shi kuma wancan muka rufesa gaba ɗayansa. Ga kuɗi sun samu amma video ya gagara samuwa a garemu. Sai ma wani tsautsayi daya so giftawa. Yarinyar ta samu nasarar cirar waya a jikin mai tsaronta tai kiran da aiki ya kusa buɗe mana. ALLAH ya taimakemu dai-dai sanda Mansoor ke kiran Attahiru akan ya kira dcp ya sanar masa Aunty na tare da shi. Shine tai kiran yaron namu akan yayi maza yabar gidan da yarinyar kada kuma ya kuskura yabar wani abu a gidan. Hakan kuwa akayi, sai dai labarin ya canja kansa a dalilin satar data saci sata. Dan kuwa dai an tare yaronmu an ƙwace Samraah, shima kuma anyi ram da shi. Mun shiga tashin hankali da baida misali, musamman ma Aunty, dan kuka ta dinga min a waya kan na rufa mata asiri dan ALLAH kada wanda yaji wannan magana. Niko na tabbatar mata zanyi hakan amma da sharaɗin bayan auren Mansoor da Samraah da sati ɗaya zamu saka ya saketa ya auri Husnah.      Tace ta yaya?.   Na amsa mata da zamu bar Mansoor ya auri Samraah ne dama dan mu amshi video ɗin hannunta. Da zarar mun amsa zamu ƙulla mata sharrin da bama shi kaɗai ba kowa sai yaji ya tsaneta. Ta jinjina al'amarin tare da sanar min ita ba itace abin ji ba Yaya ne da Mansoor. Niko nace mata karta damu komai zamu yisa a tsare ne, yanzu dai mu jira Samraah ta fito dan a lokacin bamu san Maash bane ya amsheta mun zata ƴan sanda ne. Sai daga baya muke jin ba ƴan sandan bane sai kuma hankalinmu ya sake tashi. Muna cikin yanayin ƙullawa da kwancewa sai ga Samraah ta fito. Farin ciki babu irin wanda bamu yi ba, dan mun san plans ɗinmu zasu cigaba da tafiya kenan.      Mun cigaba da tsarinmu yanda ya kamata ana gobe ɗaurin aure kuma sai komai ya canja daga yanda yake. Dan mun tafi amsar kayanmu wajen tela da wanda amarya zata saka da ba'a kai ba akai ram da mu....         💞✨💞✨💞       Shirin kwanciya yayi, lokaci-lokaci yana ɗan jan ƙaramin tsaki dan yunwa yake ji. Da farko chocolates ɗin nashi na fama ya ɗebo, sai kuma ya maidasu yana jan gajeren tsaki.  Harga ALLAH abinci kuma yafi buƙata dan rabonsa da cin wani abu matsayin normal abinci 2days kenan. Daga kayan fulawa sai fruits da chocolate yake zubama cikinsa. Saukar idanunsa akan tray ɗin data shigo da shi ɗazun ya sashi nufar wajen. Kwanikan ya buɗe tamkar wanda akaima dole. Dan sai faman yamutse fuska yake da ɓata rai. Fruit salad ɗin daya ɗan sha ɗazun ya zuba ma ido da gasashen naman kaza daketa ƙamshi alamar zai yi daɗi. Harya maida ya rufe kamar bazai ci ba sai kuma dai ya sake buɗewa dan gwara yaci koda kaɗan ne so yake yay barci kada yunwar ta takurasa. Saboda in har yaji damuwa da yunwa tofa da gaske yunwar yake ji. Duk yanda kuma yaso riƙe kansa bashi yiwuwa.         Ya tsakuri kazar zai kai baki akai kiran wayarsa. Yaso sharewa sai dai ganin Abubakar ne babban yaronsa ne shima dake riƙe da harkokinsa a ƙetare ya sashi saka ta hannunsa daya ɗiba a bakin nasa yana ɗaukar wayar. Yaci kusan lauma biyar yana wayar, sai da ya kammala magana da Hayatun ya fahimci ko bissmillah baiyi ba. Kansa ya dafe yana yamutse fuska. Sai kuma yayi bissmillar sannan ya cigaba da ci. Da yake yunwar yake ji sosai yaci ya kuma sha fruit salad ɗin shima sannan ya koma bathroom yay brush ya fito. Kansa tsaye ya nufi gadon zai kwanta sai kuma ya tsaya cak yana kallonta. Gefen lips ɗinsa ya ɗan ciza sai kuma ya ƙarasa ya ɗauki pillow biyu ya koma saman sofa ya kwanta. Bawani yaji daɗin kwanciyar bane ba kasancewar bai saba kwanciyar a hakan ba. Iska ya furzar kaɗan tare da lumshe idanunsa kawai.         Barcin ya ɗan jashi da nisa kaɗan saboda gajiyar da yayi aka fara masa mintsine-mintsine a jiki. Idanunsa ya buɗe kawai batare daya motsa daga kwancen da yake ba. Tun yana ɗaukar al'amarin wasa har dai yaji yau fa dabance, a farko ya ɗauka normal ne kamar kullum, dan ya jima yana fuskantar irin wannan yanayi amma jarumtarsa na tattare komai ta bizne saboda ya riga ya sakama ransa in har ba Ummie ta samu lafiya ya ganta a farin ciki ba baya jin yana da wani spiece a rayuwarsa na kallon wata mace da wannan siffar. To tayaya ma zai yarda hakan ta kasance. Ace mahaifiyarsa na kwance cikin lalura mai ban tashin hankali shi kuma hankalinsa nakan samawa gangar jikinsa abinda take buƙata. Kai impossible. Cikin cizar lips ya sake lumshe idanunsa a yanayin tilastama kansa kamar yanda ya saba. Dan shi bai taɓa shan wani magani domin hana faruwar haka ko samun sassauci ba. Ya dai riƙe azumi tare da takure kansa matuƙa saboda jarumta. Sai idan al'amarin yayi tsamarine yake amfani da lemon tsami bisa shawarar abokinsa Taj.. daga ba hakanba baya shan komai.         Cikin ƙanƙanin lokaci wata irin zufa ta gama jiƙe masa jiki, amma bawon ALLAH ko motsawa baiyi ba yana daga kwancen yana sauraren hukuncin UBANGIJI. Tsanantar al'amarin ya sashi yunƙurawa a karo na farko ya tashi zaune haƙoransa ya datse da lips ɗinsa kamar zai huda shi. Zaman ma gagararsa ya nema farayi, ya miƙe tsaye zuciyarsa na tsananin bugawa. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, saboda ƙullewa da cikin yay sosai ƙafafun ma kansu riƙewa suke. Ga idonsa ya sauka akan wadda ke kwance a saman gadonsa tana barcinta hankali kwance. Duk da ba ganin fiskarta yake da ƙyau ba saboda ƙarancin haske yanda tai luff cikin lallausan blanket ɗinsa ya tabbatar masa da hakan. Kansa ya kauda, sai kuma ya nufi Bathroom da ɗan yanayin sassarfa na tilastama kai jarumta. Babbar shower ɗin mai ƙarfi ya sakarma kansa. A cikin ƙanƙanin lokaci jikinsa ya gama jiƙewa sharkaf, sai dai ta saman kansa yayi amfani da shower cap gudun kada ruwa ya taɓashi yay mura. Dan shi bashi da wahalar yin mura. Sosai ruwan ya dakesa amma baiji komai ya canja ba. Sai ma sake ruruwa da yake jikinsa na sake tabbatar ma da yau ɗin fa yau ce. Cire kayansa yayi ya fito bayan ya ɗaura alwala. Sai dai raka'a biyun farko ma da ƙyar ya iya kaisu saboda yanda al'amarin ke sake ta'azzara. Shiru ya cigaba da zama a saman sallayar, kafin kuma dai ya miƙe da ƙyar. Saman gado ya tafi da nufin hawa sai kuma ya tsaya cak, karan farko ya zubama fuskar Samraah dake shaƙar barcinta a nutse idanunsa da suka juye gaba ɗaya. Ba wani tar-tar yake iya ganinta ba, sai dai yanayin ƙarancin hasken sai ya ƙara ƙawata masa ƙyawunta abinka da wanda ke cikin yanayi. A hankali ya fara takawa tamkar hawainiya mai tsohon ciki. Ya kai hannunsa duka biyu yaja igiyoyi biyu dake ɗaure da net ɗin da aka zagaye gadon tamkar rumfa. Cizar lips ɗinsa ya sakeyi yana mai duƙar da kansa tamkar wanda ke jin abinda zai aikata ba dai-dai bane. Har ya motsa jikinsa da nufin komawa sai kuma ya sake tsayawa cak sakamakon nauyin da ƙafarsa tai masa. Ga zuciyarsa na ƙara tabbatar masa da (Awwab matarka ce fa, ALLAH ya halatta maka miyyasa zaka cutar da kanka kaƙi karɓar ni'imar da yay maka. Kaje tareta, kaje) Da wani irin tashin hankali ya tura yatsunsa cikin sumar kansa ya harmutsata ya furta, “Ya rabbah Ummie! Ummie! Na, ban mata adalci ba. My ALLAH help me! I beg you”.         A dai-dai nan Samraah tayi juyi, bargon daya rufa mata har wuya ta janye ƙasa alamar ya isheta. Tamkar wadda ake juyawa da remote ta juyo sosai ta inda yake tana facing ɗinsa. Saukar idanunsa a saman ƙirjinta ya sashi runtse idanunsa da ƙarfi tare da cije lips ɗinsa har sai da ya fasashi da haƙori. Sai kawai ya zube a saman gadon hannayensa duk biyu dafe da kansa. Tsawon mintina ya ɗauka a hakan kafin zuciyarsa ta gama yanke masa shawarar mafita. Fitilar dake cikin gadon ya kunna tare da haurawa gaba ɗayansa.         Cikin barci na dinga jin saukar numfashi mai ɗumi a saman fuskata. Sosai zuciyata ta yanka na buɗe idanuna. Tar-tar na saukesu akan fuskarsa data gama canjawa zuwa yanayin da ban taɓa ganinsa ba. Sake faɗuwa gabana yayi na waro idanun gaba ɗaya a kan fuskarsa. Idanunsa dake a kaina fes ya lumshe a bala'in slowly sai kuma ya sake buɗesu cikin tsakkiyar nawa. Yanzun kam kasa jurewa nayi, cikin rawar murya data lips na furta, “Na shiga uku Awwab minene haka kake y.....”      “Shiiii!!!!” ya faɗa yana sake matso da fuskarsa daf-daf da tawa tare da ɗaura yatsarsa saman lips ɗina dake rawar tsorata. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da zama low can ƙasan maƙoshinsa, ta kuma shaƙe ya furta, “Bana son surutu”........✍️ ________________ *Aleenah’s Refreshing Scent* Ta kawo muku ingatattun turaruka na ruwa (perfumes), oil, Humra, Turaren wuta and more. Kunsan kamshi dai rahama ne, ingantaccen kamshi me rike jiki da Kaya me sa nutsuwa da shiga taro cikin kasaita. Ina hajiyoyi, uwargida, Amare da kuma masu niyyar shiga daga ciki? don’t afford to miss this golden opportunity. Aleenah’s refreshing scent ta kawo muku kayan kamshi masu kyau, inganci da kuma sauki……. Akwai Kaya Kala kala na nau’in turaruka Akan farashi me rahusa. Muna Nationwide delivery 🚚 09034259662 08081693351 Koda kuɗinka sai da rabonka. Ai ƙamshi duniya ne 😘😌😌 __________ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ......Hajiya Mammah na ganin Samraah ta wuce da aikar da tai mata ta wani saki ƙayataccen murmushi. Sai kuma tabar kitchen ɗin da sauri. Fita tayi daga sashen baki ɗaya zuwa na Maash. Cikin sanɗa ta leƙa ta window ɗin falon. Kusan abinda ya faru na farko a idonta ya faru. Sai dai ganin Maash zai fita yasa hankalinta tashi. Da sauri tabar wajen, ɗakinta ta koma, ranta a dagule ta rarumi waya tai kiran Rubayya. Bugu biyu kuwa ta ɗaga...        “Gaskiya na gaji Rubayya. Ni fa shiyyasa kikaga sam babu ruwana da wani tsigunne-tsugunnen malaman nan. Gara na tashi da kaina nayi aiki nasan ni nayi sa”.        “Haba hajjajuna relax mana. Mike faruwa irin wannan ɓaɓatu haka ko shaƙar numfashi bakiyi?”.     “Ba dole nayi ɓaɓatu ba. Yaron nan fa yau ma gashi can ya tsallake abincin can bai ciba. Sai ma shirin barin gidan yake”. “Ita yarinyar tana ina?”      “Mtsoww, oho ma shegiya, ban dai ga ta fito ba daga bedroom ɗin nasa”.     “Fantastic! Ai muna da sauran hope kenan”.      “Ta yaya muke da wani sauran Hope bayan na faɗa miki yama fita a gidan, shegen kamar wani ɗan fashi yayi shigar baƙaƙen kaya yan koransa biye da shi. Wlhy sai nayi maganin shima wancan shegen ɗan masu aikatau ɗin Hayatu yake koma wa oho mas”.      Dariya Rubayya tayi da ga can, tare da faɗin, “Ai abin naki da yawa Hajiyata. Yanzu dai kwantar min da hankalinki. Zuwa zakiyi ki kafa ki tsare ta ko wane hali kada yarinyar tabar sashen nan. Ina kuma turaren daya baki”.            “Mtsoww ke ni ajiye wani batun turare har yanzu banyi ba. Banda rainin wayo taya za'ace saka turare a wuta zai sa wanda ke nesa da gida dawowa koda ba'a Nigeria yake ba”.       “Humm. Aike kinji matsalata da ke gardama. Ke dai ki gwada mana kiga idan bai yi miki abinda yace ɗin ba sai ki faɗi koma minene yazo ranki. Amma dan ALLAH ki kwantar da hankalinki kiyi komai yanda ya kamata daga nan har zuwa safiya idan komai bai farun ba sai musan matakin ɗauka.”      Badan zancen ya shigi Hajiya Mammah ba tayi duk abinda Rubayyan ta faɗa. Dan sashen Maash taje ta kunna turaren wuta. Yana fara hayaƙi tai kiran sunansa, “Awwab duk rintsi ka kwana a gida yau. Kayima yarinyar nan fyaɗe. Ka mata kaca-kaca, fata-fata, yaga-yaga. Kona minti ɗaya kada kaji tausayinta Awwab, karka raga mata”. Ta ƙare maganar tana kokkora hayaƙin da hannu tako wace kusurwa. Sai da ta tabbatar tayi duk yanda malamin yace sannan tayi murmushi da fatan dacewa ta fice.      Koda ta koma sashen nata ba kwanciyar tayi ba. Dakon zaman jiran dawowar Maash tayi tacan balcony ɗin sashenta na upstairs. Duk yanda take jin barci har gyangyaɗi na ɗibarta bata tashi ba a wajen har sai da su Maash suka dawo wajen 1-30. Jitai kamar ta daka tsalle taita ihu dan daɗi. Tana ganin ya shige ciki shi jaɗai ta ƙara sauke ajiyar zuciya. Da alama ɗan koran nashi y sauka a gida kenan. Cikin sauri ta sauka downstairs. Kai tsaye ta can baya ta zagaya cikin garden. Dan windows ɗin Maash na bedroom duk tacan baya suke. Tako ci Sa'a bai rufe ba. Sai dai gaba ɗaya labulolin a sake suke. Cikin dabara ta ɗan janye tana leƙen bedroom ɗin. Maash ta hango yana lulluɓa ma mace blanket, sai da tayi tsamm da ranta ta tabbatar da Samraah ɗince. Jitai kamar ta kurma ihu dan daɗi, amma sai ta kanne, tadai gyara tsaiwa domin ganin yaya wasan zai kaya..      Komai daya faru tun daga ciwon Maash har zuwa hawansa saman gadon akan idanunta ne. Maash na gab da cimma burinsa taji abu yabi takan ƙafarta, firgitar da tayi da jin kamar motse-motsen mutane da gittawarsu ya sata barin wajen cikin rawar jiki. Wannan shine ya hanata ganin ƙarshen faruwar komai. Amma da tabbas taso komai-da-komai sai ta ɗauka a wayarta dan tana son tayi komai da shaida. Amma ko'a yanzu ɗin ma wanda ta ɗauka ya wadatar da ita...       Hummmm 😒 ❤️💕❤️ Hannunsa dake saman lips ɗina na ture, tare da yunƙurawa zan tashi ina faɗin, “To ka tashi min a jiki mana”        A yanayin ƙara shaƙewar muryar tasa dake seizing ya ɗan sake ƙanƙance min idanunsa cikin tsakkiyar nawa, sai kuma ya shiga hura min iskar bakinsa a hankali, babu shiri na lumshe nawa idanun ina haɗiyar numfashi. Cigaba yay da hura min iskar ta saman wuyana har a cikin kunne na, gaba ɗaya naji kamar numfashina zai ɗauke. Bam ma san na sake ƙanƙamesa ba. Sautin fitar murmushinsa naji, tare da fara min magana cikin raɗa a kunnen nawa. “Ba abinda nake ma ƴan hotels ɗin kike buƙata ba kema?”.      Sosai na waro idanuna da suka gama cika taf da hawaye ina ƙoƙarin ture kansa. Amma ko gezau, cike da shagwaɓar da ban san tazo min ba na ce, “Ni yaushe nace, kada kamun sharri. Dan ALLAH ka matsa Ummie nake dafa ma abu a kitchen fa”.          “Kin san da Ummien ai kika kawo kanki nan”.      “Na kawo kaina fa? Wlhy Hajiya Mammah ce ta aiko ni kai kuma dan mungunta ka ɗaureni, ƙilama cocaine ka shaƙa min dan nayi barci.”          Bai amsa min ba, sai wani lumshe idanunsa da yay yana matse fuska alamar da abinda ke damunsa. Gabana ne ya faɗi, saboda tunawa da zancen Mama Balki akan yanayin ciwon da yake shiga akan Ummie, sai nai tunanin ko dan na ambaci sunanta ne. Cikin suɓutar baki na ce, “Baka da lafiya ne?”. Na faɗa cikin rawar murya hawaye na rige-rigen sakko min a guje.    Maimakon amsa min sai ya wani lumshe idanunsa da matso da fuskarsa kan tawa sosai. Idanuna na runtse da sauri ina ƙanƙame jikina tare da kauda fuskar tawa gefe. Sai kawai naji saukar numfashinsa akan wuyana zuwa ƙasan wuyan nawa da cikin kunnen yana shinshinata ta.           “Na shiga uku, dan ALLAH Awwab ka rufa min asiri, wai minene haka kake yi kamar wani mage”. Na faɗa cikin zaburowa a ɗan sauran ƙarfin daya rage min. Gocewa yay daga rankwafowar da yay ya koma gefena. Da alama tanƙwaɓar hannunsa da nayi ne. A zatona na kuɓuta, sai kawai jinai ya yaye bargon gaba ɗaya ya rungumeni tsam a cikin jikinsa har ina numfashi da ƙyar. Cikin kunne ya raɗa min, “Idan na rufa miki asiri ni wazai rufe nawa Samr!”.       Yanda ya ambaci sunan nawa da wani irin salon cire wasalin kowacce harafi yasa jinina yamutsawa gaba ɗaya. Kuka na sake fashe masa da shi. Ina mai jujjuya kaina dake kwance a ƙirjinsa. “Dan ALLAH Awwab ka bari zan cutu”.       “Zan fiki cutuwa idan nayi hakan”.    “Wai dan ALLAH kai baka da tausayi ne? Baka da.....”       “Nace bana son surutu”. Ya faɗa cikin muryar data sake firgita ni, yana sake ƙanƙameni. Ɗif naga hasken cikin gadon ya koma duhu. Mutsu-mutsu na farayi na son ƙwatar kai amma yamin riƙon da ban isa aikata hakan ba. Sai kawai na buɗe baki na fasa masa ƙara. “Gayyato wani nan bazai hana ni karɓar HALAL ɗina ba, dan ina da taurin kai, idan har nace ZANYI, to sai NAYI Samrh” ya ƙare maganar da rufe min baki da nasa. Daga haka bai sake bani wata dama ba koda ta shaƙar numfashi ne cikin sauƙi. Gaba ɗaya ya canja daga wancan Maash ɗin zuwa wanda ban taɓa gani ba. Tunda nake a rayuwata ban taɓa tunanin akwai makamancin irin wannan tashin hankalin na kana ji kana gani ba sai yau. Sam baya jin roƙo, baya jin magiya. Saima sake tabbatar min da shi ɗin mayuncin zaki ne da in ya ɓalle abinda ya fito nema kawai yake farauta. Tun ina iya banbancewa har komai ya ƙwace min daga gangar jiki zuwa fitar numfashi....       🌿🌿🌿🌿🌿          Matsanancin firgicin da muka shiga na ganin wanda yasa aka satomu bazai musaltu ba. Dan kuwa ba kowa bane face Maash. Duk da sau ɗaya na taɓa ganinsa a rayuwata hakan bai hanani gane sa ba. Roƙonsa muka dinga yi da magiya amma ko sau ɗaya bai ɗaga kai ya kallemu ba. Sai da ya mula dan kansa kusan mintuna ashirin sannan ya furta, “Su wanene ku?”.      Kasa fahimtar tambayar tasa mukayi, sai da yaronsa ya daka mana tsawa sannan na bada amsa ina nuna Aunty. Nace wannan Yayata ce ni kuma ƙanwatarta ce”.         Shiru bai sake tanka mana ba. Sai yaronsa ne ya tura mana tab da hoto a jiki, cikin tsawa ya ce, “Miye haɗinku da wannan yarinyar?”.      Hoton muka kalla, ba kowa bace face budurwar Mansoor. Kasa bashi amsa mukayi, sai da Maash ɗin da bai sake tankawa ba ya jawo bindiga ya nuna mu batare da yayi magana ba shima. Atake jikinmu ya fara ɓari, kallan kallo muka fara, kafin tuni bakin Aunty ya buɗe ta shiga zayyano bayani akan alaƙarmu da Samraah. Har takai aya babu wanda ya tanka a cikinsu har tsawon wasu mintuna. Miƙewa Maash dako kallonmu bai sake yi ba yayi, sai da yaje tsakkiyar falon batare da ya juyo ba ya furta, “Ka basu Account details su saka min kuɗina. Ka kuma faɗa musu tun kafin na sakasu nadama su janye abinda suke shirin ƙullawa. Ciki harda auren yarinyar wa ɗansu, idan kuma sukayi taurin kai, su kuka da kansu. Dan sai na sakasu dana sani”.       Da ga haka yay ficewarsa batare daya sake ko waiwayo mu ba. Muna ji muna gani muna hawaye yay kiran waya aka kwashe kuɗaɗensu dake account ɗin aunty da wanda ke hannuna. Sannan ya sake tabbatar mana da musan mi mukeyi kafin lokaci ya ƙure mana. Dan Maash baya magana biyu. Akoda yaushe zamu iya ganin jami'an tsaro da ƴan jarida har gidajenmu... Bayan an dawo damu a inda aka ɗauke mu bamu nema shagon tela ba muka dawo gida a hargitse. Shawara muka shiga ƙullawa, dan ko kaɗan bamuga imani a cikin idanun Maash ɗin nan ba. Dan haka muka shawarar tsaida batun auren Mansoor da Samraah, ta hanyar zuwa gidansu muka sami iyayenta maza mukayi rashin mutunci. Aunty harda marin wan mahaifin yarinyar. Wannan shine ya fusata su sukai alƙawari har abada bazasu haɗa zuri'a damu ba. Mu kuma sauraresu a yau sai sun ɗaurama ƴarsu aure da miji gangariya..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Iyakar galabaita Samraah ta kai ƙololuwa a hannun Maash ta yanda a shi karan kansa bai san aika-aikar daya aikata ba sakamakon abinda ke aiki a jikinsa. Duk da yaso binta a nutse a farko, sai dai tsafi gaskiyar mai shi, sannan ƙaddara ta rigayi fata. Tuni komai ya ƙwace masa. Tun yana iya jiyo kuka da magiya da roƙon da Samraah ke masa har ya daina ji da gane komai sai abinda ya saka gaba. Burinsa kawai ya cimma manufarsa ko zai samu sassauci da rangwamen wutar masifar dake ruruwa a jikinsa.           Koda ya cimma inda yake fatan kaiwar sai komai ya sake ƙwace masa. Wani irin fitinannen ciwon kai mai azaba yay masa dirar mikiya. Bai sake gane ainahin halin da yake cikiba, da kuma jefa yarinyar mutane da tuni numfashinta ya rabu da gangar jikinta sai da gari ya waye gangaran. Zafin rana da haskenta suka dallare masa idanu. Da ƙyar ya iya buɗesu kuwa. Ganin hasken ranar ne muraran ya saka zuciyarsa motsawa da ƙarfi, saurin kallon ƙaramin agogon dake a bed side drawer ɗinsa yayi. 7:2am. “Ya subahanallah”. Ya faɗa yana yunƙurawa gaba ɗayansa zaune. Tashin hankalin tuna baiyi fa ko sallar asuba ba ya sashi zabura ya sauka a gadon batare da hankalinsa ya kai kan Samraah da har yanzu ke a sume ba. Cak ya tsaya yana kallon jikinsa, sai kuma ya kalla gadon da sauri zuciyarsa na tsitstsinkewa. Ji yay gaba ɗaya ƙafafunsa na neman kasa ɗaukarsa, dan take komai daya faru a daren na jiya ya shiga dawo masa dalla-dalla. Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi, cikin rawar hannu ya kai hannun nasa saman blanket ɗin kusan rabin jikinta ke a cikinsa. Janyewa yay a hankali zuciyarsa na cigaba da bugawa tamkar zata fito ta bakinsa. Da wani irin sauri ya saki blanket ɗin yay baya yana waro gaba ɗaya manyan idanunsa kalar na maguna waje. Blue ɗin tsakkiyarsu ya sake fitowa raɗam. “Innalillahi wa'inna-ilaihi raji'un” ya shiga ambata. Sai kuma ya tura hannunsa cikin sumar kansa ya hargitseta tare da maidata gaba yay kuma baya da ita yana furzar da wani irin zazzafar huci.          Rasa ma abinda ya dace yayi yay, sai da zuciyarsa ta sake ayyana masa (sallah) sannan ya zabura bathroom bayan ya sake jan blanket ɗin ya rufamata. Wanka yake amma maƙoshinsa sai kai-kawo yake. Ji yake tamkar ƙirjinsa zai fashe. Gaba ɗaya hannayensa ya tura cikin gashin kansa da ruwa ke jiƙawa. Da ƙarfi ya ƙwala kiran sunansa jikinsa na wata irin karkarwa. “Awwabbbbbb!! Are you mad?!”.      Da gaske zuciyar ƴan maza ta motsa, dan a take idanunsa gaba ɗaya suka gama juyewa. Wani irin jiri ya fara yawo kansa. Tako ina jijiyoyin jikinsa sun bayyana kansu fiye da yanda gashin jikinsa ke a mimmiƙe. Ji yake kamar yayta dukan kasan ko zai samu sassaucin abinda yake ji. Sai dai babu dama. Dole ya gaggauta yin wanka ya fito. Sallar da zuciyarsa keta sake jaddada masa ya fara gabatarwa. Gara yayi ko zai dawo a hayyacinsa ya fuskanci mike damunsa. Koda ya idar sai ya kasa motsi. Yana zaune kawai a saman sallayar ya zubama guri ɗaya idanu, sai Adams apple ɗinsa ne ke wani irin kai-kawo da sauri-sauri. Ga idanunsa gaba ɗaya sun gama juyewa. Yafi mintuna goma a wajen kafin yay jarumtar miƙewa. Kai tsaye gadon ya nufa, ya kai zaune ta gefen kanta da ɗaukar goran ruwa dake a bed side drawer ya zuba a hannunsa kaɗan sannan ya shafa mata a fuska. Shiru bata motsa ba, dole ya sake yin haka, sai da yay sau uku kafin ta zabura. Sai kuma ta ƙwalla ƙara gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa. Sai rawa jikin nata yake kaf-kaf-kaf abin tausayi. Da farko kasa ko motsi yayi, sai kuma a hankali ya kai duka hannayensa biyu a saman bayanta ya manneta a jikin nashi da ƙyau, tare da lumshe idanunsa sambatunta mai cike da roƙo da magiya da neman agaji na ratsa masa cikin kunne.        Sunfi mintuna biyar a hakan kafin ya buɗe idanunsa a hankali. Da ƙyar ya iya buɗe lips ɗinsa cikin wata iriyar muryar da baka isa fassara yanayin da yake a ciki ba ya furta, “Stop crying”.         Zabura Samraah tayi, sai kuma ta fincike jikinta gaba ɗaya dake karkarwa. Da alama jin muryar tasa ne ya firgitata. Wani irin fisga numfashinta ya shigayi, ta dinga jan jikinta dake rawa baya daga nasa da ƙyar tana jujjuya kai. Hawaye kam ai gaba ɗaya sun gama wanke fiskarta har zuwa saman wuyanta. Sai kawai ta tafi zata zube gaba ɗayanta alamar numfashin nata ya jaa. Da sauri ya riƙota ta faɗo jikinsa. Tare da yin cak ya zubama fiskarta data gama dagulewa firgitattun idanunsa kawai. Tsahon mintuna biyu ya jasu yuuuu kamar zai lunshe sai kuma ya buɗe. Kwantar da ita yay a hankali, tare da jan blanket ɗin ya sake rufa mata a jiki. Bathroom ya nufa bisa umarnin shawarar da zuciyarsa ke bashi. Sai dai me, yana tsaka da haɗa ruwan ɗumi ya ji hayaniya. Tsai yay da ransa alamar saurare, ji yay hayaniyar na sake matsoshi, jin tabbas a sashensa ne fa ya sashi miƙewa tsaye sosai. Sai dai kafin yayi wani yunƙuri yaji saukar muryar Hajiya Mammah a tsakkiyar kunensa tabbacin ta shigo ne har cikin bedroom ɗin nasa.       Yanda take ƙwala kiran sunansa a haukace ne ya sashi buɗe ƙofar ya fito a nutsensa. Fitowar tasa dai-dai da buga wani uban tsalle da tayi tana zabga salati. Sai kuma ta shiga nuna Samraah dake a saman gado. “Na shiga uku ni Nafi, Awwab mi zan gani haka? Wacece wannan a gadonka? Miya kawo mace ɗakinka a irin wannan lokacin kai da ba aure ba!! Mu'azz! Mu'azz!!”. Ta shiga ƙwala kiran sunan Paah.       Sai lokacin ne Maash yay wani irin datse haƙoran ɓacin rai yana watsa mata wani irin shegen kallon takaici, a zafafe ya nufi ƙofar da ake ƙoƙarin buɗewa ya dinkare. Itama a kausashe cike da gizago yay mata nuni da ƙofar yana faɗin, “Ki fita anan”.     “Anƙi a fitan dan ubanka, yanzu Awwab kamana adalci kenan. Yarinyar mutane kai ma fyaɗe!! Shiyyasa tun dare muke nemanta amma ko sama ko ƙasa a gidan nan. Kashemu kake son kayi? Can ga rundunar ƴan sanda nan da farar safiya sunzo kamaka, ashe kana anan kana aika-aika kuma”.           Zaka rantse bai jima mitake faɗa ba, dan ƙoƙarin sakama ƙofar key kawai yake yi, ga shi tacan baya kuma Paah nata bugawa da kiran sunansa. Zuwa yay zai wuceta yaji Paah ya fashe da kuka yana sake buga ƙofar. Cak ya tsaya daga yunƙurin isa gadon da yake yi. Ya ɗauki kusan minti ɗaya a hakan kafin ya motsa jikinsa a hankali ya koma baya, ƙofar ya buɗe, sai dai baice komai ba ya sai kallon Paah. Kafin ma yay magana Paah ɗin shi ya kamo hannunsa yana faɗin, “Muhammad akwai damuwa fa, gidan nan zagaye yake da jami'an tsaro wai zasu kamaka. Muhammad mike faruwa ne? Mi kayi musu?”.      Idanu kawai ya zubama Paah ɗin tamkar wani gunki, dai-dai nan Hayatu ya shigo shima a hargitse. Daga shi sai jallabiya alamar fitar bata shiri bace ba. Ko iya gaida Maash ɗin baiyi ba ya fara magana cikin tashin hankali. “Sir akwai shiri a wannan al'amarin babba. Dan ALLAH karka fito komi zasuyi. Ni zan bisu muje, ba sunce dai tambayoyi bane zan amsa musu duk irin wadda suke buƙata”.      Shiru Maash ɗin nan ma bai tanka ba. Sai juyawa yay ya watsama Hajiya Mammah wani irin kallo. Cikin silent voice ɗin nan tashi a daƙile ya furta, “Out!”.         “Out? Awwab ni kake cema out!”.     Cike da fusata ya sake furta, “I say Out”. Ya ƙare maganar yana matsa mata a hanya alamar dai ta fitan kawai. Gaba ɗaya jikin Mammah ya gama sanyaya. Mamakin Maash ya gama kasheta da rashin mutuncinsa. Wata wutar bala'i data hango cikin idanunsa ya sakata fitar, cikin ɓacin rai ta ce, “Mara mutunci fitsararre gani na fitan, ita kuma yarinyar daka gama wulaƙantama rayuwa a ciki fa ko sai ta mutu zaka fiddo ta?.”          Cikin mamakin furucin Hajiya Mammah ɗin duk aka zuba mata ido. Ganin ta samu nasarar samun attention ɗin kowa a wajen ta fara matse ƙwallar munafunci. “Yarinyar da ake nema tun daren jiya ce a ɗakinsa kamar matacciya. Na tambayesa miya faru yaƙi amsa min, shike nan Awwab bazai barmu muji da tashin hankali ɗaya ba fisabilillahi. Idan ba zubar da mutunci ba miya kawota cikin ɗakinsa?”.        Kallonsa Paah yayi, cikin ɗan zafi-zafi ya ce, “Muhammad mike faruwa? Wace yarinya ce a ɗakin ka? Mi take yi kuma?”.      Shiru tamkar bazai tanka ba. Sai kuma a hankali batare daya kalli Paah ɗin ba ya furta, “Kayi haƙuri abinda ya shafeni ne Paah”.          “Abinda ya shafe ka?”.      Paah ɗin ya maimaita da mamaki. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Muhammad wai miyyasa kai bazaka canja bane? Yanzu wanne kake son mu ɗauka a cikin waɗan nan tashin hankalin? Jiran da jami'an tsaro ke maka a waje runduna guda tamkar wani shugaban kidnappers kona yan fashi? Ko kuwa abinda Adda ta faɗa ka aikata anan?”.       Idan dutse ya motsa to Maash ya tankama Paah ɗin. Sai ma dai-dai nan TJ ya shigo a haukace yana kuka. Ƙasa ya durƙushe cikin matsanancin tashin hankali yake sanar musu gafa Hayatu can zai miƙa kansa ga DSS ɗin can. Sannan su kuma sun tattare ma'aikatan gidan har da su Mama Balki wai zasu wuce da su. Idan sunyi hakan Boss dole ka miƙa kanka wai”.         Idan ma yace baya a cikin tashin hankali yayi ƙarya, sai dai jarumtarsa ta shanye komai baka isa karantar abinda ke akan fuskarsa ba bayan canjawar launin idanunsa. Shi ba damuwarsa masu jiran nashi a waje ba. Yarinyar nan dake buƙatar taimakonsa itace tashin hankalin sa. A fili kam komai baice ba face raɓa Paah da Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama, sai kawunsa Abdullahi da matarsa ya fice abinsa. Cikin sauri Paah da Tj da Uncle ɗin suka take masa baya. Ganin haka itama matar Uncle ɗin ta bisu, aka bar Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama na kallan kallo. Sai kuma suka zabura suma suka bisu saboda kururuwar ihun da sukaji da basu san kona wanene ba ga ƙarar harbin bindiga......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Fitowarsa cikin takun nan nasa na isa da izza tamkar babu wani abinda ke damunsa ya saka su Azizat nutsuwa. Dan dama sune ke ihun saboda harbin da jami'in yayi sama. Duk da kasancewarsu jami'an tsaro kwarjininsa da gizago sai da ya tsarga musu zukata. Wani irin tsaiwar ƙasaita da zuba ma jami'in daya ɗaura bindiga a saman kan Hayatu yayi har kusan minti ɗaya, sai kuma ya miƙama TJ dake ta bayansa yana rawar jiki hannu, a hankali ya furta “Phone”.         Da sauri TJ ya zaro wayarsa ya miƙa masa cike da girmamawa. Batare da Maash yace komai ba, a kuma tunanin kowa wani zai kira, amma sai kawai sukaga ya shiga ɗaukar hoto. Sai da yay a ƙalla kala huɗu kafin ya tura wayar aljihu ya sake gyara tsaiwarsa. Cikin daƙilalliyar muryar da sauke idanunsa akan ogansu ya furta, “Wace doka ce ta baku damar shigowa cikin gidana kuyi harbi batare da kun samu wani dalilin yin hakan ba? Wace doka ce ta baku damar shigowa har cikin gidana kuci zarafin ahalina? Bayan ba'a turoku domin su ba an turoku ne gareni ni ɗaya”.         Rasa wace amsa ya kamata su bashi sukayi, sai ƴar kallan kallo suke. Sai da ogan nasu yaga zasu muzanta cikin aro jarumtar dole ya matso inda Maash ɗin ya ke ya miƙa masa takardar hannunsa. “Munada cikakken lasisin shigowa gidanka Mr Awwab El-Mu'azz Adams”.      Da ga shi har takardar Maash yabi da kallon wulaƙanci batare da ya amsa ba. “Baka amsa min tambaya ta ba ai”. Ya faɗa a daƙile.          Kame-kame jami'in ya fara cikin son aro jarumtar dole. Sai kawai Maash ya zare takardar daga hannunsa yana faɗin, “Okay bama sai ka amsa ba anan. Next time kawai”. Ya ƙare maganar cike da rainin wayo yana kallon takardar. Yana gama karantawa ya saki wani shegen murmushi, a saman lips ɗinsa ya furta “Mr Paul” dan ya fahimci kai tsaye daga inda saƙon yake. Nuni yay ma Hayatu da ya tashi. Babu musu kuwa ya miƙe ya nufosa. Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar TJ daya amsa da key ɗin bedroom ɗinsa ya miƙa masa.  “Ka bama Mama ta dubata. Idan akwai matsala kuje da ita asibiti zan sameku acan. Juliet taje ta ƙarasa meeting ɗin jiya”.      “Amma sir...” Ɗauke kansa yay alamar baya buƙatar jin komai da ga Hayatun. Tj ya kalla tare da faɗin, “Bani key ɗin mota”. Cikin sauri TJ ya zaro ya miƙa masa. Batare da ya kalla ko inda su Hajiya Mammah suke ba ya matsa ga jami'an tsaron. Wani ne ya yunƙuro da Handcuffs a hannunsa da sauri. Wani banzan kallo da Maash ɗin ya masa bai ma san ya taka burki ba harda cin tuntuɓe. Wucewarsa yay ga motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin driver. Sai da yazo saitin ogan nasu ya tsaya, batare da ya kallesa ba ya furta, “Zan iya wucewa ni kaɗai?”.          Kallonsa kawai shugaban jami'an yake. Dan shi kam yanzu yake sake tabbatar da rashin mutuncin Maash ɗin da ake faɗa ya zarta duk yanda aka gaya masa ashe. Ga yaron da shegen kwarjini. Duk da kasancewarsa jami'in tsaro, a shekaru kuma zai iya haifar Maash ɗin, wata irin shakkarsa yake ji har ƙarƙashin zuciyarsa. Har takai ya fara jin nadamar amsar wannan aikin da yay. Yaransa biyu ya bama umarnin shiga bayan motar, shi kuma ya shiga gaba kusa da Maash ɗin. Sauran kuma suka fita da sauri wajen gate inda motocinsu da sauran ƴan uwansu suke.          Shi Maash ma sai abin yaso bashi dariya ganin yanda aka cika kusan rabin street ɗin da jami'an tsaron kai kace sunzo kamo wani ƙasurgumin ɗan ta'adda ne daya addabi duniya. Lalataccen Murmushi ne ya suɓuce masa kaɗan. Dan in ba kallonsa kake ba bama zaka taɓa fahimtar yayisa ba. A nutsensa yake jan motar tamkar wanda baya so, har suka iso babban headquters ɗin DSS ɗin dake a garin na Lagos babu wanda yay ko tari a motar.....        ★★★       Motocin na gama fita a harabar gidan Hayatu yay wani irin sauke numfashin damuwa. Sai kuma ya maida kallonsa gasu Paah dake ƙoƙarin nufar motoci alamar zasubi bayansu. Nufarsu shima yayi, cikin girmamawa ya dakatar da su. Bayani yay musu akan suyi haƙuri kar suyi gaggawar binsu har sai ya sanar da lawyers ɗinsu yanzu.      Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shima sai yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran lawyers ɗin nasu har su uku. Yayinda shi kuma Paah ke ƙoƙarin neman Baba prof.. da baya ma ƙasar kusan sati uku kenan. Hayatu na gama kiran lawyers ɗinsu ya isa ga Mama Balki dake ta faman share hawaye ita da su Bahijja. Key ɗin da Maash ɗin ya bashi ya bata, tare da mata bayani. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke a karo na farko, dan dama hankalinsu a matuƙar tashe yake tun sabe na rashin ganin Samraah ɗin, ita a zatonta ma ko guduwa tayi. Dan ko'ina na gidan babu inda ba'a duba ba har sashen Hajiya Babba daya zama na farko amma babu ita. Batare da kowa ya farga ba Mama Balki ta zare jikinta sashen Maash. Dan su Hajiya Mammah sunata bige-bigen waya ne...        Matuƙar tausayin Samraah ne ya cika Mama Balki har sai da tayi hawaye. Bata kawo a ranta wani dalili ne ya saka Maash yin wannan ɗanyen aikin ba, sai ƙila gardama Samraah ɗin ta masa. Amma yanda tasan Maash da tausayi da ƙoƙarin tsare hakkin kowa a rayuwa da mamaki wannan al'amari. Dan gaba ɗaya al'amarin babu tausayi a ciki. (Koda yake ƙila shima ya kasa riƙe kansa ne) zuciyarta ta ayyana mata tana mai ƙoƙarin ganin bataji zafin Maash ɗin ba a ranta. Ruwa ta shafa ma Samraah ta kawo numfashi, kukan data fashe da shi cikin zabura ya saka Mama Balki riƙota jikinta ta rungume. Sai kawai itama ta fara hawayen tana lallashinta.       Jin muryar Mama Balki yanzu ba shi ba ya sakani jin nutsuwa. Sake ƙankameta nai cikin kuka ina mata magiyar dan ALLAH ta fita dani a ɗakin, idan ta barni kasheni zaiyi bashi da imani. Lallashina ta shiga yi da kalamai masu sanyi, sai da taga na sake nitsuwa sannan ta kwantar dani tana faɗin na jirata. Hawayena na cigaba dayi harta dawo bayan wasu mintina. Babu abinda ke mun kai kawo sai abinda ya farun. Sam hawaye sun gagara ƙafe min, koda Mama Balki ta kamani domin tashi sam na kasa. Sai ma kukan fitar hankali dana sakar mata dan wata irin azaba ce ta ratsani tun daga yatsun ƙafata har tsakkiyar ƙwalwata. Itama ganin bafa zan iya tashin ba ya sakata sake jin matsanancin tausayina. Rigar wankansa data ɗakko daga bathroom ɗinsa ta saka min ta sake gyarawa, sai kuma ta kamani cike da jarumta ta ɗaga gaba ɗaya na. Haka tana nishi baiwar ALLAH ta kaini har Bathroom ɗin. Sai da tamun gajeriyar nasiha da lallashi sannan ta taimaka min na shiga ruwan data haɗa. Bakina na dumtse ina mai fashewa da kuka jikina na rawa. Haka ta rirriƙeni tana cigaba da mun nasihar duk zaburar da nake bata yarda nabar cikin ruwan ba sai da ya huce. Wani ta sake haɗawa, sai da tamun haka sai uku abinka da dattiwar data san takan duniya sannan ta baroni nayi wanka.        Kuka naci sosai har sai da tamun knocking ƙofar sannan nayi wankan. Cikin jarumta da son daurewa na ɗauka wata rigar wankan na saka dan wancan ta jiƙe saboda bata cireta a jikina ba ta sakani a ruwan da ita. Duk yanda naso taka ƙafafuna na fita da kaina hakan ya gagara. Kuka na sake sanyawa mai sautin da har sai da Mama Balki taji ta shigo. Kallona ta tsaya yi, kafin cike da tausayi ta furta, “Samraah bazaki iya tafiya ba yanzu ma?”.         Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye. A sanyaye tace, “Kiyi haƙuri kinji, in sha ALLAHU zaki ci riba a rayuwarki tunda bata hanyar banza kika tsinta kanki a wannan halin ba. Amma lallai dole zamuje asibiti kenan”.      Kuka na sake fashe mata da shi batare dana iya cewa komai ba. Yanzun ma itace ta fiddoni. A saman kujera ta ajiye ni. Ta gyara ɗakin fes kamar bashi ba. Dan hatta da bedsheet ɗin ma ta canja wani. Kayana da ban san waya kawo mata ba ta bani tace na saka. Ita kuma ta koma bathroom ɗin bayan ta shinfiɗa min abin salla. Kayan na saka ina hawaye na sakko domin yin sallar, da ƙyar na iya yinta a tsaye, inayi ina kuka. Ina idarwar na zame a wajen na kwanta, kafin mama Balki ta fito zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni.      Barci ya ɗan fara figata mama Balki ta tasheni nasha tea, kasa sha nayi, sai kuka nake mata kawai. Baiwar ALLAH duk ta shiga damuwa sai lallashina take yi. Wani barcin ne ya sake figata, gigitaccen bugun ƙofar da ake ya farkar dani. Buɗe ƙofar Mama Balki taje tayi, ɗauuuu kake jin saukar mari a fuskarta. Kafin Hajiya Mammah ta hankaɗota ciki. Taga-taga tayi zata faɗi ALLAH ya taimaketa ta rike ƙarfe net ɗin gado. Har cikin rai naji zafin marin nan da taima Mama Balki yau. Cikin matuƙar masifa ta shiga surfama Mama Balki zagi wai itace kawaliyarsa dake kawo masa yara ashe yana musu fyaɗe, to yau kam sai sunci ubanta a gidan nan. Duk yanda take son musu bayani kowa yaƙi yarda da ita, sai tambayoyi suke jefe mata kuma sunƙi bari ta basu amsa.            Shiɗewa numfashina ya farayi saboda yanda hayaniyar Hajiya Mammah ke shiga har cikin tsakkiyar kaina dake ciwo. Sama-sama nake jiyo muryar Hajiya ƙarama na bada shawarar kaini asibiti. Daga haka ban sake gane komai ba........✍️ _Huuuum tofa masu karatu ƙaƙa raƙa ƙaƙa.._     *_Yaya zata kaya kenan? Maash zai sanarma ahalinsa wacece Samraah a yanzu ko zai cigaba da ɓoyewa?._*     *_Shin waye Mr Paul daya saka a aka kama Maash? Mi kuma kuke tunanin zai faru?_*    _Samraah!! Samraah!! Wane hukunci kuke tunanin zata iya ɗauka akan Maash kan abinda ya faru, da labarin da taji na al'ummar wannan gida?._      *Hajiya Mammah?* *Hajiya ƙarama?* *Paah?* *Uncle Abdullahi da matarsa?* _Shi kansa Maash bakwa tunanin akwai abinda yeke binnewa kuwa?._ _Gidan Abba, gidan su Mansoor, nan ma fa duk akwai sabuwar cakwakiya._     *_Hummm kar dai na cikaku da surutu, mu tara ranar Monday in sha ALLAHU. Banda pages dole zanyi hutun weekend ɗin nan insha ALLAHU. Dan munzo gaɓar da komai yake buƙatar fita da fitarsa. Ku muje zuwa TSUTSAR NAMA BOOK 3 Guys._* _Bana son naga numbers ɗin na tsaho ganda rubutun nake ji wlhy, dan haka zamu tafi part 3 yanda zamuyi maza kafin salla mu kammala in sha ALLAH 😘😘😘_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*