ƘASAITA NA MARYAM KABIR MASHIƘASAITA NA
Page 1
Mota ƙirar ƙasar (South Korea) ce ta tsaya a dai-dai ƙofar wani kanti, wanda zamu iya kiranshi da suna na tailoli, ma’ana shagon ɗinki kenan,Mai suna Almansir Tailoring and Fashion Design Company. Mutumin ƙofar shagon shi ya nuna mana cewa mata da maza na iya kai ɗinki a shagon. Ruwan toka ash colour shi ne fentin motar, wanda zamu iya kiran motar da suna KIA Saloon.
Farar yarinya ce,za mu ce ko budurwa, ita ce matuƙiyar motar, wacce ta fito sanye da riga da wando zubin (Suits) irin na ƙasashen tsallake (Abroad) amma na mata, kenan mai shimi mai babban maƙwancin hannun kafaɗa, sai doguwar riga ƙwat ta ɗora a sama, wacce ta kai mata har wucewar gwiwa.
Maɓallin tsakiyar doguwar rigar ƙwat ɗin ne kawai ke maƙale da rigar, ruwan toka ne ash colour kalar kayan nata. Takamin ƙafarta kuwa baƙi ne, tare da farin gilashi manne a saman dogon hancinta, wanda mafiya yawan likitoci ke sanya irin shi.
Babu komai a hannun ta sai kan wayar zamani ta Ipad,gashin kanta kuwa a sake yake wanda za mu iya cewa ya kai tsakiyar bayanta,babu wani alamar ɗanƙwali balle mayafi a saman kanta, kallo ɗaya za ka yi mata sai ka maimaita goma a lokaci ɗaya baka sani ba.
Tabbas yanayin yanda take kulle motar ta kawai zai iya nuna mana mace ce mai taƙama da ƙyan da Allah ya bata, zan iya cewa kuma ita kanta ta san duk inda ta gifta sai ta tsayar da ayyukan mutane, shi yasa na fahimce ta mai jiji da kai.
Doguwa ce, amma ba shal ba, yanayin kiran zubin jikinta kuwa,za mu iya kamanta shi da na Pretty Zeeta, ƴar ƙasar India. Kai kallo ɗaya ma ka yi mata za ka iya ce mata ba ƴar ƙasar Najeriya ba ce, saboda yanayin zubinta ya fi kama da na ƴan (Miss World),Sarauniyar ƙyau ta duniya.
Yatsun hannunta kuwa zara-zara suke, waɗanda suka sha fentin ƙwalba (Lamp paint) a saman faratanta, shi ma ruwan toka, faratanta sunyi tsayi kamar ƴan kanti, ta saka a yatsun ta. Sai da ta ɗan ɗauki sakan biyar, sannan ta sa makulli ta rufe motarta.
Ɗagowar da zata yi kuwa, sai da ta rausaya da gashin saman kanta da ya zubo mata a fuskarta,a lokacin da take kulle motarta, sai da ta duba hagu da damarta, sannan ta tsallaka titin da ke a gaban,MONAK STORE, shi ta shiga.
Tsayin minti talatin da baƙwai na yi ina dudduba kayan ƙwadayin da ke kaini duk wata (Super store), cakulet (chocolate) dasu Chingam (Chewing gum) sannan biskit (Biscuits), irin waɗanda na mayar abinci na,kayan ƙwalliya kuwa sai dai in dinga ɗaukar kala-kalar jam baki da man leɓe (Wetlips).
Leda ce a hannuna wacce aka cika ta da rubutun sunan kantin da na fito,ƙarar wayar dake hannuna, ita ta ɗan ɗauke mini hankali,a bisa tafiyar da nake yi.
“Ka san dai bana magana a titi, sai dai kayi haƙuri bayan mintuna arba’in ka bugo,a wannan lokaci na isa gidan Aunty,okey, thank bye.”
Maganar da nayi a waya kenan da (Proposed) ɗin da na tsayar a matsayin wanda zan aura nan da ɗan lokaci ƙanƙani, don ma ina ja masa rai, saboda tunanin barin gida, wannan yake ɗan tayar mini da hankali.
Zamu iya cewa yanayin da muke ciki na sanyi duk da dama mun san Garin Jos gari ne mai ni’imar gaske, dalilin haka ne ma Turawa da sauran fararan fata,sun fi yawa a can, saboda sabo da suka yi na jin sanyi a ƙasashensu.
Wannan yanayi na yau ya sha bamban da na kullum,tun da yau sanyin da sauƙi, sai dai iska da ake hurawa a hankali mai ratsa jiki, wadda za ta iya saka nishaɗi. Na ɗaga kaina sama ina kallon giza-gizan sanyi na tafiya cikin natsuwa,gashin kaina kuwa iska ke yi mini wasan ball da shi, ina faman buɗe fuskata.
Tabbas na hango motoci a tafe, amma ganin nesa suke da ni yasa na kalli ɗaya gefen nawa, na tsallaka titi, iska ta watsar mini da gashin kaina wanda ya watsu a fuskata, ina ƙoƙarin buɗe fuskata ne na ji mota ta kai mini zungura, take na faɗi zaune a ƙasa tsakiyar titi.
Ƙarar jan birki ita ta sa na ɗora hannayena a saman kaina, ina jiran ƙarfen Nasara ya bi ta saman kaina. Tsawa na ji an daka mini da ƙarfin gaske, wannan yasa na yi saurin ɗago kaina, haushi ya kama ni a take da na ga ashe daga motar baya ce ma ake yi mini wannan tsawar, ta gabana kuwa mai zubin (Cardillale Lemousine) wacce ta banke ni kenan doguwa mai ƙofa uku.
Baƙin gilashi ne daɗe da ita,babu alamar zugewa, balle in samu tabbarakin ganin ko naji ciwo, wannan ya ƙara tunzura mini zuciya,na miƙe da sauri na sa hannuna na daki gaban motar, daga sama suka faɗo,ko ko ta ƙarƙashin ƙasa? Oho ƙartin mutane ne masu kaya layi-layi, wanda na ga layin ya ƙunshi kala biyu. Dogarawa kenan, waɗanda aka fi saninsu a gidajen masarautu.
Ko gama gane su banyi ba, cikin dishi-dishin idanuna na ga wani ƙato daga cikin su ya ɗaga hannu zai kai mini mari,cikin zafin nama na riƙe hannunsa, duk da sai da hannuna ya yi kamar zai karye biyu,tsayawar shi kuwa kusa da cinyata, saboda yafi ƙarfina.
Ƙwanƙwasa baƙin gilashin muka ji anyi daga cikin motar nan ta gabanmu, shi yasa gaba ɗayanmu hankalinmu ya koma ga gilashin da yake sauka a hankali. Ƙyakkyawan mutum ne,sanye da manyan kaya na alfarma,ƙwance a kusurwar mota (Owner’s Corner) zan iya ganin gashin bakin fuskarsa mai suna ƙwata miliyon (Quater Million) farin gilashi ne manne a fuskarshi, duk cikin sakan ɗin da bai wuce uku ba na karanto hakan.
Sai da ya yatsina tamkar mace, sannan ya motsa jikinsa da ƙyar, ya ƙara gyara ƙwanciyarsa a kusurwar motar, da ƙyar ya ɗaga hannunsa ya cire gilashin fuskarsa. A tunanina magana zai yi, amma sai naga ya yi masu alama da kai, ma’ana ya girgiza kai,hannunsa mai gilashin nan ya ɗan ɗaga ya yi masu alamar su koma cikin motocinsu. Daga wannan kuwa sai dai na ga baƙin gilashin motar nan na komawa sama mazaunin sa a hankali, har gilashin ya kusan rufewa, sai na ga an cillo bandir ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ƙwaya ɗaya,an ja motar an tafi.
Ban san lokacin da na kaiwa bayan zumɓutun motar nan duka ba da ƙarfina, amma ko tsayawa ma bata yi niyyar yi ba. Wucewarsu ke da wuya mutane suka taru a kaina suna yi mini sannu, a cikin su ne wata mata,ɗaure da zani da riga masu buɗaɗɗen hannu ta kama ni, da ganin ta kaga yare, da harshen Turanci ta yi mini maganar sannunta.
“Sorry wooo!”