Garkuwan Fulani

Garkuwan Fulani Na Aisha Aliyu Garkuwa

Garkuwan Fulani Na Aisha Aliyu Garkuwa

YAHUNDE! Babban birnin ƙasar Cameroon.

Cikin wani kekyawan rugar FULANI mai tarin al’barkatun duniya.
Kota wani sashi Allah yayiwa Rugar Arɗo Babayo, ni’imomi na musamman, makiyaye ne cikakkun Fulanin ƙasar Cameroon.

Ranar wata jumma da yammaci la’asar sakaliya, makiyaya nata dawowa gida yayinda kota ina. Shanu tumaki raƙuma awaki zabbi keta kai komo ko wanne na nufar garken ma-mallakinshi domin ko dabba tasan uban gijiyinta,
Garken Arɗo Babayo yana ɗaya daga cikin garken da babu kamarsa a nahiyar Afirka baki ɗaya,
Yanada MAKIYAYA a ƙala mutun arba’in.

Garin ya fara duhuwar sanire alamun yanayin sanyin damina da ake ciki ko ina yayi kore shar ga tarin tsirrai kana ga igiyar ruwa da yayiwa rugar Babayo ƙawanya,

Wasu dattawane a zaune bisa ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake ƙofar gidan Arɗo babayo Farin dottijon ne mai cikar zarra da mutun taka ke zaune a tsakiyarsu, kana sai wasu manyan mutane dake zagaye dashi.
A gefen damanshi kuwa wani Babban mutun ne mai cikar zarra da wadatar zuciya ga tarin alamomin mutuntaka da cikar imani da haiba, bisa dukkan alamu tattaunawa sukeyi kan abinda ya shafi rayuwarsu.
Da sauri Arɗo Babayo ya ɗago kanshi ido ya zubawa sashin damanshi, inda ya hango wasu ƴan saffa-saffan samari guda huɗu suna biye da ƙatuwar suntsuwar Boleru babban cikinsu ne a gaba wanda zai kai shekaru 15 sa mai binsa wanda zai kai shekaru 13 sai mai bin masa da zai kai shekaru 11 kana sai ƙaramin cikinsu da bazai gaza shara 9 ba, gudu sukeyi sosai da iya ƙarfinsu sun tasa tsuntsuwar Boleru nan a gaba wacce ta kasa firewa sai gudu takeyi da sawunta biyu, bisa dukkan alamu tsuntsuwar tanada tsohon ciki mai girma.
Gudun da takeyi gudune na ceton rai.
Arɗon Babayo daya buɗe baki kenan da nufin zaiyi magana sai kuma ya juyo ya kalli kekyawar yarinya ƴar kimanin shekaru 8 a duniya wacce take kan cinyar mutumin nan dake gefen damanshi.
Ta miƙe da sauri cikin tsananin azama da harshen fillanci da ƙarfi tace.
(“Acce mo) Ku barta”. Sai kuma ta juyo ta fuskanci mutumin da take zaune kan cinyarshi cikin kaɗuwa da firgici da alamun tsananin tausayawa tace.
(“Appa a vi’a ɓe acca tokkugomo nɓe naunanmo) Appa kace su dena binta zasuji mata ciwofa”.
Murmushi Arɗo Babayo yayi tare da cewa.
“Kai Gainako ku barta zaku kamata a hankali ai”.
Da sauri wanda aka kira da Gainako yace.
“Baffa Giɗaɗo ne yace mu kama mishi ita mu yanka mishi”.
Da sauri suka juyo kan ƴarinyar jin wani irin ihu da tai tare da cewa.
“Ku yankata kuma, Appa kajifa wai zasu yankata, wayyo Appa kace musu kar su yankata, gashifa tanata kuka gashi sun sa taji ciwo a hannunta yanata zunda jini”.
Da mamaki suke kallon ƴarinyar sabida furucinta na wai hannunta yaji ciwo yana zubda jini, ina tsunstsuwar Boleru ina hannu?.
Wanda ta kira da Appa ne ya jawota gabanshi tare da cewa.
“Parvina tsuntsu kuma tanada hannune?.”
Da sauri ta miƙe tare da ɗaga murya tace.
“Ba tsuntsu bane Appa wlh mutunce gata nan da ciki gashi ma tana kuka tana-ta kare cikin jikinta”.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Boleru ido su dai Allah ya gani gaba ɗayansu tsuntsuwa suke gani tana guduwa da kyar wanda kuma kowa ya ganta yasan tanada tsohon cikine.
Giɗaɗo ne wanda shine ƙarami yaron ɗan shakara 9 kuka yasa tare da cewa.
“Wayyo ya Gainako kayi sauri ka kamo min ita karta gudu”.
jin haka yasa ƴarinyar nan da aka kira da Parvina ta miƙe da gudu tabi bayansu tana gudu tana kuka wanda har ga Allah daga cikin zuciyarta yake fitowa kuma ita ba tsunstsuwar Boleru take ganiba a zahiri a fili da kuma baɗinin Allah ya nuna mata mutum take gani kekyawar mace mai cikar sura da kamala kana ga ƙaton cikin dake jikinta wanda haihuwa yau ko gobe.
Ihu takeyi tana binsu tana cewa.
“Dan Allah ku barta zataji ciwo Wayyo Appa kazo mu ceceta zasu kasheta.”
Ihu tasa da dukkanin ƙarfinta tana yarfa hannu cikin gigita take kurma ihu lokacin da su Gainako suka isa kan tsuntsuwar Boleru suka danne fikafikinta suka kama suka medata baya.

Ihun da tayine yasa gaba ɗaya dattawan nan suka miƙe tsaye suka biyosu a guje dan ihun nata ya cika illahirin rugar babu wanda zaice baiji ƙaranta ba dan saida tsaunuka da kogin da suke gaɓarsu ya amsa da sautinda da take cewa.
“Wayyoooooooo! Appaaaaaa! zasu kasheta, sun karya mata hannu”.
A gigice suka ƙaraso wurin wanda ganin yadda take a gigice yasa Appa kamata da sauri, yayinda ita kuwa taketa son zillewa tana fiffizgewa daga hannunshi, Arɗo Babayo kuwa tsawa ya dannawa Gainako tare da cewa.
“Kai! Kai!! Kai!!! Gainako sake tsunstsuwar nan saketa”.
cikin sanyi Gainako ya sake tsunstsuwar, daga tsaye ta faɗi ƙasa hakan yasa,
Parvina sake saka ihu da ƙarfi ta fizge ta nufi kan tsuntsuwar da ita mace take gani kuma sanadin saketa da akayi daga sama ta faɗi ƙasa a kife yasa cikinta buguwa wanda yayi sanadin a take naƙuda ya fara murɗarta kana ga jini daya fara bin sawunta.
Tana isa gaban tsuntsuwar tasa hannunta ta kamo hannun baiwar Allah nan da ita kadai Allah ya bawa damar ganin a mutun ba tsunstsuwar Boleru ba, hannunta data riƙo su kuma kab mutanen wurin gani suke fiffigen tsunstsuwar ta riƙo.
Cikin kuka take shafa kan kurciya a ganinsu yayinda ita kuwa hawayen fuskar matar da take ganin take sharewa cikin muryar kuka tace.
“Sannu sunji miki ciwoko, kice musu ke ba tsunstsuwa bace ki gaya musu ke mutunce kamarsu ki gaya musu kema bani adam ce karsu yankaki”.
Kuka ta kuma fashewa dashi ganin matar nan bata magana sai dai hannunta data riƙo ɗin ta ganshi tamkar robo wato alamun hannun a karye yake, cikin sauri ta sake hannun tare da cewa.
“Appa mu tafi da ita mu kaita wurin masu gyaran ƙashi”.
To al’amarin parvina fa ya fara zarta zaton mai zato ya fara shallake tunanin mai tunani abin ya girmi shekarun Dattijannan.
Shi kuwa Giɗaɗo kuka ya fashe dashi tare da nufarta yana mai cewa.
“Ki bani tsunstsuwata ai tawace nine nayi ta renonta kullum tare muke cin abinci tare komai duk abinda naci sai na barmata dan tayi ƙatuwa, kuma yanzu kice baza a yanka min itaba”.
faɗawa tayi jikin matar wanda su a ganinsu ruggume tsuntsuwar tayi ita kuwa parvina cikin kuka ta juyo ta kalli Giɗaɗo tare da cewa.
“Kai mayene ko? To Wlh bazan baku itaba in dai ina raye a duniya bazan bari a cutar da itaba, babu wanda zai kasheta a gabana sai dai in bana raye ku bar ce mata tsuntsuwa wallahi tallahi mutunce kamar kowa”.
Kiran sallan magriba da akayine yasa ɗaya daga cikin dottijon mai suna Yayari yace.
“Arɗon Babayo lokacin salla yayi”.
Sai ya kuma kalli Giɗaɗo da Gainako da Seyoji da Ja’eh yace.
“Maza kuje kuyi al’wala kuzo muyi salla, kai Giɗaɗo ka bar mata tsuntsuwar kurciyar kaji ko gobe da safe zabbi za’a yanka muku ku gasa kuci”.
Cikin kuka Giɗaɗo yace.
“Wallahi Ni dai ta bani tsunstsuwata, bana son zabuwar ni ko ɗawisu zaku yanka min bana so kurciyata nake so a bani abuna”.
(Giɗaɗo sabo da kaza baya hana a yankata kenan)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *