🏃🏽♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽♀️
H U G U M A
PAGE 01
*Da sunan Allah me rahama me jin qai,dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin talikai,tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta annabi muhammadu S A W
wannan karon labarin namu zai sauka ne a qasar nijer,duk inda akaga kuskure ko gyara sai ayi haquri,domin ni banigerian ce😂
N I J E R maraɗi
Tun daga taku me nisan tazara tsakaninka da ainihin layin,amma kuma kana iya jin tashin sautin gangar kidan data karade kusan kowacce shiyya ta unguwar. Lokacin da ka cimma nasarar isowa layin kuwa,taron dandazon samari ne da ‘yammata ‘yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewa,wasu cikin ainihin tsakiyar filin da aka bari domin bawa masu sha’awar taka rawar da kyau,wasu kuma daga bayan fage suke takawa suna kuma rausayawa. Kowannensu cikin shigar dake nuna zallar wayewa da kuma sukunin rayuwa yake. Kusan fiye da rabinsu kyawawan BUZAYE ne,wadanda aka fi sani da ABZINAWA,jefi jefi kuma kana iya hangen masu surkin launin fata,wanda wasunsu suka kasance barebarin nijer zabarmawa da sauran yarukan da qasar nijer din ta hada. A hankali kyakkyawar motar fara qal qirar Yaris ke gangarowa. A kallon farko idan ka yiwa motar,yanayin yadda take gangarowa kadai zai iya sanyawa kayi zaton man fetur din dake taimakawa wajen motsawarta ne yake Shirin qarewa. Saidai kuma sam ba hakan bane. Kyakkyawan farin matashin ba’abzinen dake zaune cikin motar ne ua zabi ya tuqa motar a haka,farin buzun saurayin da tashin farko kuma kai tsaye zaka kirashi da BALARABE zalla babu mix. Fuskarsa a dinke take tsaf,yana kuma wani irin tuqi kamar wanda jinin sarauta ke zagayawa a gangar jikinsa zuwa ruhinsa. Duka duka shekarun haihuwarsa ba zasu wuce ashirin da hudu zuwa da biyar ba. Amma wani irin lafiyayyen kwarjini dake shimfide akan fuskarsa zai sanya ka dauka wani babban mutum ne dake da wani muqami na mulki ko sarauta. Tunda ya jiyo sautin kidan daga nesa ranshi ya soma baci,idan akwai abinda ya tsana cikin dabi’ar qasarsu yake da ikon da zai iya sauyawa to wannan tana daya daga ciki. Yaja tsaki har baisan adadinsa ba. Wannan hanyar itace hanya mafi sauqi a gareshi da zai isa unguwarsu,to amma yanayin yadda suka toshe layin yasan zaiyi wahala ya samu ya wuce cikin sauqi ko dadin rai. Wani siririn tsakin ya sake ja,yadan cije jajayen lips dinsa na qasa yana cusa yatsunsa cikin lallausa kuma cikakkiyar sumarsa ta asalin buzaye,ya qara hannu daya kan guda dayan da yake tuqin akai,ya soma gangarawa da motar gefe don ya samu gurin parking. Ya gwammace yabar motar a nan guraren,idan yaje ya karbo aiken daga wajen babbo din,sai ya dawo ya dauki motar ya wuce. Kashe motar yayi,sannan ya zare key din,ya miqa hannunsa ya dauki wata baqar leda sannan ya buda motar ya zura qafafunsa dake sanye cikin boots din da wandon kakin sojin dake jikinsa shi kadai ya isa ya gaya maka waye shi?. Tun tsaiwar motar taja hankalin mutane da yawa dake wajen,baisan me ya sanya ba,motar ba mallakinsa bace,amma a duk lokacin da ya shiga motar sai take qara masa kwarjini me yawa,abu daya da baiso yadda take sanyawa idanu ke yawa a kansa,wannan ya sanya ba kasafai ma ya fiya hawa din ba,saidai idan aiken gaggawa ne bobbo ko tati sukayi masa,kamar dai wannan aiken. Da kyau ya hade fuskarsa ba yana ci gaba da ratsa taron,wanda kusan maza sunfi yawa a ciki,zuciyarsa na baci a duk sanda yaga wata mace a cikinsu. Wannan wacce irin lalacewa ce?,qarfi da yaji suna daukan kansu kamar suna france?,baisan wacce irin dabi’ar banza ce wannan da har yau suka kasa dainata ba. Sake kame jikinsa yayi da kyau lokacin da yake niyyar ratsawa ta sararin da aka bawa masu sha’awar raqashewa da kyau. Duk yadda yaso ya dauke idanuwansa daga kan yarinyar dake tsaye tsakiyar filin tana taka rawa cikin wani irin salo na qwarewa da kuma gwaninta,karya jiki tako ina,kama daga qugunta har zuwa qirjinta da ko irga dangi bata farayi ba,amma tabbas tana kan hanya. Qafafunta da take kadawa tayi gaba ta dawo tayi baya kamar wadda ake matsawa remote control. Wata mummunar faduwa gabansa yayi,tun daga cikin qwaqwalwarsa zuwa kunnuwansa yaji wani irin sauti kamar an qwala masa farantin silver
“SULTANA!” ya kirayi sunanta cikin wani irin zallar fushi da ya cukuda da tsananin mamaki.
Ko kadan bata fahimci da tsaiwarsa a wajen bama bare ta jiyo kiran da yayi matan. A hankali daya cikin ‘yammatan dake tsaye daga gefe,wanda tun ratsowarsa gurin yayi matuqar tafiya da hankalinsu ta matsa daura da ita kadan tana tabota. Sai data daddaki bayanta kusan sau uku sannan ta waiwayo,saidai maimakon idanunta su sauka akan wadda ke tabata din,basu zame ko ina ba sai cikin idanunsa. Iyakar razana da firgita ta jita har tsakiyar hantarta,to amma ita din nuna tsoro ko razani saman fuskarta ba al’adarta bace,wannan ya sanya ta juya abinta,saidai kuma ta fara lissafin ta yadda zata zame tabar wajen tun kafin ya yarfata. Ta karanto tunaninsa kuwa a dai dai,sanda yake taku cikin tsananin zafi don ya cimmata tayi amfani da wannan damar ta kurda ta cikin mutane ta fice. Sama ko qasa sultana tayi masa batan dabo. Cikin zafi yaja da baya ya kutsa ta gefen mutanen cikin sassarfa yana fita daga taron,burinsa shine kawai ya cimmata. WAI YAUSHE TA KOMA HAKA?,YA AKAYI TA SAUYA GABA DAYA?,DABI’UNTA SUKE KOMAWA MASU BAN TSORO?. Wannan tambayar itace ta dinga masa rakiya tana kuma ingizashi da sassarfa,har zuwa lokacin da ya dangane da katafaren gate din gidan nasu. Cikin wani irin zafi ya tura qaramar qofar dake maqale da gate din gidan,a take ta bude ta kuma hadu da bango ta bada sautin BUM!. Farar buzuwar dake tsaye cikin parking space na gidan ta waiwayo wadda shekarunta ba zasu haura arba’in da hudu zuwa arba’in da biyar ba. Idanu ta kafeshi dashi sosai sanda yake takowa cikin gidan,ba ita kadai ba,hatta baaba leko me gadin qofar gidan shi da hamidan dake da alhakin gyara da baiwa tsirran da suka qawata harabar gidan ruwa suma binsa sukayi da kallo. Dukkaninsu ya dauki hankulansu,saboda sanin da sukayi masa. Mutum ne da fushinsa bai fiya zuwa da sauqi ba,hakanan yana da wata irin zuciya wadda a duk sanda ta motsa sai kowa cikik gidan yaji a jikinsa. Duk da cewa ba kasafai yake irin wannan fushin ba,amma abu ne da kusan kowa na cikin gidan baya da burin gani a tattare da shi. Har ta bude baki zatayi magana sai ta fasa,taja wani dogon tsaki tana dauke kanta daga gareshi. Ko ba’a gaya mata ba tasan shi da waye,yanzun nan ta wuce ta gabanta da wani mugun gudun data tabbatar ba lafiya ba.
“A kirawoshi ne hajiya?” Driver hamidou ya fada yana karya murya,saboda ya sani,ita daya ce tal a gidan zatayi furuci qwaya daya da zai dakatar dashi,duk kuwa irin girman fushin da ua debo. Yanayin fushin da ya shigo dashi din kuma ya bayyana muraran ba me sauqi bane,yasan kuma sahun wace ya biyo,ba zaiso kuma a taba lafiyarta ba,don akwai jituwa me yawa a tsakaninsu.
Harara ta watsa masa da fararen idanunta kamar zata cinyeshi danye
“Ban sakaka ba sarkin kankanba”
Gudun Kaddara na Huguma Book 1