Hamshakiyar Uwa HAusa Novels

Hamshakiyar Uwa Na Maryam Abdullahi K/Mashi

Hamshakiyar Uwa Na Maryam Abdullahi K/Mashi

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai,tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad(S.A.W).

Kamar yadda na fara lafiya,Allah ka bani ikon gamawa lafiya,Allah ka bani ikon faɗakarwa gwargwadon iyawata,Ya Allah ka yafe min duk wani kuskure da hannuna zai rubuta,Allah ka bani ladar faɗakarwar.

*Free Page 1*

Kan shi a ƙasa bayan ya zube a gaban ta gwiwoyin sa suna ƙasa tamkar mai neman gafara. A hankali ya furta Hajiya Barka da dare.Ta ɗago kai daga kan TV da ke nanne a bango cikin wata ƙatuwar ma’ajiyar ta bango guda. Ta maida kanta gare shi ta na nazarin fuskar shi, sannan ta dubi yarinyar da ke zaune a ƙasa tana shafa mata man zafi a ƙwauri ta ce, “Azima ta shi ki je ki kwanta.” Cikin sauri yarinyar ta miƙe ta re da faɗin sai da safe Hajiya. Allah ya tashe mu lafiya, Hajiya ta furta a hankali. Ta maido kallon ta ga gareshi sannan ta soma magana cikin isa “Shamaki zauna da kyau Allah ya yi maka albarka.” Ya ce Ameen Hajiya. Ta ce “Bisa dukkan alamu ka ga wadda ta yi wa ranka, ko dai birgewa ko kuma ta baka shi’awa, faɗa min wani abu dangane da ita.”

Ya sake gyara zama bai yi mamaki game da kalaman mahaifiyar ta sa ba,domin ita mace ce mai tsananin basira tare da karantar ɗan Adam, in har za ku yi zaman minti talatin da ita ba ko shakka zata iya zayyana maka abubuwa da dama daga cikin ɗabi’u ko halayyarka. Sannan babu abinda tafi saurin ganewa irin ka yi mata ƙarya. Ya ce Hajiya so ɗaya na ganta zata je Islamiyya na tsaya zan yi mata magana ta ja tsaki ta wuce, maimakon in fusata sai kawai na ci gaba da bin ta a baya bata sani ba har ta shiga makaranta.
Na san cewa kamar shidda sun ta so na koma sai ban ganta ba, yau na bi ta layin da na ganta cikin sa’a sai na hange ta a wani shago tana siyayya,na jira ta gama na bi bayan ta na ga gidansu yanzu ina neman iznin zuwa ne in Allah ya sa an bani izni.
Hajiya ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, zuwa can ta ce “Je ka kwanta amma kafin hakan ina son ka yi sallar istikhara da safe ka zo ka kuma bani wannan labarin da ka bani.” Ya miƙe a hankali tare da faɗin na gode a tashi lafiya. “Allah ya maka albarka.” Ta furta tare da ɗaukan goran ruwa a gefen ta ta buɗe da zumar sha.
Firgigit ya farka ya na kallon ɗayan sashen da take kwance, mafarkin yana dawowa a zuciyar sa, babu ko shakka sai ya yi wanka domin ya cimma hakan a mafarkin sa, bai taɓa samun hakan ba duk zaman gauran takar sa, kila gara lokacin da ya ke saurayi farkon balaga. Ya yi addu’a a sallar sa, domin bai samu zuwa Masallaci ba sakamakon makara,ba zai iya tuna lokacin da ya rasa jami’in sallar asbahi ba. Ya jima kwance jikin sa lankwas wanda yin hakan ba al adarsa ba ce. Sai ya ji kamar wani ɗan zazzaɓi ya na sarfatar sa. Cikin hakan ya ji ana kwankwaso ƙofarsa, ya tashi zaune sannan ya bada iznin a buɗe. Ta turo ƙofar ta na sanye da kayan makaranta, Azima ce. Ta ce”Yaya Shamaki Hajiya ta ce in duba ka.” Ya ce ki sanar mata ina zuwa. Ya miƙe ya ɗauki jallaiya bulu mai gajeren hannu tasha aiki da sirfani mai ruwan zaiba ya saka.
Yana fitowa falonsa Meema ta na shigowa ta nufeshi da gudu tana faɗin “Dadi! Ya sa hannu ya ɗaga ta sama ya sata a jikin sa tare da faɗin Mamana Ina Mubina ina Anisa? Ta nuna mishi hanyar ɗakinsu tare da faɗin “Suna ciki Rahin tana shirya su.” Ya lakaci kuma tun ta ke fa? Ta ce “Ni’ma yanzu za ‘a shirya ni.” Ya dire ta to maza kar ku yi latti ki tafi a shirya ki. Ta ruga da gudu. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya.
Tana zaune a kan sallayar ta ƙafafun ta a miƙe sanɓal ta rufe kanta da hijabi na alfarma ƙamshin ta na tun fil”azal ya na tashi tana riƙe da carbi tana lazimi. Ya samu gefe ya zauna zama irin na girmama wanda ka ke gaban shi. Ya kalle ta cikin darajawa tare da faɗin Hajiya ina kwanan ku? Ta sauke numfashi cikin ƙasaita, sannan ta amsa da “Lafiya lau Shamaki, me ya same ka yau ba ka je sallar asbahi ba?” Ta yi tambayar cike da kulawa. Ya sunkuyar da kai, jikina yau na tashi babu daɗi sam, kuma sai na makara. “Me ya biyo bayan neman zaɓin da ka ba Allah ajiya! Ka ji wata damuwa game da yarinyar ko kuma Allah ya haska maka wani al’amuri a cikin baccin ka?”
Ta jeho masa tambayoyi. Shamaki ya ce eto har zuwa yanzu ina jin ƙaunar ta kuma na yi mafarkinta. Ya sunkuyar da kai domin ba zai iya bada labarin mafarkin ba. Hajiya ta ce “Ina sauraron ka.” Ya sa hannu ya shafa fuskar sa sannan ya saci kallon ta ta tsira mashi ido,ba ko shakka so ta ke yi sai ta fahimci ko zai mata ƙarya. Ya ce cikin wani yanayi muka haɗu Hajiya Allah dai ya kyauta.
Ta yi ɗan murmushi da alamu ta fahimci ina ya dosa. Shike nan, ka sake bani labarin da ka bani jiya game da yarinyar. Ya gyara zama ya zayyana mata komai kamar jiyan. Ta numfasa tare da faɗin shike nan ka je ka fara bincike a kanta kafin ka je gurin ta. Sannan kar ka manta. da sharuɗɗa na akan duk wata mata da za ka aura. Bana son ka sake sakin mace daga guda ukun nan da ka yi, amma ka sa a ranka matan ka huɗu ne in Allah ya ƙaddara ina aɗdu”a. Kaje ka shirya yau kai zaka kai yaran ka makaranta domin tun jiya suka nemi alfarmar hakan.
Sannan in kaji zazzaɓin zai matsa sai ka sha magani, duk da nafi zargin zazzaɓin na soyayya ne. Ta kai ƙarahen maganar da ‘yar dariya irin ta manya cikin ƙasaita.
Ya shafa kanshi tare da yin murmushi mai sauti,ba ko shakka zolayar sa Hajiya ke yi.
Ya ɗan rusuna. zan yi yadda ki ka ce insha Allahu Hajiya. Sanna ya miƙe ya nufi ciki. A mota tare da ‘yan yaran sa mata su uku, Meema da ke zaune a gefen shi ta ce “Dadi za ka dawo ka ɗauke mu?” Ya dube ta sannan ya girgiza kai, Bazan dawo ba Mamana zan tafi kasuwa ne fa. “To zaka raka mu har ajin mu?” Ya kai hannu ya shafi kanta me zai hana zan raka ku in kuna so. Anisa ta sako hannuwan ta daga can baya ta shafo kumatun sa, Dadi muna so ‘yan ajinmu suna cewa basu taɓa ganin Babana ba. Mubina ta ce Nima haka Dadi za ka raka mu kowa ajinta. Ya ce to shike nan sai mu fara kai Anisa ita ce Smaller ko sai mu kai Mubina, sai in kai Anty Babba ko Meema? Cikin jin daɗi ta ce e Dadi na.
Sun yi kamar yadda suka tsara da ‘ya’yan na sa sannan ya ciro kuɗi ya raba wa malaman sannan ya tafi suna ta godiya sannan ya kama hanyar kasuwa.
Tun da ya zauna a ofishin sa da ke babban reshen manyan katunan sa wato Zeena Galary da ke ƙatuwar plazarsa mai suna Gidan Zeena a babbar kasuwar kwari da ke Kano. Dukan yaransa na katin sun fahimci ya na da ‘yar damuwa, kasancewar ba haka ya saba zuwa ba. Shi kansa tunda ya ke bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba game da matansa da ya aura a baya. Ko matarsa ta fari bai ji irin abinda ya ke ji a wannan lokacin ba. Yana jin in bai fita ya nemo yarinyar nan ba kafin yamma akwai matsala.
Suna idar da sallar Azahar ya cire agogo da zobe da duk wani abu da zai nunashi a mai kuɗi, ya fita ya saka salifan da ke ƙofar banɗakinsa na ofishin ya fita ba tare da ya yi wa kowa magana ba, ya je titi ya tari ɗan sahu ya hau tare da faɗin kaini Ɗan a gundi. Dai dai bakin lungun ya tsaya ya ciro kuɗi Naira ɗari biyar ya miƙa masa sannan ya sa kai cikin lungun, shi dai Ɗan sahu ya ciro canji ya ɗago kai ya ga baiga Alhaji ba, cikin jin daɗi ya yi tafiyar sa.

Na siyo gawayi ina sauri zan dafa mana taliya ‘yar murji ni da ƙannai na kasancewar Umman mu bata nan taje awon ciki. Na taka dakalin ƙofar gidanmu sai naji ance “Salamu alaikum. Na waiwayo sai naga wani Mutum wanda wanda ba zan iya siffanta shi a take ba. Na amsa sallamar ina jira ya min tambaya domin dai ƙila wani gidan yake nema a lugun namu.
Ga mamaki na sai naji ya ce “Zan iya magana da ke?” Me zai hana.Na bashi amsa ba tare da na fahimci me ya ke nufi ba. Ya ɗan ƙara matsowa ya dafa bangon gidan mu ya soma magana “Sunana Aliyu amma anfi sani na da Shamaki, kusan kwana uku baya na ganki kuma gaskiya ba wata kwana Ni ina son ki!” Na ɗan ja baya da sauri domin ban zaci inji haka daga gare shi ba,hasali ma ni ba a taɓa furta min kalmar so ba,dan haka sai na rikice ina sake kallon shi. Ya ce ,”Na ga kin firgita da gaske na ke yi.” Zan shige gida ya ce “Tsaya mana ya kamata ki bani amsa ko da rashin amincewa ce.” Na ce abinci zan dafa wa ƙannai na suna jin yunwa. “In dawo anjima da dare?” Ya tambaye ni da sauri. Na sake duban fuskar sa, nifa bantaɓa zance ba,bansani ba ko Abban zai bari. “To ki tambaya in sun dawo amma zanzo anjima ɗin.” Na ce to shike nan.
Ina girki ina tunani, duk da mutumin ba yaro bane amma naji ya birgeni, sannan kalmar so da ya furta a gare ni ta zama baƙuwa a gurina, dole ma in amsa masa ko na shiga sahun ‘yammata da ke zance a lungunmu bayan wasu ma na girme su nesa ba kusa ba. Shekaruna ashirin da haihuwa jarabawar kammala Sakandire muke yi, a Islamiya ina ajin sauka, amma ban taɓa samun wanda ya ce yana sona ba ko da sunan wasa ba. Na sha kallon kai na a madubi duk da ban kasance fara me shegen kyau ba,na tabbata ba za a sakani a layin munana ba, kuma dai dai gwargwado ina da hankali da kamun kai.
Cikin wannan yanayi na gama girki amma sai na kasa ci, haka a Islamiyya yau sai tambayata a ke yi lafiya kuwa. Domin na zama shiru sai tunani, in har iyayena sun laminci in yi soyayya da shi ba shakka zan ji daɗi domin har na fara jin cewa na ƙosa in sake sauraron muryar shi.
Bayan magariba Umma tana zaune kan tabarma ta idar da salla ta na cin ɗata, na zauna kusa da ita na ce Umma ɗazu wani mutumi ya zo ƙofar gidan nan wai gurina ya zo. Ta ɗago kai da sauri “Me ya ce miki ?” Na ce wai yana so na, nace sai in na faɗa.a gida. “Ɗan ina ne?” Ta tambaye ni, na ce wallahi bansani ba, ya ce dai zai dawo da daren nan. Tace Allah ya sa dai na gari ne,dama ranar nan sai da Umman su Fati ta gwaɓa min magana wai an saka ranar Fati ita dake suyar awarar dare, masu zuwa haddar Kur’anin dare shiru. Kuma nasan ta gwaɓa min maganar ne saboda na ce ta hana Fati yin dare sosai a gurin tuyar awara wani lokacin har shaɗayan dare take kaiwa Abbanku in ya zo sai ya yi ta faɗa. Wai an bar yarinya gurin daga ita sai yaran nan maza marasa kunya. Na ce ai yanzu faɗar gaskiya ta zama matsala Umma. Ta ce haka ne ke dai ki kula da kanki in ya zo ki fita ki saurare shi in kuma Abbanku ya dawo kafin lokacin zan faɗa masa.
Jamila ƙanwata ta matso kusa da mu tace Umma Yaya Baby ce zata fita zance? Na ce to sarkin tsegumi. Umma ta ce “Menene a ciki in kin faɗa mata, Jamila ai ƙawa zaki maida ita,na faɗa miki komai ki ke yi tare da ita shekarunta sha bakwai fa yanzu.” Na kalleta nayi murmushi tare da faɗin to ƙawata baƙo zan yi. Ta ce Allah na gode maka mu ma Allah ya sa ayi biki a gidanmu. Umma ta ce “To kije kiyi wanka ki gyara jikin ki.” Na ce har sai na yi wanka kuma, na yi da safe fa. Jamila ta ce, au da me ki ke nufi, haka zaki je kina zufa? Na tashi na je na ɗebi ruwan sanyi abinda bana wanka da shi amma dan zumuɗi na faɗa banɗaki na yi wanka aiko ina ta atishawa, cikin zuciya ta kuwa fargaba ce tana saƙamin ko ma dai ba zai zo ba.
Na idar da sallar Isha’i a ɗakin Umma na zabga tagumi gefe ga kayana sabbin na sallar bara da Umma ta ce in saka. Jamila kuwa ta tasani agaba sai fadi ta ke “Anty Baby ki tashi ki saka kayan kar ya zo baki shirya ba.” Na ce Jamila ni yanzu fargaba ke duka zuciya ta,ji na ke kamar ya fasa zuwa,kila ma ya canza shawara.Ta ce “Karki faɗi haka Anty, shifa ya zo da kansa tun farko ba ke ce ki ka nemo shiba.” Sauke ajiya zuciya ta sun zo dai-dai da sallamar Abbanmu. Umma ta amsa tana masa sannu da zuwa, muka leƙa muka yi masa sannu da zuwa ya amsa. Nace to Jamila bari in shirya ɗin,ke ki je ki kaiwa Abba abinci. Ta fita tare da faɗin “To.”
Ina jiyo Umma ta na sanar da Abba game da baƙon da zanyi,na yi kasaƙe inji me zai faɗa,sai ga muryar wani yaro ta ratso gidan da sallama. Umma da Abba suka amsa. Ya ce,”Ana sallama da Abban gidan nan inji wani mutum.” Abba ya ce to ka ce ina zuwa. Umma ta ce baka tambaya ko waye ba,yace Malam Sani ne mun yi da shi zamuje wani aiki gobe,to nasan kan maganar ne,kinsan yadda rayuwa ta ke yanzu in ka samu aiki ƙoƙari ka ke ka je in ba haka ba sai aba wani. Ta ce “Haka ne Allah yasa mu dace.” Ya ce Ameen bari in dawo yanzu.
Na gama cire rai da zuwan mutumin har takwas da rabi na yi danasani da ban saurare shi a lokacin ba, na kwance ɗankwalin da na ɗaura dan ya soma damu na,nafara ninke shi sai naji sallamar Abbanmu. Ya na kuma tambayar ina Baby?” Da sauri na amsa gani Abba, ya ce “Kije baƙonki yana waje yana jiran ki.” Gabana ya yanke ya faɗi, na ce to.Jamila ta miƙo min yar kwalba tare da faɗin ga Humra ta Umma ce ki shafa ajikin ki. Na ɗan goga na fita da sauri. Umma ta ce “Baby in kinje fa ki gaida shi .” Abba ya ce haba kema dai yaran yanzu kar suke kallon kowa. Umma tace kasan wannan ce farkon fitar ta zance dole a tuna mata. Abba ya ce “Jamila kai masa tabarma. Can na tsaya a bakin ƙofa ina shaƙar ƙamshi turare mai daɗi irin wanda na ji ɗazu, yana can gefe jingina da bango sanye da farar shada riga da wando ba hula a kanshi, gefen shi ga keke irin mai kwando a gaba na manya ya jingina. Jamila ta shimfiɗa tabarma a kan dakali sannan ta gaishe da shi ta koma ciki. Na taka a hankali na isa kusa da shi,nace sannu da zuwa Yaya. Basan lokacin da baƙi na ya furta hakan ba. Cikin yanayin jin daɗi ya amsa da “Yawwa ƙanwata.” Na nuna kishi tabarmar Yaya ka zauna. Ya ce to, ya isa bakin dakalin ya zauna,na tsugunna a gefe ya ce, ,”kema dawo nan ko ki hau sama ko ki yi irin zaman da na yi.” Na zauna sannan na rusuna na gaida shi,ya amsa “Hajiya ta ce in gaishe ki, na ce ina amsa wa amma, sai kuma na yi shiru. Ya ce amma me? Na ce nayi mamaki ya aka yi ta sannu. Yace, “Ta sannu tun ranar da na fara ganin ki, tasan na yi magana da ke ɗazu, kuma ta san ina nan yanzu.” Na ce Allah sarki to ina gaishe ta in ka koma. Sai da tuni zuciyata ta shiga fargaba e ko matar sa ce Hajiyar domin daga ganinsa ka san dai yana da iyali.
Ya katse min tunani da tambaya. “Baby Ya sunan ki na gaskiya? Saboda ko sunan ki Ni bansani ba yanzun da na yi sallama da Abba na ji yana cewa Baby.” Na ce Amira, amma na asalin gaskiya Rabi’atu sunan Maman Abbanmu ne, sai ake ce min Amira,Baby kuma Ummanmu ta ke faɗa min sai kuma ya rinjaya. Ya numfasa. “Ni ma dai Babyn ya fi min daɗi, amma zan kira kowanne in na so ko?” Na Ɗaga kai alamun eh.
Ya yi ‘yar gyaran murya “Baby gaskiya ina son ki kamar yadda na faɗa ɗazu, in har ki na sona to aure ya kawo ni kamar yadda na faɗawa Abba ɗazu. Sanna bazan ɓoye miki komai ba,ina da yara uku duka mata,kowacce mun rabu da mahaifiyar ta… Saboda me? Na jeho masa tambaya ba tare da na sani ba. Ya ɗan yi dim, sannan ya ce “Saboda Allah, kar ki damu sannu zaki san komai. Ya ci gaba Ni ƙaramin ɗankasuwa ne ina tsare shagon mai gidana a Kantin kwari. Fatan kin fahimta?” Na ɗaga kai tare da faɗin umm. Take zuciyata ta sare kuma ta soma tuhumarsa. Mata uku, kuma ba ko ɗaya yanzu, gaskiya ya kamata insan dalili. Ya katse min tunani da cewa, “Baby ta bakin ki na ke son ji ko kina so na kuma za ki iya aure na? Ni dai komai na ki ya yi min. Na numfasa cikin sanyi jiki na to gaskiya ni dai bansani ba ko ina son ka domin ban taɓa samun kaina a cikin shi ba to bansan ya yake ba. Sannan magana aure Allah shine mai ƙullawa, in har ya ƙaddari hakan zan amsa hannu biyu. Yace “Har yanzu dai ban samu amsa ba,amma zan baki zuwa jibi, kiyi nazari kuma ki ƙoƙarta ki gano ko kina so na.” Na ce, to na gode kuma zanyi yadda ka ce. “Bani lambar wayar ki zan kira kafin jibin inji wannan sanyayyar muryar.” Na ce sai dai in baka ta Ummanmu, saboda har yanzu Abbanmu bai sai min ba, yace sai mun gama walimar saukar ƙur’ani. Yace to bani ta ta ɗin, na faɗa masa sai ya yi flashin yace, “Inkin shiga sai kuyi sebin domin inna kira kai tsaye kinsan ni ne.” Nace, to. Yace “Nine ɗan auta a gurinta, kuma ni kaɗai ne namiji, yayinda huɗu duk mata, Yaya Zainab ce babba,sai Maryam A’isha da Fatima duk suna aure a nan cikin gari.” Na ce masha Allah kaji daɗinka. Ni kam bani da yaya hasalima ni ce ‘yar fari sai ƙanena uku Jamila da Jafar da kuma Habu,sai wanda za a haifa mana yanzu. Yace “Allah ya sauke ta lafiya dama ina ganin Abba na raya a zuciyata cewa ƙila ke ‘yar fari ce.” na ce Ameen, gani ka yi ba tsoho ba ko? Na tambaye shi ina ‘yar dariya. Yace “E mana.” Shima cikin dariya ya amsa. Nace, haka in ‘yan makarantarmu suka zo sai su ce wai Ummanmu Antinmu ce. Muka ƙara yin dariya tare. Ya ce “To Ni dai bari in zo in tafi kar dare ya yi sosai,na kalli kekensa nace danma kana da abin hawanka balle ma ka ce zaka rasa ɗansahu. Yace haka ne.” Nace, Ka gaida Hajiya da kyau. Ya faɗaɗa fara’a “Zan faɗa mata Insha Allahu.” Shine ya nannaɗe tabarmar ya tako har bakin soro yana faɗin in gaida su Umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *