Ku Dube Mu na Batul Mamman
Gidan Mal Ali Gidado babban gida ne a cikin karamar hukumar Sumaila dake Kano. Attajiri ne wanda Allah Ya azurta da dabbobi masu tarin yawa. Garken shanu, tumaki da awakinsa bazasu kirgu ba saboda yawansu. Wata katuwar gona ya samu a can bayan gari ya zubesu yana kula da kayansa da taimakon mutane kalilan saboda bazai juri biyan da yawa ba. Bafillatani ne na usuli dan siriri ba kiba ko kadan amma kallo daya zai tabbatar maka an zuba kyau zamanin kuruciya. Mutan gari da iyalinsa suna kiransa Malamijo. Duk tarin arzikin Malamijo kusan kowa ya sanshi a matsayin rikakken mai mako da bakar rowa. Kudinsa basa tabuwa indai ba aure ya tashi yi ba. To a nan fa yarinya da iyayenta zasu ci su tada kai. Idan anyi auren ma amarya ita ce tauraruwa taci mai kyau tasha mai kyau. Gidan gabadaya hannunta sai dawo har zuwa lokacin da Malamijo zai gaji da ita ko tayi ciki. Daga nan fa ita da babu duk daya don gwani ne wurin wulakanta mata da cin zarafinsu saboda shima ya sani kudinsa suke aure.
Malamijo ko suturar kirki baya sakawa saboda kada ya kashe kudinsa. Sau tari zaka ganshi cikin kodaddun kaya yana yawo don bai taba yarda yayi dinki daidai jikinsa ba saboda gudun raini. A halin yanzu ‘ya’yansa goma sha biyar amma shida ne kadai da iyayensu mata a cikin gidan. Sauran taran basu da gata suna ga Allah suna ga Yadikko mata ta biyu a jerin aure auren Malamijo wadda har yau ya kasa sakinta saboda mace ce da ta gagare shi juyawa. Bata taba haihuwa ba kuma nata mahaifin ma da arzikinsa lokacin da akayi aurensu. Duk da haka dai auren nasu yana da tsahon rai domin kuwa duka ‘ya’yan Malamijo akan idonta aka haifesu. Idan ya saki uwar yaran tana kokari matuka wurin kulawa dasu sai dai rashin wadatasu da yake yi yasa itama abubuwan sai a hankali. Yaran da suka ci sa’a suma sun taso da nasu iyayen a gidan to duk abinda aka kawo wawaso ake dasawa mai uwa a gindin murhu ya tsira da abin arziki. Wanda babu tasa kuma ya koma gefe yasha kallo.
Duk bakin hali na Malamijo yaransa sun tsira da abu daya wato ilimi na zamani da na arabiya. Wannan ludufi da suka samu ya samo asali ne daga shawarar da abokinsa da suke kai dabbobi kudu tare ya bashi na cewa idan sunyi karatu shine zai mora domin zasu sami aikin gwamnati kuma a matsayinsa na mahaifinsu shine zaifi kowa jindadi da samun yaran. To dayake zuciyar ta nema ce kawai ba musu ya amince. Shi kuwa abokin nasa Mal Kallamu yayi haka ne domin ya taimakawa yaran da suke walagigi a cikin gari. Shawara dai irin ta abokai yana kokarin bashi bakin gwargwado akan tsarin rayuwarsa amma yaki ji. Banda Mal Kallamun ma waye ya isa ya fadawa Malamijo magana irin wannan kai tsaye batare da ya auna masa rashin mutumci ko da rabin kwano bane ya kai masa har kofar gida.
Yau yake dawowa daga kudu inda ya kai motoci uku na dabbobi. Duk yadda aka san Fulani da son dabbobinsu haka yake a wurinsa sai dai kudi ya fiye masa komai. Kuma gashi da nasibi don yana samun alkhairi sosai kamar yau din da ya dawo.
‘Ya’ya da matansa haka suka yi ta fitowa ana masa barka da dawowa yana faman hura hanci kada wata tayi gigin neman karbar jakarsa.
‘Yan mata biyu ne a daki daya tana kwance akan yamutsatsiyar katifa dayar kuma mai alamun ta girmeta tana daga tsaye a kanta.
“Wai bakiji shigowar Malamijo bane?”
Siririn tsaki taja tana juyawa daya bangaren “naji mana”
Yayarta ta da suke daga iyaye mata daban ta zauna a gefen katifar tana rage murya “Mairama kinsan idan bamu je ba duk abinda yazo dashi su Inno karbewa zasuyi ko?”
Cikin bacin rai Mairama ta juyo “Adda Salame ban fa hanaki zuwa ba.”
Batare da kosawa ba sanin halin kanwarta ta sake murmushi “Mairama ki dena wasa da iyaye babu kyau”
Tasowa tayi a harzuke sai dai ko kafin ta fara magana ta soma kukan abinda yake ci mata rai “Adda har kin manta ranar da zai tafi yace mana mun cika masa gida kamar ‘ya’yan Allah bani, wato irin wanda ba’a kaunarsu an dai haifemu bisa lalura. Gara ma ke kina zuwa wurin Innarki, ni kuwa da kasa ta rufe idon tawa bani da wani gata”
Kuka Mairama take sosai Salame tana bata baki. Yarinya ce mai zuciya shiyasa abubuwan rashin adalcin gidan nasu suke ci mata tuwo a kwarya. Ada da suke makarantar kwana idan suka tafi ko marmarin hutu bata yi. Gashi yanzu sun gama harda watanni. Da yake sune manya Salame mahaifiyarta ce uwargidansa ita kuma Mairama tata ita ce ta uku. Dukkaninsu babu wadda ta budi ido da mahaifiyarta a gidan. Yayin da Salame take da mugun sanyin hali ita Mairama saurin fushi gareta musamman akan yanayin gidan nasu.
Labulen dakin aka bankada Hajjo mai mulkin gidan a yanzu saboda ita ce amarya kuma yayinta bai kare ba ta sakar musu harara.
“To tabbatattu isassu. Kuna kwance a daki Malamijo ya dawo bazaku je ku gaishe shi ba”
Da rawar jiki Salame ta mike tana tayar da Mairama “yanzu zamu fito”
Tsaki taja ta koma suka fito babu kowa a tsakar gidan sai kannensu maza da mata kusan kowa rike da agwaluma daidai a hannu daga su har uwayensu. Hatta Yadikko rike take da guda tana lailayawa a hannu don taji dadin sha. Kallonsu tayi idanun Mairama jajir.
“Me ya hanaku fitowa da wuri har ya gama rabon tsaraba?”
Salame taji babu dadi don ranta ya biya. Kayan kwalama irin wannan da wuya yake musu tsaraba sai anyi matukar sa’a. Harara ta gallawa Mairama don ta tuna ya taba kawo musu agwalumar kudun akwai zaki. Tare suka shiga rumfar Malamijo. Fankar kasa ce aka sakar masa a ka yana shan iska kafin a hada ruwan wanka. Tabe baki yayi ya wani juyar da kai.
“Malamijo yaya hanya?” cewar Salame ya amsa da kyar.
“Barka da dawowa” Mairama tace tana gintse fuska.
“Chege ‘yar kunama wai nan fushi kike yi saboda nashe zan dena ciyar daku kafin nayi tafiya? Baffanku Kallamu ne ya fada min kuna gamawa zaku fara aikin gwamnati ku soma daukar albashi kuna yaga min kawai kuma sai naji shiru.”
Da mamaki suke kallonsa. Ashe dalilin tijarar da yayi musu kenan a ranar harda kiransu kattin banza ‘ya’yan Allah bani. Don kansa ya saki fuska yace yayi bincike an fada masa ashe sai sunyi wata makarantar ta gaba da sakandire.
“Qur’anin Ubangiji ni kuma bazan sake biya muku komai ba. Ku fiddo mazajen aure na kawar daku a sami sarari a gidan nan. Ga kannanku nan rida-rida dasu suma kullum cikin sasake ni suke. Wannan adashin da babu alamun riba na kudin makaranta na soma gajiya”
Dije mata ta biyu a yanzu tayi burum ta fado dakin
“Yasin Malamijo yarana sai sun gama makaranta. Haka kawai wasu ma suka gama bare nawa kuma maza”
Hularsa ya turo gaba yana kankance idanu “Ki shiga hankalinki dani Dije. Sai hegen labe kamar kadangaruwa kullum kina manne da bango. Ina jiye miki kada watarana ki jiyowa kanki sallama”
Idanu ta zaro cike da tsoro su Salame suka fita suka barsu.
Kwanakin da suka biyo baya gidan bai canja zani ta kowacce fuska ba sai ma tsananin da Salame da Mairama suka kara shiga na rashin kawo mazajen aure. Malamijo har ikirarin hadasu da masu yi masa aikin dabbobi yayi. Yaran nasa ne tubarakallah ga kyau amma fa babu farinjini….da farinjinin dai tsayayye ne babu saboda babu mai kaunar hada iri da Malamijo saboda halinsa kaf babu na zabe.