MIJIN 'KWAILA ����♀
sabon salo daga labarin zahra adam ishaq
"-chapter one-"
Ahankali yake tafiya da motar sakamakon yanda ya iske saitin bakin makarantar yaran yacika yakuma batse da dandazon yaran da'aka riga aka taso daga makaranta,ya d'anja gajeren tsoki lokaci guda yana kallon tsadadden agogon dake hannunshi ya taka burki kamar yanda sauran masu ababen hawa y'an uwanshi sukaja nasu burkin sakamakon dakatar dasu da yellow piper yayi.Ranshi 'kwarai yana a dagulene koda yake ba abin mamaki bane ganin fuskar tashi babu walwala kusan dukkan na tare dashi sunsan dahakan duk. . .