DIYAM Na Maman Maama
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannan
rubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi ya kuma haneni daga rubuta
sharri. Allah ya sa wannan rubutu ya amfane ni da duk wanda Allah ya bawa ikon
karantawa. Littafin DIYAM kyauta ne, ina fatan ya zamanto min
sadakatujjariya har bayan raina. Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana, na
fili dana boye.Diyam is a total work of fiction, in yayi dai dai da labarin
ki/ka to coincidence ne ba wai da niyya ba ne.
🔥🔥🔥ZAFAFA GOMA 2023🔥🔥🔥
Diyam littafi nane, mallaka ta ce, duk wanda ya juya min
littafi ko ya siyar min ba tare da sani na ba shi da Allah.
Just follow my pen for I assure you, you are going to fall
in love with DIYAM.
Episode OneMadaidaicin dakin karatun mai dauke da dalibai 36 yayi shiru
bakajin motsin komai sai na takardu, sai kuma very clear voice din lecturer da take
gabatar da lecture ga dalibai masu karantar ilimin law a makarantar Blavatnik
school a cikin Oxford University. Darasi ne suke yi akan marital laws, inda
malamar take yi musu bayani dalla dalla game da dokokin da suka shafi
auratayya. Saboda kasancewa daliban sunzo ne daga mabanbanta kasashe, wannan
yasa malamar take daukan kasashe daya bayan daya take musu bitar dokokin
kasashen da niyyar in sun gama sai su hadu suyi comparing aga wadanne ne sukafi
kyau kuma wadanne chanji ya kamata a samar.
A yau ne kuma malamar tashigo kasashen nahiyar Afrika. Ta
fara da Nigeria, the giant of Africa. A nutse ta fara karanto wa daliban
dokokin da kasar Nijeriya take dasu wadanda suka shafi auratayya. Suna tsaka da
daukar darasin ne suka ji snicker, malamar ta dakatar da karatun da take yi ta
dago kanta a tare da duk sauran daliban suka kalli sashen da dariyar ta fito.
A extreme end of the class room, sitting alone like an
abandoned island, wata kyakkyawar budurwa ce wadda kallon farko in kayi mata
daga nesa zaka ce kyakykyawa ce, in ka matso kusa da ita kuma sai kaga tafi
yadda kake tunani kyau, as kana cigaba da kallon ta kyawunta yana cigaba da
bayyana a gare ka. Da yawa a makarantar ana yi mata kallon balarabiyya amma
nigerians suna ganin ta suke fahimtar cewa tasu ce, kabilar fulani ce, kabila
mai dangantaka da larabawa. Daga ganinta zaka fahimci ita kanta bata san cewa
tayi dariyar ba. Shirun da taji ajin yayi da kuma feeling na cewa ana kallonta
ya saka ta dago kanta da sauri, dara daran idanuwanta a bude kuma ta saka su a
cikin na malamar da take tsaye a gaban desk dinta. Suka tsaya suna kallon kallo
sannan malamar tace mata “why do you laugh? Are you finding this
funny?” Ta girgiza kanta da murmushi a gefen kumatunta. Malamar ta koma
kusa da podium ta tsaya tana kallonta sannan tace “where are you
from?” Still kanta a kasa tace “Nigeria” malamar tace
“menene ra’ayinki game da wadannan dokokin na auratayya a Nigeria. Kina
ganin sunyi dai dai ko kina da gyara?” Shiru ta sake yi na wani lokaci,
sannan tayi karamar dariya tana girgiza kanta, fuskarta na nuna cewa akwai
abinda yake damunta, suddenly kuma sai tayi magana “bani da gyara ma’am.
Saboda all those laws da kike lissafawa a rubuce kawai suke, maybe for the sake
of the likes of you da zasu nema for educational purposes, amma ba wai amfani
ake yi dasu ba” malamar looked interested, tace “so, can you tell us
the situation of marriage in Nigeria?” Nan take murmushin fuskar budurwar
ya dauke, ta hadiye wani abu a makogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta tana
kallon rubutun da yake gabanta. “You have a very beautiful handwriting
kanwata” taji muryarsa a kunnenta as clear as if yanzu yake gaya mata.
You May also Like: 🔥🔥🔥ZAFAFA GOMA 2023🔥🔥🔥