Top 10: Zafafan Littattafan Hausa na 2023

Kamar yanda Allah ya kawo mu sabuwar shekara, lokacine kuma da yakamata muyi duba zuwa ga kwazon marubuta littattafan Hausa wadanda suka samu nasarar sa ce zuciyar makaranta ta hanyar amfani da Hasashe, qage, da kaifin basira, Wadannan abubuwan ke sa wa su bar ma duniyar makaranta ababen nishadi. Shekarar da ta gabata ta 2023 ta kasance daya daga cikin shekarun da suka samu wallafar labarai masu dimbin fadakarwa, nishadantarwa har ma da ilimantarwa daga haziqan marubuta.

 A qoqarin mu na faranta ma makaranta rai ta hanyar zaqulo musu zakaran gwajin dafi na wannan shekara, mun gabatar da quri’a wadda muka kutsa cikin duniyar makaranta littattafan Hausa da kuma masana hikimar karatu,  a sakamakon hakane muka samu quri’u da suka kai yawan 1893, hakan ya nuna lallai akwai mutane masu ra’ayin karatun Hausa dayawa da ke boye a duniya.

Ku biyo mu a sannu dai ba tare da gajiyawa ba domin ganin wadannan “ZAFAFAN LITTATTAFAN HAUSA GUDA GOMA NA SHEKARAR 2023”, wadannan zababbun littattafan sun qunshi abubuwan ban al’abi, al’adun mu na gargajiya, nishadi, da kuma zaburar wa akan al’amura dayawa da suka shafi rayuwar dan Adam ciki kuwa har da soyayya.

Ya kamata mu bada dan takaitaccen labari kan kowane littafin cikin zafafan mu yanda zaku samu kwarin gwiwar neman cikakkun labarun domin kusha karatu.

10. TAFIYAR MU NA SUWAIBA MUHAMMAD

Labarin Tafiyar mu ya karkata ne kan zama da mutane masu fuska biyu, wato masu munafuntar wadanda suke rayuwa tare dasu.

Juwairiyya matar Hafiz ce shi kuma Hafiz abokin Muhammad ne, Juwairiyya ta yi rayuwa da Hafiz cikin kwanciyar hankali da qaunar juna kafin Allah ya dauki rayuwar shi wanda kafin ya rasu suka yi alkwari da abokin shi Muhammad akan duk wanda ya riga dan uwanshi Rasuwa dayan zai auri matar shi. Wannan dalilin yasa Muhammad ya kawo ma Juwairiyya maganar aure sai dai alokacin ta qi amincewa dashi saboda tana mishi kallon mai baudadden hali, dadin dadawa kuma tana ganin shi matsayin mijin qawar ta Salima, bayan haka ta auri Baban qawarta Halima, Wannan auren bai dade ba suka rabu sakamakon bashi da lafiyar sauke mata dukkan buqatun ta na yau da kullum.

Bayan auren ta na biyu ya mutu ta fuskanci qalubale masu yawa ciki har da haduwa da Salisu mai bin malaman tsibbu wanda ya asirce ta da iyayen ta sai daga baya Muhammad ya kubutar dasu ta hanyar karbo mata adduo’in karya sihiri hakan yayi silar da ta haqura ta Karbi auren abokin marigayin mijinta wato Muhammad. Juwairiyya ta sha matuqar wahala a zaman gidan Muhammad da farko kasancewar matar shi Salima mace mai fuska biyu, tana nuna ma Juwairiyya qauna a fili sai dai kuma tana hada ta fada da duk mutanen da suke rayuwa tare ciki har da mijin su. Hafsa qanwar Hafiz da kuma Iyami qanwar Muhammad su suka ceto Juwairiyya daga wannan tasku na zama da munafukar kishiya, kura lullube da fatar akuya, bayan ta fahimci halin Salima ne ta canza yanayin zaman da suke yi da mijinta suka fuskanci juna suka zauna lafiya.

Kwana dubu ta barawo rana daya tak ta mai kaya, munanan halayen Salima sun bayyana dumu dumu a gurin Muhammad wanda ya bata dukkan yardar shi bai san tana bata shi ne a gurin mutane ba, tana nuna ma duniya cewar ita mai tsananin haquri ce kuma shi yake zalintar ta wanda hakan yasa kowa ke tausaya mata suna ganin batayi dacen miji ba ciki kuwa har da juwairiyya wadda hakan na cikin silar da yasa tun da farko ta qi Muhammad.

9. MANSOOR NA SADNAF

Littafin Mansoor labari ne kan wani matsahin malamin jami’a mai suna Mansoor da ya fada soyayyar wata yarinya mai suna Humaira sai dai yayi rashin Sa’a kasancewar Humaira matar aure ce wadda hakan yasa taki kula shi har shaidan yayi ta mishi zugar da ya kai ga sace ta ya kai ta cikin daji, bayan ya kaita daji zuciya ta rinjaye shi yayi mata fyade daga baya yazo Yana nadamar hakan har ya roqi ta rufa mishi asiri.

Bayan wani lokaci sai ga ciki ya bayyana jikin Humairah wanda hakan yayi sanadiyyar da mijinta mai suna Sauban ya tirke ta Akan sai ta fadi mishi wanda ya mata cikin nan domin kuwa shi ya san yana da matsalar rashin haihuwa, Wannan dalilin yasa asirin Mansoor ya tonu kuma hakan ya Sauban ya rabu da Humairah sannan matar Mansoor mai suna Noor itama ta rabu da Mansoor.

Bayan wani lokaci Mansoor ya auri Humairah sai dai basu dade ba ya rabu da ita akan yana so ya dawo da tsohuwar matar shi Noor, bayan fadi tashin da yayi Noor ta qi dawo mishi inda tayi wani auren sai shi ma ya haqura ya koma gurin Humairah aka maida auren su wanda daga baya aka gano ita Humairah tana da alaqa da mahaifiyar Mansoor.

7. ABBAN SOJOJI NA HAFSAT BATURE (BOSS LADY)

Labarin Abban sojoji labarine na wata yarinya mai suna Sherish wadda suka kasance yan uku ne ita da yan uwanta da suka taso suna rayuwar gararamba sakamakon rashin sanin dangin su, Sherish sun rayu ne a gurin wata tsohuwa inda daga baya yan uwanta guda biyu Johad da Hosana suka fara rashin lafiyar da tayi tsamari , ga ciwo ga rashin kudin da za akula dasu wannan yasa Sherish ta fita neman aikatau gidajen masu kudi. Ta samu aiki amma kuma sai aka samu akasi gidan maza ne zalla wanda wannan gida shine gidan Abban sojoji.

Gidan Abban sojoji gida ne da wani soja da iyalan shi ke rayuwa wanda bashi da yarinya mace ko daya sai maza, mazan kuma duka sojoji ne kamar yanda shima ya kasance soja, mahaifiyar shi ma soja ce shiyasa abin na shi ya zamo mai asali. Sherish ya samu damarl shiga gidan Abban sojoji a matsayin namiji mai aiki domin kuma sai da suka samu wani mai kwalliya ya canza mata fuska t koma kamar namiji, tana aiki a gidan na tsawon lokaci kafin su gano mace ce ita ba namiji ba.

Wani abin farin cikin da ya faru da Sherish shine daga baya an gano cewar ita da yan uwanta ashe yaran daya daga cikin yan gidan da take ma aiki ne da ake kira da uncle Abusufyan, ya auri mahaifiyar su a boye ba tare da sanin yan uwan shi ba har suka rabu inda ta tafi bai san tana dauke da cikin yan uku ba, bayan rabuwar su taje ta auri ya Sayyadi da cikin nan wanda bayan ta haife su bai kula dasu ba ya bar su sukayi rayuwa a wulaqan saboda yana ganin ba jinin shi bane.

Bayan su Sherish sun gano yan uwansu na  asali rayuwa ta canza musu zuwa kyakykyawa duk da lokacin tsohuwar da ta kula dasu ta rasu. Sun ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali tare da dangin su wanda ko wacce tayi aure kuma suka samu zaman lafiya da mazajensu.

8. KA NA NAKA NA JANAFTY

Littafin Kana na ka labarin wata baiwar Allah ne mai suna Fa’iza wadda ke da tsananin haquri, juriya da tawakkali domin kuwa Allah ya hada ta zaman aure da Ishaq wanda yake ganin shi ba ajinta bane saboda yana da kyau da rufin asiri ita kuma Fa’iza yana mata kallon mummuna mara ilimi, wayewa da kuma aji, atakaice dai bata dace da zama matar shi ba ta kowane fanni.

Fa’iza ta jure wulakanci da cin fuska kala kala daga Ishaq wanda ta rayu cikin qunci da baqin cikin shi domin kuwa hatta abincin da zata ba yaran ta sai da ya fara gagarar ta duk da cewa mijinta na da rufin asirin shi. Ishaq ya auri irin zabin macen da yake so yar gidan masu kudi kuma kyakykyawa sai dai kuma kyawun hali na gurin Fa’iza.

   Bayan fuskantar tarin qalubale da Fa’iza tayi daga baya Allah ya kawo mata qarshen wahalar ta ta hanyar qawar qanwar Ishaq wadda ita kadai ke son ta cikin dangin mijin na ta. Fa’iza ta samu shiga ajin da ake koyawa mata masu rangwamen gata aka koya musu sana’o’i kuma aka basu jari inda ta fara sana’ar ta kuma Allah ya buda mata ta fara daukar nauyin gidan ta da yaran ta, Ishaq ya hadu da jarabawar rashin aikin yi wanda sanadin hakan ya gano cewar Fa’iza ba matar wulakantawa bace domin kaf nauyin shi da na iyayen shi ita ta ci gaba da daukar nauyin su har ya samu kan shi.

 Hausawa sun ce mai haquri bai iya fushi ba, hakan ce ta faru da Fa’iza domin kuwa ta nemi rabuwa da auren Ishaq wanda shi kuma yake jin lokacin ne ya fara son ta, bayan an kai ruwa rana da Fa’iza an kada an raya amma tace ta gama auren Ishaq wanda aka tilasta mishi sakin ta ya ci gaba da rayuwa da zabin ran shi.

  Mahaqurci akullum mawadaci ne domin kuwa, Fa’iza ta hadu da mai son ta don Allah wanda bai damu da duk nakasun da take dashi ba ya aure ta a hakan kuma ta samu dukkan farin ciki, qauna, tattali da zallar soyayya mara algus agurin shi da dangin shi.

6. AMATULMALIK NA MAMUHGEE

Labarin Amatulmalik anyi shi ne kan wata yarinya mai suna Amatulmalik wadda Mahaifin ta ya rasu ya bar su da ita da qanin ta a hannun mahaifiyar su, Amatulmalik sun taso cikin tsananin talauci da kunci tare da mahaifiyarsu inda dangin mahaifin su ke gallaza ma Rayuwar su kafin sauqi yazo musu na har abada.

     Sauqin su Amatulmalik ya fara zuwa ne lokacin da yar uwar mahaifiyar su da ke rayuwa a garin Abuja ta fara ciwo mai tsanani na sankarar jini. Amatulmalik sun koma rayuwa gidan Ash talba ne bayan matar shi Mommy Abida ta fara wannan matsanancin ciwon, bayan komawar su gidan talba sun samu kyakykyawar rayuwa kafin yaron qanwar talba wato Mum Aisha mai suna Naufal yayi yunqurin keta ma Amatulmalik haddi. Wannan lamari yayi tsamarin da mahaifiyar Amatulmalik tayi yunqurin komawa qauyen da ta fito saboda ta kare martabar ‘yar ta, hakan ya jawo Ash talba ya yanke hukuncin auren Amatulmalik saboda yasan ragamar gidan shi a hannun mahaifiyar Amatulmalik take kuma bai san wa zai kula mishi da yaran shi ba idan ta tafi.

Auren Amatulmalik da Ash talba ya jawo cece kuce masu yawa sun kuma fuskanci qalubale kala kala wanda cikin su har sai da Husna diyar Ash tayi sanadin rasuwar mahaifiyar ta da sunan tana taya ta kishin Amatulmalik din, Wannan abu da ya faru ya qara hargitsa rayuwar wadannan iyalin kafin daga baya abubuwan suka lafa kowa ya ci gaba da rayuwar shi cikin kwanciyar hankali.

5. KWARYA TABI KWARYA NA SADNAF

Labarin Kwarya tabi kwarya anyi shi ne kan Wata matashiya mai suna Amira da Wani matashi mai suna Amjad wadanda suke matuqar son junan su, mahaifiyar Amjad mai suna zinatu ta hana su auren saboda mahaifin Amira wanda qani ne gurin Mahaifin Amjad ya kasance talaka ita kuma tafi son ‘ya’yan ta su auri masu kudi kasancewar shi Mahaifin Amjad Alhaji Habu yana da dukiya shiyasa take son suyi auren kwarya tabi kwarya.

  Bayan zinatu tabi duk hanyoyin da zata bi ta hana auren sai Allah ya kawo ma Amira wanda yafi su dukiya kuma yariman garin gaba daya, ta auri yarima sunyi Rayuwa ta yan shekaru kafin Allah ya amshi ran shi inda daga baya iftila’i ya fada ma zinatu gurin bin bokayen ta domin a tagayyara rayuwar su Amira da Iyayen ta.

  Amjad ya samu damar auren Amira ne daga baya kuma sun rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

4. FURAR DANKO NA BILLYN ABDUL

Labarin Furar danko wanda akace ka shekara kana damu ba ta farau farau, labari ne mai cike da sarqaqiya da kuma boyyayar soyayya, labarin Aliyu Mawashi wanda akafi sani da smart mawashi da kuma Mawaddatan wa rahma da ake kira Lulu qamshi.

  Shi dai Smart mawashi ya hadu da kishiyar uwa da ta mishi sihiri, hakan yasa ya kasa buga kwallon kafa wadda itace burin rayuwar shi, sai daga baya ya hadu da kawun Lulu ya taimaka mishi asirin ya karye ya samu cikar burin shi.

  Lulu kuma yarinya ce da ta taso cikin halin rashin tarbiyya da wulaqanta talaka sai dai itama haduwar ta da mawashi da kawun ta ya kawo mata matsayin driver ya taimaka mata gurin canza rayuwar ta zuwa ta mutanen kirki bayan ta yi auren manufa dashi wanda daga baya ya koma auren soyayya mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali.

3. ZAFIN KAI NA MAMUHGEE

Labarin zafin kai anyi shi ne kan wani mutum mai suna Ababa wanda yake azabtar da matar sa Anne da yaranshi mata guda hudu Samira, Sumayya,Benazir da kuma Safnah. Tsananin azabar da yake gana musu ta sa Samira yunkurin guduwa wanda sanadin hakan Mahaifin ta ya gana mata azabar da tayi sanadin rasuwar ta. Bayan mutuwar samira safna ma ta samu nasarar guduwa daga hannun shi ta fada duniya inda sauran biyun da mahaifiyarsu suka ci gaba da shan azaba hannun Ababa da ya maida su tamkar dabbobi saboda duka da ayyukan da yake basu gashi kullum suna kulle cikin daki ga yunwa da suke zama da ita sakamakon abinci kadan da Hande mahaifiyar Ababa take basu.

   Dukkan tsanani yana tare da sauqi, Ababa ya kai benazir da Sumayya jami’a domin su qaro karatu saboda zai ba masu safarar miyagun kwayoyi auren su kuma ya san baza su karbe su ba idan basu da ilimi saidai su kuma yaran wannan makaranta itace mabudin Alkhairin su domin acan Sumayya ta hadu da Bilal Kante wanda ya fada soyayyar ta farat daya har tsautsayi ya afka musu yayi ma Sumayya ciki wadda haihuwar yarinyar mai suna Amna yayi sanadin shigar Bena cikin iyalan Kantees domin sumayya ta rasu gurin haihuwar Amna sai dai kwadayin Ababa yasa ya musanya musu Benazir a matsayin Sumayya ta auri qanin Bilal din suka raini Amna Wanda daga baya Sumayya da Bilal sun bayyana kansu sukayi bayanin basu mutu ba kawai ya dauke ta ne ya fita da ita qasar Canada domin nema mata lafiya.

2. TABARMAR KASHI NA HUGUMA

Littafin Tabarmar kashi ya kunshi labarin Sahar da Taufiq wadanda suka hadu da jarabawar rayuwa ta hanyar samun abokan zama masu son abin hannun su.

   Sahar ta auri Adam sunyi Rayuwa tare kuma ta so shi domin Allah sai dai shi duk tsawon zaman da sukayi yana zaune da ita ne ba don Allah ba sai don ya kwashe dukiyar da ta mallaka, yana gab da cikar burin shi asirin shi ya tonu wanda hakan ya zamo silar rabuwarsu.

   Toufeeq ya auri Ameesha shima da zuciya daya saboda tausayin ta da ya tsarga mishi matsayin ta na marainiya daga baya ya fara son ta wanda ita kuma ta ha’ince shi saboda dukiyar shi take so ba shi ba.

  Qaddara ta hada Sahar da Toufeeq zaman qarqashin inuwar aure inda kowa ke qin Dan uwanshi sakamakon tabon da aka bar musu a zuciya sai daga baya suka fahimci sune mafi dacewa da juna suyi zaman aure kuma suka gina kyakykyawar rayuwa tare da yaransu.

1. NIHAD NA KHALEESAT HAYDAR

Littafin Nihad labari ne kan wata yarinya mai suna Nihad,  wadda ta taso a mara nutsuwa da tarbiyya sakamakon makahon so da mahaifin ta ya nuna mata da kuma tunzurawar matar Mahaifin na ta wadda a fili take nuna kamar tafi kowa son Nihad amma a zuciyar ta tana zuga Nihad ne domin ta zama mara tarbiyya kuma gagararriya.

  Nihad ta cigaba da rashin tarbiyyar ta na yawon club da bin qawaye har sai da akayi ta yawo da hoto mai motsi da yake nuna tsaraicin Nihad a yanar gizo. Wannan lamari yayi tsamarin da har matar Mahaifin Nihad ta zuga Mahaifin ta ya ba daya cikin ma’aikatan gidan ita a tunanin ta ta qasqantar da rayuwar Nihad wanda dama shine burin ta.

 Rashin sani yafi dare duhu, domin kuma Hajiya Sumayya tayi ganganci saboda wanda tasa aka aurawa Nihad dan gidan shahararren attajiri ne wanda take tutiyar baza ta taba bari Nihad ta aura ba. Bayan wannan matsayi na mijin Nihad ya bayyana ga dangin ta, Umma ta kasance cikin matuqar dana sani saboda Nihad ta samu rayuwa irin wadda take ta ma yaranta fata su kuma yaranta abubuwan qi da taso Nihad tayi su suka dawo musu.

 Asirin da aka yi ma Mijin Nihad wato Khalil na raba shi da Mahaifin shi ya karye inda mahaifin ya nemi ya koma gida cikin yan uwanshi sai ya tafi da Nihad bayan an daura musu aure amma ya boyewa iyayen shi matsayin Nihad a gurin shi ya fadi musu mai gidan shi ne ya bashi ita ta wuce makaranta sai daga baya suka gano gaskiyar, Khalil ya hadu da bacin ran iyayen shi kafin su haqura su bar shi ya rayu da matar shi cikin qauna da tattali tare da kwanciyar hankali.

Bayan wadannan Zafafa namu guda goma, akwai wasu littattafan da suka shiga cikin jerin gwanon sunayen da muka yi tantancewar mu dasu duk da basu samu shiga cikin zafafa ba, amma suma sun samu masoya dayawa. Littattafan sune kamar haka :-

– Kyalkyalin qauna na M Shakur

-Qanwar Maza na Aisha Adam

-Rufafffen Sirri na Sadnaf

– Na fado daga bene na zarce rijiya na Badiat Ibrahim

Kammalawa

Wannan Rubutun anyi shi ne domin bayani Akan littattafan da suka zama zakaran gwajin dafı a shekarar 2023, Hakan zai qara ma marubutan himma akan aikin su saboda kwadayin rubutun su ya shiga sahun zakarun qarshen shekara kuma sakamakon hakan za a qara samun yawaitar labarai masu dadi da ma’ana wadanda zasu dauki hankulan makaranta sannan a qara fadada lamarin fadakarwa da nishadantarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *