𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣
……..Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard ɗin sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik ɗin ya dubesa. Komai a gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik ɗin. “Ranka ya daɗe Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu ƙamshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so ɗin ba. Kamarka ma ɗan manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta”.
Ƙaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. “Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faɗamin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka”.
Cikin rashin damuwa saurayin ya faɗa masa cikakken adireshin gidan su Lulu ƙamshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buɗe masa fuskarsa ƙawace da murmushi……
*_Manseer M Atik Kumo_* kenan. Ɗa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban ɗan siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin ɗan kasuwa ne da kuɗi ke kaɗa masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaɗar marasa ji na ƴaƴan manyar ƙasar sune ɓoyayyun limamai. Manemin mata ne ƙwararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziƙi abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko’ina yake yarda ya nuna halinsa mara ƙyau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya ƙaryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai….
Wannan kenan.
∆••••••∆ ★ ∆•••••∆
Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ɗin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leƙowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ɗin wulaƙanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Ko gama parking mai taxi ɗin baiyi da ƙyau ba ta ɓalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaɗa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ƙafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ƙafarta mai shegen tsini. Duk wani ma’aikaci dake gidan da ga kallo ɗaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buɗaɗɗen abune ga duk wani ma’aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ƙanƙantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ƙanƙanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ƙoƙarin mata a yanda ta buƙata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daɗi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ƙanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu’a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu’ar tasu bata amsu ba😂 dan gata ta dawo ɗin a bazata.
Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ɗagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa.
“To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faɗa cikin taɓe baki. Kamar mai jira a taɓata a fusace ta ce, “Shi ɗan uban waye a ƙasar nan da aka aikashi ɗakkoni? Miyake taƙama da shi?…”
Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ɗaya da jarida a hannu ya miƙa mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.
“Daddy babu maganar zama a fara faɗa min uban waye shi?, dan sai na wulaƙanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faɗamin ba ALLAH duk wani ma’aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan…”.
Sun san zata iya aikatawa, kaɗan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ɗin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, ƙyawun fuskar tasa ne inaga ke ruɗarsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!…..” Ta ƙarasa maganar a hankali cikin ƴar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, “Wai miya miki ne? Bai je ya ɗakkokin ba?”.
“Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faɗa mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi” yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, “An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy ɗin nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!”.
Cikin sauri dattijon ya miƙe yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace “Kinga Baby yi haƙuri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan ɗauki matakin dan bazan taɓa zama da wanda zai saɓa miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai ɓata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat ɗin Daddynta yanzu zan nema Yousef ɗin ma ya dakatar da shi”.
Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna ɗin, sauran yaran duk sai suka shiga taɓe baki. Hakama mamansu tsaki ta ɗan ja a hankali tama miƙe tabar falon. Shiko Daddy ko’a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haƙuri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine ƴar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. Kaɗan tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaɗarsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaƙin yaƙin duniya, sai kuma zuwa can ta ɗan ɗago. “Daddy kar ka kira Uncle Yousuf ɗin ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja”.
“Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke”.
“Thanks you sweet Papa..”
Ta faɗa tana ɗan rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miƙe, yatsu biyu ta ɗaya masa alamar bye ta nufi ɗakinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta ɓacema ganinsa. Bata zauna a ƙayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. Ɗaki ne haɗaɗɗen gaske kuma ƙato. Dan bayan ƙaton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai ɗakin ya haɗu tare da amsa sunansa ɗaki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faɗa da masifarta ta daka mata tsawa. “Da uwar mi kike a ɗakin da baki gama min ba har na shigo….?”
“A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma’aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da ƙyau har jikin bangon da kikace”.
Kakkauran tsaki ta ƙara ja da ƙarasa shiga ɗakin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen ƙyau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faɗa ta kwanta tana mai wargaza fillos ɗin da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buɗe, a gadarance ta ce, “Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haɗamin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza ƙazamiya sai wani tsamin zufa kike”……..✍️
*_Humm nama rasa abin cewa nikam😶😒._*