Furar Danko Hausa Novels

Furar Danko Chapter 4

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣

……..Idanun dattijuwar cike da ƙwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata ɗaga ƙafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma itafa da sauƙi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata ɗaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key ɗin ɗakin ita kaɗai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai ƙamshi amma ta ce mata tana warin zufa. “ALLAH ya shiryeki ƴarnan” ta faɗa cikin tausasawa tana ɗauke ƴar ƙwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaƙancin da Lulu ke mata tana ƙyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta ƴaƴanta dake ƙauye da ƴan jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, da2 in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf ɗin ne ya ɗan fi cin nasararta, dan shi har faɗa yakan ɗan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai ɗin bane ba….

  Wannan kenan

         ∆•••••∆ ★ ∆•••••∆

     Da ga airport babban kamfanin Jiƙamshi’s ya nufa ransa a ɓace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa’ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya ƙara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key ɗin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay ɗan rubutu ya haɗa da key ɗin. A takaice yace, “Ki bashi idan ya dawo”. Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da ɗan taɓe baki…

      Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ƙofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ƙasan maƙoshi har yanzu zuciyarsa na masa ƙuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika’il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ƙasƙantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ƙarfin ƙwanjinsa amma ba ƙasƙanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ƙarƙashin takalmin kowa ba. Da’ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ƙasusuwa ya zubar da ita a airport ɗin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ƴa mace…..

         “Ɗan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faɗa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ɗin maimakon amsa, ya zaro ɗari biyu a cikin aljihunsa ya miƙa masa. Bai jira mai napep ɗin da ke faɗa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..

       *_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ƙasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuƙar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ɗa na bakwai a gurin Malam Mika’il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huɗu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuƙar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ƙwallon ƙafa. Ya iyata matuƙa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ɗinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ƙwallo sai ya yanke jiki ya faɗi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al’amarin da asiri, sai dai shi yaƙi ɗaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara ƙwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana’a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ƙanƙanin lokaci al’amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ƙoƙarin kamo can idan nan taƙi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ƴan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika’il Idris Mawashi huɗu ne cif, hakama ƴaƴa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ƴammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu………✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *