𝗣𝗮𝗴𝗲 4️⃣
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta.
“Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa”
Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya.
“Hajiya natsuwar ce ta gagare ni samu, ba yau na fara jin bana da sukuni idan bana tare da Iyami ba, ji nake kamar wani abu ne a saman kaina, sai a yanzu da na sauwake mata sannan na ji nauyi ya sauka, ni kaina ina son Iyami amman bana jin natsuwa a zamantakewarmu yanzu, kuma na yi ta addu’a ina fatan samun sauki abun amman hakan ya gagara wata kila sakin shi ne mafi alheri daman aure rai ne da shi”
“Har saki nawa ka yi mata tsoho?”
“Daya na yi mata Hajiya”
“To da sauki idan abubuwa suka daidai wata kila za a iya gyarawa, ko dan yan diyanta Tsoho, dubi Hurriyya da Hamad ga cikin dake jikinta yaran nan ba za su taba jindadin zama a gidan idan bata ciki ba, ko ma kallon iyayen kowa na nan ta su bata nan sai ya saka su jin wani iri”
“In Sha Allahu zan ba su duk wani jindadi da farinciki da yaya suke bukata a gurin uwa da uba, ban taba fadar maganar nan a gaban kowa ba sai yau a gabanki, Hajiya duk cikin yayana na fi kaunar Hurriya, saboda kokarinta ga kuma lalurar da take tare da ita, Allah ya saka min tausayin yarinyar nan, fitowa daga gida zuwa nan Wallahi yaran nan kawai nake ta tunani a raina”
“Tsoho”
Ta kira sunansa sai ya dago ya kalli mahaifiyarsa da fatar jikinta ta fara zazzaga saboda tsufa.
“Dan Allah idan ka samu sukuni ka dawo da Iyami dakinta, ko ba komai ta saba da rayuwar jindadi ga kuma ciki ga tunanin yaranta be kamata ka saka mata da haka a irin wannan lokacin ba, idan ma baka yi hankali ba tana cika idda wani zai dauke ta mace mai kyau da kurciya haka nan, ka kusan haihuwarta fa amman tana zaune gidanka gwanin sha’awa ga girmama mutane yarinya mai hankali da tarbiya”
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi.
“Hajiya ban sake ta sai da na bata kyauta gidana da yake samaru, kuma na bata kudin da zata iya rike kanta da su naira miliyan ashiri, kuma babu abun da zan karba daga kyautar da na taba mata, kayan dakinta da komai ma gobe zan saka a kwashe a kai mata har gidansu, wata kila dai zaman auren ya kare gaba daya, dan Allah karki cilasta ni aikata abun da zai hana ni samun natsuwa ki yi mana addu’a kawai”
“Toh Tsoho Allah yasa hakan shi ya fi alheri, ya kawo mafita a tsakaninku”
Hajiya ta fada muryarta na rawa hawaye na cika idonta har suna kokarin zubowa, mikewa ta yi tsaye ta shige dakinta ta bar shi a katon falon dake cike da sanyi ac. Hannu ya saka ya dage kansa yana jin wani karin rashin natsuwar da bakinciki na kusanto shi, ada yayi tunanin idan ya rabu da ita zai samu sakewa, sai dai bakinciki rabuwa da ita ba dan zuciyarsa na so ba, da kuma tunanin damuwar da yaransa za su shiga ya hana shi samun natsuwa, arzikinsa daya a yanzu ya daina jin wannan nauyi da yake ji a lokacin da yake tare da ita. Ya dade zaune a cikin falon kamar wanda ya rasa makama sannan ya tashi ya fice yana gyara babbar rigarsa. Yana fitowa direbansa ya fito ya bude masa motar ya shiga ya maida kofar ya rufe sannanya zagaya ya shiga mazaunin tuki ya tashi motar suka fice daga gidan, kamin ya isa gurin da yake gudanar da kasuwanci kiran Bappa ya shigo wayarsa ya fi a kirga amman yaki ya daga saboda ya san maganar Iyami za su yi masa.
HURRIYA POV.
Yassar na riga da hannunta har suka isa part dinsu, shi ya fara tura kofar falon ya shiga sannan ya rikota ta shigo.
“Careful”
Ya fada yayinda take saukowa kan karamin stairs din dake bawa mutum damar shiga cikin falon.
“Hamad….!”
Yassar ya kira sunansa a tsawace sai ya juyo rike da kofin kankara yana kallon kofar falon fuska babu annurin ido sun masa ja alamar yayi kuka sosai.
“Akan me zaka daki Hurriya kuma ka fasa mata glass?”
Yassar yana fada ya saki hannun Hurriya ya nufi inda yake tsaye cikin bacin rai, a maimakon Hamad ya gudu kamar yadda sauran yara ko kuma kanen Yassar suke idan zai dake su, shi sai yayi tsaye yana jiran isowar Yassar idan ma yanka shi zai yi sai dai yayi, amman taurin zuciyarsa da jin zai iya karawa da kowa a gidan ya hana shi tsoron kowa.
“Ba magana nake maka ba?”
“Ita take shiga min hanci”
“Ba hanci ta shigar maka ba ido, ko laifi ta yi maka ba ita ce Yayarka ba? Kana namiji zaka rika fada da mace? Kuma macen ma yar’uwarka? Sannan duk abun da zaka mata be isa a fatar baki ba sai ka kai ga fasa mata gilass gashi nan ai ka ja Musib ya mareta”
Yassar na kaiwa ayar karshe Hamad ya ji ransa ya yi mugun baci zuciyarsa ta kawo kamar wani babba.
“Me ta yi masa to?”
“Ba a sani ba, da baka fasa mata gilashin ba zata tafi tana lalaben fuskarsa ne har ya kai ga marinta? Haba Hamad kai baka jin tausayin yar’uwarka ne? Kowa yana zaune lafiya amman kai ban da kai? Gidan ka fitini kowa? Ita din ma ba zaka raga mata ba?”
Yassar ya juya ya kalli Hurriya.
“Hurriya zo nan”
Daga inda take tsaye ta fara takowa cikin abun da Allah ya yassare mata na gani har ta iso gurin ta tsaya daidai inda Yayanta yake tsaye.
“Ka bata hakuri”
Hamad ya kara murtuke fuska.
“Ita zata fara ba ni hakuri ai ita ta fara taba ni”
Kasancewar Hurriya mai son zaman lafiya ce ta tsoron fitini ko tashin hankali yana rufe baki ta bude nata.
“I’m sorry”
Yassar ya kai mata duka a saman kai
“Waya aikeki shi ya kamata ya fara baki hakuri ai, ba ki ce babba ba”
“I’m sorry too”
“Okay bata hannu ku gaisa”
Yassar ya fada, nan kam ba musu Hamad ya mika mata hannu, sai ta mika hannayenta duka biyu ta lalabo hannunsa ya mika masa nata suka yi musabaha.
“Good ba fada daga yau kun yarda”
Hurriyya ta daga kai, shi kuma goga ya ki cewa komai. Yassar ya juya yana fadin
“Bari na dauko miki glass dinki da yake dakina”
Yassar na fita falon, Hamad ya kama hannun Hurriya suka isa dinning yaja mata kujera ta zauna, ya aje kofin kankarar dake hannunsa sannan ya juya ya nufi sama, kai tsaye dakinta ya shiga yana shiga ya bude gurin da take aje kayanta ya dauko box din glass din daya daya rage dakinta ya sauko da saurinsa ya tsaya gabanta ya bude glashin ya saka mata da kansa, sai gata tana murmushi ganin ganinta ya dawo da kyau kamar kowa.
“Thank You”
“Ki sha cornflakes dinki zamu tafi Islamiya”
“Kai ba zaka sha ba?”
“Na sha zobo”
“Amma ta ce… ”
Tunawa da ta yi da cewar idan ta fada masa Amma tace su daina zama da yunwa zai iya rufe da fada wata kila ma ya hada mata da duka ya saka ta fasa fadar hakan.
“Toh”
Hannu ta mika ya janyo kofinta na dazun da ta jika cornflakes din ta fara sha, bata juyo ba sai da ta ji karar bude kofar falon.
“Kin dauko wani?”
“Hamad ya dauko min, daman shi daya ya rage”
Yassar yayi murmushi daman ya san masu saurin fushi da fitina sometimes sun fi kowa zuciya mai kyau.
“Ya kyauta bari naje na aje wannan”
Ya juya sai Hurriya ta kira shi.
“Yayana”
Ya juyo
“Thank you”
Yayi mata murmushi.
“Ur welcome”
Ya fada sannan ya fice daga falon ita kuma ta juya ta cigaba da shan cornflakes dinta. Yana rike da box din glass din ya shigo part dinsu, stairs ya hadu da Hajiya Kaltume tana saukowa shi kuma yana kokarin hawa, kiran sunanta yayi sai ta tsaya tana kallonsa.
“Hajiya me kika fahimta da maganar Hurriya?”
“Wace maganar?”
“Cewar Amma zata tafi gida har sai ta haihu”
“Ikon Allah Yassar ina ce dai ni da kai duk kunne biyu muke da shi kuma kai ma ka ji maganar nan, bakin halin ne da tashi da zaka ce me na fahimta? Ina ruwanka da fahintata? Aunata fahimtata akan wane dalili?”
“Haba Hajiya magana ce kawai fa, tsoro nake ji kar dai a wani abu ya faru?”
“Koma minene ai idan ta yi tsami zamu ji, miye a hannunka?”
Ta tambaya a kokarinta na kawar da maganar. Ya kalli box din.
“Gilashin Hurriya ne”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi.
“Sai ka yi dan gatan Hurriya, gar yanzu kana ajeye da gilasanta”
“Uku ne kawai a hannuna, biyu suna hannunta Hamad ya fasa dayan yanzu sauran hudu”
“Yayi kyau ka cigaba da aje su da kyau, Allah ya raya maka yar kanwar nan taka Yassar”
“Ameen”
Ya amsa sannan ya wuce ya haye sama, Hajiya Kaltume ta bishi da harara.
“Kai kan ba dan a cikin gida na haife ka ba, sai na ce canja min kai aka yi, yaro sume sume sai munafurci fal a ciki oh ni Kaltume”
Ta ja tsaki sannan ya karasa saukar ta nufi kitchen dinta, tana shiga hannunta ta fara wankewa sannan fara juya miyar dake kan wuta, da gudu Umm Salma ta shigo kitchen da wani irin murna har haki take.
“Hajiya Khari ya kira ni tace Appa ya saki Amma?”
Hajiya ta yi mata alama da ta yi shiru da sauri tana nuna mata kofar kitchen din.
“Bari sai Yayanki ya fita kume farincikinki”
Salma ta daga kai cikin murna ta fice daga kitchen din tana tsalle saboda jindadi. Sai da Hajiya ta gama miyarta tsab sannan ya kwashe ta kawo ta a dinning kana ta nufi stairs tana kwalawa yaranta kiran
“Umm Salma ko Umm Khairi waninku ya zo ya jera mana abinci a dinning”
Salma ce ta fito har wani tangadi take tana rawa kunneta na makale da ipod, Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta dauke kai ta shige dakinta, da sauri ta karasa gurin gadonta cikin nauyin jiki irin nata ta dauki wayarta da kiran ke daf da tsinkewa.
“Hello Hajiya ina wuni”
Daga dayan bangaren Hajiya Binta ta amsa.
“Lafiya Kalau, Kaltume ke kadai kike?”
Hajiya Kaltume ta yamutsa fuska daman a gurinta uwar miji bata da wani muhimmanci.
“Eh Hajiya ni kadai nake, Lafiya dai?”
“Toh Lafiya ba kalau ba, magana nake son yi dake akan yaran nan Hurriya da Hamad”
“Me ya faru da su?”
Hajiya Binta ta sauke ajiyar zuciya.
“Dazun mijinki ya zo nan ya fada min hukuncin da ya yanke akan Iyami, ba mu san abun da Allah zai yi a gaba ba, amman kamin nan Kaltume ina son ki ji tsoron Allah ku rike Hamad da Hurriya amana, domin su da marayu duk daya a yanzu”
Hajiya Kaltume ta kai zaune saman gadonta farinciki a mamaye ta, domin dazun hasashe take yanzu kuma gaskiyarce zaharan Hajiya Binta zata fada mata.
“Hajiya ban fahimce ba”
“Ai kin san komai Tsoho ba zai rasa fada muku ba”
“Wallahi be fada mana komai, wata kila dai ita Nafisa ya fada mata, amman ni ban san komai ba”
“Dazun ya zo nan ya fada min cewar sheidan yayi nasara akansa ya sallami Iyami, sai dai saukin abun saki daya yayi mata, kuma be sallame ta ba sai da ya damka mata gidansa dake samaru area kuma ya bata kyautar naira miliyan ashiri, duk da haka dai ina kyautata zaton zata dawo dakinta kamin lokacin ke da Nafisa duk ina son ja muku kunne akan yaran nan”
Hajiya Kaltume bata san lokacin data mike tsaye ba ta daki kirjinta da karfi.
“Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un… Amman Alhaji yayi kuskure abun da ba ayi da kurciya tun can da ba za’ayi yanzu bayan ga yara”
“Ni dai na kira na ja muku kunne ne kawai, domin na san ko na nemi ya bani yaran ba zai aminta ba saboda yana son yayansa kamar yadda yake son uwarsu, Allah ya tabbatar mana da alheri”
Hajiya Binta na kaiwa nan ta katse kiran. Wani irin bille baki Hajiya Kaltume tayi ta kube shi.
“Munafurcin banza da wofi, wato ga Kaltume makiyiyar Iyami da yayanta har da wani kira ki bani amanar yara, ko mutuwa ta yi ai ba zan karbi amanar yayanta ba balle tana da rai, idan kin isa ki saka ya dawo da ita mu gani, har kina fada min yana son yayansa kamar yadda yake son matarsa tsabar kin raina ni”
Duk wani farinciki da walwala dake zuciyarta da fuskarta ya gushe tun daga lokacin da ta ji cewar sakin ďaya aka yi ma Iyami kuma an bata kyautar kudi da gida.
“Wallahi Iyami kin cuce ni, ko a haka dai kin ci ribar mijina, kin haihu da shi dan ki ci gado, kuma yanzu ya sake ki ya dauki gida da miliyan ashirin ya baki, waya taba yi ma kyautar gida a cikinmu matansa, sai dai ko wace ta siya da kudinta”
Password din wayar ta cire ta duba kiran dake kasam na surukarta Hajiya Binta ta taba na Hajiya Fatee. Kamin ta amsa duk ta kagu har ta fara saba da marwa a dakin.
“Assalamu Alaikum Kaltume”
“Hajiya Fatee zama be gan ni, tsugune bata kare ba, Saki daya Alhaji yayi ma Iyami, kuma wani abun da ya fi ko wane bakin ciki kudi ya dauka ya bata har naira miliyan ashiri”
“Million ashiri?”
“Ai ba nan haushin yake ba, ya bata kyautar gidansa dake samaru, yanzu uwarsa ta kira tana fada min har wani gargadi take min saboda ya san gatan jikokinta, kin san ba jikokin da take so irinsu, kuma tun da saki daya ne zata iya buga kafa a kasa tace sai ya maida uwarsu”
“Tsab kuwa wannan shegiyar tsohuwar zata iya, saboda ba sonki take ba”
“Ina fa, kuma ba ba zancen dawowarta kina ganin zan yarda Iyami ta bar gidan mijina kuma ta yi arziki da dukiyar mijina? Wallahi bata isa ba ai yadda ta ci amanata haka ni ma zan nuna mata ruwa ba sa’an kwando ba ne, sai an koya ma Iyami hankali, dan haka ki shirya tafiya gobe goben nan nake son mu tafi ba sai wata rana ba, kar mu sake ayi mana sakiya, domin ita ma zata iya shiga nata malaman ta janyo hankalinsa”
“Maganarki haka take Kaltume, karki damu zan kira shi tun yau na fada masa gobe zamu zo, amman fa ki zo da wuri saboda kin san dajin nan babu ďan mutum ga halin da ake ciki kara mu yi tafiyar safe kar mu yi mugun gamo”
“In Sha Allah karfe 8am a gidanki zata yi min, sai na zo”
Daga haka suka yi sallama, Hajiya Kaltume tana kwafa tana jinjina lamarin.
IYAMI POV.
“Ban san me ya hana shi daukar wayata ba, kunyar abun da ya aikata yake ji ko kuma rainin wayo ne da raina talaka”
Gwaggo ta kalli Bappa dake maganar ta girgiza kai.
“Alhaji Haruna ba shi da dabi’ar raina talaka, domin be taba mana haka ba wata kila dai yana jin kunyar abun da ya aikata ne, wata kila kuma baya son ka yi masa magana komawarta ne”
Iyami ta kalli Bappa cikin karfin hali ta ce.
“Bappa da dai zaka kyale shi da ka kyauta min, domin na yi ta tambayarsa ko na masa wani laifin ne, amman ya ce ban masa komai ba, kawai dai bana jin natsuwar zaman aure da ni ne a yanzu”
“Tun da can be san da wannan ba sai yanzu? Kuma be tashi sakinki sai yanzu da ciki wata shida?”
“Ba saki yayi mata na wulakanci ba, ya kyautata mata daidai gwargwadon yadda ake son kyautatawa a saki da zaman aure, kuma aure rai ne da shi ko babu komai idan lokacin rabuwa yayi dole sai an rabu, mu dan bashi lokaci har ya dawo hayyacinsa ni na tabbatar Alhaji Haruna yana son Iyami akwai dai abun da aka yi”
Wannan karon Gwaggo ce take maganar. Bappa ya mike tsaye yana ja tsaki.
“Akwai yadda aka yi na me? Ku yi komai ba za su bar shi ga Allah ba sai kun ci wani abu, yanzu zaki iya cewa asiri aka yi masa, kar ma ki kawo wannan maganar, ni na fita”
“Toh Allah ya dawo da kai lafiya”
“Ameen”
Ya fice yana sake gwada kiran number Alhaji Haruna Mai Yadi. Fitarsa da kamar minti uku Hindu ta shigo dakin tana sallama, Gwaggo ta amsa mata. A bakin kofar dakin ta saki jakar hannunta tana kallon amiyarta.
“Iyami da gaske Alhaji ya sake ki?”
Iyami na kallonta sai hawaye suka zubo mata, Gwaggo na ganin haka ta mike tsaye ta fice daga dakin domin bawa kawaye damar tattaunawa.