𝗣𝗮𝗴𝗲 5️⃣
“Akwai matukar mamaki ace duk son da Appan Hurriya yake miki ya sake ki, saki fa Iyami?”
Amma ta saka hannu biyu ta share hawayen fuskarta.
“Ni ma dai ganin nake kamar ba sakin ba ne, saboda ban saka ran ba mutuwa ce zata raba ba, har yanzu tunani nake ko dai boye min yayi? Wata kila na masa wani laifi ban sani ba”
“Bayan kin ce ya fada miki baki masa komai ba?”
“Hindu namiji na sakinka haka nan? Ai na ga sai da dalili”
“Dalili daya ne Iyami sa’ar da matansa suke nema sun samu, kin mata a cikin manyan mata kuma tsofin mata kike zaune? Matan da sun kusa sa’ar gwaggo? Wace ce warinki a cikinsu? Iyami babu kalar kazafi da kage da ba su miki ba duk dan saboda ki bar gidan amman burinsu be cika ba sai a yau, maganin ma na san sun gwada Allah dai ne be ba su sa’a ba sai yau”
“Hindu Waallahi ina son mijina, mijina kuma yana so na amman yau komai ya kare”
Amma ta fashe da kuka.
“Har sai kin fada? Ai kowa ya san yadda kuke zaune ya san mijinki yana sonki kuma ke ma kina sonsa, sakin ma da zai miki Iyami na musamman yayi wane namiji ne zai saki mace ya dauki dukiya ya danka mata? Ai sai zababbu cikin mata, kuma ko yanzu karki yanke kauna In Shaa Allah zaki koma dakinki ki cigaba da addu’a nima kuma zan taya ki kuma ki saka ayi miki a islamiyayo nima kuma zan zaka ayi miki”
Kasa cewa komai Amma ta yi sai kuka take kukan da da zaka iya rantsewa mutuwa aka yi mata, idan ta tuna da sakinta Appan Hurriya yayi sai ta ji zuciyarta ta narke ta rasa me ke mata dadi a duniyar nan da ace mutuwa yayi sai ta dangana amman tunawa cewar yana raye kuma shi da kansa ya zabi rabuwa da ita ya fi komai daga mata hankali.
“Toh wai a can kika bar su Hurriya?”
“Ya ce zai rike su”
Ta amsa mata cikin kuka. Hindu bata wani dade a gidan ba ta mata sallama ta fita domin komawa nata gidam ta dora girki. Haka ta wuni a daki idan Gwaggo da jikokinta suka shigo sai ta boye fuskarta ta danne kukanta har sai idan ta kadaita ita kadai, tunanin yaranta ya tsaya mata a rai, tana ta auna lokacin dawowarsu makaranta da kuma irin abubuwan da suke idan sun dawo, da dare yayi sai ta kasa bacci domin wannan ne daren farko da zata kauna a gidansu tun bayan aurenta shekara goma sha shida. Ko biki ake a gidan ko wata hidima Appa baya barin ta kwana ko da kuwa ba girkinta. Daren sai ya zame mata wani dare na dabam da bacci ya gagara kusantar idonta ma balle har ya sace ta, kukan ma sai ta neme shi ta rasa wata zuciyar nata raya mata hanyoyin da zata bi ta shirya da mijinta sai ta saka zaren idan ta karshe sai ga ba hanya ce mai bullewa ba, dare ne da yayi mata tsawo fiye da sauran dararen da suka gabata, karfe biyu da rabi ta doro alwala ta fara raya daren da sallah nafila a haka aka kira sallah asuba akan idonta.
HURRIYA POV.
Da murna ta shigo dakin Appanta ta zauna kusa da shi a kasa kamar yadda ta saba, sai ya kai hannu ya shafa kanta zuwa bayanta yana murmushi irin murmushin nan dake dauke da so da kauna da kuma farincikin abun da idanuwa suka yi arba da su.
“Hurriya toh yaya?”
“Lafiya kalau Appa, ka dawo lafiya?”
“Lafiya Kalau, ina can gurin aiki zuciya na nan tare da ku sai tunaninku nake Ina Hamad”
“Shi ya ce ba zai zo ba?”
Ta amsa tana kai hannu ta gyara gilashin idonta. Hajiya Kaltume dake zaune kan carpet ta yi murmushi, irin murmushin nan da ya zame mata dole ne, domin ta kasa hadeye maganar da Appa yayi cewa yana gurin aiki zuciyarsa na gurin yayansa ta ce.
“Hamad ai ba zai zo ba, dazun ma dukanta yayi ya fasa mata gilashi sai da Yasir ya shiga tsakaninsu”
Appa ya kalli Hurriya cikin yanayin damuwa.
“Me ya hada ku?”
Ta zayyana masa abun da ya faru daga karshe ta rufe da fadar Yasir ya shirya su. Appa ya sauke ajiyar zuciya
“Ina ganin yaran nan za su koma gurin bangarenki sa zama Kaltume, saboda a rika saka musu ido, kar wata Hamad ya ji ma yarinyar ciwo, daman ko dan kula da abincin da wasu abubuwan dole su koma can”
“Gurina kuma Alhaji? Ni da nake da yan mata cike da daki? Kuma ka san yadda bama jituwa da uwar yarinyar nan yanzu nan Hurriya ko kaya ta taka na cire mata cewa za ayi na cutar da ita, ba zan hana ta zama ba idan haka kake so, amman dai da zaka barta a hannun Nafisa wata kila zamu samun zaman lafiya, daman Nafisa bata da yara da yawa uku ne kawai kuma mazan fita suke Namra ce kawai ka ga ta samu yar’uwa a kusa ko? Amman ni Hajiya ma sai tace na mata ba daidai ba domin ta kira ni tana ja min kunne akan yaran nan”
Ko kadan maganar da Hajiya Kaltume ta yi bata yi ma Appa dadi ba, sai yake jin kamar bata son zaman yaransa a gurinta ne, hakan kuma sai ya kara jefashi a cikin damuwar sakin mahaifiyarsu da yayi gashi nan ya koma nema musu gurin zama domin ba zai iya barinsu a katon part din uwarsu su biyu kawai ba babu mai kula da su.
“Hurriya yata ina kike son zama?”
Ya tambaya yana kallon fuskarta, Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume sannan ta kalli mahaifinta ta ce.
“Gurin Hajiyarka ko Gwaggo”
“Ba zan iya bari ku zauna hannun kowa ba matukar ina raye, na fi sonku a kusa da ni na rika yaran wasu ma ta ina zan bada nawa riko? Idam har ba zan iya bari ku zauna gurin Iyami ba to ba zan iya hakurin ku zauna a gurin kowa ba, je ki kira Hamad”
Hurriya ta tashi ta fice, Hajiya Kaltume ta bita da kallo Appa kuma ya sauke ajiyar zuciya.
“Yaran nan sun zamar min kamar wasu marayu, Wallahi yau saboda tunanin abubuwan da suka faru na kasa sukuni”
“Akwai damuwa kam sosai, na da zaka hakura ka dawo da mahaifiyarsu da duk yafi wannan nema musu gurin zama da kake, idan ma wani laifin ta yi maka ka yafe mata dan Allah ko mu da muka kwana biyu aka saki a yanzu ai sai mun ji dabam balle kuma ita da take da sauran kurciyarta”
Appa be ce komai ba bayan sauke kai da yayi kasa, domin baya jin dawowa da ita mafita ne kamar yadda sakin ma ya kasa zame masa mafita domin ko yanzu jin yake kamar akan ƙaya yake saboda tunaninta domin yana matukar son matarsa ga kuma tunanin makomar yaranta. Hajiya Kaltume ta tsare mijinta da ido ganin ya noce kai kasa sai zuciyarta ta raya mata zai iya dawowa da ita kenan ganin yadda ya zurfafa a tunani ga kuma son yaranta da yake. Sai a lokacin da Hurriya ta dawo dakin tare da Hamad sannan Hajiya Kaltume ta kawar da kai tana kwafa a zuciyarta, Appa kuma ya dago ya kalli Yayansa. Hurriya ta zauna a inda ta zauna dazun Hamad kuma ya tsaya jikin kofa fuskarsa ba yabo ba fallasa.
“Hamad ka ci abinci?”
“Aa”
Ya amsawa Appa da kai. A take Alhaji Haruna ya kalli Hajiya Kaltume.
“Ba a basu abinci ba Kaltume?”
“Tuwo na girka, ka san Hamad ba ya cin ciwo kuma basa cin abinci da ake girkawa masu aiki”
“Idan shi baya ci ita Hurriya bata ci? Haba Kaltume kin san uwar yaran nan bata cikin gidan nan a matsayinki na babba ki kasa kiran yaran nan ki ba su abinci?”
“Ban yi tunanin ba su ci ba, ranka ya dade ayi hakuri ba za a koma ba In Shaa Allahu”
“Hurriya zaki ci tuwo?”
Hurriya ta daga kai a hankali daman tuwo is one of her favorite saboda abincin Appanta ne ita kuma duk abun da Appanta yake so tana sonshi, kuma yawan girka shi da Amma take ya saka ta saba da cinsa, domin Alhaji Haruna ba shi da wani abinci da ya fi tuwo duk arzikinsa ya fi son agirka masa tuwo a gidansa domin abun da ya saba da shi tun kamin zuwan arzikin.
“Zan ci tuwo Appa”
Ya kalli Hamad da ko a yau ko sannu da zuwa be masa ba kuma be gaishe ba, abun da be saba ba domin duk tsaurin kansa yana gaishe da Appa yana masa sannu da zuwa kamar yadda Amma ta koya masa.
“Kai kuma me kake son ci? Je ka kira Dahiru ko Bello ya kaika Restaurant ka siyo abun da kake so”
“Bana son komai”
Ya amsa kai tsaye ba tare da ya kalli kowa ba. Appa ya kalleshi da kyau.
“Hamad zo nan”
Ya shiga cikin dakin sai ya zauna nesa da Appa kamar wani bakonsa ko wanda be saba da shi ba, bayan kuma a da can ba haka yake masa ba idan yayi nesa da shi to yayi laifi ne, amman idan babu laifi baya zama nesa da mahaifinsa kuma sukan zauna su yi hira da juna ayi wasa da dariya sai dai ba kamar yadda suke yi da Hurriya ba.
“Me aka yi? Waya taba ka?”
“Babu ba ayi min komai ba”
Hajiya Kaltume ta tabe baki tana murmushi.
“Kai ma dai Alhaji, a gidan nan ba zai taba Hamad ya kwana lafiya? Idan ma an fi karfinshi ai kasan yadda yake yi ma mutane ruwan duwatsu ko kuma ya shammaci mutum yayi masa wata ƙetar”
Hamad ya dago ya kalli Hajiya Kaltume da irin kallon da ya fi kama da harara, daman can shi ne mai taya Amma kishi wani lokacin, Hurriya kam team babu ruwanmu ce.
“Toh na ga yana ta bata rai ne kuma yace ba zai ci abinci ba?”
“Uhm. Hmm”
Kawai Hajiya Kaltume ta ce ta cigaba da kallon Appa dake tambayar Hamad ina yake son zama.
“Ina Hurriya zata zauna?”
“Gurin Momy”
Appa ya amsa masa.
“Nima zan zauna a can”
“Toh yayi kyau, amman dai ka saki ranka Hamad ka ji? Kuma ka ci wani abun yaushe rabonka da abinci?”
“Na sha zobo da rana”
“Zobo ai ba abinci ba ne, zaka sha tea da bread a hada maka?”
“Bana son komai Appa bana jin yunwa”
“Shikenan zan yi ma Nafisa magana sai ku maida kayanku part dinta”
Appa ya fada cikin yanayi na rashin jindadin dansa be saka komai a ciki ba. Hamad ya mike tsaye ya juya. Appa ya bishi da kallo yana fadin.
“Hamad babu ko sai da safe?”
“Sai da safe Appa”
Ya fada ba tare da juyo ba har ya fice. Hurriya ta mike tsaye domin yunwa ta matsa mata lamba.
“Appa ina tuwon?”
Appa take tambaya sai Hajiya Kaltume ta amsa mata.
“Je bangarena ki zuba ki ci, mahaifinki ya rima ci balle ku ci tare”
“Toh”
Ta nufi kofar fita da saurinta. Sai da ta fice Appa ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.
“Dan Allah a rika kula da yaran nan, su da marayu duk daya yanzu”
“Alhaji, dan Allah na ci wannan alfarma dan Allah ko dan yaran nan, mahaifiyarsu ma tunaninsu sai ya isheta kuma kai yanzu baka lura Hamad fushi yake da kai ba?”
“Fushi me?”
“Ka kore mahaifiyarsu mana”
“Ba kin cw bata fada musu ba?”
“Eh amman ka san shi ya yafi yar’uwarsa wayo, ba mamaki ya gane, ita kanta Hurriya idan ta fahimta ba zata jidadi ba”
Appa ya sauke ajiyar zuciya.
“Ba zan iya ba ne Kaltume, gobe za a zo da motoci akwaishe mata kayanta”
“Subhanallahi Alhaji har saki nawa ka yi mata ne?”
“Daya”
“Amman za akwashe kaya da wuri haka? Wai me yayi zafi ne shi ba wuta ba? Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
Ta fashe da kuka ta mike tsaye ta fice daga dakin tana rusar kuka kamar gaske. Appa ya busar da iskar bakinsa shi kansa ya san it’s too early ace an kwashe kayan Amma a gidan daga sakinta, sai dai kiran da Bappa yake masa yake son amfani da damar ya nuna musu babu sauran zama tsakaninsada Amma, domin ya kasa amsa wayarsu tun jiya saboda be san abun da zai fada musu ba. Kai ya gigirza sannan ya tashi tsaye ya fice daga part dinsa zuwa part din Hajiya Nafisa wato Momy.
HURRIYA POV.
Hurriya na shiga bangaren Hajiya Kaltume ta samu Umm Khairi zaune a dinning tana cin nata abincin daren, da a bangaren mahaifiyarta ne sai da ta bude ta zuba amman a nan dole ta tsaya a zuba mata ko kuma a bata izinin zubawa.
“Yaya Khairi Hajiya ta ce na zuba abinci”
“Gashi nan ai dauki plate ki zuba mai isarki”
Hurriya ta dauki plate ta bude manya warmers din ta ta dauki mulmular tuwon da aka nade a leda ta raba uku ta zuba daya a plate ta rufe ta bude dayan ta zuba miyar kubewa ďanye ta saka nama da man shanu sannan ta rufe ta ja kujera har ta zauna ta tuna bata wanke hannu ba ta tashi ta shiga bandakin dake falon ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin tuwon, sai da ta yi nisa da cin abincin sannan Khairi ta kalleta.
“Hurriya”
Hurriya ta dago a hankali ta kalli yayarta Khairi wadda ta kira sunanta.
“Na’am?”
“Me Appa yace miki da ya aiko a kira ki?”
“Tambayarmu yayi ina muke son zama”
“Toh ina kika zaba?”
“Ni dai na ce gurin Gwaggo ko Hajiya, amman yace aa sai dai gurin Momy”
Khairi ta yi fuskar tausayi.
“Allah sarki, Wallahi na tausaya muku babu dadi rayuwa gidan babu uwa a gida, da ma dai Appa zai yi hakuri da ya dawo da Amma, Hurriya na ga Appa yana jin maganarki why not ki roke shi ya dawo da Amma idan ma wani laifin ta yi masa ya yafe mata”
Hurriya ta yi mata wani kallo na rashim fahimtar inda zancenta ya dosa.
“Amman zata dawo idan ta haihu ai”
“Toh Allah yasa ya maida ita, wata kila akwai gyara ai Wallahi duk ban jidadi ba dazun har da kukana”
Hurriya na jin haka sai kwakwalwarta ta dauka sarai ta gane karatun Khairi a take wani irin tashin hankali ya same ta, idonta dake cikin farin gilashi suka cika da hawaye ta kasa hade lomar tuwon dake bakinta. Slowly ta mike tsaye taja kujera baya ta fara tafiya zuciyarta na buga kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana fita falon ta watsa da gudu bangarensu da karfi ta tura kofar falon Amma ta shiga. Hamad na kwance kan kujera yana kallon remote a hannunsa.
“Hamad wai Appa sakin Amma yayi? Wai rabuwa suka yi? Yaya Khairi ta fada min”
Tana maganar yana kuka even though bata gama tabbatarwa ba. Hamad ya tashi zaune yana kallonta.
“Ai ke ce mahaukaciya shiyasa baki gane ba”
A nan Huriyya ta samu damar fashewa da kuka mai karfi, ta juya da sauri ta nufi bangaren mahaifinta.
*** *** ***
“Ah Ah Alhaji ina ce Kaltume ce Babba a gidan nan? Me zai hana su zauna a bangarenta?”
Appa ya mike tsaye.
“A nan nake son su zauna, kuma nan za su zauna ko kin yarda ko baki yarda ba, domin ke da su duk a karkashin ikona kuka kuma a gidana”
“Aa Alhaji gaskiya ban ci ƙashi ba ba zan ci aman tsoka ba! Har ina? Yara da girmansu da komai a kawo min su? Da wani abun arziki ne ai matarka take tarewa ta karbe sai a yanzu da yake wahala ce za a kawo min”
Appa ya nuna kansa.
“ƴaƴane wahala Nafisa? Ke dai har abada ba zaki taba zama matar kirki, har abada mai hali be taba fasa halinsa ba, kowa yana girma yana kara hankali da hali na gari amman ban da ke”
“Daman ni ban taba haske a idonka ba, masu haske Iyami ce da Kaltume, ka san ni ka san halina ni bana son a shiga sabgata ina bangarena babu ruwana da kowa, akan me yanzu za a dauko yayar sarauniyar gida mace da ta hana ka ganin martaba a kawo min”
Alhaji Haruna ya nuna ta da yatsansa.
“Sau daya tak bakinki ya sake furta wata magana marar dadi akan Iyami da yayanta sai mugun saba miki, ni na zabi su zauna a nan kuma a nan din za su zauna, idan baki son zama da ƴaƴana jinina ƙofar gidan a bude take..!”
Momy ta aje numfashi da karfi.
“Bismillah ga dakuna nan su zabi wanda suke so su zauna, gidan naka ne yaya naka ne ni ma taka ce Allah ya ba mu hakurin zama”
Fuuuu! Appa ya fice daga falon nata cikin mugun bacin rai. Namra da Musib suka bishi da kallo su kansu sun manta when last su ga mahaifinsu a cikin bacin rai irin wannan sai yau.
“Tsakani da Allah takurawa ce dawowarsu a nan, musamman ma dan iska yaron nan Hamad ni ubansa zan ci Wallahi”
Cewar Musib yana jin haushin hukuncin da mahaifinsu ya yanke. Bakinciki ya hana Momy sake cewa komai ta kai hannu ta dauki sarkar zinarinta dake kan aje a hannun kujera ta mike tsaye ta nufi upstairs, kamin ta isa dakinta ma wani aiki ne saboda izza da isa kamar wadda bata son taka kasa haka take tafiya.
Bakin gadonta ta zauna ta rike da sarkar sai cika take tana batsewa, ita dai ta san tana daga kafa akan kishi da matan Alhaji Haruna domin ganin take babu sa’arta a cikinsu Hajiya Kaltume dai yar talakawa ce arzikin na Alhaji Haruna Mai Yadi ne, Iyami ma haka rufin asirinsu na Alhaji Haruna ne domin har gidan da iyayenta suke ciki a yanzu shi ya siya musu shi yake dauke da nauyinsu.
Kuma Iyami ba sa’arta bace a shekaru, kuma ta fi Hajiya Kaltume zama makaskanciya a idonta domin ita ga aiki ta zo yi a gidan ta aure Alhaji Haruna, ba dan ma da kaddarar aure ta hana ba kuma yara sun shiga tsakani ba wata kila da ba zata iya hakurin sharing miji daya da yar aikin gida ba, kallon da take yi ma Amma bata da ajin da zata yi kishi da ita sai idan abun ya motsa.
Ita dai abun da ta fi tsana shi ne a shiga sabgarta, idan ta shiga sha’aninta na masu arziki har mantawa take da Hajiya Kaltume da Amma, a yanzu kuma kawo mata Hurriya da Hamad da Appa ya dage sai shi ne abun bacin ranta a yanzu, domin da su zauna a gurinta kara ya dawo da uwarsu ta rainin abunta, sam sam Momy bata son yayan kowa idan ba nata ba, bata mutanta kowa sai masu kumbar susa, idan baka da arziki har ganin take kamar baka cika mutum ba.