Kanwar Maza Hausa Novels

Kanwar Maza Chapter 4

p 4

Ko da sati ya zagayo, Mama tana sa ran ta ga Ruma ta shirya ta tafi makarantar allo, amma ta ga bata da niyyar yin hakan.

Sai ma aiki take a tsakar gida, wanda ba ta saba ba, tana naɗe yayyenta je komai.

Aliyu ne ya fito daga banɗaki, hannunsa riƙe da buta ya kalli Ruma ya ce “Ke ina makarantar allon?”

Ta ɗan ɓata fuska ta ce “Ni na cire kaina na daina zuwa”.

“Saboda ke ki ka saka kanki, shine sama ta ka ki ka cire kan ki ko? Da alama baki da gaskiya”

Mama ta fito tsakar gida ta ce “Ali ajiye butar nan ka je mini makarantar allon ka ji me ta aikata, dan ban yadda da ita ba”  dan jikinta ya bata Ruma wani laifin tayi.

“Wallahi Mama ba abin da na yi, ba sai ya je makarantar ba, idan ya je ma sharri za su yi mini, ba sa sona malaman”

Mama ta ce “Au malaman ne suke miki ƙarya Rumaisa, ai ko me za ace mini kin aikata ba zan musa ba”

Huzaifa daga cikin ɗaki ya ce “Dama saboda ƙawayenta ya sa ta ce ita ma a sakata a makarantar, ba dan Allah take zuwa makarantar ba “.

Aliyu ya saka jallabiyarsa ya tafi makarantar allon.

Bayan fitarsa rantse-rantse take ta yiwa Mama, akan ita fa ba abin da ta aikata a makarantar nan, amma Mama ta shareta.

“Ruma!”

“Na’am Yaya Sadik “

“Zo ki sayo mana ƙwai ki soya mana mu karya”

Kasancewar Ruma akwai kwaɗayi, ya sanya ta daina fargabar zuwan Aliyu makarantar su, ta karɓi kuɗi ta tafi aiken da Abubakar ya yi mata.

**********

A kashingiɗe take a kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta tattara dukkan wata nutsuwarta a kan ƙatuwar wayar hannunta, da alama ko me take kallo mai muhimmanci ne.

“Samha me ki ke wa wannan kallon ƙurillar ne?”

Wadda aka kira da Samhan ba ta motsa ba, balle ta daina abin da take yi.

Hannu ɗayar ta saka, ta zare wayar daga hannun Samhan, tana dubawa.

Har a wannan karon, Samha ba ta yi motsi ba, balle ta karɓi wayarta ta ba.

“Samha kina da hankali kuwa? Wai dan Allah da gaske ki ke dama?”

Samha ta ja ajiyar zuciya ta ce “Nusaiba, ke da kin ɗauka da wasa nake yi dama?”

Nusaiba ta jinjina kai ta ce “Eh, ni ban san abin da ki ke faɗa har zuciyarki ba”

Samha ta gyara zamanta ta kalli Nusaiba, cike da son tabattar mata abin da take faɗa ta ce “Nusaiba, ban fara dan na daina ba, ko zan tafi tsirara zan mallaki abin da zuciyata take muradi”

Nusaiba ta ɗan jinjina kai ta ce “Amma ya batun alaƙa fa, ko kin manta?”.

“Alaƙa bata gabana, na san a yadda zan yi wasana. Kar ki manta anjima akwai walima a gidan Shamaki”

“Hmmm Allah ya kaimu, Allah ya sa ba wani banzan abun zaki yi ba”.

Wani ɗan guntun murmushi Samha tayi, ta ce “Koma dai menene, we should see”

********

Ko da Runaisa ta dawo gida daga aiken Yaya Sadik, tana daga tsakar 6 tarar da Yaya Aliyu a falo yana wassafawa Mama abin da aka gaya masa a makarantar allonsu, ga Yaya Umar a zaune.

“Wallahi mama ba ki ji yadda ake complain a kan yarinyar nan ba, malaminsu ya ce dama ko ta dawo korarta za su yi, ba karatun take yi ba, sai tsokana da fitsara, da damben da yaran mutane, wai sam ba ta da nutsuwa da ɗa’a, malam Babba ya tara su zai hukunta su sun yi laifi ta ɗau allonta ta gudu, yana kiranta amma tayi masa banza”.

Cike da fushi Umar ya ce “Ba kune kuke goya mata baya take wani rashin mutuncin ba, tun da ta san ko me ta ɗauko zaku tare mata ba, ku bari ta tsokano waɗanda zasu nakasata yadda gobe ba zata ƙara ba. Babu wanda yake faɗar alkhairi a kan ta sai sharri” ya ƙarasa maganar yana fitowa tsakar gida cike da fushi.suna yin ido huɗu da Rumaisa ta saki ƙwan hannunta a ƙasa ta na ja da baya, saboda tsoro da fargaba.

Taku biyu ya yi ya danƙota, ya sanya hannunsa ya riƙe kunnenta ɗaya da ƙarfi.

Wani irin ihu ta kurma tana riƙe hannunsa, saboda ji tayi kamar zata ɗaga kai ta ga kunnen a hannunsa, saboda azabar zafi.

“Dan ubanki idan har ba zaki canza hali ba, makarantar kwana zan kai ki, tunda ba ki in da yake miki ciwo ba, ko mu mayar da ke can ƙauye, su miki aure”

Usman ya ce ‘Ai Rumaisa sai ka ce wadda ta sha nonon aljana, hatsabibancin ta yayi yawa, ba ta jin magana sam”

Abubakar ne ya fito daga ɗakinsu a fusace, ya ƙaraso ya riƙe hannun Rumaisa, ya kalli Yaya Umar ya ce “Sakar mata kunne” Umar ya ɗan yi turus yana kallon Sadik.

“Baka ji bane?”

Sadik ya maimaita masa. Yaya Faruk ya saki kunnen Rumaisa, da idanunta tuni suka yi ja saboda kuka.

Ya janyota ya zaunar da ita a kan tabarma, ya dinga share mata hawayen fuskarta.

Cikin ɓacin rai ya ce “Yakamata ku dinga yiwa kan ku adalci a kan yarinyar nan, ita kaɗai ta tashi a cikinmu mace, tayaya zaku ce sai kun tanƙwarata yadda ku ke so? Tayi laifi kowa yayo kanta, ba mai yi mata nasiha, daga mai ce mata munafuka sai me ce mata aljana haka ake rayuwa?”

Yasir ya ce “Wallahi Yaya Sadik, duk ranar da yarinyar nan ta kwaikwaya maka rashin mutuncin da take aikatawa zaka gane ba tsanarta aka yi ba”

“Koma dai yane, a dinga barin yarinya ta huta a daina takura mata haka “

Guntun tsaki Umar ya ja, ya fice daga gidan gaba daya, suna zaman zamansu Mama ta haifo wannan ‘yar kalen hanjin da ta gallabi rayuwarsu.

Yau cikin dare, Mama ta tashi tana ibada, kamar yadda ta saba domin a cewarta wanda duk ya tara zuriya yake neman kuma dacewa, bai ga ta bacci ba.

Fitilar ɗakinta ta kunna, haske ya gauraye ko ina, Rumaisa tayi rashe-rashe a kan katifa, zaninta daban ita daban daga ita sai wando, kanta ko ɗan kwali babu.

Mama ta girgiza kai, ta janyo zanin ta ɗaura mata, ta saka mata hula ta lulluɓeta, sannan ta fice ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Sai dai sam Ruma ba ta san an yi bama, tana ta fama da bacci.

Can Mama ta kuma juyawa, amma ta ga Rumisa ta kuma yada zanin, ƙafafuwanta duk suna ƙasan katifar, ta kuma tumɓur tana bacci.

Haushi ne ya kama Mama, ta ƙarasa in da take, ta ɗala mata duka a cinya. Amma maimakon ta tashi, sai ta sake dunƙulewa tana bacci.

“Ke Ruma, ba zaki tashi ba sai na saka miki bulala?” Da ƙyar ta tashi tana murza ido tana kalle-kalle.

‘tashi ki ɗauki rigarki ki saka, ki ɗaure kanki ki je ki yo alwala ki salla”.

“Wai har asubar ta yi ne?”

Mama ta ce “Wato ke idan ba sallar farilla ba, baki san ki yi nafila ba, sai dai ki saki leɓe kina bacci. Ki je kiyi alwala ki zo ki yi salla ki roƙi Allah ya yaye miki wannan wautar da rashin hankali da kike fama da shi” kafin Mama ta gama maganar, Rumaisa ta sake ɓingirewa ta kwanta.

Aikuwa mama ta ƙule, ta janyo mafici ta shiga rafka mata a cinyoyinta, a razane ta miƙe tana sosh-soshe.

Mama ta bata riga da ɗan kwali ta ɗaura, ta korata tayo alwala.

Mama ta koma kan tata sallayar ta cigaba da salla.

Kusan mintuna arba’in, Mama ta manta ta tura Rumaisa tayi alwala, ta kalli shimfiɗarta taga bata wurin.

Da sauri ta tashi ta fita tsakar gida tana dubawa, sai dai babu Rumaisa babu dalilinta.

Lelleƙawa Mama ta hau yi, tana nemanta a cikin gidan amma bata nan.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ina yarinyar nan ta shiga ne haka?” Tayi maganar lokacin da ta ƙarasa soro tana haska fitila, amma taga ƙofar gidan a rufe.

Ƙofar ɗakin samarin gidan ta tsaya tana bubbugawa da ɗan ƙarfi.

Usman ne ya taso cikin yanayi ya bacci, ya kalli Mama ya ce ‘Mama lafiya kuwa?”.

Cikin tashin hankali ta ce “Ruma na tasa tayi sallar dare, daga ta fito tayi alwala, na nemeta na rasa”.

Ƙwalalo ido waje yayi, ya ce “Ruman? To ina ta tafi?”

Mama ta girgiza kai ta ce “Ban sani ba, na duba ƙofar gida tana rufe da sakata ba a buɗe ba”

Mamaki duk ya cika Usman ya ce “To in ta shiga a tsohon daren nan, bari na sako rigata a buɗe gidan a dudduba”.

Ya shiga cikin ɗakin, ya kunna wutar lantarkin ɗakinsu, sai ga Ruma a tsakiyar su Yasir tana bacci.

Kunna fitilar ne ya sanya Huzaifa ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji mutum a kusa da shi, yayi zaton Yasir ne, dan haka ya dage ya hankaɗa Rumaisa, ta kifa kan Yasir amma ba ta farka ba.

Usman Ya ce “mama leƙo kiga”

Jiki na rawa mama ta shiga ɗakin, daidai lokacin da Yasir ya ji nauyi a kansa shi ma ya dage ya hankaɗata gefe guda.

Mama ta shiga tafa hannuwa tana salati, a irin magagin bacci, da shirme na Rumaisa tsaf za a saceta tana wannan baccin na asara.

A ƙufule Huzaifa ya tashi yana zage-zage ya zata Yasir ne yake damne shi, amma ya ga Ruma a tsakiyar su, ga su Mama a tsaye.

“Ke uban me ki ke yi a ɗakinmu, mama meyafaru?”

Jin hayaniya ya sanya Sadik ma farkawa, ya dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya ‘mama lafiya kuwa’.

‘lafiya lau, kai Huzaifa taso mini ita’

Abubakar ya kalli in da Rumaisa ke ta more laushin katifa tana barci.

“Wai me ya kawo yarinyar nan ɗakin nan?”

Usman yayu masa bayani kamar yadda Mama tayi masa.

Sadik ya ce “Kai Huzaifa, kai da Yasir ku sauko ku bar mata katifar dan Allah, wannan ba tashi zata yi ba”

Yasir ya ce “Kaii, Yaya haryanzu fa yarinyar nan tana fitsarin kwance, kawai a tasheta ta fita, kar ta tsula mana fitsari dan katifar nan wuyar bushewa za ta yi”.

Yaya Umar kuwa tun shigowar Rumaisa yana kallonta, lokacin bai daɗe da kwanciya ba, ya ganta ta shigo tana tangal tangal, ta nemi wuri ta kwanta, tun da ta shigo yana kallonta.

Mama ta ce “Ba zata kwana a nan ba, taso mini ita ta wuce mu tafi”.

Yasir ya daddaki Rumaisa a kafaɗa, amma ta hau surutai da irin faɗace-faɗacen da suke yi da yara a makaranta.

Ƙarshe haushi ya ƙule, Umar ya tashi danƙo Ruma ya hankaɗowa Mama ita tsakar gida, ya rufe musu ƙofa.

Mama har mamakin wannan magagi da kuma suratan baccin da Rumaisa take yi, ita duk wani da mutane suke yi, nata ya zarta ƙa’ida.

Har mama ta kama hannunta zuwa ɗaki, magagin bacci take yi.

******

Sassanyar iskar da bishiyoyin ke bayarwa ne ya haɗu da ƙamshin furanni, tare da samar wani kyakkyawan yanayi mai sanyawa zukata nutsuwa da annashuwa.

Duk da wannan tarin ni’ima, gaba ɗaya Samha ba ta jin dadin yanayin sam.

Wayar hannunta ce ta fara ringing, wadda ta katse mata dogon tunanin da take yi, ɗagawa tayi ta kara wayar a kunneta ba tare da ta ce komai ba.

“Ki fito mu tafi, ina haraba”.

“Ok, ya maganar mu? Kun yi magana da ita, zasu zo ne”.

Nusaiba ta ce “Hmm, Samha kenan ke meya hana ki tambayeta?”

“Nusaiba bana son wasa, am serious about it”.

Nusaiba ta ɗan taɓe baki ta ce “Eh, za su zo” Ta sauke wayar daga kunnenta, ta nufi hanyar fita daga lambun.

***

Mama tana yawan yin istigfari da nemawa Rumaisa shiriya, musamman yadda bakin mutane yayi yawa a kanta, duk wani rashin ji irin na ɗa namiji shi take yi, bama irin na mata sa’aninta ba, duk sa’aninta ta kere su a rashin ji. Babu yadda Mama ba tayi ba a kan aje a bawa malaman makarantar allon su haƙuri, ta koma amma mirsisi Yaya Umar ya ce sai dai a sauya mata makaranta, in da zata fi mayar da hankali, amma a ƙasan zuciyarsa zafin maganganun da malaman suka yi a kan Rumaisa ne ya fi ɓata masa rai har ya sanya ya ce ba zata koma ba.

Ita kuwa Rumaisa ganin Yaya Umar ya hana a mayar da ita makarantar allon Malam Babba, tayi ta murna a ganinta ta huta da zuwa makarantar nan mai cike da takurar tsiya, Allah ya sa makarantar bokon ma a cireta, ta dawo gida Mama ta bata jari ta dinga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida. Murmushi ta yi bayan wannan tunanin ya zo ranta.

Ta dubi Abdallah da yake ninke kayan da ya wanke ta ce “Yaya Abdallah, dan zaka gayawa abokananka zan fara sayar da wainar fulawa, naga kai ne me abokai masu kuɗi, ka talatta musu su zo su dinga saya, ba irin abokan su Huzaifa ba gayyar ƙolawa da tsamaye ba”

Saroro ya kalleta ya ce “wace irin wainar fulawa kuma?”

“Eh tun da na daina zuwa makarantar allon, sai Mama ta bani jari na diga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida”.

Huzaifa ya ce “Eh dama kin yi kalar sayar da wainar fulawar ai, ai ni da kai na zan din ga yi miki ciniki, ai suyar wainar ce ta dace da le delu”

Murguɗa baki tayi ta ce “Da dai ban san halinka bane, ci ka tsere ka rusa mini jari, kama kar ka sake ce mini wata deluna gaya maka.

Ta mayar da hankalinta kan Abdallah ta ce “Dan Allah Yaya Abdallah ka yi magana mana”.

“To ai Ruma na rasa me zance miki ne, wace irin wainar fulawa ana zaman lafiya”.

“To Yaya ba gara ace ina sana’a ba, kuma ku huta ba, ana ta shelar mata su kama sana’a, Mama ai zaki bani jari ki saka mini albarka ko?”

Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini wannan rana, kuma kar ki sake sakoni a cikin shirmenki, idan kuma ki ka sake sai na ci ubanki ke da soya wainar fulawa a ƙofar gidan, tun da ke dai Allah bai sa an raba hankali kin samu ba” ɓata fuska tayi a ranta ta ce ‘sai na tambayi Yaya Abubakar, na san shi ba zai hana ni ba ai, tun tuni ake cewa mata su kama sana’a ni kuma zan yi ana hanani’.

Umar yana ɗaki yana jin shirmen da Ruma take, ji yake kamar ya ɗauketa ya kai ta boarding kowa ya huta, amma ya san Mama ba zata taɓa amincewa ba.

Wayewar garin Allah, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe, mama na shirin fita, telar da take yiwa Mama ɗinki ta aiko da ɗinkin da Mama ta kai mata, bayan mama ta karɓi ɗinkin ta sallami yaron, ta kalli Ruma ta miƙa mata ledar ta ce “gashi nan kayanki ne”.

Da murna ta karɓi ledar ta buɗe, cike da son ganin menene a ciki.

Tana buɗewa tayi karo da wata atamfa koriya da yellow, ta kalli Mama ta kalli atamfar sannan ta ce “Wallahi Mama wannan Salamatu mai kayan ba ta kyauta mini ba, sai da nace ba na son atamfar nan, amma dan taga ba na nan shine ta liƙa miki, ki ka saya amma shikenan na gode, amma dai ba dan an ɗinka ba sai na mayar mata” ba ta gama rufe baki ba, ta buɗe kayan taga riga da zani jaka a tsaye, da wata uwar bunjumemiyar riga kamar zata tashi sama.

“Ta kalli mama ta ce “Mama wai wannan kayan nawa ne ko kuma naki?” Ruma tayi maganar a rikice.

Mama ta ce “Ni ce zan saka wannan kayan? Naki ne mana”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, yanzu mama wannan ne kayan salla na, dan Allah kalli rigar tsaf sai an saka irina sittin a ciki, mama ko gwada ni fa ba ayi ba aka ɗinka kayan”

A fusace Mama ta ce “Naji na gode, ki ajiye mini kayana tunda ba ayi miki gwaninta”.

Yasir ne ya dubi Ruma ya ce “Amma Ruma baki da kirki, yanzu mama ta sai miki kaya ta bayar a ɗinka miki, amma ƙiri-ƙiri ki nuna ba kya so”.

Mama ta ce “Rabu da ita, ta je ta ƙarata”.

“Mama kiyi haƙuri, ba cewa nayi bana so ba, amma dan Allah kalli rigar nan, ni ba tattabara ba ina zani da wannan rigar kalli hannun kamar fuka fukai, ba irin wannan rigar na gani a jikinku a wannan tsohon hoton naku ba?”

Yasir ya karɓi rigar yana dubawa, ƙunshe dariyarsa yayi ya ce “To dan ubanki maje gaba aka yi miki, tun kina yarinyarki da ke, wato kin fi son matsatsun kaya ko, to baki isa ba, wannan rigar da ita zaki yi wankan idi mu je masallaci, maje gaba ce “

Haushi ne ya gama cika Ruma, ta tura baki tana jin kamar ta yi ihu.

“Wace irin maje gaba, ai sai a bari nayi gaban tukuna, sai a ɗin ka mini daidai ni, idan ban je gaban ba fa?”

Mama ta ce “Rabu da ita, ta gama rashin mutuncinta tun da abin nata haka ne, daga wannan ba zan ɗinka mata wasu ba, da su zata yi sallar, dama ba jin maganata take yi ba, nima an zo wurin da zan fanshe, bana ba kayan salla sai kala ɗaya”.

Yasir ya ce “Wallahi mama hakan ma ta gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ai kin yi ƙoƙari, ke Ruma wannan rigar idan ki ka sakata ai ba sai kin ɗaura zanin ba, kaɗan ya rage ta zama doguwar riga, idan kuwa zaki ɗaura zanin sai ki ɗaura shi a kam rigar, ki yi ɗaurin barmana coge wallahi kyau zaki yi”

Gaba daya ta fuskanci Yasir rashin mutunci kawai yake yi mata, kamar zata fashe haka ta tattare kayan ta kai ɗaki ta zubewa Mama a kan kujera, ta barwa ranta cewa gara tayi zamanta a gida da salla, da ta saka wannan zulumbuwar rigar a matsayin kayanta na salla ta fita ayi mata dariya.

Mama ta fita yin barka a maƙwabta, hakan ya bawa Yasir damar zama ya sanya Ruma a gaba ya dinga tuntsira mata dariya, duk wanda ya shigo sai ya ɗauko masa kayan ya nuna masa, daga atamfar har ɗinkin irin na zamanin su Mama ne.

Huzaifa ya fi kowa ƙyaƙyatawa, ya ce “Lallai mama ta iya punishment, ai ni ta biyani da aka miki wannan ɗinki, kamar yadda Yasir ya faɗa, idan ki ka saka kayan nan, ki ka kafa ɗauri irin na barmana mu samo ƙorrai, da sallar nan mu baza kiɗan ƙwarya a cikin unguwa, wallahi kuɗi zamu samu, dan dama mutane duk sun watsar da al’ada”.

Abdallah har da yi mata magiya a kan ta gwada kayan yanzu, ya ga yadda za su yi mata. Tayi musu banza ta koma gefe ta ci magani.

Yaya Usman ne ya zare mata ido, wai sai ta gwada kayan sun ga yadda za suyi mata, kasancewar tana shakkarsa shima, haka ta je ta saka kayan ta fito tana danne kukan da yake ƙoƙarin ƙwace mata.

Tana fitowa tsakar gidan Huazaifa ya bushe da dariya ya ce “Waya ga babba da jaka”.

Abdallah ya ce “Allah ya bar mana Delun mu, wallahi dama delun aka saka miki, kin yi kyau”.

Usman Ya ce “Abdallah, yi mata ɗaurin barmana cogen, mu gani, zan mata video”

Duk yadda ta so haɗiye kukan sai ta kasa, sun kewayeta sai dariya suke kamar sun ga mahaukaciya, ga Usman yana yi mata video da wayarsa suna dariya.

Huzaifa sai kifawa yake, kamar wanda ya zare, yana cewa Usman”Ka yi mata hoton da Black and white mu ce ga kakar su Mama 1940″

Babu tsammani Umar ya shigo, ya tarar da Rumaisa a tsaye kamar an dasa ta, ga uban ɗauri a ka, ta ɗaura zani a kan riga, tana tsaye tana kuka su kuma sun kewayeta suna dariya.

“Meye haka?” Yayi maganar a kausashe.

Usman ya ce “kayan sallarata ne, aka kawo take ta rashin mutunci wai bata son kayan, shine nake punishing ɗinta, nan gaba ta koyi godiya ga Allah a kan duk abin da ya bata, sannan ta godewa wanda ya batan”.

Shi kansa Yaya Umar ji yayi kamar ya yi dariya, saboda yadda Ruman tayi a kayan, kai da gani ka san sun yi mata yawa, sai tayi kamar wadda ta kawo tallan kalwa birni.

Gimtse dariyarsa yayi ya wuce ɗakinsu, suka gama yi mata rashin mutunci sannan suka sallameta.

Da ta koma ɗakin ma, sai da ta sha uban kukanta, ta cire kayan ta ajiye tana jin yadda ranta yayi mugun ɓaci a kan abinda suka yi mata.

Kasancewar yau ba tuwo mama tayi da daddare ba, ya sanya ruma zaman cin abincin dare ba tare da mita ko ƙunƙuni ba, ga kuma uwa uba a ƙule take da rashin mutuncin da su Yaya Abdallah suka yi mata. Tana ta lissafa yadda zata rama abin da suka yi matan ta huce.

Duk da yadda yau tayi shiru, babu wanda ya kula da shirun nata, dama mama na jin haushin tayi mata abu ta kushe, mama ta mayar da hankalinta kan ‘yan mazanta suna ta hira.

“Mama ina da tambaya” duk suka waiwayo suka kalleta.

mama ta ce “To ina jinki, Allah ya sa na sani”

“Wallahi na san ƙarshenta banzayen tambayoyinta ne marasa kan gado, dan Allah mama kar ki saurareta” Huzaifa yayi maganar yana kallon Ruma.

Cikin tsiwa ta ce “Ban kasa da kai ba, dan haka babu ruwanka da ni”.

Mama ta ce “Yi tambayarki ina jin ki”

“Yauwa, dan Allah kar na tambayeki kuma kice mini sai an kwana biyu, menene Janaba, kuma meye fyaɗe!!!”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *