Kwai cikin kaya Book 2

Kwai Cikin Kaya Chapter 1

Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce

Assalamu alaikum, barkanku da wannan lokaci, barkanmu da sake dawowa filin daga, insha ALLAHU zan cigaba da littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA kamar yanda na fara, inafatan haɗin kai daga gareku, haɗin kan kuwa shine tsaftataccen Comments da zai iya zaburar dani akan abinda nake rubutawa, masu ɗaukar littafi su ɗaura a youtobe wlhy wlhy na rantse duk wanda ya ɗauramin ƙwai cikin ƙaya a youtobe kar yay kuka dani akan matakin da zan ɗauka yay kuka da kansa. Masu cewa kuma na maida littafin na kuɗi kudaina yimin ƙarya, inda naso hakan da tun a 1 zance na kuɗine. Masoya kumuje zuwa, yanzu za’a fara wasan .

BOOK TWO

(1)

…………Kowa yana cike da mur”nar dawowar aunty Shahudah a gidan amma banda ni, ba komai ya jawo hakanba kuwa sai irin tarbar dana samu daga gareta bayan dawowata aiki a randa ta dawo.

Cikin ɗokin ganinta da kewa na nufeta, amma saita kalleni cikin wani yanayi na wulaƙanci da ƙyama kamar yanda ta sabamin a baya, daga ƙarshe ta koma dariyar aikina. Hakan ba ƙaramin ciwo yayminba, musamman yanda naga harsu Mom sun biye mata suma suna tayata dariyar. Daurewa nai nima na tayasu, dan na ɗaukama kaina alƙawarin insha ALLAHU sun daina ganin raunina a yanzu. Sai da muka gama dariyar sannan na nufi ɗakina nabarsu, su Aunty Aamilah na bata labarin yanda akai nazama dss a yanzu.

Ina shiga ɗakina na faɗa saman gado na fashe da kuka, tabbas wulaƙanci bashida ƙyau sam a rayuwa, ƙasƙanci ga mutum abune mai muni, amma a wannan duniyar babu abinda mutane suke alfahari dashi kamar ƙasƙanta ɗan uwansu musulmi.

“Sai kaga mai dukiya yana ƙasƙanta talaka koda da magana ne, mai ilimi na ƙasƙanta marashi, mai mulki na ƙasƙanta mabiyansa, miji na ƙasƙanta iyalansa, ɗan uwa na ƙasƙanta na ƙasa dashi. koyaya mutum yafi wani saikaga yana hura hanci wajen ganin yayi tozarci ga wanda bai kaisaba, kaicon mutane da wannan ɗabi’a, kamanta ALLAHN daya baka shima bai manta da shiba, sannan badan ka fisaba ya baka shi ya hanashi, ikonsane wannan yabama wani ilimi yayi wani jahili, ya bama wani dukiya yayi wani talaka, ya bama wani haihuwa yayi wani babu ɗa, ya bama wani mulki yayi wani mabiyi, ya bama wani lafiya yayi wani mara lafiya, kowa a rayuwa akwai jarabawarsa, kaine wane bashike nuna kafi kowa ba, kai ka samu kaza ko kake da kaza bashike nuna ALLAH yafi sonka ba, nima ALLAH yana sona, kuma ina sake gode masa da yanda yayini aunty Shahudah…….”

Tun daga wannan ranar na sake jabaya ga kowa da komai na gidan, Dad dama bai dawoba, hakama Yah Qaseem yayi tafiya tun washe garin dawowar aunty Shahudah gidan. ko a wajen aiki bani da wata walwala, Ummie da wasu abokan aikina sai suka danganta rashin walwalar tawa da kewar Yah Qaseem da bayanan, dan zuwa yanzun mutane da yawa sun san alaƙar dake a tsakanina dashi.

Ni kuma a ɓangarena ba damuwar rashin yah Qaseem bane da lamarin gidanmu kawai kecin raina, akwai wani abu daban danaketa ƙoƙarin tureshi a raina, dan bana fatan gaskata zancen zuciyata koda da wasa kuwa.

★★★★★★★★

Yau data kasance juma’a dai-dai da dawowar aunty Shahudah da kwanaki huɗu Dad shima ya dawo, kowa yay murnar dawowarsa tamkar yanda muka saba, ya kuma samu tarba daga matarsa harma da Aunty Shahudah dake ganin wannan dawowar tatace. Nidai ina daga baya-baya dukda jana a jiki da Dad keyi, dan motsi kaɗan ya sako sunana a cikin zancensa, hakan na kula baƙaramin sosa zuciyar Aunty Shahudah ya keyi ba, hakama Mom. Dana kula abin zaiyi tsamari saina zare jikina na gudu ɗaki, dama dai muna zaune ne muna cin abincin dare.

Ban sake yunƙurin fitowaba kuwa har safiyar washe gari domin nima naji a raina yakamata na basu waje su gana da mahaifansu. duk da kasancewar asabar ce babu aiki ban iya komawa barci ba, dan narigada na saba yanzu da yanayin tashin sassafe. Ina zaune akan abin sallah tun bayan idar da sallar asubahi ban tashiba, na lazimci azkar nai karatun Qur’ani, rashin abunyi ya sakani tashi nahau gyaran ɗakina, hakan sai ya jani tsayin lokaci har kusan tara da wasu mintuna.

Sama-sama nake jiyo hayaniya kamar na kuka, kukan kuma yaymin kama da muryar Mom. Nai azamar ajiye tawul ɗin dana ɗauka zan shiga wanka na fita. Sosai gabana ya faɗi saboda cin karo da Mom dake kuka iyakar ƙarfinta, Dad na riƙeta, daƙyar na iya haɗa maganganunsu, daga ƙarshe na fahimci ƙanin Mom ɗine ALLAH yayma rasuwa mai suna Usman, tabbas naji suna yawan faɗar sunan Uncle Usman, sai dai ban sanshiba, ban taɓa ganinsaba, dan duk zamana a gidan ban taɓa zuwa gidansu mom ɗinba, bankuma cika ganin ƴan uwanta suna zuwaba, kowa dai yasan halin wasu ƴan bokon nan da aƙidar rashin son takura.

Nima dai tausayin Mom ya sakani bin sahun masu sharar hawaye, nan dai Dad ya cigaba da lallaɓata, kafin yajata sama, muma yace duk mu shirya domin tafiya can gidan. Hakanne ya saka kowa nufar ɗakinsa mu duka.

______________________________

A daren jiya juma’a misalin ƙarfe sha biyu da wasu mintuna mummunan labari ya iso gidansu Jawaad, cewar Uncle Usman ya samu haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa daga tafiyar da yayi ta kwanaki biyu.

Lallai wannan gida sun fuskanci tashin hankali na bazata, dan bayan mahaifin Jawaad basu ƙara rasa ko ɗaya a cikinsuba, kaf ƴaƴan malam Yusif Abdul-aziz ne kawai ALLAH yayma rasuwa. Saiko shi malam Yusif ɗin da matarsa ɗaya sai mama maryam, idan ka cire waɗanan huɗun sauran duk sunada ransu, saima yaɗuwa da suka sake yi saboda haihuwar jikoki harma da tattaɓa kunne.

Ruɗanin da mama Atika ta shigane ya sakata yanke jiki ta faɗi, dan abune da tunaninsu bai taɓa kawo musuba anan kusa duk da sunsan mutuwa tabbacice ga duk mai rai, ba Uncle Usman ba ko ita kanta data tsufa sosai bata tuna mutuwar zata iya ɗaukarta a yanzu balle shi da ayanzune ake ƙara shiryama duniyar filin zama.

Lokacin da gidansu Jawaad ke cikin wannan ruɗanin shi yanacan suna gumurzu da wasu gungun ƴan ta’adda da suke fako tun kusan sati uku da suka shige, sai a yaune ALLAH ya basu nasarar yin fito na fito dasu, sun sami nasarar kama wasu a cikinsu, yayinda wasu suka gudu.

Kusan ƙarfe huɗu na dare suka iso station ɗinsu da waɗanda suka cafko, sunyi tiɓis da gajiya, ga yunwa dake cin hanjinsu ta bala’i ma kuwa, sai dai jarumtarsu da juriya mai haɗe da trianing ɗin da suka gogu a ciki duk ya ɓoye gazawarsu. Rose cema dai kawai ta kasa juriyar kasancewar ƙarfin zuciyar mace dana namiji ba ɗayaba, dukda itama ta cancanci a kirata jarumar kuwa, Jawaad ma baiso akai aikin da itaba, amma ta matsa akan sai taje, badan yasoba ya barta ta bisu.

A station ɗin suka ƙarasa kwanan, washe gari safiyar asabar ana idar da sallar asuba Jawaad ya kira gimba akan yazo ya ɗaukesa. Yanda yaji muryan gimban ne ya bashi mamaki, cikin yanayin gizagonsa yake jefa masa tambayar lafiya?.

Sanin halinsa baya son ɓoye-ɓoye a magana ya saka Gimba faɗa masa gaskiyar tashin hankalin da ake ciki a gidan nasu.

Dukda halin da yake ciki da matsalolin dangin mahaifin nasa hakan bai hanashi shiga ƙololuwar tashin hankaliba, a take ya birkicema su Jabeer, waɗanda suma jin rasuwar tai bala’in sakasu a ruɗani. Basu wani ɓata lokaciba suka nufi gidansu Jawaad ɗin kai tsaye, duk da halin gajiya da buƙatar hutun da suke a ciki. Sun iso gidan ƙarfe kusan bakwai da wasu ƴan mintuna, hankalin Jawaad ya sake tashi sosai ganin halin da ahalinsa ke a ciki, tuni ya manta da gajiyar dake tattare dashi.

Bai zaunaba su Uncle Nasir suka jashi zuwa asibitin da gawar Uncle Usman take domin su amso, abinda yasa ba’aje tun jiyaba saboda ba’a nan cikin gari bane, inda ya baro yafi kusa da inda yay haɗarin, shiyyasa aka maidashi asibitin can garin.

★★★★★★★

Ƙarfe goma da wasu mintuna muka iso gidansu Mom, katafaren gida na alfarma da ƙawa, dukda cikin tashin hankalin mutuwa mukazo hakan bai hanani mamaki da jinjina dukiya irinta wannan ahaliba, lallai dolene su aunty Shahudah suyi wulaƙanci yanda sukeso, kaga gida tamkar ba hannune ya ginashiba, harabar gidan kawai naganimafa kenan, sai mutanen gidan da zakaima kallo ɗaya ka fahinci ƴan bokone na haƙiƙa tun zamanin da boko keda tsada da daraja kuwa……

Ina cikin wannan tunanin ne nafara jiyo ƙarfin koke-koke na ƙaruwa, babu shiri na dawo hayyacina, a sannanne na lura ashe an iso da gawar mamacinne.

Har ciki sosai Ambulance ɗin dake ɗauke da gawar ta shigo, ta tsaya dai-dai sashen danaji wasu na ambata da sashen mama Atika mahaifiyarsu Mom. Zuciyata tai masifar harbawa saboda ganin wanda ya fito daga Ambulance ɗin.

Cikin tsagwaron mamaki na furta “Boss kuma anan?” akan laɓɓana, kamar yanda nakejin zuciyata aduk sanda ta samu kusanci dashi yanzunma bata canja zaniba, dole na shiga karanto addu’a gudun kar nayi abinda zai jawo hankalin mutane a kaina.

Nayi nisa a tunanin da har aka fidda gawar ban saniba, saida suna gab da shiga sashin ne nakai idanuna kansu tare da sauraren koke-koken mutane, su biyune kawai ke ɗauke da gawar a mankara, tana lulluɓe da farin ƙyalle da yay face-face da jini, alamar dai mamacin ya bugu sakamakon Accident ɗin da yayi, nantake sai zuciyata tai rauni saboda tunowa da mutuwar nawa mahaifin, sai kawai na durƙushe a wajen na fashe da kuka mai cin rai da zuciya.

Isowar gawarce ta saka gidan ya kuma cika sosai, koke-koken da akeyi ya sake ƙaruwa, ban kuma ganinsaba kuma har aka sake fitowa da gawar kusan sha biyu na safe, da alama dai yanzu an masa sutura za’a miƙashi gidansa na gaskiyane. Wani da nake ƙyautata zaton ɗansane ya rugo da gudu ya riƙe mankarar da aka ɗakko yana kuka da roƙon su ajiye masa Dadynsa, yarone da bazai gaza shekaru sha uku ba a duniya, sai ƴanmata guda biyu da zasu iya kawai 23 da 20 suma sukazo suka riƙe. Hakan ya kuma tada hankalin jama’a, ni kaina sunyi masifar bani tausayi, suma kenan da suke da gatan dangi dana jin daɗin rayuwa, na tuna sanda baba ya tafi ya barni, har aka binnesa ma ni bansan ina nawa hankalin ya keba.

Na share ƙwallar dake gudu bisa kumatuna, dai-dai isowarsa, wajen da alama yanzune ya fito, shine ya janye yaron ya rungumesa a jikinsa yana bubbuga bayansa, hakan ya saka ƴan matanma sakin mankarar suka durƙushe a wajen suna kuka. Bai saki yaronba har saida aka fita da gawar, ya shafa kansa yana ɗago fuskarsa, babu wanda yasan miya faɗama yaron, amma kowa ya kula magana yay masa kafin ya sakesa ya fice shima zuwa waje inda za’a sallacesa.

Tashin hankalin da ake cikine yasa ban samu damar tunanin alaƙar gidan da boss ba sam, bankuma sake ganinsaba, sai dai ganin nasa da nayi yana nan daram a zuciyata, dan kwanaki kusan shida kenan ban gansaba ko’a office, tun fitar da sukai ranar sai yaune na ganshi. A mamakina sai naji raina sakayau, bakamar yanda na tsinci kaina cikin ƙunci ba a kwanakinan.

★★★★★★

Tun bayan zuwanmu gidan ban sake sanya ƴan gidanmu a idonaba, har zuwa yanzu da aketa hada-hadar sallar azhar da cin abinci, garama dad bayan sun dawo daga binne gawar ya shigo cikin gidan shi da wasu manyan mutane sunyi gaisuwa, daga haka ban sake saka ko ɗaya a cikinsu a idanunaba.

Mutane nata shiga sassan gidan domin gabatar da salla, sai dai ni narasa ina zan dosa koda na tashi, waɗanda nazo dominsu ban sake ganinsuba, ina zan shiga nikan nace zanyi salla? Tunda babu wanda ya sanni babu kuma wanda na sani.

Ina nan zaune ina saƙa mai fishsheni a zuciya budurwar dake zaune a kusa dani ta miƙomin jakkarta da waya akan na riƙe mata tana zuwa, kamar zanyi magana sai kuma na amsa ina maida mata murtanin murmushin da takemin, ina zaune a wajen ban motsaba nai uban tagumi harta dawo.

Na miƙa mata kayanta, ta amsa tana min godiya, harta tafi sai kuma ta dawo da baya idonta a kaina.

“Ƴar uwa kozaki taso muje muyi sallane? Naga kowa na harama amma ke koma motsi bakiyba, ko dai kina hutune?”.

Murmushin yaƙe naimata, sai dai ban motsaba, nace, “Karki damu zan nema waɗanda mukazo tare sai nayi a wajensu”.

Tai ɗan shiru tana kallona, kamar bazata tankaba, dan harna fara murnar ta barni, sai na tsinkayi muryarta tana faɗin, “Yanda mutane ke cike a gidannan kafin ki ganosun ai kin wahala, sannan duk inda zakiy salla a gidannan yau bazai kai nutsuwar inda zamujeba, dan sashen yaya ne kawai nasan babu mutane, indai ba kina tsoron karna saidaki bane”.

Ta bani dariya, amma sai banyiba saboda yanayin da ake ciki, sai kawai na miƙe batare danace komaiba, dan na lura akwaita da surutu.

Tun shigowarmu sashen na yarda da zancenta, dankuwa tsit yake babu wata hayaniya anan, tamjar ba cikin gidan yakeba. Sai wani daddaɗan ƙamshi daya shige mini hanci, batare dana shiryaba na shaƙa na haɗiyeshi cikin maƙoshina, karon farko a rayuwata da naga falon da yafi na gidan Dad ƙyau da tsari, ada tunanina yana bani babu gidan da yakai na Dad haɗuwa da tsaruwar kayan alatu, dan dukkan gidajen iyayen su Ummie basu kai na Dad ba, amma a yau dana tsinci kaina cikin wannan aljannar duniyar duk sai na raina wancan alfaharin nawa, yanda aka ƙawata matattakalar benen dake falon kawai abar kalloce ga mai kallo duk wayewarsa kuwa. Ban gama bama idona abinciba budurwar taja hannuna zuwa wani ɗaki, mun iske mutum uku suna salla, sai ɗaya data fito daga bayi da alama alwalar itama tayo, sai wata kwance a kan gadon dake ɗakin da yara biyu suna kallon waya. Duk suka zubomin ido na rashin sani, wadda ta fito daga bayice tace, “Wai ina kikajene haka Nabeelah? an aika Ammar ya kiraki amma yace bai gankiba”.

Hannuna ta saki tana saɓule jakkarta dake a kafaɗa, “Babu inda najefa Aunty Hanifah, ina can jikin sashen Uncle Sulaiman zaune, nima yanzu saida na leƙo naga kuna nan sannan ai na taho”.

Batace mata komaiba, hakanne ya sakani gaisheta dan naga babbace ta girmeni, na juya ga wadda ke a saman gadon tare da yara itama zan gaisheta sai tai saurin gaisheni. Murmushi kawai nayi, dan ita zan iya girmarta, suma yaran sai suka gaidani, na amsa musu da kulawa ina tambayar sunayensu. Namijin yace Ammar, macen kuma Islam. Yaran sun birgeni, gasu masu ƙyau. Wadda muka shigo tare da aka kira da Nabeelah ce tace min na shiga bayin nayo alwala, cikin tsokana take faɗin “Karnayi abin kunya gashi bansan sunan ƙawar tawabama”.

Ƴar dariya nai babu shiri, ina ƙoƙarin shigewa nace mata sunana Bilkisu. A tare naga duk sun kalleni suna ɗora hannu a bakunansu, hakama biyu a masu sallar da suka idar suma suka juyo suna kallona. Yanda naɗanyi diri-diri na alamar shakkune ya saka ɗaya a cikin waɗanda suka idar da sallar babbar mace tai murmushi da cewa “Mai babban sunace ashe”. Numfashi na sauke a hankali kafin na gaisheta cikin risinawa, ta amsamin tana sake faɗaɗa dara’ar fuskarta, kafin tace naje nai alwalar kar lokaci ya ƙure. Shigewa nayi bayin nima da tunanin ko sunan waye nasu Bilkisun? Daga gani kam dai suna girmama mai sunan sosai.

Ina fitowa Nabeelah ta shiga, suma duk sun tashi daga abin sallar alamar sun bamu waje, sai wadda muka iske tayo alwala kawaice ke salla a wajen, na gaida sauran biyun da bamu gaisaba suma sannan na kabbara sallata.

Bayan mun idar da sallar a cikinsu babu wanda ya tambayeni game dani, sai dai sunata ƙoƙarin sakoni cikin hirarsu wadda duk ta karkata ga mai irin sunana danaji manyan na ambata da Yaya Bilki, yaran kuma na kiranta Mah-mah Yanda suke hira akanta cikin damuwa da kewane ya sakani tunanin ko bata da raine? Bani da mai bani wannan amsar, dan haka na haɗiye abina cikin rai ina cigaba da saurarensu….

Kusan mintuna talatin ina sauraren hirarsu mai cike da birgewar kasancewarsu ahali ɗaya, kafin na miƙe domin tafiya, dan ya kamata naje na binciki inda su Mom suke koda su basu damu da nemanaba.

Duk kallona sukai cike da alamar tambaya.

Murmushi nayi, nace, “Zanjene kar abokan tafiyata suyita nemana”.

Suma duk murmushin sukaimin, Nabeelah ta miƙomin wayarta tana faɗin, “To sakamin Number ki muke zuminci, danni dai nayi ƙawa daga yau”. Ban musaba na amsa wayar tata fuskata har lokacin da murmushi, na saka mata Number ta ina miƙa mata wayar, wadda naji suna kira Aunty Batool tace, “Lallai kin jajubarma kanki kuma Ummien mu, dan shegen surutun Nabeelah takai a guji ƙawance da ita, gaki keman daga gani bakida yawan magana”.

Sanin dani take yasani faɗin, “Aunty ai sunfi daɗin ƙawance irinsu Nabeelah”.

Atake kowa ya shiga faɗin a’a-a’a, yayinda Nabeelah keta ƙoƙarin kare kanta, niko ina musu dariya. Godiya na sake musu kafin nai musu sallama.

Zuciyata tai wani irin harbawa lokacin da akai knocking ƙofar ɗakin tare da sallama cikin wata irin sassanyar murya dake nuna mai ita yana a matuƙar gajiye, tattare da tsagwaron damuwa. Akusan tare suka amsa, nikuma na janye hannuna dana ɗora akan mariƙin ƙofar cike da fargaba, ban gama tattara fahimtata waje gudaba aka turo ƙofar aka shigo, kaɗan ya rage ya bugeni, nai saurin ja baya kaɗan dan na bashi hanya sosai.

Idanunane suka fara sauka akan ƙyaƙyƙyawar ƙafar da baƙin wandon jeans ya sake haskawa, jijjigar da zuciyata keyine ya dasamin tsoron yarda da hasashena, dan haka na kasa ɗago idona naga wanene? Dukda ƙamshin turarensa ya nema saka zuciyata faso ƙirjina ta fito……

Ganin yaƙi shigewa ya bani hanyane ya sakani ɗago idanuna a hankali nakai dubana gareshi, a lokaci ɗaya idanunmu suka shige na juna saboda shima dai-dai ya kalleni. Naɗan sake ja da baya na alamun mamakin sake ganinsa anan, amma shi a mamakina sai naga ya janye nasa idanun babu wani alamar mamakin ganina da ya nuna.

Yanda naji su Nabeelah na rige-rigen gaishesane ya sakani aro jarumta nima nabi layinsu na gaidashi, sau ɗaya ya amsa mana tare da amsa ta’azziyar da mukai masa ya ƙarasa ga iyayensu Nabeelah, hakanne ni kuma ya bani damar saurin ficewa cike da sassarfa daga ɗakin……….

ALLAH ka gafartama iyayenmu .

4 hrs · Public

Save · More

IDAN KUNA SON KU DAUKO DOCUMENT DIN LITTAFIN GOT CHAPTER 3 YANA CAN KASA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *