mayyrah Hausa Novels

Mayraah Na Khaleesat Haiydar Part 1

Mayraah Na Khaleesat Haiydar Part 1

💖💖 MAYRAAH💖💖

By Khaleesat Haiydar📚✍🏻

“Maheer ga wannan ka ajiye a account dinka….” Cewar Alhaji Mahmud kenan yana mika ma matashin dake zaune parlon bundle din kudin dake hannunsa, Maheer ya mike ya karasa ya amshi kudin daga hannun mahaifinsa yana jujjuyawa ya koma ya zauna, sai kuma ya ɗan sosa keya yana murmurshi yace “Toh Allah ya sa kar in hada da su wajen tawa hidimar” Hajiya Hajarah ta girgiza kai tana ɗan murmushi cikin sanyayyen muryarta tace “To ai kun fi kusa da ita….” Alhaji Mahmud na kallon budurwar dake zaune kasan carpet warce bazata wuce shekara ashirin da biyu ba yace “Allah Ubangiji ya sanya alkhairi My Daughter” Ita dai kanta na kasa tana wasa da gefen karamin mayafin dake kanta bata ce komai ba, Hajiya Hajarah tace “Toh tashi ki tafi ki kwanta….” Sai a sannan ta dago manyan idonta tana kallon iyayen nata tace “Sai da safe” Alhaji Mahmud da Hajiya Hajarah suka amsa tare wajen cewa “Allah ya tashe mu lafiya” ta kalli sauran yayyinta maza dake babban parlon su ma tayi masu sai da safe daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon, Hajiya Hajarah ta sauke ajiyar zuciya, a hankali tace “Alhamdulillah, Allah Ubangiji ya nuna mana wannan lokaci lafiya, Allah ya rufa mana asiri, ya hore mana ta yanda bama tunani…” Cike da mamaki Maheer ke kallonta amma dai bai ce komai ba, Tayi murmushi tana kallonsa don ta gane nufinsa, tace “To kai wa ke ta kai zan aurar da auta and only daughter” Alhaji Mahmud yace “Rana daya aka sa da naka ai bawan Allah” Maheer was a bit surprise yace “Ohh ai ban sani ba, to Allah ya kai mu da rai da lafiya” Usman da Umar dake zaune parlon suka amsa da “Ameen ya Allah” Mikewa Maheer yayi, yayi ma parent din nasa sai da safe ya tafi sama, sauran kannensa duk suka bi bayansa, Umar ya shige Bedroom dinsa dake nan downstairs… Tana tsaye walk way da zai yi leading zuwa Bedroom ta jingina da bango, Maheer ya karaso yana kallonta ganin hawaye idonta da mamaki yace “What happened?” Kamar jira take ta fashe da kuka ta durkushe nan kasa, Usman ya karaso wajen yana kallonta yace “Me ya faru?” Cikin rawar murya take kallonsa tace “To ni yanzu aure za a min er yarinya da ni yaya?” Usman ya bi gefen Maheer yayi wucewarsa dakinsa, Maheer ya duka yana facing dinta yace “Wa yace maki aure za a maki, hutu kawai za ki je na ɗan lokaci ki dawo, ai we can’t do without ur food in this house” Ta fara goge hawayenta a hankali tana kallonsa, Maheer na murmushi yace “Toh amma dai naga ke kika kawo mana mutumin nan gidan nan ba wani ya kawosa ba ko?” Ta kalli kudin hannunsa sai kuma ta mike tace “To amma dai ka bani kudin nan in sa a account dina kar kaje ka kashe min, i don’t trust you with money….” Buda baki yayi yana kallonta da mamaki, da sauri ta bar wajen tana dariya, ya gyada kai yayi hanyar dakinsa….. Ta gama shirin kwanciya kenan wayarta dake gaban mirror dinta ya fara ring, karasawa tayi ta dauka tana kallon screen din, ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tare da sallama can ciki, cikin cool voice dinsa ya amsa, a hankali tace “Good evening sir….” Calmly yace “Evening Mayraah” kamar yana ganinta ta sunkuyar da kai don sai da gabanta ya fadi jin yanda ya kira sunanta, yace “Are you done with ur Defense slide?” Tace “A’a ina son ka fara duba min ne sai in ci gaba” yace “Ohk, that is thoughtful of you….” Shiru duk suka yi, bayan few seconds yace “Ya su Ammi?” Tace “Suna nan lafiya” Yace “Maa sha Allah, zan yi tafiya gobe, so zan kwanta da wuri, ko akwai maganar da za ki min” ta girgiza kai a hankali tace “Aa… Allah ya tashe mu lafiya” Yace “Ameen, good night” Daga haka ya katse wayar, ta kalli screen din nata wayar, tabdii… wato nufinsa ita zata fara masa maganar kudin da aka kawo shi bazai mata ba, ta langwabar da kai ta ajiye wayar tayi addu’a ta shige cikin duvet ta kwanta. Washegari da safe karfe takwas Mayraah ta shigo parlor, Ya Usman ne kadai zaune dining area yana breakfast, ta karasa tana tsaye bayan daya daga kujerun dinning din ta gaishesa, yayi mata kallo daya ya amsa yace “How was ur night?” Tace “Alhamdulillah” Shiru duk suka yi, yana ci gaba da shan shayin gabansa, can tace “Me yasa naga kake breakfast da wuri bayan ba kotu zaka ba yau” Ba tare da ya kalleta ba yace “Zan yi tafiya ne” Ta gyada kai, a hankali tace “You look cute” Ya daga ido ya kalleta babu yabo babu fallasa, ta wara masa ido tace “Yes” Ammi ce ta fito daga kitchen ganin Mayraah tsaye dining area tace “Baki da lectures ne yau Mayraah?” Mayraah tace “Ai yau asabar Ammi” Tana fadin haka ta zauna daya daga kujeran dining din tana kallon Usman tace “Yaya can i join you?” Ya matsar mata da flask din kusa da shi zuwa gabanta da kayan shayin, Kafin karfe sha daya na safiyar ranan makota suka dinga tururuwan shigowa gidan yi ma Ammi Allah ya sanya alkhairin an kawo kudin auren Only and last daughter dinta…. Duk da arzki irin na Alhaji Mahmud bai yarda yayi nesa da anguwan da aka haifesa ba, don bayan haifarsa da aka yi a nan, nan din dai kuma ya fara rayuwa da Ammi bayan sun yi aure duk da locality din anguwan don duk yaku bayi irinsa ne dwellers din area din, a nan anguwan Allah yayi ma iyayensa rasuwa Mayraah na da shekara biyu, wanda kusan samun Mayraah ne ya bude ma Alhaji Mahmud kofofin arzkinsa bayan wani bulaguro da suka yi zuwa Yola garinsu Ammi sakamakon yanayi na rayuwa gashi babu me taimako kowa na fama da kansa, a lokacin Maheer is just 10 years Usman kuma 8, Ammi na goyon Umar that was almost 3 years sannan, basu tafi da yaran ba gudun kada suje su sha wahala a yola tunda babu takamaiman abun yi, Aka bar Maheer wajen Mahaifiyar Alhaji Mahmud a sannan da ranta, Usman kuma wajen Hajja Mahaifiyar Ammi warce ita ma ke garin kano, suka tafi da Umar kawai, watansu goma a Yola kwatsam sai ga Mayraah, daga nan kuma wani ikon Allah cikin kankanin lokaci kasuwancin da Alhaji Mahmud ke yi na kai kaya kasar Cameroon ya fara bunkasa kamar wasa, kan kace me ya zama millionaire a yan watanni kadan… Shekaran Mayraah biyu suka sake dawowa garin kano don zuwa sannan Naira ta zauna sosai, A nan kano cikin unguwan da aka haifi Alhaji Mahmud ya gina dankareren gidansa da na iyayensa, wanda kaf area din babu gidan da ya kama kafar tasa, a ko da yaushe zaka tarar da almajirai, yara, maza har da mata masu deban ruwa don famfo kusan biyar Alhaji Mahmud yayi a kofar gidan don kowa da kowa su amfana tunda ana wahalan ruwa sosai a area din, ga sadaka da yake yi duk ranan laraba da Juma’a, wannan dalili yasa kofar gidan baya rabo da jama’a a ko da yaushe, Mayraah na da shekara 6 kakanninta na wajen uba duk suka rasu a shekara daya. Mayraah na kitchen tana wanke utensils da aka yi amfani da su wajen yin breakfast ta jiyo wato makociyarsu Maman Shafa tana cewa “Ikon Allah, sati biyar aka sa kenan, ki ce dai rana daya da na Maheer….” Ammi tace “Ehh hadawa kawai aka yi ayi taron lokaci daya” Maman Shafa tace “Kai abu yayi kyau wllh, to Allah Ubangiji ya sa ayi da mu, Allah ya kai mu lokacin lafiya…” Ammi tace “Ameen Ya Allah” A sanyaye Mayraah ke wanke wanken don ita bata san date din da aka sa ba banda yanzu da take ji a bakin Maman Shafa, haka kawai taji dama a fasa auren nata yanzu a bar shi next year ko upper year, by then she will be 23. Bayan ta gama wanke wanken ta tafi dakinta, kwanciya tayi gefen gado ta rasa me ke mata dadi. Bayan magrib duk suna dinning da Abba da Ammi sai Ya Usman da Umar suna cin abinci, Maheer ne kawai baya nan, Ammi na kallon Mayraah dake ta juya abincin gabanta ganin ta ki ci, tace “Meye haka kike yi da abincin nan Mimi?” Mayraah ta daga kai ta kalleta, Abba ya maida attention dinsa kanta shi ma, Mayraah ta ɗan yi murmushi a hankali tace “Ammi kinsan dazu da yamma na ci abinci, kawai na ji yanzu bana jin yunwa” Ammi tace “Toh idan baza ki ci ba ki rufe za a ba almajirai” Mayraah ta dau wani plate ta rufe abincin ta mike ta bar dinning area din tana tafiya a hankali, dakin Yaya Maheer ta nufa, ta samesa kwance yana waya da fiancee dinsa, Mayraah ta zauna saman wani single chair dake dakin tana kallonsa, ya mike zaune yace “I will call u back dear” bayan ya katse wayar ya kalleta yace “Ya aka yi?” Ta sauke idonta daga kallonsa, a hankali tace “Yaya na ji kamar bana son inyi auren kuma” Lokaci daya hawaye ya kawo idonta ta ci gaba tace “Sai gabana yayi ta faduwa, may be ba yanzu ya kamata inyi auren ba, i am still little….” Yace “Addu’a za kiyi ta yi, it’s always like that Mimi, fargaban barin su Ammi kawai kike, but this is the right time da ya kamata kiyi aure, u are in ur final year in school” Ta kallesa cikin rawan murya tace “Toh ni dai kawai a bar ni in fara gama karatun gaba daya since i am almost done” Maheer ya kalli wayarsa da ya fara ring yace “Mayraah, za mu yi magana gobe kin ga waya nake” Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita daga dakin… Bayan ta gama shirin kwanciya wajen karfe tara na dare wayarta ya fara ring ta jawo wayar tana kallo, sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, sallama yayi mata ta amsa tace “Ina yini” Yace “I told you i was traveling today, but u chose not to call all through…” Zaro ido tayi, sai kuma ta marairaice tace “Kayi hakuri sir, na manta ne….” Yace “To kinyi kokari!”

Karan Littafin Tsutsara nama anan

Ranan litinin da safe Mayraah na zaune cikin department dinsu tare da kawarta Hamida da wata Coursemate dinsu Amira, tun dazu suke tsokanarta wai amaryar next month, ita dai handout din hannunta kawai take dubawa pretending bata san da ita suke ba, a ranta kuma she is regretting telling Hamida, don tun ranan da aka kai kudin ta kirata ta gaya mata don bata da kamar ta a kawaye… Daga wani bangare na Department din clique din wasu yan mata ne in their early thirties su uku a zaune, Farar cikinsu ta gyara zama tana kallon kawayenta biyu Aisha da Amina with shock written all over her face tana sauraron abinda suke gaya mata, Aisha tace “Wllh Surayya ce taji Hamidah na ta tsokanarta da suka shigo department shine ta zo ta gaya mana, amma kar ki ce mana baki da labari, mu nan muna ta jiranki mu sha labari” Amina ta rike haɓa tace “Ikon Allah, wato baki ji ana zancen a gida ba kenan? To ko dae karya ne” Badiyyah da ta ji wani zufa na keto mata ga wani sanyin dake shigarta duk lokaci daya, ta girgiza kai cike da karfin hali tace “Kinsan naje weekend gidan yayan Babana a Bichi, yanzun ma daga can na taho makaranta….” Sai kuma ta mike ta dau jakarta tace “Bari kawai in tafi gida” Tashin hankalinta kwata kwata bai boyu ba, Amina da Aisha suka hada baki wajen cewa “Toh Lectures din fa?” Aisha ta kara da cewa “kinsan fa yanda attendance dinsa yake, kuma saura minti kadan karfe goman yayi…” Ko sauraronsu Badiyya bata yi ba ta nufi hanyar fita department din da sauri, Mayraah ta bi ta da kallo don sai a sannan tayi noticing dinta, Hamidah tayi kasa da murya tana kallon Mayraah tace “Hope tasan an kai kudin aurenki?” Mayraah tace “I don’t know” tana fadin haka ta mike ta ajiye ma Hamidah jakarta tace “Zan yi alwala in dawo” Hamida tace “Saura fa minti bakwai, yanzun nan zaki ga ya shiga class fa” Mayraah tace “Bazan jima ba” Daga haka ta bar wajen da sauri zuwa inda zata yi alwala, ko minti biyar Mayraah bata yi da barin wajen ba sai ga lecturer din, Hamidah ta mike da sauri ta tafi inda suke sallah a department din ta tadda Mayraah ta tada sallah, tuni student suka shige lecture hall sanin wanene lecturer din not because he is strict or he have problem, but because of him being a principal person, Hamidah da Amira ma tuni suka shiga Hall din suka nemi wajen zama. Yana ta tsaye gaban rostrum dake hall din, ya jira har student din suka yi settling, idonsa na kan roll din da su Hamida ke zaune amma saboda glasses da yake sanye da baza kace ga direction da yake kallo ba, the class became absolutely silent in just few seconds, kowa kuma idonsa na kan lecturer din, after about a minute ya gaishesu gaba daya sannan ya fara abinda ya kawosa ajin, wasu student biyar maza da mata ne suka karaso bakin kofar hall din da sauri, sai dai basu yi gigin shigowa ajin ba sanin rules dinsa, kallonsa kawai suke with pleading eyes, bai ce masu komai ba ya ci gaba da bayanin da yake ma class din, ganin they are distracting ya kalli wani student dake front roll zai ce masa ya kulle kofar kawai ya hango ta, da sauri ta kauda kanta ganin direction dinta yake kallo, Ya dae ci gaba da lecturing dinsa, bayan some minutes ya kalli wa enda ke gaban kofa yace “Fine! You can come in, but no attendance for u all” godiya suka dinga masa suka shigo class din, ita ce karshen shiga, taki yarda ta kallesa ya bi ta da kallo ta cikin glasses dinsa, ta nufi wajensu Hamida don sun ajiye mata seat ta zauna, ya ci gaba da bayanin da yake, Hamida tayi kasa da murya tana kallon Mayraah tace “Dama nasan dole a shigo tunda da ke a ciki” Ita dai Mayraah bata ce komai ba ta ciro littafinta da biro ta fara rubutu, duk wani student da suka zo daga baya ya bar su sun shiga ajin sai dai fa basu da attendance kamar yanda ya ce. Karfe sha daya da minti arba’in ya gama lectures dinsa ya fita daga hall din. Wani Coursemate dinsu me suna Bashir ya nufo Mayraah yace “Hajiya Mayraah mu bi bayanki mu tafi mu basa hakuri mana, wllh bani da attendance dinsa wannan semester din, kuma duk wanda bashi da attendance dinsa baya test kun sani” Mayraah ta daga kai ta kallesa ta ɗan buda ido tace “Ni kuma?” Sai ga sauran student din duk sun karaso wajen ta suna mata magiyan tayi masu jagora zuwa office dinsa, Mayraah ta ajiye biro din hannunta tace “Ni ma fa bani da attendance din nan, kuma me yasa sai ni zan bi ku” Duk suka hada baki wajen cewa “Saboda kece assistant class rep mana” Ta ɗan yi murmushi tace “Tun yaushe na ajiye maku wannan post din” Hamida tace “Ba wani ke dae kawai ki tashi ku je” Ganin yanda suka takurata, sauran yan ajin na taya su yasa Mayraah ta mike tace “Toh mu je, idan ya koro mu ai shikenan ko” Haka nan suka tisa ta a gaba su kusan goma sha biyu zuwa office dinsa dake sama, Dr M-Abdallah shine sunan dake rubuce saman kofar office din, duk yanda suka yi da ita ta yi Knocking ta fara shiga ki tayi, ta koma gefe tace “Haka kawai ya koreni, wani dai yayi sallama idan yace a shigo sai duk mu shiga” Bashir yayi Knocking hade da sallama, sai da yayi masa izini sannan ya bude kofar ya shiga, Dr Musharraf na kallonsu a bit surprise yace “What happened?” Mayraah dai na makale jikin kofa wanting to hear him say get out, gaba daya student din kuma ita suke jira tayi magana, can dai ta ɗan kallesa a hankali tace “Sir hakuri muka zo baka don Allah a bamu attendance mu rubuta, we are sorry for coming late” Sai da ya fara sauke idonsa, sai kuma ya matsar da laptop din gabansa ya ɗan kalleta yace “I see… Ke ce mouthpiece dinsu kenan.” Sunkuyar da kanta tayi, Bashir da sauran student din suka ce “Sir don Allah ayi mana hakuri, baza mu maimaita ba in Allah ya yarda” Dr Musharraf ya dau attendance sheet din gabansa ya mika ma Bashir, Bashir ya karasa da sauri ya amsa yana masa godiya tare da sauran daliban, Dr Musharraf yace “You can sign the attendance outside” Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta juya ta fita daga office din da sauri don dama a makale take jikin kofa, Bashir na signing ya mika mata ta amsa ita ma tayi, ta ba warce ke kusa da ita, har ta fara sauka stairs zata koma gun su Hamida wayarta dake hannunta yayi vibrate alamar shigowar message, duba wayar tayi… “Stay behind” shine content din message din, jingina tayi da stairs din kamar zata yi kuka don bata so haka ba, can dai ta koma daya bangaren corridor din stairs din ta tsaya, tana ganin Coursemate dinta duk suka sauka kasa bayan sun rubuta attendance din, babu kuma wanda yayi noticing dinta a cikinsu a hankali ta fara tafiya zuwa office dinsa, tana isa kofar ta kwankwasa a hankali, jin bai amsa ba ta yi sallama, sai da taji ya amsa sannan ta shiga ba tare da ta kallesa ba ta kulle masa kofar, kallonta kawai yake, tana tafiya slowly ta isa gaban table dinsa without looking at him ta ɗan risina tace “Good morning sir” Calmly yace “Mayraah” ta ɗan kallesa, sosai gabanta ya fadi taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, bata san sanda ta zauna kan daya daga kujerun dake facing dinsa ba amma bata bari sun kara hada ido ba, yace “Why were you late to my class?” Ta girgiza kai tace “Sallah naje yi” Bai ce mata komai ba, bayan few seconds yace “Look at me” Da kyar ta dago ta kallesa suka hada ido, da sauri ta daura goshinta kan table dinsa tana jin wani sabon kunyansa da bata san dalili ba ita ma, ɗan murmushi yayi bai dai ce mata komai ba, ganin taki dagowa bayan kusan 40 seconds yace “Shikenan… Idan baza ki dago ba tashi ki tafi” Kamar jira take ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi kofa ya bi ta da kallo, kafin ta fita yace “Sai ki nemi wanda zai duba maki Defense slide dinki” Da sauri ta juyo ta kallesa ta marairaice tace “Don Allah kayi hakuri” Yace “Toh dawo” Ba musu ta dawo tana sinne kai ta zauna, yace “When next ku ke da lecture yau” Tace “Sai 2” Yace “Ohk, kin zo da laptop din ki?” Ta girgiza masa kai, yace “Turo min slide din naki ta Email yanzu” Tace “Toh” Slide din ta shiga nema a wayarta zata tura masa, shi ko sai kallonta yake, can a hankali yace “Kwana nawa su Ammi suka gaya maki anyi fixing?” Sosai gabanta ya fadi, taki dago kanta balle ta basa amsa, maganar da take ta fatan kar yayi mata kenan, yayi murmushi yace “Look Mayraah….” Still taki dago kanta sai ma hade rai da tayi, yace “Toh tashi ki tafi” Da sauri ta kallesa tana buda manyan idanuwanta ta marairaice tace “Duba maka slide din nake fa Sir” Murya can kasa yace “I love you” sunkuyar da kai tayi har da rintse ido, kawai jin kamshin turarensa tayi sharply hakan yasa ta bude ido da sauri ta gansa a gabanta, ta fara kiciniyar mikewa tsabar rudewa ta harde kafa sai ga ta a kasa, ya koma baya da mamaki yace “Meye haka kike yi, do u want to injure ur sef?” Tuni ta mike tsaye kamar zata yi kuka tace “Na tura maka sir” ya duka yana kallon kafafuwanta to be sure bata ji ciwo ba, sai kuma ya mike yace “Ta fi kiyi wucewarki, gobe ki kawo min hardcopy uku na slide din” Da sauri tace “Ok Sir” Sai kuma ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, zaunawa yayi saman kujeran da ta tashi yayi letting out sigh, wondering if she will ever change, ya ga kamar kullum abun ta kara gaba yake. Karfe daya da ‘yan mintuna Mayraah na zaune tare da su Hamida a class suna jiran lokacin next lecture dinsu yayi taji wayarta yayi vibrate, dauka tayi ta duba taga sako ne ya shigo, bude message din tayi tana kallo, “Ina jiranki a parking space” shine abinda ta gani a rubuce, ta kalli su Amira da Hamida ta mike tace “Ina zuwa yanzu” Bata jira cewarsu ba ta nufi kofar fita, Mayraah na isa parking space ta karasa har inda ya ajiye lafiyayyen motarsa wanda babu tantama yana ciki a zaune, zagawa tayi ta daya side din amma bata bude motar ba har sai da ya bude daga ciki sannan ta shiga ta kulle motar, maimakon ta kallesa sai ta fara wasa da Hijab dinta, ledan eatry dake back seat ya dauko ya mika mata ta ɗan kallesa sannan ta amsa tace “Nagode” Yace “Duk sanda kika gama lectures ki kirani, am going home now” Ta gyada masa kai, yace “Sai anjima” Bude motar tayi ta sauka tace “Allah ya saka da Alkhairi” Ta kulle masa motar ta nufi cikin department ya bi ta da ido.
Badiyya na isa gida ko sallama babu ta shiga parlon kakarta, hankali tashe ta jefar da jakan hannunta tare da siririn mayafinta, Hajja kaka dake zaune parlon ta bi Badiyya da ido tace “Ke kuma lafiyar ki?” Badiyya ta zube gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta yi saurin dauke kopin kunun dake gabanta tace “Subhanallahi, lafiya Badiyya? Wani abun suka maki a can Bichin?” Cikin kuka sosai Badiyya tace “Wai Hajja da gaske an kai kudin auren Mayraah?” Hajja na kallonta da mamaki tace “Kudin Mayraah? Ina ruwanki kuma da wata Mayraah, yarinyar da ko ga maciji bakya yi da ita, kudi kuma ai yau kwana uku kenan da kawowa, shawara kika so ayi dake kafin a amsa kudin ne ko ko?” Badiyya ta daura hannu a ka ta kara rushewa da kuka tace “Amma Hajja na taɓa ce maki ina son mutumin fa amma kika bari aka amshi kudin nan, wayyo na shiga uku na lalace” Hajja ta koma baya a firgice tace “Anya kanki daya kuwa Badiyya? Me ya sameki haka? Ina ruwanki da mutumin da bai ce yana son ki ba? Ba ga ki da samarin barkatai na banza da na kirki ba, meye sai na Mayraah zaki sa ma ido fisabilillahi? Me yarinyar nan ta tsare maki a duniya ne?” Badiyya tace “Wallahi sai dai ita ma kar ya aureta duk mu hakura…” Hajja ta matsa daga kusa da ita a tsorace tace “Lallai ban san baki da hankali ba sai yau, ita er uwar taki kike ma baƙin ciki kiri kiri babu sakayawa Badiyya?” Mikewa Badiyya tayi tana kuka tace “Ni ba er uwata bace, babu abinda na hada da ita” Daga haka ta shige dakinta da sauri, Hajja ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace “To Allah ya sa ki gane, idan

Karanta Littafin Gudun Kaddara anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *