Gudun Kaddara Part 2

Gudun Kaddara Part 1

This entry is part 1 of 2 in the series GUDUN ƘADDARA

Bismillahir rahmanir rahim

🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️

H U G U M A

PAGE 01

*Da sunan Allah me rahama me jin qai,dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin talikai,tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta annabi muhammadu S A W

wannan karon labarin namu zai sauka ne a qasar nijer,duk inda akaga kuskure ko gyara sai ayi haquri,domin ni banigerian ce😂

N I J E R maraɗi

Tun daga taku me nisan tazara tsakaninka da ainihin layin,amma kuma kana iya jin tashin sautin gangar kidan data karade kusan kowacce shiyya ta unguwar.

Lokacin da ka cimma nasarar isowa layin kuwa,taron dandazon samari ne da ‘yammata ‘yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewa,wasu cikin ainihin tsakiyar filin da aka bari domin bawa masu sha’awar taka rawar da kyau,wasu kuma daga bayan fage suke takawa suna kuma rausayawa. Kowannensu cikin shigar dake nuna zallar wayewa da kuma sukunin rayuwa yake. Kusan fiye da rabinsu kyawawan BUZAYE ne,wadanda aka fi sani da ABZINAWA,jefi jefi kuma kana iya hangen masu surkin launin fata,wanda wasunsu suka kasance barebarin nijer zabarmawa da sauran yarukan da qasar nijer din ta hada.

A hankali kyakkyawar motar fara qal qirar Yaris ke gangarowa. A kallon farko idan ka yiwa motar,yanayin yadda take gangarowa kadai zai iya sanyawa kayi zaton man fetur din dake taimakawa wajen motsawarta ne yake Shirin qarewa. Saidai kuma sam ba hakan bane.

Kyakkyawan farin matashin ba’abzinen dake zaune cikin motar ne ua zabi ya tuqa motar a haka,farin buzun saurayin da tashin farko kuma kai tsaye zaka kirashi da BALARABE zalla babu mix. Fuskarsa a dinke take tsaf,yana kuma wani irin tuqi kamar wanda jinin sarauta ke zagayawa a gangar jikinsa zuwa ruhinsa. Duka duka shekarun haihuwarsa ba zasu wuce ashirin da hudu zuwa da biyar ba. Amma wani irin lafiyayyen kwarjini dake shimfide akan fuskarsa zai sanya ka dauka wani babban mutum ne dake da wani muqami na mulki ko sarauta.

Tunda ya jiyo sautin kidan daga nesa ranshi ya soma baci,idan akwai abinda ya tsana cikin dabi’ar qasarsu yake da ikon da zai iya sauyawa to wannan tana daya daga ciki. Yaja tsaki har baisan adadinsa ba. Wannan hanyar itace hanya mafi sauqi a gareshi da zai isa unguwarsu,to amma yanayin yadda suka toshe layin yasan zaiyi wahala ya samu ya wuce cikin sauqi ko dadin rai.

Wani siririn tsakin ya sake ja,yadan cije jajayen lips dinsa na qasa yana cusa yatsunsa cikin lallausa kuma cikakkiyar sumarsa ta asalin buzaye,ya qara hannu daya kan guda dayan da yake tuqin akai,ya soma gangarawa da motar gefe don ya samu gurin parking.

Ya gwammace yabar motar a nan guraren,idan yaje ya karbo aiken daga wajen babbo din,sai ya dawo ya dauki motar ya wuce.

Kashe motar yayi,sannan ya zare key din,ya miqa hannunsa ya dauki wata baqar leda sannan ya buda motar ya zura qafafunsa dake sanye cikin boots din da wandon kakin sojin dake jikinsa shi kadai ya isa ya gaya maka waye shi?.

Tun tsaiwar motar taja hankalin mutane da yawa dake wajen,baisan me ya sanya ba,motar ba mallakinsa bace,amma a duk lokacin da ya shiga motar sai take qara masa kwarjini me yawa,abu daya da baiso yadda take sanyawa idanu ke yawa a kansa,wannan ya sanya ba kasafai ma ya fiya hawa din ba,saidai idan aiken gaggawa ne bobbo ko tati sukayi masa,kamar dai wannan aiken.

Da kyau ya hade fuskarsa ba yana ci gaba da ratsa taron,wanda kusan maza sunfi yawa a ciki,zuciyarsa na baci a duk sanda yaga wata mace a cikinsu. Wannan wacce irin lalacewa ce?,qarfi da yaji suna daukan kansu kamar suna france?,baisan wacce irin dabi’ar banza ce wannan da har yau suka kasa dainata ba.

Sake kame jikinsa yayi da kyau lokacin da yake niyyar ratsawa ta sararin da aka bawa masu sha’awar raqashewa da kyau. Duk yadda yaso ya dauke idanuwansa daga kan yarinyar dake tsaye tsakiyar filin tana taka rawa cikin wani irin salo na qwarewa da kuma gwaninta,karya jiki tako ina,kama daga qugunta har zuwa qirjinta da ko irga dangi bata farayi ba,amma tabbas tana kan hanya. Qafafunta da take kadawa tayi gaba ta dawo tayi baya kamar wadda ake matsawa remote control.

Wata mummunar faduwa gabansa yayi,tun daga cikin qwaqwalwarsa zuwa kunnuwansa yaji wani irin sauti kamar an qwala masa farantin silver

“SULTANA!” ya kirayi sunanta cikin wani irin zallar fushi da ya cukuda da tsananin mamaki.

Ko kadan bata fahimci da tsaiwarsa a wajen bama bare ta jiyo kiran da yayi matan. A hankali daya cikin ‘yammatan dake tsaye daga gefe,wanda tun ratsowarsa gurin yayi matuqar tafiya da hankalinsu ta matsa daura da ita kadan tana tabota. Sai data daddaki bayanta kusan sau uku sannan ta waiwayo,saidai maimakon idanunta su sauka akan wadda ke tabata din,basu zame ko ina ba sai cikin idanunsa.

Iyakar razana da firgita ta jita har tsakiyar hantarta,to amma ita din nuna tsoro ko razani saman fuskarta ba al’adarta bace,wannan ya sanya ta juya abinta,saidai kuma ta fara lissafin ta yadda zata zame tabar wajen tun kafin ya yarfata.

Ta karanto tunaninsa kuwa a dai dai,sanda yake taku cikin tsananin zafi don ya cimmata tayi amfani da wannan damar ta kurda ta cikin mutane ta fice. Sama ko qasa sultana tayi masa batan dabo. Cikin zafi yaja da baya ya kutsa ta gefen mutanen cikin sassarfa yana fita daga taron,burinsa shine kawai ya cimmata. WAI YAUSHE TA KOMA HAKA?,YA AKAYI TA SAUYA GABA DAYA?,DABI’UNTA SUKE KOMAWA MASU BAN TSORO?. Wannan tambayar itace ta dinga masa rakiya tana kuma ingizashi da sassarfa,har zuwa lokacin da ya dangane da katafaren gate din gidan nasu.

Cikin wani irin zafi ya tura qaramar qofar dake maqale da gate din gidan,a take ta bude ta kuma hadu da bango ta bada sautin BUM!. Farar buzuwar dake tsaye cikin parking space na gidan ta waiwayo wadda shekarunta ba zasu haura arba’in da hudu zuwa arba’in da biyar ba.

Idanu ta kafeshi dashi sosai sanda yake takowa cikin gidan,ba ita kadai ba,hatta baaba leko me gadin qofar gidan shi da hamidan dake da alhakin gyara da baiwa tsirran da suka qawata harabar gidan ruwa suma binsa sukayi da kallo. Dukkaninsu ya dauki hankulansu,saboda sanin da sukayi masa. Mutum ne da fushinsa bai fiya zuwa da sauqi ba,hakanan yana da wata irin zuciya wadda a duk sanda ta motsa sai kowa cikik gidan yaji a jikinsa. Duk da cewa ba kasafai yake irin wannan fushin ba,amma abu ne da kusan kowa na cikin gidan baya da burin gani a tattare da shi.

Har ta bude baki zatayi magana sai ta fasa,taja wani dogon tsaki tana dauke kanta daga gareshi. Ko ba’a gaya mata ba tasan shi da waye,yanzun nan ta wuce ta gabanta da wani mugun gudun data tabbatar ba lafiya ba.

“A kirawoshi ne hajiya?” Driver hamidou ya fada yana karya murya,saboda ya sani,ita daya ce tal a gidan zatayi furuci qwaya daya da zai dakatar dashi,duk kuwa irin girman fushin da ua debo. Yanayin fushin da ya shigo dashi din kuma ya bayyana muraran ba me sauqi bane,yasan kuma sahun wace ya biyo,ba zaiso kuma a taba lafiyarta ba,don akwai jituwa me yawa a tsakaninsu.

Harara ta watsa masa da fararen idanunta kamar zata cinyeshi danye

“Ban sakaka ba sarkin kankanba”

“Allah ya huci zuciyarki” ya fada yana bude mata motar. Fararen qafafunta ta zura ta shige abinta,cikin ranta tana addu’ar

“Allah yasa ya kakkaryata kowa ya huta” ta fada tana sake jan tsakin me matuqar zurfi da qarfi.

“Maina…..” Muryar dattijuwar ya ratsa kunnensa sanda yake shiga qawataccen falo din da zafi zafinsa. Waiwayowa yayi yana riqe da labulen. Kallo daya tayi masa ta fahimci akwai wani irin fushi da damuwa narke cikin idanu da kuma fuskarsa

“Ina sultana?” Ya tambayi dattijuwar

“Tana dakinta a kwance bata jin dadi,ko islamiyya bata samu zuwa b……” Bai jira ta qarasa fadi masa dogon bayanin data debo ba ya wuce da sassarfa zuwa corridor din da zai sadashi da dakunan nasu.

Sosai ta sake laqewa a blanket tana jan tsaki qasa qasa,duk maganganunsu cikin kunnuwanta ne,ita sam wannan ba mainanta bane,tafiyarsa da dawowarsa a can aka canza mata shi. Tabbas tasan yaa maina da zafi akan kowa amma banda ita,ita din shalelensa ce,wadda baya barinta tayi kuka,babu wanda kuma ya isa ya tabata,koda kuwa rana ce bare ruwan sama,koda quda inda yana da iko bashi bari ya sauka a jikinta bare kuma sauro da ta manta da wanzuwar rayuwarsa cikin duniya.

Tana dire wannan tunanin taji an buda qofar da qarfi,qarar sautin qofar ya saukar mata har tsakiyar ‘ya’yan hanjinta,ta runtse ido ta kuma damqe bargon da take ciki,tsoro yana mamayarta,amma tattaurar zuciyarta na bata qwarin gwiwa.

“Ke!” Ya kirata cikin kaushi da sautin sunan da bai taba kiranta da shi ba.

Duk a tsorace take amma hakan bai hanata murguda baki cikin duhun blanket din ba,tare da ayyanawa zuciyarta ko zai shekara yana kiranta da ke ba zata taba amsa masa ba. Ta fuskanci ya sauya halayya da dabi’a gaba daya,ita kam ba zata yarda yayi mata yadda ya saba yiwa su lamira ba.

“Sultana!” Ya sake kiranta karo na biyu,fushinsa da bacin ransa suna ninkuwa,saboda yayi imanin tana jinsa.

Dakakkiyar sautin muryarsa data fita tamkar yana sansanin atisaye ya sanyata bankada blanket din ta fiddo kanta ba tare data shirya ba.

Cak ya tsaida dubansa akan fuskarta,kamannin nafeesa suna kai kawo saman fuskarta. Wani abu yaji ya ratsa zuciyarsa fushi da kuma tsananin takaicin abinda ya ganta tana yi ya sake tasirantuwa cikin ransa

“Uban waye ya kaiki rawa cikin tsakiyar maza?” Duk da tasan da wannan tambayar zata biyo baya,amma hakan bai hana gabanta sake tsananta faduwa ba,saboda ta sani,sun sha gwagwarmaya da bibi akan wannan

“Ni?,rawa kuma?,a kwance ka sameni fa yaa maina,ni ba inda na fita” ta furta maganar tana nuna kanta da kanta da yatsanta.

Mamaki hade da zallar bacin rai suka saukar masa,shi da sam baya daukan wargi ko qanqani,yau sai gashi yarinyar da ya baiwa shekara kusan goma sha biyar na neman raina masa wayo,yarinyar da yayi yaqinin inda rabonta a jikinsa yake yanzu haka ita din diyarsa ce. Ya tabbatar kaf fadin gidan ba wanda ya isa yayi masa rainin wayo me kama da wannan,hakan yana nufin sassauci da kulawar da yake nuna mata sun fara gaya mata cewa zata iyayin komai ba komai bane?!.

Bata ankara ba sai ji tayi ya fusgo qafafunta,sai gata tana Shirin direwa daga saman gadon zuwa qasa,abinda yayi matuqar razana ta ta saki wata razananniyar qara. Qarar data sanya bibi sakin matajin da take taje doguwar sumarta da har yanzu ke da tsananin tsaho,duk da tarin shekaru ba abinda ya canza daga gareta sai furfurar data jirkita ainihin baqinta. Kai tsaye dakin ta banka gabanta yana wani irin faduwa. Tun sanda ya shiga dakin taji zuciyarta bata kwanta Mata da hakan ba,to amma mu’amalarsa da sultana din ya sanya taji ta dan nutsu ta wani sashen kuma.

Dab da bakin gadon yayi mata burki,ya qara taku biyu zuwa gabanta hadi da jawo stool ya zauna yana dubanta da rinannun idanunsa

“Bariki kikeso ki fara?” Ya jefa mata tambayar fuskarsa na wani irin hucin da shi kansa yasan fushin dake cikin zuciya da gangar jikinsa ya banbanta da na ko yaushe,jinin NAFEESA CE FA?,shine abinda ke amsa kuwwa cikin kwanyarsa.

Cikin tauri da dakewar zuciya tace

“Ni me nayi?” Haushi da takaici suka sake turnuqeshi,ido cikin ido sukayi da ita,amma yanzun shi take tambayar wai me tayi?. Tana masa magana kuma cikin confidence da soyewar zuciya

“Ki gayamin me ya kaiki nan wajen?”

“Ni fa ba abinda naje,ba a kwance ka samenib…….” Bai barta ta qarasa ba ya sauke mata mari saman fuskarta,abinda yayi matuqar razanata,ya kuma razana bibi dake shigowa ta fado dakin da mugun sauri kamar zata kifa.

Wani irin kuka da gigitacciyar qara sultana din ta saki tana riqe bibi data qaraso gurin. Tallafe sultana din tayi tana fadin………

ZAFAFA BIYAR FAMILY🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba

ZAFAFA BIYAR❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥

❤‍🔥 SABUWAR SHEKARA

❤‍🔥 SABON TSARI

❤‍🔥 SABBIN LABARAI

❤‍🔥 TSUMAMMIYAR SOYAYYA

❤‍🔥 CAKWAKIYA

❤‍🔥 LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO

❤‍🔥 SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA

❤‍🔥 LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_

KWANTAR DA ZUCIYA

CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA

QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA

KWANKWASON JIMINA ME WUYAR TABAWA (miss xoxo)

TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE (Billynabdul)

AMEENATU (Mamuhghee)

GUDUN K’ADDARA GUZURIN TARAS DA ITA (Huguma)

KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI

Series NavigationGudun Kaddara Part 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *