mayyrah Hausa Novels

Mayraah Na Khaleesat Haiydar Part 2

Mayraah Na Khaleesat Haiydar Part 2

💖💖 MAYRAAH💖💖

By Khaleesat Haiydar📚✍🏻

2…..

Mayraah na zaune parlor tana danna wayarta wajen karfe biyar da rabi na yammacin ranan aka bude kofar parlorn, tana daga kai taga Hajja ce ta shigo da sallama rataye da jakarta, Mikewa tayi ta nufeta tana murmushi ta amshi jakar tace “Hajja sannu da zuwa” Hajja tace “Yauwa Mayraah, kwana biyu shiru baki je min ba, ko duk karatun ne” Mayraah tace “Dama wannan weekend din nake son zan je in sha Allah Hajja” Hajja tace “Toh Allah ya kai mu, ina Amminki?” Mayraah tace “Tana daki bari in mata magana” Daga haka ta tafi sama dakin Ammi, Hajja ta zauna a parlon tana gyara yafin gyalenta, ba a dau lokaci ba Ammi ta sauko tana ma mahaifiyarta sannu da zuwa, Hajja tace “Yauwa sannu, ya gida ya yaran?” Ammi tace “Alhamdulillah” Mayraah ta tafi ta dauko ma Hajja ruwa, Ammi na kallon Hajja tace “Ba ku zo tare da Badiyyan ba ko bata dawo Bichin ba har yanzu?” Hajja tayi kasa da murya tace “Wace Badiyya, Badiyyar da ta zama abar tsoro Hajarah, dalilin zuwa na kenan ma yanzu haka” Ammi da sai da gabanta ya fadi tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Me kuma tayi Hajja? Ai da kin kirani ma na je ba sai kin taho da yamman nan ba” Hajja dai ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba tana bin Mayraah da kallo har sai da ta ajiye mata abincin da ta debo mata, Hajja tace “Ai da baki zubo min abincin ba ma, a koshe nake Mayraah” Mayraah tayi murmushi tace “Aa ki dai ci ko kadan ne Hajja” Daga haka ta bar masu parlon ta wuce sama. Ammi dai sai kallon Hajja take tana jiran jin me Badiyyan ta kuma yi, lamarin Badiyya na damunta don iya bakin kokarinsu suke yi a kanta amma abu sai gaba yake, dama tunda Mayraah ta zo ta sanar mata zuwan Hajja ta san ba lafiya, don Hajja sai tayi shekara ma idan ba da wani dalili me girma ba baza ta zo masu gidan ba, Hajja ta kara sauke ajiyar zuciya ta labarta ma Ammi yanda suka yi da Badiyya dazu da safe, Shiru Ammi tayi tana kallon Hajja da mamaki sosai, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce tsabar yanda lamarin ya birkita mata lissafi, Hajja na girgiza kai tace “Yanzu da za ki bi ni mu koma gida sai kin ga abun ba kyau, tana can ta cika gida da kuka har sai da mai gadi ya kasa hakuri ya leko yana tambayar ko lafiya, sai nace masa bata jin dadi ne, har zuba mata abinci nayi na kai mata dakin wai duk don in fita hakkinta amma wllh bata ci ba, abun ya isheni na rasa yanda zan yi shine nace bari in zo ko hadani da Maheer za kiyi mu koma ya zane er banza, don in nace Usman sai ya iya ji mata ciwo” Ita dai Ammi ta kasa cewa komai, can dai ta dauke idonta daga kallon Hajja, Hajja tace “Ba shiru za ki yi ba Hajara, idan ba ke din ba wa zan je in tunkara da wannan magana” Ammi ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya tace “Ai da zai yarda shi bawan Allahn da sai ayi auren da ita kawai Hajja, in dai hakan zai sa hankalinta ya kwanta, ita kuma Mayraah tayi hakuri Allah ya fiddo mata da wani” Hajja ta hade rai tace “Amma ban san baki da hankali ba Ammi, in zo neman mafita gunki ki dankaro min wannan magana ba dadin ji haka, ce maki aka yi abinda na zo ki gaya min kenan, wato ina ma goyon bayan taɓaran da Badiyya tayi kenan, ni zaki yanko ma lafiyayyen baƙar maganar nan…” Da sauri Ammi tace “Aa wllh ba haka nake nufi ba Hajja, baki fahimce ni bane….” Hajja ta katse ta tace “To bari kiji ba komai ya sa na zo na sameki na gaya maki ba sai don ayi ma lamarin tufkan hanci tun wuri a taka mata burki ta dawo hayyacinta, in ma akwai wani abu dake damunta a kanta ne sai a nemo mai magani ya cire mata, amma ta yaya zaki yi furucin cewar Mayraah ta hakura ta bar mata? Ina ruwan Mayraah da katuwa Badiyya can, shi yaron dama ita yace yake so ne da zaki ce haka?” Ammi tayi murmushi tace “Toh me zance Hajja, yanda fa Mayraah take ‘ya ta, haka Badiyya ma ‘ya ta ce, abinda zan so ma Mayraah shi zan so mata…” Hajja tace “Kwarai kuwa er ki ce, don ke kika sha Mama kika sakar ma uwarta, kuma yau nasan da Rukayya na da rai ai Badiyya bata isa ba” Sai kuma Hajja ta fara matsar kwalla tace “To duk mutuwa ce ta ja hakan, ke kuma idan kina cewa Mayraah ta hakura gani nake kamar kin mayar da Badiyya bare ne, don da er ki ce ai zaki mata hukuncin da ya kamata ki taka mata burki baza kiyi wannan furucin ba, banda lalacewar zamani yaushe ma za ki ce haka, ai hukuntata ya dace kiyi don wannan babban kuskure ne” Ammi tace “Kiyi hakuri Hajja, ki bari Maheer ya kusa shigowa yanzu, sai ku tafi gidan tare” Hajja tace “To ya dai fi, idan ko ba haka ba ni sai ince ta tattara ta koma can wajen dangin ubanta a Bichi bazan iya wahala ba, kai ba ma Rukayya ba hatta ubanta da ace yana da rai yau da sai ta gane kuranta, to mutuwa ce me tonan asiri, sai dai mu ce Allah ya gafarta masu” A hankali Ammi tace “Ameen” Ammi ta mike tace “Mu je sama kiyi alwala magariba ta gabato” Hajja tace “Aa gaskiya, son samu ne ma ni bana son Mamuda ya dawo ya sameni gidan nan, bar ni inyi sallan a nan, Maheer din na shigowa mu tafi kawai” Duk yanda Ammi tayi da Hajja bata yarda ta hau sama ba ta shiga bandakin dake nan parlor zata yi alwala…. Hajja na zaune saman darduma, Ammi da Mayraah na kitchen Ammi na hado ma Hajja abinci, Maheer ya shigo gidan da sallama, mikewa Hajja tayi da sauri tace “Yauwa ɗan albarka mu tafi ka kai ni gida dama kai nake ta jira tun dazu” Maheer yace “Ikon Allah yaushe kika zo Hajjaju?” Hajja tace “Ban jima ba, mu tafi kawai dare yayi kar Mamuda ya dawo ya sameni” Bata jira cewarsa ba ta nufi kofa da jakarta a hannu, Ammi ta leko parlon tace “Don Allah Hajja ki tsaya ki ci abinci gashi nan yanzu zan kawo, shi fa Alhaji sai tara zai shigo yau ya tafi daukan karatu” Hajja tace “Banda lalura tsohuwa kamar ni me zan fito yi warhaka ina galantoyi a titi ko wacce tsohuwa na killace a gida Ammi? kawai in anyi niyyar bani abincin a zuba min ko a leda ne in tafi gida, Allah ya amfana” Ammi tasan ko me zata ce ma Hajja bazata yi convincing dinta ta tsaya ta ci abincin ba, hakan yasa tace “Toh bari a juye maki a Cooler Hajja” Mayraah tace “Hajja zan raka ki sai mu dawo tare da yaya Maheer tunda shi zai kai ki” Hajja ta juya ta kalleta, Ammi tayi saurin cewa “Aa baza ki je ba, baki ganin dare yayi” Hajja tace “kyaleta mu je kawai sai su dawo tare, abinda a mota za su kai ni su dawo” Ammi na kallon Mayraah tace “Tafi ki juye abincin a cooler….” Mayraah ta koma kitchen, Ammi ta nufi inda Hajja take tace “Hajja da dai ki bari naji tace ran sati zata je gaisheki ae…” Hajja tayi wani murmushi tace “Nasan kin fadi haka ne saboda Badiyya ko? amma kin manta ni babba ce Ammi, ai bazan ma Maheer magana a gaban Mayraah ba, tunda tace zata ki bar ta kawai mu je ba komai” Maheer dake kallonsu yace “Me Badiyyar tayi?” Hajja tace “Ka bari mu je gidan sai in maka bayanin komai”
Karfe takwas da yan mintuna Maheer ya isa gidan Hajja, Mayraah dake zaune gaban motar ta sauko ta bude ma Hajja back seat sannan ta dau abincin suka wuce cikin gidan, a nan parlor ta ajiye warmer din ta zauna… Hajja ta ja Maheer zuwa dakinta, nan tayi masa bayanin abinda ya faru dazu da safe tsakaninta da Badiyyah, Hajja ta kara yin kasa da murya tace “Ka ga ai taki fitowa taga wa enda ma suka shigo gidan ko da barayi ne, kuma tana nan dakin har yanzu ga takalmanta can bakin kofa, don haka ni ban san kan komai ba ban san me ya shiga kanta ba, hankali na yayi mugun tashi me babban suna” Maheer was totally speechless ya dinga kallon grandma din tasa, wato iskancin yarinyar nan gaba ma yake karawa maimakon ya ragu, Hajja tayi narai narai da ido tace “To ai ba shiru zaka yi ba” Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace “Amma Hajja bai kamata ki bari Mayraah ta biyo mu gidan nan ba ai…” Hajja ta daga hannu tace “Aa to kai da uwarka kamar akwai munafurci a lamarinku, ni fa wllh duk daya kowa da kowa yake a gu na, babu abinda ya isa ya lalata mana zumunci, don me za ku dinga abubuwa haka kamar Badiyyar da Mayraah wasu bare ne?” Maheer ya mike ya fita daga dakin ya bude kofar dakin Badiyya, ta juya ta kallesa daga kwancen da take, lokaci daya ta kauda kai tana gyara kwanciyarta ganinsa, ya shiga dakin ya kulle yace “Ke dama rashin hankalin naki da rashin tunaninki ya kai haka?” Badiyya ta wani murtuke fuska taki cewa komai, ya gyada kai yace “Zan yi maganinki, Allah ya kai mu gobe” Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da wani harara sai kuma ta ja tsaki. Sallama kawai yayi ma Hajja yace sai gobe zai dawo, a hankali Hajja tace “Toh Allah ya kai mu” Yayi hakan ne don baya son Mayraah ta fahimci komai don kiris ya rage ya cire belt ya zane Badiyya a dakin barin yanda ta wani juya masa baya saboda rainin wayo, Mayraah ta shiga dakin Hajja don mata sallama bayan da Maheer ya fito, Hajja tace “Toh Mayraah, Allah ya kai mu ran asabar din ina nan in zuba ido” Mayraah tace “In sha Allah, Na leka dakin Aunty Badiyya dazu naga kamar bacci take idan ta tashi kice ina gaisheta” Hajja tace “To zan gaya mata, sai da safe” Suna barin compound din Mayraah na kallon yayan nata dake driving tace “Yaya is anything going on?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Like?” Ta ɗan buda ido tace “Kawai dai nayi sensing kamar wani laifin Aunty Badiyya tayi ko?” Yace “Ai da kin shiga dakin kin tambayeta” Mayraah ta zaro ido tace “Tabb” Ya kawar da zancen ta hanyar cewa “Yanzu dai wasa wasa in less than 5 weeks zaki bar mu Mimi” Marairaice masa tayi tace “Ni bana son kana ce min haka yaya” Yayi er dariya yace “Toh ma dai su waye kawayen amaryan ke da baki da wasu kawaye??” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace “Ko Badiyya?” Nan ma dai murmushi tayi tace “Wannan ai senior sis dita ce” Yace “But…. Musharraf din yasan Badiyya ne?” Mayraah ta kallesa, sai kuma tace “Muna department daya kuma ai dole zai san ta yaya, beside he is our level co-ordinator” Maheer yace “Ohk suna mutunci saboda ke kenan?” Mayraah ta langwabar da kai tace “Not at all, ai shi kasan bai fiye magana da mutane a department din ba, most especially ladies, and sau biyu kawai yake zuwa a sati, Monday and Tuesday”

Karanta Littafin Ameenatu Complete Book anan

Maheer yace “Amma tana zuwa office dinsa gaishesa tunda ai Cousin dinta yake so…” Mayraah tayi murmushi ta girgiza masa kai tace “Ba a shiga office dinsa haka nan, sai dai class rep ko assistant class rep, ko kuma idan shi ya kira ka” Maheer bai sake ce mata komai ba don dama kawai so yake ya fahimci wani abu, bayan few minutes Mayraah tace “Yaya nan ne hanyar gidansu Aunty Haseenah ko?” Maheer ya gyada mata kai yace “Yeah” Tace “Toh don Allah mu biya mana in gaisheta since she is back, kasan ni ban taɓa ganinta ba fa sai dai mu yi magana ta waya kawai” Yace “That is because she is schooling in Abuja, amma yanzu ai ta gama and ranan friday in sha Allah zan kawota gida ta gaida Ammi, zaki ganta physically ranan” Mayraah ta marairaice tace “Don Allah yaya kilan zata ji dadi idan ta gan ni yanzu” Ya kalleta yace “I haven’t freshen up, daga fa wajen aiki nake” ta kai hancinta jikinsa perceiving his scent ta lumshe ido tace “Wallahi kamshi kake kamar yanzu kayi wanka yaya, you are smelling nice” Dariya yayi, ta langwabar masa da kai tace “Pls mana yaya” yace “Ohk then, let me call her” Daukar wayarsa yayi, yayi dialing number fiancee din tasa, yana fara ring ta daga, yace “How far?” Tace “Few Miles…” Ya ɗan yi murmushi yace “Ohk ina hanya, me zan taho maki da shi?” Tace “Really? Amma kace sai gobe” Yace “Naji ina son ganinki kuma” Tayi murmushi tace “To ba sai ka kawo min komai ba dear, ka manta gobe kace za mu je shopping?” Yace “Sure… in few minutes za ki gan ni in sha Allah” Tace “To Allah ya kawo ka my love” Yana katse wayar Mayraah ta kallesa tace “Ni dai ina son voice dinta” Murmushi Maheer yayi yace “Ae na kanwata yafi nata dadi” Mayraah ta washe hakora feeling so happy, Cikin minti sha biyar suka iso kofar gidansu Haseenah, mai gadi ya bude masa gate ya shiga katon compound din yayi parking sannan ya kirata a waya, tana dagawa yace “Ina parking lot” Tace “Ohh wai baza ka shigo ba Baby, ga shi har na ajiye maka fruits a parlor” Yace “I won’t be taking anything, kawai zuwa nayi in gan ki in wuce ba dadewa zan yi ba” A hankali tace “Toh gani nan fitowa Baby” Bayan wani lokaci sai ga ta ta fito, Mayraah ta dinga kallon dressing din da tayi na kananun kaya da suka mata kyau sosai, banda a hoto bata taɓa ganinta ba sai yau, Shi kansa Maheer kallonta yake daga cikin motar har ta Karaso, tana isowa kuma ta bude front seat, turus tayi tana kallon Mayraah, Mayraah ta sakar mata murmushi ta sakko daga motar tace “Dama ni ce nake son in gaisheki Aunty…” Daga sama har kasa Haseenah ke kallonta, Maheer yayi saurin introducing din Mayraah yace “Lil sis dita ce, Mayraah! kuna gaisawa through phone call, kuma kin santa ai a hoto, ko baki ganeta ba?” Haseenah na gyara ɗan gyalen wuyanta ta juya ido tace “Ohh i see, na gane” Mayraah ta sauke kanta tace “Ina yini Aunty” Haseenah ta koma gefe ta tsaya jikin motar tana taunar gum din bakinta tace “Lafiya lau” Maheer ya sauko motar ya zagayo yana kallon Haseenah yace “Daga gidan Grandma dinmu mu ke shine ta dage sai na kawota ta gaisheki” Haseenah tayi murmushi wanda iyakarsa lips dinta tace “I appreciate” Ita dai Mayraah na tsaye bata sake cewa komai ba, Maheer yace “Ohk then, sai na shigo gobe” Haseenah tace “Toh Allah ya kai mu, na tura maka sako via WhatsApp dazu” Yace “I will check” Ya kalli Mayraah yace “Shiga mota mu tafi” Mayraah ta kalli Haseenah tace “Sai da safe Aunty” Haseenah tace “Yauwa” Daga haka ta shiga motar, Maheer ya zaga ya shiga motar shi ma, tuni Haseenah ta juya ta nufi cikin gida babu wani kwakkwaran sallama, bayan sun bar layin Maheer na kallon Mayraah da tayi shiru yace “Do u need anything?” Girgiza masa kai tayi without looking at him, a wajen siyar da fruits ya tsaya ya siya ma Ammi fruits sannan suka kama hanyar gida, yana parking a compound Mayraah ta sauka daga cikin motar rike da Ledan fruits din ta wuce cikin gida, daukan wayarsa yayi ya shiga kiran Haseenah, tana dagawa yace “Haseenah why did u act that way toward my sister? Ko kin zata ɓare ce ita? Get this in ur head she is my sis, and I cherish her more than u can imagine, I don’t joke with her or her matter, me yasa zaki yi min treating kanwata haka??” Haseenah dake sauraronsa tace “Ohww waow, Ai ni na zata Cousin dinka ce, sai bayan kun tafi na tuna ta, ashe last born dinku ce ko??” Boiling from inside yace “Ita kuma Badiyya da kike kawance da wacece a wajena??” Tace “Come off it pls Maheer, i see no concrete reason why u should raise ur voice at me akan kanwarka, Badiyya ai kawata ce we did the same boarding school here in kano, she was my roommate and frnd then, nasan Badiyya kafin in san ka, banda ma taki karatu ai da yanzu ita ma ta kammala masters dinta just as i….” Cikin daga murya ya dakatar da ita yace “Dole in gaya maki ban ji dadin yanda kika yi welcoming kanwata ba Haseenah” Haseenah tace “Wai tun ba ayi auren ba kanwarka ta fara hadamu kenan kake nufi ko me? So kayi in doka tsalle da na ganta in fara ihu ko yaya kake so in yi?” Katse wayarsa kawai yayi ya jinginar da kansa da kujeran motar trying so hard to calm himself down, har cikin ransa yake jin zai iya hakura da auren Haseenah duk da bikin nasu bai wuce saura wata biyu ba don babban bacin ransa a duniya a taɓa Mayraah. Mayraah na zaune gefen gado a dakinta tana studying wani handout aka bude kofar dakin, daga kai tayi tana duban wanda zai shigo, Maheer yayi sallama ya shigo cikin dakin ya tsaya daga bakin kofa, Mayraah ta kalli agogo tace “Yaya baka kwanta da wuri ba yau” Yace “Yeah, hope u are not angry at Haseenah’s attitude?” Mayraah ta wara ido sai kuma tayi murmushi tace “Ohh that…. but ai bata min komai ba yaya, kawai bata yi expecting dina bane shi yasa, it’s fine” Yace “What time is ur lectures tomorrow?” Tace “8am in sha Allah” Yace “Allah ya kai mu” Daga haka ya juya ya fita daga dakin, zai kulle mata kofar tace “Good night” Yace “Allah ya tashe mu lafiya” Kulle mata dakin yayi ta ci gaba da karatun da take.
Washegari har Mayraah ta gama shiryawa zata tafi makaranta bata ga Ammi ba which is very unusual, mai aiki kadai ce a kitchen tana hada breakfast, hakan ya sa ta tafi har bangaren dakin Ammi tayi sallama bakin kofa, sai da Ammi ta amsa mata sannan ta bude kofar ta shiga, kwance taga Ammi saman gado, ta karasa da sauri ta zauna gefenta tace “Ammi ko baki da lafiya ne?” Ammi ta mike zaune tace “Ehh na ɗan yi zazzaɓi ne cikin dare amma da sauki yanzu” Da damuwa Mayraah ta kai hannu jikinta tace “Baki sha magani ba kuma?” Ammi tace “A’a Abbanku ya ma Maheer magana tun cikin daren ya ban magani na sha, ai na ma ji sauki Alhamdulillah” Mayraah tayi shiru tana kallonta, da damuwa sosai tace “Ammi u look stressed” Ammi ta cire duvet din jikinta tana kallon agogo dake nuna karfe bakwai da rabi tace “Ki tashi ki tafi kar ki makara Mayraah” Mayraah ta girgiza mata kai a hankali tace “A’a ni bazan je makarantar ba Ammi, zan zauna in kula da ke, ina maganin da ya Maheer ya baki in gani” Ammi tace “Bana son shashanci nace maki naji sauki ki tashi kiyi tafiyarki” Mayraah ta marairaice mata tace “Allah Ammi bazan iya tafiya in bar ki ba, don Allah ki bari gobe zan je, yanzu ki gaya min inda ke maki ciwo” Ammi tace “Kinsan idan Abbanku ya fito dakinsa ya ganki baki je makaranta ba zai maki fada ko?” Mayraah tace “Zan ce masa bani da lectures yau, don Allah ki gaya min yanda kike ji yanzu” Ammi tace “Ba abinda nake ji, kuma babu inda ke min ciwo kawai bacci nake so inyi sosai” Mayraah tace “Bari in kawo maki shayi ki sha sai ki sake shan magani ki kwanta” bata jira cewar Ammi ba ta nufi kofa, Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, lokaci daya hawaye ya kawo idonta ta koma a hankali ta kwanta trying hard to control her self amma ta kasa, dole tayi kokarin composing kanta kafin Mayraah ta dawo dakin, ba a dau lokaci ba sai ga ta da cup din shayin, sai kuma da ta tabbatar Ammi ta sha kafin ta fara duba magungunan da ta gani gaban Mirror, ta ajiye wani daga ciki tace “Baza ki sha wannan ba…” Maheer ne ya shigo dakin yana kallonta yace “Bazata sha wanne ba?” Mayraah ta juya ta kallesa tace “Analgesic…” Yace “To sannu Aunty Nurse da tafi Dr” Mayraah tayi murmushi tace “Ni dai ban ce na fi ka ba” ya karaso ya duka gaban Ammi yace “Ya jikin Ammin?” Ammi na kallonsa tace “Alhamdulillah na ji sauki” Yace “Toh Allah ya kara lafiya” A hankali Ammi tace “Ameen” Kallon Mayraah yayi yace “ke ba 8am kika ce kina da lectures ba?” Mayraah tace “Ina kwana yaya” Yace “Lafiya lau” Ta mika ma Ammi maganin hannunta da ruwa a glass cup, bayan Ammi ta sha maganin Maheer ya mike ya fita, A hankali Ammi tace “Mayraah tashi kije ya ajiyeki makaranta” Mayraah ta girgiza kai ta dau cup din shayin da Ammi ta rage tace “I will stay with you and make sure u are fine Ammi, bazan iya tafiya in bar ki baki da lafiya ba” Daga haka ta fita da cup din da Ammi ta sha shayi zuwa kitchen, ta ajiye cup din a sink tana kallon Usman dake hada coffee a kitchen din tace “ina kwana yaya” Yace “Lafiya” juyawa tayi ta fita ta koma wajen Ammi.
Haseenah ta shigo Bedroom dinta rike da tray din lemo da cupcakes ta ajiye tana kallon Badiyya dake zaune tayi tagumi tace “Ke ba a ganinki sai idan abu ya sha maki kai ko? Yau sati na nawa da dawowa Kano amma ko sau daya baki taɓa takowa kin zo inda nake ba” Badiyya ta daga kai tana kallonta tare da sauke ajiyar zuciya tace “Ina cikin tashin hankali Haseenah, kuma bani da wanda zan gaya ma da ya wuce ke” Haseenah ta zauna tace “Allah ya rabamu da tashin hankali, gaya min menene ya dame ki kawata?” Badiyya tace “Ina wannan lecturer din namu da nake baki labari?” Haseenah ta juya ido tace “Ke samarin naki ai yawa ne da su, wanne a ciki?” Badiyya tace “Level co-ordinator dinmu mana, yawanci yanzu ai labarinsa nake maki a chat” Haseenah tace “Ohh, wannan da kika ce kike karanta a whole textbook a Library saboda course dinsa?” Badiyya tace “Allah maki albarka shi fa….” Haseenah ta dakatar da ita tace “Bari dai in fara baki nawa labarin, ba jiya sai ga Maheer ya zo nan da wannan cousin din naki bayan magriba ba, ni fa dama tun ma ban ganta physically ba naji bata min ba, ko gaisheni zata yi a waya idan Maheer ya bata da kyar nake amsawa haka kawai naji na tsaneta, sannan na lura favorite dinsa ce yana ji da ita, magana daya biyu sai ya sakota yayi misali da ita, daga haduwar mu jiya da ita har fa sai da muka samu matsala da Maheer a kanta, to in gaya maki tun jiya rabon da Maheer ya kira wayata akan ban doka tsalle da na ganta ba, har yanzu na kasa daina mamaki wai Maheer ne zai iya yini daya curr yaki kirana abinda bai taɓa min ba tun da dating dinmu yayi karfi, meaning yana fushi da ni akan gantalalliyar yarinyar kenan” Badiyya tace “Haseenah ki bar duk wannan ki ji damuwata don tafi taki wllh… Haseenah lecturer din nan dai ya turo iyayensa few days back an kawo kudi har an sa ranan bikinsa da Mayraah ina can Bichi ban san abinda ke faruwa ba, wllh Haseenah kullum da son mutumin nan nake kwana nake tashi nake yini, saboda shi na maida hankali a Nursing Science har nake coping, wai gashi yanzu cousin dita yake shirin aure ba ni ba alhalin ni ya fara noticing a department din ba ita ba, kafin ya ma mutum tambaya daya ya min uku a Class, na shiga uku wllh ji nake kamar zuciyata zata buga in huta, rabona da abinci tun jiya da safe Haseenah” Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Haseenah ta rike haɓa cike da mamaki tace “Ikon Allah, to ke garin yaya kika bari har suke dating juna bayan kina sonsa, me yasa baki taka mata burki ba tunda kince tana shakkar ki sosai” Badiyya tace “To wllh daga ita har shi munafukai ne, ni ban ma taɓa ganin munafukai irin su ba, ko kallon juna fa baza ki ga suna yi a department din ba, ita ma ko kallon inda yake bata yi, kai ya sha koranta idan tayi lattin zuwa ajinsa sannan bai taɓa yi mata tambaya a aji ba, kinsan idan lecturer na ji da student zaki ga yana yawan yi masa question a class, to i am among the students da yake yi ma question, wllh baza ki taɓa cewa akwai abu a tsakaninsa da Mayraah ba komin abunki in har dai ba shegen lura ke gare ki ba kamar Asma’u don ita ta fara ankarar da ni, kin san tana da Asthma din karya ita Mayraan, to ranan sai tayi pretending Asthma dinta ya tashi a class wai an goge ƙura kusa da ita, kuma lectures dinsa mu ke yi, u need to see the care and attention she got from him that day, lectures din da bamu yi ba kenan, ya kai ta dai office dinsa ya dubata har da bata magani, shi da baya sake ma yan mata fuska, wasu student din ma sunce shi ya mayar da ita gida ranan, to bayan haka kuma ni ban sake ganin ya kalli inda take ba a department din balle ya mata magana, ko sunanta ban taɓa jin ya kira ba wllh, Haseenah baki ga yanda na ke karatu ahead of this guys lectures ba tsabar sonsa da nake kuma don in burgesa, duk wani textbook din course dinsa sai na san yanda na takura a siya min a gida, tambaya kuwa idan yayi a class ina daya daga cikin masu bashi amsa, ni ban taɓa sanin ina da ƙwaƙwalwa ba sai da nayi arba da mutumin nan, kokarin da yaga nake yi ne ma ya sa fa ya fara noticing dina a department din lokacin muna level two 1st semester….” Haseenah dake danne dariyarta tace “Noticing dinki as how?” Badiyya tace “Like idan yayi

Karanta Littafin Canjin Rayuwa Complete Book anan

tambaya sai ki ga yana kallona ko zan bada amsa tunda ina yawan basa amsan duk tambayoyinsa, a haka dai ranan bayan yayi tambaya na bada amsa ya tambayi sunana a gaban kowa da kowa a ajin wllh….” Kawai sai ta fashe da kuka saboda wani abu da ya tsaya mata a makogwaro, Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace “Toh ke tun daga sannan zaki yi using privilege din ai” Badiyya dai ta kasa cewa komai sai kuka, Haseenah tace “Toh ita kuma cousin din taki ta yaya har suka fara soyayya baki sani ba” Badiyya na share idonta tace “Shine har yau nake son sani, don yanda kika san statue haka take a class ba um ba um um, infact clique din nata ma kauyawa ne yan ghetto fa wa enda da kyar ake biyan tuition fee dinsu per session, haka zaki gansu da Hijab zumbula zumbula wata er kauyen waratallawa ce fa kawarta a department din ana kiranta Hamidah, to a haka zaki gansu sun samu kujera can bayan class sun zauna ba um ba um um sai yan idanuwa kamar mayu, ni kuma dama front seat nake zama duk ranan da muke da lectures dinsa kinga dole dole ya san ni ko bana answering question balle ni kadai ce mace me bashi amsa a kaf ajin” Haseenah tace “To daga tambayar sunan naki ba abinda ya sake shiga tsakaninku?” Badiyya tace “Wa yace maki? Ai duk inda muka hadu a makarantar na gaishesa to haka zaki ji yace how are you Badiyyah, kaff matan department din babu sunan warce yake kira kai tsaye sai ni, ke kya ce shi ya rada min sunan, har fa haushina wasu yan matan suka fara ji a department saboda yanda yake amsa min gaisuwa” Haseenah tace “Ni ko zan so in ji yanda suka fara soyayya da cousin din nan taki” Badiyya ta share hawayen da yaki tsaya mata tace “Kilan da na yarda na zauna gidansu kamar yanda Ammi ke takurani da zan fahimci wani abu, amma ni rainin hankalin Maheer da Usman ne bana so, barin ma Usman din nan, shi yasa naki zaman gidan wllh, shi dama Umar ba ruwansa” Haseenah tace “Kin ga mu tashi mu tafi gidansu Zaliha bazata rasa shawaran da zata bada ba, ni kam gaskiya ban san me zance ba, da ma dai ba a kai kudin bane, amma wannan ai zance yayi nisa” Badiyya ta mike tace “Tashi mu je don Allah”

Har na fara hango maku littafin nan fans, baza ku gane ba😁

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *