Labarin Abadan da’iman labari ne akan wata matashiya mai suna Maryam wadda ta samu jarabawar rashin aure da wuri wanda sakamakon haka take fuskantar kalubale na rayuwa ta hanyar zagi, habaice habaice da kuma gori daga gurin Matan Mahaifinta har ma dashi kanshi Mahaifin nata a wasu lokuta. Maryam itace Babbar yarinya a gidan su kuma tana da qanne dayawa da suke yan uba sai dai qanwa daya Allah ya bata da suka fito ciki daya wato Hindatu, Su biyu ne Mamansu mama Amina ta Haifa suka rayu sai sauran da duk suka rasu tun gurin haihuwa.
Maryam tayi karatun ta har ta kai matakin degree a fannin girke girke inda ta fara aiki da wata mata mai siyar da abinci da kuma shirya wajen taro, Maryam tana da qawa daya mai suna Raliya wadda ke auren ta da Mijinta Nasir kuma suna da da daya mai suna Fadil. Wata rana Maryam ta kaiwa Raliya ziyara sai Allah ya hada ta da daya daga cikin abokan Nasir wato Jabir inda ya bayyana mata irin son da yake mata kuma da niyyar auren ta wanda sai da akazo ranar daurin auren sannan aka maida shi kan qanwarta Jamila ta hanyar bin bokaye da maman Jamilar tayi aka juye kwakwalwar Jabir din wanda sakamakon haka ita da mahaifiyarta da yar uwarta suka shiga damuwa.
Maryam ta samu aikin dafa abinci da kula da wani matashin mai kudi mai suna Abdallah wanda Mahaifin shi ya rasu ya bar mishi tarin dukiya kuma shi kadai ya haifa inda hakan ya janyo maqiya ke son ganin bayanshi. Bayan Maryam ta fara aiki dasu ne suka yaba da hankali da amanar ta har mahaifiyar shi ta hada shi aure da ita inda itama ta samu kyakykyawar rayuwa har ta ci gaba da taimakon iyaye da yan uwanta.
Abubuwan Burgewa
- Matubuciyar tayi qoqarin zaqulo matsalar da muke fama da ita ta rashin yarda da qaddara inda mutane ke yiwa wanda ya jarabtu da wani ibtila’i izgili kamar dai Rayuwar Maryam da yan gidansu.
- Maryam ta samu kyakykyawar rayuwa daga qarshe saboda jarabawar rayuwarta bata sa ta fada a halaka ba sai ma haquri da juriya da sukayi ita da mahaifiyarta suka fawwalawa Allah lamarin.
Kurakurai
- Labarin yayi tsawo sosai ta yanda ba kowa zai jure karanta shi har qarshe ba kuma rashin kaiwa qarshen zai sai mutum bazai koyi darussan dake ciki ba.
- A yanda aka nuna halin Abdallah da Mahaifiyarshi sunyi saurin sakin jiki da sabawa da Maryam duba da kasancewar ta daga gidan talauci sosai.
Karshe
Rayuwar Maryam rayuwa ce da ke cike da qalubale akan rashin samun mijin aure da wuri wanda hakan bai kawo mata tangarda a ci gaban ta ba saboda juriya, hakuri, kawaici, da kuma yakana da mahaifiyarta ta koya mata wanda haka ya zama sanadiyyar samun gagarumar nasarar ta inda a matsayin ta na yar talaka mai neman na sawa a baki ta qare da auren shahararren attajirin da babu kamarshi a duk fadin garinsu.