Tabarmar Kashi Chapter 1

Tabarmar Kashi Chapter 1

01

          K’awataccen bedroom ne me yalwa,wanda ya wadatu da kyawawan kayan gado da suka kasance cikamakin ado da kyawun dakin,komai dake cikin dakin an hada masa color iri daya CREAMY WHITE da ratsin gold me daukar idanu,ya wadatu da sanyin ac da kuma haske sosai tarwai.

Saidai kuma abinda zai baka mamaki shine,duk da irin kayan ado da qawar da bedroom din ya mallaka,kusan komai na dakin a hargitse yake,hatta da tattausan farin bedsheet din da comforter din dake daga gaban gadon a yamutse suke guri guda,uwa uba kuma dukkansu sunyi staining da wasu abubuwa da bazaka iya tantance meye a jiki ba,illa dai ka ragewa kanka wahala ka kirasu da datti kai tsaye.

           Daga can tsakiyar gadon kuwa, matashiya ce zaune sannan a cure waje daya,tamkar wadda ke shirin saka kanta cikin gangar jikinta ta koma abu guda,ta rungume gwiwoyinta sosai a qirjinta. Baka iya hangen fuskarta,amma kana iya hangen sassalkan gashinta me tsaho da santsi daya cukurkude,kwatankwacin yadda zare yake cakudewa guri guda,tsahon sumar ya sanyata barbazuwa har saman qafafunta,ya kuma rufe dogayen fararen singalalin hannunta. Rigar jikinta doguwar riga ce ta wani material ne ruwan madara,kallo daya zakayi masa kasan me tsada ne,saidai shi kansa ya canza yanayi yayi wani irin azababben squeezing.

            Idan ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukanta,sautin da bashi da wani qarfi ko karsashi a cikinsa ko misqala zarratin,saboda rashin wadatacciyar garkuwar jiki da zata bata wannan damar,uwa uba kuma…….tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba,ta zubda hawayen har sai data daina sanin lokacin tahowarsu……har sai da idanunta suka fara gani dishi dishi,ta yanke tsammani daga samun dukkan dauki,ta kuma gama sallamawa qaddara rayuwarta.

            Duk da cewa a hankali ya bude qofar dakin amma hakan bai hanata jin alamun an bude din ba,a hankali ta daga kanta,ta kuma sauke dubanta ga bakin qofar,duk da mummunar wahala da ibtila’i me gigita hankali da gusar da imanin me raunin tauhidi da take fuskanta,amma har yanzu kyakkyawar fuskar nan tata tana nan yadda take,wani irin kyau na daban me matuqar tasiri da fusgar hankali da ya gagara gushewa shimfide saman fuskar tata,saidai kana kallonta kasan ba haka take ba,abubuwa da yawa sun canza wanna fuskar.

           Shi da ita suka zubawa juna ido kamar yau ce ranar farko da suka fara ganin juna,kowannensu da kalar kallon da yakewa dan uwansa. Dariya ya saki ya cire hannuwansa daga aljihun trouser din jikinsa,ya fara takowa zuwa cikin dakin bayan ya sanya hannu ya maida murfin qofar dakin ya rufe. Yana takowa yana tafa hannayensa, idanuwansa kuma a kanta kamar yadda dariyarsa bata yanke ba,ita kuma taci gaba da binsa da kallo,zuciyarta tana la’antarsa,tana sake daukaka qararsa zuwa ga sammai wajen ubangijin al’arshi.

            A haka ya qaraso,ya jawo stool zuwa gaban gadon,ya zauna sosai yana fuskantarta hadi da taka gefen gadon da qafarsa guda daya

“Kewai kina tunanin akwai abinda zakiyi da zai warware dukka shirina?,ko kina zaton zaki kubuta da sauqi haka?” Kyawawan idanunta da suka sake zama manya manya ta lumshe,ragowar hawayen da basu samu damar zubowa ba suka gangaro,sannan ta budesu tarwai a kansa

“Bani da tsumi kuma bani da dabara,ban isa na fidda kaina ba,amma na kaiwa me kowa me komai,mai iko akan kowa qararka,koda kayi ajalina…..koda bayan raina ina fatan nutsuwa da salama suyi qaura daga rayuwarka,ka girbe fiye da abinda ka shuka” ido ya runtse ya kuma bude a tare yana sakin qaramin murmushi,sai ya miqe tsaye

“Dadina dake tawakkali…..” Yayi furucin yana qara taku biyu zuwa gaban gado,ya haye gefan gadon ya zauna,sai tayi saurin sake tattare qafafunta ta rungumesu da kyau,kamar wanda yake shirin raaba mata maciji a jikinta.

          Qafafun nata yabi da kallo har ya zuwa fuskarta,sai ya sake qyalqyalewa da dariya

“Ina sonki…..kuma banajin zan daina sonki,saidai kin shiga hurumin daba naki ba,kin shigar gonar daba taki ba,kin tsallake iyakarki,kuma a yanzu nafi buqatar wadan nan abubuwan fiye dake,ki daukominsu ki damqamin,ke kuma na barki kici gaba da rayuwarki cikin salama” kai take girgizawa tana hawaye,wani irin mamakinsa tana jin kamar zai kasheta, kowacce rana da zata bullo zuwa faduwarta cikin shakka da kokwanto take,anya wannan din ADAM NE?,anya adam dinta ne?,anya musanyensa akayi mata ba?,ko kuma wata rundunar mugayen shaidanun aljanu ta shige jikinsa ne ta samu mafaka?,don abinda yakeyi a yanzun da ainihin wannan suffar tasa ta yanzu…….bata taba ganinta a tattare da adam dinta ba,koda kuwa cikin mafarkan bacci bare a kai ga rayuwa ta zahiri,adam din da ko quda baya qaunar ya sauka a kanta?,adam din dake kuka da idanunsa idan bata da lafiya?,adam din da yake kasa bacci saboda ta shiga damuwa?,adam din da yake kasa sukuni idan tana da buqata har sai ya adar mata?,dole ta shiga shakka…..amma kuma kullum yana qara tabbatar mata da cewa shi dinne fa,bawai kama ko musaye bane,to me yake faruwa?.

“Bazan taba baka ba…..burinka bazai taba cika ba,saidai na rasa rayuwata,kayi duk abinda kaga dama” ta fada tana jin bacin rai yana taso mata,tare da wani irin qwarin gwiwar tunkarar duk nau’in kalar azaba tuggu da makircin daya shirya mata.

           Wani murmushi ya kuma saki yana dubanta,da wani irin kallo na qasa qasa mai cike da tarin mugunta

“Ke kike jawa kanki koma meye,tunda ke muguwa ce ba zaki iya sallamamin abinda kikafi qarfinsa ba tako ina,to nima bazan sassauta miki ba har sai sanda kika gasu,kikaji cewa zaki iya sallamawa” daga haka ya miqe,ya fara fidda kayan jikinsa yana zubarwa a wajen.

            Idanu ta bude da kyau cikin tsananin tashin hankali tana dubansa,kada dai ace haqqinsa na aure yake shirin karba kamar yadda ya saba?,zallar rashin imanin da yake gwada mata bai sanya ya daga mata qafa ba,yakance

“Har yanzu fa a sunan matata kike,ban saki igiyar ba,wannan abun dake faruwa wani issue ne na daban daya shafi interest dina da kuma naki”. A duk lokaci irin wannan idan ya rabeta tana jin inama zata bude idanu taganta kwance cikin ramin qabarinta?,banda addininmu ya haramta kisan kai,naka ko na Wani,tabbas da tuni ta tsufa da kai kanta kiyama.

           Da gaske so yake ya kusanceta alhalin yasan cewa cikin jinin al’ada take,rashin imanin nasa qara gaba yake,dole tace rundunar shaidanun aljanu ne suka shigeshi,don lamarinsa yafi qarfin shaidani guda daya.

       Kansa tsaye ya nufota gadan gadan,kamar ba adam din nan da abaya a lokutta irin wanann yake sanyata taji babu ya ita cikin ‘ya’ya mata ba,ya sanyata taji duk duniya babu macen da tayi sa’ar abokin rayuwa irinta ba,a yanzu ya koma mata wani tsohon annamimin ifritu mashayin jinin bil’adama da ko motsinsa bataso ji bare ya rabeta,bashi da maraba da qaton shaidani a idanuwanta.

         Ringing din wayarsa ya dakatar dashi daga sake tunkarota,sai ya koma cikin aljihun wandonsa da ya yasar yana lalubar wayar. Cikin hanzari ya karata a kunnensa,sai kuma yace

“Ok,yanzu yanzu?,tom” ya latse wayar da sauri ya maidata,sannan ya soma mayar da kayan jikin nasa tana daga zaune tana kallonsa.

          Ga mamakinta sai taga yana bi yana balle button na rigarsa yana watsarwa,ya kama gaban rigar da qarfin tsiya ya ciccisge,sannan ya tsugunna ya jawo plate din tangaran din dake ajjiye gefe wanda ya kawo mata abincin da bata budawa bare ta taba,ya dagashi har abincin ya tamfatsa shi da qasa ya tarwatse,ya dauki wani yanki daga ciki ya yanki jikinsa ya kuma shashshafe maiqon a jikinsa.

           Sake miqewa yayi ya fara fatali da kayan dake saman madubi da duk wani abu na glass dake dakin yana cewa da matuqar daukaka murya

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,ki tsaya……ki tsaya don Allah,ya salam,karki jiwa kanki ciwo, Hasbunallahu wa ni’imal wakeel,ya hayyu ya qayyumu ya baki lafiya” yana fada hawaye na sauka a idanunsa,yana kuma ci gaba da tarwatsa dakin tare da sake hargitsashi,bayan tsaiwa da tayi tayi masa gyara na nutsuwa,waiko hakan zai sanya wani daga cikin ahalin nata su ankara da cewa akwai hankali tattare da ita.

            Sanqamewa tayi a zaune,tunaninta ya dinke cifff kan meye manufar adam na aikata haka?,saidai koma meye tasan halinsa,ungulu ne baya jewar banza,ba shakka akwai abinda yake shirin sake qullawa. Kafin takai ga lalubo abinda ke shirin faruwa sai ta tsinci muryoyin mutanen da a kullum take addu’ar isowarsu gareta,qila akwai wani haske da zai risketa,ya kuma zama silar fitarta daga duhu zuwa haske.

         Da mugun qarfi ta yunqura zata dira daga gadon,yayi caraf ya tsallako ya damqeta ya cukuikuyeta da kyau yana sake yamutsa rigata da yamutsatsen gashinta.

           Ya mata mugun riqon da bazata iya qwacewa ba,saboda banbancin qarfi da kuma qarancin garkuwa jiki dake tare da ita,don haka ta bude baki da zummar kiran daya daga ciki

“Koda kin kirasun ma sun shigo sunanki bazai canza ba a idanunsu,sunanki mahaukaciya har yau har gobe,sai ranar da kika fanshi kanki,ni kuma zan wankeki a idon duniya” daga haka yaci gaba da qaraji da ambaton sunan Allah yana mata kyakkyawan riqo,ita kuma taci gaba da yunqurin qwacewa hawaye na gudu bisa fuskarta, kokawa ta barke a tsakaninsu duk da cewa ba wata nasara a hakan sai azabar riqon da yayi mata da takesha,dai dai sanda aka turo qofar da sauri aka shigo,ya saki wani lafiyayyen murmushi daga can qasan zuciyarsa,burinsa ya cika,plan dinsa ya tafi a dai dai,dama abinda yakeso kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *