04
“mahmud abba gana…..kinsan wayeshi kuwa saahar?” Afifa ta jefa mata tambayar cikin kwantar da murya da salon rarrashi,kamar saahar din ba zata tanka ba,sai kuma ta motsa labbanta a hankali
“Ban damu insan waye shi ba,bana kuma buqatar na sani”
“Amma me yasa zaki wulaqantashi saahar?”
“Me yasa ba zasu gane ba…..me yasa ba zasu rabu dani nayi rayuwata ni kadai ba?” Ta jefawa afifa tambayar tana ware dukka idanuwanta akanta
“Ba zasu gane ba ba kuma zasu rabu dake ba,saboda qaddararki daban tasu daban,abinda kike hangowa daban abinda suke hangowa daban,kina yaudarar kanki ne kawai…..amma a irin surarki kinyi qarya ki hana maza su biki ko su soki” maida idanunta tayi ya lumshe zuciyarta na bugawa,bata taba jin kyanta na neman zame mata barazana ba irin a wannan dan tsukin da take gujewa mazan irin gudun da rai zai yiwa mutuwa,ta tsanesu fiye da yadda dukka wani abun halitta yake gudun kishiya,tanaji inama ace bata da wannan kyan da ya zame mata jarabta,inama ace ita mummuna ce,qila wannan munin zai siya mutu da nutsuwa,zai kuma barrantata daga dukkan wata barazana,ya hutar da zuciyarta da kwanyarta
“Duk yadda mace takai ga muni…..duk yadda takai ga zamantowa cikin matakin qasa qasa na rayuwa…… ba’a rabata da samun soyayyar maza wadda take dai dai da matsayin tata rayuwar……” Afifa ta fadi idanunta nakan hanya,kamar tasan abinda ke kai komo a zuciyar saahar din,saidai batakai ga qarasawa ba saahar ta dakatar da ita
“Na roqeki kibar kiramin sunansu a wajen nan” duk da yadda tausayin saahar ya tabata amma sai data murmusa don dole
“Bayan tsanarsu da kikayi,i think harda tsoronsu ma yanzun kikeji ko?,keda mukayi dake zaki qarasa kiyi biya kudi saiki gudu ki barni dasu suna jifana da tambayoyin ina kudinsu?, anyway alhmdlh, mahmud ya fansheki ya biya” ta qarasa fada tana waiwayowa cikin son ganin reaction na fuskar saahar din,akayi sa’a itama ta waiwaya din,saita watsawa afifa wani irin kallo kafin ta janye idanunta tana gyara kwanciyarta sosai cikin motar hadi da fadin
“Allah ya baki sa’a” kalma data sanya afifa dariya sosai,tasan sarai me saahar ke nufin aikatawa muddin tace mata haka. A haka suka qarasa gida,saidai duk yadda tayi da saahar ta tsaya ta dauka musu takeaway din cewa tayi
“Ban fara yunwa ba da zanci abinda wani ne ya siya da kudinsa,i have enough da zan iya siya cikin account dina nima,dama asali ni rakiya nayi,so na yafe” ta wuce cikin gidan cikin nutsatstsen takunta,afifa ta bita da kallo tanason sakin dariya.
Yalwataccen falo ne da ya sha shimfidu da ado cikin kalolin silver and royal blue,rukunin kujeru guda biyu kenan,daya nau’in kalar silver,daya kuma kalar royal din,stairs guda biyu ne qawatattu kewaye da falon da ya cika dukkan sharuddan zama qawataccen falo na alfarma dake nuni da zallar dukiya da kuma wadatar da ahalin suke ciki.
Kana sanya qafarka abu biyu zaiyi maka maraba,sassanyan qamshin turaren da humidifier ke bayarwa da kuma qamshin girkin dake fita a kitchen din gidan dake manne da falon qarqashin daya daga cikin stairs din.
Mutum biyu ne cikin falon,kyakkyawar baqa ko muce black beauty din macace da a qiyasin da idanuwanka zasu iyayi ba zata haura shekaru talatin da biyar ba. Kallon farko kawai da zaka yi mata zaka san cewa GIDAN GAYU ce,gayu da iya ado da kashewa jiki kudade masu nauyi saboda gyaransa ya samu mazauni a tattare da ita,cikin furucinta idan ka nutsu da kyau kana iya tsintar yadda harshen KANURI ya ratsata da kyau yadan gurbata hausar tata kadan,cikin matuqar girmamawa take magana da kamilar matar data kusa ninka shekarunta kadanne babu,MAAMA me shekara hamsin da biyar,farace sol da take da kamannin da SÃAHAR ainun,zallar jin dadi da samun sukunin rayuwa ya boye shekarunta sosai,saidai shi girma duk yadda kakai ga son tureshi da bawa jiki kulawa baya hanashi bayyana,illa dai ana samun sauqi yazo cikin cikakkiyar qoshin lafiya da kuma siffa nagartacciya.
Sallamar sãhaar din taja hankulansu,fuskar matar ta fadada da fara’a idanunta bisa fuskar sãahar din
“Yanzun nake shirin kiranki,ya akayi kuka dade haka?” Ta tambayeta sanda take gaggawar isowa ga matar,dukka idanunta suna kan kyakkyawar yarinyar dake kwance a gefanta saman kujerun falon tana wutsil wutsil da qafafuwanta cikin wata overall me taushi,yalwataccen gashin yarinyar yayi luf saboda gyara da yasha cikin zallar tsafta da kulawa,wannan ya sake fidda kyan yarinyar sosai.
“Sannu da gida maama” sãahar din ta fada dai dai sanda take duqawa ta dauki baby girl din,fuskarta na sake wadata da fara’a,ta daga yarinyar tana kallonta,tana jin wani tsohon emotion yana taso mata,saita sanya yarinyar cikin qirjinta ta rungumeta tana sumbatar ta.
Dukkansu a fakaice suke kallonta,kowannensu tausayinta yana ratsa zuciyarsa,duk da cewa suna qoqarin dannewa sa hana bayyanuwarsa saman fuskarsu
“Afifa ce,haka kawai ta lallabani ta jani rakiya zata kaini inda……” Sai kuma ta kalmashe ragowar maganarta cikin cikinta,tana dan shafa kan yarinyar a hankali,yarinyar tayi luf a qirjinta kamar wadda barci ke shirin dauka.
“Ina afifan takaimin ke?” Matar da suke kira da suna anty farheen matar aure ga dan uwanta shaqiqi ta furta cikin nuna kulawa,dukka idanunta suna kan sãahar din tana son jin amsar tambayarta
“Anty,ki tayani tambayar qanwarki dai,bayan tsanar data yiwa maza,hala ta fara tsoronsu kuma” afifa dake shigowa Parlor din hannunta riqe da ledar takeaway dinsu ta fada fuskarta yalwace da murmushin da baka rabata dashi,akasin hali da dabi’ar dake tsakaninta da sãahar kenan. Kafin anty farheen tace komai sãahar taja wani dogon tsaki tana sakarwa afifa harara
“Don dai tuwon gobe ake wanke tukunya” ta fada mata tana takawa a hankali zuwa gaba,dariya ta subucewa afifa,yayin da maama da anty farheen suka murmusa
“Inyeeee,to barkanki da kike sake jin hausa haka da kyau” afifa ta fada cikin salon tsokana tana neman gurin zama. Ta fuskanci idan ta biyewa afifa surutu zata yita sanyata,bayan ciwon kan data so saka mata yanzu,don haka ta waiwaya ga anty farheen
“Brother fa?”
“Yana gurin abba,inajin dama ke yake jira tun dazun” kai ta jinjina,ya kirata a dazun sanda take zaman jiran afifa,don haka ta fara takawa a hankali zuwa hanyar da zata sadar da ita da sashen mahaifinta,baby aleena na kwance saman kafadarta
“Nazo nayi rakiya?” Afifa ta fada tana bude ledarta,ci kanki batace mata ba kamar yadda tayi zato,ta wuce abinta,sai afifan ta saki dariya tana fidda kayan cikin ledar
“Me yasa kikeso ki dinga tunzuramin qanwa ne afifa?,za’a ji kanmu fa” anty farheen ta fada dukka idanunta akan afifa bayan maama ta miqe zuwa dakinta dauke da ledar kayan da farheen din ta kawo mata kyautarsu,fuskar farheen din a sake ta yiwa afifa tambayar. Ta buda takeaway dinta ta saka fork a ciki tana dariya
“Abun sãahar ne anty kamar sake gaba yake,duk waje idan akwai maza suka wuce uku saita sakawa gurin karan tsana?,me yayi zafi haka?” Kai farheen ke gyadawa a hankali idanuwanta akan afifa,ta bude baki a nutse tace
“Babu halittar dake saurin ruguza dukkan buri mafarkai yadda da aminci na diya mace irin halittar da namiji,idan ta dace da abokin rayuwa na gari……sai kiga tana yiwa maza dukka kallon abu daya,hakanan idan aka samu akasi shima haka abun yake,a dukkanin kafatanin rayuwa kuma babu abinda yakai ciwo irin cin amana ha’inci ko yaudara daga wajen wanda ka miqawa dukkan yarda aminci da kuma qauna,a maimakon ka samu ninkin abinda ka bayar…..ko ka samu koda ace kwatankwacinsa ne, a’ah……sai ka samu akasin dukkan abinda kai din ka miqa,ba kowanne yanayi muke fahimta ba…..har sai lokacin da muka samu kanmu a kwatankwacin irin wanna hali ko yanayin” kai afifa ke gyadawa,maganganun farheen sun shigeta,musamman daya kasance kamar wani tuni ne ta sakewa afifa bawai kuma don afifan ta manta ba,a’ah…..don dai kawai zuciyarta ta kwadaitu dason ganin wasu abubuwa masu kyau na wanzuwa cikin rayuwar sãahar din tata,gyara zamanta sosai afifa tayi tana fuskantar farheen tana kuma ajiiye meatpie din hannunta data gutsura saman dan qaramin farantin tangaran din data kirayi baaba sa’a ta kawo mata,ta kawo seriousness ta dora saman fuskarta,da gasken gaske abinda bakinta zai furta a yanzu yana daya daga cikin abubuwan da ya shiga list na burikanta a yanzu
“Amma anty……shikenan sanadiyyar kuskure ko son zuciyar wani sai kabi ka kashe taka rayuwar?,saboda wani laifi na wani can mutum guda sai ayiwa kowa kudin goro a tsundumashi cikin matsalar da babu ruwansa?,matsalar da baisan da wanzuwarta ba?” Kai farheen ta girgiza,bata kai ga cewa komai ba afifa ta dora
“Mahmud abba gana fa anty……. bakiga cin kashin da taso yi masa ba yau,don kawai yayi mata magana” tun kafin afifa ta qarasa farheen ta fidda dukka idanunta waje tana dubanta cikin yanayi mamaki matuqa da gaske
“How comes afifa?” Dukka kafadunta ta dage tana yarfa hannu,alamun abun itama sam bai mata dadi ba