Tabarmar Kashi Chapter 5

Tabarmar Kashi Chapter 5

PAGE 05

“Ban sani ba anty,nazo na sameshi ne a tsaye yana kallon motar,Tayi disappointing nashi sosai wallahi anty,ni kaina i was so shock da naganshi tsaye a wajen,nasan halinta,may be banza tayi dashi,ko kuma ta gaggaya masa maganganu marasa dadi” shuru farheen tayi tana juya kai cike da jimami,mahmud was so familiar,kusan sananne ne shi da mahaifinsa,matashin dake da arziqi da kuma nasaba cikakkiya,dan asalin garinta ne wato borno,wanda tayi imanin babu a inda bazai nema aure ko ya nemi mace a dauka a bashi ba da gudun gaske

“He really broke her heart……..yayi mata illa da yawa,that’s why ta kasa bari ta warke har yau” farheen ta fada tana sake ci gaba da juya kanta,kallonta afifa keyi itama tana hadiye wani abu me daci,ko zancansa ta tsani ayi itakam,batason tuna komai daya wuce a baya,tana jin kamar ba zata iya yafewa ba tabar komai kamar yadda abba yayi umarni ba

“Amma dolen dole……she need to move on,bazai yiwu ta rayu har abada a haka ba”

“Haka nake gayawa kaina kullum,nidai na riga na bashi phone number dinta,saidai ta hadiyi zuciya bayan yayi kiranta idan taso” qaramin murmushi ya subucewa farheen

“Babu wannan zancan,zamu ci gaba da lallabata ne tayi accepting koma meye zaizo mata,inajin yau da ita zamu wuce gida ma”

“Hakan yayi anty,nima dama yau zoo road zan wuce”.

            Tana rungume da aleena tayi sallama da muryarta me cike da wani irin sanyi da maganadisun dake fusgar hankali,dukkansu mutum biyun dake falon suka waiwayo suna amsa mata sallamar cikin bata attention dinsu,fuskokinsu suka wadata da murmushi,farin dattijon dake zaune cikin sofa qafafunsa miqe,daga gefansa takardu ne masu yawa da kuma wani kyakkyawan biro a hannunsa,da alama yana signing ne,sai matashi me jini a jika me surkin kala wanda ya kwashe kamannin dattijon tsaf!,nutsuwa da cikar kamala ta lullube fuskar nan dake cike da danyan jini da jin shekaru da yake ganiyar yi.

“Abba……barka da warhaka” ta fada tana rusunawa a gabansa,ya saki murmushi yana ajjiye takardun hannunsa ya miqa mata hannun nasa yana cewa

“Bani amaryar nan tawa da batayi dani” wani dan qaramin murmushi daya fidda ainihin kyanta ta saki,ta matsa tana miqa masa aleena din,ya karbeta yana tsokanarta,saita maida kanta ga dan uwanta ta zauna sosai tana tanqwashe qafafunta

“Yaaya barka da yamma” hararar wasa yadan watsa mata bayan yadan dauke kansa daga takardun kadan

“Yamma ko dare,tunda na shigo nake nemanki da kyakkyawan albishir amma baku tashi shigowa ba sai yanzu,nima komawa zanyi da albishir dina” yanayin yadda yake magana da ita kadai ya isa ya gaya maka zallar shaquwa da kulawa da suke bata,yadda ita dinma take ganin girmansu da basu dukkan wani respect daya dace. Kai ta langabar gefe guda

“Haba yaaya,kada muyi haka don Allah,ban taba abu naji na matsu na samu feedback ba Allah sai wannan abun”

“Naqi nima” ya fada yana buda shafukan gaba da na takardun hannunsa. Idanunta ta maida ga abbansu dake zaune yana jinsu ba tare da yace komai ba

“Abba ka saka baki don Allah” murmushi ya saki,yana sauke qafafunsa dake harde a dazun waje daya yada gyara zamansa,yatsunsa na riqe da yatsun aleena daketa bangala masa dariya

“Kayi haquri mana yaaya qarami a gaya mata ko?,nima na matsu na tayata ji” kansa ya daga daga takardun yana rufesu fuskarsa da murmushi,ya ajjiyesu gefansa sannan ya dubeta kai tsaye

“Shikenan tunda abba yasa baki,zan gaya miki amma bisa sharadin kome na buqata zakiyimin?” Ya furta yana murmushi qasa qasa hadi da dan juya kansa,alamun deal ne idan har ta amince din.

              Ba tare data kawo komai a ranta ba,don ta dokanta taji feedback din ta gyada kai,lallausan murmushin nan nata yana fita a fuskarta

“We made it!” Ya fada with full excitement idonsa a kanta,don sosai ta sakashi jin alfahari da ita,musamman lokacin da  yake gaban alhj ahmad girema yake lissafa masa benefits da za’a iya samu a tattare da ita. Manyan idanunta a yaunta fiddo waje cikin jin mamaki da kuma farincikin da taji yana ratsata,yanayin data jima bata ji irinsa ba,sai tasa zara zaran yatsunta tana rufe fuskarta,qaramin kyakkyawan bakinta yana furta

“Alhamdulillah” can qasa,cikin zuciyarta tana jin dadi data zama solution na problem din dan uwanta,a rayuwa tana qaunar taga ta zama silar warwarewar matsalar wani,yana daya daga cikin abubuwan dake faranta mata rai a duniyarta,bayan son yara da Allah ya jarabceta dashi

“Thank you sãahar…… thank you ummin abba(sunan da suke kiranta kenan sometimes,saboda taci sunan mahaifiyar mahaifinsu wato kakarsu kenan KHADEEJA)”

“Don’t mention it yaaya” ta fada tana girgiza kai, murmushi har yanzu bai bar fuskarta ba,sai dukka hakan ya sanyaya musu rai,don sun jima basuga hakan ba tattare da ita,lallai abun ya sanya farinciki me yawa a zuciyarta

“Yauwa……saura deal dinmu kuma” ya fada yana tanqwashe qafafunsa

“Eheennn” ta fada tana gyada kai

“Yadda kika tsara komai muka bi kuma aka kai ga cimma gaci,wannan ya burge alhaji sosai,ya sanya masa interest akanki,ya nema alfarma a wajena ta ki karba aiki a company dinsa dake shirin durqushewa a yanzu yake fafutukar tayar dashi,zaki tsaya tare da yaronsa kuyi aiki tare alfarma ce ya roqeni,nayi rushing wajen accepting,saboda girma da kimarsa,na kuma san cewa bani da matsala ta wajenki” ya qarashe maganar yana ritsata da idanu.

              Kaf! Ya gama daureta da dukka wata jijiya dake jikinta,ya salam ya alhadi,me yasa yaya muhyi zaiyi mata haka?,yafi kowa saninta ciki da bai,yasan a yanzun bata da wani sauran buri,bata buqatar aiki ko kadan,infact fita ma waje tun bayan kammala karatunta bata dameta ba,tana ma daya daga cikin abubuwan data sanyasu a jerin ababen takura a wajenta,wannan ya sanya ma hatta da key din motarta ta dade da bada ajiyarsa,ta yaya zata iya fita kullum da sunan aiki?,ta kuma tunkari wata matsala,matsalarma ta company?.

             Yadda ta gaza cewa komai haka falon yayi Shuru,hakanan kuma daga abba har yaa muhyi basu janye idanuwansu daga kanta ba,abinda ya sake mata nauyi kenan,ta kasa motsawa bare ta amsa.

“Mama na” muryar abbanta ta yanke shirun dake wanzuwa a falon,ta daga kai a hankali

“Na’am abba”

“An baki dama kije kiyi tunani”

“To abba,na gode” ta fada har ranta tana jin dadi, atleast ta kubuta daga titsiyen da yaa muhyi yakeson yi mata

“Karki manta da istikhara” abba ya fada sanda take dab da fita a falon,kai ta jinjina

“In sha Allah” tanajin a ranta ta yaya zata sakeyin sake?,ta yaya zata manta da istikhara?, bayan taga illar hakan?,har abada ba zata sake yankewa kanta hukunci kai tsaye ba,bata fatan ruwan daya shanyeta a baya a yanzun ya sake mamayarta.

              Sanda ta isko falon tuni afifa ta gama cin nata takeaway din,hira ma sukeyi da farheen,dukansu suka bita da kallo,yanayinta ya sauya ba kamar yadda tabar wajen ba a dazun,saidai ba wanda yace komai da ita,ta dora aleena saman cinyar farheen ta zauna itama,dai dai sanda baaba rabi ta fito

“Tunda kuka shigo nake cigiyarki,akace kin shiga wajen alhaji” ta fada cikin fara’a da nuna kulawa,hannu tasa ta zame veil din kanta baya tana lumshe ido,cikin jikinta tana jin wata gajiya da weakness yana ratsata,wanda tasan bata komai bace ta zancan yaa muhyi ne,sumarta me santsi dake gaban goshinta ta fito sosai

“Zan samu coffee?” Kai ta jinjina da sauri

“Ai bana zama babu shi saboda ke” daga haka ta juya cikin kitchen din a gaggauce.

          Bata ce da kowa komai ba,sai suma basu tambayeta ba,tana da zurfin ciki sãahar din sosai,ba komai take iya bayaninsa kota fadi ba

“Ki rakani gida mana kiyimin weekend din nan a can?” Farheen ta fada tana duban sãahar,saita bude idanunta tana kallon farheen,cikin zuciyarta tana jin ta gamsu ta bita din,to amma kuma kamar ta kusanta kanta ne da yaa muhyi da take fatan a kwanakin da abba yace taje tayi tunani daga nan har abada zancan da yazo mata dashi yabi ruwa,bata da wani interest akan aikin ko kadan,amma kuma qin amincewarta tamkar ta damtsi qasa ta watsawa idanun yaa muhyi din

“Zaki din?,khalipha nata kewarki” ta fada cikin kwnatar da murya,khalipha shine makami daya da zatayi amfani dashi ta amintar da ita ta bita gidan,Allah ya jarabceta da son yara matuqa da gaske.

           Sai da baaba rabi ta kawo mata coffee din taji tana cewa ta hada mata kayanta kala biyu sannan ta fahimci ta aminta zata din

“Miskili kafi mahaukaci ban haushi” anty farheen ta fada a ranta tana murmushi,a hakanma ita daya ke iyawa da sãahar,tana da dadin zama idan ka karanceta,idan ba haka ba kuma ba zaka taba jin dadin zama da ita ba,infact ma ba zaka taba fahimtar tata ba.

         Tana rungume da aleena a seat din baya,yaa muhyi da anty farheen na gaba suna hirarsu,komai suke tattaunawa tana jinsu amma bata sanya musu baki ba,ta dade tana kwatanta cewa inama ace dukkan maza nagartattu ne kamar yayun nata,lallai inda addini ya halasta aure tsakanin dan uwa da dan uwa,ta tabbatar cewa bata da sauran matsala a rayuwarta.

             Tafiyar da bata wuce minti talatin da biyar ba suka isa unguwar,ya muhyi dake tuqi a nutse ya saka signal,ya shiga layin da ya shiga hannun damansa a hankali. A qofar wani qawataccen gida dake dauke da manyan katangu ya tsaya,a ido kawai idan ka kalleshi zaka san cewa akwai sukunin rayuwa me yawa tattare da me gidan. Ya danna hon,cikin sakannin da basu wuce biyar ba aka wangale masa qofar,daya daga cikin masu tsaron qofar gidan mutum biyu ya rusuna cikin girmamawa har zuwa sanda motar ta sulala ta shige ciki kai tsaye zuwa yalwataccen parking lot na gidan.

              Ko kafin yakai ga tsaida motar su fita masu aikin farheen su biyu sun iso,daya nanny dinsu khalipha ce daya kuma tana kula da tsaftace sashen farheen,don sam bata yarda koda wasa me aiki ta karbi wani abu da ya shafi hidimar mai gidanta ba komai qanqantarta.

             Cikin girmamawa suke yiwa sãahar barka da zuwa,don dukkaninsu bawai baquwar su bace,kai tsaye ma za’a kirata da ‘yar gida,saboda zaman shekaru kusan biyu da tayi dasu,har yanzu kuma bata rufa wata biyu bata zo tayi kwana daya ko biyu ba,daki ne da ita na musamman a gidan.

            Baraka ta miqa hannu zata karba aleena sãahar ta hanata,tadai barta da hand bag da kuma qaramar luggage dinta ta wuce ciki rungume da yarinyar dake lafe a qirjinta,don tuni tayi bacci. Bata sauketa ko ina ba sai data dangana da ita har gadonta dake dakin farheen,ta fito Parlor ta samu farheen din na gayawa baraka ta tsaftace dakin da sãahar din zata sauka,duk da fes yake,sannan kuma lubabatu ta tambayi abinda sãahar din zataci a dora mata. Kai sãahar ta girgiza,cikin lallausar muryar ta take fadin

“don’t mind,I can take care of myself”

“Really?,kinsan dole a kula da amanar auta” farheen ta fada cikin sigar tsokana kamar yadda ta saba takan zolayeta haka time to time. Dole wani murmushin ya sake kubcewa sãahar,ta motsa bakinta kadan,farheen na daya daga cikin mutane masu matuqar muhimmanci a rayuwarta,ba zata iya fadin adadin yadda taji dadin zama da ita ba a shekarun baya,har yanzun kuma tana jin dadin kasancewa da ita,shi yasa duk duniya ba inda take iya tafiya ta kwana idan na nan gidan ba.

        Cikin qanqanin lokaci baraka ta gama kintsa dakin ta kuma shirya mata kayanta, bath set dinta ta fitar,ta zare kayan jikinya ta daura babban lallausan farin towel,ta zare farin ribbom din kanta,yalwataccen gashinta mai tsaho da sulbi ya baje saman lallausar farar fatar jikinta,hakan ya qarawa fuskarta wani kyau da haiba,tamkar ire iren jaruman indai mata,kai tsaye ta dauki kayan wankanta tana takawa a nutsenta zuwa toilet,ta hada ruwan wanka me dumi sosai ta shige,tayi wanka sosai da ruwan ya ratsata, idanunta a lumshe cikin shower din tana qoqarin tattara dukka wasu qananun damuwoyi da taci karo dasu a wunin yau tana watsar dasu daya bayan daya,so takeyi yau din tayi bacci me kyau ta kuma huta sosai,daga qarshe ta dauraye jikinta dake faman fidda qamshin shower gel dinta mai matuqar kyau da tsada,ta nade fatarta daketa sulbi cikin towel ta fito bayan ta sanya pad,kasancewar tana fashin sallah ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *