Tafiyar Mu Hausa Novels

Tafiyar Mu Chapter 5

(5)

Kwanaki suka shuɗe suka dawo satittika, satittikan suma haka suka wuce suka dawo watanni. A hankali duk wasu alamu da zasu nuna ta taɓa rayuwa dashi suka fara ɓacewa. Bata sake ganin fuskarshi ba tun ranar da aka rufeshi da bargonta, sai dai a kullum yana cikin mafarkanta.

 Rayuwarta ta fara dawowa kamar da a lokacin da take budurwa a gidansu, zata ci zata sha amma tana cikin gida bata fita ko’ina. Komai ya dawo normal amma banda ita, domin kuwa bata jin kanta kamar yanda ta saba. Ya tafi ya barta da wani gurbi a zuciyarta da babu mai iya cikawa sai shi, Hafiz ɗinta.

 Tunaninshi yana bibiyarta a kowanne lokaci kamar baƙon da ba’a gayyaceshi ba. A ko’ina take sannan ko menene take aikatawa yana nan maƙale a zuciyarta da kuma kwakwalwarta wanda hakan yasa bata iya maida dukkan hankalinta akan abun da take yi.

 Da dare in ta kwanta idanunta zasu bushe daga ƙin yin bacci, zata shafe awanni tana tuno rayuwarsu wanda su suke gaskata mata cewa ta taɓa sanin shi. Da wannan tunanin zata tashi ta ɗauro alwala ta fara sallah tana nema mishi gafara a gurin ubangiji har kwakwalwarta ta nemi hutun dole ta sanyata baccin da bata yi niyya ba.

********

  Salima ta haihu ta samu ɗa namiji wanda yau ake bikin suna amma Juwairiyya bata da niyyar zuwa. Tana kwance a ɗakinta ta jiyo sallamar yaro a tsakar gidansu, bata amsa ba don ba aikinta bane. Tunani take yi da Hafiz yana da rai da yanzu tana can gidan sunan tana shige da fice a matsayinta na matar abokin mijin mai jegon.

 Tana jin immediate ƙanwarta Sumayya ta amsa sallamar daga can bakin kitchen sannan ta bi yaron da tambayar dalilin shigowarshi.

“Wai ana sallama da Juwairiyya a waje.”

“Je ka tambaya in ji waye.”

Jimawa kaɗan yaron ya dawo ya ce,

“Wai in ji Hussaini ne wanda suka gama makaranta tare.”

 Juwairiyya da take ɗaki ta ja wata doguwar tsaki tana jin kamar ta fita waje ta gaurawa Hussaini mari. Yaron ya rainata sosai yanda bata tsammani, zata iya tunawa shine mutum na farko da ya taɓa nuna yana sonta bayan ta gama takaba. Tsabar rashin kunyarshi har cikin gidansu ya shigo ya samu Mamanta wai ya zo yana sonta ta bashi izinin zuwa hira. Duk ransu ya ɓaci amma Mama bata nuna mishi a fuska ba ƙarshe tace ya je ya ƙara haƙuri sai mutuwar ta fita a ranta.

“Wallahi in ya sake taka cikin gidan nan da sunan wai yana sona sai na sa yaran unguwa sun mishi wanka da kwata. Don uwarshi ni sa’arshi ce? Yaro ƙarami da shi wataƙila ma na fishi shine zai zo mini da maganar aure? To don ubanshi an ce mishi neman mijin auren nake? Kuma in zan yi auren in rasa waye zan aura sai kucakin yaro mara sana’a irinshi?”

“Ina tunanin ya ɗauka a littafin Ruwan Zuma kuke, a ciki ne matar ƴar shekara arba’in (40) ta auri saurayi ɗan shekara ashirin da tara (29), suka yi ta soyewa wallahi har abin kunya yake bani.” Faɗin Surayya ƙanwarta ta biyu wacce kwata-kwata shekarunta sha huɗu ne (14).

Maman su da tayi kasaƙe tana kallonsu sai yanzu ta yi niyyar magana, da Surayya ta fara wacce sai da ta gama maganan sannan ta gane ta tafka uban kuskure.

“Wato har yanzu baki daina karance-karancen littafin Hausan ba? Kenan duk nasiha da kuma faɗan da nake miki baki ɗauka ba? Laifina ne da na sayi waya na baki, ki tashi ki ɗauko mini wayar daga yau babu ke babu riƙeta har sai kin gama secondary school an kusa miki aure. Ina ce dama auren kike so shiyasa kike karatun soyayya? To ko yanzu wani ya zo yace yana sonki aurar da ke zan yi sai ki je can kiyi karatun da tushe.”

 Kuka Surayya ta saka ta fara bawa Mamansu haƙuri amma ta kafe, ƙarshe ta zare mata ido ta ce in ta sake magana sai ta mata duka. Da haka ta tashi tana kuka ta tafi ɗakin baccinsu don ɗauko wayar tata.

Nan ido ya dawo kan Juwairiyya wacce ta wani gefen ta ji daɗin karɓe wayar Surayya, domin watarana har ƙarfe biyun dare take kaiwa tana karatun novels wanda ta tabbatar ciki har da na batsa tunda ya zama tamkar ruwan dare a gurin marubutan online ɗin. Ta wani gefe kuma ta ji tausayinta domin in bata manta ba itama a baya Mama ta sha kwace nata tana ɓoyewa in tayi laifin da ya kai a hukuntata da haka, tana tunawa in aka kwace sai ta ji kamar ranta aka karɓe ta yi kuka har ta bonu kafin ta haƙura.

“Ke kuma kika zauna kina ta ashariya a gabana ko? Mutum daga cewa yana sonki sai ki ce zaki tara yara su mishi wanka da kwata? Ke ƴar daba ce ko ƴar iskar unguwa?”

Shiru Juwairiyya ta yi kanta a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta.

“Ina tambayarki kina mini shiru.”

“A’a Mama.”

“To wallahi akul in ji ko baƙar magana kin mishi. Ki nemi yanda zaku rabu lafiya kar in kuskura in ji abun da zai ɓata mini rai, ba tarbiyyar da na baku ba kenan. Allah Ya gani nayi iya bakin ƙoƙarina kuma ina kan yi akan tarbiyarku har kika yi aure ana yabonki a cikin unguwar nan cewa kin fi sauran ƴan matan kamun kai. Baku tashi da uba ba amma ba’a zageku a dalilin rashin gurbinshi a rayuwarku ba. Kar ki ga kuma kin taɓa aure kiyi tunanin zaki ci gashin kanki a cikin gidan nan, as far as ni nake ciyar da ke, kike kuma zaune a gidana ni ce mai last say babu abun da ya canja.”

Sumayya mai bin Juwairiyya, tana da shekara sha takwas wacce a yanzu ta gama secondary school tana gefe tana jinsu, ita dama ba kasafai ake mata faɗa ba domin tana kiyayewa sannan kaff yaran Mama ita ce shiru-shiru. Autansu Walid kuma shine yake son gagaran Mamarsu, shekararshi yanzu goma sha ɗaya amma yawo ya saka a gaba sannan baya son karatu. Kuma duk dukan da zata mishi ba zai hana gobe ya ƙara abun da aka dakeshi a kai ba. Wannan kenan.

“Adda Juwai wai Hussaini yana waje.” Faɗin Sumayya daga can bakin ƙofar ɗakinsu.

“A faɗa mishi na samu mijin aure har na ƙarɓi sadaki.” Ta bata amsa a numfashi ɗaya.

Dariya Sumayya tayi sannan ta wuce ta faɗawa yaron saƙon yayartata shi kuma ya fita don isar da nashi. Sai dai bai jima ba ya dawo.

“Wai don Allah magana ɗaya zai faɗa mata ta yi haƙuri ta fito.”

Tun kafin Sumayya ta shigo Juwairiyya ta miƙe a hanzarce domin a yau tana son ta kawo ƙarshen rainin hankalin Hussaini, ta gane in ba ita ta sameshi suka yi magana ba zai yi wuya ya haƙura ya barta.

A bakin ƙofa taci karo da ƙanwar tata,

“Ohh ashe kin jiyo mu.”

“In ba saitashi nayi akan hanya ba yanzu zai buɗewa sauran ƙofar zuwa su dameni. Ba aure ne a gabana ba, kwata-kwata ma yaushe Hafiz ya rasu? Yanzu ne ma yake cikin wata na shida shine zai zo mini da maganar banza?”

“Kiyi haƙuri, wasu mutanen basu da lissafi. Amma dai ki bishi a hankali kar yi abun da Mama zata miki faɗa.”

Bata amsa ba ta wuce waje tana rangaji domin ramewar da ta yi har yanzu bata maida jikinta ba. A ƙofar gida ta samu Hussaini jingine da gate ɗin gidan nasu yayi wata tsayuwa tamkar ciwon baya, shi ala Allah yayi hakan ne don ya burge Juwairiyya.

“Gimbiya kuma tauraruwa cikin mata. Nagode kwarai da kika bani wannan damar na ga kyakkyawar fuskarki.”

“Shi ɗan aikan bai faɗa maka cewa na karɓi sadakin wani ba? Ko ƙarya kayi da ka aiko cewa magana ɗaya zaka faɗa mini mu rabu?”

“Ashsha! Kin san Bahaushe ya ce matar mutum kabarinshi. Sau nawa ana taruwa don ɗaura aure amma ki ga an watse saboda Allah

bai yi zasu zauna a rufin auratayya ba?”

Wani malolon baƙin ciki ne ta ji ya zo ya tokare mata a maƙoshinta, so take ta kurma mishi ashar ta zagi uwarshi da ubanshi ta yanda ko labarinta ake yi zai bar gurin amma Mama ta mata katanga da aikata hakan. Don haka kamar zata yi kuka ta ce,

“Hussaini ina ganin girmanka ina kuma tuna zaman da muka yi a school cikin aminci, don Allah ina roƙanka kar ka ɓata wannan zumuncin. Ba aure bane a gabana ba, in ma auren ne ba zan aureka ba dalilin na ƙarbi sadakin wani. Neman aure a cikin wani auren haramun ne kar ka saɓawa Allah don son zuciyarka. Na barka lafiya.” Ta juya da niyyar shiga gida ya sha gabanta ya haɗe hannayensa guri guda.

“Wallahi Juwairiyya tun muna makaranta nake sonki amma nasan kin fi ƙarfina shiyasa ban taɓa nuna miki ba, yanzu kuma da kike bazawara ni kuma nake saurayi na san akwai chance ɗin kasancewarmu tare kuma wallahi ba zan damu da maganar mutane cewa na auri bazawara ba. Ki ceceni ki karɓi soyayyata don wallahi na jima da sonki a birnin zuciyata.”

Yanzu kam ji take yi kamar ta rufeshi da duka har sai ya daina motsi, wani wawan kallo mai cike da tsana take bin shi dashi. A yanzu bata damu da duk hukuncin da Mama zata ɗauka a kanta ba, sai ta zage Hussaini zagin da ba’a taɓa mishi irinshi ba, zagin da ko a hanya ya ganta zai canja akalarshi.

Ta buɗi baki da niyyar fara azalzalarshi motar Muhammad ta yi parking a ƙofar gidansu. Da ita da Hussaini tsayawa suka yi suna ganin lokacin da Muhammad ya buɗe marfin motarshi ya kwalawa wasu yara kira dake kan yashi suna wasa, da gudu suka iso gurinshi fuskar nan tashi kamar kullum a turnuƙe amma ba shine damuwarsu ba, ɗari biyu-biyu da zai basu in sun gama mishi aikin ne damuwarsu. Suka gaisheshi bai amsa ba, dama sun san za’a rina wai an saci zanin mai hauka.

Nuni ya musu da booth ɗinshi ba tare da ya buɗe bakinshi ba, babu wani dogon bayani suka nufi bayan motar suka buɗe kana suka fara fito da kayan abincin da suke ciki suna shigarwa cikin gidansu Juwairiyya, ba kaya ne masu yawa ba illa ƙananun buhun shinfakar dafawa da ta tuwo, kayan haɗa shayi, sabulun wanka da wanki da kuma manja, mangyaɗa da maggi.

Duk abun nan da ake yi Juwairiyya da Hussaini suna kallonsu amma shi ko kallo basu isheshi ba. Wani tunani Juwairiyya ta yi wanda yasa wani murmushi ya wanzu a fuskarta kana ta dubi Hussaini da ɗan damuwa a fuskarta ta ce,

“Ga wanda na karɓi sadakin nashi, don Allah in ya fito ka nuna mishi gaisuwan rasuwa kawai ka zo ka mini, ka ganshi ƙaton nan wallahi in ranshi ya ɓaci dukanka zai yi.”

Muƙut Hussaini ya haɗiyi yawu kana ya dubi yanda Muhammad yake ƙoƙarin fita daga mota girman jikinshi na bashi wahala. Bayan ya fito ya miƙawa yaran ɗari biyu-biyu kamar kullum suka tafi murna fal a fuskarsu, abun ka da yaro, basu san cewa shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma ba.

Ganin ya nufosu fuska a tamke yasa Hussaini ya mata sallama ya tafi ba tare da ya tsaya sun gaisa ba, shi har cikin ranshi ya yarda Muhammad zai mishi duka, ina shi ina faɗa da wannan basamuden?

“I see har kin fara tara zawarawa a ƙofar gidanku.” Ya faɗa bayan ya iso gabanta.

“Idan wannan ne ya kawoka kayi saurin tafiya don baka da amsa.”

“Salima ta haihu.”

“Ina sane.”

“Yau suna bikin suna.”

“Shima na sani.”

“Ta haifi yaro ɗa namiji.”

“Haka na ji.” Da haka ta juya da niyyar komawa cikin gida amma ta tsinkayi muryarshi yana cewa,

“Na saka mishi sunan abokina Muhammad Hafiz.” Da haka shima ya juya ya koma motarshi don dama ya gaji da tsayuwar.

Juwairiyya daskarewa ta yi a gurin tana jin kanta kamar ba’a duniyar take ba, wai da gaske Muhammad ya raɗawa ɗanshi sunan masoyinta Hafiz? Nan da nan sai ta ji kunya ya rufeta domin bata kyautata mishi duk da ƙoƙarin da yake yi a kanta. Sai dai tana juyawa ta ga yayi reverse ya tafi.

Tun bayan rasuwar Hafiz ya koyi yi mata magana, ya mata ta’aziyya wanda daga shi har matarshi a gidan karɓan gaisuwar suke yini tun safe har dare har aka yi sadakan bakwai. Sannan ta samu labarin da Muhammad ɗin ya ga gawar abokin nashi kuka yake cur-cur da idanunshi har aka yi tunanin ƙin zuwa dashi maƙabarta don kar ya ga sa’ilin da ake saka abokin nashi a cikin ƙasa ya rasa hankalinshi. Sai dai babu wanda ya isa ya hanashi, ya je kuma tare da shi aka bunneshi bakinshi bai bar motsi ba har aka dawo yana mishi addu’a.

Juwairiyya ta san Muhammad ba wani mai wadata bane amma ya ɗaurawa kanshi wahalanta, domin kuwa kowanne wata sai ya yi mata shopping na kayan masarufi daidai ƙarfinshi ya kawo mata ya kuma gaisheta. Daga nan ba zata sake ganinshi ba sai wani watan, abun mamaki shine ko sau ɗaya bata taɓa mishi godiya ba balle ta nuna a fuska cewa abun da yake mata yana taimakonta kwarai da gaske.

Mahaifiyarta ‘Mama’ Nurse ce wanda kullum tana fita aiki da safe zuwa ƙarfe ɗayan rana, duk nauyin gidan na ci, sha, sutura, rashin lafiya da kuma abun da ya shafi makarantar ƙannenta a kanta yake babu mai taimaka mata. A hakan kuma ga kakarsu  wato mahaifiyar Mama da kullum ake kashe kuɗi a kanta dalilin rashin lafiyan da tsufa ke kawoshi. Don haka wannan ɗawainiyan da Muhammad yake musu ba ƙaramin taimakon Mama yayi wajen samun sauƙin hidimar gidan ba. Kullum tana faɗawa Juwairiyya ta miƙa godiyarta amma bata da masaniyar ko sau ɗaya ita Juwairiyyan bata taɓa isarwa ba.

Dalili kuwa shine, meyasa tun lokacin da Hafiz yake da rai baya mata magana ko amsa gaisuwarta sai da ya rasu zai nuna ya fi kowa tausayinta? Kuma bata nemi taimakonshi ba, jira take yi ta dawo hayyacinta ta fara sana’a don ta taya Mama kula da gidan. Aure kuma babu shi a babinta domin karatu take so ta fara a Gombe State University tun da daga unguwarsu Arawa sai makarantar ko da ƙafa zata dinga zuwa tana dawowa.

Da wannan tunanin ta shige cikin gida ta samu Sumayya na tattara kayan tana kaiwa falon Mama wanda a da shine na Babansu.

“Wannan bawan Allah bai manta da zaman amanan da yayi da abokinshi ba, Allah Ya biyashi da mafificin alkhairi.” Faɗin Sumayya a lokacin da Juwairiyya ta tsuguna zata ware kayan shayin ta kai ɗakinsu domin Mama tace ta dinga ɗauka.

 Shiru ta yi amma a zuciyarta ta amsa, har ta miƙe da niyyar tafiya sai ta samu kanta da tsayawa ta dubi Sumayya da murmushi a fuskarta ta ce,

“Hafiz ɗina dai ya yiwa takwara Sumayya, wallahi ko yanzu ban gama gaskatawa, ji nake yi kamar wasa yake mini.”

“Allahu Akbar!” Sumayya ta kama bakinta har tana jin hawaye na taruwa a idanunta.

Itama Juwairiyya hawayen ne ya taru a nata idaniyar har suka kwaranyo kan ƙuncinta, saurin sharesu ta yi kana ta nufi ɗakin nasu don adana abubuwan hannunta.

Minti goma da haka Sumayya ta gama girkin rana, hakan kuma yayi daidai da dawowar Mama daga aiki wacce ta kwaso gajiya ta nemi guri ta zauna a falonta aka kawo mata abinci.

Tana cin abinci Juwairiyya ta shigo mata sannu da dawowa Mama ta amsa tana tambayarta ko ta ci nata.

“Mama sai anjima zan ci bana jin yunwa yanzu.”

“Adda Juwai ki bata labarin abun alkhairin da ya faru.” Faɗin Sumayya da take kwance akan kujera hannunta riƙe da wayarta tana chat da saurayinta da aka musu baiko.

“Me za’a faɗa mini?” Mama ta kasa haƙura ta tambaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

“Muhammad ne ya sakawa ɗanshi sunan marigayi Hafiz.”

“Allahu Akbar. Allah Sarki, mutumin nan ba ƙaramin so yake yiwa abokinshi ba. Allah Ya rayashi Ya sa ya ɗauko halin takwaranshi kyawawa, shi kuma Allah Ya gafarta mishi.”

“Ameen.” Duk suka amsa cikin sanyin jiki.

“Sai ki shirya ki je ki dubota da jaririn ki samu abun da zaki kai musu. Ƴan’uwan marigayin sun sani kuwa?”

“Bana tunanin sun sani don da ƙannenshi sun kirani sun faɗa mini ko Ummarshi.”

“To ki kirasu ki sanar dasu, zai yi wuya su ji basu faɗa miki ba kam.” Faɗin Mama domin ta san an yi zaman lafiya da mutunta juna tsakanin dangin Hafiz da ɗiyarta, wanda har yanzu suna zuwa dubata in an kwana biyu.

Juwairiyya bata jima a gurin Mama ba ta koma ɗaki dama can ne gurin zamanta kamar matar Liman. Tana zaune tana tunanin me ya kamata ta yiwa Salima na fitan biƙi Sumayya ta shigo ta sameta.

“Yanzu ke kina ganin me zan saya mata? Na san kaya kam iyayenta sun loda mata don masu kuɗi ne, haka sauran ƴan’uwa da abokan arziki. Ina son in yimata kyautan da zata yi amfani dashi kuma zata ji daɗinshi.”

Shiru Sumayya ta yi, can kuma fuskarta ta yalwatu da murmushi ta ce,

“Babu kyautan da zaki mata yanzu ta ji daɗin shi irin Turaren wuta da kuma Humrah. Kuma shine zata yi amfani dashi ba zata kyautar ko ta sayar ba, kin san shi baya yiwa mace yawa sai dai ya mata kaɗan.”

“Amma kin kawo shawara wallahi. Yanzu ni da nake tunanin zuwa gobe ta yaya zan samu turaren wutan a ƙanƙanin lokaci haka?”

“Ga Dukhan By Ain a Instagram 08088929221. A Abuja take kuma ana yabon turarenta sosai, don ina ganin yanda ake bada positive reviews a Highlights ɗinta. Kwanaki da aka yi auren ƙawata Salma a gurinta duk aka sayi su Turaren wutan, su Kulacca da Humrah. Bari in binciko miki page ɗin don ina following ɗinta, kuma na faɗawa Mama a gurinta za’a haɗa mini turarukana.”

Juwairiyya ta harari Sumayya cikin wasa tana cewa,

“Yaran zamani baku da kunya wallahi. Yanzu baki ji kunyata ba?”

“Ki ji Adda Juwai da wata magana, akan turaren wuta fa muka yi magana ba maganin mata ba.” Sumayya ta amsa tana danna wayarta tana dariya.

“Shi ɗin ma ai zaki iya, yaran yanzu menene baku sani ba.”

“Ni kam mu bar maganan nan kina sakani kunya, yauwa gata nan, ki duba daga ganin turarukan an san na ƴan gayu ne sannan na amare don kowanne ta bashi sunan da ya dace dashi.”

“Su kuma uwaren gidan fa?”

“Suma zasu iya saya su saje cikin amaren.”

Murmushi kawai Juwairiyya ta yi kana ta karɓi wayar daga hannun Sumayya ta fara ganin pictures ɗin da sunansu da kuma yanda za’ayi amfani dasu. Nan Sumayya ta dawo ta bayanta ta fara mata bayani dalla-dalla.

 “Akwai ‘Irresistible’ wanda Sandal flakes ne ita mai sayarwan ta canja mishi suna. Ga kuma ‘Coated Kajiji’ wanda ta haɗa da secret ingredients ɗinta. Ga kuma ‘Blissful’ gab-gab, wanda ta ce it’s best used on clothes, home & body because it’s very strong & last long. Wa zata bari wannan ya wuceta? Not me!”

“Ga kuma ‘Soothing sandal’ shi kuma Sandal Coconut ne, ta ce it has a very soothing scent, best use in ana neman sudden ƙamshi. Musamman in maigida ya kiraki a waya wai gashi yana zuwa da baƙi.”

“Wai dama haka kike da surutu Sumayya?” Faɗin Juwairiyya tana duban ƙanwar tata.

“Adda Juwai ke kam ki saurara mana. Yauwa, sannan akwai ‘Down to Earth’ wato Halut kenan, sai ‘Malaak’ Halut-hawi mix ne, can be used for clothes, body and home. ‘Field of dreams’ daga jin sunan kin san yafi daɗi a saka in ana ruwan sama, wai niƙeƙƙen kajiji ne mai sa nishaɗi.

‘Habiby mix’ kuma signature ɗinta kenan, 3 sticks ta haɗa for clothes, body and home. Gasu nan dai birjik sai wanda kika zaɓa.”

“Ni babu abun da yafi burgeni irin ‘Earthly wonders’ saboda sau nawa ina ɗaukan kaya amma sai in ji yana warin damshi? Shi kuma wardrobe ball ne da zaki jefa a cikin wardrobe yana saka ƙamshi sannan yana ɗauke warin damshin.” (Mum Fateey ma tayi order)

“Gurin Khumrah kuma akwai Khalty (normal Black Khumrah), Fatum (normal White Khumrah),

Liquid Gold (oudbased white khumrah). Sai Maya (Oudbased black Khumrah),

Royalty in a bottle (musk based Khumrah), sai uwarsu ubansu wato ‘Ain’s Signature’ Bodymilk ne na jiki, ana iya sawa a ruwan wanka, da ke da bathroom ɗinki duk ku ɗau Ƙamshi. Yana hana warin zufa. Kuma both maza da mata can use it. It has the nicest scent.”

“Tana da Kulaccam, ‘Malika’ (Lotion Kulaccam) ‘Ahlaam’ (Vaseline kulaccam).”

“Yanda kika zauna kina zayyane turarukan nan kamar haɗin gwiwa aka yi ke da ita. Yanzu dai zan saya mata kala huɗu ki tayani zaɓe.”

Da haka suka darje suka zaɓi turaren wuta kala huɗu, khumrah kala biyu da kuma Kulaccam kala biyu. Sai da suka zaba suka kira numbernta 08088929221, daga nan ta basu account number Juwairiyya ta tura kuɗi, kana ta musu alƙawarin gobe da hantsi kayansu zai iso su karɓa a tasha.

“Ya kika ji muryarta?” Faɗin Sumayya tana murmshi.

“Me muryan ya yi?”

“Wallahi kalan ƴan gayu.”

Dariya Juwairiyya ta yi kana ta gyaɗa kanta ta ce,

“Ba laifi tana da zaƙin murya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *