Tsutsar nama Book 2 Hausa Novel

Tsutsarnama Part 2 Book 2

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐

…….Hankalinsu ya tashi matuƙa da ganin yanayin Samraah a asibiti. Yayinda Dr Su’adah ta sake ruɗar da su da bayanin haɗarin da Samraah ke ciki. Tare da tabbatar musu idan ba’a sadata da ƙwararren likitansu dake birnin tarayya Abuja da zama ba za’a iya rasata, dan zuciyarta na gab da bugawa saboda yanda jininta yay tsananin hawa sama. Sam babu wanda yay musu akan yarda da hakan. Sai dai sun nema alfarmar Hayatu akan Musaddiq zai bisu zuwa Abuja ɗin. Rasa abincewa Hayatu yayi, dan ya tabbatar tafiya da Musaddiq bazai yiwu ba. Amma rashin mafita sai ya amsa musu da to su jira suji daga likitar yaya za’ai tafiyar. Sun gamsu da hakan, dan haka ya lallaɓa ya koma gefe ya sake samun Dr Su’adah akan ta taimakesa ya fita a tarkon mutanen nan, dan yana da dalilin da yasa baya so kowa ya bisu. Ita dai Dr Su’adah bata san ainahin mike faruwa ba, dan Hayatu ɗan uwanta ne na jini, abinda ya gaya mata kuma bashi ne ainahin alaƙar dake tsakanin Samraah da Maash ba. Dan haka babu musu ta taimaka masan. Ita ce ta tsara su Kawu Musa ta hanyar da dole suka gamsu akan za’a fara tafiya da Samraah ta jirgi ne, masu son bin bayanta sai suyi hakuri subi a baya ta mota nan da kwana biyu haka. Haka kawai sai hankalin Musaddiq ya kasa kwanciya, sai dai babu yanda zai yi tunda su Kawu Musa sun yarda. Haka dai yana ji yana gani aka shiga yima Samraah shirye-shirye dan wai za’a wuce da ita ne a jirgin ƙarfe takwas na dare…

        ★✓★✓★✓★✓

    ABUJA AIRPORT
  
     Ƙarfe tara dai-dai jirgin daya taso daga Kano zuwa Abuja ya sauka a filin jirgin na birnin tarayya. Maash da tawagarsa na ɗaya daga cikin passinges ɗin wannan jirgi. Hakama Samraah da likitan da take tare da ita suna a jirgin. Sai dai a tsarin tafiyar sam babu abinda ya alaƙantasu da Maash. Hasalima shi yana a private section ne. Yayinda ita da likita suke a sashen kowa da kowa, koda yake ita bama ta a hayyacinta balle ta fahimta. Dan an shigo da ita ne a yanayin wadda take bisa umarnin likita da zataje gani a Anuja. Ko’a airport ɗin ma tuni Maash ya shige ɗaya daga cikin tawagar jerin motocin da suka zo ɗaukarsu. Yayinda ita kuma ambulance ta ɗauketa ta wani babban private asibiti da ake matuƙar ji da shi anan birnin Abuja ɗin..

KANO
 
       Anan Kano an wuce da Samraah an bar danginta da jimamami. Musamman ma Musaddiq da sam zuciyarsa ta kasa zama waje ɗaya. Kai shi tunma jiya hankalinsa a tashe yake da wannan aure. Sai dai babu yanda ya iya tunda su Kawu Musa sun bama mijin da suka aura matan yarda ɗari bisa ɗari. An ƙarasa dai wannan dare cike da jajantama juna bisa ga halin da Samraah ɗin ke a ciki. Daga ƙarshe dai a washe gari kowa ya shirya ya kama gabansa saboda wayar da akai da mijin na Samraah akan jikin da sauƙi suka ganta ta hanyar video call. Taro dai ya tashi an bar Mom da mijinta sai auta da Musaddiq da Hafizzullah kawai a gidan dan su Baby basa nan. Sai a washe gari suka dawo gidan. Hafizzullah ma dai shirin komawa makaranta yayi, duk da yaso zuwa wajen Samraah Musaddiq ya lallashesa akan yayi haƙuri tunda an kusa musu hutu, yanzu zuwa Abuja dubata ba nashi bane, shima ɗin da akace zai je su Kawu since ya dakata kada mijin yaga kamar ana nuna ya gaza ne. Badan yaso ba ya shirya ya wuce zuciyarsa duk babu daɗi. Dan duk wani masoyin Samraah ɗin zuciyarsa a ƙuntace take da abinda ya faru akan wannan aure da kuma halin ciwo da take a ciki yanzu. Dan idan ta shine ma baza’a ɗaura mata aure da wani da bata sani ba tun farko. Amma dai su Kawu Musa sun bada goyon baya babu abinda su zasu iya musamman ma shi dake amsa sunan ƙani a wajenta. Amma zai cigaba da binta da addu’a kamar yanda Yaya Musaddiq yace yayi. Musaddiq ɗin ne ya kaisa har Katsina da kansa. Ya sake masa nasiha sosai sannan ya juyo gida…..

          MANSOOR

     Kowa ka kalla a ahalin gidan hankalinsa a tashe yake. Dan kusan duk manyan suna a sashen su Mansoor da aketa ƙoƙarin gaggaɓe ƙofar ɗakinsa. Yau kwanaki uku kenan yana a kulle a ciki yaƙi ya fito. Lallashin duniya da roƙo yay biris da kowa. Tun ana ɗaukar abin nasa a fushi na ɗan lokaci har abin ya wuce makaɗi da rawa, dan zuwa yau ko motsinsa an bar ji a ɗakin, dole fa aka nemo mai gyara domin gaggaɓe ƙofar. Kuka sosai Mamynsu keyi tun jiya, dan ita kanta har sai da hawan jininta ya motsa. A yanzu haka a nane take da ƙofar ji take mai aikin ma kamar baya sauri ne.
        Ana ɓalle ƙofar mafi yawansu duk suka afka ciki, tsakanin Attahir da Mamy har turereniyar rige-rigen isa ake kan Mansoor dake kwance samɓal a ƙasa babu alamar rai a tare da shi. A tare suka ɗagosa, sai dai me yaraf ya koma alamar babu rai. Wani mahaukacin ƙara Mamy ta fasa mai firgitarwa, tamkar ƙiftawar ido sai gata ƙasa wanwar itama ta sume musu. Sake harmutsewa ɗakin yayi, dole aka kwashesu zuwa asibiti kamar yanda wasu suka bada shawara…..

        
       ABUJA

    Kaifin hasken rana da nake ji mai ƙarfi a saman fatar idanuna ya sani motsasu a hankali. Sosai sun min nauyi, dan illahirin jijiyoyinsu a takure suke waje guda. Hannuna da nake ji kamar an ɗaure nai ƙoƙarin motsawa domin kaiwa saman idanun, sai naji an sake damƙesa da ƙyau, tare da jin saukar wata murya cikin kunnena. “Bi a hankali akwai abu a hannunki. Sannu kin farka bari nai kiran likita”.
        Sosai naji gabana ta faɗi. A can ƙasan zuciyata na ayyana (likita) a fili kam babu abinda nake iya motsawa a jikina saboda illahirinsa yay min nauyi. Amma sai na shiga ƙoƙarin buɗe idanuna. Dishi-dishi nake gani, sai dai hakan bai hanasu sauka akan mutumin daya shigo bayansa da wasu mata guda biyu ba saboda yanda hayaniyar maganar da suke taja hankalina. Duk da ba ihu suke ba ko fidda sautin maganar tasu da ƙarfi. Ƙarasa buɗe idanun nayi da ƙyar sakamakon jin inuwar mutum a kaina. Wani irin faɗuwar gaba naji ta sake riskata, dan kuwa tabbas a asibiti nake, dan shigar wanda ke kaina tsaye kawai ta tabbatar min da shi ɗin likita ne. Sannu suka shiga jeramin, sai dai na gagara amsawa kowa a cikinsu, na dai zuba musu ido ne kawai ina binsu da kallon ƙurilla. Ko tambayoyin da likitan ke jeromin game da jikina na gagara amsa masa ko ɗaya. Fahimtar kamar a rikice nake da yanda nake bin ɗakin da kallo ya sakashi ƙyaleni shima. Sai cikin matan da ya shigo da su ne ke ƙoƙarin cire min allurar drip dake a hannuna. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya sake juyowa ya fuskanceni. Cikin harshen turanci ya furta. “I understand that you are confused. This is a hospital, you are under the care of a doctor. Alhamdulillah, your body is very easy.”
        A hankali na kai hannuna saman kaina da har yanzu nake jinsa da nauyi, kafin na sake ɗagowa na dubesu murya a karye na ce, “Who brought me? Which hospital is this? Since when have I been?”.
    Da alama yanda na jera tambayoyin sun bashi mamaki, dan sai da ya ɗan waro idanunsa, sai kuma yay murmushi da faɗin, “Oh relax! You will all know. Now they will help you to fix your body, eat something and I will come back and answer your questions”. Ya ƙare maganar yana nuna min Nurses ɗin. Fuska na ɗan ɓata, sai dai bance komai ba. Shi kuma ya juya ya fita da Nurse ɗaya ya barni da biyu. Da farko naso naƙi yarda, dan nafi son na fara sanin a ina nake. Sai dai yanda suka nuna damuwarsu da tabbatar min ƙin yardata zai iya taɓa aikinsu yasa na amince. Amma zuciyata taƙi gajiya da daina kai-kawon ganin ɗakin da naken matsayin wai asibiti. Saboda sam bai kama da asibiti ba fa, duk da gado da tarkacen ɗakin duk irin na asibitin ne, sai dai da gani na musamman ne su. Ga television ga freight, sannan toilet da suka kamani suka kaini a cikin ɗakin dai yake shima sam bai kama da asibi ba. Ciwon da jikina kemin ya sakani bin umarninsu nayi wanka da ruwan da suka tara min mai ɗumi. Nako ji daɗin wankan, na saka doguwar riga irin wadda na cire pitch color da alama ta asibitin ce. Bata sauka min har ƙasa can ba sosai, amma dai banyi tsirara ba. Gashi tana da faɗi babu wani takura. Alwala na ɗauro na daddafa bango na fito. Da sauri suka iso gareni suka taimaka min muka ƙarasa, a saman lallausar sofa ɗin ɗakin nace su zaunar dani, sannan na buƙaci hijjab na salla da sallaya. Sai dai da alama babu, sai ɗaya ce tace bari ta sanarma doctor a kawo min. Komai bance ba, na jingina kaina da kujerar na lumshe idanuna.
Bata fi mintuna biyar ba sai gata ta dawo da sallaya da sabon hijjab a ledarsa. Ita ta ciromin shi, sannan ta shinfiɗa min sallayar. Har ƙasa hijjab ɗin ya sauka min sosai dan ko ƙafafuna ba’a gani, hakan yasa naji nutsuwa dan dama rigar bai gama sauka ba. Juyawa nai na tambayesa “What day is today?”. A tare suka amsa min da, “Today is Monday”.
      (Litinin) na maimaita a zuciyata. A zahiri kam sai na sake tambayarsu alƙibla. Ɗayarce mai kama da musulma duk da shigarta zata iya saka kace ba musulmar bace amma akwai ƙaton tabon salla a goshinta ta nuna min tare da bayani, bance komai ba na kabbara sallata. Tun inayi a tsaye har hakan ya nema gagara. Dan dole na koma a zaune kasancewar duk sallolin da nasan suna kaina sai da na ramasu na kwanaki biyun nan da bana a hayyacina………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *