Amatulmalik Chapter 5

Amatulmaleek Chapter 2

This entry is part 2 of 6 in the series Amatulmalik na Mamuhgee

2

Nisan dayake tsakanin Asmau da abeeda Bai taba rage kauna ko girman  junansu ba a zuciyarsu,

Babu dawowar da Abeeda zatai Nigeria Bata zo har kauye ta ziyarci Yar uwar tata ba Dan haka kusan kaf dangin mijin asmaun Babu Wanda baisan girman alaqarta da kaunar Dake tsakaninta da Abeeda ba,

Duk wata sutura da abincin datake ci Daya bambamta Dana Yan kauyen duka abeeda ce ta tsaya Mata akansu Koda Bata qasa ko tana qasar duk lokaci bayan lokaci sai an aikowa da Asmau abinci da suturar datake sakawa.

Acan dangin mahaifiyar abeeda Babu Wanda Bai gama sanin matsayin kaunar Dake tsakaninsu ba Dan haka Babu Wanda yayi yunkurin hanawa saima tsayuwa da sukai akan inganta rayuwar asmaun duk da tana kauye Dan haka itama asmaun Bata da tamkarsu.

Nisansu Bai hanasu zama abokan sirrin juna ba Dan kuwa Babu matsalar Asmau da abeeda Bata saniba kamar yanda asmaun Babu damuwar abeeda da Bata saniba.,

Rashin samun haihuwar Asmau da wuri yasaka Abeeda ta samu Samar dauko asmaun ta tafi da ita ganin Wani likita a porthcrt,

Da farko hankalin Asmau Bai tashi ba da rashin haihuwarta ba Amma ganin yanda abeeda ta damu ta kwallafa Rai Akai sai hankalinta ya tashi Wanda yasaka dole aka tsaya aka ringa yawon asibiti da asmaun.

Kamar yanda hausawa sukace ita dai kaddara yashi ce ko an dunkulata Bata dunquluwa, Abeeda ta tsaya da karfi da dukiyarta an nemawa Asmau lafiya Bata samu nutsuwa da Kwanciyar hankaliba Saida Asmau ta wayi gari ta samu ciki a jikinta.

Cikin Asmau nada wata biyu Aka kulla Auren Abeeda da Wani ‘dan babban Aminin mahaifinta Aleeyu Muh’d Talba Wanda dagashi har ita bawai suna son juna bane Amma dayake Auren na connection ne Basu damu ba.

Auren Abeeda da Aleeyu aure ne na fitowar Rabon haihuwa kawai Wanda Allah ya kaddaro a tsakaninsu sbd Auren da wata uku Allah ya karbi ransa sanadin jinyar ciwon cikin kwana Daya kacal.

Bayan rasuwarsa ranar da Abeeda ta fita takaba ranar Asmau ta haifi AmatulMaleek wadda taci sunan Abeeda Amma suke kiranta da AmatulMaleek din sbd shine sunan da mahaifinta yafiso din Dan haka take amsa sunan AmatulMaleek din Amma a rubuce Abeeda AmatulMaleek ne sunanta.

Abeeda Bata samu zuwa haihuwar AmatulMaleek ba sbd itama tana fama da tsohon ciki me tsananin wahala Wanda ya Sakata shiga ciwo sosai.

Asmau duk da jegonta bata zaunaba haka taxo ta zauna jinyar abeeda harta samu sauki itama ta qarasa watanninta ta haifi ‘ya mace itama take aka Saka mata sunan ASMAU Amma ana kiranta da Husnah.

A ranar da akai sunan Husnah a ranar aka daura Auren Abeeda da ASHRAF MUH’D TALBA ‘dan uwan Aleeyu Wanda suke Yan biyu batareda sun taba ganin juna ba Amma hakanan zuciyar abeeda tafi kamuwa da son Ash Talba akan Aleeyu sedai Kuma halin Aleeyu ya bambamta sosai da ASH Dan haka zamanta dashi yafara Bata wuya ta bangarora da dama.

Wanna shine damuwar data fara Sako Auren Abeeda a gaba sedai Kuma Asmau ta tsaya sosai gurin Bata qwarin gwiwa Dan ta fuskanci aurenta ta tsaya ta riqe mijinta da kyau.

ASH baida raayin Auren mace biyu Bai taba shaawan Hakan ba Dan haka a zuciya da gangar jikinsa ya amshi abeeda dari bisa dari sedai rashin fuskantar halin juna da sanin juna yanda ya kamata yake azabtar da Auren nasu Amma Kuma kasancewar sunada ilimi dukkaninsu ya Saka Basu taba nunawa junansu gajiya ko gazawa da zamanba bare juna ba,

Matsalar datafi quntatar da Auren nasu shine rashin iya kulawa da soyayyar Auren Abeeda wadda Sam ta kasa yanda zata iya shiga zuciyarsa ta mallakesa ta hanyar kauna ko soyayyarta.

A idanuwansa tana iya hango tsananin girmamawa ne kawai yake mata Babu wata soyayyarta bayan Hakan Dan haka ta dage sosai dan ganin ta mallakarwa kanta zuciyarsa da Babu kowa a cikinta.

A duniya da yawa basusan ba Ash ne mahaifin Husnah ba kaman yanda Babu Wanda yasan matar Ash din bashine ya fara aurentaba.

Zamansu me dadi da Kwanciyar hankali da wayewa suke rayuwar aurensu Dan haka ya dauketa daga kasar suka tafiyarsu inda yake rasuwarsa tareda mahaifiyarsa da kanwarsu qwalli Daya wadda ta kasance tana gida bayan auranta Daya mutu ta fito da saurayin ‘danta Wanda ya girma sosai Yana karatu Shima.

Duk Nisan da Asmau tayi da Abeeda Hakan Bai Hana ASH yiwa Asmau farin sani ba sbd shaquwa da kusancinsu hakama da kansa ya fahimci irin girman junansu a zuciyarsu Dan haka yake respecting Asmau sosai tareda Mai gidanta Wanda yaso ya taimakawa sosai Amma Babah din yaqi yarda da Hakan Dan haka sai kawai mutunci da kusanci suka ya shiga tsakaninsu duk da Hakan ya taimakawa babah din sosai.

Bayan shekaru sunja sosai a rayuwar kowannensu Abeeda tayi nasarar shiga zuciyar ASH sedai batada tabbacin ta mamaye zuciyar ne duka Amma ko a iya inda ta samu din a zuciyarsa tanada tabbacin babu Wani guri da wata zata samu shiga sbd ita kanta gurin data samu a zuciyar tasa sai data share shekaru a cikin auren kafin ta samu wannan gurin a zuciyarsa Dan haka ta tabbatarda zuciyar ASH ba guri me saukin samu ga kowace mace ba.

Baida raayin mata kaman yanda baida Wani raayi ko time na abubuwan dasuka danganci soyayya bayan ta matarsa Abeeda wadda yake ganin iya sonta da ita din ta ishesa a rayuwarsa Bata buqatan Qari sbd baida Wani gurin bawa wata macen a rayuwarsa kwata kwata.

Rayuwar Abeeda ta sauya ne ta tashi daga arzikin mahaifinta ta koma arzikin mijinta Wanda ya take ya rufe arzikin mahaifinta datake ganin yanada ta gado,

A familyn ASH kusan shi kadaice me irin wannan arzikin duk da mahaifiyarsu ma nada arzikin Amma ba kamar na mahaifinsu da suka gada ba.

ASH da Aleeyu mahaifinsu daban Wanda bayan rasuwarsa mahaifiyarsu tayi aure ta haifi Aysha wadda ita mahaifinta daban dasu Amma dai mahaifiyar tasu Daya ce.

Sune masu arziki sosai sbd mahaifinsu shine me arziki sabanin Aysha da nata mahaifin baida Wani abun bayan rufin asiri.

Da wannan qyashi da Jin zafin Aysha ta tashi a cikinsu har Allah yasa Akai mata aure ta haihu ta fito daganan aurenta uku tana fitowa karshe dai ta hakura da auren sbd takasa samun masu iri arzikin ‘dan uwanta ASH dashi kadaine yanzu ya rage mata hakama ummansu ta rasu Dan haka ta tattara itada ‘danta NAUFAL ta suka dawo karkashin ASH tamkar shine Uba mahaifin Naufal duk Wani gata da Jin dadi Babu abinda basa samu a gidan karshe dai kusan gidan ya dawo hannun mom Aysha kaman yanda ake kiranta da girma yazo mata sbd ta girma Abeeda sosai ba laifi Dan haka kusan gidan idan aka cire Mai girma me gidan the grt ASH TALBA mom Aysha itace me fada a ji Dan kusan kamar matsayinsu Daya agidan Ash itada abeeda.

Rayuwar mom Aysha a cikinsu ya Saka duk yanda kusancin Asmau da abeeda yake yafara raguwa sbd mom Aysha Asmau ce macen datake Jin har cikin zuciyarta Bata kaunar kusantuwarta da Yan ahalin gidan Dan haka tsauri da kaidojin mom Aysha akan Asmau yasa taji Bata shaawan zuwa gidan Abeeda Koda suna gari Dan haka da wannan kusancinsu yafara raguwa dakuma manyanci Daya zo musu dukkaninsu.

Bayan haihuwar husnah Abeeda Bata sake haihuwa ba Saida manyanci yaxo musu ta haifi ‘da namiji Wanda ya kasance a gurin ASH TALBA shi kadaine jininsa Amma Kuma a zuciyarsa haydar din da Husnah matsayinsu Daya Dan kuwa ita kanta Husnah duk da ta girma batasan ba ASH TALBA mahaifin Daya haifetaba.

AmatulMaleek tanada shekaru goma sha uku a duniya maamah ta sake haihuwar ta haifi qaninta Abdulhameed Wanda harya girma baisan mahaifinsa ba tinda kafin sunansa Babah ya rasu yabarsu cikin halin qaqanikayi.

Rayuwarsu ta zama me Wani irin babban gibine da basusan tayaya zamu cikesaba ko samun me cike musu shi,

Qunci da wahala da yunwa da azaba tareda hantara suke rayuwa acikinsa har Abdulhameed ya girma yayi wayo,

Tunda tagama primary karatunta ya tsaya,

Abdulhameed kuwa karfi da yaji ya zama kamar almajiri sbd ko suturar da zai Saka basuda ita sai abinda Allah ya Basu kawai suke Samu.

A gidan kaf Babu Wanda yake iya Basu abincim da zasuci sbd kowa ta kansa yakeyi kowa na fama da rashi.

Madame abeeda wadda a yanxu matsayinsu da sunansu ya zarce na Baya sbd matsayin da ASH yake dashi a gurin Al’ummar Dake tsananin son ya tsaya musu a matsayin gwamnan jahar Amma baida raayin siyasa duk da Hakan jamaa sosai sukeyinsa Dan haka kusan Babu Wanda baisan the grt ASH TALBA ba.

Rayuwarsa data iyalansa kwata kwata baa qasar yake yinta ba sai dai yakan Fi iyalan nasa zuwa Dan haka jamaa sukeyinsa sbd taimakon dayake bayarwa kaman baisan zafin dukiyar ba Dan haka manya da yawa mutanensa ne hakama talakawan ma mutanensa ne hakama masu kudin Dan haka kowa yinsa yakeyi duk da da yawa baisanma sunayi ba Amma Kam sosai aketa Daman gwagwarmaya da rigimar shi akeso amma Sam Baya raayi.

Ta bangaren matarsa Abeeda kuwa wadda duniya ke kira da Madame abeeda Talba tini rayuwarta data ‘yayanta ta zama abin kallo daga nesa sbd tsaron da ake Basu bana wasa bane sbd ASH Bai hadasu da komai nasa ba Dan haka a yanzu tsakaninta da maamah aike ne kawai Shima sai can idan lokaci me tsayi yaja Dan haka itama maaman ta hakura ta rungumi marayun ‘yayanta.

*****Bayan rasuwar Babah da shekara biyu kawu bello ya aure Maamah din wadda bayan wahala da ukubar data ringa sha a hannun kishiyoyi Babu abinda suka Qaru dashi itada ‘yayanta

Ahakan suka ringa Shan kuncin rayuwa har kawun ya gaji ya saketa sbd yace bazai iyaba lalurar tai masa yawa Dan haka dai anan cikin gidan Akai auren anan Akai sakin taci gaba da gwagwarmaya itada ‘yayanta Wanda tanaji tana Gani Abdulhameed yakoma almajiri AmatulMaleek kuwa haka take zaman gidan Bata taba barinta fita ba Koda zuwa cikin gidan sbd yanda gidan yake sake zama hadari sosai ga duk Yan matan gidan da Yara qanana ma Dake tasowa duk da yawa sun lalace a tsakaninsu batareda sanin iyayensu ba.

AmatulMaleek tinda tafara wayo rayuwarta ta zama tamkar kurma sbd rashin magana tinda basuda abin magantuwa akansa Dan bayan tarin kunci Babu komai a rayuwarsu Dan haka ta taso a miskilar gaske Wanda Hakan yafiwa maamah dadi da farin ciki sbd kullum kukan maamah a gaban Allah shine yanda zata bawa ‘yayanta kariya daga masifar gidan musamman AmatulMaleek datake mace.

AMATULMALEEK

Regular 700

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

Series Navigation<< Amatulmaleek Chapter 1Amatulmaleek Chapter 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *