Furar Danko Hausa Novels

Furar Danko Chapter 1

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*

_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

……..Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ƙyaƙƴƙyawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ɗaukar idanun duk wanda ya kalleta ta miƙe a hankali tana ɗan wani ɓata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ɗin da ya kasance fari tas, an ɗan faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ɗan yana a saman kanta ya matuƙar ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuƙar ɗauki ƙafar tata musamman da wandon ya kasance baije ƙasa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarƙar ƙafarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa ɗar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya ƙara saka fuskarta kwarjini da bayyana ƙyawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara’a, sannan babu kwalliya ko ɗigo idan ka cire ɗan lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laɓɓanta. A kallo ɗaya zaka ɗauka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da ƙabilar kudancin ƙasar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin ƙasar musamman inda addinin Muslunci keda ƙarfi irin su kano.

          A hankali taja ƙaramin tsaki dai-dai tana miƙewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones ɗin kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta ɓare ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaɗan harara, tun ɗazun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag ɗinta ta fisga ta ɗora a kafaɗa ɗaya sannan ta ɗauka Apple laptop ɗin ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miƙe tai ficewarta cikin takunta na ƴammata marasa jin magana..

          Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu ƴammatan kuwa kishine ya lulluɓesu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baƙar fata haihuwar Africa sai dai ɗabi’u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen ƙamshi da duk wanda ke a kusa da ita kaɗan dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips ɗinta a taunar chewing gum ɗin bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau ɗaya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH…

       *_Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu ƙamshi_ ƙyaƙyƙyawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huɗu a duniya. Itace ɗiya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma’il l. Jiƙamshi. Babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin *_Jiƙamshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma’il Ibrahim Jiƙamshi da Kawunta Yousuf Ibrahim Jiƙamshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanɗararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu ƙamshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle ɗin su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita ɗin lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da ƙyar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba ɗaya karatunta a ƙasar ƙetare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a ɓangaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu ƙamshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai ɗan uban waye a kuɗi ko nasabar zuri’a baka ishi Lulu ƙamshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaɗi tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an ɗan taɓa samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuɓuta da ƙyar.

     Wannan itace Mawaddat Isma’il Jiƙamshi (Lulu ƙamshi) a taƙaice.

         Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauƙi da yanga. Wannan ita kaɗai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi ɗaga murya wajen faɗin,

       _“K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!”._

    Ɓuɗaɗɗiyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima ɗin wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da ƙoƙarin cimmata ƴammatan da duk suka juya garesa suka shiga taɓe baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai ƙoƙarin cimmata da yake yi dai-dai tana ƙoƙarin isa ga inda motocin ɗaukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa.

      Fuska ya marairaice yana mai haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faɗin, “Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu ɗaya ne Please. Address ko phone number abeg you”.

           Cike da yauƙi da yanga ta furta, “A matsayinka na wa?”.

Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, “Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama ƙasashen Africa ya sansh…..”

     “Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face ɗin nan naka zubin alakoro da mari stupid”. Ta faɗa cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaƙa domin tarihi haka yay tsaye ƙiƙam yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko’a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai ɗauki wani mataki…..

       “Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu ɗin nan”.

   Wani ɗan ƙyaƙyƙyawan yaro dake saman jibgegiyar mota baƙa siɗik ya faɗa yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a ƙasa da keypad waya ƙirar Nokia a hanunsa ya ɗago a hankali tamkar mai ciwon wuya………✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *