Gishrin Zaman Duniya Chapter

Gishirin Zaman Duniya Chapter 6

This entry is part 6 of 6 in the series Gishirin Zaman Duniya by Badi'at Ibrahim

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

ina mik’a sak’on gaisuwar ban girma ga masoyan littafinnan, kuma aminaina na arxiki.

Maman Yaseer Kina k’arfafamin guiwata Hajiyata.

Anty Yabi yunusa Kin bani gudunmawa ta musamman ina jinjinar ban girma.

oum shuraim 1 Dear ke tawace har abada

oum shuraim 2 Godiya ta musamman gareki

ummu safais ina jin dad’in comments

Aisha Auwal godiya nake yi

Ban mance da ‘yan amanata ba

kabo dota.

khadija Beebee

Ta marad’i

Atitin mama

Anty faty Rayyana

Mrs Abdul

Anty Baraka

Mmn Nour

ummi Barwa

Soopy ta yanzu 😀

Da duk masoyan wannan littafin da basu ji sunayensu ba, kuyi hakuri abunne da yawa.

Bazan manta da iyayen gidana ba

ANTY HADIZA BARA’U GIDAN IKO.

FAUZIYYA D SULAIMAN

SUMAYYA ABDULK’ADIR TAKORI

ina mik’a gaisuwata gareku

Kashi na 1

Babi na 11~12

Goggo Hansatu ce ta dafa baya na. ta ce da ni.

“Haba Sadiya. kar ki bari shaid’an ya yi miki wasa da zuchiya. ki dena kuka, kar ki ji kinyi dana sani akan kasancewarki a wannan k’auyan. iliminki zai fi amfani a wannan k’auyan. ba mu san mai Allah ya ke nufi da had’a wannan Auran ba. k’ila ta dalilinki Gishirin zaman duniya ya yawaitu a wannan karkarar. Aliyu kuma kisan yanda za ki yi, ki ja hankalinshi gareki. nasan kinyi girman da kin riga da kin san ta kan duniya. ki yi amfani da iliminki. ki dena duban shi a matsayin k’aninki, tunda k’addarar Aure ta maida ki k’asanshi. dole shine jagoranki, kuma shugaba a gareki, kiyi k’ok’arin k’irk’irarma kanki farin ciki da kwanciyar hankali, Aliyu masanin addinine bazai salwantar da hakkin daya rataya a kanshi ba. ki gode ma Allah mijinki zai dawo a matsayin malamin Addinine. Ba jahili kamar Asabe uwarshi ba.”

baki Goggo Hansatu ta dinga ba ni. tare da yi mun musalan matan da su ka sha gwagwarmaya kuma daga baya su ka samu nasara. Allah ya d’aukaka su, har tauraruwarsu ta haska duniya ta san da zamansu. da misalan matsalolin da mata su ke fuskanta a gidajen Aure. har da ma gararin da yaran jahilar uwa su ke fa’dawa, da kuma shafarsu da jahilcin uwar ta su ya ke yi. tad’aura da cewa.

“Shi rayuwar Aure. Sanyi da taushi ce. Ba zafi da Haushi ba. shi zaman Aure hak’uri da juriya ne. Ba rashin ha’kuri da mita bane. Miji d’an lallashine, ba abun tsokanar fad’a bane. Sadiya in ki ka bi da Aliyu ta hanyar daya dace. sai ya zame mijin alkhairin da ba lallai samarin ki na maraya su zame miki ba. sha’anin zamatakewar Aure ya tab’arb’are ba irin na mu na da bane. amma da yawan tashin hankula da fitintunun da su ke tashi a gidan Aure. kaso mafi tsoka matsalar daga matan mu na hausawa ne.  Bance mazan basu da laifi ba, dan sun d’auki kaso mafi rinjaye, tunda sun fimu kaifi hankali da tunani. ke kam kina da ilimin da ni kaina ina alfahari da kasantuwarki d’iyata. Sadiya kar ki yi saken da Aliyu zai soma amsar Budurcin waccan yarinyar da zai Aura. domun shi daren Farko na musamman ne, a rayuwa. duk sanda zai tuno da macen daya soma jin d’uminta a rayuwarshi. toh ke zai tuno. kuma za ki samu Babban matsayi na musamman a matsayinki na uwar gidan Aliyu. Ban sanki da taurin kai da raini ba.”

wunin ranar kab Goggo Hansatu ta na yi mun jawabai ne na yanda zan gyara rayuwar Aure na. kuma na ji dadin hakan matuk’a. Hakan ya wawuce mun kaso mafi tsoka na damuwar dake addabata.

washe gari da safe.

bayan na yi wanka. ina sanye cikin atampar soso. jikin atamfar bak’ine, sai manyan fulawa jajaye da aka k’awata atampar da shi. kwalliya na yi me kyau. Goggo Hansatu tace.

“Sadiya na ji dad’in yanda jawabai na su ka shige ki. shine gudummawata ta bikin ki da ban bayar ba. kuma na ji dad’in yanda naga annuri a fuskarki, kuma kin saki jikinki sosai, tare da rungume k’addararki hannu bibbiyu, ina fata da rok’on Allah yasa hakan ya zame miki alkhairin duniya da lahira, ki samo tikitin shiga aljannah a hannun Aliyu.”

murmushi kawai na yi mata. tabbas na d’auki dakon duk shawarwarinta domun babu na yadawa. amma a xuchiyata akwai wani miki da bansan yaushe zai warke ba na soyayyar Ahmad da yai ma rayuwata raunin da bana jin akwai namijin da zai iya warkar mun da wannan raunin. k’addarata kam na amsheta. domun bazanyi jayayya da buwayar Allah ba.

Goggo hakane. in sha Allah za ku same ni mai biyayya a gareku. kuma zan hau kan tsanin da kika d’aura ni akai har zuwa Aljanna. zanje in.Gaishe da su Goggo ne. sai in shiga wajan Bilkisu za ta sanar da ni dokokin da aka gindayawa surukan gidannan, kamar yanda kawu ya umarceni.

” Toh Sadiya. sai kin dawo.

fita na yi. tare da bin Goggonnina d’aya bayan d’aya ina gaidasu. gabaki d’aya a tsarge na ke. dan surukan gidan sai wani tab’e baki su ke yi da ganina. wasu ma har barin abinda su ke gudanarwa su ke yi, su shige d’aki. dan karma mu gaisa. ga habaici da Hasiya matar Dauda take yi mun a duk sanda zamu had’u kan cewar na gama tsofewa a birni ba miji, daga k’arshe an kawo ni k’auye. na Auri k’anin bayana, abun kunya. data gama sai ta sa dariya. yauma hakanne ya faru. dana wuce ta, sai na yi murmushi a raina na ce.

jahilci ciwo wanda ya fi hauka. da sallama na shiga d’akin Bilkisu, bayan ta ba ni izini. zama na yi a saman kujerarta muka gaisa.

d’akinta ba k’azanta sam a gyare yake tsab ta kunna turare d’an tsinke ya na ta ‘kamshi. d’iyarta tana zaune a kan po ta na bayan gida. ga kuma wainar gero a hannunta ta na ci abunta kuma da hanun hagu.

Bilkisu ki hanata cin abinci da hannun hagu. sannan bai dace mutum na kan bayan gida kuma ya na cin abinci ba. d’an murmushi Bilkisu tayi tace.

“lahh ai ni bansan hagu da damar yara ba.”

da mamaki na bita da kallo. tana k’ok’arin k’arb’e wainar hannun d’iyar tata. murmushi kawai na yi na ce.

Dama kawu ne ya turo ni wajanki, ki sanar dani dokokin da ke kan surukan gidannan. dan in san su.

tace

“Toh doka dai ta farko shine. Kawu matan shi basa d’aura sanwa. duk wata suruka a gidannan za ta zuba mishi abinci a kai mishi amma sau d’aya a rana. toh sai mu ka yi tsarin da mu ka kasafta kan mu gida uku. wasu da safe, wasu da rana, wasu da daddare, mu ke kaiwa. kuma babu fashi. komai ciwo. na biyu kuma shine za ki dinga yin girki da surukarki wato uwar mijinki. safe. rana,dare. shima ba fashi.

da abincin gandu ake yi. bayan wani rikici daya afku a tsakaninmu. shine kawu ya saka wannan dokar, cewar kowa ta yi girkinta, shine ko wacce mace ta samu sauk’in rayuwa. Abu na gaba shine.

wajibine ki bi matan yayun mijinki, duk safiya ku gaisa. akwai fitowa hira tsakar gida, wanda ya ke wajibi ne. dan sada zumunci. dole yaranmu su kasance a tare. domun akwai d’akin yara mata. da d’akin yara maza da aka ware suna kwana, dan shak’uwa. kuma baki da wani iko a matsayinki na matar k’ane sai abinda matan yayu suka zartar akan kowa ma.

wannan su ne dokokin wannan gida.

murmushi na yi mai k’unshe da ma’anoni da dama wanda na barsu a raina. godiya na yi mata ta fito, zuwa d’akina.

Goggo Asabe ce a gaban mai gari su na k’arashe zancan su.

“ni hak’urin da na ke ta nema ka yi mun shine. Abar yaronnan ya Auri Khadija. kar a tauye musu hakkinsu. Aure kuma, ai ba Aliyu bane ya ga mace ya ce ya na so ba. ni ma kaina fa na fi son Khadija.” mai gari ya ce.

“maganar gaskiya Asabe. ba na jin zan iya sauka akan wagga baka. Aure ko? na amince ya Aure ta. amma in ya Saki waccan ‘yar barikin daya Auro. in kuwa ba haka ba. wallahi sai dai a hak’ura da Auran. dama yarinya ta na da manema. sabida al’kawarin da ke kanmu ne yasa ban ba ma kowa dama ba”

Goggo Asabe gabaki d’aya kanta ya chaza sosai. kuma ta san Aliyu zai shiga tashin hankali mai yawa in aka ce yau ya wayi gari ya bar Khadija. cikin sauke murya tace.

“Toh ranka shi dad’e, ni zan koma. duk abunda mu ka yanke da ‘yan uwa na, da shi kanshi k’usar yak’in in ya dawo, za ka ji a bakin mai dambu. Maganar saki daya dawo, kafinma ya shiga d’akinta ta juya mishi kai, zan sa ya sauwak’e mata. Ka sauraremu.” ( hmm maman Yaseer ke fa kinji)

“Toh madallah ina saurarenki Asabe, yaro Allah ya dawo dashi lafiya.”

sallama ta yi mishi ta fito.

ta na tafe ta na ta faman tunani akan wannan lamari da komai ya ke son lalace mata.

“duk Bala ne ya ja mun wannan tsiyar. ya k’ak’aba ma yaro Auran dole, yaro da wacce ya ke so shi kuma. ni wannan kafiya ta me gari ta ishe ni wallahi”

duk maganganun nan ta na yin su ne, ita kad’ai a hanya. har ta iso gida. ( Oum Shuraim tace, “kya ji da shi dai )

Sadiya

wunin wannan ranar cikin nasiha Goggo Hansatu ta k’arar mana da yinin.

washe gari ma ta d’aura daga inda ta tsaya. na saki jiki na sosai babu laifi.

kullum da safe ina zuwa gaishe da Goggonnina da kawu da matan shi. haka duk wacce na had’u da ita a tsakar gida, ni dai zan gaishe su. wasu su amsa, wasu su yi kunnen uwar shegu da ni. Ina jiyo su, suna hirar tsakar gida tare da shewa. Amma ban tab’a ko lek’awa ba.

Allah ya kawo mu ranar Dawowar Aliyu. Goggo Hansatu tun safe ta yi ma matan gida sallama ta kama hanyarta. Ni kuwa a ranar na ci kuka har sai da idanuna su ka yi wani mummunan kumburi. ji na ke yi tamkar in sa hannu na a ka, in rintima uban ihu, ko zan ji sanyi a raina. Wani irin suya zuchiyata take yi mun.

bayan na share hawayena  ne, sai na mik’e na duba agogo na ‘karfe biyu da rabi na rana.

kitchen na shiga, na kunna ritso na d’aura ruwan tea. ina tsaye ya tafasa. a cup na zuba wanda zan sha. sauran kuma na zuba a tea flase na barshi a kitchen d’in.

dai dai  zan fito daga kitchen kenan. sai ga Fatima yayar.Aliyu ta shigo da sallamarta. cikin fara’a na tarbeta. amma kuma sai na ga ta turb’une fuskarta. babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata. na ce da ita.

mu shiga daga ciki mana Fatima, naga kin tsaya daga nesa. Bud’ar bakinta tace.

“Fatima kuma, hala kin manta ni Yar Mijinki ce?  Koda ma, mun yi tunanin ganin rashin d’a’a a wajan ‘yar boko. dama d’abi’arku ce rashin kunya da fitsara.  Goggo na jiranki ki fito za mu je d’auko  K’anina mijinki kuma a filin jirgi. cijewa na yi. tare da bin bayan Fatima da kallo wacce ta fice fuu. murmushin ba’kin ciki kawai na yi.

kaya na sake daga atamfa zuwa material mai taushi. d’inkin riga da siket wanda ya kama ni ya zauna.daram a jikina. kirjina ya d’an fito ta saman rigar har ana ganin tsagun daya raba mamana biyu. gyalen kayan babba ne sosai kuma yana da kauri. yane shi na yi a kaina tare da kama shi da pin. turare na fesa mai cool k’amshi. takalmi na mai tudu na d’auko na sa kalar kaya na. ni kaina da na dubi madubi nasan na yi kyau sosai. amma gabana sai fad’uwa ya ke yi. ga maganar da Fatima ta caka mun yana ta dukan zuchiyata, ga ganawa da Aliyu da zanyi. Shima sai fad’ar mun da gaba ya ke yi. Da hanzari na fito tare da sa ma k’ofata kwad’o na rufe ruf.

A babban tsakar gidan na samu su Goggo. ita da kawu, da Anas, da Fatima, Sai wata yarinya fara da ban santaba. Amma kuma naga ta na watsomun wani mugun kallo.

“Ku yi hak’uri in na b’ata muku lokaci.”

Kawune kawai ya ce.

“Babu komai Sadiya. Khadija ma yanzu ta zo.”

kallon ta na yi muka had’a idanu. harara ta sakar mun. Sai yanxu na gane ta. Itace yarinyar da Aliyu zai Aura.

ta b’angaren khadija kuma gabanta ne ya fad’i da ganin kyau da tsarin sura irinna Sadiya. ta ke ta shiga kokawa da hawayen da ya ke shirin zubowa ya kunyatata. jikinta ne yayi sanyi, tare da karayar zuchiya..Amma kuma data tuno Aliyu na dawowa zai sake ta. kafin ma ya shiga d’akinta. sai ta yi dariyar mugunta  kawai.

Sadiya

D’unguma mu ka yi baki d’ayan mu. mu ka hau Babur dan zuwa kan iyakar da za mu samu motar zuwa sokoto.

na sha wuya a wannan hanya. mai tarin kwazazzabai. kafin mu sauka na yi wurjanjan dani.

kai tsaye mu ka shiga motar cikin garin Sokoton Shehu.

ina zaune a mota, gabana sai fad’uwa ya ke yi. kuma ni kaina ina jima kaina kunyar in kalli Aliyu A matsayin mijina. Babba dani. Sannan ina fargabar irin amsar da zai yi mun. da ma irin Rayuwar da za mu shinfid’a, mai dad’i ko akasinta.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

    _Mrs Bukhari_

 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*

     _Miss Hajo_

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

Kashi na 1

Babi na 13~14

Sultan Abbakar the 3rd international airport Sokoto State

A tsaye ya ke. ya na ciniki da masu taxi d’in da ke sana’a a bakin get d’in Airport d’in.

dogone sosai, ba irin tsayinnan mara tsari ba. domun faffad’an kakkauran k’irjinshi ya k’awata tsayin  na shi. Kasancewar su Goggo Asabe irin dogayen sakkwatawanne sosai. domun mahaifin Sadiya har wani doron tsayi ya ajjiye. Haka mahaifinsu mai Hula ya ke. shi tsabar tsayinshi ya wuce misali.

Aliyu Fari ne sosai, irin fararen fatarmu na nan gida Najeria. shi ba siriri bane. kuma ba mai k’iba bane. sai dai ya na da zubin gwarazan maza. kan shi babu tarin suma. saisayan aski ne a kanshi. siririyar fuskarshi na d’auke da k’asumba da gemu me yawa, wanda kuma ya ke shan gyara, da taza a kai a kai. yana da hanci daidai misali amma ba kamar biro ba. bakinshi kuma, madaidaicine. idanunshi su na da tudu ta saman idanun na shi. sai dai a cikin asalin idanun. ba su da girma sosai. gira da gashin idanunshi, irinna mazan mu na gida Najeria. wato dai dai da misali.

Sanye ya ke cikin Farar jallabiyya mai kyau sosai. kanshi sanye da hular ustazan larabawa wacce ake kifata  a kai. a gida najeria ma ana samun irenta da mata ke yi mata sak’ar lilo. sannan ana samun ‘yan kantinsu a kasuwa.

k’afarshi na sanye da wasu slipas mai yatsa, bak’i. wanda ya fito da zara zaran siraran yatsunshi masu kyau.

yana rataye da k’atuwar jakar baya. da akwatinshi trolla, sai kuma jakar tsaraba.

bayan sun gama daidaitawa da mai taxi zai shiga kenan, motar su su Goggo Asabe ta iso.

Sadiya

jiki a mace na sakko daga cikin motar nan. zuba ma wanda Goggo Asabe ta kira da K’usar yak’i, idanu na yi. ina karantar shi da kyau. daga sama zuwa k’asa na kalleshi. gaskiya in na kushe Aliyu ban kyauta ba. domun yanda na karanceshi, matashine mai hankali da nutsuwa. kuma bashi da k’azanta a ido dana ganshi.

murmushi ya yi yace.

“Ahhh Baba ashe kunsan zan dawo ne?

da sauri ya iso wajan Kawu ya rungumshi. suna murnar ganin junansu. Goggo Asabe tace.

“wato kawunka ya debe ma hankali, wajanshi ma ka soma zuwa ko?

murmushi mai burgewa Aliyu ya yi ma Goggo Asabe. bai ce komai ba ya rungumeta  yana lumshe idanunshi. Fatima da Khadija kuwa sai dariya su ke yi.

ni kuwa ina cikinsu tsamo tamkar wata bare. Gabana sai dokawa yake ta faman yi.

“Barka da zuwa Aliyu.”

cewar khadija. harda wani sassauta murya dan ta yi taushi.

cikin dariya ya ce.

“Dijengala ke ce ki ka girma haka? Ai ko a hanya na ganki sai dai in wuce.”

dariya su ka yi duka. Fatima tace.

“Ai kaine ka girma Aliyu. ji wata k’asumba daka tara. sai kace babban mutum. kuma ka sake yin fari.

“Yaya Fatima kenan. ina yaran?”

“Suna gidan su Kawu na barosu acan.

Goggo Asabe ta ce.

“Ni kaina sai na ga ya mun wani bawai. ji uban gemu kamar soson waya k’usar yak’i. Ai wani sai ya d’aura irin manyannan ne. Yaro da kai da d’anyan jininka ka zama wani babba.”

kawu ya ce.

“Ai kuwa yayi kyau sosai. Sai dai dole zai canja mana. Shekaru hud’u fa. malam Iliya ne ya sanar damu ranar da za ka dawo. ya ce kun had’u a Umara da ya je.”

kai ya girgiza ya ce.

“Gaskiya ne. har gidan da muke ya je.

carab mu ka had’a idanu dashi. na ji matuk’ar kunya daya kamani dumu dumu ina kallonshi.  Da sauri na kawar da kaina.

yamutse fuska yayi, tare da d’aura d’an yatsanshi a gefen kanshi. Alamar tunani.

” Kawu wannan ba Anty Sadiya bace. Ta gidan Baffana?”

mai taxi ne yai musu magana da ya ga hirar tasu tak’i ci tak’i cinyewa.

“Malam ka fa barni a tsaye.

da sauri Aliyu ya juya, wajan mai taxi d’innan. yana mai bashi hak’uri.  Sun tattauna ba mai yawa ba. Sannan ya juyo ya ce.

” Kawu muje ko?”

Dawowa yayi zai ‘dauki akwatin ya sa a bayan mota.

Goggo Asabe tayi tarab tace.

“Ke Sadiya. Aike ya dace ki d’aukar mishi. Ko a gabana ma zaki nuna mun ke ‘yar duniya ce?”

wani abune ya tokare mun mak’oshina. Murya a sanyaye na ce.

“Kiyi Hak’uri Goggo.

take idanuwana su ka kawo ruwa. Ajjiyar zuchiya na ke ta saukewa a hankali. Aliyu da bai fahimci Abinda Goggo Asabe ta ke nufi ba. Na hango rashin jin dad’i a fuskarshi.

Akwatin na d’auka. Har zuwa gaban motar. juyawa na yi, na d’auko jakar na ajjiye a kusa da akwatin.

Mai taxi ya zuba komai a bayan mota.

Aliyu da kawu. suka zauna a gaban mota.

mu kuma mu na bayan mota dukkan mu.

Hira su ke ta yi, cikin raha da burgewa. Ni ko kaina a sauke ya ke, ina share hawayen da na kasa dakatar da shi.

Ashe Aliyu ya na kallona ta glass d’in  hannun da yake ta waje. Kasancewar ni ina zaune ne a bak’in kofar shiga. Sabida sai da kowa ya shiga. Sannan na shiga gudun kar in yi wani laifin da za’a sake tsinka ni.

kai ya girgiza tare da cije lebe.

Yace Baaba. Yaushe  Anty Sadiya ta zo ne? ni fa ba dan jini ba. Wallahi bazan gane ta ba. Sau biyu na tab’a ganinta.”

Goggo.Asabe, ta tab’e baki tace.

“Ni banma san ka tab’a ganinta ba ai.

Aisha ai bazata barta ta shiga dangin Adamu ba.

Su ‘yan boko ne. Masu raina mutanen k’auye. kuma ai kasan Aisha bata tare da dangin mijinta sam. Shi kuma Adamun, Inka tab’a jemammiyar matarshi. Sai ya ji gwara ka zare ranshi. Ba a hakan bane ta ci nasarar mallakarshi da asiriba.  yai ta ma iyayenta da danginta bauta.”

Aliyu ji yayi tamkar k’asa ta tsage ya fad’a ciki dan kunya. Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi.

Ni kuwa dama kaina na k’asa. Hawayene su ka ci gaba da gudu a fuskata. Fatima tace.

“Goggo ki ce kun k’unshi bak’in ciki? ku da kuka sha d’awainiya da k’aninku. Amma tashi d’aya rana d’aya. Sai wata ta malleke muku shi. Ku kun tashi a tutar babu.

Gashi na ji ance har zuwa yanzu, ana biyanshi mak’udan k’ud’ad’e a wajan aikin shi ko?”

Ai fatima dama kamar da biyu tai ma Goggo wannan tambayar. Sai cewa ta yi.

” Sosai ma. Amma ta yi rub da ciki akan dukiyar. Harfa gida ta zo, bayan rasuwar Adamu. Ta samu Kawunku ga shinan. Wai an barta da marainiya, mu ba ma tallafa mata. Dan haka tazo ne a bata gadon mijinta.  Za ta ci gaba da kula da karatun yarinyarta. Mu na ji muna gani, Akaima wajan kud’i, sai aka biyata iya nata. Kasancewar mace gare ta. Mu ma aka bamu namu fa.”

Fatima tana k’ok’arin bud’e baki ta yi magana. Aliyu ya daure ya ce.

“Yaya Fatima. Su Yaya Anas da Yaya Dauda, basa gida ne? Banga sun zo taryata ba.”

” Gona mu ka barosu zasu je. za’a fita da dawa cikin Zamfara.”

da k’arfi Aliyu ya canja zancan dole.

na sha muggan maganganu kafin mu iso gida.

dandazon matasan garin, suna k’ofar gida an cika. da ganin Aliyu, su ka shiga sowa suna kiran sunanshi.

A wajan mu ka shiga gida mu ka barshi.”

Ina tafe kici kici da akwati da jaka. Duk ni kad’ai. Fatima da Khadija har sun wuce nima. Hasiya matar Dauda. ta dube ni, ta tintsire da dariya tare da tafa hannunata tace.

“Ahhh andai yi fad’uwar bak’ar tasa. wai Yaya da auren k’aninta.”

harna tsaya dan inaso in yi ma Hasiya gargad’i. Amma dana tuna ciwon jahilci ke damunta. Sai kawai na yi wucewata.

cikin k’uryar d’akin Goggo na shigar da kayan. Alokacin har gidan ya gama cika da jama’ar k’auyan, sun zo yi ma Aliyu barka da zuwa. zama nake so in yi a falon Goggo, amma carab tace.

“Ai abunda ya fi dacewa shine ki yi maza ki girka ma Aliyu abinci. Tunda baki da wannan tunanin sai an fad’a miki. k’ila haka malaman boko d’in su ka koya miki ko?”

Bazan iya cewa da Goggo komai ba. Fita na yi jikina a mace. ina jiyo dariyar Fatima da Khadija.

Jama’a sai kallona su ke yi, suna xund’ena . baba wanda na nuna na gani, wucewa ta kawai na yi.

bilkisu ce ta yi mun magana ina daf da shiga b’arayina.

“Aliyu ya dawo lafiya?”

Dubanta na yi da kyau na ce mata.

“Bilkisu ni banga aibun Auran yaro ba. Danna girmeshi sai me.? inaga baku da tarihin magabata shiyasa. k’aramin sani k’uk’umi.

tsaki na ja na wuce na barta rik’e da k’ugu a wajan.

Hasiya ce ta iso wajanta da gudu tace.

“Barta za mu yi maganinta a cikin gidannan. ke ni wallahi baki ji yanda na tsaneta ba. kishi na ke yi da ita, fiye da kishiyar da za’a kawo mun.

Bilkisu tace.

“Ni kaina mugun kishi nake yi da ita. Bana ko san ganinta. Ga shegen iyayi wai ita uwar mata. Sai dai uwar mijinta ma kad’ai ta isheta.

Sadiya

shinkafa fara na dafa. Ina da miyar stew wacce ta ji naman kaza da jan nama. Wanda Goggo Hansatu ta yi mun da yawa, akan in tafi da’ita gidan Ahmad dan in samu sauk’i kafin in soma girki.

Ban tab’ata ba tunda mu ka zo. Sai d’umamata da na ke yi sau biyu a rana.

food flaks na bud’e sabo mai guda hud’u.

A ciki na zuba na Aliyu. Goggo da Kawu kuma na bud’e musu wata kular mai biyu.

Sai da na kai na Aliyu da Goggo, Sannan na wuce na kai b’arayin Kawu.

ina dawowa na yo wanka. minti talatin na kwashe a komai da komai.

Ina sanye da doguwar rigar bak’in yadi ‘yan kanti. Rigar ta matse ni sosai. hakanne ya ba ma kirjina damar fitowa sosai ta cikin rigar. ga mazaunaina sai motsowa su ke yi, koya na yi tafiya. K’amshi kuwa ba’a magana. D’akina sar da shi, komai ya na inda ya dace.

ina zaune a falo, gabana sai fad’uwa yake yi. damuwata shine ta ya zan iya kallon Aliyu.

Mik’ewa na yi, Sallar la’asar da bamu yi ba na rama. ina zaune a wajan da nai Sallah har zuwa magriba, ban tashi ba har sai da na yi Sallar isha. Abinci na zuba d’an kad’an. Amma bana ko jin dad’in bakina. Tutturawa na dinga yi harna k’oshi na sha ruwa.

Ina zaune a wajan Har zuwa k’arfe taran dare, sai wasik’ar jaki na ke karantawa.

motsin k’ofar shigowa b’arayina naji. Gabanane ya tsananta bugawa da ‘karfi. Har zufa na soma yi, kamar wacce jaki ya kayar da ita.

” Assalamu Alaikum!”

take na ji bakina yayi mun mugun nauyin da yasa na kasa amsa sallamarshi. Inaji ya sake yin sallamar.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

    _Mrs Bukhari_

 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*

     _Miss Hajo_

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

Kashi na 1

Babi na 15~16

Ji na yi an sake doka sallamar. cikin sark’ewar murya na amsa. mik’ewa na yi xuwa bak’in k’ofar.

Dauda ne ashe.

“kina ji ana sallama kin yi ma mutane banza. irin halayyarku ta raini na ‘yan boko. Hak’uri na ke son in bud’e baki in bashi. Amma abun mamaki sai naji ya dakamun tsawa.

“Dallah dakata malama karma ki sake ki ce zaki zageni. mara kunya fitsararriya. (Aisha Lawal ta ce. Kai kuma a suwa?)

Akwatin Aliyu ya sauke mun a yatsun k’afata. fuu ya fice a gidana.

Idanu na runtse dan inajin wani xugi da kafata ke yi. Da alama ciwo na ji. Amma ciwon da zuchiyata take yi, yafi gaban misali. cikin dakewa na sauke akwatin akan k’afata. jini sai zuba yake yi. Babban yatsanane ya fashe.

Akwatin na kinkima na shiga dashi ciki. box d’ina na d’auko na dressing k’afar tawa.

rigar bacci na xura doguwa mai santsin yadi. brosh na je na yo.

ina kwance lamo amma xuchiyata sai ciwo take yi mun.

Wai me yasa kowa ya tsaneni, na zama abar wulak’antawa. sai kace ba ‘yan uwana ba? Duk wanda na yi mu’amala dashi, sai in ji babu dad’i, ji yanda rayuwa ta sauya mun, sai tamaula take dani. k’ila shima Aliyun bazan ji sanyi a hannunshi ba. K’ila ya gasani fiye da masara ma. (Maman Yaseer tace. Mai hak’uri ya kan dafa dutse ya sha romanshi)

hawaye na share fuskata.  Na shiga tunano yanda na tashi a cikin gata. mama da Baba su na matuk’ar sona. Burinsu in yi ilimi in zama wata. su suka cusamun son karatu. hakanne yasa na yi karatu sosai. kuma Baba ya bani gudummawa sosai a karatuna. A asibiti kuwa. likitoci da marasa lafiya b’angaren ‘yan haihuwa suna alfahari dani. domun nasan makamar aikina sosai. harma ana maganar an saka sunana a cikin wad’anda gwamnati zata tura india dan gabatar da couse akan b’angaren  da kowa ya kware a akai. hakan ya faru ne a sakamakon karb’ar haihuwar yarinyar gwamna da nayi. Da yanda na tafiyar da ita. na samu lambobin yabo da dama. asibitinmu suna ji dani matuk’a, inajin dad’in kasancewata ma’aikaciyar jinya, b’angaren anguwar zoma.

Amma dubi yanda rayuwa ta maidani, na dawo cikin k’auye anan zan rayu. k’auyan da ko asibiti babu a ciki balle in yi musu aiki kyauta, ko dan ceto rayukan ‘yan uwana mata. An rusa mun abunda iyayena suka wahala wajan ginashi. gashi kowa a cikin gidannan ya tsaneni.”

Aliyu

sai bayan Sallar isha Abokanshi su ka sake shi ya shigo gidan.

Allah Allah yake yi ya isa d’akin Goggo domun yana son jin gaskiyar maganganun daya samu daga manyan Abokanshi na hannun dama.

Da sallama ya shiga falon. Dukkansu iyayen nashi suna ciki, Harda d’an uwan mahaifinshi kawu Bala.

Cikin nutsuwa ya nemi waje ya zauna. Goggo ce ta ce.

“Sai yanzu su ka barka ka shigo? Khadija ta gama zaman jiranka. tana d’aki ita da Fatima. Kila ma sun yi bacci.” Ahankali ya d’ago ya dubi Goggo yace.

“Wallahi kinsan an dade ba’a had’uba. Yaya Fatima kwana zata yi a gidan?” Goggo Safiya ta ce.

“Auran ma ya k’are kenan. dan ba baiwa aka bashi ba. shi ya wulak’antata. ‘Yan uwanshi ma su taya shi. Akan me? Gobe zai sake ta a gaban kotun mai gari.”

” Saki kuma Goggo, Toh yaran da ke tsakaninsu fa? Adai yi hak’uri a duba rayuwar yaran” Goggo Mariya tace.

“Yara k’anana biyu ne  a gabanta. Sauran mazan duk suna almajirci. Akan yara baza mu bari ta wulak’anta ba.” Sauke kanshi k’asa kawai yayi. Kawu ya ce.

“Nasan ba zaka rasa jin abunda ke gudana ba. Domun Kamilu abokinka ya san komai. Akan maganar Auranka da Sadiya, domun ya sha d’awainiya a hidimar bikin.Ga Baffanka Bala shi ya amshi wannan Auran. Sannan kuma, ni na shigo da maganar wajan su Yaya Asabe. Acikinsu babu wacce ta amince da had’in. Iyayen khadija kuma su ka gindaya tsattsaran sharad’in da bansan me Yaya Asabe ta ke nufi ba. Aliyu Sadiya dai makarka ce a tak’aice. Amma ka yi hak’uri, k’addara ta riga fata” Goggo Asabe tace.

“Nasan hakan bazai tab’a yi ma dad’i ba. Kamar yanda bazai tab’a yi mun dad’i ba, Ansha artabu dani. Komai inayi dan farin cikin ka kai da khadija ne. Mahaifin khadija kuma ya tabbatar mun, Babu Aure a tsakaninka da khadija face ka saki Sadiya. Duba da yanda ku kai zurfi a son juna, na amsa mishi daka dawo zaka sauwak’e mata.  Ka sake ta tun wuri ta kama gabanta. Kar wataran zuchiya tasa in yi mata wani mummunan aika aikar.” Aliyu dai bai d’ago kanshi ba. Goggo Safiya tace.

“Inba sakinta  ka yi ba. Jama’ar k’auyannan za su yi zarginka a matsayin mayaudari. manyan mutane harda dattijai, sun fito naiman Auran khadija. Amma mai gari ya ce an mata miji. Kuma har rantsuwa yayi kan cewar d’iyarshi baza ta yi zaman kishi da ‘yar boko ba.” Goggo Mariya tace.

“Aimu kan mu. in yaronnan bai Auri khadija  ba.Za’ai mana kallon mutanen banza” Aliyu dai yayi shiru yana sauraron kowa, cike da mamakin furucinsu. Kawu Bala ne yace.

“Amma ita yarinyar bai dace ace za’a sake ta sati d’aya da Aure ba. A shawarce dai abar wannan sakin har sai bikin ya matso. Amma ba daidai bane. Allah zai iya kama mu da hakkinta fa. Aliyu ni dai ubanka ne, kuma ni na karb’ar maka wannan Auran. Babu hannuna akan wannan maganar sakin. Bansan cewar Asabe bata shiri da mahaifiyar yarinyar ba. Da bazan ma shige gaba wajan Auran ba, domun naga ‘yar k’aninta ce. Na barku lafiya.”

tashi yayi ya fice abunshi. Kawu ya dubi Aliyu yace.

“Kai muke saurare Aliyu. numfasawa yayi ya d’ago kanshi ya dubesu.

“Bawai zan bijire ma umarninku bane. Sai dai yin abunda kuka umarceni yana da wahala. Anty Sadiya batai mun komai ba, me yasa zan sake ta Sabida khadija?. Lallai dukkan ku kunsan inason khadija, kuma na shak’u da ita. Ita kuma Sadiya ‘yar uwata ce jinina ce. Bazan ji dad’i ace Auranta ya mutu a wani gidan, wajen wani mijin ba ni ba Balle kuma ni da kaina.  Baffana Adamu da yana raye bazai yi farin ciki da hakan ba. Nayi mamaki da har Anty Sadiya ta amince ta kashe rayuwarta tazo zaman Aure wannan k’auyan da ko ni da a ciki aka haifeni nake gudun shi ba. Ashe kuwa tana da hankali da biyayyar da yaci ace an dubeta, an kuma…”

” Dakata k’usar yaki. Wallahi kana k’arashe zancanka zan zabgama mari. ni Asabe uwarka umarni na baka ka saki Sadiya a daren yau. gobe ta wuce wajan uwarta. Kai yaro ne bakasan ta kan duniya ba. Aisha jinin Adamu ne  kawai bata sha ba. Amma juyashi ta dinga yi. Har bak’in ciki yasa ya fad’i ya mutu. Bazan so in ga hakan  a kan ka ba.”

khadija kuwa tana lab’e a bayan labule ta na mamakin dalilin da yasa Aliyu ya yi kaddamar sakin Sadiya. mace tsuhuwa da ita. a cewar khadija. (Ta marad’i tace. Sadiya tafi k’arfin kice zaki yi kishi da ita)

Aliyu ya dubi Kawu alamar yana buk’atar taimakonshi. kawu yace.

“Asabe. Abi komai a hankali inaga zaifi. Abar yaronnan da maganar sakin tukunna. Mai gari kuma ni zan je in same shi aci gaba da maganar biki. Nanda wata d’aya kamar yanda aka saka.” Goggo Asabe ta runtse idanu tace ita Allanfur sai Aliyu yayi saki a darennan.

Aliyu daya rasa ta cewa wanda yake jin ba Adalci bane ayi saki babu dalili. kuma yana duba dangantaka. yace.

“Baba toh ki mun hak’uri zuwa jibi inna huta sai in sake ta. murmushi tayi tace.

“Aliyu ni nai dakon cikinka wata tara. Kaga wad’annan cinyoyin?. ta bugi cinyarta tana nuna mai. tace.

“toh akai ka yi rayuwarka. Har akwai wani wayo da zaka fini kuwa? Toh ka ji na bari sai jibin. Amman inka yi mu’amalar Aure da Sadiya bazan yafe maka ba. kuma zan iya d’aga maka nono akan hakan.”

Khadija ta yi wani tsallen murna tare da toshe baki kar su jiyo ihunta. Lallai yau ta sake gasgatawa cewar Goggo tana sonta. kuma za ta ji dad’i  a wajanta in ta Auri Aliyu. ta wani b’angaren na zuchiyarta kuma. Cike take da jin zafi da haushin Aliyu. Domun rashin Sakin Sadiya tamkar ruguje maganar Auransu ne.”

Aliyu kuwa. Tamkar k’asa ta tsage ya shiga tsabar kunyar da ya ji dangane da furucin Goggo, ita kuwa ko a jikinta. gabanshi ne ya fad’i sosai, ya kasa cewa komai ma. Kawu ne yace.

“Asabe ya isa haka. Yaji kuma sharad’in da kika gindaya mishi. sai mu jira jibin.” su Goggo Safiya duk su ka amince akan tai hak’uri zuwa jibin.”

jiki a mace Aliyu ya bud’e jaka ya soma ciro tsaraba. su Goggonninshi duk ya mik’a musu nasu. Cikin washewar baki su ka amsa. Kawu ya mik’ama nashi da na matan shi. sannan ya ware na khadija da na Goggo.

Sallama su Goggo Safiya su kai ma Goggo, Dan har goma ta gota. d’akin ya rage daga Goggo sai Aliyu tace.

“Kai da ka je karatu shine har da tsaraba, sai kace wanda ya tafi aiki. naga kayan masu tsada.

“murmushin dole Aliyu ya k’ak’aro. Dan a halin da yake ciwo kanshi ma yake yi. Goggo ta caza mai kai da kalamanta.

“Da yake suna biyanmu kud’in abinci. kuma Aikin ma in mun samu muna tattab’awa. Karatu zanci gaba dayi inaso in shiga kuma jami’ar boko in had’a digiri a fannin daya dace.” Goggo tace.

“Ina karatu kam ka yi na muhammadiyya Amma wallahi indai ni ce uwarka baka isa kayi wani dagiri a boko ba. Allah ya amfana wannan d’inma.

“Ameen” kawai ya ce mata. sannan ya ce.

“Baba ni zan tafi in kwanta duk na gaji. ko jiya da muka sauka a Abuja banyi wani baccin kirkiba. Kaina na ciwo.” Khadija Goggo ta shiga kwad’ama kira. Cikin hanzari khadija ta fito falon tana wani sulkui da kai. Goggo ta mik’e ta ce.

“Nizan ta fi in kwanta bacci ya dame ni. khadija kam ya kamata ka bata lokaci kuyi hira sosai. An dad’e ba’a had’uba.”

tana kaiwa nan ta shige d’aki. Aliyu kuwa baiji dad’in hakan ba. koba komai ya kamata ya daraja Sadiya tunda dai matar shi ce. kuma ‘yar uwarshi.”

khadija sai b’are b’aren jiki take yi. Tana jera mishi kwanukan Abinci a gabanshi. ciki harda kular abincin Sadiya.

“Ali na. ga abinci sai wanda ranka yai maka. Amma wannan shine abincin da na dafa maka da hannuna.” ta nuna mishi kwanon.

murmushi yai mata ya zuba mata idanunshi, bin jikinta kawai ya ke yi da kallo. yanda ta xama mace har mamaki abun ya ke bashi. yana son khadija a cikin ranshi sosai. domun da sonta ya reni jaririyar zuchiyarshi har ta girma. lumshe idanu yayi yace.

“Dije na nayi kewarki sosai.” fari ta yi da idanu tace.

“amma ai na ji ja in jar da ka gama yi a falonnan akan tsohuwar matarka. ni na zaci ko ka daina so na ne ma. harna soma fargabar ta yanda jaririyar xuchiyata zata rayu ba mai rainonta.”

gyara zama yayi ya fuskanceta da kyau.

“Dije na. Babu wani namiji da zai so ki irin rabin son da na ke yi miki. Bazan bari ki subce mun ba. ai bazan iya gudanar da rayuwa mai dad’i ba. ko kin manta da sonki na ke rayuwa.? Nan su ka shagala a soyayya. Suna yi ya na cin abincin da khadija ta kawo mishi. Har sha biyu na dare bai sani ba.”  Da kyar su ka yi sallama da juna. dan ji ya  ke yi kamar ya rungumeta su kwana a waje d’aya. ya kasa d’auke idanunshi akan khadijar. domun ta kara mishi wani kyau ne na musamman.

Da sallama ya shiga cikin b’arayin na shi, wanda khadija ce ta nuna mishi ma wajan.

Babu motsin kowa.

tura k’ofar d’akin yayi gabanshi na dokawa.”

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

    _Mrs Bukhari_

 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*

     _Miss Hajo_

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

Kashi na 1

Babi na 17~18

Falon ya turo ya shiga. k’arema falon kallo yake ta yi. komai tsab ga k’amshin sabunta da falon ya ke yi, ga kuma k’amshin turaren wuta na hulut sai tashi yake yi a d’akin. Mamaki ya ke ji. Yau shine ya Auri Sadiya yayarshi, kuma duk kyan d’akinnan nashi ne. k’ofar d’akin da Sadiya ta ke ciki ya tura, cikin fad’uwar gaba. Yana son shiga Amma yana jin nauyinta sosai.

Sadiya

Da sauri na share hawayena, nai saurin kulle idanuna. Kunya na ke ji in sake ma ganin Aliyu.” Da sallama a bakinshi ya shigo. A cikin zuchiyata na amsa mishi sallamar tashi. gabana sai sake tsananta bugu ya ke yi. Tamkar wacce aka kama ta yi k’arya. Ajjiyar zuchiya na ji ya sauke da bansan ta meye ba. shiru ya na tsaye a inda ya ke. Amma ina jin tsinin idanunshi a jikina. Da dukkan alama k’arema surata kallo ya ke yi.” k’ut ya had’iye tsinkakken yawunshi da ganin surata ya tsinka shi. tudun kirjina kawai ya ke bi da kallo ba ko k’ibtawa. ina kallonshi ta k’asan idona. sai ajjiyar zuchiya ya ke saukewa a jere a jere.

Aliyu kuwa tunda yai arba da Sadiya a kwance cikin goduwar rigar bacci, a take ta kwance shi. surarta wacce ta tsaru ya ke kallo. bai tab’a ganin cikakkiyar mace mai cikakkiyar sura irin Sadiya ba. kirjinta yafi komai jan hankalinshi. yana hangosu ta cikin riga suna k’ara burgeshi. lumshe idanu yayi.

Sadiya.

Ni kuwa duk halin da ya ke ciki ina gani. kallo na kai kan wandonshi daya cika yai fam. har wani danshi na gani a jiki. Da sauri Aliyu ya juya ya fice a d’akin. akan kujera ya zauna tare da dafe kan shi. mararshi na wani juya mishi.

Ajjiyar xuchiya na sauke. Kwanciyata na gyara tare da juya ma k’ofar shigowa d’akin baya. amma abun takaici da haushin na kasa samun bacci sam. damuwowin da su ke damuna yawa garesu sosai.

Aliyu

kwanciya Aliyu yayi a saman kujera. ya na rik’e da mararshi. Bai tab’a jin wani abu mai zurfi haka game da mace ba sai akan Sadiya. lumshe idanu yayi. hoton kirjinta suna sake haska kansu a cikin duniyar tunaninshi. mararshi ya kuma rik’ewa sosai tare da sakin nishi a hankali. A cikin daren dai daga Sadiya har Aliyu Babu wanda ya runtsa. Hakanne yasa su ka wayi gari da matsanancin ciwon kai mai zafi. Sadiya har bata iya bud’e idanunta da kyau.

Sadiya

kiraye kirayen Sallar Asuba ne ya mik’ar dani daga kan gadona. fitowa na yi falon. Aliyu na gani a kwance a kujera Bacci ya fisgeshi. wandonshi na bi da idanu. sai da gabana ya buga.  A take tsoro da fargaba ya kamani. Maganar Amina ce ta fad’omun da tace NAMIJI BAYA KAD’AN naga halama. bud’e idanu  Aliyu ya yi fes a kaina. Akan kirjina idanunshi ya sauka. Ni kuma duk na dibibice dan kunya. cikin in ina nace.

Dama dama naji za’a shiga Sallah ne. shi ne ka je masallaci.”

” Toh” kawai ya iya ce mun. Da sauri na wuce band’aki na d’auro Alwala na fito. ina shiga Falon Aliyu ya mik’e ya fita.”

Sallah na soma yi. Ina jiyo fitar shi daga gidan.

Aliyu

yana tafe ya na tunanin taya zaije d’akin Goggo ya ce ta bashi kaya zai sake da asubar nan? Gashi bazai iya zuwa wajan kamilu ya ce ya bashi kaya ba. Dan hakan tamkar tona asirin auren su ne. Duk da dai Kamilu ya zarce aboki a wajanshi. Amma wannan wani sirrine da yake a b’oye. hakan cikin taraddadin abunda zai faru yai k’undunbalar shiga b’arayin su Goggo. tura k’ofar d’akin Goggo ya yi a hankali tamkar b’arawo. A falo ya samu Goggo idar da sallarta kenan. da sauri ya tsugunna dan karta kama danshin dake jikin wandonshi, wanda ya fito ta cikin jallabiyar jikinshi, ga Jallabiyyar ta kunbura. kai ya sauke kunya ta lullub’eshi ya ce.

“Barka da Asuba Baba Ina kwana?” Harara ta zabga mishi tana bin yanayin da ya zo mata da kallo. cikin zargi tace.”

“Ka aikata abunda na haneka da aikatawa ko k’usar yak’i?” Kuka ta fashe mai da shi tace.

“wallahi tsinema zan yi insan na sallamama duniya kai. Da kuma Sadiya. Sai ka koma.Aisha ta zama uwarka.” bakinshi na rawa ya ce.

” Babu abunda na aikata. wallahi a falo ma na kwana.” Ajjiyar zuchiya ta sauke. dan tasan Aliyu ba ya k’arya. Balle kuma ya rantse ma. Tace.

“Akwatin kayan na ka ya na can an kaima ita Sadiyar.”

“Toh” kawai ya ce.

“Aliyu” ta kira sunanshi da manyan bak’i. Harya kai bakin k’ofa ya tsaya.

“Kar ka manta gobe da safe ka tawo mun da takaddar sakin Sadiya.  karka shigo sai da takaddar.”

Bai ce komai ba ya fita. Da sauri ya wuce b’arayinsu. Hasiya ce ta bishi da harara.

Sadiya

ina zaune ina karatun Qur’ani cikin suratul maryam. ya shigo da Sallamar shi. A hankali na Amsa. Kaina na k’asa na ce.

“Barka da asuba an tashi lafiya?. Jin dad’in shi har ya kasa b’oyuwa a fuskarshi. cikin kulawa ya ce.

“Lafiya lau Anty. Amma bari na yi sallah sai in zo mu gaisa a tsanake.” Wajan Akwatinshi da ya gani a gefen sip ya wuce.

Jallabiya ya zaro da wandonta. Sannan ya koma falo ya wuce band’aki yayo wanka. Sallah ya yi. Mik’ewa yayi. ya soma nad’e kayan na shi. Daidai  fitowata. Ahankali na ce.

Dama ka barshi.”  Da murmushi ya ce.

“Babu damuwa Anty. Zo ki zauna mu gaisa.” dukkan mu a kunyace muke magana. Amma kasancewar shi namiji ne harya soma sakewa.

Zama na yi a saman kujera. Na yi shiru ina sauraronshi. Shima shirun ya yi. Sallamar da aka doko a bakin k’ofar d’akin ce ta katse shirun.

Anas ne. Da dauri Aliyu ya fita.

“Yaya Anas? Rungume juna su ka yi cikin tsananin murna. Anas ya d’agoshi daga jikinshi ya ce.

“Aliyu kaine ka zama babban mutum haka?  kai kawai ya sosa yana dariya.

“Yaya naga kowa amma banda kai da yaya Dauda.”

“Kaidai ka bari. masu sayan hatsine daga Zamfara su ka shigo. Shine mu ka tsaya a kansu sai da aka gama komai. Ni da Dauda mu ka lissafi. Kusan buhu talatinne ba mu samu ba. Ana yawan yi mana satar da ba mu da masaniyar ko waye a cikin gidannan. Ni da Dauda ne ke rike da makullin rumbun.”

“Aliyu ya ce idanu za’asa sosai Yaya. Tunda dai a cikin gidane. Kai amma ko waye ke yin wannan b’arna bai kyauta ma kanshi ba. mu shiga daga ciki mana Yaya.”

“Wanne ciki kuma? tsarabata kawai za ka bani malam.” Dariya Aliyu yayi. Tare da zura takalma yace.

“muje tsaraba na d’akin Baba ai. Su murtala suna almajirci har yanzu basu gama ba ko? Ficewa su ka yi a gidan nawa. sai da na dena jin muryarsu sannan na mike.

Kitchen na nufa. Na yi tsaye ina tunanin shin mai zan girka a matsayin abincin safe?” shiru na yi can sai na tuno bari kawai in dafa kuskus tunda bani da d’anyen kayan miya a hannuna. cikin k’ank’anin lokaci na dafa kuskus dina. Ta yi warawara sosai abun sha’awa. kula na sake farkewa na zuba ma.Aliyu. ruwan wanka na d’aura minti goma yayi akan wuta na juye. Rishon na rage tare da d’aura dumamen miya.

Cikin minti Talatin na gama kintsawa. ina sanye cikin wata jar atamfa hightaget. Dinkin diga da siket. Atampar ta amsheni sosai ta kuma dace da kalar skin dina. Dan jan abu na haska bak’i sosai. Kitchin na koma na kashe miyar. zubawa na yi a cikin kular Aliyu ta miya. Sannan na zubama Goggo Asabe nata. a basket na jera komai. takalmi flat shoe ne ja a k’afata. bak’in mayafi na yafa. Sabida atamfar da bak’in kala akai mata ado.

fitowa na yi babban tsakar gidan. Da Hasiya na ci karo ta na k’arema takuna kallo. Shewa na ji ta yi tace.

“Allah ya wadaran naka ya lalace. An salwantar da budurci dole a fito babu d’ingishin komai. Mu kuwa a ranar da komai ya faru munfi sati muna jinya.”  Da sauri na dubi Hasiya. Tana rik’e da k’ugunta da ganin fuskarta a cike take da ni. Karasawa nayi har inna take nace.

Wannan jahilcin naki ya soma isata. Ya kamata kisan ni ba sa’arki bane, sannan ni ba kishiyarki bace balle in zama abar tsokanarki. Ya isheki na Fad’a miki kenan.

Tafi Hasiya tayi tace.

“ke ce dai jahila wacce ba ta san me ke yi mata ciwo ba. wacce ta kasa auruwa  a maraya kawai. Kuma ki sani duk wani wanda ya ci ciwo da ni miya yasha.”

“miyar ma bazai gane ya sha ba. “Wato ke Sadiya rashin kunyar taki har takai ki zagarmun mata a matsayinta na matar.wanki? Dauda ke magana daga bakin k’ofarshi.

“Toh ki sani mu a gidannan baza mu d’auki raini da iskancinnan naki ba. Maras kunyar kawai. Ai dama barewa baza ta yi gudu d’anta yai rarrafe….. Kafin ya idasa na daka mishi tsawa.

“Dakata cin kashin ya tsaya iyakar kaina. Kar ka kuskura iyayena su shigo. Dan zamu yi uwar watsi. iyayena sunfi mun kowa da komai a daniya.” Da sauri Dauda ya nufoni Banyi Aune ba na ji saukar hannunshi akan fuskata ya zabgamun marin da saida idona ya makance na wucin gadi. ya sake d’aga hannu zai sake sauke mun . Da sauri na tare fuskata Ina jiran inji a inda hannun nashi zai sauka. sai na ji shiru. Ahankali na bud’e idona. Aliyu ne a tsaye ya had’e ranshi hannun da Dauda ya d’aga zai mare ni Aliyu na rik’e da shi. Rannan nashi a murtuke.

“Ba daidai bane dukan mata.  Balle macen da take matar Aure. Danme za dukar mun mata? Bakasan darajarta bane ko me? Ina daraja matata bazan ba da wata k’ofa da za’aci kashi a kanta ba, domun a k’ark’ashin kulawata take, kuma hakkinane kula da mutumcinta. Kai wane girmanka ya dace ka rik’e. Dauda ya fisge hannunshi ya na nuna Aliyu da yatsa jikinshi har rawa ya ke cikin d’aga murya ya ce.

“Akan wannan karuwar ‘yar bokon ka rik’emun hannu a matsayina na Yayanka. Kuma ba tare da ka yi tambaya akan wanne irin rashin kunya ta yi ba?” Bilkisu ce ta fito dan taji ana hayaniya har da ihu. Ganin abunda ke faruwa ne ta zame jikinta.zuwa b’arayin Goggo Asabe ta sanar mata. Ta wuce wajan kawu ta sanar mishi.

Aliyu  ya rintse ido, dan kalmar karuwa ta gigita tunaninshi ya ce.

” Babu buk’atar sai na ji me ta yi maka. Amma ai kasan ba matarka bace. Matata ce kuma inasonta duk karuwancinta. Domun y’ar uwata ce ita, Anty bakiji ciwo ba ko?.”

“Ai kuwa wallahi baka isa ka ci gaba da zama da ita ba yau ba sai goben ba Auranka da Sadiya ya k’are.” cewar Goggo Asabe wacce ta iso ita da kawu da matanshi. Gabana ya yanke ya fad’i take na soma zubda hawaye. Isowa ta yi gabana tace.

“Makirar ‘yar duniyar mace. Harkin juya mishi kai kenan yau k’usar yaki ne ke yin fad’a. Fad’anma da wanshi. yaron da ya samu shaidar jama’a a gari bai tab’a fad’aba. Shine da zuwanki kin soma haddasa husuma ko. Kinaso ki raba shi da danginshi kamar yanda uwarki ta raba mu da d’an uwanmu. wallahi Allah ba ki isa ba.” Nidai ina tsaye jikina har rawa ya ke yi. Aliyu yace.

“Baba zuwa na yi na tadda ya mareta fa. me yasa zai d’aura hannu a jikinta matar Aure ce fa.”

“Auran wa? kama daina kallonta a matsayin matar Aure dan indai nonona kasha toh sai ka saki Sadiya yau d’innan ta koma wajan muguwar uwarta.” Kawu yace.

“Ke Sadiya ba su fad’a miki doka da tsarin gidannan bane akan girmama kowa ba? kuka na ke yi sosai kukan da ba na ma iya ganin kowa. cikin shesshek’a kuka na ce.

An fad’amun. Amm”

“Dakata Sadiya iyakar abunda na tambaya kenan. Dauda ya ce.

“kuma fa fitowa na yi sai na ji ta na zage Hasiya. Har da ma Goggo Asabe. Shine daga magana ta hau zagina. kuma ita ta soma marina.” cikin kururuwa Goggo da Fatima su ka rufu a kaina da duka kakaf kakaf. ina tsugunne ina kuka. ko yunk’urin guduwa na kasa yi. Aliyu duk ya bi ya rud’e Goggo ya ke ta ba hak’uri. Amma ta k’i fur. Sai da tai mun lis bakina da hancina duk sai yayyon jini ya ke yi sannan ta na huci tace.

“Shegiya maras kunya fitsararriya. kai kuma ka kawo takaddarta yanzu ina jiranka ko kaga mai zai biyo baya. Shashasha mai fad’a akan macen da bata cancanta ba.” Fuuu ta fice a gidan. Kawu kuma ya ce.

“Kai Dauda kar ka sake dukanta. Kome ya faru ka kawo gaban manya. Kai kuma Aliyu ka bi umarnin mahaifiyarka kar tai ma baki.”

watsewa kowa ya yi ya barmu. Zuchiyar Hasiya da Bilkisu fes dan murna. Aliyu ya zuba mun idanunshi da suka kad’a su ka zama jawur, tausayina tsantsa na gani a idanun Aliyu, kuma ko ba komai ya daraja auranmu, ya kuma kira ni matarshi. Wani sanyi naji a zuchiyata.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

    _Mrs Bukhari_

 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*

     _Miss Hajo_

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

*INA MIK’A SAK’ON GAISUWA GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN GISHIRIN ZAMAN DUNIYA, HAK’IK’A NAJI DAD’IN ADDU’ARKU GARENI. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA YA D’AUKAKA FIYE DA TUNANINA, YA TSALLAKA INDA MA BANYI TUNANIBA. TUN JIYA NAKE TA SAMUN SAK’ONNI DA KIRAYE KIRAYEN MASOYANA. INA GODIYA SOSAI, ALLAH YA BAR K’AUNA.*

Kashi na 1

Babi na 19~20

Kallona ya sake yi cikin tausayi da tausayawa. Hannunshi ya saka ya d’agoni tsaye. Tare da jinginani da jikinshi. wani irin shocking mu  ka ji a jikin juna. wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke, tare da haki, ga bakina a fashe sai jini yake zubarwa Hannu yasa rik’e mun k’uguna, ahankali ya soma tafiya. Har d’ingishi nake yi tsabar azaba.” Hasiya ta na lab’e ta na cizar yatsa. Domun ko a mafarki Dauda bai tab’a mata hakanba. ko a Zamanin amarcinta Sanda gishiri ya ke kan kaza kenan. Ko yau ta ji mamaki da ya shigar mata fad’a. Dauda ne dake bayanta, inda take a lab’e ya ce.

“malama matsa zan wuce in kin gama gulmar. Da sauri ta saki labulen nata. Tare da sauke kanta.

“Dama nasan ko me ake ciki kece mara gaskiya. munafuka mai ta da husuma. Amma Abokiyar husumarki ta nanan zuwa, ‘yar sarkin magulmata.”  Wucewa ya yi ya barta  a wajan tare da ficewa a gidan. Ita kuma ya barta da cizon yatsa.

Sadiya

Ahankali muke ta fe. Aliyu ya jera mun sannu ya fi sau a k’irga. akan doguwar kujerar falona ya sauke ni. Hawaye kuwa bai bar.zuba  a idanuna ba. tsugunnawa yayi a gurwarsa ya ce.

“Anty ki yi hak’uri dan Allah da dukkan abubbuwan da suka Faru. Goggo ba ta tsaya ta yi bincike bane, kuma zan d’auki tsattsaran mataki akan Yaya Dauda, bazan bari ya bige ki a banza ba.Amma me ya had’aki da Yaya Dauda?.

A cikin kuka na bashi labarin kab habaice habaicen da Hasiya ta sani a gaba da shi. Har zuwa wanda tai mun yau. Shiru yayi ya na kallona k’ur, kallon da duk shekaruna na kasa fassarashi. na ce.

“Yanxu sakin nawa zaka yi ko?”

Bansan sanda bakina ya furta hakanba. Domun duk abunnan da ake ciki maganar sakin ya girgizani. Ban sani ba ko dan ban jima da yin auran bane. Bana son duniya ta kafa hujja a kaina wajan zagin ‘yan boko. Na dai tsinci kaina cikin tsoron SAKI. tunda nai wannan maganar ya ke bina da kallo kawai. Ni kuma kunya duk ta kama ni.

“Bari in hura kara in d’aura miki ruwan zafi ki gaza jikinki. zanje Lamba in siyo miki magani a kemis. Da sauri na ce. Akwai kalanzir a risho. Magani kuma i na da shi a box d’ina.”

bai ce komai ba ya fita. hawayen fuskata na share. zuchiyata a cikin zugi da tashin hankali ta ke. Haka

Aliyu

 Aliyu ma. Tunda ya d’aura ruwan wankan a kan risho. ya ke tsaye a kitchin din. sai tunanin mafita kawai yake yi. shi bai ji cewar zai iya sakin Sadiya ba. baisan alkhairin dake cikin auran shi da ita ba.  Kuma a zahiri Sadiya ta kai macen da ko wanne namiji ya sota, ya kuma ji yana son kasancewa da ita. bugu da k’ari gata ‘yar uwa ta jini, wacce bai kamata a yasar da’ita ba.Amm ya na auna kalaman da Goggo ta jefe shi da shi. cewar indai nononta ya sha ya rayu toh dole ya saki Sadiya. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya rasa tudun dafawa, balle makamar da zai kama. Ruwan ya juye mata ya sirka. har ban d’akin ya kai ruwan.

Sadiya

ya shigowa yayi ya sameni da box d’ina da mirro ina dressing bakina da Goggo ta fasa mini. Zama ya yi yana kallona k’uri yace.”

“Ashe da likita na ke tare ban sani ba. Kai masha Allah. Murmushinshi ya fad’ad’a.

Bance dashi komai ba. sai da na gama tas nace.

” ‘yar koyo dai waneni da likita. murmushi yai mun.

“Ki je ki yi wankan. zan je in dawo yanzu, ina mai baki hak’uri a karo na barkatai, kuma ki sani ina tare da ke.” fita ya yi. ni kuma na shiga toilet na dinga gasa jikina dan ko ina ciwo ya ke yi mun, juyayin maganganun Goggo kawai nake yi, cike nake da mamaki. Wai dama ashe haka lalurar jahilci take? Wallahi gara mahaukaci sau dubu akan jahili.

Aliyu

Fitarshi ke da wuya ya zarce gidansu kamilu.

Kamilu ya fito k’ofar gida, Sai kawai ya ga abokinshi a cikin yanayin tashin hankali mara musaltuwa. Dafa kafad’arshi yayi dan bai ma san Kamilu ya fito ba.

“Aliyu lafiya kake kuwa na ganka a cikin irin wannan yanayin, Meke faruwa?  Aliyu ya juyo ya kalli kamilu, idanunshi sunyi jawur, ga wani ciwon kai dake addabarshi, hatta d’and’anon yawunshi ya gurb’ace tsabar tashin hankali.

“Kamilu Baba ce ke son birkita mun fissafi na. Waifa magana take yi akan sai na saki Sadiya, kuma ni bazan iyaba wallahi.” Hannunshi Kamilu ya rik’o zuwa cikin gidan na shi. Kai tsaye su ka shiga d’akin da anan ya ke. Kasancewar matanshi biyu ne. Sai da su ka zauna Kamilu yace.

“Saki kuma daga dawowarka. wani abun Sadiyar ta yi ko me?” Labarin komai da komai Aliyu ya ba Kamilu ciki harda abunda ya faru yau.”

“Tabb aiki ja kenan. Amma tunda Sadiya ta amince ta zauna da kai a wannan k’auyan namu da mu kanmu muke gudunshi. Ai kuwa ta cancanci a yabeta. Ni nasan duk akan khadija Baba ta ke yin wannan abun. Ita bata san khadija ta canja ba shiyasa.” Aliyu ya gyara zama ya ce.

“kamar ya Kamilu wanne irin canjawa ta yi?”

” Aliyu nasan k’ila abun bazai xo maka da sauk’i ba ko. Amma sau uku ina had’uwa da khadija da mahaifiyarta a wajan rabe. Amma su ba su ganni ba. Duk fad’in k’auyannan waye bai san Rabe ba?. Bazan bari ka cutu ba, dama naso sai ka huta sannan zan sanar maka, yanayin da ake cikine yass dole na sanar maka yanzu. Aliyu ya girgiza da jin wannan labari. take har idanunshi ya sake kad’awa yayi jawur, har wata jijiyace ta faso a goshinshi. yace.

“Indai har na yi bincike na gano abunda ke kai khadija da mahaifiyarta wajan Rabe. Toh Aure ni da khadija babu shi. Yanxu mu kawar da wannan matsalar Kamilu Baba na can tana jiran in kawo mata takaddar sakinne fa. Kamilu yace.

” Ni ina ganin muje mafara wajan Iya mai Tubani. A ganina ita ce kawai za ta iya dakatar da Baba akan abunda tai k’udiri.”

“Kamilu Baba mahaifiyata ce na santa fiye da tunanin mai tunani. Iya mai Tubani kuma k’anwa ce ga gyatumarsu Baba. Baba babu wanda ya isa ya sa ta yi hakuri akan wannan sakin, kasan muguwar tsanar mahaifiyar Sadiya dake zuchiyar Baba kuwa? ina tunanin ubangiji ya bani Sadiya ne dan mu zama silar kawar da duk wani gaba. Ni tunani nake yi ko in mai da Sadiya gidane zuwa komai in ya lafa sai ta dawo, wallahi Kamilu ina son Sadiya. Amma me ka ce? Kamilu yace.

“zuwa gidanne bazai mata kyau ba Aliyu. Sati guda da.Aure a ganta a gida, Hakan zai iya b’ata mata suna. Sannan mahaifiyarta abun zai mata ciwo. Kaga da haka sai zumunci yai ta lalacewa. Mu jarraba zuwa wajan Iya. In yaso mu tafi da Sadiya. Ko a can ne sai ta zauna xuwa wani lokacin.” A hakan su ka samu matsaya. Mik’ewa Aliyu yayi yace.

“Ka shirya bari in sanar da ita ta shirya sai mu tafi kawai.” Kamilu ya dafa kafad’ar shi yace.

“Kar kayi sake lu’u lu’un da rabbi ya baka ya subce a hannunka. Ka yi iya yinka, Saki dai a hannunka yake. Kuma ka k’arfafi guiwarka karka basu damar karaya. Sadiya alkhairice.

Ficewa yayi a gidan Kamilu. Gida ya wuce da Sauri, kuma cikin k’arfin guiwar da Kamilu ya aro ya yafa mishi.

Sadiya

Ina zaune a saman kujera. ina karanta wasik’ar jaki. tare da yin lissafin dokin rano. Sallamar Aliyu ce ta katsemun tunanin da na ke yi. Idanamu muka zuba ma juna, murmushi ya sakar mun.

“Anty ki shirya za mu d’an fita yanzu. Bari na sake kaya.”

uwar d’aki ya shiga. Take zuchiyata ta shiga bugawa da k’arfi. Harya fito ina zaune a wajan cikin muryar kuka nace.

“Aliyu ka sake ni ko. Amma me nayi maka toh?” lumshe idanu yayi yace da ni.

“Ban sake ki ba Anty, babu wanda zai iya kwace mun ke. gidan Iya mai Tubani zan kai ki ki d’an zauna acan zuwa wani lokacin. ki yi hak’uri da yanayin da muka riski kan mu a ciki. amma ki sani Ni bazan iya sakin ki ba.” jikina a mace na shiga cikin d’aki tare da tattare ‘yan suturu na nasa a k’aramar jaka. mayafi na yafa na fito. kallona yayi da kyau yace.

“Baki da hijab ne?” Da mamaki nadubeshi sannan nace.

Ina da na yin Sallah.”

” Ki je ki saka shi. Daga yau karna kuma ganin kinsa mayafi. Ni namiji ne mai tsananin kishi sosai.” mamaki Aliyu ya bani. Yanda ya b’ata rai bai ko ji nauyi na ba. Yake bani umarni. Bani da yanda zanyi haka na koma na zumbulo hijab har kusan k’asa.

Bai ce komai ba. Jakar hannuna ya karb’a ya shige gaba. ni kuma ina biye dashi a baya

Ta k’ofar baya mu ka fita. Kamilu ya na tsaye a gindin bishiya yana jiranmu. Da isowarmu muka wuce. Babur muka hau har zuwa bustop. Daga nan kuma mu ka hau motar da zata kaimu Mafara k’aramar hukuma.

Ina zaune a kusa da Aliyu jikina yana gugan nashi. musamman in an shiga kwazazzabo. wani irin yanayi nake shiga in jikina ya manne da nashi. Duk da suna d’an jefa hira shi da kamilu Amma kuma hankalinshi yana kaina. Ina kallon irin satar kallona da ya ke yi. Ni kuma tunane tunane duk ya cika mun kaina. A haka har muka iso mafara.

Babur muka sake hawa har zuwa cikin anguwar su Iya. Sukam naga suna da makarantun gwamnati da ma babban Asibitin gwamnati, ga wutar lantarki.

sai kalle kalle na ke yi. Ina ganin mata da k’ananun yara. ga ‘yan makaranta an tasosu su na tafe suna wasanninsu. wasu ko takalmi babu, wasu kuma kayan makarantar duk datti. wasu nasu a yage, Abun gwanin tausayi. Ta ya ma yaro zai yi karatu mai kyau. Jikinshi duk tsami da datti, makarantar duk a rub’e ajujuwan ko bencin zama babu dana hango,ga wani zarni dake tashi na bayan gidan makarantar, wanda  kab rabin anguwar zarnin ya damesu, ina ga malamai da d’aliban cikin makarantar? Shi yasa manyan masu muk’amin k’asar suke sanya yaransu a makarantun kud’i,domun sunfi kowa sanin me suka shuga a makarantun gwamnatin nasu. Ya ilayi ka tab’a zukata shuwagabanninmu su dube mu.  a kofar wani gida muka sauka. ni dai ina biye da su har cikin gidan, sai kalle kalle nake yi. Kai kallo na k’auye.”

mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

21~22

Da sallama a bakinmu dukkanmu mu ka shiga.

Iya ta tsakar gida ta na k’wad’a zogale da rama. sai da yawuna ya tsinke da ganin wannan k’wad’on.

” A ahhhh Aure yau igiya goma sha biyu. Yaushe a gari inji mak’i bak’o. masu kwalli a ido Ai sun san da dawowarka, amma ni da yake ba’a auran dani ai saida ka yi kwantai.” Dariya Aliyu yayi ya ce.

“Da surutu dama nasan zaki tarbeni ke irin auran naki kenan. Kinga kishiyarki magana bata fiye damunta ba, amma ke magana ta yi miki yawa.” Dariya Iya ta yi. Tabarma ta nuna mana.

” Ku zauna. Kamilu baka da mutumci Ace rabon da in sanya ka a ido. shekara sama da hud’u. Tunda mai gidan ya tafi madina karatu ka d’auke k’afarka a gidannan sabida Allah dai_dai kenan?. Dubana ta yi tace.

” uhmm baiwar Allah sannu da zuwa. ganin mazajennan nawa ne yaimun dad’i sosai. Kamilu wannan itace Amaryar da aka ce ka yi?  Sai yau Allah yayi n ganta. Kai amma kuwa ka mori mace, ji mace a dire. Kamilu yace.

“Ki bari mu gaisa tukunna.  Nina soma gaisheta dubana take yi da kod’addun idanunta da baza kai zaton tana gani ba ma, gasu fici_fici kamar k’wark’wata.

“Ai wannan kamar Sadiya ta wajan Adamu ko?  Nayi matu’kar mamaki data kama sunana. Aliyu ya ce itace.

Kuka Iya ta fashe da shi, tana yi tana sharce majina, ta ce.

“Allah ya jik’an Adamu d’an boko mai mata ‘yar boko. yaro mai hakuri da yakana. kai Adamu ya sha wahala a Hannun dangi da suka sashi a gaba. Dan kawai ya auri ‘yar boko, musamman Asabe. Ni banga laifin Aisha ba. Tunda mahaifinta shi ya d’aga darajar Adamu har ya shiga gwamnati, Amma dangi sun d’aura ma Aisha wata iriyar jahilar tsana. Ke Sadiya taho in ji d’umin Adamu a jikin ki, ko na ji sanyi, haihuwa mai rana kenan.

Hawaye ne su ka soma xubo mun. A karon farko da na ji yabo daga dangin Babana kenan akan mahaifiyata, Aliyu ne ya girgizamun kanshi cikin sigar lallashi. Idanuna na lumshe. Ina isa inda take na rungumeta mu ka ci gaba da kuka.Kuka nake rerawa mai tab’a zuchiyar mai sauraro. Iya  kuwa har da fyace majina. Mun jima a haka sannan ta d’agoni tace.

“Yaushe ki ka zo Sadiya? rabona da ke tun kina ‘yar shekara goma, nayi mamaki dana ganeki ma. Ni kin sanni?” kai na girgiza mata. Wannan shine karo na farko da na soma ganinta a rayuwata.

“Assha wannan illar ta rashin zumunci ce. zumuncinnan inma ba’ayi anan gidan duniya ba, ayi a k’iyamar Allah. An hura wata iriyar muguwar gabar da tasa ‘yan uwa suka mance da Adamu, balle su waiwayi abunda ya bari. Yaron.arxiki mai kunya. Adamu shine mutum na farko da yayi karatun boko a Raquma, dama na addinin mai zurfi.  k’arfi da ya ji Sulaiman  ya hana kowa zumunci da iyalan Adamu. Shi na d’aurama laifin tunda shine babban banza. Asabe ita ba kai bane da ita. shegen taurin kai da kafiya shiya sa ta auri ubanka ta k’are a wahale a gidan haya. Sai da ubanta mai hula ya mutu ta samu matsuguni na kai.”

Aliyu yace.

“yanzu ma fa Iya sabida ita mu ka zo wajanki. Wani al’amarine ya faru ina madina lokacin.” Nan ya kwashe komai da komai ya sanar mata.

Kuka ta kuma fashewa da shi har ta na bubbuga k’afa. cikin kuka tace.

“Amma Sulaimanu da Asabe sun yi Asara, sunyi fad’uwar bak’ar tasa, zan kuma b’ata musu tura takai bango zan nuna musu ni uwarsu ce. Dan k’asa ta rufe idan Adamu iyalanshi har sun kai ai musu wannan wulak’ancin saki fa? da data amince fa. akan bare Asabe zata sa a saki d’iyar k’aninta? Jahilci masu gari, yau saina sa Asabe ta shiga hankalinta. Aliyu yace.

“yanzu haka Yaya Fatima ta na gida. Wai dole sai mijinta ya sake ta. Yau za su je gaban me gari ma.

Nan ta mik’e tsaye tace.

“Haka asabe ta sake lalacewa? ta zama me kashe kashen Aure kenan, ko hauka tayi ne?. Ku barni da su wallahi sai sun yi dana sanin zuwana gidan dan yau wallahi sai kowa ya zubar da hawaye. Kai bacci ma sai naga dama za’ayi a gidan. Dauda da matarshi kuwa duka zansa jama’ar gari su yi musu, Bansan yaushe Dauds ya zama sallamamme ba. Me gari ko ya baka Dijangala ko kar ya baka duk d’aya. ga mata dirarriya mai k’ira mai kyau ka samu. Ni bazan so a had’ata zama da kishiya bak’auya ba ma. Bazan yadda da wani k’arin Aure nan kusa ba.

Ta inda Iya ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Iya irin mafad’atan jinin sakkwatawannan ne. Har wani hunguna hancinta ya ke yi tsabar fad’a. Aliyu da Kamilu sai farin ciki su ke yi da goyon bayan da su ka samu a wajan Iya. Ni kaina banso maganar Saki ba har ga Allah. Ashe furucim saki masiface ga duk macen  da tasan darajar kanta ? Sai yanxu ne na soma shak’ar iskar duniya. Kwad’on zogalennan Iya ta sa jikarta ta zuzzuba mana tare da kawo mana Dawo  bako sukari dan su a haka su ke sha, kuma sun saba.

” ku ci abinci sai mu hanzarta tafiya. Jikina bazai daina rawa ba har sai na ga Asabe a cikin damuwar da ta fi damuwar da ta sanya ku a ciki, domun walahi sai hawayen  Asabe ya k’afe yau.  Ba wanda ya ce mata wani abun. Ni dai zogalen na ci. na kasa sabawa da dawonnan na sokotawa. Ba mu b’ata lokaciba muka kammala. Iya ta kwad’ama jikarta Hafsatu kira ta yi. da sauri ta fito tare da tsugunnawa. cikin ladabi ta gaida mu. Iya tace.

” ki ciro mun kaya kala biyu a akwati ki sa a leda maza. Idan Ramatu ta dawo daga asibiti ki ce mata na tafi RAQUMA ta kula da ku sosai. ko da Jikar Iya ta shiga ciki bata jima ba ta dawo da leda a hannunta. Ni na amshi ledar. mu ka fita.

“iya Yaya Ramatu har yanzu ba.aga mijin nata ba ko? Iya tace.

“kaidai ka bari. wannan yaro kwai tsinanne ba wani b’ata da yayi fa. wallahi talauci ne da jahilci su kai mai yawa, jahilin mutum, wallahi yafi mahaukaci ban haushi, ai duk wani sauk’i da wayewa ya k’are a wajan mutum mai ilimi, wanda yasan kanshi, dama ‘yancinshi. Meye ba’a fad’ama Ramatu ba? Fur tsuntsun soyayyaya d’ebeta ta fad’a hannun jahilin namiji, ya dinga gasata, daga k’arshe yaci biredi ya yaga leda. Ni in mun je RAQUMA ma za’a yi har da maganar tata. ace a cikin su Sulaimanu an rasa wanda zai taimaki rayuwar Ramatu. Yara goma ace miji ya tsallake ya barka da su. Ai akwai tashin hankali. A asibitin gwamnati take shara da wanke kewaye. yaran nata kuma na ce su zo mu zauna. Tunda dangin uban nasu sunki d’aukar ko d’aya, sabida suma jahilanne. dukka suna zuwa makarantar gwamnati, suna tsinto karatun a haka. sai makarantar allo da suke zuwa. Ai mu mu ka yi karatu a cikin gata. a lokacin turawa ke koyar damu,har gida suke bi suna kwasar yara, free education, kuma karatu nagartacce. Allah sarki k’awata Zainaba, bana mantawa har gidan wak’afi aka kai mahaifinta, dan ya hanata karatun boko, wani alk’ali ne a lokacin mr Bensin, shi ya taimaka mata. A sanadiyyar Zainabu karkararsu ta samu hasken ilimi yake haskawa har yanxu, har gwamnati ta gina musu katafariyar makaranta a lokacin ‘yar gaske. Iya ta shiga fece majina ta na hawaye.

Ni kaina da bansan kan labarin ba. Amma na tausaya  ma Anty Ramatu gaya. Kuma naji dad’in labarin da iya ta bamu, dan ni inason sauraron tariihi, musamman na manyan matan da suka sha gwagwarmaya a rayuwa. Aliyu yace.

“tunda aka dena taron da ake yi na duk shekara. Shikenan zumuncin ya sake lalacewa.  Iya kin tuna mun ma. makaranta na ke so in bud’e a raquma makarantar addini. Dan ina tausayama rayuwar jama’ar k’auyan raquma yanda su ke rayuwarsu da ka. Ba sani a tare da su ba kuma ba sa buk’atar saninma. Amma nasan Baba za ta iya hanani cikar burina. wallahi sabida al’ummar Raquma na dage na yi zurfin ilimin muhammadiyya ko Allah zai sa ta dalilina haske ya bayyana a cikin garin. Ta yanda nan gaba zan bud’e musu makarantar boko ma. A wannan zamanin baza’ace mun  saki hannayenmu suna bin cinyoyinmu ba, da sunan muna jiran gwamnati ta yi mana ba. Bana ko ji. Gwamnatin jirar Sokoto bata san da zaman jama’ar Raquma ba. K’ila da sun kawo mana tallafi. ba mu da makarantar boko, Bamu da ta islamiyya, ba mu da kwalta, ba wutar lantarki, ba asibiti. Ba d’in ta yi mana yawan da sai dai mu ce ni ‘yasu. ki duba fa.”

Aliyu na ke ta bi da kallo domun tunaninshi ya burgeni. Lallai Aliyu jarumi ne tunda ya ke so da k’arfinshi da lokacinshi ya k’wato k’auyan Raquma daga halakar da su ke ciki. a karon farko da Aliyu ya burge ni fiye da tunani  kenan. Harna k’udurce a raina zan bashi taimako d’ari bisa d’ari, da dukkan k’arfina.

“kai Aliyu gaskiya tunaninka da kyau. Amma yin makaranta ya na buk’atar kud’i dan gudanar da komai yanda ya dace. Allah Sarki mai hula. da irin k’udirinka a ranshi ya amsa kiran ubangiji. ya so ace ko Adamu ko Sulaimanu su kasance masu cire jama’ar k’auyan Raquma daga cikin duhun jahilci. wanda a lokacin maggi su ke siya a matsayin maganin kashin hak’ori tsabar duhun kai. amma in kana buk’atar taimako daga gareni zan taimaka.  nima lada zan samu. Ke Sadiya ki taya mijinki wannan yak’in dan watak’il sai sun yi gangamin zuwa k’one gidan mai hula. Dan ba k’aunar karatu suke ba. Dariya mu ka sa duka har da ita. Babur mu ka hau. suka fita damu daga layin su Iya. Daga nan kuma, mota muka shiga zuwa bustop. mu na sauka a nan kuma mu ka sake hawa Babur xuwa cikin Raquma.

Goggo

Goggo Asabe ta na tsakar gida sai kuka ta ke yi tana fad’a. Domun da kanta ta je b’arayin su Aliyu , bata same su ba. ihu take yi kan Sadiya ta shanye mata yaro ya zama bita zai_zai.

Sadiya

Iya ta girgiza kai ta dubi Aliyu da ni tace.

“ku soma shiga inga uban da za tai muku. duk wannan fad’an ni ta gado. Amma wallahi banayin fad’an rashin gaskiya, sabida ni ina da ilimina.”

wucewa muka yi zuwa cikin babban tsakar gida. Goggo Asabe ta na ganinmu ta nufo mu da gudu, A gaban Aliyu ta tsaya. mari ta sakar mishi, wanda sai da marin ya shafi idanunshi. take idanunshi su ka rufe ya dena ganin komai.

“Ka sake ta ko in tsine maka albarka. ka sake ta na ce.

Ke kuma gayyar asiri. tunda nake da k’usar ya’ki bai tab’a jinkirta bin umarnina ba, sai da ki ka zo kika juya mai kwakwalwa da asiri, kece harda fita tare da shi? zaki rabashi da Raquma kenan, kamar yanda uwarki ta raba Adamu da Raquma dama danginshi ko?.” Kaina na k’asa ina tsiyaya hawaye, ni abun ya isheni har ga Allah, hak’urina ya kusan gazawa. Iya ce ta shigo. Aliyu kuwa sai kallonshi na ke yi. dan naga ya kasa bud’e idanunshi d’aya kuma sai ruwa idan yake zubarwa.

Goggo Asabe juyowar da za ta yi, su ka had’a idanu da Iya.

“Yayi kyau. Asabe ashe haka kike d’ibar albarka a cikin gidannan. Ke kin isa kisa ya saki matarshi bacin yana son abunshi. Ashe zaki iya ja da hukuncin ubangiji kenan” Ko da ya ke. Ance mun kin zama mai dalilin kashe aure, Fatima gata a gabanki za ki kashe mata aure. Asabe kin yi k’arkon kifi daga ruwa izuwa wuta. kuma wallahi sai na d’auki mummunan mataki akan kowacce mace a gidannan. Har da baren da kika basu dama su wulak’anta Sadiya. Dan haka ko wacce shegiya ta bar duk abunda ta ke yi, ta same ni a b’arayin na god’i sulaimanu babban banza. yau sai an saki duk sirikan gidannan ko da uwayensu su ke tafe.”

tana kaiwa nan, ta juya izuwa b’arayin Kawu sulaiman. Wanda tunda ta soma magana hankalinshi ya tashi, dan yasan a wuyanshi zata sauke alhakin komai, surukan gidan kuwa kowa tasha jinin jikinta.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

23~24

WANAN SHAFIN NAKI NE MAMAN YASEER KI YI YANDA KIKE SO DASHI.

Jiki a mugun sanyaye kowa ya bi Iya a baya. wad’anda su ka d’aura tukunyar sanwa ba shiri su ka sauke. Dan su kansu sun san mai k’watar su sai dai Allah, dan Iya bata da wasa sam.

Iya na zaune a babban falon Kawu Sulaiman. Da sallama dukka mu ka shiga. a tabarmar da ta malale falon kowa ya nemi waje ya zauna. Iya tace.

“kai Gadanga, ka shiga b’arayin Safiya, da mariya. suma su tawo. munafukan kawai, yau zaku sha mamakina.”

Cikin  Nutsuwa Aliyu ya tashi ya fice. Iya ta dawo da dubanta gun Hasiya tace.

“ke kam hukuncinki da girma ke da wanda ya ajjiyekin, da ma ubanshi dukka. Kina tunanin har kinyi kafuwar da za ki taka Sadiya a cikin gidannan. in banda lalacewa irin ta Asabe? Toh yau a gidan ubanki zaki kwana, kije ki ci gaba da tallar kalwa.Sallamar su Goggo Safiya ce ta katse Iya. waje su ka samu a d’arare su ka zauna.

“Iya saukar yanzu?. Bata ko kalli Goggo Safiya da take tambayarta ba, magana ta soma yi kawai.

“Na tara wannan taron ne dan k’wato ma Aliyu hakkinshi da uwarshi Asabe ta ke so ta danne mai. kan cewar sai ya saki matarshi. tare da yi mai barazanar tsinuwa in ya kusanci Matarshi. Kafin in ce komai, zanso Asabe ta fad’i hujjojinta dan bazan tauye ta ba. Albarkacin nak’uda da reno. Amma ki sani ba halittar Aliyu ki ka yi ba.”

Goggo Asabe cikin sanyin murya tace.

“Iya a gaban idanki Aisha ta dinga mulkar rayuwar Adamu. Matarnan ‘yar duniya ce, kuma ‘yan shige shigen asiri ce. dad’in dad’awa kuma. Yarinyar nan Sadiya ta girmi Aliyu wayo za tai ta yi mishi a banza. ‘Yar boko ce a gwamnati take aiki a b’angaren kiwon lafiya.  ‘yan bokonnan mafi yawansu basa iya ma zaman aure. idanunsu ya gama bud’ewa, sun saba cud’anya da maza.  Iya da ba dan Sadiya ta kasa Auruwa ba. Aisha ba za ta yarda d’iyarta ta auri wani daga cikin dangin Adamu ba. Nifa cutata za’ayi wallahi in dai su ka ci gaba da zama. tsanar da Nai ma Aisha ita ta shafi Sadiya. Ina tsoron kadda ta shafi k’usar yakin shi kanshi. A karon farko kenan da yaronnan yayi abubbuwan mamaki har kashi biyu. na farko. Na bashi umarni ya sab’a. Na biyu, yayi fad’a da Dauda…..”

” Ke dakata mai ragaggen tunani. wad’annan labaran marasa tushe da madafa fa? Bari ki ji Asabe karki sake ki zame ma d’iyoyinki bak’ar  uwa mai sa a zubda hawaye. ki yi k’ok’arin zama farar uwa farin cikin ‘ya’yaye. Ba’ace kasancewarki na uwa ya baki lasisin da za ki yi tsiyarki yanda ki ke so ba. Asabe in baki janye maganar sakinnan ba. Zan iya tsine miki nima dan ubanki.” Ke wacce iriyar bijire mana ne baki yi ba lokacin da ki ka kawo mana shi mahaifin na su Aliyun? Dan dai akwai surukai nan da na yi miki figar kaza. Daudan banza kike magana dan anyi sa in sa da shi, inta kama ai sai a doke shi ma. Aliyu yace bazai yarda da marin da Dauda yaima matarshi ba, nima ina bayanshi, dan haka zan d’aukar mishi fana da kaina. Kai kuma

Sulaimanu na god’i. sunan da ya fi dacewa da kai kenan. Kana cikin mata kana haddasa husuma ko? Sabida jahilcin dake damunka. kuka Iya ta fashe da shi tace.

“Allah wadaranka Sulaimanu. Bari kaji kar na ji kar na ga wanda ya sake takura ma Aliyu da Sadiya. Ka jama Dauda d’anka kunne akan Sadiya, da matarshi ‘yar mai kalwa. Maganar Auren shi da ake yi. ni na baku umarni a dakatar da maganar Auren Sadiya ba za ta zauna da kishiya ba.

surukan gidannan kuma ina mai gargad’inku akan Sadiya, dan ba sa’arku bace. ita mai ilimi ce, wayayya wacce ta fi ku sanan rayuwa da makamar rayuwar. Dan haka ku girmamata. ke kuma Wallahi saina dake ki zan bar wajannan, saina tabbatar a gidanku kika kwana zan bar Raquma. ta mik’e ta nufi Hasiya da duka kakakaf kakakaf. sai da ta yi mai isarta ta dawo ta zauna. Ba wanda ya iya cewa komai, Dauda sai dariya k’asa k’asa yake ma Hasiya. Ita kuma sai kuka take yi danta mugun daku.

” Ke Sadiya ki sake ki kula da mijinki. A yau ba sai gobe ba. Ku zama cikakkun ma’aurata tun kafin in tafi ta sauya zane. Dan Asabe kunnen k’ashi gareta. Na rufe wannan babin. Sai maganar zama da akeyi duk shekara da aka daina yi. Toh  an dawo dashi,  a aikema kowa da kowa. da bikin sallah kowa ya hallara. Aci gaba da d’abbaka zumunci. Ko a bari in an taru a bikin Dauda, sai a tattauna. Yanzu Ramatu na hannuna da yara goma. miji ya gudu ya barsu. Sabida rashin zumunci an kasa samun mai taimakon mu. duk yawan da mu ke da shi. yarinyarnan sai aikin shara take fita ta yi. Sulaimanu ka na da ranka?”

Kuka sosai Iya ta fashe da shi. falon yayi tsit na wasu dak’ik’u. Daga bisani Kawu ya dinga ba Iya hak’uri shi da su Goggo baki d’aya. Haka ma surukan gidan su kai ta ba ta hak’uri. Da kyar Kawu sulaiman ya shawo kan Iya tayi hak’uri akan maganar sakin surukan gidan. Musamman ma Hasiya. Iya  tace.

“Nifa banyi fishi ba. Asabe ina fatan kin janye maganar tsinuwa da saki ko?”

Goggo cikin ‘dacin zuchiya da bak’in ciki mai mugun tsananin daya kasa b’oyuwa a fuskarta.tace.

” Na janye Iya amma gaskiya maganar Auranshi da khadija ta na nan babu makawa. Domun Iya, yarinyarnan tsawon shekaru ta kwashe a matsayin mallakin Aliyu. girma zai zube in aka ce daga b’angarenmu aka fasa, ki yi hak’uri Iya.”

Iya tace.

“Uban yarinya ya ce bazai aurad da d’iyarshi ga Aliyu ba, har sai ya saki ‘yar boko. Ita kuma ‘yar boko mutu ka raba takalmin kaza. bansan meyasa ki ke son wannan yarinyar ba.”

Kawu yace.

“Iya ayi hak’uri a tuntub’i iyayenta. In sun amince shikenan. in basu amince ba shikenan.

“Kai Aliyu kana son ita Dijangalar har yanzu, ba za ka yi zaman ka da zuk’ek’iyar matarka ba?” Sauke kai Aliyu yayi, sai ya ji ya na jin nauyin ya amsa tambayarnan a gabana, a yanda na lura Aliyu mutum ne da yasan darajar mutane. Kasa cewa komai yayi, sai Kamilu ne ya wakilceshi da cewa.

“Iya yana santa. Duk da akwai bincike daya taso ta b’angarenmu mu na so mu kammala tukunna.” Da fad’a Goggo Asabe tace.

“Ba mu da lokacin jiran komai. Bikinnan tare da Dauda ne, Ba za a d’aga ba. Duk wannan wata sabuwar hanya ce kuke shirin kawo wa, dan a fasa bikin kawai.”

“A ta ki cewar kenan ko? in ji Iya. ta d’aura da cewa.

“bincike halas ne a neman Aure. Je ku yi binciken ku. ku kuma ku bani waje, zan gana da ‘ya’yana.

Sum sum sum Su Bilkisu su ka fita. Hasiya na cizon yatsanta.”

dafata Bikisu ta yi tace.

“Amma wannan tsohuwar matar Aliyunnan ta ci mutumcinki. kinga a ruwan sanyi tasa an rama mata marin da mai gidanki yai mata. duka ma ki ka samu. Dubi yanda ta tara k’aton taro ta juyar ma da Aliyu k’wak’walwa har ya na so ya fasa auren khadija.” Hasiya ta yi wata dariyar mugunta tace.

” Bilkisu sai Sadiya tai nadamar shiga harkata da ta yi. ni cikakkiyar basakkwaciya ce, kuma fulanin daji. mugunta zama damu ake yi a koya. taurin kai da taurin rai, daga kan fulani ake shafa fatiha. sai na saka mu a cikin ukun da ni da ita ba za mu iya fita ba. Amma raina zai farantu, tunda tana cikin ukun. ki xuba idanu duk daren dad’ewa.

Bilkisu ta girgiza da maganar Hasiya. domun tasan karo da  Hasiya ba wasa bane, amma da ya ke ta na cikin k’iyayyar Sadiya, a wajan ta mara ma Hasiya baya, kan cikar k’udirinta.

Iya ta dubi Aliyu da ni kaina tace.

“Ku yi tafiyarku kuma. Kamilu kafin in tafi zam shigo in ga amarya.”

Fita mu ka yi. Nidai ban tsaya ba, b’arayina na wuce. Aliyu kuma na barshi a tsaye tare da Kamilu. Basket d’in abincin da na dafa da safe na tsinta a k’ofar d’akina. ko da na bud’e kular kuskus d’in ya na turiri. goge kulolin na yi da tsumma mai kyau a kitchen d’ina, miyar na bud’e na k’ara loda nama a ciki. Iya na kaima har falon  Kawu. Adda’a ta dinga zunguma mun.

dana dawo kitchen na koma tare da kunna risho. tuwon alkama da tuk’a na d’aure a leda. a k’atuwar kula na saka. sannan na fito. D’aki na shiga na zaro kud’i a jakata daga cikin kud’in da mama ta ba ni. Barayin Bilkisu na wuce da sallama. Tana tsakar gidan ta na haramar tuk’a tuwo, na shigo da sallama. Babu fara’a a fuskarta dama ban tsammaci hakan ba.

Bilkisu na ce ina zan samu kayan miya d’anye?. da baki ta nuna mun.

“Da kin fita daura da gidannan. gidan kayan miyar kenan. Da mamaki na dubeta, tare da duban yaronta da na ji ana maganar ya dawo daga almarci. yana zaune baya aikin cas bare na as. Amma ba ta ce ya siyo mun ba. yaron ma babu ko tarbiyyar gaida mutane a babin rayuwarshi. Godiya na yi mata na fice. Gidan kayan miyan na shiga da sallama. wata tsohuwa na gani  tana gaban murhu ta na kad’a miya ta tarbeni.

“maraba. me za’a baki?”

cikin Harshen ladabin yin magana da manya nace.

“mama d’anyen kayan miya na ke so a had’amun komai da komai na d’ari uku.

Sakin bulugarin data gama burga miyar ta ta yi. kayan miyan ta xuba mun cikin babbar laida mai zane zane. kud’in na bata na fita.

Cikin gaggauwa na tsaida sanwar miyata ta kub’ewa bushasshiya wacce na wadata tata da kifi bushasshe, tare da sunadarin k’amshi dangin su citta, kanunfari, d’iyar miya, tafannuwa, tumeric, corry, thiyme, da dai sauransu. kan kice me gidan ya cika da k’amshin miyata. haka kawai na ji ina samun wata nutsuwa ta na saukarmun. Zuwa bayan isha, na kammala komai, na fesa wanka, cikin shigar doguwar riga ‘yar kanti wanda ta amshe ni sosai. Sai da na kunna turare d’an tsinke, da kuma turaren wuta na hulut. na d’auki basket d’in abinci na fice. Kawu na soma kai ma na shi. sannan na wuce b’arayin Goggo Asabe. Gabana ya na bugawa. a haka na shiga d’akin da sallama a bakina. Iya ce ta amsa mini Sallamata, Goggo Asabe kuwa kawar da kanta ta yi gefe ta ba banza ajiyata.

Iya ga tuwo na kawo miki ki ci. Iya ta washe baki ta ce.

“kai Sadiya Allah yai miki albarka. A gaskiya Aliyu ya fi yaran gidannan more mace mai kirki. Sadiya ki sake hak’uri, ki yi k’o’karin ba mara d’a kunya. Da sannu za ki samu farin cikin a gidan auranki. murmushi kawai na yi kaina a k’asa, har ta kammala mun nasiharta. Sallama nai musu na nufi b’arayina.

A k’ofar d’akina na ga takalman Aliyu a gefe halamar ya na cikin d’akin. cikin sallama na shiga. Ya na zaune a k’asa, daura da shi na zauna.

Sannu da shigowa. Murmushi ya sakar mun yace.

“Yunwa na ke ji sosai, ban ko karya ba yau, sai k’wad’on da mu ka ci a zamfara, toh ina kwanciyar hankalinma na samu?”  ta ke sai na ji na tausaya mishi. ni kaina sai lokacin na tuno in banda zogalen da na ci a gidan Iya, babu abunda na ci. ko ba komai  na ga halamar zan samu sauk’i  a wajan Aliyu, dan a wunin yau da mu ka kasance a tare, na fahimci ya na da sanyin hali. kular tuwo da miya na kawo gabanshi,sannan na koma na kawo ruwan wanke hannu tare da ruwan sha. Zama nayi na zuba mishi tuwon.

Bismillah ka ci abinci. Kallona ya yi, cikin tausasawa ya ce.

“Amma ke kinci wani abu ne?” Yanda ya k’ure ni da idanunshi, sai na ji yai mun kwarjini sosai a idona. Ahankali na bud’e baki na ce

Aa ban ci ba.”

Turo abincin ya yi gabana ya ce.

“Bismillah mu ci tare Anty. Ai hakkinane in tabbatar kin ci abinci. mu ci, ko in baki a baki, sabida karki fama ciwonki?

Da sauri na zaro ido. na ce.

Aa zan ci zuwa anjima.”

Da wata iriyar murya ya kira sunana ya ce.

“Sadiya. bana son gaddama ki sa hannu mu ci, kar ki bari wannan hatsaniyar da ke faruwa ta shiga tsakanin mu. Sadiya nasan ba’a kyauta miki ba da aka had’aki aure da ni. Abun bazai zo miki da sauk’i ba. Amma idan kin bani dama, zan kula da ke kamar yanda ko wanne miji zai kula da matarshi. Ni nasan yaro ne, Amma zan iya baki abunda ki ke so, zan sama miki nutsuwa. kin amince da maganganuna?

Jikina ya mutu murus da jin kalaman Aliyu. Bayanan shi ne, ya sa na auna mizanin iliminshi. Domun komai Aliyu cikin nutsuwa da kamala irinta manyan maza ya ke yi. in yana magana nakan manta cewar ni ce gaba dashi. cikin juyayi na ce.

“Amma ta ya kake tunanin zan samu kwanciyar hankali, bacin Goggo ta na cikin fishi da mu. Aliyu ni ina jin tsoron mai fishin Goggo zai haifar mana a zamantakewarmu. Aliyu uwa ta fi gaban hankali ya kwanta in tana cikin fishi da kai. domun fishinta zai iya tab’a duniyarka. Ni abunda na ke so shine, ka je ka rok’i Goggo ta yafe maka, ko zamu ga Haske a rayuwar auranmu.

Na riga da na amshi k’addarata hannu bibbiyu, tun lokacin da lamarin ya iso mun. Babu komai, ina tare da kai, kuma zan yi maka biyayya, tare da mayar da kai jariri a cikin mazaje..”

Aliyu ya sauke ajjiyar zuchiya ya ce.

” Sadiya ke macace mai kaifin hankali da tunani. Naji dad’in yanda kika fi maida hankali kan fishin da Baba ta ke yi a kaina. Baba na bata lokacine ta d’an huce sai in je in bata hak’uri, In sha Allah. Yanzu dai mu ci abincin sai ki bani labarin wanne fannin kika karanta a matsayinki na malamar kiwon lafiya.”

Murmushi kawai na yi mishi. mu ka soma cin abincin. Nanfa Aliyu ya shiga yi mun santin dad’i. Ni kuwa murmushi kawai na ke yi mishi. Bayan mun kammala. Sai na kwashe kayan da mu ka ci abincin, tare da gyara wajan. dawowa na yi na zauna.”

“Toh ina jinki, me kika karanta?”

widwive na karanta wato anguwar zoma. ina b’angaren karb’ar haihuwa ne. na yi aiki a asibitin Aminu kano. Ina samun albashi babu laifi.” kai ya shiga jijjigawa sannan ya ce.

“uhmm. Amma me ya ja ra’ayinki wajan karantar fannin anguwar zoma?” kallonshi na yi. sannan nai murmushi na ce.

“Sabida kishin mata ‘yan uwana. Ina da sha’awar ganin mata sun samu sakewa a ko wanne fanni. nakanji takaicin ganin mace ta tafi asibiti da matsalarta. kuma ace Namiji ne zai ganta. musamman ta fannin haihuwa. Hakanne yasa na zab’i wannan fannin, kuma ina jin dad’in aikina sosai” shiru yayi ya na tunani. tare da auna kalamaina. sannan yace.”

“Babu abunda zance da Kawu Bala da Kawu Sulaiman da su ka zab’a mun mace mai ilimi wacce ta zamo uwar gidana. kuma in sha Allahu uwar ‘ya’yana, zan baki farin cikin da sai kin manta duk wata rayuwar da kika yi a baya. Kin tabbatar ma da duniya ke ‘yace mai biyayya ga iyayenta. Na tabbatar zaki zama mai biyayya ga Aliyu ko?”

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

25~26

wannan shafin naki ne Anty Hadiza Bara’u ( Gidan Iko) Alkhairin Allah ya kai miki

Sadiya zan baki cikakkiyar dama, tare da cikakken lokacin da zamu fahimci juna. Ina fatan zaki saki jiki da k’anin na ki?” Hararar wasa na yi mishi. Ashe hararar ta shigi Aliyu sosai. Take naga ya canja, idanunshi sun sake launi. Ahankali ya ce.

“Ni kuma karatun boko na iya secondry ya tsaya. wannan da na samu ma, A lokacin ina hijar gomber ne a cikin wani k’auye mai suna Bara, Gari mai arzikin kankana. Almajirci ne ya kaini. Sai na ji sha’awar karatun boko. Ina shiga kasuwa dakon kankana da abokaina, da d’an kud’in da na ke samu nasa kaina a makarantar gwamnati dake cikin k’auyan bara. tare da karatun bokon na kammala karatun almajircina. ko da na dawo gida. sai ban zauna ba, sai na shiga makarantar Arabiyya ta manya. na soma daga S S 1. Na kammala da sakamako mai kyau, ina d’aya daga cikin hazik’an d’alibai a makarantar, duk inda za’ayi musabak’a, ni suke turawa, kuma ban tab’a fad’uwa ba. gwamnati ce ta d’auki nauyin tura mu madina. dan yin digiri a Arabiyya, mu goma cib. Alhamdulllahi. Burina shine kawo canji da haske cikin wannan k’auyan, kamar yadda ki ka ji d’azu muna hirar da Iya. makarantar Arabiyya na ke so in bud’e tare da ta bokon baki d’aya. yara da safe manyan mata da yamma. maza kuma da daddare. Da fatan zaki bada gudummawarki a cikin wannan tafiyar. ta yiwu Allah ya shigo dake cikin wannan k’auyanne dan mu had’u mu fitar da jama’ar k’auyannan daga cikin duhun jahilcin da suke ciki. Rayuwa su ke yi tamkar mutanen da.” Lumshe idanu yayi tare da bin k’irjina da wani mayen kallon da saida komai na jikina ya saki.Kamar zai cinye ni tsabar kallo. kasa cewa komai na yi. Dagowa nayi muka had’a idanu.”

Hak’ik’a ni ba yarinya bace na fahimci a halin da Aliyu ya ke ciki. Sai dai kash bazan iyayi mishi komai akan hakan ba. Har zuwa lokacin xuchiyata ta na faman jinyar soyayyar Ahmad ne. Mik’ewa na yi.

Sai da safe. nace da shi, Da sauri na nufi k’ofar d’akina.

“Sadiya” ya kira sunana k’asa k’asa. Na kasa ko motsi a wajan na tsaya cak. kallon surata da Aliyu ya ke yi. k’ara ruramai wutar san kasancewa dani ya ke yi. Ban sani ba da zan tashi. jikina yayi rawa sosai. hakanne ya sa Aliyu ya kasa rik’e kan shi.

Ahankali ya iso gabana ya in healing k’amshin da ke fita a jikina. wanda ya sake shid’ar da shi. Ya kasa cewa komai sai ajjiyar zuchiya ya ke saukewa ahankali, jikinshi har rawa yake yi, amma ya kasa tab’ani. Da sauri na rab’a ta gefenshi na shige d’aki da sauri.  K’ofar d’akin na kulle har da sakata.”

Haka dai al’amura su kai ta turawa. na sake da Aliyu, mu na hira babu laifi, shak’uwa ta shiga tsakaninmu sosai. Amma Goggo ko gaisuwata bata amsawa. kuma ta dena amsar abincina. amma ban gaji ba kullum ina kai mata.

Matan gidan tsakaninsu da ni harara da habaice habaice ne kawai, ni kuwa ko a jikina, domun ba zamansu na ke yi b. A wajan Aliyu kad’ai na ke samun farin ciki. Gashi shima yanzu bashi da lokaci sosai. ginin b’arayina da b’arayin khadija su ka sa a gaba. dan an samu an shawo kan mahaifinta da kyar ya amince. yau kuma ya tafi zuwa Birni.

Ina zaune a tsakar gidana shiru bani da abokin hira, shewa da raha nake ta jiyowa a tsakar gida. Su Bilkisune suke hira a tsakaninsu, hirar da bata tab’a bani sha’awa ba kenan, rana d’aid’aikune suke wanyewa lafiya, anfi k’arkewa da fad’a da cacar baki.Ko kuma a kama wasu sunyi gulmar wasu a bayan idansu, da dai sauransu. Aliyu na tuno da yananan da mu na zaune a tsakar gidan tare muna hirarmu. Idanu na lumshe tare da tuno cewar saura sati guda Aliyu ya zama ba mallakina ni kad’ai ba. Sai na ji babu dad’i, bansan dalilin da yasa na ji hakan ba. haka nai ta tunane tunane na. Sannan na mik’e na shiga kitchen.”

Aliyu

Da sallama ya shigo gidan shi da Kamilu. da akwatuna kici kici. Kai tsaye d’akin Goggo su ka wuce da akwatunan. Tana zaune ta gansu da akwatuna. Gintse fuska ta yi. Dan ganin akwatin kala biyu daban daban.

” Ya naga akwatin daban daban Kamilu?” Goggo ta watso wannan tambayar ga Kamilu. cikin sosa kai Kamilu yace.

“Dama Baba wai da na Sadiya ne. Tunda itama ba’ai mata ba. Al’adace ta tanadar da hakan…..” shiru Goggo tayi ta na k’arema Aliyu kallo. Cikin b’acin rai tace.

“Da kyau Aliyu. sai ka had’a mata dukka tunda ita sarauniya ce. Sabida baka d’auken da mahimmanciba, Ai ba’a fad’amun ba. Ashe wannan kitumurmurar kuka k’ulla kai da Kamilu. Wallahi baka isa ba. dukka za’a kaima khadija.”

Aliyu cikin tashin hankali da damuwa yace.

“Baba kiyi hak’uri aba Sadiya nata. ki duba ki gani komai na siyo ne akan farashi d’aya ban fifita kowa ba. Baba Sadiya bazata ji dad’i ace ban mata akwati ba. Amma na yi ma khadija.”

” Lallai ‘kusar yak’i. Sadiya ta mallakeka tsoronta ma kake ji.

Hawayene su ka gangaro a idanun Aliyu d’aya.” Salatu Goggo ta zabga. mik’ewa tayi ta fice a d’akin”

Kamilu yace.

“Aliyu gudun matsala ka barma ita khadijan dukka. In yaso zan koma wajan Salisu mai kaya zuwa bayan biki, ita Sadiya sai a had’o mata wasu kayan ko a leda ne, domun in ka sa a akwati Baba baza ta yadda ba, sai a siyo a b’oye ko maman Aliyu uwargidana sai ta kawo mata a b’oye.”  cikin damuwa Aliyu yace.

“Kamilu tunda na dawo Baba ta hana mun kwanciyar hankali kawai sabida Sadiya. ita kanta a cikin tsangwamar kowa take a cikin gidannan.  nine kad’ai abokin hirarta. kuma Khadija tana ‘kara rura wutar tsanar Sadiya a zuchiyar Baba.

“Ka yi hak’uri Aliyu. k’ila in anyi auran da Baba ta ke so. za ku samu nutsuwa da ga kai har Sadiyan. ka rage damuwa a ranka. Duk ka rame ka yi duhu sabida Sadiya.” Aliyu ya ce.

“Bakasan matsayin da Sadiya take da shi a rayuwata bane. Jinta nake tamkar jigo.” Goggo ce ta shigo da masifa kamar zata ari baki tace.

“Ai sai ka mayar da ita da dawo uwarka. Aliyu ni na hak’ura da kai. na barma Sadiya kai. ka je ta maye maka gurbina. kar ka kuma zuwa dubani. nayafe bazan yi ma baki ba. Amma kuma ka dena ganin walwala da farin cikina. Tunda ka ki sakin Wannan ‘yar bokon data lashe ma xuchiya.” dam dam Aliyu gabanshi ya fad’i. kalaman Goggo sun d’umama kwakwalwarshi sosai. a take jikinshi ya soma rawa. Kuka kawai ya saka yace.

“Baba ki yi mun rai. Wallahi ina son Sadiya da yawa. Rabuwa da Sadiya zai iya zamemun matsala mai mugun girma.”

Sallamar Iya ce ta katse musu maganar su. Ajjiyar zuchiya Aliyu ya sauke, yai saurin share hawayenshi.

“Lafiya kuwa naga angon duk ya rame haka?” d’agowa yayi ya kalli Iya.

” Lafiya k’alau Iya har kin tawo bikinne?

Zama iya ta yi a k’asa. Kawu ne ya shigo. Goggo kuma duk sai ta dibibice.

anan Aliyu ya samu ya kub’uta daga hannun Goggo. Bayan an gama gaisawa. Sulalewa su ka yi shi da Kamilu su ka fice.”

Sadiya

Ina kwance akan kujera sai kuka nake yi. dan yanzu Goggo ta bar gidana. Zagina ta yi ta uwa ta uba har tana cewa bazata yafe mun ba. A wannan yanayin Aliyu ya shigo ya sameni. Yanayin da ya firgita shi. Nan ya shiga tambayata amma fur naki sanar dashi komai. Haka dole yai hak’uri ya shiga aikin lallashin. Aliyu namijine mai nuna kulawarshi ga mace. ina jin dad’in kasancewarshi a b’angarena.

An shiga hidimar biki zanga zanga babu tsayawa. Dangi sun cika gidan dam daga gari gari. Ni kuwa aiki Goggo take ta sani bako tausayina.

ranar sakun lalle na koma sabon b’arayina. wanda matan Kamilu su ka ta ya ni kwashe kaya da jerawa.

masha.Allah Aliyu yayi mana gini mai kyau da yalwa. ban d’akina mai kyau. kuma bana langa langa ba. haka ma kitchen d’ina. da b’arayina da na amarya duk an shafesu da farar k’asa.”

washe gari tun safe aketa toya wainar gero  ga fura anata dakawa. ga mata masu kid’an kwarya suna ta bugawa.Anata rawa irinta gad’a, kuma msnyan mata ne da ‘ya’ya, harda masu jikoki. suna wata waka mai taken shaudi. ga baitin wakar kamar haka.

shaudi shaudi

shaudi shaudi

shaudi ta cikin wando, bata bar yaro ba bare babba, balle jikanta abun tausai.

shaudi shaudi

shaudi shaudi.

Da abani ruwan tulu gara abani ruwan shaudi. ruwan tulu na k’arewa ruwan shaudi bai k’arewa.

shaudi shaudi

shaudi shaudi

mai gwalagwalan zan ba

shaudi shaudi

mai d’an kulu jajaye

shaudi shaudi.

Har zuwa dai k’arshen wak’ar, mata sai ihu suke yi a tsakar gida.

Tun safe rabon da in sa.Aliyu a idanuna. Sai na ji na kasance a cikin begen san ganinshi. da wannan muryar tashi, mai cike da kulawa da girmamawa.

  Misalin k’arfe biyun rana. Aka d’aura Auran Aliyu, da matarshi khadija. tare da Dauda shima da Amaryarshi.

a wannan lokaci na ji na tsinci kaina a cikin wani irin yanayin da ya, tilastamun guduwa d’aki dan in ba kuka hakkinshi. Na yi kuka mai yawan da sai da na ba kaina da kaina mamaki. wani abune yake tsokanar.xuchiyata. Kuna had’iye kukan inason fita. Sai inji na sake b’allewa da kukan. hakanne ya tilastamun samun waje in zauna.

Saida na shafe sama da awa d’aya a zaune zama mara tushe da makama. gabana sai fa’duwa ya ke ta faman yi.  Addu’o’i na shiga cabko duk wacce ta zo bakina. harda ta su shiga band’aki.

sowa na ke jiyowa daga tsakar gida. ana fad’in angwaye kun sha k’amshi.”

Aliyu

Tunda ya shigo ya ke baza ido ko Allah zai sa ya ga Sadiya. Amma wayam bata wajan, taraddadin had’a idanu da Sadiyar ya ke yi. Dangi sai sanya Albarka su ke yi. Ana cikin haka masu danki su ka iso (jere)

Aliyu da sauri yayi b’arayin Goggo, dan ya na da tabbacin tana jiyo gud’ar matan da su ka taryeshi sanda ya shigo. A k’ofar d’akin  ya tsugunna kai a k’asa,ya gaishe da Aminan mahaifiyarshi wanda su ne a cike da falon. Goggo ta zuba mai idanu, tabbas sai yau ta ga ramar da Aliyu ya yi a cikin kwana biyunnan. Bata jin kuma za ta sarara mai, har sai ya saki Sadiya. ko tsirara za ta yi yawo, ta d’aura d’amarar kwato d’anta daga hannun muguwar ‘yar bokon matarshi.”  Daga nan ya wuce b’arayin kawu, Kamilu da sauran abokan nashi suna biye da shi. Anan ya tarar da dangin mahaifinshi, da dangin Goggon ma duk suna wajan matan kawu. nan ya shige cikin kakannin aka soma barkwanci. Iya tace”

” Ba za ku yi kid’an garayar bane abokan ango?” Kamilu yace.

” Ke dai bari Iya. ya mayar mana da biki lami, ba’a tab’ayin bikin matashi a k’auyan Raquma ba’ai kid’an garaya ba, sai na shi.” Iya ta yi gud’a tace.

“kai ilimi yayi rana Wallahi, masha Allah ko kufa. rawa ai mata aka sani da shi, wak’a kuma sai ‘yan daudu.”

Nan su kai ta wasan barkwancinsu. Aliyu bai samu ganawa da Sadiya ba. dan abokai sun jashi zamfara yin cefanan shiga siyan baki.

Sadiya

 ni kuwa ina tsakar gida. an tara mun tulin wanke wanken bikinnan. har masu kawo Amarya anan su ka taddani. ina kallon Amarya ta rufu da mayafi kanta kirib a rufe. Wanke wanken na saki, na bisu da kallo har su ka shige d’akin Goggo. wasu hawaye da bansan dalilin zubowarsu ba su ka zubo mun. sun jima sosai a d’akin Goggo, sannan su ka sake fitowa, su ka wuce ni.Babu ma wanda ya dubi inda nike. Jikina a mace na kammala komai na share wajan, sannan na shige gidana. wanka nayo. riga da wandon bacci ne a jikina. Farare masu matuk’ar kyau. wandon rigar ko guiwata bai kai ba. rigar kuma mitsitsiyace mai hannun bra. Turare na cakud’a a jikina, kana na fesa na kaya. maganin gajiya na had’iya, dan iya gajiya yau na gaji matuk’a. Ina kwance na yi rub da ciki. damuwar da bansan dalilin wanzuwarta ba, gami da fad’uwar gaban da bansan ma’anarshi ba. su su ka addabeni.  Aliyu yau d’aya da na wuni ban ganshi ba, hakan ya matuk’ar jigata ni. dan Aliyu ya sabar dani, zamu zauna mu yi hira, mu yi dariya, ya taya ni girki, ga kulawa, da wani irin girma da yake bani. tabbas ina hango b’oyayyen sona da sha’awata kullum a idanun Aliyu, dama muryarshi. Amma tun ranar da na gudu na barshi a falo, bai sake yin wani abu makamancin ya nuna mun yana buk’atata ba. Bamu tab’a kwana gado d’aya ba. Na saba da shi da yawa, hancina ya saba da k’amshin shi. Ina dai kwance sai inna kamo wannan tunanin sai in sake. Ni macece mai tsananin sha’awa shi yasa na ke yawanta yin azumi. Amma na yi Auran kuma, na kasa sallamama mijina kaina. Na fiso zuchiyata ta warke fes akan batun Ahmad ne.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

27~28

wannan shafin naki ne Anty Yabi Yunusa Jibril. kin ba da gudunmawa.

Aliyu

Da misalin k’arfe goman dare, aka rako ango Aliyu. Kamilu yana biye da manyan leda har biyu. Cikin sallama su ka shiga dakin Amarya.

sun gudanar da siyan baki kamar yadda yazo bisa Al’adun gargajiya. kowa ya watse, ango ya fito dan taka ma abokan nashi. Kamilu ne ya ja Aliyu gefe

“Aliyu ka rarrashi Sadiya sosai. lallai ba’aima Sadiya adalciba, babu wani lokaci da ta samu na Amarci,Baba ta hana ayi mata lefe. Ga Amarya ta danno kai, na fahimci a halin yanzu Sadiya tafi soyuwa a ranka fiye da Khadija. Amma ka kwatanta Adalci a tsakaninsu. Kaje kar ka jima.” Aliyu ya kasa cewa komai. Jiki a mace ya koma cikin gida. d’akin Amarya ya koma, a zaune ya same ta in da ya fita ya barta, amma ta cire rufar. Da murmushi ta tarbeshi. zama yayi a kusa da’ita, bayyi aune ba ya ji ta kawo mishi runguma. sai gata  a saman kirjinshi ta na zuba mishi sambatun k’auna.

” kullum sai na yi mafarkin ganina a jikinka. yau nice zan kwana a kirjinka, ina shak’ar k’amshinka.”

Sokoko Aliyu ya ke dubanta cike da d’umbun mamakita fal cikinshi. har ta gama ki’danta da rawarta, ya kasa kamata ma. Yanzu ne ya ke sake ganin yarinta da ‘karancin shekarunta. Tuno Sadiya yayi, da cikar halittarta da kirjinta cikakku yayi. wawuyar Ajjiyar zuchiya ya saki, wanda khadija ta yi tunanin da ita ya ke yi. murmushi yai mata kawai.

“Amarya ba kya laifi. Ina zuwa, zan je in ma Yayarki sallama. Mirsisi Khadija ta yi da ita tace.

” Bari in taso, sai mu je tare in mata ya gajiyar aiki, da ta biki, ledar kajin ta d’aukar ma Sadiya nata.” dad’in hakan ya ji sosai, sai lokacin ta ga murmushinshi na asali. Ita kuma khadija da dalilinta na fad’ar zata bishin. bata k’aunar abunda zai sa su keb’e a cikin darennan da Sadiya. Dan Goggo Asabe ta yi mata jan kunne akan hakan sosai, hakama  mahaifiyarta tai ta mata hud’ubar tsiya.

Su na tafe yana d’an janta da hira. Tana amsawa jifa jifa, dan hankalinta baya tare da ita sam.”

Sadiya

ina kwance na jiyo Sallamar Aliyu, ban yi aune ba, na sake jiyo sallamar mace. Gabana yayi wata iriyar mummunan fad’uwar da sai da na runtse idanuna, dan ji nake zuchiyata ta na mun tsalle. Take idona ya cika tab da hawaye.

Hannu Aliyu yasa ya amshi ledar hannun Khadija.

“zauna bari in fito.”

Muryar Aliyu ce ta ratsa kwanyata. Khadija kuma tunda ta shigo falona ta tsure. dama ta jima da jin labarin had’uwar d’akina a bakunan wad’anda su ka san d’akin nawa.

‘kofar d’akin ya turo da siririyar sallama abakin shi, sallamar da banji sanda ya k’arasheta ba.

mutuwar tsaye yayi da ganin kyawun surata. Tim ya yar da laidar dake hannunshi. ni na mance shaf a cikin yanayin ma da nake, sabida shan iska nake yi. sai da na jiyo takun tafiyarshi, wuf na rufe idanuna tamkar mai bacci. a bakin gadon ya zauna. shuru na tsawon lokaci. Aliyu sai karema fuskata kallo yake yi. Ban yi aune ba naji hannun Aliyu a jikina, ya mirgino dani ina kallon sama. but still idanuna a rufe. rumfa yayi mun. jinayi kirjina na gugan nashi kirjin. D’an nishin da ya subce mai abakinshi, ya jefa ni a wata duniyar taurari da gajimare. tsam naji Aliyu ya matseni a kirjinshi, tare da cusa kanshi tsakankanin kirjina. shidewa nayi. ba shiri naja wani numfashi, a hankali na fesar dashi. D’ago fuskata yayi. Amma ni na kasa bud’e idanuna in kalleshi. jin d’umin numfashinshi da d’umun lips d’inshi nayi.Rik’on alewar yara yai ma lips d’ina. A mugun tsorace na bud’e idanuna, tare da k’o’karin kwatar kaina. Ina Aliyu ya yi mun rik’on da bazan iya kwacewa a hannunshi ba. luguiguitar bakina yai ta faman yi. ban dawo hayyacina ba. Sai da naji halamar yana shirin wuce gona da iri.

Kuka kawai na sakar mishi. zare bakinshi yayi a nawa, baya ko iya bud’e idanunshi. kyara mun zama yayi a ‘kirjinshi, cikin wata dashasshiyar murya mai zurfi yace.

“Ki Amince in soma gudanar da Amarci a kan ki Sadiya. i want to fill you. kallona ya ke yi kamar zai had’iye ni da narkakkun idanunshi, wad’anda su ke sake zautani a cikin darennan. Wata iriyar sha’awace take fisgata izuwa ga Aliyu, ni kuma sai kokawar tsare kima ta nake, gudun mummunar fassara. Amma inaji tamkar in mayar da lips d’inshi cikin nawa. hakanne ya tilassatamun kasa d’auke idanuna akan lips d’in masu taushin gaske.” bakin nashi yake k’ok’arin sake shigarwa cikin nawa, dan ya gane sakon da na ke isar mishi. kwankwasa k’ofa mu ka jiyo a na yi. kai ya dafe kamar mai ciwon kai. runtse ido na yi, har ga Allah an cuce ni. dan an katse mun hanzari.

Sake kwankwasa kofar   a ka yi tamkar tamkar za’a b’allata. Ala tilas Aliyu ya mik’e tsaye. Ni kuma kunya duk ta isheni, na kasa had’a ido da shi.  Ledar da ya yar a k’ofar d’akin ya koma d’akkowa. Ajjiyemun yayi a gefen gadona.

“sai da safe. zan tattala miki samartaka na, har zuwa lokacin da zaki bani kan ki, na yi miki Alkawarin ke ce mace ta farko da zan kwanta da ita. bazan miki tilasba. Aliyu mallakinki ne har yanzu, har abada. sai na isheki sannan zan samma wacce ta dace a samma za’a bata. i promise you that.”

juyawa yayi ya fita.

hawayen da suka wanke fuskata, tun soma maganar Aliyu, na share. pillow na kawo ma wani mugun cabkar da da mutum ne, sai ya samu targad’e ko tsagewar k’ashi.

Aliyu kuwa ko da ya fito falon, wayam bai ga khadija ba, bai ji wani ‘dar ba sam. dan zuchiyarshi a cike take da farin cikin, yau

Na bashi wata ‘yar dama.

maganganun da Aliyu ya fad’amun ne sukai ta mun amsa kuuwa  a kunnena. tsintar kaina na yi a mugun sha’awar da marata ta rik’e sai mugun juya mun take yi, tamkar zan mutu. duk wata daskararriyar sha’awa yau Aliyu ya narko mun ita. ya kuma barni a cikin masifa. wannan yanayin da Aliyu ya sanya ni, shine na farko a rayuwata. hakan ya tsaya mun. har ma nake tunanin mai yasa ma ban bashi kaina bane a wannan daren  ayi duk wacce za’ayi?”

Aliyu

yana tafe ya na gauraye hanyar shi. wata iriyar muguwar sha’awa ce ke barazanar fasa mishi mararshi. Da kyar ya kai kan shi d’akin khadija.

mara a hannu ya shiga d’akin yana runtse idanunshi, tare da cije leb’anshi. Khadija kuma tana tsaye sai jijjiga take yi. Idanunta cab’e cab’e da hawaye. Amma ganin halin da Aliyu ke ciki ya mantar da’ita komai. da sauri ta yi kanshi, yana shirin fad’uwa. tare su ka zube a k’asa. khadija ta sake birkita shi. rarumar bakinta yayi ya tura harshenshi a ciki. nan ya shiga rassafa khadija, ita kuwa muk’us ta yi a jikinshi, sai ajjiyar zuchiya take saukewa. Sassauci ya d’an samu daga jikin khadija. Mik’ewa yayi, tare da rik’o hannunta zuwa ciki. A bakin gado ya zauna yana yamutsa fuskarshi.

” Aliyu shine kai mun wulakanci a d’akin matarka ka nuna mata banda daraja ina amarya?

Hannu ya yi saurin d’aga mata, murya a lumshe ya ce.

“Me yasa baki soma tambayata ciwon da ke damuna ba yanzu” Ke baki isa ki hanani keb’ewa da matata ba.

Malum malum d’inshi ya zame, tare da cire dukka kayan jikinshi. daga shi sai gajeren wando da singlet. kwanciya yayi tare da juya ma khadija baya.

a zafafe ta haye kan gadon tace

” me kake nufi da nine Aliyu, naga ka juya mun baya, haka daren  farkonmu ya dace ya kasance? na yi tunanin yanda nake azarb’ab’in had’a jiki dakai, kai ma haka kake yi. Yanzu in k’awayena su ka tambayeni labari, me kake so in ce musu? ka juya baya kayi baccinka. Bayan jagwalgwani da ka gama yi. baka ji tausayin ko ka motso mun da sha’awata ba?

kuka ta fashe dashi, tare da had’e hannayenta dukka biyu cikin sigar rok’o tace.

“Aliyu raya darennan shine cikakkiyar soyayya, wannan daren, dare ne na tarihi a cikin tarwirar masoya.Aliyu ka kwanta dani dan Allah, karya zame mun abun gori a wajan k’awayena

Aliyu zuba mata idanu kawai yayi, tare da d’umbun zargin khadija a zuchiyarshi.

“Anya ya dace budurwar da bata tab’a sanin namiji ba ta yi haka a daren farkonta? daren da angwaye kan zama tamkar dodanni a idanun Amarensu, daren da cikakkiyar mace take jin tsoronshi. Anya khadija?

Duk cikin zuchiyarshi ya ke tattauna wanga batu. Jawo ta yayi kirjinshi, tare da yi mata matashi da hannunshi. Hannu yasa yana share mata hawayenta

“khadija, ba dole bane sai na kwanta dake a cikin darennan shine kika cika amarya ba. Ke baki ga banda lafiya bane? bazan iyayin komai ba.”

cikin kuka ta katseshi da cewa.

“Ni dai ka fitar dani kunyar kawayena.

” bari kiji, babu kyau tattauna wanga irin batu da kawaye, ko ‘yar uwarshi bai dace ki sanar da’ita komai akan kwanciyarki da mijinki ba. Ki kiyaye sam babu kyau. zuwa gobe inna warke sai muyi koma meye.”

kusan kwana khadija ta yi tana kuka. Aliyu tun yana rarrashi harya fita shirginta. Falo ta koma ta yi kwanciyarta cikin zabarin wayewar gari, dan sanar ma da Goggo Asabe.”

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

29~30

*washe gari*

Tun sassafe khadija ta isa b’angaren Goggo, ga jama’ar biki cike da gidan, ita damuwarta shine ta sanar ma Goggo abunda ke faruwa aima tubkar hanci tun wuri. Bayan gida Goggo ta jata, nanne ke da rangwamen jama’a”

Gashi da hayaniya gidan yau aka tashi, tsakanin Hasiya da Amaryarta.

” khadija in ce dai komai lafiya ko? naga fuskarki babu walwala ne,a matsayinki na amarya?.

hawaye ta soma zubarwa bakinta har yana rawa ta fad’ama Goggo komai”

“Baba Aliyu bai bari komai ya shiga tsakaninmu ba. tunda ya shiga d’akin matarshi, ya je ya jima, sai ya dawo mun wai bashi da lafiya. Sai a falo na kwana.”

Goggo ta dubi khadija da kyau tace.

” Kila wani asirin ta bashi. Barni da su dukkansu, yanzu ina shi Aliyu yake?

” Tunda ya yi wanka ya fice bai dawo ba.”

Goggo tace.

“Sha kuruminki zai dawo ya tadda ni har in da nake, Abunda ya ke gudunnan sai ya faru dole. Ni da nake son ganin jikokina ta jikinki.” Nan Goggo tai ta lallab’a khadija, tace ta koma d’akinta kar ai mata kallon mara kunya.”

jiki a mace khadija ta zo ta wuce su Hasiya anata rikici, har da cin d’amara ita ala dole sai ta daki amarya. Dauda ne a tsakaninsu amma furr Hasiya ta k’i ta bar fad’an

tab’e baki khadija ta yi, babu wanda ta kalla ta yi wucewarta.

mayafi Goggo ta ja, ficewa ta yi a gidan.

“me dambu ni kawai ki kaini wajan malaminnan, domun in ba tsaye na tashi ba.Sadiya sai ta raba kowa da Aliyu. gara ni in rabata da shi tun wuri, kafin zuri’a ta soma shiga a tsakaninsu.” mai dambu ta ji dad’i sosai a ranta, kuma lallai  burinta na gani tasa Asabe a uku ya kusan cika. a zahiri kuma tace.

“ni na zuba miki idanune kawai.Asabe, irin yarannan ‘yan boko sai fa kin had’a su da aikin malam. ni kaina k’arfin asiri ke zaune da ni a cikin gidannan, haka su ke bugawa su barni. Aliyun wata ran sai kinga ya yi ma Sadiyan dukan mutuwa muna nan da ke. Bari in sako mayafi mu je, ai da zafi zafi ake dukan k’are.

cikin hanzari mai dambu ta kammala ta fito.

“mu je kin ji Aminiyata.”

haka mai dambu ta kai Goggo wajan boka”

” Boka wannan Aminiyata ce, diyata na aure a hannun d’anta. Akwai d’ayar matar ta shi ne da mu ke so a shiga tsakaninsu da juna. a haddasa gaba da tashe tashen hankula a tsakaninsu.”

murmushi bokan ya yi ya ce.

” Duk yanda ku ke so za ku samu, amma aikin zai zama mai s’auki a wajanmu mai wuya a wajan ku. Dan sai an d’ebo mun gashin hammatar ita yarinyar da kuma gashin gaban mijin, toh da su za mu had’a aikin. Amma ga wannan turaren matsawar zai kwanta da matar shi wacce ya ke son, wato amarya ta tabbatar ta yi amfani da turaren wajan kwararashi a gabanta. Da zaran ya sadu da ita. waccen kuma kashinta ya gama bushewa, kafin wancan kuma ya kammala.”

Goggo ta sa hannu ta amshi turaren ta na jin dadi, tace.

“Amma boka ina zan samo gashin hammatar ita yarinyar dama dama ma nashi shi yaron zai samu. Na tanne aiki.”

“Duk yanda za ku yi ya rage naku. ta tabbatar ta yi amsani da turaren yau, zuwa gobe ya lalace, yakan d’ebe mu sama da shekaru biyu kafin mu samu nasarar samun wannan turaren.In ta zuba turaren, ta tabbatar da ita ya soma Saduwa. In ba da ita ya soma saduwa ba toh akwai matsala, wacce ba za ku ji daga gare ni ba. zaku zo ne kuna ba ni labarin abinda ku ka gani, kuma na mugun tashin hankaline., dan haka ku kiyaye.

mai dambu tace

“wannan babu matsala boka, Amarya ce yarinyar a d’akinta ya ke, ba wata matsala da za’a samu. Me ye abun hasafi?

” Bana karb’ar komai ke ma kin sani, ku je har sai buk’atarku ta biya, toh angama.”

fita su ka yi daga gidan boka, su na tafe su na hira.

“wallahi mai dambu na matsu ace dare yayi khadija ta yi amfani da wannan maganin na boka. na tsani in bud’e idanuna in ga Sadiya ta na rayuwa a cikin gidannan a matsayin matar Aliyu. mai Dambu tace.

“kwantar da hankalinki, bafa banza bane, za ki ga mai gari sai fa abunda na ce mishi. Asabe kusan ni ke mulkin k’auyan Raquma. duk wannan nasarorin a wajan wannan bokan na samu, ni na yarda da aikinshi sosai.” Goggo nan ta sake samun nutsuwa. ta na shiga gida ta nufi b’arayin khadija, keb’ewa su ka yi.

“Ungo khadija, in dai ina raye bazan bari ki yi kuka da hawayenki akan takaicin namiji ko kishiya ba. nina haifi Aliyu, amma taurin kai gare shi da zafin rai kamar wuta.”

Hannu khadija ta sa ta amshi kwalbar turarenan.

“Yauwa, kisan duk yanda za ki yi ki jawo ra’ayinshi kan ki, zan yi mai barazana da tsinuwa in bai sadu da ke ba a cikin wannan daren ba. Turaren duka zaki juye a gabanki. da ya kwanta da ke. fam fam fam, bazai sake kwanciya da Sadiya ba, kinga dole ta buk’aci saki ko?”

tsallen murna khadija ta yi ta rungume  Goggo suna dariya.

“khadija ki kula, sannan kar ki sanar ma kowa wannan labarin na fad’a miki kenan. Ba ire iren labarannan ake bayarwa ba.

Aliyu ba shi ya shigo gidan ba, sai wajajen magriba. Son ganin Sadiya ne ma ya shigo da shi cikin gidan.

b’arayin Goggo ya nufa ko zai ganta a can, sai da ya shiga ya ga ba ta nan. Gefe Goggo ta ja shi.

“Aliyu na ji duk d’ibar Albarkar da ka yi ma khadija a daren jiya. umarni na ke baka, yau in baka sauke hakkin khadija da ya rataya a wuyan ka ba. Toh Allah ya isa ban yafe ba.”

tana kaiwa nan ta wuce ta barshi da ciwon kai.

wato khadija k’ararshi ta kawo wajan Goggo dan rashin kunya?. lumshe idanu yayi, jiki a mace ya bar wajan.

Sadiya.

“Ina kwance sai tunane tunanen Aliyu na ke yi, Al’amarin da ya faru jiya a tsakaninmu ya fi komai tsaya mun.

Shigowar Aliyu na ji, da siriryar muryar shi. da kallo na bi shi. Sakata na ga ya saka, ni dai ina dankare a kan gado na, kallon mamaki na bishi dashi.

fad’owa jikina Aliyu yayi, bai bani damar furta komai ba, bakina ya rufe da nashi, tare da dannamun harshen shi a cikin bakina. Tsintar kaina kawai na yi da cabka tamkar na samu Alawa.

Na d’auka wasa ne, Ashe Aliyu da gaske ya ke yi, na kasa kwace  kaina, dan ko hannu bana iya d’agawa. Komai na jikina ya saki. cikin mintunan da ba su wuce minti talatin ba. Aliyu ya farke tantanin budurcina, na ji asabar da ban tab’a jin irinta a rayuwa ba. Na yi mamakin jin Aliyu sosai, domun ba haka na yi zato ba.

k’ank’ameni tsam ya yi a jikinshi. ni kuma sai ajjiyar zuchiyar wuya na ke ta saukewa. Sai sake gyara mun kwanciya a k’irjinshi ya ke yi. d’ago fuskata ya yi, wani hannuri, da farin ciki ne su kai ma fuskarshi k’awa. k’asa k’asa da murya ya ce.

“Ina fatan dai k’anin ki ya gamsar da ke ko? sunne kaina na yi a kirjinshi, dariya na ke yi k’asa k’asa.

“Sadiya na gode da tattalamun kan ki da ki ka yi,gashi yau na kwashi gara. na mayar da ke cikakkiyar uwar gidana. Sadiya ina sonki irin son da ban ma wata mace irin shi ba. Da sauri na d’ago. Kai ya gyad’a mun tabbacin kalmar daya furta.

“Har da khadija?

kwanciya ya gyara mun ya ce.

“khadija son yarinta na yi mata, a lokacin banda zab’in kalar maccen da na ke son rayuwar Aure da ita.

ke kuma kinfi ma irin matar da na ke burin Aure komai. Sadiya kin shigar dani wata sabuwar duniya mai.cike da haske.

marata jin ta na ke fayau. Allah yasa na yi miki ajjiyar Baby. Ina matuk’ar sonki Sadiya.

Ban ce mai uffan ba ni dai. sai kalaman k’auna da godiya ya ke ta jero mun. kiran sallar magriba ce ta katse mana hirarmu.

Ban so Aliyu ya raba jikinshi da nawa ba, Fita ya yi daga d’akin zane na ya d’aure a k’ugunshi. Da ruwan sanyi ya yo wankan shi. kitchen ya wuce ya d’aura mun ruwan wanka.

A inda ya barni ya dawo ya same ni.

“Sadiya na d’aura miki ruwan zafi, akwai taimakon da zan iya miki? dad’in kulawar da ya nuna mun na ji.

A’a zan iya kula da kaina. Ka yi maza za’a shiga sallah.”

sumbatar goshi na yayi. tare da rad’a mun wasu kalamai da har abada bazan mance da su ba. A guje ya fice, ni kuma na bishi da kallon birgewa.

Ahankali na mik’e tsaye, zafi ne na ji ya ratsa ni. A hakan na daure, ruwan zafi na juye a boket, na shiga wanka. na gargasa jikina sosai da sosai, sannan nayo wanka, na fito. zafin kad’an kad’an na ke ji, kuma bazai hanani aikin komai ba. Sallah na gabatar, ina zaune a wajan ina ragargaxo mana addu’a kan Allah ya sa wannan aure mutuwa ce kad’ai zata iya rabawa, Allah ya ba mu xuriya ma su albarka, yai mana katangar k’arfe ga dukkan mak’iyan mu, Allah ya kare mu daga dukkannin mugunta ko  sharrin bil’adama. Da dai sauransu nai ta jerowa, dan yanzu zuchiya fal take da son Aliyu. Bana fatan dukkan abunda zai kawo sab’ani a gare mu. yau jina na ke tamkar an sabunta ni. A haka har isha ta ruskeni.

misalin k’arfe sha d’ayan dare. Aliyu ya zo ga matarshi khadija. a hanali ya dinga bi da ita, har zuwa matakin k’arshe. Amma sai ya ji tamkar Reza aka sa ake tsattsagashi. ihu Khadija ta ke yi tamkar ranta ake zarewa. jini Aliyu ya soma gani ya na xuba. Ba shiri ya fita. Amma raunin da ya gani a jikinshi ya fi komai d’aga mai hankali, ga jini sai zuba ya ke yi. wani zafi da rad’ad’i na ratsa kwanyarshi. kallon khadija ya yi. jini take zubarwa sosai, tsabar azabar da take ciki har ta soma fisge fisge. Ambaton Allah Aliyu ya shiga yi, dan ya tsorata da wannan al’amari gaya.

cikin dauriya da cijewa ya matsa kusa da khadijan, ya na d’igar da jini ya ce.

“khadija lafiya wannan wanne al’amarine haka, meye wannan khadija, ciwo mu ka ji fa dukkan mu. runtse idanunshi ya yi wasu hawayen wahala su ka zubo mai, tsabar zafin da yake ratsa dukkan rassan jikinshi, ji yake kamar ranshi ake fisga. ga khadija a mawuyacin halin da ya fi nashi, ya rasa wanne taimakon zai mata. jallabiyyarshi ya zura, a daddale ya fita daga d’akin, ya na tafe ya na cije leb’e. b’angaren Anas yayan shi ya nufa. Da kyar ya isa yana yi ya na hutawa. kwankwasa ma Anas  k’ofar gida ya dinga yi da k’arfi, dan ciwon na shi sake tsananta ya ke yi. Anas ya tawo da tocilarshi mai batir. yana bud’ewa ya ci karo da Aliyu jina jina, yana jingina a jikin bango. azabar da ya ke ji a k’asanshi da mararshi, tafi gaban kwatance. ba ya jin zai iya motsa k’afarshi ma. A rud’e Anas ya ce.

“meye wannan Aliyu jini fa kake zubarwa?” Aliyu hannunshi na rawa ya d’aga jallabiyar ta shi sama. Salati Anas ya saka tare da raushewa da kukan abunda ya gani a k’asan d’an uwan na shi.

mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

31~32

Cikin nishin wahala, Aliyu ya ce.

“khadija ta na can a kwance ita ma.” Rud’ewa sosai Anas yayi, rik’e Aliyu ya yi a b’arayin damanshi, dan ya zame mai garkuwa. d’akin zaure ya kaishi, ba kowa a ciki, zaunar dashi a k’asa yayi.

“Zan je in kira maka wanzan, kafinnan zan kira maka Kawu, ita kuma khadija zan kira Baba ta dubata.” Bai ko tsaya jin abunda Aliyu zai ce ba ya fice a guje. b’arayin Goggo ya nufa. Kwankwasa k’ofar ya shiga yi da k’arfi. abunka da aikin dare. har makwabta sai da su ka ji wannan bugun k’ofa, da sunan Goggo da Anas yake ambata, Ba ma ‘yan cikin gida ba. Kawu ne da  su Dauda, da Kabiru su ka fito cikin hanzari, har da gora a hannunsu, dan su a tunaninsu ko b’arayine suka shigo musu, ga tsirarin mata da su ka tawo biki, basu koma ba, ciki duk ya d’uri ruwa. Ji yayi Goggo na bud’e sakata, ta na mita. Kawu ya hasko Anas da tocilarshi yace.

” kai Anas lafiya kuwa?

da sauri ya isa gaban kawu, daidai fitowar Goggo.

“Ba lafiya ba kawu, Aliyu ya na cikin d’akin zaure, rai a hannun Allah sai zubar jini ya ke yi, Yaji ciwo faca faca haka matarshi khadija ma a cikin uquba yace mun ya barota.” ras Goggo gabanta ya fad’i taji wani abu ya tsirgo daga k’afarta zuwa kwanyarta, da sauri ta matso tace.

“Aliyu fa kace Anas?

“Eh Baba, ki je wajan khadija, kawu ku zauna dashi, zanje wajan malam wanzan yanzu.  A wajan ya tafi ya barsu cikin taraddadin abunda ka je ka zo, Goggo duk ta bi ta rud’e. Babu shiri ta fad’a d’akin da khadija ta ke kwance a cikin jini male male ta taddata, sai risgar kukan azaba take yi.

kuka Goggo ta fasa, tallafo khadija ta yi, wacce ta gama galabaita ta fice a haiyacinta.

“Khadija me ya faru aka samu matsala? na shiga uku na, duk abunda ya faru da yaronnan ni na jawo mishi. me dambu ta cuce ni da ta bani gurguwar shawara. A matsayina ta uwa, za’a had’a baki dani a kassara rayuwar yarona mai tsananin yi mun biyayya. Kuka take yi sosai. khadija ba ma ta gane sam me ta ke cewa. Bilkisu ce ta shigo da sallamarta. Amma gani halin da khadija ta ke ciki da yanayin da take ciki ta girgiza  sosai, hankalinta yai matuk’ar tashi.

“Baba cewa na yi ko a d’aura ruwan magarya da lalle a wuta ne, shima zai taimaka mata. Abun yazo musu da tsautsayi sosai, ko ta sha maganin daya fi k’arfinta ne k’ila. Goggo ta na hawaye, cikin girgiza kai na nadamar da bata da amfani tace.

“Ki d’aura Bilki. Amma ba abun da kike tunani bane wannan. dubi jini fa faca faca a d’akinnan. ko a wanne hali Aliyu ya ke ciki shi kuma oho. Bilkisu bata ce komai ba, ta fita. kara ta had’a a murhu. ta d’aura tukunyar ruwa. ganyen lalle da ganyen bagaruwa, da ganyen magarya ta zuba a cikin ruwa. Sai da yai ta tafasa, sannan ta juye a kwatanniya. ta surka yanda khadija zata iya shiga. D’akin ta shiga da kwatanniyar.

“Goggo ko za ki koma d’akin ki, zan kira Hasiya ta taimaka mun.” Goggo bata ce komai ba ta fice tana sharce hawayen da su ke ta sabunta kansu.

Hasiya Bilkisu ta fita ta kira. A cikin ruwan zafi su ka sa khadija, ihu ta zunduma cikin muryar galabaita. Haka dai su ka tsaya a kanta akai ta canja mata ruwan.

Babu laifi a cikin kaso d’ari, kaso talatin na zugi da rad’ad’in da yake damun ta sun ragu. jinin ma ya koma zuba kamar yanda mace mai al’ada jini ke zubar mata.

k’unzugu tayi, Bikisu ta taimaka mata ta saka wata doguwar rigar atampa. Amma ji take tamkar gabanta zai jijjigo ya fice ne.

Goggo kuwa ko da ta koma d’aki ta kasa zama sai zurga zurga take ta faman yi. fita ta yi, zuwa d’akin zaure.

kawu ne ya lek’o”

“Ya ake ciki Yaya, sun iso kuwa?” Ajjiyar zuchiya kawu ya sauke, cikin damuwa yace.

“Ba su iso ba tukunna, gashi yaron ya na cikin rad’ad’i mai azaba, rauni  a wannan wajan ba’abu bane na wasa. Amma Asabe ko mai ya faru da yarannan?” shigowar su wanzan ce ta katse su.

shigewa su ka yi aka bar goggo a tsaye. Aliyu yana zaune kamar ‘dan shayi, yakan cije lebenshi, kai da gani kasan ya na cikin azaba.

wanzan yayi duban da duk zaiyi. ya ciro wani koren magani yace.

“Anas kawo ruwan d’umi a kofi yanzu. fita Anas yayi a d’akin. Wanzan ya goge jinin dake zubowa a jikin Aliyu, ya barbad’a mishi magani a wajan da ya kwaile, ya yi jawur, fatar wajan ta sab’ule. wani zugine ya shiga kwakwalwar Aliyu,na azabar wannan magani na wanzan. take jinin ya tsaya tsak.

dawowa Anas ya yi da kofi cike da ruwan d’umi. magunguna wanzan ya zuba a cikin ruwan, Aliyu ya mik’a ma kofin ya ce.

“kafa kai kasha maganinnan zai taimaka maka wajan rage rad’ad’i, bacci zai d’ebeka, sai ka huta.”

Hannu Aliyu ya mik’o ya amshi kofin maganin. kafa kai yayi, bai d’ago ba sai da ya shanye tas.

“Sannu Allah ya yaye. ga wannan maganin kullum da safe a dinga basu a cikin ruwan kokko suna sha.

Amsa Anas yayi, wanzan ya kuma mik’o mishi wani k’ullin  maganin

“wannan aba mata, kamar yanda na barbad’a mishi, itama a barbad’a mata, zan had’a mata wanda za’a bata yanzu. In sha Allah, za su samu sassauci. gobe zan dawo in duba su, da wasu magungunan ma, har zuwa su warke.

magungun da ya ha’dama Aliyu, irinshi ya had’ama khadija a kofi yace a zuba ruwan d’umi a bata.

tare da Kawu su ka fito, Anas kuma ya tafi ya kai maganin khadija, Dauda ke zaune da Aliyu da baccin wahala ya kwashe shi a zaune.

“Agaskiya malam Sulaimanu akwai matsala tattare da lalurar yaronnan Aliyu, domun abune mai wuya ace gabanshi zai tashi har ya yi aiki. Ba lalle bane har ya iya samun magaji. raunin yayi yawa, sab’ulewa fa, ga wasu wajan sunji raunin da yawa. Amma kar ka fad’ama mata. Allah ya kare gaba, k’una babu kyau.” Kawu ya yi shiru kai a k’asa ya na nazari akan maganganun wanzan, can ya nisa ya ce.

“yanzu wanzan babu wani taimako kenan daya dace a bashi, yaronnan in haka ta faru, rayuwarshi durk’ushewa za ta yi, yana matashi mai k’arancin shekaru ace gabanshi ya dena aiki,ko bazai haihu ba. Ai za’a shiga mummunan tashin hankali da damuwa. wanzan duk wani abunda ya dace na magani da kulawa a mai.” Shiru wanzan yayi cikin tausayawa yace.

“zuwa wayewar gari, zan lek’a jeji. zan harhad’o duk wani kauci da ya ke da nasaba da wannan lalura, zan d’aura shi akan magungunan hausa. in Allah yasa da rabon farfad’owar abun, sai ka ga ya farfad’o” Sallama wanzan ya yi ma kawu. shi kuwa kawu yafi sama da awa d’aya a inda  wanzan ya barshi, ya shiga rud’u da tashin hankali. ya na mamakin garin yaya su Aliyu su ka k’one daga shi har matar tashi.”

“Yaya, lafiya, mekakeyi anan?” Su Goggo Safiye da Goggo mariya, da Goggo Asabe ne suka iso gabanshi.

Juyowa yayi ya kallesu, cikinshi a matuk’ar mace. Bayanin da wanzan yayi mishi yanzu, ya zayyana musu suma.

Goggo Asabe babu abunda ta iya cewa sai kuka, tasan ta zalunci d’anta. Gashi ta jefa shi a cikin mummunar lalura, mai cike da tashin hankali, yaya zata iya wanke laifinta? Ji tayi wutar tsanar Sadiya na sake ruruwa a zuchiyarta, domun duk sabida k’iyayyar da take ma Sadiyanne ya ja wannan abun. yanzu kam lokaci yayi da zata tasanma cin mutumcinta har sai ta yi zuchiya ta bar auran. Allah Allah take yi gari ya waye ta je wajan mai dambu, su san nayi. Goggo mariya tace.

“wannan tashin hankali da mai yayi kama, bama fatan haka ta faru, zan je k’auyan me gidana, zan karb’o mishi magani, a wajan wani shahararren mai bada magani ko za’a dace.

Goggo Safiya tace.

“Amma Yaya kar’a sanar da kowa wannan lamarin. Ni ina zargin Sadiya da sa hannunta a cikin wannan ciwon. Asiri k’ila ta yi, danta lalata musu rayuwa, uwarta ma fa haka take muguwa, in ba asiriba me yasa ita hakan bai faru da ita ba, sai khadija?.”

Kawu yace

“Asabe kiyi hak’uri, karki d’aga hankalinki. Ba na fad’a miki wannan abun bane, dan ki tayar da hankalinki ba. na fad’a miki ne, a matsayinki na uwa dan ki san da zaman hakan.” kiran sallar  asuba su ka soma jiyowa. Barin wajan su ka yi, kowa ba guiwa.

Anas ne ya ta fi b’arayin Sadiya dan sanar mata meke faruwa.

Sadiya

fitowa ta kenan daga ban’daki, sai naji ana doka mun sallama. Cikin fad’uwar gaba na so jin waye.

“Anas ne, Aliyu ba lafiya yana d’akin zauran su Baba. Ki je ki zauna dashi, za mu ta fi masallaci. Rass gabana ya fad’i. Rashin lafiya, mutumun da muka rabu da shi cikin farin ciki. Anas tuni har ya yi gaba. A rud’e na koma ciki, hijab d’ina na d’auka na fita cikin sauri.

Da sallama na shiga d’akin, Aliyu ya farka ya na kici kicin mik’ewa amma ya kasa. Da sauri na k’arasa nasa hannu dan in taimaka mishi ya tashi.

Kai ya girgiza mun halamar  a’a. zamewa yayi da dabara ya koma. Dubana yayi idanunshi sun kad’a sun yi jawur yace.

“k’addarace ta same ni Sadiya. Bansan dalilin faruwar hakanba.  d’an tsumman da ya rufe jikinshi da shi ya yaye mun. tocilar dake cikin d’akin na jawo, tare da haskawa.” zare idanu na na yi waje. take na soma zubar hawaye. cikin gijijicewa nace.

“Aliyu k’onewa kayi garin yaya?”

Labarin duk abunda ya faru da su ya bani turyan turyan.

“Ki yi hak’uri Sadiya mu d’auka wannan k’addararmuce, bana son ganinki a mawuyacin hali plz. Shesshek’ar kuka na ke yi na ce.

Kayi hak’uri, amma bai dace ace irin wannan ciwon ana zaune a gida ba. Aliyu ka tashi mu je Asibiti. plz” Hannuna ya rik’o yana d’an murzawa a hankali yace.”

” ki kwantar da hankalinki Sadiya na. dama ina jira ki zo ne, sai mu tafi, ki kaini Asibiti, nasan zako iya kulawa dani, amma nasan ba lallai bane su Baba su yarda da hakan.” Matsawa nayi kusa da shi dab, sumbatar leb’enshi na yi. A take ya lumshe idanunshi. murmushi mu ka sakarma juna. Rarrashinshi na shiga yi, tare da bashi baki. Lamo yayi a jikina. Sai can ya ce.

” Toh taimaka mun in tashi, In nayi sallah sai mu tafi kafin su sani ko?. mik’ewa na yi, na kamashi. da taimakon Allah har zuwa b’arayinmu. Nina taimaka mishi ya d’auro alwala. a zaune akan kujera yayi Salla. Ni kuma kaya na sake na d’auki jakata na fito.

“Akwai kud’i a k’aramar jakata Sadiya. Ki debo mu rik’e. Komawa ciki na yi na bi umarnin abunda ya ce mun.

“Ki je ki kirawo khadija mu tafi, dan itama tana cikin mawuyacin Hali, sai Kamilu ya taimaka miki. 

Toh. kawai na ce mishi na fice.

Kamilu na je na soma kirawowa. wuce ni ma yayi da sauri, ni kuma ta k’ofar gaba na biyo. da sallama na shiga d’akin khadija. Bilkisu ta na zaune tare da ita.

“Ya mai jikin Bilkisu?” Babu yabo babu fallasa tace.

“Ga jikinnan tana jin jiki, wannan lamari duk mai hannu ya ciki Allah ya toni airinshi.” kallon khadijar na yi, tana kwance ido biyu, Bilkisu kuwa banza na ba ajiyarta. nace

“Sannu Allah ya baki lafiya. Zaki iya tashi muje Aliyu nasan ganinki?” Cikin yamutse fuska ta soma yunk’urin mik’ewa. Amma sai ta kasa. Taimaka mata na yi, na mik’ar da’ita tsaye. mayafinta dake kan gadon na yafa mata. Tana rik’e a hannuna har zuwa b’arayina. Ba tare da b’ata lokaciba mu ka fice ta k’ofar baya.

Babur biyu mu ka samu, Kamilu yasa Aliyu a tsakiya, ni ma nasa khadija a tsakiya.

Sun sha wahala sosai, kafin mu isa bostop. kasancewar yau talata, ranar kasuwar mafara ke ci. Mota ba wuya, kuma nan da nan take cika. Muna isa mu ka samu mota mu ka shiga. Kan Aliyu ya na kafad’ata. Hannunshi kuma yana ta bayana ya rik’emun kuguna yana d’an matsamun a hankali. Amma da ganin yanayin shi, jiki ya ke ji. Dauriyace irinta jaruman maza. Amma khadija kuka take yi ita sosai.”

Goggo Asabe, tana yin sallah ta fice a gidan, sai wajan mai dambu.

“Lafiya Asabe irin wannan fitowar duku dukun?

“Ga yaranmu can rai a hannun Allah mai dambu, boka ya cuceni, ya mayar mun da yaro ba namiji ba. Gabaki d’aya yaran, gabansu ya lalace.”

K’irji mai dambu ta dafe, tace.

“Nashiga uku har da khadijar abun ya shafa. ya boka zai mun haka?” Sororo Goggo tabi mai dambu da kallo, ita kuwa mai dambu bata san ma ta furta wannan furucin ba.

“Ohh mai dambu, kinso komai ya k’are akan shi Aliyun ne? baki da laifi ni ce na zama lusarar uwa mai yima d’an cikinta asiri. In da iyaye za su ji kuskuren dana aikata, nasan za su tambayeni, ina wannan son na uwa da d’a na jefar dashi. kaicona, mai dambu.

mai dambu ta zulle tace.

“Ba abunda ki ke nufi bane Asabe. wato yaronnan dan rashin Adalci sai da yayi tarayya da Sadiya, bacin a d’akin khadija yake? Asabe aiki ne ja a gabanki, ina yaronnan ba haka aka bar miki shi ba.

“me dambu, abunda yake gabana yanxu shine, mu tafi wajan boka ya warware wannan asirin da yai ma yarannan.

mayafi kawai mai dambu ta yafa su ka fice a gidan, sai gidan boka.”

Mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

33~34

“Boka ta fa b’aci, yaronnan sai da ya sadu da d’ayar matar tashi, sannan ya je ga d’ayar. Yanzu haka dukkansu suna kwance, jinya su ke yi, sosai ga zubar jini, muna cikin tashin hanali mara misaltuwa.”

Dariya boka ya saki, yace.

“Dama ni nasan da wuya su tsallake, laulayine da asirin sosai. gashi da wuyar karyuwa. Aikine a gabanku ja. Domun har sai furen da shine mahad’in makarin, asirin ya fito. Kuma sai shekara ta zago, da damina yake fitowa.”

Goggo Asabe wacce ta kasa magana tun zuwansu tace.

“shi yaron fa, wanne taimako za’a bashi?”

“Ai tashi ta k’are, shi da kwanciyar Aure kuma, sai a mafarki. maganin   kashe namiji mus yake yi, sai dai ha’kuri.” wasu hawayene suka shiga sunturi a kumatun Goggo, tana mai nadamar kuskuren data tabka. Mai dambu duk da dai ba ta so, abun yai tsanani haka ba. amma taji fari a ranta sosai, kuma kad’anma Asabe ta gani indai itace. A nata wautar tana ganin kamar Sadiya bazata amince ta zauna ba.

magani ya mik’o musu.

“Ga wannan, a samu bado a dafa musu da shi, sai su cinye badon, su kuma shanye romon. Za su samu sassaucin d’aukewar zafi.”

Jiki  a mace su ka fito

“Mai dambu ki kaini wajan wani bokan ko za a dace ya warware wannan asirin yaronnan ya samu zuriya. Na cuci kaina dana biye miki, mu ka zo wajan boka. na gwammaci da dole na yi mishi ya saki Sadiya, ko na fatattaketa da kaina, ai ina da wannan k’arfin.

“Haba Asabe, taya zan cutar da mijin ‘diyata da gangan? Ni kaina bansan hakan bane zai faru. Kina ji fa, itama kanta a cikin hatsarin take, tunda shekara guda za ta yi a cikin ciwo.”

“Shifa da rayuwar duniyarshi na lalata mishi fa? mai dambu na yi nadamar saninki ma a rayuwata, Allah ya tsine miki, ke da halinki, da masu irin muguwar nifak’a irin taki, tsinanna matsiyaciya”

A wajan Goggo Asabe ta tafi ta bar mai dambu. Mai dambu kuwa sai kiran sunanta take yi.

“Haba Asabe, fishi ba naki bane a cikin wannan halin. ki biyo ni mu je wajan fa’da da cikawa.”

Goggo Asabe, ba ta da mafita. Haka su kai ta zagaye bokaye da ‘yan tsibbu, har wajan ‘yan bori sai da su ka je. Nasarar samo makarin Asirin khadija kawai aka samo. Amma Aliyu magana d’aya ake yi, cewar gabanshi har abada bazai sake aiki ba. Iya tashin hankali Goggo tana cikinshi.

cirko cirko su ka samu mata da mazan gidan. Gabanta ne yai mummunan fad’uwa.

“Sun mutu ko? Allah sarki Aliyu ka yafe mun. mai dambu cikin kuka tace.

“Shikenan khadija ashe hanyar Ajalinki kenan.

“Ba fa mutuwa su ka yi ba”  Kawu ne ya katse musu, sambatun da su ka shiga yi. tsit su ka yi.

“Ba mu gansu bane, daga Aliyun har khadija, Sadiya ma ba ta nan.

Abokin su Aliyu ne Bilya ya shigo, cirko cirko ya samu jama’ar gidan. Bayan ya gaishesu ne yace.

“Kamilu ne ya bani sak’o in sanar da ku, sun wuce babban Asibitin cikin gari, domun ciwon bana gida bane.” Godiya kawu yai ma Bilya.

“Ni nasan wannan matar tashi uwar kilbibi ita ce zata kawo wannan gurguwar shawarar, wannan ciwon ai ba na asibiti bane.” Kawu ya ce.

“Ba komai, kai Anas sai ka zo mu tafi, zamu dawo da su gida, ga wanzan ya kawo  magunguna. Sadiya kuma sai na ci mutumcinta baza ta zo mana da iyayin zuwa wani asibiti ba. Gargajiyar mu ta ishe mu. mutane nawa ne su ka kasa warkewa a asibiti, kuma su ka

 warke a gargajiya.”

SOKOTO GENERAL HOSPITAL

ba mu sha wata wahala ba, aka ba su Aliyu gado. shi ya na b’angaren maza, ita kuma tana b’angaren mata. Likocine a kansu duka, ana kan binciken gano kan matsalar dan maganceta. Ni kuma na kasa zaune na kasa tsaye. Ni ce a b’angaren mata, ni ce a b’angaren maza. Haka nai ta zurga zurga. likitan dake duba khadija ne ya soma fitowa. Binshi nayi, nace da Kamilu.

“Ka tsaya a k’ofar d’akin da Aliyu ya ke ciki, ko likitan zai buk’aci ganinka kafin in dawo.

A office na samu Dr yana rubuta wasu allurai da magunguna.

mik’o mun takaddar yayi.

“A gurguje, ga Allurai da magani ki je kantin maganin dake cikin asibitinnan sai ki siyo. ana buk’atarsu da gaggawa.” Amsa nayi na fita. Ban samu magungunan a cikin asibitin ba, sai da nai doguwar tafiya. bayan na kawo ma Dr magungunan, da alluran, sai kuma na je na bud’e ma su fail a asibitin.” Dawowata kenan. Dr ya fito daga d’akin da aka shiga da Aliyu. yace.

“D’aya ya biyo ni, d’aya ya zauna da shi.

Ni na bi Dr dan inaso sanin meke damun Aliyu.

“Madam da me k’aninki ya k’one, ruwan zafi ko mai? shiru na yi na wasu mintuna. Bayani na yi mishi Dalla dalla kan abinda ya haddasa wannan ciwon. Kai ya girgiza yace.

“Wala Allah ta yi cushe cushen magungunan da mata su ka saba yi da sunan maganin mata ne, shine ya haifar musu da wannan matsalar. Ya samu rauni da kyailewar fatar wajan, fatar da take ba abun kariya ta sab’ule, abune mai wahala ace, ko zai iya gamsar da mace, ko da zai yi d’in, zai zama very wick. But za mu d’aurashi akan magunguna na sha da shafawa. Sannan kuskurene, wannan garin maganin da aka barbad’a mishi, domun da ba dan kunyi sauri ba. infection zai iya shiga ciwon, ya iya haifar mai da daji. Zan baki ki je phamacy a siyo Allurai da magunguna, ki same ni a d’akin.” Jikina a mace na fita, na sake shiga cikin gari na siyo magungunan da alluran na dawo.

Aliyu ya na kwance, amma idanunshi biyu. d’akine da ba’a cika barin mace ta shigo ba. domun maza ne a d’akin, yawanci masu d’auke da lalurar ciwon gaba ne, da masu infection, wasu ma harda robar fitsari a jikinsu. Naga Aliyu ma an sa mishi robar fitsari. Dr na kanshi.

ledar hannuna na mik’ama Dr.

gefen Aliyu na dawo. Hannuna ya rik’e dam a cikin nashi, bai ce komai ba sai ido da ya kafamun.

“Sannu da d’awainiya Sadiya, Allah ya saka miki da aikhairi.” Kamilu ke magana. da ameen kawai na bishi.

Allurai aka ma Aliyu, sai magani da aka bashi na had’iya, kana Dr ya shafa mishi tobe.

“A lemo mishi Abinci, domun zuwa nan da wasu mintuna zai samu bacci.” Kamilu ne ya mik’e ya ce.

“Bari in nemo maka abunda zaka ci ko” Na yi saurin cewa.

Bari in nemo mishi, zan dubo Khadija daga nan.”  Fita na yi daga d’akin na lek’a dakin da khadija take, a zaune na tarad da ita. Nose na d’aura mata ruwa na biyu.

“Sannu yaya jikin? Kau da kai ta yi tace.

“likitoci tun d’azu su ka ce a nemo mun abinda zan ci, sannan likita yace ya na son ganinku.

juyawa na yi na fita. tea da biredi kawai na iya samo musu. Akwai jerin masu sai da abinci ta waje, amma ban gamsu da tsabtar abuncin ba. Aliyu na soma kaima, na tsuguno daidai kunnenshi nace

“Zan je in zauna da khadija, ba daidai bane a barta ita d’aya, kuma likitanta ya na jirana. Sannan inaso in ta samu bacci zan d’an shiga cikin gari dan Allah.” Hanuna ya rik’e gam yana girgiza mun kai.

“No Sadiya kasancewarki na k’aramun lafiya, ki je dai ki ga Dr ki dawo. Baxan jure rashin naki ba.

kan shi na shafa cikin sigar lallashi.

Toh na ji, bari in je in ga Dr din zan dawo.

Ahankali nake tafiya, harna fice a d’akin, dan na gaji sosai. wajan Dr’n khadija na isa.

“Dr gani, na shiga d’azu take fad’amun sak’onka. d’agowa yayi ya kalleni.

“Eh hakane, inaso in san meye abunda ya faru da ita? dan nasha samun ire iren casses d’innan. Yanzu haka a d’akin da take, akwai mata fin goma, masu d’auke da lalurarta. Sakamakon wata masifa da ta b’ullo na magungunan mata da ake ba ku ku dinga cusawa a gabanku, kuna kashe kanku da mazajen ku da magungunan da dayawa ba’asanma dame ake had’asu ba. wata baiwar Allah na ta ke d’akin jinyar take sanar dani, wai kashin raqumi ne ta cusa a al’aurarta ya haifar mata da mummunan matsala kwananta talatin a cikin asibitinnan tana jinye. Shima kuma mijin nata, yasha jinyarshi, dan gabanshi tsattsagewa yayi. Ya kamata fa ku hankalta da kyau mata.

Ajjiyar zuchiya na sauke, domun na gamsu da maganganun Dr, kuma ina tunanin abunda ya faru kenan da su Aliyun, dan ni a daren lafiya lau muka rabu.

Dr ayi ha’kuri, Amarya ce, wata k’ila tasha abunda yai mata yawa ne. yanzu haka mai gidan nata yana d’akin jinya a wannan asibitin. Amma wanne magunguna za’a d’aurata akai?

“mu na ta k’ok’arinmu dai a kwai tesses da mu ka yi, basu fito ba tukunna. An d’aurata akan magani, da mayukan shafawa, yanzu jinyar raunin da taji zata yi, dan raunin da yawa.”

godiya nai ma likita. na koma wajan Aliyu.

Kawu da Anas na gani a d’akin, sunyi tsaye akan Aliyu sun balbaleshi da fad’a. Isowa ta wajan yasa, fad’an da kawu ya ke yi, ya dawo kaina. Har marina sai da kawu yayi, ya zageni ta uwa ta uba. Gefe na koma kaina a ‘kasa ina shirgar Hawaye. Ala tilas su ka tursasama Aliyu sai ya tashi sun koma gida. Aliyu shi kuma yana ta k’ok’arin fahimtar da su Amma fur Kawu ya ki. Dole muka ne mi sallama, mu ka koma gida.

Goggo ta balbaleni da ruwan fad’a, ta uwa ta uba itama tai mun.

D’akinta ta buk’aci Aliyu ya koma da zama, khadija kuma mai dambu ta tafi da’ita jinya gida.

Magunguna kala kala na gargajiya ake ta d’irkama Aliyu. jama’ar k’auyannan sai tururuwar zuwa duba Aliyu su ke yi. Ni da Aliyu sai kallo, dan Goggo ta kafa ta tsare. Kullum wanzan yana zuwa duba lafiyar Aliyu. magunguna dai yana shansu sosai.

*BAYAN WATA D’AYA*

har zuwa lokacin Aliyu jinya ya ke yi, amma dai jiki da sauk’i ya na ta warkewa.

kamar kullum yauma ina zaune a gaban Aliyu Goggo bata nan, ta je dubo khadija. hannuna ya na cikin na Aliyu ina wasa da shi, shi kuma sai jawo ni jikinshi ya ke yi.

Ka yi hakankali, kar ka fama ciwonka fa.” murmushi yai mun yace

“Ina kewarki ne sosai, kuma na yi na yi da Baba ta barni in koma d’akin ki, amma fur tak’i amincewa.”

Tsoro take kar mu keb’e mu famo ciwon da rashin hak’uri. Inka warke ai shikenan. Amma ya kake jin jikin naka? yamutse fuska yayi, tare da yaye mun tsumman da Anas yake rufa mai. Babu laifi ciwon na warkewa, har ya soma b’awo b’awo. Kuma nima akwai had’i na musamman da na yi mishi, dan farfad’o mai da kuzarinshi, a islamic kemist na harhad’o gasu kamar haka.

man zaitun

man habbatus sauda

man tafarnuwa

man kwakwa

man rid’i

zuma farar sak’a

garin hulba

da man shi

sai garin b’aure

da

garin ruman

dukka na cak’ud’a waje guda, nake bashi babban cokali uku da safe kafin ya ci komai

maganine sadidan, wanda yake farfad’o da sha’awar d’a namiji, kuma ya ke k’ara masa lafiyar wajan, har da ma k’arfi.

masha Allah dan muna ganin canji, dan in ina tare da Aliyu, yana jin feelings, kuma yana nunawa, amma ba sosai ba. Babu wanda yasan wannan batun, wannan tsakaninmu ne kawai.”

Gidan su Khadija

Goggo ce a zaune a falon mai dambu.

“Sai yaushe wai yarinyar nan zata koma d’akinta ne mai dambu? naga ai jikin fa da sauk’i, yaci ace ta koma ai ko? amma kin mun shiru sabida Allah fa.”

mai dambu ta b’ata fuska tace.

“Toh Asabe, ki bari wannan yaro ya samu ya warke mana, ba gara tana gabana ina ganin komai ba. Kofa ta koma gidannan sai dai kawai ta yi zaman hak’uri, sabida yaronnan fanko ne.”

wannan magana ta daki Goggo Asabe sosai, cikin zafi tace.

“Fanko fa ki ka ce mai dambu, har Aliyu ya kai matakin a soma yi mishi gori, sabida asirin jikin naki ‘yar ya karye ko? Da kyau, ai na jima da gane duk take taken ki, nason ganin kin hana khadija komawa d’akinta. Da kyau Mai dambu, kuma kin ban mamaki, bayan da duk shawararki nayi amfani har kika jefa mu a cikin wannan halin shine yanzu kike son zuk’ewa .

mai dambu tace

“Amma Asabe ni kin ban mamaki ma da har kike tunanin wai khadija za ta komawa Aliyu. Tsakani da Allah auransu bazai ci gaba ba, mahaifinta ma haka yace. Babu fa iyayen da zasu amince akai ‘yarsu, wajan mijin da bazai iya gamsar da ita ba. Ai aure baya yiwu ne sai da lafiya. Ina fatan Allah ya bashi lafiya, ita kuma Allah ya b’ullo mata da wani mijin, tunda itama tace bazata koma ba, babu mai yi mata dole kuma ehe”

“mai dambu kin cuceni, bazan fasa maimaita tsinuwa akan ki ba. kuma zaku gani, shi alhaki kuikuyo ne, sharri kuma d’an aike ne, duk daren dad’ewa zai dawo maka. Za’a aiko ma da khadija takaddarta.”

“Asabe kenan har ya fad’amun sharri d’an aike ne? Ai ko yanzun ma aikenshi kika yi ya dawo miki, itama Sadiyan ai rai gareta. ‘yar d’an uwanki baki ji kunyar cutar da’ita ba, sai khadija ce bazai cutar ba nan gaba, ai mugu shi yasan makwancin mugu.

Aranar dai saida Goggo Asabe su ka yi dambe da Mai dambu, suka tarama kansu jama’a da k’yar mak’ota da kishiyoyin mai dambu suka raba wannan dambe na aminai.

Fita Goggo ta yi ta na kuka, a b’arayin Goggo Safiya ta ya da zango.

Sadiya

ina jikin Aliyu mu na ta hirar mu abun sha’awa, kamar kar Goggo ta shigo haka mu ke ji.

Bakinshi ya danna a cikin nawa. tsotsa ya ke yi tamkar ya samu Alawa, gam ya rik’eni, kamar za’a kwace ni. Munfi minti goma a haka ni da Aliyu, sannan na samu na kwaci kaina da kyar.

Aliyu, tun jiya na ke son mu yi magana da kai, Amma ban samu damar hakan ba.”

sake gyara mun zama yayi a gefenshi, muka sark’e hannayen mu a cikin na juna.

“Ina sauraron ki Sadiya ta, menene?”

Dama uhm juna biyu gareni. wata zabura Aliyu yayi, tare da sake damk’e hannuna.

“Da gaske ki ke yi Sadiya?”

Eh da gaske na ke yi, duk wani halamu sun nuna hakan, ga kasala, da yawan yin amai, kuma abu kad’an da na yi sai in ji duk na gaji.”

Rumgumeni tsam Aliyu yayi a k’irjina, yana wani murna mara misaltuwa

“Sadiya nagode, Allah yai miki Albarka, yanzu nine na kusa zama Abba? Allah na gode ma daka azurta ni da samun rabo.

ni dai kaina na sunne a k’irjinshi, kunya na ta kamani.

d’agoni yayi, yana kallona.

“Me ki ke so in miki Sadiya?” Dubanshi nayi da kyau, duk ya wani rud’e sai lallab’ani ya ke yi.”

Aliyu, so na ke yi, in dinga zuwa asibiti awo, sannan inaso in haihu a asibiti. Aliyu sannan dan Allah kar a kai yarona almajirci dan Allah.

hawaye na soma zubarwa, dan bazan iya haifar d’a a cikina akai mun wata uwa duniyar ba. bani da wannan juriyar d’a yafi gaban ai wasa da rayuwarshi. Sake rungumeni yayi yana rarrashina.

“ya isa Sadiya ki dena kukan haka. na miki alk’awarin zaki je asibiti, kuma zaki haihu a asibiti, dake da Babyn bazan so wani abun ya same ku ba. maganar Almajirci kuma, zan iya iya k’ok’arina, dan ganin yaranmu sun rayu a gabanmu. Sadiya ina samun lafiya zan bud’e makaranta. yarana a tsangaya ta za su yi karatun arabic d’insu. Kuma ina da tabbacin za ki koyar da su boko. uhm haba maman twins.” Dariya muka yi. na sake mak’alk’ale mijina

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

35~36

“Wai yaya Asabe, lafiya? tunda kika shigo ki ke ta runtuma kuka. Kuma naga jikin Aliyu ai da sauk’i sosai. Goggo Asabe tace.

“hmmm Safiya bari, mai dambu ce take so a raba Auran Aliyu da khadija, ki duba duk irin hidimta musu da Aliyu yayi, wanne irin so ne ban nuna ma khadija ba, dama ita kanta mai dambun? Har gori take yi, wai Aliyu bai da kuzarin iya gamsar da mace, Bacin duk khadijan ita ta jefa shi a cikin wannan kaddarar.” mamaki ne ya kama Goggo Safiya ainun, domun in ba dan a bakin Goggo ta ji wannan labarin ba, toh da k’aryatawa za ta yi tsab.”

“Yaya ita mai dambun ce ta ce hakan, ko kuwa har da mai gari?” majina Goggo ta share tace.

” mai dambu ta sanar dani, shima kanshi mai garin yace, Aba khadija takaddarta. duk irin kud’in da Aliyu ya narka ma khadija a lefenta. Sannan kuma fa, sun kwashe adakar baki d’aya.” Goggo Safiya tace.

“Tunda haka su ka zaba, Yaya ni ina ganin a basu takaddar, tun kafin a yi rikici, kinsan mai dambu ba mutunci gareta ba.”

“Ni babbar damuwata shine, Aliyu zai rayu ne a cikin damuwar rashin magaji, ko dad’in Aure d’and’anashi yayi kawai na d’an lokaci. Abun yana damuna Safiya. Duk da wanzan yana ta k’arfafa mana guiwa akan hakan”

Sun jima su na tattaunawa, sannan Goggo ta koma b’arayinta.

Sadiya

Da sauri na fita daga jikin Aliyu, zuwa can gefe in da na saba zama. Goggo ce ta shigo, duban Aliyu ta yi.

“Kai kuma lafiya kake dariya haka?” cewa yayi zauna Baba.

Xama Goggo ta yi kusanshi.

“Goggo Allah kenan mai k’arfin iko akan dukkan bawanshi, Allah ya k’addari zaki samu jika daga gareni.” Sororo Goggo take kallonshi tace.

“Banfa gane komai ba.” Hannunta ya kama yace

“Baba Allah ya axurta Sadiya da juna biyu.” Da sauri nai k’asa da kaina. Ina sauraron shin wanne irin farin ciki Goggo zata bayyawa. Fashewar kukanta mu ka ji. Daga ni har Aliyu mun yi tunanin kukan farin ciki ne. Ashe sab’anin hakanne.”Shikenan ta faru ta k’are, zamu sake cud’anya da Aisha ni Asabe, sai kuma yanda su ka yi da Aliyu.” kuka ta ke yi sosai. mamakine ya cika ni, take wasu zafafan hawayen bak’in ciki su ka shiga sunturi a kumatuna, gashi na na kasa mik’ewa dan jikina har rawa ya ke yi, tsabar jin haushi. Aliyu kuwa ganin zubar hawayena, duk sai ya rud’e ya rasa wacce zai rarrasa a cikinmu, Yace”

“Baba mu fa muka yanke k’auna da samun rabon d’a, sakamakon abunda ya faru da ni, ni na zaci murna zaki yi Baba, a tunanina komai ya xo k’arshe.” Tana kuka tace.

“Yanzu komai zai fara Aliyu, ita kanta Aisha sai da ta haifi Sadiya ne, boka ya bata nasarar raba mu da d’an uwanmu. Bazan zuba ido haka ta faru da ni ba. Bana farin ciki da samun juna biyun Sadiya, dan juna biyunnan barazana ce ta rasa gudan jinina.” mik’ewa Goggo ta yi, tare da shiga cikin uwar d’aki, a bakin gado ta zauna, ta shiga tunanin meye mafita, mai dambu ce ta fad’o mata a rai, Amma sai ta tuna da irin yanda suka kashe baran baran, amma lallai ta k’udirin niyyar zubar ma da Sadiya cikin dake jikinta, ko kuma ta tilasta mishi ya sake ta. Tabawa k’awarta ce ta fad’o mata. wani murmushin mugunta ta saki.”

Ni kuma, da kyar na samu na yunk’ura zuwa tsaye, dan duk wata lakar jikina, ta gaza ba ma jikina sapot d’in daya dace.

Aliyu ne ya kira sunana a hankali, sai da tsigar jikina ta tashi.

Ahankali na juyo ina kallonshi, shima a cikin tashin hankalin yake, idanuwanshi su na dab da su zubo da ruwa, sun kad’a sun yi jawur, tausayinshi ne ya kamani, duk ta dalilina ya kasa jituwa da mahaifiyarshi. Ina ganin barin gidannan shine A’ala a gareni.

“Sadiya ki yi hak’uri kinji, kar ki sama kanki wata damuwar kinga ba ke kad’ai bace.” runtse idanuna na yi, nace.

Aliyu ka yi hak’uri bazan iya ci gaba da zama da kai a cikin wannan halin ba, Goggo bata sona, yau na sake gasgata cewar har abada baza ta soni ba, bazata amshi jika daga gare ni ba. tafiya zanyi.”

A guje na fita a cikin d’akin. ina jiyo muryarshi da k’arfi yana kirana.

Da sauri Goggo ta fito daga d’aki, hawaye ta samu yana zubarwa. Tare da kung’urin tashi.

“Kar ka kuskura ka taka k’afarka daga cikin d’akinnan. Sabida k’anwar uwarka tana kuka shine kai ma kake ta ya ta ko shanyayye? Aliyu ka ji kunya wallahi. Ina saninka ya tafi ne? an gama birkita maka rayuwa da asiri, wama ya sani ko ba cikin ka bane ma, har kake wani b’are b’are. Toh babu inda zaka fita ka bita. Tafi ruwa gudu, ta kaima duk uban da zata kaima k’arata. Inji sammaci a kotu, tunda su ‘yan boko ne, masu sanin hakkokin kansu.

Ina shiga d’aki na soma harhad’a kayana iyakar wanda zan iya d’auka. Hijabina na zura, fitowa nayi tare da kulle b’arayin nawa. Hawaye kuwa ya gama wanke mun fuskata, ga wani matsanancin ciwo da kaina ya ke yi mun. K’ofar baya na bi nai ficewata.

wajajen Azahar Babur d’ina ya sauke ni a bustop, motar dake kan lodin zuwa zamfara na shiga. Na galabaita ainun, har amai sanda na yi. Ina zaune a motar nan shiru, ina tunano maganganun Goggo da irin k’iyayyar da take yi mun ni da mahaifiyata. Yau ina ma Baban da ake magana ma a kanshi? Babu ya kwanta dama, amma ace har zuwa wannan lokacin su Goggo baza su xubar da makaman ya’kinsu da mahaifiyata ba. A ganina tsantsar son da zan nuna ma Aliyu shine in fita a rayuwarshi ya samu daidaito da mahaifiyarshi, duk da akan daidai yake, amma mahaifiya tafi gaban a dinga jayayya da ita, kullum tana cikin fishi da Allah wadai a kan ka. Girman uwa yafi gaban misalin da za’ayi wasa da furucin da zata dinga fad’ama marasa dad’i, kullum a hassale take da kai. Hakan sai ya tab’a maka rayuwa ta yanda baza ka samu albarka rayuwa ba. Babban farin cikin ka yau shine, iyayenka ka yi duk yinka ka rabu da su lafiya.” Idanu na lumshe, motar mu kuma ta hau tafiya. wani nishin kukane ya taso mun, ina ganin nayi nisa da Aliyu. Da kyar na sa harshe na danne kukan, sai wasu wahalallun hawaye ne su ka gangaro mun, da sauri na sa hannu na share su.

Misalin k’arfe hud’un yamma motar mu ta shiga cikin tasha, inda ake lodi gari gari, sa’ar da na yi, motar kano saura mutum guda su ke jira, ina shiga mota ta cika, mu ka d’auki hanya, sai kano.”

Aliyu

jagob ya zauna, kan shi har wani juyawa ya ke yi, kalmar da goggo ta fad’i game da cikin Sadiya yafi gomai d’imauta shi, dolen shi ya cire kunya ya fayyace ma Goggo a yaya ya samu Sadiya.

“Baba kar ki sheganta mun jini, wallahi Allah Baba, Sadiya na sameta a matsayin cikakkiyar budurwar data tsare kanta, tai ma mijinta kyakkyawan tanadi, khadija ce ban sameta a hakan ba ma. Amma na rufa mata asiri ko ita bata san da hakan ba, cikin nawa ne.”  kukan shi ya ke son had’iyewa dan gudun kar Goggo tace, Sadiya ya ke yi ma.

“Na ji ka sameta Budurwa. ka sani, indai jika daga tsottson Aisha zai samu, harko duniya ta nad’e bazan k’aunace shi ba, nama gwammaci ace baka da d’a Aliyu. Son da kake ma Sadiya ya wuce kimar da za’aimai kallon hankali, dubi fa yanda ka gigice dan kawai ta ce ma zata tafi, tunda khadija ta koma gida sau nawa ka tambayeni ita, ko ita ba matarka bace? Ahir d’inka dani.”  yaya Fatima ce ta banko cikin d’akin tana kururuwa, Goggo tace.

“Ina fatan ba dukan ki yayi ba? dan in dukan ki yayi, mai rabani da uwarshi Habi sai Allah.” cikin shesshek’a  Fatima tace.

“Saki na yayi Baba, shikenan dama shekarun baya ya mun saki d’aya, yanzu kuma ya mun saki biyu, ya rabani da yarana Baba.”

Duk kurin Goggo sai da wannan mutuwar Aure ya jijjigata.  D’akin ya d’auki shiru na fin minti goma. Ko wanne a cikinsu da abunda ya ke sak’awa.”

Tabawa ce ta doko sallama tare da shigowa a tare. Goggo ce ta amsa mata, Tabawa ta bi kowa da ido”

“Lafiya ciwonne ya tashi ko yaya?”  Goggo ta nisa tace.”

“Ko d’aya, ita wannan sakinta mijinta yayi, shi kuma shanyayye kan mace ne ya shiga wannan yanayin. Kawata kamar kinsan ina nemanki ruwa a jallo. Tabawa tace

“Badai ruwa a jallo ba, Dan ban ganki a cikin gidana ba. Aliyu ya jikin?  “da sauk’i” ya ce mata, sannan ya gaisheta. Fatima ma gaisheta tayi. Goggo tace.

“Fatima ki je d’akin Safiya ki jira mu, kai kuma zaka iya komawa, b’arayinka, tunda ga Fatima ta dawo gida, dole zan bar kwana a wajan Safiya mu dawo nan”

Suna shiga ya mik’e da sauri, har yana fama ciwonshi, ya nufi gidanshi. kwad’on da ya gani a k’ofar shi ya tabbatar mishi da Sadiya ta tafi. zama yayi a kofar gidan nashi, yana sauke ajjiyar zuchiya. Lallai tafiya kano ta kama shi dole. Jiki a sab’ule ya nufi wajan kamilu.

“Kamilu ka ji duk abunda ya faru, Baba so take in mutu kowa ya huta, su suka sa ni a cikin wannan halin, Baba ta kasa kwantar da hankalinta ta d’auki Sadiya, ‘ya kuma suruka, Cikina ne fa a jikin Sadiya, ya zanji in sanadin wannan doguwar tafiyar da take gabanta wani abun ya cutar da ita ko abunda ke cikinta fa? Kamilu likitoci cewa su ka yi, ba lallai gabana ya sake tashi har yayi aikin da zan iya saduwar Aure ba, balle samun rabo, toh ga rabo Allah ya bani, da daren mu na farko, daren da mummunar k’addara ta gifta mun. Sadiya ita ke kula dani, tunda na soma ciwonnan, khadija ta na gidansu, tana jinya ita ma, amma ai an fad’amun ana ganinta tana lek’a waje, daidai da sau d’aya bata tab’a zuwa dubani ba, haka mahaifiyarta da mahaifinta. Ashe Sadiya ba ta yi k’ok’arin da yaci a yaba mata ba? Baba ta ki yadda da k’addarar auran daya kawo Sadiya wannan k’auyan ta na ‘yar boko, ma’aikaciya, mai ci daga asusun gwamnati kai tsaye.

Kamilu ya dafa kafad’ar Aliyu yace.

“Ni ina ga zuwa gobe ka yi shirin zuwa bikon matarka kawai, domun ba baza su dawo maka da ita ba, sai anje biko, a al’adance. Baba kuma bazata wakilta kowa dan zuwa bikonnan ba. Aliyu baka da d’an wani wajan zuwa ne, a birni haka? Da mamaki ya ke kallon Kamilu, domun bai san me ya kawo zancannan ba.

“Meye had’in tambayarnan da maganar Sadiya?”

“In da ace kasan wani a birni, da sai in ce, kud’anyi wata ‘yar tafiya da Sadiya mana dan samun keb’ewa, ace itama ta samu kulawa daga gareka, duk da dai kana cikin lalura ne.” Aliyu yai shiru kamar mai nazari, can sai ya ce.

“Ai kuwa akwai Abokina Haidar tare mu kai karatu da shi a madina, kuma wallahi ya ban adireshin shi, suna garin Abuja. Dan ko da jirginmu ya sauka a garin, ya gabatar da ni a wajan iyayenshi, kuma mutanen kirki ne. Mahaifinshi na da wata babbar makarantar boko da arabiyya a cikin garin na Abuja, Haidar d’inma makarantar zai je ya kular ma da mahaifin nashi, sakamakon ‘yan bani na iya da su ke son durk’usar da makarantar, dama karatun makarantar. Ya had’ani Allah Annabi kar mu watsar da zumunci, zai zo har inda nake.” Kamilu yace.

“Lokaci yayi da za ka kai ma Haidar ziyara a Abuja. Kuma ina son sanar maka kafin ka dawo zan kwashe iyalaina za mu bar Raquma. Aliyu babu ci gaban komai a Raquma. Ko dako zan fita in nema. sokoton shehu zan koma. Aliyu yai shiru”

“Amma kamilu zan yi kewa sosai.”

“Kai ma ina mai baka shawara kar ka ce za ka ‘kare rayuwarka a cikin Raquma, domun ba lallai burinka ya cika ba, nason bud’e makarantar addini a Raquma ba. kar kaso kaji yanda matasa da mata ke zaginka kan wannan ci gaba da kake son bayarwa a wannan k’auye namu. Yau in dai bakwa Raquma ziyara ku ke shigowa yi, ai za ku zauna lafiya da Baba.” Dariya kawai Aliyu yayi, dan ya san babu wani abu da zai fad’a wanda Baba zata amince dashi har yabar k’auyannan. domun in banda almajirci, babu wanda yake rayuwa a wani wajan a gidan su, kowa ya na gida, da dama sun yi yunk’urin hakan Amma manyan gidan sun k’i su amince da hakan, dan Goggo ita baki ma tai ma yaranta akan duk mai son barin Asalinshi, bata yafe ba.”

Goggo

Tabawa, nifa tunda Aliyu yai Aurannan bana cikin hayyacina. Har mafarki na ke yi da matar tashi tana bina da wuk’a zata kasheni.  Aliyu har kuka ya ke yi tsabar son yarinyar, ta gama lashe mai zuchiya da asiri. Toh ga ciki kuma yanxu ya b’ullo,  kinga data haihu zata mik’e k’afa sai kuma abunda ta ce shi za mu yi ni da Aliyu, Ga fatima aure ya k’are. ga masifar da mai dambu ta jefa ni a ciki, ta kaini wajan boka aka kashema yaro al’aurarshi, boka fa cewa yayi bazai sake mik’ewa ba, shi da mace sai dai kallo.”

Tabawa ta yi dariya irinta ‘yan duniya tace.

“Ta xo ma da sauk’i ai Asabe, rashin lafiyar da ya ke d’auke da shi, bazai barta ta dauwama da shiba, dole za’a je matsayar da za ta buk’aci saki dole. maganar zubar da cikin ne a gabanmu, sai kuma mu had’a da sa boka ya cusa k’iyayyar juna, da jin haushin juna a tsakaninsu. da na zuba miki idanune ke da Aminiyar taki mai dambu, ba gashi ba. Mai dambu k’ananan bokaye take bi, kixo in kai ki gidan ‘yan bori da ‘yan tsubbu.”

Goggo tace.

“Hmmm ai mai dambu ta ban mamaki. Kuma a hakan so su ke Aliyu ya saki d’iyar ta su, wai har da mai gari ma sakin dai su ke buk’ata. Tabawa ta ce.

“Ke dai sako mayafi mu wuce, dama ni ma da kyar guntuwar matsalata. ma karashe hirar a hanya” cikin sauri Goggo ta saka mayafi su ka fice a gidan, Babur su ka hau zuwa can cikin k’auyan nasu.”

mrs Bukari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

37~38

Kano State

Sadiya

motar mu ce ta shiga cikin tashar Anguwa uku. Da misalin k’arfe Goma sha biyun dare, garin yayi shiru babu kowa, babu abun haka na haya a titi, sai motocin gida.

Ahankali na ke fitowa daga cikin tashar, ashe haka mata masu k’aramin ciki su ke mugun galabaita a sakamakon doguwar tafiya? Kai cikin ma kan shi rainon shi akwai wahala, jiki baya sake samun cikakkiyar lafiya kuma, har sai Allah ya raba lafiya.”

Ina tsaye a titi nama rasa tudun dafawa, ga wani zazzab’i da ya addabeni tun a hanya, wunya ta dameni sossi.”

motar da bazan tab’a mance mamallakinta a rayuwa ba, itace ta tsaya a gabana.

Kawar da kaina nayi gefe tamkar ban ma san da tsaiwar motar ba.” fitowa yayi, zuwa in da na ke tsaye.

“Sadiya, saukar yanzu kenan? Bari in kai ki gida, yanxu ba zaki samu abun hawa ba.” wani irin miki Ahmad ke famo mun a cikin zuchiyata, amma jiri da zazzab’in da ke damuna, yasa ban nemi zab’i wajan shiga motar Ahmad ba.” Ba wanda ya ce da wani uffan, sai sharara gudu kawai ya ke yi dani a titi, Har zuwa k’ofar gidanmu.

kwakwalwata sai hasko mun abubbuwa da dama take yi, domun Ahmad ya sha suntirin zuwa k’ofar gidannan. Fitowa na yi a cikin motar, shima ya fito, jakata ya ciro mun tare da cewa.

“A huta gajiya Sadiya, gobe in Allah ya kaimu zan lek’o kafin in je office.” Bani da lokacin sauraron Ahmad, jakata na d’auka zuwa k’ofar gida. Ahmad bai gushe a wajan ba, har sai da ya ga shigana cikin gida. k’anwar mahaifiyata ce Goggo Binta da ta ke aure a Saudiyya ita ta bud’e mun k’ofar gidan. Jikinta na fad’a tare da sakin wani irin kuka. k’ofar gidan ta kulle, ta rik’e hannuna, da jakata zuwa ciki. mama na hango a kwance a kan gado, Goggo Hansatu kuma tana gefenta, magani ta ke bata.

Da sallama mu ka shiga cikin d’akin, mama ta dube ni cike da kallon tuhuma, kallo d’aya nai mata tsoro duk ya bi ya kamani, dan kallon da take watso mun na riga nasan me ta ke nufi, na ga Mama ta rame sosai, da dukkan halamu bata da lafiya ne. Amon muryar mama ne ya katseni.

“Kin kaso auren naki kenan ko Sadiya? lallai kin ba da mata ‘yan boko, kuma ma’aikata, irinku ke sa ake mana kud’in goro a cikin al’umma. D’auka su ke yi cewar ba ma iya zaman aure. kin kyauta, da ki ka nuna ma dangin mahaifinki ban gina ki bisa tartibiyar tarbiya ba, na kuma gode da kika kunyata ni.” Kan ta ta kawar a kaina, jikina na rawa na isa bakin gadon da take, hannunta na kamo, ajjiyar zuchiyace ta kubce mata ba shiri.

Mama ba aurena na kaso ba, asalima babu wata b’araka data tab’a shiga tsakanina da Aliyu. Mama amma kowa a gidan ya tsaneni, barin ma Goggo Asabe wacce har abada baza ta tab’a so na ba. Juna biyu dana samu bai sa ta sassauta mun ba, kullum a cikin umartar Aliyu ya sake ni ta ke, kullum a cikin fad’a da shi take. Ni ina tsoron kar Allah yai fishi da shi, a sakamakon fishin da Goggo take yi dashi ne, shiyasa na dawo gida.” Rungumeni mama ta yi kawai a jikinta, ina jin dumin jikinta irinna marasa lafiya. Goggo Binta tace.

“Tun farko Yaya ke kika jama yarinyar nan, wanne irin k’iyayya ne Asabe bata nuna miki ba, matar da har gobe ba k’aunarki take ba, sai Sadiya za ta k’aunata, ni fa ina ganin dole aurannan yazo k’arshe bazai yuwu mu xuba idanu muna kallon Sadiya  a cikin irin wannan halin ba, gashi har rabo ya shiga tsakaninsu.” Goggo Hansatu tace

“Gaskiya kam, bafa k’aramin cutarwa su kai ma Sadiya ba. Yarinya da iliminta da aikinta, a kai ta aure k’auye. wallahi ko musulunci ma bai yarda da wannan ba, domun akwai cutarwa da gurk’usarma da mutum rayuwa, ni ya bata takaddarta kawai, Yaya Binta in zata koma Saudiyya su tafi tare da ita kawai.” dam gabana ya yanke ya fad’i, tsuru tsuru na yi a cikinsu. mama tace.

“Binta da Hansatu hoo, ai in muka yi haka ba mu nuna dattaku ba, kuma ba haka iyayemu su ka koyar da mu ba, ba zan tab’a sa hannu wajan mutuwar auran Sadiya ba, sai dai ma in bata ha’kuri, domun duk wani aure in za ki kalla hak’uri ke rik’e da shi, bawai soyayya kad’ai ba. Ga rabo a jikinta, bazan so ace Sadiya ta haihu kuma bata tare da uban d’an ko ‘yar da zata haifa ba. wuya fa bata kisa, ni d’innan babu da irin abunda Asabe bata jefe ni da shi ba, na kunshi takaici da bak’in cikin Asabe kashi kashi. Yanzu nan damar da bata samu ba a baya, sabida Adam bai bama kowa k’ofar da zai wulak’antani a gabanshi ba, shine take so tai mun horo akan Sadiya. ita bata girma, duhun jahilci na cin rayuwarta.” Ajjiyar zuchiya na sauke. Mama ta sauka daga kan gadon da take, ta rik’o hannuna ta zaunar dani akan gadon, sannan ta fita.

Goggo Hansatu ta dube ni tace.

“An yi auran shi Aliyun da ita khadijar da Asabe ta fi so? kai na d’aga mata kawai, dan wani zazzab’ine ke hawa kaina, na kasa ko da magana.

mama ce ta shigo da ruwa a boket, ta shigar mun da shi toilet.

“ki watsa ruwa, sai ki zo ki sha tea, kamar cikin na baki wahala ko? naga kin rame sosai. A hankali nace.

“Zazzab’ine ya rufe ni mama, tun a mota nake jin shi, na sha wuya a mota sosai.” Nan su ka shiga yi mun sannu tare da lallab’ani. Ai wankan da na yi kamar zazzab’in na tsokano, na fa jikina ya shiga kerma, amai na tunkud’omun, gashi babu komai a cikina. A kaina su Goggo Hansatu su ka kwana, dan har zabura na ke yi, washe gari da sassafe sai asibiti, cikin gaggawa aka bani gado.”

“Yaya Aisha, yarinyar nan bai fa kamata ace mun tursasa mata komawa dangin mahaifinta ba, ga k’aramin ciki a jikinta amma su ka barta ta fito, ai shima Aliyun ya kamata ya biyo sawunta. Goggo Binta tace.

“In baki da k’arfin fad’a da su, mu muna da shi, Sadiya kuma da ita zan koma Saudiyya kowa ma sai ya huta, ji yanda ta fad’a ta yi duhu.” mama ta dubesu ta girgiza kai.

“Baku da lissafi sosai, taya zamu zama silar mutuwar auranta, saidai in shi Aliyunne ya bata takadda, toh anan fa ba wanda ya isa ya tank’warani Sadiya ta sake koma mai, amma dan komawa d’akinta zata koma. Ana Sallamarta ni da kaina zan mayar da ita.  ba dole sai ta rayu a birni bane zata samu farin ciki, haka ba dole sai ta samu dukkan wani abu da take so ba. Mu bi komai a sannu, indai Asabe ce, zata tursasa sai Aliyu ya saki Sadiya, saidai in rabon da ke tsakaninsu mai yawa ne, Asabe muguwar jahilar macece, tsabaragen masifarta, kab ‘yan uwan nata tsoronta su ke ji, har shi Yaya sulaiman, sai fa abinda tace mishi. Ziyara kawai Asabe zata kawo mana, amma sai ta ne mi ta fini iko da komai. Wallahi ban tab’a nuna musu fishi ko da akan fuskata bane, ban tab’a nuna musu gajiyawata da yi musu hidima ba, har masoyina ya gushe ya na mai shi mun albarkar da su gani su ke yi na dabaibaye shi da asirine, kyakkyawar mu’amala da fahimtar halin juna shine ginshik’in zaman aure, in kina so ki more miji, yai miki biyayyar da bai ma san yana miki ba, ki kasance mai tausayinshi, ki kasance mai amsar ya kwai wa babu, juriya, kawaici, fahimtar me gidanki, girmama danginshi, yi musu hidima, nuna mai zallar soyayya. In kuka kama wannan abun kunci zuchiyar namiji kyauta ba boka babu malam, ni ban tab’a yaji ba, domun ban taso na tab’a ganin mahaifiyarmu cikin samun sab’ani da mahaifinmu ba balle har ta kai su da yin yaji, irin yakana, da alkunya irinta iyayenmu, da ace zamu dawo da ita cikin wannan zamanin namu da ba haka ba. Malam bahaushe yana da al’adu tsabtattu kuma nagartattu, amma yanzu  Hausa fulani, ta fi ko wacce k’abila yin watsi da aure, saki da yaji ya zama ba bakin komai ba, wai shin duniyar nawa take ne? ‘yan uwana ku duba tun sanda Sadiya ta bar gabana, ta tafi aure dangin mahaifinta, na shiga tunani da zulumin abunda kaje kazo, har hakan sai da ya haifarmun da hawan jini. Samun lafiyata shine ta samu farin ciki a hannun mijinta. Alhamdullilah Sadiya ta yabi Aliyu, na kuma ji dad’in hakan, halamu sun nuna a maganarta sun samu fahimtar juna a tsakaninsu, ku yi hak’uri ku barta ta koma cikin gatanta, Asabe duk haukar da ke damunta bazata iya cutar da Sadiya ba, jininta ne ke yawo a jikinta.”  gabaki d’aya su Goggo Hansatu jikinsu ya mutu murus, ko wacce cikinsu sai da kunyar abunda suka aikata ya lullub’esu, Goggo.Hansatu tace.

“Gaskiya ne Yaya, kinyi magana mai ma’anar da mai hankali zai d’auka. In sha Allah da zaran Sadiya ta warware, ni da Ya Binta za mu maidata d’akinta, za mu ci gaba da k’arfafa guiwarta in sha Allah, burinmu shine ta zauna lafiya, kuma Sadiya ta yi k’ok’arin rungumar k’addararta, ta yi biyayyar da bazata tab’e ba.” Mama tace.

“Akan Sadiya saida idona ya soye, sam bana samun bacci, tsaiwar dare, sadaka, Ina tawassali da wad’annan aiyuka wajan rok’on Allah ya sanya haske da albarka a cikin rayuwar Auranta.” Goggo Binta tace.

“Yaya wallahi kin maye mana gurban mahaifanmu da su ka kwanta dama, ke uwace wacce za’a bigi k’irji a nuna ma duniya, madalla da samun Yaya kuma uwa kamarki. Sadiya kuma daga asibitinnan sai gidan mijinta, kuma zamu bada hak’uri, dan mu dawo da martabarta da kimarta, dan gudun kar ai mata kallon wacce ta gaza, yanxu na gane yin yaji gazawar hak’urine a wajan mace, musamman yajin da zaka dako badan zafin abunda miji yai maka ba, sai dan maganganun mutane.” Dr ce ta fito daga d’akin da Sadiya take, tace da su mama.

“karku dama, k’aramin ciki gareta, kuma abunda ke cikin nata ya sha wahala ne da ita kanta ma, Allurai nai mata, sai ruwa dana d’aura mata. zuwa anjima zata tashi, sai kuma ku tafi gida.” Mama tace.

” ‘yannan mun gode, amma ba mu yanki kati ba, bamu biya komai ba.” murmushi Dr d’in tayi tace.

“Sadiya ta wuci haka anan asibitin, kuma wannan asibitin yayi rashin jajirtacciyar ma’aikaciya. Irinsu Sadiya ba su da madadi sam.” wucewa ta yi ta bar su Goggo na zunduma mata Albarka. mama tace.

“Hansatu, ki zo ki tafi gida, a had’o kan kayan Sadiya. Sannan ki yi mata siyayyar abunda kike ganin ya dace kuma zata buk’ata, sai ki biyo ku kama hanya, ta lallab’a.” Goggo Hansatu, ba tai musu ba ta amshi key a hannun mama, da kuma dubu ashirin data mik’a mata ta wuce.

Bayan awa biyu

Sadiya

Ahankali na bud’e idanuna. Salatin Annabi S A W na soma jerowa a hankali, wata iriyar nadama da jin haushin kaina duk suka lullub’eni. Mama ita kad’aice a zaune a kan gadon da nake, da sauri ta matso.

“Kin farka Sadiya, sannu yaya k’arfin jikin?” Dubanta nayi, ta rame ta lalace nace.

“Mama ciwo kike yi ne, jiya na ji jikinki da zafi? cijewa Mama ta yi tace.

“Zazzab’ine na kwana biyu na yi Sadiya, jikin naki da dama dama ko? Lumshe idanuna nayi, uwa mai dad’i ji yanda mama take nannan dani, in banda uwa wazai ma haka? Aliyu ne ya fad’o mun, shi kam ya rasa wannan kulawar a wajan Goggo sabida ni kawai, na tabbatar kawaici yake yi mun, amma bazai tab’a jin nutsuwa ba. Mama ce ta katseni da cewa.

” Zaki iya tafiya ko, dan yanzu su Binta na dawowa za ku koma Inda kika fito, wannan kuma ya zame miki na k’arshe karki bari ko da wasa ki zubar da kimar ki a idon miji, kar ki sake ya ga gazawarki, Yaya Asabe ai uwace a wajanki, bawai Aliyu bane ya had’aku ba. Duk fad’an da zata miki a ‘ya take kallonki ba suruka ba. Ki kyautata mata iya kyautatawa ki yi mata biyayya. Mijinki kuna zaman lafiya ko, in ce dai bakya raina shi? zaine na tashi a hankali na jingina, sannan nace.

“mu na zaune lafiya, wallahi yana kyautata mun sosai, kuma akwai girmamawa sosai a mu’amalar tamu, shi kam bana samun ko wacce matsala da shi”

“Ita abokiyar zaman taki fa, ba dai kwa samun matsala dai ko?”

A’a babu matsala tsakanina da ita.”

“Toh masha Allah, kibi mijinki shine tsaninki, sai inda ya ajjiyeki, karki sake Sadiya.”

Ahankali ya iso inda muke, sanye yake a cikin malum malum, da hula dara a kanshi, sai k’amshi yake busawa idanunshi sanye da glasses fari, amma da gani na k’arin ganine. dattijo ne,gemunshi da gashin bakinshi duk furfura, hakama ‘yar sumar da ya tara a kanshi, akwai furfura amma d’aid’aiku. Mamakine ya cika ni ganinshi tsaye a bakin gadon da nake zaune, hannunshi cike da leda d’auke da lemo da ayaba.” mama ta yi murmushi, irin wanda rabon da inga murmushi irin wannan a fuskar mama, tun Baba yana da rai.”

“Barka da zuwa yallab’ai, ya kasan muna asibiti?” wani dattijon  murmushi ya saki mata.

“Hansatu ce tai mun ido, na isa k’ofar gidan ina jiran yaron aike, sai gata ta fito, shine take sanar mun d’iyarmu babu lafiya, toh ai zama bai ganni ba, sai kawai na biyo ta.” Mama tace.

“D’aliban fa, wa kabar ma su?”

“Wa yake ta wasu d’alibai ‘diyata babu lafiya?” ni dai sai rarraba idanu nake yi a tsakani, cikin halin girma na gaishe da wannan dattijon da na ji ko iya had’a idanu na kasa yi da shi. Da far’arshi ya amsa mun gaisuwata, tare da tambayata kufan jiki,

Da sauk’i” Shine amsar da na mayar mishi.

“Sadiya wannan sunanshi, malam mustapha kaka, malam mustapha wannan itace d’iyata Sadiya, wacce kullum sai na tsokata maka labarinta.” Murmushi yayi, yace.

“Allah yai ma rayuwa albarka, ita ta zo duba ki da jiki, sai kuma ta kwanta jinya kuma, Toh Allah ya baku lafiya, ga kayan marmari ki bata, zan jira ku a waje, in Hansatu ta dawo daga kasuwa sai in kaisu ai, ina fatan za ki rakata ko? murmushi mama tayi kawai irinna manya, ta amshi laidar hannunshi, shi kuma ya ajjiyemun, dubu uku a gefen gadona, yai maza ya fita.”

sha’awa soyayyar tsofaffin ta bani, cikin zolaya nace.

“Mama wannan shine Abban nawa? dukan wasa ta kawo mun, na kauce ina dariya. wani farin ciki ne ya lullub’eni da mama ta samu masoyi, dan na jima da lura, ganina a gabanta ne ya hanata ba ko wanne namiji wata dama, dan mama ba tsohuwa bace, kuma ta na da kyan jiki, ‘yar boko ce mai son kwalliya da kyaran jikinta. Farin cikina na nuna mata a fili, sannan nace.

“Mama Amma taren za mu tafi ko, tunda a mota zai kaimu? mama tace.

“Sam ni bazani ba, ban tab’a shiga motarshi ba gudun fassarar da mutane za su yi mun, k’ofar gida yake zuwa, shima a bakin zaure muke hirar a tsaye, da rana ko da safe, dan gujema sharrin shaid’an.” kai na girgiza tare da jinjina ma mama. Su Goggo Binta na dawowa mu ka wuce, dama ita gida can family house ta je ta d’ebo mun tsarabata. rankaya muka yi wajan motar tashi, bayan na kewaya mun gaggaisa da ‘yan tsirarin k’awayena. Sai da malam ya neman ma mama abun hawa, yaga tafiyarta. Sai muma muka kama hanya.”

mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

37~38

Kano State

Sadiya

motar mu ce ta shiga cikin tashar Anguwa uku. Da misalin k’arfe Goma sha biyun dare, garin yayi shiru babu kowa, babu abun hawa na haya a titi, sai motocin gida.

Ahankali na ke fitowa daga cikin tashar, ashe haka mata masu k’aramin ciki su ke mugun galabaita a sakamakon doguwar tafiya? Kai cikin ma kan shi rainon shi akwai wahala, jiki baya sake samun cikakkiyar lafiya kuma, har sai Allah ya raba lafiya.”

Ina tsaye a titi nama rasa tudun dafawa, ga wani zazzab’i da ya addabeni tun a hanya, wunya ta dameni sossi.”

motar da bazan tab’a mance mamallakinta a rayuwa ba, itace ta tsaya a gabana.

Kawar da kaina nayi gefe tamkar ban ma san da tsaiwar motar ba.” fitowa yayi, zuwa in da na ke tsaye.

“Sadiya, saukar yanzu kenan? Bari in kai ki gida, yanxu ba zaki samu abun hawa ba.” wani irin miki Ahmad ke famo mun a cikin zuchiyata, amma jiri da zazzab’in da ke damuna, yasa ban nemi zab’i wajan shiga motar Ahmad ba.” Ba wanda ya ce da wani uffan, sai sharara gudu kawai ya ke yi dani a titi, Har zuwa k’ofar gidanmu.

k’wakwalwata sai hasko mun abubbuwa da dama take yi, domun Ahmad ya sha suntirin zuwa k’ofar gidannan. Fitowa na yi a cikin motar, shima ya fito, jakata ya ciro mun tare da cewa.

“A huta gajiya Sadiya, gobe in Allah ya kaimu zan lek’o kafin in je office.” Bani da lokacin sauraron Ahmad, jakata na d’auka zuwa k’ofar gida. Ahmad bai gushe a wajan ba, har sai da ya ga shigana cikin gida. k’anwar mahaifiyata ce Goggo Binta da ta ke aure a Saudiyya ita ta bud’e mun k’ofar gidan. Jikinta na fad’a tare da sakin wani irin kuka. k’ofar gidan ta kulle, ta rik’e hannuna, da jakata zuwa ciki. mama na hango a kwance a kan gado, Goggo Hansatu kuma tana gefenta, magani ta ke bata.

Da sallama mu ka shiga cikin d’akin, mama ta dube ni cike da kallon tuhuma, kallo d’aya nai mata tsoro duk ya bi ya kamani, dan kallon da take watso mun na riga nasan me ta ke nufi, na ga Mama ta rame sosai, da dukkan halamu bata da lafiya ne. Amon muryar mama ne ya katseni.

“Kin kaso auren naki kenan ko Sadiya? lallai kin ba da mata ‘yan boko, kuma ma’aikata, irinku ke sa ake mana kud’in goro a cikin al’umma. D’auka su ke yi cewar ba ma iya zaman aure. kin kyauta, da ki ka nuna ma dangin mahaifinki ban gina ki bisa tartibiyar tarbiya ba, na kuma gode da kika kunyata ni.” Kan ta ta kawar a kaina, jikina na rawa na isa bakin gadon da take, hannunta na kamo, ajjiyar zuchiyace ta kubce mata ba shiri.

Mama ba aurena na kaso ba, asalima babu wata b’araka data tab’a shiga tsakanina da Aliyu. Mama amma kowa a gidan ya tsaneni, barin ma Goggo Asabe wacce har abada baza ta tab’a so na ba. Juna biyu dana samu bai sa ta sassauta mun ba, kullum a cikin umartar Aliyu ya sake ni ta ke, kullum a cikin fad’a da shi take. Ni ina tsoron kar Allah yai fishi da shi, a sakamakon fishin da Goggo take yi dashi ne, shiyasa na dawo gida.” Rungumeni mama ta yi kawai a jikinta, ina jin dumin jikinta irinna marasa lafiya. Goggo Binta tace.

“Tun farko Yaya ke kika jama yarinyar nan, wanne irin k’iyayya ne Asabe bata nuna miki ba, matar da har gobe ba k’aunarki take ba, sai Sadiya za ta k’aunata, ni fa ina ganin dole aurannan yazo k’arshe bazai yuwu mu xuba idanu muna kallon Sadiya  a cikin irin wannan halin ba, gashi har rabo ya shiga tsakaninsu.” Goggo Hansatu tace

“Gaskiya kam, bafa k’aramin cutarwa su kai ma Sadiya ba. Yarinya da iliminta da aikinta, a kai ta aure k’auye. wallahi ko musulunci ma bai yarda da wannan ba, domun akwai cutarwa da durk’usarma da mutum rayuwa, ni ya bata takaddarta kawai, Yaya Binta in zata koma Saudiyya su tafi tare da ita kawai.” dam gabana ya yanke ya fad’i, tsuru tsuru na yi a cikinsu. mama tace.

“Binta da Hansatu hoo, ai in muka yi haka ba mu nuna dattaku ba, kuma ba haka iyayemu su ka koyar da mu ba, mun zama bamu da banbanci da su kenan. ba zan tab’a sa hannu wajan mutuwar auran Sadiya ba, sai dai ma in bata ha’kuri, domun duk wani aure in za ki kalla hak’uri ke rik’e da shi, bawai soyayya kad’ai ba. Ga rabo a jikinta, bazan so ace Sadiya ta haihu kuma bata tare da uban d’an ko ‘yar da zata haifa ba. wuya fa bata kisa, ni d’innan babu da irin abunda Asabe bata jefe ni da shi ba, na kunshi takaici da bak’in cikin Asabe kashi kashi. Yanzu nan damar da bata samu ba a baya, sabida Adam bai bama kowa k’ofar da zai wulak’antani a gabanshi ba, shine take so tai mun horo akan Sadiya. ita bata girma, duhun jahilci na cin rayuwarta.” Ajjiyar zuchiya na sauke. Mama ta sauka daga kan gadon da take, ta rik’o hannuna ta zaunar dani akan gadon, sannan ta fita.

Goggo Hansatu ta dube ni tace.

“An yi auran shi Aliyun da ita khadijar da Asabe ta fi so? kai na d’aga mata kawai, dan wani zazzab’ine ke hawa kaina, na kasa ko da magana.

mama ce ta shigo da ruwa a boket, ta shigar mun da shi toilet.

“ki watsa ruwa, sai ki zo ki sha tea, kamar cikin na baki wahala ko? naga kin rame sosai. A hankali nace.

“Zazzab’ine ya rufe ni mama, tun a mota nake jin shi, na sha wuya a mota sosai.” Nan su ka shiga yi mun sannu tare da lallab’ani. Ai wankan da na yi kamar zazzab’in na tsokano, na fa jikina ya shiga kerma, amai na tunkud’omun, gashi babu komai a cikina. A kaina su Goggo Hansatu su ka kwana, dan har zabura na ke yi, washe gari da sassafe sai asibiti, cikin gaggawa aka bani gado.”

“Yaya Aisha, yarinyar nan bai fa kamata ace mun tursasa mata komawa dangin mahaifinta ba, ga k’aramin ciki a jikinta amma su ka barta ta fito, ai shima Aliyun ya kamata ya biyo sawunta. Goggo Binta tace.

“In baki da k’arfin fad’a da su, mu muna da shi, Sadiya kuma da ita zan koma Saudiyya kowa ma sai ya huta, ji yanda ta fad’a ta yi duhu.” mama ta dubesu ta girgiza kai.

“Baku da lissafi sosai, taya zamu zama silar mutuwar auranta, saidai in shi Aliyunne ya bata takadda, toh anan fa ba wanda ya isa ya tank’warani Sadiya ta sake koma mai, amma dan komawa d’akinta zata koma. Ana Sallamarta ni da kaina zan mayar da ita.  ba dole sai ta rayu a birni bane zata samu farin ciki, haka ba dole sai ta samu dukkan wani abu da take so ba. Mu bi komai a sannu, indai Asabe ce, zata tursasa sai Aliyu ya saki Sadiya, saidai in rabon da ke tsakaninsu mai yawa ne, Asabe muguwar jahilar macece, tsabaragen masifarta, kab ‘yan uwan nata tsoronta su ke ji, har shi Yaya sulaiman, sai fa abinda tace mishi. Ziyara kawai Asabe zata kawo mana, amma sai ta ne mi ta fini iko da komai. Wallahi ban tab’a nuna musu fishi ko da akan fuskata bane, ban tab’a nuna musu gajiyawata da yi musu hidima ba, har masoyina ya gushe ya na mai shi mun albarkar da su gani su ke yi na dabaibaye shi da asirine, kyakkyawar mu’amala da fahimtar halin juna shine ginshik’in zaman aure, in kina so ki more miji, yai miki biyayyar da bai ma san yana miki ba, ki kasance mai tausayinshi, ki kasance mai amsar ya kwai wa babu, juriya, kawaici, fahimtar me gidanki, girmama danginshi, yi musu hidima, nuna mai zallar soyayya. In kuka kama wannan abun kunci zuchiyar namiji kyauta ba boka babu malam, ni ban tab’a yaji ba, domun ban taso na tab’a ganin mahaifiyarmu cikin samun sab’ani da mahaifinmu ba balle har ta kai su da yin yaji, irin yakana, da alkunya irinta iyayenmu, da ace zamu dawo da ita cikin wannan zamanin namu da ba haka ba. Malam bahaushe yana da al’adu tsabtatattu kuma nagartattu, amma yanzu  Hausa fulani, ta fi ko wacce k’abila yin watsi da aure, saki da yaji ya zama ba bakin komai ba, wai shin duniyar nawa take ne? ‘yan uwana ku duba tun sanda Sadiya ta bar gabana, ta tafi aure dangin mahaifinta, na shiga tunani da zulumin abunda kaje kazo, har hakan sai da ya haifarmun da hawan jini. Samun lafiyata shine ta samu farin ciki a hannun mijinta. Alhamdullilah Sadiya ta yabi Aliyu, na kuma ji dad’in hakan, halamu sun nuna a maganarta sun samu fahimtar juna a tsakaninsu, ku yi hak’uri ku barta ta koma cikin gatanta, Asabe duk haukar da ke damunta bazata iya cutar da Sadiya ba, jininta ne ke yawo a jikinta.”  gabaki d’aya su Goggo Hansatu jikinsu ya mutu murus, ko wacce cikinsu sai da kunyar abunda suka aikata ya lullub’esu, Goggo.Hansatu tace.

“Gaskiya ne Yaya, kinyi magana mai ma’anar da mai hankali zai d’auka. In sha Allah da zaran Sadiya ta warware, ni da Ya Binta za mu maidata d’akinta, za mu ci gaba da k’arfafa guiwarta in sha Allah, burinmu shine ta zauna lafiya, kuma Sadiya ta yi k’ok’arin rungumar k’addararta, ta yi biyayyar da bazata tab’e ba.” Mama tace.

“Akan Sadiya saida idona ya soye, sam bana samun bacci, tsaiwar dare, sadaka, Ina tawassali da wad’annan aiyuka wajan rok’on Allah ya sanya haske da albarka a cikin rayuwar Auranta.” Goggo Binta tace.

“Yaya wallahi kin maye mana gurban mahaifanmu da su ka kwanta dama, ke uwace wacce za’a bigi k’irji a nuna ma duniya, madalla da samun Yaya kuma uwa kamarki. Sadiya kuma daga asibitinnan sai gidan mijinta, kuma zamu bada hak’uri, dan mu dawo da martabarta da kimarta, dan gudun kar ai mata kallon wacce ta gaza, yanxu na gane yin yaji gazawar hak’urine a wajan mace, musamman yajin da zaka dako badan zafin abunda miji yai maka ba, sai dan maganganun mutane.” Dr ce ta fito daga d’akin da Sadiya take, tace da su mama.

“karku damu, k’aramin ciki gareta, kuma abunda ke cikin nata ya sha wahala ne da ita kanta ma, Allurai nai mata, sai ruwa dana d’aura mata. zuwa anjima zata tashi, sai kuma ku tafi gida.” Mama tace.

” ‘yannan mun gode, amma ba mu yanki kati ba, bamu biya komai ba.” murmushi Dr d’in tayi tace.

“Sadiya ta wuci haka anan asibitin, kuma wannan asibitin yayi rashin jajirtacciyar ma’aikaciya. Irinsu Sadiya ba su da madadi sam.” wucewa ta yi ta bar su Goggo na zunduma mata Albarka. mama tace.

“Hansatu, ki zo ki tafi gida, a had’o kan kayan Sadiya. Sannan ki yi mata siyayyar abunda kike ganin ya dace kuma zata buk’ata, sai ki biyo ku kama hanya, ta lallab’a.” Goggo Hansatu, ba tai musu ba ta amshi key a hannun mama, da kuma dubu ashirin data mik’a mata ta wuce.

Bayan awa biyu

Sadiya

Ahankali na bud’e idanuna. Salatin Annabi S A W na soma jerowa a hankali, wata iriyar nadama da jin haushin kaina duk suka lullub’eni. Mama ita kad’aice a zaune a kan gadon da nake, da sauri ta matso.

“Kin farka Sadiya, sannu yaya k’arfin jikin?” Dubanta nayi, ta rame ta lalace nace.

“Mama ciwo kike yi ne, jiya na ji jikinki da zafi? cijewa Mama ta yi tace.

“Zazzab’ine na kwana biyu na yi Sadiya, jikin naki da dama dama ko? Lumshe idanuna nayi, uwa mai dad’i ji yanda mama take nannan dani, in banda uwa wazai ma haka? Aliyu ne ya fad’o mun, shi kam ya rasa wannan kulawar a wajan Goggo sabida ni kawai, na tabbatar kawaici yake yi mun, amma bazai tab’a jin nutsuwa ba. Mama ce ta katseni da cewa.

” Zaki iya tafiya ko, dan yanzu su Binta na dawowa za ku koma Inda kika fito, wannan kuma ya zame miki na k’arshe karki bari ko da wasa ki zubar da kimar ki a idon miji, kar ki sake ya ga gazawarki, Yaya Asabe ai uwace a wajanki, bawai Aliyu bane ya had’aku ba. Duk fad’an da zata miki a ‘ya take kallonki ba suruka ba. Ki kyautata mata iya kyautatawa ki yi mata biyayya. Mijinki kuna zaman lafiya ko, in ce dai bakya raina shi? zaune na tashi a hankali na jingina, sannan nace.

“mu na zaune lafiya, wallahi yana kyautata mun sosai, kuma akwai girmamawa sosai a mu’amalar tamu, shi kam bana samun ko wacce matsala da shi”

“Ita abokiyar zaman taki fa, ba dai kwa samun matsala dai ko?”

A’a babu matsala tsakanina da ita.”

“Toh masha Allah, kibi mijinki shine tsaninki, sai inda ya ajjiyeki, karki sake Sadiya.”

Ahankali ya iso inda muke, sanye yake a cikin malum malum, da hula dara a kanshi, sai k’amshi yake busawa idanunshi sanye da glasses fari, amma da gani na k’arin ganine. dattijo ne,gemunshi da gashin bakinshi duk furfura, hakama ‘yar sumar da ya tara a kanshi, akwai furfura amma d’aid’aiku. Mamakine ya cika ni ganinshi tsaye a bakin gadon da nake zaune, hannunshi cike da leda d’auke da lemo da ayaba.” mama ta yi murmushi, irin wanda rabon da inga murmushi irin wannan a fuskar mama, tun Baba yana da rai.”

“Barka da zuwa yallab’ai, ya kasan muna asibiti?” wani dattijon  murmushi ya saki mata.

“Hansatu ce tai mun ido, na isa k’ofar gidan ina jiran yaron aike, sai gata ta fito, shine take sanar mun d’iyarmu babu lafiya, toh ai zama bai ganni ba, sai kawai na biyo ta.” Mama tace.

“D’aliban fa, wa kabar ma su?”

“Wa yake ta wasu d’alibai ‘diyata babu lafiya?” ni dai sai rarraba idanu nake yi a tsakani, cikin halin girma na gaishe da wannan dattijon da na ji ko iya had’a idanu na kasa yi da shi. Da far’arshi ya amsa mun gaisuwata, tare da tambayata kufan jiki,

Da sauk’i” Shine amsar da na mayar mishi.

“Sadiya wannan sunanshi, malam mustapha kaka, malam mustapha wannan itace d’iyata Sadiya, wacce kullum sai na tsokata maka labarinta.” Murmushi yayi, yace.

“Allah yai ma rayuwa albarka, ita ta zo duba ki da jiki, sai kuma ta kwanta jinya kuma, Toh Allah ya baku lafiya, ga kayan marmari ki bata, zan jira ku a waje, in Hansatu ta dawo daga kasuwa sai in kaisu ai, ina fatan za ki rakata ko? murmushi mama tayi kawai irinna manya, ta amshi laidar hannunshi, shi kuma ya ajjiyemun, dubu uku a gefen gadona, yai maza ya fita.”

sha’awa soyayyar tsofaffin ta bani, cikin zolaya nace.

“Mama wannan shine Abban nawa? dukan wasa ta kawo mun, na kauce ina dariya. wani farin ciki ne ya lullub’eni da mama ta samu masoyi, dan na jima da lura, ganina a gabanta ne ya hanata ba ko wanne namiji wata dama, dan mama ba tsohuwa bace, kuma ta na da kyan jiki, ‘yar boko ce mai son kwalliya da gyaran jikinta. Farin cikina na nuna mata a fili, sannan nace.

“Mama Amma taren za mu tafi ko, tunda a mota zai kaimu? mama tace.

“Sam ni bazani ba, ban tab’a shiga motarshi ba gudun fassarar da mutane za su yi mun, k’ofar gida yake zuwa, shima a bakin zaure muke hirar a tsaye, da rana ko da safe, dan gujema sharrin shaid’an.” kai na girgiza tare da jinjina ma mama. Su Goggo Binta na dawowa mu ka wuce, dama ita gida can family house ta je ta d’ebo mun tsarabata. rankaya muka yi wajan motar tashi, bayan na kewaya mun gaggaisa da ‘yan tsirarin k’awayena. Sai da malam ya neman ma mama abun hawa, yaga tafiyarta. Sai muma muka kama hanya.”

mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

39~40

RAQUMA

JIYA

Goggo

Sun sha tafiya a kan Babur na tsawon awa biyu, ko da suka sauka ma, saida su ka kuma yin tafiyar awa guda akan dugadugansu.

Goggo ta tsorata da shiga cikin Bukkar bokan, domun irin abubbuwan da ta gani na ban tsoro a cikin wajan abun ba’a cewa komai. Nanfa Goggo ta tsure tare da raxana, take jikinta ya shiga kakkarwa takota ina. wata tsawa bokan ya saki.

“Ku dakata a wajan yau ba ma marabtar bak’in zuwa.” wani garin magani ya jefo musu ya fad’i a gaban Goggo fat.”

“ki zuba mata a abinci ko a abun sha, in tasha angama, angama, angama. sai ta zama mujiya a idanun mijinta, cikin zai zube, bazata sake samun haihuwa ba har duniya ta nad’e, duk duniya babu mai makarin wannan asirin sai ni nan boka jemau, mai rauhanai, ku tafi.” Tabawa tace.

“Jemau duk wani al’amura nawa yana ga Allah yana gareka, na yarda da kai. Baka tab’a fad’a bai yuwu ba, daga kai ba wani aradun Allah, a lafiya sarkin bokaye.”

“Tabawa na baki d’an mutum da uwarsa, Tabawa taki ta yi kyau, bak’uwa ma ta ci albarkacin ki, magani taci kyauta na bata. Ke kuma fad’i ko me kike so kin samu. Tabawa tace.

“Kasuwancin ya ja Baya, amma da in na yi wainar goronnan da k’uli da safennan ciniki har sai na ture.” Dariya ya fashe mata dashi.

“Ki sabunta Tabawa, Jeki ya sabuntu.”

Haka suka fito, ko wacce zuchiyarta fal da farin cikin cikar buri. sun yi dare sosai sabida nisan wajan, Amma duk da wannan daren Aliyu yana zaune a falon Goggo yana jiranta ta dawo.

da sallama ta shiga d’akin, turus ta yi a tsaye tare da cewa.

“Kai me kake yi a cikin d’akinnan, ba na sallameka ba?” Ajjiyar zuchiya ya sauke, da ganinshi kasan yana cikin damuwa.

“Baba zan tafi, dama inaso mu yi magana ne, dan girma Allah Baba ki saurare ni.” Harara Goggo ta bishi da shi, kan tabarma ta zauna.

“Ina jinka, ai bazai wuci akan mayyar matarka ba ko?”

“Ba wai a kanta kad’ai maganar tawa zata tsaya ba. Baba ki yi hak’uri a bisa dukkannin wasu abubbuwa da suka faru a baya, Baba ina rik’onki da girman Allah ki sake dani kamar k’usar yak’i naki na da, wannan wanda kike jira sai ya dawo gona za ki ci abinci, wannan wanda kike tarama k’anzo mai tarin yawan da ya fi na kab almajirai ‘yan uwan tafiyata, wanda kike yi mai sutura mai kyau, wanda tsabar so kika kashe duk wani dukiyar ki domun shi, Baba kin jani a jiki, nayi sabo dake, bai kamata ace akan mace, muna samun irin haka ba da ke.Baba Sadiya macece da da’ace kin zauna da ita zaki fahimceta, kiga k’ok’arin da ta dinga yi akan lalurata, kuma tanayi mun biyayya, Baba nasan kinfi kowa son farin cikina, kuma bazaki so duk wani abu da zai cutar da ni ba a rayuwa, kuma kinba rayuwata duk gudunmawar daya dace. Ki yafe ma Sadiya in ta yi miki laifi, nima ki yafe mun a bisa sab’a miki da nayi. Ki mun izini gobe in je in dawo da Sadiya, juna biyu gareta Baba Allah ya k’addari rabo a tsakaninmu shi yasa ma akai auran, ubangiji shike tsara komai.” Goggo ta ji wani kuka yana tunkud’o kanshi daga huhunta, da kyar ta cije ta mayar da shi, jin yanda Aliyu ke lissafo mata abubbuwa yasa ta karaya sosai, tabbacin da d’a yake da ita cewar mahaifiyarshi bazata tab’a cutar da shi ba, kuma baza’a had’a kai a cutar da shi da ita ba. wannan yana zuchiyar ko wanne yaro, gashi ita a wannan fannin ta gaza, ita ta jefa rayuwar d’anta na cikinta a cikin garari, ta kashe mai gabanshi mus, gashi ta na son a karo na biyu ta kashe mai d’a.

mik’ewa ta yi da niyyar shigewa cikin d’aki, Aliyu ya kirata da raguwar murya yace.

“Baba” wani yar ta ji, Aliyu fa ita ta haifeshi, duk wannan abun tana yi ne, dan ceto d’anta soyayya ce ita a nata wautar yasa take yin duk wannan abubbuwan, dan ganin ba’a shanye mata d’anta ba. Sabida bata da ilimin addini, hakan yasa bata tausaya ma d’an data haifa ba, k’udirinta na b’arar da cikin jikin Sadiya ya na nan bata canja ra’ayiba. Ganin Aliyu a cikin wannan damuwar ya tabbatar mata Sadiya ba k’aramin mallake Aliyu ta yi ba, ita ta tsallake ta barshi, shi kuma yana nan ya hana kanshi sukuni.

“Ka tafi zuwa da safe ka ji wanne irin hukunci na yanke kan zuwa bikon ita mayyar data lashema zuchiya.” Shigewa ciki ta yi, a sanyaye ya fita a d’akin.

kai tsaye gidanshi ya nufa, ko ina tsab. jallabiyyar jikinshi ya cire, tare da rataye ta a hannun sip, ya rage daga shi sai gajeren wando, da siglet. kwanciya yayi a daidai in da Sadiya ta saba kwanciya, wani irin kewarta ce ke muk’urk’usar zuchiyarshi, tambayar kan shi ya soma yi, Ashe dama haka so yake da dad’i, kuma ya ke da wahala, ashe haka so yake da nauyin daya zarce a d’aurashi a sikeli dan tantance ingancinshi?” Had’uwa da Sadiya ne ya gane ainihin soyayyar gaskiya ba lalube a cikin duhun da yai ma khadija ba. Bawai son khadija bane ba yayi, a’a mizanin son da yake ma khadija da Sadiya ne da banbanci, baya jin nauyin son da yake ma khadija, in aka auna zai wuci nauyin buhun omo. So yai ma khadija mai cike da yarinta, Sadiya kuma Sonta ya ke yi da girmanshi da hankalinshi, da kuma tunanin abunda zai fi dacewa da rayuwarshi. A cikin wannan dare Aliyu ya kasa bacci sam, sai tunanin Sadiya, tare da son kasancewa da ita yake yi, first night d’insu kuwa sai tariyo kanshi da kanshi ya ke yi, kai tsaye daga kwakwalwarshi.

Hakama Goggo Asabe tunani sukaita yawo a kanta, ta na mai cike da jin ciwon mutuwar auren Fatima, kuma a lokaci d’aya ta na mai takaicin samun cikin Sadiya, ga maganar takaddar saki da su mai dambu su ke so a basu, damuwowi goma da ashirin ne suka dameta, a haka har alfijir ya keto assalatu.”  Aliyu ne ya mik’e akan daddumar da ya gama sallar nafila, tare da addu’ar in dai alkhairine auranshi da Sadiya Allah ya dauwamar da zamansu a matsayin ma’aurata anan gidan duniyar har da k’iyamar, in kuma babu alkhairi, Allah ya kawo musu mafita. raka’atanilfajir ya gabatar, sannan ya wuce masallaci, dan shine limamin masallacin gidan mai gari wato sirikinshi mahaifin khadija. Bayan an idar da sallar ne Aliyu ya matsa kusa da sirikinshi bayan sun gaisa yace.

“inaso in yi magana da talakawanka ne ranka shi dad’e.” mai gari yace.

“Babu damuwa an baka izini, in ka gama nima sai muyi tamu maganar. mik’ewa Aliyu yayi, bayan yai sallama tare da bud’e maganar da zai gabatar da adda’a sai ya d’aura da cewa.

“Dama akwai tunani da nake da shi ne akan Al’ummar wannan k’auye namu, duba da bamu da wata makaranta wacce ake d’aukar darasi, kuma gwamnati har zuwa yanzu babu wani tallafi da muka tab’a samu daga gareta, shine nake neman had’in kan ku a karan kanku, inaso in bud’e makaranta wacce zan dinga koyar da ku ku kanku iyaye da yayyu na, sannan da safe kuma sai yaranmu da k’annenmu kuma in koyar da su, zuwa yamma kuma

mata iyayenmu da k’annenmu suma sai su zo gida in koyar da su. wannan wata hanyace da ilimin sanin addini zai yawaita a wannan k’auyan domun muna da k’arancin ilimin addini, bama karatu sai zuwa gona, kiwon shanu, sai zaman hira, da yawa ba su san ma yaya za su yi wankan janaba ba, alwala wannan wani bai iyata ba, baka da wata hujja da zaka gabatar a gaban ubangijinka, wa summu da yawa sun fita yawon almajirci, kun sani na sani, ba wani shiga karatun yake yi ba, wani yaron sai ya shafe shekaru yana koyon bak’ine ma, tukunna azo kan karatun da yunwa, da rashin wanka, da rashin nutsuwa baya bamu damar gane shi. ya ku ‘yan uwana muna neman had’in kan ku, domun ceto wannan k’auyan daga cikin duhun jahilcin da yai mana yawa. sunan wannan makaranta. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA. nagode” komawa yayi ya zauna. masallaci ya d’auki shiru an rasa wanda zaice wani abun,  Yaya kabiru yaron Goggo mariya ne ya mik’e tare da jan tsaki.

“ko su waye sa’anninka da kake tunanin koyarwa oho, mai gari yaro yai kuskure ayi hak’uri. ficewa yayi a masallacin, nan  kowa sai yahau fita masu magangun zagi nayi masu harararshi nayi, akwai d’abi’ar mugun girman kai a wajan jama’ar k’auyan Raquma, kowa gani yake yi yafi kowa, gasu da d’an karen taurin kai, domun kusan rabin Raquma fulanine, gashi abun ya had’u da duhun jahilci. Haka dai masallacin ya rage daga Aliyu sai kamilu, sai kuma mai gari wanda ranshi yai mummunan b’aci, dan gani yake yi Aliyu yazo mishi da raini, kuma ya taka wani tsani da talakawanshi za su iya rainashi, tare da ganin gazawarshi, cewar shi bai bud’e musu makaranta  ya kuma koyar da su ba, sai Aliyu, bacin shi mai garin yasan bashi da ilimin koyarwa, na sallama fisga akeyi da k’arfi.

“Sannu wanda ya iya ya je ya koyo, ina da rai ni kuma ke mulkin Raquma ka sake zuwa da wagga batu, zan yanke ma hukunci mai tsauri, kaga yaro da tsaurin ido, ko Sulaimanu bazai shiga gonata haka ba, ka fini tunanine? in ma makarantar ce sai dai ta fito a k’ark’ashin mulkina kuma in zama mai makarantar kuma malamin. in ba gwamnati ba banga wanda zai bud’e makaranta a Raquma ba saini.” Aliyu yai sororo yana duban shi, yanda yake magana cike da duhun jahilci, an barshi da sab’a malum malum, da tuk’ar goro a baki.” Kamilu ne yace.

“Allah ya huci zuchiyarka mai martaba, ba yana nufin cin fuskarka bane, a tunaninshi fari ciki za’a yi a bisa ci gaban k’auyanmu da samun makarantar addini ta farko a tarihin k’auyan.” mai gari ya watsa ma Kamilu harara yace.

“To mak’unshin gishiri, sannu da bayani shi bashi da bakin ba da hak’uri ne?” Aliyu wanda zanshi ya b’aci ainun ya dubi sirikin nashi yace.

“ai ba laifi nayi ba. maganar ilimin addini akeyi, makaranta ta Muhammadiyya.” shiru kuma yayi tuno cewar shi babbane kuma ko ba komai yana auran d’iyarshi, amma da kyar yai controlling  fishinshi, domun kunsanfa gadanga  akwai zuchiya sai in ba’a tab’osu ba.” mai gari shima cikin fishi ya ce.”

“Yarinya ta wajena da Allah ya k’addari aure a tsakaninku, toh kai dai ga yadda ka zama, ka zama ba namiji ba, shine muka yanke shawarar a tsakaninmu a yi hak’uri haka da auran tunda dai baka da kuzarin da zaka iya rik’e mace, dan haka ka sake ta, taje ta samu wani namijin can ta aura.”

cikin jin tsananin zafi, jikinshi har rawa yake yi, wata jijiyace guda d’aya ta tsaya mai a tsakiyar goshinshi.

“Tunda saki ku ke nema sai ku biyani duk  abinda na kashe mata, ta kuma biya ni sadakina.” mik’ewa yayi ya fice a masallacin tsabar b’acin rai ko gani sosai ma ba yayi.

sai zuwa can kamilu ya fito, bayan ya gama tausar mai gari wanda ke cewa za su je kotun musulunci a Zamfara.

Aliyu na tsaye a k’ofar gidansu kamilu, a wajan kamilu ya iske shi, idanunnan sun yi jawur sun cika da ruwa, damma jarumine da sai yayi kuka, domun abunda ya ke ji a cikin zuchiyarshi bazai kwatantuba, babban abunda yafi b’ata mai rai a cikin zancan Khadija shine kalmar rashin kuzarin da mahaifinta ya jefeshi da shi.

mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

41~42

“Aliyu da baka biye mishi ba, kai kan ka kasan waye mai gari, kuma ko babu komai kana auran d’iyarshi ne.” Aliyu ya dubeshi da jajayen idanunshi yace.

“Ya riga dama ya gama tunzura ni a bisa maganar makaranta, ni inason kawo haske, shi yana kare kujerar shi.”

“Toh yanzu yace kotu zai maka k’ara saika sakar mai d’iya.”

“Zan ga wanda ya isa ya sani dole, jahilci ne zai sa ya kaini kotu, acan al’kalin da yake girmamawa ya ji komai daga gareshi.” Kamilu yace.

“Mu bar wannan, tafiyar tawa na d’aga ta zuwa k’arshen shekarar nan da muke ciki. Ya kuka yi da Baaba kuwa?” Ajjiyar zuchiya Aliyu ya sauke, labarta mai komai yayi.”

“Ina jiran me zata ce yau ne, jiya ban ko iya runtsawa ba, tsabar damuwa Kamilu. Daga nan wajan Baaba zanje dan jin me zata ce mun, ni fa ko bata bani umarnin zuwa dawo da Sadiya ba, zanje kamilu, domun ya kamata abu sahunta” Kamilu ya dafa shi yace.

“Duk yanda kuka yi da Baaba zanji, inta kama ni inje in dawo ma da’ita sai in je. Maganar makaranta ka ajjiye a gefe tukunna.”

Sallama su kai da juna, kamilu ya shiga gida, Aliyu ma ya nufi hanyar gidan.

da Yaya Kabiru, da Yaya Sulaiman yaran Goggo mariya kuma manya a gidan ya ci karo, su na tsaye suna jiran shigowar tashi.

Su Yaya Sajida, da Yaya Rukayya, da Yaya Safiya, yaran Kawu ne su ka shigo gidan da gayyar yaransu. A wajan su Yaya Kabiru su ka tsaya.

“K’aramin taro mazan gidan su ke yi ne? Banga Dauda da Anas ba.” Cewar Yaya Sajida data kasance Babba a mata a gidan. Kabiru yace.

“Hmmm wannan shashashan yaron ne ya ajjiyemu a masallacin gidan mai Gari, sabida tsaurin idanu wai mu zai dinga koyarwa a masallaci, sai kowa ya bar abunda ya ke yi ya zauna yana sauraranshi, kuma wai har matan mu duk zai had’a ya koyar.” Baki Ya Sajida ta tab’e tace.

“Ada mu Bamu san k’aninmu da rashin kunya ba, har saida ya auro ‘yar boko, mai bud’ad’d’en idanu, wacce bata ganin kowa da gashi, shine ya zama mara kunya. Amma za mui maganinta a cikin gidannan damu take zancan.” Yaya Ruk’ayya tace.

“Sadiya fa ance ba k’aramar ‘yar duniya bace, ita da take aiki a cakud’e da maza, suna gugarta tana gugarsu.” Runtse idanu Aliyu yayi, domun gangar kishin matarshi ce ta kad’a a zuchiyarshi, har sai da zuchiyar shi ta girgiza. ‘Daurawa tayi da cewa.

“Ba dole Aliyu ya zama mara kunya ba, Hmmm nikam na shiga ciki.” wucewa ta yi b’angaren kawu mahaifinsu. Yaya Safiya tace.

“Amma ba daidai bane a sama Sadiya k’ahon zuk’a haka ba, Sadiya fa ba bare bace a gidannan, itan jininmu ce, dan k’asa ta rufe ma mahaifinta idanu, sai kuma d’iyar da ya haifa ta zama mujiya a cikinmu, dan kawai ta yi Ilimin zamani?” Ranta bai yi da’di ba da taji ana yab’ama Sadiya irin wad’annan muggan alkaba’en. Aliyu dai yana jinsu bai ce musu komai ba, Su Yaya Kabiru su ka mai tatass a tsaye a wajan. A wajan su ka wuce suka barshi, yana bin takunsu da kallo, baki ya ciza kawai, shi yayi musu uziri dan yasa jahilci ke d’awainiya da su, amma ba k’aramin tausar zuchiyarshi yayi ba shiyasa bai tanka musu ba, domun in cewa yayi zai tanka. ba za’a kwace lafiya ba, abunda ke gabanshi shine zuwa dawo da Sadiya.” Ahankali ya juya zuwa d’akin su.

Goggo na zaune ita da Fatima, yai sallama ya shiga, waje ya samu ya zauna, Goggo ta bishi da Harara.

“Baaba taron me za’ayi a gidannan da ni ban sani ba? Naga su Yaya Sajida har sun hallara.

ciki ciki tace.

“Sabida maganar Fatima da Ramatu ta wajan Iya, sai kuma taron cikin gida da aka jima ba’ayi ba, Iya ma tana hanya, in ta zo kayi k’ok’arin had’amu fad’an da zata tsine mun, kai kuma sai kasa ruwa  a k’asa kasha. k’asa yayi da kanshi wanda ke yi mishi ciwo sosai.

“Baaba toh da inason tafiya Kano yau sabida dawo da Sadiya.”

“Toh Sarki na Sadiya, babu inda zaka je baka da lafiya, tafiya ma da kyar kake yi, amma a haka za ka yi zaman mota, ciwon da aka cema baya son zafi, da jijjiga.” murya cikin sanyi, cikin tsantsar biyayya yace.

“Baaba toh ko akwai wanda kika wakilta dan zuwa bikon nata? Juna biyu gareta na fi son tana gabana ina kulawa da su, tunda hakkinane yin hakan.” Goggo tace.

“Kai fita idanuna ka ji, Sadiya anan dai babu mai zuwa bikonta, domun babu mai k’aunarta balle ya ji kewar rashinta. Af ni na manta, mai dambu da mai gari, harma da yardar khadijan dan a gabanta akai komai. So suke ka saki khadija, tunda yanzu baka da lafiya cikakkiya.” wani b’oyayyan murmushi ya saki ta gefen bakin shi kawai.

“Mai garin ya yi mun magana yau, mun gama magana, zaki ji komai k’ila a wajan mai dambu ma.”

Sallama su ka jiyo daga bakin k’ofar d’akin nasu. zainaba, da zuwaira yaran Fatima ne su ka shigo a guje. Babansu yana tsaye a bak’in k’ofar d’akin, Aliyu yace.

“ka shigo Baban Ibrahim.” shigowa yayi a mugun kunyace, kasa had’a idanu da kowa yayi, Fatima ma sauke kanta k’asa ta yi, yaranta na jikinta suna wasanninsu, cikin girmamawa ya gaishe da Goggo, a da’kile ta amsa mishi”

“Dama yaranne su ka ce in kawo su wajan umman su, jiya ko bacci ban samu yi ba, sai kuka suke yi.” Aliyu yace.

“Dama ina da shirin zuwa in sameka har gida domun naji, menene Yaya Fatima tayi ma har ka yanke d’anyan hukuncinnan? Ga yaranku har biyar.” Goggo ta mik’e ta ja Fatima tace.

“Mu je Fatima, yara kuma in zaka wuce ka wuce da su, ka kaima mahaifiyarka ta rik’esu.” Fita su ka yi, Aliyu kuwa dan kunya kamar zai nutse a wajan.

“Aliyu wallahi daidai da sau d’aya Fatima bata tab’a kwatanta yi mun biyayya ba a zamantakewarmu, kwanciya da ita in zan yi, sai ta nemi shinfid’amun dokoki masu tsauri, har mahaifiyata Fatima take yi ma rashin kunya, har kuka mahaifiyata take yi akan Fatima, hakan ne ya sanya yayyu da k’annena basa mutumci da ita. Abunda ya faru har na sake ta shine, tunzurani tayi, dan kawai nace aure nake so in sake, Aliyu a sanadiyyar Fatima har matan banza nake bi dan in biya muk’atata, ni namiji ne wanda bazan ma iya kwana biyu ba tare da d’umin matata a jikina ba. Daga cewa zan yi aure, sai Fatima ta d’auko ruwan zafi ta shek’amun a jikina, cikina ma akwai inda ruwan ya k’onani, Allah yasa ruwan bai tafasa bane.” Baban Ibrahim ya d’aga rigarshi ya nuna ma Aliyu wajan k’unan k’aton k’una an barbad’eshi da maganin galgajiya. Baban Ibrahim ya d’aura da cewa.

“kuma haka ta zage ni ta uwa ta uba, hakanne yasa na saketa saki biyu, ni na manta shaf cewar akwai saki d’aya a baya” Shiru Aliyu yayi, domun ya girgiza da rashin kunyar Yayar tashi, ya tsinke da lamarin, a hanakali Aliyu yace.

“Baban Ibrahim abunda ka aikata na zina laifine babba, ka yi kuskure da har ka bar xuchiyarka ta rinjeyi gangar jikin ka wajan aikata zina, dan kawai mace. Mai yasa ba ka d’auki azumi ba, ko kuma ka bari sha’awar ta kashe ka ka huta ma baki d’aya? ka yi gaggawar tuba kaita istingifari Allah zai yafe ma kuskuren daka aikata, amma ka dage wajan adda’a kar dattin zina ya hau kan yaranka da basu ji ba, ba su gani ba, ka koma da yaranka, kai musu tarbiya mai kyau, bayanin da kai mun na ire iren rashin mutumci da Yaya Fatima tai ta tabkama, zan sanar da su in mun je wajan zama, sirrinka kuma ka d’auka tamkar ka hak’a rami ne ka zuba shi.” Godiya sosai yai ma Aliyu, a tare su ka fito daga d’akin Goggo, Aliyu yai b’arayin Kawu, shi kuma ya na ri’ke da hannun yaranshi ya fice a gida.

Da Sallama Aliyu ya shiga falon, kowa ya hallara Iya yanzu isowarta kenan, ganin Aliyu shi kad’ai ne yasa tace.

“Sadiya ma ta zo ayi da ita, ai ita ba suruka bace.” Yaya Sajida ta tab’e bakinta ta kau da kai gefe. Aliyu kuma bai ce da Iya komai ba, dan baisan me zai ce ba. Kawu yayi k’arfin halin mik’ewa ya soma jawabin abunda ya hassasa wannan taron na gaggawa, tare da ba Aliyu umarnin bud’e taro da adda’a” cikin nutsuwa ya dinga ragargazo adda’a da harshen larabci, bayan ya gama adda’ar ne Iya tace.

“Toh manya manyan abubbuwa sun faru, na farko shine batun b’atan mijin Rahama, da kuma batun Sakin Fatima, wanda shi Sulaimanu yai k’ok’arin zuwa ya sanar da ni.

Ku mata matan bari in soma daku, Aure ba hauka bane, hakurine, ki sani ko kin kaso auranki kin dawo gida, wani namijin zaki aura, dan ba uwarki zaki aura ba. Fatima za mu baki dama muji me ya had’aki da mijin naki, ko kuma Asabe ta cika burinta na ganin kin dawo bazawara?” Fatima ta shiga nuk’u nuk’u na rashin gaskiya aka yi a ka yi ta k’i ta yi magana. Aliyu ne ya d’aga hannu ya ce.

“Ina da magana” Dama aka bashi, nan ya basu labarin rashin mutumcin Fatima tiryan tiryan, sai sirrin mijinta ne kad’ai bai yi magana a kai ba.

Nan kowa ya shiga tafa hannu da karkata kai, ai kuwa nan Iya ta caccaketa iya son rai, Fatima taci kuka ta k’oshi.

“Sai maganar  Rahama, tsakani da Allah ni inaso Rahama ta bar gabana ita da yaranta, Safiya babbar ce kad’ai za mu ci gaba da zama da’ita, Sauran yaran tara da ita cikon na goma za su zauna anan, dana koma zan sako su a abun hawa su tawo, za so mata da kayanta. wallahi in na ci gaba da zama da ita a gabana tausayinta ne zai ajalina, abun yayi mata yawa kai jama’a. Kuka iya ta  fashe musu da shi, harda sheshshek’a. Kowa a falon ya amince da dawowar Rahama da yaranta gidan, Aliyu ne yace yana da magana.

“Iya ni a ganina Yaya Rahama ta ci gaba da zama dake zai fi, duk wani tallafi da za mu yi mata, tana gaban naki za mu yi mata. Iya yaran nake dubawa, suna makarantar arabi da boko, kuma ita ma tana d’an aikinta, Iya ki barsu a gabanki, hatsi dai zan taimaka muku dashi, na cefane kuma su Yaya Kabiru sa  dinga harhad’a muku. Ilimi na da amfani Iya musamman ilimin ‘ya mace” nan fa aka yi ca a kan Aliyu da maganganu, harara Goggo ta zuba mishi, tasan duk wannan maganar ilimin da ya ke yi dan Sadiya ne. Iya ta ce.

“Ya isa hayaniyar haka, yaro ya fad’i gaskiya kuma sai na ji na gamsu, dan yaran ko basu tsira da komai ba sa tsira da ilimi, kuma zai rik’esu a gaba. Dama rashin abincinne yake tayar mun da hankali, kuma duk laifin Sulaimanu ne.” Kawu ya sauke kai ya dinga ba iya baki.

a haka dai aka gama wannan taron kowa ya  kama gabanshi.”

Sadiya

Babur d’inmu ne ya sauka a k’ofar gida, da kyar na sakko, dan ciwo ya sake tsananta fiye da na da ma, marata sai karta mun ciwo take yi, ga jiri, da bushewar baki duk ni kad’ai. Sallama mu ka yi a cikin gidan. Ba kowa a tsakar gidan, ko wacce tana shashinta

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

43~44

Kai tsaye muka wuce shashen Goggo Asabe, Yayi daidai da b’ullowar Aliyu ta wata ‘kofar, dan ‘kofofine a gidan kashi kashi. Idanu ya zuba mini, cikin wani kallo me ma’anar me yasa zaki yi mun haka?” jikinane ya sake mutuwa sabida marairaicemun da yayi, tare da cika ni da kallon k’auna. Ni kaina naji sanyi sosai dana yi tozali da Aliyu. Da sauri ya iso wajansu Goggo hansatu, ya amshi jakar kayana, da wata k’atuwar laida wacce ni kaina bansan meye a ciki ba.”

“Goggo barkan ku da zuwa, inata shirin tahowa sai kuma ga ku. Sai sauke kai yake yi dan kunya. Goggo Hansatu tace.”

“Aliyu kenan babu komai ai duk d’aya muke, an riga an had’u ai, yanzu dai tare muke da bak’o yana waje ka shigo dashi.” Sai satar kallona Aliyu ya ke yi, ni kuma bance mishi komai ba. Da sauri ya nufi b’arayinmu, na bi takunshi da kallo, har zuwa wannan lokacin Aliyu jinya yake yi, domun baya tafiya daidai. A bakin d’akin Goggo mu ka yi Sallama, izinin shigowa ta bamu, ganin mune yasa ta had’e rai, ko me kuma ta tuno sai ta d’an saki fuska har tana cewa.

” ‘Yan balaguro an dawo?” k’asa nayi da kaina kawai, cikin ladabi na gaisheta, tare da tsantsar kunya. Babu yabo babu fallasa ta amsa mun. Goggo Binta tace”

“Asabe bayan rabuwa, mun same ku lafiya ko?” Goggo tace.

“cikin k’oshin lafiya Binta, saukar yaushe?” Goggo Binta tace.

“Kusan sati biyu kenan.”

“Ayya” shine abunda Goggo Asabe tace, gaisawa su ka yi da Goggo Hansatu, daga nan ta tsuke bakinta tai shiru, Goggo Binta tace.

“Asabe ga Sadiya mun dawo muku da abunku, sai hak’uri, kuma bata kyauta ba data tsallake gidan mijinta ta tawo gida, ga k’aramin ciki a jikinta, sun sha wuya sosai baki gani ba” Goggo Hansatu tace.”

“Toh in banda Sadiya, ai ta san Mahaifiyarta ba zata yarda da zuwa gida ba, dan ba tarbiyyar da ta ba Sadiya kenan ba, ita kanta ba haka ta taso ta gani a gidan mu ba, dan ita kanta Yaya Aisha Bata tab’a kawo mana k’arar Mijinta ba.” Goggo tana sane ta gane magana aka caka mata.

“in banda abunki Hansatu, d’an mutumci ake sai ma mutumci, sannan kowa yaga alkaki yasan daga cikin zak’i ya fito, ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake yi, Ba za ki sai ma Aisha k’uri’ar mutumci a idanunana ba.” Tsaki ta yi, tare da kawar da kai, Goggo Hansatu zata yi magana, Goggo Binta ta d’aga mata hannu cikin dauriya tace.

“Bari mu shiga daga ciki, mu samu daga nan mu wuce, Asabe da alkhairi” Ba su tsaya jiran amsar Goggo ba, mu ka fita zuwa b’arayina.

Aliyu yana zaune a falo shi da Malam mustapha Kaka, suna ta hira cikin sakewa tamkar sun san juna. Da sallama muka shiga d’akin, Goggo Hansatu tace.

“Malam Kaka kuna tab’a hira da surukin naka ne?, toh bari mu zo sai mu koma.” D’aki muka shige, Aliyu ya bini da kallon zan kama ki ne, murmushi kawai na yi mishi.

“Sadiya ki yi hak’uri da duk abunda Asabe zata yi miki, ki mayar da hankali wajan kula da kan ki da mijinki, kinga bake kad’ai bace, kar ki sama kan ki damuwa, na ga sonki a idanun Aliyu, kuma yaron yana da hankali kamar ba Asabe bace uwarki, nan da wata bakwai zan dawo in zauna dake har sai kin haihu kuma, sai in koma.” Goggo Hansatu ke magana, Goggo Binta tace.

“Kar ki sake yin yaji  koma meye zai faru in dai ba shi Aliyun bane ya ce ki tafi, ai sai matan gidan sui miki dariya, mu za mu koma, Sadiya ki dinga cin abinci ko dan lafiyar Bab’yn na ki, kuma ki tabbatar kinje awo koda sau uku ne.  mu kam zamu tafi.”

Goggo ba ku ci komai ba toh.”

“A’a babu komai za mu sai abinci a hanya, ki kwanta ki huta kinga kina jiri.”

Na so in musu rakiya amma fur basu amince ba, sai Aliyu ne ya raka su zuwa waje, Goggo Hansatu tace.

“Aliyu sai ka kula da ita, ka dinga taimaka mata wajan kama mata aiki, dan bata da cikakkiyar lafiya, daga asibiti kai tsaye mu ka dawo da’ita, tasha wuya ita da Babyn.”

Aliyu yace.

“Babu damuwa in sha Allah zan taimaka mata, bazan ma dinga barinta ta na yin aiki ba, nagode sosai, ace ma mama nagode, sai mun zo.”

Sallama su ka yi,ya na Allah  Allah ya koma wajan ‘yar matar shi.

Sadiya

 a tsaye ya same ni ina gyara gyara gado, kuguna ya rik’e da dukka hannunshi, ya manna bayana a jikinshi.  idanu na lumshe kawai, dan naji kewarshi sosai, wani abu ne naji yana yi mini zullo a jikina. a kunnena ya soma mun rad’a.

“Ashe zaki iya tafiya ki barni a lokacin da nake tsananin buk’atar kulawarki a gareni, Sadiya baki san cewar zan iya sadaukar da dukkan abunda na mallaka domunki ba? Soyayyar da nake miki tafi gaban misalin da harshe zai iya furtawa. Gangar jiki ce kawai zata iya amfani wajan fallasa miki asirin zuchiyata.”

Ahankali ya juyo da ni, ya manna ni a jikinshi.

“kin ji Sadiya na samu lafiya, kin ji ko?” kai na kawai na gyad’a mishi, dan bana jin harshena zai iya sarrafuwa wajan had’a kalma mai ma’anar da zai fahimta. Amma naji takaicin tafiyar da nayi na barshi. Kuma ni kaina na jigata

“A shirye nake na kai ki duniyar ma’aurata. kuma daga yau har zuwa ranar da zaki haihu na haramta miki yin ko wanne irin aiki ne, zan miki komai da kaina, ke sarauniyace ki zauna, ni bawanki ne Sadiya.”

Bakinshi ya saka a cikin nawa, harshenshi nai ma rik’on alawar yara, munfi minti goma muna turama juna sak’on kewar junanmu. kwana d’aya babu Aliyu ji nake tamkar shekara ne. Ina mamakin yanda Aliyu ya cika zuchiyata, har yake shirin zuba, dan zuchiya ta cika da son nashi.”

kwantar dani yayi a hankali, jikina ya bi yana ta yi mun tausa mai dad’i, wani feelings yana fisgata, idanuna a lumshe suke sosai. Hakan ya sa Aliyu shiga wani halin, gashi bai warke ba, balle in bada kai bori ya hau.”

Bansan sanda bacci yai awon gaba da ni ba.

Aliyu

zuba ma Sadiya idanu yayi, yana ji tamkar yafi kowa more mata a duniyar nan, yana mata wani irin so da bazai musaltuba. yanxu ganinta har ya warware mai duk wata damuwa da ya tsinci kanshi a ciki.”

Fita yayi kai tsaye zuwa kitchen, kananzir, ya duba ko akwai, ai kuwa ya ‘kare.

karar da take gefe a tsakar gidan ya nufa, murhun dutse ya had’a, ya jera karar nan, ya kunna mata wuta, duk ya had’a zufa. Bayan wutar ta kama mishi da kyar, sai ya d’aura ruwan tea. Komawa yayi cikin d’aki ya fito da wankin shi da na Sadiya, ya soma yi. Ya gama shanya mata rigar baccinta kenan. Goggo na shigowa gidan.

turus ta tsaya ta zuba ma Aliyu idanu wanda ya ke ta gurzar siket d’in atampa, bai ma san Goggo ta shigo ba. Hawaye ta soma zubarwa.

“Aliyu kenan, kai ne da girki da wanki, ka ce bawa Sadiya ta mayar mun da kai? Ni ko har ina damo mata fura, ashe ni ta mayar mun da yaro bawanta.” Ahankali Aliyu ya d’ago ya dubi mahaifiyarshi yace.

“ko d’aya Baaba Sadiya bata san ina yin wannan aikin ba, ni na saka kaina, Manzon Allah S A W ma yakan ta ya matanshi aikace aikacen gida Baaba.” Kuka Goggo ta ci gaba dayi tace.

“Kace kai kafin tace ne, Gaskiya Aisha ta cuceni” Kofin silbar dake hannunta ta dangwarar a k’asa tace.

“In ta fito tauraruwar taka sai ka bata tasha, yana taimakama masu juna biyu.” Ficewa ta yi a b’arayin, cikin b’acin ran da ya makanta ganinta, zama ta yi shiru akan gadonta mai rumfa, tunanin yanda zata cire Sadiya daga cikin rayuwar Aliyu kenan. Fatima ce ta shigo, itama duk a dame take, tunanin tsohon mijinta duk ya addabeta, tun kamun aje ko ina ta soma jin nadamar baro d’akin auranta ta dawo gida. akan Goggo ta tsaya.

“Baaba amma lafiya na ganki a cikin wannan yanayin?” Goggo ta dubi Fatima rai a jagule tace.

“Aliyu naje na tarar yana yi ma Sadiya wanki, harda girki fa, abun mamaki ita kuma tana d’aki, in nayi sake wallahi wata ran sai Aliyu ya ne mi izini a wajan Sadiya zai gaishe ni, ni burina shine ya sake ta uban kowa ya huta, abunda ke cikinta ma ni bana buk’atar sake had’a iri da su. Ni da Aisha ta fi tsana, yau d’iyarta ce ke aure a cikin gidan d’ana? Kai ina wallahi sai yarinyar nan ta bar gidannan nasan yanda zan b’ullowa lamarin” zama Fatima ta yi.

“Baaba raba auran Sadiya da Aliyu shi ya fi, domun wayau za ta yi ta mai, balle yanzu data samu ciki, zata fake da ciki tai ta gasa shi, shi kuma dake sabon shigane, haka zaita rawar kai.” Tattaunawa suka jima sunayi, tare da shawarwarin ina zasu b’ullo dan ganin wannan auran ya rabu.

Sadiya

Na jima banyi bacci mai dad’i irin wannan ba, mai cike da mafarkan alkhairi. sakkowa nayi, na fito falo dan zuwa bayan gida, a tunanina Aliyu ya fita ne, ina d’aga labule, sai kawai na ganshi a gaban murhun dutse yana juya abinci, d’aga kan da zanyi, naga ya yi wanki nawa da na shi. Tausayinshi ne naji ya kama ni, lumshe idanu nayi, tare da gode ma Allah a bisa ni’imar da yayi mun, na auran miji irin Aliyu.

Bai san na fito ba har na iso bayanshi, tsugunnawa nayi, na sak’a hannuna na zagaye cikinshi, na d’aura kaina a bayan shi.

“Ina sonka Aliyu, zan rayu da kai rayuwa irin ta har abada.” Aliyu baisan sanda ya saki ludayin da ya ke juya miya da shi ba, idanu ya lumshe, hannuna dake zagaye a cikinshi ya  rik’o taushi da d’umin hannunshi sune  suka shige ni sosai.

“wannan ta zama rana mai mahimmanci sosai wacce bazan manta da ita ba a cikin kundin rayuwata, a karon farko da kika soma furta mun kalmar so kenan, zan kasance mai rik’e miki amanar kaina, na karb’i amanar sonki, bazan tab’a kasancewa silar zuban hawayenki ba, sai dai in kasance silar saki dariya.” mik’ewa yayi dani a bayan shi, nan ya shiga zagayawa dani a bayan shi.

“Da naso ki raka ni Abuja wajan abokina, wanda muka gama jami’atul madina da shi, toh sai na ji Goggo tace mun har a asibiti kika kwanta, kuma a hanyar dawowa ma kinsha wuya, gashi jikin ki da zafi sosai. Yau zan ciyar dake girki na, na soyayya, in kika ci sai in miki wanka, ko? sannan sai ki yi sallah ki koma kiyi kwanciyarki, ai kece da ni baki d’aya, sai yadda giyar k’aunarki ta jani ta kaini.” Ni dai nayi lakwas, ji nake tamkar mu kwana a cikin wannan shauk’in son.”

Aliyu harya juya zai kaini d’aki, sai kuma na ga ya juyo. Fatima da Goggo muka gani a tsaye a bakin k’ofar shigowa, da dukkan alamu kuma sun jima da tsaiwa. Turus Aliyu yayi a tsaye, ni ma tsabar fad’uwar gaba, da yanda jikina ya ke rawa, ga kunyar data baibayeni kasa sakkowa sam nayi a bayan Aliyu, shima ya kasa sauke ni,k’asa mu ka yi da kanmu.

Goggo kuma ta zuba mana ido tana k’are mana kallo, ita kad’ai tasan me take ji a zuchiyarta a wannan lokacin, domun yanayinta ya nuna cewar ta shiga cikin tashin hankali sosai.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

45~46

—-” Kasame ni a shashe na, in ta baka umarnin amsa kiran mahaifiyarka, in kuma uwarka ka mayar da ita ma dai na gani”

Tafiya ta yi ta barmu a wajan jiki a mace, ahankali Aliyu ya sauke ni, idanunshi sun kad’a sun zama jawur ya juyo ya kalleni, karayar da ya gani a fuskata ne yasa shi ya rungumeni tsam a jikinshi, yana shafa mun baya na, cikin rad’a yace.

“Karki damu kan ki, zanje in dawo, ban amince ki yi kuka ba, ai ke matata ce kowa ya shaida, ke dai shiga d’aki. Idanu na xuba ma Aliyu wanda ya ke takawa ahankali, ban bar tsakar gidan ba har sai da na daina hangoshi. Ko da na shiga d’akin na kasa tsaye na kasa zaune, in kai mari in kai gauro, haka nai ta suntiri, kirjina na aikin dokawa, dan bansan meye zai biyo baya ba.”

Goggo sai zagaye falonta take yi, tana yi tana dukan tafin hannunta da d’ayan hannun nata wanda ta dunk’ule, idanuwanta sunyi wata iriyar kad’awa. Da sallamarshi ya shiga falon, Goggo ta yi saurin matsowa kusa da shi daf. Mari ta zabga mai, ta sake zabga mai, bata tsaya nan ba, kawai ta rufeshi da duka kamar wani k’aramin yaro, shi kuwa yana durk’ushe a gabanta, kanshi  a k’asa. sai da ta dake shi ya isheta sannan tace.”

“Ashe mulkin mallakar dake faruwa a cikin gidan naku kenan, kai ne wanke wanke, kaine wanki, girki, wanka, bada abinci a baki, ni da nake uwarka wanne ka tab’a yi mini a cikin dukka wannan abun dana lissafo, duk d’awainiya da wahalar da na sha akan ka? Alokacin da na samu cikin ka, ban sake samun lafiya ba, saida kaxo duniya, Bantab’a yin ciki mai wahala irin naka ba, ‘yan uwana sun yi tunanin mutuwa zanyi, tsabar wahala, kuma nazo na haifeka bakwaini, babu iriyar wahalar da ban sha ba Aliyu. Yau gashi kayi girman sanin mace, wai kai ke mata hidima irin wannan, ko Adamu Aisha bata bautar da shi irin haka ba. Ka saki Sadiya yanzu na fad’a maka kenan.” Aliyu bai ce komai ba, amma jikinshi har rawa ya ke yi mishi.

“Ka saketa nace, wallahi yau Sadiya ba zata sake kwana da igiyar auranka a kanta ba.

Runtse idanu yayi, dan wata iriyar girgiza da k’irjinshi yayi, duniyarshi sai faman hajijiya take yi da rayuwarshi, bakin shi, har wani d’aci ya ke yi mishi, tsabar tashin hankali.” Tabawa ce ta fad’o d’akin kamar an jefo ta.

“Haba Asabe ya zaki ce yaro ya sau matar shi, ga juna biyu a jikinta? ki dai ja mishi kunne akan abunda kika ga bazaki iya d’auka ba. Kai kuma Aliyu ka kula, duk abunda ta nuna bata so. Toh ka kiyaye aikata hakan dan gudun fad’awa fishin iyaye.” Shi dai baice komai ba, dan zuchiyarshi ta riga da ta kad’a.

“Kiyi hak’uri Baaba hakan ba zata sake faruwa ba.” Harara ta bishi da shi kawai har ya fice, dawo da dubanta tayi wajan Tabawa.

“Me yasa kika kashe maganar nan Tabawa, kinsan shaid’aniyar yarinyar nan ta samu yaro sai azabtar da shi take yi da aikace aikace? Wannan jaraba da mai ta yi kama, ni naga yaro sai rama ya ke yi. Tabawa ta dafa kafad’ar Asabe tace.

“Asabe irin makiran matannan wuyar sha’ani gare su, abunda nake so dake shine ki rabu dasu har sai ta ji buk’atuwarta ta kai matakin da ba zata iya rik’e kanta ba, dole zata ne mi saki, a lokacin zai ji ya tsaneta sosai, itama ta gane baida wani amfani. amma yanda  aikin bokansu ke  ci, ko kinsa an sake ta, to tsugunne bata k’areba. Yaya kin zuba mata maganin  taci?” Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.

“Na zuba mata a cikin dawo, ni  da kaina ma na kai mata, ai shine naga masifa zuwan nawa.”

“Ke dai kiyi fatan tasha cikin ya xube, kuma ita da sake samun rabo har duniya ta nad’e. kinga dole ya sake wani auran, tunda mai dambu ta miki tsiya, amma ai akwai ‘yan mata a gidana har guda shida, kika kasa bashi guda. da nice yaushe haka zata faru.

Zama su ka yi, Goggo tace.

“Yanxu ma bata b’aci ba ai in dai zaki yadda, amma matsalar guda d’aya ce, kinga ba lafiya gare shi ba, kar aje a cuci ‘yar mutane.” Tabawa tace. kwantar da hankalin ki Asabe, zan ma Talatu ‘yar gayu magana, in ta amince sai ayi ai, kuma zata yaga miki yarinyar yanda bakya zato, domun ko ni wallahi ta isheni, so nake ta yi aure in huta.

Goggo tace

“Zan so hakan ta faru Tabawa, ki tuntub’eta in fa ta amince, aure kuwa kamar an yishi an gama, in kuma bata amince ba, shikenan ba rabon shi bace”

Sadiya

Tunda Aliyu ya fita, nake tsaye gashi ya jima da yawa, ya sani a cikin zulumi sosai.

Shigowa yayi, da sauri na isa gareshi, da niyyar tambayarshi yanda suka yi da Goggo na bud’e baki, Amma Aliyu sai ya zura bakinshi cikin nawa, ya jani na fad’o jikinshi, lumshe idanuna nayi, sak’onnin Aliyu suna ratsa jikina, tsaiwarce ta gagare mu, da baya da baya Aliyu ke tafiya, ni kuma idanuna a rufe suke dan na kasa bud’esu. kan gado ya jefa ni, yai mun rumfa, a wannan ranar naji zafi da dad’in da bai tab’a ratso tarihin rayuwata ba, in dai haka ma’aurata suke hawa jirgin yawo duniyar soyayya, toh lallai zan kasance a cikin layin matan da suke kasancewa harijai. k’ank’ame Aliyu na yi a jikina, dukkan mu ajjiyar zuchiya muke saukewa, amma ni fa bai isheni ba, amma kunya ba zata barni in iya sanarwa ba, kallon k’urullah Aliyu ya ke yi mun, da dashasshiyar murya yace.

“Baki k’oshi ba kema?”

kasa cewa komai na yi, jawoni ya kuma yi jikinshi, nan muka kuma shiga jirgin yawo.” Ni dai bansan sanda bacci yai awon gaba da ni ba. zuchiyata fal farin ciki, tuni mun manta da zancen damuwar da muke ciki, shi kanshi Aliyun yayi hakanne dan ya kawar mana da damuwa, duk da gwaji yayi, kuma masha Allah sauk’i ya samu, sai dai ya fama ciwon nashi har jini yake yi, nan bacci shima ya kwasheshi.

Ba mu muka farka ba sai yamma sakaliya,a tare muka farka, Aliyu ya sake jawoni jikinshi, a cikin shagwab’a yace.

“Ciwona ciwo yake yi, na fame shi. idanunshi nake kallo, ina yima Aliyu wani irin so nagartacce, mara misaltuwa, amma son da ya ke yi mun yafi gaban misali.

Kaga ni ko, kana son mayar mun da jinyata baya ko?” kunne ya kama cikin muryar yara yace.

“Bazan sake ba toh” Dariya muka yi dukka.

Aliyu Amma ya kamata ka soma sana’a inaga zaifi, ko kana son ka tsaya a iya noma da  kiwo ne?. k’ur na zuba mishi idanuna. Fuskata yake zagayewa da d’an yatsanshi yace.”

“Na yi tunanin bud’e makaranta Ne kamar yanda kika sani, amma kuma bazai yuwu yanzu ba, domun ban samu had’in kai ba. Zan soma koyarwa a Zamfara nan da shekara guda mu gani.” Na sake dubanshi da kyau, yau inajin motsin son shi sosai a raina.

“Toh Allah yasa mudace, saidai bazan so ka yi nisa da ni ba.” Bakina ya kamo, idanuna na lumshe, bayan ya saki bakina yace.

“Bari in yo wanka, sai in zubo miki abinci ko? Baaba ma ta kawo miki dawo, yana waje a sulba, kina sha’awa?. Kai na girgiza dan bana ko san ganin dawon ma. Ina kwance Aliyu yayi wanka, ya shigo mun da abinci, abun mamaki tuwo na gani miyar d’anyar kub’ewa. Da zumud’ina na soma cin tuwonnan, a gaskiya Aliyu ya iya girki sosai.

“Ina ka koyi girki haka mai dad’i, anya zan sake yin girki a gidannan kuwa? Dariyar jin dad’i na gani a bayyane a fuskarshi, yace.

“Sadiya raina ne kawai bazan iya zare miki ba, amma zan iya miki komai a rayuwa, zaki ji dad’i fiye da ko wacce mace.” Godiya nayi mishi, dawon da Goggo ta kawo mun yake ta sha yana santi abunshi. Har akai kiran sallar magriba muna hira, da kyar na yakice Aliyu a jikina, ya fita zuwa masallaci, nima na lallab’a jikina nayo wanka, naxo na gabatar da sallar magriba, bani nabar wajan ba, sai da na gabatar da sallar isha.

kamar daga sama nake jiyo kururuwar kuka da ihu a babban tsakar gida, sai na ji gabana ya yanke mun ya fad’i, da sauri na fita, zuwa inda nake jiyo kururuwar. cincirindon mutane naban mamaki na gani a cure a waje d’aya, da halama wani abun tashin hankalin suke kallo, ni dai ina dosar su, gabana yana yawanta fad’uwa”

Mrs Bukhari

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

47~48

Tutture jama’a na ke ta yi, ni dai burina in ga shin me suke gani ne.

Tashin hankalin dana gani ayau bazan tab’a mancewa da shi ba iyakar tsawon rayuwata ba. Aliyu na gani a kwance yana aman jini, Anas da kamilu suna rike da shi, Hawaye sun gama wanke mun fuskata, har bana iya ganin Aliyun ma da kyau, zubewa nayi a gabansu, na tallafi kan Aliyu ya dawo cinyata, baki naga yana motsawa amma ya kasa magana.

“Sadiya yaci wani abunne? Goggo ce ta jefo mun wannan tambayar, itama a cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa take. Cikin rawar murya mai cike da gunjin kuka nace.

“Dawon da kika kawo mun kad’ai yasha, yana gama sha ya fita sallah, tarin da Aliyu ya ke yi ne, ya sa na mai do hankalina dukka a kanshi, hannuna ya rik’e tsam, ni kuma nace.

“Ku taimaka mu kai shi asibiti karya mutu, jinin yayi yawa. K’ank’ame hannuna Aliyu yayi, yana girgiza mun kai, bakinshi sai motsi yake, cikin kad’awar hanta na matso da kunnena saitin bakinshi, maganar ta fito a bakinshi kamar an fisgeta.

“Sadiya d’ana a hannunki har abada, ki…….Nan maganar tashi ta shiga karkatsewa, salati kawai Aliyu naji ya kama, Mala’ikan zare rai ya zare ran Aliyu kanshi na kan cinyata, hannunshi na cikin nawa. D’imuwa da zaucewar da na yi, bazata fad’uba, duk wani mai imani saida ya tausayamun, jikin Aliyu na fad’a sumammiya. Ban sake sanin ina kaina yake ba, sai farkawa na yi na ganni a cikin uwar d’akin Goggo,  su Goggo Safiya ne a kaina, ina ganinsu na sake fashewa da kuka, domun fuskokinsu kawai ya sake tabbatarmun da Aliyu ya rasu a zahiri ba mafarki nake yi ba, babu wanda yace dani wani abun, kuka dukkanmu muke yi, duniya ta yi mun zafi sosai, sai salati nake ta jerowa ahankali, sai a sannanne wata nutsuwa da tsoron Allah ya sake shigana, kuka mai sauti na dena, sai hawaye kawai nake sharararwa, sai a lokacin na gane babu duhun dare a gari, da dukkan halama safiya ta yi dan gari ya soma wayewa. Kamilu ne ya shigo.

“Baaba Sadiyan ta farfad’o? Goggo Safiya yake tambaya, cikin sarewa tace.

“Ta farfad’o, amma ta kasa yi ma kowa magana, Asabe ta farfad’o kuwa? girgiza kai yayi halamar a’a.

“Baaba a tawo da Sadiya tai ma  Aliyu adda’a, zamu kai shi makwancinshi, ku tawo da ita.”

Haka su Goggo Safiya suka rirrik’eni, muka fito, gidannan damk’am da jama’a, niko gabana bana iya gani, duhu kawai nake gani, ga muryar Aliyu dake ta faman yi mun amsa kuuwa, wani matsanancin jiri ke d’ibata, zazzab’i kuwa mai azababben zafi ne ya lullub’eni sosai. cikin maza mu ka kutsa xuwa ciki inda gawar Aliyu take shinfid’e a cikin makara. durk’usawa na yi a gaban gawar Aliyu, daurewa nayi dan bana son in yi kuka a gaban gawar tashi, adda’a na dinga yi mishi, muryata na d’aukewa tsabar tashin hankali. Mutum ba a bakin komai yake ba. Yanzu yanzu Aliyu yake a raye amma gashi a kwance a mace a gabana. Goggo mariya ce ta rik’o hannuna, ta fito dani. Sai lokacin na fashe da kuka mai sauti, kamar na zautu, haka ina ji ina gani aka fita da gawar Aliyu, jiki na sake yankewa na fad’i Hangurarriya ( sumammiya)

Goggo Asabe

a firgice ta farka, ‘yan uwan nata duk suna kanta, tace.

“Ya mutu ko? shikenan na cuci kaina, na mutu na lalace, kai jama’a, na kashe d’ana da kaina, rayuwarshi ta k’are, ya barmun duniyar, ya sani a masifar da bansan k’arshenta ba. Zabura ta yi zata mik’e. Goggo Safiya ta danne ta, nan suka shiga salati.  A tunaninsu d’imuwace ta yi dan babu abunda suka kawo a ransu.

“Ina Aliyun yake? Kawu ne ya shigo d’akin da Goggo take, yace.

“Oh jama’a Asaben itama bata farfad’o ba tun jiya? wallahi duk mai imani in ya dubi Sadiya dolenshi ya tausaya mata sosai, sai suma take ta faman yi, ana yayyafa mata ruwa. Shigowa ciki yayi, Goggo ya gani a zaune tana kuka sosai.

“Asabe kin farka ashe? ki dena kukannan Aliyu kam Ya samu mutane, kuma ya samu yabo a cikin k’auyannan, Allah yayi shi ba mai tsawon rai bane, adda’a yake buk’ata. Ita kuma matar tashi, Allah ya sauketa lafiya, ko babu komai zamu dinga kallon jinin Aliyu. Kinga Asabe zafin rabone ya kawo Sadiya aure cikin k’auyannan, rabon mai zafi ne, Allah ya nufa ta jikinta zai samu rabo, Anas ya wuce tuni dan ya sanar ma da Aisha halin da ake ciki, itama ko zata ga ‘yan uwanta ta ji sanyi. Goggo tace.

“Aliyun da gasken dai ya mutu ya barmu, ya mutu saidai matarshi ta haifa mana madadinshi, harma an kaishi makwancinshi? wayyo Allah na tuba ka yafe mun. Da kyar suka rarrashi Goggo ta koma falonta da zama, hannunta rik’e da carbi, sai ja take, k’awayenta da ‘yan uwa sun cika falon suna taya ta amsar gaisuwa.

Sadiya

Na suma bansan sau nawa ba, da kyar hankali da nitsuwata suka farfad’o adda’a ce kawai a bakina, haka aka shiryani, xuwa falon Goggo, dan jama’a na tambayata, kowa a lokacin yasan akwai k’aramin ciki gare ni. Ina zaune bana ko iya amsar gaisuwar, khadija tana gefe na, ita ke iya amsa gaisuwa, ni kuwa sai hawaye ne ke zubo mun, ga zazzab’i dake mugun damuna. Wannan ranar, wani yanki ne na musamman  a rayuwata, ranar da na d’and’ani ‘zakin ainihin son Aliyu, ranar da na furta mai kalmar so, ranar da Aliyu yai mun girki, ya goyani a bayanshi. kuma a dai ranar ya mutu akan cinyoyina, hannayena na cikin nashi. Har duniya ta nad’e bazan manta da wannan ranar ba, rana mai d’unbun tarihi a babin rayuwata. Hawayena na share, ina tuno, murna da farin cikin da Aliyu ya shiga a lokacin dana sanar da shi juna biyu gareni. kalmar shi ta k’arshe kuwa sai kad’a mun k’ararrawa take yi.

“Sadiya d’ana a hannunki har abada ki….. daga nan maganar ta yanke, a hankali na soma magana.

Aliyu zan tsaya ma d’an ka ko ‘yar ka irin tsaiwar da ka so kayi  a rayuwata, zan bashi/bata ilimi, arabi da boko, dan ilimin ‘ya mace mahimmanci gareshi.

wunin ranar maza da mata sai shigowa gaisuwa suke yi, ni dai tunda na zauna na kasa cewa komai, Haka ma Goggo wacce sai ana zaune jingum, sai ta soma kururuwa tana sambatu. tukwane naga anata shigo da su manya manya, murhuna aka kafa manya, kamar za’a dafa abincin gidan biki.

tuwon dawa da miyar kuka su ka yi, ina kallon mata, suna ci suna hirarsu tamkar ba gidan mutuwa ba, wanda aka yi ma mutuwa shi kad’ai abun yake shafa. zuwa yamma lis kuwa, har da su dariya ina jiyowa anayi. kusa da magriba su Goggo Hansatu, da mama, ds Goggo Binta, da Amina suka iso. Ganinsu ya kuma jefa ni cikin wani irin mawuyacin hali, mutuwar saita fama kanta. Kuka su ka ta yani mu ka dinga yi, ana bamu hak’uri, Goggo Hansatu ce ta kama hannuna tace.

“Xo mu je ciki, ki samu kisa wani abun a bakin ki, in dai kina so, abunda Aliyu ya bari, ya rayu har ya dinga yi mishi adda’a, toh dole sai kin tursasa kan ki wajan cin abinci.”

Tea kakkaura aka had’amun, kai na d’aga na shanye dukka, dake babu zafi sosai, kuma bakina d’aci ya ke yi mun. A tak’aice a deren ranar a babban asibitin cikin sokoto na kwana, likitoci na ta k’ok’arinsu dan ceto rayuwata dana abunda ke cikina. Da kyar suka samo kan munfashina ya dawo, hankalin kowa a tashe yake, Goggo ita babban damuwarta kar cikin dake jikina  ya zube dan a halin yanzu babu abunda take so sama da cikin jikina”

Ina kwance ina zubar da hawaye, Goggo Hansatu hannunta ri’ke da kofin tea, amma fur nak’i juyowa balle in karb’i tea d’in. kawu ne ya shigo.

“Hansatu, tunda yarinyar nan aka samo kanta taci wani abun kuwa?. Goggo tace

“Wallahi Yaya Sulaiman bata ci komai ba, tea ma na had’a mata ta samu ta d’umama cikinta, hanjinta ya samu ya warware, Sadiya kiwa Allah karki wahalar da bawan Allahn dake rayuwa a jikinki, cinki da shanki shi ke bashi kariya, wannan damuwar kad’ai ta isa ciki ya zube, ko a haifeshi lokacin haihuwar bai ba.” Jin furucin Goggo ne yasa na tashi zaune, a baki ta dinga bani shayin har saida na shanye tas. Allura nose ta sake zuwa ta yi mun, sai bacci.”

Goggo Hansatu tace

“Yarinyar nan, in anason gano kanta, dole sai dai in tafiya da ita zamu yi, zamanta a gidan bazai yuwu ba, hakan zai iya fama mata ciwon da muke burin lafawarshi. Mama tace.

“Ita musulmace dole ta d’auki k’addarar data tunkaro mata, amma yin takaba a d’akinta yafi ye mata, Hansatu ke zaki zauna a wajanta kawai dan ki dinga lura da ita, ni da anyi bakwai zan koma. Goggo tace.

“Batun Auranki da Kaka sai dai a d’aga kenan ko kuma za’ayin? Mama tace.

“Shi da kanshi, tun a hanya ya ce mu dakatar da maganar bikin zuwa wani lokaci”

“Gaskiya Kaka yana bala’in sonki, dubi yanda ya shiga dangin Baban Sadiya, dashi ake ta k’arbar makoki. Mama tace

“Na yi mai ta yin tafiya ma, yace sai tare dani zai tafi, ya ba da ajjiyar motar shi, a wajan makiyayan da suke kula da dabbobinsu a wajan bustop  d’in.

Mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

49~50

kwanana shidda ina shan jinya  a babban asibiti, jama’ar k’auyan Raquma kuwa sai tururuwar zuwa gaisheni suke yi, Malan Kaka kuwa Bazawarin mama ya taka rawar gani, danshi yaita hidima dani, har muka koma gida. Dawowa ta cikin gidan ya fama mun duk wani mikin cikin zuchiyata, gadon da mu kai rayuwar aure tak’aitacce da Aliyu na ke kallo, kwanciyar da mu ka yi ta k’arshe na shiga bege, ‘kamshin fatar Aliyu, da yanda yake girmamani, nake ta kallo.  Gashi yau ya zama sai tarihi, Aliyu ya shud’e a doron k’asa. wasu siraran hawaye ke kwaranya a kumatuna. Goggo Asabe da k’afafunta ta tako har zuwa b’arayina dan duba lafiyata da na abunda ke cikina, ta rame sosai ta fice a hayyacinta, ni dai nasan Goggo na da sa hannu wajan mutuwar Aliyu na, ko san ganinta bana yi, ta cuceni ta kassaramun rayuwata, ta yi mun yankan k’auna da masoyina. Ranar bakwai kawayena da dama sun zo dan ayi adda’ar bakwai, ciki har da Hadixa ‘yar katsina kawata, da Zainab. Sun zagaye ni suna bani magana, a haka na soma samun sassauci, an yi adda’ar bakwai, tare da tattare duk wani kadara na Aliyu dan jiran me zan haifa sai ayi rabon gado. Washe gari kowa ya watse a gidan rasuwar, daga ni sai Goggo Hansatu ne kawai. Ta b’angaren Goggo a lokacinne abun duniya ya kuma isarta, da gida ya watse sai tunanin Aliyu ya soma hanata bacci, sai mafarkai akan Aliyu, kafin  a rufa wata da rasuwar Aliyu Goggo Asabe ta kwanta jinya sosai, jinyar da bata ko iya gane wanda ya ke kanta, sai wasu abubbuwa take yi kamar mai shafar aljanu, sanbatu iri iri. Iya bata san da rasuwar Aliyu ba, domun bata nan sai da ta dawo labarin ya isketa, ba shiri ta tawo, tana zuwa kuma ta tarad da Goggo tana cikin halin jinya.

“Ohh duniya ni haihuwar sokotawa, Asabe kece kika zama haka a wata d’aya da rasuwar Aliyu? me yayi zafi haka kamar ba musulmaba, Ina daga gefe ina sauraronsu, cikin murya irinta halin jinya, mai cike da d’imuwa tace.

“Iya ki rok’amun Allah ya yafe mun a bisa zaluntar Aliyu dama kaina da na yi, a sanadiyya ta Aliyu ya ma bar duniyar” Kaina na sauke wani tuk’uk’in bak’in ciki na turnik’eni,tuni hawaye ya gama wanke mun fuskata, ni daman nasan akwai wani abu a cikin dawon da.Aliyu ya sha, da nasan da wani abun a ciki da ni na sha na mutu Goggo ta huta ai. Muryar Iya ce ta dawo dani daga nisan da xuchiyata ta yi.

“Asabe akwai wani abunda kika aikata kenan akan mutuwar Aliyu ko? cikin nishi Goggo tace.

“Iya na cuci kaina, Tabawa ta kashe ni, mai dambu ta cuceni. ita ta kaini wajan bokan da zai zubar mun da cikin Sadiya, na zuba a cikin dawo, ashe Aliyu ne zai sha. mai dambu kuma ta kaini wajan ‘yan bori aka bani maganin da zai kassara rayuwar Sadiya. Iya Aliyu ne ya fad’a halin jinyar da bai ma warke ba ya rasu.” Kuka ne ya ci ‘karfinta, nima fashewa da kuka nayi, da gudu na bar d’akin ina haki.

“Lallai Asabe kin cika jahilar uwa, mara tsoron Allah, kin kasa d’aukar wannan auren a matsayin k’addara, kina wasa da auran da akwai rabo a cikin shi, Asabe har rashin imanin naki yakai ki iya aikata wad’annan abubbuwan da kika aikata? Toh Aliyu ya bar doron duniyar, sai ki zuba ruwa a k’asa kisha ya rabu da Sadiya, rabuwa irinta har abada. kuka ta fashe dashi, tace.

“Amma Allah  wadaranki Asabe, Allah ya tsine masu hali irin naki, ni kinga tafiyata” Iya ta suri jakar ledar ta ta fice, batai ma kowa sallama ba a gidan.” Fatima da take zaune a wajan, a gabanta aka tattauna komai tace.

“Baaba amma baki kyauta ma Aliyu ba, yaron da yake yi miki biyayya sosai, gashi kin kasheshi, nima kin zugani inai ma mijina rashin kunya, kin kashe mun aure na, kin raba ni da yarana, Aliyu kuma kin rabashi da duniya da, d’iyarshi ko ‘danshi da za’a haifo a matsayin maraya.” kuka ta fashe da shi, me ciwo. Goggo kuwa hawaye ya gama jik’e pillown da take kwance  a kai.

Sadiya

jikin Goggo Hansatu na fad’a tare da rikice mata da kuka, ina fad’in nidai tazo mu bar gidannan. Da kyar Goggo Hansatu ta rarrasheni na dawo Hayyacina, fayyace mata duk abunda Goggo tace na yi, ta tsorata sosai, kuma ta sake ganin amfanin ilimin mace, dan wannan aikin jahilci ne.

kwanci tashi asarar kwana

yau cikina yana da wata takwas, yayin da Aliyu ke da wata bakwai a kwance, ga laulayin ciki, ga rashin miji duk sai na had’e na lalace sosai, nayi wata muguwar rama, ga b’aki da na kuma yi, babu a duniya abunda ke mun dad’i. duk kwanan duniya mutuwar Aliyu sabunta kanta take yi. Dan dare da rana a cikin rok’a mishi rahamar ubangiji nake. Goggo kuma tasha jinya mai tsayi har da kwanciya gadon asibiti, amma yanzu ta warke sumul, saidai ta dawo shiru shiru abun tausayi, tayi rama sosai sai dai ta bi jama’a da ido kawai. khadija kuma ta  na gidansu har ta mance da Aliyu a rayuwarta, ta sake ta na harkokinta na yau da kullum.

Rayuwa kenan. matar Yaya kabiru, da matar Anas sun samu juna biyu, yayin da Hasiya ita kuma kullum jaraba ita da abokiyar zaman nata, sun haddasama Dauda deeprecion, domun kullum a cikin tashin hankali da tunani yake, ko wacce yai mata saki guda guda, ya korasu gidan tsofaffinsu.

cikina na kwata takwas da kwana goma sha biyu, na tashi da safe, sai na soma jin halamun nak’uda na ke yi, da kad’an kad’an, ni anguwar zoma ce, na tabbatar wannan haihuwace, Goggo Hansatu wacce yau kwananta uku da zuwa na sanar ma, babu shiri ta had’a kayan Babyn da na bata kud’i ta shiga kasuwar Zamfara ta harhad’o mana. Ina rik’e a hannun Goggo Hansatu ina d’an cijawa, Goggo Asabe tace.”

“Hansatu Lafiya kuwa, ina zaku je da kaya a cikin riyo da jaka?” Goggo Hansatu tace.”

“Nak’uda ta soma ji, shine za mu yi hanzarin zuwa asibiti, dan a can zata haihu.” Nan fa Goggo Asabe ta dirar mata.

“Ai mu a gidannan bama xuwa asibiti, canjan yara su ke yi, ko kuma su kashe muku d’a, tun daga kan margayiya Zainab matar wannan yaron aka dena zuwa Asibiti a gidannan, kasheta su ka yi, abunda ta haifa ma su ka kashe, ranar munga tashin hankali.” Goggo Hansatu tace.

“Hak’uri za ki yi Asabe, akwai had’ari babba a ce mace zata haihu an barta a gida, musamman haihuwar fari,yanda akeso ma, ko a gidan ka haihu sai ka tafi asibiti, dan a duba lafiyarki data jaririnki, ki yi hak’uri, a samu wacce zata raka mu kawai.” Fur Goggo Asabe ta k’i, da k’arfin tsiya Goggo Hansatu ta fige ni a hannun Goggo, kamar za su yi dambe, ta tasa k’eyata muka fice. Ni dai ba bakin ma magana. kafin mu isa asibiti, nak’uda zanga zanga, dan da k’yar na iya k’arasawa cikin harabar Asibitin, a harabar na kakare. wai ashe haka haihuwar take?

Goggo

sai raraka fad’a ta ke yi, har zuwa shashen Goggo Safiya tace.

“Safiya ki xo mu je, mu gani da idanunmu dan kar su yi mun canjan jika, Hansatu ta figi hannun Sadiya zuwa Asibiti, ki fito muje.” Goggo Safiya tace

“Ba mu ci ta zama ba, muje kinji” mik’ewa ta yi, ta sa mayafi su ka fice. A wajan hawa babur ne suka had’u da Kamilu yace.

“Baaba gari zaku shiga? Goggo Safiya tace.

“Matar aminin naka ne haihuwar taxo. Cikin gigicewa yace.

“Yaushe? ko d’azu naje na duba lafiyarta fa. Goggo tace

“Ai kasan nak’uda, yanzu haka suna asibitin birni. kamilu yanke uxirin da ke gabanshi yayi, ya ma manta matarshi ce kwance ba lafiya, daga lamba yake, ya siyo mata kwayar bature. Tare da shi su ka wuce zuwa asibitin.

Sadiya

Ina cikin labour room na had’a mugun zufa, idanuna duk sun firfito waje, sai cije baki da rik’e baya na ke yi. Adda’a kam duk wacce tazo yin ta kawai nake, Nafi awa biyu ina abu d’aya. tun ina iya nishin har ma na dena, marata kuwa ta d’auki d’umi tamkar zata tarwatse. ruwa da allurai sunyi mun babu adadi, a hankali nace da wata anguwar zoma.

“Ku yi mun tiyata k’arfina ya k’are bazan iya haihuwa ba.” tace

“Gaskiya ne madam, bari in samu mijinki yasa hannu sai ayi miki tiyatar kema ki huta, ga matan da su ka zo su ka same ki a d’akin duk sun haihu, har sun tafi ‘dakin hutu.”

Tana fita su Goggo na isowa.

“waye mijin Sadiya, ya biyo ni.” Kamilu bai tsaya kwana kwana ba ya bita. Goggo Asabe ta harari Goggo Hansatu tace

“Bata haihu ba har yanzu?

“Eh wallahi tukunna dai, amma in sha Allah ta kusa. Goggo Asabe tace.

“Allah yasa yarinyarnan ta haifi abunda ke cikinta lafiya, yaronnan yazo duniya ko zanji sanyi, in ina kallon Aliyu a fuskar jaririn.”

“Malam Hannu zaka saka mana, dan baza ta iya haihuwa da kanta ba, bayan dubawa da mu ka yi, sai mu ka gano kamar ‘yan biyu ne a cikin nata, zuwa wani d’an lokaci in bata haihu ba, zamu shiga da ita tiyata” inda zai sa hannun aka nuna mishi ya saka, cikin tashin hankali ya dawo wajan su Goggo”

Sadiya

wani nishi ne naji yanayin kan shi da kanshi, k’arfen gadon da nake na rik’e, kamar yanda muke ce ma mata su yi, jaririne ya sunb’ulo, amma kafin in kai dubana ga abunda na haifa, sai na ji sabuwar nak’uda zanga zanga, amma ba tai tsawo ba, na sunkuto yarinyata. Numfashi na shiga saukewa a hankali, hawaye sai zubo mun suke yi, ana yanke musu cibi aka manna mun su a jikina. Sai lokacin na bud’e idanuna na dubesu.

Kau idanuna ya d’auka, gabana yai mummunar Fad’uwa da ganin irin abun dana haifa. Runtse idanu na yi na sake bud’ewa. Tabbas zahiri idanuna suka nuna mun, rungumesu na yi sai na fashe da kuka, aduk yanda suke sai naji son su na bubbud’e mun k’ofofin jinina. ina son su, kamar yanda ko wacce uwa take son abunda ta haifa. Amma ina mai cike da tausaya musu, a yanda na haifesu, ga kuma maraici, ko ya za’a amshesu a matsayin ‘ya’ya oho, dan al’umma mugun kyamarsu da tsangwamarsu suke yi, ni kuma bazan iya juran ganin marayun yarana a irin wannan halin ba. Nose ce ta zare su a jikina, ta fita da su, ina kwance ana kwashe mun jini, mutuwar Aliyu ta dawo mun d’anya, yaranshi sun fama mun mikin dake zuchiyata. Kuka na ke yi sosai.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo

51~52

“Baiwar Allah ki dena kuka akan abunda kika haifa su ma fa mutanene kamar kowa, kuma suna rayuwa mai tsayi kamar kowa, ki taso in raka ki d’akin hutu.” Bance da ita komai ba, ni ba kukan kyautar da Allah yayi mun nake yi ba, in na yi hakan ai tamkar na butulcema kyautar da Allah ya bani kenan, ga mata da yawa na neman haihuwa Allah bai basu ba. Aliyu ne ya dawo mun d’anye. Gado ta nuna mun, da dabara nahau kan gadon, ina ta kallon matan da muka haihu a d’aki ‘daya da su, ko wacce ga mijinta a kusa da ita, ana basu kula amma banda ni. Allah ya jik’an ka Aliyu, Allah ya isar da haske kabarinka. Ga yaranka nan Aliyu, in sha Allah duniyar musulunci za su yi alfahari da su, ba zan bari su yi maraici ba. Hawaye na na share, dan na hango tahowar Su Goggo.

Sannu su ka shiga yi mun, na kasa amsa kowa, sai kuka na nake had’iyewa, amma ina. da kuka na fashe mai tsanani, kowa na wajan sai da ya tausaya, domun sun fahimci halin rashin Aliyu nake, dan an riga an sanar musu na sauka lafiya, Allah ya azurta ni da mace da namiji.

“Ki yi shiru Sadiya, tsakanin ki da Aliyu sai adda’a, dan ma Allah ya nufi zamu ga jininshi.” Goggo Safiya ke rarrashina. kamilu yayi shiru daga gefe sai bina da idanu ya ke yi. wasu ma’aikatan kiwon lafiya ne, su ka shigo da yaran a hannunsu, daya an sa mai saiti fari, dayar kuma ovaroll mai kauri da hula aka saka mata, a cikin bargo d’aya aka nannad’esu, kasancewar kayan mutum d’aya mu ka tawo da shi. Goggo Asabe da murna ta amshi yaran a hannun  wannan Nose d’in, dayar kuma ta nufo ni dan ta duba lafiyata.”

“Wayyo Allah mutane ko aljanu?  Goggo hannunta na rawa ta saki yaran a k’asa, su ka fad’i tum. Idanu na rintse, dan wani irin abu na ji a zuchiyata mara misaltuwa. Kuka na fashe da shi, da Sauri Goggo Safiya da Goggo H su ka nufi jariran da kukansu ya cika ward d’in da muke. Amma ganin yaran yasa Goggo Safiya ja da baya, Goggo Hansatu ce, ta yi k’arfin d’aukar yaran ta rungume a jikinta tare da aikin jijjigasu.

Suna kafad’ar Goggo H, Kamilu ya je ya lek’a fuskar yaran.

“Allahu akbar” shine kalmar da ta fito a bakin shi, mutanen d’akin sai bin mu da kallo su ke yi.

“Ke Hansatu, wad’annan yaran aljanu Sadiya ta haifa? Ji yara kamar yasan sarkin aljanu, tsabar fari” cikin zafin xuchiya Goggo.H tace.

“zabiya ne Allah ya bata, amma ai ko ba ku tab’a ganin zabiya ba, ai bai dace ki yar da jarirai haka a k’asa ba.

Goggo Asabe da muryarta har rawa take tace.

“Wallahi Allah ban tab’a ganin zabiya ido da ido ba, nasan dai ‘ya’yan k’azanta ne, wanda aka haifa a k’azance.”  Kai Goggo H ta girgiza kawai, za ta yi magana, wata nose ta k’araso tace.

“Dan Allah a ara mana jariran za mu d’an k’arashe gwaje gwaje a kan su.” Goggo H tace.

“Akwai wani damuwa ne a tattare da yaran?

“A’a Baaba, kinsan su irin wannan bayin Allah yawanci masu lalurar ido ce, ba su cika gani sosai ba, idanun nasu za’a duba dan a san a wanne matsayi suke.” Goggo ta mik’asu, ni dai na yi shiru na zuba ma sarautar Allah idanu.

Bayan kamar awa guda da fita da jariran da aka yi, ina zaune ina shan tea da kamilu ya sawo mun a waje, Dr ya shigo, a gabana ya tsaya ya dube ni.

“Maman biyu ya jikin na ki?”

Da sauk’i. kawai na ce mishi, ruwan da ke d’aure a hannuna ya cire mun sannan yace.

“ke kam mun sallame ki, Amma twins mun basu gado a b’angaren yara, zuwa gobe zamu tura ku zuwa asibitin sokoto, dan acan za su fi samun kulawa.” kwarewa da tea d’in nayi nan na shiga tari, aka shiga yi mun sannu.

Sai tsiyayar hawayen tausayin marayun zabiyan yarana nake yi, nan nace.

Allah ya jik’an ka Aliyu, da rabon ba zaka gana da kyawawan yaranka ba.” Dr ya zuba mun idanu. su Goggo dukka kowa ya dubi Likita. Kamilu yace

“Dr me ya same su? bayan ya gama cire mun ruwan yace.

“Basa gani sam, kasan zabiya da ma da matsalar idanu, toh wad’annan ganin ma basa yi, amma zan tura ku zuwa babban asibiti, dan a yi musu bincike da kyau, tunda sunfi nan kayan aiki, nima ina aiki a can d’in.” Kuka na fashe da shi sosai. Nan jikin kowa yayi sanyi kowa ya tausaya halin damuwar da nake ciki. D’unguma mu ka yi d’akin da ‘yan biyu su ke kwance. D’akin yarana, ga sunan lalurori iri iri, jarirai da na’urar numfashi, wasu da roba ta hancinsu, ga wata yarinya itama a kusa damu abun tausayi, uwar sai kuka take yi. Dr na ke kallo yanda naga yana juya Husaina abun ya tsorata ni, bayan ya gama aune aunen shi. sai kawai ya juyo ya dube ni tamkar mai jin tsorona yace.

“Allah ya amshi rayuwarta ita kam.” Sumewa ne kawai ban yi ba, amma duk mai tausayi saiya zubar mun  da hawayen tausayi. inaji ina gani,  Su Goggo Asabe, da Goggo Safiya su ka tafi da gawar Husaina, da k’yar su ka iya rik’eta.

Jikin Goggo H na fad’a na kuma sau kuka.

Goggo yanzu shikenan itama yarinyar mahaifinta ta bi kenan, itama rasata na yi? Allah na gode maka, ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawar, shi kuma wannan bawa naka ka raya mun shi da imani.” Hawaye na na share, na saki Goggo H wacce itama kukan ta ke yi, take wani dangana gami da juriya su ka saukar mun, ban sake yin kuka ba.

Da yamma Dr ya sake shigowa duba mu, duba na yayi.

“Yaron ya farka kuwa?”

A’a bai farka ba tukunna, kuma k’alau ya ke? murmushi ya yi mun.

“k’alau ya ke ba ya d’auke da wani ciwo in ba ciwon idanunnan ba. ki same ni a office zan rubuta miki allura a je a siyo.” Juyawa yayi ya fice. Goggo H tace.

“Toh maza jeki, ko ni zani, sabida yanayin jego ga ba ruwan zafi. Murmushi na yi mata nace.

“Babu damuwa bari in je, zan iya.

Wuce wa na yi zuwa waje, dai dai ya b’ille wata kwana, ahankali na ke jan jikina, dan har jiri nake ji, babu abunda nake buk’ata face ruwan zafi. Ko da na b’uulla inda naga yabi, ban ganshi ba, gashi ni bansan sunan shi ba. haka na gama bukayi na, harna juya zan koma sai na ji yace.

“Gani nan Halima” Da sauri na juyo, yana tsaye a baya na, yace.

“Jikin ki baya miki  dad’i ko? Nace

“Babu damuwa, akwai magungunan da zan siya dan kare lafiyar jikina, in sha. Da mamaki yace.

“Kina da ilimin hakan kenan? Bance mishi komai ba, takaddar allurar ya nuna mun, amma bai ba ni ba, yace

“Ki koma, zan kawo miki, shima wanda zaki sha d’in zan kawo miki, kije”

Wuce wa na yi, ina shiga na tadda Iya da Anty Ramatu sun iso, da ruwan zafi a flaks da abincinsu. Hassan yana hannun iya tana tofe shi da adda’a.

“Sadiya sannu da jiki, ayi hak’uri da yanda aka tsinci kai.” murmushi kawai na yi, na gaishesu da ladabi, buta Goggo.H ta mik’a mun.

“Ungo je ki kama ruwa ki ji dadi, ga abinci mai nauyi kici, kafin yaronnan ya tashi, dan nono zai naima afujajan.” Iya tacs.

“Ga zam zam da dabino ma, daya farka a tauna a cusa mai a baki, kuma a bashi zamzam ya sha.” Na sa hannu na amshi butar a hannun Goggo.H, ina jin dad’in yanda Iya ta nuna kulawarta akan Hassan, Ni sai lokacin na tuna cewar ban yi musu adda’a ba. Lallai na tabka kuskure babb.”

Dr ne ya isa wajan gadon da Sallama, Allura yai ma jaririn, sannan ya ba da sallahun magani na.

Dana fito ne Iya ke mik’a mun, karb’a na yi na sha, sai na ci tuwon da Iya ta kawo, amma ba dan inaso ba, so nake Hassan in ya farka ya samu abinda zai sha. Ina kwanciya Sai baccin gajiyar nak’uda ya kwashe ni. Su Iya sun tausaya mun a halin da na ke ciki.

Ina bacci su Anas su ka zo, Anas ne yai ma jaririn hud’uba da Sunan Aliyu.

“Iya sunan shi Aliyu Allah ya raya.”

Iya ta sa hannu ta amshe shi ta na kuka.

Bani na farka ba sai jefin taran dare, rabona da irin baccinnan tun Aliyu na da ran shi”

mrs Bukari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

53~54

“Sadiya bashi nono bawan Allah tun d’azu ya tashi, ya d’an yi kuka kad’an” Kab’ar shi na yi a hannun Goggo.

man zaitun da muka tawo da shi na bud’e. na goggoga a kayikan nonon nawa. Sannan na zura mishi.

Addu’ar da d’axu ban samu nutsuwar yi musu ba, yanxu na yi mishi nashi. Goggo ta sanar dani Aliyu aka mayar mishi.

Goggo a rink’a kiran shi Haidar. Goggo Hansatu tace.

“Babu laifi Sadiya. ni ina zuwa. Fita ta yi ta barni da kallon Haidar, fari k’al da shi, gashin kan shi ja, haka bakinshi jawur da shi, a raina nace.

Ina ma zai tsaya a haka ba tare da yayi wannan kurajen da dabbara dabbaran ciwo a jikin shi ba, da zan yi farin ciki. Murmushi na yi na shafi fuskar Haidar bawan Allah kenan, sai mama ya ke sha, ni kuma zafin shan maman har can cikin raina na ke ji.

Washe gari da safe akai mana transpar zuwa asibitin cikin gari.

Dr ne ya amshi Haidar ya shiga da shi zuwa ciki.

waje mu ka samu ni da Goggo Hansatu mu ka zauna. Mu na wajan Sai ga Kawu ya tawo, shi da Yaya Kabiru. Babu yabo babu fallasa su ka amsa gaisuwata, kawar da kaina na yi daga gare su, dan k’iyayyar da su ke nuna mun ta yi mun yawa, kuma lokaci ma ya cika da zan bar musu gidansu, Ina ji Kawu na fad’an garin yaya na haifi ‘ya’yan k’azanta, yaran da ake samun su ta hanyar, in mace na jinin al’ada aka sadu da ita shine ake haifar zabiya. Wannan a canfin da hausawa su kai ma zabiya kenan, hakanne yasa suke ganin kamar k’abilar kirista sun fi musulmai yawan haifar zabiya, musamman ma Inyamurai.” Dr ne ya ne mi ganina, ina hawaye na wuce su, sai zabga fad’a kawu ya ke yi, Yaya Kabiru na ta ya shi.

“Zauna madam”

Waje na samu na zauna, cikin k’arfafa guiwa da ya zama halayyar likitocin kwarai yace.

“Haidar kyakkyawa ne sosai, zan so ki kula da shi, da fatar shi, ta yanda ba zai samu kuraje da k’onewar fata dama, dabbara dabbaran bak’i ba. Ko dan ma guje ma Sankarar fata da ke addabar zabiya.

Duban shi nayi

“Dr in sha Allah in dai ina numfashi, kuma in dai akwai magangunam da zan yi ma Haidar amfani da shi ba tare da fatar shi ta k’one ba. Toh ni kuwa ko nawa ne zan jure siya mai. Amma Dr meye sababin da ke sa  a haifi zabiya?

yace

“Good  Albinism cuta ce da ake iya kamuwa da ita daga Iyaye, wanda abun ya shafi wasu kwayoyin halittar da ke d’auke da rashin daidaituwa  ta hanyar samar da melaninn. za a iya yad’a shi ga yaro.” Cikin fahimta nace

“Dr yaya zan yi in kare yarona daga kamuwa da sankarar fata?”

“Binciken ido da dermatological yana da mahimmanci, dan gyara lahani na gani da ke da alak’a da cutar zabiya.

mutanen da ke da albinism, riga kafin rana yana da mahimmanci don guje ma had’arin ciwon daji, sabida fatar su mai rauni ce sosai, kuma ta na kula da hasken UV. don haka kariya ga fata da idanu na da mahimmanci. ya kasance ko da yaushe ya na cikin inuwa, tare da sanya tufafi mai rufe jiki kirib. Sa tabarau dan kare ido daga hasken rana, sai shafa 50+index cream dan yana taka muhimmiyar rawa. Akwai mayuka da sabulan da zan rubuta miki. Da su za’a mishi amfani ko da yaushe.

B’angaren matsalar idanun shi kuwa, ku je zuwa nan da wata d’aya sai ku dawo dan a sake dubawa, xuwa kafin lokacin idanun zai iya bud’ewa ya soma gani ba tare da mun yi mishi komai ba.” Godiya na yi mishi sosai. sannan na fito, Haidar na je na d’akko na fito.

Gida mu ka koma, abun mamaki sokotawa Allah ya yisu da canfi, nan fa labari ya karad’e k’auyan na haifi yaran k’azanta, babu wanda ya xo mun barka, har matan gida, Goggo Asabe da su Goggo Safiya ma, babu wanda ya zo. ranar suna daga ni Sai Goggo Hansatu sai matan Kamilu ne kad’ai. Kamilu ya yanka ma Haidar k’aton rago, haka mu ka yi sunan mu, daga mu sai mu. Bayan kwana biyu muka tattara ya namu ya namu, motar kayan da zata bi yanke cikin jeji, ita mu ka bi, babu wanda yai mun batun gadon Haidar, haka na yi musu sallama ina kukan tuno da Aliyu.

Kano state

Mama na zaune a tsakar gida, tana shirin had’ama Malam Kaka sob’o, mu ka shigo. Baki ta rik’e.

“Hansatu kaddai har ta sauka?” Dariya Goggo Hansatu tayi.

“Tun yaushe har an yi suna ma, an samu Aliyu Haidar. Hamdala Mama ta yi, a baya na ta sunto Haidar, wanda na rufe kirib, hular zata janye na yi maza na rik’e hannunta.

“Mama mu shiga daga ciki, Haidar ba ya son rana. Bata ce komai ba, mu ka shiga ciki. Goggo Hansatu ta labarta mata komai, sai da ta yi hawaye.

“Ki yi hak’uri Sadiya komai mai wuce wa ne, yau ina Aliyu, baya kwanta dama ba? Toh haka za a k’are a duniyar ma. ki kula da yaronki, ki samu nutsuwar shayarwa Babu komai. Hansatu kin yi zumunci Allah ya biya ki.”

Cikin kwanciyar hankali na ke shayar da Haidar, ya yi b’ulb’ul abun shi, gwanin sha’awa da shi, kullum a k’unshe a cikin suturar da zata rufe mai jiki yake. K’awayena da basu samu damar zuwa mun ta’aziyya ba, sun zazzo, har da abokan aiki na duk sun zo. cikin shekara guda Haidar ya zama kamar yaron turawa, babu ko sofane a jikin shi, kuma yana gani da idanunshi, sosai Haidar ke samun kulawa, sai da ya cika shekara biyu cib na cire shi a mama, yana gudun shi ko ina, baki kuwa rairai. tsawon wannan lokacin babu wanda ya tab’a zuwa duba Haidar daga cikin dangin mahaifinshi.  Na koma bakin aiki na, a nan ne fa manaima su ka soma yi mun yawa, amma ni kula da Haidar da aiki na ya fi mun komai. Couse gwamnati ta d’auki nauyin tura mu ‘kasar India, bayan ‘yan setin farko  sun dawo. Tare da Haidar na tafi, couse ne da zai d’auke mu tsawon shekaru biyu. Da hakan na samu damar jefa Haidar makaranta, tunda shekarun shi uku a lokacin, muna gama couse d’inmu mu ka dawo najeria, a lokacin Haidar na da shekara biyar a duniya. Ya sake yin mugun kyau, duk in da na shiga da Haidar sai ya samu masoya, fatar shi ta yi kyau, dan acan k’asar India na samu wasu mayuka ba irin namu na gida najaria ba, kuma sun amshi fatar tashi sosai.

Na murje na sake yin wani irin kyau, fatata ta murje sosai, na k’aro ilimi na kuma sake wayewa sosai. Mama ta ji dad’in ganinmu dukkan mu, bayan mun nutsa ne sai na jefa Haidar a makarantar firamare, da kuma islamiyya.

“Sadiya na zuba miki idanu in ga gudun ruwan ki amma fur kin k’i yin batun aure, sai hidima da Haidar kawai kike yi, kinga kar mu zama abun zagi a anguwa ke ba aure ni ba aure, kinsan yanzu kiwon mutane ake yi ba dabba ba.  Ajjiyar zuchiya na sauke

Mama ba aure na k’i yi ba, ina tunanin yanda Haidar zai soma agolanci ne, amma da na yi auren, akwai wani Dr Saminu da ya jima ya na biyiyata, tare kuma mu ka tafi da shi wannan couse d’in, bayan shi akwai su da dama, Mama ba kowa ke iya auran bazawara me d’a ba, kuma ya iya rik’esu dukka, ba tare da ya nu na ma wannan agolan banbanci ba, ni kuma akan Haidar zan iya hak’ura da auran.”

“Dallah rufa mun baki, shashasha, akan ki aka soma yin aure a tafi da agola ne,ko so ki ke yi sai bakin jama’a yai ma rayuwarki illah? tun wuri ki fito da mijin aure. wata d’aya na baki, in ba haka ba za ki ga hukuncin da zan d’auka akan ki, shekarunki sama da arba’in ” A zaune mama ta barni ina tunani, Haidar na tuno da lokacin tashin su a makaranta yayi, ai ba shiri na fita da sauri zuwa makarantar.

Da gudu Haidar ya iso wajena na, rungumeshi, mu na dariya.

“umma zo ku gaisa da Abbana, kullum ya na gaisheki. Shafa kan shi na yi.

Haidar ka bari sai wani lokacin mana. Fur Haidar yak’i, hannuna ya rik’e har cikin ofishin malaman makarantar.  Da sallama mu ka shiga. D’ago kai yayi mu ka had’a idanu, saurin kawar da kaina na yi, dan ban cika son had’a ido da maza ba.

“Angle ga umma na.”

Murmushi malamin yayi.

“Sannu da zuwa umman mu.” Dariya na yi kad’an nace.

“yauwa sannu malam da k’ak’arin aiki. Ina jin labarinka a bakin Haidar, kuma na yi farin ciki sosai da kake kula dashi, ya fad’a mun baka barinshi wasa a cikin rana. Ina godiya sosai da kulawarka ga Haidar.”

Kallona ya ke yi. Ba yaro bane dan zai iya ba ni shekaru fin goma ma.

“Babu damuwa umman mu, ai d’a na kowa ne, kuma na yaba da k’ok’arin ki dan inganta rayuwar Haidar, zan zo gidan in sha Allah.” Godiya na yi mishi, na kama hannun Haidar mu ka tafi.

wasa wasa malam Safwan kusan kullum sai ya zo wajan Haidar, tare da hidimomin da ya ke yi ma Haidar, Ahmad ma ya dawo waje na, kamar zai mai da ni ciki tsabar so, amma na kasa ba kowa Fuska, Kamilu ma yayi halacci, dan yana zuwa duba Haidar sannan ya na bashi kulawa dai dai da yanda zai iya.  Ya nuna ya na son aure na, amma na nuna mishi yayi hak’uri, kuma na gode da kulawarshi gare mu.

Amina ce ta haihu yau suna, daga wajan aiki na wuce” K’awayenmu na makaranta duk sun zazzo, mu na zaune ana hira kawai sai ga Fatima, da k’aton cikinta ta shigo, sai tsokanarta ake yi, Fatima ta ji kunyar ganina dan tunda Ahmad ya aureta ba mu sake had’uwa ba.”

“Sadiya ke ce kika zama haka? Hmmm manyan mata. zama ta yi, na ce.

“Fatima ai fishi na ke yi dake, ace duk a cikin k’awayenmu babu wacce bata zo mun ta’aziyya ba, sai ke.” kai ta sosa.

“Wallahi ni kunyar abunda na yi miki ne ya sa na kasa zuwa. Dariya na yi.

“Haba.Fatima ai matar mutum kabarinshi, yaranki fa hud’u ga na biyar a cikin ki, da ya za’ayi da rabon yarannan? komai ki ka ga ya faru, ubangiji shi ya tsara faruwar shi. Dad’i Fatima ta ji, ta sake mu kai ta hirar mu abun sha’awa. Da na tashi tafiya ma ita ta yi mun ta yin mu je Ahmad ya rage mun hanya.

“Ahmad ka ga fa mutuniyar mun shirya, kuma ta fahimce ni sosai, shi dai Ahmad ta mirror ya ke kashe ni da mayyar soyayyar shi, dan shi d’in gwanine fagen iya soyayya.  yace

“Na ji dad’in wannan had’in kan na ku sosai. Hira mu kai ta tab’awa, Fatima ya soma ajjiyewa sannan ya kaini k’ofar gida.

“Sadiya so ki ke yi son ki yai mun illah ko me? Sai bani wahala sonki ya ke yi, ke kuwa sai k’ara kyau ki ke yi abunki, ni ne fa Ahmad mai yawan sonki da k’aunarki, kuma na yi miki bayanin ba laifi na bane fasa auranki da na yi ba. Hannu na d’aga mishi.

“Dakata Ahmad kar ma ka soma cewa haka, dan in ba da sanin ka hakan ta faru ba, ba zaka auri Fatima a ranar da ka fasa aure na ba, wannan abun a shirye yake, kai da ita duk munafurtata ku kayi, bazan iya baka wata dama ba.” Fitowa na yi daga cikin motar. Da Safwan mu ka had’a idanu, ashe ya na zaune a k’ofar gida yana jira na, kishi ‘karara na gani a idanun shi, har ruwa ruwa k’wayar idanun shi ta yi. Sai na ji jikina ya mutu, a hankali na iso in da yake, zama na yi a dakalin da yake zaune. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya sanya idanun shi a cikin nawa.

“Sadiya sannu da dawowa.” Kasa amsawa na yi, shi kuma sai bina da kallo ya ke yi. Mik’ewa yayi, tare da ajjiye mun ledar da ke hannunshi yace.

“Ki tashi ki shiga ciki, ni zan wuce gida, dama duba ki kawai na zo yi, ki gaishe da Haidar duk da shi yai ta taya ni hira.”

A wajen ya tafi ya barni. idanunnan nashi sun yi jawur da su, Nasan Safwan yana sona, amma nauyi da kunya sun hana shi furta wa, gashi yau ya tafi cikin ciwon zuchiya. a sanyaye na shiga cikin gida.”

mrs Bukari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

55~56

Mama da Haidar su na tsakar gida, shi yana aikin da aka basu na makaranta, ita kuma ta na karanta mujalla. Haidar ya tawo da gudu, tsugunnawa na yi na rungumeshi ina dariya. Mama ta zuba mun idanu.

“Sadiya zo ki zauna, Haidar k’arbi kayan hannunta ka shiga ciki.

Xama na yi kamar yanda mama ta umarce ni, Haidar kuma ya shiga ciki.

“Sadiya yaronnan Safwan meye matsayar maganar ku?  Na ga ya na hidima da yawa a kan ki da Haidar, me yasa ba zaki bashi dama ba? Bana son in yi aure in barki a gidannan, domun hakan ba mutuncin bane. Ko ba kya son Safwan d’in shima? Ajjiyar zuchiya na sauke nace.

“Mama bawai bai yi mun bane, ni halin da Haidar zai shiga ne damuwata. Duk da dai Safwan ya na son Haidar, amma mama bai tab’a mun maganar soyayya ba gaskiya, iyakata da shi mutunci.”

“Sadiya ho, duk wannan jewar da Safwan ya ke yi, kin fi so sai ya furta miki yana sonki? Toh ki mai maganar turo magabatanshi, sai su je can Raquma a d’aura auran ke ma ki huta.

Toh mama in yazo zan sanar mishi.”

D’aki na shiga, bayan na rage kayan jikina, wanka na yo, nazo na samu Haidar ya barbaje kayan da Safwan ya kawo mana.

mayukan Haidar ne, da sabulan wankan shi, lallai Safwan ya cancanci in bashi dukkan wata dama. Amma ta ina zan soma rarrashin shi ma? dan da fishi ya tafi.

Tun daga wannan lokacin Safwan bai sake zuwa gidanmu ba, sai dai ya aiko mun  da sak’on gaisuwa. Da dai naga tafiyar ta mik’e har wata guda, ranar na taso aiki da safe, kai tsaye makarantar su Haidar na wuce. Aike nayi a kira mun Safwan.

Yana sanye cikin wani yadi da ya sake fito da kamalar shi. Shima sai kallona ya ke yi da mamaki, take kunya ta lullub’eni. Nama rasa in ya k’araso me zan ce mishi.

“Malama Sadiya barka da wannan yanayin, idanki kenan?” Tausayi ya ba ni sosai

Safwan kwana biyu me ya faru ka dena.zuwa zance gida? Hannayenshi ya zura a aljihun shi yace.

“Sadiya na lura kamar takura miki hakan ya ke, kuma bana son Bazawarin ki me mota da yake yawan  suntiri a k’ofar gidan ku yayi tunanin ko akwai wani a tsakaninmu, kuma ni wajan Haidar Aliyu mai hula na ke zuwa. Gabana ya fad’i sosai, bansan son Safwan ya shige ni har haka ba. Jiki a sanyaye mu ka yi sallama da Safwan.

ko da na koma gida kasa nutsuwa na yi. da yamma lis yaro ya turo kira na. Da zumud’i na fita a tunanina Safwan ne, ina fita na ci karo da Ahmad. yana jingine a bakin motar tashi, raina bai so zuwa ba, dan dai na riga na fito ne. Ina zuwa in da ya ke, Safwan ya na shawo kwana Idanu muka had’a, a mugun zuciye ya koma. Ni kuwa sai lek’e na ke yi, ji na ke tamkar in bishi da gudu.

“Sadiya lafiya kuwa, naga hankalin ki baya tare da ni?” Harara na zabga mishi tare da jan tsaki na koma cikin gida na barshi a nan a tsaye.”

Safwan  yana tafe yana tunanin me yasa ma ya damu da Sadiya alhalin ita bata ma san yana yi ba? da tunane tunanen daya isa gida kenan.

Badiya ya samu ta na wanke wanke a tsakar gida, murmushi su ka sakarma juna, kujera ya jawo ya zauna a gaban wanke wanken, ya shiga d’auraye mata.

“Sannu da zuwa, yau baka je wajan su Haidar bane, naga ka dawo da wuri, kuma ranka a b’ace ?”

“Badiyya ni na hak’ura da Sadiya kawai, kamar ba sona ta ke yi ba Allah.” murmushin danne kishinta ta yi tace.”

“Gobe zan je ni da kaina dan yi ma yak’in nemo soyayyarta,burina shine inga ka samu magaji, ko ni ma na huta da gorin da ‘yan uwanka su ke yi mun.

Inna ce ta bankad’o gidan ta shigo, salati ta shiga jerawa.

“Safwan bawan Badiyya ka zama? ka fita ka nemo abinci, aikin gidanma sai ka taya ta? Dama ta cika mun gidannan da jikoki ai duk da sauk’i, yarinya ta hana ka sak’at da makirci irin namu na mata.” Da Sauri Badiyya ta mik’e, tare da rik’e jakar ledar Innah.

“Sannu da xuwa Innanmu.kawo jakar in shigar miki da’ita.” Fisge jakarta Inna ta yi tace.

“Ke zan ma sannu da xuwa dan ke ce bak’uwa, nan gidan d’anane.” Tana kaiwa nan ta shige ciki ta barsu a wajan, Safwan ya kalli Badiyya wacce take ta faman aikin tsilalar da hawaye. Rungumeta yayi yana shafan bayanta cikin sigar rarrashi. Hannunta ya kamo su ka shiga matsakaicin falon na su, da hanzari Badiyya ta zame hannunta a na shi, ita ta soma isa wajan Innah.

“Ina wuni Inna ya hanya, ya aka baro mutanen Azare?” Babu yabo Babu fallasa Inna ta amsa mata. Mik’ewa ta yi dan kawo ruwa da abinci. Safwan kuma yana gefen Inna a zaune, yana gaisheta ta yashe baki da fara’a ta amsa.

“Baffan ka yana godiya da irin hidima da kake yi da su, Safwan ni dai kwanciyar hankalina shine ka komo gida, sannan ka yi aure, anan d’in koyarwa kake yi, a can ma akwai koyarwar, ni nafison ina ganinku a kusa dani. Ya batun bazawarar da kai mun maganar ta, kwanaki dana zo? na tafi cike da murna wallahi.” Kai ya sosa yace.

“Yanxu maganar da mu ke yi da Badiyya kenan, akan gobe zata je da kanta da shawo mun kan Sadiyan.” Had’e fuska Innah ta yi tace.

“Ni na shiga uku na da zancen Badiyya, dama fa kakarta ance mayya ce, yarinyar nan dai ni na ja ma kaina, tunda ni na had’a wannan aure na jaraba. Ni da kaina zanje gidan su Sadiyar mu yi magana da gyatumarta, ayi komai a gama, amma fa a Azare zaku zauna, in ba haka ba, Badiyya ba zata barka ka yi adalci ba, da shanyayyen jiki zaka tashi gaban ubangiji, ni kuma bazan so hakan ba, zai fi mun sauk’i ka dawo gida.”

“Toh Inna sai yanda kika ce ai, sai in koma d’in ai Innah” Badiyya ce ta kawo ma Inna tuwon shinkafa da miyar taushe, taji tantakwashi da man shanu, da ruwan sha da na wanke hannu.

Safwan ne ya zuba abincin suna ci tare da Innah ya na bata labarin Sadiya da d’an yaronta.” Badiyya kuma tana uwar d’akinta ta yi rub da ciki, sai kuka ta ke yi mara sauti.”

Bayan sun kammala cin abincin, sun tab’a hira,sai Innah tace.

“Bari in shiga daga ciki in d’an huce gajiya, in Badiyya ta gama mulkinta. Kace ta kai mun ruwa ban d’aki.”

Da “Toh” Kawai ya bi Innah.

Da sallama ya shiga cikin d’akin, sautin shesshek’ar kukan Badiyya ya doki dodon kunnenshi. Da sassarfa ya isa gareta, tare da jawota ta fad’a kirjinshi. Tsintar kanta ta yi da sake rushe mishi da sabon kuka. Cikin nuna kulawa ya shiga rarrashinta.

“Haba Badiyya ta. Ki yi hak’uri da mahaifiyata, ita ta haifeni, kuma in kina sona, so na gaskiya. Dole ki yi mata biyayya. Ni ne mijinki, rashin haihuwarki ba ya damuna sam, shekaru goma sha biyu mu ka yi tare, ki ka yi rayuwa da ni ke kad’ai. Ta b’angarena baki tab’a fuskantar wani k’alubale ba. Inna fa ta yi hak’uri maganar gaskiya, kinsan iyayenmu da maganar jikoki. Yin Aure na, shine zai kawo kwanciyar hankalinmu baki d’aya. Kuma ina son Sadiya, da Haidar. Ki share hawayenki, ki kaima Inna ruwan wanka band’aki.”

Hawayenta ta share tace.

“Amman Safwan bai kamata ace Inna….”

“Dakata Badiyya! Bazan lamunci ki fad’i ko wacce irin kalma bace akan mahaifiyata, dole ki bi abunda tace, in dai ni ki ke Aure. Son da na ke miki bazai  hana in sa  sab’a miki akan mahaifiyata ba. Kin ko san irin fad’i tashin da ta yi dan ganin na tsaya da k’afafuna?” Ficewa Badiyya ta yi ranta na tafasa, ta ma rasa da me za ta ji, ga zancen Sadiya kullum da Safwan ya ke cika ta da shi, da irin k’aunar Haidar da ya ke yi. Ga cusgunawar da danginshi, da mahaifiyarshi su ke yi mata, da me za ta ji, sai a dake ka a hana ka kuka?”

Ruwan zafin dake wuta akan (Itace), ta juye ma Innah, sai da ta kai ban d’aki tukunna, ta je ta sanar ma Innah ta kai ruwan” Amma ko kallon banzan da Inna ta saba yi mata ba ta yi mata ba, dan ko bud’e idanunta ba ta yi ba, balle ta san ta ji ko ba ta ji ba. Haka ta k’araci tsugunno, ala tilas ta mik’e ta fita. Da harara Inna ta bi bayanta.”

Safwan ya na kwance a kan katifa, ya yi zurfi cikin tunanin Sadiya, tare da fargabar wanne irin sakamako Inna za ta dawo da shi in ta je gidan su Sadiya? Tsoron shi Allah, tsoronshi kar ace Sadiya na da wanda za ta aura.”

Badiyya ta zauna a bakin katifar ta su, idanu ta xuba ma Safwan. Ta na jin tsantsar kishin shi na nuk’urk’ushe mata zuchiya.”

Yanzu nan da wani d’an lokaci Safwan zai zama mallakin su, su biyu?” Duk wannan batu a cikin zuchiyarta ta ke yi”

Mrs Bukhari ce.

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

57-58

Sadiya

Ko da na shiga gida kasa sukuni na yi, ina jin babu dad’i sam, a bisa halin da Safwan ya tafi a ciki. Tsaki na ja mai tsayi. Haidar ne ya shigo da gudu Mama na biye da shi da bulala. Jikina ya haye sai faman sukuwa ya ke yi. Na kasa ce musu komai, da idanu kawai na ke binsu.

“Umma kinga Mama zata dake ni ko? Ki yi mata Bulala ke ma.” Mama tace.

“In ita uwarka ce, ni kuma uwarta ce, ba za ta iya duka na ba. Amma ni dukkan ku zan iya duka.” Haidar ya juyo mun da fuskata yace.”

“Umma hakane?” Kai kawai na gyad’a mai, ba tare da na ce komai ba. Mama ce ta ce.

“Maza je ka gaisa da Baba kace ina zuwa yanxu.” Aguje Haidar ya fita zuwa zaure dan sanarma Malam Kaka sak’on Mama.

Ita kuma zama ta yi a gefe na.”

“Sadiya, na lura tunda ki ka dawo daga wajan kiran da Safwan yai miki, sai walwalarki ta d’auke.” Ajjiyar zuchiya na sauke.

Mama ba ma Safwan d’in bane, Ahmad ne. Mu na tsaye da shi, sai ga Safwan d’in ya zo. Amma ganin Ahmad yasa bai ‘karaso wajen ba. A cikin fishi ya tafi, sai banji dad’i ba. Ko dan hidimar da ya ke yi da Haidar Mama.” Kaina na sauke k’asa ina jiran me Mama za ta ce.

“Sadiya kenan. Ki rabu da shi, zai zo da k’afarshi. Da ya zo ki sanar mishi ina neman shi. Ga shi mun tsaida lokacin Aure da Kaka, sai dai hakan bazai yuwu ba, har sai na kawar da ke a gabana. Ni ma sai in koma gidan mijina. Yanzu dai bari in je in same shi.” Fita Mama ta yi  a d’akin. Ni kuma ina jin kunyar zance da Mama su ke yawan yi da Malam Kaka, kuma ni ma ana zuwa waje na.”

……

washe gari.

Ina tsakar gida na fito da wankin Mama da na Haidar, kasancewar yau ba ni da aiki sam.

Mama ta na kan tabarma, ita da Haidar, suna karatun makaranta.

Sallamar mace mu ka jiyo daga zaure.

“Ameen wa’alaikis salam, shigo baiwar Allah” Mama ce ta yi magana. Dattijuwar matar ta shigo cikin gidan. Da fara’a Mama ta tarbeta, tare da nuna mata wajan zama.

Ni kuma na shiga kitchen na kawo mata ruwan sha, sannan mu ka gaisa.”

“Ko ke ce Sadiya Maman Haidar?” Da mamaki na ce mata.

Eh ni ce” Baki ta yashe”

“Tubarkallah Safwan ya iya zab’in mace. Ji yarinya kub’ul_kub’ul da ita, dirarriyar mace ma malam.” Murmushi kawai na yi mata, a raina ita tunanin To ita kuma wacece?. Kamar ta ji me na ce, sai tace ma Mama.”

“Mahaifiyar Safwan ce, daga Azare. Wannan baturen shine Haidar?” Mama da fara’arta ta k’aru tace.”

“Maraba lale da zuwa. Eh Haidar kenan. Haidar ga Kaka, ka yi gaisuwa” Ni kuma kunya duk ta lullub’eni, a tsaneke na shige ‘daki, ina jiyo ta, ta na hira da Haidar. A bayan labule na lab’e dan zumud’in son jin me za su tattauna.”

“Dama shi Safwan d’in ne ya turo ni, tunda na zo, akan ita Sadiya ne, ya na naiman Auranta, in har babu wanda ya riga shi, mu dai mu na so. In kuma za mu samu, ba ma so ya wuce wata biyu, tunda su ba yara bane k’anana. Ya na da mata Badiyya sunanta. Amma Allah bai azurtasu da samun rabo da’ita ba.” Mama tace.

“In ma dai akwai wani, toh ni dai na ba yarona Safwan. Sai dai dangin mahaifinta suna Zamfara cikin k’auyan rak’uma. A can zai je ya biya sadakin na ta, sai kuma Ayi bikin anan. An baku ita dai a ta’kaice.”

“Kai amma na yi farin ciki ainun. Allah yasa ayi damu, Babu damuwa, in aka ba mu adirishin can Raquman, sai Baffan shi ya je, a kai sadakin ai. Wani hanzari ba gudu ba. A garin Azare za su zauna in an yi bikin, dan zai tattara duka ya koma Azaren, da fatan babu matsala?” Mama ta yi murmushi, ta ce.”

“Babu damuwa, ai aure babu inda baya kai mace, shi Aure haka yake, sai ya cillaka k’asar da ba kai zato ba.”

Ina daga bayan labule. murmushin farin ciki na sauke, ashe dai dama Safwan na sona? Allah sarki bawan Allah, yayi wuff ya riga Ahmad turowa, gudun kar garin kallon ruwa kwad’o yai mishi k’afa. Barin wajan na yi na zauna, ina tunanin Azare kuma Aure zai d’ebe ni ya kai. Ahh iko sai Allah.” Mama ce ta katsemun tunanin da na yi zurfi a cikin shi.”

Mama har ta tafi ne?”

“Ta tafi, na san kinji komai, ni dai na basu dama. Ke ma kuma nasan hakan take a wajanki. Sadiya sai ki bi mijinki sau da k’afa. Danginshi, iyayenshi. Kuma zan yi magana da shi, ko Allah zai sa ya amince miki, ki ci gaba da aikin na ki, bayan kun yi aure. Kuma zan baki shawarar ki bud’e shagon sai da magani a can. Allah yasa albarka.Zan sa ai mun bincike kamar yadda sharia ta tanadar”

Ameen Mama” Kawai na iya cewa. Amma kuma inajin wani karsashi na sabuwar soyayya na fisgata. Kai soyayya me dad’i”

Safwan

Kasancewar yau Asabar ce, ya na gida, ya ba matar shi dukka lokacinshi. Ita kuma ta saki jiki da shi tamkar ba su samu d’an sab’ani jiya ba.

“Ka ga har yanzu Inna ba ta dawo ba. Allah ya sa a dace dai”

“Toh ameen Badiyya gimbiya, gabana tun fitar ta ya ke fad’uwa wallahi.” Danne kukan da ya ke shirin tsinka ta a idon Safwan ta yi, cikin dakewar zuchiya, tare da nuna jarumta ta ce.

“Ni kuwa zan so ganin wannan Sadiya da ta rud’amun mai gida, kai da kallon mata bai dame ka ba. Ba ka damu da kula su ba ma”

Jawo Badiyya ya yi kusa da shi, dan ya fahimci a cikin maganarta akwai kishi. Kunyarta ma ya ji, yanda ta saki jiki su na hirar Sadiya.”

“Za ki ganta ne, macece kamarki, amma ita bak’a ce, ba kamarki  fara ba, kin fi Sadiya kyau ne sa ba kusa ba. Amma yanayin ku ne ba d’aya ba. Akwai abubbuwa da yawa tattare da’ita. Badiyya” Fasali ya ja tare da k’ura mata idanunshi, wanda ya riga da ya san sune logonta.

“Ke ta musamman ce a rayuwata. Babu macen da za ta shigo gidana, ta taka mun ke, ki na da mahimmanci a cikin rayuwata. Kuma ina girmamaki as uwar gidan gidana. Dole ko wacce mace da za ta shigo rayuwarmu, ta girmamaki. wallahi a kan ki zan iya sakin Sadiya kinji na rantse miki, kuma kinsan bazan yi miki rantsuwa dan ki ji dad’i ba. Muddin Sadiya tak’i girmamaki, ta kuma k’i yadda da zaman lafiya. Toh sallamarta zan yi.”

Wani dad’ine ya lullub’e zuchiyar Badiyya. Jinta ta ke yi tamkar wata sarauniyar matan duniya. Murmushi ta yi, tare da cewar.

“Ni kuma zan baka goyon baya d’ari bisa d’ari, kuma zan ta ya ka mu so Sadiya. Na yi maka alk’awarin sai zamana da Sadiya ya zame ma mata abun ko yi, abun sha’awa. Abunda na ke nema a wajen ka shine. Kar ka rufe ni a duk wani hali da za ka kasance, yanda na ke da matsayin matarka, uwar gidanka, kuma aminiyarka. Ina fargabar ka sauke ni daga kan matsayina ko da guda d’aya ne. Hakan zai cutar da ni gaya” Hawayen kishin mijinta ta soma zubarwa. D’ora kanta a kafad’arshi ta yi.

“Ina kishin ka fa Safwan. Ba na jin akwai macen da za ta yi ma irin kishin da na ke yi ma” Kukan ta sake raushewa da shi.

Shi kuwa tuni ya dibibice ya rud’e da aikin rarrashin matarshi, tare da mata magana masu kyautar da rai. Sallamar Inna ce  ta sa, ya yi saurin sakinta. Ita kuma ta yi saurin goge hawayenta. Da harara Inna ta bita, shi kuma ta ce mai.

“Lafiya na ganku a tsaye cirko cirko, kamar wanda aka turo ma da sak’on mutuwa? Ita kuma na ga idanta ta yi kuka.”  Cikin sosa kai Safwan ya ce.

“Abu ne ya fad’a mata idan, shine ta zo na hure mata.”

“Ayya. Toh albishinka? Sadiya dai an baka ita, nan da wata biyu ma za’ayi komai a gama.”

Tsabar farin cikin da ya shiga kasa magana ya yi. Badiyya ta na tsaye sai murmushin k’arfin hali ta ke yi. Da zumud’i ya dubi Badiyya ya ce.

“Nu na mun gabas Badiyya” Da hannu ta nu na mishi gabas d’in. Sujjadar godiya ga ubangiji ya yi, sannan ya taso ya na kallon Inna. Ita kuma ji ta ke tamkar ta goye shi, tsabar dad’in da ta ji, ganin d’an na ta a cikin farin ciki irin haka.

Badiyya kuwa, shigewarta ta yi ciki, dan gudun kar zuchiyarta ta fad’o ta fashe.

Mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

59~60

“Inna ki ka ce fa an ba ni Sadiya, kuma kin ga Sadiyar?” Safwan ke tambayar Innah”

“Na ganta tubarkallah masha Allah, amma yaron na ganshi bature yaro mai kyau.” Dariya kawai yai ma Inna dan baya son su shiga maganar Haidar, dan gudun kar kwab’arshi ta yi ruwa.”

“Yanzu ni gobe zan koma, amma Baffanka zai tafi can Raquma d’in a gama maganar baki d’aya kawai, kai kuma sai ka bud’e b’angaren mahaifinka da ka gada, ka ga dama zaman mutum biyu ne, kuma ya fi ko ina kyau a gidan, ‘yan gyare gyaren da ya da ce a yi, za mu gani sai ayin, ni dai zan k’uk’uta in ba da sadakin.”

“Inna nagode sosai, sai dai fa Inna, babu kud’i ishasshe a hannuna, ga maganar lefe, ga maganar komawar mu Azare, ga gyare gyaren da zan yi, ga kayan fad’ar kishiya da zan yi ma Badiyya bisa al’adar malam Bahaushe, ga ‘yan kunji_kunji da ba’a rasa ba.” Inna tace.

“Kai dai ka yi adda’a, sai ka ga komai ya zo da sauk’i, kuma zan had’e kan yayyinka me taro me sisi duk sai mu gaggand’a, ayi a wuce wurin, tunda yarinyar nan Bazawara ce, za ta yi hak’uri da abinda ta samu ne. Kuma ka ke cewa maganar Badiyya, ni da kai babu damu magana sai ka sako mun Badiyya, ahir d’inka Safwan.” Kai ya sauke yace.

“Allah ya huci zuchiyarki.”

“Ameen, ni zan je in kwanta. Ka fad’a mata tuwon farar dawa da miyar kub’ewa bushasshiya na ke so, kafin in ta shi.”

Da “Toh” Ya bita. A wajan ya zauna na kusan minti talatin, sannan ya mik’e ya fice, zuwa wajan abokinshi, Abdullahi.”

*BAYAN SATI BIYU*

komai ya kammala, Safwan an kai mishi kud’in Auran shi Raquma. Kuma sun amsa, Kawu da kan shi ya tattak’o ya zo Kano.

Ganin girma da kyan da Haidar ya yi ya matuk’ar bashi mamaki, kuma ya ji kunya ainun.

Sadakina ya ba Mama, tare da sanar mata cewar Safwan ya buk’aci nan da wata biyu ya ke son komai ya kammala, wanda a ranar ya zama saura kwana arba’in da shidda cib, wanda yai dai_dai da ranar juma’a.

Amsar kud’in ta yi, nera dubu goma tare da sanya albarka. Kwanan shi d’aya a gida ya juya.

Sai shirye shirye na ke yi a hankali_a hankali, duk da har yau da biki ya rage saura kwana talatin ban sa Safwan a idanuna ba sam.

Goggo ce ta dawo gida da zama baki d’aya, ta na tai mun gyare gyaren jiki, da magunguna tamkar wata sabon aure. Mama ta yi k’ok’ari sosai dan ta sake mun kayan kitchen d’ina. Sababbin kayan katako na bayar kafinta zai yi mun, ta b’angaren su Amina da Hadiza kuwa har sun fidda da ashibinsu.

ranar wata asabar sakaliya, ina d’aki a zaune na ci kwalliya, ina shirin zuwa gidan Amina k’awata, mun yi da ita yau zan zo, akwai magunguna masu zafi da za ta bani. Yaro ne yai sallama ya shigo.

“wai ana kiran Sadiya a waje.”

Ina daga d’aki na ji wani farin ciki ya lullub’emun zuchiyata. Sai da yaronnan ya sake maimaita kanshi na dawo daga duniyar tunanin da na shige. Kasancewar Mama, da Haidar, da Goggo Hansatu  basa nan. Da hanzari nace.

 Kace ina zuwa yanxu.”

Turare na sake fesawa a jikina, na yafa mayafina, na d’auki ‘yar jakata na fice. K’ofar gidan na kulle da d’an makulli.

Ahmad na ga ni jingine a motar shi, ya cusa hannayen shi cikin aljihunan rigar jikinshi. Cikin hassala na isa gare shi nace.

“Haba Ahmad wannan nacin ya isa haka, dan saura kwanaki k’alilan ya rage in auri masoyina, wanda ya san darajata. Da ka san ka na sona, shine ka fasa aure na.”

“Assalamu Alaikum Malam” Muryar Safwan ce ta daki dodon kunnena, gabanane ya fad’i ras. Da sauri na juyo, mu ka had’a idanu, idanunnan nashi sun kad’a sun yi jawur. Hannun Ahmad ya mik’a mishi, su kai musabaha. Ya ce.

“Ba dai_dai bane nema a cikin nema, saura kwanaki na mallaketa, sadakina ya na gidansu, matatace, ka kiyaye.” Sab’ule hannunshi yayi a cikin na Ahmad, dakalin da mu ka saba zama ya je ya zauna, Ahmad ya shige motarshi rai b’ace, ni kuma cikin sanyin jiki na isa wajan Safwan. Waje na samu na zauna. Amma mun fi minti goma babu wanda ya ce da wani komai, Safwan sai ajjiyar zuchiya kawai ya ke saukewa. Minti talatin na cika ya mik’e, ya kasa cemun komai, tafiya yayi ya barni a zaune a wajan.

Idan raina yai dubu ya b’aci yau, domun jikina har rawa ya ke yi, ko ma meye ai bai dace ya shanyani na tsawon minti talatin ba, kuma ya yi wucewarshi ya barni a zaune ba.”

Tafiyata na yi gidan Amina, raina a dagule sosai, da murna ta tarbeni tana zaulayata.

“Amarya mai maganar siga.Sai yanzu kika zo, ni harfa na cire rai da ke.”

Tsaki na ja na zauna, bance da ita komai ba. Zama ta yi a kusa da ni.

“Ke lafiyarki kuwa, ko dai ke da Mama ne?”

Hmmm wacce Mama, Amina Safwan ne ya b’ata mun rai wallahi.”

Labarin abunda ya shiga tsakaninmu na bata, dariya ta fashe mun dashi, tace.”

“Amma Sadiya ke ‘yar rainin hankalice, shine kika kasa bashi hak’uri bisa laifin da kika aikata mishi? Baki kyauta ba, shima k’ila shi yasa yai tafiyarshi, kinsan zai ga kamar kin raina shine, shi yasa ki ka kasa ba shi hak’uri? Kuma maganar gaskiya, ko waye zai yi fishi sosai, Sadiya baki kyauta ba.”

Jikina ya sake yin sanyi k’alau.”

“Hakane Amina, sai da nake tawowa ne na gane sake k’ular da Safwan na yi shi yasa ya tafi ya barni, tunda na kasa ba shi hak’uri, kuma na kasa yi mishi bayanin da zai fahimta. Yanzu yaya zanyi Amina?”

“Hak’uri za ki yi, ki bari zai zo da kan shi, sai ki bashi hak’uri, ba daraja bane ki bishi makaranta ki ba shi hak’uri, da sai in ce ki je. Shawara d’aya ce, ki sai mishi card na ban hak’uri, da fulawa me kyau, sai ki ba Haidar ya ta fi mishi da shi makaranta.”

Ido na zare nace

Haba  zan azabtu da yawa, yaufa asabar ne, kina nufin har sai monday? Bazan iyaba gaskiya, meye mafita kawai?”

Dariya Amina ta yi, uwar d’akinta ta shige, da goruna manya biyu ta fito a hannunta”

“Ga wannan ki shanye dukka, ko da a hankali a hankaline, in kin tashi tafiya kuma, akwai gumbar ‘yar gata da zan baki, k’aramar robar fenti guda, kita ci kawai har ta k’are. Maganar Safwan kuma, ki sai card d’in yau, sai ki je layinsu ki tura yaro ya aika mishi gida.”

Amina ai bansan gidan shi ba, shine matsalar.”

“Ai kuwa ya zame miki dole ki yi hak’uri zuwa monday dan ba ni da mafita ni kam.”

Haka dai mu ka d’an tab’a hirar, na yi dawowata gida.

Safwan kuwa yana isa gida, sai zazzab’i mai mugun zafin gaske ya kama shi, sai had’iyar zuchiya kawai ya ke yi. Allah ya halicceshi, namijine mai tsananin mugun kishin da har ya ke jin tsoron duk wani abu da zai motso mai da kishin abunda ya ke so. Kishin da yake da shi, ya zame mai matattakalar daya taka ya gama karatu da sakamako mai kyau da first class ya fito. Badiyya a rud’e ta fita siyo mishi magani a kemis, shi kuwa ya fice a hayyacinshi, hawaye kawai ke bin gefen idanunshi, ya na jin kishi da takaicin ma son Sadiya da ya ke yi. Ya ma zata kula wani da ranar shi a kanta? Kuma dan ya fad’a mishi gaskiya, Sadiya ta yi fishin da ko hak’uri ta kasa bud’e baki ta ba shi, sai k’aratar zaman shi ya yi ya tafi. Ga shi ya ganta a cikin kwalliya da k’amshi.”

Mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

61-62

Badiyya ce ta shigo d’akin hannunta rik’e da kofin silver na ruwa, da maganin zazzab’i. Tallafo kan shi ta yi, ta jinginar da shi a jikin pillow. Magani ta b’alla ta bashi, tare da kora mishi ruwa.

Hawayen gefen fuskarshi ta share mishi.”

“Me ya saka a cikin wani hali haka ne, ashe son da ka ke yi ma Sadiya ya kai haka? Safwan ka tausaya mun kar ka tunzura kishina ya fito waje, kullum a cikin son faranta maka nake, kar ka bar hawayena zuba tun kafin Sadiyan ta shigo mana.” Tausayin kalamanta ya ji, sai kuma kunya duk ta lullub’eshi. Matsowa yayi ya d’aura kan shi a cinyarta.

“ki yi hak’uri uwar gida, kishinki bazai tunzura ba, ki yafe mun bazan sake ba” Hawayen daya taru  a idanunta ne suka shiga suntiri a kumatun ta, kishin Sadiya ta ke yi, tamkar ta kashe kanta. Son da take ma Safwan kuma bazai barta ta juya mishi baya ba. Tunda su ka yi aure, ta kasance a cikin son duk wani abu da Safwan ya ke so. Saukar nunfashinshi ta jiyo halamar bacci ne ma ya kwashe shi.”

Sadiya

A kwance na ke ina jiran bacci yai awon gaba da ni, amma ji kake shiru malam ya ci shirwa. Sai juyi na ke yi akan gadon, ban yi zaton son da na ke yi ma Safwan ya kai wannan matakin ba. A daren ranar dai, kusan raba dare na yi ina tunanin Safwan.

Weekend d’in baki d’aya banyi a cikin walwala ba sam.

Yau ya sakance Monday ranar aiki. A shirye na fito tsab da ni, cikin doguwar rigar atampar soso, mai kalar bak’i da ruwan goro, card d’in dake hannuna na saka a cikin jakar bayan Haidar.

In ka je makaranta, ka ba ma Abba wannan katin kaji?

“Toh Umma, yaushe Abba zai dawo gidanmu, Jafar abokina ya ce, Abbanshi  gidansu d’aya. Kuma tare da Ummanshi su ke kwana. Ni Abbana kullum sai dai mu had’u a makaranta.”

Wani mikin rashin Aliyu Haidar ya fama mun a zuchiyata. Take na birkice da kukan da Haidar ya dinga rarrashina.

“Umma ki yi hak’uri ki share hawayenki. Umma ‘yan makarantar mu duka na kullum su ke yi, suna ture ni, wai ni k’azami ne, Zabiya.”

Bakin shi na toshe mishi da hannuna, cikin tashin hankali nace.

Haka su ke kiran ka Zabiya! Abbanka ya sani kuma?”

“A’a bai sani ba, ni bana fad’a mai, zai musu bulala.”

Ka yi hak’uri kai ba k’azami bane, haka Allah ya so ganinka Haidar mai kyau.”

Murmushi ya yi mun, kanshi na shafa nace.

Adawo lafiya Haidar.”

Hawaye ya dinga share mun. Mama ce ta fito da mayafi a jikinta.”

“Toh jikalle mu je kar ayi latti. Sadiya aikin safe ki ke da shi ne?”

Eh mama, aikin safe ne.” Mama tace.

“Toh aje lafiya a dawo lafiya. Da

Ameen” Na bita.

Ko da na je Asibiti sam bani da walwala da kuzari a jikina. Tunanin Aliyu ya hanani sukuni sam, sai hawaye na ke yi.

Sister Zarah ce ta iso cikin ofishinmu.”

“Sister Sadiya, Dr Rabo na nemanki, akwai mata masu labour a labour room har biyu.” Dubanta na yi na ce.

Sister Fatima da sister Zakiya ke da duty yanzu, ni sai 10 zan karb’i duty.”

“Ahh ai an canja tsari, meeting d’in da aka tsaya ranar juma’a da baki halarta ba. An canja tsarin karb’a_karb’a. Daga takwas na safe, ‘yan kwana za su hutu, zuwa takwas da rabi ‘yan safe su amshi nasu,  zuwa k’arfe hudun yamma.

Kai masha Allah, abun yayi kyau.”

Mik’ewa na yi, labour room na wuce kai tsaye, dan amsar haihuwa. Yau kam labour room d’in cike yake da mata masu haihuwa, hakanne yasa aiki yai mana face face a wannan ranar, bani na samu kaina ba sai kusan biyun rana. Kai tsaye masallacin mata na wuce dan gabatar da Sallah. Daga nan na wuce ofishinmu dan in ci abinci, amma ga abincin a gabana na tusa shi na kasa ci.

Sister Nadiya ce ta shigo da sallama tace.”

“Sister Sadiya, kina da bak’o yana zaune a reseption yana jiranki, kusan awa guda kenan, a lokacin kina labour room, amma an sanar da shi.”

Da mamaki na dubeta tare da maimaita.

Bak’o?”

Cike da mamaki na mik’e na fita, bance da kowa komai ba, reseption na nufa kai tsaye, ahankali nake takawo dan babu kuzari a jikina sam, Safwan na hango duk da ta baya na hangoshi, amma shi d’in ne dai.

Assalamu Alaikum yallab’ai barka da zuwa.” Idanu ya zuba mun yana kallona cikin kayan aikin asibiti, murmushi yai mun mai sanyi.

Waje na samu na zauna, kaina na sauke ina wasa da zoben zinaren dake hannuna, fuskata babu walwala sosai.”

“Ameen wa’alaikis salam, barka da aiki Sadiya.”

Murmushi kawai na yi mishi, amma ban d’ago kaina ba.

“Ki yi hak’uri kamar zuwana bai miki dad’i ba ko, ko akwai wani abunda yake damunki wanda ni mijinki ba za ki iya sanar da ni ba, uhm Sadiya?”

Hawayen daya taru a idanunane suka gangaro kamar wata k’aramar yarinya.

Safwan ya sake dubana cikin sigar lallashi yace.

“Haba Sadiya, shin ba gani a kusa da ke ba, ai na d’auka wanzuwata zai goge dukkan wani bak’in cikin da ya ke damunki. Ko dai mai motar nan ya fi baki farin ciki sama da ni ne, ko tunaninki son da nake miki bai kai mizanin da za’a kalla ba? Ina sonki da yawa Sadiya, sonki da kishinki har kwantar da ni su ka yi, yanzu haka ban gama warwarewa ba. Come on ki share hawayenki kinji amarya ta?”

Bansan sanda na yi murmushi ba, ji na yi kalmar so da Safwan ya furta mun a karon farko ya kori duk wata damuwa da take son damuna, fes na ke jin zuchiyata a yanxu, cikin shagwab’a irin ta mu ta mata, mai yanje hankalin wanda a ka yi domun sa na ce.”

“ka yi hak’uri akan dukkan abunda ya faru, a bisa akasi duk suka faru. Ahmad ba saurayina bane, mun yi soyayya a da, ranar da za’a d’aura aure na da shi, magabatan shi su ka sanarma nawa magabatan cewar, d’ansu bazai auri ‘yar boko ma aikaciyar gwamnati ba. Shikenan aka d’aura aure na da mahaifin Haidar wanda ya kasance d’an yar Babana ne. Shi kuma Ahmad ya auri k’awata Fatima.” Safwan ya ce.”

“Amma da ma ya na son k’awar ta ki ne, ko yaya?” Ajjiyar zuchiya na sauke nace.”

“Al’amarin da ya ba kowa mamaki kenan, domun a ranar d’aurin auran mu, aka d’aura auran shi da Fatima. abunda zai baka mamaki shine har da kalanda su ka buga”

Murmushi Safwan ya yi mun kawai, agogon fatan hannunshi ya kalla yace.”

“Zan gudu Sadiya, kar in tsaida miki da aikin ki.” Murmushi na yi na ce.

“Amma ya jikin na ka, da sauk’i ko?” Hararar soyayya ya jefa mun, sai da tsigar jikina ta tashi.

“Ashe kin damu da ciwon nawa? Bacin ke ki ka sa na kwanta”

Ni ma fa na azabtu da rashinka sosai, da ma san gidanka, da baka zo ba sai dai ka ganni kwatsam.” Dariya ya yi mun kawai.”

“Jikin ya yi sauk’i musamman da na zo na ci karo da kyakkyawar fuskarki, sai na dawo dai dai. Badiyya ta ce in gaisheki da kyau.” Kallon tuhuma na yi mishi.

” Ka na nufin matarka ta san da zama na kenan?” mik’ewa ya yi tsaye.

“Sosai ma, tare mu ke gudanar da duk wani abu da ya shafi junanmu, kuma ta na farin cikin shigowarki rayuwata. Madam zan gudu, ban tashi a makaranta ba, ga shi lokacin tashin har ya kusa, kafin in koma makaranta an tashi.”

Agogon hannuna na duba, hud’u saura.

Ka jirani kawai mu ta fi tare k’arfe hud’u zan tashi.”

Kai ya d’aga mun halamar toh.

A wajan na barshi, na sanya aka kawo mishi ruwa, ni kuma na ci gaba da aikina har zuwa lokacin tashi.

Tafe mu ke mu na hira irin hirar da bamu tab’a yin irinta ba. Safwan ya bani labarin matar shi da irin son da ta ke yi mishi, da irin tsananin son haihuwa da su ke yi dukka, amma bai bani labarin asalinshi ba, maganar matarshi ya gundureni sosai, dan ina jin kishinta.

Mun iso k’ofar gidanmu mu na zaune  akan dakali na dube shi na ce.

“Baka bani labarin ahalinka ba, da musabbabin da ya kawo ka Kano, ka baro azare.”

“Sadiya zan baki wannan labarin amma sai mun yi aure tukunna, duk wani bincike da za ku gudanar a kaina kuna da dama, musulunci ya yarda da hakan. Dariya na yi.

“Tuni su Mama su ka gama duk wani bincikensu a kan ka ai, shi yasa hankalina ya sake nutsuwa, duk da ko da an samo matsala ni dai na ji na gani.” Dariya na ba shi sosai.

“Sadiya kina burgeni kin iya tsara magana. Toh kin amince za ki zauna da mijinki a k’auye kuwa?”

Sosai ma, sai dai ina naiman alfarmar ka barni in ci gaba da aikina” Gintsewa ya yi, zunbur ya mik’e yace.”

” Da daddare zan zo sai mu yi magana Sadiya, zan ta fi, ki shiga ki huta kema, ki gaishe da Haidar da Mama” Sallama mu ka yi, ya nufi gida, ni kuma na shige ciki da sallamata.

Haka kwanaki su ka ci gaba da tafiya shirye shirye ya ci gaba da kankama ta ko wanne b’angare, yanzu haka ma Safwan sun tafi Azare shi da Badiyya matar shi.”

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

63-64

Azare

Safwan ne gurfane a gaban Innaj da Baffan shi, suna ta tattauna al’amuran biki.

“Safwan ga kud’i da aka tara nera dubu d’ari da sittin, daga wajan yayyunka maza da mata. Yayarku Saliha kuma ta d’auke nauyin duk abincin da za’aci a biki, ka ga har rago ta siya. Kawu malam k’anin mahaifinka kuma zai gyara maka b’arayin da zaka zauna, har an soma gyaran ma.” Innah ta ce.

“Ya maganar Akwati kuma?” Safwan yace.

“Mun had’a akwati biyu ni da Badiyya, kugunmawar ta kenan, ita ta sai komai da komai da kud’in sark’ar zinarenta da azurfarta data gada.” Innah ta yi tsalle ta dira akan Safwan da fad’a.

“Akan me za ta sai da kadarorinta data zo da shi daga gidansu, kalan ta dinga gorantama Sadiya a gaba cewar ita ta yi lefen bikinta? Ita kanta Sadiyan ai ba dad’i zata ji ba.”

“Haba Rakiya haba Rakiya, wannan ai fad’an rashin gaskiya ne. Yarinya ta yi abin yabawar da ya kamata ki yabeta. Kayan gadonta fa ta siyar danta taimaka ma mijinta, Safwan Allah yai muku albarka dukka” Safwan ya amsa da.

“Ameen Baffa” Innah tace

“Ina kayan su ke, ko da su ta tafi gidan nasu? Yarinya fur ta k’i ta sauka a gidan mijinta sai gidan iyayenta, kai kuma ka amince mata, wai sai bayan biki da sati d’aya ma zata tare” Safwan yace.

“Innah na ga hakan ba laifi bane. Ta fi shekara biyu ba ta zo gida ba, ko zan tawo sabida rashin kud’i, sai dai in tawo ni kad’ai, kuma ba ta tab’a yi mun magiya ba. Yanzu kuma ta ne mi alfarmar hakan bai dace a ce na tauye ta ba, duba da yanda ta shige gaba a cikin hidimar bikina.” Baffa ya ce.”

“Hakan da ka yi na nuna kai adaline Safwan, amma ka sallameta da kayan fad’ar kishiya dai ko?” Kai Safwan ya sosa.”

“A’a tukunna dai Baffa amma tunda kud’i sun samu zan yi mata. Sai dai ina so in yi mata d’inkunan biki ita da Innah kafin lokacin.” Baffa yace.

“Allah yai ma Albarka, tashi ka je, Mudi ya na ta jewa a gidannan, rabon da in sa Mudi a idanuna ai bana ce ga ranar ba. Sai dai iyalan na shi na zuwa wajan ita gyatumar taku. Murmushi Safwan ya yi ya ce.

“Dama gidan Anty Saliha zai raka ni can Bauchi in gaishe ta, na jima ban je ba, sai in lek’a gidan Kawu Tanko, da gidan Goggo Ta sallah. Innah tace.

“Ka kuwa kyauta sosai, ka je ya na ta faman jiranka. Fita ya yi a d’akin tare da yi musu sallama, su kai mai fatan dawowa lafiya.

Yana fita tsakar gidan na su, matan yayyunshi maza su ka shiga tsokanar shi.

Ango ka sha k’amshi Angon Sadiya ba da kan ka a sare ka je gida ka ce ya fad’i. Dariya ya bi su da shi kawai ya dubi matar Babban wansu ya ce.

“Anty Jamila wai har da ke?” Dariyar dattijuwar ta yi tace.

“Ai dole a yi da ni Safwan, mu dai fatanmu Allah yasa Sadiya ta shekara da d’anta a gidannan” Baisan sanda ya ce da ita “Ameen” Ba. Sallama yai musu akan zai je Bauchi ya na dubo Anty Saliha.

Yana fita ya ci karo da Mudi a cikin motar shi k’irar ( Beetil ) Hajiya ba 🤭.. Tsaki ya ja ya ce.

“Kai tsiyata da kai ka fiye nawa, tun yaushe na ke jiranka a nan wajan. Dariya Safwan ya yi, motar ya bud’e ya shiga gidan gaba, Mudi ya ja motar su hau titi.

“Amma fa Safwan na yi farin cikin dawowarka Azare wallahi, kuma ina ta ya ka murnar wannan Aure da za ka yi, Allah ya sa ka na da rabon ganin d’anka kaima a duniya.”

“Ameen Mudi, amma ni lafiyata k’alau Badiyya ce ba ta da lafiya, itace ba za ta haihu ba, gudun kar ta shiga tashin hankali. Sai na boye takaddar da likita ya ba mu, na sanar da’ita dukkanmu lafiya muke lokacine kawai.” Mudi ya dubi Safwan ya ce.

“Aboki a gaskiya ka ko yi halacci sosai, ka kuma rufa mata asiri da ka rufe mata lalurarta. Gashi itama ta yi k’ok’ari wajan goyon bayanka dan ganin ka samu Sadiya”

“Kuma na yi alk’awarin Sadiya in ta haihu zan ba Badiyya yaron kyauta ya zama d’anta.” Mudi ya dube shi ya ce.

“Nan fa d’aya kuma Safwan. kar ka raba uwa da mahaifiyarshi mana, yaranka dai kowa ya san na Badiyya ne, ai ba sai ka bata ba, gidanku fa d’aya.” Idanu ya lumshe domun shi kan shi ya san ba lallai Sadiya ta bashi wannan goyon bayan ba, duba da yanda ya ga ta na da son yara, amma ya na son jarraba hakan. Dan ya warkar da mikin da ke cikin zuchiyar Badiyya na rashin haihuwa. Da wad’annan tunane tunanen su ka isa garin Bauchi. Da gidan Anty Saliha su ka soma.

“Ohh Mudi idanka kenan, kuma an shaida mun a garin Bauchi kamfanin da kake aiki ya ke, ai ko abinci ka rik’a zuwa ci.” Kai Mudi ya sosa. Anty ayi hak’uri, da ke ba ko da yaushe na ke shigowa Bauchin ba, a Azare kamfanin ya ke, kamfanin shinkafa ne, toh store d’insu kuma a Bauchi ya ke, lokaci zuwa lokaci na ke b’ullowa Bauchi. Dariya ta yi ta ce.

“Ina Sabuwa matarka yaranta nawa yanxu?”

“Bakwai Anty. Babban yaron na mu ya na karatu a makarantar kwana ta takanikal sayins J s s 2.

“Ahh masha Allah shima Safwan Allah ya nu na mana lokacin da zai ga na shi jinin.”

Da ameen su ka amsa dukka, sai yanzu ne hankalin Safwan ya koma kan son yara da zumud’in samun su. Bayan sun huta sun ci abinci ne Safwan ya ce.

“Anty na ji abun arziki na gudun mawarki, na gode sosai Allah ya k’ara bud’i.  Anty tace

“Ameen babu komai sati mai zuwa ma zan tawo gidan ayi komai ina nan, Allah ya baka ikon zama adali a gare su.”

Bayan sun tab’a hira kuma, sai su kai mata sallama, gidan kawu Tanko da Goggo Ta sallah, duk yayyen mahaifiyarsu ne suka wuce akayi zumunci.”

Sadiya

wasa wasa yau saura sati guda bikina da Safwan. Yau sati biyu rabon da in sa shi a idanuna, yana Azare.

Na yi wani kyau wanda ko a aurena na fari banyi ba, dan na sha gyara sosai, magungunna kayan mata kuwa Goggo sai d’irka mun ta ke yi, da na yi magana sai ta ce wai kishiya gare ni, dole in gyara kaina.

Biki ya rage saura kwana biyu, bak’i fal gidanmu daga gari gari, daga dangin mahaifina Kawu da Anas ne kad’ai su ka samu halartar bikina, k’awayena ‘yan amana sun zo daga gari gari suma, Hadiza ‘yar mutan katsinawa tace.”

“Toh Allah ya kawo mu a karo na biyu kuma na k’arshe da izinin Allah.

Haka dai k’awayena su kai ta zaulayata suna dariya, ni tsabar farin ciki fal zuchiyata ba na ko iya magana ma.

washe gari da misalin k’arfe biyun rana, bayan an sakko daga masallaci. aka d’aura aurena da Safwan. Dubban jama’a ne su ka shaida.

Da misalin hud’un yamma kuma dangin Safwan su ka shigo gidanmu da akwatunan lefe guda biyu, bayan an musu tarbar arziki sun ci abinci sun sha lemo, sai kuma aka d’au haramar tafiya da ni.

Abun mamaki neman hawaye na na yi na rasa saima farin ciki da ya mamayeni. Ni ba yarinya bace an dai yi mun nasiha a gurguje, k’awayena da su Goggo Hansatu su ka mara mun baya, ina hannun dangin Safwan.

Mota d’aya na shiga da dangin Safwan, ina jiyo ihun Haidar da na barshi a wajan Mama zuwa wani lokaci, in zo in tafi da shi.

Motocinmu sun harba kan titi sai lula gudu su ke yi.

Su Amina da mamanta kuwa tun safe su ka wuce Azare tare da motar kaya.”

Tafiya mabud’in ilimi kenan. Tunda na ke ban tab’a zuwa Bauchi ba. Amma ga Aure zai kaini Azare.

Azare

D’akin amarya ya tsaru sai k’amshin d’akin amare ya ke zubawa, komai na cikin falon bak’ine da ash, cikin uwar d’akin kuma komai ash and red ne, iya tsaruwa d’akin yai kyau. Kuma ‘yan danki sun samu tarba me kyau. kaji da lemon kwalba da masar Bauchi a ka tarbesu da shi, kuma dangin Safwan su suka ta ya su suka jera komai ras, musamman Anty Jamila da tai ruwa tai tsaki a cikin lamarin. Abun dai gwanin sha’awa.

A ranar kuma suma dangin Badiyya su ka zo na su jeren, komai sabo Safwan yai mata a mazaunin dannar k’irjinta, ya yi bajinta sosai, ‘yan uwanta kuma su kai mata karo karo aka siya mata kayan aikace aikacen gida suma sababbi dal. Ko wanne d’aki ya yi kyau ainun. Shima Safwan ya gyara turakarshi sosai, ya saka gado Babba, da sib, sai doguwar kujera a falo, da labulaye kyawawa.

Badiyya ta na gida zazzab’i ya ka da ita, sai rawar d’ari ta ke yi, wani irin duhu take gani tsabar kishin Safwan da ya ke cin k’asan zuchiyarta.

Misalin k’arfe goma sha d’ayan dare, motocin amarya suka iso garin Azare. Masha Allah sun iso lafiya.

Sadiya

Ni dai sai rarraba idanu na ke yi a cikin mayafi, muryar Safwan na jiyo, ashe zugar motocin abokan ango na biye da mu a baya.

“Goggo ku rik’eta a hankali kar kui mun asara man.” Goggo Ta sallah ta yi mai dak’uwa.

“Ungo na ka d’an nema” Murmushi na yi kawai. D’akin Innah a ka wuce da ni, ta sanya mun albarka da auran ma, sannan ta ce.

“Yaya Ta sallah ku kai d’iyata d’aki ta huta, zuwa gobe a zaga da’ita dan gidan akwai girma, kowa ya yi bacci an gaji.” D’akko ni su ka yi zuwa b’arayina. Sai da na yi adda’a sannan na shiga, cikin sallama mu ka shiga d’akin, Goggo Ta sallah ta dank’ani a hannun Goggo Hansatu, su kai mana a huta gajiya.

Safwan

labarin rashin lafiyar Badiyya ya isar ma Safwan, babu shiri a daren ya nufi gidan su Badiyya, ana cikin cecekucen Safwan bai ma Badiyya adalciba ya fad’o tsakar gidan. Mata ya gani tuli guda a tsakar gidan, tsugunnawa ya yi ya gaishesu, sannan ya ce.

“Na zo duba jikin Badiyya ne, yanzu dawowarmu kenan na ji labarin rashin lafiyar tata, zan ga jikin nata, sai mu ta fi asibiti tun wuri.”

Da hannu Maman Badiyya ta nuna mishi d’akin da ta ke a kwance, k’awayenta sai lallashinta su ke yi.

Da sallama ya kutsa kai cikin d’akin, idanu su ka had’a shi da Badiyya.”

Mrs Bukhari ce

MRS BUKHARI

65-66

Idanu ya lumshe ganin yanda lokaci d’aya ta fige ta fad’a. Zama ya yi a bakin gadon da ta ke kwance. Bai ko kula da ‘kawayenta da ke wajan ba, hannu ya sa ya jawota jikinshi. K’amshin turarenshi ta shak’a, a hankali ta shiga rera kukan da ya rasa ina zai tsoma ta, da d’aya da d’aya k’awayenta su ka watse tas, d’akin ya rage da ga Safwan sai Badiyya” Jikinta ya ji ya d’auki zafi rau.

“Ya salam haba Badiyya. yanzu abunda za ki yi mun kenan? kin sa k’afa kin shure alk’awarin da ki ka d’aukar mun, kan Aure na bazai zama abun d’aga hankalinki ba. Gashi ba’aje ko’ina ba kin yi ta kuka, har zazzab’i ya sauka miki.” Hannu tasa ta k’ank’ameshi gam a jikinta, ahankali ta soma sassauta kukan na ta, shi kuma ya na ta aikin rarrashinta, tare da shafa bayanta, cikin shigar rarrashi, sai magana ya ke bata. Sai da ta tabbatar nutsuwarta ta dawo mata ta d’ago kanta hawaye cab’e cab’e.

“Safwan rayuwata amana ta ke a hannunka, ka yi k’ok’arin zamewa namiji d’an goyo da zani. Kar ka wulak’antani, kar ka ba da k’ofar da za’a wulakanta ni. Zuchiyata jaririyar zuchiyace, tattali da lallab’a kawai ta sani. Na san kai mun halacci da ka zauna da ni fin shekaru goma babu haihuwa, duk da irin gori da danginka su ke yi mun.” Hannunshi ya sa ya rufe mata bakinta da shi, cikin mutuwar jiki ya ce.

“Badiyya kishi ne ya saki subda  hawaye ko? Iya k’ok’ari kin yi, kuma na yaba. Ki sani k’arin auren da na yi ba ya nufin kin gaza ta ko ina. Wallahi na yi aure ne, dan buk’atar hakan ta taso mun, amma ki sani ke macece tamkar da dubu. Baki rageni da komai ba. Ba na son uwar gidana ta sake yin kuka, ki ta shi mu je asibiti.”

“A’a Safwan Na warke, dama fargaba ce kawai ta haifar da zazzab’in Amma yanzu ka k’arfafa mun guiwata. Je kai kwamciyarka ka huta.”

Cikin soyayya su kai sallama, kai tsaye d’akin zaure ya nufa. Mudi ne ya shiga da sallama, hannunshi rik’e da ledar kaji da shayi mai kauri a cikin k’aramar robar fenti.

“Safwan ga shi a kai ma amarya da k’awayenta.” Ya na dariya ya amsa. A kunyace yai sallama b’arayin su Sadiya ya mik’a musu kajin. Hadiza ce ta amsa tace.

“Bari a kirawo ma Sadiyan.”

Sadiya

Muna ta zabga hirar mu kamar ba dare ba, Hadiza ta shigo da ledar kaji da shayi. Da ta ajjiye tace.

“Sadiya ki je Safwan na son ganinki.”

Duban ta na yi na ce

Ni wallahi Hadiza kunyar su Goggo na ke ji, kawai sai in wuce su?

“Munafuka, duk sun yi bacci tuni, ki tsallake su ki fice kawai.

Ahankali cikin sand’a na fice a d’akin.

A jingine na same shi a garu, da ganina ya zuba mun idanunshi masu karya mun kuzarina. Kallon da Safwan ya ke jifa na da shi na musamman ne, ni na fahimci in da kallon ya dosa.”

Barka da dare angon Sadiya” Murmushi ya mun, yai k’asa da muryarshi kamar mai jin bacci yace.”

“Barka da shigowa rayuwata Sadiya, barka da sabunta mun jini da kike k’ok’arin yi gobe uwar haka, ina miki barka da shigowa familyn Safwan Sales Gwarzo.” murmushi kawai na bishi da shi.

Matsowa ya yi daf da ni, take numfashina na ji ya na katsewa, soma jawo shi da kyar na yi kamar wata mai ciwon asma. Hannayena ya kamo yana murzawa a hankali_ a hankali. D’umi da taushin hannunshi su ka sanya ni bisa wani yanayi na daban.

“Sadiya ki shirya amsar Baby na gobe, ki shirya jiyar da ni dad’inki, ina mararinki Sadiya. ki je ki kwanta, dan ki samu bacci har da na gobe.”

Hannuna ya saki, ya soma ja da baya da baya. Ni kuma ina tsaye a wajan ya maishe ni tamkar poster, har sai da na ga k’ulewarshi, na sauke numfashin da na ja. Idanu na lumshe tare da shigewa ciki.”

Washe gari aka shiga bud’ar kai. Eh lallai nasan na auri d’an dangi. Kuma abun sha’awar duk k’anne da yayyun Safwan kamanninsu d’aya, har da wad’anda ba ciki d’aya su ka fito ba. Anty Salaha ce ta shigo d’akina tare da Badiyya. Ina uwar d’aki da k’awayena su ka yo sallama.

“Anty Saliha kin dawo?” Murmushi ta yi mun

“Uwar gidan Safwan ce ta dawo da ni, ta na son ganinki tun jiya amma cunkoso ya hanata ganin naki.

Da kallo na bita, iya mace Badiyya ta kai mace, tsaiwar diri da cikar k’irji kawai zan nuna mata,farace sol. gata doguwa siririya. Ta sha kwalliya har da jan k’unshi ta yi shar tamkar amarya. Yak’en dole na yi mata.

“Barka da isowa uwar gida.”

“Ke zan yi ma barka da zuwa, da fatan ba ki yi fishi da ni ba ko?” Da sauri na girgixa kai na, jikina ya mutu lakwas. dan ba haka na yi tsammanin ganin Badiyya ba. Katse mun tunani ta yi da cewa.

“Ga wannan babu yawa, tawa gudunmawar kenan” Laida ta mik’o mun cike. Hadiza ce ta amsa tare da yi mata godiya. Anty Saliha tace.

“Abincin k’awaye da aka aiko da shi, ita ta yi komai da komai.” Godiya su Hadiza su ka shiga yi mata. Har suka juya ni dai na kasa d’auke idanuna akan Badiyya. Fargabace ta tasan mun. Gani nake Safwan ya Aure ni ne, kawai dan in haihu mishi, kuma sabida tausayin Haidar. Nan take damuwa ta shigeni.

Ina gani su Hadiza da su Goggo su ka had’a yana su yana su, Su ka wuce, Bayan sun zagaya da ni wajan matan yayyen Safwan maza, da ma sauran dangin nashi, Anty Saliha ita ta dinga yi mun bayanai dalla dalla. Ni ba gane komai da kowa na ke yi ba. Bayan tafiyar su Goggo. ina k’unshe a d’aki. Yayyen Safwan suna falo dank’am Har dare.

Da misalin k’arfe goman dare na jiyo Sallamar Safwan. Ajjiyar zuchiya na sauke. Amma abun mamaki sai na ji na shak’i k’amshin turaren da ban san Safwan da shi ba.” Badiyya ce ashe, hannuna ta kamo, ni kuwa na biyota tamkar rak’umi da akala har zuwa falo.

Ita ce ‘yar rakiyar Ango. Doguwar nasiha tai mana, tare da yi mana sallama.

Ta na fita Safwan ya matso jikina cikin zumud’i. Manna ni yayi a yalwataccen k’irjinshi. Idanu na lumshe hawaye su ka kwaranyo mun, bansan na fashe da kuka ba sai da na ji, labb’an Safwan a kan nawa, yana lallashina.

A daren babu wata hira data gudana a tsakanina da Safwan, bayan gabatar da nafila bisa koyarwar addini, sai kaza da madara da Safwan ya baje mana, ni tsabar sanyi jiki, madarar kawai na sha.

A cikin darennan Safwan ya raya sunna da ni, sai dai fa lallai na san na auri jarumi, awa guda Safwan ya yi a kaina. Sannan da komai ya lafa ya murgina yai bacci. Sambatun kalmar da Safwan ya dinga nanata mun ita ce ta sa ni na kwana cur ina kuka.

“Ki sama mun d’a Sadiya, zan baki Baby a cikin darennan, ki haifa mun kyawawan ‘ya’ya.” Sune kalmar da Safwan yai ta nanata mun, sai hud’un asuba bacci ya fisgeni, idanuna duk a kumbure. Sai ajjiyar zuchiya na ke saukewa a cikin baccin kamar k’aramar yarinyar da ta wuni kukan rigima.

“Sadiya Sadiya, uwar ‘ya’yana, ki tashi ki yi sallah, shidda har da rabi.”

A cikin mafarki nake jiyo sautin muryar Safwan ya na dukan dodon kunnena. A hankali na bud’e idanuna, banko kalli in da ya ke ba, sauka na yi akan gadon, tare da fita zuwa kitchen. Risho na kunna na d’aura ruwan zafi, wankan sallah na yi, tare da gargasa jikina.

Da sallama a bakina na shigo, ya na tsaye a gaban madubi, yana gyara tsaiwar hular shi.”

“Kin fito uwar ‘ya’yana?”

Eh. Kawai na iya ce mai.

“Bari in je in duba ya Badiyya ta kwana da jiki, ki jira ni kar ki yi kumallo, Innah zata aiko da shi.” Fuskata ya shafa, ya fice.

Yuuu na bishi da idanuna da suka cika tab da hawaye, ina zubar da hawaye na yi sallah, bayan na idar zama na, na yi akan sallayar ina ta ragargazo adda’a tare da neman dacewar Aure.

Gidan na gyara ko ta ina, turaren wuta d’an tsinke 999 na kunna, ko ina ya d’auki k’amshi.

‘yar kwalliya na yi a fuskata mara hayaniya. Shadda ce a jikina d’inkin doguwar riga ruwan goro. Mayafi na yafa, na fice zuwa cikin gidan.”

d’akin Innah  kawai na shiga, su Anty Saliha, da su Anty Murja duk su na nan, amma da halama shirin tafiya ma su ke yi. Farin cikinsu ya kasa b’oyuwa har akan fuskarsu, musamman Innah wacce ta rasa inda za ta tsoma ni. A kunyace na gaishe su dukka, kaina a k’asa. Cikin fara’a da zaulaya su ka amsa mun, Innah ta ce.

” ‘Yannan na ji dad’in ganinki sosai, inai miki maraba da zuwa gidannan, dama yanzu mu ke shirin zuwa wajan na ki da su Murja da su ke shirin tafiya. Tunda kin shigo mu yi komai a nan, Bilkisu ga Sadiya, a yi mata nasiha, sannan ki fayyace mata waye mijinta a sauk’ak’e dan ta ji dad’in zama da shi cikin sauk’i, da ma abokiyar zaman na ta”

mrs Bukhari ce.

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

67-68

Anty Bilkisu ta ce.

“Safwan ya na da sauk’i, ga shi da d’aukar shawara. kuma ya na da kafiya da taurin kai a bisa abun da ya sanya a gaba dan gudanarwa. Ya na da hak’uri, amma kuma akwai zafi musamman in ki ka tab’a dangin shi, Akwai biyayya da jin maganar na gaba. Ya na wani irin murd’add’en hali wanda in ya birkice babu mai iya gano kanshi. Abincin da ya fi so shine. Tuwon shinkafa miyar kub’ewa d’anya da bushasshen kifi da man shanu, Baya shan shayi sai kunu, kuma ya fi son mai tsami. Ya na da tsabta wanda a lokacin da yake yaro mu kai tunanin ko aljanune su ka shafe shi. Matar shi Badiyya kuma ni bansan wani halinta ba. Gare ki Anty Saliha an zo wajan ku. Dariya Anty Saliha ta yi ta ce.

“Badiyya dai ta na kirki da kawaici sosai dan ta shanye abubbuwa da yawa a cikin dangin mu, kuma ta ba Safwan goyon baya d’ari bisa d’ari a rayuwar shi ma ba ki d’aya. Ba mu santa da mummunan hali ba. Mu na fatan ke ma ki zama kamarta ko fin ta ma. Allah ya baku zaman hak’uri ya kawo ‘yan biyu sau hudu.” Dariya mu ka yi dukka.

Ina zaune a falon Innah surukan gidan su ka rik’a shigowa gaisheta d’aya bayan d’aya. Sai a yanzu ne na ke kallonsu da kyau tare da k’ok’arin rik’e sunayensu.

Na jima a d’akin Innah ina jiran Safwan ganin bai shirya dawowa yanxu ba, na mik’e tare da yi musu sallama.

Tare da Madina muka fito, yarinyar wajan Anty Saliha ce, tana rik’e da kwanukan abincinmu har zuwa b’arayinmu.

Ina zaune kwalam tamkar wata mara gata, agogon dake kafe a bangon d’akin na ke ta kallo, sai sha d’ayan rana Safwan ya shigo d’akin.”

“Amarya bakya laifi, aimun afuwa Yayarki ce ta d’auke mun hankali. amma a yi hak’uri dan Allah.”

Zama ya yi a kusa da ni, tare da hamo hannaye na dukka biyun ya na murzasu. Lumshe idanuna kawai na yi amma na kasa cewa da shi komai.

“Kin ta shi lafiya?” Sai lokacin na dube shi, fuskarshi da bakinshi duk janbaki yayi jawur. Ajjiyar zuchiya na sauke, ahankali na zame hannayena.

Ina kwana, ya gajiyar hanya?”

Jawo ni ya yi na fad’a jikin shi a hankali, k’amshin turaren shi da k’amshin turaren Badiyya ya cakud’e a jikinshi ya ba da wani kalar k’amshi na da ban.”

“Sadiya kamar fishi ki ke yi da Angon na ki ko, ko akwai wani abun da na aikata wanda bai miki ba? Ki sanar da ni in baki hak’uri, yanayin tamkar horo kike mun.” Cikin cijewa na aro dauriya da juriya na dangana ma kaina. Da murmushi na d’ago fuskata na dube shi. murmushi mu ka sakar ma juna, Hannu nasa na goge mishi bakin shi da fuskar shi.

Babu laifin da kai mun, sam gajiyar biki ce ba ta sake ni ba. Kuma ka sake d’aura mun wata gajiyar….

Ban rufe baki ba, Safwan ya rufe mun da na shi, kusan minti 30 ya na muzata yanda ya ga dama, ga ciki na babu komai.

A cikin satikan amarcin mu na murzu a hannun Safwan. ga tsaiwar dare da ya ke yi kullum kan Allah ya dube shi ya ba shi magaji.

Ranar da na cika sati guda a gidan Safwan, har da kwana ukun da Badiyya ta k’aramun a kai. Ranar Badiyya ta tare a d’akinta. Na ga zumud’i da rawar kai sosai a wajan Safwan, dan tun magriba ban kuma sa shi a idanuna ba.”

A shashen Innah na ke kusan rabin wuni na, kullum inai mata wanki, shara, gyaran d’aki, har kitso da tsifa duk ni na ke yi mata. Hakanne ya d’aga darajata a idanun Yayyen Safwan maza da mata da ma shi kan shi Safwan d’in.”

Yau dai na ta shi jikina babu wani ishasshen k’arfi, ga amai da duk ya addabe ni sai ta so mun ya ke yi, Safwan a d’akina ya ke. bayan na sallameshi ya ta fi wajan aikin da Mudi ya ne ma mai a kamfanin shinkafar da ya ke aiki. Safwan ya na ‘daya daga cikin masu d’ura shinkafa a buhu su sa a inji ya rufe bakinta, sannan in za’a sa a mota a tafi da shinkafar zuwa store d’insu a Bauchi. su za su yi dakon shinkafar.

Lallab’awa na yi na shiga d’akin Badiyya dan muna zaune lafiya kan mu a had’e ya ke sosai, dan duk zuk’e jikina da na ke yi, Badiyya tak’i yarda fur, a jiki ta dinga jana, kuma na ga Safwan na k’aunar hakan dole na saki jiki da Badiyya.

“Ah Sadiya ya dai yau na ganki haka lafiya dai ko?” Sai da na zauna tukunna na ce.”

Ke dai bari Badiyya rai dangin goro, yau jikin dai sai lallab’awa kawai na ke yi. Amma ya maganar mu, dan Allah kin yi mai maganar kuwa? Na ga ya shigo nan kafin ya fita.”

Dariya ta sakar mun

“Wallahi Sadiya na yi mishi magana, kuma cikin yardar ubangiji ya amince da hakan, ya ce mun zai karb’i takaddun naki, zai je asibitin da kan shi zuwa gobe akwai abokinshi likita zai kai mishi, ya ne ma miki gurbi, dama mu na da k’arancin mata  a harkar kiwon lafiya, ni kaina sai na ji dama na yi boko, ko dan in ba da tawa gudunmawar ga d’umbun lada da zan samu.” Ajjiyar zuchiya na sauke na dinga yi mata godiya, ita dai sai dariya ta ke yi mun.

“Amma fa ya kwab’eni kan cewar kar in fad’a miki. Sai ki ja bakin ki ki yi shiru.” Magana na bud’e bakina zan yi, wani tari me had’e da amai ya tunk’uro mun. A guje na isa madugana na dinga shek’a amai Badiyya na kaina ta na mun sannu, na yi amai sosai a wajan. Da taimakon Badiyya na gyara bakina da jikina da na soma b’atawa. Ita ta kaini har kan gado na.

“Alhamdulullahi abun naima fa ya samu, yau zan mallaki k’aton goron albishir kenan.”

Hannunta na rik’e ina haki na ce.

Badiyya dan Allah kar ki sanar da shi komai, ki bari takaddar samun aikina ta zo hannuna, na baki dama ya ji a bakin ki.”

“Toh babu damuwa, amma na yi farin ciki matuk’a. tsawon shekaru sama da goma sha muna neman d’a amma sai yanxu Allah ya amshi rok’onmu. Sadiya ko akwai wani abun da ki ke sha’awar ci?” Kai na girgiza mata na ce.

“Zan lallab’a in je wajan Innah akwai kunun tsamiya shi kad’ai na ke sha’awar sha.” Ta ce

“Amma za ki iya zuwan? Ki huta mana” Dariya na yi mata.

Ai ba na jin ciwon komai, dama amanne ya dame ni, kuma da na yi sai na samu sauk’i, zan lallab’a”

B’arayin Innah na wuce, a can na wuni cur, har abincin dare a can na ci, kasancewar Safwan a d’akin Badiyya ya ke yau.

Ina zaune ina matsa ma Innah k’afa, mu ka jiyo sallamar Safwan, hannunshi rik’e da jaka, ga Haidar na biye da shi a baya.”

Na yi farin cikin ganin Haidar sosai, shima yaron ya yi farin cikin ganina, sai tumurmusata ya ke yi. Innah ta dinga jan Haidar da wasa, shi kuwa da ya ke mai d’an banzan surutune, sai ya sake da’ita kamar sun saba sosai.

Bayan mun tafi b’angarenmu, a falon Badiyya mu ka ya da zango, kamar yanda ya ke a tsarin Safwan, duk d’akin da ya ke, toh anan za’aci abinci ayi hira kafin a watse. Muna shiga Badiyya ta soma murnar ganin Haidar, na ji dad’i yanda kowa ya amshi Haidar hannu Bibbiyu ba kyama.”

Dama Kano ka ta fi Safwan shine ko Labari? Dariya kawai ya mun ya na kallona.

“Uhm ai d’aurin Auran Mama na je, an d’aura auran, shine na tawo da Haidar, ta yi mana k’ok’ari ai.” Kunya ce duk ta lullub’eni a wajan har na kasa cewa komai.” Abinci mu ke ci, da ya ke miyar ganye ce sai na ji dad’in abincin sosai, ina gamawa na rik’e hannun Haidar na ce.

Toh mu kam za mu ta fi, bacci na ke ji sosai.”

Safwan ne ya mik’e.

“Mu je in ra ka ku.”

Sallama mu ka yi da Badiyya, mu ka fice, Haidar na saman kafad’ar Safwan a kwance”

A kan gadona ya shinfid’eshi, har ya yi bacci abunshi, rumgune ni ya yi a jikinshi yace.”

“Ya a ka yi ne uwar ‘ya’yana, plz ki yi ma Haidar k’anwa mana.” Dariya maganar ta shi ta ba ni, kanshi na shafa na ce.

Lokacine kwanannan za ka ji kyakkyawan labarin da zai dadad’a rayuwarka, ya zama sanyin idaniyarka.”

Cikina ya shafo idanu a lumshe ya ce.

“Allah yasa Uwar ‘ya’yana.”

Ameen

Saman sib d’ina ya zarce ya d’anyi bincike a wajan,  takaddun makarantata ya d’auka ya fice. Da ido kawai na bi shi, kaya na tub’e, wanka na je na yo, na zura rigar bacci mai sauk’i. Ina kwanciya sai bacci.

Asuba ta gari

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

69-70

Washe gari ma, haka wunin ya k’are mun a daddafe na ke yin komai, dan laulayi na ke yi sosai. Yau a d’aki na wuni a kwance, Innah da sauran matan gidan sun tafi Bauchi ana bikin Madina d’iyar Anty Saliha, Badiyya ma ta tafi, ganin ba na jin dad’ine Innah ta ce in zauna a gida kawai. Na dai ga ta fita ta na d’aga hannayen ta sama halamar ta na godiya ga Allah. Murmushi na yi dan na fahimci Innah ta ga ne a wanne halin na ke.

Da daddare mu na zaune ni da Haidar, na gama amai kenan na shigo ina nishi, na jiyo dawowar su Badiyya.

Innah ce ta soma shigowa ta same ni sai ni shi na ke yi, duk na galabaita.

” Sadiya, laulayin ne ya ke baki wahala haka? kai Allah ya raba lafiya.Allah na gode ma in da rabo ashe zanga jinin Safwan.”

Wuff Safwan ya shigo d’akin, Badiyya na biye da shi. Sai murmushi take yi.

“Innah na ji kamar kin ce laulayi ko?” Duk ya bi ya rud’e dan ji ya ke yi tamkar mafarki.”

“Eh Safwan laulayi, juna biyu gareta, Allah ya amshi addu’o’inmu

Sujjada Safwan ya yi na godiya ga Allah, ya kusan minti goma a durkuse yana mai godiya ga Allah. Innah sai sharce hawayenta ta ke yi. Safwan d’ima da hawaye ya d’ago a fuskar shi.

Sannu kawai ya shiga jera mun ya ma rasa ina zai sani. Innah tace.

“Me ki ke son ci Sadiya?” Cikin munfashi sama sama na ce mata.

Tuwo zanji.”

“Toh shikenan, Badiyya sai ki je wajan Jamila ta zubo mata tuwo, aiki ai ya same ki, dan ko tsinke Sadiya ta dena d’agawa a gidannan. Kai kuma dole Sadiya ta koma turakar ka kwata kwata. Haidar ma tafiya da shi zanyi, jibi zan tafi b’oto da shi zan ta fi.”

Sallama ta yi mana, ta ja hannun Haidar su ka wuce.

k’ank’ame ni Safwan ya yi, ya na jin d’umina da na yaron shi a jikina. Sai shafar bayana ya ke yi kawai.

Badiyya ce ta yi sallama, Anty Jamila na biye da ita.

jikina na zame a hankali, ina jin kunyar wannan terere.

“Masha Allah sannu Sadiya, kai abun murna. An dad’e ba’a shiga murna irin ta yau ba a family, su Saliha da su Bilki ma duk dai sun ce a yi miki sannu.

Ni dai kaina na k’asa kunya duk ta tufe ni.

Badiyya ta dure mun tuwon a gabana, har sai da Anty Jamila ta fita sannan na soma cin tuwon.”

“Badiyya” Safwan ya kira sunanta da

“Na’am” Ta amsa”

“Za ki yi hak’uri zan kasance tare da Sadiya har zuwa wasu ‘yan watanni kafin jikinta ya warware. Ina ga hutu zan d’auka a wajan aiki ko na sati ne. Ki d’ebo mata kayanta a sib ki kai mun turakata. Gashi da har na sama mata aiki a Babban asibiti na nan, kuma Dr Jibril har ya d’auketa.”

Ina jin haka zumbur na gyara zama na nace.”

Zan iya amma ai Safwan, wallahi ina son aikina” Shafar cikina ya yi

“Ni ma haka ina son Baby na, hak’uri za ki yi kawai.”

Badiyya dai, mik’ewa ta yi abunta ta yi abunda Safwan ya umarce ta.

Tun daga wannan ranar na zama sha lele a gidan su Safwan, dan ina samun kulawa ta musamman a wajan kowa da kowa. Innah ta na b’oto ita da Haidar. Sai rainon cikina na ke yi cikin k’oshin lafiya, Badiyya ma na ga k’ok’arinta a kaina, dan har mamaki take bani, ko tsinke ta hanani d’auka, hatta ruwan wanka in Safwan ya fita ita ke kai mun.

Su Anty Saliha kuwa duk sai da su ka zazzo ganina, ni kunya ma duk ta isheni.

cikina na da wata uku

Fitowa na yi da ‘yar jakata a hannu, Haidar kuma ya na makaranta. Badiyya na yi ma sallama.

B’angaren Innah na nufa.

Innah na fito zan je asibiti. Baki Innah ta washe ta ce.

“Masha Allah, ko Jamila ta rakaki ne, Sadiya.?” Kai na girfiza na ce.

A’a Innah, Anty Jamila akwai k’ok’ari, kullum sai ta aiko mun da tuwo, ban da su goba da yalo.”

“Toh shikenan, ki d’an tattaka a k’afa tunda ba nisa, sabida tsinka jinin na da kyau a wajan mai juna biyu. Da

Toh” na bi Innah”

Ahankali na ke tafiya har na isa asibiti, kati na yanka, sannan na ja layi, mata ana zazzaune, masu tsohon ciki, da masu sabon ciki, sai hira su ke yi a tsakaninsu gwanin sha’awa. Zama na ke da wuya, wata baiwar Allah ta k’araso a galabaice, da k’yar ta zauna, sai da na taimaka mata ma.

“wash wannan ciki ya na bani wuya, ko fa bacci bana yi, Allah dai ya ba mu ma su jin k’anmu” wannan matar da ta zo yanzu ce ta yi magana, na ce

“Ameen, amma rainon ciki da rainon yaro bansan wanda ya fi wuya ba.” Matar nan cikin cijewa ta ce.

“Kai rainon Yaro ya fi wuya, shifa ciki dududu, wuyarshi ka haihu wata tara zuwa goma. Shi Yaro kuma, sama da shekaru ashirin kana rainonshi da ceta shi, balle ni da Allah ya jarabceni da ‘Ya’ya mata har bakwai. Maza uku, ga ciki kuma. Da idanu na bita ina jinjina ma Uwa, ba ya uwa a duk duniya. Ji wuyar da ta ke sha amma ga cikin na goma sha d’aya a jikinta.

Tabbb mu ma su na biyu kuma fa, ai ba ma tantance komai ba.

Tace

“Kinga baiwar Allah, duk ciki haka ya ke zuwa mun da laulayi, ga fitinar yara da hayaniyar su, ga hawan jini ina fama da shi, Duk k’ok’arinka kuma Namiji akan k’ank’anin abu  sai ya ce ka ga za.

Da safe in ta ta shi kamar maukaciya haka na ke komawa, in sallami me gidan ya ta fi aiki, Yaran in sallami ‘yan makaranta suma su ta fi, yungu yungun muna tare a gida, wallahi har ‘yan makaranta su dawo ina aiki. Sai sun dawo ne na ke samu in sa d’uwawuna a k’asa, hayaniyarsu ba za ta barni in d’anyi k’ailulaba, ga makaranta ina zuwa ta adults education dan yak’i da jahilci, yanzu haka na kusa kammala sakandare, kuma zan fad’a tsangayar ilimin likitanci. Rayuwar mace bata tafiya da kyau sai da ilimi, yawan yara bazai hana ka karatuba, ko dan ka inganta tarbiyyar yaranka ai ka je makaranta kai ilimi. Mace uwar al’umma ce fa.”

Mamakin wannan baiwar Allah duk ya bi ya cika ni, ga ta tsab da’ita kai ba ka ce ta hayayyafa har goma ba, ga karatu ta na yi, abunda ya fi komai burgeni kenan nace mata.

Sunana Sadiya, kuma kina da ra’ayin in kin kammala karatun likitancinki, ki yi aiki akan abunda ki ka karanta? Dariya ta yi, cikin hali irin na masu tsohon ciki tace.

“Sosai ma, ai amfanin karatun kenan, mata da yawa su na zaune basa neman ilimi, sai su fake da aure ko yara. Kuma dukka basa hana  ilimi ko aiki. Shi yasa mu mata mu ka zama koma baya sosai, ko asibitocinmu ki ka shiga, sai ki ga maza  sun fi yawa. Mazan da yawa suna k’alubalantar ilimin mace, sai ki ga mace ta dage ta ci karatu dan ta yi ma k’asarta hidima, amma daga k’arshe sai ta rasa mijin aure. Za ki ji wasu har d’an kira su ke yi mata da sunan karuwa ko ‘yar bariki, ga masu cewa ‘Yan boko basa zaman aure ga raini, Wannan ma ya na dak’ushe k’wazon mata kan neman ilmi.” Ajjiyar zuchiya na sauke nace.

“Abunda ke faruwa a Al’ummar mu kenan, matan da su ka yi zurfin karatu suna fuskantar tsangwama da kyara. Gani su ke tamkar mace bazata tab’a fitowa da kwalin gama jami’a lafiya ba face sai ta siyar da darajarta na d’iya mace. Da yawa yawan mazan dalilinsu na gudun ‘Yan bokon kenan. Iyaye ma wannan dalilin ke sa su hana Yaransu yin zurfin karatun sai ki ga an yi ma yarinya aure da k’arancin shekaru a jikinta. Kuma hakan ba k’aramin cutarwa bane. Sai kin je asibiti b’angaren ‘Yan yoyyon fitsari. Nan zaki ga mata k’anana wanda wasu garin haihuwane cutar ta kama su, wasu ta hanyar saduwa ne cutar  ta kama su.”

Baiwar Allah’n nan tace.

“Sadiya ni kaina, ina da shekaru goma aka aurad dani, na sha bak’ar wahalar rayuwar aure, dan a lokacin ma bansan mai ke mun ciwo ba, dan ko jinin al’ada ban soma ba. Haihuwata ta fari, a lokacin shekaruna sha uku, na haifi ni’ima, sai da na yi wata shida a b’angaren ‘Yan yoyyon fitsari. A lokacinma turawane likitocin da suke duba mu. Shekaruna  Talatin da yin Aure. Babbar yarinya ta, ta na jami’ar Bayare dake kano. Sauran kuma duk suna gabana. Sunana Safara’u Maman Ummi.”

Sunana da na ta mu ka jiyo ana kira, tare mu ka shiga d’akin awo da’ita. Tare mu ka gama komai, mu na tafe mu na hira dan Maman Ummi akwaita da hira.

“Nan shine gidana Sadiya, wata me zuwa in mun had’u na biki in ga na ku gidan.

Toh Maman Ummi nagode sosai, a gaida yara.”

Sallama mu ka yi da Maman ummi, na wuce gida.

Wasa wasa cikina na ta girma, kuma yanzu garau na ke ji na sosai. Xumunci ya k’ulle sosai a tsakanina da Maman Ummi, dan da ta haihu ma har suna na je, turmin da ni da omo na kai mata.

Ciiki na ya na da wata bakwai, Mama da Goggo Hansatu su ka kawo mun ziyara. Na ji dad’in ganin Mama yanda ta sauya, ta yi kyau sosai.

Haka su ma sunyi farin cikin yanda su ka ga zaman mu da Badiyya. Yaro na aika zuwa gidan Maman Ummi, kan ta zo su gaisa da su Mama.

Ai kuwa kafin ma ta zo, ta aiko yaranta da lafiyayyen tuwon masara miyar karkashi.

Shi su Mama su ka ci, sun yi farin cikin ganin k’awata Maman ummi.

Kwana d’aya tak su ka yi, shima kamar a kan k’aya su ke su ka ta fi.

Ciki na na wata takwas, Safwan ya sa yi komai da komai, siyayyar har da ta hauka abuka da ba saban ba 😀.

Ranar wani Lahadi kuwa da daddare nak’uda ta kama ni, Safwan da Badiyya ne su ka kaini asibiti.

nak’uda na ke ta faman yi, kafin gari ya waye asibitin ya cika da jama’a. Har zuwa lokacin nak’uda na ke yi. Sai wajajen bakwai saura na haifo kyakkyawan  Yaro mai tsananin kama da Safwan.”

Mrs Bukhari ce

MRS BUKHARI

71-72

D’akin hutu a ka wuce da ni, tuni bacci ya d’ebe ni.

Safwan

Sai suntiri Safwan ya ke yi a k’ofar labour room. Wata nose ce ta fito hannunta rik’e da jariri wanda ya sha seti mai ruwan madara.”

“Ina ta ya ku murna. Sadiya Adam ta sauka lafiya, Allah ya azurtata da haihuwar D’a namiji.

Safwan jikinshi har rawa ya ke yi ya sa hannu ya amshi jaririnan. Rungumeshi ya yi a kirjinshi, ya na jin so da k’aunar d’an na ratsa duk tsokokin jikinshi. Kunnen yaron ya kai bakin shi ya shiga jero mai adduo’i tare da yi mishi hud’uba. Badiyya ya mik’a ma jaririn. Ta yi maza ta amshe shi ta rungumeshi tsam.

Su Anty Jamila duk su ka d’auki jaririn ana ta yi mishi adda’a.  Zukatan su cike da ta ya Safwan farin ciki, Kallon Anty Jamila ya yi ya ce.

“Anty wannan jaririn na mallaka ma Badiyya shi duniya da lahira, d’anta ne, kuma ko mutuwana na yi ban amince a k’wace yaronnan da ga hannunta ba.”

Kuka Badiyya ta fashe da shi tare da sake k’ank’ame jaririn a jikinta.”

“Hak’i’ka bani da kalmar da zan iya maka godiya bisa ga wannan kyauta da ka yi mun, ina godiya Allah ya ba ni lafiyar shayar da shi, kuma in sha Allah ba za a samu matsala ta b’angare na ba.” Anty Jamila ta ce.

“Amma fa wannan d’anyen hukunci ka yanke Safwan, Sadiyan ba za ta shayar da jaririn ba ma?”

“Eh Anty kuma na wakilta ki yi ma Innah baya ni, ko da wasa wannan yaron ba na son yasan cewar ba Badiyya ba ce ta Haifeshi ba. Ita za ta shayar da shi, Anty ku ta fi gida ke da Badiyya, da jaririn, a samu gadali  a bata ta sha, dan ta samu ruwan nonon da zai sha, Anty Zulai mu je ciki mu ga jikin Sadiyan.”

Mamakine ya ishi kowa a wajan, Anty Jamila ta ja hannun Badiyya wacce ta k’ank’ame jariri kamar za’a kwace mata, su ka bar cikin asibitin zuwa gida.

Su Anty Zulai kuma su ka bi bayan Safwan zungui zungui. a bakin gadon da Sadiya ta ke kwance su ka tsaya. Anty Zulai cikin rashin hak’uri ta ce.

“Hukuncin da ka yanke babu abunda zai haifar sai d’a mara ido, ni na tab’a jin irin wannan lamari Safwan, Anya ka na son Sadiya kuwa, ko dai yaran da za ta haifa maka kawai ka ke dubawa, tai ta haifa ma yara ka na ba Badiyya su, ita ta na shayar da su, kai kasan me ye zafin nak’uda kuwa? Tun wuri kafin Sadiya ta farka daga wannan baccin hawalar haihuwar gara ka yi tunani akan wannan lamari, kar zaman lafiyan da ya ke gidanka ya lalace a sanadin abunda ka aikata.” Safwan ya dube ta, ya ce da ita.”

“Anty Zulai ni a nawa ganin, yaronnan dai nawa ne, kuma ba wani gida na kai shi ba, Sadiya na da damar ganin shi a ko da yaushe. Banyi tunanin wannan zai kawo rashin fahimta a tsakani ba. Dukkansu matana ne, yaro kuma nawa ne.” Cikin juyayi Anty Zulai ta ce.”

“Tsakanin d’a da uwa sai Allah, bana ko shakkar zuchiyar Sadiya ba zata iya jure wannan horon ba. Ta ya ma zaka raba ta da yaronta tun a tsunman haihuwarshi, ka dank’a shi ga kishiyarta, kyauta ta halak malak, me yasa ba za ka bar mata wannan d’in ba in yaso in ta kuma haihuwa sai ka ba ma ita Badiyyan, gaba na ke jiye maka me hakan zai haifar.”

Sadiya

Ahankali na bud’e idanuna wanda su kai mun mugun nauyi, gefena na soma kallo dan sake kallon jaririna amma sai na ga wayam. Muryar Safwan na ji yo.

“Sannu Sadiya kin farka?” Murmushi na yi mishi na ce

Na farka.” Ina son in tambaye shi yarona amma kunyar su Anty Zulai da su ke ta yi mun sannu ya hana ni tambaya. Maman ummi ce ta k’araso hannunta rik’e da katon flacks na ruwan zafi, da kuma k’aramar kular abinci.”

“Me jego sannu, Angon k’arni ina ta ya ku farin cikin samun k’aruwa Allah ya raya shi da imani, ai ta gida na biya na ga yaron a hannun Badiyya wallahi tubarkallah masha Allah.” Da mamaki a fuskata na juyo na dubi Safwan, yayin da maganar maman ummi ta shiga yi mun amsa kuuwa. Safwan kuwa dakewa na ga ya yi, ya wani kawar da kan shi daga kallona. Anty Zulai na kalla, amma ban fahimci komai a fuskarta ba, na dai ga ta girgiza kai irinna wanda takaici ya isheshi, sai na ji ta ce.”

“Maman Ummi tunda ga ki kin zo, mu za mu je gida, mu rarrage aikace aikace, Sadiya sai kun dawo, Allah ya ba da lafiya.”

Ameen” kawai na iya ce wa da su, kamar wawuya na bisu da ido, Safwan ne ya mara musu baya, k’asa_k’asa ya ce.

“Bari in raka su waje” Ya ma kasa had’a idanu da ni sam, sai wani sun sun da kai ya ke yi.

Kamar mahaukaciya haka na d’amk’i hannun Maman Ummi nace.”

Ki ka ce kin ga jaririna a gida, a hannun Badiyya?” Da mamaki Maman Ummi ta kalle ni, d’an nazarina ta yi na wasu dak’ik’u, sannan ta ja nunfashi tace.”

“Safwan bai sanar da ke komai ba ne Sadiya?” Haushi tambayar da ta je fo mun ma ta bani, ba abunda na shirya ji kenan a matsayin amsa ba. Wato nose ce ta iso hannunta rik’e da takadda, Maman ummi ta mik’ama.”

“Gashi in ya shigo a bashi, an yi sallama, Tana cikin k’oshin lafiya haka ma abunda ta haifa. Malama sai ki kula da jikin ki, da ma jaririnki, Allah ya ba da lafiyar shayarwa.” Ko kallo ba ta isheni ba, Maman ummi ce ta had’a mun ruwan tea.

“Ungo Sadiya ki sha, ki samu hanjinki ya warware, ki kwantar da hankalinki, ni shawarar da zan baki shine ki bi komai a sannu, kuma da za ki iya zuba ma Safwan idanu kiga iyakar in da zai k’are gudun na shi ruwan da zai fi. In kin lura kunyarki ce cike a guraben idanunshi. Kar kuma ki tambayeni komai, domun babu abunda za ki iya ji daga gare ni, kar kuma ki tambayi Safwan jaririnki. Ungo sha.” Hannuna na rawa na karb’a, dan dama wata iriyar muguwar yunwar haihuwace na ji tana kad’a hanjina. Da zafi zafi na kukkurb’i tean har na shanye. Farfesun d’anyen kifi ta zuba mun, shima na cinye, amma banji na k’oshi ba sam, nan ta ke cikina ya soma murd’amun, marata na wani irin karta, ji nake tamkar mutuwa zan yi, dan abunda na ke ji a k’asan marata ya fi k’arfin abunda na ji a cikin labour room. A guje Maman Ummi ta fita, tare da noses ta dawo. Nan su ka rufu a kaina, sai zufa ke keto mun, idanuna na neman kakkafewa. Daga nan ban sake sanin in da kaina ya ke ba, Allura na ga anyi mun, nan na soma ganin kowa dishi dishi, harda Safwan da shigowarshi kenan.”

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA…*🔥

      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚

      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥

      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

Badi’at Ibrahim

    _Mrs Bukhari_

 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨

     _Miss Hajo_

73/74

SAFWAN

“Maman Ummi lafiya me ke damunta kuma, da ta farka sumul?”

Nose ce ta ce.

“Ba wata matsala bane babba, ku kwantar da hankalinku, wannan yana faruwa da mata a bayan haihuwarsu, amma ba wani damuwa, da zaran ta farka ma za ku iya tafiya.” Ajjiyar zuchiya ya sauke.

“Mun gode sosai.”

Maman Ummi ta mik’a mishi takaddar sallama.

“Ga takaddar sallama sun rubuto, amma kafin ka je biya ina so in yi wata muhimmiyar magana da kai.”

Sallamar shigowar su Innah da Matar Baffa  Goggo Hadiza ne ya katse Maman ummi.”

Wani mugun kallo Innah ta ke watsa ma Safwan, gabaki d’aya jikinshi yai wani irin mugun sanyi. Flacks d’in da ke hannun su yai maza zai amsa, Innah tai saurin kaucewa, sai na hannun Goggo Hadiza ya amsa ya ajjiye a saman durowar gefen gadon.

Waje Maman ummi ta ba Innah, Safwan ya fita da hanzari ya kawo ma Goggo  Hadiza wata kujerar.

“Barka da  Goggo, Barka da zuwa Innah.” Da fara’a Goggo Hadiza ta amsa mishi, ta na zaulayarshi.

“Ahh kaga Angon k’arni kana asibiti ashe har yanzu? Toh Allah ya raya wannan yaro da imani, Allah ya yi albarka. Na yi murna na yi murna.” Innah ta ce ma Maman Ummi wacce su ka gama gaisawa.

“Bata farka ba har yanzu baiwar Allah?”

“Toh farka har ma ta sha tea da farfesu, sai kuma ciwon ciki ya murd’eta, shine su kai mata allura. amma har an ba da sallama ma.” Innah tace.

“Sannu Maman Ummi da k’ok’ari mun gode Allah ya bar ‘kauna.” Innah sam ta k’i yarda su had’a idanu da Safwan, shi kuma sai sosa kai ya ke yi. Goggo Hadiza tace.

“Safwan sak’on ka ya isa, kamar yanda ka wakilta Jamila. Toh ta isar maka da sak’onka. Amma ka sani ka d’auko hanyar rushe duk wani gini na zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidanka, in ban da wauta irin ta ku ta yaran zamani, ina kai ina yin kyautar d’an mutum guda ba b’ari ba. Wannan ai ganganci ne, kuma ba son yarinyar nan Sadiya ka ke yi ba. Yarinya mai hankali da yakana irin haka iyi.”

Tsugunnawa Safwan ya yi a gaban Goggo Hadiza ya ce.”

“Kui mun afuwa a bisa hukuncin da na zartar a kan iyalina. Ni na yi hakanne dan a sake samun had’in kai a tsakani, Badiyya ba ta tab’a haihuwa ba, ni na yi zaton kowa zaiyi farin ciki ne da abunda na aikata, amma sai na ga sab’anin haka. Ku yi hak’uri, Allah zai ba ita Sadiyan wani.” Innah da ba ta so yin magana amma jin abunda Safwan ya ce, ya hasala zuchiyarta, cikin b’acin rai ta ce.”

“Ubangiji ne bai ba Badiyya haihuwa ba, shi kuma ya ba Sadiya. Kai baka isa kai ma Badiyya d’a da d’an da ta rayu wata tara a cikin mahaifiyarshi ba, kuma tana rayuwa a doron k’asa, ba nakasa ba ciwo. Amma da ya ke ku maza haka kuke baku da burin da ya wuce ku d’and’ana ma mace mad’aci a cikin rayuwarta, ga ku da son kan tsiya. Safwan za ka yi nadamar abunda ka aikata gaba. Za ka sha ruwan mamaki, ka ci nadama akan irin hukuncin da zan yanke ma. Ka sanar ma duniya ba son Sadiya ka ke yi ba.” Maman ummi tace.”

“Innah ni ina ganin maganar nan ko a barta  ba yanzu ba, in an je gida a tattauna komai, Ni fargabata ma shine ya Sadiya zata d’auki wannan lamarin?”

” ‘Yannan ai kinga daga nan ? Toh maganar nan ta k’are, bana so a sake tayo mun da ita, zai ga kafiya nima a waje na, kuma jariri ko ya maido ma Sadiya ba za ta k’arb’a ba, ya je ya kaima mowa.”

Sadiya

Farkawa na yi, na samu a na wasu irin maganganu da na kasa fahimtarsu, Innah  ce ta iso bakin gadon da na ke.”

“Sadiya kin farka, sannu, akwai in da ya ke yi miki ciwo ne?” A jere tai mun tambayar. na ce mata

A’a ba na jin ciwon komai Innah.”

“Toh tawo mu tafi gida kinji, Sadiya na.”

Hannuna ta kama na sakko a kan gadon, Safwan ya na gefe ya jingina da bango, da gani kasan a cikin rud’u yake.

Innah Jaririn fa?” Kasa hak’uri na yi, shi yasa na tambayi Innah, in ji daga bakinta cewar Jaririna na hannun Badiyya.”

“Mu je Sadiya, Jaririnki na gida.” Safwan na kafe da idanuwana wanda su ka sauya launi, wasu zafafan hawayene su ka surnano daga guraben idanuna zuwa kan kumatukana, ni kaina bansan ko kukan me na ke yi ba, ko dan an ce Jaririna na hannun Badiyya ne oho, amma kuma bakina cike ya ke fal da tarin tambayoyin da kowa ya kasa bani dama balle in amayar da su, abunda na ke ta juyawa a xuchiyata shine, meye dalilin da za’a tafi mun da Jaririna gida, alhalin ni ina asibiti? Gashi kallo d’aya na yi mishi, idanuwana a cike suke fal da son sake yin tozali da kyakkyawan jaririna, wanda k’aunarshi na baibaye jini da tsokar jikina, a matsayina na uwa.

Safwan binmu ya yi da idanu har mu ka bar cikin d’akin.

mamaki ya ke yi da aka kasa fahimtar manufarshi na alkhairi da ya sa ya mallakawa Badiyya Jaririnnan, A d’aya b’anrayin na xuchiyarshi kuma, sai juyayin maganganun Innah ya ke yi, a k’ok’arinshi na son ganin lallai ya fahimci in da furucinta ya dosa, amma ina tunanin na shi ma k’arewa ya yi kab. Idanu ya lumshe ya ce.

“Ya Allah”

Ya rada ina tudu balle ya dafa, jiki a mace ya fice a ofishin kwakwalwarshi na hasko mai videon kallon tuhumar da Sadiya ta bi shi da shi, tare da tausayin hawayen da ya ga suna zuba a fuskarta.

Wajan biyan kud’i ya nufa, duk abunda ya dace yayi sai da ya yi, kafin ya baro asibitin.”

Sadiya

Abun hawan da mu ke ciki gudu ya ke yi, amma ni ga ni nake yi tamkar ma baya wata tafiyar arziki, zuchiyata sai tunzura ta ke yi ita kad’ai, har wani amai ke taso mun.

Har k’ofar gida motar ta kaimu, mak’ota ne su ka soma fitowa, ganinmu da basket da flacks, ya tabbatar musu jikina da sauk’i. Tun daga waje aka so ma yi mun barka barka, da saukar Jaririn da kallo d’aya kawai na yi mishi.

Shiga mu ka yi cikin gidan Innah na rik’e da ni. Yayin da ni kuma sai ware ido na ke yi ko zan ga Jaririna. Amma ina babu kowa ma a tsakar gidan.

Kwanar b’arayin Innah na ga mun sha, ni dai ina biye da ita na zuba ma sarautar Allah idanu. A falonta mu ka ya da zango”

“Ungo Maman Ummi da kin sha ‘yar kwana bayan d’akina, za ki ga wani d’aki ta damanki. Ki bud’e ki share, a b’allo gadon Sadiya da sib d’in kayanta a mayar mata cikin d’akin maza. Bari in Kira Zulai ta taimaka miki.” Key d’in d’akin Innah ta ke mik’ama Maman Ummi, jiki a sab’ule ta amsa ta fice. Innah ta dawo da dubanta ga Goggo Hadiza.

“Hadiza had’a mata tea d’in ta sha, kafin a kawo kunun kanwa da tuwo, kafin fitarmu na sa Jamila ta yi, ina zuwa ni kuma.” Fice wa Innah ta yi a d’akin, ni dai a cikin duhu na ke sosai.

B’arayin Zulai Innah ta soma zuwa, ta sanar da ita, ta je ta ta ya Maman Ummi aiki. Daga nan ta wuce b’angaren Anty Jamila.

Badiyya ta na d’akin, Anty Jamila ta na kwatanta mata yanda zata shayar da Jaririn. domun har ruwan nono ya zo mata. Ana cikin haka Innah ta d’aga labule, Kawar da kai ta yi dan gudun ganin abun takaici.

“Jamila, yarinyar nan mun dawo, ki had’a wuta a d’aura kwatanniya, sannan a kai mata kunun tsamiya da tuwon, ki bad’e shi da ya jin daddawa, da man shanu.

In kuma Safwan ya shigo, ki ba shi sak’o cewar ya kawo naman gashi,  da kaza da za’ayi mata farfesu, ki lillisa mun farin kwalli.”

juyawa ta yi abunta, Anty Jamila ta yi tsaye jiki a mace, dama irin abunda ta gudanma Safwan kenan tun farko, ita kanta tasan hukuncin da ya yanke, yayi tsauri, ba daidai bane abunda ya aikata.

Duban Badiyya ta yi wacce ta ke zubar da hawaye, tace.

“Ki dena Kuka Badiyya da sakel bari Safwan d’in ya shigo, ki dank’a mishi d’an shi, ni dama na fad’a miki ma da baki sha wani gadali ba, domun wannan kyauta bazata kyautu ba. I na dai zuwa bari in aiwatar da abunda Innah ta sa ka ni.”

MRS BUKHARI

75/76

Sadiya

Ni dai ina zaune kamar wata gunki, tea na ke kurb’a amma ruhina baya tare da gangar jikina sam. Al’amuran sai d’aure mun kai su ke yi, zarge_zarge iri_ iri ne su ke bijirowa a zuchiyata.

Anty Jamila ce ta kawo mun tuwo da kunun kanwa, Goggo Hadiza ta tusa ni gaba,  kan lallai sai na ci a gabanta.”

Bayan awa guda, su Maman Ummi su ka kammala gyaran d’akin da Innah ta sa musu hannu aka yi tare da ita. Dukkan su ukun su ka shigo nan in da muke.

“Sadiya ta so kinji, ki ta fi d’aki ki kwanta, kafin ruwan wankan ya tafasa. A d’akin da na sa aka gyara miki za ki zauna zuwa wasu lokacin. Ki yi hak’uri da duk abunda zan zo in sanar miki.” Inna ce ke magana da ni, Anty Zulai ta ce.

“Innah ba’ayi haka ba, ni bari Safwan d’in ya zo da kaina zan sa ya karb’o jaririn a hannun Badiyya ya dank’a ma uwarshi kayanta, bai yi tunani ba ne shi yasa ya yanke wannan hukuncin.”

” Zulai ba na so a sake ta yar da wannan maganar, iyalanshi ne, shima jaririn ai na shi ne. Ki je d’akin ki kawai maganar ta k’are daga nan.”

Ni dai jikina har rawa ya ke yi haka na fita ina gauraye hanya, Maman ummi ce ta rik’e ni har zuwa cikin d’akin da su ka gyara yai tsab. A kan gado ta zaunar da ni. Dubanta na yi ina murmushi na ce.

Badiyya ya ba kyautar Jaririna in dai na fahimci zancan. Lallai kuwa zamana da Safwan ya k’are, tun a daren farko da na yi a gidan na fahimci dan in haihu mishi ya auro ni, tsantsar so kuma matarshi kad’ai ya ke yi ma. Kaico na. Kukan da na ke dannewa ne ya kwace mun, na jima ina kuka mai cike da tuk’uk’in bak’in cikin da duk wanda ke saurarom sautin kukan zai ga ne. Maman Ummi ta san abunda a kai mun mai girma ne irin wanda harshe baya iya bayyana zafi da radad’in shi, shi yasa sam ba ta yi yunk’urin hanani kukan ba. Har sai da na yi ma’ishina tukunna, na yi shiru a karan kan kin kaina. Sannan ta dafa ni.

“Sadiya kar ki ce za ki yi wani abu da za ki zo kina cizan yatsanki, ki bi komai sannu kan hankali ke fa ba yarinya bace, kuma kin d’and’ani zafi da gararin zawarci.”

Ban d’and’ani komai ba, ilimina ya d’ebe mun kewar da ko lokacin kaina aiki baya ba ni balle har tunane tunane su addabi rayuwata. Ke ba ki ga k’ask’antar da ni da.Safwan ya yi ba? Jaririna ya na tsumman haihuwa ya raba ni da shi, sabida ya fi kyaunar ganin Badiyya ta na dariya. Maman Ummi da wanne idon ma Safwan zai dube ni yai mun bayani?”

“Ni Sadiya abunda na ke nufi shine, ki nunar mishi kuskuren shi ko dan ya gyara gaba. Sannan lallai a baki d’anki ya kasance dake, in kuwa ya ci nasarar raba ki da wannan Jaririn, kuma ya hana ki shayar da shi, toh wallahi ko me yaron zai zama a gaba, bazai dube ki ba, Badiyya zai bud’e idanu ya gani a matsayin uwarshi. Shi goyo yana da mugun tasiri, bawai dan kin yi nak’udar silar zuwan shi duniya bane kad’ai zai sa ya soki har ya dinga jin motsin sonki da shak’uwa a ranshi ba. goyo da cin kashin yaro da fitsarinshi, da shayarwa, da kula da rayuwarshi, shi ke haddasa wannan soyayyar a tsakanin D’a da uwa. Ko gidan marayu ki ka je ki ka d’akko d’a sabowar haihuwa, ki ka rene shi, ki kai wahala da shi, toh fa ko da bayan ya girma za ki nunar mishi ke fa ba ke ki ka haifeshi ba. Shi kuma a wajan shi babu wata uwa bayan ke. Har abada kuma ke ce uwarshi…

Ya isa Maman Ummi kar ki sa zuchiyata ta fashe. Saurin dakatar da’ita na yi tare da saurin mik’ewa. Ficewa na yi daga d’akin ina kukan da hawayena ya ke ‘kok’arin makanta ganina.

Da Innah na ci karo, kuka na fashe mata da shi, ba wani kawaici da zan iya ci gaba da yi, domun cutata hakan zai yi. Duk wata kunya dole na shureta gefe, ina kukan fitar hayyaci, muryarta ma sai katsewa ta ke yi.

In nah, D’ana na ke so in karb’o zuchiyata ba za ta samu nutsuwa ba. A bani in shayar da Jaririna, d’uminshi kawai na ke son ji. Wallahi Innah shima ya fi buk’atata..

Kukane yaimun illar da dole na yi shiru, sai kuka da na ke ta rintimawa. Innah da Anty Jamila da za ta mun wankan jego su kai shiru, Anty Jamila ce ta ce.

“Sadiya ki yi hak’uri, dukkanmu iyayene mu san irin zafi da rad’ad’in da ki ke ji. Amma ki yi shiru, bari Safwan d’in ya dawo, ni da kaina zan karb’o miki  Jaririn in kawo miki. Na rok’eki kar ki je b’arayin da Badiyya ta ke, dan kin ga Safwan shi ya ba ta Jaririn da hannun shi. zai fi kyau ace shi ya karb’o miki Jaririnki.” K’uta Innah kawai ta yi ta ce.

“Shige ai miki wanka Sadiya, ki bar komai a hannuna, bazan zuba ido Safwan ya salwantar miki da hakkinki ba.”

Ban d’akin na wuce ina sharar hawaye, ga nonuwana sun yi mugun nauyi, sun ciccika da mama, har zuba su ke yi. Take nonon su ka sakarmun da wani mugun zazzab’i mai zafin gaske.”

Safwan

Jiki a sab’ule ya shigo gidan, matan gidan kowa ya yi jigum jigum a cikin tausayin Sadiya, tare da ganin rashin kyautawar Safwan da ita kanta Badiyya. Anty Jamila ta ce.

“Yauwa Safwan kai na ke ta zurga zurgar jira, mu je mu yi magana.

Ledar hannun shi ya mik’a ma Anty Zulai ya ce.

“Anty Zulai ga naman k’auri na me jego, itama Badiyya a d’ebar mata, tunda shayarwa za ta shiga.” Hannu Anty Zulai ta mik’a ya saka mata ledar. Ya bi Anty Jamila har falonta.

“Safwan ya yanke hukunci mai tsaurin gaske ita kanta Sadiya ta shiga wani mawuyacin hali na jin zafi da rad’ad’i, barin fad’ama gaskiya. Babu wata uwa da za ta yadda a kwace mata Jariri bisa wani dalili mara tushe da kan gado, ko da kuwa wannan uwar a cikin hauka tuburan take. Yanxu haka Sadiya ta na can kwance a cikin mashassara mai zafi, mamanta sun yi tauri, a ban d’aki sai da na d’an matse mata su ta d’an samu sassauci, ga kuka da ta ke ta faman yi. Innah ta yi mugun fishin da za ta iya yin mummunan furuci a kan ka. Ita kanta Badiyya ba za ta iya rik’e Jaririn a wajanta a na cikin wannan turku_ turkar ba. Abune ko da ya yuwu kamar yanda ka ke fata. Toh zukata da yawa za su kasance a jagule kuma a cikin rik’o tare da ajjiye miki a zuchiya mara warkewa sai dai ruruwa. Safwan ka mayar ma da Sadiya Jaririnta.” Murmushi abun ma ya ba shi. Sororo Anty Jamila ta bishi da idanu, da ma fa kowa ya san Safwan da kafiya akan duk abunda ya sa a gaba, musamman in ya san cewar ba addininshi ya tab’a ba”

“Anty Jamila kenan ni fa mamakin wannan lsmarin na ke yi. Jaririnnan fa D’a na ne, kuma ina da damar da zan iya kyautar da shi ga duk wanda nai niyya. Kuma Sadiya ta ba ni mamaki da ta kasa yi mun biyayya bisa abinda na yanke duk girmanshi, balle ma Jaririnnan nawa ne. Badiyya kuma matatace, tsawon shekaru goma sha uku mu na tare Allah bai ba ta Haihuwa ba, dan na bata D’a jinina ban yi zaton zai zama damuwa ba.

Anty barin fayyace miki wani sirri. Likitoci sun tabbatar mun Badiyya ba za ta tab’a haihuwa ba, ita kanta ba ta san da hakan ba, shi tasa nai mata wannan kyautar, kuma ni ba na son Jaririn ma yasan ba Badiyya bace ta haifeshi ba, duniya da lahira na ba Badiyya Jaririnnan ita na ke so ta zamo uwarshi. Sadiya hak’uri za ta yi Allah zai ba ta wani, ga Haidar ma.

Ajjiyar zuchiya Anty Jamila ta sauke ta lura Safwan ba zai sauka a kan bakan shi ba, mik’ewa ma ya yi ficewar shi a d’akin. D’akin Badiyya ya shiga.

Tana zaune a takure a bakin gado, Jaririnta na shan nono. Dubanta ya yi cikin tausayawa, Jaririn ya fi dacewa da’ita sosai. Idanu Badiyya ta zuba mishi ta na shirin yin kuka. Da sauri ya k’araso gareta. Waje ya samu kusanta ya zauna.”

“Badiyya ki toshe kunnuwanki da duk abunda za ki ji, idanuwanki ma ki runtse su, na tabbatar babu mai iya kwace jaririnnan a hannunki. Ni kuma kyauta na ba ki shi, na rad’a mishi suna Adam sunan mahaifin Sadiya, domun in nuna mata godiyata a bisa jariri da ta ba ni.” Kuka Badiyya ta fashe da shi.

“Wallahi Safwan so da k’aunar Adam ta shige ni, wallahi bazan iya rayuwa ba tare da Adam ba, ko ni na haifeshi ban yi zaton zan so shi kamar haka ba. Ka ba Sadiya hak’uri kar ta yi mun mummunar fassara. Adam zai samu kulawa da soyayyar da ko a wajan ta ba zai sa mu ba. Zan gina shi bisa tartibiyar tarbiyyar da za ta yi alfahari da hakan bazan iya ba ta yaron ba.” Hawayenta Safwan ya ke ta sharewa.

“Badiyya ba na son kukannan na ki sam ki dena. Kin ga yanda yaron da ke kan ki ku ka yi mun kyau kuwa, kamar in mayar da ku ciki.” Shafa fuskar yaron su kai ta yi, shi kuwa ya sha nono ya k’oshi baccin shi ya ke yi bawan Allah.”

Mik’ewa Safwan ya yi.

“Toh bari in lek’a mai jego da jiki, ba ta jin dad’i zazzabi da ciwon nono ya kamata, ki goya Adam sai ki je ki gaisheta.” Murya a sark’e Badiyya ta ce.

“Nauyi da kunyar Sadiya ba zai barni in iya had’a idanu da’ita ba. Sannan na dai ga su Anty Zulai sun fita da gado da katifar ta, da kuma kayanta na sawa da sib d’in tata.”

Ji ya yi kanshi ya mugun sara mishi, da hanzari ya fice a d’akin, kai tsaye zuwa d’akin Innah.”

Ta na zaune a k’asa ta mimmik’e k’afafunta ta na shan fura. Ba ta ko kalle shi ba. Ko sallamarshi ba dan ta san muhimmancin sallama ba, da bazata iya amsawa ba.

Waje ya samu a nutse ya zauna.”

Mrs Bukhari ce

MRS BUKHARI

77/78

“Innah ki yi hak’uri dan Allah a bisa fishi da ni da ki ke yi, ba ku gane manufata na yin wannan abun bane, wallahi na yi tunanin za ki yi farin ciki a bisa wannan abun sai na ci karo da sab’anin hakan…

“Dakata Safwan, ka ga maganar nan? Toh ba na son sa ke jinta a kunnuwana, zab’i d’aya zan baka a cikin umarnin da zan baka biyu, wallahi ka ji na rantse dole ka d’auki d’aya.

Ko ka dawo ma da Sadiya Jaririnta, ko ka sake ta domun ba sonta ka ke yi ba, bazan zura ido ka salwantar mata da hakkinta ba, amfani da ita kawai ka ke so ka yi na lura.”

Tashin hankali da firgicin da ya ke ciki yafi gaban k’awatance, kai ya sake sunnewa, ya na jiyo k’wak’walwarshi na kad’a mishi k’ararrawar da ta ke shirin salwantar da nutsuwarshi, da kuzarinshi, ya na son Sadiya so irin wanda ba ya yi ma Badiyya sam, shi manufar alkhairice ta sa ya ba Badiyya jariri, bai jin zai iya kyautar zobe, kamar yanda ya ke jin in duniya zata taru a kan shi bazai iya sakin Sadiya ba. Cikin dashasshiyar murya ya ce ma Innah.”

“Ki yi hak’uri dai Innah, babu kyau kyautar zobe, ba dai_dai bane in yi ma Badiyya ta lek’o ta koma ba. Kuma wallahi ina son Sadiya, ni bazan iya rabuwa da’ita ba.” Ya na kaiwa nan ya fice a d’akin, kan shi sai sarawa ya ke yi, idanuwanshi sun zama jawur da su, Anty Zulai ce ta zo wucewa da kwanon gashasshen nama, wanda aka bad’eshi da farin kwalli. Duban Safwan ta yi, tare da girgiza kai, har ta gota shi sai kuma ta juyo.

“Safwan ka kuwa shiga wajan Sadiya ka ga yanayin jikin nata kuwa? Jikin sai tsanani ya ke yi fa. Mamanta ya kumbura yayi him, ruwan da ya ke fitowa ma ya sauya kala, daga fari zuwa ja_ja. ” cikin rud’ewa ya juyo da mugun zafin naman da bai san ya na da shi ba.

“Ina ta ke Anty Zulai, bansan inda ta ke ba ai.”

“Ka biyoni wajanta zani.” Bin bayanta ya yi, har zuwa cikin d’akin.”

Sadiya

Ina kwance sai cije baki na ke yi, ji na ke tamkar mutuwata ce ta riske ni, a cikin azaba na ke sosai, kirjina kamar zai tsinke dan nauyi, mamana sun yi sutu sutu, sai digar wani ruwa mai kala su ke yi. Ba ko riga a jikina, sai tsumma da na d’aura a tudun cikina da bai gama sauka ba.

Amma ganin Safwan tsaye a tsakiyar d’akin ya sa a take na had’iye duk wani rad’ad’i da na ke ji.

Kwanciya na yi tare da juya mishi baya. Har ga Allah ba na son ganin Safwan sam_sam, sanin shi ma ina nadama.

Anty Zulai ta ajjiye kwanon gashsshen naman a gefen gadona.”

“Sadiya, sannu, na ga jikin sai tsananta ya ke yi, bari kirawa Yaya Jamila ta zo ta ga ni.” Ficewa ta yi a d’akin, hakan ya ba ma Safwan damar zama a bakin gadon da na ke, ya d’aura hannunshi a gefen wuyana, kau ya ji zafin jikina. Wuff na mik’e zaune, ina huci kamar wacce ta ci gudu. Wani rad’ad’ine ya shige ni sosai, sakamakon na fama Mamana.”

Kar ka sake k’azamin hannunka ya sa ke tab’a jikina. Ka fita a d’akinnan wallahi bana son ganinka, zan iya zaginka na rantse da Allah.” Cike da mamaki ya zuba mun idanuwanshi kawai, mamakina k’arara a shinfid’e a fuskarshi.”

“Sadiya ni ki ke fad’ama maganganu son ranki, akan wani dalili na ki can na sakarci?” Idanu na ware cike da tsiwar da bansan na iya ba.

Kaine sakarai amma ba dai ni ba. Kuskure na tabka ashe na zab’an tumin dare, ka bani mamaki da ka iya aure na dan kawai in haifama yara ka kwace ka dinga ba bagidajiyar matarka, ka sani sai Allah ya saka mun.

Kuka na raushe da shi, na d’aura da cewa.

Allah Sarki Aliyu, kaine ka nuna mun son da babu wanda zai iya min irinshi, kai ka soni da zuchiya guda, ka sadaukar da farin cikinka domun ka kasance da ni…

“Sadiya baki da hankali ko, a gabana ki ke kiran sunan mataccen tsohon mijinki ko?

Jikin Safwan har rawa ya ke yi, cikin tsawa ya mun wannan maganar idanunshi na kawo ruwa.”

Eh na fad’a, Aliyu sabo ne fil a zuchiyata, shi ya soma sanina mace, shiyasa ya fi ko wanne namiji sanin mutuna da darajata, na yi imani da shine bazai mun haka ba….

Tas na ji saukar mari a kuncina, wanda ya makanta mun ganina na wucin gadi, na ji mugun zafin marin. Kuka na saka tare da zama a kan gado jagwab, na fama mamana, nan su ka shiga sabon zugi, amma na ji dad’i na motso ma da Safwan kishi, na tabbatar ya na cikin cunkushewar zuchiya.

Da wata murya mai rawa ya ce mun.

“Bansan baki da kunya ba sai yau ai, Jariri kuma na kyautar da shi ki yi duk abunda za ki yi. D’anane ni ke da iko akan kan shi. Ki kula da irin furucin da zai dinga fitowa  a bakin ki dan bazan d’auki rashin kunya ba.”  Innah ce ta shigo d’akin, ina ganinta na ce.”

Ni ka mara Safwan, ga mari ga tsinka jaka?” Innah tai saurin matsowa in da na ke, fuskata ta d’ago, shatin hannun Safwan ta ga ni kwance a kuncina. A zafafe ta d’ago ta zabga mishi mari, hawayene ya gangaro a idanun da ya ke kuncin da Innah ta mare shi. Wani abu ya had’iye k’ut, ya na jin zuchiyar shi na tafasa. Cikin rawar murya da jiki ya ce.”

“Ta taso mu je Asibiti.”

“Ba zata taso ba, ka je abunka. Ko mutuwa Sadiya za ta yi ina ruwanka? Dubi jikinta yanda yai zafi, ga mamanta na ciwo, ga gyanbon da zuchiyarta ta samu sanadin zaluncinka, amma a hakan ka d’aga hannu ka doketa, sabida zalunci da son kai na maza.” Dubana ya yi idanunshi tamkar garwashi, ya kad’a kai. Wani zazzab’ine na kishi ke saukar mishi.

“Sadiya saka hijabi mu je asibiti kinji?”

Ban yi mata musu ba, dan jikina har rawa ya ke yi tsabar azabar da mamana su ke yi mun.

Hijabi na saka kawai, ta rik’e hannuna mu ka fita.

Yana biye da mu har Asibiti. Rannan na shi a mugun b’ace.

Gado aka ba ni, sauran abun da ya kamata a yi Safwan duk ya yi shi.

Ya na gefe na a zaune ya na mun sannu, wata nose na matse mun ruwan mamana, ni bana ma cikin haiyacina sam.

Tuni Safwan ya dena fishi da ni ya shiga yi mun sannu cikin tausayawa. Sannun Innah kawai na ke amsawa.

Magunguna aka ba ni da allurai, da yamma a ka sallame ni.

Mu na zuwa gida na tarad Goggo Hansatu ta zo. Duk hankalin Safwan ya bi ya tashi ainun.

“Sadiya ni na zo banga jaririn ma da ki ka haifa ba, ciwon nonon nan ya sa na sha’afa.”

Cikin juyayin me zan ce ma Goggo Hansatu na ke, ina ganin kamar za mu daidaita da Safwan ya mai do mun da d’ana. Dabara ta fad’o mun na ce mata.”

“Sabida maman nawa ya gurb’ace ga ciwo kuma, shine Badiyya ta taimaka mun da shayar da Jaririn, mu je ki ganshi ya na wajanta.” Duk wannan maganganun da na ke yi cikin dariyar yak’e nake yi.

Idanu Goggo Hansatu ta zuba mun kawai ta yi murmushi.

“Sadiya ta yaro kyau ta ke yi ba ta k’arko. Ni uwarki ce, bazaki tab’a ninkeni bai_bai ba. Ki sanar da ni kawai me ke faruwa?”

Safwan

“Innah ki dena maganar saki dan Allah ni fa ina son matata gaskiya.”

“Sai in tsine maka wallahi akan Sadiya. Ka rubuta mata takaddarta yanzu kafin ka bar d’akinnan, ka je can ka zauna da matarka Badiyya wacce ta nifi daraja, da k’arfin fad’a ka ji. In ka yi wata magana anan falon Allah ya isa nonona da ka sha, ka rubuta mata takaddarta.”

Safwan gigicewa ya yi sai ambaton Allah kawai ya ke yi, yanason yai ma Innah magana, amma ta riga da ta d’aure shi da jijiyoyin jikinshi, ta kafa mai dokar da ko hauka ya ke yi bai isa ya tsallake ba.”

_”Ni Safwan na saki matata Sadiya saki d’aya.”_

Abunda ya rubuta a takaddar kenan mai kunshe da rubutu rabin layi. Sai sa hannu daga k’asa.”

A gaban Innah ya ajjiye takaddar ya fita fuuuu, Turakar shi ya shige ya kulle k’ofar shi. Yana tunanin fuskar Sadiya, tare da auna sonta a sikelilin zuchiyarshi, tana da babban keji mai girma a rayuwarshi. Ta ya zai ko yi rayuwa kuma ba tare da Sadiya ba, sannan ya zai yi da nauyin sonta. Cikin dakiyar zuchiya ya busar da iskar bakin shi, tare da zama a bakin gadonshi.”

“Itama ba sona ta ke yi ba. Tunda da Aure na a kanta ta na beken mijinta na da matacce ma.” K’ut ya had’ye wani curi mai zafi daga mak’ogorinshi zuwa cikin shi. Gani ya ke yi abun kamar almara, wai shine ya saki Sadiya yau, da hannunshi ya rubuta takaddar sakin nata”

kwanciya ya yi a kan gado tare da lumshe idanunshi. Zazzab’ine ya saukar mishi bai mugun zafi, take ya soma jin d’ari. Bargo ya jawo ya lullub’a, hak’oranshi sai kakkarwa su ke yi.”

Sadiya

Da hawaye shab’e_shab’e a kumatuka na kamar wata k’aramar yarinya, na ba Goggo Hansatu labarin abunda ke faruwa.”

“Hmmm Sadiya rayuwarki cike da ke da k’addarori masu girma da tayar da hankali. Amma shawarata a gareki shine in za ki iya zaman hak’uri da Safwan toh, in kuma ba zaki iya ba, sai ki sanar da shi ya sauwak’e miki.

Amma gaskiya abunda ya aikata zalunci ne, kuma zan fad’a miki gaskiya ba sonki ya ke yi ba. Bazan so in ganki a cikin damuwa ba, kuma bazan saki a cikin damuwa da kaina ba. Amma ki san meye matsayinki taka mai_mai a wajan Safwan mata, ko Baby Mama? Domun duk wanda zai kalli wannan lamarin dole kan shi ya d’aure sosai.” Ni dai kuka kawai na ke yi, kuma na fi gamsuwa da Baby mama Safwan ya d’auke ni, ba sona ya ke yi ba tun farko.”

Innah ce tai sallama tare da shigowa hannunta rik’e da takaddar da ganinta ya fad’armun da gaba, jiki a mace ta ce.”

“Hansatu, ke da Sadiya ku yi hak’uri da abunda na zo muku da shi, a nawa ganin hakan shine maslaha. Wannan takaddar sakin Sadiya ce, da na tursasa Safwan ya sake ta, bisa sharad’in in bai sake ta ba, saina tsine mishi. Ga takadda ya rubuta. Hansatu inaso Sadiya tai nisa sosai, ta yanda Safwan ba zai ganta ba sai nan da wasu shekaru, inaso ya san mahimmancin Sadiya a rayuwarshine, inaso ya san amfaninta, ya kuma reni sonta, yayi begenta, har da damuwar rashinta kusa da shi.”

Sadiya ki yi hak’uri inason in kwatar miki ‘yancinki ne a wajan Safwan.”

Mrs Bukhari ce

MRS BUKHARI

79/80

KATSINA/JIBIYA:

(Asalin Jibia ya samo asaline tun lokacin yaƙin cin nasara da Sarakunan Katsinq su ka yi, inda su ka yi hijirar maraɗi da Katsina kan yanki da addini, musamman bayan jihadin Usman Bin Fodiyo)

Gari  ne mai cuɗanyar ƙabulu, Fulani da buzayen da yunwa ke fito da su daga Niger, da ma hausawa mazauna wajan. A garin jibia babbar budar da ta raba Niger da Najeria take.

Da misalin ƙarfe shida na yamma mu ka shiga cikin garin jibiya, sau uku na taɓa biyo Mama mu ka tawo ziyarar danginta da su ka kasance Fulani mazauna Jibia.

Da sallama mu ka shiga Family House ɗin su Mama.

Gidan gandu ne tabkeken gaske mai ɗauke da sashe daban daban, Dangine masu matuƙar son zumunci da soyayyar  juna a tsakani.

Jama’ar gidan sai murna su ke yi da ganinmu, a ɓarayin matan asalin mai gidan mu ka sauka, Kakan su Mama, shi ya haifi mahaifiyarsu. wanda ya jima da rasuwa, ya bar mata huɗu da tarin yara maza da mata wanda za su kai arba’in. Daga baya matan da ya bari duk suma su ka shuɗe. Yaran mazan gidan su ke riƙe da gida, suna zaune tare da iyalansu.

D’akin Kawu Shafi’i mu sauka, wanda ya kasance wa ga su Mama na huɗu. Matanshi uku, yara kuma yanzu ba na ce ga yawan su ba.

Da fara’a uwar gidan Kawu Shafi’i ta tarbemu, dawo ta kawo mana da ruwa.

Kafin ta dawo ta zauna.

“Hansatu saduwa ta yi wuya, zumunci sai ja baya ya ke yi, dama kawun naku kuwa ya ke magana akan zai tura Saminu ya bi kan dangi duk a harhad’o zuwa babbar sallah za’ayi taro kamar yanda ake gudanarwa a baya. Dan gudun sake taɓarɓarewar zumunci. Ina su Aisha, har yanzu Aisha ta na zaune ba aure ko? Ke ma Hansatu kin ƙi aure, shi fa rayuwar duniya ɗan haƙurine, gashi mu muna ta turawa, da daɗi ba daɗi ana ta tafiya, kafin mu tunkuyi ƙasa kuma. ” Hawayen da ya taru a gurbin idanunta ta sharce tace.

” wacece wannan kuma Hansatu?” kafin Goggo ta bata amsa, Kishiyoyin Goggo Kulu su ka shigo.

“Hansatu yau a gari in ji maƙi baƙo? In ji daya daga cikin matan da na ji Goggo Hansatu ta kirata da suna Goggo Fatima.

Nan aka shiga gaisuwa tare da hirarrakin yaushe gamo. Da ɗaya da ɗaya sai da matan gidan su ka cika falon Goggo Kulu tab, sai gaisuwar yaushe gamo su ke yi, ni dai da ido na ke bin kowa, domun wasu na gane su wasu kuma ban gane su ba sam.

“Hansatu amma za ki bar mun Sadiya da Haidar a nan ko? Domun a zaga da ita cikin dangi tasan lallai ita ƴar gatan dangi ce.” Goggo Hansatu ta ce.

“Ai Goggo Kulu zaman Sadiya ya dawo Jibiya ina fatan ta samu wani daga cikin dangi, ayi tuwona maina da shi, Allah ya kawo mutuwar aurenta, Mijinta na farko ɗan Asabe ta aura, Yar mahaifinta, sai Allah yai mashi rasuwa, sai kuma ta yi wani auren dai na rashin soyayya a Azare, kina ji ko Goggo Kulu? ” Goggo Kulu tace.

” Uhm ina jinki Hansatuwa.

“Yaronnan rimi rimi kamar abun arziki ya nuna ya na son yarinyar nan, ashe in faɗa miki shigo_shigo ba zurfi yai mata, ba sonta ya ke yi ba. Aure shekara guda bai cika ba. Auranta ya yi dan ta dinga haihuwar mishi yara, yana ƙwacewa yana ba uwar gidan shi. Kinganta nan yanzu haka jego take yi, kwananta uku da haihuwa, ya ƙwace Jaririn ya ba uwar gidan wai ta shayar da shi, gashi ita ciwon mama ya rabke ta. ” Goggo Kulu sai girgiza kai ta ke yi ta na faɗin” Ashsha” Sannan ta ce.

“Bayan duk wannan zalunci da yaima marainiyar yarinyar nan shine ya biyo ta da saki, yanzu Jaririn a Azare ku ka baro shi? ” Kuka ne ya ci ƙarfina, dan ba na ko ƙaunar in ji ana batun Jaririna, ni ƙaɗai na san halin da na ke sake faɗawa in aka yi maganar Safwan da Jaririna. Ni dai bazan yafe cutarwar da Safwan yai mun ba. Goggo Hansatu tace.

“gyatumarshi ita ta ƙarɓo ma Sadiya takaddarta, dan ta lura amfani da Sadiya kawai ɗanta zai yi. Tana so Safwan ɗin ya san mahimmancin Sadiya, da kuma iriyar asarar daya tabka wajan rabuwa da itan, har kuɗi ta ɗauko ta ba Sadiyan dan dai duk ta rage mata zafin zuchiyar da ɗanta ya haddasa mata. Na ga ƙoƙarinta kuma rabuwar auren shine maslaha, dan zaman ba zai sake yin kyau ba. ” Goggo Kulu ta dube ni tace.

” Sadiya ki dena kuka, rayuwarmu mu mata cike take da tarin ƙalubale da karakaina, abunda zan jaddada miki kuwa shine ki tsare mutumcinki da kimar ki, kinsan al’ummarmu su nai ma Zawara wani kallo wanda bai dace ba, amma in ki ka riƙe darajarki ta ƴa mace sai ki fi budurwar da bata taɓayin aure ba daraja. Ɗauki jakarki ku shiga ɗaki ke da Haidar, ƴar uwarki ta na wajan aiki, itama auren ya ƙare kusan shekara biyu kenan mace macen auren yai yawa, ki rasa ta ina ake samun ɓarakar, tunda za ki ga ko wanne ɓangaren da na shi irin laifin.

Da sallama ya shigo cikin ɗakin, cike da fara, a ya ce.

“Goggo aka ce mun kun zo, wallahi ni na zaci wasa ne. Zama yayi a ƙasa kusa da ƙafar Goggo.

“Ina wuni Goggo, ya hanya, ya kuma aka baro mutanen kano? Goggo cikin fara’a tace

“Iko sai Allah Sauban ka na duniya, kai dai sai in an zo Jibiya ake iya ganinka, sam baka sada zumunci. Goggo Kulu tace.

“Mutanen Katsina da dutsen ma, suma kullum ƙarafinsu akan shi su ke yi, baya son zumunci, ga shi yaƙi aure Hansatu, duk matar da aka kawo mishi sai ya ce bai so, an taɓa yin haka? Dan matarka Allah ya yi mata rasuwa, shikenan sai ba za ka ƙara aure ba. ” kai ya so sa, yace.

” Komai lokacine Iya da zaran lokacin yayi za’ayine. Akwai wata yarinya da na soma ne ma, amma ba mu gama daidaita kan mu bane tukunna. Goggo Hansatu tace.

“Ai ya kamata ayi a gama komai, kaiba yaro ba, ka doshi shekaru hamsin fa. Goggo Kulu tace.

“Hamsin ɗin zai cika zuwa jibinnan fa. Ka shiga ciki ƴar uwarka na ciki, Sadiya yarinyar Babarku Aisha. Baki ya washe yace.

“Allah sarki da’ita aka zo kenan? An soma kiran sallah bari in na fito masallaci zan zo mu yi hirar zumunci. Baba ma ya dawo, ya na ƙofar gida. “

A tsanake ya fita a cikin ɗakin, mu ma muka shiga yin alwala dan gabatar da sallar magriba.

Abinci kuwa haka a kai ta shigo da shi, har daga maƙota, k’auye akwaisu da karamci da girmama baƙo. Sai da na yi sallar isha sannan na fito falon inda na jiyo muryar Kawu Shafi’u suna ta hira da Goggo Hansatu. Tsugunnawa na yi a gefe na gaishe shi kaina a sunkuye. Cikin kulawa da washe baki mu ka gaisa, Haidar kuma ya je ya ɗale ƙafarshi kamar ya san shi.

“Sadiya na ji duk abinda ya faru, Hansatu ta yi mun bayanin komai, ki yi haƙuri ki kuma cire damuwa a ranki, ki shinfiɗa sabuwar rayuwa, gobe Sauban zai kai ki asibiti a sake duba lafiyar mamanki da ya ke yi miki ciwo, in kika samu lafiya kuma, saina nemo miki aiki, me kika karanta a kiwon lafiyan? Kaina na sunne nace.

Ɓangaren Anguwar zoma na karanta Baba.

“Toh babu damuwa akwai asibitin gwamnati zan nema miki gurbi, ƴar uwar ta ki ma Mai sunan kyatumarki Aisha, ita ma a asibitin take aiki, amma ita tana ɓangaren masu ba da kati ne. ” Da sallama ta shigo, da gani a gajiye take. Kawu ya ce.

” Kinga ƴar halak, Aisha kin dawo?” murnar ganimu ce ta hana ta amsa maganar Kawu, rungumeni ta yi, ta na dariya, sannan ta koma wajan Goggo ta rungumeta.

“Goggo kune a Jibiya da Sadiya? Ikon Allah, rabona da Sadiya ya jima sosai. Sauban ne ya shigo da sallama, ɗagowa na yi mu ka haɗa idanu, dariya na yi mishi, shima fuskarshi ƙunshe da murmushi yace.

“Sadiya idanunki kenan, kin maƙale a Kano abunki. Kunzo lafiya? “

Lafiya lau Yaya, mun same ku lafiya?

” Lafiya lau Sadiya, wannan baturen sojan na wajenki ne? ” murmushi kawai na yi, Goggo ce ta amsa mishi.

Aisha ta ce

” Sadiya ta so mu shiga daga ciki mu sha hirarmu. Sauban yace.

“Kaji ƴar son kai ko Baba, wai su shige daga ciki. Ina ta zauna mu yi hirarmu anan dukka.

Kawu dai sai dariya ya ke binmu da shi, ficewa ya yi abunshi, Goggo Kulu ta bishi zuwa turakar shi. Goggo Hansatu kuma ta shige cikin ɗakin da ya ke kallon inda na shiga ɗazu.

Nan hira ta ɓalle a tsakanimu, tare muka ci abinci a kwano ɗaya ma, mun jima muna hira kafin mu ka tafi kwanciya.

Ni da Aisha sabuwar hira mu ka ɓalle, har bacci yai awon gaba da ita. Ni kuwa sai juye juye kawai na ke yi, tunanin Jaririna wanda naima kallo ɗaya na ke ta faman yi, duk yanda na kai da son yakice tunanin amma ina abun ya ci tura. Sai da na yi kuka ma’ishina sannan na yi bacci?

Mrs Bukhari ce

MRS BUKHARI

81/82

Washe gari da safe, Aisha ce ta dinga zagaye da ni a cikin gidan, ɗaki ɗakin kawunan Mama manya da ƙanana, tare da iyalansu. Na ji zuchiyata ta yi mun sawai, kasancewar yanda dangin mahaifiyata su ke ta yin nan nan da ni, barin ba Yaya Sauban, da Yaya Saminu. Haidar ma ya samu gata a cikin dangina, dan babu wanda ya nuna mishi kyama a matsayinshi na zabiya. Kwanan Goggo Hansatu bakwai ta koma Kano. Goggo Kulu mata mai karamci, itace tsaye a kaina wajan ganin na gudanar da jego mai kyau da gata, Yaya Sauban kuma, kullum sai ya shigo mun da  balango mai ruwa ruwa na ci. Haka na ci gaba da jegona cikin kulawa, mamana tuni ya warke, watsi na yi da tunanin Safwan da Jaririna da ban ma san sunanshi ba yanzu.

Cikin kwanciyar hankali na ke sosai, bayan na kammala jego na tas, Kawu ya sa Yaya Sauban zagayawa da ni danginmu na dutsen ma da manunfashi.

Munyi ziraya mun dawo, Kawu ya naima mun gurbin aiki a asibitin gwamnati, mu na tafiya tare da Aisha.

A yanzu ba ni da wata matsala, aikina kawai na ba ma hankalina, sai Haidar da na ke ba shi dukkan wani kulawa.

Makarantar gwamnati ya ci gaba da zuwa kamar yanda sauran yaran gidan su ke zuwa. Sai Islamiyya mai kyau da na sanyashi. Yaya Sauban yana ta nuna mun so, amma ni na yi kamar ma bansan me ya ke nufi ba, har yanzu dai ya kasa sanar mun, bana fatan ya fallasamun sirrin zuchiyarshi sam, domun ba zai samu so daga gare ni ba. A haka rayuwa tai ta garawa har tsawon shekaru.

A cikin shekaru biyar abubbuwa da dama sun faru, na asarar rayuka, da kuma samun ƙaruwar haife haife, aure aure, da ma mace macen aure.

A halin yanzu Mama ta san halin da na ke ciki, ta na yawan kawo mana ziyara.

Haidar yanzu ya na karatu a makarantar gwamnati ta bai ɗaya ta Unity dake malumfashi. Yana ajin farko a sakandare.

A lokacin manaima sun yi mun mugun ca, manya mutane masu ji da mulki da kuɗi, amma ni fur na kasa sakin jikima da su.

Shekaruna sun ja, kasancewata ƴar boko da gaye kuma, baza ka ce na manyanta ba, fatata ta sake wani murjewa da gogewa, na zama babbar mace sosai, kullum a cikin gyaran jiki da gashi na ke.

Mama na kwance ta na wata iriyar jinya mai tsananin gaske, haka dole na baro Jibiya na dawo Kano jinyar Mama, anan Goggo Hansatu ta ke sanar mun irin ɗawainiyoyin da Safwan ya dinga yi da Mama, da duba ta da ya ke zuwa yi a kai a kai, Innah ma ta yi ƙoƙari wajan yin zumunci da dangina.

Goggo da ma Safwan ya na zuwa, shine ba ku taɓa sanar da ni ba? ” Goggo ta ce.

” Sadiya ho, mu sabida gudun fama miki ne yasa ba wanda ya sake yi miki zancan Safwan, amma har matar shi tana zuwa kawo ziyara danginki, da yaronsu Adam ɗan gayu. Da mamaki na ce.

“Haihuwa Badiyyan ta yi ne? ” Goggo ta ce.

” Jaririnki dai da Safwan ya ƙwace ya bata, baki ga son da take yi ma yaron ba wallahi, yaro ɗan gata gaba da baya. Yanzu haka ba dan sabida yana jigilar kai Innarshi Asibiti ba lafiya itama, amma da yau juma’a za ki gansu sun zo a motarsu, tare da kayan tsaraba iri iri, Sadiya ya kamata ki yafe ma Safwan, sai daga baya ya soma bani tausayi, domun a halin yanzu Safwan ya na buƙatarki a cikin rayuwarshi, kuma ya gane mahimmancinki kamar yanda mahaifiyarshi ta so. Kuma ya ba yaronki Adam duk wani gata da kulawa, ita kanta Badiyyan ta yi matuƙar ƙoƙari gaskiya.

Ni dai na kasa cewa komai, zuchiyata ce tai wani irin duhu da na tuno Jaririna wanda bai san wacece ni ba, Ashe sunan Babane da shi. Safwan na shiga tunowa da irin rayuwar da mu ka yi a baya.

Ɗaki na shiga, nan na shiga zurfin tunani, ni kaina ina da nawa laifin da na kasa rungumar ƙaddarata, kuma banso Innah ta sa Safwan ya sake ni ba, naso dai a dawo mun da Jaririnane kawai. Haƙiƙa, abunda haƙuri bai baka ba rashin shi bazai baka ba, ko ba komai da zan rayu da ɗana, ina kallonshi ina jin sanyi, amma haka na tsallake na barshi a tsunman goyo, da na zauna ko babu komai kullum da zan ganshi, tunda ba gida daban daban muke ba.

Zuchiya kenan mai ingiza mutum a cikin kogin aikin dana sani, kaita nutson da baka da wata madafa balle ka dafa ka fito, daga ƙarshe ciwon zuchiya ko hawan jini yai sanadinka.

Take hankalina ya karkata wajan Safwan da ɗana, tare da kwaɗayin son ganinsu ko da sau ɗaya ne, dan yanzu kam nasan na yi ma Safwan tsufa. A haka na kwana cur a cikin tunani, har zuwa washe gari da na tashi sukuku, ina ta so Goggo Hansatu ta sake yi mun zancan Safwan, ko zan samu damar jin labarin Jaririna, amma Goggo bata sake yi mun ba sam.

Wata ranar asabar, ina tsakar gida, ina wanke kayan Mama, kamar daga sama na jiyo sallama da zazzaƙar muryar da bazata taɓa gogewa a kaina ba, ƙamshin turerenshi na asali ya kaima hancina ziyara, ƙwabƙwab na jiyo takun takalman shi sau ciki, a hankali na saki wankin da na ke, na ɗago kaina, daidai Safwan yana leƙen fuskata dan son tabbatar da wacece ɗin a zahiri, wani irin nunfashi ya zuƙa tare da kafe ni da dattijan idanunshi masu burge wanda ake kallo. Safwan ya zama babban mutum, girma ya kamashi, ya zama wani irin wayayyen ɗan gaye, mai cike da haiba da kamala irinta dattijan asali, har wani haske ya kuma yi, ga key ɗin mota yana reto a  yatsan hannunshi. Shima idanu ya kafa mini tamkar zai cinyeni, sai ajjiyar zuchiya ya ke ta saukewa a jere, sai dai fuskarshi a tamke babu walwala, hakanne ya kashe mun jiki sosai. Sallamar Badiyya, da wani kyakkyawan yaro ne ya dawo dani daga kallon Safwan da na ke yi, basarwa na yi, har ina wani yamutse fuska. Duban Badiyya na yi, wacce ta yi kyau farinta da kyanta ya kuma fitowa, tana sanye da tsadaddun kaya na mutunci, hannunta riƙe da Adam, wanda shima kallo guda na yi mishi na watsar, wankina na ci gaba dayi, amma a baɗini, zuchiyata sai tsalle ta ke yi, a ƙoƙarinta na son tona mun asirin tsohon son Safwan daya tashi a zuchiyata, wani kishinshi ne ya tokari zuchiyata, a yanzu na gane kuskuren barin Safwan da na yi tsawon shekaru.

“Sadiya, Maman ta na ciki kuwa?. Safwan ne yai magana da dattijuwar muryarshi. ” kafin in ce wani abun, Goggo Hansatu ta fito, ganinsu Safwan yasa ta shiga washe baki, tare da tsokanar Adam.

” Ga mai gidana oyoyo, kazo duba matar taka ko? ” Shigewa ciki Safwan yayi kamar gidansu, Badiyya kuma a ɗarare tace.

” Sadiya barka da zuwa mutanen jibia, kwana da yawa” Banko ɗago na dubeta ba nace

Yauwa barkan ku da zuwa” Daga haka na tsame hannuna a wankin na shige daki, Badiyya kuma ta shige ɗakin Mama. ” Kuka na rushe da shi a tsakiyar ɗakina, ciwon son Safwan na taɓa duk wani rassa na jikina, son kasancewa da Yarona ya shigeni, yaron farat ɗaya ya shiga raina, abunka da Ɗa da Uwa. Zama na yi a bakin gadona, na dafe kaina kawai, na rasa shin wanne irin tunani ya dace ace na yi ne ma, dan na shiga wani irin damuwa ainun, ga Safwan ko a fuska bai nuna ya damu da ganina ba, ko fara’a ya kasa. Kiran da Goggo ta shiga kwaɗamun ne ya dawo da ni daga tunanin da na ke, labulen ɗakin nawa ta yaye, sannan ta shigo, zama ta yi a kusa da ni.

“Sadiya, ki saki jikinki da Safwan, har yanzu yana sonki, baki ga wata fara’a da ya ke ta yi ba. In ya buƙaci yana son magana da ke, karki musa, ki je ki saurareshi, in bai nema ba ki riƙe kanki karki bari ya gane kin damu da shi, tashi kije ku gaisa, kar matarshi ta ga kamar kishi kike yi. ” Bance komai ba, na miƙe na bi bayanta zuwa ɗakin Mama.

Da idanu ya bini harna nemi waje na zauna, kallon Adam na yi na ce.

” Zo ubana taho” Bai yi musu ba ya taso daga cinyar Safwan zuwa tawa cinyar, lumshe idanu na yi ina jin son yarona na daɗa shigata, a halin yanzu ji na ke yi mai raba ni da ɗana sai dai Allah.

Safwan ina yini, ya bayan rabuwa, ina su Innah da su Anty Jamila da Anty Zulai? ” murmushi ya sakarmun mai birgewa yace.

” Lafiya lau Sadiya, ina Haidar ɗina ya girma ko, yanzu ajinshi nawa? ” na nisa nace

Ajin farko a sakandare, yana malunfashi makarantar kwana, gobe ma zan je in dawo dashi za su yi hutu.” Kai ya girgiza yace.

“Na yi kewar Haidar sosai, goben zan zo sai mu je tare mu dawo da shi, sai mu je da Adam, shima ya miki hutu tunda kina nan. Satar kallon Badiyya nayi ko zan ga sauyin fuskarta. Amma ina sai murmushinta data sake fad’ad’awa” Na ji daɗi sosai da zai bar mun Adam yai mun hutu a wajena, gashi hutune mai dogon zango na karshen shekara. Badiyya tace

” Ina yini Sadiya, ya jikin Mama kuma? ” Daurewa na yi na dubeta ina jin kishinta na taso mun nace.

” Lafiya lau Badiyya ya gidan, sannu da ƙoƙarin raino fa an gode, Adam ya girma. ” murmushi kawai ta yi mun, abinci da ruwa aka kawo musu, ni kuma na ja Adam zuwa ɗakina, sai hira ya ke yi mun, Adam yarone mai ɗan karen surutu da kuma saurin sabo, Nima jiki na sake da shi inata biye ma surutan shi, ina ta dariya. Sai da yamma lis su ka fito, fitowa na yi cikin kwalliya da ƙamshi, kwalliyar da na tabbatar zata tafi da hankalin Safwan dan nasan abunda ya ke so. Bina da ido kawai ya ke ta yi.

Da Adam ɗin za ku tafi, sai goben ku dawo ko zaku barshi anan ne? “Safwan ya ce, zai zauna anan, ai dole a garin Kano za mu kwana, Zanje in kai Badiyya gidan ƙawarta ne, acan zata kwana, ni kuma zan kwana a zangon baƙi, da daddare zan zo sai mu tsara yanda za mu yi tafiyar.” Cikin kashe murya na ce da shi.

Toh babu damuwa, sai ka dawo, Badiyya sai anjima. Sallama mu ka yi su ka fice, Safwan ya waigo ya sake dubana ya sakarmun tattausan murmushi, bai dai ce mun komai ba.

Adam kuwa ya saki jiki sosai, dama ya saba da ganin su Mama, duk inda ya wulga da ido nake kallonshi kawai. Bayan sallar isha, Goggo Hansatu tace.

“Sadiya ki tashi ki je ki sabunta wanka, ƙila Safwan ya na hanyar zuwa, wannan damace kika samu, ki tabbatar kun sasanta kan ku a kan hanyar tafiyarku, tunda kun samu keɓewa. Nace.

“Mu da za mu bi motar haya Goggo wani hirane? ” sororo Goggo ta dube ni tace.

” Motar Haya kuma? Ai Safwan ya jima da siyan mota, aikin kamfani ya ke yi fa, kuma ya samu ƙarin girma, a Azaren ma ba a family House yanzu su ke da zama ba. ” Kai na jijjiga kawai, na wuce wanka. Abun mamaki nafi minti talatin a bakin madubi ina kwalliya, in shafa wancan in lakata wannan, sai tashin ƙamshi na ke yi. Fakistan ne a jikina riga da wando, mai kalar jinin kare, rigar ta shige guiwata sosai, sai burgujejen wandon daya ɗan leƙo ta ƙasa, adone a jikin kayan faca faca, gyalen kayan na yafa, ina sake fesa turare na jiyo maganar Safwan da Goggo. Murmushi na saki, zuchiyata na mun wani irin daɗi, wanda nake ta mamakin tsintar kaina a ciki da na yi. ji nake yi tamkar an sabunta xuchiyata ne, salon son Safwan daya motsa mun, ya yi mun sak da irin soyayyar da sabuwar zuchiyar da babu kowa acikinta ta shiga.

MRS BUKHARI CE

83/84

Tabarma Goggo ta shinfid’a mishi a tsakar gida. Nafi minti goma sha biyar ban fito ba, sabida jan aji irin namu na mata, amma zuchiyata a cike take tab da son kasancewa da shi, in ji d’uminshi a gefena, tare da tattausan k’amshin turarenshi na Tony Mantana.

A yangance na fito da kofin silver d’auke da ruwan sanyi, a gabanshi na ajjiye kofin sannan na nemi waje a gefenshi na zauna.

Idanu kawai ya ke bina da shi, ni kuma sai wani basarwa na ke yi, harda cin maganin.

“Sadiya, ganinki ya yi mun wuya sosai, tsawon shekaru baki sake waiwayar kowa ba.” Dubanshi na yi, cikin had’e fuska nace.”

Tunda kana zuwa nasan ba zaka kasa samun labarin ina Jibiya ba, tunda har Gimbiya Badiyya mai sarautar birnin xuchiyarka ta san garin da nike. Ni kake nufin in waiwayeka? Ai in kaga an waiwayi baya toh gaba ba ta yi kyau bane, me zan waiwaya dan kuma wa zan waiwayo?.” Murmushi ya yi mun yana wani kashe ni da kallo da mayun idanunshi, ni kuwa fur na k’i yarda mu had’a idanu, dan gudun kar asirin son shi da nake dannewa ya tonu.”

“Ba abunda na ke nufi ba kenan, da nace baki waiwaye mu ba. Na zaci za ki dinga waiwayar Adam, kina duba lafiyarshi.

A matsayina ta wa a wajanshi, yaron da ba’aso yasan wacece asalin mahaifiyarshi, sai Badiyya, in ina yawan zuwa ai da kun jima da koroni, ni da ka nuna ma baka buk’atar in shayar da gudan jinina. K’ila ko tarbiyyata ce bataima ba shiyasa ka kwace d’a a hannuna ba tare da ka yi tunanin komai ba,  kaba matar da ba ta san zafin haihuwarshi ba.” Rai na ga ya had’e, ni kaina saida maganar ta fito daga bakina na gane ban kyauta ba, domun nima ba ni naba kaina haihuwa ba, sai sai ina cikin b’acin rai da zafin zuchiya ne, ni kad’ai nasan irin azabtuwar da xuchiyata take yi.”

“Abun naki har ya kai ki yi ma Matata gorin haihuwa a gaban idanuna Sadiya, bakiji nauyi na ba? Amma baki kyauta ba” Cikin dakiyar zuchiyar da take son wanke kanta nace.

“Ni ya dace aji kunya, ni da ka raba ni da gudan jinina tun yana tsunman goyo, ka zuba sona a faranti ka d’agama duniya shi, a matsayin bora, ka nuna mun daka dawo mun da d’ana gara ka rabu dani.” Hawayene su ka silalo mun a kumatuna. Nan take ya wani rikirkice mun, hankici ya ciro a aljihunshi ya bani, karb’a na yi ina goge hawayena.

“Sadiya, ina sonki son da ya fi na Badiyya wallahi bazan yi miki k’arya dan kiji dad’i ba. Badiyya uwar gidana ce, ina kuma girmamata domun ta aure ni tun bani da aikin komai, tasha wuya da ni, kuma likitoci sun tabbatarmun ba zata tab’a haihuwaba, tausayinta ne yasa na yi mata kyautar Adam. Kuma ta na yi mishi rik’on da ko ke ba lalle ki yi mishi ba, ta na yi mishi son da bazai misaltuba, ko ni da na kasance Uba ga Adam, kuma wanda ya jima bai haihu ba, Ba na yi ma Adam irin son da take yi mishi, yaci a yabeta Sadiya. Kuma ta rik’e danginki tana zumunci da su, Amma tsantsar so ke na ke yi ma. Ko kinsan halin da na shiga a sakamakon rashinki kuwa? Ita kanta Badiyya ta yarda na fi sonki fiye da ita, kuma ta rungumi hakan a matsayin k’addararta, babu irin kuka da tashin hankalin da bata shiga ba. Babu yanda za’ayi dama son da na ke muku ya zama daidai, amma dai_dai da rana d’aya Badiyya bata tab’a canja mun ba.” Shiru na yi ina saurarenshi, domun ni kaina na san Badiyya jaruma ce, kuma a zaman da na yi da ita bata tab’a canja mun fuska ba a matsayina na kishiyarta ba, ta rungumeni tamkar yaya da k’anwa, in ban yabe ta ba, ba na kushe ta ba, babu irin hidimar da ba tai mun ba a lokacin da na ke da juna biyu, babu irin abunda bata shanye ba, domun har rabon kwana denawa aka yi, tana ji tana gani dole ta sallamamun Safwan. A gaskiya juriyar da Badiyya ta yi a zamantakewarmu bazan ma iya irinshi ba sam, har mamaki take bani in ta yi wani abun, kuma wallahi da zuchiya d’aya take yi. Na yi imani da Badiyya ce ta haihu Safwan ya bani jaririn, ba za ta tanka ba, ko da kuwa ranta bai so ba. Kawaici da karamcinta ya cika, a hakan ta ci gaba da bin dangina tana zumunci da su. A take kunya duk ta lullub’eni, a baya duk wannan tunane_tunanen ba su zo mun ba sam. Ni kawai abunda na d’auka an zalunceni kawai. Na yarda Badiyya ta fi ni son  Safwan nesa ba kusa ba.”

“Baki ce komai ba Sadiya, baki yarda da ni ba ko? wallahil azim nafi sonki fiye da Badiyya. Badiyya da zan aureki ita taimun kayan lefenki kab, zinarenta na gado ta siyar ta yi wannan bajintar.Ni dai na ma rasa me zance mishi, gaskiya na tabka abun kunya gaskiya.

Na yarda da kai Safwan, sai mu yafi juna duka itama Badiyya ka bata hak’uri.” Ajjiyar zuchiya ya sauke, ni kaina ji na ke yi tamkar an sauke mini wani nannauyan dutse a k’irjina.

Nan kuma hirar soyayya ta b’alle kowa na fallasama d’an uwanshi halin da ya shiga a sakamakon rashin juna. A daren Safwan ji ya yi tamkar ya kwana yana hira da ni, nima a nawa b’angaren hakan na ke ji. Da k’yar muka yi sallama da juna. Sawai na ke jin zuchiyata a daren.

D’akin Mama na shiga, ta samu bacci Goggo Hansatu na samu a zaune ta na kallon labarai a tashar NTA.

“Ah ya tafi ne? A kunyace na ce mata

Eh ya tafi”

“In ce dai kun sasanta kan ku tunda ku ba yara bane kuma ba sabuwar soyayya bace?” Cikin kunya na ce mata

Eh mun sasanta, duk rashin hak’uri ya haifar da komai, da kuma kasa bashi dama da na yi in saurari jawabin da zai mun. Amma a yanxu ni da kaina na bar ma Badiyya Adam. Kuma bana so har abada yasan ba ita ta haifeshi ba.” Goggo Hansatu tace.

“Gaskiya ne Sadiya kinyi aikin hankali, dan Badiyya ta yi k’ok’ari ainun, mahaifiyarki za ta ji dad’in labarinnan, amman ni ina ganin, daga Malunfashi in kuka d’auko Haidar, Sadiya ku daure ki kai Haidar wajan dangin mahaifinshi. Kar ki biye musu duk tsiya sune gatanshi, kuma ko aure zai yi sune za su shige mishi gaba.” Kuka na soma yi ma Goggo ta na ta aikin lallashina.

washe gari

Da asuba na shirya kamar yanda mu ka yi da Safwan, cewar a masallacin unguwarmu zai yi sallar asuba. Ai kuwa hakan aka yi, ana idar da sallah sai ga shi, sallama mu kai ma su Mama, Safwan ya rungume Adam wanda bacci bai isheshi ba, mu ka d’auki hanya a motar Safwan k’irar civic.

Tafiya ce wacce ta kasance ta shiga tarihin rayuwata. Domun cikin shauk’in soyayya mu ke ta cin hanya. Ji na ke yi Safwan ya dawo fil a xuchiyata, ban sha wuya ba har muka isa malunfashi.

Cikin makarantar mu ka shiga, ga d’alibai sai fita suke yi da akwatunan kwano,.wasu a motar gida, wasu a motar haya, wasu kuma da k’afa suke fita zuwa titi dan tarar abun hawa, ba mamaki k’ila su ‘yan cikin garinne ko k’auyukan da suke makwabtaka.

Haidar na hango yana tafe a guje ashe harya hango mu. Hannayena na ware ina jiran isowarshi. Wuce ni yayi ya fad’a jikin Safwan, duk girman da Haidar yayi bai hana Safwan d’agashi ba, tare da jujjuyawa kamar yanda ya ke yi mishi a da.

Hawayene suka sintiri a kumatu na, ina jin k’aunar Safwan ta na hudani.”

Haidar ne ya rungumeni, yana share mun hawayen fuskata. K’ank’ameshi na yi a k’irjina ina rok’on Allah ya gafartama mahaifinshi.

Mota mu ka shige, tare da barin  harabar makarantar.

Jibiya mu ka nufa, nan na zazzaga da Safwan dangina. Kawu Shafi’e ne ya mayar da aurena da Safwan, a masallacin gidan, sai shigowa ya yi kawai ya mik’a mun sadakina. Yaya Sauban kuwa ya ji zafin rasani, amma yayi mun fatan alkhairi, tare da yi mun kyauta.

Kwanan mu biyu a Jibiya, mu ka wuce kai tsaye sai Raquma.

k’auyan Raquma ya na nan inda na baroshi, babu wani ci gaba daya shiga cikin k’auyan, yana nan a inda na san shi. Ina kan babur, ina tuno kyakkyawar rayuwar da na yi a cikin k’auyan ni da Aliyu, da irin abubbuwan da suka faru. A k’ofar gidansu Aliyu mu ka tsaya. Gidan ya kuma tsufa da ragwab’ewa sosai. Safwan a waje ya tsaya, ni kuma na rik’e hannun Haidar da Adam mu ka shiga cikin gidan da sallama.”

Tsakar gidan duk shara da tarkace, ko’ina ya kwarab’e. Ga wata mai mugun zafi data k’walle, k’irjina sai duka ya ke yi, ta maza na yi, nai ta kutsa kaina ina ta sallama, Amma sai na ji shiru, daidai k’ofar d’akin Goggo Asabe, sai ga Bilkisu matar Anas ta fito da kwano a hannunta. Duk ta tsofe ta wani yankwane, ga duhu data sake yi. Dubana ta yi ta kuma.

“Sadiya kece haka ki ka waiwayemu, baki yi fishi da mu ba, wannan Aliyu ne ya girma haka?

Ajere ta yi mun wannan tambayar, ni kuma murmushi na yi mata nace.

“Malama Bilkisu nice, Allah yayi na waiwayo ku, ga Haidar nan. Goggo fa suna ciki?

“Dukka suna ciki suna tattaunawa” Murmushi na yi mata nace.

“Ina Hasiya mutuniyar fad’ana?”

“Hmmmm rayuwa kenan, Hasiya ta rasu shekaru biyu kenan da su ka wuce, sakamakon..

Fitowar Kawu ne ya katse mata maganarta.

“Ahh Aliyu ne ya dawo bature haka? Sadiyana kice ki ka zo. Murmushi na yi cikin ladabi na ce

“Nice Kawu, tare ma da Baban Adam muke yana waje.”

“Shiga daga ciki iyayen naki na ciki, bari in sa Kabiru ya shigo dashi d’akin zaure ya hutu. Kun shawo hanya.”

Haidar dai sai gaishesu kawai ya ke yi bai san ko su waye ba.”

“Umma Inane nan? Naga kowa ya sanni ni ban san su ba.”

Hannunshi na rik’o nace.

“Gidan kakanninka ne nan, a tsakar gidannan mahaifinka yai rarrafe har da ma wasan k’asa. wannan daya wuce wan mahaifinane, kuma wan mahaifiyar Abbanka ne.” Hannunsu na ja muka shiga.

wani wari da zarni ne suka doki salansar hancina, cikin daurewa na kutsa kaina cikin k’uryar ‘dakin.

Goggo Asabe na gani a kwance, ga k’afarta ta kunbura ta yi him sosai, k’afar sai fitar da wani irin ruwa ta ke yi.

“Sadiya kece a tafe. Aliyu kaine?”

Jikina a mugun mace na isa gabansu ina hawaye.

Dukkansu sun yi mugun tsufan da na yi mamakin ganeni da suka yi. Muryata na rawa nace.

“Goggo Mariya, mai ya samu Goggo Asabe haka, ji k’afarta yanda ta koma?” Goggo Safiyya tace.

“Ke dai bari Sadiya Sankara ce ke damunta, anyi maganin anyi har mun gaji komai namu ya k’are tas, abinci ma da k’yar muke samu muci, duk akan ciwon Yaya, ga k’afa daga k’urji ya fito mata, shine fa wajan ya dinga rurewa. Munje asibiti suka yanko mana kud’i masu yawa har nera dubu ashirin wai zamu biya a yanke k’afar, in ba haka ba zai cinye mata duk jikinta. Toh wallahi a haka dai muka komo gida, watanmu biyu a asibiti mun kashe kud’i masu yawa. Na gargajiya dai yanxu muka mai da hankali kawai muke yi….

maganar Goggo Asabe ce ta katsemu, ta na kiran sunana da wata murya mai amo. Duban Haidar da Adam na yi nace.

“Haidar rik’e hannun k’aninka kuje wajan Abbanku a d’akin zauren da muka shigo gidan.”

Kai Goggo ta girgiza halamar kar su fita, hannayenta ta ke ta mik’o mana.

Ni da Haidar mu ka kama.

“Sadiya ki yafe mun na saki takaba da rasa miji. Aliyu ka yafe mun na saka maraici. Sadiya nina kashe Aliyu, wajan boka naje dan ya bani maganin da cikin ki zai zube, ya bani ni kuma na zuba miki a dawo. Aliyu kuma yasha ya mutu. Ciwon mazantaka da Aliyu yayi duk nice sila. Ku yafe mun ko haske zai lullub’e kabarina, a baya na fad’a ma Iya  a gabanki, amma ban rok’i gafararki ba Sadiya. Aisha ma ta yafe mun, ni kad’ai nasan mai nake ji. Tunda Aliyu ya mutu na rasa duk wata kwanciyar hankalin duniya, kullum a cikin mafarke mafarken na shiga wuta ko kabarina ya kama da wuta na ke yi, ga rad’ad’in ciwo wanda bazan iya kwatanta muku ba. Gadon Aliyu k’arami na had’a na handame ki rok’amun shi ya yafe mun”

Da sauri na zame hannuna na dinga kuka Haidar na lallashina. A haka Kawu Da Anas suka shigo su ka same mu, gafarata su ka dinga nema. Ni nama kasa magana fir. Sai Haidar ne ya ke ta tambayata su d’in su waye.

Ajjiyar zuchiya na sauke, na gabatar mishi da kowa, na kuma rok’eshi ya yafe musu. Nima na yafe musu dukka, Haidar ya so ya kafe mun kan cewar shi bazai yafe ba,amma da nai mai nasiha take sai ya yafe musu.

Amma kawu ya kamata a kai Goggo Asibiti aci gaba da kulawa da’ita acan.”

A kunyace Kawu yace.

“Sadiya na, ki bar Asabe kawai a gida ta mutu a suturce a d’akin mijinta. Iya ma Allah ya yi mata rasuwa da jimawa.”

Allah sarki rayuwa. D’akin Bilkisu aka kaini, matan gidan sai nan nan su ke yi damu baki d’aya.

Bilkisu ciwo Hasiya ta yi ne?

“O’o sata aka kamata ta na yi, hatsin da ake adanawa a cikin rumbu, shine take sacewa, tana kaiwa gidansu,ana siyar mata a birni. Da dubu ta cika Dauda da kanshi ya kamata, shine fa jama’ar k’auyannan su ka tasar mata da jifa, mata da k’ananun yara, da kyar ta sha. Sanadin da ta soma cutar ajali kenan, tace ga garinku nan.” Na tausaya mata sosai.

Toh ina khadija da mai dambu fa? Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.

“Bayan tafiyarki daga Raquma khadija ta auri wani hamshak’in mai arziki a Zamfara, tana zaune dashi cikin rufin asiri, ta yi kyau ta canja, sai ya mutu. yara biyu ta haifa dashi, sun samu dukiya mai yawa mai dambu ta dinga watayawa a gari, sai wani saurayi ya fito neman auren khadija, ya kuma ci nasara ta aureshi, ke daga k’arshe dai ciwon sida ce ta kasheta ita da mijinta na uku.  kuma ance a wajan mijinta me rasuwa ta kwaso, cutar da tai sanadinshi kenan”

Me dambu tana nan, amma bata da hankali sosai kwakwalwarta ta tab’u, dan wani sa’in  a waje sai ta shiga tub’e sutura ga tsufa a jikinta. Ciwon tashi ya ke yi. wasu na cewa asiri taje ayi mata sai abun ya dawo kanta.

Lallai duniya zancan banza, da d’aya da d’aya kowa ya girbe duk abunda ya shuka. Shi yasa a rayuwa ka shiga Alkhairi yafi.

mrs Bukharice

MRS BUKHARI CE

85/86

Washe gari muka wayi gari da mutuwar Goggo Asabe,mutuwar data girgiza ni matuk’a. k’auyan rak’uma duk ya d’auka.

Kafin rana gidan ya cika ya batse, k’ofar gidama haka.

Khadija ma ta xo Ta’aziyya anan muka had’u, yaranta biyar, ta zama babbar mace sosai.

Ranar sadakar uku muka baro garin Raquma. Muka dawo Kano.

Da rasuwar Mama na ci karo. Kwananta biyu da rasuwa ban sani ba.

Iya tashin hankali na shigeshi, amma duk wani mai rai mamacine, haka na dangana, ban tare ba har sai da Mama ta yi arba’in sannan na tare a gidana.

Zaman lafiyan da muka bud’e da soyayyar juna ba’a magana. Mak’ota har sama gidanmu suna su ka yi da GIDAN ZAMAN LAFIYA. Yarana uku yanzu, banda Adam, Na samu Aisha, da mai sunan Innar Safwan wacce bata jima da rasuwa ba itama.

shekaru da dama sun shud’e rayuwa sai tafiya ta ke yi, Haidar ya kammala karantu shi, ya zama malamin Addini, Adam kuma Likitan k’ashi ya zama, Aisha tana gama sakandare tayi aure, tana zaune da mijinta a Abuja, y’ar auta Ummi kuma tana kan yin karatune.

Gidan yau a hargitse yake sosai, domun dumu dumu mun shiga shirye shiryen bikin Haidar ne, wanda ya rage saura sati uku cib.

A zaune nake a falo ina danna salulata. Haidar ne ya shigo falon da Sallama, yana sanye cikin malum_malum wanda su ka kasance sune kayan shi, kasancewarshi na matashin malamin da ake ji dashi.

A gabana ya tsugunnan.”

“Hajiya barka da Safiya, an tashi lafiya?” Jigum na bishi da ido, tsantsar kamsnninshi da Aliyu sai yanzu ne ya sake fitowa, ina hango Aliyun a shekarun shi da bai haura na Haidar d’in ba.

Lafiya lau Haidar ya k’ok’ari? Jiya umman naka ta kawo mun akwati da ka yi mana, na ce har da mu? mu muna ta faman kici kicin mu kammala had’a maka laifen a samu akai, ashe kai a shirye kake. Toh madallah Allah yayi albarka.”

“Ameen ummi, dama Adam ne ya aike ni wajan Abba da kuma na je na samu Abban sai ya fatattakoni da maganar da na kawo mishi, ni je wajan ummanshi itama saita koroni.” Cikin mamaki nace.

Menene wannan sak’on da ake ta fatattakar ka da shi haka?” Kai Haidar ya sosa yace

“Dama cewa yayi in sanar ma Abba ya samu matan da ya ke so ya aura. Toh da na je ma Abba da zancan jin mata biyu a lokaci guda da Adam ke son yi shine ya koroni, itama umman nashi abunda yasa ta koroni kenan. Kuma ummi wallahi Adam ya na son ‘yan matan dukka, a daure a duba.” Ajjiyar zuchiya na sauke na ce.

“Kar ku ji komai, bari su fito zamu tattauna, yanxu ba sai anjima ba, yaro yazo da abu mai kyau sosai. Kila zaman mu da kyatumarshi ne ya bashi sha’awa harya kwad’aitu da mata biyu. Yanxun ina zaka je naga kaci ado. Gidan su mai sunan Mamana zaka je da safennan?”

“A’a ummi. Raquma zani, kuma zan yi sati guda, inaso in zama nine malamin da zai shiga Raquma a wannan shekarar, na tanadar musu abubbuwa da yawa da zai taimaka musu, kafin su samu d’auki daga gwamnati, kuma in sha Allah da kansu wata rana za su buk’aci a bud’e musu makarantar addini, ni kuma a shirye nake ko komawa ne inta kama sai in yi.”  Hawaye na sharce nace.

“Allah yai ma albarka.Ka fanshi mahaifinka domun ya rasu da tunanin k’auyan raquma.”

“Ummi ki dena kuka, komai na da sanadi, in sha Allah sanadiyyar wannan labarin, al’ummar da ke rayuwa a cikin k’auyan Raquma za su zamu tallaifi daga gwamnati, harma da fararen hular. Mutane da dama za su yi mamakin jama’ar da ke rayuwa a cikin raquma. Rayuwa ce suke gudanarwa abun tausayi. Babu makaranta ko d’aya a k’auyen boko da islamiyya, ba wuta, ba Asibiti, ba injinan nik’a. Rayuwa ta wahala rayuwa irin ta mutanen da can.”

Hawayen shi ya share dan tsananin tausayin al’ummar cikin Raquma, da yake tunani anya kuwa gwamnatin jihar sokoto ta san da zaman k’auyan raquma kuwa? kai da wuya.

Sallama ya yi mun ya fita. Bayan shi na bi da kallo kawai, na sauke ajjiyar zuchiya.

Ina zaune a wajan Badiyya ta shigo da sallama ta nemi waje ta zauna.

“Yau baki fita bane Hajiya Sadiya,ko ba aikin ne?”

Akwai aikin Hajiya Badi sai zuwa sha d’aya zan shiga Asibiti. Yanxu Haidar ya zo mun da wata magana.”

Rai ta had’e tace.

“Wato sai da Haidar ya kuma sanya kan shi a sabgar Adam ko? yaro in banda sakarci babu abunda ya ke yi, ko dan ya ga na damu da shine oho. Wai mata biyu zai aura a lokaci guda fa.”

Haba Hajiya Badi, menene abun sakarci anan wajan?” Alhaji Safwan ne ya tsoma bakinshi, fitowarshi kenan daga turakarshi. Ya sha kyau yana sanye cikin malum malum, dattijo d’an kwalisa kenan, ras yake iya jerawa da yaranshi, kuma ba wani tsufa ya yi sosai ba, sai  dai yayi furfura sosai.

“Sakarci mana, an fad’a mishi rik’e mata biyu na ragon namiji ne?”

Dariya ni ya bani ma.

Kana nufin kai jarumine kenan?”

“Sosai ma, wuyar da kika bani lokacin da kika tsallake kika tafi ta wasa ce, da ace matasine ya shiga halin da na shiga a lokacin, k’ila haukacewa zai yi.” Dariya mu ka sanya mu dukkanmu, waje ya samu ya zauna yace.

“Sadiya akwai wani abu da na aiwatar, ina fatan hakan bazai haifar da matsala ba, tunda dai nasan akwai fahimta a tsakaninmu. Ita Hajiya Badi na bud’ema shago, a kasuwa, shagon siyar da kayan masarufi, duba da yanda ita bata zuwa aikin komai, kuma ba ta yi wani karatuba, kullum sai dai mu fice mu barta a gida. Shine na bud’e mata shago, duk da ba ita zata dinga zama ba, yaro zan nema, amma kuma, zata dinga amfana da ribar da za’a samu, koba komai zata dinga juya taro ya koma sisi.”

Murmushi na yi na dubi agogon fatan hannuna, goma da rabi na dawo da dubana ga Safwan.”

Alhaji kenan, ai matsayin Hajiya Badi ya wuce yanda kai ka ke tunani, wallahi ko duk dukiyarka zaka mallaka mata bazai mun ciwo ba. Nima fa na tara kadarori, ina da gidaje biyu na zuba haya, ina da d’an shago na, ga Asibiti har yanzu ana lek’awa. Toh bak’in cikin me zan yi mata. Allah ya sanya alkhairi, Allah yasa a bud’e a sa’a.” Da Ameen su ka amsa, sannan tace.”

“Hajiya Sadiya, a gaskiya ke macece mai tausayi da k’arfin zuchiya, tunda har kika mallakamun d’anki meye ma ba zaki mallakamun ba, naso ace na yi ilimi mai zurfi domun shi ilimi gishirin zaman duniya ne, ko ba komai da na yi ma k’asata hidima. Amma tunda mai gida da abokiyar zama, dama yara sun yi sai dai in ce Alhamdullahi.

Safwan ma yace.

“Sadiya nagode, Allah ya yi muku albarka. Da ace haka magidanta suke samun walwala da farin ciki a tsakanin matan su, wallahi da ba gidan da zaka shiga kaga mace d’ayace ke rayuwa a ciki, da mata hurhud’u za’a dinga yi, domun a rage ma yawan matan da suke gararanba a gari, ga zawarawa da suka cika gari. Mu fa maza wallahi muna son mata a kusa da mu, fitintinu da rabe raben kawunan yara ke sanya da yawan maza su hak’ura da mace guda. Amma wallahi mata biyu, uku, hud’u sun fi dad’i. Da wannan nake ganin zan k’aro aure, sannan Adam na bashi dama yayi aurenshi, duk a had’e auran namu a d’aura rana guda.”

Mrs Bukhari ce.

MRS BUKHARI CE

87/88

“A haba wasa dai ko, tsofai tsofai da mu, za ai mana kishiya?” Cewar Hajiya Badi, ni kuma nace.

Ke ma dai kya fad’a Hajiya Badi, ina dai fatan ba yarinya zaka auro mana ba? Yanda nake da k’ibarnan zaune ta zanyi.”

Mik’ewa yayi yace.

“Taso mu je in sauke ki a wajan aiki, in wuce nima. Tashi na yi, mu kaima Hajiya Badi sallama muka fice.”

Wai director da gaske kake yi zaka sake aure, duk mu d’in bamu isheka ba?”

“Wasa na ke yi Sadiya, ke kad’aima ai bakya isata, kina gani kullum sai na yi mik’i sambatu, kullum yarinya kike dawowa.”

Haba dai, wane yarinya, nono da tuwon mazaunai duk sun yamushe, ciki duk nankarwa.”

Juyowa yayi ya dubeni yace.

“Ba yarana bane su ka mayar mun dake haka ba? Ai ba’a haka na auroki ba, ras kike, ni da yarana ne muka sukurkutaki, gashi yanzu kin zama ‘yar lukuta, jibi tumbinki fa yanata girma. Amma wallahi a hakan kike d’iban hankalina, sabida kece daidai dani Sadiya.”

Shiru nayi ina nazari gaskiya Safwan adaline, kuma masoyine masanin darajar mace. Duk yanda tsufa da lalacewar fata da gashi ta ruskemu, amma shi ganinmu yake yi tamkar ‘yan mata ‘yan bana, baya nuna gyama ko jin wani iri idan zai yi mu’amar aure damu, kullum a cikin yi mana santi yake a wajan kwanciya.

Har ya kawo Asibiti bance komai ba,

“Dr mun iso asibiti, na saki cikin tunani ko? Kinga”

“Soyayyar gaskiya ita bata tsufa, sai dai ma’abotanta su tsofe, ni a zuchiyata gadagau nake jinku Sadiya. Kome zaku zama ni kune taurarina, kije aikin ceton rai, ga wata mai ciki can an kawo ta.

Haka rayuwar taci gaba da garawa damu, kwanakin mu na ta k’ara tafiya, Haidar yayi aure har da yara biyu, Badiyya Da Sadiya, Adam kuma yaran shi uku, Safwan, Aliyu, da Adam, mai sunan shi. Tsufa ya saukar mana sosai, musamman ma ni, ga ciwon baya da na k’afa, kasancewar ni mai k’ibace, kullum Hajiya Badiyya a cikin taimaka mana take yi, da Safwan ma yana kwance ciwon suger, da ciwon tsufa ya kama shi, Su Haidar su ke jinyarshi. Dangina duk sun k’are, su Goggo Hansatu, dasu kawu, Sulaiman, da su Goggo Kulu, da mijinta Kawu Shafi’i. Duk sun shud’e.

Haka yau muka wayi gari da mutuwar Safwan, mutuwar data gigita iyalan gidan.

Gidan ya cika mak’il da ‘yan uwa da abokan arziki, Alhaji Safwan mutum ne na jama’a, yana d’aya daga cikin dattijan anguwa, wanda suka kafa kwamitin matasa,dan tallafama rayuwar matasa da aikin yi.

Rabuwa da masoyi babu Dadi, hak’ik’a mutuwar miji tana rad’ad’i da zafin da sai wanda akaima ne kad’ai zai fahimta.

Haka mu ka shiga takaba ni da Badiyya.

Ranar da Safwan yai arba’in aka raba gadonshi. Adam yaso ya d’auke mu, mu koma gidanshi, fur muka k’i amincewa, domun baya baya da zama da surukai yafi alkhairi. Ragamar rayuwarmu ta yi tsalle, daga kan Safwan, zuwa kan yaranmu, da sannu sannu har yayi tsalle ya koma kan jikokinmu. A lokacin bana iya gani sosai, tafiya kuwa sai da sanda bibbiyu. Rayuwa kenan, duniya budurwar wawa.

Yanzu ina diri da kyau da nake tak’amar ina dashi, duk babu ya tsud’e, fatata duk ta yamutse, gashin kaina ya kakkab’e tamkar wacce akaima aski, hatta gashin idanuna sai da tsofa ya k’one mun su tas. Rayuwa kenan.

Ina tsakar gida a zaune, ina d’an shan iska. Dattijon d’ana ya shigo da Sallama ya zube a gabana.

Duk tsufana da yank’wanewar da nayi, bai hana Haidar ya sa hannayenshi duka biyu ya tallafoni jikinshi ya mik’ar dani tsaye ba.”

“Ummina daure ki tattaka, kinji fa abunda likita yace miki.”

Badiyya ta fito, harta fini yamutsewa kasancewar ita fara ce sosai. tulin gashinta da take yanga dashi lokacin ‘yanmatanci, ya dawo fari fat babu kyan gani.

“Yauwa Alhaji Haidar, ka tattaka da ita, saita zagaye duka gidannan, Bata ji Sadiya sam.”

Turjewa nake ta yi, irinna rikitattun tsofaffi, da rarrashi Haidar ya dinga zagawa dani. Oh rayuwa, yaron dana haifa a cikina, wai yau shike ri’ke da hannuna ya na koyar dani tafiya, rayuwa rud’un banza, duniya zancan banza. Mutum ba a bakin komai yake ba.

Haka rayuwar taci gaba da tafiya, muna tsakankanin jikokin da k’adanne ma ba su yi aure sun haihu ba.

Haidar ya zama hamshak’in malami wanda ake ji dashi sosai, yanxu haka, d’anshi na jami’atul madina shima yana karatun addini.”

End

Alhamdullahi

Anan na kawo k’arshen wannan littafi mai suna GISHIRIN ZAMAN DUNIYA  labarin daya faru a gaske. Darasin dake cikin wannan labarin Allah ya bamu damar d’auka muyi aiki dashi. kura kuran dake ciki kuma Allah ya yafe mana baki d’aya.

Sai Allah ya sake sadamu a cikin sababbin littattafan Gawurtattu biyar 🤚🏻

Masoyana sai mun had’u a cikin littafina mai suna……

wanne irin darasi kika koya a cikin wannan littafin?

menene yafi burgeki?

Menene ya baki haushi?

A dunk’ule wanne sak’o littafinnan ya isar, a naki ganin?

duba da ya tab’o manya manyan jigo.

Amma wanne jigo ne yafi jan hankalinki, kuma ya k’ayatar dake?

Shin wanne irin maki zaki ba Badiyya da Sadiya a cikin zamantakewarsu?

Ita data mallaka mata d’a, ko ita data mallaka mata miji?

Nagode sai na ji sharhinku akan wannan littafin.

sannan duk mai son wannan littafin a buge, zan buga shi, saidai bazai shiga kasuwa ba, a hannuna kawai za’a samu, duk mai so sai ta yi magana a sa sunanta.

NASAN BA KOWA BA KOWA ZAN FARANTAMA RAI BA, AMMA INA BAMA KOWA HAK’URI, INA MAI KARA JADDADA MUKU TRUE LIFE STORY NE MASOYAN LITTAFINNAN INA GODIYA.

GISHIRIN ZAMAN DUNIYA PAID  GROUP INA ALFAHARI DA KU BANASO MU RABU HAR GA ALLAH 😭😭😭😭😭

Series Navigation<< Gishirin Zaman Duniya Chapter 5
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *