Gishrin Zaman Duniya Chapter

Gishirin Zaman Duniya Chapter 3

*Mrs Bukhari Ibrahim*

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

True life story

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

Kashi na 1

Babi na 5~6

A zaune na ke a bakin gadon Mama, a cikin ado da kwalliya na ke irinna amare. Material ne a jikina, d’inkin riga da siket, ja ne jikin material d’in, sai fulawowi da a ka yi ma material din  milk colour. Dan kunne da sarka  na sanya na azurfa harda awarwaro. K’afata sanye da takalmi me tsinin gaske milk colour. Light make up na yi ma kaina. Bak’a ce ni, amma ba can sosai ba, kuma baza a kira ni da wankan  tarwad’a ba. Ba doguwa  bace ni, gajerace ‘yar duma duma, domun ina da k’iba amma ba can ba, amma ba za’a kirani da siririya ba. k’irjina  a cike ya ke dam da dukiyar  Fulani tamkar za su tsago rigata su fito. Ina da tudun  mazaune sosai, sannan ina da fa’di, wato hip’s. Idanuna  manya ne kuma farare, sai dan hancina wanda bai yawanta  tsawo ba, baki na kuwa leben saman bak’i ne, sai leben kasan kuma mai haske ne, amma ba ja bane. Ba ni da gashi sosai, amma ina kama shi da ribbon sai dai babu wata jela mai yawa, amma ina da cikar gashi sosai, gashin kaina ba ba’ki bane sosai ya d’an sirka da ja ta sama saman gashin, kuma ba mai laushi bane sosai, kuma bana amfani da man k’one gashi. Girata ta na ga gashi sosai, gashin idanuna  basu da tsayi sosai amma a cike suke.  Mata da yawa suna sha’awar irin k’ira da surar  da Allah yai mun, musamman inna juya ina  muskuta mazaunaina. Ba ni da tsantsar kyau ta fuska amma diri  kam sai dai in ce Masha Allah. Ajjiyar zuchiya na sauke nan ta ke na shiga tunani mai zurfi. Hirar da ta wanzu a tsakanina  da Ahmad, a shekaran  jiya da daddare, bayan masu sanya ni a lalle sun sanya ni, na shiga tunanowa.

Zaune muke a cikin motar Ahmad k’irar Hala. Shagwab’a ya ke ta zuba mun cewar lailai  sai na raka  shi  dubiyar  mara lafiya abokinshi, a gidansu. Ni kuma na ce da shi.

Ahmad ba daidai bane mu fita tare, domun sai zuwa gobe ne za’a d’aura auranmu, ka d’an k’ara hak’uri ka’dan, zuwa jibi ina gidanka sai mu je mu duba shi. Idanu ya zuba mun ya na ma kirjina  wani irin mayun kallo, kasancewar doguwar rigar wani yadi  mai laushi na saka, kuma yadin  yana la’bewa a jiki. K’irjina  sun fito sosai ta cikin rigar, har shatin  bra d’ina ana gani. Gabaki d’aya sai na lura hakan ya firgitashi  sosai, da sigar lallashi ya ce.

“Haba Sadiya ashe ma baki yarda da ni ba har kika amince in zama mijinki gobe?” Da muryar soyayya na ce.

Haba Ahmad wallahi na yarda da kai. Ina kare  martaba  da darajar kaina ne, da ma gidanmu. Kamata ya yi ka ta ya ni. Ha’da idanun da na yi da Ahmad yasa gabana  ya fa’di sosai. Sha’awata  k’arara  na ke karantowa  a idanun Ahmad, sai dai na kasa fassara ma’anar  launin fuskarshi gabaki d’aya da ta canja. A cikin mak’oshi ya ambaci sunana.

“Sadiya” shid’ewa na yi, domun duk illahirin tsigogin da su ke jikina sai da su ka tashi. Ban yi aune ba, na ji hannun Ahmad a cikin nawa. Sai da numfashina  ya d’auke na wucin gadi. Da kyar na yi kokawar dawo dashi. Cikin sauri na fisge hannuna, na kuma ha’de rai na.

Meye hakan kuma Ahmad, sai da aski ya zo gaban goshi  za ka shigo da irin wannan lalatar?”  Da sauri na b’alle murfin motar. Wuf Ahmad ya sake rike mun hannuna. A fusace na juyo, kallon dana  watsa mai ne, ya sanya ba shiri ya saki hannuna. Ban ko yi waiwaye  ba na shige gida, ina ji ya na biyo ni ya na ta aikin ba ni hak’uri, ni kuwa nai kunnen  uwar shegu da shi. Da sallama mama ta shigo ta katse mun tunanina. Ta ce.

“Sadiya zo ga karin  kumallo ki yi. K’awayenki  na wajan aiki sun iso, su na jiranki a d’akin ki. Kuma yaya sulaiman ya ce da wuri za ku wuce, zuwa sha d’ayan rana. Waje ba kusa ba.” Ban ce Mata komai ba, na amshi karin  kumallon na ci da yawa, dan mama ta ji sanyi. Magani ta ba ni na ha’diya. Sannan na fice zuwa wajan su Jamila.

*******

Asalin tarihin Sadiya da ahalinta.

Malam Buhari mai hula shine sunan kakana, wato mahaifin Babana. Sananne ne sosai a k’auyan su. Domun Allah ya hore mai arziki sosai, ya na da tarin shanu da rak’uma a wannan zamanin sama da guda d’ari. Gonakan shi kuwa sun fi na kowa yawa a kauyan. Gidan malam mai Hula babban gida ne mai k’ofa hudu. Ko yaro ka tara a hanya zai kawo ka gidan. Ya na daga cikin manyan dakatan k’auyan. Matar shi d’aya mai suna Safiya. Yaranshi kuma biyar maza biyu mata uku Kawu sulaiman shine babban ‘dan shi, sai Goggo Asabe ita ce mai bi mishi, sai Goggo mariya, sannan Goggo Safiya ita ce ta ci sunan mahaifiyarsu, sai Adamu wato Babana, shi kuma sunan mahaifin malam Buhari mai Hula ya ci, shine d’an auta. Ya taso a cikin gata sosai daga wajan iyaye, har wajan yayyu.

K’auyan RAQUMA shine sunan k’auyan da aka haifi mahaifina. Kuma shine k’auyan da zan je zaman Aure. A cikin garin Zamfara k’auyan yake.a kar’kashin  ‘karamar hukumar MAFARA

Kauye ne wanda ya kasance mai cike da duhun jahilci. babu ko asibiti a cikin kauyan. . Sai in gagarumin ciwo ya rabke su. sai a kai mutum mafara  local government akwai asibitin gwamnati a wajan, asibiti ne wanda ba su da wadatar kayan aiki, haka ma likitocin  ba su da yawa. Ko kuma a shiga k’auyan Lamba a sai magani a kemis, wanda  wannan kemis ya kasance shi ka’dai ne a wannan yanki, in kuma ba haka ba dai, sai an dangana da  k’auyanTuraita, anan ma akwai wani ‘dan asibiti gajiyayye mai su na SHA KA TAFI. Ba su da gadajen ajjiye mara lafiya.Amma abunda jama’ar ‘kauyan RAQUMA  su ka fi ga ne ma shine. in yara da manya ba su da lafiya. Sai a shiga jeji duk bishiyar da aka soma cin karo da ita a hanya, toh fa ta zama magani, ganyenta za’a debo ayi sirace ma mara lafiyar nan. Kuma cikin amincewar  ubangiji  sai ya tashi. In kuma gudawa ce ta kama babba ko yaro, kashin  giwa za’a debo a jik’a sai a sha ruwan. Kuma gudawan  zai tsaya. Daidai da ban ‘daki na ba haya , basu cika yi a gida ba. Sai dai su je gonakan su, aciki su ke yi, maza da mata. Ban ‘dakin wanka kawai su ke yi a cikin gida. Bangaren makarantar muhammadiyya kuwa, babu sam a wannan zamanin. malami sau d’aya yake zuwa a shekara ya ba da karatu, wanda ya ri’ke ya samu na Sallah, wanda ma bai ri’ke ba a hakan zai yi Sallah. Maganar makarantar boko ma ba’a magana. ‘Yan boko tamkar kafurai mutanen kauyan RAQUMA, su ka d’auke su. Babu arabi  babu boko haka su ke rayuwa kara zube. Ba su da hasken wutar lantarki sam. Kuma ba su da injinan ni’ka. A turmi su ke daka hatsi, su sarrafa shi ya zama abinci. Mata da kan su, su ke fita su yo karar da za su d’aura sanwa. Ba sa noman masara. Dawa, gero, su ne abunda su ke nomawa. Da yawansu makiyayane. Kuma har yanzu wannan ‘kauyan a haka su ke gudanar da rayuwarsu, babu wani canji, ko tallafi da su ka samu, daga b’angaren gwamnati, ko ma daga fararen hular ne.

Kakana mai Hula ya ci alwashin ya na so d’aya daga cikin yaranshi maza su kawo canji a kauyan RAQUMA. Amma ko da kawu sulaiman ya ta so, sai ya k’i sam ya ta fi  almajirci, ya fi  mai da hankalinshi akan Noma da kiwo. Ga shi shine babba a gidan ragamar gidan ba’ki daya a hannunshi take, ga iyalai ya tara. Matan shi biyu, Ladi da Tabawa sai dai a wannan lokacin bai samu magajiba tukunna. Toh sai Hankalin mai Hula ya dawo kan Baba na. Ya na da shekara biyar aka tura shi almajirci. Ya shafe  tsawon shekaru sama da goma sha biyu, ya na almajirci. A K’auyan makoli da ke jihar kanon dabo.Har Allah ya amshi ran Malam Mai Hula, burinshi  shine Adamu ya yi karatu mai zurfi. Ragamar gidan kacokam ta sake hawa kan kawu sulaiman duk wani kadara  ta na hannunshi, kama daga kan gonaki, shanu da rak’uma, har zuwa kan dukiya  tsabarta. Sai malamai su ka je su ka samu a garin Zamfara, su ka raba  musu gadonsu. Ananne su Goggo Asabe su ka samu gidajen  da su ka dawo ciki tare da mazajensu, da yaransu. Kuma gidajen sun kasance a Jere suke reras har guda shidda da asalin family house d’in su.

Goggo Asabe yaranta uku. Anas  shine Babba, sai fatima, sannan Aliyu. Goggo safiya kuma Allah bai bata haihuwa ba. Goggo Mariya kuma yaranta maza ne guda hu’du, akwai Adamu, Sulaiman, kabiru, sai Dauda. Kawu Sulaiman kuma yaranshi uku, Sajida, Rukayya, Safiya. Babana daya kammala karatun almajircin shi, Kano ya dawo sai ya shiga  makarantar boko abu kamar wasa kawai sai ya soma yin yaron shago a kasuwar  kurmi. Shagon Alhaji Nuru doron nera mahaifin Mama na. wasa_wasa Baba ya na ta karatun boko, kuma ya mai da hankalinshi sosai. Shine har matakin jama’a. Kakana daya lura Baba mai amana ne sai ya d’auki diyarshi Aisha wato Mama ya aura mishi. Mama na ita ce babba a gidansu. ‘Kannenta uku kuma dukka mata. Goggo Hansatu itace mai bi mata, sai Goggo Sadiya wacce Allah yai ma rasuwa, sai Goggo Harira, sai kuma Goggo Binta. Wacce take garin saudiyya da aure. Gidan su Mama ‘yan boko ne sosai. Ana yin karatun boko da na muhammadiyya sosai.

Mama tasha tsangwama a wajan dangin Baba sosai ba sa kaunarta sam su a tunaninsu  ita ce silar  da ya sa Baba ya ki komawa kauye. Kuma gani su ke yi, ta mallakeshi ne, kuma ta na mai wayo  sabida ‘yar boko ce ita. Baba ya yi aiki ne a kar’kashin gwamnati. Haka ma Mama, ma’aikaciyar gwamnati ce. Ni ka’dai Babana ya haifa. Mahaifiyata ta samu matsala a mahaifarta, wanda hakanne yasa ban da k’ane bare wa. Na taso cikin soyayya da gata na mahaifa. Burin Baba shine in zama ma’aikaciyar asibiti. Alhamdullah na cika ma Baba burinshi. Ko da Allah yai mai rasuwa karatuna  bai tsaya ba. Da ku’din pension da garatutin Baba na samu na ha’de karatun likitanci na.  Sai dai na fuskanci kalubale da dama a rayuwa. A sakamakon k’alubalantar karatun ‘ya mace da Malam bahaushe ya ke yi. Hakanne ya kawo mun jinkirin aure. Sau uku ana kawo sadaki na. Daga baya a dawo a kar’ba. Sabida kawai na kasance ‘yar boko kuma ma’aikaciya a ‘kar’kashin asibitin gwamnati.Wannan shine ta’kaitaccen labarina.

Dawowa daga labari

Tafiya su Goggo Hansatu su ke ta faman ci. Tafiya yankin azaba. Hadiza ta ce.

“Goggo wai  da ma Sadiya ba a garin Kano za ta zauna bane? Ni na ga wannan kamar hanyar Zamfara ce fa, ina karanta sunayen k’auyukan da ke kafe  a allon  kan titi. Sai kuma na ga mu na ta kutsawa cikin k’auye.” Goggo Hansatu cikin takaici ta ce.

“Gidan Sadiya mu ke zuwa. A wannan k’ungurmin k’auyan k’addarar Aure ta kawo ta.” Hawaye ta share tace.

“Ahmad iyayenshi sun ‘ki amincewa ya Auri Sadiya. Hakanne ya sa dangin mahaifinta su ka ha’da ta Aure da ‘dan uwanta. Da gyatumar shi yaron da gyatumin Sadiya Uwa d’aya uba d’aya. Ku yi mata fatan alkhairi kawai.” Mamaki da tausayin  Sadiya ya hana Hadiza da Amina samun zarafin cewa komai. Goggo sadiya, da Anas kuwa. In kun tanka ku da ba kwa wajan, toh sun tanka su ma. Sai kauyen  kawai su ke bi da kallo su na zubar hawayen tausayin Sadiya. Motar su ce ta tsaya a wata madakata wanda a iya nan mota ta ke tsayawa. Sai dai kuma a shiga a kori kura, ko a hau mashin  ya shiga da mutum cikin k’auyan. Daga nan madakatar tafiyar  mill 7 za’ayi kafin a isa cikin k’auyan. Ga hanyar sam babu kyau. Sakkowa  su ka yi daga cikin motar. Goggo Hansatu ta ce.

“Lafiya Safiya mu ka sauka anan, Kuma banga  gida ba kwata  kwata? Anas  ne ya ce.

” Goggo anan za mu tsaya mu jira motar akori kura, sai mu shiga ta k’arasa da mu. A hakan ma sai dai in yanke za mu bi, wannan hanyar ta mu tayar Babur ce ka’dai ta ke  iya bi, da jama’ar da ke tafiyar  k’afa. ko kuma ku hau Babur ya isa da ku. Zan shiga motar kayan amarya, mu sai mu bi yanke. Amma k’ananun mota basa iya shiga. Hanyar a lalace ta ke.” Salati  Goggo Hansatu ta shiga yi ta ce.

“Amma Safiya bakwa  jin tsoron Allah, da ku ka dakko  yarinya a maraya  aka dawo da ita k’auye irin wannan. Wannan wanne irin bala’i ne? Dole a warware wannan auran domun Sadiya sai wahala ta kasheta anan. Hmmm wallahi na ga illar auran ‘dan cirani  wanda ya fito daga kauye. Da  ace Yaya Aisha bata auri Adamu  ba, da duk haka ba za ta soma faruwa ba.” Cikin fa’da da rashin ilimin arabi  da boko Goggo Safiya tace.

“Hansatu kenan. Sai dai in kece ba kya tsoron Allah. Mu sunnar muhammada  Rasulullahi ( S A W) mu ka ha’da. Da k’auyan nan ya na kisa, da Adamu bai rayu har Aisha ta aure shi, ta raba  mu da shi ba. Ai  matar mutum kabarinshi. Bari ki ji, baki isa ki fa’da mun magana in barki ba, yanzu sai mu da ku.” Goggo Hansatu tace.

“Toh sai me mu daku  mana, mai jaki  ma ya ce ai tsere  ballantana mai doki? Nanfa rikici mai girma ya ‘balle a wajannan. Mata matan wajan da su ka fito cin kasuwar  kauye za su koma gida. Su ne su ka raba  wannan rikici, da kuma Anas. Hadiza da Amina kasa magana su ka yi, sun tsinke da lamarin. A kori kura ce ta iso, a hakanma a cike take fam  babu waje, dole Babur dai su ka hau. Sun sha ‘dan banzan  wahala a hanya. Domun surquqin jeji su kai ta ratsawa. Ga wasu kwazazzabai a hanyar.  Ga tafiya bata wasa ba, mill 7 su ka yi a kan Babur d’innan. Wujiga wujiga su ka isa. A barayin surukan  gidan aka musu masauki. Wato matan yara mazan gidan. A d’akin matar Anas  a ka sauke su. Dan d’akinta ya fi ko wanne d’aki a gidan kyau. Kasancewar daga kauyan  Lamba a ka Auro  ta, kuma mahaifinta shine mai gari.

Sai bayan sun huta sun sha ruwa, da tuwon dawa miyar  bushasshen karkashi, da ake kira da bak’ar miya. Sai wata dawo ( fura) k’azamar damu babu sikari ba nono, a ka kawo musu. Sannan motar kaya kuma ta iso.

Abunka da ‘kauye, kafin kace me gidan ya cika da mata da ‘kananun  yara. Ana tambayar Anas  ” Amarya aka kawo ne” sai sanar musu ya ke yi. Cewar Aliyu ne ya yi Aure. Mamaki da almara su kai ta yi. Kafin dare ya rufa kowa a cikin RAQUMA ya ji labarin Auran Aliyu da ya Auro  ‘yar masu ku’di. Wanda akai mata kaya na mamaki. Mata fam  gidan suna mamakin ganin irin kayan ‘dakin Sadiya. Matan mazan gidanne su ka ta ya su Goggo Hansatu kintsa d’akin amarya. Har bayan isha su na Abu d’aya. Bacci su ka yi a cikin ‘dakin na ta suna jiran wayewar gari su ‘daura daga in da su ka tsaya. Sun kuwa sha cizon sauro, har hakan ya tilasta musu hak’ura da baccin  ma baki ‘daya. Ga  babu wutar lantarki sam a k’auyan, sai dai aci balbal da shi su ke amfani.Cikin daren su ka mi’ke, su ka ci gaba da jera  komai a in da ya dace.

*WAYEWAR GARI*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *