*Mrs Bukhari Ibrahim*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al’kalamin_
_Badi’at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
Wannan Labari true life story ne, duk abunda na rubuta, abune daya faru a zahiri, sai d’an k’alilan dana canja, kamar sunaye, da sauransu. Ku bini a sannu, akwai d’umbun darasi sosai.
Kashi na farko
Babi na 3~4
Da sanyin murya na yi sallama a k’ofar ‘kuryar ‘dakin mama. Ban ma jira amsar sallamar da na yi ba, na kutsa kai kawai. Idanu ta zuba mun, ta na ko’karin karantar yanayi na. Kaifin tsinin idanuwanta ne ke mun yawo a jikina. Zuchiyata ta shiga cikin taraddadi. Domun bansan meke wanzuwa ba, jikina ya na ba ni babu lafiya. Gwauron numfashi mahaifiyata ta sauke ta ce da ni.
“Sadiya! Ga waje k’araso ki zauna, domun ni da ke inaso mu tattauna sosai.” Hantar cikina tana kakkarwa na k’arasa in da ta nuna mun da manuniyarta. Zama na yi, kai na a k’asa, jikina kuwa sai bari ya ke yi. Takowa ta yi, ta zauna ta na fuskantata.”
“Sadiya” ta kira sunana da babbar murya.”
“Kinsan irin power d’in da dangin mahaifi su ke da shi, kinsan irin rawar da su ke takawa?” Cikin daurewar kai na dubeta, sam ban yi zaton jin wannan Kalmar da ga bakinta ba. Lumshe idanu na yi, ina tunanin dangin Babana sun ci mutumcin mama ne kamar yanda su ka saba. A sanyaye na ce.
“Dangine da su ke jibantar al’aumara, kuma sai da su komai ke iya gudana. Da amincewarsu komai zai iya faruwa, domun da uba ake ado, su guma dangin uba. In ba mahaifi da su zaka yi ado. Amma mama……” Hannu da d’aga mun halamar bata son jin tambaya. Mu’kut na ha’diye tambayata.
“Sadiya! Ahmad iyayenshi ba su amince mishi ya auri ‘yar boko ba. A sakamakon haka ya fasa auranki.” Nunfashi naja tamkar wacce aka zare ma rai haka na kasance na wucin gadi, ji na yi kalmar da mama ta jefomun tamkar bulalace wacce ta zane rayuwata tai mata dukan da baza ta iya boruwa a gaba ba. Iya so ina yi ma Ahmad, Allah shine masanin tsantsar son shi da ke raina. Wasu dun’kulallun hawaye ne su ka fashe a kumatu na. Ta ke zazzab’in da ya ke ta shirin kada ni ya samu nasara, har wani turirin zafi ne ya ke busowa daga jikina.”
“Amma dangin mahaifinki da su ka fini iko da gadara akan ki, ba tare da sun girmama ni a matsayina na Uwa an shawarce ni ba. Sun d’aura auranki da ‘dan uwanki. Biyayya kawai na ke so ki yi musu Sadiya.” Tsintar kaina kawai na yi a tsaye cak, cikin rawar jiki da rawar murya na so in jefo mata tambaya. Amma kash harshena bai bama baki na damar hakan ba, domun ya kasa ha’da kalma mai ma’anar da za’a fahimta, sai in ina kawai na ke yi. Nan ta ke duniyata ta yi duhu, tare da yin ta maule da gangar jikina.” Zaunar da ni mahaifiyata ta yi.
“Sadiya na sani abun za ki ji shi tamkar albamara, toh a zahiri yanzu ke matar aure ce wacce igiyoyi uku su ka rataye rayuwarki, dai dai da k’ofar gida in za ki lek’a a yanzu haka sai da izinin mijinki. Sadiya girma da darajar miji ya wuce zato ko tsammani, biyayyarki a gare ni shi zai ba ni damar tsallake jarabawar da dangin mahaifinki su ka za na mun. Ki amshi k’addarar da su ka ‘kadarto miki.
Sadiya ina so ki cire wannan abun a zukatan al ummar da su ke kalubalantar ilimin Mace, ki nuna musu ‘yar boko diyace mai tarbiya kamar ko wacce ‘d’iya. Ki nuna musu cewar ‘yar boko na iya zaman aure, ‘yar boko ba mara tarbiya bace, kuma ba karuwa bace, ki nuna musu ‘yar boko ita mace ce tamkar ko wacce mace, kuma ‘yar boko ta na daraja mijinta, kuma tana yi mai tsantsar biyayya, ki cire musu k’ya matar macen da ta yi boko, ki fito da darajar gidan mahaifinki, domun ko wanne tsuntsu kukan gidansu ya ke yi, ki nuna musu kin haifu cikin ‘yar boko, kuma ta dauraki bisa tartibiyar tarbiya. Sadiya ki yi ma dangin mijinki biyayya, dangin mahaifinki ne. Aliyu k’usar yak’i wanda ya ke karatu a jami’atul madina kar’kashin scholarship, ‘kaninki. shine mijinki. Sadiya kar ki ce komai ki yi musu biyayya, sannan ki ajjiye aikin ki babu komai. Amma zuwanki wannan kauyan inaso ki yi amfani da iliminki ki shiga gaba wajan wayar da kan ‘yan uwanki mata kan muhimmancin ilimin Mace, da irin gudummawar da ilimin mace ke bayarwa a duniya ba ki d’aya, ita mace uwar duniya ce. Ki yi k’ok’ari ki zama malamar ilimi a kauyannan, amma komai za ki aiwatar ki tabbatar da yardar mijinki. Ki yi ko’karin fahimtar da shi, tunda shi ba jahili ba ne.”
Kuka na rushe da shi, wanda ya dauke ni da’ki’ku masu dama. Mama zuba mun idanu ta yi ba ta yi yun’kurin rarrashina ko katsemun kuka na ba. A lokacin zuchiyata da kwakwalwata ba sa amsar ko wanne irin sa’ko, ji na ke yi tamkar na zama wata halitta ce ta daban. Tausayin kai na da kai na ma ka’dai ya isheni. K’ok’ari na yi in tuno da fuskar Aliyun da aka kira shi da mijina. Amma na kasa, domun bai fi sau biyar mu ka ta’ba ha’duwa ba. Abunda kawai na sa ni game da shi, shine. Shine d’an auta a wajan Goggo Asabe, kuma na girme mishi da kusan shekaru biyar. Taya za’a aura mun ‘kanina, ina babbar mace mai shekaru talatin da biyar? Wanne irin zaman Aure su ka zab’ar mana mu yi, dama har yanzu a na yin auran dole ne, ko kuwa a kaina abun ya juyo?” Dukkan Wa’dannan maganganun ni da zuchiyata na ke yi. Na shiga rudin da ya fi k’arfin gaban a misalta balle har ya rubutu. Cikin karyayyar muryar da ta ke sa ke jefa ni a damuwa mama ta ce.
“Sadiya! Ko ba za ki yi mun biyayya ba ne?”
Zan yi miki biyayya mama, amma mama me yasa za’a tauye mun hakkina, a hana ni ci gaba da aiki na? Aikin ceton rayuka fa na ke yi, mama na d’auki ilimi a matsayin GISHIRIN ZAMAN DUNIYA. asara ne boye ilmi, domun yin hakan bai baka damar ka sha romon ilmi ba. Na sha wuya wajan karatu, babu irin fa’di tashin da ba ki yi ba akan ganin kin cika wasiccin da Baba ya yi miki, sai kin yi kamar za ki fa’di, sai ubangiji ya taro ki. Dangin ki kuma su ka nuna mun soyayyar da su ka tsaya mun kan lammuran karatuna, har na ta ka matsayin da na ke a yau na anguwar zoma. Mama a iya sanina tun mahaifina da ran shi, kawo yanzu, babu wani tallafi ko gudummawar da ta ta’ba fitowa daga bangaren dangin Baba. Asali ma sai tauye hakkinmu da su ka so yi. Sai yanzu da na zama mutum……” Sadiya” mahaifiyata ta kira sunana da murya mai amo.
“Za ki yi mun biyayya ki amshi auranki a matsayin k’addarar rayuwarki ko yaya?” Cikin rauni da kuka na ce.
Na amince Mama na amshi auran, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi. Amma an dur’kusar mun da rayuwata, ko a addinance ba daidai bane a mai da mutumin daya rayu a maraya kauye, sai dai a fito da na kauye zuwa maraya.” Jawo ni ta yi jikinta ta mayar da ni tamkar karamar yarinya shekshekar kukan ta na soma jiyowa, rabon da na ji kuka ko rauni a muryar mama, tun rasuwar Baba. Domun Mama ta kasance mace mai kamar maza jarumar Uwa. Da sauri na dago kaina, na dubeta. Hannu na sa ina share hawayenta, kukan nawa na ha’diye na ce.
“Haba Mama kar wannan auran ya d’aga miki Hankalin ki, ki kwantar da Hankalin ki, zan yi muku biyayya, da sannu dangin mahaifina za su yi alfahari da ilimin da ki ka tsaya mun nayi.” A maimakon Mama ce za ta lallashe ni, sai ni ce na ke lallashinta. Akwatin sarka da ‘dan kunnen azurfata, da kuma da d’an kunnen zinari na ta mi’ka mun. Hannu nasa na amsa ta ce.
“Ki rike su da kyau wata rana za su yi miki amfani, bansan ko yau za su ta fi da ke ba, ko sai gobe. Amma zan yi ko’karin zuwa in duba ki Sadiya. Sannan wannan dubu ashirin da biyu ne gudummawar biki da na soma samu daga kawayena. Shi ma ki ri’ke ki ta fi da shi, ki adana shi. Ahmad kuma da zaran an watse taro zan sa Hansatu ta ne mo shi, a ba su kayan lefen su da akwatin su. Sadiya ki na da suttura kar ki matsa sai Aliyu ya yi miki lefe, amma bazan hana ki amsa ba in dai sun yi miki adalci sun ba ki.” Cikin murya mai taushi na ce
“Amma Mama za’a rake kayan d’aki na ko? Domun za su iya ma in da za’a ajjiye ni yawa.” Sunkui da kaina na yi dan wasu sabbin ruwan hawaye ne su ka sulalo mun. Cike da tausayi da kulawa Mama ta ce.
“Babu abunda aka rage Sadiya kayan ki ne, kuma abunda bazai sa mu waje ba, bazai wuci kayan kitchen ba domun kitchen a tsakar gida ne na matan gida ba ki d’aya. Hansatu za ta ji da komai.” Murmushi na yi ma Mama tare da sauke ajjiyar zuchiya mai k’una, na ce.
Toh shikenan Mama. ” umarnin sa ke sutura Mama ta ba ni. A ban d’akinta na sa ke yo wanka. Riga da zani na sa ka, na lace d’inkin buba. Lace d’in ya amshe ni sosai. Popul colour ne jikin lace d’in, sai manyan fulawowi da aka zana a jikin lace d’in da bak’in zare. Bak’in mayafi da takalmi mai tsini mama ta ba ni. Bada son rai na na ke yin komai ba. Turare mai k’amshi ta fesa mun a jikina tace.
“Ki je ki samu kawayenki Sadiya. Na ji dad’in yanda ki ka shanye duk damuwar da ki ka shiga, tare da rungumar k’addarar rayuwar da dama ba kasan in da za ta gara ka ba. Ki je kar na ri’ke ki.” Jikina a mace na fito. Kowa na ta kallona ana fadin “amarya” kunsan amarya ko ta buzuzuce farin jini gare ta. Cikin su Jamila kawayena na koma. Amma tunanina sam baya ma tare da su, su kan ji ina sauke ajjiyar zuchiya minti minti. Ni ba auran dolen da akai mun ba ne ya jefa ni cikin damuwa da tashin hankali ba. Bazan ce ban shiga ru’du ba, amma rashin aikina da karatuna da na ke ganin zai ta shi a tutar babu, ya fi komai caza mun kai na. Lumshe idanu na yi kawai, cikin kan’kanin lokacin jikina ya rincabe da zazzab’in da bibbiyu na ke ganin mutane, kuma na kasa magana sam, ga ciwon son Ahmad na nukurkusar zuchiyata, ga auran Dole da akaimun da k’anina, kuma ake shirin raba ni da maraya, aiki na na fi bashi mahimmanci fiye da komai, dan burina shine in yi suna, na zama fitacciyar unguwar zoma wacce tasan makamar aikinta. Ni dai ban sa ke sanin in da kaina ya ke ba, sai bayan isha, na farka na ganni akan gado na. Ga Mama da ‘yan tsirarin dangin mahaifina ciki har da sirikata yar mahaifina Goggo Asabe. Baki ta tab’e tare da cewa.
“Tabbb ke da aka taimakama, kin kasa auruwa ke ce wai har da sumewa. Ashe shi k’usar yak’i, in labarin auranku ya ruske shi, mutuwa kenan ya kamata ya yi. Ai ni sulaimanu ya cuce ni da ya ha’da wannan auran. Yaro karami an ha’da shi aure da Babbar macen da ta fishi shekaru da wayo. Ba lallai bane ya samu tantanin budurci ma a jikinta ba, an gama cudanya da maza, har jiki ya ‘d’auki warin maza. Ko wannan ya na karya jazbiyyar jikin d’iya mace, ku kuma gani ku ke yi waye wa ce. Abunda namiji in ba mijin auranki bane, ko a kujera ya zauna ya tashi, bai kamata mace ta zauna ba, dan kare jazbiyyarta, sai ta bari kujerar ta huce dan gudun lalacewar jiki. Amma ‘yar boko ai ba ta san wannan ba. Maza su ne abokanta, tunda har ha’da hannaye suke yi da maza da sunan waye wa, tur da irin wayewar da ba ta addininmu da al’adunmu kyawawa na hausa Fulani ba.”
Jina yi gabaki d’aya na muzanta a wajan, jina na ke yi tamkar tsirara. Wai surukata ce ta ke ya’ba mun muggan kalamai irin Wa’dannan tun kafin ma in tare a gidan ‘danta. Ashe har zargina su ke yi da salwantar da budurcina? Ni tunda na karaci karatuna bana yawan mu’amula da maza, sau d’aya tak namiji ya ta’ba ri’ke mun hannuna. Ahmad ne, shine ya kafa wannan tarihin a rayuwata. Ni babbar mace ce, na kasance mai k’arfin sha’awa da son jin dumin namiji a kusa da ni. Lura da na yi da yanayi na ne, yasa ba na sake ma maza fuska dan gudun samun wata matsalar. Ko da yaushe a cikin azumi nake dan ganin na kare martaba da k’imata ta d’iya mace. Ashe na shiga ban d’auka ba bata fidda barawo. Mama na kalla wacce ta ha’de girar sama da ta k’asa tace.
“Yaya Asabe, bai dace kina jifan ‘yar d’an uwanki da irin Wa’dannan alkaba’en ba. Ai ni a tunanina ya ci ace an jinjina ma tawakkalin da ta yi. Maganar kauye fa ake yi, da mutuwar aikinta. Uwa uba yaronnan k’aninta ne, ku………. Dakata Aisha yayar za ki yi ma rashin kunya, ashe za ki iya zagin Adamu ma?” Goggo Mariya ce ta ke wannan Maganar. Hannuna Mama ta ri’ke tace.
“Mu je ki kwanta a d’aki na, ki sha magani sai ki yi sallah.” Sum sum sum na bita Goggo Asabe kuwa kamar za ta ari baki tsabar fa’da. Sai hak’uri ‘yan Uwa da su ka zo biki daga sauran garuruwa su ke ta bata. Wanka na yi dan in samu k’arfin jikina. Sannan na rama sallolina, na jima ina rokon Allah yasa mun albarka a Aure na, ya kare ni daga dukkan wani sharri, yasa in samu rayuwa da sauk’i. Mama ta saka ni a gaba ta ba ni ruwan tea mai kauri na sha, amma daci kawai baki na ya ke yi. Magani na sha, nasa rigar baccina. Mama tace.
“Ki yi kwanciyarki anan Sadiya. Bance da Mama komai ba, domun in nace zan yi magana kuka ne zai balle mun. Kwanciya kawai na yi. Mama ta dinga shafar kaina kamar karamar yarinya. A daren ranar tare da Mama mu ka kwana gado d’aya, ba ta bar ni na yi tunanin komai ba.
Allah ya yi dare gari ya waye, yau ne budar kai, kuma yau za’a wuce da ni gidan mijina.