*Mrs Bukhari ce*
*GISHIRIN*
Ā Ā Ā Ā Ā Ā *ZAMAN*
*DUNIYA*
Ā Ā _Daga Alākalamin_
_Badiāat Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR š¤š»
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwaĀ ga alāumma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
True life story
Kashi na 1
Babi na 7~8
Shiga ādāakin da su Jamila su ke na yi. Nan fa su ka soma yi mun guāda tamkar za su tsinke hancinsu. Sister Murja ta ce.
āSadiya gaskiya za mu yi matuākar kewar ki a Asibiti. Kafin ki gama cin amarci ki dawo.ā Dariya na kāwakāwulo cike da farāaĀ na ce.
āNi kuwa ba kewar da zan yi. Bazan so ma hutun nawa ya kāare in dawo ba, na fi so in ta zama wajan angona. Sister Jamila ta sa ka shewa ta ce.
ā lallai Ahmad ya sa mu babban rabo da ya same ki a matsayin umman āyaāyanshi. Zai yi alfahari da kasancewarkiĀ matar shi. Uwa uba ga ki da tsoron Allah, kin kuma kasance mai alkhairi, da son taimako. Sadiya ba ki ci ka duba kan ki ba, hankalinki ya fi taāallakāa ne akan ganin ko wacce mace ina ma ace ta samu ilimi , da duniya za ta yi alfahari da ita. Ina ji a jikina wata rana za ki zama wata.ā KokawaĀ na ke ta yi da hawaye na kar ya zubo, dan gudun kar ya fallasani. Amma sai da ya ci amanaĀ ta ya zubo da gudu. Kukan kawai na shiga rerawa a hankali, ina tuno yaya rayuwa za ta kasance mun a kauye, kuma a kāarkāashin namijin da na ba shi shekara biyar, waiĀ me ya sa baāa cika bai ma mace dama bane? Bayan addininĀ musulunci ya faādi girma da daraja, da ma baiwar da Allah yai ma mace. Rarrashina su ka shiga yi, a na su tunanin kukan rabuwa da gida ne. Dan har Jamila ta na yi mun tsiya da cewa. āSai kace wata karamarĀ yarinya, har da kukan zuwa gidan miji?ā Ni dai ban da kuzarin da zan ci gaba da biye ma ceceĀ ku ce dāin su.
Sha dāaya na yi, Goggo Mariya ta shigo har dāakin da na ke ta ja hannuna, zuwa dāakin Mama na. Mun yi kuka ni da Mama tamkar rabuwarĀ da baza mu sa ke haāduwa ba. JakaĀ ta Mama ta zuge ta sa ka mun wani abu. Da kyar ala zare ni a jikin Mama a ka yi waje da ni. Kowa ya shiga mota. Ina zaune a bayan mota kusa da maman su Amina, wacce ta kasance aminiyaĀ ga mahaifiyata. A kusa da ita Goggo Mariya ta zauna, sannan Goggo Asabe. A gaban mota kuma Kawu Sulaiman ne zaune bangaren me zaman banza. Dāayar motar kuma su kawu Bala ne da sauran matan da aka tawo da su. Mama na hango a kāofar gida, ta na dāaga mun hannu. Nutsa kai na, na yi a tsakankanin cinya ta. Na fi awa huādu ina kuka mai taāba zuchiya, abubbuwa da yawa ne a karākashin wannan kukan nawa. Zazzabāi da wani irin jahilin ciwon kai ne, su ka rabke ni. Awa takwas mu ka yi a titi mu na zirara gudu. Kauyan mafara mu ka tsaya a ka yi sallar azahar da laāasar. Daga nan kuma mu ka sa ke miākar hanya. Su Goggo Asabe sai hira da dariya su ke yi abinsu. Ni kuwa ina zaune na yi tsuruĀ tsuru, ko kāwakkāwaran motsi ba na iya yi. Maman Amina takan sa musu baki a cikin firarĀ ta su jefi jefi. A. Haka har mu ka isoĀ bus top. Babura aka tarar mana. Hawaye sai sabunta kansu su ke ta yi a kumatu na. Kowa ya hau Babur dinshi, ga kaya niāki niāki a hannun ko wacce daga cikin mu, kaya har a gaba aka saka masu Baburan su ka ta ya mu rikāewa. Gudu akeyi cikin ciyayi da kaucina, Hankalina baya tare da ni sam. Gani na ke yi wani nannauyan bacci ne na ke yi, mai cike da muggan mafarkaiĀ kawai, tunda uwataĀ ta haife ni ban taāba ganin kāungurmin kāauyeĀ irin wannan ba. Domun ban taāba zuwa da wayoĀ na ba. Sai lokacin ina kāarama Mama ta na zuwa da ni, a lokacin bansan komai ba.ā
Gidan Amarya
Goggo Hansatu na hango a tsaye a dan kāaramin tsakar gidan da ke bāarayinĀ Sadiya hannunta riāke da kāugunta ta tusa kayan kitchen dāin Sadiya a gaba, ta na ta tunani. Amina ta ce.
āGoggo me zai hana mu yi ma yayanĀ shi Angon magana, ko da kafinta ne a nemoĀ mana wanda zai buga mata kitchen ko da na langa langa ne, kamar yanda aka yi mata bayan gida da langa langa. In ba hakan mu ka yi ba, sai dai in da kayan za mu koma. Goggo Hansatu ta zare idanu ta ce.
ā mu koma da me? āYannan ni kai na da taimakon Allah na isoĀ lafiya a Babur. Ni kaādai ma kenan balle kuma ace da kaya. Shawarar da ki ka bayar ta yi kyau sosai. Bari in je wajan matar AnasĀ dāin, ko Allah zai sa mu dace a samu kafintan.ā Goggo Hansatu da kanta tayi tattaki har zuwa bāarayinĀ Matar Anas. Bilkisu na tsugunneĀ ta na ta kici kicin huraĀ kara ta na son dāaura dāumame. Shi kuma AnasĀ dāin fitowarshi daga dāaki kenan zai fita waje, Goggo Hansatu ta shigo.
āAhh Goggo Hansatu, aiĀ da kin aikoĀ ni nazo, da ba ki wahalĀ da kan ki ba.ā Cewar Anas. Bayan Goggo Hansatu sun gama gaisawa da Bilkisu. Sai ta ce da Anas.
āBabu komai ādannan. Ka ga kafintaĀ na ke so ka ne mo mana. Zai buga mana madafiĀ ne da langa langa, kamar yanda aka buga ban dāakin na Sadiya. Na ga wajan ba madafi. Shiru AnasĀ ya yi, sannan ya ce.
ā toh bari zan fita yanzu, in je gidan mai gari, yaron wajan shi shine kafinta, sai mu zo da shi ya ga wajan.ā Godiya Goggo Hansatu ta yi mishi ta fita, ta koma bāarayin Sadiya. Amina ta ce.
āAndace kuwa Goggo?āĀ Ā Ā Zama Goggo Hansatu ta yi tukunna, sannan ta ce.
āZa dai a dace. Ya ta fi kiran kafintan sai ya zo ma ji ta bakinshi. Ba ma wannan ba Hadiza, ina ganin dole ku zan aika zuwa cikin garin Zamfara. Yarinyar nan a siyo mata tocila irin wanda su ke yin chaji da hasken rana. Wannan duhuĀ ya yi yawa, damuwar za tai mata yawa, a siyo mata kalanzir shima, ta ādanyiĀ amfani da shi, kafin ta ko yi kunna kara kuma, abun tuwo na buhu ma, a kāaro mata kamar buhu hudāu. Da tarkacen da kuka san zata sha wuya kafin ta sameshi a wannan kufan.ā Bilkisu, da matar Dauda Hasiya ne, su ka shigo hannayensu rike da kwanukan abinci. āDakin amarya su ka wuce dan ajjiye kwanukan. Tsurewa su ka yi dan ganin haāduwar dāakin. Bilkisu tace.
āHasiya ji dāaki, komai a tsare kuma babu kaloli barkatai. Baki Hasiya ta tabāe tace.
ā dāakin āyar boko ba. Wallahi ni sai na ji na tsane ta tun kafin ta zo. Kishin balbali sai tafarfasamun ruhina yake yi. Goggo ma ta ce babbace Amaryar ta fi kāarfin Aliyun fa. Kuma kwantaiĀ ta yi a burninĀ shine aka kāakāaba mishi ita.ā Bilkisu tace.
āHaka na ji a wajan Anas, sai dai Baaba ta ce, auran shi ya na nan daramĀ da khadija, daya dawo da wata guda. Tun yarinyar ta na kāarama aka ba shi ita.Ni ai na fiki jin kishin balbali a kanta, da dāakina yafi na kowa tsaruwa a kab surukan gidannan, yanzu an kawo kishiyar da dāakinta ya fi nawa hmm.āĀ Hasiya ta ce.
ā mu lekāa kāuryarĀ dāakin mu ga ni. Bilkisu ta riāke hannunta tace.
āAlkurāan ba ruwa na. Ki zo mu fita.ā Fitowa su ka yi.
āGoggo ga karinĀ kumallo mun shigar muku. Goggo Hansatu ta ce.
ā An godeā bayan su Goggo Hansatu sun gama tattaunawa. Dāakin su ka koma. Dumamen tuwon jiya ne da ruwan kokkon gero Ā wanda babu sikarin arziki, shine kumallon. Kokkon kawai su ka sha, tuwon kuma su ka mayar musu da shi. Hadiza da Amina, Goggo Hansatu ta ba su wadataccen kuādi, su ka tafi dan hawa Babur ya fita da su zuwa bus top. Daga nan kuma sai su hau motar da za ta shiga da su, cikin garin Zamfara. Jamaāar gidan Malam mai Hula kuwa, a na ta hidimaĀ da shirye shiryenĀ tarbar Amarya, dan Goggo Safiya ta sanar mu su da cewar yau zaāa kawo amarya kuma za su yi buādar kai. Duk an shisshiga makāota an sanar musu. Dan haka gidan ya kasance a cike fam. Sai tsegumi da gulmeĀ gulme ne ya ke ta shi a gidan. Wasu su na ganin baāa kyauta ma Khadija ba, ita data ta so cikin so da begenĀ Aliyu. Mari mai dawo tace.
āAnceĀ tun jiya Khadija ta ke ta faman kuka ko abinci ta kasa ci. Hasiya matar Dauda ta ce.
ā wannan yarinya abun a tausaya mata ne, zaāa hadata kishi da āyar boko, āyar bariki, ga ta rayayyar maraya, kuma anceĀ Babba ce, dan ta girmiĀ Aliyun.ā Nan fa tsegumi ya ci gaba, kaya kaya kawai ka ke ji.
Duk wannan surutun bai hana su aikin su ba. Wainar geroĀ su ke toyawa. Bisa alāadar kauyan RAQUMA, wainar geroĀ ana yin ta ne in ana wani shaāani. Kamar bikin Sallah, bikin Aure, da bikin haihuwa. Sun kāwareĀ sosai wajan iya wainar gero. Wasu kuma suna gaban turmiĀ suna daka dawo ( fura) ma su curata daban, masu sa ta a cikin gari daban. Kowa dai ka ganshi, a cikin aiki ya ke.ā Kāauyan raquma ta gama dāaukar harami, gida a cike yake tab da mata, abokan Ango ma suna waje, suna jira amaryarsu ta iso, su tarbeta.ā
*Mrs Bukhari Ibrahim*
*GAWURTATTU BIYAR,5š¤TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ĘASA..š„*
Ā Ā Ā Ā Ā _Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ĘWAI..š„*
Ā Ā Ā Ā Ā _Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*š„
Ā Ā Ā Ā Ā _Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*š
Ā Ā Ā _Mrs Bukhari_
Ā 5_ *AUREN WATA TARAš©āā¤ļøāšØ*
Ā Ā Ā Ā _Miss Hajo_
ā¦ā¦ā¦..š„š©āā¤ļøāšØš„šā¦.