*GISHIRIN*
Ā Ā Ā Ā Ā Ā *ZAMAN*
*DUNIYA*
Ā Ā _Daga Alākalamin_
_Badiāat Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR š¤š»
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwaĀ ga alāumma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
Kashi na 1
Babi na 9~10
Anas ne ya shigo ābarayin Sadiya shi da Amadi kafinta.
āGoggo wannan shine kafintan kin ganshi, kusan duk kauyan nan shi ke yin aikin kafinta.ā Goggo tace.
āKaga madafiĀ na ke so ka buga mun na langa langa ko da ta can bangaren ne.ā Ta nuna mai dai dai in da ya dace.
āAsaĀ kāofa da abun kullewa a jiki. Amma yau na ke so, ko in ce ma yanzu.ā Amadi ya duba ya ce.
āToh da tsohon langa langa ko da sabo?ā Goggo tace.
āSabon dai zai fi, tunda na Amarya ne.ā Shiru ya dāan yi sannan ya ce.
āNera dubu uku da dāari biyar zaāa biya. Zan buga mata me kyau, kuma na sa har da kuādin abun hawa. Jiya na siyo langa langar, zan yi gyara, amma zan yi muku da shi. Ina gamawa sai in shiga Gusau in siyo wasu.ā Goggo ta ciro kuādin a jakaĀ ta ba shi. A cikin minti talatin ya kammala buga kitchen dāin, har da buga katakai zagayen kitchen dāin. Yanda zaāa iya jeraĀ wasu kayan. Goggo Hansatu ta na tsaye a kitchen dāin ta na jera Ā kaya. Mamaki da alāajabin irin muguntarĀ da dangin mijin yartaĀ su kai ma Sadiya ta ke yi. Domun zaman wannan kāauyan kāayau tashin hankaline ga wanda yai rayuwar maraya. Ta gama jeraĀ komai da komai, kuma duk da haka akwai sarariĀ sosai, kitchen ya yi mugun kyau, sai dai kāasanĀ ba simintiĀ kāasa ce kawai. Kayayyaki da dama baza su yi ma Sadiya amfanin komai ba domun kayan wuta ne. Sauran kayan da su ka rage, Goggo ta dāaga karākashin gado ta zuba mata shi.
******
Khadija ta na tsakar gida sai kuka ta ke ta faman yi. Mahaifinta mai gari ne ya fito tsakar gidan, ganin Khadija na kuka ya sake jagula shi.
āKhadija ke tun jiya wannan kukan bai kāare ba? Na faāda miki kiyi shiru, dole Aliyu ya zaābi dāaya ko ke, ko āyar bokonĀ da aka Aura mishi, amma bazan bari a haāda ki kishi da āyar duniya masu budadden idanu ba. Ina ganin ki yi hakāuri da Aliyu shi zai fi.Domun anci amanarmu, yarinyar shekara nawa ina mishi rainonta, sai ace kuma yanzu anyi mishi aure. Mai dambu mahaifiyaĀ a wajan Khadija, kuma aminiya ga Goggo Asabe. tace.
ā Haba malam baāa gaggauwarĀ yanke kāauna, musamman kāauna irin ta Aliyu da Khadija. Yarinyar nan tun tana yarinya Aliyu ke kula da ita, tun sanda aka ce matar shi ce. AĀ RAQUMA babu wanda bai san son da su ke yi ma juna ba. Kuma ni na tabbatar Aliyu ba zai fifita tsohuwar guxumar da aka ce an aura mishi ba, sama da Khadija. Yana yima khadija wani irin makahon so, kai ka sani malam. Ni gani na ke yi ka bari tukunna Asabe ta dawo in ji meye nufinta, aiĀ yau za su dawo.ā Girgiza kai yayi yace.
āMai dambu hoo. Toh Allah ya kaimu ta dawo dāin. Ni zan fita. Tace.
ā Adawo lafiya malam. Amma za mu je gidan bikin da Khadija inna gama share dāakin tumakai.ā Ya ce.
āGidan watsewaĀ zai yi yau kenan. HauwaĀ da Hajara ma duk sun tambayi anguwa. Toh su kuma tumakan fa?ā Mai dambu tace.
āHamisuĀ ya na gida, baza shi ko ina ba. Har sai na dawo.ā
āSai kun dawoā ya sa kai ya fice. Mai dambu ta kammala duk aikace aikacenĀ da ya dace ta yi na gida. Sannan ta yo wanka. Da kāyar ta lallabāa Khadija sannan ta yo wankan. Mai dambu tace.
āNace ki saki jikinki Khadija, dolen Aliyu ya aureki, kuma dole ki mallakeshi, kamar yanda na mallake ubanki, kema ke ce zaki yi mulki a gidan Aliyu. Kuma ai ke ya ke so kab kāauyannan babu wanda bai sani ba. Ki share hawayenki, in dai nice uwarki, toh hatta Asabe saikin fita iko da Aliyu.
Ā Sallama mai Dambu tai ma abokan zaman ta akan cewar ta fita. Adawo lafiya su ka yi mata. Ficewa su ka yi a gidan.
Khadija ta na tafe sukukuĀ babu laka a jikinta, hankali da tunanintaĀ sam baya tare da ita. Gani ta ke yi, in dai ta rasa Aliyu, tamkar munfashintaĀ zai iya tsayawa ne. Sai dai kuma maganganun mahaifiyarta na yi mata wani irin yawon da yake shirin farfadāo da kuzaranta. Amma sai gabanta ya tsananta fadāuwaĀ da su ka isoĀ kāofar gidan su Aliyu. Abokan shi ta gani a kāofar gidan. Wani kallo ta watsa musu, wanda su kan su sai da su ka sha jinin jikin su.Kuma sun yarda baāa kyauta mata ba, sai dai suna taya abokinsu murnar samun matar birni. Su Goggo Asabe ne su ka isoĀ a kan Babur.
Sadiya
TsaiĀ Khadija ta yi ta na kallo na, wasu zafafan hawaye ne su ka zubo mata. Ni ko kaina na kāasa ba ma a iya ganin fuskata. Maman Amina ce ta ke riāke da ni. Goggo Mariya ce ta nuna ma maman su Amina gidan da za mu shiga. Ina cikin mayafi na ke jiyo muryar wasu maza su na mun sannu da zuwa.
GOGGO
Goggo Asabe da ta ga mai dambu ta ce.
āOhh mai dambu yanzu fa kina raina, niyya ta shine, daga nan in wuce gidanki.ā Khadija ce ta karaso ta faāda jikin Goggo Asabe ta saki kukan da ta ke ta riākewa. Goggo Asabe ta ce.
āāki kwantar da hankalinki khadija. Aliyu dai na ki ne. kuma babu mai raba ku. mai dambu mu je mu daga ciki.
hannun khadija na cikin na Goggo Asabe, su ka kutsa zuwa cikin gidan,
Sadiya
ni kuwa mu na shiga jama,ar biki su ka tarbe ni. Mata an yi cincirindon son ganin Amaryar Aliyu. Nayi mamakin irin taron da aka hadāa na mata. kai tsayeĀ dāakin Goggo Asabe cikin kāuryar dāakinta aka shige da ni. a tabarma na zauna tare da sauke ajjiyar xuchiya na azabar da mu ka sha a hanya. ga zazzabāi da ke ta damuna.Gabaki dāaya babu abunda ke mun dadāi. Hankalina ya kāara tashi matukāa da ganin irin kāauyan da aka kawoni zanyi rayuwar Aure a ciki. Rayuwar da ake mata fatan dāorewa har abada. fatima yayar Aliyu ce ta zauna kusa da ni.
āBarka da isowa Amarya ina miki maraba. murmushin yakāe na yi mata, na ce.
nagode Fatima. Ina yaran su ke?
āsuna kāwar gida, wasa su ke yi. Sallamar su Goggo Asabe ce ta katse mu ni da Fatima.
āshigo mai dambu ki ji kan labari. zama mai dambu ta yi, khadija ma ta zauna.
āmai dambu Bala ne ki na ji ya cuce ni, ya hadāa Aurannan. Allah shine shaida ta bana son wannan Auran. kuma yaronnan nawa ne, daya dawo zaāayi bikin a lokacin da yake a tsaye, ai mijin mata hudu ne kāusar yakāi. Sannan Khadija ce surukar da nake so Aliyu ya kawo mun ita cikin gidannan. Ke mai dambu kinsan irin amincin dake tsakanina dake, babu batun yaudara, asalima dan zumuncinmu ya sake yin dankāone muka hadāa yarannan namu. Ko ba gaskiya ba? Kuyi hakāuri bisa kāaddarar data kunno kai.
Ā mai dambu tace
āmatsalar fa Asabe ita ce. tsakani da Allah baāayi mana adalci ba.babu dattaku a cikin wannan lamarin. kuma mahaifin yarinyar nan cewa ya yi dole Aliyu sai dai ya zabāi dāaya. ko āyar boko, ko khadija. amma bazai haāda su ba. kuma ni kai na inaĀ bayan hakan Asabe. Yarinya dai kun cutar mun da ita. Tunda labarinnan ya isheta take ta faman kuka, hankalinmu ba a kwance yake ba sam.
Goggo Asabe ta ce.
ātunda mu mu ke neman iri, zanje in sami mai garinĀ zuwa da daddare in na wuta. saura kwana biyar yaronnan ya dawo.ā
mukāut na hadāiye wani kakkauran yawu mai dāaci, hawaye sirara su ka surnano mun. na zama abun tausayi. Goggo da kanta ta ke fadama bare cewar cutar ta aka yi da aka aura ma Aliyu ni? yar mahaifina uwa dāaya uba dāaya. Wannan wanne irin kāiyayya Goggo take nuna mini haka?Ā Fatima ta miāke ta fita. ana ta hidimar biki. ni kuwa babu wanda ya sake bi ta kaina. ga zazzabāi ga yunwa, uwa uba kāishin ruwa na ke ji. amma na kasa ko da motsi mai kyau. A mugun takure nake, gashi duk wanda ya shigo sai Goggo ta bashi labarin, a birni sau uku ana sa bikina, amma sabida boko na kasa auruwa, shine aka cuceta aka aura ma kāusar yakāi ni.
Su Amina ne a cikin kasuwar kanawa me suna samaru ta cikin garin Gusau. sun sai duk waniĀ abunda Goggo Hansatu ta ba su sallahu. harda ma wanda su ka tabbatar Sadiya za ta bukāata. hanyar dawowa su ka nufa. sun wahala sosai wujiga wujiga su ka dawo da yamma lis. Goggo Hansatu za ta fito daga bāarayin Sadiya kenan su kuma su na shigowa.
āwayyo yarannan ina ta tunaninku. ga su Sadiya ma sun iso tun tuni. shine zanje in dawo daāita ta shiga dāakinta. ku shiga ku huta, yanzu ma zaāa kira sallah.
fita Goggo ta yi, ta nufi cikin bāarayin su Goggo Asabe. a bakin kāofa ta tsaya ta budāe labulen da sallama tace.
āYaya Asabe kun iso lafiya?ā Goggo Asabe tace.
ālafiyaā Goggo Safiya tace.
ādama yanzu mu ke shirin za mu kawo ta da kin kāara hakuri ba cinye ta za mu yi ba. Goggo Asabe ce ta dāagama Goggo Safiya hannu sannan tace.
ādama zaāa kawo ta. akwai abunda muke jira ne. tunda kun kasa hakāuri zaāa kawota ki je.ā juyawa Goggo tayi. Tana mayar musu da martanin cewar ai ta zaci cinyenin za su yi. ni ko ina dāaki a takure, ina jiyo su. sai wajajen bayan isha. A lokacin na gama galabaita da zazzabāi da yunwa. Goggo mariya ta shigo dāakin da na ke.
āta so mu je Sadiya in kai ki dāakin mijinki.ā da sauri na mikāe, ta na gaba. ina biye da ita a baya har zuwa falon Goggo Asabe. wasu mata na gani da gani Kāawayen Goggo ne. sune su ka rakani dāakina. a falo su ka zazzauna. nasiha su ka shiga yi mun. sannan su ka yi sallama su ka fice.
da sauri na budāe mayafina. ina hawaye Goggo Hansatu ce ta matso kusa da ni. da sauri na fadāa kirjinta nai lamo. kau ta ji jikina da zafi rau. nan hankalinta ya tashi.
āSadiya kin kuwa sha maganinki kuwa, kin ma ci abinci kuwa?
kai kawai na iya girgiza mata dan a mugun galabaice nake. Amina ce ta shiga kitchen ta kunna risho. ruwan zafi ta dāaura mun da zan yi wanka. ina zaune kusa da Goggo. kaina na dāaga na kalli rufin dāakina. lantarki mai yin chaji da hasken rana na gani a manne. kamar kwan wuta ya ke, ya na da haske sosai. kuma ya na rikāe chaji. ajjiyar zuchiya na sauke dan na dāanji sanyi a raina. rufin dāakin na sake kallo inaso in tantance da me aka rufe saman dāakin. naga dai abu bakāi zare zare a jere ras. da kyar na gane igiyar dake cikin video kaset ne wannan bakāin mai dāan fadāi na ciki. Goggo Hansatu ce ta katse mun tunani na da cewar.
āSadiya mu je in nuna miki toilet ki yi wanka. ga shayi ki sha sai in baki magani.ā
mikāewa na yi. na bita a baya. langa langa ta nuna mun ta ce.
āga toilet dāinnan ki shiga ruwan na ciki.ā
to.
kawai na iya ce mata.
na shige toiket dāinnan ya sha plasta ya yi kyau. ga shadda irinta gargajiya mai kāaramin baki. cikin nutsuwa na yo wankan tare da dāauro alwala na fito.
bedroom na shiga dukkansu su na ciki. wadrope dāina wacce ta cika bango guda na budāe. kaya na su na jere reras. doguwar rigar bacci mai saukāi na sanya. turare na fesa a jikin rigar. sannan na yi sallah. Hadiza ta mikāamun tea a kofi mai kauri, dan har kayan tea duk sun siyo mun manyan gwangwamaye.
ahankali na ke sha har na shanye. sannan na sha magani. ina jin su suna ta tabāa hirarsu da ban dariyar jamaāar kāauyannan, yanda su kaita tururuwar zuwa ganin dāakina. ganin hakanne yasa har na dāan sake. a lokacinne na samu damar karema dāakin kallo. iya haāduwa ya tsaru ko a birni dāaki ne na azo a gani.
tabkeken gadoneĀ 6 by 7 fararene kayan katakonĀ sai ratsin gold da ke jiki. wadrope dina babbace mai kofa shida, sannan ga dresing mirror na a gefe harda kujerar zaman kwalliya. labulayen dāakin kuma gold colour ne. haka ma kafet din dake malale a cikin uwar dāakin shima kalar gold ne.
falona kuma kujerune kirar Royal masu kalar gold da ja. manya manya ne sosai daga gefe kuma show glass ce me biyu da abun ādaura tv a tsakiya. show glass dinnan ta sha roses da kiristal masu kyau sai tv na a tsakiya aka ajjiyeshi da video a kāasan shi. kafet ne ja malala a kasan falon haka labulayen falon jajayene masu kyau. falon ba tarkace sam abun shaāawa.
Goggo Hansatu tace.
āSadiya hauro ki kwanta kinji. kuma ya kamata mu bar hirar nan haka nan gobe zaāa dāauki hanyar gida kuma.
koda na kwanta na kasa bacci sam. sai tunane tunane na ke yi. babu abunda ya fi tsaya mun sai zancan Auran Aliyu bayan dawowarshi da wata guda. idanu na lumshe a raina nace.
āyau ni ce a tsakankanin masoya biyu na shigo rayuwarsu ba tare da sun shirya ba. na rusa musu duk abunda su ka jima su na tsarawa. Haka nima duk wani tanadi da tsara yanda zan gudanar da rayuwar aurena, da yanda zan gigita mijina da soyayyar da saina juya mishi kāwakāwalwa, yanxu duk ya kau. Na auri dāan kāauye yaro kāarami.Da wanne idanunma zan iya mishi kallon miji.Ā Shin yama rayuwar kāauyan zata kasancemun?
haka nai ta tunani. sai jefin asuba bacci yai awon gaba da ni.
WASHE GARI
Ā tun sassafe na yi wanka. sanye nake da shadda mai ruwan kāasa. dinkin riga da siket yasha surrani da milk colour dāin zare. dāinkin ya zauna a jikina sosai. kwalliya na yi mai tsari, jikina kuma sai tashin kamshi ya ke yi. takalmi ne mai tsini a kafata milk colour, haka ma mayafin jikina ya kasance milk. Goggo Hansatu tace.
ā su Hadiza su raka ki ku gaisa daĀ ayagin surukarki da matan gida. kafin su dāau haramar tafiya kuma. dubanta na yi nace.
Goggo kema yau za ki tafi?
āAāa Sadiya. zan zauna sai nan da kwana hudāu ranar da Aliyu zai dawo sai in tafi. a kāalla zan dāebe miki kewa.
daādi naji sosai da jin bayanin Goggo.
fita mu ka yi da su Hadiza. mu na tafe ne nace.
Hadiza lallai Bashir yayi kokāari daya barki ki ka zo bikina tun daga katsina. gaki har kauyenmu. dariya Hadiza ta yi tace.
āHaba Sadiya ai muna tare. abinda na ke so dake shine. karki sake kallon rayuwar da ki ka gudanar ta baya. Sadiya abu guda mace take bukāata a rayuwarta shine ta samu kulawa da tausayi a gidan mijinta. in gidan aure ya samu wannan toh magana ta kāare. ni shawarar da zan baki shine. ki kawo walwala da farin ciki gidan auranki. ki gaiyato haske da raha a zamanki da.Aliyu. ke wayayyace kinsan meye makamar dāa namiji. idan ki ka yi hakan zaki samu nutsuwar da sai kauyannan ya zame miki tamkar America.
kai na kadāa. maganarta gaskiya ne.
Hakane Hadiza zanyi kokarin hakan. amma wannan sai mun samu fahimtar juna tare da shi. kinsan yaro ne, dole alāamuran ba za su zo mun da saukāi ba. ni wallahi kunya ma nake ji.
Amina tace
āshi namiji ba ya kadāan. ni mijina sai da na shekara dāaya a hannunshi ba muāamalar Aure. sai dai mu yi wasa da juna kawai. gaban na shi ashe ya na da matsala. sai da ga baya ne ya samu lafiya. amma ba wanda yasan wannan labarin sai ku da na sanar ma yau. shi namiji baāa shekaru bane. kar ki yi girman kai ki je ki shiga wuta a banza.ā
hirar ta mu ta tsaya ne, a sakamakon isowa bāarayin su Goggo Asabe. da sallama mu ka shiga falon Goggo Asabe. duk yayyan Babana su na ciki, da alama tattaunawa su ke yi. gurfana mu ka yi a gabansu mu ka gaishesu da girmamawa. sun amsa a sake babu laifi. kawu Sulaiman yace.
āSadiya. sai ki sake hakuri nan da kwana hudu mu ke sa ran Aliyu zai dawo. ki kula dan baza mu yadda da fitsara irin taku ta āyan boko ba ma su ido a tsakar ka. Aliyu kuma dole ki mai biyayya domun duk shekarunki da matsayinki kin dawo karkashin ikon shi ne. kar kuma ki ji wani iri. bayan wata guda da dawowarshi zaāa dāaura Auranshi. gyatumarki ma ta san da hakan. akwai dokoki da kāaāidoji akan ko wacce surukar gidannan. dan haka za ki iya samun Bilkisu. matar wan Aliyu ta yi miki bayanan daya dace.
A sanyaye na ce.
Toh kawu zan yi hakan in sha Allah.
Su Goggo Asabe a cikinsu ba wacce ta ce da mu uffan. sai daga baya Goggo Asabe tace.
āToh ki koma dāakin ki. magana mu ke yi.
dole na kalato murmushi na dāaura ma fuskata nace.
Toh Goggo.
jiki a mace mu ka fito. mun dāan zazzaga cikin gidan Bilkisu ce tai mana jagora. tare da gabatar mun da surukan gidan. gaggaisawa mu ka yi da kowa. sai dai da dukkan alama ban samu karbāuwa ba sam a wajansu. Dan sai wani hararata suke yi, su nai mun kallon banza haka.
komawa mu ka yi bāangare na. Sallama muka soma jiyowa ta namiji a kāofar bāarayina. Hadiza ce ta fita.
āSannu baiwar Allah, kune kāawayen Amaryar tamu ko? Hadiza da dariya a fuskarta tace.
āEh muneā
Murmushi yayi yace.
āSunana Kamilu, nine aminin Aliyu, tun jiya naso in zo dan mu gana da ku, toh sauran abokan namu suna waje, dama a game da sallamar kāayawyene, bisa ga alāada.ā
Hadiza tace.
āHakane, sai ku bayar da duk abunda ya sauwakāa, jiya ma baku kawo mana abinci baā kai Kamilu ya sosa.
āEh ayi mana afuwa, sai yau na gama harhadāo kan abokan, Amma ga abun kari.ā Hannu tasa ta amsa, leda ce mai dāauke da gasassun zabi, sai robar fenti cike da tea, wanda sai da Kamilu ya fita zuwa cikin zamfara ya siyo kayan tean. nera dubu biyar ya mikāama Hadizaā
āGa wannan ayi hakāuri, abun yazo mana babu shiri.ā
āAh babu komai mun godeā ciki Hadiza ta dawo ta kawo mana kayan kari, tare da yi mana bayanin yanda su ka yi da Kamilu. bayan sun gama karyawa, sun yi wanka. sai kuma su ka fito dan tafiya.
ina kuka mu ka rabu da su. tare da mun alākawarin za su kewayo ni.
Goggo ce ta riāke hannuna mu ka koma ciki. kan gado na fadāa ina ta kuka amma mara sauti.
wai wanne irin matsalolin zan fuskanta ne a wannan zaman Auran?
mrs Bukhari ce