𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣
Babban gidan sama ne mai dauke da bangare biyar, na farkon da na biyu zuwa na uku da hudu sukansu suna facing din babban gate din gidan. Yayinda dayan wanda shi ne na biyar yake dama da part din hudun, dukannin part din suna da karamin gate da zaka iya hango wanda zai shiga ko ya fita, haka zalika ko wane part yana da gurin aje mota kamar uku sai kuma karamin filin da za a iya wata hidimar idan da bukata. An kawata kowane entrance na parts din da fulawowayin na kasko, a ko wane bangare akwai kujeru da aka tanada domin hutawa ko shan iska.
Babbar harabar gidan wani katon fili ne da za a iya gina kananan gidaje hudu ko biyar, ko wace kusurwa da ginin na jikin gidan an dasa masa dagayen itatuwa, tsakiyar compound din kuma an yi masa round da flowers. Ko masu gadin gidan kadai ka kalla ka san ba kananan kudi suke samu ba, balle kuma ka sauke idonka akan manyan motoci da aka jere a harabar da aka tanada domin aje motocin Alfarma, bayan mota biyu wasu daya wata uku da suke aje a kowane bangaren uku da suke gidan.
End of discussion shi ne sunan da mafi akasarin jama’ar unguwar suke kiran gidan da shi, ba a unguwar Millions Quarters ba kawai, kusan duk wanda yake cikin garin Gusau ya san gidan Alhaji Haruna Mai Yadi, saboda yadda jama’a suke yawan labarin gidan da irinsa a rare a garin Gusau. Kasancewar ba kowa yake damuwa ya gina gida mai kyau da fasali kamar yadda shi ya zabi ya bayyana nashi arzikin ba a fili ba.
A cikin part hudu da suke gidan uku ne suke dauke da iyalai yayinda dayan da ya banbanta da saura kuma ya kasance na Alhaji Haruna Mai Yadi, part din farko na Hajiya Kaltume ne uwargida ran gida, wato Uwargidan Alhaji Haruna a yanzu, sai mai bi mata Hajiya Nafisa da ake kira da Momy, sai ta ukunsu wadda ta zama turmin tsakar gida hausawa suka ce sha luguden mahassada wato Hajiya Iyami ake kira da Amma. Dayan part din wanda shi ne cikon na hudu, part ne da ba a taba zamansa ba, kasancewar matansa uku ne a yanzu tsabanin hudun da ya ci burin yi.
A kowane part akwai dakin yara na maza dabam na matan dabam, akwai sitting room har biyu karami da babba, sai bedrooms din ko wace mata dake dauke da mayan furnitures na alfarma, dukannin furniture din parts din iri daya ne sai dai kala ta banbanta. Na dakin Hajiya Kaltume red color ne tun daga kan kayan dakin kujeru har zuwa curtains dinta, sai dai an yi musu ado da ratsin golden hakan ya kara musu kyau gashi yaranta na taya ta gyara bangarenta kasancewarsu yan mata masu wayo da son kwalliya domin yan matanta hudu, Umm Kultoon wadda ta ci sunan mahaifiyarsu ake kiranta da Maama, sai mai bin ta Umm Salma, Umm Khairi, da kuma yar auta Umm Ruman, sai dai dukansu suna bin bayan babban ďanta Yassar ne da ya kasance namiji daya tilo a yayanta.
Bangaren Hajiya Nafisa kuma wato Momy ta kawata nata bangaren ne da ash color, white curtains dinta ne kadai suka banbanta da Turkish cushion din da suke falon ita ma tana da yaya uku mazanta biyu Musib, Miwan sai auta mace Namra.
A dayan part din kuma wanda ya kasance na Hajiya Iyami wato Amma ya fita dabam da sauran dakunan domin komai nata na daki da falo fari ne fol, irin farin nan mai kyau da burge idon mai kallo, duk kuwa da kasancewar nata yaran kanana ne Hurriya sai mai binta Hamad sai kuma cikin da take dauke da shi a yanzu, ita ce karama a cikin matansa kana kallon Alhaji Haruna ka kalleta ka san ya kusa haihuwarta ko ma ace ya haifi kamar ta.
Bayan wadannan iyalan Alhaji Haruna Mai yadi yana da wata yar da ya haifa da matarsa ta farko mai suna Maryama, sun yi zama a tare tun a lokacin da yake amsa sunansa na Haruna Mai Yadi, kusan duk wata wahala da fadi tashin rayuwa tare da ita aka yi, kamin daga bisani ya auro Hajiya Kaltume wadda ita ce uwargida a yanzu sakamakon rasuwar da uwar yarsa ta farko ta yi wato Sapna wadda take a gidan aurenta a yanzu, sai dai kulawarta da ta mijinta duk yana karkashin mahaifinta ne, abun da hausawa ke cewa an siyar da akuya ta dawo tana cin danga, domin an aurar da ita ne ga talaka kuma a lokacin da mahaifinta yake talaka kamin arzikin ya bude masa, hakan ya saka a yanzu gidansa ya cika da ƴaƴan yan’uwansa da na yan’uwan matansa.
Daga uwargidansa mai rasuwa Maryam har Hajiya Kaltume irin matan nan da ake cewa auren fari auren talauci, ya auresu sun kamin yayi arziki ba tare da duba kyau hallita ba, kyau hali dai abu ne da yake a bayyana domin uwargidansa ta farko da kuma Uwargidansa ta yanzu basa ga maciji da juna, basa da aiki sai yawan fitina da fada da juna, har Allah ya dauke rayuwar Maryamu.
Arziki kashi inji hausawa, bayan rasuwarta ne Haruna mai Yadi ya fara samun daukaka kofofin arziki suka bude masa gabas da yamma, a cikin lokacin ne ya auro Hajiya Nafisa yar mai gidansa, kasancewarsa mutum ne da ba shi da ra’ayin zama da mace daya, ba laifi tana da nata kyaun kuma ya dauko mace yar gidan mutunci da karamci sai dai ko kadan albasa ba ta yi halin ruwa ba, domin tana zuwa gidansa ta fara yi masa gorin arziki duba da nata mahaifin ya ninka Alhaji Haruna Mai Yadi kudi ta ko’ina, a lokacin da ya auro ta nasa arzikin be kai kamar yanzu ba, abu kadan idan aka taba ta sai tace ita yar Alhaji Garba kudi Kasa ce, hakan yana daya daga cikin abubuwan da suke yawan hada ta fada da Hajiya Kaltume da kuma Mijinta Alhaji Haruna, domin tana yi ma Hajiya Kaltume gorin arziki Hajiya Kaltume kuma tana mata gorin anga mijinta da kudi an aure.
Ta bangaren Alhaji Haruna kuma ba sha da dadi a hannunta domin so take komai sai ya banbanta mata da Hajiya Kaltume saboda ita yar masu hannu da maiko ce, shi kuma a gurinsa yana ganin hakan kamar rashin adalci ne, kuma be yarda ya aikata abun da zai hana shi zaman lafiya bayan mutuwarsa ba. A haka dai aka yi ta zaman da dadi ba dadi har Allah ya kara buda masa ya tashi daga Alhaji Haruna Mai Yadi zuwa Alhaji Haruna Mai Motoci. Duk wanda ke garin Gusau ya san Mai Yadi Motors a ciki da wajen Zamfara, domin babban kamfani ne mai kawo manyan motoci na zamani, ba a iya nan ya tsaya ba, ya raba hannu ta bangaren shigo da kayan masarufi da gine gine na zamani a garin Gusau, Kaduna da kuma Abuja. A lokacin da ya zama cikaken mai kudi ne Hajiya Kaltume ta nemi daukar masu yi mata hidima ta komai a gida miji, domin Momy da nata masu aikin ta zo tun daga gidansu tsabar nuna isa da gata.
Sai dai ko kadan surukarta kuma mahaifiyar Alhaji Haruna Mai Yadi bata so haka ba, Wato Hajiya Binta, Hajiya Kaltume har Momyi ba su saurareta ba saboda rashin ganin kimarta da girmamata, ita ma kuma tana taka tsantsan da matan ďan nata gudun kar suce ta shige musu hanci domin mace ce mai gudun fushi da kiyayyar zuciyar kowa. Wannan ya saka a lokacin da Allah ya buda masa ta nemi yayi mata nata gidan dabam, ta zauna tare da nata yayan idan sun zo da kuma jikokinta. Balkisu ce farkon mai aikin da aka fara kawowa a gidan a bangaren Hajiya Kaltume, Balkisu yarinya ce mai tsabta da iya aiki ga far’a da son aiki, hakan ya saka Hajiya Kaltume ta riketa da kyau ta sakar mata ragamar komai ciki har da kula da yayanta da kuma girka abincin mijinta. Daga lokacin da ta karbi girki komai ya canja ko yaranta sai da suka yaba da canjin da aka samu domin Balkisu wadda ake yi wa inkiya da Iyami tun tashinta yarinya ce yar zamani ce da ta san kan kalolin girki da ďanďannonsu, shi kansa Alhaji Haruna sai da ya yaba da girkin sabuwar mai aikin tasa tun kamin ya yalla idonsa a kanta.
A lokacin da idonsa suka yi arba da ita kuma sai kimarta da kwarjinta suka karu a idonsa, kasancewarta kyakkyawa mai kurciya fiye da matansa ga jiki daidai ba mai ƙiba da baƙi kamar Hajiya Kaltume ba, fara doguwa ba guntuwa da kiba kamar Momy ba, jikinta be yi yawa ba kuma be yi kadan ba, yar bulbul da ita, haskenta mai kyaun ne cikin ma bata samu hutu da jindadi ba.
Ga tarbiya da girmamawa idan zata gaishe shi sai ta kai har kasa, idan ya bata abu hannu biyu zata saka ta karba, da haka ta fara siye zuciyarsa har ta kai ya fara ninka albashinta kamin ya fara nuna mata alama, daga baya kuma ya fito fili ya fada mata burinsa bayan ya san komai a akanta.
Tsoron Hajiya Kaltume da duban level din arzikinsa da nata ba daya ba, ya karya mata guiwa gurin amsa masa bukatar da ya zo mata da ita. Sai dai kuma rabo idan ya rantse dole komai sai ya afku, rabon samun Hurriyya da Hamad da kuma karamin cikin dake jikinta ya saka Alhaji Haruna yayi nasarar lurar da ita cewar tana cikin irin matan da yake so tare da nuna mata shi ma a da can talaka ne kamar ita, kuma a yanzu zai saka zane ya tare duk wata ƙura da zata taso.
Kwadayi irin na talaka ya leka gidan mai arziki da kuma burin son taimakon iyaye da samun rayuwar jindadi ya saka Iyami ta amince da bukatar Alhaji Haruna. Sai aka shirya auren a boye sai bayan da da Hajiya Kaltume ta tafi Ummara sannan aka daura auren, Amarya ta tare da Mahaifiyarsa Hajiya Binta, daga lokacin ne sunan ya tashi daga Iyami wanda ta taso da shi tun kirciya ya koma Amma domin a lokacin ta wuce ƴaƴansa su kirata da sunanta Iyami dole su sakaya saboda mahaifinsu.
A lokacin da Hajiya Kaltume ta dawo sai zaman lafiya ya gagari Amma da mijinta saboda fitina irin ta Hajiya Kaltume da gori da wulakanci saboda tana ganinta yar aikinta, gashi kuma Momy ma da take ganin kamar ita aka yi kishiyar bata raga mata, ba ita kadai ba kusan duk wanda ya san ta yi aiki a gidan kuma ya ji ta aure mai gida zai jefeta da kalmar cin amana.
Wannan abun ya tabata matuka sai dai samun Hajiya Binta wato mahaifiyar Alhaji Haruna ya wanke mata rabin damuwarta domin tana sonta fiye da yadda take son abokan zamanta Hajiya Kaltume da Momy, domin Amma tana yi mata biyayya gwargwadon hali, ta dauke ta tamkar uwa da ta haifeta, ta rike da mutumci abun da sauran matan suka gagara yi mata. Tana jin dadi zama da ita kamin Hajiya Kaltume da Momy su ta da fitinar cewar sai dai ya hade su guri daya, suna ganin kamar ita Iyami da ya ware dabam ya hade da mahaifiyarshi ya fi bata jindadi fiye da su, hakan ya saka shi gina babban gida a unguwar Millions Quarters cikin rukunin manyan gidajen da ake ta gasar ginawa a unguwar.
Na shi gidan ya fita dabam saboda kyau da tsari da aka yi ma katon gidan. Bayan haihuwar Hurriya Alhaji Haruna ya tare a gidan tare da Iyalinsa, a lokacin Amma tana da tsohon cikin Hamad, bayan tarewa gidan da wata daya ta haifo ďanta Hamad mai shekara goma da daya a yanzu, tun daga lokacin kuma sai haihuwar ta yi mata shiru tun tana damuwa har ta daina, ta rumgume yayanta biyu da Allah ya bata Hurriya da Hamad. Amma ba mace ce mai yawan shige shige ba wannan ya saka a duk lokacin da aka ce ta nemi taimako sai ta ki, domin bata san gurin waye zata duka ta tara hannu ya bata magani ba, sai Allah.
A yanzu kuma da Allah ya tashi bata haihuwar sai ya kawo cikin na uku daman da kurciyarta a yanzu ne take cin nata lokacin ba kamar abokan zamanta da mijinta da suka bata kusan shekara goma sha biyar biyar ba, mijinta kuma ya bata kusan shekara ashiri. Domin yarta ta farko Hurriya a yanzu tana da shekara goma sha biyar ne, a yayinda ita kuma take da shekara goma sha shida da auren a gidan Alhaji Haruna Mai Yadi wanda shi ne mijinta na farko. Hajiya Kaltume da Momy kuma duka last born dinsu shekarunsu goma sha bakwai ne a yanzu. Iyami ta sha wahala sosai a gurin abokan zamanta na makirci da tukgu irin na kishiyoyi, yarta Hurriya kuma ta sha wahalar yan’uwa wadanda suke uba daya tun tana karama har girma, suna yawan hantararta da gori ga duka kamar ita din ba ďaya take da su ba.
Hurriya kyakkyawa ce sosai irin kyau nan mai matukar daga hankalin wanda ya san kyau da sirrin kyau, irin kyau da ke shiga cikin ido ya afka a kwakwalwa ya zauna a zuciyar mai yinsa, irin kyau da idan ka kalleta sai ka sanar da zuciyarka tabbas tana da kyau, irin kyau da sai bakin ya bawa dan’uwansa labarin kyauta, ko kadan bata dauko mahaifinta a baki da muni ba, domin kowa ya san Alhaji Haruna ya san ba kyakkyawa ba ne, wasu har kirari suke masa ba dan kudi ba da sai bola, shiyasa a lokacin da aka yi aurensu da Iyami kowa yake cewa ta bi kudi shi kuma ya bi kyau. Hurriya mahaifiyarta ta dauko sai dai ta dara mahaifiyarta kyau nesa ba kusa ba, ta fita haske ta fita komai hakan ya saka ta fita dabam kamar ba yar gidan ba, domin yaran Momy ma da suke da kyau ba su kai Hurriya kyau ba balle kuma yaran Hajiya Kaltume da suka dauko ta wasu kuma suka biyo mahaifinsu, ba laifi suna da nasa kalar kyau, domin ko wace halitta ta Allah kyakkyawa ce.
Duk tarin kyau da haibar da Hurriyya take da shi tana da wata lalura da aka haife ta da ita ta rashin gani, bata iya tantance komai sai da gilashi, idan babu gilashin ido a tare da ita wato medical glasses bata iya banbance fuskar kowa sai dai ta yi amfani da murya, tana iya ganin abun da ke gabanta ko gefenta haka ma ta kan iya banbance mace da namiji ta hanyar sifar da tufafin jiki, sai dai ba zata iya fadar yadda fuskarsu take ba, domin dishe-dishe take gani, kusan eyeglasses shi ne rayuwarta bata iya komai sai da shi idan yana a idonta tana ganin komai clearly kamar yadda kowa zai gani ko ma fiye da haka, idan kuma babu bata iya karatu bata iya ganin kyau ko munin mutum, hakan ya saka bachi kadai ke rabata da gilashi.
An nema mata magani har an gaji amman babu sauki babu alamarsa, wani gurin ma a madadin samun sauki sai idon ya kara dishewa, tsoron kar ta rasa idon gaba daya ya saka aka daina nema mata magani Alhaji Haruna ya saka likita kwarare ya duba idonta ya fadi kalar gilashin da zai dace da ita mai kyau da tsada, mahaifinta ya saka aka kera mata har guda biyar a lokaci daya.
Biyu daga cikin gilasan da mahaifinta ya saka aka kera mata ne suke hannunta, sauran ukun suna gurin Yayanta Yassar ya aje mata a bangarensa gudun kar su bata, domin tasu ta zo daya shi kadai ne take jin sanyinsa a cikin Yayan Hajiya Kaltume ya ke sonta da nuna mata kulawa tsakani da Allah kamar kanensa da suke uwa daya uba daya, Yassar kam ya fita dabam kusan ya fi sabawa da Hurriya ma fiye da sauran yara da suke gidan, yana sake mata fuska tana wasa da shi kamar ita da shi din abokan wasa ne. Idan yana gidan bata da hutu ga tsokanarta da yake yawan yi. Yassar yaro ne mai mutunci da kamanta gaskiya, domin yana ba wa Amma da Momy dukanin girmansu sam baya biye hudubar da mahaifiyarsa take masa, be taba yarda ya hau turbar da take dorashi ba, Munib da Miwan suke kan gaba gaba gurin taya Momy kishi dama da hagu har sun fi yar’uwarsu maace taya mahaifiyarsu kishi.
*** *** ***
Wannan Kenan, shimfida ce da share fagen yadda labarin zai tafi, labari ne mai ƙayatarwa da sarkakiya da kuma ƙulla-ƙulla sannan yana dauke da darasi na rayuwa. Allah ya sa mu amfana da shi kuma ya ba ni ikon gamawa lafiya kamar yadda na fara. Sannan ina son ku sani labarin nan ban yi shi dan wani ko wata ba, idan ma ya yi daidai ko ya ci karo da rayuwar wasu, to arashi aka samu. Tare da fatar za ku tara hannu biyu ku karɓa kamar yadda kuka saba karɓar labaraina cikin farinciki da ɗauki, sai a taya ni da addu’a na baku abun da kuke so, ma’ana na faranta ranku fesss 😀