Zafin Kai Chapter 6

This entry is part 6 of 6 in the series Zafin Kai by Mamugee

6

Anne data fisu jiqata sbd ba zato tana barci taji saukan masifar tako ina gashi daman bata da lafiya kasa kuka tayi sai wani wahalallen numfashi datake saukewa tana daga kwance kanta na juyawa,

Sumayyah ma kusan kaman a sume take dan bata iya jan numfashi daidai cikin tsananin firgici da azaba take koina nata rawa yake ta qame guri daya idanuwanta a kafe da tsananin tsoron da tashin Hankali ina safnah ta gudu ta tafi tabarsu cikin masifar barnar data aikata dan kuwa har ranar da Allah zai yanke musu wannan wahalar sune zasu ringa azabtuwa da hukuncin wannan abin data aikata.

Benazir kuwa data fi sumayyah da Anne dakuwa sbd kusan itace ta ringa hawa samansu sbd dukan ya fi sauka akanta,bakinta jini yakeyi sosai ga gefen fuskarta ya kumbura a take kaman wadda mashin ya kade,

Wasu hawaye ne masu dumi da bayyanarda radadi da ciwon dayake cikin zuciyarta suka gangaro daga cikin idanuwanta ta rintse idanuwan a hankali tana kasa cewa komai dan kuwa a yanzu qaddararsu ita da ‘yar uwarta da mahaifiyarsu ta sauya ne zuwa wani yankin azabar da zatace safnah itace mummunar sanadin sauya musu rayuwa zuwa wata sabuwar wahalar da basusan inda zata kaisu ba.

Shiru dakin yayi tsit babu motsin kowannensu sbd babu mai iya maganar ko abin cewar,

Har tsakar dare kowannensu na makure a inda yake batareda sun motsa ba.

Rawar da kakkarwan da jikin Annensu keyi sosai yasa Benazir da jikinta yayi tsananin tsami motsawa ta isa gurinta da qarfin hali sbd bakinta itama ya kumbura ya sauya kamanni sosai,

Kamo Annen tayi taji jikinta yayi wani irin zafi mai tsanani

Numfashi ta sauke a kasalance sbd rashin sanin abin yi amma kuma ko yayane dole zata rage mata ko zafin jikin ne dan haka ta miqe da qyar ta dafe cikinta dayasha harbi da qafafun Ababa din tana takawa ahankali ba kuzari ta fito ta debo ruwa a roba ta dawo ta zauna gefen Annen tafara goge mata jikinta da fuskarta da itama yaji mata ciwo gurin dukan.

Sai data gama goge jikin Annen taji sumayyah itama jikinta yayi zafi sosai har taja jijjiga dan haka itama ta dawo kanta ta ringa goge mata jikinta tana rungumeta sbd sumayyar tafi Anne jigata gashi daman rauninta yafi na Annen.

Daqyar benazir din tasamu jikin sumayyah ya dena fizga tana neman sumewa,

Kwantar dash tayi ta rufe kowannensu sbd baccin wahala dasuka samu ya daukesu.

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke a hankali tareda jinginar da bayanta jikin bango taba cusa kanta cikin qafafunta daga zaunen tana rintse idanuwanta sbd itama wani azababben zazzabi da tsamin jiki takeji mai radadi amma batada mai dubata bare bata kulawa dan haka a hakan baccin wahala ya dauketa.

Da sassafe itace tafara tashi tafara duba jikin nasu kafin ta miqe daqyar sbd jiki daya qara tsami ta fito tayi alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta tada Sumayyah da itama jikinta ke tsananin ciwo da tsami ta fito daqyar tayo alwala tazo tayi sallar suna idarwa suka fito dan ayyukan dasuke dole akansu.

Da Ababa suka fara cin karo ya fito cikin farin yadi fuskarsa a hade tsaf babu sakewa bare rahama,

Da sauri dukkaninsu sukai qasa suka gaishesa cikin girmamawa da ‘da,a mai tsanani kansu a qasa.

Ko kallonsu baiyiba ya wuce kai tsaye dakinsu ya fada bai tsaya komaiba ya damqo Annensu dake zaune tana rarraba ido cikin azaba ya fara janta ya fito da ita yana cewa

“Zamanki a nan ya qare sbd daman na fada muku tana bayyanarda haukarta ta gama zama a nan bolar mahaukata zan kaita tabi mahaukata yan uwanta can su qarata a bola bola”

A tare Benazir da sumayyah suka zube qasa gabansu suna wani irin hawayen mafi munin tashin hankali suna rokonsa akan karya rabasu da mahaifiyarsu.

Ko sauraronsu baiyiba sbd basu kai matsayin da zaiji ko rokonsuba, sake jan uwar tasu yakeyi wadda take riqe Benazir da qarfi kaman ranta duk da hankalinta bai gama dawowa daidaiba dika tasan su din yayanta ne da bazata iya rabuwa dasuba ba koda zaa rabata da ranta ne tafison a rabata dashi a tana tare da su.

Sumayyah kuwa a neman rasa kanta takeyi sbd itama qwaqwalwan tata neman juyewa takeyi da uwa da ake kokarin rabasu da ita dan haka ta dunqule guri daya tana kasa motsawa sai fizga da kanta keyi.

Benazir data ke neman zaucewa itama kuka ta fasa mai qarfi tareda rarrafawa ta riqe qafafunsa tana rokonsa cikin qasqantar da kai tana masa Alqawarin yin duk abinda yakeso na ‘yan uwanta dasuka tafi samirah da safnah indai zai bar musu Annensu koda bangaren dabbobinsa ne sun yarda zasuyi duk abinda yakeson harda nasu safnah data gudu da samirah data rasu.

Da farko dakatawa yayi sbd dama baida niyar yafewa ko bata fada ba daman rabonsa na sisi da kwabo akanta da sumayyah zai fanshe harna samirah da safnah.

Hande da sai alokacin ta fito ta kalli su benezir din da uwarsu kafin ta maida kallonta kan Ababa daya tsaya lissafin yanda zaiyi amfani da Annesu ya juya rayuwarsu yanda yakeso hankali kwance koda kuwa karuwanci ne indai zai fanshe kudinsa akansu.

Hande kuwa tana kallonsa tace

“Kai yanzu Abubakar Tinanin me kayi daka yanke shawarar korar Benazir bayan kasan matuqar ka koreta rubatacce ne guduwar ‘yayanta daga gidan nan dan kuwa koda namansu zaka yanka ka tsaga qashinsu ka saka musu kwado da kaca ka daure wlh matuqar sun san uwarsu na can tana yawon bola wlh sai sun gudu sun nemota kaga kuwa asarar dai da kake gudu itace zata bika dan haka maza ka sauya shawara ka barsu da uwarsu idan kanason zamansu a qarqashinka itace jigo”

Shiru yayi tabbas yasan ko zai kashesu ya binne bayan rabasu da Annensu sai fatalwarsu ta fita nemanta musamman Benazir,

Sakin Annen yayi tareda saka qafa yayi ball da ita yana sakin hucin bacin rai ya kalli benazir data sauke kanta kasa tana kallon yanda yasa qafa yayi ball da mahaifiyarta.

Mahaifiyarku itace a tafin hannuna ku sani daga yanzu ko kofar gida wani a cikinku yakuma kalla da wani nufin guduwa wlh tallahi uwarku ce zataji a jiki da jininta.

Qafa yasa ya take hannuwan Benazir din dake gabansa ya wuce yabar gidan yana cewa Hande kar wanda aka bawa abincinsa sai washe gari.

Yana fita Benazir ta rintse ido tareda zubewa zaune hawaye na tsiyayo mata mai zafi da radadi dan kuwa tabbas akan Annensu babu kalar azabar da bazasu iya jurewaba.

Hande Annen tasu dake kwance ta kalla tareda nufarta ta kamata ta tayar tsaye saidai bata iya tsayawa

Kallon Benazir data kasa motsawa sbd nauyin zuciya tace”

Kizo ki kamata kuyi ciki baqi zanyi kada suzo su sameku anan ku ja mana abin magana asan kiwon mahaukata mukeyi a gidan.

Bude idanuwanta da sukai jajir tayi ta tareda miqewa ahankali tazo ta kama Annen takai daki ta dawo ta kama sumayyah da itama kanta ke neman juyewa takai daki bata tsaya musu komaiba dan batasan me zatai taimaka musu dashi ba dan haka ta fito tahau ayyukan gidan datasan wajibinsu ne yinsu kuma sumayyah bazata iyaba a halinda take ciki.

Sai magriba ta gama ayyukan dasuka saba yi su biyar harda Annensu a baya amma ayau ita daya ce tayi aikin dan haka koda ta gama ta dawo dakinsu tayi sallar magrib da ishai kwanciya tayi gefen sumayyah da har lokacin take kaman bata dawo hayyacinta ba.

Washe gari daqyar ta iya ayyukan gidan tasamu aka basu abincinsu ta kawo daki suka rufa su ukun suka cinye batareda ko wannensu ya koshi ba dan haka gurin wanke wanke wanda Ababan ya rage ta kawowa Annensu ta qarasa cinyewa ta koshi ita kuma sumayyah wanda Hande ta rage ta kawo mata itama ta qarasa koshi.

Washe gari ma haka itace tayi ayyukan gidan sbd har lokacin sumayyah bata gama dawowa daidaiba.

A cikin kwana biyu ta qarasa zabgewa sbd wahala da rashin bacci ga damuwa da tinanin da yayiwa rayuwarsu daurin minti.

*********A hankali sumayyah da Anne suka warke suka dawo daidai

Annensu ta dawo saidai kaman batai haukar kwana biyu ba tadawo yanda take saidai kullum cikin fargabar kada ciwon ya sake tashi suke dan haka suketa kokarin hanata tina su Samirah da safnah suka dage suka maye mata gurbinsu batareda bata dama ko kankanuwa ba ta tinasu dan sai saukin haukan yazo mata da mantuwa mantuwa kwata kwata sai tana mantawa da basu biyun ne kawai yayanta ba sai can lokaci lokaci tace ina samirah?ina safnah?

Data fara maganarsu da sauri suke dubarar dasuka mantar da ita zancen sbd kada ciwonta ya tashi komai ya lalace musu.

A yanzu rayuwa tayi musu wani irin juyi zuwa mafi wahala da ukuba sbd wahalarsu tafi yawa a yanzu da suke iya su biyu kawai,

Ababa a yanzu Annensu itace mukullun daya kama na juya rayuwarsu yanda yake so sbd yagama gane itace kawai abinda zai kama yace su fada wuta su fada batareda tinanin komaiba,

A yanzu daya dauki wannan tsarin sai haukarta dake hawa tana sauka tayi masa daidai,

Ya zauna ya tsara sabon lale ga rayuwarsu gabaki daya ta hanyar miqasu ga auren jari ga wasu dilolin miyagun qwaya da masu safarar mutane da ya samu amma sam hadin bazaiyi ba saiya wadatar dasu da ilimin boko mai dan zurfi dan haka kai tsaye ya fidda kudi aka nemar musu gurbin karatun diploma wanda yafi wata yana lissafin kudin dazai kashe kafin yakai ga maida kudinsa yana jinjina maqudan dukiyar da zai samu daga manyan dealers din na qwayoyi da akace suna sakarwa matayensu da iyayen matansu.

Ita benazir kai tsaye Wani hamshaqin drugs dealer dake zaune a lagos da qasar Germany ana tallata masa hotonta yace ya amsa aurenta sbd dari bisa dari tayi masa dan haka ita take yafara yiwa Ababa barin kudi dan haka koda Ababan ya dawo dag lagos ita take aka sauya mata karatun da zatayi zuwa degree.

Cikin saa Tana rubuta jamb taci Admission dinta bai wani zama wahala ba sbd komai acikin saa ta rubuta taci.

Sumayyah ma kusan komai nata ya kammala itama Aminin Ababan Alhaji Sadau shine ya gabatar musu da komai aka jira lokacin fara karatun nasu.

A rayuwar quncin da suke ciki babu abinda ya sauya saima qaruwa sbd duk ya kallesu a yanzu tsagwaron dukiyarsa yake musu kallo dan kuwa kudin daya kashe a shigar dasu makaranta jin yake idan kudinsa basu dawoba ko qasar qetare sai yaje ya nemo masu siyan bayi sun siyesu an basa kudinsa.

Tsananinsa akansu ya qaru fiyeda ko yaushe sbd wasu irin dokoki da tsananin daya dora musu akan ko kallon wani namijn sukai a waje wallahi saiya maidasu makafi dan babu wadda bai gama jingar aurentaba ga wainda zasu maida masa asararsa.

Maganar kula kowane irin namiji a waje ko makaranta ya tsayar dasu ya maimaita musu kusan fiyeda yanda yake maimaita musu qiyayyr dayake musu,

Daga qarshe yayi musu alqawarin binne uwarsu da rai duk ranar dayaji koya gan dayarsu tareda wani.

Hankalinsu tashi yayi da maganar dan kuwa sai tsoron karatun gabaki daya ya shigesu sukaji basa shaawa musamman daya shimfida sabuwar dokar duk wahala da aikin gidan akan uwarsu zai koma duk suna fita harsai sun dawo.

Chapter 7

Wani babban tashin hankali mafi tsoratarwa da Benazir ta shiga bayan wasu shekaru shine fara lura da sumayyah data fara samun ciwon qwaqwalwa kaman Annensu sbd lokuta da dama haka zata zauna tayi shiru ta qurawa guri daya ido tana magana a hankali kokuma ta ringa kuka a hankali tana kiran sunan Ababa dana samirah sbd Safnah haka kawai Allah ya cire musu ita cikin ransu sbd abinda tayi din kafin guduwarta wanda kuma guduwar naya ya sake tsanananta musu komai daga gurin Ababa din.

Azabar dasuke ciki da qunci yayi nasarar taba qwaqwalwanta kaman mahaifiyarsu,

Wace qaddara mai girma ce wannan ta hau kanta?

Tayaya zataji da wannan masifar?

Ya zatayi da sumayyah din?

Tayaya zata ringa boye wannan lamarin?sbd komai tsananin tsanani bazata iya bari Ababa ko hande su san da wannan sabuwar qaddarar ba sbd Ababa komai zai iya aikatawa akanta sbd ganin itama tamkar wata asarar ce zaiyi na dukiyar daya kashe akanta.

Zubewa tayi tsakiyar dakinsu ta fashe wani irin kuka mara sauti dayake yankan kirjinta sbd tausayin kanta danasu sumayyah da Annen,

Inama itama zata haukace gabaki daya ta yanda zata dena jin radadi da kuncin dayake ranta ta manta komai.

Sumayyah dake zaune shiru tana magana ita daya a hankali ganin benazir din a hakan yasata tasowa ta dawo gurinta tana rungumota muryarta a hankali ba kuzari tace

“Benazir kuka kikeyi nima na fara samun matsala ko?

Karki damu nima mutuwa zanyi idan na mutu komai zaizo miki da sauki zaki iya samun damar dauke Anne ku tafiyarku ko bara kuyi zakuji dadi a gaba insha Allah…

Girgiza kai Benazir tafara hawayenta na tsananta gudu bata iya cewa komai sbd matukar Sumayyah ko Anne a yanzu ta sake rasa daya itama nata lokacin na zaucewa tayi.

Hawaye ne suka gangarowa Sumayyah ta sake rungume Benazir din jikinta cikin rauni da mutuwar jiki tareda sarewa tace”

Benazir nima banason na haukace ko na mutu amma da alama kaddarata ta haukacewan kafin mutuwar a kusa take,

Kuka mai sauti Benazir ta kasa riqewa ta fashe dashi tana cusa kanta cikin tafin hannuwanta dukkanin zuciyarta na karyewa dan Allah ya sani a jininta da tsokan zuciyanta take jin Sumayyah,

Itace qanwa sumayyah din ce yayarta amma a gareta kaman sumayyah din ce qanwa sbd jin takeyi alhakin kulawa dasu a ynzu duka a kanta yake.

Ita kanta sumayyah kukan mai sauti ta sake tana yin qasa da kanta sbd sanin lalura zasu zamarwa Benazir itada Anne dan haka har cikin ranta take rokon Allah idan zata zamewa Benazir ‘dinta da Annensu kaddara mai wahala da nauyi Allah ya dauki ranta ta huta.

Kaman Benazir tasan adduar da Sumayyah din keyi ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Sumayyah kafin ta kalli Annensu dake gefe tana kallonsu cikin tsananin kukan da itama take rokon Allah ya dauki ranta idan har ‘yayanta zasu samu ‘yancin guduwa daga ukubar mahaifinsu su samu kyakkyaqar rayuwa a waje.

Ahankali Benazir din ta bude baki muryarta a shaqe sbd kuka tace”

Insha Allah zamu rayu a tare mu sauyi a tare

Idanma mutuwar itace hutu garemu duka Allah ya kawo mata ita gabaki daya mu tafi garesa mu huta.

Sunkuyar da kai sumayyah tayi tanajin kaman itace kaddarar Benazir a yanzu sbd halin datake neman sakata na dawainiya da ita.

Benazir ganin naz tashin hankalinta akan lalurar sumayyah din na neman qarasa taba qwaqwalwanta dan haka ta sakawa kanta juriya ta danne ta nuna mata ba komai bane babu abinda yake samunta lafiyanta kalau hakama qwaqwalwanta lafiyanta kalau.

Hakan yasa kaman yarinya qarama sumayyah din ta yarda ta sake suka koma rayuwar wahalarsu a tare harda Annensu sbd sun gano a yanzu hadin kansu da girman kaunar dasu kewa juna shine qarfinsu.

A duk kowace rana kafin fitan Ababa sai maimaita musu gargadinsa mai tsoratarwa akan kada ko a tsautsayi su kula kowane namiji a makaranta ko a hanya.

Wannan gargadin nasa kusan kullum yayi sa sai sunji hankalinsu ya tashi saidai daman babu wata niyar kula kowa a ransu bare dasuka tabbatarda maimaicin gargadinsa akan maganar na nufin komai mai muni zai iya faruwa idan makamancin hakan ta faru.

****wannan dalilin ne yasa suka kama kansu acikin dubban mutane fiyeda kowa a makaranta,

Sun fara zuwa makaranta tamkar mujiyoyi acikin mutane ahakan suke zuwa su dawo,

Basu taba qara mintina ko biyu ba da an tashi suke dawowa gida sbd aduk lokacin da suka saka qafa suka fita Azabar Annensu ke farawa dawowarsu da wuri shine samun saukin azabarta dan haka da an fito lectures basa bata lokaci da sauri suke dawowa.

Da haka Ababan ya riqe lokacin dawowarsu kan lokaci batareda magana ba idan sun dawo Annensu ta huta idan basu dawoba tana cikin wuya.

Da zasu fara karatu Hande yabawa kudi ta siyo musu atamfo masu saukin kudi kusan guda biyar biyar sai jallabiya masu saukin kudi suka kusan guda uku uku shikanan sai mayafai biyu da hijab biyu kowannensu sai takarma daddaya.

Ahaka suka fara karatun cikin taka tsantsan da tsoro da fargaba,

Babu wani mutum daya dasuke hulda dashi a makarantar kaman yanda basa yarda ko bada fuskan ayi hulda dasu.

Sumayyah fara shigarta cikin mutane sai yake kokarin bayyanarda matsalarta ta cikin qwaqwalwanta a fili sbd a duk lokacinda ta shiga mutane sai take jin kanta na juyawa,

Sam tunda suka fara karatun bata wani gane komai sam sbd mummunan sabon da Ababa yayi musu bata iya shiga mutane tafi son zaman gidan.

Benazir kuwa sosai ta maida hankali ta qwallafa rai a karatun sbd samun Abin tsira daga mahaifinsu da yardar Allah saidai kuma yanayin Sumayyah yafara hanata kwanciyar hankali a yanda ya kamata a karatun.

A duk lokacin suka fito suka zo makaranta hankalinta yakan rabu biyu ne akan sumayyah da karatun,

Tin tana boyewa cikin kama kai daga kowa har kusan anfara ankarewa da Sumayyah din na dan da tabin kai duk da ba laifi wani lokacin takan gane karatu harma da tambaya.

Ahaka suka ringa lallabawa suna karatunsu cikin kame kai daga wulaqanci da tazarcin mutane dasuke samu.

A gida kuwa idan sun daga daga makaranta babu wani sauyi daga rayuwar dasuka saba saima qari dan yanzu ganin yakeyi dukiyarsa suke ce fiye da baya dan haka a yanzu har shagon sanaar wankau ya bude wadda idan ankawo sune suke yi saidai acan shagon ayi guga a hada a leda a bayar idan masu karba sunzo dan haka yanzu wahalar taketa sake qaruwar musu sbd wankin kayan maza wani Abu ne mai tsananin wahala garesu sbd nauyi musamman manyan riguna wanda sai sunyita wankinsu kusan so uku kafin su wanku sbd sunfi qarfin hannuwansu rigunan.

Basu taba nuna gajiya ko wahalarsu a fili ba sbd babu abinda hakan zai haifar sai qarin azabar dan haka suke rayuwarsu a hakan.

A makaranta akwai wainda da yawa suke shaawar mu’amalantarsu sbd kame kansu sai yake nuni da kaman tarbiyace da suke da ita amma rashin fuskarsu da kamewarsa tareda tsoron shiga mutane dasuke a fili yasa baa tinkararsu.

Yanayin fatarsu mai duhu da kyau ga kamanninsu dasuke kusan daya ga kyan jiki na mata mai kyau da daukan hankali da Allah yayi musu yasa aka dan fara Ankara dasu wanda da basa kame kansu da tini sunfara tara samari da abokai barkatai.

*****A haka lokaci ya gangara dasu har suka gama session daya kuma babu wani sauyi ko daya bayan na Ilimi da wayewar dasuke samu cikin mutane Hakama sumayyah ta fara sabawa tini da rayuwa cikin mutane kuma a hakan bawai ta warke ko samun saukine ba kwata kwata Benazir ce a gurin kulawa da ita sosai tana kaffa kaffa kada Ababa ko hande su gane gashi Annensu a yanzu rayuwar tafi yi mata tsanani dan harsu je su dawo tana kan qafafunta tana aiki bata hutaba ko na daqiqa daya.

Results dinsu na exams na sumayyah ko kadan baiyi kyau ba duk da bata fadi duka ba amma kusan fiyeda rabi duka ta fadi,

Ababan bai wani damu ba sbd shidai iya ilimin yakeson su samu da turancin bawai cin jarabawa ba da sakamako mai kyau sam babu matsalarsa da wannan amma dik da hakan saida yayi mata dukan data kusan sati bata miqewa daidai harda Annensu da benazir ya hada duk da ita nata sakamakon yayi kyau matuka sbd babu course daya data fadi.

********Sun kammala hutunsu sun koma session na biyu wanda ita sumayyah ba dan rashin kyan sakamakon ta ba da session dinta na karshe ne tun karatun 2years ne.

Dawowarsu hutu yasa sumayyah takura qwaqwalwanta gane karatu sbd Azabar data ringa sha daga Ababa tin daga farkon hutun har qarshensa gashi harda Annensu da Benazir yake hadawa kaman jakuna haka yake binsu kullum ya musu duka ga fucewarsa.

*****Sumayyah yau tsaban azaba har yamma takai makaranta wata abokiyar karatunta da itama bata ganewa irinta suka kai sunata bita suna takura qwaqwalwanrsu har Allah yasa suka gane abinda suke son ganewa tabiyo hanyarta tabi ta department dinsu Benazir wadda tasan bazata taba tafiya ba bata jurata ba.

Sauri takeyi hankalinta a tashe sbd tasan Yau sai Ababa ya yanki naman jikinsu ya zubar a bola sbd kusan anfara kiran magrib.

“Excuse me,Aslm alkim” taji anfada daga bayanta kusan gab da ita A hankali ta dakata tareda juyowa zuciyarta na bugawa kaman zata fado sbd tsoro jin muryar namiji Abinda tafi tsoro a komai duniya yanzu shine wani namijin ya mata magana.

Wanda tagani ne yasata neman rasa numfashinta sbd tsananin tsoro da rudewa tareda firgici mai tsananin gaske.

Rawa qafafunta suka dauka ta juya da sauri zata wuce batareda ko sallamarsa ta amsa ba dan tabbas batajin ma da ita yake.

Da kallon mamaki ya bita da Id card dinta a hannunsa yana dan yamutsa fuskar kalau take kuwa,

Ta gabansa ta zubarda id card din bata saniba ya dauka ya miqa mata amma ta wucesa kaman wadda taga abin tsoro.

Isowar professor Abdallah gabansa fuska a matukar sake da zallar girmamawa yana cewa”

BILAL KAANTE you are highly welcome Sir.

Wani qayataccen murmushi ya saki tareda saka id card din aljihun wandon tsadaddiyar yadin dake jikinsa ya miqawa prof Abdallah din hannunnsa mai haske da taushin hutu yana cewa

“Thanks prof,

Bazan dauki time dinka da yawa ba time ya shige sai gobe zan dawo muyi magana insha Allah

Nazo ne sbd nayi maka alqwarin zuwa din yau din amma wanj aikin ne ya dan riqe ni.”

“Ba komai zan jira ka goben idan kuma zan sameka a Kaante ne duk ba damuwa tinda nasan abubuwan nada yawa a gabanka”

“No karka damu insha Allah zan samar da time din nazo gaben”

Juyawa yayi prof din na biye dashi suna magana har zuwa ina wata lafiyayyar tsadaddiyar motarsa ta Lexus take black yana bude securityn motar prof yayi saurin bude masa yana ce masa

“A sauka lafiya Sir”

Ngd yafada a hankali cikin nutsuwarsa da Allah yayi masa ta rashin garaje ga komai.

Yana zama cikin motar ya prof ya rufe masa ya tada motar a hankali ya fice daga makarantar yana duba time na gold Agogon rolex dake hannunsa sai kuma a lokacin yaji Id card din dake aljihunsa ya saka hannunsa daya ha ciro tareda kallon fuskarta yana karanta sunan Dake rubuce a id card din SUMAYYAH ABABA.

Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiye card din gefensa a hankali yana maida hankalinsa kan tuqin dayake yi.

Chapter 8

8

Hankalinsu duka baa kwance ba suka isa gida saidai cikin saa har lokacin Ababa bai dawo gida ba Hande ce kawai taketa fadan sun samu sake sunyi dare babu wanda yayi magana acikinsu saida tagama yi musu tatas kafin suka hanzarta yin sallah suka fito suka karbarwa Annensu aikin da bata gamaba har lokacin.

Wani sabon wankin ne suka fara cikin dare basu gamaba sai guraren karfe tara na dare

Daqyar sukai sallah sukaci dan abincin da aka basu suka kwanta kowannensu gababin jikinsa na ciwo.

Washe gari haka guraren 9 na safe suka isa makaranta.

Sumayyah kai tsaye libry ta isa sbd acan zasuyi karatu da wadda sukai jiya,

Tana isa zata shiga ta nema id card dinta ta rasa,

Gefe ta koma ta zazzage jakarta tafara dubawa hankalinta na fara tashi sbd batasan ya zatayi ta samu wani ba komai Benazir ce take yi mata bata iya zuwa da kanta.

Dubawa takeyi da gaske tana bin pages damuwarta na bayyanuwa duk da tanada tabbacin yana jakar bata fiddasa ba.

Duk abinda yake jakar tayi masa daddaya amma bata gansa ba,

Tattara kayanta tayi ta maida jakar ta nufi gurin Benazir cikin dan sauri da damuwa,tsoronta da tashin hankalinta shine ace sai ka biya kudi zaa maka wani,

Ina zata samu kudin?Ababa idan suka fada masa saiya kusan rabata da duniya kafin ya bada kudin,ya Allah yasa ta gansa kokuma baa biyan kudi ake bada wani.

A yau dinma tashin hankalinta bai bari tana tantance inda take saka kafafunta ba kanta a qasa har ta isa department dinsu Benazir din.

Kiris ya rage tayi karo da wanda yake tahowa yana amsa waya cikin nutsuwa da sanyin hali

Da sauri ya dago hannuwansa yayi saurin tareta sbd kada jikinsu ya hadu.

A firgice ta dago tana ja da baya cikin qarfin gaske sai gata a qasa

Bata damuba ta miqe da sauri kanta na yin qasa a sanyaye ta basa hakuri tana sake sauke kai kaman wadda take gaban Ababa.

Cikin dan mamaki ya kalleta  yana tabbatarda itace mai student id card din hannunsa,

Juyawa tayi zata wuce batareda ta dago ta kallesa ba zuwa lokacin jikinta rawa yakeyi sosai dan gabaki daya Azabar Ababa kawai take jin har tafara sauka jikinta.

“Hey Miss” yafada da muryarsa mai kamala yana taba Aljihun tsadaddun qananun kayan givenchy dake jikinsa baiji card din ba ya dan rintse ido a hankali yana tino yana cikin motar daya shigo makarantar jiya da ita.

Ba damuwan komai a ransa ya ambaci sunanta kai tsaye daya tina shine a jikin katin ganin tana sake sauri kaman mai tsoron mutane a bayyane sai kawai ya qyaleta ya wuce yana duba time din agogonsa sbd ba lokaci zai bata ba a school din zaiyi magana ne kawai da prof ya wuce gurin aikinsa.

Yana wucewa Sumayyah data labe daga gefen wasu students ta futo tana kallon inda yabi da ido tsoronta na qaruwa sbd ta tina fuskarsa shine ta gani jiyan ya tsaidata.

Meyake so a gurinta?

Baiyi kama da student ba sbd shekarunsa da jikinsa tareda maturity dinsa sun bayyanarda hakan,

Kyawunsa da kwarjininsa tsoro ya bata matuqa tareda firgitata,babban tashin hankalinta kada ya sake tsayar da ita wani yagani tsautsayi yasa Ababa ya sani Alkiyamarta ta tsaya.

Benazir data qaraso gurinta tana dafata daga baya saida sumayyar takusa shaqewa sbd tsoro da tashin firgita,tana waiwayowa taga Benazir ce wasu hawayen mutuwat jiki suka ciko idanuwanta ta sauke tana kokarin hanasu saukowa.

Benazir data ga hakan hankalinta ya tashi cikin mamaki qasa qasa sbd kar ajisu tace”

Me yafaru?

Ababa yazo nan ne?

Wani abu yafaru ne?

Kasa magana sumayyah tayi ta silale ta zube zaune kan  gurin zama tana kokarin daidaita numfashinta dayake futa da sauri na tashin hankali biyu datake ciki na batan student id card dinta dakuma mutumin daya tsayar da ita wadda sunfi kaunar hadarin mashin da wani namiji ya tsaidasu.

Shafa bayanta Benazir ta ringa yi ahankali ta cikin hijab dinta tana cewa

“Ki kwantar da hankalinki kada ki bari yanayinki ya sauya asan halinda muke ciki kaman yanda Ababa yafada mana.”

A hankali ta ringa sauke numfashi tana kokarin daidaito nutsuwarta har tsowon mintina kafin ta dan dawo daidai ta dago idanuwanta da har sunyi jajir ta kalli Benazir dake jiran bayaninta cikin fargaban idan ba wani abin ne ya sameta ba.

Bude baki tayi ahankali ta yiwa Benazir din bayanin batan student id card dinta tareda kasa fada mata mutumin da yayi mata magana sbd tinowa da hakan kawai girgiza kayan cikinta da zuciyarta yake bare iya bude baki ta fadawa ko Benazir cewan wani namiji ya tsaidata.

Shiru Benazir tayi sbd itama batasan ta ina zara fara ba tunda ba muaamala sikeyi ba da mutane bare su tambaya qarin bayani.

Shiru sukayi sun jima a hakan batareda sanin abin yi ba,ganin hakan Sumayyah taji gabaki daya hankalinta ya qara tashi suka fito daga department din suka nufi gurin da babu mutane sosai suka zauna take Sumayyah ta fashe da kuka mara sauti tana jin yanda zasu sanar da Ababa hakan.

Shiru benazir tayi itama jikinta na mutuwa sbd tasan bawai tsallakewa zatayiba itama hadasu zaiyi ya musu hukunci daya.

Kasa cewa Antyn tata sumayyah ta dena kuka tayi sbd batasan wane qwarin gwiwar zata bata ba dan haka sukai tsit sai kukan sumyayah da ita kadai ce take jin sautinsa.

Basu san zaune suke gefen wata lafiyayyar black beymack ba saida mai motar ya doso gurin kai tsaye idanuwansa akan Sumayyah wadda idanuwanta sukai jajir jikinta yai sanyi gaba daya.

Kallo daya Benazir tayi masa tayi qasa da kanta bugun zuciyarta na tsananta tareda wata irin fargaba mai tsanani wadda ta sanya numfashinta fita da sauri saidai tinda tayi qasa da kanta bata dago ba.

Shi kuwa sumayyah data qarasa rikicewa da ganinsa yake kalla mamakinta na sake kamasa sbd kai tsaye ya gane tsoron maza takeyi kokuma irin tarbiyar da aka bata ne daga gidansu.

Tsoro ya hana sumayyah dauke idanuwanta daga kansa hannuwanta dake qanqame da jakarta suna rawa.

Kasa shiga motarsa yayi sbd zuciyar kulawa da tausayi tareda sanyi da Allah yayi masa fiyeda kowa a familynsa ya juyo ahankali cikin nutsuwa ya dawo gabansu ya tsaya murya a kamale yacewa sumayyah

“Student id card din ki na gurina nayi kokarin baki a jiyan amma baki tsaya ba,

Yau kuma ban fito da motan dana barsa ba a jiyan amma insha Allah gobe zan sake shigowa wani abin zan taho dashi ki jira ni anan around 4 haka lokacin na shigo sai na baki”

Daga sumayyah din har Benazir a tare suka dago suka kallesa suna masa wats irin godiyar data bayyanar da fadawar tashin hankalinsu.

Da mamaki ya zubawa Sumayyah idanuwansa masu haske yana cewa

“Kina kuka ne sbd Batan card din ne?”

“Are you for real?

Share hawayenta ta hau yi tana sauke kanta qasa daga idanuwansa dasuka fara firgitata.

Kamanninta da Benazir yasashi fahimtar ‘yar uwarta ce kuma kusan halinsu daya na rashin iya kallon mutune da alama itama tsoron mazan takeyi.

Wani gajeran murmushi ya saki tareda bude motarsa ya fada ya tada tabar gurin yana kallansu ta mirror harya bace basu dago sun kalla inda yabi ba.

Ajiyar zuciya Sumayyah ta ringa saukewa a jere tana jin sanyi na mamaye zuciyarta data kusa bugawa da tsoro.

Tashi sukai suka koma kowannensu ya nufi gurin da zaiyi lectures basu koma gida ba sai 6 saura.

Suna isa sallar magrib kawai sikai sika fito aikin wanki saida suka gama aka basu abincinsu suka zauna sukaci tareda Annensu dake dan fama da zazzabi kwana biyun sbd yammacin dasuke kaiwa aikin na mata yawan dayafi karfinta.

Basa karatu gida ko sun dawo sbd basuda abin haskawa haka suke hakura duk yanda sukazo karatu musamman sumayyah datakeson Benazir din ta ringa dan wayar mata da kai akan wasu kalmomin.

Washe gari tinda suka wayi gari sike cikin faduwar gaba da fargaban yanda zasu tafi gurin wani namiji karban student id card din na Sumayyah,

Sumayyah tafi Benazir din shiga tsoro da fargaba sbd itace tayi sakacin yar da card din hakama saninsu ne Ababa wasu lokutan yana sakawa ana bibiyarsu dan haka sike cikin fargaban.

Har sika isa makaranta babu mai walwala ko nutsuwar zuciya,

Haka sika wuni ba sukunin rai har 4 din tayi sika isa inda yace din suka tsaya suna waige waige ciki fargaba.

Sam hankalinsu bai kwanta ba da haduwar dan haka a matse suke kusan mintina ashirin kafin motarsa ta danno kai a gurin dan shi tini ya manta dasu din saida ya qaraso gurin ya gansu tsaye ya tina Allah yasa da motar yazo.

Yana parking tin bai fito ba ya ciro card din ya miqa musu ta window

Hannu biyu sumayyah tasaka ta karba batareda ta dago ba cikin girmamawa mai tsanani sukai masa godiya kaman wanda yayi musu wata babbar kyauta.

Mamaki suka sake basa tareda birgesa musamman sumayyah wadda Sanyinta da rauninta dayake bayyane yafi basa tausayinta da burgewa.

Juyawa sukayi suka bace bat daga gurin qafafunsu na sarkewa.

Saida suka bacewa ganinsa kafin kowannensu ya saki boyayar ajiyar zuciya basu cewa juna kala ba suka tinkari hanyar ficewa daga makarantar zuwa gida.

Saida suka isa gida suka shiga dakinsu suka zauna kusa da Annensu hankalinsu ya kwanta daidai suka sake ajiyar zuciya a tare batareda sunyi yunqurin zantawa akan komaiba game da lamarin batan id card din gaba daya.

******kaddara zaace ko tsautsayi kokuma rabo?

Haduwar sumayyah da Bilal kaante daga wannan lokacin sai ta zama kaman wainda ake turowa dan kuwa kusan babu ranar da zai shigo makarantar Allah bai qaddara haduwarsa da sumayyah ba wadda tsoro da firgicin datake shiga a duk lokacinda zata gansa yake sake qarfafa masa tinanin hulda da ita dan kuwa nutsuwarta da kamala tareda tarbiyarta a bayyane take,

Rauninta kaman wani abin birgewa ya zama garesa dan kuwa hawayenta a kusa suke

A kwai ranar daya tsayar da ita ga mamakinsa hawaye yaga suna gangaro mata sai hakan ya sake sakasa tinani da kwadayin son saninta a ransa.

Chapter 9

9

Sumayyah tsananin tsoro da tashin hankalin yanda mutumin yake tinkararta kai tsaye lokuta da dama idan suka hadu a hanya yasa ciwon damuwa da tsoro mai tsanani suka shigeta,

Ta fadawa Benazir ma ta kasa, tsoro da fargaba takeji dan haka daga karshe saita dena fitowa kwata kwata daga hall din lecture dinta idan tashiga,

Wannan matakin data dauka yasa ta dauki lokaci mai tsayi bata sake haduwa dashi ba har tafara mantawa da lamarinsa gabaki daya ta koma tana fitowa kaman yanda ta saba.

Ta nasa bangaren Bilal kaante kasa mantawa yayi da ita musamman yanzu sbd ita din yake dan shigowa gurin prof duk da prof dinne ya kamata ya ringa zuwa yana samunsa sbd matsayi da karfin power tareda tarin Asalin dukiyar dasuke dashi Kaante Family harma da suna.

Rashin ganinta kwana biyu ya fahimci da kanta take boye kanta din sbd shi dan haka shima sai bai takurata ba a boye yafara bibiyarta yayi bincike akanta ya fahimci Mahaifinsu mai tsanani da zafin gaske ne hakama yanada tsaurin hukunci amma sam bai samu sanin irin halin da rayuwarsu take ciki ba a karkashin mahaifin nasu sbd wata rayuwa ce da babu wanda yasan asalin balai da ukubar dasuke ciki iya tsananinsa kawai aka sani sai Aikin wahalar dasuke yi musamman na wankin qattin mazan dasuke masa na shagon shagon wankin daya bude babba.

A qanqanin lokaci da gajeran bincikensa ya dan fahimci rayuwar tsanani suke ciki sbd ko a yanayin rayuwarsu zaka iya fahimtar basa rayuwar ‘yanci da sakewa sai yanda akai da rayuwarsu.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan kwanaki yana yawo da tinanin rayuwarsu yana bibiyarta daga dai ya tabbatarda tausayinta ne tareda soyayyarta suke shigesa abinda bai taba faruwa dashiba soyayyar wata mace bayan ta mahaifiyarsu da qanwarsu qwalli daya dasuke uwa daya wadda itama DD ne ya saka masa kaunarta mai tsanani sbd yanda duk tsananin zafinsa daga Mammah sai Zeenah din yake ragawa a duniyarsa da babu kowa acikinta bayan kebe kansa daga yan uwa da familyn nasa.

Bilal Sumayyah ta shiga zuciyarsa cikin sanyi da nutsuwa,

Yanajin sonta na qarfafa zuciyarsa saidai kuma damuwarsa ta yanda bazata samu karbuwa a familynsa   Ba dan fitowarta daga ahalin da ba kowa ba kuma basuda abinda shi a nasa familyn ake kira Girma maana kalman nan ta kwarya tabi kwarya,

KAANTE family wani babba,sananne,attajiran family ne da ake kiransu da billionaires wasu kuma su ce musu the family of power.

KAANTE’s Sun kasance wasu irin sananni dasu hada,fame,wealth,power harma da lokaci da Allah ya basu sam an kasa samun wanda ya wucesu ko ya fisu,

Idan akwai wanda zai iya tsayawa gaban KAANTEs din ya nuna musu isarsa da zafin kai a duniyarsu to DD KAANTE wato DAWOOD DAUDA KAANTE,wanda yake ‘da kuma guguwar da ita kadai take girgiza familyn batareda sun iya yin komai ba akai haka shine kadai yake tsayawa gaban duk wanda zai kawowa familyn Hayaqi batareda batawa kai lokaci ba.

Tayaya zai iya gabatar da Sumayyah ga familynsa a matsayin wadda yake so da kaunar mallaka.

Kusan shine babba a familyn dan haka sunada high hopes akansa na auro macen data dace da matsayinsu,

‘Yar babban gida,wayayya ‘yar boko mai zurfi ilimi da class kaman yanda duka sauran mazan familyn suke auro matayensu.

Tayaya zai fara dan shi dai zuciyarsa tayi naam da sumayyah bayajin zai ja da baya saidai kuma fargabarsa bata gushe ba saima qaruwa datake yi.

*******Sumayyah data manta dashi sukaci gaba da rayuwarsu kaman mujiya acikin mutane suna sake maida hankali ga karatunsu ahankali ciwonta yafara dawowa sosai kaman qwaqwalwanta zai juye gabaki daya sbd yawon makarantarsu yanda yake cin kudin Ababa yasa Ababan ya tsananta musu azabarsu da wahalarsu sun koma yanzu so daya ake basu abinci hakama aikin wankin shagonsa harma da guga yanzu sune sukeyi ga aikin gida ga aikin sharewa da wankewar gurin dabbobinsa masu yawa da tsananin qazanta ga nasa wankin gana Hande ga girki da wanke wanke gashi komai qanqantar laifi duka suke sha sbd tsananin kiyayewarsu yasa ya dena samun dalilin dukan nasu kaman jakuna shiyasa yanzu komai qanqantar lefi yake sauke gajiyarsa akansu da duka.

Basa samun lokacin karatu ko kadan sai ya zama makarantar ma idan sunje yanzu kusan daqyar Benazir ke ganewa Sumayyah kuwa sam ta dena ganewa wasu lokutan ma magana takeyi ita daya ana lectures sai hakan yasa mutane suka fara ankara da kaman tana matsalar juyewar kai,

Tin maganar na yawo iya tsakanin course mate dinta sai maganar ta fara yaduwa har gurin da baa zato

Sai abin yafara zama kaman ana tsokanarta ana nunata akan tanada juyewar kai.

Tin tana daurewa tana nesanta kanta da mutane sosai har abin yafara yawa ko inda mutane suke bata iya zuwa sbd yanda ake mata kaman mai ciwon hauka sosai.

Tayi kuka,tayi kuka,tayi kuka amma babu wani sauki ko sassauci,

A hankali karatun da makarantar suka fita randa da kanta gabaki daya musamman da mutane suka gano bata gane komai na karatun,

Abin tsokana ta zama a gurin dalibai yan uwanta batada me tsaya mata kuma tunda taga matsalarta tasa rayuwar Benazir ta juye gabaki daya itama yanzu karatun nata yafara lalacewa tare suke zuwa can baya gurin da babu mutane suyi kukansu babu mai iya rarrashin wani su gama su dawo babu mai iya kallonsu da daraja saima aka saka musu wani sunan tozartawa MENTALS.

A gida babu daman su bari Ababa yaji abinda yake faruwa zai iya kusan kashesu dan haka kullum da Annensu suke zaunawa tsakar dare sukai kusan asuba suna kuka babu mai iya magana bare rarrashin wani idan sukai suka gama saisu kwanta wani lokacin kuma alwala suke yowa suyi nafila suyita kaiwa ubangiji kukansu,

Rayuwar gidan tin shekarun dasuka gabata suka manta da cewan basu kadai bane ‘yayan Annensu sbd Tini Sunayen su Safnah suka zama shafaffen tarihi a gidan shi kansa Ababa tini ya manta dasu daga rayuwarsa har mantawa yakeyi da ba iya su Benazir da sumayyah ne kadai aka haifa da sunansa ba.

*******Exams dinsu ta matso sosai dan haka hankalinsu su duka ya tashi musamman sumayyah data san Alqawarin Ababa na cewan saiya karya qafarta da hannunta idan ta sake faduwa jarabawa dan haka gabaki daya ta fice hayyacinta a kwanakin bata rintsawa kwana takeyi a zaune tana karatu amma babu kalma ko daya datake shiga kanta kaman an rufe qwaqwalwanta da kwado.

Benazir ajiye nata karatun tayi kullum na Sumayyah din sukeyi tana kokarin koya mata amma babu wani motsi ko daya,

Data ga lokaci nata qurewa babu sauyi sai kawai takoma tana skipping lectures dinta tana shiga nasu sumayyah din dayake suna kama sosai sai lecturers din basa wani ganewa students din kawai ke ganewa sai suka ringa tsokanarta suna cin mutuncinta itama amma bata taba dago kai ta kallesu ba.

Sosai hankalin Benazir yasake tashi data gama fahimtar abinda take tsoro ne yake tabbata wato irin ciwon rasa hankalin Annensu sumayyah ta kamu dashi  wanda tsananin depression ne yake haifar musu dashi yakaisu ga wannan lalurar.

Gabaki daya mutuwa jikin Benazir yayi ta rasa tata nutsuwar da tinani harma da kusan nata hankalin itama tafara rasawa sbd wannan babbar masiface da tashin hankalin da ita kadaice zai kashe dan kuwa daga sumayyah har Anne kusan kashesu ne bazaiyiba sbd azaba,

Idan ya bar Annensu gidan duk da haukarta sbd ya ringa juya rayuwarsu yanda yakeso ita sumayyah bazai taba barinta gidansa ba sbd babu amfanin da zata masa,bazai tsaya komaiba zai rabasu da ita yakai bola ya yar babu ruwansa da hadarin hakan ga budurwar data girma sosai.

Wannan tinanin ya sanya rayuwar Benazir ga mummunan hadarin datake gab da rasa nata hankalin itama,

Ita kanta yanxu dataga gaskiar lamarin sumayyah addua takeyi da fatan nata hankalin ya gushe Ababan ya tattara su su biyun da Annensu ya watsar bola indai zasu rayu a tare.

Gugar kayan dasuka wanke suna dawowa sukeyi sbd Ababan yace da safe masu kayan zasuje karba shago dan haka tinda suka dawo suke wankin basu gama ba sai bayan ishai dayake ana iska sosai kayan sun bushe da wuri karfe biyu da mintina arbain suka tashi suna goge kayan.

Sumayyah da bata gane komai yanzu sosai tana farawa tabar iron din kan kayan data fara gogewa tana dan bubbuga kanta da hannu tana kiran sunan kanta dana benazir din kaman me fira da wasu.

Hayaqin konewar kayan yasa Benazir data duqufa tana  goge kayan da sauri sbd suje su kwanta tareda Annensu ta dago da sauri ta dauke iron din kan kayan tana kallon kayan jikinta da daukan rawa gabaki daya zuciyarta na neman dakatawa daga bugawa.

Kallon Sumayyah tayi da idanuwanta dasukai ja take sbd tashin hankali taga sumayyah din itama kayan take kalla jikinta na wani irin kyarma tana neman ficewa hayyacinta kanta na neman juyewa gabaki daya sbd tsananin firgici da tashin hankali mai tsanani.

Ganin tana fisga tana neman buga kanta da qasa Benazir tayi sauri ajiye iron din ta kamota ta rungume tana hanata bayyanarda matsalar tata dan kada tsautsayi yasa Ababa ya gane ko Hande.

Fisga Sumayyah keyi sosai tana kokarin kamo iron din daya kona kayan matsanancin tsoronta na bayyanuwa a fili duk da tana samun gushewar hankali lokuta da dama amma sam tsoron Ababa daya ginu cikin jini da zuciyarsu bai taba gushe mata.

Qaurin wutar kayan ya sanya Ababan dayake palonsa fitowa tsakar gidan idan suke gugar daman baiyi bacci ba sbd wani lissafi dayake yi kusan awanni ya kasa gamawa kusan dama duk ranar daya samu kudi masu dan kauri baya bacci har asuba.

Akan babbar rigar wata farar tsadaddiyar shadda idanuwansa suka

Shaddar harta kone iron din ya fasa zanin qasanga harya kona tabarbar datake qasa itama ta cinye daidai shape din iron din gugar.

Benazir na ganinsa ta saki Sumayyah wadda rawar jikinta yai tsananin gaske suka gyara zamansu zuwa kan gwiwarsu kansu na yin qasa sosai babu wanda jikinsa baya rawa mai tsanani acikinsu.

Kayan ya sake kalla fuskarsa na dauke rahamarsa gabaki daya yace

“Uban waye yayi wannan aikin?”

Benazir ce ta dan dago ahankali batareda ta iya kallan fuskarsa ba sbd tsoronsu akansa bazai bar hakan ba ta bude baki zata basa hakuri bai bari ta gama bude bakinba yasa qafa ya shura bakin nata tayi baya ta fada bakinta na fashewa da jini tareda radadin azaba.

Sumayyah qamewa tayi dukkanin wutar jikinta na daukewa numfashinta yafara kokarin daukewa saidai kafin ta fice hayyacinta tafara jin saukan azaba ajikinta tin tana jin dukansa da wani radadi a jikinta har ta dena ji bata sake sanin inda kanta yake ba.

A tsakar gidan suka kwana har asuba Benazir na qarasa goge sauran tulin kayan zuciyarta na tsalle da radadin kallon ‘yar uwarta a gefenta some babu daman bata taimako sbd yana zaune har ta gama.

Sanyin Asuba yasa Sumayyah farfadowa cikin tsananin azaba lokacin Benazir tagama har Ababan ya bar gurin da sauri ta ringa daukan kayan tana kaiwa palonsa tana gama kwashesu duka ta dawo da sauri ta kama Sumayyah din da hawaye ke gangarowa daga idanuwanta ahankali,

Miqar da ita tsaye tayi saidai azabar da Sumayyahn taji a tsakiyar tafin qafafunta yasata daka tawa tana rintse idanuwanta suna kasa kallon juna ita da Benazir din.

Chapter 10

Suna isa dakinsu suka tararda Annensu zaune tana hawaye masu dumi da ciwo sbd duk abinda yake faruwa tsakiyar gidan tana ji amma batada iko ko daman fitowa.

Suna shigowa ta bisu da ita batareda ta motsa ba dan batasan me zatayi ba yanda zuciyarta ke radadi.

Zaunar da Sumayyah Benazir tayi tareda zubewa gefenta itama saida sukai shiru kukan Sumayyah kawai ke tashi tsawon lokaci kowa da damuwar datake yankar zuciyarsu.

Kusan awa daya a hakan kafin Benazir da Anne suka fito sukai Alwala suka dawo daki kafin itama Sumayyah din ta fito cikin azabar tayi alwala ta koma dakin.

Sallah kawai sukai tareda addua suka fito fara aikinsu gadan gadan harda Sumayyah din sbd baa basu damar hutawa daga aikin ba koda ciwo kuwa.

Sai guraren 9 suka gama wanda suka iya suka shirya Hande ta basu abincin karyawan da Ababa ya rage sukaci suka fice zuwa makaranta lokacin kusan Benazir harta rasa lecture dinta na 8 to 10 suna isa ta shiga ta 10 to 12 Sumayyah kuwa kasa shiga lectures tayi sbd wani irin azabababban zazzabi mai qarfin gaske daya rufeta,

Qafarta wani irin radadi da zogin azaba take mata sbd iron din da Ababan ya wurgeta dashi ya kona tafin qafarta sosai ba daman ta nuna azabar datake ciki a haka tayi aiki kafin su fito gashi zuwa lokacin kafar gabaki daya ta cabe daqyar ta iso makarantar ta nunawa Benazir babu wata matsala ne da qafar sbd ta samu ta shiga lectures nata da yanzu bata samun attending yanda ya kamata amma kam tana cikin mawuyacin hali.

A hankali ta daddafa ta kebe kanta cikin mawuyacin hali ta isa inda suka saba kebe kansu ta zauna jikinta na tsananin rawa ko numfashi daqyar take ja,

Dan dago kafar tayi a hankali ta leqa inda konuwar take.

Sanyayyan Numfashi ta sake jikinta na sake daukan rawar zafin zazzafi

Qafar tini tafara yan ruwa masu maiqo sbd sosai iron din ya shigeta.

Jajir idanuwanta sikayi tana kasa fidda koda hawaye ta samu sassaucin radadin datake ciki cikinta da fili.

Zamewa tayi ta kwanta yashe a gurin azabarta na qaruwa idanuwanta na qanqancewa,

Tsawon lokaci ta dauka ahakan kuma kowace daqiqa tana wucewa ne tareda qaruwar azabarta.

Sama sama take jiyo hayaniya da maganganun mutane masu wucewa,

Tashi takeson yi ko zata iya kai kanta gurin Benazir sbd ciwon yafara fin karfinta yasha ruwa ne caba caba gurin aikinsu na safe hakama duk ta takesa ya cabar da qafar gabaki daya ya zabure da ciwo baji ba gani.

Daqyar idanuwanta dasuke kanne suka budu tana sake kokarin tashi sedai hakan sam yakasa samuwa Na idanuwanta dake rufewa ahankali tana neman somewa sbd tsanani da zafin azaba.

********Bayan Awa bakwai

A hankali ta bude idanuwanta da sukai mata wani irin nauyi sbd baccin wahala da jan azabar dasukai har lokacin basu washe ba.

Akan Benazir dake gefenta idanuwanta suka fara sauka wadda itama nata idanuwan suke jajir sbd tsananin tashin hankali biyu dayake dabaibaiye da ita,

Na ganin yar uwarta a wannan halin dakuma na zaman dasukeyi a tsadaddiyar private asibitin wanda shi kansa sbd gudun asan halin da yake ciki ya sanyashj kawosu wata asibitin ba KAANTE SPECIALIST,

Babban tsoro da mafi tashin hankalinta shine sikai magrib Sumayyah din bata farka ba dan kuwa ko a bayanta ne zata goyata su isa gida kafin magrib din matuqar bata farka ba.

Ganin budewan idanuwan Sumayyah a kanta ya sanyata sake ajiyar zuciya masu karfi a jejjere tareda rintse idanuwanta da sukai jajir Allah ne kawai yasan a tsananin halin data share wainnan awannin tana jiran farfadowar Sumayyah din,

A rayuwarsu bata taba tinanin zasu samu kansu a hali irin wannan ba na zuwa wani gurin neman lafiya kuma a qarqashin kulawan wani namiji wanda ko a tsautsayi Ababa yaji ko ya gano hakan tabbas Allah ne kawai zai ceto su daga mummunan qanin kisar da zaiyi musu.

Daga ita har sumayyah ba da izini ko saninsu Bilal kaante ya dauko sumayyah din ba ya kawo asibiti

Seda ya kawota asibitin bayan ya tsinceta a halin datake ciki a some har saida aka gama yimata komai kafin ma ya koma makarantar ya nema Benazir ya sanar mata suka taho asibitin tare wanda wannan shine karon ta na farko shiga mota.

Rayuwarsu basa fita kaman yanda aka sani,

Sunyi rayuwar karatun primary da na secondary har sukayi suka gama a qafa suke zuwa su dawo a qafa,

Tunda suka gama basa fita koina kullum suna gida a kulle kaman kayan sata,

Yanzu da suke jamia bai taba basu abinda zasu hau mota ba kullum a mashin suke zuwa kuma overload sukeyi shiyasa ko daya nada lecture daya dayan nada fiyeda hakan dole suke jiran juna komai dadewan da dayan zaiyi kuwa sbd Ababa bai taba yarda suna dawowa daban daban sbd kudin abin hawan.

Sumayyah data juyar da idanuwanta da qyar suka sauka kan Bilal Kaante dake tsaye bayan Benazir yana kallonta cike da kulawa da damuwa harma da mamakin halin daya sameta,

Ganinsa yasa hankalin sumayyah dawowa jikinta da sauri ta yunqura ta tashi zaune tana kallon Benazir jikinta na daukan rawa ita kanta Benazir datake cikin halin tashin hankali har lokacin matse take dasu bar asibitin da Bilal din su koma gida da gaggawa.

Saukowa gadon Sumayyah tafara a rikice tana cewa Benazir su tafi gida kada Ababa ya rigasu komawa gidan duk da Hande ko sunr rigasa komawa saita fada masa amma sassauci zai samu idan sun rigasa komawa din.

Benazir da sauri ta miqe tsaye tana kamata ba bata lokaci suka fara kokarin guduwa hankulansu a tashe sbd sam babu wanda yake cikin nutsuwarsa bare wani tinanin da ba nakomawa gida ba yanzu yanzu.

Cikeda mamaki Bilal ya matso ya dakatar dasu yana cewa

“Meye hakan kuke kokarin yi?

Tayaya zata iya taka qafafun nata ta isa gida musamman wannan rawar jikin da kukeyi tana taka qafar zata qarasa tadawa kanta wani matsalan.

Daga Benazir har sumayyahn babu wanda ya iya dagowa ya kallesa sai shiru da sukayi dan dai bazasu iya tsayawar ba hakama bazasu iya qalesa su tafiyarsu ba sbd taimakon da yayiwa Sumayyah din ta saidai itama kila su rasata.

Benazir ce daqyar ta iya bude baki cikin girmamawa sosai kanta a qasa ta basa hakuri tareda masa godiya sosai akan abinda ya musu din.

Kallon Sumayyah datake tsiyayar zufan wahala da azabar tsayuwar datayi akan qafafunta yaji zuciyarsa bazata iya dauka ba dan haka kai tsaye ya kai hannunwan ya maidata zaune kan gadon tareda durqusawa ya kamo qafar ya duba yana jin tsakan jikansa na tashi sbd yanda gurin ya sake cabewa take da yar tsayuwar datayi to bare tace zata taka zuwa gida.

Cikin fada ya kalli Benazir data sake daukan rawar jiki zuciyarta na bugawa kaman zata faso kirjinta ganin yakai hannunsa kan sumayyah wadda itama kusan kanta ya kusa juyewa sbd tsoro da firgicin jin hannun wani namiji a jikinta take tafara kokarin rasa numfashi sbd tino Fuskan Ababa idan ya san hakan.

Benazir din da Bilal sukai kanta suna girgizata

Sake jij hannunsa jikinta yasata qarasa gigicewa tana neman rasa hankalinta

Benazir da sauri ta janye hannun Sumayyah din daga hannunsa tana kasa kallonsa ta miqe tana ce masa gida kawai zasu tafi.

Kama sumayyahn tayi wadda ta ringa taka qafafunta cikin azabar datake jin gwara ita da wadda Ababa zaiyi musu idan yarigasu isa gida.

Bilal mamakinsa qaruwa yayi tareda wani irin tausayinsu da soyayyar Sumayyah din mai qarfi na sake mamaye zuciya da jininsa dan kuwa duk takun ta daya har cikin tsakiyan zuciyarsa yake jin radadinta.

Suna fitowa harabar asibitin bai tsaya komaiba ya qaraso gurinsu ya kama sumayyah din ya isa da ita motarsa ya bude ya sakata a seat din gaba ya rufe ya kalli Benazir datai mutuwar tsaye kai tsaye ya nuna mata bayan motar fuska a daure yace ta shiga.

Daga inda take tsaye bata motsa ba sbd wannan wani abun ne da bazai taba yiyuwa ba gashi kai sumayyah cikin motarsa ya gama firgita duk wata qarfin zuciya datake dashi.

Ganin bata motsaba itama ya dawo inda take ya kamota ya bude bayan motar ya sakata sbd shi rayuwarsu da sukayi a turai yasa bai tsaya tinanin komaiba ya kama sumayyah dan daukanta a matsayin matarsa insha Allah,

Ita kuma Benazir ya janyota ne sbd yariga ya sakata matsayin daya da Aleeyah kanwarsa.

Yana shiga motar bai tsaya sauraran tsananin tashin hankalin dasuke cikiba ya tada motar ya fice daga asibitin.

Tinda ya tinkari hanyar gidansu kowaccensu ta rasa motsi sbd sunsan yau Alkiyamarsu ta tsaya.

Wani babban chemist ya tsaya ya siya magani masu yawa da aka rubuto ya qaraso har hanyar dajin gidansu yayi parkin daga nesa dayake duhun magrib ya fara suka fito ya miqa musu ledan maganin A tare suka girgiza kai suna cewa bazasu iya tafiya dashi gidan ba.

Sumayyah ya zubawa kyawawan idanuwansa yana kwatanta radadin datake ciki sai kawai ya bude motar ya fito yana cewa” muje na kai maganin da kaina”

Suna jin hakan sumayyah ta fashe da wani irin wahalallan kuka ita kanta Benazir hawaye tafara batareda ta sani ba take suka zube qasa suna rokonsa kaman bayin da zaa cirewa kai.

Kallansu yayi ransa na suya sbd zuwa lokacin baya kaunar ganinsu a irin hakan.

Kallon Benazir daya fahimci itace qanwa amma itace ke fadan yanda sumayyah din zatayi yace

“Idan har bakwason naje da kaina gidan to sai kunyi alqawarin yarda da kullum zan kaiku asibiti aduba ciwon ana dressing harta warke idan ba haka ba zata iya rasa qafarta gabaki daya.

Idan kun yarda shikenan idan ba hakan ba a ynxu zan biku har gidan nayi bayanin yanayin ciwon nata.

Babu wani tinani ko nazari Benazir ta gyada masa kai ta amince sbd yabar gurin kada mummunan kaddara tasa wani ya gansu kokuma muguwar kaddara tasa ya bisu gidan.

“Kin tabbatar?” Yafada yana kallon Benazir din wadda tini suka fara tafiya hankali tashe ta sake gyado masa kai suna jefa qafafunsu cikin sauri hankali tashe.

Wani irin sanyayyan Numfashi ya sauke tareda komawa cikin mota ya zauna yana kallonsu ta mirror har saida suka shige kwanar gidansu.

Tayaya ‘yaya mata daya kamata su zama zinariyar kowane Ahali ace suna cikin irin wannan tsoron mai muni?

Meyesa iyayensu ke musu tsanani haka wanda ya ciresu daga lafiyayyun mutane sbd tamkar Mujiya suke acikin mutane.

Tada motarsa yayi yabar gurin yana sake jinsu acikin ransa fiyema da baya dan kuwa a yanzu bayajin zai iya janyewa daga kaunarsa ga Sumayyah.

Chapter 11

************

Suna shiga gida Hande dake tsakar gida zaune tana jiran dawowarsu tahau fada da masifa sosai tana hadasu da kalmomi marasa dadi iri iri amma babu wanda ya dago kai acikinsu kansu na qasa harta gama fadan tace su matsa mata daga ka tukuna suka bar gurin suka isa dakinsu jakunkunan hannunsu kawai sika aje suka fito sikai Alwala suka koma suka hau sallolin dake kansu tin daga azahar sbd a asibitin Benazir bata samu ko motsawa ba ita kuma Sumayyah batama san ina kanta yake ba.

Suna gama sallah Annensu ta kalli Sumayyah dake sallah tana hawayen azaba tayi mata sannu tareda kamo qafar ta duba ta tofa mata addua cikeda jin qai da tausayawa ‘yar tata datake jinsu su biyun a zuciyarta fiyeda yanda take jin kanta.

Benazir da Annensu ne suka fito suka hau wankin kayan shago da aka kawo Sumayyah kuma tana daki kwance tana fama da azabar ciwon ga yunwa a cikinsu kaman bazasu iya jan numfashi daidai ba.

Sai bayan ishai suka gama kuma har lokacin Ababa bai dawoba dan haka Hande na basu abincinsu suka koma daki suka zauna suka cinye sukasha ruwa suka kwanta.

Saar da suka samu a ranar Ababa koda ya dawo Hande tayi bacci bata samu sanar dashi sunyi lattin dawowa gida ba,

Qarfe hudu na asuba suka tashi suna gama sallah Benazir ta fito tafara goge kayan da sukai wankin da daddare

Gari na fara haske Sumayyah ta fito ta fara gugar itama sbd kada Ababa ya fito yaga ita batayi,

Akwai zazzabi da rashin qarfin jiki sosai a tareda da ita amma hakanan ta daure sika qarasa gugan tareda Benazir suna kammalawa sukai wanka tareda shirin makaranta Hande ta basu sauran taliyar da aka dafa musu da safen suka karya,

Banda sumayyah wadda ko ruwa takasa sha sbd qarfin zazzabin dake cinta haka suka lallaba suka fice har lokacin Ababa bai tashi ba.

Suna fitowa gurin hawa mashin dinsu baqar lexus na parking gabansu babu bata lokaci suka shiga sbd Sumayyah dake gap da zubewa qasa

Aikuwa suna shiga motar ta some dan haka hankali tashe suka isa asibiti dan kuwa daga Benazir din har Bilal babu wanda yake tina komai bayan samuwar sumayyar da rayuwarta daga halinda take ciki.

Kaman wancan karon take aka kwantar da ita nurse da likita suka fara abinda ya kamata akanta Bilal din da Benazir suna waje babu mai iya magana a cikinsu sbd Benazir datake neman zauncewa da tashin hankali.

Haka sukai zaman jira bayan an barsu a dakin su kadai suna tsimayin farfadowarta.

Guraren qarfe goma numfashinta ya dawo daidai alaman bacci mai qarfi ya dauketa daga wahalar,

Kallan Benazir Sir Bilal yayi yace mata zai tafi office yanada masu jiransa zai dawo ba jimawa.

Gyada masa kai kawai ta iya yi harya fice bata iya motsawa ba.

Zaman jira ta dasa har bayan azahar ta samu tayi alwala a toilet din Amenity room din dasuke ta futo tayi sallah tana idarwa Sumayyah din na farkawa ta taimaka mata zuwa toilet tayo fitsari da Alwala tazo a zaune tayi sallah tana idarwa Akai knocking kofar dakin tareda turowa aka shigo.

Kallon wanda ya shigo sukayi dukkaninsu a tare harda Sumayyah dake cikin mutuwar jiki.

Kallansu yayi shima cikin yar girmamawa yace Sir bilal ne ya aikosa ya kawo musu sako,

Ajiye ledojin hannunsa yayi gaban Benazir yana juyawa bayan yayi musu fatan samun sauki ya fice daga dakin tareda rufo kofar.

Kaman bazasu taba ledojin ba tsawon mintina kafin Benazir ta bude ta duba taga take aways ne masu dauke da sunan tsadaddan restaurant din KAANTEs Hotels & Suites.

Wasu irin tsadaddun Deserts ne da crispy chicken sai chicken biryani da kuma salad sai drinks marasa sanyi sosai da ruwa katan daya.

Wani tsinkakken yawu ya wuce maqogwaransu su duka biyun sbd wani irin kamshi da basu saba ji ba dayake shiga hancinsu.

Kallon juna sikai kowannen hanjinsa na fidda wani sautin kukan yunwar datake tauye dasu.

Babu wanda yayi magana a cikinsu abincin sike sake kalla Sumayyah na jin kaman zatayi amai sbd yunwa da matsuwa taci abincin,

Ita kanta Benazir yawunta sun kasa tsayawa sai tsinkewa sikeyi suna wucewa maqogaranta.

Sun jima suna shawarwari da zuciya da hanjinsu kafin daga karshe dai suka afkawa abincin da bismillah suka cinye komai tas sbd Nama wani abu ne da a iya shekarunsu bazasu iya fadan so nawa suka taba cinsa ba,layya Ababa bayayi,baya siyo nama gidansa baya yanka,idan kaga yaci nama iya wanda zaici ne shi kadai sai Hande dayake bawa dan haka a rayuwarsu dai bakinsu bai wani san dandanon namaba dan haka yau din suka ci kaman ba gobe.

Suna gamawa Nurse ta shigo ta bawa Sumayyah magani tareda wasu allurai take sumayyah din takoma bacci.

Ita kanta Benazir din sbd hutu da Cimar da basu saba ba take bacci ya dan dauketa daga kujerar datake zaune.

Basu farkaba sai bayan laasar da sauri Benazir ta tashi ta fada toilet din dakin ta wanko fuskarta tareda Alwala ta fito ta kama Sumayyah tayo Alwala itama suka fito babu bata lokaci sikar sallar laasar suna idarwa sika fara tinanin tafiya gida sbd ba laifi sosai Sumayyah din ta samu sassauci daga mummunan azabar datake ciki,

Babban abinda yasa duk ha’darin hakan Benazir ta yarda suka zo asibitin shine tinawa takeyi da hadda qonuwar wuta ne yayi sanadin Rasuwar Samirah,

Idan ta tina hakan jin takeyi zauncewa zatayi daga ita har Annensu idan wani abu mai kama da hakan ya samu Sumayyah sbd a yanzu da suka debo shekaru iya su tini sika manta da komai da kowa bayan junansu,

Wata irin kauna ce mai tsananin gaske da qarfi take sukewa junansu,

Tin shekarun baya da suke tareda sauran yan uwansu daman Kaunar Benazir a ran sumayyah daban ce hakama ita kanta Benazir din sumayyah daban take a ranta bayan Annensu,sai samirah da itama suke ji da ita sbd tana kaunar yan uwanta sosai da zuciya daya,Safnah ce zasu ce basu tabbatarda tasu kaunarba a ranta amma a nasu ran itama suna kaunarta har cikin zuciyarsu amma daga ranar datayi amfani da Annensu ga gudu suka rufeta daga zuciyoyinsu dan bazasu iya ciretaba jininsu ce kuma suna sonta gaskia.

Kokarin barin dakin sukeyi Nurse ta shigo ta hanasu tareda sanar dasu sai Sir Kaante ya dawo umarninsa ne.

Babu yanda basuyiba su tafi aka qi barinsu haka suka zauna suna jiransa har Sumayyah ta sake komawa bacci sbd akwai abinda yake sakata baccin tsakanin allurar da aka saka mata a drip nata kokuma maganin  da aka bata.

Benazir zuwa lokacin hankalinta ya dawo jikinta gabaji daya bata cikin nutsuwa tsoro da bugawar zuciyarta gabaki daya sun zaburo,ko wane iskar numfashin datake shaqa tafe yake da zallar tsoro da fargaba.

Wani abincin aka kuma kawo musu wannan karon snacks ne,Samosas manya masu kyan gani sai doughnuts masu girma da taushin gaske sai cup cakes da wata kalar crispy chicken din,

Ladar daya kuwa drinks ne sai Apples.

Numfashi ta sauke sbd wannan karon kam Asarar kayan zaayi dan bazasu iya cinyewa ba haka bazasu iya zuwa gida dashi ba.

Sumayyah data farka kadan taci sbd maganinta akwai me saka cin abinci sbd ganowa da akai akwai yunwa tareda uta sun dauka itace batason cin abinci basusan samun abincin ne batayiba taci ta koshi.

Benazir kasa cin komai tayi sbd fargaban zuwa gida da abubuwan gashi a yanayin ciwon sumayyah da maganinta tana buqatan abinci.

Tana cikin shawarwari akazo tafiya dasu gida ba Bilal din bane aiki ya riqesa suna ganin hakan suka saka ya ajiyesu makaranta daga can suka hau mashin suka koma gida.

Cikin tsoro da fargaba mai tsanani suka shiga gidan

Hande na dakinta Annensu ce kawai tsakar gidan tana aikin wankin kayan Hande dasu zannuwan gadon Ababa.

Suna ture ture sbd rawar jiki da tsoro suka fada dakinsu

cikik rawar jiki Benazir ta fidda ledan kayan ta tura cikin kayansu na sakawa dake daure a gefe

Sai alokacin ta saki ajiyan zuciya gabanta na tsananta faduwa tinda ba cinyewa akai ba har lokacin suna cikin hadari mai girma.

Sumayyah da zuciyarta da jikinta suka kasa dena rawa itama kallon Benazir tayi murya a sarke tace

“Bena ki shigo da Anne tin Ababa be dawoba a cinye kayan nan mu saka ledojin a bra tsoro nakeji sosai wlh,

Idan tsautsayi da kadda yasa Ababa yaga ledan nan sai rasuwar samirah tafi tamu sauki da rahama.

Ita kanta Benazir bata cikin kwanciyar hankali idan ba kawar da komai akai ba tunda mummunan kaddara tasasu shigowa gidan da kayan sbd Annensu sukeso itama yau taciwa cikinta abinda zai koshi tinda abune da basu taba ba arayuwarsu ci a koshi.

Sallar magrib sukayi suna idarwa suka fito Benazir ta kamawa Anne wankin suka qarasa ba bata lokaci suna gama shanya suka shigo daki.

Benazir ce ta zauna setin kofa tana hango mai tahowa suka fidda kayan tareda budewa Anne suka ce tayi sauri taci ta koshi.

Wani tsalle zuciyar Anne tayi kaman zata fado sbd tsananin tsoro da firgita muryanta na rawa qasa qasa tace

“Ina kuka samo?

Menene wannan din?

Meyasa kuka taho dashi gidan nan?

Kusan kashemu Ababa zaiyi idan yaga wannan kayan ko Hande.

Sumayyah ce ta dauko doughnut hannunta na rawa sbd tsoro ta tura mata a baki itama murya na rawar tashin hankali tace

“Anne kiyi sauri kici zamu fada miki daga baya inda muka samu”

Laushinsa da qamshin mai dadi tareda azababbiyar yunwar cikin Annen yasata yagar rabinsa tafara ci take taji cikinta yana kukan yunwar ya samu abinci.

Hannu baka hannu qwarya takecin kayan musamman kazar me shegen dadi tana gamawa ta shanye orange drink din dasuka juye a leda suka dauro mata sbd bazasu iya shigowa da robar gidan ba.

Hamdala Annen tayi bayan da cikinta ya cika sosai

Ta hada wani irin uban zuba sbd tana cin kowace irin loma cikin babban tashin hankali da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa,

Yanda kasan barayi haka dukkanin idanuwansu suke a waje kowannensu na hada gumi suna kallonta ta koshi.

Sauran abinda ta rage Sumayyah taci ta bawa Benazir sauran itama ta cinye suka nade ledojin kowacce ta tura cikin rigarta dasu suka kwana ajiki dan abincin da aka basu ma dole suka turasa sbd kar a gane sunci wani abin.

Washe gari ba laifi jikin Sumayyah saidai akwai zazzabi data kuma tashi dashi sbd yanayin makwancinsu basuda kofa a dakinsu shiyasa kusan kullum ko lafiyansu kalau kusan da zazzabi suke tashi kowannensu sbd sanyi dan duk zafi su yanada wahala sujisa sosai sbd anguwar tasu kaman daji take ba mutane dan haka akwai sanyi sosai.

Chapter 12

******

Sauran ruwan zafin lipton da Ababa yasha shayi aka basu babu bread haka suka shanye zallar ruwan zafin da ko sugar baijiba sukai shirin makaranta suka fice.

Suna fita yauma tafiya kadan sukai motar Bilal daya kwana dasu a ransa baida sukuni ta tsaida mashin dinsu a kunyace suka sauko sbd overload dinsu ba kyan gani itace a tsakiya sun matsu iya matsuwa suda mai mashin dayake jin tudun kirjinta wanda kusan hakan suke zuwa makarantar kullum babu ranar da har akai makaranta ba cikin baqin ciki da quncin yanda jikinsu ke manne dana mai mashin din ba.

Shi kansa Bilal dake cikin motarsa qarewa yanayinsu dana mai mashin dain yayi yaji wani irin abu ya tokare kirjinsa musamman yanda kowaccensu dazata sauko kusan daida jikinta dana mai acaban ya hadu.

Rufe idanuwansa yayi ahankali tareda dauke kai daga kallon gurin glass ya aka sauke drivernsa ya miqawa mai mashin din 2k yace ya wuce kawai.

Drivern da kansa ya fito ya bude musu bayan motar suka shiga sbd Sir bilal din yana seat din gaba.

Suna shiga aka bar anguwar dasu babu wanda ya iya magana acikinsu bayan gaisuwar da sukai masa cikin girmamawa da nutsuwarsu dake sake samar musu da gurbi a zuciyarsa.

Hanyar asibiti suka nufa kai tsaye

Yau babu bata lokaci dubata akai aka canja dressing din qafar wanda suna kama hanyar gida suke ciresa su yar sbd kada a gani.

Ana gama dressing gurin aka bata magani tasha suka fito ya ajiyesu makaranta bayan yasa akawo musu abinci daga restaurant dinsu na Kaante hotel and suites.

Suna fitowa first lectures dinsu aka kawo musu abincin har kofar hall dinsu sumayyah din sbd Sir bilal ya sanar dashi hall din dazai sameta tinda ba waya ne dasu ba.

Sumayyah ganin mutane dakuma tsoron jawa kai attention yasa ta karba da sauri tabar gabansa ta nufi gurin Benazir da itama tsoron ganin abincin yasata jan sumayyah suka bar cikin mutane.

Nesa da mutane suka boye suka zauna tareda zubawa ledojin ido hankalinsu tashe sbd zuwa lokacin har ga Allah taimakon ya ishesu tinda sumayyah din tasamu sauki ba laifi.

Har aka tashi basu ci abincin ba suka fito saiga driver yana jiransu a gate suka dauke kai suna shigewa mutane sbd kada ya gansu amma haka ya ringa binsu yana sanar dasu Sir bilal yace kada abari su hau mashin.

Benazir kaman zatai masa sujjada ta ringa rokonsa ya dena binsu shima kaman zai musu sujjadar ya ringa rokonsu akan umarnin mai gidansa ne.

Sumayyah datafi shiga tsoro tana kalle kalle tace su shiga kada wani yagani tinda ba tafiyar zaiyi ba.

Haka suka iso anguwarsu kaman zasuyi zawon kayan cikinsu sbd tsoro.

Yana ajiyesu suka fito qafafu na rawa suka nufi hanyar gidansu suna waiwaye sbd ledan dake cikin hijabansu.

Yauma cikin saa Hande bata tsakar gida sukai saurin isa daki.

Na yau basu ci ba sbd yanada qamshi zaa iya jinsu dan haka suka boye cikin kayansu sai tsakar dare suka tashi yunwa na neman kashesu suka hau ci kaman wainda sukai shekaru ba abinci.

Suna gama ci ko ruwa kasa fitowa su sha sikai sbd fargaba dan haka a hakan suka kwana yauma ledojin a cikin jikinsu suka kwana dasu.

Anne da sukaiwa bayanin Abinda yake faruwa tsorone yafara shigarta sbd ranar ra zaa ganesu take tsoro dan kuwa ranar ruwan masifar fa zaayi a gidan hakama shi kansa mutumin dake taimaka musun Ababan ba barinsa zaiyiba da balainsa dan haka ta ringa musu nasiha da gargadin su kiyaye su nesanta kansu da abinda zai qarasa kashe musu dan kwanciyar hankalin dasuke samu wasu lokutan idan masifar Ababa da hande ta kwanta.

Tamkar wanda aka wajabtawa haka Alh bilal kaman yanda su suke fada yafara sauya rayuwarsu daga wahalalliyar azababbiyar yunwa,

Kullum sai ankawo musu abinci a boye suke karba suna isa dashi gidan sunaci su da mahaifiyarsu wadda a yanxu ciwon yunwar daya gama cinye hanjinta yafara dan sakewa sbd a baya haka take kullum a mokade kaman ledar da aka jefa cikin tafasasshen ruwa.

Aduk sanda suke shigowa da cin abincin cikin masifaffen tashin hankali da firgici mai tsanani sike cinsa su gama dan kuwa sun sani na lahira sai yafisu jin dadi duk randa mummunan tsautsayi yasa kaddarar tonan asiri ya kamasu.

Shi kansa Alh bilal din daya sake fahimtar yanayin da suke ciki na ba qaramin taimakawa abincin ke musu ba daya fara fahimtar yunwar dake tareda sumayyah tafara sakinta kaman yanda likitan dake dubata yafada sai ya dage da ciyar dasu din a boye ta yanda shima nasa familyn basu san rayuwar daya jefa kansa ba.

A yanzu da ya zama kaman biyayyarsa shima kusan tilas ce garesu sbd kyautatawarsa garesu sai ya zama wani irin girma da darajarsa suke gani gashi shima din sai ya dena tinkararsu kai tsaye cikin mutane sbd fahimtar suka tsananin shiga firgici da tashin hankali idan yayi hakan dan haka haduwarsu sai ya zama a sirrance sukeyi.

Hawa Mashin din zuwansu makaranta daya tsana fiyeda komai sai ya siya musu napep kai tsaye sbd kaisu kawai da daukosu tinda basa son shiga motarsa koyaushe suka shiga cikin yanayi na mummuna suke dan haka wanda ya bawa napep din aikinsa kawai kaisu da dauko su.

Da farko tsoron hakan sukeji sosai sbd basu san yanda zasiyi da kudin mashin din da ake basu ba,

Basu iya boye kudi ba sbd ko sun boye basu san me zasiyi dashi ba tinda basu taba sakawa ransu tinanin guduwa subar gida ba bare su ringa boye kudin gashi idanma sun gwada boyewan tinda suka fara zuwa makaranta akai akai Ababa ke sawa hande tana bincikesu da kayansu dan haka basu taba tinanin boye wani abin ba ko ba kudi ba

Abincinmq dasuke shigowa dashi dan suna cinyewa ne a take dasun shigo dashi, dan haka kaman yanda Allah ya kawo musu mai taimakonsu a boye sai suma sike bawa wani tsoho makaho kudin a hanyarsu ta tafiya kullum sbd baida kowa shima yana cikin mawuyacin hali.

Tsohon daya gama wanyewa dasu kullum shima a duk lokacinda ya bude bakinsa Benazir yakewa addua sbd itace mai fitowa ta basa,

Adduarsa kullum Allah yakaita matsayinda bata taba tinanin zuwaba tareda rayuwa mai Albarka da kwanciyar hankali tareda zuria dayyaba.

Exams dinsu aka fara dan haka hankalinsu ya rabu sbd kowa karatunsa yake kokarin maida hankali akai musamman Benazir sbd lectures da dama data ringa rasawa a lokutan sbd sumayyah da ciwon datayi bayan nan dan haka idan suka shigo makaranta sumayyah bata sake ganinta sbd Sosai karatunta ya samu ci baya shiyasa ta dage sosai kafin ta fadi Ababa ya kusa kashesu su dukan gwara a samu mai taimakawa wani acikinsu.

Sumayyah da kanta ya daure matiqa sbd exam din farko da suka fara babu abinda ta gane sunanta kawai ta rubuta sai questions din data maimaita masa a booklet bayan question daya babu abinda ta amsa said ta fito idanuwanta cike da hawayen tausayin kanta da yanda rayuwa zatai mata idan ta gama shekarun nan biyu duka a fail,

Wane mataki Ababa zai dauka akanta?

Siyar da ita zaiyi ga ‘yan qwaya da gaske ko me?

Inda suke zama ta nufa ta zauna ahankali tana sauke kanta qasa dukkanin jikinta na mutuwa hakama tsoron dake mamaye zuciyarta na qara bayyanuwa a kan fuskarta.

Haka ta jima a gurin tana saqa da warwara cikin damuwa har lokaci yayi suka sake shiga wata exam din nan ma kusan biredi ne ke dukan fanke bata tsinano abin arziki ba dan haka wannan karon tashin hankalinta da tsoronta qaruwa yayi sbd azabar datasha wancan karon data fadi exams din a hannun Ababa.

Tana fitowa kasa riqe zuciyarta tayi taje maboyarsu ta zauna hawaye na tsiyayo mata ta saka fuskarta tafin hannuwanta tana sakin kuka mara sauti gashi bazata iya fadawa Benazir ba ta sakata damuwa nata karatun ya fita kanta,

Bazata so hakan ba sbd ko yayane tanason Benazir ta samu kammala karatun da sakamako mai kyau.

Tana gurin zaune har yamma Benazir ta gama suka tafi gida a napep gurin komawarsu Benazir ta lura da yanayin Sumayyah din ta tambayeta exams dinta.

Kasa magana Sumayyah tayi sbd hawayen dasuka cika idanuwanta kafin tayi wata magana Benazir ta fahimci komai cikin damuwa da tausayin yar uwarta tayi shiru ta kasa cewa komai sbd itama tasan suna dagewa ne suyi karatun sbd azaba da hukuncin Ababa,ita kanta idan ta tina da azabar da zata biyo bayan faduwa jarabawar tashi hankalinta keyi bare Sumayyah data dandana azabar hukuncinsa na faduwan.

Shirun Benazir yasa hawayen sumayyah saukowa tana rufe fuskarta da hannuwanta sbd kukan dayake zuwar mata zuciya a karye.

Har suka isa gida kuka sumayyah din keyi itama Benazir kukan zucin takeyi jikinta a mace,

Mai napep na jiyesu suka nufi hanyar gida sumayyah na goge hawayenta dan kada hande ta gani wani masifar ya biyo baya.

Sulaiman drivern napep dinsu na aje su wayarsa ya fidda ya nemo numbern Alh bilal ya saka kira sbd umarnin daya basa akan duk yaga matsala ko damuwarsu ya sanar masa.

Kai tsaye ya sanar masa suna cikin wata matsalar sbd Sumayyah nata kuka har suka isa.

Shiru Alh bilal din yayi sbd yana tareda Mahaifinsa a lokacin.

Dan numfashi ya sauke ahankali tareda bude baci yace

“Ok shikenan idan na samu time zan kira naji qarin bayani.”

Kashe wayar yayi tareda ajiyewa gefensa yana qin kallon mahaifinsa sbd zai iya tambayarsa daga ina ne kiran.

Kallonsa Alhaji DAUDA KAANTE yayi sbd yasan Bilal din da zurfin ciki yanzu haka wata matsalar ce dan haka kai tsaye ya gyara zamansa kan lafiyayyar luxury couch din dayake kai cikin babban palonsa dake Kaante Mansion yace

“Da matsala ne?”

Dagowa Alh Bilal yayi ya kalli Dad Kaante yana basar da tinaninsa akan zancen kukan sumayyah yace

” ba komai bane wani yaron dana sa aka dauka aiki ne ya kira.”

Basar da zancen Dad kaante yayi cikin manyanci irin na wanda tarin arziki yagama hudawa tako ina komai a hankali kwance ba sakawa hayaniya sai ciwon kai da ‘dayan ‘dansa yake sakar masa wanda idan ba DD kaante din ba babu wanda ya isa tayar masa da hankali ya sanyasa shiga tinani.

Kallan hoton DD din da shi kadaine hotonsa ya isa a maqala a palon Dad kaante din dana Oga kwata kwata wato kakansu shugaban family din gabaki daya wanda shine Asalin Kaante din wato Dalhat kante.

Shi kansa Alh bilal hoton DD din ya kalla kafin ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa yace

“Dad insha Allah zan gwada masa magana zai dawo ko zuwa qarshen watan nan ne”

Numfashi mai dumi Dad kaante din yakuma sakewa a karo na ba adadi sbd ya rasa tayaya DD yake iya sakar musu pressure,

Tayaya zai dauke mahaifiyarsa da qanwarsa sama da watanni Shida suna gurinsa Zurich,

Meyasa bazaiyi tinanin anan din yaya ake ji babu su din ba,

Ina matsayin mijin Mahaifiyar tasa kuma mahaifinsa dana qanwar tasa daga zuwar masa ziyara ya riqesu,

Sam baya duba bacin Raina dana DD babba akan hakan koyaushe mahaifiyarsa kawai ya sani.

Chapter 13

Hakuri Sir bilal ya sake bawa Dad kaante tareda tabbatar masa da zasu dawo qarshen watan da yardar Allah harma da DD din idan Allah ya dorasa akanshi.

Cikin ‘yar damuwa Dad kaante din yayi sallam da Bilal ya fito yana fidda wayarsa dan kiran Sulaiman da hankalinsa yake kansa.

Motarsa ya nufa batareda ya nufi babban part dinsa ba dayake gefen mansion din iyayensa ba duk acikin guri daya.

Yana shiga motar ya rufe ya saka kiran Sulaiman wanda shima yake zaune yana jiran kiran maigidan nasa dan sake kora masa bayani.

Kiran Sir bilal din na shigowa wayarsa ya dauka da sauri yana sake gaishesa kafin ya sake masa bayanin komai na abinda ya fahimta.

Shiru Sir bilal din yayi kafin ya kashe wayar yana tinanin menene zai saka sumayyah kuka da damuwa har a hanya?

Tada motarsa yayi yana kallon time sbd yanada meeting da baqin masu mahimmanci ga DD yana buqatan nutsuwa yayi magana dashi ta waya Dan haka ya daure ya wuce office idan Yaso washe gari da wuri zai sameta school yaganta.

Washe gari Koda ya isa suna cikin exams dan haka ya zauna cikin motarsa yana jiranta.

Tsawon mintina talatin da shida yayi yana jira sai gata ta fito ta nufa inda suke zama yau din ma bata cikin kuzari sbd zuwa lokacin tagama saddaqar da masifar da zata shiga ta Ababa.

Kokarin zama takeyi qamshin tirarensa ya shiga hancinta ta dago da sauri tana ganinsa tayi saurin maida kanta qasa tareda zamewa ta durqusa ta gaidasa cikin tsananin girmamawa.

Yanayinta yake sake karanta yanason magana da ita amma sanin hankalinta bazai taba kwanciya ba sai yace ta biyosa kawai.

Kaman baiwarsa haka tabi bayansa kanta a qasa cikin nutsuwa.

Motarsa ya bude mata tashiga shima ya zagaya ya shiga tareda rufe motar yaja suka bar makarantar saida sukai tafiya mai dan nisa zuciyarta na bugawa

Qafafunta tini suka fara rawa saidai bata iya magana ba.

Inda babu mutane sosai yayi parking ba tareda ya kashe motarba sbd Ac ya juyo ya kalleta cikin nutsuwa ya sauke numfashi mai dumi tareda ajiyar zuciya kai tsaye yace

“Meyasa kiketa kuka yau sulaiman yace akwai matsalan dayake damunki,

Ko zan iya sani idan ba damuwa.

Idanuwansa ya zuba mata yana jiran amsarta,

Shiru tayi bugun zuciyarta da rawar jikinta na bayyanuwa ga hannuwanta dake rawa.

Hannuwanta ya kalla yaga yanda suke rawa a hankali kafin ya maida idanuwansa kan fuskarta yana sake tabbatarda akwai matsalar dake damunta.

Maimaita tambayarsa yayi cikin kulawa nan ma kasa magana tayi ta girgiza masa kai kawai ahankali.

Ganin hakan yace

“Inaga zanje gidan da kaina naga Babanku sai naji ko wani ne a gidan ba lafiya”

Jin hakan yasa gabanta mummunan faduwa sbd duk yanda suka kai ga kamewa da kiyayewa tareda taka tsantsan koyaushe da zuwa gidansu yake musu barazana yana taimakonsu dan kuwa duk abubuwan dayake musu saiya basu tsoro ya firgitasu da cewan zashi gidansu gurin babansu suke yarda su karba taimkonsa.

Bude baki tayi cikin sanyin jiki da damuwa ta sanar dashi bata gane komai na karatun da sukeyi ne har jarabawar.

Shiru yayi yanason fahimtar zancen nata da kyau sbd jin zancen yayi kaman kai tsaye da yawa dan haka ya sake kallanta da kulawa yace

“Karantarwar ne malaman basu iya ba basayin yanda zaku gane kokuwa?

Shiru tayi sbd muzantar datayi saidai kuma daman su din ba masu wata darajar da zasuce basu saba da muzantar ba dan haka a sanyaye tace

“Aa nice bana ganewa,kaina baya gane komau” da wasu irin hawayen kunya da muzantar kai ta qarasa zancen.

Ya fahimci abinda take nufi dan haka jikinsa yayi sanyi da tausayinta dakuma nauyin zancen dan kuwa a familynsa marasa ilimi zaune a kansu basa karbuwa a Kaantes saukin abin suna dubawa hardana Addini ba iya bokon kawai suke so daga matayensu ba.

Ahankali ya sake kallanta yana sake jera mata tambayar yanayin yanda tayi last session dinta da yaya results din suke.

Batada zabi bayan fada masa gaskiar bataci komaiba a bayan duka wannan semister din ma courses din datake carry over dinsu yafi wainda zatayi a semister din yawa.

Wayarsa ya dauka ya saka kiran wata number ta wata lecturer mace wanda tana dauka kai tsaye ta hau gaishesa.

Cikin mutuntawa ya amsa yana tambayarta aiki da dama da student ta amsa da duk lafiya kalau,

Cikin natsatsen turancinsa daya kama bakinsa kusanma fiyeda hausarsa sbd zamansu a qasashen turawa fiyeda nan din idan ba yanzu daya dawoba sbd su biyu ne ‘yaya maza a familyn kuma idan ba shi din ba DD bazai taba dawowa dan karban ragamar kula da huldodin kaantes ba.

Bayani sosai yayi mata akan zata samar masa da wadda zata ringa yiwa Sumayyah karatu yanda zata gane.

Kai tsaye ta amsa masa da an gama insha Allah ita da kanta ma zata ringa dan budewa sumayyah din karatun da engausa sbd a yanda ta fahimta may be harda turancin yasa bata gane karatun dan haka zata ringa gwada yi mata bayanin karatun da mafi hausa kafin idan tagane sai akoma na turancin.

Godiya yayiwa Ms Ayshan ya kashe wayarsa bayan ta basa time din dazai ringa kai mata sumayyah din gidanta.

Sumayyah data dan fahimci wasu abubuwan dayake tattaunawa da Matar shiru kawai tayi sbd iya saninta hakan bamai taba yiyuwa bane zuwanta wani gurin ita daya,

Me zata cewa Ababa,Anne da Benazir idan suka ji?

Bayani yakeson yi mata amma yana iya ganin tashin hankalinta afili akan zancen dan haka sai kawai ya dora hannuwansa akan steering motar yaja suka fara tafiya yana mata bayanin cewan zai sake magana da Ms ayshan ta ringa yi mata karatun a makaranta kawai ba sai gidanta ba.

Da haka ya maidata school ya tafi cikin sauri sbd yayi lattin meeting dinsa,

Ita kuma tana komawa wata exam din tashiga tana cikine Ms aysha din tazo nemanta dan haka tana fitowa kai tsaye office dinta ta nufa.

Da farko qare mata kallo Ms aysha tayi tana mamakin meya hada Sir bilal da sumayyah din amma kuma data qure mata kallan sai taga kyakkyawa ce hutu da gyara ne kawai bata samuba,to kuma koma menene ba ruwanta abinda yake gabansu zasuyi.

Gurin zama ta nunawa Sumayyah din tana mata tambayoyi daya bayan daya.

A tsarge sumayyah din take amsawa har Ms ayshan ta ringa dan janta da fira sbd ta saki jikinta ganin duk a kame take da rashin sakewa.

Ms Aysha wayayyar babbar mace ce kuma mai saukin kai da fahimtar komai cikin sauri,

Kai tsaye ta fahimci so da kaunar sumayyah mai tsanani a tareda Sir bilal gashi sumayyah din kuma kaman bagidajiya ce.

A ranar dai basuyi komaiba fira kawai Ms ayshan tayita janta dashi sbd tafison tafara sakewa da ita ta yanda zata fahimci matsalar karatun sumayyah din da kyau.

Chapter 14

***********

A hanyarsu ta komawa gida Sumayyah ta fadawa Benazir komai tana tambayarta ya zatayi.

Numfashi Benazir din ta sauke sbd ita kanta yanzu karatunta ya cake wahalarsa take sha sbd yanda kusan semister din taqare mata gurin attending lectures din sumayyah da kula da sumayyahn gashi daman yau gabaki daya da tinanin yanda zata taimkawa ‘yar uwar tata ta wuni har acikin exams dinta tinanin takeyi shiyasa yauma duka jarabawan datayi sai duai itama.

To amma jin hakan yasata shiga nazari sbd Ms Aysha babbar mace ce da kusan makarantar kowa ya santa dan tanada kulawa da mutunta kanta dan haka idan har zata taimakawa Sumayyah karatun kuma acikin makaranta ha wani gurin daban ba to kaman duka an taimakesu ne sbd itama sanin sumayyah nada inda ake koyar da ita karatunta to itama zata samu nutsuwar yin nata karatun kada ayi haihuwar guzuma a tsakaninsu kowa da F.

Hankali kwance suka dawo gida saidai koda suka dawo Annensu ta kona kayan guga kaman yanda sumayyah tayi kwanaki,

Bai daketa ba ita amma wani mahaukacin marin daya taba lafiyar kunnenta daya ya shimfida mata a fuska take kunnanta daya ya dauke sauti batajin komai har dashi har sika dawo.

Fuskarta dukkansu suka kalla lokacinda suka shigo tana zaune tsakar gidan tana tuqa tuwon yamma datayi a tsakar gida kan gawayi.

Gefen fuskarta a kumbure yake shatin hannuwansa duka biyar sun fito baro baro akan fuskar,

Bakinta daga gefe ya kumbura shima yayi tsayi kaman anja ledar ruwa.

Karyewa zuciyoyinsu sukai da ganinta a hakan amma ba daman nunawa idan ba daki suka shigaba gashi hande na zaune tsakar gidan tana shan redionta hankali kwance.

Daki suka wuce bayan sun gaida Handen ta amsa

Suna shiga suka tube abincin da sukazo dashi yau din jin sikai duk ya fice musu aka sbd ganin halinda Annensu take ciki.

Ajiye jakunkunansu dasuka gama yagewa da warwarewa tin na shekarar farkon da aka siya musu kuma ma na gwanjo ne.

Fitowa sikayi Benazir ta amshi aikin abincin kai tsaye taci gaba duk da ga magrib ana kokarin kira,

Sumayyah kuwa tarin wanke wanken dayake jibge ta debo ruwa a drum ta zauna tafara gashi tsaban tsaftar Ababa baa wanke kayan cin abincinsa so daya sai anyi so biyu a dauraye kusan so uku sbd duk randa yaji qamshin omon wanke wanken a cup idan zaisha ruwa kokuma a plate idan zaici abinci to wanda yayi wanke wanken saiya gagara shan ruwa a ranar sbd mari ko harbi da qafa.

Anne kuwa tsintsiya ta dauka ta hau shara sbd ayyukan daman koda suka dawo duk sun hade mata gashi tin karin safe sai abincin da Ababa din ya rage da rana Yabata yunwa ke cin hanjinta amma sam bata nunawa ‘yayanta ne kawai suke mata kallo daya su gane halinda take ciki.

Sai bayan magriba suka kammala ayyukan sikai alwala suka shige ciki bayan anbasu kasonsu na abinci a roba daya suda Annensu daman haka aka saba tin lokacin sunada yawansu bare yanzu da iya su uku ne kawai.

Sallah sukayi suna idarwa Benazir ta fito ta dora ruwan zafi a kofin silver sukai zafi sosai ta dawo daki dasu ta dauki dankwalinta wankakke ta ringa taba ruwan zafin dashi tana matsewa tana dan gasawa Annen fuskarta da bakinta harma da idonta daya dayayi kwanciyar jini aciki.

Bayan tagama mata Annen taji dan saukin radadin da gurin ke mata suka fidda abincinsu sukaci suka koshi sauran Apple Biyu da wani tsadaddan cookies Benazir tayi masa wani irin boyo a cikin kayansu sbd Annensu taci ta safe dan yau sunga alamar ta jigata da yunwa sosai da alama andena bata abincin rana itama sbd suma baa basu yanzu idan suka karya suka fice sai sun dawo da yamma abasu na dare.

Da zazzabi mai qarfi Annensu ta kwana ko tashi zaune bata iya yi sosai,

Kallanta Benazir tayi taji bazata iya barinta ahakan ba kuma aikine zatayi bayan tafiyarsu har saita kusa sumewa kilan,

Dan haka taqi tafiya ranar makaranta sbd exam daya ce da ita kuma sai 2 na rana dan haka bayan fitar Ababa sumayyah ce kawai ta tafi ita ta zauna tabawa Annen apple da cookies din taci daqyar tareda ruwan lipton din da aka basu matsayin karin safiyar.

Chapter 15

Akace Salati baya hana daukan rai hakama qaddara yashi ce ko an daunqulata bata dunquluwa,zuciyar Sumayyah batai shawara da ita ba acikin qanqanin lokaci ta saka bilal cikin kanta.

Har Benazir ta samu sauki kuma interval nata ya qare ta dawo suka ci gaba da exams bata fahimci ‘yar kusanci da shaquwan da Sumayyah ta samu da Ms aysha da Sir bilal ba sbd hankalinta gabaki daya akan jarabawarta ya koma sbd babu tsayawa yanzu saita gama duka exams din.

Sumayyah kuwa itama ba dan laifi Ms aysha na iya kokarinta akanta ga bilal yanzu da duk ranarda baizo ya ganta ba a wayar Ms aysha yake magana da ita.

Tin tana jin nauyin ms ayshan sosai harta dan sake da ita sbd a rayuwarsu basu taba samun kulawa,kauna ko tattali da sakewa daga wani ba wannan ne karan farko datake samun hakan daga Bilal da ms ayshan.

Koda suka gama exams suka fara zaman hutu daga bilal din har sumayyah jin sukeyi ba dadi musamman shi din.

Benazir Tinanin result da yanda wahalarsu ta qaru ba sauki yasata gaba,

Abincin dasuka saba dashi kuma na Kaantes H&S yanzu dasuke hutu ba daman cinsa sai suka taru sukai wata irin rama sbd yunwa kaman wainda ake dibansu ana girkin gidan dasu.

Yar lafiyar dasuka samu ta jiki sbd cimar dasike ci mai kyau da lfiya tini ta gagaresu sbd yanzu aiki ne kan aiki da yunwa kan yumwa duk sun sake ficewa hayyacinsu gasu yau lafiya gobe babu sbd marika da harbin qafa,Annensu kuwa tini Ababa ya haukatar da dodan kunnuwanta da marika dan haka yanzu kusan idan kana nesa da ita bata jinka sosai idan ba murya zaka dago ba.

Cikin ha ula’i da ukuba sikai hutun sika gama aka koma karatu,

Ranar dasuka koma mashin sika hau kaman yanda suke hawa a baya,

Sunje makaranta sun duba time table nasu kaman mayu suna cikin wainda basu qara ko kwana dayaba,

A gantale suka wuni makarantar sika dawo Ms aysha ma bata shigo ba ranar dan haka Sumayya jiki a sanyeye ta dawo gida.

Sallah sukai suka fito qarasa aikin da Anne bata gama ba suka shige bayan sinci Shinkafar da aka basu.

Washe gari suna fitowa suka ga sulaiman yana jiransu inda suka saba ba bata lokaci suka shige a yanzu dasuka fara ita boye abu kudinsu na makaranta sun dena bayarwa dika rabi suke boyewa suna sadakar rabin shiyasa harsun fara tara ‘yan kudaden da ko basu fada ba na guduwa da Annensu ne insha Allah.

Suna isa makaranta Sumayyah na kama hanyarta Ms aysha ta aiko kiranta dan haka itama cikin jin sanyi a ranta ta nufa office dinta.

Cikin kulawa da farin cikim ganinta sosai ms aysha ta tarbeta tareda cewa ta zauna

Nan ta fara tambayarta ya hutu da sauran abubuwan.

Bata wani jimaba ta tafi lectures saidai baa kira  Sir bilal ba yau din sukai magana.

Tana barin office din ms aysha ta kira Bilal ta sanar dashi irin ramar da Sumayyah din tayi sosai a dan lokacin hutun.

Suna fitowa da yamma maimakon sulaiman Bilal ne yazo daukansu cikin daya daga cikim motocinsa masu shigen daukan ido da hankaliz

Kaman marasa gaskia suka gaidasa ya amsa cikeda kulawa idanuwansa na kan sumayyah data kasa dagowa ta kallesa sbd kunya da farin cikin ganinsa.

Shiga motar sukayi suka bar makarantar tin kan wani ya gansu duka kama hanyar gida.

A motar Benazir kawai ya danyi magana da ita sumayyah kuwa da idamuwansa yake maganarsa da ita

Ita kuma bata iyaba bata ganewa duk sai neman rikicewa takeyi.

Suna isa a tare suka fice motar suka kama hanyar gida batareda Benazir ta taba tinani ko fahimtar wani abu na faruwa da Sir bilal ba da Yar uwarta.

Ayau abincinsu na musamman ne sbd da kansa ya karbo musu dan haka sina sallar magrib suka zauna sukaci suka koshi take Anne tafara amai sbd wunin ranar so daya taci abinci.

A boye tagama aman suka kwashe suka wanke sbd kada aga aman asan sunci wani abin bayan tuwon da akai gidan.

Da omo mai qamshi sika wanke koina dan haka dakin bayan qamshin omo babu abinday yakeyi baka cewa anyi amai.

Suna gamawa sallar ishai sukai kawai suka fito suka danyi wankin shago da baida yawa yau koda 9 tayi sun gama sun shige sun kwanta.

Washe gari ma Bilal ne yazo daukansu hakama a dawowa.

Saida suka share kusan sati da komawa Bilal ne yake kaisu da daukosu har saida tsarguwa da tsoron Benazir ya bayyana a fili tukuna Sumayyah ta rokesa ya dena zuwa din sulaiman yaci gaba da daukansu.

Koda result dinsu ya fiffito Benazir ta fadi Course daya Sumayyah kuwa a duka uku kawai taci suma da pass,

Dukan dasuka sha kuwa saida Sumayyah ta kwanta jinya sosai wadda ta qara mata shakuwa da kusanci da Bilal da ms Aysha dasuka fahimci babansu ne keda wani irin zafin dayake dukansu.

Kulawa da tattali sosai sumayyah ke samu daga ms aysha da bilal harma da benazir ana tattalinta saidai nata bai kai wanda sumayyahn take samu ba.

*******lokaci ya dan ja semister tayi nisa zuwa lokacin tafaru ta qare soyayya mai qarfin gaske ce a zuciyoyin Bilal da sumayyah wanda suke yinta boye batareda sanin kowaba sai ms aysha da benazir wadda ba qaramin shock ta shiga ba da Sumayyah din ta sanar mata amma kuma kirki da tsananin mutinci da girman kaunar da Sir Bilal ke musu yasata jin hope a ranta na akwai yiyuwar Allah ya kubutar dasu ta hanyar Bilal din kila.

Kuma ganin yanzu sumayyahn na gane karatu ba laifi yasata sake jin girman Sir bilal din da ms aysha cikin ranta,.

Tafiya tayi tafiya Ita kanta Benazir Ms aysha ta shaqu da ita sbd wani irin tsananin tausayinsu datake ji yasa mata kaunarsu sosai musamman Benazir wadda zuciyarta ke danqare da damuwa da quncin rayuwa fiyeda sumayyah sbd sumayyah yanzu Bilal shine sanyin dayake narkar da nauyi da quncin zuciyarta.

Sunyi hutun qarshen session din results dinsu yayi kyau Benazir bata fadi ko daya ba sumayyah ma kusan taci sosai dan iya biyu kawai ta fadi duka da sauran daqyar aka wucesu.

Zuwa lokacin boyayyar soyayyarta da Bilal tayi wani irin nisa da qarfi ta yanda aurenta yakeson yi matiqa saidai babban tashin hankalin daya fara tinkarosu shine mahaifinsa kai tsaye baiyi naam da maganar ba batareda yaji sauran bayanin ba yace sun riga sunyi magana da senate president ‘yarsa zai aura.

Sumayyah ma a nata bangaren yanatason yazo yayi magana da Ababa amma tsoro ya hanata barinsa sbd abinda bai saniba duk ranar da ababa yasan sun taba kallan wani namiji ba bare soyayya wlh zai iya konata bare yayi alqawarin fasa idanuwansu idan hakan ta faru.

Ta bangare daya kuma cimar dasuke ci mai kyau da lafiya tasa fatar jikinsu da jikin nasu sauyawa sosai tayi fresh da kyau alaman ana cin cima mai rai da lafiya.

Komai yana son siya musu sbd yanason ya sauya rayuwarsu zuwa rayuwar da basu taba tinanin zasu kai ba,

Yanason barar musu da dukiyar da basu taba tinanin akwai ba,

Yanason inganta rayuwarsu ingatawar da wasu yayan masu arzikin basu samu ba sbd Nasu arziki da dukiyar da Allah yabasu kaates tanada yawan da bazasu iya fadar adadinta ba.

A bangaren Ababa rayuwarsu bata taba canjawa ba da matsayinsu na kamar dabbobi gidan,

Dukansu da azabar da ake basu tana nan babu abinda ya sauya saima qaruwa sbd kullum karatunsu sake cin kudinsa yakeyi dan haka azabarsa akansu take qaruwa ga shagonsa na wanki ya sake bude wani sbd sosai kasuwancin wankin ke tafiya dan haka ya sake bude wani shagon kuma duk sune masu wanki da gugar kawai dai iyakaci yaran shagon su saka a leda ayi packaging kaman na kamfani a bawa me kaya idan yazo karba kuma yawanci manyan mutane sosai yanzu suke kawo wanki shagon dan haka manyan motoci matsu tsada ake aiko masu karban kayan wanki shima kansa Ababa tini ya tanadi mashin suka fara delivery din kayan da kansu idan an wanke.

Ms Aysha itace take taimaka musu sosai yanzu kusan itama a boye dan haka soyayyar Bilal da sumayyah taketa qara nisa da qarfi.

Sumayyah sun gama nasu karatun gyara ne kawai takeyi yanzu sabanin Benazir da yanzu karatunta yake qara nauyi sbd tana 300lvl gashi Accountancy take karanta.

Sosai hankalin Benazir ya duqufa kan karatunta sbd ganin sumayyah na gane kartu sosai dan haka ta dena damuwa da karatin sumayyahn ta kama nata.

Yanayin yanda karatin nasu ya hargitse yasa dole badan Ababa yaso ba a ringa raba musu kudin abin hawa sbd tsananta tsaronsa akansu duk wanda ya gama baya jiran daya ya dawo gida.

Nasir Ahmed wani dan kyakkyawan saurayi dayake final year dinsa a Accounting kuma kuma kusan shine guru din course mates dinsa tin Benazir na first year dinta Allah ya saka masa kaunarta amma bai taba tinkararta ba sbd yanda take kame kanta.

Ya dade yana bibiyarta amma ba fuska sai gashi Allah ya hadasu sanadiyar wani course da itace tafi kowa cinsa shine lecturer din ya hadata da Nasir yana qara mata haske akan course din sbd yanada matiqar wuyar gaske shiyasa malamin ya jinjina mata data cinye tana mace.

Karatu shine ya kawo mutunci da yar shaquwa a tsakaninsu amma sam babu sakewa sbd yanda take tsorace sosai da Muamalar tasu,

Shi kansa daya fahimci tsoro fa fargabar ganinsu da akeyi tare sai ya ringa sirrintawa yana samunta gurin zamansu da sumayyah inda ba mutane acan suke karatun.

Son Benazir yake sosai da gaske dan haka yake tsananin mutunta ta kuma ita kanta tana mutuntasa a zuciyarta saidai duk yanda zuciyarta taso saka mata wani abin daya zarce hakan saita hana kanta sbd idan suka bari wani abin ya shiga tsakaninsu to tabbas ita a bangarenta tasan suicide mission ne dan kuwa shi kansa Nasir din tasan saiya shiga tashin hankalin abinda zai biyo bayansa idan ubanta ya sani dan haka take dan baya baya da duk wani tinanin daban amma kuma zuciyarta ta basa matsayi mai mahimmanci amma bai zurfafa ba.

Chapter 16

16

Annensu yanayin manyanci da wahala ga kunnenta da bataji yanzu sosai yanda ya kamata yasa jikinta da lafiya suka fara yimata qaranci yau da gobe wasu ayyukan bata iya yinsu da kyau dan haka sune suka karbe mata duk wani aiki saidai idan suna makaranta a bata wani aikin shima suna dawowa zasu karban mata hande tayi ta fada amma karba sukeyi saidai wata ran susha marika gurin Ababa akan sun fara Rena hande.

Sbd Anne yasa Benazir takoma gaggawa takewa karantunta ana tashi take dawowa bata batar da lokaci ko qanqani Shiyasa basa dawowa tare da sumayyah kusan tafiyarsu yanzu tare ta rage sosai,

Sumayyah tafara IT dinta a wata makarantar kusa da anguwarsu dan haka Ababa ya dena bata kudin mashin ita da qafa take zuwa ta dawo da qafa dan haka take rigan Benazir fita tinda safe.

Bilal ne da kansa yake kaita lokuta da dama kuma ya daukota ita kuma Benazir Sulaiman ne yaci gaba da kaita kuma abincinta babu wanda aka fasa kawo mata makaranta kaman yanda itama sumayyah acan ake kai mata nata.

IT din sumayyah ya sake kusancinta da Bilal kwatsam saiga maganar aurenta da wanda yayi alqawarin bawa yana karban kudinsa akan karatunta ta taso sbd karatun nata yazo karshe dan haka maganar aure ta taso take gadan gadan ba daukan lokaci.

Maganar auren ta rusa duk wani kwanciyar hankalin Bilal ita kuma dukkanin hope din data samu ya wargaje sbd tasan maganar Ababa bamai fasuwa bace ko gardamawa,ko mahaukacin kare ya cijeta bazata iya ko dagowa ta kalli Hukuncin Ababan ba bare gardamawa.

Abinda ya dagawa bilal hankali kenan wato sarewarta da kasa iya cewa komai akan hakan sbd shi anasa bangaren yaso ta basa hadin kai da goyan baya ya sakewa Ababan Nera ba yar kadan ba dan ya hanawa kowa aurenta ya basa ita sbd a hankali ya fahimci irin asalin rayuwar rashin gata da yancin dasukeyi hannunsa dan hakan ne ma yakejin idan bai karbesu su dakan daga hannun Ababan ba kaman zai iya shiga wani halin sbd zai iya komai dan ya rabasu da gidan dan haka auren Sumayyah din yake jin tabbas ba fashi garesa da yardar Allah.

Benazir tayi nisa a karatunta batasan tashin hankalin da suke cikiba saida Yaje daukanta da kansa ranar yake sanar da ita irin yanda yakeson daukesu daga gidan suyi rayuwarsu kaman kowa.

Haka kuma a shirye yake da auren Sumayyah ta roketa tabarsa yaje gurin Ababan dan yana qin zuwan ne sbd baisan kalan azabar da zai janyo musu ba shiyasa yaketa kiyayewa.

Ita kanta Benazir jin hakan saida takusa shidewar mintina sbd firgitaccen tashin hankalin wucin gadin data shiga sbd zuwansa gurin Ababa koda motar kudi zai ake masa wlh saiya kusa aikasu lahira kafin ya amsa kudin sbd sun take qaqqarfan doka da sharadinsa akansu na kula kowane irin namiji.

Cikin rashin boye masa tashin hankali da tsoronta taqi amincewa zuwansa itama,

Anne ma dataji da sauri ta hanasu qarasa zancen sbd kusan da hannu suka kwatanta mata rabin zancen tinda bataji sosai sai an dan daga murya gashi zancen bana a daga murya bane wani yaji Alqiyamarsu ta tsaya.

Wanna maganar tasa ta sanya kwata kwata suka fara qaurace masa ga tsananin Ababa akansu ta qaru dan kusan yanzu dabiar kai musu ziyarar ba zata ya dauko dan haka suka shiga taitayinsu ba shiri

Ko hanya suke tafiya basa dagowa.

Kusan sati biyu Bilal yayi bai saka daga Sumayyah har benazir a idanuwansa ba dan haka ya shiga damuwa da tashin hankali sosai sbd kar Ababa fa yayiwa Sumayyah aure bai saniba.

Ita kanta sumayyah tana cikin damuwa da qunci ga dukan da yanzu kusan kullum sai tasha sbd tinani ya hanata nutsuwa ta aikin data saba kullum saita qona manyan kayan mutane gurin guga dan haka a cikin qanqanin lokaci ciwonta yafara kokarin dawowa na kai,

Benazir na ganin haka tafara kokarin kada Ababan ya gane ciwon Sumayyah saidai kuma kusan abin gaba gaba yafara sbd da asarar datake ja masa tayi yawa sai ya hanata fita kwata kwata makarantar datake IT din bayan wahala da duka babu abinda take samu kullum a gurinsa.

Ganin lamarin yafara yawa tsoron Benazir sai qaruwa yakeyi ga Anne itama yau lafiya gobe ciwo sai abin yawa Benazir yawa tafara skipping lectures itama sbd lalura da ayyukan da karatun.

Daqyar da Addua Ababan yabar sumayyah tafara fita takoma makaranta bayan ta share kusan sati uku ko kofar gida bata isa ta leqa ba.

Koda tafara fita batada lafiya sosai dan haka suna isa makaranta Ms aysha ta dauketa da kanta a motarta sukai asibiti ita kuma Benazir tanada test a ranar dan haka ms aysha tace tayi zamanta.

A asibitin ba bata lokaci Bilal da ms aysha ta kira ya iso cikin mummunar damuwar halinda sumayyah din take ciki ta rame sosai ta sauya gabaki daya kaman wadda tai jinyar shekara guda kwance.

Ruwa da magani aka hau dara mata

Ko minti uku basuyi da fara shiga ba ta hau zubo amai mai qarfi.

Sosai ta bata jikinta dan haka ms Aysha ta kamata bayan ta gama suka shiga toilet tayo wanka akai mata ordern kayan ba jimawa mai delivery ya kawo Bilal dinne ya karba ya miqa mata ta kofar toilet din sbd Ms aysha ta wuce ankirata da gaggawa Mijinta ya dan samu accident.

Sauya kayan tayi jiki ba qwari ta fito jiri na dibanta daqyar ta dawo da kanta gadon ta zube take aka sake maida mata ruwan wani wahalallan bacci ya dauketa.

Baccin awa hudu tayi ta farka,

Abinci yafara bata taci ba laifi kafin taje toilet da qyar tayo fitsari da Alwala ta dawo tayi sallar a zaune sbd bazata iya tsayuwaba,

Tana idarwa ya karban musu sauran maganinta yace gida zasu sbd kayanta dayakeson suje a wanke a shanya su bushe in time ta mayar dan yasan ko tsautsayi bazaisa sumayyahn taje gida da wasu kayan ba wanda ta fito dasu ba kuma gashi doguwar riga ce mara nauyi har qasa amma ta kwanta jikinta tayi mata kyau sosai duk da tana cikin hali na ciwo.

Kai tsaye wata anguwar dake zagaye kaman ta masu qasa ya nufa da ita wadda ta sanyata jin zazzabinta na sakinta sbd kusan duka gidajen anguwar ba tsarin ginin Nigeria bane,

Anguwa ce mai tsarin gine ginen Turawa masu tsada na asalin masu abun Hannu na gasken,

Tin daga babban gate din shigowa anguwar baka shiga saika fada inda kazo ka kuma nuna id card din kowane iri hakama commercial abubuwan hawa basa shiga anguwar kwata kwata,

Manyan samudawan Securities ne wani kamfanin securities mai zaman kansa suke gadin Anguwar da bazaa kirata da estate ba sbd ba estates din bace amma   Tamafi estate tsari.

Id card dinsa ya fiddar suka duba suka scanning motarsa yafada gidan wanda zashi saida ya fada private security code na gidan da zashi din wanda kowane gida akwai private security code da ake basa duk wanda zaizo gidanka sai fada masa code din ya fada a gate abarsa ya shigo.

Wangale masa manyan kofofin gari guda akai ya shigo da motarsa tareda miqewa kai tsaye zuwa gidan DD kaante wanda kaf gidan shine ya zabi zama wata anguwar daban ba acikin babban kaantes ba,

Shi kadai ya zabi rayuwarsa daban sbd yinta yanda yake so da buqata,ba damuwa,ba hayaniya,ba takura haka zalika rayuwarsa da zafin kansa dake hanasa jituwa da Mutane musamman Dad kaante wato mahaifinsa daya kasa gane haka Allah yayisa.

Duk matsi da takura tareda fadan Dad kaante da dd babba wato kakansu sunyi sun hakura amma bazai iya zama a can cikin family ba,

Baya son kusanci da gidane sbd rayuwarsa bayason duk abinda yake amfani dasu na daily life dinsa ya zama mutane na kusanta,

Idan har yana gida yasan umminsa da sister dinsa da brothern nasa da dad kaante harma da wasu baqin wata rana duk zasu ringa shigar masa ana muamalantar abubuwansa dan haka ya zabi zama a gidansa a anguwar datake da iya tsaro,tsafta,tsari da dokikin dayake so na rashin hayadan ko horn baayi aciki idan ka shigo.

Isarsu kofar gidan yasa Jikin sumayyah sake daukan rawa sbd kusan ko a hanya dasuke wucewa a anguwanni hanyarsu zuwa makaranta bata ganin irin wainnan gidajen dan haka jikinta yayi sanyi ta qara rasa kuzarinta.

Codes na bude kofar qaramin gate din gidan ya saka gidan ya bude suka shige ya sake saka na kofar shiga asalin cikin gidan kofar ta bude ya saka kai ciki kai tsaye yana janye da hannunta sbd batada karfin tsayuwa da kyau.

Dummm kirjinta yayi na kokarin rage jan numfashi sbd wani Ni’imtaccen qamshi daya shiga hancinta duk da gidan tsawon lokaci sosai ba kowa amma qamshinsa daya gama kama komai da koina na gidan ya kasa fita hakama komai na gidan tamkar kullum ana shigowa ana gyarawa komai nasa daban ne.

A rayuwar DD kaante daga black sai fari iya sune kalolinsa sai ta kama cancan ga gansa da wasu kalolin da bazasu wuce milk,ash,navy blue shikenan suma dan suna yanayi da kalolin nasa ne wato black and white,dan haka gidan nasa ya zama kusan komai na cikinsa iya wainnan kalolin ne dan haka komai yake unique na masu dala,

Luxuries kawai ta ko ina daga dala sai dala babu abinda bana Waje waje ba.

Zaunar da ita Bilal yayi yaje ya kunno switch na wutar gidan take ta kawo koina ya dauki wani irin Haske su Ac daman duk a kunne suke switch dinne aka kashe na wutar gidan kai tsaye dan haka take suka fara aiki.

Dayake harda bra dinta ne a kayan shiyasa bai bawa wani ya wanke ba yazo yayi da kansa tinda Benazir na makaranta gashi ko sumayyah bazataso a hanata test dinta ba haka shima a yanzu dayake jin Benazir din tamkar Aleeya qanwarsa ta jini bayajin zai taba bari karatunta ya ringa samun tangarda.

Abinci da magani ya bata tanasha bacci mai qarfi ya dauketa ya kaita dayan dakin dake gidan bayan na DD sbd yasan ko DD bayanan wani ya hau masa gado zai gane sbd hancinsa dayake daukan qamshi ko sabaninsa nan take koman qanqantarsa yasan halinsa dan haka baiko kwatanta kaita dakik DD dinba wanda babu ma wanda ya taba shigar masa harshi Bilal din da baida tamkarsa.

Gyara mata kwanciya yayi ya rufeta ya rage Ac dayayi mata yawa sbd yanda ta dan takure duk da sanyi na wahala sun saba dashi.

Toilet yaje ya nade kayansa ya wanke mata kayan fes duk da bai wani iyaba sbd rayuwarsa kaf bai taba wanki ba sai ranar sbd undies dinsama a machine yake sakawa bawai wankin hannu ba suma mafi yawan lokuta mai aikinsa jamil ke wanke masa.

Bayan ya gama duk ya jiqa kayansa sbd rashin iyawar toilet dinma duk ya jiqa koina,

Chapter 17

17

Kallan kansa yayi a bathroom din yaga yanda ya lalata kansa da kayansa sai a lokacin ya tina da a washing machine ya wanke amma sai tinanin bai zo masa ba sbd kusan haka yake komai nasa na wautan ‘yayan fari wani lokacin duk da ya zama babban mutum hakan ne yasa kusan ko yaushe dd babba a gurinsa koyaushe DD ne a gaba sbd shima yanada zafi da rashin wasa dan haka komai na DD ya masa duk da zafin kan DDn ya wuce gaban nasa sbd shi harda lokacinsa dayake kai na young billionaire sbd dukiyarsa bata Familyn kaantes bace shine ya tara abarsa da businesses nasa wainda ke qara saka dd babba dukan kirji da DD kaante jininsa ne baibar komaiba a halinsaba sak,

Yayi kudi bada kudin familynsa ko iyayensa ba.

Sake kallan kansa yakeyi yaga ko fita bazai iya daga bathroom din a hakan ba ruwa ne sosai a jikinsa dan haka ya zare kayansa kawai ya sakarwa kansa ruwan zafi ya danyi wanka sbd jin kaman yana qarnin wankin ma.

Yana gamawa ya fito ya sanye da Bathrobe mai kauri da girma datai masa yawa sbd Baiyi jikin DD ba,

Shi jikin fulani ne dashi ba girna sosai,shi kuwa DD qaqqarfan jiki ne dashi daya bude sosai sbd Geamin dayake dan haka yanayin jikinsu sam ba daya ba.

Bacci takeyi sosai dan haka ya fice dakin ya nufi bedroom din DD amma a rufe yake kuma baisan codes ne ko key ba ya hana kofan budewa sai kawai ya hakura ya dawo ya koma bathroom ya jefa kayansa a Machine dan wankewa sbd idan yayi ordern sabbin kafin kafin su iso garesa time ya tafi sosai sbd a first gate ma zaa karba delivery din tukuna shima ayo masa aikesensu daga first gate duk taruwa zaayi a qara bata time dinsu.

Yana gama wankewa ya fito ya zauna kan lafiyayyar sofa din dakin yana amsa wayoyinsa a Ahankali.

******qarfe 6 na yamma Benazir ta kammala komai ta fito makarantar ta rasa yanda zatayi tasan Sumayyah na school kokuma ta wuce gida ko tana Asibiti har lokacin.

Batada wayar kira bare ta sani dan haka ta yankara kanta da sumayyah din tikitin Qaddara ta nufi gida tana fatan sumayyar na gida idan ba hakan ba yau suna cikin lissafin kwanan wahala.

Ana sallar magriba ta iso gida bata tadda sumayyah ba take jikinta yayi sanyi ta saddaqar da yau din saita Allah su a hannun Ababa.

Sallah sukayi da Anne ta fito tana wanki hankalinta na kan kofa cikin tsautsayi sai ga Ababa ya riga sumayyahn dawowa yana ganin yanda hankalin Benazir da Annensu ya tashi yasan Sumayyah bata gidan,Hande dake jiran dawowarsa tini tafara fesa masa labarin sumayyah bata iso gida ba har lolacin.

Shiru kawai yayi yana gyada kai idanuwansa akan Benazir zaiyi magana sai Sumayyahn ta shigo jiki a matuqar mace ba qwari zazzabi ne a jikinta sosai ga jiri tana gani komai na jikinta bata jinsa da qyar take daga qafafunta dasukai nauyi tana isowa tsakar gidan ta zube Benazir ta tarota tana jin zafin da jikinta yayi sosai.

Kallansu Ababan keyi cikin tsananin zafi da bacin rai da zallan takaici sbd hakurinsa akansu ya kusa qarewa kwata kwata,

Lissafin kudinsa akansu dayake yi yasa yake hana kansa yi musu dukan da zasu kakkarye ya zubar dasu a bola,

Hijab din jikin sumayyah ya cafko ta wuya yana shaqureta a zafafe yake saukar mata da marika yana tambayar uban me ta tsaya a hanya.

Daqyar ta iya bude baki tace masa batada lafiya tin jiyan shine a hanya ta fadi sai da aka kaita wani qaramin asibiti aka bata taimako.

Bakinta ya hau mari yana sake shawe wuyanta data kasa numfashi tana neman macewa.

Sai data kusa rasa ranta ya saketa yana wurgi da ita tareda qarasa sanya qafa ya rufeta da duka.

Daqyar suka sha bayan ya musu laushi itada benazir saidai Benazir din yan marika ne da basu wuce uku ba nata da sauki sosai sumayyahn ce dai taji jiki sosai.

Daki suka koma Annensu ta gasawa sumayyahn dake rawar sanyin zazzabi sosau jiki ta kwantar da ita tareda rufeta bayan sun bata maganin dasuke dasu yanzu suna boyewa batareda sunsan asalin meyake damunta ba take baccin wahala ya dauketa sbd Acanma saida Wata likita mace tazo ta bata magani da Allurar wani babban lamarin daya samesu.

Koda gari ya waye sbd kawai Sumayyahn ta samu ganin likita a asibiti yasa Benazir da Anne lallabata suka fita makaranta amma kam ko tsayuwa bata iyawa abin harya fara basu tsoro matiqa sbd bata taba zazzabin daya hanata ko iya daga qafafuwanta haka ba.

Suna fitowa ga mamakin Benazir Bilal ne yazo daukansu a qage yake kaman wanda yasan Sumayyahn batada lafiya dan kuwa gabaki daya damuwarsa da rashin sukuninsa a bayyane yake.

Da sauri ya fito motar ya budewa Benazir ta sakata baya ta kwantar ita kuma ta shiga gaba suka wuce.

Ba tambayar komai asibiti ya nufa dasu suna isa dayake likatansa ta jiyan ce sunriga sunyi magana karban sumayyan kawai akai aka daura mata ruwa da allurai dakuma sauran abubuwan dasuka bi baya.

Benazir bata taba ganin damuwa ko rashin sukunin Alh Bilal din ba sai yau duk da ba wani kallan mutane sukeyiba bare su tsaya karantar yanayinsu amma na yau din a bayyane damuwarsa take.

Wani irin tattali da kulawa tareda kauna mai tsananin gaske yake nunawa Sumayyah yana asibitin har ta dan farfado guraren 12 na rana,

Lafiyayyun abinci kala kusan uku aka kawo daga Kaante H&S

Benazir ce ta bawa Sumayyah abincin tasamu taci kadan dr zulfa tasaka wata nurse ta shiga da Sumayyahn toilet ta taimaka tayo mata wasu yan dubarun sai gashi sumayyar ta dan samu qwarin jikinta daga nan tayi sallah tana idarwa Wani baccin ya sake daukanta lokacin jikinta ya dan warware ba laifi.

Anan suka wuni daga ita har Bilal din wanda ya kasa ya tsare bai matsa koina ba saida yamma tayi ya dawo dasu gida kaman ya cinye Sumayyan da idanuwansa masu haske da kaunarta

Ita kuma takasa koda dagowa ta kallesa sbd Halinda zuciyarta da gangar jikinta sike ciki.

A gidan ma haka ta daure tana nuna kuzari da samuwar dan sauki sbd hankalin Anne da sumayyah ya kwanta.

Washe gari Benazir nada wata test dinma dan haka Bilal dake neman dama ya samu shi kadaine yayi jinyarta cikeda so mai tsanani da kauna tareda kulawa kaman ya mayar da ciwon jikinsa.

Dayake iya su biyu ne ranar kuka ta ringa masa zuciyarta cike da qunci saidai shima zuciyar tasa bata cikin dadi sai damuwar amma haka ya ringa lallabata harta dan warware sukai wunin cikin kulawa suka gama da yamma ya biya ya dauki Benazir suka koma gida.

Cikin kwanaki kusan bakwai shine yake jinyarta a sirrance harta warke sosai ta koma lafiya kalau hakama a daidai wannan gabar ya riga ya tabbatarwa da kansa aurenta koda zai dauketa ne subar qasar bada sanin kowa ba amma tabbas sumayyah tasa ce wlh babu me aurar masa ita.

Ita kanta sumayyahn a yanzu da qaddara ta kaisu wani matakin zuciyarta ta sake jarabtuwa dashi,

Yanda suke jin junansu fiyeda tinani cikin ransu.

Kulawarsa akansu ta qaru fiyeda koyaushe hakama yafara shirye shiryen yimusu passports dukkaninsu su ukun.

Sumayyah da benazir aka fara yiwa sbd zuwa lokacin ya sanar musu da manufarsa ta daukesu daga hannun Ababa zasu bar qasar zai kaisu inda zasuyi rayuwa kuma kafin su bar qasar yanason a daura aurensa da sumayyah din dan tini ya tanadi masu daura musu auren manyan malamai na mutunci.

Hoton Annensu akeso da thumbprint amma an rasa mafita saidai daga baya ya bawa Benazir camera a boye cikin dakinsu suka shirya Annen da Hande ta fita da rana sukai mata hoton sai bayan azahar suka tafi makaranta ranar sbd hoton kawai suna fita suka basa kuma cikin saa hotunan sunyi amma sam bazasuyi abinda akeson ba dan haka dole sai anyi dabarar fiddo Anne a gidan.

Anata wannan process din Tafiya ta kamasa dan haka yabar komai ga aje saiya dawo sbd case din DD ne da Dad dinsu sam yaqi dawowa gashi bayan zamansa ‘dan Kaantes business partner dinsu ne sbd ya zuba hannun jarinsa sosai a kamfanoninsu dan haka shares dinsa a kaantes suna dan da kauri kadan duk da suma akwai tarin abar.

***Bayan tafiyarsa sai sumayyah tayi sanyi sbd wani irin sabo da shaquwar da sukai kusan kullum saiyazo makaranta ya dubata da kulawarsa,

Ms aysha ma zuwa lokacin ta zama kaman wata uwarsu sbd sosai take hana kebawar Sumayyahn da Bilal dan ganin yanda yake tsananin santa kuma gashi akwai ‘yar rayuwar turai a tare dashi kada barna ta shiga.

Benazir kuwa karatinta takeyi bil haqqi hakama Nasir itama a nata bangaren tana jinsa cikin zuciyarta amma kuma bata taba jin zata iya tsayawa ta kulasa sbd Ababa da sharadinsa tareda gujewa babban masifar da zata biyo bayan ganewarsa Ababan.

Da wayar ms aysha kullum yake samun magana da ita har dai yayi dan busy ya rage kiran sai dare yake samun time kuma lolacin yasan ba lallai tana tareda ms aysha ba dukda time ba daya ba.

****Acikin sati uku zuwa hudu da tafiyarsa ramar sumayyah ta bayyana sbd yanda bata iya cin abinci sai iya na gidansu da ake basu bata iya cin wanda ake kawo musu daga Kaantes,

Gabaki daya tayi sanyi ta dena kuzari,Annensu data ga hakan ta dan ringa lallabata itada benazir a boye ba halin nunawa,

Makarantar daurewa kawai takeyi tana zuwa sbd kawai samun yin magana dashi a wayar ms aysha amma sam ko fita batason yi.

Aikin wahalarsu na gida kuwa kusan akan Benazir ya dawo sbd sumayyahn data fara yanzu rawa jikinta yake dauka sai jiri.

Tin Benazir da Anne basa lura har suka fahimta sosai take hankalinsu ya tashi sbd tsoron idan wani ciwon ne ya shigeta tinda yanzu ta koma yau lafiya gobe ciwo.

Maganin zazzabi da paracetamol suka ringa bata a boye sbd kada ciwon koma wane iri ne yayi mata karfi gwara ta warware kafin Ababa ya sani ya hadasu ya hukunta sbd ta dena aiki sai yakusa dawowa ta fito dan karya gane.

Tin suna boye ciwon Sumayyahn daya fara qarfi sbd koyaushe a zazzabi da jiri take makarantar ma ta dena zuwa har Hande ta gane tayita masifa tana qarawa daga qarshe dole suka ringa saka sumayyahn warewa tayi yan wasu ayyikan sbd kada Ababa yaji ya tsananta mata aiki.

Chapter 18

18

Ranar da suka wayi gari da sassafe a dakin sumayyah ta ringa amai tana dafe kanta dake ciwo cikin galabaituwa sbd da zazzabi ta kwana kuma ta tashi dashi.

Tausayinta sukeji sosai sbd sanin malaria ce kuma basuda wani taimakon bata bayan Addua dasukeyi akan samuwar saukinta dan Ababa ko zata shide bazai iya siyo mata magani ba bare kaita asibiti sam babu wannan a tarihin gidanma kwata kwata,

Bilal ne baya wasa da ciwonsu kowane iri ne koman qanqantarsa gashi bayanan bai dawoba.

Bayan gama Aman na Sumayyah da Hande na jin yunqurinta na aman me qarfi amma tayi banza dasu sbd tinanin sun fiya raki,

Shiru Anne tayi tana kallanta da idanuwanta dasukai zuru zuru tana qure kallanta sosai akan Sumayayan wadda duk sun qarar da maganinsu dasuke boyewa akanta cikin kwanakin amma babu wani sauki gashi ciwon dai baa kwance rigis ba a laulaye take yinsa kaman wata me qaramin ciki.

Dummm kunnuwanta da kirjinta sukayi lokacinda takai qarshen wannan kalmar tata ta qarshe cikin ranta,

Wani busashen yawu mai kauri ta hadiye tana sake qure kallanta kan Sumayyar datayi fayau kaman mara jini tayi haske sosai.

Benazir ta kalla taga ita sam batai fayau din ba,

Dawo da kallanta kan sumayyar takuma yi ta sake kalla takuma kallan benazir data gama gyare gurin tana kallan yanda Annen ke kallonsu kaman me tantance kamanninsu.

Anne data kasa furta abinda shedan da zuciyarta suka dirsar mata rawa qafafunta da hannuwanta suka fara dauka tukuna bakinta dayake son budewa

Daqyar ta fizgo kalmar

“Sumayyah! Yaushe rabanki da wanki?

Kinyi wannan watan kuwa??

Meyasa ciwonki yanayinsa daban wannan karan?

Benazir da bata fahimci maganar Annenba ci gaba tayi da kokarin saka kayan data nade cikin jakar buhun kayansu da ko zib babu,

Itama sumayyahn dake jin makoshinta a bushe ruwa masu dan sanyi takeson sha ba dama bata fahimci me Annen take nufi da wankin ba a hankali cikin rashin kuzari tace,

“Anne bayan kullum muna wanki kuma”

Nauyi jikin Annen yakuma dauka yawunta na dan sake kauri da wuyar hadiyewa tace,

“Al’adarki nake nufi Sumayyah,kinyi kuwa a wannan watan??

Dummmmm kunnuwan Benazir dana sumayyah sukai daukewar jin wucin gadi sbd tsananin bazata da girman zancen tareda rashin tabbacin inda ta dosa.

Idanuwa suka zubawa Annen duka kowannensu na hadiye wani yawu tsinkakke,

Benazir ta kalli kofar dakinsu tana tabbatarda hande bata tsakar gidan ta sake dawo da idanuwanta kan Anne da itama akansu take rarraba ido cikin faduwar gana da tsinkewa.

“Anne me kike fada haka ne?

Me wannan tambayar take nufi?

Daman budurwa tana fashin watan Al’adarta ne?

Sumayyah kuma miqewa tayi zaune daga kwancen datake tana kallan Anne da Benazir din itama zuciyarta na mummanan tsinkewa saidai dukansu daga ita har Benazir babu wanda ya kawo tinanin abinda Annen ke nufi har lokacin,

Sun firgita da tambayar ne sbd basusan me hakan ke nufi ba gashi tashin hankalin da basu taba ganinta acikinsa ya bayyana sosai akan fuskarta.

Anne bata da uwa, batada uba, batada dangi, ba amini ba makusanci,

Yayanta sune uwarta sune ubanta sune danginta sune Abokanta sune aminan shawararta suma kuma hakan ne a nasa bangaren itace uwa,uba,dangi,abokiya kuma aminiya babu wani boyo ko sirri tsakaninsu dan haka kai tsaye Annen ta kalli sumayyah kafin ta maida kallanta kan Benazir tace

“Ciwonta da yanayinta kaman name juna biyu shiyasa na tambaya,ni kaina tambayar zuwar mun tayi badan tinanina zai sauka akan hakan ba sbd rashin yiyuwar hakan.

Cikin slow Sbd tsananin firgita Benazir ta hana Annen qarasawa tana leqa kofa tace

“Anne wane irin tinani ne wannan shedan ya saka miki,

Tayaya zaki bari ma kiyi tinanin ciki a jikin daya daga cikinmu,

Ciki a gidan nan Ababa kona aure ne muka dawo masa dashi kinsan zai iya sittin Akanmu bare cikin da ba…..

Kasa qarasawa tayi tana girgiza kai sbd bazata iya qarasa fadan zancen bama a bakinta tsoro takeji dan kuwa iya maganar kawai gabaki daya jikinsu wata irin tsima yakeyi zuciyoyinsu na bugawa musamman Sumayyah datayi shiru sbd tama fita hayyacinta take sbd tinanin mai tattareda tsananin firgici da tsoro.

Anne kasa shiru tayi sbd takasa yakice tinani da tsoron cikin ranta ta kalli sumayyah zatayi magana Benazir ta katseta cikin roko da magiya tace

“Anne dan Allah kada tsautsayi yasa Hande taji zancen nan kinji”?

Sumayyah suka jiyo sika kalla tare Anne tace”

Bazakiyi magana ba to ke sumayyah?

Ido Benazir ta qura mata tana jiran amsar da zata bawa Annen sbd abar zancen ita zancen kawai gigita qwaqwalwarta yakeyi bare,

Kasa magana Sumayyah tayi saida Benazir takuma maimaita maganar Annen kafin ta dawo hayyacinta kai kawai ta daga musu zuciyarta na yamutsa da tashin hankali mafi muni.

Tana fadar haka Benazir ta roko Anne aka bar maganar sbd bama mai dadin fada bace.

Anne hankalinta bai kwantaba amma dai itama tunda tasan babu tsautsayi da qaddarar da zata saka ‘yayan nata abu irin hakan sbd sunsan a yaya suke rayuwar gashi sumayyahn tace tayi aladar dan haka ta cire tinanin komai cikin ranta amma badan zuciyarta ta rabu da tsoro da fargaba ba.

Washe gari suna fita cikin Saa Bilal ne yazo daukansu ya dawo kenan dan haka ta ringa jera ajiyar zuciya daban daban har suka isa saidai bata iya masa wani zancen ba tinda ita kanta tasan bazai yiyu ace tana dauke da abinda Annen ta fada ba dan haka sai kawai sukai iya maganar da zasuyi ya tafi bayan yasa taci abinci sosai sbd ganinta dayayi duk ta rame tayi fayau kaman ya saceta yaje yayi jinyarta cikin kyakyawan guri mai nutsuwa da kwanciyar hankali tareda kulawa.

Har suka tashi sama sama take dan haka ta riga Benazir komawa gida tana isa gidan dole ta kamawa Anne aiki saidai ko rabi batayiba ta yanke jiki ta fadi Allah yasa Yauma hande bata gidan dan haka Anne cikin firgici ta zuba mata ruwa ta farfado sukai daki ta kwanta.

Koda Benazir ta dawo jikin nata yayi dan tsanani saidai tana bacci dan haka batayi dogon motsiba dan kar ta tadata ta fita suka cigaba da qarasa sauran aikin.

******Bayan kwana biyu sunata jinyarta a boye ba tare da sanin Hande ko Ababa ba,

Tana cikin rashin kuzari ko kadan ga yawan Amai yanzu datakeyi babu wata wata Anne cikin tashin hankali da baa saka masa rana ba tace wlh ciki ne a jikin Sumayyahn.

Benazir kusan sumewa tayi da zancen ita sumayyar kuwa daman bata hayyacinta,

A zaune suka kwana dare cikin matsanancin tashin hankali da fargaba da jiran tabbatarwa,

Daqyar sukaga gari ya waye cikin rashin sanya yau suka tattara sumayyar ta dan samu qwari suka fice makaranta sbd a can zasu samu tabbacin Zargin Annen.

Kaman yanda Benazir ke addua Alh bilal dinne da kansa yazo daukansu ganin halinda Sumayyah take suka wuce kai tsaye asibiti sina zuwa aka kwantar da ita.

Tashin farko likita ta iso musu da sakon ciki ne a jikin Sumayyah na sati hudu.

Wuta ce ta dauke masa Benazir kuwa duhu idanuwanta sikai lokaci daya kuma qafafunta na kasa daukanta ta zube qasa tana kokarin samun ganinta ya dawo.

Chapter 19

19

Ganinta neman gagararta dawowa yayi sbd bata taba samun kanta a mafi tashin hankali irin na wannan daqiqun ba datake cikinsu a yanzu,

Cikin haihuwa fa ake magana sumayyah take dauke dashi,

Ta haifa ‘da ko ‘ya masu rai fa,Innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Qalu innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Ya ilahi meye haka kunnuwanta yau sukaji,

Babbar kadaddariyar jarabawarsu ce yau ranarta ta tsaya,

Tsikar jikinta ne gabaki daya suka tashi sbd tinaninta daya dade da tsayawa babu abinda take gani sai gawar kansu su uku ita da Annensu da sumayyar harma da cikin.

Bilal kaante kuwa wutar data dauke jikinsa babu abinda yake zuwa kansa sai tausayin Sumayyah da abinda yake cikin wanda baisan me zai fada akansu ba yanzu,

Kalmar cikin ta girgiza sa ne sbd abune da bai taba zuwa tinaninsa ba a wannan lokacin.

Shi kansa a nasa bangaren wannan wani babban qalubalen ne da tashin hankali sbd tsakaninsa da iyayensa da danginsa wani abune da ko zasu rasa komai bazasu yarda da wannan zancenba sbd karma ya fita,dan gwara ya jewa dd babba da dad kaante da labarin sunyi asarar miliyoyin kudi masu yawan da hankali bazai dauka ba akan yaje musu da wannan labarin.

Daga shi har Benazir babu wanda yakeda nutsuwa ko tinanin kallan junansu kowannesu da nisan da yayi cikin nasa tashin hankalin da baa saka masa rana ba.

Kaman masu jiran sakon mutuwa haka suke babu me motsi,har lokacin Benazir na zube qasa zaune batada qarfin tasowa shima har lokacin yana tsaye,

Benazir tashin hankalinta yasa tini ta manta da yanayi sumayya tinaninta akan cikin yake har lokacin dan kuwa zancen ya kasa zaunuwa a ranta tayaya sumayyarsu zata samu ciki?

Ina ta samesa?

Da wa?

Yaushe?

Sam kanta ya kasa daukan zancen bare tasan yanda zuciyarta zata aje zancen.

Acikin zaman jiran da baifi na awa daya ba Idanuwanta sukai wani fadawa tareda yin jajir

Daqyar take iya hadiye busashen yawu a makoshinta daga bakinta daya bushe qayau,

Bilal kaante kansa bakin nasa a bushen yake saidai yanayinsa yasa baa iya gane zallar damuwa da tashin hankalin dayake ciki.

Sumayyah batasan halinda take ciki da wanda suke ciki sai bayan awa hudu data share tana bacci sbd ruwan bacci dayake cikin ruwan da aka daura mata,

Tana farkawa Abinci mai lafiya da rashin nauyi Bilal yasa aka kawo mata,

Benazir har lokacin bata dawo cikakken hayyacinta ba gabaki daya bata gane komai sosai dan haka tana gefe rakube tayi zugum batasan me take tinaniba ita kanta tadai san tana cikin mafi girman tashin hankalin rayuwarsu.

Shine da kansa ya bawa sumayyar abinci cikin kulawa da so mai tsanani yanajin inama da aure ne tsakaninsu wannan qaddarar qaruwar ta same su da sai ya nuna mata soyayyar da zata manta da quntatacciyar rayuwarsu ta baya,

Yanzu gashi qaddara ta riga fata,waye zai fara tara da wannan maganar mai girma?

Sumayyah data dan samu kanta sai alokacin ta maida kallanta da hankalinta kan Benazir da zama abin tausayi cikin awanninsu a asibitin,

Magana takeson yi mata amma ganin gabaki daya Benazir na wani yanayi yasa ta kasa mata maganar ta dan dawo da kallanta kan Bilal da shima tin dazun ita yake kalla cikin tsananin tausayi da kulawa dan bayajin zai iya gangancin yimata abortion sbd tsoron abinda zai iya samunta kuma cikin ba laifinsa ne ba qaddara ce ta samar dashi wadda suma suke cikin nadama da neman yafiyar ubangiji tun ranar ra tsautsayin ya afka musu har yanzu kuma bazasu dena neman yafiyar Allah ba har qarshen rayuwarsu sbd shedan da kaddarar wannan samun ya afka musu.

Sabon zaman makokin da bana mutuwa ba suka dasa babu mai iya magana acikinsu kowa da tashin hankalin dayake tada zaman lafiyar zuciyarsa.

Benazir data rasa tinanin kamawa miqewa tayi jiri na neman dibanta tace gida zasu tafi kawai.

Kallanta Bilal yayi yana dago wayarsa da kira ya shigo yaga sunan dd babba ne kuma baa qin daga wayarsa idan ba babban dalili ba dan haka ya daga cikin tattaro nutsuwarsa datake kokarin barin jikinsa sbd komawan sumayyah gida da wannan cikin a yanxu babban hadari ne ga rayuwarta sbd komai ma zai iya faruwa idan Ababa ya sani.

dd babba dake babban lafiyayyan office dinsa na gida yanajin Bilal ya daga wayar kai tsaye yace yazo yanzu yanzu yana nemansa.

Rintse idanuwansa yayi cikin damuwarsa dake bayyana yana kallan su Benazir data miqar da sumayyah har sun kusa kofa yana jin kansa na sarawa da ya biyo bayansu ya bude musu mota yana kallan Benazir da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da sanyin jiki tareda kunyar kansa yace mata gobe da safe zasuyi magana idan ya taho daukansu amma ta kula da Sumayyan kafin goben.

Kai kawai ta iya gyada masa sbd bazata iya magana ba kuma bazata iya dagowa ta kallesaba.

A motar ma babu mai iya magana hankalinsa yayi mummunan tashi zuwansu gida da abinda zai iya biyowa kafin safiyar gashi dd babba na masa neman gaggawa wanda bai taba jin hankalinsa ya rabu biyu akan zuwan kiran dd babba ba sai yau din.

Yana ji yana gani dukkaninsu sukai shahadar rabuwa ya ajesu ya wuce yana sake jin fargaba na shigarsa na barinsu ya nufi gida.

Suna shiga gida suma kai tsaye dakinsu suka nufa sbd ba kowa tsakar gidan Annensu na bangaren dabbobinsa tana shara batasan dawowarsu ba,hande kuma tana daki tana baccin rana.

Kwantar da sumayyah tayi har lokacin bata ce mata komaiba sbd batasan me zata fada din ba sbd zuciyarta data kasa dawowa da bugawa daidai.

Zubewa tayi gefen sumayyar tareda rafka wani mummunan tagumi nauyin idanuwanta na qaruwa,

Sumayyah datake kallanta cikin nauyin idanuwan itama tashi tayi zaune tana kallan Benazir din da damuwa ta bude baki cikin taushin murya mara karfi tace

“Bena meya faru?

Meyasa kike cikin yanayin nan?

Wani abin ya faru ne?

Juyowa Benazir tayi da jajayen idanuwanta ta zubawa Sumayyahn sai alokacin taji hawaye na ciko idanuwanta.

Cikin mutuwar jiki da damuwa mai tsanani sumayyah ta dafa hannun Benazir din dake rawa muryarta na shiga tashin hankalin ganin hawayen dake ciko idanuwan Benazir tace

“Meya faru Bena?

Dan Allah fadamun meya faru,

Meya sameki?

Wani irin kuka mai ciwo da radadi ne ya kufcewa Benazir din mai qarfi da rshin sauti ta sunkuyar da kanta tana kasa magana.

Kukanta ya saka jikin Sumayyah daukan rawa sosai cikin tsoro da fargaba mai girma sbd duk abinda ya saka Benazir hawaye babba ne bare kuka mai qarfi irin haka.

Annensu data shigo dakin tayo alwalar sallar laasar zatayi tana ganinsu ta qaraso tana kallan Benazir datake kuka mai ciwo da radadin rai.

A tare cikin rudewa suka sake jefa mata tambayar abinda ya faru.

Annensu ta dago ta kalla tausayinta ya kamata saidai babu abinda zasu tare daga qaddarar da ubangiji ya doro musu saidai tasan wannan qaddarar mai nauyi ce garesu musamman Annensu da bazata iya daukan wata azabar ba da ciwon lamarin a matsayinta na uwa kuma mahaifiyar sumayyah.

“Menene Benazir ki fada mana,meya faru?”

Takardar da aka basu a asibitin ta cikin Sumayyah ta ciro daga cikik rigarta ta miqawa sumayyah sbd Anne bazata iya karantawaba, taja wani numfashi mai zafi da mutuwar jiki Muryarta a sanyaye ta bude baki tace

“Anne ciki ne kaman yanda kikai tinani……

Kasa qarasa bude takardar Sumayyah tayi ta tsaya cak tareda dagowa tana kallan Benazir datake hana kukanta dawowa tana kallan Annensu data dauke wuta.

“Anne, Anne, Anne” tafada hankali tashe tana taro Annen jikinta sbd yankewan da jikinta ne neman yi.

Tashi tayi hankali tashe koina jikinta na rawa ta taro Annen tana sake kiran sunanta cikin sabon tashin Hankali murya qasa qasa sbd ba daman daga muryar kada a jisu.

Sumayyah da itama tayi mutuwar zaune ta juyo ta kalla cikin tashin hankali tace kawo ruwa Anne zata siqe.

Sumayyahn bata san me Benazir take fada ba sbd suman datayi a zaunen itama.

Tashi Benazir tayi da sauri ko gabanta bata gani tana kimfewa ta sake tashi da sauri ta fice ta debo ruwa tana zuwa ta zubawa Annensu kofin ruwan gabaki daya kafin ta sake fita qafafunta na hardewa ta debo wasu ta zubawa sumayyah ta wurgar da kofin tayi kan Annensu dake jan numfashi daqyar tana dafe kirjinta dake toshewa.

Cikin tashin hankali da tsoro mai tsanani Benazir take shafa mata bayanta tana karanto mata adduoi tana kiran sunanta a hankali.

Sumayyah data dawo hayyacinta kuwa wasu hawayen tashin hankalin da baa saka masa rana bane suka tsinke mata tana jin tsoron da bata taba jinsa ba a rayuwarta yana shigarta sbd tabbas lokacinta yayi.

A hankali Anne ta dawo daidai ta dago ta kalli Benazir da idanuwanta sukai jajir ta maida kallanta kan sumayyah take suka fashe da wani irin kuka mai tsananin ciwo da tashin hankali duka su ukun a lokaci daya.

Kuka sikeyi sosai mara sauti kowannensu na rasa abin fada tsawon lokaci mai tsayi kafin Benazir ta dago tana share fuskarta sbd jin motsin fitowar Hande tsakar gidan tana kwada kiran Annensu dan batasan suma sun dawo ba.

Kowannensu taqaita kukansa yayi suka share fuskokinsu babu wanda yace komai suka fito daya bayan daya fuskokinsu a qasa sbd yanda idanuwan kowannensu yayi jajir ya kumbura.

Kallansu Hande batayiba bare taga halinda sike ciki kai tsaye ruwan datasa a debo mata a bokiti Benazir ta debo mata takai mata bandaki ta fito sukai alwala sai alokacin suka samu damar yin sallolin dake kansu itama Annen me alwalar laasar saida ta sake wata.

Koda suka gama sallah jigum jigum sukayi har lokacin babu me magana sbd bude bakinsu ma a yanzu tsoro sukeji dan basusan ta inda zasu faro wannan maganar ba a cikin gidan da fitar maganar daidai take da tsayuwar alqiyamarsu.

Har akai sallar magriba aka fito babu wanda ya fita acikinsu da alwalar sukai sallar suka sake komawa zaune kowa yayi shiru yayi nisa a tinaninda babu komai acikinsa sai tashin hankali da tsoro tareda tinanin makomarsu a gurin Ababa.

Abincin dare da aka basu a ranar haka ya kwana bar safe babu wanda ya sake kallan inda yake sbd masifar da suke ciki.

Suna gama sallar asuba Anne ta kalli sumayyah da a daren guda ta zabge sbd tashin hankali.

Dukkaninsu babu wanda idanuwansa basu fada ba sukai jajir sbd duk kasancewar bacci barawo a ranar ya kasa sace su ynda suka ga rana haka suka dare.

“Waye yayi miki haka Sumayyah?

Wane qaddara ce wannan sumayyah?

Tsautsayin menene wannan?

Meyasa sumayyah?

Waye ne??

Tsit dakin ya dauka bayan numfashin dake fita a sarqe da damuwa mai tsanani babu abinda akeji a dakin.

Sunkuyar da kai Sumayyah tayi wasu hawayen na gudu kan fuskarta quncinta na tsananta tareda kunyar kanta dana mahaifiyarta da ‘yar uwarta sbd wannan qaddarar masifarta ba iya kanta zata tsaya ba dukansu ukun ta tabbatarda sai sun mafi munin halin quncin rayuwa a gurin Ababa. “Alh Bilal”  tafada muryarta na yankewa sbd kuka mai qarfin dayazo mata.

Chapter 20

20

Shiru dukkaninsu sikayi sbd daman sunsan bazai wuce Alh bilal dinba dan haka kowannensu ya sake shiru sbd basusan mafitar wannan qaddarar ba data rigayi fata.

Cikin rudewa da tashin hankali Annen batama san me dame take fada ba ta fara fada ciwonta na neman tashi sbd kanta da yayi nauyi neman juyewa yakeyi

Benazir ta taso ta dawo gurinta da sauri tana kwantar mata da hankali sbd kar ciwon ya tashi komai ya lalace asan halinda suke ciki.

Har gari yayi haske suna daki suna fama da kansu ba sauki ko kadan dole Benazir ta fito ta hau aikin gidan gabaki daya ba maganar zuwa makaranta sbd tsoron fita takeyi ma tabarsu kada kafin ta dawo Ababa ya sani ta dawo ta tadda babu su ga kuma yanayin Annen daketa surutai cikin tashin hankali da fita hayyaci

Sumayyah ma idanuwanta sunkai ko budewa basayi sosai sbd kumbura ga yanayinta na rashin lafiya.

Abincinsu na dare da basu ci ba haka suka zauna su ukun suka turasa cikinsu da sanyinsa harma ta sakewar daya fara yi sbd kada su fitar a san basu ci a fahimci suna cikin wani halin a gano.

Babu mai dadin rai ko nutsuwa a cikinsu haka kowa ya ringa diban abincin yana turawa bakinsa bame magana suna gamawa Benazir ta dauki kwanon ta fice taje tafara wanke wanke.

Annensu zaune take a dakin nasu ta kasa fitowa idanuwanta sunyi ciki ciki tsaban kuka da damuwa ta rafka tagumin da basusan yanzu kuma yanda rayuwa zatayi dasu ba.

Sumayyah kuwa ciwo ne yake cinta sosai amma tashin hankali da damuwa ya hanata nunawa itama tagumin ne ta rafka dukkaninsu kaman wainda ke jiran sakamakon mutuwa.

Benazir ma ayyukan gidan takeyi ba’a cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali ba kowannensu tinanin makomarsu yakeyi.

Sai bayan sallar Azahar ta kammala aikin tayi wanka da alwala tazo tayi sallah aka basu abincinsu data gama girkawa ta kawo ta ajiye musu dole sukai sallah suka zauna suka turawa cikinsu babu me jin dandanon komai a bakinsa cikinsu kowa ‘dacin bakinsa yakeji musamman Sumayyah da nata ya hada dana ciwo da laulayi.

Tsit Hande taji gidan yayi suna daki babu me iya motsin kirki sbd damuwa da tinani dan haka ta fito tana qwala kiransu tana tambayar lafiya suke zaman daki kaman masu abin kunya.

Tsinkewa cikinsu yayi Anne ta kalli Benazir da itama ita ta kalla suka kalla sumayyah a tare kafin Anne ta bude baki cikin mutuwar jiki tace

“Ki zauna a dakin karki fito”

Gyada kai Sumayyah tayi tana rintse idanuwanta sbd kunyarsu dake cin zuciya da ganganr jikinta gashi ta kasa ko bude baki ta fada musu kaddara ce da shedan daya shigo ciki.

Anne da Benazir ne suka fito sbd kada hande ta tsananta maganar.

Kallansu tayi taga duk sun jeme a dare daya kaman wainda sukai kwanan zaune,

Fuskar Benazir ta kalla taga yanda ta sauya kwata kwata da alamar bata rintsa ba kuma harda alaman kuka bayan rashin baccin.

Kan Anne ta maida kallanta taga itama fuskarta tayi jajir ta kumbura,

Shiru tayi tana nazarinsu sbd da alamar akwai abinda ya samesu dan duk wuya duk tsanani su biyun nan basu cika kuka ba sbd Anne ta dade da samun rashin lafiyar rashin kuka sbd shekarun data debo a rayuwar gidan zuciyarta ta mace bata iya kukan hakama Benazir sbd taurin rai da juriya ba qaramin tashin hankali da masifa ke sakata kuka ba amma yau gashi da alama kukan suka kwana yi..

“Kodai sumayyah ta mutu ne tsakar dare?” Tayi tambayar kai tsaye tana kallan hanyar kofar dakinsu da mamaki.

Anne wani numfashi mai sanyi ta sauke zuciyarta na sosuwa da abinda Handen ta fada tayi qasa da kanta tana kasa cewa komai.

Benazir ma numfashin mara sauti mai dumi ta sauke tana girgizawa handen kai tace

“Tana nan lafiya ce batada tin jiyan”

“Shine kuka kwana kuna kuka ko me? Ta sake jefa musu tambayar tana kallan Benazir da idanuwanta ke sake yin qasa.

Shirunsu yasata rufesu da fadan batasan dabiar koke koke a cikin gidan da ba mutuwa akai musu ba.

Fada ta ringa yi sosai sai data gaji ta dena tace su wuce ga wankin shagon Ababa can an kawo.

Wucewa sukai inda manyan kullin kayan wankin masu yawa suke suka warware suka ringa kwashe kayan zuwa inda suke wankin.

Benazir ce ta fara debo ruwa masu yawa ta tara musu

Suna fara wankin Anne ta sunkuyar da kanta qasa wani irin kuka mai sauti na subuce mata mai tafe da tsananin ciwo da quncin da zuciyarta take ciki.

Benazir radadin sautin kukan mahaifiyar tata ya sata kasa wanke kayan dake hannunta tayi qasa da kai itama wasu hawaye na tsinke mata,

Me zasuyi?

Meye mafitar halinda suke ciki?

Ya Allah ka dubi maraicinsu” shine abinda zuciyarta kawai ta iya fada sbd sunsani sun tabbatar mawuyacin hali ne suke ciki mai nauyi.

Saida sukai kuka sosai kafin suka hakura suka fara wankin babu mai magana har suka wuni sunayi sai gab da magriba suka gama sbd abincin dare da Benazir ta dora tanayi tana tashi.

Daki suka shige bayan sunyi Alwala abincin dare kawai sukaci sukai ishai da akai suka lafe dakin babu wanda ya sake fitowa saida Ababa ya dawo Benazir ce ta fita taje takai masa abinci da ruwa ta dawo dakin suka cigaba da zaman damuwa.

Washe gari ma hakan ce ta kasance babu wanda ya fita makaranta cikinsu haka suka wuni cikin mummunan yanayi na damuwa.

*****kusan kwanaki hudu sika share a hakan cikin zallan damuwa da qunci tareda tsoro da firgici mai tsanani,

Sumayyah na daki jikin nata sai tsanani yake qarawa amma basa barinta fitowa sai idan zata je bandaki kokuma idan Ababa ya dawo sbd kada ya saka musu idon zargin wani sai ta daure ta fito dan kawai ya gansu yasan suna nan kalau ba matsala,

Hande data ankara da yanayinsu gabaki daya ya sauya a kwanakin sai ta saka musu ido sosai ga Benazir data dena zuwa makaranta sbd tsoron kada ta fita a ganosu tinda daga Anne har sumayyah idan bata nan zasu iya firgicewa suyi abinda zai bayyanarda halinda suke ciki.

Ta bangaren Alh bilal kaante kuwa a cikin kwana biyun da baya ganinsu duk zuwan dayake yi kullum dan daukansu kaman zaiyi hauka a cikin kwanakin sbd gabaki daya shima ya shiga tashin hankali mai girma rashin ganinsu,

Tsoron Ababa da abinda zai iya yi musu yasashi komawa kaman mai tabin hankali shima dayake mutum ne mai nutsuwa da kamun kai take aka gano yana cikin mummunan yanayi na damuwa da tashin hankali,

Dad kaante da dd babba tini suka fahimci yana cikin mawuyacin hali sukaita tambayarsa ko lafiya amma sam zurfin cikinsa baya barinsa fada musu komai dan haka ran dad kaante ya baci ya kira Mahaifiyarsu Bilal din ya bata lokacin dawowarta idan ba haka ba damuwa zata kashe mata ‘da a banza tana can gurin wancan da baya buqatan kowa tinda shine ya zabi zama baa cikin family dinsaba.

Dd babba kuwa ganin da gaske lamarin yayi yawa sai kawai ya tura bilal din wani aiki Kenya dole Bilal ya tafi bayan kusan har kwanciyar jinyar kwana biyu yayi sbd rashin sanin halinda su Sumayyah suke ciki,

Yayi yawo anguwar yafi so hamsin a kwanakin amma babu alamarsu gashi yana gudun ya tinkari Ababan kai tsaye kila bai saniba tukuna kada ya janyo musu fitina wanda ya san da DD ne da tini zai tinkari Ababan duk abinda zai faru ya faru kowama ya dade bai saniba.

Ms aysha ce Aminiyarsa da zata iya masa komai ko baya nan dan haka ita ya sanarwa komai tareda rokonta taje ta dubo masa su tareda kular masa dasu.

Ranar daya wuce washe gari cikin saa sai ga Benazir tazo makarantar itama sbd Ababa yafara fahimtar ta dena zuwa hakama suna neman mafitan yanda zasuyi da cikin daga Bilal din tinda basuda kowa basuda gurin zuwa hakama bayyanar cikin dede yake da basusan ma me zasu ce ba.

Zuwan Benazir makarantar ya hana ms aysha zuwa gidansu ta zauna da Benazir din cikin kulawa ta tambayeta lafiyarsu da yanayin Sumayyar.

Shiru Benazir tayi takasa magana sbd kukan dayazo mata a hankali

Ta sanar da ms aysha mafita suke nema basuda yanda zasuyi da rayuwarsu.

Kukan Benazir ya taba zuciyarta sosai kusan saida idanuwanta suka ciko da hawayen itama dan haka

Cikin tausayi da baqin cikin qaddarar itama ta ringa rarrashinta tareda yanke shawarar zaa  cire cikin kawai kokuma dole Alh Bilal ya fito fili a yi maganar aure tin kafin maganar cikin ta bayyana.

A gaban Benazir Ms aysha ta kira Bilal sukai magana sosai ta nuna masa damuwar dasu Benazir suke ciki.

Kai tsaye kasa amincewa yayi da cire cikin sbd hadarinsa da cutatarwa ga Sumayyah zatayi yawa.

Bai taba jin karfin soyayyar data danne tsananin tsoro da shakkar dd babba da dad kaante ba sai a yanzu dayake jin zai iya daukan hukuncinsu dana familyn kaantes gabaki daya akan sumayyah.

Kaman yanda Benazir da Anne suke neman mafitar lamarin Ms aysha da Alh Bilal din sun musu alqawarin yana dawowa zai nema auren Sumayyah batareda Ababa yasan da maganar cikin ba hakama duk dukiyar dayakeso yayi alqawarin basa dan ya basa auren sumayyah din.

Wannan alqawarin yasa Benazir daurewa ta tsaya makaranta bayan Ms aysha tayi mata alqawarin tsaya musu har qarshen rayuwarta insha Allah.

Ana tashi makaranta ms aysha ce ta dauketa ranar da kanta ta kaita gida kuma cikin saa Ababa bayanan hakama hande tana baccin ranar data saba dan haka har cikin dakinsu dayasa ms ayshan zubda hawaye suka shiga ta duba sumayyah tareda yiwa Anne Alqawarin zata kula dasu Benazir kaman yayan data haifa a cikinta da yardar Allah.

Kudi ta basu amma tashin hankalin dasuka shiga ma na ganin kudin yasata maidawa jaka ba shiri sbd tsoron kudin.

Tanaji tana gani ta tafi batareda bar musu komaiba sbd sunqi karban kudin.

Tana ficewa Hande ta tashi data fito ta ringa mitar qamshin tiraren manya take jin ya cika gidan koina.

Shi kansa Ababa daya dawo saida ya tsinci qamshin musamman dakinsu dan haka aka bincike kayansu tsaf baa ga komai ba dole aka hakura sedai saka idanun da akai akansu sosai sbd sam hande ta kasa yarda dasu a kwanakin.

Benazir dole ta koma makaranta kullum tana zuwa

Sumayyah dai dole aka hakura saita warke tukuna.

Kullum idan taje sai tayi magana da Alh bilal din a waya yaji ya jikin Sumayyah ta fada masa da sauki ta wuce karatunta.

Chapter 21

21

Taka tsantsan suka hau yi da duk wani abin da zai saka a fahimci halinda sike ciki komai qanqantar kuskure kiyayesa sukeyi,

Sumayyar ita kanta dole ta ringa tilasta kanta tana nemo kuzari da qarfin hali tana fitowa wasu ayyukan sbd saka idon Hande akansu yayi yawa.

Benazir ma datake zuwa makaranta tini sukaiwa kansu fada komai na Alh bilal harma dana ms aysha sun dena karba duk tsananin yunwa da rashin lafiya sun dena karban abincinsa da maganin dasuke fitowa daga garesa duk da bak dawo din ba kawo musu akeyi makaranta amma sam Benazir ta dena karba.

Saida suka share sati kusan uku suna fama da jikin Sumayyahn kafin ta fara fita makaranta.

Annensu duk suka fita harsu dawo hankalinta baya jikinta sai taga dawowarsu sbd yanzu tsoron mutanen waje ma takeyi,

Benazir yanzu takeji duk da tasan ita tanada kame kai da hankali fiyeda yayarta Sumayyah din duk da ba dubararka bace tsarewar Allah ce.

Ita kanta Sumayyah tinda ta dawo makarantar take cikin damuwa da tsarguwa tareda kunyar dagowa ta kalli mutane sbd kunyar abinda yake jikin nata ganin takeyi kaman zaa ganeta.

Dan haka rayuwar makarantar ta zamar mata kaman wani sabon qunci da damuwa dan kuwa gabaki daya a muzance take cikin mutane,

Mummunan hali ta samu kanta aciki wanda ya saka rayuwar makarantar da karatun ficewa kanta gaba daya,

Tamkar mujiya haka ta koma acikin mutane,

Tin tana daurewa har takasa damuwa da qunci yayi mata yawa dole ta dena shiga mutane kwata kwata sbd itama ciwonta dake neman dawowa.

Hankalin Benazir tashi yayi ya rabu biyu akan karatunta da kuma Sumayyah din musamman yanzu dayake tana daukeda lalurar juna biyu.

Daga ita har sumayyar karatun acikin kwanaki kalilan neman lalace musu yakeyi ga jikin Sumayyah din ciwo yau gobe lafiya tin suna iya controlling abin suna boyewa har hande tagane sumayyah dai dale akwai abinda yake damunta bayan malaria da sukace.

Ana cikin wannan matsuwar da tashin hankalin sukai exam wadda daga Benazir din har sumayyahn babu wanda ya iya karatu bare rubuta abin arziki.

Ranar da suka gama exams wani babban tashin hankali ya samesu na rasuwar mijin Ms ayshansu wadda a ranar ta bar garin zuwa jos garin mijinta inda acan zaayi janaizarsa.

Wannan babban sabon tashin hankalin yasanya jikin Sumayyah rikicewa gabaki daya sbd ms aysha itace gata da mafitarsu dasuke gani itama ta tafi ta barsu.

A ranar sabon tashin hankalin kwanan zaune sukai duka su ukun babu wanda ya rintsa sbd a yanzu kam babu mafita sai wadda ubangiji zai sake aiko musu kokuwa dai qaddarar ce dai ahakan tazo musu.

Wannan karan kukan da Benazir tayi yafi na kowannensu tashin hankali da taba zuciya sbd itace take iya hango kowannensu ciwonsa dap yake da tashi wanda tasan suna juyewa shikenan ita kadai zaa bari da dawainiya da wannan quncin da radadin wanda daqyar itama wannan karan idan bata samu mental problem dinba,

Ya zasuyi da cikin sumyayyah?

Zatayi da babyn idan aka haifa?

Me zata fadawa ababa?

Me duniya zata fada akan babyn?

Tayaya takeda tabbacin Alh bilal zai waiwayesu?

Innalillahi wainna ilayhi rajiun.

Kuka tayi sosai wanda ya saka jikin Sumayyah da Anne sanyi dan kuwa sunsan ko a gurin azabar idan zasusha nata zai fi yawa sbd itace mai lafiyar da zatafisu jin radadi da ciwo tareda qunci mai yawa.

Sai dataji hawayenta har sun qafe idanuwanta ko buduwa basayi sosai ta dena kukan ta kallesu cikin tausayawa sbd a yanzu ta rungumi qaddarar cikin lafiyarsu da abinda zai samesu idan suka rasa hankalinsu take ji yana cin zuciyarta.

Tausayin tausayi akeyi tsakaninsu

Su suna tausayinta ita kuma tana tausayinsu da babyn da zaa haifa wanda zai taso cikin uquba da masifar da uwarsu ta taso aciki suma suka taso aciki.

Abincin dare ta fito ta dora tana gamawa tayi sallah ta fito ta hau wankin hande.

Sai goma da mintina hamshin ta shigo dakin ta tadda Annensu zaune tayi shiru tareda nisa cikin tinani idanuwanta na kan sumayyah wadda baccin wahala da dole ya fizgeta.

Qarasowa tayi ta zauna gefen Anne tareda zamewa ta kwanta tana yiwa Annen saida safe cikin dasashiyar murya.

Har kusan asuba Annensu bata rintsa ba tana zaune cikin nisa a tinaninda batama san me take tinanawarba,

Ita kanta Benazir har kusan asubar batai bacci ba sai daga baya ya dan dauketa bata jimawa akai kiran asuba ta farka ta fito.

Tare sukai sallar asuba dukkaninsu

Suna gamawa Anne da Benazir suka fito

Itama sumayyar daga baya biyosu tayi suka fara aikin gaba dayansu.

Sai 11 suka dan samu saukin aiki suka zauna suka ci abinci

Ko tashi gurin basu yiba amai ya subucewa Sumayyah mai qarfi sbd cikinta daya kasa karban abincin da suka cin.

Amai takeyi mai qarfi da sauti wanda yasa dukkaninsu miqewa suna rarraba ido,

Hande kuwa da sauri tayo dakin tana tambayarsu aman lafiya ne kuwa?

Shiru sukai tayita maganarta ta gaji ta tafi kafin Anne ta wuce da sumayyan dan tayata wanke jiki

Benazir kuwa gyaran gurin tahau yi ta kwashe ta wanke gurin fes da omo me qamshin ta goge.

Acan koda Anne ta wanke jikin Sumayyahn zazzabi da ciwon ciki mai qarfi ya rufeta saida Benazir tazo suka kamata suka kai daki

Take ta juye cikin ciwo mai tsanan koina nata jijjiga yakeyi.

Anne ta zauna da ita Benazir ta fita ta qarasa aikin tareda girkin rana tana gamawa suka zauna kan sumayyar wadda take cire rai da rayuwa.

Haka suka wuni da ita a daki cikin damuwa da mutuwar jiki

Haka kuma suka kwana da ita.

Washe gari ma haka suka kima wuni da ita jikin ba dadi sam sai addua ba wanda ya kulasu

Hande ma ido ta kawo ta saka musu sbd tasan ko zasu mutu Ababa bazai saka kudinsa yakaita asibiti ba dan haka ba ruwanta tinda ba lafiyar zata basu ba bazata iya yawon sanni ba.

********acikin sati biyu sumayyah gabaki daya ta koma kaman mai ciwon qanjamau sbd rama da rashin kuzari,

Ciwonta yaqi sauki sam kullum haka suke fama da ita,

Benazir da Anne ma kaman masu qanjamau din suma dan itace take ciwon amma ramar da zabgewar dukansu ne sukai babu me dubuwa acikinsu banbancinsu da ita kawai ita cikin ne yake ajikinta amma duk damuwa da kuncin daidai yake a zikatansu.

Har lokacin babu labarin ms aysha hakama ba na Alh bilal,

A kullum yanzu sallamar ababa da tarinsa tashin hankalin na fits hayyaci yake sakasu sbd sunsan yau da gobe bata barin komai.

Babban sabon tashin hankalin dasuka shiga shine fara bullowar cikin,

Ciki dai ya bullo bazai boyu ba,

Fitowa tsakar gida yanzu kam ya gagari sumayyah indai da rana tsaka ne sbd kada hande tagani ta sanar da ababa.

Idan sun lissafa daidai watan cikin uku kenan ake magana.

Ajiyar zuciya tareda numfashi mai zafi Anne ta sake tana kallan sumayyah da benazir ke cirewa farce sbd tsayi da sukayi da wata tsohuwar rezarsu da suka siyo kwanaki a hanyar makaranta.

Sanyi jikin Annen ya sake dauka suma sanyi jikinsu yayi ganin irin kallan da Anne ke musu cikin sarewa da sadaqarwa.

Ajiye rezar hannunta benazir tayi tana dafa hannun sumayyah daya dauki rawa ganin Annensu datake sake tsinkar dasu.

A hankali anne ta bude baki cikin sanyi tace

“Ya zamuyi da cikin nan na sumayyah daya fara bayyana?”

Kunsan cewan daga wannan watan cikin nan bazai taba boyuwaba,

Tayaya zaa hana hande da Ababa ganinsa,innalillahi wainna ilayhi rajiun”  tafada cikin fidda rai daba dukkanin sauki.

Sunyi kukan har hawayensu ya dena fita dan haka idanuwansu sukai jajir Benazir ta dago ta kalli Anne zatayi magana idanuwanta ya sauka kan hande dake gefen dakinsu tsaye tayi mutuwar tsaye tsaban tashin hankali da firgicin abinda kunnuwanta suka jiyo mata

“Ciki a jikin sumayyah kuma”?

Miqewa tsaye dukkaninsu sukayi cikin firgici da tashin hankali mai girma suna kallan handen.

Sai data share mintina kusan shifa a qame kafin ta iya motsawa ta rufe idanuwanta ta bude ta sake taba kirjinta taji zuciyarta na bugawa daidai bata sume ba,

Tsikar jikinta je suka miqe gabaki daya sbd tsoro dan kuwa ita kanta tsoron maganar shigarta tayi tinanin idan ababa kawai yaji zancen.

Babu wanda ya motsa acikinsu tsaban tashin hankali da tsoron yau ranar da suke tsoro tazo.

Qafafuwan hande na rawa ta qaraso cikin dakin tana kallan sumayyah da cikinta yake bayyane dan qarami a jikinta

Bakinta ya dauki rawa da yankewar kalma tace

“Cikin haihuwa a jikin sumayyah,

Ciki dai ciki dai na ‘dan mutum,Qalu innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Benazir,Benazir yanzu daman cikin mutum ne ajikin sumayyah kuke boyo?

Meya kaiku?

Wace qaddarar ce wannan?

Uban waye yayi mata cikin?

A in?

Aljanun hauka ne suka shigeku duk ku dukan ko me?

Cabdijam,babbar magana,attt.

Babu wanda ya iya magana acikinsu sbd dai rana ta riga ta baci ba gyara.

Janyo sumayyah hande tayi da qarfi tana qara kallanta cikin kunya da baqin ciki da takaici tareda mamakinsu.

Numfashi ga koma saukewa sbd bata da bakin magana lamarin ya shallake tinaninta.

Fitowa tayi dakin a rikice ta zube tsakar gida tana sake sauke numfashi a jere sbd ita kanta kwatanta tashin hankalin da zaayi a gidan kawai tayar mata da tsikan jiki yakeyi.

Duk bayan sakanni sai ta sauke numfashi mai zafi tana kallan kofar dakin nasu dasuka kasa fitowa kaman yanda kowannensu wuta ta dauke masa babu me iya magana.

Kaman masu jiran sakamako haka suka kasa ko zaunawa dukkaninsu suna a tsaye har akai magrib sukai sallah babu wanda zuciyarsa ke harbawa daidai har handen itama ranar tana idar da Sallah ta fito tsakar gidan ta dasa kejera ta zauna jiran dawowar ababa.

Chapter 22

22

Dagowa Anne tayi ta kalli Benazir da sumayyah tsawon mintina tana rasa tinanin kamawa kafin ta tsaida tinaninta akan Sumayyah dake dauke da juna biyun zatafisu zama cikin hadari idan suka fara cin dukan azaba.

Benazir ma tinaninta akan Sumayyah dake dauke da cikin yake sbd tsoron hadarin da zata iya shiga idan Ababa ya kasa controlling kansa.

Suna nan zaune akai sallar ishai suka miqe sukayi ba jira sbd basu sani ba ko idan ababa ya dawo zasu samu lafiya ko kuzarin yi din.

Hande ma miqewa tayi ta shiga dakinta tayo sallar

Tana gamawa ta sake fitowa ta zauna tana hadiye wani yawun tsinkewa sbd itama tasan tau balain sai Allah idan ba har akanta zaa dora laifinba tinda itace ya barwa saka musu ido akan kowane motsinsu ta sanar dashi halin dasuke ciki

Amma ace har sumayyah tayi gogewar sani wani namijin har yayi mata ciki bata fahimta ba kuma da alama ba fyade akai mata ba da bazasu boye ba kuma da tini Ababan ya qaddamarwa wanda yayi fyaden ko dan uban waye gashi ciki yanzu ya dauko hanyar girma suna gida daya basuda labari,

Ababa kafin tashin masifarsa mamaki ma kawai ya isa ya kashe masa jiki shi kansa.

Qarfe tara saura mintina shida Ababa ya turo kofar gidan ya shigo yana amsa waya hannunsa riqe da ledar lemu daya siyo zai sha.

Ganin hande zaune tsakar gidan tana kallansa tana masa barka da dawowa yasashi taqaita wayar yayi sallama ya kashe yana saka wayar aljihunsa yana amsa barkan datake masa yana gaidata itama.

Satar kallan dakinsu Benazir tayi tana jin shakkar fada masa itama sedai kuma dole ya sani dan idan bata fada ba ciki dai baya boyuwa

Ranar daya gansa da kansa idan ya qara girma kilan wuta zai cinnawa gidan ya kona su duka.

Shima dakin nasu ya kalla tareda bude baki ya daga murya ya kira sunan Sumayyah.

Lokaci daya a tare gabaki dayansu har Hande kansu yayi mummunan sarawa tareda bugawar zuciyar data kusa sakawa hande hearts attack sbd bata saba da wannan tashin hankalin tsoro da fargabar ba.

Su kuwa acan daki take jini ya tsinkewa Sumayyah mummunan bugawar da zuciyarta tayi tareda sarawar kai mai qarfi.

Benazir da Anne ma kusan kowannensu daqyar ya samu yawun hadiyewa sbd makoshinsu daya bushe take qam hakama yawun sun kafe basu ma ankara da jinin daya fara zubowa sumayyah ba wadda itama bata tsars lura da jinin ba sbd zuciyarta data tsinke.

Cikin mamakin rashin amsawarta da fitowarta ya juyo ya kalli Hande wadda ta kasa kallansa tana dan dauke kanta zuciyarta na sake shiga wasi wasin fada masa.

Kallan kofar dakin yayi yana matse fuska ya sake qwala kiran sunan sumayyar.

Daqyar da wani irin mummunan yanayi ta iya bude baki ta amsa kiran nasa tareda miqewa tsaye qafafunta na rawa ta nufi kofar

Sai alokacin su Benazir sukaga jini a kayanta da sauri Anne ta miqe tayi gaba Benazir ta tsaya bayanta suka sakata tsakiya sbd dare ne duk da akwai wutar nepa amma idan suka dan kakkare ba lallai yaga cikin ba harma da jinin sbd ba hijab jikinta tinda basu saba zama da hijab cikin gidanba sbd basuda sitira da yawa shiyasa suke lallaba wainda sike da.

Yanda suka jero masa kaman kashin awaki yasashi tsayawa da kyau yana kallansu cikin sake tsuke fuska da mamakin sabon salon nasu na samun guri.

Sun zuwa suka tsaya gabansa dukkansu kansu a qasa

Anne ce kawai ta dan kallesa tayi masa sannu da zuwa cikin girmamawa kafin suma cikin girmamawa mai tsanani sukai masa barka da dawowa.

Ledar hannunsa ya miqawa sumayyah yana cewa

“Ki gyaro lemu ne ki kawomin banason manyan yanka kuma kin sani……Maganarsa yankewa tayi ganin yanda hannuwanta ke tsananin rawa gurin karban ledar.

Janye ledar yayi yana kallan hannuwanta dasuka sake rikicewa da tsananta rawa,

Fuskarta ya maida kallansa fuskarsa na sauyawa da mamaki yaga fuskarta na hada wani irin gumi da kasa motsa idanuwanta dan kada su dago.

Kan Anne ya maida idanuwanta yana kallanta itama zufan take cikinsa sharkaf hakama hannuwanta rawa sukeyi harma da qafafunta.

Juyar da kallan yayi kan Benazir datake a kame batai gumin ba amma yanda kirjinta ke bugawa yana iya gani da kuma yanda takasa dogowar itama.

Wani numfashi mai zafi ya sauke bayan ya gama karance yanayinsu duka

Ya dawo da kallansa kan hande zaiyi magana yaga itama a jiqe take da zufan yau itama takasa dagowa ta kallesa da kyau.

Sake kallan kowa yayi acikinsu daya bayan daya

Gurin yayi tsit ko sautin numfashinsu baka ji

gyara tsayuwa yayi a hankali,

“Meyake faruwa zaa fadamun yanzu nan”…sukaji saukar muryarsa kai tsaye.

Idanuwansa akan Hande suke sbd daga bakinta yake buqatan ji menene dayasa take hada zufa itama.

Kallansa hande tayi kafin ta kalli sumayyah data riga ta saddaqar su dikan ma sun saddaqar din.

Maimaita tambayarsa yayi hakurinsa na qarewa sbd tini kansa ya fara daukan zafi.

Wani nannauyan numfashi hande ta sauke tareda kallan sumayyah a karo na farko dataji tausayinsu ya dan saukan mata a rai sbd tasan suma duk yanda akai mummunan kaddarar samunsu tayi bada son ransu sbd yanda suke tsoro da kiyaye dokokin Ababa bazasu taba irin wannan aikin da ganganba.

Muryarta ba qarfi da kuzari ta bude baki tace

“Ciki ne a jikin sumayyah gashinan harya fito”.

Shiru gurin ya sake dauka wanda wannan karan har dashi Ababan ya dauke wutar ba zata sbd saukan zancen kaman tsawa me qarfi haka ya jisa.

Hande dataji shiru dagowa tayi ta kallesa taga yayi shiru kaman baiji abinda ta fada masa ba dan haka ta miqe tsaye tana kallansa cikin dan daga sauti takira sunansa tana cewa

“Kaji abinda na fada kuwa?

Nace Ciki ne a jikin sumayyah gatanan na haihuwa,

Da alama kuma zekai wata uku koma fiye,

Kuma wallahi tallahi bansaniba sai yau dinnan nake kamasu suna maganar,

Duk ciwon datake ta fama dashi duk tsawon lokacin nan ashe laulayin ciki takeyi bamu saniba daga uwarta sai yar uwarta suka sani sunata boyan abinsu da saidai idan an haihu munji kukan jariri a gidan mu ankara…..

Ledar lemun hannunsa data subuce masa ce yasata yin shiru tana kallan lemun dasuka watse tsakar gidan kowannen na ganganrawa nasa gefen.

Rintse idanuwansu dasukai jajir dukkaninsu sukai suna sauke numfashi mai dumi.

Ababa ma numfashin ya ringa jerowa yana kokarin sanyaya wutar data kunno cikin zuciyarsa tana cin jininsa sbd yasamu fahimtar komai daki daki akan abinda handen ke fada sbd yasan dai ciki a gidansa ba magana me yiyuwa bace sbd soyayyama ya fada musu sun sani bame yiyuwa bace haka hukuncinta me girma ne,yanzu kuma yaji ana maganar cikin haihuwar dan mutum a gidansa,

Wannan ba labarin da zai taba yarda dashi bane sbd bame yiyuwa bane acikin gidansa dai Kuma a tsakanin yayan nasa.

Gyara tsayuwa yayi yana sake calming kansa sbd Kai tsaye zancen Mai shigesa ba kafin ya kalli hande yaga lafiyarta kalau da alama ba soki burutsun zancen take ba,amma ai akwai tsufa a tareda ita Kuma tsufa nasaka zance mara kan gado,

Da Annensu ce ta fada masa da sai yace haukartace ta tashi.

Benazir dayasan gidan kaf ita kadai ce me cikakkiyar lafiyar qwaqwalwa ya kalla kai tsaye yace

“Ke Benazir fadamun meye hande take fada,kuma komai nakeson ji dalla Dalla ba irin wannan rikicin zancen data fada ba yanzu Kuma idan kika yiwa kowane zance kwaskwarima gurin fada wlh saina karya wuyan uwarki gatanan a tsaye gefenki.”

Mutuwa jikin benazir yayi ta sake boyayyan numfashi mai zafi sosai ta dan dago kanta kadan batareda ta kallesa ba ta bude baki muryarta na rawa ba wahalarda Kai Kai tinda komai ya Riga ya fito Kai tsaye tace

“Eh ciki ne wata uku”.

Shiru gurin ya sake dauka suna jiran wata tambayar saidai tsit ababan baice komaiba sbd har lokacin dai Bai yarda da abinda kunnuwansa suke jiba Dan kuwa ko Anne ta dauka cikinsa a yanzu dukan tashi Kisha ruwan gishiri zai mata bare,

Sai daya Dan gyara tsayuwa ya sauke numfashi Yace,

“Annen ce da ciki kuke magana kokuwa”??

Shiru sukayi zuciyar kowannensu na kokarin Faso kirjinsu ta fito har handen wadda take sake qarewa cikin na sumayyah kallo ranta na tafasa.

Jin shiru yasa shi dagowa kallo daya yayiwa Benazir tayi qasa da Kai qafafunta na sake daukan rawa tace,

“Aa ba Anne ba”

Cikin zafi da tafasan Rai a hasalce Yace

“Waye yake da cikin Dan a gidan Nan ita kadai Ce aure”

Saida Benazir ta fixgi numfashinta Dake Neman daukewa sbd tsananin tashin hankali da tsoron dasuke ciki na tinanin Ko Basu rasa ransu duka ba Kila sai daya ko biyu sun tafi lahira sun bar daya muryarta na fita da karyewa tace

“Sumayyah Ce ta…. Bata qarasa ba sai jin tayi ya shaqurota da hannuwansa biyu yana kokarin rabata da numfashinta da karfin gaske cikin wani irin zafi da fushin da basu taba ganinsa dashi ba da murya me qarfi da zafi yace

“Zaki fadamun komai danace kokuwa uwar taki kike jiran na balla,

Cikin mutane ne kokuwa na aljanu?

Dan kuwa sai dai na Aljanu suka shafeta sukai mata shi.

Cikin azaba da neman cetan ranta dayake neman rabata dashi tafara wintsila qafafu tana Neman barin duniya idanuwanta take suka firfito suna neman rufewa.

Wurgi yayi da ita qasa tareda saka qafarsa daya ya take cikinta cikin masifar data saka Sumayyah sakin qaramin fitsari jinin dayake zubar mata yana dan qara gudu sbd masifaffen masifar datafi qarfin balain da sika saba gani.

Cikin wahalalliyar muryar da bata fita sosai Benazir tace

“Na mutum ne a makarant ta hadu dashi,

Yace ze aureta,bamusan da cikin ba sai daga baya…. Marin daya saka bakinta fashewa da jini ya sakar mata na bayan hannu, take ta kife a gurin kunnuwanta na dauke ji kwata kwata haka idanuwanta na ganin wasu irin taurarin wuta jinin bakinta kuwa kaman wadda ta fasa kai.

Sumayyar ya damqo yana kallan cikinta zuciyarsa na wata irin tafasar da shi kansa bai taba jin wuta irin wannan na ci a jini da zuciyarsa ba,

Kallan cikin ya tsaya yi yana rasa me zai mata sbd zafin da kansa keyi bayajin idan ya daga hannunsa ya dora akanta zai barta da rai.

Wlh Bai yarda mutum yayi mata ciki ba saidai Aljanu Dan kuwa Wanda ya taba ta kawai ma bare ciki ai bindigarsa zaisa ya fasa Kansa wlh saidai yayi prison,

Jikin bango ya jefata da qarfi tareda binta ya rufe da masifaffen duka yana nanata kalman cikin tareda qin yarda da cikin mutum ne a jikinsa.

Dukan dayake mata ne shi kansa bayaji baya gani yasa Anne da hande yunqurawa dan cetan ta sedai suna isa ya kama Annan itama ya rufe da dukan yana nanata kalmar ciki har wata uku a cikin gidansa.

Hande data ga ‘dan nata ya zauce da gudu cikin tashin hankali tayi cikinsa ta riqesa tana fashewa da kuka tana cewa Anne da ‘yayanta sun zautar mata da ‘da da baqin cikinsu.

Tinda yake a rayuwarsa bai taba ji ko haduwa da abinda yake neman sakar masa bugawar zuciya ya mutu ba sai a wannan ranar.

Rawa jikinsa keyi yana fizga kaman dan taurin da aka kadawa gangar kirari.

Kuka hande keyi sosai sbd ganin halinda yake ciki ga Sumayyah da Anne kaman sun mace ba rai a jikinsu.

Benazir kuwa har lokacin jinta bai dawo daidai ba sama sama take jin ihunsu da hayaniyarsu hakama ganinta bibbiyu take gani.

Daki hande tayi dashi ta zaunar jikinsa na wata irin rawa Kansa na Neman juyewa yana cewa wlh gobe asibiti zai kaita sai an auna yagani zai yarda da cikine a jikinta na mutum tukuna yasan ma kalan matakin da zai dauka akanta da duk Wanda yakeda sani akan cikin aka boye masa da yanda ma aka samu cikin,saiya kashe wanda yayi mata cikin nan ko dan uban waye,

Sai ya daure zuriarsu kaf a gidan yari,

Sai ya buga musu tambarin da har zuriar su qare a duniya sai sun ringa tinasa da abinda sukai masa.

Hawaye hande keyi tana tsinewa koma waye da zuriarsa tareda tsinewa karatun nasu Sumayyah da sanadinsa suka hadu da wannan muguwar kaddarar.

Chapter 23

23

Mintina kusan goma Sha wani Abu suka share a tsakar gidan yashe Babu Wanda ya dawo hayyacinsa acikinsu bare yataimaki Dan uwansa,

Benazir datasan itace komai dadewa zata taimaka musu tafara kokarin miqewa ta rarrafa tana Dan bubbuga kanta sbd kunnuwanta su dawo daidai da Ganinta.

Gurin Anne ta fara nufa Amma Annen ita Kuma kokarin motsawa takeyi ta nufi gurin sumayyah datake kaman ba Rai jikinta.

Ganin haka itama benazir din ta nufi sumayyahn tana dagota jikinta tana Kiran sunanta da qaramin sauti sbd bakinta daya kumbura a take baya iya buduwa sosai.

Anne ma sumayyahn take Kira murya a shaqe tana Jin zuciyarta na karyewa idan wani Abu ya samu sumayyahn,

Ba zasu iya rayuwa Babu ita ba,

Benazir din ta ma zata iya rasa tata qwaqwalwan idan suka rasa sumayyahn,

Idan benazir datake jinsu da ganinsu tareda zama kaman itace uwarsu ta rasa kanta Yaya ita zata kasance?

Hawayen da zafinsu yasa take tinanin na kukan jini ne da ake fada anayi Idan balai da masifa sukai yawa anayi suka gangaro mata tareda benazir data dago sumayyahn gabaki daya sai alokacin taga jini a jikin sumayyahn tana zuba Sedai ba sosaiba take hankalinta ya tashi sai alokacin ta fashe da wani irin kuka mai qarfi dayasa Anne rikicewa tana qanqame benazir din hawayenta na gudu tanacewa

“Bena ta karki haukace kece gatanmu ni da sumayyah,

Idan wani Abu yasameki kaman yanda muke bamuda sauran Saka Rai daga sauki,

Kasa motsi benazir din tayi kukanta na tsananta tana sake rungume sumayyah.

Inama Ababa zai Basu mahaifiyarsu su tafi ko bolar ce su bi,

Zata zabi arawa kanta haukan itama tabi uwarta da yan uwanta subi bolan yafi musu Wannan masifar,

Zuciyarta tafara raunanan da Kila bazata iya daukaba,

Tabbas idan suka rasa sumayyah itama kanta juyewa zaiyi sbd bazata iya kallan mahaifiyarsu a cikin Hali na haukan rasa sumayyah ba.

Anne ganin benazir din na cikin tsananin halin kukan sai kawai ta daure ita ta miqe tsaye da qyar qafarta na wani irin radadin azaba da tsami Amma a haka ta kama sumayyahn daga jikin benazir din suka kamata zuwa can bangaren dabbobi benazir ta rungumeta Anne ta aro jarumta da dauriya wadda Benazir ke tinanin bama a hayyacinta Annen take ba kawai dai girman soyayyar uwa da ‘yayanta ne yasata rikicewa tana Neman ganin sumayyahn ta tashi.

Ruwan ta debo takawo dukkaninsu jikinsu na rawa suka hau wankewa sumayyahn jiki Wanda sanyin ruwan yasata Bude idanuwanta a wahalce tana kallan sararin sama sbd bazata ma iya kallan mahaifiyarsu da Bena dinta ba sbd wahala da baqar kaddarar data janyo musu,

A yanxu da cikinta ya bayyana sunsani Babu ranar sauki ko kadan daga rayuwarsu sai Kuma yanda Allah yayi dasu,

Inama ta mutu da cikin ta tafi ta rage musu wahalarsu musamman Bena sbd Anne da qwaqwalwanta yajuye bazata tantance komaiba bare ya tsaya zuciyarta Amma Bena komai na rayuwarta tsayawa zaiyi,

Acikinsu kowa ya cimma tasa qaddarar ita idan duka suka barta batasan ya nata kaddarar yake ba.

Benazir data San tinanin da sumayyahn keyi rungumeta tayi ahankali bayan sun wanketa tas kaman gawa sbd ko motsi Bata iyawa da kanta.

Annensu sai alokacin take Jin zuciyarta na nauyi Bata ko iya Jan numfashi daidai Saida benazir itama ta rungumota sukai shiru a hakan tsawon lokacin kafin suka taso suka shige dakinsu har lokacin hande na gurin Ababa tana fama dashi sbd shi Kansa kaman qwaqwalwansa Neman juyewa takeyi sbd a rayuwarsa Bai taba Jin tashin hankali da masifar wuta na cin zuciyarsa kaman yau ba,

‘yayansa datake tinanin ko tirelar qwaya mutum yasha bazai tinkaresu bama bare har kebewa Harma da ciki,

Ko waye wannan tsautsayi yakaisa tabbas ya jawa Kansa da kaf danginsa da kuwa wlh kafin hukuma ta shigo ciki su zuba muguwar makauniyar shariar da sai ya tabbata an rufesa kafin can saiya fasa masa gaban wando da bindigarsa idan ya warke ayi shariar sbd lokacin ya rasa lafiyar wandonsa ta yanda shi da mace sai kallo.

Hande kuwa tsinuwar datake rafkawa akan me cikin da karatun nasu da ma Anne data bi bayansu aka boye cikin gashi suna Neman cinnawa ‘danta hauka kokuma tace sunma cinna masa.

Gari kawai yake jiran ya waye yakaita asibiti a auna masa ita a duba a fada masa cikin idan na gaske ne Kuma watansa nawa ta yanda zaizo yayi dalla Dalla dasu yasan ta inda zai fara karya qafar uwarsu kafin ita me cikin Dan kuwa ko watansa daya saita haifesa a ranar batareda anbata komai na fitowar tasa ba.

Benazir ruwan zafi ta fito ta Dora a sace ta zubo a roba tazo ta gasa jikin sumayyahn koina

Kafin ta gasa Anne itama data fara kokarin birkicewa Amma benazir ta dage tana shafata da adduoi har ta lafa sai Kuma ciwon jiki da zafin jiki a haka har tayi baccin wahala.

Sumayyah ma baccin wahala ne ya fizgeta

Sai a lokacin benazir ta zauna ta dasa kukan dayake cinta tanata dannewa sbd Anne data rude da kukan nata.

Kasa bacci tayi tana gadinsu idanuwanta jajir sbd tsoron kada suyi bacci Ababa yazo ya rufesu da duka kokuma fushi yasa ya cinnawa dakin wuta.

A zaune ta kwana tashin hankali da tsoro Bai bari ta iya ko rintsawa ba sai  gab da asuba ta fito tayi alwala ta ringa nafila tana kuka cikin sujjada tana fadawa Allah kukansu.

Anne da sumayyah dayake ba lafiyar sunyi baccinsu cikin wahala jiki duk yayi tsami ko motsawa sukai ciwo jikin ke musu koina.

Sai datayi sallan asuba ta tayar dasu Anne tayi sallah sumayyahn Kuma suna Saka ran cikin ya qarasa zubewa Amma a mamakinsu Jininma ya tsaya Babu ko alamansa Dan sai jikinsu ya sake sanyi dole tayi sallah jinin da alama na tashin hankali ne ya zubo.

Bayan gama sallar su Saida benazir ta sake gasa musu jikinsu harda ita sbd idan ba hakan ba ko miqewa tsaye daidai Babu Mai iyawa a cikinsu.

Ita da Anne dole suka daure suka fito suka hau aikin gidan a tsorace sbd sunsan baayi komaiba jiyan tinda bai tambayi komaiba sai yanzu ne zai tambayi komai yasan yanda zaiyi dasu.

Tsit tsakar gidan yake daga hande har Ababan babu Wanda ya fito Kuma da alama duk sun tashi kawai dai kowa baqin ciki da tinanin yanda zaayi dasu akeyi.

Suna gama aikin qafafun benazir na rawa zuciyarta na tsalle takaiwa Ababan abincinsa saidai ko dagowa baiyi ya kalleta ba sbd kaman yanda sukai kwanan zaune Shima yau shi yai sbd an shammacesa Tako Ina,

Anci Amanarsa,

An yaudaresa duk a cikin gidansa,

An lalata masa komai,

Duk Wanda ya sakasa wannan baqin cikin da ciwon ran wlh Shima sai yayi uban ubansa,

Ita sumayyahn naqudar dole zai sakata a yau din tasan me ake nufi kame Kai dayace suyi daga kula uban kowa.

Hande da Benazir takai mata abincinta harara da fada Mai zafi ta rufeta dashi harda jifanta da maficin roba dayake hannunta tana kiransu da sunaye.

Bata iya dagowa ta kalletaba bare tankawa harta gama ta Korota ta fito da nasu da handen ta Basu takawo musu daki.

Babu Wanda ya kalli ruwan Lipton din da biredin sbd damuwa da rashin sanin mezai faru.

Anne daga baya ta takurawa sumayyah Tasha kafin Suma suka Sha suna gamawa hande ta leqo dakin tana kallan sumayyah da Benazir tace su shirya su fito inji Ababa asibiti zasu.

Tana fada musu ta bar gurin tana cewa suyi sauri karsu Bata lokaci Aljanun masifarsa su tashi.

Shiru sikai dukkaninsu tareda sauke numfashi Mai sanyi jikinsu na sake sanyi tareda saddaqarwa suna barin komai ga ubangiji.

Anne kaman wadda zata rabu da ‘yayan nata haka takeji zuciyarta na sanyi tareda jikinta,

Da kanta ta taya sumayyah shiryawa bayan tayo wanka jiki mace,

Benazir ma jikin nata a mace yake har suka shirya suka fito Anne Bata iya fitowa dakinba har suka fice tana Jinsu.

Ababan ne a gaba sai hande a bayansa sai benazir din da sumayyah kaman marayu Babu Mai kuzari da qwarin jiki.

Taxi ya Tara ya shiga gaba hande tafara shiga kafin tace su shigo,

Sumayyah Ce ta fara shiga benazir na taimaka mata kafin itama ta shiga ta rufe suka bar gurin.

Babu Mai magana a cikin motar tsit ake kowa da yanda zuciyarsa ke bugawa da kalan tinaninsa,

A motar kaf idan aka cire direban kowa fatan yakeyi idan anje a auna aga bakomai cikin ace Babu ya fice.

Shi kansa Ababan dayake Jin Yana ci da wuta Kansa na zafi fatan yake cikin ace Babu.

Wata private asibiti sukaje sbd bazai juri zuwa Inda zaa masa aikinda zaa kasa basa cikakkiyar bayani yanda yakeso.

Kudin yankar kati da komai ya cire ya biya zuciyarsa na sake daukan zafi sbd kusan wata dubu goma ya kashe.

Zaunawa sukai zaman jiran layi duk da Babu wani layi mutum biyu ne gabansu,

Gabaki daya fuskar Ababa da dukkaninsa Babu annuri ko kadan a tare dashi,

Wani zafi Kansa ke sake dauka har lokacin Babu kalma ko daya data hadasa dasu har Handen datake ta masifa qasa qasa tana zungurar Sumayyahn ta qafa.

Sumayyah kuwa hannunta Yana cikin na benazir sun qanqame hannuwan junansu kaman zasu hade junansu,

Da ace ana cire cikin wani a Maida na wani tabbas da tin kafin asirinsu ya tonu zata dawo da cikin sumayyah jikinta, ta dauki duk wata wahala da ukuba Harma da azabar Ababa a maimakon Sumayyahn.

Yanda zuciyoyinsu ke bugawa cikin fargaba da tsoro kaman lokacin ne zaa fada musu cikin,

Hande ma sai zare Ido takeyi tana qarawa ta matsu ayi musu bayani suji su koma su San yanda zasuyi da cikin tin wuri.

Kiran sunan sumayyahn Akai take gabanta yai mummunan faduwa ta sake qanqame benazir tana kallanta idanuwanta na cikowa da hawayen.

Ababa ne yayi mata wani kallo daya fuskarsa Babu sauki ko kadan,

Sakin benazir tayi tareda miqewa tsaye tabi bayansa suka shiga dakin likitan.

Kallansu likitan Dake zaune yai Yana mamakin shigowarsu su biyun.

Ababa da Bai tsaya jiran komaiba ya zauna Kai tsaye ya korowa likitan bayanin ‘yarsa Ce Kuma budurwa Amma suna tinanin ciki ne jikinta a duba masa ita dakyau idan da gaske ne.

Kallanta Dr yayi take ya hangi nutsuwa a tareda ita Amma Kuma yasan baka shedan mutune yanzu Dan haka Yace Ababan ya fita yabasu guri.

Fitowa Ababa yai Dr ya dubata tareda tambayoyi duk abinda suka dace kafin ya turata office din kusan dashi ya biyo bayanta yayi mata scanning da Kansa ya duba duk abinda yake buqata suka fito.

Office dinsa suka koma ya Kira Ababa Kai tsaye ya miqa masa takardar ya sanar dashi ciki ne Kuma kusan wata uku Harma da kwanaki.

Yanda Ababa yayi shiru yasa likitan yayi tinanin tawakkali ne mahaifin nata yayi sai kawai ya Basu yan shawarwari tareda nuna musu ilolin cire ciki Harma da nasiha sosai kafin ya sallamesu suka fito.

Suna fitowa hande fuskar Ababa takalla tasan masifa ta qullu kenan Dan haka suka taso itada benazir Dake kallan ‘yar uwarta ta qarasa suka kama hannun juna suka fito Ababa na gaba suna bayansa.

Chapter 24

24

A motarsu ta dawowa tinda suka shigo hande Ce Mai magana cikin takacinsu Dana uwarsu sai fada takeyi tana qarawa Amma Babu Mai iya ko dogon motsi a cikinsu bare dagowa su tanka,

Hankalinsu da tashin hankalinsu Yana kan Ababa ne da yake shiru har lokacin Bai Ce qala ba,

Idanuwansa sun kada sinyi jajir sbd tafasar zuciya da bacin ran dayake fal cikinsa.

Suna isowa nesa da gida aka ajiyesu ya biya Mai taxi suka nufi hanyar gida.

Duk taku daya dasu benazir keyi na hanyar zuwa gidan bugun zuciyarsu da numfashinsu sauyawa yakeyi har suka iso.

Annensu da tin bayan fitarsu kowane second daya shude fargabarta da tsoranta qaruwa yakeyi,

Aikin girkin da aka barta tai na Rana har suka je suka dawo Bata iya aikata komaiba sbd Bata cikakken hayyacinta matiqar ba yayanta taga sun dawo mata ba,

Tsoro da tashin hankalin datake ciki Mai girma ne sbd tinaninta da sanin Ababa zai iya Kai mata yayan wani guri ya barosu akan wannan laifin dasuka aikata.

Suna shigowa ta miqe tsaye daga zaunen datake tsakar gida tana jiran tsammani,

Idanuwanta akan Yayanta suke saidai kafin tai yunqurin Isa garesu Ababa ya dago fuskarsa yana zama kan kujerar robar zamansa Dake tsakar gidan.

Numfashi ya sauke tsawon mintina kafin ya dago ya kallesu daya bayan daya ya zare hular Kansa ya ajiye gefe tareda nade hannuwan rigarda daga zaunen cikin kwantar da hankali yace

“Wannan cikin zaa min bayaninsa Dalla Dalla,

yaushe aka samesa,

Dan gidan uban waye yayisa kokuma uban waye yayisa,

Tayaya aka Sami wannan damar,

Yaushe kuka San dashi aka boye min Kuma ubanwaye a cikinku ya Bada shawarar a boyemin,

Komai Zaku fada mun daya bayan daya kafin yanzu ta haife shege Dan bazai kwana a cikinta yau dinnan ba.

Sumayyah ya kalla wadda tini qafafunta suka fara mazari suna Neman gagara tsayuwa.

Kan benazir da itama take rawar jikin ya maida idanuwansa kafin daga qarshe ya jefawa Anne nata kallon Yana tinanin ita yanda zaiyi da ita idan ya gama da wainda ta daurewa gindi akaci Amanarsa a cikin gidansa.

Shirunsu yasa zuciyarsa qarasa birkicewa a haukace yayi ball da butar hande Dake kusa Yana cewa Zaku min bayanin ko saina taka wuyan uwarku gatanan.

Rawa jikin sumayyahn ya dauka take ta rude harshenta ya karye takasa magana ta zube qasa kan gwiwowinta tana Neman hawaye daga idanuwanta da Sukai jajir din tashin hankali.

Wuyanta ya kamo ya sauke mata wani lafiyayyan Marin daya sata qarasa rudewa tana kasa magana ga wuyanta a hannunsa Yana neman rabata da numfashinta.

Cikin zafi ya sake shaqar wuyan nata Yana cewa

“Ubanwaye yayi Miki cikin?

Ni Zaku yaudara?

Ni Zaku ciwa mutunci?

Ni Zaku tozarta?

Yaushe kuka Sami damar da har kuka fara Kula Wanda yayi Miki cikin??

Firfitowa idanuwanta sukai tana shura qafa azaba zatasa ta rasa ranta…

Cikin tashina hankali da tsoro Mai tsananin gaske benazir tace

“A makaranta suka hadu ya taimaka ya kaimu asibiti batada lfy,

Sunansa ALH BILAL KAANTE.

Shiru yayi tareda juyowa ya kallo Benazir da jajayen idanuwansa sbd kunnuwansa da kaman Basu Ji masa daidai ba,

Shirun minti daya yayi Yana neman Inda zai Dora zacenta cikin Kansa Amma ina Sam zancen Bai doru ba Dan haka ya sake danqar wuyan sumayyahn Yana cewa gwara ta mutu data haifar masa wannan cikin wlh.

Cikin kuka mara sauti da tashin hankali da tsoran karya kashe sumayyahn ta sake cewa

“Wallahi Ababa sunansa Alh Bilal kaante,

Shine…shine hakan ta faru dashi…

Sakin sumayyahn yayi ya fizgo Benazir din cikin zafi da wutar Dake cin Kansa Ya daga hannu zai mareta sbd Kansa ya kasa dauka zancen nata Neman cinna masa hauka takeyi yanajin kaman tana fadan sunan Alh Bilal kaante a matsayin uban cikin,

KAANTEs KAANTEs dai daya sani a labarai da jarida take fada,

Ta Ina?

Ta Yaya?

Gari Yaya?

Cikin azaba murya Bata fita daqyar sumayyah ta Bude Baki tace

“Shine,

Bilal kaante…

Dauke wuta Ababan yayi Yana juyowa ya kalli sumayyahn sbd yanda ta fadi sunan Bilal din zalla ba Alhaji ba sir da alaman da gasken kenan,

Amma tayaya kansa zai dauki wanna zancen?

Tayaya zasu Ce masa cikin nan Dan kaantes ne yayi sa.

Inaaaa haukatasa zasuyi wlh dukan rini zai musu su dawo hayyacinsu idanma ciwon qwaqwalwa ya kamasa su dukan.

Janyosu yayi ya hade guri daya ya fara duka Anne tayi saurin zuwa ta zube gabansa cikin magiya da kaskantar da Kai tahau rantsuwa akan Bilal dinne.

Bai saurara Saida Benazir ta sake rantse masa da Allah cikin azaba da wahala sbd kusan dukan kare sumayyah taita Yi Yana sauka kanta sbd cikin.

Hande data rasa gane kan zancen cikin zafi ta taresa ta janye gefe tana cewa

“Ba gashi sun fada sunan me barnar ba meyasa bazaka tsaya kaji sauran bayaninba asan hanyar bi.”

Kallan hande yayi zaiyi magana sai ya fasa sbd bazata fahimci mema zai fada din ba Dan haka ya juya a zafafe yabar gurin ya fada dakinsa sbd bacin ransa da baqin cikinsa ayau Babu wanda yakaisa shi a Dunia.

Cikin sauri da tausayi Anne tayi kan Yayanta ta kamasu suka miqe tayi daki dasu.

Zaunar dasu tai Allah yasa Basu wani daku ba Dan haka itace yau tayi musu gashin jikin suka Dan Ji sauki tafito ta Dora abincin Rana kafin ya nema ace batayiba.

Hankalinta a rarrabe tayi aikin tagama lokacin har sunyi sallar azahar,

Sumayyah Ce kejin zazzabi Amma benazir dole ta warware sbd kada aikin yawa Annen yawa.

Shiru gidan yayi har yamma Babu motsin kowa Suma suna daki sbd dukkaninsu Ba Wanda bejin zazzabi Amma sumayyah Ce kawai ta Sami damar kwatawa sbd yafi mata karfi akansu sbd yanayinta.

Haka suka wuni cikin zullumi da wasi wasi tareda fargaba har dare yayi har sika kwanta Ababa Bai sake nemansu ba.

Yau dayake tana Jin zazzabi fiye da jiyan duk yanda taso gadinsu kada a riskesu da daddare a illata su bacci Bai barta ba 12 na yi bacci Mai karfi ya dauketa itama jiki duk a mace.

Washe gari qarfe 7 na safe Ababa yasake Kiran kowa qaramin palonsa suka zazzzauna Yace yanzu Yana sauraro ai masa bayanin ta Yanda sukasan Alh Bilal kaante din har ake maganar shine uban cikin.

Wanna Karan sunsan suba tsimi ba dabara Dan haka jiki mace a tsorace sumayyah na rawar jiki Harma data harshe ta fada masa a makaranta suka hadu ya ringa bibiyanta akan Yana sonta.

Daga Nan shiru tayi sbd batasan me zata fada ba Dan bazata iya fadan abubuwan daya ringa ciyar dasu ba da yanda suke shiga motarsa da napep daya siya don kaisu makaranta Harma da yanda yaje da ita gidan qaninsa kaddarar samun cikin ta samesu.

Idan ta fada wannan bayanin kashesu zaiyi take a gurin shiyasa rudewarta ma Bata kaita fada ba.

Shiru yai Shima sbd har lokacin ya kasa gamsuwa da zancen shigowar Alh Bilal kaante cikin zancen cikin nan,

To Amma shi mutum ne Mai komai akan lissafinsa da tsarinsa daya San zai fiddasa

Dan haka ya kwana Yana nazari da lissafi da tinani daban daban.

Idan har Alh Bilal kaante ne uban cikin ba maganar haihuwar ciki yanzu sai ya girma ya Isa haihuwa sbd lissafi da zance ya canja gabaki daya,

Yanzu kam wani labarin zasu Dora ba na baya ba,haduwarsa da Alh Dd babba kaante yazo.

Amma bazai Yi garaje ba sai ya tabbatarda gaskiar maganarsu tukuna.

Kallan Anne yai cikin takacinsu Yana Jin kaman ya mangareta Yace

“Kiyi adduar ‘yayanki ba qarya suka fadamun ba Dan kuwa Idan nagama gano qarya suka fadamun Dan na barsu wlh cikinku ba tsira Zaku ga asalin fushi Wanda Baku taba gani ba”

Kan benazir ya maida kallansa Yace

“Ke Kuma naga alaman Nemo muku hanyar rabuwa da cikin kikeyi wlh motsi daya ban yarda ayisa a gidan Nan ba tareda sanina ba,

Har cikin yanzu ban yarda da wani motsi akansa ba Bada izininaba,

Tinda ta dauko cikin masu karfi wlh saita haifesa da izinin Allah Daman can Banda niyar zubar mata da cikin haifesa naso tayi yanzu lokaci ne na qara mata maimakon haihuwar yau din.

Hande ya kalla Yana sake matse fuska Yace

“Ki Saka ido Sosai kan yaran Nan sbd Tim farko kece kikai sake duk wannan ya faru,

Gashi yanzu Kuna nema zautani da tinani da lissafi,

Wlh na zaune a gidan Nan kowama yasan mokamarsa”.

Yacewa yayi kowa ya fice yabasa guri.

Kaman munafukai haka suka fito daya bayan daya suka koma dakinsu saidai ko zama Basuyi ba hande ta Kira Benazir ta fito aiki.

Sumayyah yanzu da aka San da cikin hakanan dole ta fito Dan kamawa benazir din aiki da Anne.

Ba Bata lokaci suka gama dafa Karin safiyar,taliya Ce da Alayyahu.

Ana Basu nasu suka ci sbd Basu taba tinanin abun zaizo da sauki haka ba,

Babu Wanda Bai sadaqar da barin Dunia ba acikinsu Amma sai gashi Ababan yazo da sauki Amma dai duk da hakan basu cire ran masifar na kwance tana jiransu bane.

Anne kuwa tashin hankalin Dake cin ranta da tsananin damuwa da fargabarta kada Ababa ya nemi Alh Bilal din Yace baisan da cikin ba,

Idan haka ta faru tabbas ‘yarta na cikin mawuyacin Hali Dan su Basu damu da duk abinda zai musu ba kaman abinda zaiwa sumayyahn,

Ita benazir Bata shiga shakka da tsoran abinda Alh Bilal zai fada ba sbd ta shedar da tsananin son dayakewa sumayyah bazai gujetaba Amma dai ta yanda Ababan zai tinkaresa da yanda lamarin zai kasance ne tsoronta da tashin hankalinta.

Sumayyah kuwa a yanzu jikinta yayi sanyin da batada saura tinani ko fargaba,

Qaddara dai ta Riga ta hau kanta,

Batada ikon kanta batada dabarar kanta,

Idan aka barta ta haifesa da acire mata shi duk batada tacewa ko zabi sbd kowanne Akai mata rayuwarta ta Riga ta lalace.

****Kwana biyu Ababa Bai sake tada maganar cikin ba ya kyale kowa sbd tsananta bincikensa dayakeyi ba dare ba Rana akan Familyn kaantes,

A saninsa dukiyarsu a bayyane take gurin alumma Amma daya tsananta bincike sai gashi Yana Jin dukiyoyin Dake Neman juyar da lissafinsa,

Komai nasa a tsarin lissafi yake binsa shiyasa yake wani mugun bincike akansu na boye dayake buqatan sanin duk wani sirrinsu na Fili Dana boye sbd Yana tinkararsu da maganar cikin ‘yarsa zancen ma a masa musu Bai taso ba asiri rufe a karba cikin.

Chapter 25

25

Duk wannan shirun da Ababa yayi sudai hankalinsu bai kwantaba sbd sunsan ba shirun lafiyane ba,

Sumayyahn Kuma yanayin jikinta kaman kada a San da cikin sai ciwonta yayi sauki sbd Daman kullum harda qarin fargaba da tsananin tashin hankalin tsoron ranar bayyanar cikin Amma yanzu Tinda ta faru ta qare Ababa yasan da cikin sai zuciyoyinsu suka Dan dawo hayyacinsu kadan duk da Basu San makomarsu dashi cikin Kansa har lokacin ba Amma dai suna jiran tsammani daga shirun Ababan.

Hande kuwa duk motsin da zasuyi yanzu ta Saka musu Ido kullum fada da hantara sbd ita har lokacin takasa saukowa daga fushi da bacin ran samun cikin gashi Ababan ta rasa gane Kansa yaqi fadan komai har lokacin.

Shikuwa Sam baimasan handen nayi a Dan kuwa kusan kaman zaucewa yake Neman Yi duk Daren Allah har gari ya kusa wayewa lissafi yake na dukiyar kaantes da tsaban arzikin da Allah yayi musu,

Ya kasa yarda da jinin kaantes ne a gidansa Dan haka ya yariga ya yanke shawarar sai an haife cikin Ras da yardar Allah.

Anne ba yanda ta iya itama bayan taya ‘yarta rainan cikin tinda dai kaddara ta rigayi fata,

Kulawa sukeyi da sumayyah sosai ita da Benazir,

Gaba daya aikin gidan sun dauke mata sune sukeyi duk da kusan Benazir Ce kawai me aikin Annen tafara sanyi Bata wani iya aikin sosai.

Kwanaki da satika suka shude a hakan sunata fama har hutunsu ya qare Benazir Ce kawai ta koma makaranta Banda sumayyah sbd ita kam nata karatun da alama ya tsaya Kuma ga ciki daya Dan fito ana ganinsa.

Da aka koma hutun Benazir komai Ababa Bai fada mata ba akan kula Maza bayan kalma daya

“Idan kuka kawo min wani cikin gidan Nan wlh ko na bill gates saina binne ki da Rai,

Ki kula namiji harya dirko Miki ciki kigani idan bazan iyaba”.

Bata buqatan qarin bayani sbd tasan Babu abinda ya fada Wanda bazai iya aikatawa ba,

Kuma ko da Bai fada din ba tinda ciki ya bayyana jikin sumayyah wani irin sabon tsoron Maza Mai tsanani ya shigeta sam Bata ko iya gaisawa dasu tayi nesa nesa dasu,

Nasir ma tini hankalinta yake mummunan tashi idan ta gansa bare ya kusantota Yana son Yi mata magana.

Ms Aysha dai Bata dawoba da alama tabar Nan din Kila ba lallai ta dawoba kwata kwata Dan haka jikinsu yayi sanyi sbd Basu cire ran samun mafita ba daga gareta Amma yanzu da suke da tabbacin Kila ba dawowan zatayi ba sai jikinsu ya mutu tareda fidda Rai daga ganin Alh Bilal Shima.

Dayake Kuma wannan Karan ba sumayyah a makaranta sai Benazir ta Sami nutsuwar tsayar da tinaninta da hankalinta guri daya sosai tana fuskantar karatun nata.

Wannan Karan Kai tsaye cikin tsoro da gudun sabuwar masifa tacewa sulaiman Mai napep dinsu ya dena zuwa kwata kwata ita dai zata ringa zuwa a mashin din dasuka saba.

*****Ahankali lokacin yaketa sake Dan tafiya sunata sake zubawa sarautar Allah Ido suna jiran Ababa da har lokacin baice komai ba,

Abinda Basu sani ba Yana sane da Alh Bilal baya qasar sbd binciken tsaf Da sirrin daya yiwa zuriar kaantes yasan har boyayyan sirrinsu da duniya Bata sani ba sbd har abada bazasu taba bari a sani ba,shi kuwa kudin gaske ya barar masu yawa kusan fiye da Rabin tattalin arzikinsa sai daya qare gurin bincikensu sbd su din bana wasa bane yama Yi arziki da ba duka dukiyarsa tashige ta qare gurin binciken nasu ba Dan haka gabaki daya lissafinsa akan cikin da sumayyah da komaima daya shafi cikin ya sauya kwata kwata Kai tsaye magana Ce ta dalolin gaske kawai kokuma wlh duniya tasan abinda basa son a sani.

Satin benazir uku da komawa makaranta cikin sumayyah ya fita wata hudu ya shiga na biyar a lokacin Kuma sai lafiyar tafara gagararta sbd rashin kula da rashin abinci Harma da rashin magani irin Wanda masu ciki suke buqata,

Jini isashe ma Sam da alama Babu a jikinta Dan haka hankalin Anne Dana Benazir yafara tashi.

Tin yanayin jikinta kadan kadan ne har jikin yafara tsanani ruwa ma Bata iya Sha tana Sha zata amayar dasu ga zazzabi da kullum dashi take kwana dashi take tashi.

Babban tashin hankalinsu da tsoronsa kada wani Abu ya sameta har ita har cikin sbd yanzu Kuma akan cikin sunsan Ababa da wani abin ya samu cikin ya fison sumayyahn ta rasa komai Amma dai ta haife cikin.

Hande tana gani yanda kwana biyun suketa fama da sumayyahn data fara rikicewa gabaki daya Amma tai musu biris sbd ba itace ta aikesu dauko abin kunyar da takaicin ba kokuma taje ta ta shiga lamarin Nasu cikin ya samu matsala Ababa ya haukace musu a cikin gidan Dan ita yanzu ta rasa masifar data samesa ya Hana su bari komai ya samu cikin.

Cikin dare sosai jikin sumayyah ya rikice wani irin ciwon mara da zazzabi Mai qarfin gaske da rashin gani suka taso mata haiqan,

Rawa da kakkarwa dukkanin jikinta keyi hakama numfashinta na Neman daukewa,

Benazir da Anne idanuwansu wani irin ja yai kukan ma ya kasa zuwar musu sbd tashin hankalinsu yafi qarfin kukan,

Rungume suke da ita a jikin Benazir

Anne taje ta debo ruwa takawo suka Ringa goge mata zufan dayake jiqata da tsananin ciwo.

Basuda mafita basuda yanda zasuyi

Tsoro biyu ne fal cikeda ransu dayake gigita ruhi da gangar jikinsu,

Tsoron rasa sumayyahnsu da tsoron rasa cikin na Ababa Dan yanzu ya zama tamkar nasa ne gurin Iko.

Idan wani Abu ya samu cikin ba lallai ya barsu da sumayyahn tasu ba Idan ita ta tsira kenan bayan rasa cikin.

Cikin karyewar zuciya benazir ta kalli Anne da jajayen idanuwanta tace

“Anne mu fadawa Ababa sbd kada wani Abu yafaru Yace mune muka kashe cikin nan tinda Yana zargin munason cire cikin ne.”

Cikin sauri Anne ta gyada Kai Bata hayyacinta sbd mafita take nema kada ta rasa yarta.

Miqewa tayi da sauri cikin duhun dare ko gabanta Bata gani Amma dayake sun saba da duhu su basuda hasken rayuwa Basu a hasken fitila

Ta nufi hanyar dakin Ababan tana Isa Saida tayita rawar hannuwa data qafafu sbd kada ta buga Yace ta buga masa kofa da karfi ta tayar masa da hankali cikin baccinsa.

Ahankali kaman mara laka a jiki ta Dan fara buga kofar da qaramin sautin da bazai razana baccinsa ba.

Jin shiru ya sata sake bugawa sbd kowane second Jin zuciyarta takeyi kaman zata fito kirjinta sbd tsananin tashin hankalin ciwon sumayyah.

Mintina kusan biyar ta share tana buga masa kofar kafin ya taso ya Bude Yana kallanta idanuwansa cike da bacci sbd idanuwansa dasuka kumbura a yan kwanakin sbd rashin bacci akan lissafin yanda rayuwa cikin ahalin kaantes zata kasance masa.

Ganin Anne tsaye tana hada uban zufan duk ta jiqe idanuwanta duka a waje yasa gabansa faduwa ya murxa qananun idanuwansa cikin saurin da Bai san yana shi ba yace

“Lafiya? Me akayi ne?

Rawa muryanta ya sake dauka zuciyarta na karyewa tace

“Sumayyah Ce ba……” Bata qarasa ba ya tureta gefe Yana nufar dakin da sauri sbd idan aka samu matsala wlh kariyar arzikinsa yazo Dan komai baida yanzu na kirki duk ya barar kudin bin diddiqinsa.

‘daruruwan kudi masu nauyi ke binciko sirrikan irin su kaantes

Su ya zubar ya samu lagwansu daya idan ya rasa cikin nan ai sunansa ya tashi daga Ababa yakoma Nobaba.

Yana Isa dakin ya tadda sumayyahn ta sume a jikin Benazir

Benazir na wani irin kuka mai hade da radadin zuciya.

Kafar benazir ya take Yana taba kirjin sumayyahn yaji idan ta mutu ne.

Anne data dauka sumayyahn ta mutu zubewa tayi bakin kofa tana Neman rasa nata numfashin itama hannuwanta da qafafunta na wani irin rawa.

Bugawa zuciyar Benazir ta kusa Yi ganin annensu na neman rasa ranta

Cikin sabon tashin hankali ta zaburo zatayo gurin Annenta kar tayi biyu Babu,

Danqota Ababa yayi ya dawo da ita kan sumayyah Yana hanata Isa ga Annen a zafafe Yace

“Gurin ubanwa Zaki ga Mai buqatan taimako,kamota asibiti zamu babu abinda zai samu cikin nan.”

Annenta take kalla idanuwanta na cikowa da hawayen qaqanikayi.

Sumayyahn ta kama masa hankalinta na rabuwa biyu sbd Annen dai ta kusa somewa a gurin Amma haka Ababa ya jata suka tsallake Anne suka fice da sumayyah dakin.

Suna fitowa tsakar gida hande na fitowa a rikice Jin ihun Ababa na fada a cikin Daren.

Ganinsu dauke da sumayyah ya sata wartsakewa daga sauran baccin itama tana Jin firgicin kada komai ya samu cikin su shiga uku su lalace a gidan Dan wlh Kila su da abinci Kila saidai kowa ya dauka robar bara ya nemo nasa yaci Dan Ababa rantsuwa yayi aka rasa cikin wlh garin kwaki ma a gidan bame sake gani bare abinci sai randa baba tagani.

Ganin fitowar hande yasa Benazir Jin yar dama akan annensu Dan hande zata dubata ko yayane.

Suna fitowa mashin dinsa da tini ya dena Hawa ya janyo daqyar ma mashin din ya tashi sbd dadewa baayi amfani dashi ba.

Tsakiya suka Saka sumayyahn benazir tahau Yana cewa

“Wlh ki riqeta kaman ranki ne a hannunki banason shashanci.”

Buga mashin din yayi ya hau titi suna juye juye a kan titin sbd ya dena tuqin mashin da dadewa Dan haka yafara iya tuqin yake Dan kunce masa.

Asibitin da suka tafi ranar ya nufa dasu tinda acan aka Bude mata file bazaije wata asibitin ba ya sake biyan wasu kudin file din ba Kuma yafison ta kudin Inda zaa masa komai ba Bata lokaci Dan shi Dan Kai tsaye ne rayuwarsa.

Suna Isa aka karbeta Ba Bata lokaci kuwa ya miqa karamin card dinta daya dauko Bai manta ba

Aka fiddo file dinta tini aka karbeta emergency ward dinsu.

Zama yayi a waiting chair din dake bakin ward din Yana girgiza qafa cikin shiga fatan abubuwa su tafi su dore yanda yake buqata da fata,idan ba hakan ba akwai gagurumar shimfidaddiyar matsala.

Benazir Dake gefensa tsaye rakube hankalinta yafi nasa tashi ta bangaren Annenta da ‘yar uwarta Harma da cikin Wanda a yanzu cikin shine igiyar zamansu lafiya da kwanciyar hankali da haka Suma cikin ya zama abin tattalawarsu.

Zaman jiran Dake cin zuciyoyinsu sukeyi shiru shiru ba’a waiwayesu ba.

Duk bayan sakanni saiya waiwayo yayiwa Benazir kallan dayake Jin kaman ya rufeta da duka da Basu fada masa matsalar da wuri ba kokuma Kila wani abin suka Bata Dan cire cikin Amma dai yanzu shawo kan matsalan yake fatan Ayi kafin yayi lokacinsu Benazir da Annen.

Yana wannan tinanin nurse ta fito ta miqa musu takardar abubuwan da zasu siyo.

Karba yayi ba musu yaje ya siyo komai ya dawo Yana Jinjina ledan sbd kudin daya kashe gurin siyo abubuwan Da aka rubuta din.

Yana kawowa nurse ta sake miqa masa wata takardar kudin gado da zaije ya biya.

Chapter 26

26

Kallan kudin Dake rubuce kan takardar yayi duk da bokonsa bamai zurfi bane Amma sosai yakeda lissafi da ilimin gane lissafi a rubuce a kuma bayyane.

Dubu goma kudin gado” ya sake maimaita karantawa Yana Jin zuwan jikinsa na sake daukan tafasa Dan kuwa Wannan zubin da baisan ko zaiyi kwasa ba dayake yafara cin tsakiyar zuciyarsa ba ruwan jikinsa da jini ba kawai.

Benazir yacira kudin yace

“Kije ki biya kuma wlh duk a lissafe nake ko cikin nan yafita saina ballawa kowaccenku qafa daddaya Kuma wlh Suma kaates sai sun ragemun asara tinda dai anyi cikin Kuma wlh Allah ya Isa zan ringa zabga muku duk ku daidaice tinda kune kuka jamun.

Karban kudin tayi da hannu biyu kanta na qasa jikinta na mutuwa tana fatan cikin nan dai ya tsira yazo duniyar da Babu komai cikinta sai qunci da wahala.

Juyawa tayi ta nufi Inda ake biyan ta biya ta dawo jiki mace ta sake rakubewa ta tsaya Inda take tin farko.

Suna gurin zaman jiran har Akai asuba Ababa ya wuce yaje yayi sallah ya dawo

Yana dawowa ya tadda Babu wani bayani take ransa ya qarasa baci yahau masifar data Saka nurses fitowa dole suka masa bayanin sumayyahn tayi bacci ne na wahala sbd suna Saka ran ba jini jikinta sai anmata Qari pcv dinta suke jiran akawo su gani da B group dinta.

Su kansu likitocin da nurses din sun so Yi masa fadan yanayin da suka samu sumayyahn sbd akwai yunwa da wahala a tare da ita da rashin jini duk ga Mai ciki amma baa kula da ita ba Saida komai yai tsanani tukuna Amma masifarsa da zafinsa yasa suka bige da kokarin fahimtar dashi abinda yake faruwa Dan kuwa kallo daya zakai masa kasan ransa ya gama daukan zafi sai sukai masa uzurin tinanin damuwar ciwon marar lafiyar yasashi ficewa hayyacinsa cikin masifa.

Benazir na gefe rakube duk abinda yake faruwa Bata Isa dago kai ta kalla ba harya gama fadan akace to gaskiar magana jini ake buqata sosai.

Shiru yayi bayan anbasu takardar kawo jinin Yana sake duba takardar zuciyarsa na nauyi Dan kuwa bayajin bayan dukiyarsa zai iya Bada jininsa Dan Shima Yana buqatan jinin

Kudin daya kashe sun gama Kone jininsa baida na bayarwa,

Bazai iya Bada jininsa ba yaxo Bai fita ba abin ya masa yawa Dan haka gwara dai idan akwai na siyan ya siya duk zai Saka a lissafi.

Dakin da aka kwantar da sumayyahn aka kaisu,

kallan baqin ciki da zafin zuciya ya ringa jifan sumayyahn dashi ransa na tafasa Amma Baice komaiba ya juya ya fice yabar Benazir gurinta.

Yana ficewa dakin Sumayyah ta Bude idanuwanta dasukai jajir ahankali ta saukesu akan benazir wadda itama sumayyahn take kallo idanuwanta na cikowa da hawaye masu zafi da radadi.

A tare hawayensu suka gangaro daga idanuwansu batareda kowannensu ya iya cewa komaiba sbd sun Kai matsayin da basa buqatan Bude Baki su fada quncin ransu saidai hawayensu su isar da sakon.

Ahankali Benazir takai hannu ta dafa na sumayyah suna sauke qaramin numfashi a tare.

Shiru ne ya ratsa dakin tsawon lokaci Babu mai iya magana acikinsu suna jiran tsammanin Ababa jikin sumayyahn Babu qwari ko kadan.

****A gida Tin bayan fitarsu hande taga Anne na Neman shidewa ta debo ruwa Kofi daya ta hau yayyafa mata ba Ji ba gani tana cewa

“Benazir bazaki mace ba ki barni da Renan jikan gaban fatiha bayan na gama naki Renan nayi na ‘yayanki,

Maza tashi kece Zaki Rena jikanki tinda kune kukasan ya Akai kuka somosa.”

Numfashi da ajiyar zuciya Anne ta hau jerowa tana Bude idanuwanta da Dan qarfi sbd ita kanta bazata so ta mutu a yanzun ba tabar ‘yayanta Harma da jikan idan yazo cikin wanna masifar su kadai tanason kayanta,jikan ma na gaba da fatihar tana sonsa ahakan tinda Allah ne ya qaddaro musu hakan Kuma sun karba.

Hande wurgi tai da kofin hannunta tana wucewa cikin masifa da cewa

“Tinda kukayo cikin nan kuka hanamu samun zaman lafiya a gida Nan,

Duk Kun zautar mun da ‘da ya haukace ba dare ba Rana magana yake shi kadai da Kansa duk akan cikin nan,

Gashi yanzu Yana musu Barazanar yunwar da Babu ranar dawowa daidai idan aka rasa cikin,

Benazir aurenki dai ba Alkhairi bane ga Ababa tin kuruciya har girma Bai ganewa komai akanki ba”.

Sai alokacin wasu hawaye masu dumi da zafi suka gangarowa Anne ta dafe zuciyarta Dake Neman fashewa sbd abinda takeji cikinta na tsananin qunci da damuwa.

Kasa komawa daki tayi ta rarrafa ta miqe tsaye ta Isa Inda kujerar tsakar gidan take ta zauna tana dafe kirjinta dake Dan mata nauyi da radadi ta dasa zaman jiransu har Akai asuba tana gurin zaune.

Sai da gari yafara haske ta iya daurewa ta tashi taje tayi sallah ta sake fitowa tana kokarin sake zaunawa zaman jira hande ta fito tana cewa kasheni zakiyi da yunwa kenan bazakiyi abinci ba tinda ‘yarki Rai na hannun Allah.

Fasa zaunawa tayi ta nufi kicin tafara kokarin sharewa kafin tafara hura wutan aikin.

*****Ababa har qarfe goman safe Yana yawon Asibiti Neman jinin da zaa sakawa sumayyahn Amma Sam baa samu na siya ba hakama shi bazai iya qanqantar da Kansa rokan kowa jini ba.

Ransa ba qaramin baci yai ba,fushinsa sai qara Hawa yakeyi sbd ko ciwo Bai taba hanasa fita nemansa ba sai yau gashi tin asuba Yana gantalin nemawa jikan da a yanzu yafi kowa son zuwansa duniya.

Yunwa ma bayaji sbd a yau ida Bai samu jini ba dole ya Isa KAANTES su Dd babba Aturo Mai Bada jini wlh,

Yaso ya bari sai Alh Bilal ya dawo qasar ya tinkaresa Amma idan har baa samu ba gwara yaje tin wuri kar yayi biyu babu

Koda Babu me Bada jinin dai su San da cikin ta yanda ko cikin ya matu shikam zai samu abinda zai Maida dukiyar daya rasa.

Koda yadawo dakin daga benazir har sumayyahn idanuwansu a kumbure da kukan dasuka Sha sosai suna ganinsa benazir tai qasa da Kai sumayyah kuwa Dake kwace rufe idanuwanta tayi ahankali tana Jan numfashinta Dake fita daqyar.

Kallan da yayi musu yana Jin inama jinin uwarsu zaiyi da daukota zaiyi a kwashe duka jininta a sakawa sumayyahn da akeda buqatan lafiyanta yanxu.

Kokarin zama yakeyi nurse ta shigo tana fadan baa kawo jininba ana fa buqatansa da gaggawa gaskia.

Cikin takacin rashin sanin abin Yi yace

“Baa samu ba ni nawa Babu yawa bazan iya badawa ba Idan akwai Inda zaa samu na siyan bayan Nan ku fadan nawa ne Kuma nawa ne.

Da mamaki nurse dn ke kallansa Jin wai bazai Bada nasa ba bayan shine mahaifin sumayyahn kaman yanda ya fada.

Ganin kaman zata ma batawa kanta lokaci ne yasata juyawa tana cewa Leda biyu mukeso Kuma ko wanne ka tanadi kudinsa muje Akira aji idan akwai Inda muke saka ran zaa samu.

Miqewa yayi Yana take kafar benazir cikin zafi ya fice daga dakin Yana bin bayan nurse din ransa a bace Jin har Leda biyu bayan yasan jinin mutum sai yayi tsada sosai Kila.

Bayan fitarsa Babu Wanda ya iya motsawa har tsawon mintina kafin sumayyah datasan ba jinin da Ababan zai iya siya a Saka mata bare ma ta rayu,

Hawaye ne suka cika idonta tana kallan benazir data kasa kallanta sbd karyawar zuciyarta yayi yawa.

“Bena” takira sunanta ahankali da wani irin rauni tana Jin karyewar zuciyan itama dan idan ta mutu ta barsu da wahalar da taci alhakinsu.

“Bena ku yafemun ke da Anne….

Kukan da Benazir tafashe dashi ne yasata maganarta karyewa itama tana sakin kuka.

Kasa sauraranta benazir tai ta miqe tsaye tareda barin bakin gadon ta juya mata baya tana kuka mara sauti sbd harga Allah zuciyarta bazata iya daukan rashin sumayyah ba bare Anne.

Ahakan suka ringa kuka har sumayyahn ta dawo tana rarrashin Benazir a hakan sukai shiru dole

ta dawo kusa da ita ta zauna tana Bata tabbacin zaa Sami jinin da yardar Allah.

******

Ababa kuwa Inda aka Saka ran samun jinin baa samu ba take tashin hankalinsa ya Qaru Dan haka Kai tsaye ya yanke shawarar gwara ayita gaba daya bazai haukace ba a hanya gwara Suma su shigo lamarin.

Securityn Dake masa duk wani mugun bincike da boyayyan aikinsa ne ya kirasa a waya daidai lokacin da ya shiga dakinda sumayyahn take ya rufo kofa.

Wayar yakalla cikin zafi da masifar daya rasa yanda zaiyi da ita tana cinsa,

Ganin Mai Kiran yasashi furzar da numfashin bacin Rai Mai zafi ya dauka zaiyi magana aka rigasa da fadin

“Sir Bilal Kaante ya Sauka kasar yau dinnan A Lagos,

Komin dare yau zai biyo wani girjin ya iso gida”.

Tinda aka fara wannan masifar sai wannan lokacin yaji wani sanyi ya Sauka cikin zuciyarsa Yana sanyaya wutar Dake cin zuciyarsa da gangan jikinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke a Fili Yana cewa

“Ayau Nima zanga Manyan kaates din da yardar Allah,

Komai na aikina ya zama shirye Ina awa biyar bakajini ba kasan abinda na fada Maka dai.”

Kashe wayar yayi Yana juyowa yakalli su benazir Dake jinsa Yace

“Alh Bilal kaante ya dawo

Ayau zanje musan matsayar gaskiar wannan maganar,

Kuyi adduar komai ya tafi daidai idan ba haka nadawo kisan ku zanyi naje gidan yari Nima ba huta da masifarku data isheni.

Juyawa yayi yafice dakin batareda ya waiwayosu ba bare tinanin suna buqatan abinda zasu Dan sakawa cikinsu.

Yana fita Kai tsaye gida ya nufa Dan yin wanka ya sauya kaya zuwa shigar alfarma Dan koba komai ta yanda zasu San lafiyarsa kalau ba mahaukaci bane yaxo Yana karanta musu hauka.

*****Barinsa asibiti da kusan awa daya suna zaune jigum jigum cikin fargabar abinda zai biyo baya idan aka samu matsalar da Alh Bilal ya gaddada cikin,

Faduwan gaba da tashin hankalin dasuke ciki ya hanasu Jin yunwa,

Musamman sumayyah datafi shiga tashin hankalin me Bilal din nata zaice.

Kofar dakin nasu Akai knocking ahankali tareda budewa aka shigo cikin sanyi da nutsuwa

Take atmosphere din dakin ya sauya gabaki daya da wani irin qamshin luxury turaran _CARON POIVRE_ na DD dayake amfani dashi kwana biyu yayi tare dashi akan zasu dawo qasar tare Amma wayar sulaiman daya saka bibiyan motsin su Benazir yasashi dawowa Bai jira DD ba dazai dawo tareda su umminsu.

Qamshin yasa sumayyahn kasa gane shi dinne Kai tsaye sbd wannan ba qamshinsa bane kwata kwata da Suka saba Ji.

Ganinsa a tsaye Yana kallansu zuciyarsa na karyewa yasa daga sumayyah har benazir fara hawayen da suka kasa tantance na farin cikin ganinsa ne kokuwa na murnar sumayyahn tasamu Mai Nemo mata jinin da ake Neman.

Chapter 27

27

Kaman saukan ruwa Mai sanyi cikin maqoshin daya bushe da qishi haka dukkaninsu ganinsa ya sanyaya zuciyarsu musamman sumayyah data fara hawayen da bata shirya ba idanuwanta na Kansa.

Shima ita yake kallo idanuwansa na bayyanarda rauninsa da tsananin son da Allah ya Saka masa nata.

Benazir ma farin ganinsa takeyi a Fili idanuwanta na cika da hawaye sbd koba komai idan su Basu samu gatan rayuwa ba ‘dan da zaa Haifa musu zai samu gatan daga ubansa idan har zai aminta dashine uba Kuma magajin abinda zaa Haifa din.

Qarasowa yayi Kai tsaye gurinta ya nufa Bai tsaya Bata lokaciba ya zauna bakin gadon ya rungumota jikinsa a karo farko hawaye na ciko idanuwansa sbd tsananin karywan da zuciyarsa tayi da ganin yananinta gabaki daya ta rame sosai ga cikin Shima yafito ana ganinsa.

Saukowa hawaynsa sukai sbd yakasa riqesu,

Yayi kewanta fiyeda yanda ya tsammata zai iya daurewa,

Ga halin daya sakata yasani zuwa yanzu Ababa ya gama hukuntar da ita Harma dasu Anne ga ciki da yanxu kam dole kowa zai girbi abinda ya shuka,

Babu maganar boyo tinda ciki baa boyesa saidai babban tashin hankalinsa da baqin cikinsa tin daga ranar da aka sanar dasu wanzuwar cikin shine tarihi ya sake maimaita Kansa akanshi.,

Tayaya familynsa zasu karbi wannan girmamman zancen dazai kawo tashin hankula da damuwa.

Shigowar nurse yasa Bilal din sakin sumayyah Yana goge fuskarsa da black handkerchief din dayake aljihun kayan jikinsa.

Qarasowa tayi tana fadan har yanxu baa kawo jinin ba sai ta mutu ne zaa fara kukan ta mutu bayan sune suke son kasheta sbd ance musu da gaggawa ake buqatan jinin.

Kallan nurse yai Yana Maida kallansa kan sumayyah Yace suje Yana buqatan ganin likita.

Juyawa tai ya kalli benazir cikin kulawa da sanyin jiki Yace mata Yana zuwa.

Bin bayan nurse din yayi suka fice daga dakin.

Duka wani bayani dayake buqata yaji daga bakin likita da nurse Dan haka take Yace a duba jininsa idan zaiyi a Saka mata.

Babban Saar dataci jininsa O- ne Dan haka Babu Bata lokaci aka hau diban jininsa a Saka mata hankalinsa na rabuwa biyu sbd baisan ta inda zai fara tinkarar su Dd babba da dad Kaante da zancen kaddarar data samesa.

Benazir kuwa kwanciyar hankali da nutsuwa data samu ta lokacin ta ganin a qalla sun samu jinin da zai taimakawa yar uwarta warware.

********Karfe hudu na yamma bayan yar tafiya Mai tsayi daga gidasa zuwa kaates Ababa ya Isa qatuwar makeken gate din kaates Wanda Saida ya daga Kansa tsawon mintina ya qarewa gate din kallo Yana mamakin Wanda yake rayuwa a wannan gidan kwadayi me ze Kaisa gurin ‘yar marasa galihu.

Securities din Dake zaune a kofar gate din ya hanasa tinkarar qatuwar gate din Kai tsaye Yana Jin qarfin zuciyarsa na qaruwa Dan kuwa dole su Dd babban daya sani a jaridu da labarai su tsaya a sauraresa idan Sunki baida asara bayyanarda maganar cikin zaiyi duniya ta sani har gidan jaridu Dan kuwa tini ya tanadi makaman yaqinsa.

Ko su karba ciki ko yaja musu bacin sunan da kafin suna da mutuncinsu ya dawo daidai ba shekarun kusa ba.

Kuma ya Maka su kotu Koda sunfi karfinsa ya dai Bata musu sunan da duniya taji abinda Akai.

Tin shigowarsa anguwar securities suke kallansa Amma Babu Wanda ya kulasa tinda Basu San Ina ya nufa ba.

Gurinsu ya nufa Kai tsaye Yana Isa suka dakatar dashi daga nesa Dan basa bari ana isowa jikin doguwar katantar gidan.

Daka tawa yayi Yana kallansu kai tsaye Yace musu gurin Dd kaante yazo.

Gabaki daya securities din suka zubo masa idanuwa Jin sunan Wanda Yace yazo gurinsa.

Cikin son dakatar da koma wane irin shirme Ababan ke shirin Yi shugaban securities din fuska ba sakewa Yace

“Sir DD kaante baya qasar shekaru da dama so kabar Nan please”.

Hanya ya nunawa Ababa dayake kallansa Yana Jin takaici Amma tinda Neman ganin Ddn yake dole zai sauke Kai harya samu ganinsa tukuna.

Sanyaya murya yayi cikin Basu girma a gurin aikin nasu Yace

“Officer Alhaji Dd babba dinne baya qasar?

Dan ayimun alfarmar na gansa wlh lamari ne mai mahimmcin da idan natafi yau zaa iya rasa Rai,

Kuma ran ‘dan Nan dinne ne maana jininsu ne.

Wani kallo tsaf chief security din yake masa Yana son tabbatarda idan Ababan ba mahaukaci bane acikin kaya lullube.

Idanuwan Ababan yake kalla Yana sake katantar yanayinsa Dan kada su tsaya batawa kansu time da mahaukaci basu sani ba.

Ganin ana tantancesa yasa Ababa tsayawa da kyau idanuwansa na kan kofar gate din da aka wangale wata mahaukaciyar Lexus black ta fito baa ganin Wanda yake ciki sbd Nisan datake da Inda suke tsaye.

Ta gabansu motar ta wuce idanuwan Ababa kaman zasu zasu fado subi motar Dan son ganin Wanda yake ciki amma chief securityn ya hanasa ko motsawa daga Inda yake bare ya Isa gate din.

Sallamarsa sukai da cewan ya wuce daga layin gabaki daya basason ganinsa.

Qin tafiya yayi ya tsaya Inda yake Yana sake qudurcewa a ransa yafison su masa duka a gurin idan yaso dole a tsaya a sauraresa ya sake samun damar nunawa duniya dukan da Akai masa bayan anwa ‘yarsa fyade so uku.

Sharesa sukai a gurin tsaye suka koma bakin aikinsu iyakaci Yana kusanto babba gate din farkon dukan da zasu masa ko haukace saita sakesa.

Gyara tsayuwa Ababa yai a gurin sbd yau din a shirye yake da kwana tsaye a gurin indai zai samu dacewa da fitowan Wanda zaisa a barsa yaga Dd babba.

Rana Ce tafara gasa Kansa yafara daukan zafi Yana tsiyayar wani irin zufa Yana jiqasa kaman Wanda ya hadiye kunama da ranta.

Sanyi da gajiya qafafunsa sukai matiqa Amma Sam bayajin zai hakura ya tafi gashi hankalinsa duk ya gama tashi zuwa yanzu Kila sumayyahn ma ta mutu da rashin jinin.

Azabar ranar wunin akansa ta qare har Rana ta fadi Yana gurin Yana zare idanuwansa da wahala ta sake rinarwa.

******Acan asibiti kuwa har aka gama diban jininsa aka sakawa sumayyah ba Ababa ba labarinsa.

Daki aka sauyawa sumayyahn zuwa sama dakunan da suke ajiye masu kudi.

Komai sake siyowa akai tareda abubuwa buqatanta dasu abinci kala kala take nurses ba kunya suka hau hidima dasu.

Wanka Benazir ta taimaka mata tayo bayan angama Saka mata jakar jinin daya.

Dan qarfi ta samu a jikinta sumayyahn kafin ta zauna da Kansa ya Bata abinci tanaci a hankali itama benazir ta shiga toilet ta watso ruwan ta shirya tin a can tafito ganin sumayyah taci abinci yanda ya Dan kamata sai alokacin itama ta daure taci lafiyayyan abincin da aka kawo musu iri iri.

Har yamma Alh Bilal Yana tare dasu cikin kulawa Yana jiran Ababa sbd ganin juna da yanxu garesu ya zama dole tinda dalili Mai qarfi ya Saka.

Dayake wayoyinsa a kashe suke Babu Wanda ya Kira nemansa bayan yasan iyayensa sun San ya iso tinda daga gida driver yaje daukansa airport Kuma daga can Nan ya ajesa.

Ana kokarin Sallan magrib dole ya baro asibitin ya nufi gida da niyar zai dawo daga baya.

Driver har lokacin Yana Nan Shima Yana jiran fitowar Bilal din dan haka Yana ganin fitowarsa ya taso daga Inda yake Zaune suna fira da wani Wanda ya sani da sauri.

Motar suka shiga kusan a tare da sir Bilal din dan lokacin ya kunna wayoyinsa Kiran Dd babba ne yafara shigowa wayarsa take ya dauka jikinsa a mace.

Kicin muryarsa ta Kai tsaye Yace yazo Yana buqatan ganinsa.

To Yace cikin girmamawa sbd yasan Shima Bai kyautaba rashin Isa gidan su San da isowar tasa.

Numfashi ya sauke zuciyarsa na tsinkewa da Neman da Dd babban yake masa dan muryarsa ba sauki Kai tsaye take.

*****Ababa babbar sa’arsa daga Allah ne kaman yanda yake fada sbd ana Kiran sallar magrib a babban masallacin kaates Dake manne da qatuwar katangar gidan sai ga fitowar tsohon daya gama jiquwa a cikin arzkin Allah da tarin Hutu da dukiya Harma da boko da ilimin addini ya fito Dan shiga sallah Kuma cikin wata sabuwar sa’ar shi dayane yau sbd dad Kaante da sauran mazan dasuke dasu a gidan sunyi tafiyan kwana daya wani mahimmin daurin auren da dole kaates su halarta.

Duk kowace Rana daidai wanna lokacin Dd babba ke fitowa sallar magrib baya taba fashi matiqar Yana qasar Kuma garin.

Ababa Bai taba tinanin zai samu dama a ranar farko ba lokaci daya ta ganin Dd babba kaante Dan haka yake sake Jin Kansa me Saa.

Da gudun fanfalaki yaso zuwa gurin Ddn Amma securities sukayo Kansa Dan haka ya jujjuya baiga ruwa ko gurin alwala ba bare shima ya fada masallacin Dan haka juyawa yayi da sauri yana Neman Inda zai samu qasar taimama Amma anguwar kaman ta kafiran turawa Babu koina a tsare.

Daqyar ya samu Inda keda yar qasa yayi taimama jiki na rawa ya dawo da gudu gudu sauri sauri yana Isa ya shige masallacin kafin securities su ankare Kuma Daman baa Hana shiga masallacin Sedai bama kowa ke zuwa ya shigaba tinda anguwar akwai tsaro ba mutane.

Ba mutane sosai Dan haka ya kutsa ya shige sahun gaba Inda Dd babban yake aka tada sallah.

Ana idarwa salati da istigfar kawai Ababa yayi ya juyo Yana Satan kallan Dd babba Dake adhkar cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin masu abin duniya.

Ahankali kowa ya fice aka bar limamin masallacin kaantes din sai Dd babba sai Kuma Ababan da bakinsa ke rawa sbd maganar Dake cinsa kada damarsa ta qwace.

Daya daga cikin securities din dazu ne ya shigo zai masa magana

Yana ganin hakan ya miqe ka tsaye ya nufa gurin Dd babba Yana miqa masa sallama da gaisuwa a tare.

Jinjina Kai kawai Dd babba yayi batareda ya amsa da Baki ba sbd Bai gama laziminsa ba Kuma Bai dago ganin kowaye ba.

Chapter 28

28

Ganin security din na sake nufosa ya sanya Ababan zubewa ya zauna gefen Dd babba Yana sake Dan saita muryarsa cikin nuna nutsuwa da mutuntuwa ahankali Yace

“Ranka ya Dade gurinka nazo tin safe an hanani ganinka a waje na wuni tsaye har Rana ta fadi akaina,

Alhaji ka saurareni maganar danake tafe da ita Mai tsananin girma da mahimmanci Ce sbd maganar Rai da mutuwa akeyi data shafe ahalinka da nawa ahalin.”

Kalmarsa ta qarshe Ce ta Saka Dd babba waiwayowa ta kallesa tinda ya fara magana bai juyoba,

“Maganar Rai da mutuwa tsakanin ahalinsa dana kaantes?

Daga Ina wannan din yake?

Lafiyayye ne ko kuwa?” Shine kallan da Dd yayi wa shugaban securities na gidan nasu kafin ya maida kallansa kan Ababa Dake a shirye qyam zantikansa a tsare tsaf cikin ransa da zai jero.

Ganin kallan da Dd ke masa yasa take yayi fuskar tausayi da bacin Rai tareda bayyanarda baqin cikin rayuwa na tareda shi kaman Wanda yayi rashin uwa da uba da kowa na duniya.

Cikin nutsuwa Securityn ya Dan matsosa Yace

“Bismillah malam ko¿Mu Dan je daga waje sai naji abinda ya kawo ka zaa duba matsalarka,muje Bismillah.

Girgiza kai Ababa yayi cikin sake bayyanarda Yana cikin balai da masifar rayuwa Ya sake Maida kallansa kan Dd babba dayake shafa adduarsa daya gama Yace

“Ranka ya Dade Dan Allah ka saurareni,

Kai kadai ya kamata yaji matsalar data kawo ni,

Ina cikin tashin hankali da masifar da bazan iya kallan jamaa ba,

Ni nawa mutuncin ya Riga ya fara rauni a idan duniya,

Banda zabi ne shiyasa nazo Dan kaima kasa muguwar tsautsayi ko kaddara zance data faru tsakanin ‘dan gurinku da ‘ya…..

Bai qarasaba Dd ya juyo ya zuba masa idanuwansa masu kwarjinin arziki da dattako sbd a duniya idan akwai abinda Dd babba ya tsana Ji shine hada Kalmar

“wani abu ya faru tsakani”

Ababa kuwa sake qasqantar dakai yayi idanuwansa na bayyanarda hawaye masu bayyanarda radadi da zafi tareda quncin rayuwar tsaka me wuyar dayake son nunawa Dd babba Yana ciki.

Shiru Dd babba yayi tsawon mintina Yana nazarin Ababa da kukan dayake Yi a matsayinsa na dattijo kafin ya dago kalli Securityn Dake tsaye a kansu cikin nutsuwa Yace

“Ba komai kaje kawai”

“Yes Sir” Yace tareda kallan Ababa ya juya ya bar gurin ya fice masallacin gabaki daya.

Saida securityn ya fice gabaki daya

Dd babba ya Dan sake kallan Ababa Bai basa Daman magana ba sukai shiru sai da limamin masallacin ya gama nasa lazimin ya fice ganin alaman magana zasuyi Kila Mai mahimmanci musamman duk Wanda yasan Dd babba yasan baya wasa da tattali da Hana kowa yaji sirrin ahalinsa,

Bai yarda ko yayane wani yaji sirrin kaates ba sbd a yanda suka kafu Allah ya girkasu da sanin sirrinsu Kawai zaa iya ganin an rusa su,

A baya hakan yaso faruwa dasu Amma ya tsaya tsayin daka Allah ya taimakesa ya Hana matsalar rusa ahalin daya wahala yagina,

Ginin da har jikokin jikokinsa inshallah bazasu San meye talauci wahala da quncin Rashi na arziki ba saidai wata jarabawar ta rayuwa daga ubangiji.

Kalman Ababa ta cewa “wani qaddara ko tsautsayi tsakanin ahalinsa na kaantes da nasa” ya sakasa basa Daman sauraransa dan farajin koma menene idan ba mahaukaci bane lullube a cikin kaya Bai sani ba.

Bayan ficewan malam liman Dd babba ya Dan sake kallan Ababa daya share hawayensa hannuwansa na rawar tashin hankalin dayake tattare dashi da damuwa ya sunkuyar da Kai cikin rawan murya wani kukan na son sake zuwar masa Yace

“Ranka ya Dade ‘dan gurinku Alh Bilal kaante Yana soyayya da ‘yata bansaniba sai cikin qaddara kwatsam muka tsinta a jikinta,

Ranka ya Dade ku taimakeni kumin Rai wlh mutuwa zanyi idan ta haife wannan cikin a gida,

Bazata taba samun mijin aurena rayuwarta ta lalace,ta gurbace,ta nakasa,ta…..Jin shiru ba motsin Dd babba ba maganarsa ya Saka Ababan dagowa Ya kallesa kafin yaci gaba da bayaninsa.

Kallansa Dd babba keyi cikin wani irin yanayi na mamaki da Hana zancen kaiwa zuciyarsa bare shiga cikinta,

Yama rasa yanda zai juya zancen bare ya karba cikin Kansa Dan haka ya Dan sauke numfashi a hankali Yana Dan gyara zamansa sai alokacin ya Bude Baki cikin nutsuwa yace

“Meye sunanka?

Daga Ina kake?

Kasan Bilal kaante din Da kake magana akansa?

Ka taba ganinsa a zahiri?

Maana ka taba ganinsa tare da ‘yar taka?

Wani zufa ne ya yankowa Ababa Amma Kuma a yanda ya zo ba gudu ba ja da baya wlh sai ankarba cikin yarsa ko kowa yasan Dan kaantes yawa yarsa fyade.

Dan haka sake tattaro nutsuwa yayi cikin daidaita murya Yace

“Sunana Ababa Sulaiman,

Daga kauyen bairi iyayena suke ni anan na tashi anan nake zaune da iyali na,

Alhaji Bilal din Kuma ban taba ganinsa ba a zahiri,

Amma ita ta san shi farin sani,

Ni dai rokona A yimun adalci ya duba lamarin sbd nine a cikin cutatarwa da qunci da bacin Rai,

‘yata na asibiti yanzu haka Rai hannun Allah..

Shiru Dd babba ya sake Yi sbd zancan yafara basa mamaki da shakku Kuma,

Meye hakan yake nufi?

Ciki Bilal yaiwa wata ko me?

Sam ba halinsa bane,

Baya kula mata ma bare nemansu da fasiqanci,

Tayaya Rana tsaka haka kawai kaman almara kokuma aikin rashin hankali azo masa da zancen bama yanzu ne ake zarginsa da laifin kebewa da macen ba aa cikin ma gabaki daya aka zo da zancen har ansamu,

Wani nannauyan numfashi ya sauke zuwa lokacin zuciyarsa tafara sauyawa duk da haka dai zancen sam Bai shigesa ba bare karbuwa

Yafara saka Ababan a jerin batan hanya yayi kokuma ansamu kuskuren gurin zuwa sbd sunan Kila yazo daya da wani Bilal din ba nasu ba.

Amma baya garage Sam a rayuwarsa Dan haka komai nasa yake yinsa a tsari da lissafi Shima kaman Ababa saidai nasa lissafin daya baya wasa dashi shine akan suna da mutuncin ahalinsa, sbd yayansa uku duk Maza Babu qaramin mutum a cikinsu,har senator akwai aciki hakama jikansa daya Minister ne tayaya zai bari mutuncinsu da sunansu ya tabu daga shi har ‘yayansa qasa zasuyi Harma da sauran jikokinsa Dake dake cikin lokacin nasu sunan da mutuncin tinda sun zama Manyan mutane suma Dan haka lissafi indai akan ahalinsa ne baya batan lissafi ko garaje.

Kallan Ababa yasake ya sake sauke numfashi Mai dumi kafin Yace

“Ba damuwa naji zancenka,

Zaa warware Maka kuskuren fahimtar da aka samu akan lamarin duka,

Bilal kaante dakake Ji daban Wanda yanzu kake magana akansa daban,

Allah ya tsare gaba ya kare Yakuma shirya mana yayanmu duka,

Wannan sabanin fahimta ne kayi.

Da sauri Ababa ya Bude Baki zaiyi magana Dd babban ya dakatar dashi sbd shi ko sunan zancan baisan ana dangantawa da Bilal din dan ma dah da DD aka danganta zancen bazai iya danne bacin ransa ba ko Hana fushinsa bayyana akan wannan mutumin.

Miqewa yai tsaye a hankali cikin nutsuwa Yace Ababan ya biyosa

Suka fice masallacin zuwa cikin gidan Kaantes din.

Abinda yasa zai tafi da Ababan dan warware masa fahimtarsa da tinaninsa akan ya cire zancen sunan kaante ne kwata kwata acikin zancen basuda alaqa ko daya da maganar.

Securities na ganin Ababa bayan Dd babba suka Dan taso Dan dakatar dashi Amma Dd ya dakatar dasu Yace su barsa kawai zai gansa ne.

Ciki suka shige Kai tsaye

Gate din na farko yasa hankalin Ababan tashi suna shiga gate na biyu asalin Inda harabar gidan take makekiya komai a tsare da kyau da aji kaman ya baro qasarsa yaji,

Motocin dasuka kunce masa lissafi yake kalla idanuwansa kaman zasu fado qasa,

Take lissafinsa gabaki daya kwata kwata ya kunce wlh bazai yarda ba cikin nan ya zube,

Idanma ya zube bazai yarda ba sai anbiyasa diyyar keta haddin yarsa da dirka mata cikin farko ba aure.

Wata firgita ya sake Yi lokacinda suka Isa office din Dd babban Dake cikin gidan Dake gefe daya daga bangarensa dayake farko farko.

Sanyin Ac daya tarbesa yasaka shi Saka lissafin Ac take a budget dinsa na gaba cikin abinda zaa kasafto masa.

Italian office set din dasuka qayatar da palon yake kalla Yana sake kokarin yaqi da Hana zallan zalamansa fita ya danne Kansa da nutsuwa da kame Kai.

Gurin zama Dd babba ya nuna masa daya daga cikin kujerun alfarmar Dake jere.

Zama yai Yana sake Satan kallan wata drawer dafi komai tsayi da wani glass a office din zuciyarsa na kissima masa Kila uwayen daloli ne a ciki.

Numfashi Dd babba yasake sakewa a karo ba adadi tin farkon Jin zancen dake tafe da Ababan kafin ya miqa hannu kan wayarsa Daya bari kan stool na set din kujerun dakin dazai fita sallah take ya nemo numbern Bilal ya Saka kiransa.

Yana dauka Kai tsaye Yace ya samesa Daman yasan da dawowansa Bai nemesa bane Dan ya bari ya huta kafin su zauna maganar aikin dayayo acan tsawon watannin biyu.

Jin Bilal aka Kira yasa Ababa Jin fargabarsa ta fada Dan kuwa gwara ayita ta qare din

Dan tin farko da yasan ya dawo ai shi zai fara tinkara kafin su qaraso gurin Dd din.

Shiru sukai Babu mai magana kowannensu yayi Nisa a nasa tinanin da shakkar yanda zata kasance.

Shidai Dd babba fatansa daya kawai duk tsanani kada ma ya kasance Bilal yasan wanna mutumin bare ‘yarsan dayake magana Akai,

Zaifi farin cikin ace anzo masa da labarin sunyi asarar miliyoyin kudi masu yawan gaske akan wannan labarin ya sake kasancewa a zuriarsa,

Ya karbi jikan farko ta wannan hanyar bazai yarda ya rungumi tattaba kunnen farko ba ta wanna qaddarar sbd wani tabo da ciwo ne Mai qarfin gaske da haryanzu yake dandana ciwonsa duk da qaddarar ta banbanta da wannan.

Ya kasa karba Bilal zuciya Dari bisa Dari sbd baida shedan auren da ‘dansa ya daura boye da mahaifiyarsu Bilal din farko har aka samu cikin,

Madaurin auren ya mutu masu shedan auren sun mutu tayaya zai yarda da auren nasu?

Ya kwato mutunci da sunansa daqyar yayiwa zancen lullubi da wata irin dukiya Mai yawan gaske da har kullum yake shakkar fitarsa sbd baisan ta wace fuska mutane zasu karbi matsayin Bilal din ba jikansa na farko,A matsayin Dan gaban fatiha ko a matsayin Dan Sunna.

Wannan dalilin nasa yasa har ko yaushe DD ne asalin Wanda zuciyarsa ta karba ta riqe bari bisa Dari fiyeda duka sauran jikokinsa sbd Saida ya sake daura auren Fatima da dayyab din tukuna hankalinsa ya karbi auren nasu kafin haihuwa DD da sauran kanwarsu.

Ta Ina yanzu zai fara da wannan Shima idan ya tabbata cikin ne daga ahalinsu wannan mutumin yake magana.

Chapter 29

29

Zaman shirun yake sake girmama tinani da burikan Ababa game da lamarin komai ya sauya na lissafinsa Kuma,

A yanzu baida burin daya wuce su karba cikin kawai ya Dora sharidansa kai tsaye ba batawa juna lokaci.

Dd babba zuwa lokacin jininsa yafara kokarin Hawa Amma dayake jajirtaccen mutum ne Mai qarfin zuciya da Iko sai ya danne ya Hana Kansa karban zancen Tako Ina daga zuciyarsa har cikin Kansa.

Bilal kawai yake jira a datse zancen ya sallami mutumin tareda gargadin ko sunansu karya sake shiga cikin zancen ko gun Bada labari ne na yayi sabanin fahimtar zuwa gurinsu.

Knocking kofar da akai yasa gaban Ababa daka tsalle zuciyarsa na tsinkewa take shakku da fargaba Kuma Mai tsanani yashigesa na abinda Bilal zai fada akan cikin yanzu shine zai tabbatarda matsayin samunsa da rashinsa yanzu kam,

Dan idan Bilal Yace Bai san sumayyah ba kokuma cikin to tabbas ta tabbata daga yau yakoma Nobaba,

Idan Kuma Yace yasan da sumayyahn ko Bai san cikin ba wlh sai sun karba Dan ko ba nasa bane sai ya maqala musu kafin ya koma gida su fuskanci juna shi da sumayyahn Harma da uwarta da Benazir.

Shi kansa Dd babba sai daya sauke numfashi ahankali Mai sanyi kafin ya Bada izinin shigowar.

Kaman yanda suka tsammata Bilal dinne

Gabaki dayansu idanuwansu akansa suna kallansa a tare kowannensu da fata da abinda yake buqatan Bilal din ya tabbatar.

Shi kuwa Bilal hankalinsa akan Dd babban yake sbd baisan Ababan ba Dan Bai taba ganinsa ba sai so daya Kuma da yamma ne daga nesa Dan haka Bai qarar da kamanninsa ba dan haka Yana shigowa cikeda nutsuwa da ladabi ya qarasa ciki ya Isa gaban Dd ya zauna ya gaidasa cikin girman da nutsuwa kaman yanda ya saba.

Numfashi Dd ya sake saukewa kafin ya amsa gaisuwar cikin kulawa ya masa barka da dawowa.

Amsawa yayi Yana kokarin danne tasa damuwar da tashin hankalin dayake ciki na zancen sumayyahn sbd baisan ta inda zai bullo ba Dan yasani Babu maganar karban wannan qaddararriyar maganar a cikin dictionaryn Kaantes din Dan haka yake cikin tsaka me wuyan da baisan Ina zai Saka Kansa Harma da sumayyahn ba.

Gyara murya Dd babba yayi da kyau cikin nutsuwa kafin ya fara da cewa

“Ga bako Nan a bayanka zaune ka duba da kyau ko ka Sansa Dan bakon kusan na ke.”

Juyawa yayi cikin nutsuwa ya kalli Ababa ya gaidasa jiki a mace tareda dawo da kallansa ka Dd babba Yace

“Ban Ganesa ba gaskia sai an tinatar Dani.”

Magana Ababa zaiyi Dd babba ya daga masa hannu fuskarsa ba sauki ko sakewa ko kadan

Take kwarjininsa ya cika masa Ido gabaki daya dan haka dole yayi shiru zuciyarsa na sake tsinkewa da zancen da Bilal yafara dashi.

“BILAL” Dd ya kirasa Yana kallansa Kai tsaye da son tabbatar masa mahimmanci maganar da zaiyi masa.

“Na’am”

Shima ya amsa cikin nutsuwa da jikinsa dayake bayyanarda sanyinsa a yanzu.

“Bilal wannan bawan Allah gashi Nan yazo tin safe Yace Yana son ganina bai samu damar ba sai da magrib ya Dana fita ya sameni a masallaci da wani babban zancen daya sami yarsa,

Magana yakeyi akan ‘yarsa ta hadu da tsautsayin qaruwa ta juna biyu Kuma Wanda yakeda alhakin hakan sunansa Bilal.,

Yazo ne Nan akan Kai Bilal din yake zargi da hakan kokuma Nace yazo ne kan ‘yar tasa ta basa tabbacin ka Bilal kaante din ne yayi mata wannan cin mutuncin.

Tinda Dd yafara maganar maqoshin Ababa ke motsi kaman ya karbi zancen ya qarasa sbd ganin Dd babban yakasa fitowa ka tsaye yai maganar data Tara su din sai alokacin da yakai qarshen maganar Ababan ya saki ajiyar zuciya a boye Yana zubawa Bilal idanuwansa kirjinsa na harbawa da jiran amsar dazai Bada.

Sunkuyar da Kai Bilal yayi ahankali a karo na farko dayaji kunyar Kansa data Dd babba Harma data iyayensa da basa gurin,

idan har wannan shine Ababa mahaifin sumayyah to tabbas komai ya Riga ya bayyana gaban Dd Babu sauran tsimi Babu dabara.

“Sumayyah sunanta,nine Ababa mahaifinta”…suka Ji muryar Ababan Yana fada Shima muryasa na rawa sbd matsiwa da fargaba.

Wata sabuwar kunya da damuwa Mai qarfin gaske Ce ta lullube Bilal a gurin Dan kuwa ya tabbata dai Ababan ne yazo gurin Dd babba da zancen.

“Innalillahi wainna ilayhi rajiun”

Wannan shine iya Kalmar da ya iya furtawa cikin zuciyarsa Dake harbawa da karfi.

Jin shirun Bilal da yanayinsa daya bayyanar da tsananin kunya,Dana sani da baqin ciki ya kasa dagowa ya kallesa yasa Dd babba tsayar da kallan sa akansa Yana jiran amsarsa.

Cikin kame murya fiyeda farko wannan Karan dan sirkin zafi kadan a sautin Yace

“Kayi magana a sallamesa ba zancen batawa Kai lokaci tinani bane,

Idan baka sansuba ba buqatan tsayawa nazari ko wani tinanin

ka fada Kai tsaye a sallamesa.”

A karo na biyu ya sake Jin hawaye game da kaddara sun ciko idanuwansa duk da kasancewarsa babba bame qananun shekaru ba Amma Kuma tinda komai ya zo a qaddarawan ubangiji baida kaucewa bayan fadan gaskiar.

Ba iya dago Kansa ba yakalli Dd babba ya Bude bakinsa cikin Rauni Yace

“Na Santa,Kuma qaddara Ce ta gifta Banda niyar cutatarwa ko keta mutuncinta,

Da niyar zan aureta na bibiyeta tin farko,Ina matiqar Dana sani da Bada hakuri ga wannan qaddarar data shigo.

A jejjere Ababa ya ringa jero ajiyar zuciya a boye Yana hamdala kala kala ga ubangiji Yana Jin wani farin ciki da sanyi na mamaye ransa.

Bai taba sakawa sumayyahn albarka ba sai yau din yaji zuciyarsa na Saka mata albarka da Bata fada masa karya ba,

Tinda dai Bilal ya tabbatarda ciki nasa ne ai komai ba zai zo da sauki.

Dd babba kuwa shiru yai Bai iya cewa komaiba

Suma duk sukai tsit gurin ya dauke sauti ko motsi Babu.

Minti kusan hudu a hakan kafin Dd ya motsa ahankali ya dauki wayarsa ya Saka kiran Abbakar yaransa tin na shekaru har yanzu.

Abbakar din na dagawa Dd Yace yazo yanzun nan.

Ajiye wayar yai Yana kokarin Hana Kansa bayyanarda attack din daya riskesa take a gurin Saidai daga muryarsa Bilal yagane ya samu attack take ya miqe da sauri yai Kansa Yana Kiran sunansa cikin kulawa

kafin wani yunqurin tini numfashin Dd din ya fara kokarin daukewa saiga Abbakar Yana ganin hakan hankali tashe yayo Kansa Shima.

Ababa ma hankalinsa tashi yayi ya miqe tsaye Yana fatan kada komai ya samu Dd babban a samu matsala Dan haka dashi aka hau yi masa firfita Bilal kuwa likita ya fara kokarin Kira hankalinsa a matiqar tashe.

Cikin mitinan da Basu wuce qalilan ba tsohon yake Neman rasa ransa Dan haka kasa jira sukai take Akai kaante specialist dashi.

Ababa kuwa silalewa yayi dole ya tafi gida bayan an dakatar da kowa shiga Inda Dd babban yake.

Kai tsaye gida ya wuce Baima samu biyawa asibitin ba Dan jikinsa koina ciwo yake Shima yau din yaci wuya Amma tinda dai buqata kusan ta samu shiga komai yazo da sauki.

Anne data kusan haukacewa a kwana daya da wuni biyu sbd rashin ganinsu benazir da rashin sanin wane Hali sike ciki yasa gabaki daya Bata hayyacinta gashi Ababan yaqi fada mata komai bare taji dan sanyi aranta.

Dan haka ma da Daren yana shigowa ya shigewarsa ko abinci Bai samu damar ci ba ya kwanta sbd gobe sammako zaiyi zuwa asibiti da Kansa zaiyi jinyar sumayyahn shi da Benazir.

******A asibiti kuwa sumayyah da Benazir sun Dan samu sassaucin zuciya Dana jiki tinda basa aikin komai sai zama da bacci,

Tinanin Anne ne kawai yake tsananin damun benazir ita datasan halin data barota

Amma koma yayane tinda bataji Ababa Yace ta mutu ba to tasan tasamu tsira kenan.

Sunyi ta zuba idon dawowan Ababa Basu gansa ba har suka kwanta dan haka suka fara addua da fatan Allah yasa lfy ba wata masifar Ce acan gida annensu take Sha ba.

Jinin da aka Saka mata ishashe da magani masu kyau da lafiyayyan abinci wadatacce Harma da gurin kwanciyar me kyau yasa jikin sumayyah samun sauki Sosai tanata samun bacci.

Benazir kuwa ganin samun saukin sumayyah yasata Jin samun saukin zuciya itama dan haka suka dasa jiran tsammanin mekuma zai faru gaba.

Qarfe Tara na safe Ababa ya shigo dakin nasu da aka sauya musu wata nurse ta rakosa tana fada masa Wanda ya Saka a sauya musu dakin sbd Bai saniba shi bayanan.

Dakin yaqarewa kallo Yana mamaki da lissafin kudin da Bilal din ya kashe musu daga jiya zuwa yau din.

Baqin ciki da takaici ne yazo masa wuya ya tsaya wato dai ta tabbata yaran na sun jima suna cin arzikin Bilal baida labari.

Benazir data miqe daga zaunen datake ta gaishesa kanta qasa ya jefawa wani irin kallo zuciyarsa na tafasa ya jefeta da ledan ruwan tea da bread din daya siyo musu Dan karyawa.

Tanaji ruwan zafin ya Sauka qafarta Allah yasa ledan Bai fashe mata a kafa ba dan haka ta durkusa ta dauke ledan tana sunkuyar da Kai.

Sumayyah na ganin hakan ta rakube kan gadon tana jiran nata jifan,

Zaiyi magana aka bubbuga kofar dakin aka shigo.

Sulaiman ne tareda maaikancin babban hotel din kaante bangaren restaurant dauke suke da Manyan ledojin abinci Harma da cikin basket ankawo musu abinci masu Rai da lafiya tareda inganci.

Kallansu Ababa keyi suna ajiye kayan suna gaidasa kai tsaye Yace

“Daga Ina?”

Cikin girmamawa Mai tsanani duka su biyun suka Ce masa daga hotel din kaantes ne Sir Bilal yabada umarnin kawo abincin safe Rana yamma da dare kullum tin jiya.

Kallan kayan da aka jere din yai Yana Juya zancen cikin ransa kafin ya dawo  da kallansa kansu sulaiman din ya Dan saki fuska Yace

“Auyo eh lallai hakane

An kyauta to ngd sosai”.

Sallama sukai masa cikin girmamawa kaman shine Bilal din Wanda hakan yasa Ababa Jin Kansa na qara daukan zafi.

Suna ficewa ya zauna hankali kwance kan kujera yasa Benazir ta Bude kayan yaga abubuwan da suka ake tabbatar masa fa daga yanxu duniyarsa ta Riga ta sauya zuwa wani matsayin dan kuwa ta Bude sabon babin rayuwa cikin masu daloli irin wainda yake buri da muradi.

Daman Bai tsaya ya karyo ba Dan haka Kai tsaye yasa akai masa wani hadadden combination na abincin da aka kawo ya fara ci zuciyarsa fes hankalinsa na kwanciya.

Kuma Yana gamawa zai nufi asibiti duba Dd babba Dan karma ya manta da waye sila kokuma meye silansa kwanciya asibitin.

Saida yaci ya koshi da abinda bazai iya Saka kudinsa ya siya yaci ba Dan ganin kaman yayi Riya Amma daga yanxu yasan komai ya canja.

Sauran yabar musu ya miqe ya fice bayan ya tabbatarda koma baya damun sumayyahn yanzu Tinda ance ansaka mata jinin Bilal.

Yana fita benazir ta zubawa sumayyah abincin sukaci tare Suma suka bar sauran kafin ta tattara gurin Mai gyara dakin ta sake shigowa a karo na biyu Dan gyarawa.

Chapter 30

30

Ababa na fitowa daga Asibitin Kai tsaye Asibitin su alh Bilal din ya nufa Yana addua da fatan dd babba ya samu sauki ya Dan dawo Kansa.

Yanda ya dauka Asibitin ba Hakan ya sameta ba sbd tin a gate ake Hana shiga saika Fadi Abinda kazo Yi,

Idan Kai patient ne bangaren da zaa nuna Maka kabi daban,

Idan dubiya kazo Kuma in ba time na dubiyan bane baa barinka shiga sai time na dubiyan yayi.

Ma’aikatan Asibitin ne kawai ake budewa Kai tsaye su shige harma da barka da zuwa sbd Asibitin kusan duka manya da masu abin duniya ne sukeda files da kati a cikinta.

Dan haka tin a gate Bai samu shiga ba bare qarasawa gurin dubiyar dd babba.

Guri ya nema Yana kokarin zaunawa zaman Jira securities na Asibitin suka hanasa Dan haka baida zabi dole sai komawa gida yasha baccin Rana kafin da yamma ya sake shiryawa ya fito ya nufi Asibitin Dan yasan ankai abincin Rana daga hotel din kaantes shiyasa Bai tsaya yaci abincin gida ba ya fice.

Kaman yanda suka San halinsa da Abinda zai iya biyowa baya idan suka taba duk Abinda zaa kawo batareda izininsa ba tinda yanzu yasan komai yasa tinda aka kawo Basu taba ba Yana Nan aje sai Ababan yazo yabasu Wanda zasu ci.

Yana zuwa kuwa abincin yafara sakawa benazir ta zuba masa yaci ya koshi kafin ya bar musu sauran Suma suka ci anan yace su Basa numbern Alh Bilal ta waya tinda yasan bazasu riqeta Akai ba tinda sun Dade da zama tsofin munafukai akansa.

Shiru sukai suna shakkar fada masa Basu da ita,

Benazir data shirya daukan marinsa ta Bude baki ahankali tana Dan sauke Kai qasa tace

“Bamu San numbernsa ba,bamu taba karba ba.”

Kaman yanda suka sani su dukan harbeta yayi da qafa Saida tayi baya Amma Bata Fadi ba

Cikin takaici yace

“Kwadayi kawai Kuka iya ya Baku kayan Dadi kuci ku shiga motarsa

Gashinan kun kwasa mana kayan wahala ko?”

Shiru sukai cikeda kunya da radadin kalmominsa babu Mai iya ko dagowa.

Yana cikin fadan aka buga dakin aka shigo ga mamakinsu su duka Alh Bilal dinne gabaki days sauya a cikin dare Daya damuwa Mai tsanani da rashin sanin mafita yasa idanuwansa har Wani zurfi sukai sbd kaman komai ya lalace masa ne.

Ababa na ganinsa ya miqe tsaye Yana masa barka da zuwa fuska a Dan sake kafin daga baya yakoma kalan jimami Yana tambayar ya jikin dd babba.

A hankali ya amsa masa tareda tambayan ya jikin sumayyah.

Kai tsaye Ababa ya amsa da tanajin sauki itama.

Sumayyahn Bilal ya kalla ta kasa dagowa ta kallesa daga ita har benazir sbd Ababa dake gurin.

Shi Kansa bazaiso su dago su kallesa ba a wannan yanayin Dayake ciki na rashin kwanciyar hankali ko Daya da tsananin damuwa.

Shiru dakin ya dauka har Ababa Mai son yin magana kasawa yayi yai shiru sbd sosai da gaske Bilal din yake cikin mawuyacin hali a bayyane.

Ajiyar zuciya Bilal ya sake bayan tsawon lokaci da shirun ya ratsa dakin zaiyi magana Ababa ya katsesa da kora benazir waje Shima ya fice Dan bawa Bilal din Daman magana da sumayyah

Suna ficewa sumayyah ta dago ahankali ta kallesa da idanuwanta dake cikowa da hawaye a duk lokacin da zata gansa sbd batasan meye matsayarta ba,

Ina rayuwar zata kaita da wannan cikin na jikinta,

Yaya alumma zasu karbeta da Abinda zata Haifa,

A wane matsayi Abinda zata Haifa yake da mahaifinsa.

Kallan datake masa idonta na cikowa da hawaye Shima shi yake mata idanuwansa na cikowa da hawaye sbd  Wani radadi ne shi da Abinda zaa Haifa masa zasu kasance aciki Mai kaifi,

Dd babba bai taba karbansa kaman yanda ya karbi sauran jikokinsa,

Bai taba kaunarsa kaman yanda yake kaunar DD,

Baa taba basa matsayi da mahimmancin da aka bawa DD ba tin suna Yara har suka girma matsayin DD daban yake dashi,

Duk Wani aikin wahala da rashin Hutu shine ake damqawa ahakan baa taba nuna godia ko Yabawar da zata saka yajisa Dan asalin kaantes ne Shima,

Ya taso da girmamman tabon rashin soyayyar gaskia ta asalin Dan gadon iyayensa a cikin kaantes,

DD shine hasken idanuwan dd babba,

Shine abin alfaharinsa,

Shine Wanda dd babba kadai kejinsa cikin tsakiyar zuciyarsa fiyeda ma yayansa duk da kasancewarsa jika,

Tin suna qanana banbancin da ake nunawa tsakaninsa da DD a bayyane yake Wanda Hakan Bai taba damunsa ba sbd irin kaunar da DD ke masa tana rufe gurbin da ake bar masa a zuci na nuna masa shi din ‘dan gaban fatiha ne bayan iyayensa nada tabbacin da aure suka haifesa.

A duniyarsa kaf tin tasowarsa mahaifiyarsa ce kawai sai DD suke masa Wani irin son Dayake basa qwarin gwiwan ci gaba da rayuwar cikin jarumta da karfin halin da a bayyane kawai yake dashi Amma a zahirin zuciyarsa shi din me tsananin rauni ne Wanda yake saka sa Jin duniyar na isarsa lokuta da dama,

Tin Yana qaraminsa ya taso cikin mawuyacin halin samun tinanin daidai na yanayin da aka sakasa,

Har girmansa Yana cikin wannan yanayin shiyasa tin daga ranar Daya fara kaunar sumayyah ya fahimci kusan ciwo Daya ke damunsu,

Nata ya shiga kwakwalwanta sabanin nasa da Bai shiga ba Amma dai ya sakasa cikin rauni sosai na zuciya.

A yanzu da wannan abin ya faru yasani ya qarasa ficewa ne a ran dd babba hakama zai saka mahaifiyarsa damuwa da kunqi DD kuwa zaiyita samun sabanine da mahaifinsu harma da dd babba sbd bazai taba yarda a tozartasa ba ko kuntata masa akan Abinda yayi.

Gangarowan hawayensa kan kyakkawan fuskarsa yasa sumayyah Kai hannunta hawayen ya sauka hannunta tana Jin zuciyanta narkewa

Take nata hawayen suka gangaro ahankali itama batareda ta iya cewa komaiba sbd basai yayi magana ba daga ita har shi tasan kowa na cikin mawuyacin halin da basusan meye makomarsu da Abinda zasu haifan ba.

Hawayensa Daya kasa riqewa ne suka koma Kuka ahankali mara sauti sai dai radadin zuci da jikinsa Daya gama sanyi da mutuwa.

Itama kasa tiqe nata Kukan tayi ta sunkuyar da Kai tana tsiyayo hawaye masu zafi.

Ahakan suka share lokaci Mai Dan tsayi babu Mai magana sai Kukan dasuka sha kafin ya Ciro handkerchief ya share hawayensa ya goge fuskarsa ya Ciro glass dinsa ya saka kafin ya share mata nata hawayen ya Kalli cikin idanuwanta ya Bata tabbacin inshallah komai zai tafi daidai,

Duk tsanani bazai taba rabuwa da itaba zai Samar musu rayuwar kwanciyar hankali Koda babu kowa acikinta.

Tambayanta yayi babu matsalan Dayake damunta ko babyn

Ta gyada masa Kai tana kallansa kaman Wainda ke bankwana sbd kukansa ba qaramin Bata tabbacin suna cikin tsaka Mai wuya yayiba.

Juyawa yayi ya fice a dakin bayan ya ajiye mata wayarsa Daya da layinsa da komai aciki.

Yana fitowa Ababa dake tareda benazir a zaune miqewa sukai tare tsaye Yana cewa harya fito.

Kasa kallon Ababan yayi sai kawai yace benazir tazo suje yabada Sako Koda zaa nemi Wani abin baya kusa.

Kasa motsawa tayi sbd Bata ma fahimci me yake nufi ba dan haka Ababa ya kalleta yace

“Kije ki karbo Sako akace”.

Bayan Bilal din tabi babu Mai magana a cikin su

Suna Isa ya Bude motar ya shiga ya Ciro rafar 1k guda biyu ya miqa mata yace yabar waya a hannun sumayyah duk Abinda ake buqata benazir din ta kirasa.

Yana barin Asibitin ta juyo ta dawo ciki,

Tana shigowa dakin a tsaye ta tadda Ababa Yana jiranta.

Kudin ta Ciro Kai tsaye daga cikin hijabinta ta miqa masa.

Karba yayi yana sakawa aljihu sbd yasani Kai tsaye dubi Dari biyu ne.

Wayar da Bilal din ya bari ya kalla yana kokarin Hana zuciyarsa fasa wayar sbd shi Sam bazai dauki wannan wayar dayakeson su rinqa Yi ba Amma zai Basu kwana biyu daga Nan zai dakatar sai yasan matsayarsa da cikin jikin ‘yarsa tukuna Dan shi a mutu a dawo so yake tabbas tinda Akai mata cikin sai sun aureta,

Sai sun shiga cikin ahalin kaantes Suma da yardar Allah.

Barin Asibitin yayi Bai sake dawowa sai dare ya sanmusu abincin Daren da aka kawo sauran yayi gida dashi acan yaci ya koshi har hande ta samu taci ciki itama Anne Kam saidai ta wanke kayan da akaci abincin dashi.

Washe gari Koda Ababa ya iso Asibitin an sallamesu Dan haka Yana zuwa kwasowa sukai suka dawo gida.

Anne gurin rawar jikin farin jikin ganin ‘yayanta har faduwa tayi taji ciwo a Dan yatsar qafa Amma Bata damuba,

A rayuwarta Bata taba farin cikin ranar ba sbd sai yanzu ne ta sake tabbatarda bazata iya rayuwar babu su ba Dan haka suna shiga dakinsu ta fasa Kuka ahankali da batasan ko na menene ba Amma dai tasan ganinsu ya dawo mata da rayuwarta ne.

Su kansu jikinsu mutuwa yayi ganin yanda tayi wata mummunan rama kaman wadda ko ruwa Bata taba sha ba tinda suka tafi.

Rungumeta benazir tayi tana sauke numfashi ahankali sbd ita yanzu haka kawai taji batajin Dadin komai,

Yanda zasu Rena babyn kawai take tinani

Idan Kuma su Bilal suka karbe babynsu Yaya sumayyah zata rayuwar batareda ciwonta ya dawo ba,

Nakudar haihuwar kawai tayar mata da hankali takeyi sbd radadin ciwon kawai zai tayar da ciwon sumayyahn.

Dan haka benazir ta shiga Wani tinani daya sanyaya jikinta tinda ta lura Ababa yanzu akan cikin babu Abinda bazai iyaba tasan sumayyah data Rai ko lafiya baida baqin cikin ko Daya.

*******Ahalin kaantes gabaki Daya hankalinsu ya tashi da Jin ciwon dd babba katsam Kuma wai attack ya samu,

Take duk na kusa Dana nesa suka hallaro a cikin kwana biyu Kuma har lokacin Yana Jin jiki sosai gashi an rasa meya samesa sbd Bilal ya kasa fada Dan haka yafi kowa shiga damuwa Daya San shine sanadin

Fatansa dai kada Wani mummunan abin ya faru ya zama Sila.

Lokacin da labari ya Isa ga DD kaante Kai tsaye yasan ba qaramin abu bane ya bawa dd babba attack sbd jajirtaccen tsoho ne Mai tsananin karfin zuciyar Dan haka koma menene yasan babba ne.

Take ya saka su ummensa fara Shirin tafiya zasu taho a cikin satin Suma sbd zuwansa kawai zaisa dd babban Jin sanyi ya sani Shima.

Chapter 31

31

Dd babba tinda ya dawo hayyacinsa numfashinsa da bugun zuciyarsa Daya dawo daidai ya farka Bai ko Kalli gefen da Bilal yake ba sbd Sam ko ganinsa baya son Yi Dan ciwonsa zai iya dawowa harma fiyeda na farkon,

Duka yayansa da daidaikun jikokinsa da suka samu zuwa babu Wanda baiyi kokarin son sanin meya kawowa dd din samun attack a take bayan kowa yasan lafiya yake,

Hakama dad kaante da ko a yammacin ranar sunyi waya lafiya kalau baisani ba Kuma baiji alamar damuwa ko Wani ciwon a yanayin dd babban a lokacin ba.

Dan haka suketa shiga damuwa da mamakin Abinda ya samesa Amma Sam yamaqi yarda ya bayyanarda ko kafa Daya dazata bayyanarda akwai Wani abin ya sanar dasu zuwan kaddara ne kawai Allah ya Aiko masa da attack din.

Dole kowa ya bar zancen aka Maida hankali gurin kulawa dashi sosai.

Bilal Daya fahimci ko kallansa dd bayayi sai jikinsa ya sake mutuwa yayi sanyi ya sake shiga damuwa da mutuwar jikin yanda zancen zai bayyana ga sauran familyn.

Kwana biyi dd yayi a Asibitin ya sa aka sallamosa suka dawo gida a qarasa jinyar a can duk da zuciyarsa ba saukin zata samu sbd shi kadaine yasan tsananin zafi,bacin Rai,baqin ciki da damuwan Dayake ciki akan babu Wanda yasani daga shi sai Bilal sai Allahn su.

Bayan dawowa da jinyar dd babban gida sosai kaantes ke karban baquncin manyan mutane masu riqe da qasar dake zuwa duba dd daban daban,

Dan haka har lokacin dd Baiyi lokacin Bilal ba.

Babu Wanda ya fahimci Wani Abu ko rashin kulawan da dd babba kewa Bilal sbd anriga an Saba da sanin babu wata shaquwa Mai zurfi Ra girma tsakaninsu Dan haka babu Wanda ya ankara da rashin kulasan da dd babba kewa Bilal din.

Damuwa tasako Bilal din gaba sbd babu inda a yanzu yakejin saukin rayuwar,

Komai ya lalace masa ya tsaya masa cak,

Mahaifiyarsa da DD ne farin ciki da sanyin idanuwansa sai ‘yar qanwarsu

Gashi duk Basa tare dashi.

Sumayyah Kuma Ababa ya hanasa zuwa ganinta yace sai dd babba yaji sauki asan matsayar magana.

Ababa ya Hana Bilal din zuwa ne sbd rashin zuwansa yasa yake aikowa Ababan kudi kaman Bai San zafinsu ba Dan kada sumayyah dasu benazir su nema komai su rasa na kulawa da baby da lafiyan sumayyahn.

A bangarensu benazir kuwa a yanzu da babu zabin Daya wuce musu karban ciki su hau renansa su Haifa komai menene yazo duniyar yasa suka Maida hankali gurin kulawa da sumayyah sosai.

A dayan bangaren Kuma a rayuwar da suka Saba suka taso cikinta babu Abinda ya sauya musu.

Wahalarsu,bautarsu,qunci da damuwansu babu Abinda ya ragu ko aka dauke musu.

Aikin a yanzu ma yafi na ko yaushe ga benazir sbd wankin shagunansa duka itace take yi hakama ayyukan gida da kulawa da dabbobi

Ga karatinta Dayake baya sbd rashin lokaci da wahalarta data qaru Dan haka duk ta forgice tafara ficewa hayyacinta itama ta rame Takoma kaman itace me cikin.

Anne ma ciwon tsufa ne yake Neman kamata ya rufeta sbd ayyukan sun mata yawa da nauyi itama Dana haka daga ita har benazir babu Mai hutun zuciya dana gangar jiki.

Sumayyah data ga wahala na Neman illatasu qarfinsu ya fara gazawa dole itama ta sakawa kanta qarfi da jarumta ta koma kan aikin itama kaman yanda suka Saba a baya.

******Dd babba tini ya warke ya sake saidai ciwon dake cin zuciyarsa Bai warke ba ko kadan

Tin ranar da abin yafaru baya iya bacci kowane dare tinanin yanda zai kashe zancen yayi Rami ya birne ya rufe yake,

Fushinsa da Bilal Yana qaruwa ne a duk lokacinda ya Tina cikin Yana girma ne yana sake kusantar lokacin haihuwa.

Danne zuciyarsa dd babba yayi ya sake Neman Ababa wannan Karan da Kansa ya gayyatosa Dan suyi magana.

Da qarfe 7 na bayan magrib ya iso Dayake Abbakar ya San da izinin da dd babba ya bayar na ganin Ababa yasa yana babban gate din farkon har Ababa ya iso da Kansa yayi masa barka da zuwa yayi masa iso.

Wannan Karan ma Ababa gidan sake shiga ransa da qwaqwalwansa yake Amma Dayake yafara hangowa Kansa dahir na zamowa Shima Dan haka ya Maida hankali kan dd babba da zai Gani.

Har cikin palon baqin dd babba Abbakar ya rako Ababa ya nuna masa gurin zama ya juya ya fice Dan tsare kofa sbd duk tsananin babu Wanda zaiji me dd babba zai tattauna da Ababan ko ganinsa dd babba yace kada ko Daya a ahalin suyi,

Magana ce zaiyi dashi sukai karshe a rufeta batareda kowa yaji ko yasan komaiba Koda tsautsayi.

Numfashi Mai sanyi da nutsuwa dd babba yayi kafin ya amsa gaisuwar da Ababan ke masa tareda ya karfin jiki.

Bayan ya amsa dagowa yayi ya Kalli Ababa da nutsuwa tareda son nufar maganarsa Kai tsaye,

A natse yafara da cewa

“Malam Ababa daga Kai har mu bama buqatan maimaita zancen baya mara Dadi da bacin zuciya Dan haka Ina Mai baka hakuri da Abinda ya samu yarka,

Allah ya tsare gaba ya yafe musu damu gabaki Daya,

Maganar ciki Dayake jikinta Kuma aikin kaddara ne data Riga fata Dan haka dai Ina sake baka hakuri.

Shigowar Bilal ne Daya saka Abbakar kira masa yasan ya shi dagowa a Karan farko yayi masa Wani Kallo ya Basa izinin zaunawa Shima.

Cikin sanyi da girmamawa Bilal ya gaida Ababa da tini ya fara Jin Kansa Wani ya amsa cikin yar kamewa.

Kallansu su biyun dd babba yayi kafin ya sake Dan yin shiru zuciyarsa cikeda nazari da Abinda ya Yanke akan lamarin Dan haka ya kallesu Kai tsaye ya sake fara da tambayar watannin cikin zuciyarsa na daci.

Ababa ne ya amsa Shima Kai tsaye da fiddo takardar scanning din dake aljihunsa ta cikin ya miqawa dd babban.

Kallan takardar yayi batareda ya amsa ba mamakin Ababa na fara shiga ransa sbd zuwa yanzu babu Wani ciwo ko baqin cikin lamarin a tattare da uban da ‘yarsa ke dauke da cikin da bana aure ba.

Bai karbi takardar ba ya buqaci sanin watannin cikin kawai.

Bilal ne ya amsa masa Kai tsaye cikin sanyin jiki sbd sanin dd din baya son tambayar da yayi Maka dabam amsar da zaka Basa daban.

“Wata shida cikin yanzu Inshallah”

Shiru palon ya sake dauka Dan kuwa dai ta tabbata cikin haihuwarsa zaayi.

Ababa dd ya kalla yace

“A yanzu tinda qaddara ce ta shigo babu Abinda zamu iya Yi face zamu Bada muhalli,kudi da rayuwa me kyau da uwar da Abinda zata haifa inshallah bazamu gasa ba har lokacin da uwar zata samu miji tayi aurenta Amma bazamu karbi Abinda zaa haifa ba,

Komai ake buqata har Wanda baa buqatan ma zaa Baku.

Maganar dangantakar ciki da kaantes kuwa Sam babu maganar,

Ba’a ma yita ba,Bata taba yinta ba zancen anrufesa anan karya taba fita har abada…

Daga Ababa har Bilal cikin rashin hankali da firgici suke kallan dd babban sbd babu Wanda ya taba tinanin zaice a rufe maganar ‘dan mutum har abada kar a sake tayarwa hakama shi Bilal tayaya ake tinanin yayi rayuwa ya binne zancen har abada bayan Yana sane da Yana ‘da ko ‘ya?

Tayaya ma zai iya rayuwa ba sumayyahn da Abinda take dauke dashi nasa?

Ababa Wani zazzafan zufa ne ya yanko masa ya Bude baki cikin maqoqon baqin ciki zaiyi magana dd babba ya katsesa da cewa

“Miliyan nawa?”

“In nairas ko in dollars?

“Cash ko wiring?

Rikicewa Ababa yayi Wani zufan na keto masa Tako ina

Take bayanin yake Neman qwace masa Jin bayanin ddn.

Hankali tashe Bilal yake kallan Ababa Yana jiran bayanin amsar da Ababa zai Bada Dan kuwa idan har shi din Uba ne bazai zabi kudin banza akan farin ciki da kare martabar yarsa ba harma da rayuwarta ta gaba sbd Yana karban kudin ya yarda da har abada bazai alaqanta cikin ko babyn da sunan kaantes ba.

Nazari Ababa ya shiga zuciyarsa na tsalle tana rikicewa,

Saidai Kuma duk son kudinsa a lissafe yake Shima,

A yanda yasani Kuma a yanda Alh dd babba da Kansa ya Basa zabin nawa yakeso da Kansa ya tabbatarda ko miliyan nawa ya fada Basa zaayi,

To Amma idan ya karbi miliyoyan kudin qarewa zasuyi komai daran dadewa sabanin idan ya tsaya tsayin Dakan da ‘yarsa da jininsu ta shiga ahalin to famfon arzikin samun kudinsa bamai yankewa bane har sai inda arzkin kaantes ya tsaya.

Dan haka take ya fizgo hankalinsa ya dawo hayyacinsa daidai ya Hana Kansa zaban kudin dayasan ko agurin Bilal zai ringa yagarsu gwara dai ya shiga kaantes tsundum ayi dashi Shima.

Dagowa yayi ya Kalli dd babba dake kallansa tini Yana sake nazartarsa take ya gano akwai kwadayin arziki a tattare da Ababan Amma bari ya tabbatarda halinsa ta hanyar zabinsa tukuna.

Zufa Ababa ya share da handkerchief dinsa sbd a rayuwa bai taba shiga tsaka me wuyar zabi ba irin wannan ranar,

Dollars fa akace zaa sallamesa dasu

Amma Kuma akace idan zaka Sha giya ka Sha ta dubu,

Gwara ya shigo daga ciki saiyafi samun manyan dololin akan wainda zaa qirga yanzu a Basa.

Numfashi ya sake ya Kalli dd babba yace

“Ranka ya Dade kudi bazasu Hana bayyabar zancan Nan ba har abada sbd mutum zaa haifa Kuma dole wataran sai Anso sani kokuma sanin ma waye asalin Ubansa duk da kasancewarsa Dan kaddara”.

Me zai Hana idan adalci zaa mun Nima Amin yadda akaiwa iyayen mahaifiyar shi Alh Bilal din………..

Cikin Wani mummunan tashin hankali da bugawar zuciya Bilal da dd Daya kasa gasgata Abinda kunnuwansa suka ji masa suke kallansa cikeda mamakin Da hankalinsu duka ya kasa dauka.

Ababa kuwa ganin ya buga daidai kan ga’ba yasa ya sake Jin karfin zuciya dana hali Dan kuwa gwara suyi su gama a rufe babin su fada babin gaba.

Ganin duk sun dauke wuta yasashi sake Dan gyara zama yaci gaba da cewa

“Ayi hakuri ranka ya Dade Nima a bani adalcin daya kamaci ‘yata da ni Nima,wlh Banda inda zan saka kaina idan aka barmu da wannan Abinda zaa haifa din.

Ni kaina bazanzo a sani ko aji haihuwar kaddarar da zaayi a cikin gidana ba Amma idan aka haihun babu Wani lullubi da zaayiwa zancen dazai hanasa fita har abada,

Kaddara ce hakuri zamuyi mu dauka a rufawa juna asiri kaman yanda babu Wanda yasan waye Alh Bilal haka Nima idan aka rufa aka karba ‘yata har abada wlh nayi alqawarin babu Mai ji.

Yana Kaiwa karshen zancen ya sauke nannauyan boyayyan numfashin karfin zuciyar Daya maqalawa Kansa ya iya furta kalaman a gaban dd babba sbd yasan ba qaramin ganganci Mai hade da ban mamaki yayi ba saidai wannan sarar kawai zai aikawa dd babba a karbi yarsa ba wahala.

Chapter 32

32

Tsit palon ya dauka kusan kowanne tsakanin dd babba da Bilal sun dauke wuta da mamaki tareda firgicin zancen da Ababan ya zaro,

Bilal Kansa ya sauke cikin baqin ciki da damuwa Mai tsananin gaske tareda sanyin jiki sbd tin zuwansa duniya ko dd babba Bai taba fitowa Kai tsaye ya tinatar dashi ko shi din wayeba,

Iyayensa da suka haifesa dinma daga ranar da aka daura musu aure ko a tsakaninsu Basu sake tayar da zancen ba sbd umarni da qaqqafar rantsuwar da dd babba yayi Akai Amma ayau Rana tsaka Kai tsaye a gaban idon dd babban ga Wani Yana fadan maganar Kai tsaye batareda mutunta shi Bilal din ba.

Dd babba kuwa shiru yayi batareda iya cewa komaiba tsawon mintina kafin ya dago ya sakewa Ababa kallan tsaf na mintina,

Ayau Rana ta farko da Wani yake zaune gabansa ya fada maganar da zata iya sakawa yasa a batar dashi da labarinsa,

Ko a cikin familyn kaantes ba kowa ne ba yasan asalin Tayaya aka haifi Bilal din ba bayan shi da Kansa sai Mahaifin Bilal da mahaifiyarsa sai Dawood da Kuma kanin dadynsu Bilal din da matarsa.,

Bayan wainnan babu Wanda ya sani a  familyn sai dangin mahaifiyar Bilal Suma kawunta da matarsa ne kawai suka sani Kuma kawun ya rasu matarsa da yayanta Kuma sun koma asalin garinsu sunbar Nan din gabaki Daya Wanda dd babba da Kansa ya Bata Abinda zatayi nesa dasu kada ta dawo har abada saidai Fatima takai musu ziyara sbd kawai kada ma zancen ya iya fita wataran ta hanyar matar kawun.

Tabbas Ababa yazo da zance Mai girma,

Idan ya fahimci zancensa da yanayin yanda ya isar da zancen cikeda sakon nufin

“Ko a karba yarsa da cikin itama ko ya fallasa zancen cikinta Dana uban cikinta.”

Kan Bilal ya Maida kallansa sbd a yanzu kam ya sake tabbatarda illar zamtowar Bilal cikin ahalin kaantes.

Basai dd ya fada ba Bilal da Kansa yasan wannan tinanin ne acikin zuciyar dd babba yanzu akansa Daman Kuma tin ba yanzu ba yasan da Hakan.

A Karo na farko bayan zancen dd babba ya Bude baki yacewa Ababa

“Yama kace sunanka na gaskia malam Ababa?

“Abubakar nake” Ababa ya fada Kai tsaye.

“Malam abubakar a ringa kulawa sosai da aibin harshe,

Maganar ‘yar ka Kuma kaje kawai zan sake nemanka.

Magana Ababa zaiyi ddn ya kira Abbakar Sam ko kalma Daya baa bari ya furta ba aka fice da dashi Yana waiwaye sbd Bai fahimci me Hakan ke nufi ba.

Ana fitowa dashi Abbakar ya sallamesa har gate din waje ya koma.

Gida ya nufa Yana shiga nazari saidai Kuma bazaiyi qasa a gwiwa ba zai tsaya tsayin Daka a maganarsa kokuma a mutu har liman.

Bilal kaante ranar yau na cikin ranakun dasuka wuce masa a baya na radadin zuciya sbd maganar Ababa ta sosa masa tabon Daya jima cikin rayuwarsa Yana dannewa,

Bayan tafiyar Ababa shi Kansa ya sosa masa maganar data sakasa rufe Kansa a part dinsa ya zubar da hawayen da suka dawo masa da ciwo da radadin zuciyar Daya jima da dannewa.

Haka damuwarsa tin ta yarinta Mikn ya dawo masa sabo fil baida Mai zaunawa kusa dashi ya sanyaya masa kaman baya da mahaifiyarsa da DD ke zaunawa gefensa su rungumesa.

Kaf ahalin gidan babu Wanda ya asan meyake faruwa sbd gargadin dd babba na kada ya sake kowa yasan da zancen.

Dad dinsa baisan Abinda yake faruwaba tsakanin dd babban da Bilal sbd ko a fuska baka Isa ka Gane akwai Wani abin ba a qasa.

A tinani da hukuncin dd babba so yke ya dakile zancen ya rufe batareda kowa ma ya san da wannan qaddarar ba Amma Kuma da alama Ababa bazai lanqwasu da sauki ba.

Ta bangare Daya Abbakar ya saka yayi masa bincike Mai zurfi akan Ababan da duka huldodinsa.

Karan farko ana gama sanar dashi waye Ababan ya fahimci Yana Hana Ababan Abinda yakeso zai Bata musu sunan Daya debo shekaru masu tsayin  gaske Yana ginawa.

Yanada plans me kyau akan rayuwar jikokinsa Dan haka bayajin zai iya hada iri ko zuria da Ababa sbd a halayensa babu na gari to Amma idan har karban yarsa shine maslahar Hana fidda sirrin A kaantes suna yayan gaban fatiha zai sake dubawa ya Gani.

Sake kiran Ababa yayi wannan Karan dukiyar da yayi masa alqawarin Basa harta fita lissafi Amma Sam Ababan ya tsaya akan sai Bilal ya auri yarsa tinda idan an barsu da ‘yar baisan yanda zaiyi da ita ba.

Wannan Karan ran dd babban ya tsananta Baci Dan haka ya sauke fushinsa a sirrance kan Bilal ya dakatar dashi daga wasu hildodin ya hanasa ko fita daga kaantes din sbd lura da Bilal din zai iya sallamawa ya zabi yarinyar da ake maganar Wanda Hakan zai iya kawo tonan asirin maganar ga family dama duniya gabaki Daya.

Iyakance Bilal daga komai yasa Ababa qara kafewa sbd da alama dai waton ko Bilal din ya zabi sumayyah ba wasu dalolin arzkin zai samu daga gunsa ba tinda zaa iya dakatar dashi daga komai na dukiyar kaantes Dan haka ya sake tsayuwa akan raayin sai Bilal ya auri ‘yarsa kokuma yayi qara.

Akwai matakai da hanyoyin daukan mataki me kyau da sabaninsa da suke dashi akan irinsu Ababa Amma a zuciya da halin dd babban Yana dakatarwa ne sbd duba da yarinyar dake dauke da juna Biyun Wanda rayuwarta tabbas an Riga an lalata mata,

Sunada ‘yaya mata da jikoki Wanda ya tabbatarda idan aka cutatar da wannan yarinyar Allah zai iya jarabtarsu tinda ba kudi ko dubarar bace zasu tsare Maka yayanka daga Hakan,

Shi kuwa a duniyarsa da irin qaddarar Hakan ta samu ‘yayansa ko jikokinsa koma ahalinsa gaba Daya mata gwara Allah ya dauki ransa ya bar duniyar.

Ta bangare Daya Bilal ya qasqantar da Kansa a gaban dd babba ya rokesa akan yabarsa ya auri sumayyahn sbd Yana kaunarta har lokacin harma da duk Abinda zata haifa,

Yayi alqawarin zaiyi nesa da ita inda zasu Rena Abinda zata haifa batareda kowa yasan Tayaya suka haifesa ba,

Bazai taba barin sunan zuriarsa ta lalace ba sbd shi.

Da fari dd babba kasa karban wannan rokon yayi Amma ganin yanda Bilal yake qasqantar da Kai akan Hakan dakuma zaunawa da yayi ya duba tafiyar Bilal din zata ankarar da mutane a iya sani hakama Ababan Nan ba abin yarda bane matiqar suka barsa a Raye to zaa iya sanin gaskia Dan haka zai amince da auran yarinyar ta yanda zasu batar da zancen su Hana a fahimci ansamu wata qaruwar Bata hanyar aure ba daga baya zaisan yanda zaiyi da Ababa.

Saidai ya gindaya manyan sharuddan da daga Ababa har Bilal jiki na rawa suka amince aka bar maganar a rufe akan ana haihuwa zaa daura musu aure a rufe maganar haihuwar ta dawo kaantes.

******Amincewar dd babba yasa Ababa Jin duniyarsa gabaki Daya ta dawo sabuwa sbd farin ciki da samun biyan buqata cikin sauki,

Bilal ma samun Kansa yayi cikin samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya duk da Sam dd babba ya hanasa zuwa ganinta sbd kada aga Yana zuwa gidan Amma suna magana a waya duk bayan kwana biyu Shima da wayar Ababa sbd Ababan ya mayar masa da tasa wayar Daya bata.

Ta bangare Daya Kuma bakin aljihun kaantes aka budewa Ababan na kulawa da sumayyah wadda basusan meyake faruwa ba Dan kuwa wahalarsu sai Abinda ya qaru ba sauki.

*****Zuwa yanzu rayuwa ta sake yiwa su benazir wahala sbd rashin isashen hutu da yunwa harma da karatun benazir din Dan ita sumayyah tini aka watsar da nata karatun.

Gabaki dayansu sun bushe sun koma kaman wainda ke rayuwa a cikin Sahara sbd daidaicewar yunwa da wahala,

Sumayyah kuwa a yanzu cikinta ne kawai mai tsoka a jikinta,

Komai na masu ciki Tin daga cima har hutu da magani Bata taba samun ko Daya ba tinda ta baro asibiti.

Hande a yanzu tafi koyaushe tsangwamarsu sbd ita kam har lokacin tsanar cikin takeyi harma dasu gabaki Daya Dan ganin takeyi sun haukatar mata da Ababa sbd yanzu duk ya sauya babu Wanda yake Gane Kansa.

***A haka suka ringa gangarawa har cikin ya shiga wata Tara Wanda shigarsa ya saka rayuka da dama shiga tashin hankali da fargaba,

Ababa hankalinsa a yanzu data shiga wata Tara ya tashi cikin fargaban me zaa haifa hakama da fargaba Mai tsanani kan a haihu lafiya ba tareda matsalar komaiba Dan a yanzu haihuwar itace zata tabbatarda hayewarsa zuwa Ababansa ko faduwarsa zuwa Nobaba.

Chapter 33

33

Acan bangaren Familyn kaantes tini Dd babba ya sanar da ‘yayansa yayiwa Bilal matar aure Kuma ba lokaci zaa dauka ba zaa daura musu aure kawai ba buqatan wani biki ko wata bidiar kawai daurin auren alfarma zaa daura musu shikenan. 

Da mamaki kowa yake son sani ‘yar waye aka nemowa Bilal aurenta haka har cikin qanqanin lokaci zaa Ce zaa daura auren?

Dad Kaante yaso sanin ‘yar gidan wace Amma Dd babba sam Yaqi barin tambayoyinsu da zancen ya zurfafa har su fahimci auren na manufa ne da akwai dalilin yinsa,

A yanda yakeso kada kowa ya fahimta ko yasani sai ‘yar ta shigo hannunsu sai su taru su rufe zancen cikin gida bame sani sai an shakara da auren a bari duniya tasanta dacewa ‘yarsu Bilal din Ce ta yanda ba kowane zai tsaya lissafin yaushe Akai auren yaushe aka haihuba.

Umminsa da zancen auren Bilal ya risketa kaman zata shide Dan farin ciki Mai tsananin gaske sbd matar aurensa Ce kawai zata iya Saka mata Bilal dinta cikin farin ciki su taru su goge masa tareda maye masa gurbin so da kaunar dayake rasawa a cikin familynsa.

Zancen auren Bilal Babu abinda ya qara mata sai tsanani na buqatan Shima Dawood yayi auren sbd tini Shima anan din tai masa matar datake tsananin so itama.

Qaninta ‘dan kawunta daya jima da yin nasa arzikin Shima tin tsawon shekaru Ashirin har da yan kai daya Rabu da matarsa ta fari baya tayi barin ciki kafin rabuwarsu

yayi aure har so biyu Amma Bai taba samun haihuwa ba ko barin baa taba sake samu gidansa ba gashi Shima yafara manyanta Amma ba ‘yaya ga tarin arziki ya Tara Babu magada.

Daga ita ummen har hajiya Mahaifiyarsu suna cikin damuwar hakan da tausaya masa shiyasa aketa sake auro masa wasu Matan ko Allah zai basa wata ran idan akwai Rabon samun.

    A wannan yanayin ne suna cikin fata da adduoi koyaushe da sadaka da komai sai gashi Allah ya share musu kukansu ta hanyar dawowar tsohuwar matarsa da ‘yar qaramar budurwar ‘yar da Bata Gaza shekaru Sha uku zuwa Sha hudu ba Ashe cikin daya bare kafin rabuwarsu Yananan Bai qarasa zubewa ta haifi ‘yar harta girma. 

Duk da basa kaunar tsohuwar matar tasa daga ita har hajiya Mahaifiyarsu sbd son Rai da kwadayi tareda rashin girmamawa Harma da iya yin komai akan kudi da rashin godiyar Allah yasa suka rabun dakuma a lokacin Yana talakansa ne baida komai.

Amma dai tinda Allah yasa takawo musu Rabo na haihuwar da suke fata take suka manta komai suka hau tsananin farin ciki da nunawa ‘yar so mai tsanani.

Da farko hajiya dashi Kansa hankalinsu bai wani kwanta ba Saida akayo DNA Wanda a asibitin qanin tsohuwar matar tasa Akai komai Kuma suka samu sakamako na tabbacin ‘yarsa Ce jininsa Ce Dan haka tini suka hau farin ciki da murnar da bazasu iya kwatantawa ba.    

Shi kansa Alh Basheer bulama a wannan lokacin tsananin so da kaunar ‘yarsa ya shigesa fiyeda komai da kowa,

Kauna da soyayyar da ake nuna mata tareda halaye da tarbiyar da mahaifiyarta take Dora yarinyar yasa cikin qanqanin lokaci ta sauya daga wuya da talaucin dasuka fito da uwar na rayuwarsu duka ta baya su biyun suka fara kokarin shimfida rayuwar da sukeso ta yanda sukai raayi.  

    A lokacin matansa biyu ya Rabu da sauran Dan haka ba ja ‘yarsa tasa ya sake daura aure da mommynta cikin shekarun da Basu Gaza biyar Ba da auren suka sauyawa Hajiyarsa da yan uwansa shi bayaji baya gani idan akan lamarin ‘yarsa ita Kuma ‘yar komai mommynta take sakawa Yana yiwa sbd ita Kuma mommyn da ‘yar take amfani tana rayuwarta yanda takeso a cikin dukiyarsa.

Har wannan lokacin hajiya da ummin kaante kaman yanda take Kiran yayar mahaifin nata haj Fatima kaante suma basu taba Jin so da kaunar ta ya Sauka a ransu ba dan haka Tako Ina yarinyar ta samu gatan daya lalatata kusan gabaki daya dan kuwa tini ta rufe kowane Babi da ake cewa babin Tina baya.

   Da karatun SS 1 ta fara bayan dawowansu hannun Daddynta tana gama secondary school ta fara karatun jamia a Lagos Amma shekara daya kawai tayi dad dinta ya cireta ya maidata Malaysia dayake Daman mummynta itama tai bokon Sosai tare suka koma can da zama itada mummyn dan bazata iya barin ‘yar tata ita daya ba  can tinda ita din Bata komai a Nigeria din Kuma ‘yar tamkar mukullin juya rayuwar Alh basheer ce a hannunta shiyasa Bata wasa ko nesa da ita.

SBB shine sunan da ake kiranta tinda ta waye rayuwarta ta sauya gabaki daya,ita din ‘yar gatace a yanzu gaba da baya, ‘yar masu tarin arziki Ce,

Babu abinda take nema ta rasa Daddynta Bai mata shi ba,

ta gama karatunta ta sake fadawa wani Dan zurfafawa, tsawon shekarun da Sukai a qasar ta waje tini suka bar Malaysia Takoma Zurich mommynta kuwa Takoma Nigeria Amma kusan Akai Akai tana zuwa Dan akwai shaquwa da kauna Mai tsananin gaske tsakaninta da mummyn.   

Wayewarta tayi yawan da yawanci acan gida Nigeria idan tazo sauran dangi na mata kallan mara tarbiya kokuma tashin turai da bayan rayuwarsu Bata iya rayuwar ‘yayan Nan.  Shekarunta a yanzu sun haura Ashirin da biyar zuwa da shida ko da bakwai ma Amma gata da rayuwar Datake yasa koyaushe a yarinya sharaf iyayenta ke kallanta.

Bata taba sanin DD kaante ‘dan ummen kaante ba duk tsawon shekarun Saida ummen tazo qasar ranar data je gurinta a ranar idanuwanta da zuciyarta sukai kyakyawan Gamo dashi,

idan tace tafada soyayya to ta ragewa zancen karfin gaske Dan haka ba soyayya ta fada ba Kai tsaye ta kamu da mahaukaciyar soyayyar da zata iya yadda ta mutu ba aure matiqar ba Dawood Dayyab dauda kaante zata samu ba. 

Bata kula kowane namiji a rayuwarta da sunan soyayya sbd Sam ita tama manta da ana tsayawa Ayi soyayya da aure gaba,

  Tin a Malaysia datai wani saurayi Dan qasar yaso aurenta Amma yanaso su ringa qwanciya tare taqi sai hakan ya lalata soyayyar tasu duk da suna son juna Amma shi yafi buqatan ta dawo gidansa da zama.

Soyayyar DD kaante a rayuwarta tasan abu ne Mai wuya kafin ta samu Amma tinda umme na sonta kaman yanda take son Zeenah yasa Bata boye ba Dan batasan wata kunya ba a yanzu ta bayyanar da soyayyarta a Fili Kuma ta samu Goyan baya tareda bayyanarda farin ciki sosai da amincewa daga ummen.

  Hakan yasaka kusan kullum tana gidan Akai Akai danma taso dawowa gidan gabaki daya Amma qa’idar DD ce bayason mutane a gidansa baya iya rayuwa da wasu a guri daya,su ummen ma Dan mahaifiyarsa Ce Bai hadata da kowa ba sai qanwarsa dayake jinta cikin tsakiyar ransa itama Bai hadata da komaiba dan haka su baida damuwan zamansu a gidansa duk da ummen tasan Dan Yana son su fiyeda komai ya barsu Amma ba wai dan Yana sakewa da hakan bane ta sani.

   DD a rayuwarsa bayan baturiyar budurwarsa lizz Shima Bai taba soyayya da kowace mace ba sbd bama zai iya Tina wace macen bace yayiwa kallan tsaf da har zai iya soyayyar da ita

Zuwan ummensa Zurich ta rabasa da Lizz dan tsoran kada ‘dan nata ya fada Zina sbd ganin yanda Lizz din ke maqale da hannunsa ko yaushe Idan tazo gidan batareda damuwa da ita uwarsa tana gidan ba.

Babban Saa da Daman da Sbb ta samu shine maganar ummensa kaman yankan wuqa ne Bai taba musawa ba Dan haka tana rabasa da Lizz ta fara Saka masa zancen yai aure tinda zaman a haka ya Isa.  Bai taba tinanin aure a yanzu ba Amma sbd bayason ana maimaita magana a rayuwarsa yasa ya barwa ummen zabin komai Dan tasan kalar matar da bazata taba binsa tadamesa ba zata zabar masa.

   Sbb na ganin zancenta da DD ya tabbata yasata Jin duniyarta ta sake sauyawa gabaki daya, ita ‘yar  millionaire zata auri ‘dan billionaires Shima Kansa billionaire. 

Daga lokacin tafara Jin kanta qarasa juyewa gabaki daya a sonsa Bata Ji Bata gani Bata ganewa duk zancen da babu sunan DD kaante dinta aciki.

  Duk wannan bidirin Bai taba tsayawa ma yasan asalin kamannintaba bare tantance muryarta sbd Bai taba maganar data wuce ta minti daya zuwa biyu Ba da ita Amma a hakan taji tagani ta amince. 

  ********

Zancen maganar auren Bilal ya sanya umme ta yiwa Dad kaante magana dan a hade auren Dana DD tinda tare zasu dawo,

Shima Dad kaanten yanason dawowar DD din da zamansa anan Dan haka wannan shawarar tai masa daidai dan haka da kansa ya samu Dd babba da maganar dayake Alh Basheer bulama nasu ne babban mutum ne sosai Shima gashi akwai sanayya Dan haka aka yanke shawarar  Neman auren kawai a hade Dan kuwa Dd babban Yana buqatan dawowar DD a kusa dashi suna buqatansa.

Da wannan Shirin aka fara Shirin auren DD da Bilal lokaci Daya.

******Benazir zuwa yanzu rayuwar ta sake matse musu babu sauki sai a gurin ubangiji,

Sumayyah lafiya tafara qaranci sbd rashin Cima Mai lafiya isassa da yawa aikin wahala.

Anne ma depression ya fara tayar mata da ciwonta itama yau lafiya gobe sai ahankali Dan haka benazir ta ‘daidaice Takoma abin tausayi,

Sumayyahn ma nata ciwon Yi yakeyi Yana kokarin tashi ga cikin jikinta yayi girma sosai kaman me cikin ‘yan biyu.

Tashin hankalin benazir a yanzu shine yanda zata iya karban haihuwar sumayyahn sbd da alama Anne sai ahankali,

Hande Kuma ko sumayyahn zata yage gurin haihuwa bazata taimaka musu ba a yanda ta tsani cikin da su gabaki Daya akansa.

Ta bangare Daya ga karatunta suna kokarin fara exams a satin.

Abinci ta koshi ta manta rabonta da Hakan sbd kullum barwa sumayyahn dake dauke da juna Biyu sukeyi saita koshi suci sauran Wanda itama sumayyahn bawai cin takeyi ta koshi ba tana Dan ci zata ce ta koshi sbd tabar musu itama su samu suci.

Lokacinda benazir suka fara exam lokacin tini depression Mai tsanani yafara kokarin juyar mata da Kai itama sbd Anne da ciwonta ya tashi sai tayi fiyeda kwana nawa kafin ta dawo daidai

Hakama sumayyah sai ahankali itama Dan haka hankalinta ya rarrabe cikin damuwa da rashin sanin madafa,

Bata iya karatun Daya kamata,

Ga aikin gida ga wankin shagon Ababa Idan ankawo wuni takeyi ta raba dare tanayi harda guga,

Ga kula da Anne da sumayyahn wadda a yanzu cikin takejin kaman zai kasheta sbd numfashi ma gagararta Yi daidai yake sbd cikin.

Chapter 34

34

Dd babba dukkanin tsare tsarensa na jiran haihuwar ya gama,

Shirin Daya tanadarwa Ababa ana haihuwar zai saka a batar masa da hankali yanda babu me iya Tina komai sai Abinda zaa Dora a Nan gaba Dan haka ya sanarwa Ababa lokacin haihuwa na zuwa a sanar masa ya turo mota akaita asibiti haihuwa.

Ababa komai yakeyi Yana tsayawa ya Kalli lamari Dalla Dalla kada ta kwabe masa Dan haka Sam ya kasa yarda da maganar Wani Kai sumayyah asibiti haihuwa sbd komai ma zaa iya yiwa cikin a kashesa gurin haihuwa a rufe zancen Dan haka bazai taba yarda ba a gida zata haihu idan an maqale da Kansa ze kaita Asibitin Daya yarda a haifo masa Dan a Basa a hannunsa yaga me kashesa bayan Wanda ya Basa Rai ya aikosa duniya.

Shi Kansa yanzu ya rage fita sosai koyaushe Yana gida tinda cikin zo gangar haihuwa Dan bayason ma baya kusa haihuwar ta taso ayi masa katsalandan kaita Asibiti.

Benazir azabarsa duka akanta yake qarewa sbd ganin itace yanzu mara amfani a gurinsa,

Duka asarar duniya ganin yakeyi ta qare akanta batada amfani komai gurinsa a yanzu,

Jiran ma yakeyi a gama auren sumayyah ya samu su shiga kaantes ya miqawa yan dilar qwayar dayayi alqawari benazir din Dan bama zai iya cigaba da biyan nata karatun ba tazo ta debo masa Wani abin maganar Dan kuwa ita binneta zeyi da Rai idan tayo masa Hakan sbd babu wasu sauran masu kudi a idonsa bayan kaantes.

***Rayuwa tayiwa benazir tsananin da ko ruwa ta saka bakinta ‘dacinsu takeji,

Babu Daren da Anne da sumayyah Basa kukan tausayinta sbd a kanta wahalar kacokan take yanzu.

Exam dinta dasuka fara kullum zuwa kawai takeyi ta rubuto ta dawo Badan tana Gane komai ba ko karatun komai din.

Qwaqwalwarta datafi ta kowa lafiya a kaf gidan har Ababa da hande

Itama tafara samun rauni sbd a yanzu itama kusan magana takeji kaman anayi mata cikin kan saidai Sam qarfin zuciyarta ya Hana kowa Gane halinda take ciki.

Ranar da suka gama exam tana dawowa gida ta tadda ayyukan dake jiranta

Sallah kawai tayi ta fito tafara aikin

Sai dare ta kammala ta shigo dakinsu ta Kalli sumayyah dake zaune shiru tayi Nisa a tinani cikin mutuwar jiki da tausayin kansu Dana Annensu dake gefe zaune shiru itama batama San tinanin datakeyi ba.

Ajiyar zuciya benazir ta sauke ahankali tareda zaunawa itama Bata iya cewa komaiba zuciyarta na Wani irin rawa sbd ta Kai zuciyarta tagama tsotsewan da babu komai a cikinta sai iska da fili.

Zuba mata idanuwan dasuka gama fadawa sbd rama sumayyah tayi tanajin cikinta na motsawa a hankali.

Benazir batasan kallan da sumayyah ke mata ba na tsananin tausayinta da tsanar kanta akan sakasu cikin wannan halin datai Amma itama ba itace ta zabarwa kanta qaddarar haihuwa a yanzu ba,

Hawayene suka gangaro mata masu tsananin zafi Daya Sanya benazir juyowa ta Kalli sumayyahn zatai magana jikinta amace itama

Sumayyah ta fashe da Wani irin Kuka mara sauti tana sunkuyar da Kai Dan kuwa komai Basu samu a wannan rayuwar ta duniya ba face tarin jarabawa da darasi,

Samirah jarabawarta ta qare da wuri ta tafi ta huta hakama Safnah,

itama tana fatan a daidai wannan gabar Allah ya Yanke mata wahalar ta tafiyarta tabar duniyar ta huta

Benazir ma ta samu sassaucin ukubar.

Benazir data San tinanin da sumayyah takeyi take idanuwanta dasuka Fi kwanaki a bushe Bata iya Kuka sbd azaba idan tai yawa Kukama baya zuwa,

A hankali Idanuwanta suka fara Tara ruwan hawaye masu dumin dasuka fara gangarowa fuskarta.

Hawayenta yasaka Anne kasa riqe nata kukan itama sbd kukan benazir Yana karyar da duk Wani kuzarinsu Dan itace qwarin gwiwarsu Kuma karfinsu.

Kukan Anne yasaka benazir kokarin Hana hawayenta cigaba da sauka Amma sun kasa tsayuwa hakama Wani sheshekan kukan Mai tsananin ciwo da nauyi ya taho mata ta rufe bakinta da hannuwanta biyu tana cusa kanta cikin qafafunta sbd nata quncin yafi nasu Dan su suna Mata Kuka su bayyanarda radadinsu

Ita Kuma batada inda zatai kukan ta bayyanarda damuwarta sbd sune nata Rabin jikinta Amma basuda lafiya ko hankalin fahimtar nata quncin bayan ma ta sake gigitasu da nata kukan shiyasa duk tsanani take dannewa ta riqe komai ta barwa zuciyarta.

Wani irin Kuka suka rufu a dakin suka Taya benazir sbd tayi kukan sosai ko zata samu sassaucin Abinda take dannewa tana riqewa a zuciyarta batareda fitarwa taji sauki ba.

Suna cikin kukan marar sumayyah tayi Wani irin riqewa ta daure ta kasa nunawa saidai kaman bazata iya dannewar ba Dan haka ta Dan dago jajayen idanuwanta ta Kalli Annensu kafin ta Maida kallanta kan benazir ahankali ta Bude baki tace

“Zanje bandaki”

Hawaye benazir ta share da tafin hannuwanta kafin ta janye daga jikin Anne data rungumeta Dan rarrashinta ta miqe tsaye tana sake goge fuskarta kada a Gane kukan da sukai Hande ta hau Wani fadan Kuma.

Daman sumayyahn ba kasafai take iya komai ba da kanta a yanzu sai an taimaka mata sbd ko kuzarin tsayuwa da kanta batada shi sbd wahala da yunwa.

Kamata tayi suka fito tana riqe da ita suka je bandakin tayo Abinda zatayi suka dawo suna isowa inda zata ajiye butar ta Dan saki sumayyahn da ajiye butar Ashe Bata tsayu daidaiba sai Jin tayi sumayyahn ta zube qasa.

Faduwarta yayi daidai da fitowar hande da Anne a kusan tare suka saki ihun tashin hankalin Daya saka Ababa fitowa da rigarsa a hannu dagashi sai dogon wando da singlet.

Rawa jikin benazir ya dauka cikin tsananin tashin hankali ta durqusa tana kamo sumayyahn data fara Wani wahalallan Nishin da bama na faduwar bane na halinda take ciki ne kafin faduwar.

Azabar datafi Wanda suke ciki tsawon shekaru ne sumayyah taji Wanda yasaka kasa motsawa tafara Jan numfashin wahala jikinta na daukan rawa take.

Salati me karfin gaske hande ta saki tana cewa

“Mun shiga uku benazir kin tado mata nakuda lokaci baiyiba

Wannan ‘da dai Allah yasa rabo ne”…

Kalmar hande ta saka Ababa Jin zufa da tashin hankali Mai tsanani rufesa

Ya Kalli benazir daketa rawar jikin taimakawa sumayyahn ta tashi Amma ta kasa.

Fizgota yayi kafin ta motsa ya sauke mata wasu Marika biyu a Jere da suka dauke mata jinta na daqiqu

Gefen bakinta take ya Dan fashe.

Cikin tsananin zafin zuciya da masifa yace

“Wlh kiyi adduar a haihu lafiya na dauki ‘dan da hannun idan ba haka ba kece kika kashe cikin Nan Kuma wlh bazai dauki asarar Rai ba miqa ki zanyi hannun yan sandan gidan yari”.

Hande kuwa gabaki Daya dagawa kowa hankali tayi da ihun ai an kashe babyn tin baizo duniya ba shikenan.

Wannan kalaman nata suka haukatar da Ababa Kansa na Neman kuncewa.

Anne ma duk da ciwonta take lafiyanta ta dawo ganin zata rasa sumayyah,

Benazir duk da jinta daya dauke tana Jin hayaniyarsu sama sama haka ta taso Bata ko Gani sosai ta nufo sumayyahn suka kamata zuwa daki ita kanta sumayyahn lokacin ciwon yayi mata tsanani Amma ahakan ta qanqame hannun benazir tanajin ita tafi buqata a yanzu fiye da kowa Dan a hannunta takeson haihuwar koma me zata Haifa,

Tana son Abinda zata haifa Yana fadowa duniya ya fado hannun benazir dinta sbd Anne ko an bar mata shi bata Gane kanta wasu lokutan bare Abinda zaa bar mata.

Suna shiga daki da ita Anne da jikinta ke rawa haka kawai ta Kalli sumayyahn dake hada Wani zufan gaske tanason tayi magana ta kasa.

Hande shigowa dakin tayi ta koma kofar dakinta ta zauna tana jiran haihuwar itama Ido awaje.

Ababa kuwa rigar Daya fito da ita Bai iya sakawa ba haka ya tsaya tsakar gidan Yana kaida kawo zuciyarsa na tsalle da fargaba da tashin hankali harma da tsoro Mai tsanani sbd ayau ne ranar da zai karbi mukullin shigarsa kaantes,

Wannan haihuwar ta sumayyah itace tabbacin makomarsa da matsayarsa a babin gaba.

Naquda sumayyah ta fara gadan gadan cikin tsananin azaba da wahalar data fara qarar mata da karfin da Daman batada dashi,

Anne da benazir Basu taba shiga matsanancin halin fargaba da tashin hankalin wannan Daren ba,

Tin tanada karfin iya motsawa da numfasawa daidai harta rasa dukkanin karfinta.

Ababa a tsakar gidan kuwa wutar ruwan zafi ya kunna da Kansa ya ringa tura itatuwa suna cinyewa Yana saka wasu sbd idan ya tsaya guri Daya zai iya kasa riqe Kansa ya fada dakin.

Shi Kansa tinda yake a duniya Bai taba shiga hali na fargaba da tsoron wannan Daren ba gashi haihuwar na Neman zuwa da gardama Dan kuwa Tim suna Jin Nishi da kukan sumayyahn harsun Dena ji.

Sumayyah data cire daga rayuwa gabaki Dayanta tini jini ya fara tsinke mata Bata iya ganin fuskokin Anne da benazir dake kanta dishi dishi take ganinsu tana kokarin Hana kanta sarewa Amma Kuma numfashinta baa hannunta yake ba da zata iya daidaitasa.

Babban fatanta idan gurin haihuwar Allah zai dauki ranta ya dauki ranta da Abinda zata haifa Shima ya bita sbd ta tafi da masifar da zata qarawa benazir da Anne,

Bazasu iya renan jariri a wannan wannan matsin rayuwar da suke ciki ba.

Har Akai sallar Asuba sumayyah Bata haihu ba tagama ficewa hayyacinta.

********

A safiyar ranar karfe 6 na safe jirgin da DD kaante ya sauka a Nigeria tareda ummensa da Zeenah,

Motar Bilal kaante ce tazo daukansu,

Sai Amintaccen DD na tintini wato Naseer Wanda baida kaman DD din Shima Dan kuwa DD ne ya dauke nauyin karatunsa tin secondary har gama jamiarsa daya gama last year,

Abinda yasaka Bai bi DD ba acan sbd akwai wasu ayyukan DD din dashine yake kulawa dasu ta Wani bangaren Kuma soyayyar wadda takasa yardama ko sakewa dashi tayi harya bar makarantar Dan haka yake Jin bazai iya tafiya koina batareda ya sameta ba.

Shi Bilal da Naseer suka fara hangowa a tafe cikin kalar kayansa da baya sauyawa sai Dace wato black.

Michael kors Black sweatshirt ce jikinsa da black Balmain jean,

Qafarsa ma black BV saldals ne da suke bayyanarda hasken kafarsa dake kaman bada ita yake tafiya ba a rayuwarsa.

Hannunsa na dama a cikin aljihun wandonsa yake dayan hannun kuwa hannun ummensa ne a cikin nasa suna tafe gabaki Daya baka iya ganin fuskarsa daga gefen fuskarsa da bayan wuyansa da farar fatarsa ke bayyane sbd facemask din dake rufe da fuskarsa da tsadaddiyar luxury black Fcap din flexfit dake Kansa.

Idanuwan Naseer Daya jima baiga maigidan nasa a fili ba kusan kasa dauke idonsa yayi akansa sbd gabaki Daya wannan dake doso sa shi ake nufi da Asalin kaantes Dan kuwa babu kamarsa Kai tsaye a harka indai acikin familyn ne.

Kafin isowarsu Naseer ya nufosa da sauri Yana Isa DD ya dago fararen idanuwansa dasuka saka Ba Naseer ba hatta Bilal Jin jikinsa ya mutu da kwarjinsa take ya zaro hannunsa daga aljihun wandonsa ya ware ahankali ya rungume Bilal din Wanda ganinsu su ukun ya saka sa Jin Kansa kaman qaramin yaro gabansu yanaso tsiyayo da hawayen quncin dake damunsa a Rai na tsawon lokacin da basa Nan Dama Abinda yake damunsa kwanakin.

Chapter 35

35

Ajiyar zuciya Bilal ya sake saki a hankali tareda sake rungume DD yana Jin nutsuwar daqiqun.

DD dayasan Bilal ciki da Bai a take ya Jiyo damuwa a tare da Bilal din daga rungumar kawai sbd Allah yayi masa wata fitinanniyar baiwar karantar mutane ko a yanayin Aiki da jininsu.

Sakin juna sukai ahankali

Naseer yayi saurin miqa hannu babu kamewar komai DD ya miqa nasa hannun Naseer yayi saurin kamawa Yana cewa

“Munyi kewanka sosai Sir D,barka da dawowa”

Idanuwansa dake sake rudar da Naseer din cikin farin cikin ganinsa ya dago ya kallesa tareda gyada masa Kai a hankali cikin nutsuwa kafin suka wuto zuwa motocinsu.

Umme Kallo Daya tayiwa Bilal bayan tsayuwarsu gurin taji jikinta gabaki Daya na Neman sanyi murnarta na Neman komawa ciki sbd rama da sanyin dayayi.

Tabbas akwai qunci ko damuwar dake damunsa Dan haka daga ita har Zeenah jiki a matiqar mace suka rungumesa Shima yanajinsa jikin mahaifiyarsa Mai tsananin so da kaunarsa jikinsa ya sake mutuwa Yana kokarin danne damuwar dake shimfide cikeda ransa.

Kaman Umme ba zata sakesa ba Amma haka suka nufi motacin hannunta na riqe cikin na Bilal din Wanda ya kasa hada Ido da ita sbd tausayin Kansa da nata da ranta zaiyita Baci yanzu akan duk Abinda akeyi masa na nuna bambamci da rashin kauna kaman sauran.

A qa’idar DD ko motocinsa na Hawa gabaki Daya black ne,

Black Mercedes beymach Naseer yazo daukansa shikuma Bilal da tasa motar yazo daukan su Umme.

Luggages dinsa Naseer ya zuba a motarsa yafara wucewa dasu gidan DD din Kai tsaye shikuma ya shiga motan Bilal sbd su tafi kaantes tare daga baya zai tafi gidan idan yaga dd babba da dad dinsa.

A hanyarsu ta Isa gidan gabaki Daya motar babu me magana sai ummen dake kokarin fahimtar Abinda yake damun Bilal.

A rayuwarta ita Kuma kusan tafi so da kaunar Bilal din fiyeda komai da kowa,

Ya taso a wata gurguwar rayuwar rashin gata da zallan banbanci da ake masa tareda ganin kaman alfarma ce Akai masa yake zaune acikin kaantes din shiyasa yake ‘dan wahalarsu duk Wani wahala da aikin da babu Mai iyawa akansa yake Kuma duk a banza babu Mai nuna godewa ko daukan Hakan a matsayin kokari da fasaharsa saidai a alfarma da ake masa Dan haka ta fifita soyayyarsa itama akan sauran ‘yayanta kada abin yayi masa yawa ya samu matsala.

Suna Isa kaantes take securities suka Bude musu gate motar ta shige suna daga hannuwansu Dan isar da sakon barka da zuwa ga Sir DD kaante.

Babu me matsayi ko muqamin da dd babba ke iya fitowa tarba a gidan bayan Dawood Dan haka Koda sukai parking harabar gidan dd babba Yana tsaye Yana jiransu kaman yanda ya Saba tarbon Dawood duk zuwan Dayake Yi.

Abbakar ne yayi saurin qarasawa ya budewa DD kofar motar bakinsa a washe Yana masa barka da zuwa cikin girmamawa.

Fitowa DD din yayi Yana nufar dd babba Wanda ba kasafai kake ganin dariyarsa ba saidai murmushinsa Amma bayyanar Dawood gabansa baya iya riqe ko taqaita farin cikinsa Dan haka hannu ya ware Shima Dawood din qarasowa yayi a natse ya rungume dd babban.

“Welcome my Lion”

A hankali ya saki Wani qayataccen murmushin Daya saka dd babba dagosa Shima Yana murmushin.

Gaisuwar Umme dake gaidasa cikin girmamawa da sakewa ya amsa kafin ta Zeenah dake gefensa itama tana gaidasan.

Motar Dad kaante ce ta shigo harabar gidan suka tsaya duka suna kallansa driver ya Bude masa ya fito ya nufosu Kai tsaye Shima fuskarsa dauke da farin cikin ganinsu musamman DD duk da basa doguwar jituwa kaman ba Uba da ‘da ba akan banbancin dasuke nunawa Bilal yasa Sam basa jituwa da dad din.

Yana isowa Zeenah ce ta Isa gurinsa da gudu ta rungumesa tana Kiran sunansa.

Da farin ciki ya riqo hannunta suka qaraso Yana kallan DD da sai alokacin yake zare facemask dinsa idanuwansa akan dad dinsa dashima shi yake kalla.

“Dad”yafada cikin kauna Yana miqawa Dad din hannu suka damqe hannuwan juna kowannensu na bayyanarda farin cikin ganin Dan uwansa.

Dunguma sukai zuwa ciki dd babba da Dawood din na gaba harma da dad suna magana DD din na sauransu kawai sbd yasan zancensu ba qarewa zaiyi ba.

Bilal dake bayansu tini suka manta dashi Dan haka yake biye dasu kaman bodyguard nasu.

Umminsa zuciyarta sanyi tayi Wanda Abu ne da suka Saba dashi shekaru matsu tsayi Daya kamata ace sun Dena Jin ciwonsa saidai ciwon Hakan ba Abinda zaka iya cirewa ko Hana ji bane saidai kawai koyaushe kayita dannewa sbd haka Allah ya tsarowa ‘dan nata.

Hannunta na dama takai a hankali ta riqosa ta bayansa ya tsaya ahankali tareda juyowa ya kalleta sai yaga idanuwanta na Neman sauyawa

Ya girgiza mata Kai ahankali Yana sake murmushin yaqe.

Juyawa sukai zuwa part din su ummen Wanda Zeenah tini tayi gaba masu Aiki sun ja kayansu sunyi can dasu.

*********

Lamari yayi tsanani ya Baci,ya lalace komai ya kuncewa benazir da Anne dake cikin daki an sakasu karban haihuwar,

Benazir Bata taba Jin kanta Yana Neman juyewa gadan gadan ba sai a yau din Datake ganin ran sumayyah na Neman fita a gabansu,

Sumayyah tabar mata maganganun dasuka Fi mata kama da wasiyya Wanda ya sakata kasa riqe kanta ta fasa kukan tashin hankalin Daya saka Ababa leqowa dakin hankalinsa tashe qafafunsa na rawa Yana cewa

“An mutu ne?”

Daga benazir har Anne babu Wanda ya iya dagowa bare iya amsa zancensa da bama su ji sa ba Dan babu Wanda yake hayyacinsa.

Wani irin ciwo da nauyi zuciyar Anne takeyi Wanda ya sakata rarrafowa ta dawo gefen sumayyah takai hannuwanta ta rungumota jikinta a hankali tana rufe Idanuwanta dasukai jajir hawaye masu zafin gaske sune tsinke mata batareda ta iya cewa komaiba Amma da Wani zai iya dauke ciwon Wani da ayau ta dawo da ciwon sumayyah jikinta ta haife mata cikin.

Benazir kuwa da hannunta na cikin na sumayyahn data riqesa da kyau cikin nata duk da tana cikin azabar ciwon da ficewar hayyaci benazir a cikin tsakiyar zuciyarta take,

Tana Jin tsananin halin qunci da tashin hankalin da benazir ke ciki cikin zuciyarta.

Benazir datake zaune gaban sumayyahn hankalinta ya Dade da barin jikinta Kuka takeson Yi Amma masifar data qamar da zuciyarta ta tashin hankali mara misali ta hana ko hawaye taruwa cikin idanuwanta.

Jinin dake zubowa ne ya sake gudu idanuwan sumayyahn na Neman juyewa sbd zuwa lokacin numfashi ma Bata iyawa da kyau

Wasu siraran hawaye masu dumi ne ke gangarowa gefen fuskarta Wanda yake sake qamar da benazir da itama zuciyarta ke kokarin Dena bugawa dukkanin jikinta na Dena motsawa.

Anne dake rungume da sumayyahn har lokacin tana ganin yanayin sumayyahn rasuwar sameerah ta dawo mata sabuwa a cikin zuciyarta take taji itama tata zuciyar na kokarin tsayawa ta fashe da Wani irin Kuka Mai radadi da ciwo tana sake riqe sumayyahn tace

“Sumayyah Dan Allah duk tsanani karki barmu,

Kece sanyin idanuwanmu, ba zamu iya babu ke ba babu Abinda kika bari,

Karki tafi ki barmu,

Benazir rayuwarta lalacewa zatayi itama hankalinta zata rasa idan ta rasaki,

Idan na rasu waye zai sharewa benazir hawaye da baqin cikin wannan rayuwar mara Dadi……

Kalaman Anne suka saka benazir fasa Wani irin Kuka tana cusa kanta cikin qafafunta,

Bata taba yiwa kanta fatar mutuwa sai ayau,

Idan tafiya sumayyah zatayi ta barsu ya Allah ka dauki ransu a tare su tafi dukkaninsu su bar wannan duniyar da Basu San meye acikinta ba bayan Kuka da baqin cikin rayuwa.

Kukan dasuke Yi a kanta kaman ransu zai fita yasa Ababa kasa riqe Kansa yaje jikinsa na rawa ko gabansa baya Gani ya dauko wayarsa ko ganin numbers daidai bayayi ya Nemo sunan Bilal ya saka kiransa.

Bilal dake zaune gaban ummensa Yana Jin zuciyarsa na tsinkewa Tin safiyar yau din sai yanajin Hakan damuwar yanda zai iya sanar da mahaifiyarsa da ‘dan uwansa Abinda yake faruwa na qaruwar haihuwar da zai samu ta qaddara.

Ummensa da itama tata zuciyar ke tsinkewa tinda suka shigo kaantes kallan Bilal tayi tana sake Jin jikinta na mutuwa ta riqo hannunsa tana Kiran sunansa ahankali tace,

“Bilal….kafin tayi magana wayarsa tayi ringing Ya saka hannu cikin aljihunsa jiki a mace Shima ya Ciro wayar Yana dagowa yaga sunan Ababa take gabansa ya Fadi jikinsa ya sake mutuwa.

Kallan ummensa yayi yaga itama shi take Kallo jikinta a mace.

Wayar ya dauka tareda Dan janyewa daga gabanta.

Murya na rawa hankali tashe Ababa yace

“Kayi sauri kazo yanzu da gaggawa Sumayyah da Abinda yake cikinta na cikin mummunan hadari tin jiya take nakuda ba haihuwa har…..

Bai qarasa ba Bilal ya katsesa hankalinsa a matiqar tashe jikinsa na daukan rawa yace

“Meyasa ba’a kirani ba tin jiyan?

An kaita Asibiti ne?

Ganinan zuwa yanzu.

Kashe wayar yayi ya juyo ya nufi kofa zai fice

Umme tayi saurin riqesa hannuwanta na rawa a tsorace tace

“Waye ne?

Waye Kuma ba lafiya?

Meyake faruwa ne?

Ina zakaje?

Kasa amsawa yayi sbd hankalinsa Daya matiqar tashi

Kasa magana yayi idanuwansa na sauyawa da tsoron Daya kasa nutsuwa dashi.

Sake jero masa tambayoyin Umme ke kokarin Yi Amma Bai gama ji ba yayi gaba Yana sake saka Kiran Ababan yaji a gida suke ko asibiti Amma yakasa samunsa sbd Ababan Yana can ya kira dd babba ganin Bilal baigama sauraronsa ba ya kashe wayar.

Dd babba dake zaune a palonsa na alfarma suna magana da DD da dad kaante Kiran Ababan ya shigo wayarsa yaqi dauka.

Bai gama dauke idonsa daga kan wayar ba Wani Kiran ya sake shigowa kaman bazai dauka ba Amma tinanin zai iya Kiran Bilal ya fada masa Kuma Bilal din zuwa zaiyi a samu matsala idan Wani ya gansa can Dan haka ya dauki wayar a natse ya daga Kiran.

Ababan Bai iya tsayawa ko sallama ba a rikice yace

“Alh babba ‘yata mutuwa zatayi daga ita har Abinda yake cikin nata nakira Alh Bilal nafara magana ya kashe wayar,kunce idan haihuwa tazo a sanar ma…

Shima Bai qarasa ba dd babba ya katse Kiran hankalinsa na tashi ya miqe Dan tsayar da Bilal Dan kuwa matiqar Ababa ya kira Bilal to kuwa babu Abinda zai hanasa zuwa saidai komai ya faru Dan haka Bai tsaya Bata lokaci ba ya miqe da Kansa ya nufi kofa Yana saka Kiran wayar Bilal Wanda harya shiga mota.

Daga DD har dad kaante bayan dd babba suka biyo cikin mamakin meya daga masa hankali ya fice haka cikin sauri da bacin Rai.

Chapter 36

Bilal Yana fitowa daga part din su Umme harabar gidan ya nufa Yana Ciro keys na motarsa duka hannuwansa na rawa,

Tashin hankalinsa da ficewa hayyacinsa akan Abinda yake tsoran Ababa zai iya Yi har sumayyah da Abinda yake cikinta su samu matsala duka Dan haka bazai taba tsayawaba anan tanacan tana fama tsakanin Rai da mutuwa.

Ummensa hankali tashe ta biyo bayansa tana son sanin meya faru sbd Bata taba ganin ‘danta me sanyi da nutsuwa ba acikin wannan mummunan yanayin Dan haka ta biyosa tana Kiran sunansa hankali tashe Wanda yayi daidai da fitowar su  dd babba Suma Yana Kiran Bilal din cikin karaji da babban sautin daya tabbatarwa dasu dad kaante ba lafiya ba akwai babban lamarin Dayake faruwa.

Bilal a Karo na farko rayuwarsa Daya take umarni da Kiran dd babba ya fada motarsa tareda tayarwa da Wani mugun ribas ya nufi gate ko Gani bayayi sosai.

Dd babba cikin tsananin bacin Rai da fushi ya daga murya yace securities kada su budewa Bilal din gate

Sunajin haka take suka Maida gate din suka rife gashi yariga ya kawo Dan haka motarsa ta daki gate din Amma Bai tsaya ba kokarin sake yin gaba yayi ribas yakeyi ya sake dukan gate din Amma kafin yayi Wani yunquri DD ya iso gefen motar ya Bude ya zare key din Yana kallansa da idanuwansa dasuke masa kallan mamaki Mai tsanani Yana Jin da akwai babban lamarin dake faruwa da ‘dan uwan nasa.

Umme ta Riga dd babba isowa ga Bilal din hankalinta tashe hannuwanta na rawa ta fito dashi motar tana kallansa zatayi magana dd babba dashima ransa yagama mummunan Baci Yana zuwa ya dauke Bilal din da Wani lafiyayyan Marin Daya saka Bilal din dawowa hayyacinsa ya sauke Kansa hawaye masu dumi suna gangaro masa da tsananin damuwa da baqin cikin rashin darajarsa takai a saka masa hannu duk girman shekarunsa masu yawa.

Saukan Marin dd babba akan fuskar Bilal yasaka DD da Umme da dad kaante harma da securities shiga mummunan tashin hankali da tsoro.

Umme hannuwanta na rawa tana son kamo sa Amma bacin ran dd ya saka kowa kasa motsawa.

Kaman daga sama muryar DD Mai sanyi da nutsuwa a kame yace

“Me yake faruwa ne anan?”

Akwai Abinda ya kamata mu sani ne?

Bilal ya kalla Wanda hawaye yakeyi sosai kaman karamin yaro Amma yakasa dago Kansa,

Yau na Daya daga cikin ranakun da bazai taba mantawaba a matsayinsa na me amsa sunan kaantes.

DD Maida kallansa kan dd babba da ransa ya gama Baci yayi kafin suyi Wani yunquri

Umme ta riqo hannun ‘dan zasuyi ciki idanuwanta na cikowa da hawaye sosai itama.

A fusace dd ya Kalli Abbakar yace ya Bada umarni na doka Mai tsananin gaske kada a budewa Bilal gate ya fita gidan Bada izininsa ba

Da sauri Abbakar ya nufi gate Dan isar da sakon ga securities na gidan gabaki Daya.

Kiran Ababa ne ya sake shigowa wayar Bilal wannan Karan Umme ce ta karbe wayar tana kallan sunan me kira kafin tayi yunqurin dauka Bilal din ya amsa ya daga kafin ya iya Bude baki yayi magana Ababa Daya kusa haukacewa sbd tashin hankali kukan da benazir keyi cikin mafi girman tashin hankali kawai ya karawa Bilal din take ya tsaya cak tareda rintse idanuwansa dasukai jajir sbd masifaffen tashin hankali ya kashe wayar tareda juyowa kawai ya zube gaban dd babba Kansa a qasa cikin qunci da Wani irin ‘daci Mai tsanani na zuciya muryarsa na danne halinda zuciyarsa ke ciki yace

“Nayi alqawarin bazan taba barin kowa ya Ganni a gurinsu ba Amma Dan Allah ka bani izinin zuwa nakaisu asibiti.

Rintse idanuwa dd babba yayi sbd dai anzo gabar da dole dadynsa da mahaifiyarsa da DD su San Abinda yake faruwa tinda hakan ta faru gabansu.

Kallansa dd babba yayi Kai tsaye yace baka buqatan zuwa zaa aika driver yakaisu Asibiti idan ta haihu anfasa Kai auren Wani wata satin Nan zaa daura auren qasar zaka bari gabaki Daya ba yanzu zaku dawo ba sai ranar danace.

Kallan dad kaante yayi cikin bacin Rai Mai tsananin gaske da Bai samu ya fidda ba tin ranarda maganar cikin ta bayyana sai yau din yace

“Yarinyar da zaa daura masa aure da ita ciki ne da ita Kuma nasa haihuwa zatayi a yau din,

Ku sheda matiqar yabar cikin gidan Nan wlh karya dawo ya hada komai nasa daga can wata qasar zai tafi bazai taba dawowaba,

Wannan shine umarnina.

Yana gama fadar Hakan ya bar gurin ransa a bace yabar su dad da Umme da mutuwar tsaye zuciyoyinsu na sanqarewa.

Dad kaante mamakin kusan illata masa numfashi yaso Yi Saida Abbakar ya kamasa da sauri sukai ciki baya ganin gabansa sosai sbd jininsa ya hau Nan take Yana buqatan likita da gaggawa Shima.

Umme ma kusan Yanke jikin tayi zata Fadi DD da Bilal din sukai saurin tarota a tare sukayo ciki da ita zuwa lokacin itama tafara ganin dishi dishi take jininta itama yake Neman hayewa Dayake tanada asthma take taso mata sbd numfashinta Daya tsaya cak na wucin gadi.

Rikicewa jikin ummen yayi kaman kiftawar Ido Dan haka hankalinsu ya tashi musamman Bilal Dayake ganin shine sila.

Likitan gaggawa aka kira Wanda yasaka familyn kaantes din ankara da tashin hankalin da ake ciki Abinda dd babba ya gudara sai gashi ya bayyana Amma a iya familyn.

Ummensu a cikin Abinda Bai gasa awa uku ba ta koma kalan tausayi Amma a hakan ta riqe hannun Bilal tana son Kuka Amma ta kasa tace ya fada mata gskia.

Sunkuyar da Kai yayi cikeda kunyarta data DD dake rungume da ita dayan gefen saidai Kuma bazai iya mata karya ba kokuma gyaran zance Dan haka cikin sanyin jiki da damuwa ya sanar dasu irin tsananin son dayakewa Yarinyar,

Itace farin cikin Daya rasa tin tasowarsa,

Kuma Bai taba Jin sonta ya sauyaba a ransa duk da Abinda ya faru tsakaninsu,

Yana sonta tsakaninsa da Allah fiyeda yanda yake son komai nasa,

Idan zaa barsa ya tafi yayi rayuwarsa da ita ya yarda aturasa kowace qasar ce abarsa da ita.

Maganganunsa suka Sanya Umme da DD yin shiru suna sauraronsa,

Bilal bamai hayaniya da son maganganu bane,

Baka Gane Abinda yake ransa duk tsanani sbd ya iya binne komai cikin ransa

Amma ayau Bilal Yana bayyanarda soyayyarsa ga macenda Allah ya qaddaro masa haduwa da ita,

Wane irin so ne wannan Daya sanyashi yakejin zai iya zabarta yabar ahalinsa.

Umme kuwa Kuka ta fashe dashi a hankali tana girgiza tareda riqe hannunsa gam tace

“Karka tafi ka barni bazan iya rayuwa babu Kai ba,

Karka zabi barina ka tafi,

Kabi umarnin dd babba ka bari ta haihu a daura Muku auren zan karbeta hannu biyu nayi Maka alqawari Amma Dan Allah kada ka karya umarninsa a rabani dakai.

Shiru yayi batareda ya iya cewa komaiba sbd maganganun ummen kashe masa jiki suke Yi Dan ita da sumayyah sune mata biyu dayafi so fiyeda komai a rayuwarsa.

Yanda take rokonsa gata batada karfi ko kadan jikinta yasa DD janyota daga hannuwan Bilal data riqe Yana kokarin Kwantar mata da hankali sbd numfashinta ya far sake kokarin daukewa Yana fizgowa.

Juyawa Bilal yayi yabar dakin sbd baya iya kallan idanuwan ummen tasa Dan damuwa da rashin sanin mafita da zabi.

Kai tsaye Bai saduda ba sbd yanajin sumayyah na tsananin buqatansa ayanzu Dan haka ya sake komawa sashen dd babba Dan rokonsa.

jiki ba qwari yana hada hanya ya Isa kofar palon zai shiga ya tadda kofar Bude Bata qararasa rufewa ba kunnuwansa suka Jiyo masa Abinda ya sanyashi Jin Wani mummunan jiri daukansa.

“Aje da mota akaisu asibiti tana haihuwa da ita da babyn da iyayenta a kaisu inda bazasu sake waiwayo Nan din ba,

Abasu dukiyar da zata hanasu sake tinanin sunyi zama anan ma bare sanin sunan kaantes,

Duka wannan bayan Angama da matsalar Mahaifin nata ta yanda baisan meyake ba bare ya Hana barinsu garin.”

Abbakar ne yake wannan wayar a palon dd babba shikuma ddn bayama Palon.

Wannan umarni ne da dd babba Wanda yasaka ayi Bada sanin Bilal ba ta yanda zai nemeta ya rasa Kuma a satin yakeda niyar daura masa aure da ‘yar babban gidan da yayi Niya.

Jin wannan mummunan zancen yasa Bilal kusan somewa a gurin Saida ya share mintina Bai iya motsawa ba sbd tashin hankali da firgici.

Tsoro ne ya kamasa na Abinda zaa iya Yi din Dan haka qafafunsa na rawa baya Gani ya nufi motarsa wannan Karan cikin saarsa Yana ta-da motar ana Bude gate motar DD da Naseer ya tuqo zata shigo gidan

Bai tsaya jiran komai ba yayi gate Dina guje ya fice bayan motarsa data DD din sunyi kusan kaura har Saida goshinsa ya bugu ya Dan fashe Amma Bai tsayaba yahau titi a guje.

Daga securities har Abbakar da Naseer da sauran jamaan gidan dasuka fito a rikice Basu tadda ko kurar motarsa ba ya bace bat.

******

Bayan sallar magrib ne lokacin Kuma a daidai wannan lokacin sumayyah tayi haihuwar da baa so ta yagata.

Daga babyn har uwar babu me motsi a cikinsu sbd galabaituw mai tsanani da azaba.

A hannun benazir yar ta fado Dan haka jikinta na rawa ta rungume ‘yar maqoshinta na bushewa tareda idanuwanta dake qafewa ganin sumayyah Bata motsaba bare numfasawa.

Anne ma hannuwanta rawa sukeyi idanuwanta na Neman dauke Gani sbd ganin sumayyah kwance idanuwanta a rufe ba alaman Rai a tareda ita ta Yanke cibiyar mahaifar ta fado ko ta kan komai Basu bi ba itada benazir a tare hannuwansu suka Isa jikin sumayyahn suka kira sunanta a tare kowannensu muryarsa na yankewa.

Ababa dayaji shiru sake fadowa dakin yayi Yana Jin tsoro da tashin hankali Shima ya Kalli sumayyahn yaganta kwance babu alamar Rai a tareda ita take yaji jiri ya debesa ya dafa bango

Daidai Nan babyn ta saki Wani irin kukan jarirai Mai karfin gaske tana motsawa da karfi cikin jikin benazir Datake a dunkule.

Kukan babyn yasaka Ababa kallan benazir da sauri muryarsa na yankewa da tsinkewa yace

“Ta haihu kafin ta rasu ne?”

Wannan Kalmar tasa ta saka Benazir da Anne tsayar da hannuwansu daga kokarin sake taba sumayyahn dasuke hannuwan Anne suka fara Wani irin rawa suna jijjigawa numfashinta na Neman tsayawa.

Benazir kuwa ganinta da jinta ne ya dauke take saidai taji Ababa Yana cire  ‘yar daga jikinta Amma Bata ganinsa Bata jinsa hakama Bata iya motsa ko Dan yatsanta.

Hande dake dakinta tana sallar ishai ya Kaiwa ‘yar harya tuntube Dan tayi mata wanka.

Yana fitowa dakin hande dawowa yayi gurinsu benazir din zaiyi magana  yaga gabaki dayansu Suma kaman sun mutu daga inda kowannensu yake zaune

Gabansa yayi mummunan faduwa Dan haka ya fito dakin da sauri Dan dauko fitilarsa ta Mai tsananin haske sbd duhun dakin yayi yawa.

Yana fitowa Anne ta miqe tsaye ta fito dakin batasan Ina take jefa qafa ba ta nufi waje.

Chapter 37

37

Ababa na dawowa dakin ya haska fitila yaga benazir zaune ta sankare da alama Bata hayyacinta ta zaunce ne a take da rasuwar sumayyahn.

Dayan gefen ya haska baiga Annensu ba,

Kokarin haska dakin yafara koina babu alaman Annen

Yana kokarin juyowa yaga kaman sumayyah ta motsa Amma Dayake tashin hankalinsa a yanzu kada Annen tabi hanya yasa ya fice dakin da sauri Yana kwala Kiran sunanta a rikice.

Hande da jaririyar ta isheta da kuka Jin ihun Ababan Yana Kiran Anne yasata fitowa daga daki a rikice rungume da ‘yar acikin zanin uwarta.

Hankali tashe ya sanar da hande Annensu ta bi daji a Daren,

Hande cikin firgici tace

“Mun shiga uku da wannan qaddara,

Daga mutuwa sai hauka ga Kuma jinjirar ‘ya anbarni da ita a hannu wayyo Allah mun shiga uku.

Dakin su Annen ta fada ta fizgo Benazir dake riqe gam da hannun sumayyah suna fitowa tsakar gidan ta dungura mata ‘yar tana fasa kukan sun shiga uku sun lalace ‘danta ya hada iri da Anne me jinin Kaddara baqa iri iri.

Qanqame ‘yar benazir tayi kaman sumayyahnta ce ta qanqame

Ahankali take dawowa hayyacinta tafara Jin sama sama hande da Ababa na ihun Anne tabi daji haukanta ya tashi.

Fizgo tinaninta da hankalinta tayi da qyar tareda shiga girmamammen tashin hankali da masifar rayuwa.

Daqyar taji qafafuwanta a jikinta ta iya motsawa tafara jefa kafa koina ta samu ba nutsuwa ta nufi hanyar bangaren dabbobi Ababan dataga shi da hande sun nufa suna Kiran sunan Annen cikin mamakin ganinta zaune cikin dabbobi tana Kuka kaman ranta zai fita.

Benazir na hango Annen ta qaraso da tsananin gudu ta fada jikinta da babyn a hannu suka fasa Wani tsimamman kukan Daya taba zuciyar hande a Karo na farko.

Kuka sukeyi sosai hande da Ababa na kansu hande na fadan baa yiwa Mamaci Kuka,

Shi kuwa Ababa kokarin Ciro ‘yar daga tsakiyarsu yakeyi kada a kashe masa ita

Ta Daya bangaren baya hayyacinsa Shima kwata kwata sbd rasuwar sumayyahn Neman juyar masa da Kai takeyi,

Kakkarwa jikinsa yakeyi Yana hada gumi Mai tsananin yawa.

Rikosa hande tayi tana kokarin zaunar dashi sukaji motsi can cikin gidan da sauri hande ta sakesa Dan dubowa tana shigowa tsakar gidan bataga kowa ba.

Faduwa gabanta yayi ta waiwaya ta Kalli dakin su benazir saidai bazata iya leqawa ba tayi Ido biyu da gawa Dan haka take tsoro ya Dan shigeta ta juya zata koma Ababa ya iso Yana Neman zubewa qasa sbd jiri da bushewar yawun tashin hankali.

Dakin ta sake kalla tace masa

“A dakin Nan fa Akai motsin dazu fa,

Kodai Bata rasu bane sumayy….Bata qarasa ba Ababa yayi Wani irin zabura ya fada dakin sbd tinawa da dazu kaman yaga motsawanta saidai Yana fadawa ya haska Kansa ya juye take sbd ganin wayam babu sumayyah a dakin koma me Rai koma gawarta.

Hande data biyo bayansa tana ganin babu gawar ta saki Wani gigitaccen salatin dayafi kama da ihun Daya saka Anne da benazir tasowa suka fado dakin gigice tinanin sumayyah ta tashi.

Ganin ba sumayyahn yasa benazir rarraba Ido a dakin tana Neman sake zaucewa.

Anne kuwa fadawa tayi inda sumayyahn take kwance tana lalubawa ko idonta ne Basa ganin gawan Sumayyah hannuwanta suji mata.

Sabon tashin hankalin da Basu saka masa rana bane suka samu kansu a ciki na rashin ganin sumayyah ace ta bace bat idan da Rai idan gawar.

Ababa da Kansa ya gama juyewa tsaf lokacin barin kayan gidan yafara yana Neman haukacewa ya dauko bindigarsa ya fito idanuwansa jajir baya ganin ko gabansa ya fita yafara duba zagayen da kewayan gidan da anguwar ko zai San wane balain da masifar ne ya samu Kansa,

Shin guduwa sumayyah tayi itama kokuwa sace gawarta Akai?

To waye yasan da ita da halinda ake ciki da har zai shigo gidan ya sace gawarta.

Benazir da Anne kuwa zuwa lokacin Kuka ma Wani gata da arziki ne dayafi karfinsu,

Kukan sukeson Yi Amma babu hawayen idanuwan sun bushe bayan kukan babyn Dayake cika gidan babu me iya ko motsi sbd girma da tashin hankalin lamarin.

A inda benazir take zaune cikin duhun dakin rungume da babyn da har lokacin Bata samu an mata wanka ba,

Qamshin da hancinta ya shaqar mata ne ya sakata miqewa a zabure tana tabbatarda Alh Bilal ya shigo gidan.

Fitowa tayi daga dakin Anne ma ta biyota kaman zariya suka fara ware idanuwa a tsakar gidan cikin duhu Amma Basu ga kowa ko komai ba Dan haka Suka koma bakin kofar dakin suka rakube suna jiran dawowar Ababa da Koda gawar sumayyahn ne.

Shiru shiru babu Ababa babu labarin dawowarsa Yana can yabi hanya Baya hayyacinsa gurin Neman sumayyah ko gawarta,

Tin yana yawon dubawa cikin anguwar harya fice anguwar Bai saniba kaman tsohon mahaukaci haka yakoma acikin tsakar Daren.

Hande dataji jaririyar ta kasa Dena Kuka Kuma makotan kusa zasu iya Jin kukan su San da haihuwar dole ta fito ta karbi yar ta shiga dakinta da ita acan tayo mata wanka ta saka mata kayan da Ababa ya siyo na haihuwar ta fito ta miqawa benazir ita ta sake komawa dakinta sbd sanyi illa zai mata da tsufanta.

Benazir da Anne kuwa suna tsakar gidan Basu motsaba ko Nan da can suna jiran dawowar Ababa zuciyoyinsu na Wani irin tsallan tashin hankali mara misali.

Babyn a cikin hijabi benazir ta sakata ta dunkule sbd sanyi tin tana Kuka har ta Dena tayi shiru tana baccinta da jarirai.

A rayuwarsu Basu taba shiga tashin hankali irin Daren ba,

Yanda suka ga Rana haka sukaga Daren gurin Jiran tsammanin tashin hankali,

Kiran Asuba Akai aka gama har Akai sallah aka fito babu labarin Ababa Suma babu alaman zasu motsa har gari yayi haske tukuna Benazir taja Anne da babyn a dayan hannunta sukaje sukai sallah suka sake fitowa babu me iya ko tsayuwa a cikinsu sbd fargaba da tashin hankalin.

Karfe 6 na safe Ababa ya shigo gidan ko Gani bayayi Yana kawowa tsakar gidan ya yanke jiki ya Fadi.

Hande da gudu tayi Kansa tana fashewa da kuka

Benazir da Bata gansa da sumayyah ba itama sarewa qafafunta sukai ta zube a gurin durqushe tana Neman Kuka ya taho mata ko zata samu sassaucin Abinda take ji a cikin kirjinta.

Anne kuwa a wannan lokacin Ido kawai ta zubawa benazir tana kasa motsawa bare iyayin kukan itama.

*********A Kaantes ma a tsaye suka kwana kan ummensu Bilal data rikice gabaki Daya sbd zuciyarta Datake tsinkewa tana shiga tsoro da firgici akan ‘danta.

Duka wayoyin Bilal din Basa shiga hakama ga ummen asthma ya tashi gabaki Daya kaman wadda ta jima tana jinya kiransa DD keyi Yana qarawa Amma Sam wayoyin Basa shiga.

Hakan yasaka dole DD a ranar ya kwana cikin KAANTES Bai tafi gidansa ba,

Dad kaante ma hankalinsa yayi mummunan tashi shikuma dayaga baa samun Bilal din Kuma har tsakiyar dare har Asuba har safiya Bai dawoba Dan haka Suka Yanke shawarar Neman Ababa.

Zazzaune suke jigum jigum kaman gidan makoki a palon dd babba suna jiran dd babban ya kira Ababa Wanda shikuma aketa kira baya dauka.

Daga DD har dad kaante dashi Kansa dd babba harma ummensa zuwa lokacin hakurinsu yafara qarewa suna buqatan Jin komai gameda haihuwar da zuwan Bilal din dama Asibitin da suke.

Kokarin sake saka Kiran dd babba yayi daidai Nan wayar dad kaante tayi ringing cikin zaquwa ya daga Kiran ganin number sbd ko Bilal dinne Dan haka kawai wannan Karan suke Jin yanayi mara Dadi akan lamarin nasa.

A kunnensa ya Kara wayar tareda cewa hello da sallama.

Wani bayani aka fara Koro masa Daya sakasa yin shiru Yana kasa tanka kalma ko Daya sbd jinsa Daya fara daukewa kafin ganinsa.

Subucewa wayar hannunsa tayi yafara kokarin Kai hannunsa kirjinsa ya Dafe zuciyarsa Amma Bai karasa Kai hannunba ya Yanke jiki ya Fadi

Abbakar da DD sukai Kansa shi Kansa dd babba zuwa lokacin gab yake da samun attack Dan haka da sauri Abbakar ya dauki wayar dad kaante din ya miqawa Dd babba Amma ya girgiza masa alaman ya amsa wayar.

Cikin karfin hali da jarumta Abbakar ya gama sauraron bayanin da jamian tsaron suka gama jerowa ya kashe wayar zufa na tsinke masa sharkaf tareda tsananin tausayi da jimama harma da tashin hankali Amma Kuma ba dalilin boye zancen tinda dole aji,

Sauke Kansa yayi cikin raunin murya da tsananin bayyanarda damuwa yace

“Sir Bilal ne ya samu hadari motarsa ta Kone kurmus,Ansamu konanniyar gawarsa a m…..

Bai qarasa ba suka ji Wani irin Kukan Umme Daya saka kaantes din dauka tsit baka Jin motsin komai.

Mum Khadija ce matar qanin dad kaante dasuka iso gurin tare ta riqota jikinta na daukan rawa itama da mummunan labari tashin hankalin da babu wanda ya saka masa rana.

DD kuwa kasa gasgata Abinda aka fada din yayi sbd yanda jikinsa yake wata irin rawa idanuwansa dake farare masu tsananin kwarjini take sukai jajir ya fice palon da sauri ko gabansa baya Gani ya fito Ya nufi motarsa Naseer Dayake shigowa Yana hangosa ya taho da sauri ya Bude masa motar Bai tsaya cewa komai ba yace su nufi hanyar barin gari inda accident din ya afku.

Umme kuwa Wani irin Kuka takeyi Dayake tayarda tsikar jikin Masu jinta

Dad kuwa tini Akai part dinsa dashi sbd likitocin da aka kirawo har biyu da zasu dubasa Dan take numfashinsa ya tsaya.

Dd babba ma zaune yake Amma duk ilahirin hannuwansa da kafafunsa rawa sukeyi,

Zuciyarta tayi nauyi baya iya motsawa kowane lokaci attack zai iya samu Dan haka Shima take akai ciki dashi Dan jiran likita.

Zeenah dake Kuka sosai da mum Khadija harma da wasu daga masu aikin gidan suka kama Umme Akai ciki da ita,

Bata taba saka ran mutuwar danta ce ta sanyashi fita yabar gida ba da bazata bari ya bar ko kofar part dinta ba,

Irin Kukan datakeyi ne yasa mum Khadija fashewa da kukan tausayinta sbd kowa ya sheda soyayyar dakewa danta wadda ya kasa samu gurin kowa daga familynsa.

*****Koda DD ya Isa Shima Saida ambulance tazo ta daukesa daga gurin da hadarin ya faru sbd gawar Ta Kone kurmus ta yanda baa ganeta motarce kawai ake iya Ganewa itama sbd kafin konewar da alama ya daki Wani abin ne lambar motar ta fita harma da baya motar Shima ya balle ya fita.

Hakan yasa Akai saurin Ganewa aka kirasu sbd matsayinsu.

Rasuwar Bilal kaante a cikin Bata rufa awa biyu ba labarin ya bazu koina

Aka fara kokarin saka lokacin janaiza, manyan mutane kuwa tini suka fara kira da Kuma fara Siyan tickets na zuwa gaisuwa da janaiza.

*****A lokacinda labarin rasuwar ya shiga kunnan Ababa a lokaci Daya shi da benazir wannan Karan suka Yanke jiki suka fadi sbd sani da tabbacin Data Basu na cewan Bilal ne ya dauke sumayyah.

Anne da zuciyarta ta qyame kyam a tsakanin Daren jiya zuwa safiyar itace ta zubawa benazir ruwa ta farfado itama tata zuciyar na qamewa tana tashi daga tsoka.

Ababa kuwa Yana farfadowa ya sake yanke jiki ya Fadi sbd ta tabbata sumayyah da Bilal sun mutu sun bar duniya.

Chapter 38

38

Benazir data kasa yadda da sumayyah ta tafi barsu rawa dukkanin jikinta rawa yakeyi ahankali tana kasa Jin hawaye ko Daya cikin idanuwanta,

Bakinta da makoshinta Wani irin bushewa sukai tana kasa samun yawu ko kadan cikin bakin da moqoshinta.

Babyn dake jikinta ce ta motsa ahankali

Hannuwanta dake rawa ahankali tasaka ta sake rungume ‘yar tana sake Jin zuciyarsa, idanuwanta da bakinta na bushewa sbd su ‘yar uwarsu,Rabin jikinsu suka rasa ita Kuma babyn uwa da ubanta ta rasa a lokaci Daya.

Ababa Da ake kokarin kwasa zuwa Asibiti Anne ta kalla da idanuwanta dasukai jajir Amma babu Wanda ya samu Kuka a cikinsu sbd basuda sauran Abinda suke ji a zuciyoyinsu dasuka sanqare,

Hande Kuka takeyi tana qarawa akan kada ta rasa ‘danta,

Mutane ta samo aka shigo aka dauki Ababan zuwa Asibiti cikin tashin hankalin kada a rasa shi.

A wannan lokacin ne Wani irin kukan da Bata San dashiba ya zuwar mata dukkanin jikinta na rawa da jijjjiga ganin ita tata ‘yar kusan mutuwa tayi cikin tsananin wahala baa damu da akaisu asibiti ba har aka rasata gashi yanzu gawar ma sun rasa a lokacinda suke sakaran Bata mutu ba Kuma labarin hadarin ta da mutuwarta da Bilal yasake tsinka fatansu,

To su kuwa a yanzu meye suke da Wani buqata ko fata bayan mutuwar Suma su huta,

Ga sabuwar Alhaki Allah ya sake jefo musu a cikin wannan lokacin da Suka gama sarewa gabaki Daya da duniyar da rayuwarma.

Benazir na Jin kukan Anne na shiga zuciyarta yana yankan Amma Bata iya matsawa saima sake rungume babynsu datayi tana Jin a yanzu da babu shigowa wannan babyn rayuwarsu da babu Abinda zai hanasu samun bugawar zuciya a ayau din su mutu su huta Amma duk motsin da babyn keyi jikinta Jin sumayyahnta takeyi a jikinta da zuciyarta Dan haka take sake qanqame babyn.

Kukan da Anne tayi Mai tsananin gaske Bai rage mata komai na nauyin da takejin zuciyarta tayi mata ba Dan haka ta share hawayenta ta miqe tsaye ta kama benazir din itama ta tayar da ita suka koma dakinsu.

Suna shiga Annen ta hau tattara dakin ta kwashe kayan da sumayyah ta haihu Akai ta fito dasu ta debo ruwa tahau aikin wankewa batareda ta furta kalma ko Daya ba.

Tana gamawa ta dawo dakin ta gyaran musu shi tas

Har lokacin benazir na zaune rungume da ‘yar Bata motsaba idanuwanta a bushe.

Anne ma da aikin fitan hayyaci takeyi tana gama gyara dakin ta fito ta share tsakar gidan ta gama ta Dora ruwan zafi suna tafasa ta juye tayo dakin dasu ta ajiye ta Kalli benazir tana miqa hannu zata karbi babyn tace

“Kawota a sake mata wanka”

Sai alokacin benazir ta dago da busashin idanuwanta ta Kalli Annen tsawon mintina

Take a lokacin siraran hawayen tausayin mahaifiyarta suka gangaro mata sbd tasan baa cikakken hayyacinta take ba.

Hannu Daya ta saka ta share hawayen tareda daurewa ta dawo hayyacinta ta Kalli Annen ta girgiza mata Kai ahankali tana Ciro babyn daga jikinta ahankali tace

“Zan Yi mata Anne ki zauna ki huta”

Hakan data fada ya saka jikin Annen sanyi sbd tasan tsoron Bata yar takeyi sbd tinanin Bata hayyacinta kada ta jefata cikin ruwan zafi.

Dan haka Bata Musa ba ta juya ahankali ta koma gefe ta zauna tana kallan benazir zubawa benazir da babyn Ido.

Hannuwa na rawa da tsoron rashin iyawa Benazir tayi qarfin halin yiwa babyn wanka hannuwanta na tsananta rawa.

Bayan ta gama mata duk ta jiqa jikinta da gurin.

Ta miqawa Anne babyn Dan ta samu miqewa ta kwashe kayan wankan

Anne ta girgiza mata Kai tareda cewa ta riqeta kawai bari ita ta kwashe kayan.

Kayan ta kwasa ta fitar ta dawo ta goge gurin tana gamawa ta karbi yar benazir ta sauya kayanta sbd kada sanyinsu ya damu babyn dake jikin nata

Tana gama saka kayan ta fice tayo alwala sbd lokacin sallar azahar da yayi tini.

Tareda Anne sukai sallah babyn na tsakiyarsu shimfide.

Suna idar da sallah suka fara jerowa sumayyah addua zuciyoyin kowannensu na dakewa da qarfafa tawakkalinsu,

Gawarta ma Basu saka ran Gani ba sbd zuwa lokacin sun sani an hadata da Bilal anrufe tinda danginsa sun San ita zai aura,

Basuda masaniyar komai sai Ababa ya dawo yajiyo idan gawar zaa Basu kokuma an rufeta tini.

Babyn suka zubawa Ido dukkaninsu suna qarewa fuskarta Kallo zuciyar benazir na karban duk Wani feeling akan babyn.

Sai alokacin takejin ‘yar cikin ranta sbd dama da sumayyahn na Raye da Bata Nan ‘yar sumayyah ‘yarta ce,

Cikin ne kawai Bata dauka ba da haihuwarsa Amma kusan duk Wani wahala,Reno,farin cikinsa da baqin cikinsa Dede sukaisa da sumayyahn a yanzu Kuma ta tafi tabar mata ‘yar bayan tazo duniya.

Anne kuwa miqewa tayi ta fito ta Dora musu abinci duk da tasan ba cinsa zasu iya ba Amma dole zasu rayu suci gaba da rayuwa sbd ‘yar sumayyah data barmusu Dan haka komai a yanzu ba Dan kansu zasuyi ba sbd babyn zasuyi.

Tana gamawa ta tilasta benazir suka zauna suna cusa abincin a dole

Suna gamawa sukai sallar laasar

Lokacin babyn tafara Kuka sosai tana Neman Nono.

Kukanta ya saka radadinsu dasuke dannewa Neman tsinkewa Amma Anne ta daure ta shiga dakin Ababa cikin kayan haihuwar Daya Tara ta samo ruwan zamzam suka taho suna cikin bawa yarinyar Aka dawo da Ababa a jeme ya zabge cikin wuni Daya.

Hande ma har lokacin kukan takeyi Akai Akai.

Gidan tsit ya dauka kowa na jimamin mutuwa da rashin da sukai gashi kaman yan kankan Kai baa ma San anyi mutuwa ba gidan bare a shigo musu gaisuwa tinda baa ga ana janaiza ba bare karban gaisuwa.

Ababa Dayake fama da Kansa Jin kukan babyn yayi yawa yasa jamilu yaronsa siyo madarar jarirai gwangwani uku da ruwan roba Katan Daya.

Ana kawowa aka bawa benazir batareda an sanar da ita yanda ake bayarwar ba.

Dayake babyn tafara galabaita Bata tsaya Bata lokaci ba itada Anne suka dafa ruwan zafi suka hada mata a fidar dake cikin kayan haihuwar da hande ta watso musu daki bayan dawowar tasu.

Ana sakawa jaririyar fidar farko kasa kamawa tayi dai daga baya Anne ta karba ta ringa diga mata madarar cikin baki tukuna ta Dan fara motsa bakinta madaran na shigewa.

Hawaye masu zafi ne suka gangarowa benazir lokacin da babyn ke Shan madaran tana motsawa ahankali batareda tasan Tayaya zasuyi rayuwa da babyn a haka ba.

A haka suka kwana zaune gidan babu Wanda ya iya kwantawa bare ya iya rintsawa sai hande kawai Amma Ababan ma a zaune ya kwana cikin ciwon zuciya Dayake Neman Kaisa lahira a kwana daya da wuni biyu.

 Har safe zuciyarsa cikin mummunan hali take ciki Yana saka da warwara Dan kuwa yasan ya tabbatarda sumayyah akwai Abinda dai yake qasan bacewarta bat,

Gawar da aka samu cikin motar Bilal kaante guda Daya ce bayan biyu ya kamata a gani idan Kuma drivernsa ne ya tuqosa gawa uku yakamata a gani Amma Daya aka samu wadda Suma jamian tsaron kaman wainda aka Basu San aikinsu ba baida tabbacin anduba gawar an tabbatarda ya waye.

Zafin da Kansa ya dauka ya sakasa kasa tantance komai bayan tabbatarda koma meyake qasan wannan lamarin Bai lalata komai nasa ba ya janyo masa lukutar masifar dazata Kaisa qasa.

Dan haka da safe bayana ya sake samun saukin dawowa hayyacinsa Ya Yanke Wani mummunan kudirinsa akan Abinda yayi Niya Dan haka Yana fitowa Abinda yafara shine sanar da benazir da Anne dake jiransa akan maganar sumayyahn cewa anriga anyi janaizarta tareda Bilal tin jiyan addua da fatan samun rahamar ubangiji kawai zaa ringa mata harma da Bilal din.

Daga Anne har benazir ga mamakinsa babu Wanda ya some masa kaman yanda ya tsammata,. Abinda Bai saniba sun riqa sun Riga zuciyoyinsu sun bushe sun saddakar sun karbi kaddarar mutuwar sumayyahn tin jiyan dan haka suna samun tabbacin daga bakinsa suka sake daukan taurin zuciya suka sawa kansu.

Ababa kuwa Daman Hakan yakeso Dan haka shiryawa yayi ya nufi KAANTES gurin gaisuwa da sanar dasu an haihu lafiya kalau.

*******A Kaantes ana cikin tsananin hali da qunci da baqin cikin rasuwar ta Bilal wadda kusan duka ta taba iyayensa da kakan nasa da basusan suna kaunarsa ba sai a yanzu da bayanan yabar musu duniyar Dan haka dukkaninsu babu Wanda yake zaune da qafafunsa a kwance suke ba lafiya hakanan ake daurewa ana karban gaisuwar daga manyan mutane da baqin dake zuwa na kusa Dana nesa.

DD kaante ma rashin lafiya ce a jikinsa sosai sbd Bilal Wani bangare ne na jikinsa da bayan iyayensa shine halittar dayafi tsananin so a duniya,

Rashin Bilal lokaci Daya ya girgiza duniyarsa da Bata taba girgizuwa ba,

Dan haka tin ranar da Bilal din Ya rasu Yana bangarensa Nan kaantes Yana fama da Kansa Shima

Sai likitan dake zuwa dubasa kullum ko gurin karban gaisuwar baya iya fitowa.

Ababa Koda ya iso baisha wahalan shigowaba sbd Abbakar dake gate Dan haka Kai tsaye Akai masa iso ciki.

A palon dd babba ya zauna cikin jimami yafara yiwa dd babban gaisuwa kafin yayiwa dad kaante da sauran uncle din Bilal din dake gurin.

Amsa gaisuwar sukai kafin Shima ya zauna cikin yan karban gaisuwar Yana bayyanarda jimaminsa harda Kuka sosai Wanda yasaka dad kaante Ganewa da shine Mahaifin yarinyar da Bilal din su ke tsananin so harya rasa ransa akanta.

Ganin suna cikin jamaa ya Hana dd babba da dad kaante tambayan idan ‘yar Ababan ta sauka lafiya ita.

Ababa da Kansa ya bayyanarda Yana son yiwa ummen Bilal gaisuwa babu musawa Abbakar yayi masa jagora zuwan babban palon dad kaante aka shiga aka kirawo ta.

Zata fito DD na shigawa palonta sanye cikin black Balmain jumpsuits kyakyawan fuskarsa fresh a kame kaman baa tabawa da hannu

Duka masu masa gaisuwan Bilal din Daya shigo amsawa yayi a takaice cikin nutsuwa batareda ya tantance su waye da waye ba duk da harda mummyn Sbb amaryasa aciki.

Ganinsa yasaka Umme hadiye hawayenta tana kama hannunsa Daya miqa mata Dan kuwa yanzu shine sanyin idaniyarta.

Tare suka juya zuwa palon dad kaante suna shiga qamshinsa yafara ankarar da Ababa ba haj fatman bace kadai ta shigo Dan haka ya dago idanuwansa daidai tsayuwar DD a palon ya zubawa Ababa idanuwansa a Karo na farko Daya zubawa Wani idanuwansa Yana kallan tsaf.

Kwarjininsa yasa Ababa miqewa tsaye  daga zaunen Dayake bakinsa na Tara masa yawun dazai hadiywa maqoshinsa Daya bushe sbd tabbatarda wannan shine DAWOOD KAANTE din da duniya tafi sani akan duka sauran ‘yaya da jikokin gidan,Kuma qanin Alh Bilal.

Rawa hannuwansa suka dauka take baisan lokacinda yace

“Nine Mahaifin Benazir,

Yarinyar da Alh Bilal zai aura kafin afkuwan wannan kaddarar ta rashinsa”……

Daga Umme har DD a tare suka sake sauke masa idanuwansu bakin Umme na rawa tace

“Ta haihu?

Me ta….. Bata qarasa ba Ababan ya katseta da cewa

“Ta haihu lafiya ta samu ‘ya mace Kuma duk suna lafiya uwar da ‘yar.”

Daidai Nan dd babba da dad kaante dakeson magana dashi din suka shigo Kuma a kunnesu zancen an haihun ya sauka.

Wani kukan da Umme batasan ko na menene ba ya kunce mata tana Jin bayan babyn a yanzu baby Abinda take buqatan a kawo mata tagani.

Ababa kuwa take ya Yanke shawarar benazir ce uwar yar Kuma babu Mai sanin ba ita din bace matiqar Yana Raye.

Chapter 39

39

Dd babba ne ya shigo dad kaante na bayansa suna kallan Ababan a tare sbd Jin Abinda ya fada zuciyoyinsu na karban sakon nasa da sanyi batareda sun ankare ba.

DD kuwa Dan rintse idanuwansa yayi Shima a hankali sakon na sanyaya zuciyarsa duka batareda sun saniba Dan kowa tashin hankali yasa sun manta da akwai jinin da Bilal ya bari duniya,

Sun cire Rai daga samun Abinda zai dawwamar musu da kaunarsa da soyayyar da suka kasa nuna masa sai gashi Allah ya dawo musu da jinin Bilal tsatsonsa.

Daga dd babba har dad kaante suna zaunawa kallan Ababa Dayake star kallansu Daya bayan Daya sukai

Dd babba na sake sauke ajiyar zuciya a Karo na babu adadi sbd Bayajin Dadi sosai tin lokacinda rasuwar Bilal din ta riskesu babu me isashiyar lafiya a gidan.

Ahankali dd babba ya Bude baki yace

“Abinda aka samu din lafiya take itama?”

Gyada Kai Ababa yayi cikin zumudinsa Dayake boyewa Yace

“Lafiyarta kalau daga ita har uwar”

Umme ce ta Bude baki cikin hawaye masu sanyi ta zube gaban dd babba cikin bayyanarda quncin ranta da qanqantar da kai tace

“Babba Dan Allah a kawo min Babyn Bilal ni ta kowace hanyar aka sameta Ina sonta a hakan,

Ina buqatan ta a hakan,

Zan reneta a hakan,Dan Allah kabada Daman a kawo min ita sbd ita kadai ce jinin Bilal dazata maye mana gurbin Daya bar mana….kukane yaci karfin Mai qaramin sauti da cin zuciya.

Dad kaante ma kallan dd babba yayi cikin rashin qwarin gwiwa Dana jikinsa da ba lafiyar Shima yace

“Ta hanyar dawo da ita Nan zamu ingatanta rayuwarta yanda ya dace harma da Hana kowa sanin matsayin nata tinda da Yana Rayen a yanda kayi alqawari ranar sunanta ranar daurawa iyayenta aure.”

Shiru dd babba yayi Yana sauraronsu Wanda ko Basu roqa din ba a yanzu da Bilal baya duniyar bazasu banzatar da jininsa Daya qwal Daya bari ba a duniyar sbd jininsu ce Kuma itace a yanzu zata maye gurbinsa a zuciyar mutane da yawa a familyn.

Ababa zufane ya fara tsatsafo masa cikin rigarsa Yana kallan bakin dd babba yaji Abinda zai fada akan roqon iyayen Bilal din.

DD ne ya katse musu zancen Kai tsaye a natse da cewa

“Akwai buqatan Wani tinani ne Daman akan dawowan babyn hannun mu?”

Muna buqatan sai muyi nazari ne akan Hakan?

Kai tsaye daga lokacinda ya fado duniya ita din ta zama kaantes,

Akwai dalilin barinta Wani gurin ne daga lokacin da ta amsa sunan?

Shiru iyayensa sukai sbd shi Daya ne Daman yake fadan maganarsa a tsaye gaban dd babba ba acikin raini ko rashin daa ba Amma shi Sam baya kwana kwanar magana ko inane kuwa yinta yakeyi Kai tsaye ta gaskia da gaskiarsa.

Ababa kuwa Jin ana nanata maganar karban baby dai,baby dai baby dai sai kawai ya Dan gyara Yana kallan DD Da kyakyawan fuskarsa yake a kame duk da idanuwansa sun Dan fada a kwana dayan.

Dd babba cikin sanyi ya Bude baki cikin Yana kallan Ababa yace

“Kaji dai ko malam Ababa?

A kawo mana yarinyar zamu karbeta tinda dai a yanzu mutuwa ta shiga tsakani Allah beyi zamu cimma manufar hada iyayenta aure ba.

Hummmmmnnn” Ababa ya sauke Wani boyayyan numfashi Yana Jin Kansa na daukan zafi Amma dai ya daure yana daidaita Kansa.

Dagowa yayi idanuwansa taf da hawayen da baisan lokacinda ya janyosu take ba.

Cikin rawar muryar sautin kukan Dayake daurewa ya kallesu su dukan yace

“Wace jaririyar zaku karbe?

“Yar dake jikin uwarta zaa rabasu kwana daya da haihuwa?

Anyiwa “ya ta adalcin rabata da ‘yarta  acikin wannan halin Datake ciki na rasa mijin aurenta?

Tayaya idan tayi aure Nan gaba zata kasa nunawa mijinta tana da wata ‘yar a Nan?

Wannan zancen ai bazai binnu a Hakan ba,

Abar mana babyn Nima Ina kaunarta zan rungumi kaddara mu Reneta idan uwarta ta samu Muji zuwa gaba tayi aure taje da ita can sbd bazamu bar ‘yar ta tashi babu Uba ba anan ne zaa San Yaya ‘yar take Kuma waye ubanta Koda baya Raye,

Idan mutane suka shegantamun jika kokuma shi Wanda uwarta zata aura wataran ya sheganta mini ita nayi muku alqawarin bazan bari ba zan dauki mataki Kuma zan kula sosai da wannan babyn Amma kuyi hakuri bazan iya bari ku qwace mana ita ba a rabata da uwarta bayan wahala da gwagwarmayar da uwarta Tasha daga renon cikin zuwa haihuwarsa.

Yana gama fadan maganganunsa ya musu gaisuwar Bilal tareda sallama ya fuske ya juya Yana share hawayensa alaman iya gaskiarsa yake fada a matsayin Uba Kuma kaka.

A zuciyarsa kuwa qyam yake sbd yasan madokarsu Kuma itace ya doka Dan haka gida zai komawarsa Yana zaune zasu sake nemansa da yardar Allah.

Yana ficewa hawayen Umme suka qara gudu ta miqe tana ganin jiri tabar palon zuciyarta na nauyi.

Dad kaante ma kallan dd babba yayi jikinsa na mutuwa da zantikan Ababa Amma Kuma koma mene Suma suna buqatan ‘yar ai a matsayinsu na kakanninta dasuka rasa mahaifinta.

Dd babba kuwa Jin Ababan kawai yayi Dan kuwa maganar komaima Bata tasoba yarinya bazata taba zama a wajen kaantes ba.

DD ma ficewa yayi daga palon sbd a nasa bangaren Shima yasan maganar barin jinin Bilal dinsa a Wani wajen ma har ana lissafin zuwanta agolanci tin yanzu ai baima San Hakan ba.

Babyn tagama dawowa hannunsa saidai uwar babyn ta hakura.

Ababa kuwa Yana fita Zeenah ta fice da driver suna fitowa ta karbi key tace ya jirata a hanya zataje ta dawo.

Bayan Ababa Zeenah tabi tiryan tiryan har gidansa.

Saida ta Dan jima a gurin cikin mota ta tabbatarda gidan ne kafin ta juya motarta tabar gurin.

Driver ta dawo ta dauka suka koma gida Kai tsaye gurin umme ta nufa daki ta sanar mata da ta gano gidan maman Babyn Bilal din.

*****Ababa na Isa gida shigewa yayi ya zauna palonsa ya rufe kofa ya fara warware tinani da abubuwan dake cikin qwaqwalwansa Dan ya huta shi Kansa sbd Kansa ya gama daukan zafi ya dauko maganar da baisan inda zata Kaisa ba tsakanin Ababa da Nobaba.

Amma dai koma yayane a mutu ko ayi Rai babu Wanda ya haifi wannan babyn idanba benazir ba ko duniya ma bazai yarda ta saniba bare kaantes.

Karatunta kuwa daga wannan lokacin babusa Dan kuwa haihuwa tahau kanta,

Su kuwa kaantes ba hawan jini suke fama dashi ba ko saukan jini ne bazai bayarda babyn ba matiqar bada uwar babyn zasu amsa ba.

Benazir da Anne a daki kuwa zaune suke shiru babu komai sai jaririyar dasuke lallabawa kaman Basa son ko motsata sbd so da kulawa.

A yanda rasuwar sumayyah tazo musu da har ita har babyn suka rasu da ba lallai su samu qarfin wannan tawakkalin ba Amma Suma kansu a yanzu sunsan Wani irin dangana ne da Basu taba tinanin zasu iya samu ba Allah ya Sako musu.

A jikin benazir babyn take kowane lokaci sbd ita yanzu so na tamkar itace ta tsuguna ta Haifa babyn takeji Wanda Daman ko sumayyah na Nan tasan zata mata wannan son,yanzu Abinda yasa yafi qarfi da tsanani sbd batada uwa batada Uba sai su kokuma tace sai ita tinda Anne Allah ne kawai yasan yaushe da yaushe ne take daidai bare ta nuna mata soyayyar kaka.

Saidai Abinda Bata saniba ba kaman yanda take Jin yar cikin tsakiyan ranta kaman sumayyah ce a hannunta haka Anne ke Jin ‘yar itama cikin ranta kaman sumayyahnta ce ta dawo musu a matsayin jaririya Dan haka kallan ‘yar kawai idan tayi sai taji zuciyarta na Neman narkewa ta fashe da kuka shiyasa take Dan dakatar da kanta tana barwa benazir sbd itace uwarta a yanzu da babu sumayyah Dan tanada tabbacin akanta benazir babu sadaukarwar da bazata iyaba a ciki gidan tinda Suma dasuke manyan tana musu tin baya.

Sai yamma Ababa ya fito bayan ya cire kayan dayaje dasu kaantes ya Sako wainda yafi sabawa da sakawa na yadika marasa nauyi su kuwa idan zasu uwar shadda yakesha harda babban Riga sbd nuna mutincin Kansa.

A tsakar gidan ya janyo kujerarsa ta roba ya zauna gefen hande da itama zamanta kenan tsakar gidan kan tabarma ta fito Tasha iska sbd Kuma ta kasa ta tsare Basa buqatan bako kowane iri ne Dan kadama a ankare da halinda suke ciki na haihuwar banza a gidan.

Ita yanzu fatanta tinda sumayyah ta rasu tabarwa su benazir ‘yar so take Ababa ya samowa benazir koma waye ya daura mata aure dashi benazir ta tafi da ‘yar can su qarata gidan auren a huta kada yarinya ta girma jamaa su rasa inda aka samota idan Kuma auren bazai yiyuba to gwara tin wuri ace Anne ta haihu ta yanda ko yar ta girma babu Wanda zai San shegu suka fara haihuwa a gidan Suma Dan daga wuyan dasukewa mutane ya fadi.

Shi dai Ababa duk tinanin hande nata ne kawai nasa tinanin da burin daban Kuma nasan shine magana tinda shine me Yanke yanda yakeso ayi.

Abinci yayi Kiran Anne ta fito ta kawo masa sbd Bai samu Daman cin abincin Rana ba Yana ciki Saida yagama lissafe.

Ajiye masa abincin tayi zata bar gurin ya Kalli kofar dakinsu yace

“Uwar me benazir takeyi a ciki da ‘yar Amanata duk sai zafi da sauro ya cinyeta daki kaman dakin boka tsabar duhu da kaya.”

Ahankali Anne ta Dan kallesa kafin ta Bude baki tace

“Idan anfito da ita waje akwai sanyi zai iya kamata”

Ajiye abincin Daya dauka zai fara ci yayi ya Kalli hande data matse fuska yace

“Wai hakane hande?”

A siqe handen tace

“Eh Amma Kuma ai da uwar datayi naqudar ‘yar ce zaa ce kada ta fito dakin sanyi zai iya shigarta……

Katseta Ababa yayi Yana dire abincin hannunsa da qarfi yace

“To waye ne yace uwar datai naqudarta ta haifeta Bata gidan.?

Da sauri dukkaninsu suka miqe suna waiwaye hande cikin fargaba da tsoro Anne kuwa cikin mamaki da firgicin itama

Hakama benazir take ta fito dakin rungume da babyn Yana raba idon son ganin sumayyah da Ababa ke maganar.

Kallan benazir data fito yayi yana sake fuska sbd lissafinsa da gabaki Daya yanzune zai hau daidai idan komai ya tabbata yace

“Kunga uwarta Nan wadda tayi cikin tayi naqudar Kuma ta haihu”

Chapter 40

40

Dakatawa daga dube duben dasukeyi kowanne cikin tashin hankali da firgici suka dawo da kallansu a Kansa gabaki dayansu.

Baki sake hande tace nashiga uku yau ina Shirin ganin baqar Rana,

Ciwon qwaqwalwa ka samu Ababan khairi??

Mutuwar sumayyahn ta taba ka hakane bansaniba?

Benazir ce fa a gabanka,

Gizo sumayyahn ke Yi Maka ne?

Qalu innalillahi.

Anne da benazir kuwa tsayawa sukai cikin mamaki da fargaban maganar hande kodai gizo sumayyahn ke Yi masa sbd wahalan dasuka Sha a hannunsa.

Shiru yayi musu Saida hande tagama tsoki burutsun zancenta ta saurara taba kallansa da mamakin ganin hankalinsa kwance Bai shiga tashin hankali ba.

Tattaro duka nutsuwa da hankalinsa yayi ya fara kallansu Daya bayan Daya yaga su dinma dukkaninsu hankalinsu na akansa.

Akan benazir ya tsaida idanuwansa yafara da cewa

“Ke kina son ‘yar hannunki kuwa?”

Shiru sukai hande na sake shiga mamaki hakama Anne dagowa tayi ta Dan kallesa ahankali sbd Jin tambayar abinda bama sai anyi tambayar ba sbd ansan amsar.

Shiru benazir tayi tana kasa ko motsawa bare iya magana Dan kuwa fadanma tana son babyn hannunta kaman ragewa Miya gishiri ne.

Tsuke fuska Ababa yayi Yana fara hasala a siqe yace

“Ba tambaya nayi bane?kuka tsaya mun kaman wasu gumaka.”

Ahankali benazir ta gyada Kai batareda ta dago kan ba.

“Bakinki Zaki Bude ki ban amsa kan na tashi na fasa bakin ki a gurin”

Cikin sanyi Kai tsaye ta Bude baki a natse tace

“Eh Ina kaunarta sosai.”

Wani zafaffen tsoki ya sake Yana Hana zuciyarsa fusatan da zata sanyashi tashi yayi mata dukan fita hayyaci sbd a ciki ‘yayan hudun kaf Bai qaru da komai dasu itace last hope dinsa Kuma itace wadda zata kasance mukullin samunsa Dan haka yake sake tausan zuciyarsa Yana Hana kansa Dora hannu akanta.

Bayason rufa rufa ko batawa Kai lokaci har Wani lissafin ya kunce masa Dan haka ya sake hade fuska sosai yace

“Dukkaninsu ku Bude kunnuwanku da hankalinku harma da nutsuwarku ku saurari Abinda zan fada sbd magana ce da fitarta ko bayyanar gaskiyarta daidai yake da masifar da mutum bazai iya dauka ba.,

Hande ya kalla datake kallansa a matse da son Jin meyake faruwa da Ababan ne yace

“Ki nitsu hande kijini da kyau,

Kema me ciwon qwaqwalwa ki nutsu ki Jini Kuma ki fahimceni dakyau Dan wlh kuna kaucewa magana zan dauki ‘yar Nan nakai Tasha na ajiye Wani ya tsinta.

Daga yau benazir itace uwar data Reni cikin wannan yar takuma haifeta.

Anne ce kawai ta Dan kallesa sbd wannan ai maganar dazu ce ya maimaita.

“Idan nace itace ta Rena cikin Kuma ta Haifa Ina nufin babu Wanda zaisan munama da sumayyah anan gidan bare haihuwarta,

Benazir ce kawai ‘yata Kuma itace wadda ta Haifawa Bilal kaante ‘ya gatanan a hannunta,

Babu Wanda ya Isa yasan gaskiyar maganar Nan har sai ranar Danaso.

Wannan Karan harda benazir cikin masu kallansa Dan ita har lokacin Bata fahimci meye ainihin Abinda yake nufi ba.

Shiru sukai babu Wanda yace “toh” ko Wani abin sbd har lokacin dai ita hande kallan ya tabu take masa Anne kuwa Kai tsaye tasan meyake Shirin aikatawa da wannan maganar tasa.

Benazir ta Maida idanuwanta ahankali ta kalla sbd idan har ta fahimci inda Ababa yake Shirin dosa da zancensa itama lokacin rabuwarsu ne yazo zata tafi ta barta shikenan,

Amma a bangarenta idan har zai cusawa dangin Bilal benazir a matsayin sumayyah su amsheta da ‘yarta to zuciyarta zata yarda da wannan shawarar Dari bisa dari sbd benazir taje ta samu rayuwa Mai kyau ta fita daga wannan rayuwar da saidai su mutu a wahala tinda duka ‘yayanta sun mutu a wahalar sun barta.

Da wannan tinanin Anne Bata tsaya nazarin komaiba itace ta fara dagowa ahankali tace

“Na amince da Hakan”.

Wata dariyar Jin dadi ya sake mara sauti Yana kallan Annen da mamaki yace

“Na buga a daidai notin hankalinki ya dawo kenan?.

Sake dariyar yayi Yana cigaba da cewa

“Kuma yaushe aka baki zabin da kike maganar kin amince?

Magana ce nayi da Wanda ya amince da Wanda Bai amince ba da Wanda ya fahimta da Wanda Bai fahimta ba duka a banza sbd magana ta zaunu babu Wanda ya Isa a cikinku ya dagata,

Ke benazir ki sakawa kanki da qwaqwalwanki kece uwa kece mahaifiyar ‘yarki gatanan,

Ni bansan wata sumayyah ba anan gidan bare haihuwarta.

Hande ya kalla Yana cewa

“Hande ko ke kinsani ne?

Kinsan sumayyah a gidan Nan me haihuwa?

Baki sake hande tace

“Sumayyah a Nan gidan Kuma?

Labarin ya shude ai Kuma,

Allah dai ya Daya Miki ‘yarki benazir.

Wata dariyar farin ciki ya sake Yana Maida kallansa kan Anne da jikinta gabaki yayi sanyi ya mace yace

“Kin sake fahimtar komai yanzu da kyau ko?.”

Ahankali ta gyada Kai tana rintse idanuwanta dake radadin zafin Kuka Amma bayama iya zuwan.

Benazir data fara fahimtar inda aka dosa hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ahankali ta zube qasa tana sake riqe ‘yar da kyau idanuwanta na sauyawa zuwa jajir itama tana kasa Kuka ko hawaye sbd tashin hankalin da Bata taba tsammani ba.

“Ki shirya kowane lokaci idan muka gama maganar manya daura Miki aure zanyi a satin Nan sbd bazan yarda a Rena yarinyar Nan ba a waje mutane su ringa sheganta min ‘yar jika ba”

Kalmar aure Daya fada ya saka Benazir qarasa zubewa qasa tana Neman fita hayyacinta hannuwanta na rawa sosai hakama duka jikinta.

Anne ce ta durqusa ta riqota tana karban babyn dake Neman subucewa daga hannunta tana hadasu ta rungumo jikinta idanuwanta na qanqancewa Amma ba kukan.

Ababa daidai lokacin hade fuskarsa yayi sosai ransa na Dan shiga Baci yace

“Wannan maganar tawa yankan wuqa ce nayi nagama ki sakawa kanki qarfin halin Hawa matsayin uwar ‘yar idan ba haka ba kuskure Daya kikayi akan wannan maganar wallahi tallahi dauke ‘yar zanyi har abada bazaku sake ganinta ba zaku rasata kaman yanda Kuka rasa uwarta.”

Rarrafowa benazir tayi koina jikinta na rawa zata zube gabansa tayi roqo Anne ta riqeta hannuwanta itama suna rawa duka zuciyoyinsu kaman zasu Fashe a tare da babban tashin hankalin dayake Neman dimauta benazir,

Tayaya zatayi aure tabar Anne a wannan masifar ita kadai,

Tayaya Anne zatayi rayuwa babu ko dayansu a cikin su hudun,

Annensu barin ta a gidan a hannun Ababa da hande gwara Susan hankalinta ya gushe Koda an cutatar da ita bazata ji komaiba.

Miqewa Ababa yayi tsaye yabar gurin batareda ya sake bi ta kansu ba ya fice gidan.

Hande ma miqewar tayi sbd itama lamarin yamata daidai gwara benazir tayita tafiya da ‘yar sudai Abar musu gidan da ita kafin a ankara da haihuwar.

Daki hande ta shige tabarsu tsakar gidan sai alokacin Benazir ta fashe da Wani irin Kuka Mai tsananin ciwo da radadin zuciya tana qanqame Annenta.

Annen daurewa takeyi tana Hana kukanta fasuwa sbd ta sadaqar gwara benazir da ‘yarta su tafi inda rayuwarsu zata inganta Dan haka dole ta danne tsananin qunci da ciwon rabuwa da benazir din Datake ji ta nuna jarumta Dan nunawa benazir zata iya zama ita daya a tsakanin Ababa da hande.

Irin Kukan da benazir keyi a tsakar gidan jikinta na jijjjiga duk Wani baqin ciki,qunci damuwa da tashin hankalin data jima tana boyewa suna bayyana sbd Bata taba kawo tinanin aure ko tafiya ta rabu da Annenta ba kaman yanda bazata iya rabuwa da ‘yar sumayyah ba har abadan da Ababan ya furta.

Rarrashinta Anne keyi da hannuwanta batareda ta iya Bude baki ta furta kalma ko Daya ba Dan tana Bude baki kukan Datake riqewa ne zai fashe mata ta sake daga hankalin benazir.

Sai da suka jima a gurin benazir na kukan daya kasa raqe mata nauyin Abinda takeji danne a kirjinta,

Kamata Anne tayi suka miqe ko tsayuwa Bata iya Yi a ahankali suka koma dakinsu suka shige ta zube qasa tana fatan kanta ya juye itama ko zata samu sassaucin ko yayane taji sauki.

Zaunawa Anne tayi gefenta tareda dora mata babyn a jikinta tana Bude baki cikin qarfin hali da dauriya murya a sanyaye tace

“Karkiyi Kukan baqin cikin Hakan kokuma tinanin bazaki iya Hakan ba,.

Zaki iya benazir,

Zaki iya,

Kiyi Hakan sbd ni sbd ‘yar uwarki Kuma sbd ‘yarki,

Kije benazir ki samu ingantacciyar rayuwa na yafe,

Na yafe Miki ki tafi kinji bena,

Ke kadaice sanyin idaniyata da zuciyata a yanzu,

Kije ki samu rayuwar da kowannenmu ya kasa samu Dan Allah,

Kiyi Hakan sbd ni da ‘yarki.,

Kafin zuwanku duniya ni kadaice a cikinsu Ababan Kuma na rayu wahala Bata kashe ni ba Kuma Dan Kun tafi dukkaninku zan rayu inshallah sai ranar da Allah yayi kwana na a duniya zai qare..

Maganganun Anne suka sake rusa zuciyan benazir ta fasa Wani sabon kukan Daya saka jikin Anne sake mutuwa da sanyi Amma bazata nuna rauni da qunci Mai tsananin dake dabaibaiye da ita a lokacin zata daure koma yayane.

Kuka babyn dake jikin benazir tafara ahankali tana motsawa.

Anne ce tayi saurin karbanta tana jijjigawa sbd ta Dena kallo da sauraren benazir data kusa karya mata dakewa da qarfin halinta.

Ita kanta benazir Bata iya dagowa ta Kalli Annen sbd tasan daurewa ce da jarumtan dole Annen keyi Amma Kuma ko suyi jarumta ko kada suyi bazasu iya kaucewa tabbatar maganar Ababa ba har dai a yanzu da batada zabi sai na bin Abinda yace tinda ko guduwa bazata iyayi tabar Annenta ba ga Kuma ‘yar da batajin zata iya rabuwa ma da ita Koda Ababa zai ringa yanka Naman jikinta.

Chapter 41

41

Shiru dakin ya dauka bayan lokacin da benazir ta dauka tana kukan da bazata iya sanin ko yaushe tsawon rayuwarta tayi irinsa ba sbd duk masifa da tashin hankali Bata cika Kuka ba kukan ta Dade da qafewa saidai tayi hawaye ko mara sauti Amma a yau din har Kukan shekaru Sha sha dake cikin zuciyarta tayi zuciyarta ta rage mata nauyi.

Tashi tayi ta fito daga daki jiki ba qwari ta nufi toilet tayo fitsari tayi alwala ta dawo dakin,

Sallah tafara Yi ta magrib kafin ta fito ta Dora ruwan zafi ta dawo daki ta hadawa baby Madara ta karbeta daga hannun Anne datayi shiru tana bin benazir din da Kallo duk inda ta motsa tinda tasan itama rabuwarsu tazo din.

Bude fuskan babyn benazir tayi ta zuba mata idanuwanta dake kumbure tana kallanta soyayyar uwar data tsuguna ta Haifa ‘da na shigarta akan yarinyar,

Ko Ababa ya fada ko kada ya fada soyayyar datakewa babyn na irin Wanda tasan sumayyahn ma zatai mata ne.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda  gyarata jikinta tafara Bata madaran ahankali tana Dan rufe Idanuwanta sbd kanta dake tsakanin ciwon da kaman zai sauka daga jikinta.

Shiru dakin ya sake dauka babu me magana har tagama bawa babyn ta koshi ta miqe ta bawa Anne ita ta tsaftace mata fidan da cup din data hada Madarar ta kaisu inda take adanawa ta ajiye.

Sauran ruwan ta debo ta shigo daki dasu a babban roba Anne ta kama mata tayi mata wanka suka sake shiryata tsaf tini Takoma bacci Dan haka Anne ta goyata ita Kuma benazir jiki ba qwari ta fito tattara gidan da kitchen kafin su shige.

Har ta gama komai ta shigo musu da abincinsu hande Bata fito ba hakama Ababa Bai dawo ba Dan haka Suka shigewarsu.

Da daddare bayan benazir ta kwanta duqunqune da babyn ciki abin rufa sbd sauro da sanyi tayi shiru tareda shiga tinani Mai zurfi jikinta na mutuwa daga kwancen datake.,

Anne data kasa bacci Jin shiru benazir tayi bacci

Ta tashi zaune ahankali zuciyarta na karyewa kukan Datake ta riqewa tin lokacin ya subuce mata Mai tsananin ciwo da quncin zuciya ahankali ta fasa shi cikin qanqanin sauti kada ta tada benazir wadda idonta biyu tana jin saukan sautin kukan Annen hawaye masu dumi suka gangaro gefen idonta batareda ta motsa ba sbd Daman ta sani qunce ne Mai tsanani a ran Annen ta danne Dan kawai tana son fiddata wannan gidan zuwa Wani gidan.

Anne da batasan benazir na jinta ba Kuka sosai Tasha Mai ban tausayi tsawon lokaci kafin ta rarrashi zuciyarta ta kwanta bayan benazir din hawayenta na cigaba da gangara gefen idanuwanta daga kwance,

Benazir dake tsiyayan hawaye daga kwancen itama rintse idanuwanta tayi tana fatan wannan ya zama shine alkhairi ga rayuwarsu su ukun ita da babynta da Annenta.

Washe gari daga Annen har benazir din kasa kallan juna sukai sbd kowannensu fuskarsa da idanuwansa a kumbure suke sbd kukan dasuka kwana Yi mara sauti.

Ta bangare Daya Kuma kowannensu ya dauki dangana da qarfin zuciya ya sake sakawa Kansa Dan haka ayyukan gabansu sukahau Yi Wanda kusan wannan Karan Anne ce tafi Benazir din Aiki sbd babyn da benazir keta dawainiya da ita gashi yau din tanata Kuka daqyar benazir ta samu tayi bacci ta Kwantar da ita taje tayo wanka tana dawowa ta shirya tana Shirin goyata Ababa yace Akai masa ita.

A dakinsa da komai na hutawa yake yasa aka Kwantar da ita kan gadonsa Takoma bacci abinta hankali kwance.

Aiki benazir tazo ta karbanwa Anne suka gama kan lokaci suna shiga daki Akai sallama gidan Wanda ya saka Anne fitowa tana amsa sallaman sbd hande na daki ba lallai ta fito ba.

Budurwar yarinya kyakyawa Anne tagani tsaye a tsakar gidan hannunta riqe da babbar qatuwar leda tana kallan Annen itama cikin muryar me nutsuwa tace

“Sannu Ina wuni.”

Kallanta Anne takeyi kafin ta Dan sauke kallanta ta amsa a sanyaye ta Dora da cewa

“Bari a kira hande.

Juyawa tayi zata nufi dakin hande Zeenah ta katseta da cewa

“Nan ne gidan su benazir????

Dakatawa Anne tayi tareda juyowa tana kallan Zeenah din kafin tayi Wani motsin Ababa da hande suka fito lokaci Daya Jin ana tambayar benazir Dan kuwa yanzu bazaiyi wasa ko barin kowance kuskure ba Dan haka ya fito yaga waye ke nemanta Kuma lafiya.

Kallo Daya Ababa yayi mata yaga kammanin zuriar kaantes take zuciyarsa tayi Wani tsalle ta dawo kirjinsa ya Dan saki fuska Yana cewa

“Barka da zuwa,daga Ina?

Benazir kike nema?

Numfashi Zeenah ta sauke ahankali tareda kallan Ababan ta Dan gaidasa a jagarce kafin ya gaida hande itama tace

“Daga kaantes nake baby nazo Gani”

Wani farin ciki Mai girma ne ya rufe Ababa yace Mata ta qaraso ciki

“Bismillah Bismillah”

A palonsa aka sauketa ta zauna ahankali tareda ajiye ledarta hannunta tareda key din motanta da wayarya gefe tana Dan kallan yanayin palon.

Ababa da Kansa yaje ya kirawa benazir yace taje da kanta ta dauko babyn ta kawowa baquwar.

Jiki sanyaye benazir ta shigo palon da siririyan sallama ta qarasa Kai tsaye dakin Ababan dama suna shiga tinda sune masu gyarawa ta dauko babyn dake bacci hankali kwance ta fito da ita hannuwanta da zuciyarta na rawa sbd daga wannan lokacin dai ya tabbata itace tayi cikin Kuma ta haihu,tazama uwa ta zama mahaifiyar babynta har abada.

Rintse idanuwanta tayi ahankali tareda sauke numfashi da ajiyar zuciya Mai sanyi ta Bude idanuwanta daidai lokacin da ta iso gaban Zeenah wadda itama ta zubawa benazir din da babynta idanuwa tanajin hawaye na ciko idanuwanta da tsananin son babyn harma da benazir din da tausayinsu na rashin jigonsu Bilal.

Cikin nutsuwa benazir ta miqa mata babyn bayan sun gaisa kowannensu cikin sanyi.

Hannuwan Zeenah har rawa suke gurin karban Babyn tana amsarta ta rungumeta a hankali tsawon mintina biyu kafin ta Kwantar da ita cinyarta tana kallan fuskarta da babu Abinda ta baro na kamannin kaantes saima sake a girma zatafi yin kama dasu din.

Ahankali ta dago ta Kalli benazir da kanta ke qasa tana kasa kallan Zeenah sbd kunyar qaryat Datake dabaibaiye da ita.

Cikin kulawa Zeenah tace

“Yaya babyn lafiyanta kalau right?

Kema duk Kuna lafiya Amma ko??

Gyada Kai benazir din tayi tana cewa

“Eh alhmdllh”

Ababa na ganin Hakan ya fita yana cewa hande ya biyosa sbd Ababa Zeenah din Daman ganin babyn da kyau.

Suna ficewa Zeenah ta Kalli babyn hawaye na gangaro mata na rashin dadyn yarinyar

ahankali itama benazir nata hawayen suka gangaro na rashin tata yar uwar Amma ba Daman nuna ma tanada yar uwa sumayyah kaman yanda Ababa ya a fada har abada saidai tayi kukan kewanta cikin ranta badai a fili ba.

Ganin hawayen benazir yasa Zeenah kasa riqe kukanta cikin tausayin benazir datai rashin Bilal din itama sai ta ringa rarrashinta sbd kukan benazir da yayi karfi a hankali.

Sun jima a palon su kadai daga Kuka Zeenah ta gabatar mata da kanta tareda Bata tabbacin duka familynsu suna tsananin son babyn kaman yanda suke son Dan uwansu dasuka rasa Bilal.

Hotunan da zata Kaiwa Umme Zeenah ta dauki babyn kafin ta bawa benazir kayan data kawowa babyn kafin su karbeta ta dawo hannunsu.

Zeenah kaman kada ta tafi tabar babyn taji Amma haka ta daure ta tafi tana zuwa gida takaiwa ummensu hotunan wainda suka saka hankalin Umme sake tashi akan sai ankarba babyn Bilal din tadawo hannunsu kokuma kawai tabar kaantes din su koma gidan DD ta Reni jikarta acan.

Wannan Kalmar tata da tashin hankalin datai harma da hoton babyn yasaka dad kaante da ubangayya DD Jin buqatan dawowar ‘yar hannunsu cikin gaggawa shi Kansa dd babban baisan Yana son ‘yar ba Saida yaga hotonta abin tausayi kayan jikinta ma masu tsananin arha da rashin nauyi ne da zai saka sanyi shigarta ya illatata da wuri.

Washe gari Ababa Yanata Kai kawo tsakanin gida da waje Yana lissafin yaushe Kaantes zasu nemesa sai kwatsam ga Kiran Abbakar akan dd babba na nemansa.

Bai tsaya batawa Kansa lokaci ba ya nufi KAANTES din sbd zuwa lokacin ya matsu ayi me yiyiwa kafin DD kaante ya tattara ya koma inda ya fito lissafinsa ya Kuma watsewa a Karo na biyu.

Yana Isa kaantes Kai tsaye yanzu an tantancesa Yana zuwa ake barinsa shiga Dan haka shida Abbakar palon dd babba suka nufa Yana zaune Shima Yana jiransu.

Gaida dd babba yayi tareda dad kaante dake palon Shima kafin ya zauna a natse Dan Jin meye dalilin nemansa.

Numfashi dd babba ya sauke kafin ya dago ya Kalli Ababa cikin nuna manyanta yace

“Malam Ababa maganar jaririyar dake hannunku ce mun Yanke shawarar karbanta tin yanzu sbd a dauke muku nauyi dama duk Wani Barnar sunan da kuke gudu mu zamu ji da komai ba zaa San ‘yarka ta taba haihuwa ba inshallah.”

Numfashi Shima Ababa ya sauke Mai sauti kafin ya dago ya Kalli dd babba Bai tsaya kwana kwana ba Shima yace

“Ni yanzu na aminta na yarda sunan nawa Dana ‘yata ya lalace kowa zai San ta haihu ba aure ya sani Amma bazan taba raba ‘ya da uwa ba,

Yarinyar Nan tazo duniya a ranar da mahaifinta yabar duniya sannan Kuma a rabata da mahaifiyarta?

Harma da tinanin bazata San mahaifiyar tata har abada ba??

Daukan haqqin wannan marainiyar jaririyar ‘yar zaiyi yawa,

Nayi alqawarin barinta tareda uwarta tinda ta rasa ubanta inshallah zuwa gaba uwarta zata samu mijin dazai aureta da ‘yarta Dan Allah ya rufa musu asiri,

Maganar asan waye mahaifinta har sunanku ya Baci nayi muku alqawarin bama zamu taba bari tasan waye mahaifinta bare danginsa har sunanku ya Baci Dan haka daga yau na hakura zan dauki bacin sunan Amma abarni da jikata zata samu gurin agolanci Mai kyau inshallah.

Da gaskiyarsa yake maganar Yana bayyanarda qunci da damuwarsa akan zancen Dan haka take gabaki Daya palon ya dauki tsit.

Dd babba da dad kaante shiru sukai sbd har ga Allah zancensa da ya shigesu yayi magana Mai maanar da zaa duba idan har zaa yiwa marainiyar jinjirar adalci batareda sun duba sunansu sun cutatar da itaba.

DD kuwa daya shigo alokacin maganar agolancin da Ababa yafada tafi sokan zuciyarsa,

Idan har Yana Raye har abada ‘yar Bilal bazata taba agolanci gidan kowa ba.

Ababa miqewa yayi Bai Jira Mai zasu fada ba yace

“Insha Allah gobe zamu bar garin gabaki Daya zamu koma asalin mu acan kauye zamu samun kwanciyar hankali da rufin asirin renanta ba maganganu Dan haka idan Kuna buqatan ganinta ko so Daya ne zaku iya zuwa kafin mu wuce nagode sosai Allah ya saka muku da Alkhairi Yakuma ji qan Alh Bilal ya masa rahama.

  kofa ya nufa Kai tsaye zuciyarsa na tsallen Allah yasa maganarsa ta Doki inda yakeso ta doka.

Dad kaante da Dawood ne suka Bude baki a tare suka ce

“Zamu karbeta har uwar idan tayi wayon shekaru biyu uwar ta dawo gida tayi auren……

Katsesu yayi ta hanyar juyowa ya katsesu da cewa

“Aa ni ‘yata yanzu zan mata aure bazata zo renan shekaru biyu ba ta qarasa lalata sauran rayuwarta,

Kuyi hakuri mu tafiyar mu ka…….

“ZAN DAURA MATA AURE DA QANIN BILAL IDAN HAR HAKAN ZAI SAKA KA BADA ITA DA BABYN”..

Kalmomin dd babba kenan dasuka saka Ababa dauke wuta Yana juyowa Wani haqayin farin ciki da firgita na fita daga Kansa da kunnuwansa.

Dad kaante kuwa ajiyar zuciya ya sauke Bai shirya sbd shock duk da kusan Shima Abinda ya shirya fada kenan.

Chapter 42

42

Ababa Suma ne kawai Bai yiba a inda ya tsaya cak lakacin da kalaman dd babba sukai dirar mikiya cikin kunnuwansa,

Kasa gasgatawa da gasken Abinda yaji yasakashi juyowa ahankali idanuwansa a kafe kan dd babban ya tsaya Yana zaunar da zancen cikin Kansa da zuciyarsa tareda boye shock dinsa.

DD kuwa wuta ya dauke na wasu daqiqun da baisan meyema zaiyi tinani Akai?

Wane qanin Bilal din ake maganar ya auri mahaifiyar ‘yar Dan uwansa?

A saninsa bayan shi akwai qannan dangi dasuke dashi Amma dai koyaushe akace qanin Bilal yasan shi ake nufi duk da a cikin familyn ne kawai ake kiransa qanin Bilal Shima daga mahaifiyarsu sai dad kaante Amma kusan babu kiransa qanin Bilal sbd ganin yafi Bilal din samun cigaban rayuwa ta bangaren dukiya da suna.

Muryar Ababa dake rawa Yana damqeta Dan Hana bayyanarda zalamarsa a natse Yana kallan dd babba yace

“Idan har aurenta zakuyi Banda matsala da Hakan a shirye nake Amma dai Reno ko zuwanta zaman Dan Wani lokacin ne ban yarda dashi kwata kwata sbd babu adalci ahakan.”

Dd babba numfashi ya sauke Kansa na sarawa da hukuncin Daya Yanke din Amma Kuma basuda zabin Daya wuce Hakan a yanzu sbd suna buqatan karban babyn ta dawo hannunsu Kuma rabata da mahaifiyarta kaman yanda Ababa ya fada cutatarwa ne,

Dad kaante ya kalla Wanda Shima dd babban yake Kallo kafin suka Maida kallansu kan DD a tare Wanda shikuma Sam hankalinsa Bai tashi ba sbd baima dauka cewan dashi ake ba akan maganar kawai dai buqatansa ‘daya Daya sani shine ‘yar Bilal ‘yarsa ce a yanzu halak malak da Bilal baya duniya,

Idan akwai wainda ya Isa ya karbi babyn yayi Iko da to shine Dan haka zai karbi babyn kota halin Yaya sbd sanin dayayi babu inda dukiya Bata magana Kuma Bata Aiki.

Dago kyawawan idanuwansa dasuka Dan fada yayi yaga kalar kallan da dd babba da dad kaante suke masa hakama Ababa Shima kallansa yakeyi Yana Jin kaman ya janyosa ya daura masa aure da benazir a lokacin.

Irin kallan da suke masa ya sakasa Sakin Wani gajeran crazy numfashin murmushi cikin zuciyarsa Yana cewa

“Wane crazy tinanin ne yake cikin kan tsoffin Nan”

A fili kuwa Kai tsaye cikin hade fuskarsa daga mamakin tinanin Dayake gudana cikin kansu yace

“You gotta be kidding me,

Ba Abinda nake tinani ba kuke nufi kenan ba right?

Kallan da dd babba ke masa ya tabbatar masa da Abinda suke tinani

Dan haka shi bai iya boye boye ba baya Yi

so tsayuwarsa ya gyara a natse ya Kalli Ababa dake masa kallan mukullin arzkinsa kafin ya dawo da kallansa kansu dd babba ya Bude baki a natse yace

“Babu raayi ko gurin auran mace biyu a rayuwana,

Dayan is ok so bana buqatan Qarin kowanne macen bayan dayan

Please kar ayi complicating things anan,

Maida kallansa yayi akan Ababa dake jiran matsaya Bai masa kallan tsaf ba Kai tsaye yace

“Zan baka blank cheque lissafinka yafara daga naira milayan 100 zuwa sama ka rubuta nawa kakeso ka kawon ‘yata da kanka yau”……

Wani jiri ne ya dibi Ababa ya zubar qasan palon gaban DD din batareda ya sani ba sbd kudin Daya fada shi Koda an auri yar tasa Bai taba lissafin zai samu kudin zasu Kai miliyan darin ba bare zuwa sama.

Zufa ne ya tsatsafo masa ta ko Ina ya karye Yana tsiyayo masa,

Kasa dagowa yayi ya Kalli kowa sbd yaqin dayakeyi da zuciyarsa da hankalinsa dake Neman gushewa akan Jin kudin,

Rawa hannuwansa suka dauka yayi saurin zirasu cikin babbar rigarsa kada a gani asan gushewan hankalin Daya samu na ‘dan lokacin.

Girgiza Kansa ya hau Yi Yana Hana kansa bayyanarda halinda yake ciki

Amma idan har wannan kudin zai iya sakasa haka hakama Idan DD kaante zai iya bayarda wannan kudin kaman ba komai bane to idan ya auri yarsa yaya kenan?

Abinda zai samu zai zama nin ba ninkin wannan???

Hummmnn ya sauke numfashi a boye tareda yaqar zuciyarsa ya dago ya Kalli dd babba da Suma duk suka rasa abin fada sbd Tim farko kowannensu yasan waye Dawood da raayinsa da kalan yanayin rayuwarsa,

To Amma a yanzu dukkaninsu suna buqatan ‘yar dake hannun Ababan Dan haka suna buqatan sacrificing wasu raayoyinsu Dan samun Abinda suke so da buqatan kaman yanda dd babba ya sauke nasa tsananin raayin.

Ganin kaman Basa hayyacin fahimtar Abinda yake fada ya juya yabar palon may be idan Basa ganinsa su kawo Wani tinanin na Abinda zai yiyu.

Yana ficewa Ababa ma Dayake ta yaqi da zuciyarsa gurin Hana kansa karban kudin Dawood kaante din ya fice zuwa gida Yana hada hanya zufa na sake jiqasa.

Bayan barin Dawood da Ababa palon dd babba Kai tsaye Kiran Umme yayi a waya wadda itama take matse da akirata din Jin zuwan Ababa kaantes taji ya aka Kai karshen magana Dan Bata hayyacinta matiqar ba gabanta taga ‘yar Bilal dinta Kuma jikarta ta fari ta dawo ba.

Lokacin da tashigo palon Kallo Daya dd babba yayi mata ya dauke Kai sbd ganin yanda gabaki Daya ta fita hayyacinta sbd ciwon rashin ‘danta,

Kaman wadda take kwance jinyar watanni Takoma idanuwanta kuwa sun kasa hucewa daga munin kumburin da sukai na kukan data kasa denawa har yau din na rashin Bilal da tsananin buqatan ‘yarsa ta dawo gunta.

Cikin nutsuwa da sanyin jiki dd babba ya Bata tabbacin ‘yar zata dawo hannunsu Amma sai idan ta saka Dawood amincewa da auren mahaifiyar babyn wannan shine sharadin Mahaifin maman Babyn idan ba Hakan ba a gobe zai tafuyarsa Subar garin gabaki Daya.

Hawaye masu dumi ne suka gangarowa ummen sbd lalata rayuwar ‘danta da ake magana a maimaikon ‘yar Dan uwansa da suke buqata su dukan,

Auren Sbb dole ne garesa Badan raayinsa ko buqatan Hakan yake ba Amma ya amince sbd ita Dayake son farantawa Amma tasani Wanda bayason hada ko muhalli da kowa har iyayensa ansamu ya aminta zaiyi aure yanzu tin baayi ba ana sake kawo masa Qarin mace ta biyu.,

Yaya Dawood zaiyi da auren mace biyu lokaci Daya?

Tako wane saqo anshiga haqqin rayuwarsa,

Amma Kuma Tayaya suna Kallo zasu rabu da ‘yar Bilal ta tafi tabarsu kaman yanda Bilal ya tafi yabarsu da gibi me girman gaske a zukatansu.

A Karo na biyu zata sake zama uwa Mai son Kai ga Dawood Dan kuwa zata sake shiga rayuwarsa da Qarin wata macen.

Hannu takai ahankali ta share hawayenta tareda jinjina Kai tana Bada tabbacin zata gwada shawo Kansa akan maganar auren.

Miqewa tayi ta fito Kai tsaye part din Bilal da DD din yake ta nufa zuciyarta na karyewa.

Tana Isa a Palo ta taddasa zaune Yana amsa wayar Naseer a hankali Wanda ya kira akan yazo daukansa yau zai koma gidansa.

Jin qarshen wayarsa na tafuyarsa dazaiyi yasaka ummensa kasa riqe hawayenta suka gangaro tayi saurin sharewa da hannunta.

Zaunawa tayi gefensa tareda kasa juyowa ta kallesa sbd kunyar rokon da zata yimasa a Karo na biyu.

Idanuwansa ya dago ahankali ya zuba mata ya karance yanayinta tsaf tsawon mintina kafin ya Dan dauke idanuwansa Yana ajiye wayarsa dake hannunsa gefensa ya kalleta cikin nutsuwa yace

“Umme idan kikace nayi auren Nan Hakan na nufin Zaki janye wancan maganar auren na farko,

Na baki zabin duk Wanda acikinsu kikeso ki zaba Daya zan aura kowace a cikinsu”.

Yana fadan Hakan yayi mata shiru sbd babu Abinda zai qara Akai,

Maganar zasuyita Janta ne har sai waninsu ya samu ciwon Daya shigesa na damuwa da maimaicin Abu Daya Wanda Sam Hakan baya cikin Abinda yake buqata a rayuwarsa.

Shiru ummen tayi tana kallansa da idanuwanta dasukai laushi sbd a cikin Biyun yanzu babu Wanda zata iya zaba tabar Wani.

Ajiyar zuciya tayi ahankali sbd da Bilal dinta na Nan da duk bazasu shiga wannan tsaka me wuyan ba daga ita har Dawood da zaa aurawa mata biyu duka badan Yana sonsu ba.

Miqewa tayi ta fito Bata iya zabar ko Dayaba a zancen ta koma part dinta tana shiga tinani da damuwan Tayaya ma zata iya kallan Dan uwanta da hajiyarsu ta fada musu Dawood bazai auri Sbb ba wata zai aura?

Wannan maganar kadai zata iya shiga tsakaninta da Dan uwanta da hajiyarsu komai ya lalace a zumincinsu.

Dad kaante ma da Kansa yaje yayo magana sosai da Dawood din Amma Sam raayinsa ya kasa sauyuwa Saida dd babba ya rokesa a matsayin shine zaiwa alfarmar Benazir,

Idan ummensa ta rokesa ta zabar masa Sbb shikuma ya rokesa ya zabar masa benazir Dan haka Suka sakasa a tsakiya sbd sune mafi soyuwa a ransa su Biyun sai babyn da ayanzu tin batazo hannunsa ba yake jinta cikin ransa ta maye gurbin da Dan uwansa yabar masa.

Tinda dd babba yake babu Abinda suka taba ganin ya kwantarwa Kai sai wannan buqatan tasa ta auren Benazir wadda ta saka kusan sauran yayansa sanin halinda ake ciki.

DD kuwa daya gama fahimtar babu Abinda zai sauya tinanin su dd babban daga maganar auren dole ya amince sbd yasan auren sbd ‘yar dasuke buqatan karba zaayisa hakama bayajin zai iya kallan matar da Bilal yagama mallaka a matsayin tasa matar,

Bama zai iya saka kalman aurenta cikin Kansa ba sbd Dan uwansa musamman da haihuwa a tsakaninsu.

A cikin Daren zancen yarda da auren isarwa Ababa,

Da farko kasa yarda yayi da Abinda dad kaante ya kirasa ya sanar masa akan zuwansu Neman auren ‘yarsa gobe Saida ya kashe wayar ya sake dubawa yaga tabbas sunan dad kaante ne suka gama magana a lokacin.

Sakin wayar yayi tareda zubewa qasa da sauri yayiwa ubangiji sujjada ya taso ya fito zufa na tsinke masa ya tsaya tsakar gidan ya kwada sunan benazir wadda ke daki zaune tana bawa baby Madara.

Jin Kiran Ababa ya sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta sanyi da faduwar gaba ta miqe ta fito kanta a qasa ta tsaya gabansa daga nesa kadan rungume da babyn.

Anne ma dake dake rakube zaune fitowa tayi gabanta na faduwan ta tsaya gefen benazir.

Hande ma da sauri ta fito tana tsoron idan ba mutuwa benazir din tayiba itama yake wannan ihun Dan kuwa benazir na mutuwa wannan Karan zaucewa Ababan zaiyi.

Tinda aka haifesu shekaru masu yawa benazir Bata taba ganin murmushin Ababa akansu ba Dan haka daidai lokacinda ya kalleta ya saki murmushin baya tayi ahankali qafafunta na Neman sarewa da tsananin tsoro da fargaba tana sauke Kanta qasa.

“Benazir kin cika mun burina na shekarun Dana debo Ina wahala daku,.

Kallan yarinyar hannunta yayi yaji zuciyarsa na sake sanyaya da farin cikin ganin wannan ranar

Yace

“Sunan benazir sunan sa’a ta ne a yanzu Dan haka itama na saka mata BENAZIR sbd idan Kuka je Tako ina sa’a tayita fasomin ba kakkautawa,

Aurenki zaa taho nema gobe a satin Nan zaa daura Miki aure.

Anne data ji saukan zancen har cikin zuciyarta ta rintse idanuwanta a hankali tana tilasatawa zuciyarta karban zancen da sanyin farin cikin dole.

Chapter 43

43

Benazir Bata iya dagowa ta kallesa ko Annenta ba sake Yin baya tayi ahankali ta dafa bango idanuwanta na kasa taro ruwan hawaye sbd takai matakin da ko kukan yanzu Bata iyawa Amma dai zancen har lokacin jinsa takeyi kaman almara,

Rabata zaayi da Annenta,

Ya Anne zatayi rayuwa babu kowannensu,

Sameerah ta rasu, Safnah ta tafiyarta, sumayyah ta rasu

Ita Kuma yanzu gashi zata tafi tabar Annen da sunan aure,

Bata tausayin kanta sbd babu inda bazata iya rayuwa ba komai tsanani da wahala da rashin kauna hakama batada sauran Jin feelings a zuciyarta dama rayuwarta gabaki Daya da zata ji komai na duk abinda zata tarar a rayuwar da mahaifinta ya Saidata Akai.

Ababa cikin farin cikin dabai taba Jin irinsa ba ya tinkaro Benazir ya karbi babyn hannunta Yana mata wasa baki a washe Yana saka mata albarka harma da rungumeta Yana Jin kaunarta Mai tsanani wadda yake ganin kaman ta kudin dazaiyi ne sanadinta.

Hande ma farin cikin me tsanani na Jin zasu rabu da ‘yar ta washe baki tana cewa

“Barkanmu da arziki daga qarshe dai zamu samu mu aurar da Daya daga cikin haihuwar Anne da babu Wanda aka amfana dashi.”

Kalmar hande ta saka idanuwan Anne dasuke danne halinda zuciyarta ke ciki na rabuwa da ‘yarta cikowa da hawayen data kasa barinsu saukowa ta hadiyesu suka koma maqoshinta sukai cikinta.

Benazir ma Kalmar sakata tayi qarasa silalewa ta zube qasa zaune tana rufe Idanuwanta dasukai mata nauyi.

Ababa kuwa wayarsa ta fidda babyn na hannunsa ya kira yaronsa Bilymanin yazo take ya fidda kudi ya sako aka bazama siyayya.

Har qarfe goman dare Mai saka Kofa da windows da masu Fenti na gidan Yana sakawa su benazir a dakinsu,

Tsakar gidan da waje kuwa da yamma Akai Fentinsu ba Bata lokaci.

Tinda safe masu qatuwar katifa da fanka aka zo aka saka musu dakinsu harma da labule da sabuwar Ghana must go ta saka kayansu na sakawa,

Hadda sabuwar cerpet din daki aka zo aka shimfide dakin duka da ita sbd sanyin siminti dasuke Sha shekara da shekaru kada ya kama baby benazir.

Koda karfe goma Sha dayan Rana tayi gidan gabaki Daya kaman ba gidansu ba,

Benazir da Anne suna daki zaune ko mamakin sun kasa Dan a yanzu babu Abinda zai Basu mamaki ko tsoro daga wannan rayuwar.

Sabbin kayan sawa masu kyau da maana aka siyowa benazir na jallabiya Mai kyau da yar tsada harma da tirarika masu Dan kudi.

Itama Anne an siyo mata Riga da zani na atampa ready-made masu yar tsada

Ya sakasu cin abinci duk bayan awa data saiyace su sake ci sbd so yake fuskokinsu dasuka Fi kama dana qwarangwal su Dan ciko kafin zuwansu kaantes.

Tin safe yasaka aka gyare koina aka siyo abinci lafiyayye daga restaurant me yawa aka ajiye sunta fama yimasa cin dole kafin Kuma yasaka hande da kanta ta zaunar da benazir tayi mata wankin Kai Dana qafafu duk da Bata cikin qazanta sbd sunada tsaftansu sosai kaman ba wainda ke cikin wahala ba Amma sbd muzantawa hande ce ta zaunar da ita ta Riga zuba mata ruwa tana wanke mata Kai kaman yarinya qarama.

Bata motsaba har handen tayi ta gama ta Bata Daman tashi tkuna ta miqe jiki ba qarfi tabar gurin taje tayo wanka ta dawo dakinsu ta zauna bakin katifar da tsoron Hawa ma sukeyi sbd kada baqin su tafi yace abada katifar yace sun lalata masa Dan haka yasaka ma sun kasa sakewa su hau katifar.

Mai tashafa ahankali jikinta babu me magana a tsakanin ita da Anne har tagama ta shirya cikin kayan da aka siyo din ta shirya baby bena itama cikin kaya masu kyau da nauyi na Zeenah data kawo mata shekaran jiyan datazo.

Anne ma wankan tayi ta shirya cikin nata kayan da aka Bata suka zauna daki jigum jigum kaman wainda zaayi shooting film dasu.

Hande ma fes ta shirya cikin lace Blue da fari ta fito kaman tsohuwar albarka.

Ababa kam Jin yake kaman ranar ce zaa daura auren Dan haka yayi Shirin mutinci da babbar Riga da Hula tareda Wanda ya aminta ya tayasa tarban bakin da Bada auren.

Qarfe hudu bayan sallar laasar baqin suka iso ga mamakin Ababa harda dd babba aka taho da dad kaante sai Hon   kaante qanin dad kaante,

Dd babba ko auren yayansa babu Wanda taba zuwa da Kansa nemawa aure sai wannan Karan Wanda Daman alqawarinsa ne shine zai je namawa Dawood aure,

Bai samu yaje ya amso masa na Sbb ba Dan haka ya taso da Kansa Dan nema masa na benazir.

Hadda Umme da mum Khadija akaso sai Zeenah da Siyam kaante autan mum Khadija itama.

Su dd babba kofar palon Ababa ta waje aka Bude musu suka shiga su kuwa su Umme Kai tsaye cikin gidan suka shigo Dan ganin baby Benazir da mamanta.

Hande na ganinsu ta saki fuska tana musu barka da zuwa cikin girmamawa da nuna farin cikin zuwansu.

Anne ma dole ta fito tayo dakin handen sbd a can aka saukesu.

Cikin nutsuwa da sanyi tareda girmamawa ta shigo dakin ta gaidasu tareda musu barka da zuwa.

Umme Datake kallanta a natse ta hango nutsuwa da rashin son kallan mutanen Anne sai taji Dan sanyi yaqara shigarta sbd koba komai mahaifiyar benazir nada nutsuwa Allah yasa hakama benazir din.

Zeenah ce ta Kalli Anne bayan ta gaidata tace

“Benazir da baby fa?”

Cikin nutsuwa da sanyi tace tana daki bari tazo ta kawo muku ‘yar.

Juyawa tayi ta fice.

Daki taje ta kirawa benazir da jikinta yagama sanyi Amma babu gudu ba ja da baya ga wannan sabuwar qaddarar Dan haka ta miqe rungume da bena a jikinta ta fito.

Tana fitowa Zeenah na fitowa daga can zata amsa waya Amma tana ganinsu ta fasa ta nufo tana miqa hannu ta karbi little bena.

Gaisawa sukai da benazir da batasan me zata ce suka nufi dakin hande qafafunta na rawa.

Zeenah ce a gaba rungume da baby ta shigo ta nufi su Umme tana miqawa Umme babyn tana cewa

“Ga benazir Nan ta shigo Umme.”

Hannu na rawa cikin Jin sanyi da farin ciki Umme ta karbi Babyn kafin ta dago ta zubawa benazir data qarasa shigowa cikin nutsuwa kanta aqasa itama Ido.

Ahankali cikin sanyi da yar rawar murya benazir ta Bude baki ta gaidasu Daya bayan Daya batareda ta dago ta Kalli kowannensu ba.

Ajiyar zuciya Umme ta sauke sbd sai yanzu ne take fahimtar Abinda yasaka Bilal kamuwa da son benazir din,

Bilal na son nitsatsiyar mace Mai tsananin sanyi,

To Amma Dawood total opposite ne na Bilal anan bangaren shi baamasan irin matar Dayake so ba kokuma raayin aura,

Amma ita dai idan har wannan nutsuwar Data ga benazir da mahaifiyarta da ita to benazir din ba Abar qyama ko baqin cikin aura bace.

Kasa zama cikinsu tayi kaman yanda Zeenah taso Dan haka ta silale Takoma daki

Anne Kuma itace ta kawo musu ruwa da abin Sha harma da abinci da snacks masu kyau da akayo order acikin sabbin plates da Ababa yasaka aka siyo.

Itama tana gama Jere musu kayan ta fice sbd bazata iya tsayawa cikinsu ba.

Daki tabi benazir Suka Kalli juna Annen ta qaqalo murmushin da ko kyau baiyi mata ba sbd zamansa na qarya da qarfin hali.

Benazir ganin Hakan ta saki nata murmushin Mai ciwo Daya bayyanarda zafin quncin dake qasan zuciyarta tana nunawa Annen gefenta da hannu ta qaraso ta zauna.

Annen ce a hankali ta sauke numfashi ta Bude baki tace

“Benazir na Amince kuma nayi na’am da wannan auren da zaa dauka Miki har cikin zuciyata a matsayina mahaifiyar data dauko cikinki ta haifeki Ina Miki fatan samun sauyun rayuwa ta hanyar wannan auren,

Allah ya albarkaci rayuwar da Zaki tarar acan keda Benazir qarama hakama inshallah zanyi juriyar da banyi a baya ba,babu Abinda zai sameni sai Abinda Allah ya Riga ya qaddara zai sameni.”

Sunkuyar da Kai benazir tayi kalaman Anne na sanyaya jiki da zuciyarta sbd tabbatarda dai auren zaa yimata ta tafi tabar Anne.

Numfashi kawai ta iya saukewa jikinta na sake mutuwa da sanyi a hankali ta furta

“Komai zai zo karshe Anne,

Dukkanin tsanani Yana tare da samu inshallah,

Zaki rayu kiga auren Baby benazir Anne,

Zaki rayu,wahala Bata kisa,komai zai wuce Anne…..riqe hawayen dasuka ciko idanuwanta tayi tana hanasu saukowa sbd baqin dake gidan.

Annen ma kasa magana tayi tana Hana kanta sauko da nata hawayen itama.

Sake kiransu Akai suka fito mum Khadija ta saka Benazir din zama tareda su dole suna Dan tambayanta lafiyan baby da ita kanta tana Basu amsa a taqaice cikin girmamawa.

Ahakan sukaita kokarin Janta da magana kafin aka Sako maganar Bilal Wanda ya saka Benazir kasa riqe hawayenta na rashin ‘yar uwarta da hawayen Datake ta dannewa tin a daki sukuwa jikinsu duka yayi sanyi Suma hadda hawayen sbd tinanin rashin Bilal takewa hawaye.

Yanda benazir ta bayyanarda kukanta a fili na rashin Bilal ya sakata shiga ran ummensa dasu Zeenah Dan haka Suka matsu ma kawai ayi auren ta dawo cikinsu su mayar mata soyayyar dasukewa Bilal ita da baby Benazir wadda a take Zeenah ta Dora make AMNAH akan sunan benazir din da aka sakawa babyn.

Da zasu tafi kaman kada su bar mata babyn haka Suka fita suka tafi Anne naji nauyin zuciyarta na Dan raguwa sbd ganin mutanen da Bena dinta zata Yi rayuwa acikinsu.

Sun nema auren Benazir Ababa ya Basu sun Bada kudin aure masu yawa dasu sake qarawa Ababa kaunar baby Benazir,

An saka ranar daurin aure 6 ga watan Sept sati biyu masu zuwa kenan.

*******Maganar auren ta yadu har inda Ababa Bai taba tinanin zaa fada ba Jin yake ana fada,

Kullum sai ya saurari redio da kafofin yada labari Dan kawai sauraron sunansa a cikin sanarwar daurin auren duk da kullum zuciyarsa quna takeyi idan ya Tina mace biyu zaa daurawa Dawood din lokaci Daya Amma tinda dai tasa zata shiga baida matsala hakama Amnah zata sa a Fi fifita benazir akan dayar tinda ita Amnah kowa na sonta.

Sati na zagayowa Akai yankan sunan benazir Amnah Wanda Akai a sirrance batareda ma kowa yasaniba,

Har lokacin Dawood Bai San waye benazir da zai aura ba hakama sunanta takamamai ya kasa riqewa sbd ko maganar ya dakatar da ayi masa buqata kawai a daura auren yarinyarsa ta dawo hannunsa qarqashinsa.

Ranar da Kai sunanta a ranar Zeenah tazo ta dauki Amnah taje da ita kaantes.

A ranar DD yafara ganin ta a hannunsa ya zubawa fuskarta Ido babu Abinda ta baro na Bilal,

Wani irin feelings ne na soyayyar Uba Mai tsananin gaske yaji yanawa babyn,

Shi baya ko daukan Yara sbd Basu damesa Sam baya ma Wani San Yara Kuma kowa ya shedesa da Hakan,

Amma ayau ranar farko babyn farko dayaji tashiga ransa,

Duk buqatan karban babyn Dayake Yi a baki sai Daya rungumi babyn yakejin Abinda ma yafi buqatan ta a kusa,

A rayuwarsa kwata kwata yake buqatanta sbd bazata taba maraicin Mahaifinta ba matiqar Yana Raye shine Mahaifin dazai nuna mata soyayyar Uba,uncle harma da uwa idan ya tafi da ita.

Chapter 44

44

Sai yamma aka Maida baby Amnah gurin mamanta tareda da kayan da saidai aka Kai wasu dakin Ababa dakinsu ba guri,

Ababa kuwa shanun da aka yanka haka ya kama fiyeda Rabi ya siyar sauran Kuma yayi sadakar Rabi sbd Amnah tayi albarka Wanda ya rage kuwa aka Soya suka ringa cin abinsu hankali kwance,

Su benazir din Suma wanna Karan anbasu me Dan yawan dasuka ajiye Dan bazasu iya cin ba,

A cikin damuwa suke da sanyin jiki Dana zuciya na rabuwar da zasuji da juna,

Daga hande sai Ababan ne suke cikin tsananin farin ciki da murnar auren Dan haka yanzu baa musu Horan yunwa abinci yake Basu sosai tareda yiwa Benazir alqawarin idan ta Kwantar da hankalinta a auren take ta zama hamshaqiyar da zata ringa Basa dukiya kaman batasan metake ba shikuma yai mata alqawarin Annenta zatai rayuwar ‘yanci da kwanciyar hankali.

Idan ta je ta Saba umarninsa kuwa Annenta ce zata dauki hukuncin babu tausayi ba sauki tasan halinsa.

Abincin dasuke samu ana Basu tareda saka su cin dole harma da kayan gyaran jikin da ake gyarata ya saka Benazir Dan cikowa daga bushen Datake.

Hande kuwa ita dai matse take da ayi bikin su huta Dan haka ta ringa gayyata tana shelan gidan da ‘yarsu zatayi auren.

Kayan lefen aure Mum Khadija ita Daya ta kawo sai Zeenah da Siyam sbd Basa buqatan daukaka bikin komai a kaman sirrance zaayi sa

Sai daga baya idan Sbb ta dawo zata tare ayi bikin da kowa zaiji ayi gayyatar da aka San bazaa ji kunya ba.

Lefen da aka a cikin akwatinan lv set ne Dan

situran alfarma da kaf gidan har Ababa baisan kudinsu ba da darajansu aka kawo mata bare ita da batama San wata sitarar ta alfarmar ba,

Breeziers da panties da komai na cikin kayan foreign ne masu tsada designers Dan gashi kusan komai daidai na matashiyan mace ne aka Sako hande naji tana Gani babu abin dauka aciki sai laces data kwasa da atampa kusan guda goma.

Anne kuwa komai batada shaawan mallaka a kayan bare Kuma ma me kayan benazir da kasa ma kallan kayan tayi bayan da dare yayi suka shige.

****Ta bangaren Kaantes babu Wani biki bayan daurin aure Dan haka babi Wani hidiman dasuke Yi sai jiran lokaci.

Umme wata damuwan ta sake shiga a lokacinda Dan uwanta yace a boyewa Sbb maganar auren Dawood da wata bayan nata tinda bata qasar Dan haka Umme taketa Jin damuwa kada Sbb din taji ta tada rigima da tashin hankalin da zai saka hajiyarsu taji ba Dadi kokuma laifin Dawood akan zai auri wata lokaci Daya da Sbb dinsu.

Ita kuwa sbb din acan farin ciki takeyi Mai tsananin gaske Jin zaa daura aurenta da DD kaante kafin daga Baya ayi bikin tarewarta idan ta gama sauran karatun nata ta dawo.

Ango DD kuwa babu Wani Abu na farin ciki ko baqin ciki Dayake ji gameda aurensa,

Abinda ya sani shine aure ne zaa daura masa da matan da babu wadda yake so aciki,

Daya zabin mahaifiyarsa,

Daya zabin kakansa Kuma baby mamah dinsa Dan haka duk Wanda Bata sakawa Kanta tinanin dayafi karfinta ba itace zata zauna kaantes lfy.

Ana sauran kwana daya daurin auren Ababa yaje Kaantes da maganar kayan daki Kai tsaye suka sanar dashi babu Abinda suke buqata nasa bayan benazir da babynta.

Daman yasan zaayi Hakan Dan haka ya dawo yaci gaba da shirye shiryensa cikin farin cikin samun cikar burinsa.

Benazir kuwa kullum dare sai sunyi Kuka sosai itada Annenta na rabuwar da zasuyi da juna Bada San ransu ba,

Duk yanda Annen takeson daurewa da dannewa kasawa tayi Dan haka duk dare take Shan kukanta a boye

Itama benazir duk dare tareda Annen take kukan daga kwance batareda Annen tasan Benazir tasan tana Kukanba kullum.

Ta bangare Daya a Dan qanqanin lokacin Reno tamkar da uwar data haihu yariga ya shigeta Dan idan ba nono da Bata Hawa Amnah ba tini itama ta sakawa ranta itace ta Haifa Amnah kaman yanda Ababa ya fada.

Renon Amnah yasaka yanzu aikin gidan tini aka dauke mata sai ga me Aiki hande ta saka ankawo mata wata bazawa daga kauye.

*****

Ranar Friday 6 ga watan Sept aka daura auren DAWOOD D KAANTE Dana BENAZIR ABABA kafin daga Baya aka sake daura na DAWOOD D KAANTE din da SAFNAH BASHEER BULAMA.

Daga lokacinda aka gama daura auren Benazir da Dawood Ababa a cikin bainar jamaa ya zube qasa yayiwa ubangiji sujjada ya miqe ya sake Yi Yana miqa godiyarsa ga Allah.

Sunan Safnah da aka ambata gurin daura auren ba biyu ya saka Ababa dakatawa daga farin cikin Dayake yi yana Tino tasa Safnar data gudu Yana jin baqin ciki tareda fatan wannan Safnar ta gudu daga auren Nan kaman Yanda Safnar gidansa ba a gudu.

Taron daurin dauren ya hada manyan mutane masu yawa daga garuruwa daban daban.

Fadan Taron da aka samu a gurin bazai yiyuba

Securities kuwa koina na anguwar da kewanta hakama jiniyas na motocin tsaro koina.

Akwai mutanen DD dasuka halarci daurin dauren da damansu Dan haka dole ya tsaya ya amsa adduoin mutane da dama kafin ya bar gurin daurin auren Kai tsaye gidansa ya wuce sbd Yana buqatan hutu daga mutane.

Naseer ne Daya kasa yarda da benazir din Dayake bibiya ce tin makaranta aka daurawa DD aure da ita sbd yasan dai itace Benazir Ababan.

Suna isowa a natse ya fito mota Kai tsaye ya wuce ciki Yana cewa Naseer kada ya bari kowama yasan Yana gida hutawa zaiyi Yana fama da headache.

Shi Kansa Naseer Yana fama da headache din Dan haka kashe wayar DD din yayi ya ajiye masa ita a palonsa ya fito yabar gidan ya tafi gida Shima ya samu Kansa ya warware Shima.

Yana shiga bedroom dinsa kayan jikinsa na sky blue tsadaddiyar shadda ya ciresu gabaki Daya tareda shiga closet room dinsa ya janyo drawer da towels ke jere aciki ya Ciro Daya ya daura a qugunsa da babu kaya a jiki ya nufi toilet.

Komai Dayake toilet dinsa na musamman ne domin buqatansa sbd baya iya sharing toilet da kowa,baima taba ba duk tsanani baya amfani da toilet koina sai gidansa sai kuwa na part din Bilal Dayayi amfani dashi a kwanakin dayayi Kaantes.

Ahankali ya sakarwa Kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwansa ahankali sbd relief dayaji yafara samu  daga gajiyansa.

Bai dauki time sosai ba yagama ya fito jikinsa da toilet din gabaki Daya ya cika da sanyin qamshin English pear shower gel na Jo Malone.

Daurin towel din qugunsa kaman yanda ya Saba daurawa a sassake kaman zai Fadi yabarsa ya nufi mirror Bai tsaya batawa Kansa time kaman Wani mace ba body oil na Aesop kawai ya shafawa lafiyayyan fatansa dake daukan Ido kaman baby da baya shiga Rana kwata kwata.

Spray kawai ya fesa Wanda ya sake kashe dakin da sanyin qamshinsa ya bar gaban mirror yaje ya saka black Calvin Klein sleeveless shirt da black quarter trouser da slippers masu taushi ya fito Palo ya wuce kitchen ya Bude fridge ya dauko ruwa mara sanyi ya Sha kadan ya koma daki ya kwantawarsa Daman Bai Wani Yi baccin safen ba sbd daurin auren.

Yana kwantawa sbd rashin damuwa da gajiya take bacci ya daukesa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

*******A gidan Ababa kuwa ranar ce ranar farko da Ababan ya sakawa tasa haihuwar albarka Dan kuwa benazir din ya dinga zundumawa albarka ba kunyar Allah bare ta su Benazir din da Annenta.

Kaman yanda akewa kowace haka Anne ta zauna da benazir da idanuwanta suka bushe sukai jajir Bata iya cewa komai sbd ayau nauyin zuciyarta yafi na kullum,

Bata taba tinanin ta wannan hanyar zata rabu da Annenba,

Kuka takeson Yi na barin mahaifiyarta da itama zatayi su barta a hali da rayuwar ukubar da basusan ya zamu sameta a gaba ba.

Kwata kwata takasa kuka tin lokacinda aka tabbatarda an daura auren,

Jajir kawai idanuwanta sukai suka bushe jikinta ne kawai yake rawa a boye Shima sbd halinda zuciyarta ke ciki.

Ita kanta Annen daurewa kawai takeyi tana Hana rauninta bayyana gashi akwai mutane a gidan,

Kaman marayu daga benazir din har Anne babu me walwala ko kuzari suna rakube a daki cikin mawuyacin hali gashi Basu Saba shiga mutane sosai ba Daman.

Su kansu yan bikin duka mutanen hande ne da wasu daga danginta dasuka zo daga kauye Dan haka baa damu da nemansu ba har sai yamma da Ababa ya dawo gidan lokacin kusan duk an watse ba kowa sai su sai baqin hande na kauye mutum uku da suka taho Kuma suna can sunata faman Aiki kaman wasu injin baji ba Gani.

Ana gama sallar magrib Ababa yayi kiransu take gabansu a tare ya Fadi lokaci Daya Anne tayi qasa da kanta tana hade hannuwanta dake rawa ahankali ta damqe tana kasa dagowa ta Kalli benazir data juyo ta zubawa Annen idanuwanta da take suka ciko da wasu ruwan hawaye masu tsananin zafi.

Anne najin daukan hawayen benazir a hannunta ta miqe tsaye tareda juya baya bazata iya kallan benazir din ba hannuwanta na tsananta rawa tana Hana kanta kukan Dayake yanka zuciyarta fitowa ta sunkuyar da kanta.

Benazir data ga Hakan kukanta ya kufce ta kasa motsawa itama sbd Bata taba Jin radadi irin Wanda take jiba a lokacin ba.

Hande dataji shiru shigowa dakin tayi Kai tsaye Bata Jira komaiba ta kamo hannun benazir ta fara Janta tana kokarin ficewa da ita, sai alokacin ne benazir ta iya Bude baki ta kira sunan Annen a hankali.

Kasa juyowa Annen tayi sbd hawayenta dake saukowa da gudu kan fuskarta zuwa kirjinta,

Bazata iya Kallon a rabata da benazir a tafi da ita ba duk da tanason Hakan tamafi Ababan buqatan benazir dinta ta tafi tasamu ‘yanci da rayuwa Mai kyau.

Benazir na ficewa daga dakin ta fasa Wani irin Kuka Mai tsananin ciwo da qarfin gaske tana Jin wannan rabuwar tafi mata ciwo akan ta sauran yan uwanta sbd su tasan mutuwa sukai suka bar duniyar

Annenta kuwa batada tabbacin rayuwar da zatayi a gidan cikin lafiya sbd tafiyarta kawai zata iya tayarda ciwon Annen Kuma babu me iya ko kallanta bare ya taimaka mata.

A palon Ababa suna shiga hande ta dire Benazir din tana cewa

“Kuka takeyi a daki itada uwarta kaman wadda muka siyar gidan wahala.”

Tsoki Ababa yayi sbd baida lokacin duk Wani sabon renin hankali ko Bata masa lokaci Dan haka ya Kalli benazir din fuska a daure babu rahama ko kadan yace

“Babu Abinda zan fada Miki

Kinsan daidai sbd ganganci Daya zakiya akan asalin waye mahaifiyar Amnah ki nema mahaifiyarki ki rasa bat zan batar da ita wlh,

Kiyayewanki shine zaman uwarki lfy,

Gangancinki kuwa a jikinta zataji,

Duk Abinda Zaki zama a Nan gaba kada ki manta uwarki na hannuna itace alqalamin juya rayuwarki a duk inda kike,Dan haka bazance komai ba sai Allah ya Bada zaman lafiya da sa’a,

Kuma wlh karki yarda naji ko naga kinje kin zama baiwa ko wata wawuya a gidan,

Kaantes Zaki zama ki koma hamshaqiyan matansu ta yanda zan Riga fada da alfahari ‘yata ce a gidan ba baiwa na siyar musu ba mata na Basu.”

Chapter 45

45

Benazir kasa ko motsawa tayi da maganganunsa hakama Anne data biyo bayansu ta tsaya daga wajen palon tanajin duka Abinda yake fadawa Benazir tayi qasa da kanta tanajin inama itama ta mutu ya rasa Abinda zai juya rayuwar Benazir a gidan aurenta ta samu tayi rayuwar kwanciyar hankali kaman kowa.

Wani Abu me nauyi ne ya tsaya kirjin Annen tana Jin jikinta na sake sanyi tinda masifar Bata qarewa benazir ba kenan,.Tayaya zata taimakawa ‘yarta qwalli Daya data rage mata a duniya?

Tayaya zata Hana Ababa juya rayuwar Benazir a gidan aurenta.

Wani numfashi ta sauke ahankali hannuwanta na Dan rawa daga tinanikan da zuciyarta ke Bata.

Benazir kuwa numfashi itama ta saki boyayye Wanda yasakata qarasa sarewa daga duniyan gabaki Daya hakama tinaninta ya koma empty Bata ma iya Gane komai yanzu bayan maganar Ababa dake ta amsa sauti cikin kanta.

Kaman makauniya haka hande ta sake kamata ta tayar suka fito

A lokacin ne suka tadda Anne a kofa wadda ta share hawayenta daga idanuwanta da babu sauran hawaye Kuma.

Ga mamakin hande Anne da kanta ta amsa Benazir ta nufi daki da ita ta shiryo benazir din da itama Bata iya komai sai yanda Akai da ita.

Duk yanda hannuwan Anne ke rawa sosai gurin shiryata Benazir na ji Amma Bata iya ko motsawa bare kallan Annen har suka gama ta itama ta sake shiryawa ta dauki Amnah da ta shirya itama ta dorawa benazir din a jiki ta rungumeta ahankali ta suka miqe Anne da riqe da hannun benazir din Daya suka fito.

Hande kallan mamaki takewa Anne data nuna qarfin hali da juriyar shiryo Benazir ta fito da ita da kanta.

Ababa baiyi Wani mamaki ba Dan yasan dole suyi Abinda yace din,

Baiyi mamaki ba sai lokacinda Anne da kanta ta Bude baki tace zata raka Benazir har gidan aurenta idan anbata dama.

Shiru Hande tayi tana kallan Annen Shima Ababan kallanta yayi Yana Maida kallansa gun hande yace

“Ciwonta Daman ya tashi ne shine baku fadamun ba?”

Lumshe idanuwa Benazir tayi batareda ta motsa ba

Itama Anne Dan rufe idanuwan tayi ta Bude ahankali tareda girgiza Kai cikin sanyi tace

“Bai tashiba lafiyata kalau,kawai so nake na Rakata din sbd bansan yaushe zamu sake ganin juna ba.”

Kallanta hande tayi zatayi magana cikin fada Ababa ya katseta da cewa barta ta tafi din tinda Daman ba kowa ne ze raka Benazir din ba ke kince bazaki ba gwara ita ta rakatan.

Da wannan hande tayita fadan waye ya taba ganin uwa ta Raka ‘yarta gidan miji sai akan Annen wadda ita ta tabbatarda haukarta ce ta tashi shiyasa,Daman idan bakada hankali komaima zaka iya Yi.

Anne kuwa hannun Benazir kawai ta kama Bata dago Kai ga fadan hande ba suka fito.

A BMW 7-series aka Aiko Abbakar daukan benazir tareda mum Khadija wadda da kanta ta amso benazir Suka shigo mota harda Anne wadda dukkanin jikinta rawa yakeyi da Abinda yake zuciyarta datasan zai iya zama sanadin rayuwarta Amma tayi na’am da hakan Koda ta rasa ranta tasan ta taimaki ‘yarta takuma tseratar da ita inshallah ta yanda ko bayan barinta duniyar Benazir zata rayu cikin aminci da kwanciyar hankali.

Har suka Isa babu me ko motsi bare magana a motar.

Tin a gate din farko jikin Anne ta tsananta rawa numfashinta na fita da sauri maqoshinta na bushewa tana Jin kanta na juyawa kaman ciwonta zai tashi Dan kusan duk ta fita Hakan takeji matiqar ba komawa gidan Ababa tayiba.

Daga benazir din har Anne babu Wanda hankalinsa da tinaninsa yake kan aljannar duniyar dasuka shigo sbd kusan babu Wanda yake hayyacinsa cikinsu.

Zeenah ce da wasu baqin suka fito suka tarbi benazir Amnah na hannun Mum Khadija suka karbeta cikin farin ciki sukai ciki suna mantawa da Anne dake mota, benazir Kuma Daman babu Abinda take Ganewa sbd kanta ma Dayake Neman juyewa duk inda Akai da ita can take zuwa.

Anne data kasa fitowa hannuwanta da qafafunta na tsananta rawa Wani busashen yawu ta hadiye daqyar kafin ta Bude baki muryarta na rawa tana kallan Abbakar daya Bude mata motar Yana jiran fitowar ta tace

“Inason zanyi magana da dd babba Dan Allah ka mun iso”

Kallanta Abbakar ya juyo yayi cikin mamaki da tinanin lafiya Kuma bayan anyi musu Abinda suke so an auri ‘yarsu.

Kaman zai Bata hakuri akan Hakan sai Kuma dai ya Ciro wayarsa ya kira wayar dd babban ya sanar masa Abinda yake faruwan.

Shi Kansa dd babba shiru yayi Yana nazari sbd baya buqatan ganin kowa yanzu Yana Dan fama da jikinsa da isashiyar lafiya na duk tashe tashen hankalin da akaita shiga a Dan lokacin dakuma auren da aka daura yau Dan haka yace baya buqatan ganin kowa.

Yanda jikin Anne ke rawa tana cikin matsanancin tsoro da ficewan hayyaci ya saka Abbakar cewa ta sanar dashi sakon zai isar mata.

Rawa jikinta ta tsananta ta kallesa tana tattara nutsuwarta ahankali tace zancen yanada mahimmanci sosai dd babban kawai zan iya fadawa gameda gaskiyar haihuwar Benazir ne.

Da sauri Abbakar ya dakatar da ita Yana juyawa koina sbd kada Wani ya jisu yace ta fito ta biyosa.

Kai tsaye palon dd babba ya nufa tana bayansa qafafunta na hadewa cikin tsananin tsoro da fargaba tareda zuciyarta dake hanata Amma bazata iya barin Benazir dinta ta gidan rayuwar aurenta cikin tsoron ranar bayyanar gaskia da Ababa ya ringa juyata kaman babyn roba ba duk da tasan hukuncin Hakan mutuwa ne gareta idan Ababa yaji.

Suna shiga palon Abbakar ya sakawa kofar key ya nuna mata guri ta zauna ya wuce ciki Dan sanar da dd babban.

Zaune take Amma duk sakan zuciyarta dap take da Faso kirjinta ta fado,

Hakama rawar da qafafunta da hannuwanta keyi qaruwa takeyi.

Fitowa dd babba yasakata sauke Kanta qasa Hana Dafe hannuwanta dake qara rawa sosai kirjinta na bugawa.

Zaunawa yayi ahankali cikin nutsuwa Ya dago ya kalleta yana ganin yanda jikinta ke kakkarwa gabaki Daya da alama tana cikin mawuyacin hali na shakkan Abinda zata fada Daya danganci gaskiyar haihuwar data fada.

Shi Kansa zuciyarsa Neman sauya masa tinani takeyi sbd son sanin wace gaskiyar ce take magana Akai.

Daga ita har shi kasa gaisawa sukai da juna ahankali ta Bude baki tafara da fadin Asalin maraicin data taso acikinsa zuciyarta na rawa hawayen Datake riqewa suna cika idanuwanta Amma radadinsu ya hanasu saukowa fuskarta.

Halinda dasuka taso ita da ‘yayanta tafara jero masa muryanta na rawa Yana iya Jiyo quncinta da rashin madafarta a muryarta.

Yanda yayanta suka mutu Daya bayan Daya ta fada masa tareda saukowa qasa ta zube gabansa sai alokacin hawayenta masu tsananin zafi suka sauko ta fada masa gaskiyar haihuwar Amnah tareda fashewa da Wani irin Kuka tana rokonsa akan Benazir marainiyar da batada kowa saisu a yanzu ce.

Barazanar da Ababa zai ringa yiwa Benazir da ita ta sanar masa tareda sake fashewa da Wani irin Kuka mara sauti da radadin zuciyar Datake cikin qunci ta rokesa akan Amanar ‘yarta benazir.

Tinda dd babba yayi gwagwarmayar rayuwa bai taba ji ko ganin Abinda ya tayar masa da hankali ba kaman abubuwan da yaji daga bakin mahaifiyar benazir ba,

Wace rayuwa take fada tayi itada yayanta kaman dabbobi,

Wane irin Uba ne mahaifi wannan Ababan?

Hankalinsa mummunan tashin dayayi yasaka nasa hannuwan rawa Shima ga Wani sabon tinanin tashin hankalin Daya shigesa akan maganar rasuwar sumayyah da Bilal dasuke dauka shi kadai ya rasu gashi yanzu da ana sanar dashi tareda sumayyah ya gudu,

To Yaya Akai gawa Daya aka Gani a motar,

Meyasa tinda Bilal ya rasu Basu taba ganin drivernsa ba Wanda kusan kullum Yana tareda Bilal din.

Me Hakan ke nufi?

Qaddara ce wanna ko Amanar Benazir ne da Allah yakeson damqa masa a hannuwansa sbd tinda ya karbo aurenta yakejin kaman shine gatanta Dana ‘yarta.

Abbakar da Shima duk jarimtarsa Saida ya kasa motsawa daga inda kowannensu yake sbd sarawa Ababa takoina daga kafircinsa gashi a dare Daya Anne ta wargaza masa game dinsa ta shekaru.

Numfashin Dd babba sama sama yake Neman Yi

Da gudu Abbakar ya dauko magani jiki na rawa ya Basa tareda ruwa Yana Dan masa firgita duk da akwai sanyin AC Daya cike palon.

Ajiyar zuciya da numfashi Mara karfi yayita saukewa tsawon lokaci Yana kokarin samun relief na attack dayake kokarin sake samu.

Tsawon mintina kafin ya iya dagowa da idanuwansa dasukai jajir ya Kalli Anne da Abbakar a hankali yace

“Wannan maganar zata tsaya a Nan tsakaninmu kada Wanda ya San gaskiyar ba Benazir ce mahaifiyar babyn Bilal ba sbd zata rasa kaunar data fara samu daga family,

Ni kadai ne nasani Kuma ni kadai zan sani har sai lokacin da nagama bincike akan gaskiyar rasuwar Bilal da sumayyah…..

Kallansa ya Maida akan Anne da ko numfashi Bata iyawa daidai sbd kukan datayi na tsawon shekarun Datake ajiye da maganar rayuwar dasukai da yayanta batada Wanda zata fadawa

Yau ta fada taji Wani nauyi ya ragu a zuciyarta tana fadan Hakan yazama silar samun yancin benazir dinta da ‘yarta a cikin Kaantes.

Cikin dauriya da Bata Wani irin radadin da dd babba keji a zuciyarsa game da dukkanin zancen ya sake kallan Anne yace

“Nayi Miki Alqawarin zama gatan benazir Koda auren jikana ko Bada aurensa ba sbd gaskiyar ki da maraicinku gabaki Daya,

Ababa ya rasa benazir har abada bazai sake samun damarta ba matiqar Ina Raye,

Benazir ta Riga ta zama kaantes daga lokacinda na amsa aurenta wa jikana Dan haka kije adduar samun zaman lafiya da mijinta kawai Zaki mata Amma wahalarta ta qare inshallah.

Wasu hawayen da Anne Bata taba yiba masu sanyi ne suka gangaro mata ta kasa magana sai sunkuyar da kanta datayi qasa tana tana tare hawayenta da tafukan hannuwanta zuciyarta na samun sukunin da ko mutuwa tayi yanzu batada damuwa.

Kirjin dd babba dake nauyi da zafi ne yasaka Abbakar Yi Kansa Yana kokarin kamasa

Dd babban ya dakatar dashi Yana cewa

“Ka maidata gida batareda kowa yasan na ganta ba.”

Da sauri Abbakar din ya Kalli Anne yace su je.

Hawayen godia kawai Anne ta sakarwa dd babba batareda ta iya magana ba har suka fice.

Bata shiga cikin gidan ba Abbakar ya juya da ita zuwa gida a mota tana hawayen bankwana da Bena dinta da batasan ranar da zasu sake haduwa ba.

Kaman yanda dd babba yace kada kowa yasan sunyi magana dakuma alqawarinsa dayayi mata akan Bena yasa Koda ta dawo zuciyarta na da qwari da sukuni Kai tsaye daki ta shigewarta tana Hana kanta hawayen rashin Bena Amma takasa riqe kanta da fasa kukan yau ta wayi gari yanda tazo ita Daya gidan babu ‘yayanta ko Daya a tareda ita.

Abbakar kuwa Yana komawa hankali tashe yadawo gurin dd babba da jikinsa ya rikice gabaki Daya cikin qanqanin lokaci ya sanar dasu dad kaante aka kira likita

Shima Dawood dake gidansa anyi sa’a ya kunna wayarsa lokacin aka sanar dashi dd babban ba lafiya sosai dole ya fito da Kansa ya dauko key din mota ya tuqo da kayan jikinsa na gajeran Nike three quarter da sleeveless hoodie shirt ya nufo kaantes din.

##MAMUH#

#LOVE

#HOTHOT

#DBENA

#BABY MAMAH

#MARRIAGE

#SAFNAH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

46

Koda DD ya shigo kaantes karfe goma Sha Daya,

Parking yayi ya fito Kai tsaye part din dd babban ya nufa inda kusan kowa na gidan Yana can a Palo suna jiran fitowar likitan Dayake Kansa da nurse Daya.

Yana shigowa dukkaninsu suka dawo da kallansu akansa ya qaraso fuskarsa fresh da alaman ya samu isashen hutun Dayake buqata na hayaniya da hidimar yau.

Kai tsaye gurin ummensa dake kallansa cikin nutsuwa da kulawa ya nufa ya tsaya gefenta tareda Dan zagayota da hannunsa Daya Yana Dan babbugawa ahankali alaman komai zai tafi daidai batareda yayi magana ba.

Zaunawa sukai tsawon wasu mintina suna Jira kafin likitan ya fito ya tabbatar musu da dole zasu tafi da dd babban asibiti Koda awanni ne yayi idan ya dawo daidai sai a dawo dashi gida idan Kuma Basu amince ba ya gayyato sauran likitocin asibitinsu suxo a ringa dubasan a gida.

Kai tsaye dad kaante da DD sukace sun amince din Dan haka babu Bata lokaci Akai Kiran ambulance ta asibitinsu akazo aka dauki dd babban Akai asibiti dashi.

Bayan tafiyar dashi DD kaman hannun ummensa yayi ya kaita har cikin bedroom dinta ya zaunar da ita ya fice yabisu Asibitin a motarsa.

Bayan tafiyarsa fitowa tayi ta nufi dakin Zeenah da benazir da Amnah suke ciki harma da Zeenah din.

Zaune suke Bena na bawa Amnah Madara babu kuzari ko walwala a tareda ita.

Zeenah kuwa tana toilet gurin wanka.

Shigowa ummen tayi tana kallan Amnah tace

“Daman tana Shan Madara ne Benazir?

Ahankali benazir din ta Dan gyada Kai cikin sanyi da nutsuwa tace

“Eh madaran Daman kawai take Sha sbd ba ruwan mamah yaqi zuwa.”

Qarasowa gefen gadon Umme tayi cikin damuwa sosai da tausayawa ta zauna tana cewa

“Shine tintina baa fada mana ba da sai ayi wata dabarar da breast milk din zaixo,.Amma gaskia Hakan madaran zallah kawai bazai isheta ba.”

Karbanta ummen tayi tana goge mata baki tissue tana Jin tausayin Amnah din na rashin Nono gashi yanzu har anyi kusan sati uku da haihuwa bare ayi wata dabarar.

Fitowan Zeenah daga wanka yasa ummen kallan benazir dake zaune Kai a qasa tace

“Kiyi hakuri ki kwana a Nan din yau gobe zaa gyara Miki naki dakin ne a canja Miki komai kafin a saka ranar tarewan ki idan kin Dan Saba da Nan din Kuma Dawood din sai yaje Zurich ya dawo saiki tare gaba Daya kinji?

Ki sake jikinki inshallah zakiji Dadin zama damu hakama Amnah.

Ahankali hadiye Wani numfashi Mara qarfi ta Dan dago batareda ta iya kallan ummen ba ta gyada Kai tana Bude baki cikin nutsuwa da sanyi tace

“Nagode.”

Murmush Mai sanyi itama ummen ta saki cikin mutuwan jikin halinda suketa samun kansu aciki.

Miqewa tayi tareda Kwantar da Amnah din zata fice tana cewa

“Zeenah Kinga ga Amnah Nan da benazir kada ki saki ac da yawa sbd benazir na Bata gama jego ba hakama baby Amnah sanyin zai mata yawa ki kula sosai.”

Ficewa tayi tana sake jadaddawa Zeenah wadda taketa cewa to sbd itama tasan bama zata saki ac din sosai ba.

Bayan fitar Umme Zeenah kallan benazir tayi bayan ta gama sauyawa Amnah kaya tayi mata Shirin bacci tace

“Ki Kwantar da ita kema kina buqatan gasa jikinki sbd wannan hidiman dole akwai gajiya.”

Benazir da batasan me zata ce ba hakama bazata iya musantawa sai ta Kwantar da Amnah din ta nufi bayan Zeenah datace ta biyota toilet din ta taimaka mata da sabbin abubuwan amfani.

Duk quncin rayuwar dasuka taso aciki da rashin gata da rufin asiri Allah Bai taba saka musu kwadayin rayuwar datafi karfinsu ba hakama sunada nutsuwarsu a duk inda zasu samu kansu shiyasa data shiga bathroom din Mai kama da wata duniyar daban Bata daga hankali ko Damar da kanta ko Jin tana shaawar tsayawa kallan Abinda yake toilet dinba,wankan ma kasawa tayi ta Saida ta jima sosai tana Kukan data rasa Kona meye kafin tayi wankan ta fito sbd idan batayiba ta fito Kila su baa kwanciya a gidan sai anyi wanka ancire datti komai kankantarsa.

Qaton towel din da Zeenah ta Bata shi ta dauro ta fito jikinta rufe da Wani sbd Bata Saba fitowa ahakan ba.

Koda ta fito Zeenah ta rage hasken dakin sosai Wani qamshi da sanyi kadan ne ya gauraye dakin ni’iman qamshi na ratsa kowane numfashi da zaka ja a hancinka.

Kaya ne Zeenah ta nuna mata Riga da wando masu tsayi da kauri sosai da taushi suna qamshi Mai sanyi tace ta saka.

Karba tayi ba musu ta koma toilet ta Sako ta fito sbd bazata iya tsayawa musawa a rayuwar datasan kaman anriga an siyota ne Dan haka batada Wani zabi bayan yin kusan duk Abinda aka umarceta batareda ta tsaya azabtar da kanta ko batawa Wainda take zamansu lokaci.

Tana sakawa Zeenah ta nuna mata inda zata kwanta babu musu tazo ahankali ta kwanta kaman mara lafiya a rakube ta janyo Amnah cikin jikinta tana rintse idanuwanta tana Jin zuciyarta na Neman karyewa da tinanin a wane hali Anne take ciki a wanna Daren da zata kwanta ita Daya babu ko Daya acikin ‘yayanta.

Zeenah bata jima ba bacci Mai nutsuwa ya dauketa,

Ita kuwa benazir har kusan karfe Biyun dare bacci Bai ziyarci idanuwanta ba sbd radadin rashin sanin halin da Annenta take ciki.

Amnah ce ta motsa daidai karfe uku Dan haka ta tashi zaune ahankali ta sauko gadon jiki ba qarfi ta hada mata Madara da komai da aka aje musu akan bedside.

Madaran ta Bata ta sauya mata pampas harma da Riga sbd sanyin madaran Daya Dan taba rigar kada sanyi ya shigeta.

Tana gamawa ta Kwantar da ita Takoma itama kaman me tsoron kwanciyar ta kwanta tareda rufe Idanuwanta wannan Karan Bata jima ba baccin ya dauketa sama sama.

Rashin baccin datai da wuri ya saka Zeenah kyaleta dataga tasamu baccin sai qarfe 7 ta tada ita tayi sallah.

Zeenah komawa bacci tayi ita Kuma Amnah tasake bawa Madara tanason mata wanka tana jiran Zeenah ta tashi ta Basu ruwan zafi Dan haka ta zauna kan dadduman datai sallah rungume da Amnah data koma bacci itama.

Tana zaune har qarfe Tara na safe lokacin Zeenah ta tashi ta sauko gadon tana kallan benazir din da mamaki tana shafa wuyanta Dan ya Dan sake tace

“Bena a zaune kikai baccin safen ne?”

Girgiza mata Kai benazir din tana cewa

“Ban koma ba Amnah na bawa Madara”

Toilet Zeenah ta wuce tana cewa

“Duk da hakan ya kamata ace kin koma baccin safe sbd samun Qarin lafiya.

Brush tayo ta fito tana kallan benazir dake jiranta tayiwa Amnah wanka.

Komawa sukai ciki ta Tara mata ruwan zafi Dayake Bata Saba ba a roba suke mata a can gida

Itama Kuma Zeenah din kwata kwata batama San ya akewa babys wanka ba Dan haka dole kusan tare sukaiwa Amnah wanka sbd kasawan da benazir tayi ita Daya anan din.

Duka su Biyun sun gama jiqa kayansu Dan haka Zeenah ce ta fito da Amnah tace Benazir din tafara wankan kawai.

Bata jima ba ta gamo wankan da sabulun Zeenah da qamshinsa ya cika toilet din ta fito ta karbi kayan da Zeenah ta miqa mata na wata dagowan Ashape din embellished English super exclusive purple.

Undies data Bata dasu takasa kalla sbd su Basu Saba da panties irin haka ba gajerun wandina suke sakawa Suma hande idan taje siyowa wasu ma kaman na gwanjo,

 hakanan ta saka da sauri kada Wani ya shigo dakin saidai rigar sai takejin kaman ta kamata daga saman tinda Bata Saba saka kaya irin Hakan ba.

Tana gamawa ta zauna ta shirya Amnah wadda tafara Kuka tin tanayi a hankali har tafara Yi sosai duk ta rikita benazir din wadda Daman duk a cikin damuwa da rashin kuzari take.

Umme ce ta shigo bedroom din Jin kukan Amnah din Dayake Neman cika koina.

Shigowar Umme ya saka Benazir sunkuyar da kanta qasa cikin sanyin jiki tana sake rufe kanta da dankwalin kayanta tinda Zeenah bata Bata mayafi ba gashi ita batama San Ina aka Kai nata kayan ba bare ta dauko ciki.

Cikin nutsuwa da girmamawa ta Bude baki a hankali ta gaida Umme.

Amsawa ummen tayi cikin kulawa tana cewa

“Meya faru ne?

Kin Bata madaran kuwa?

Ko kun kwana cikin sanyi Mura ya shigeta ne??

Kasa magana benazir tayi sbd batasan me zata ce ba tinda itama batasan me Amnah din kewa Kuka ba.

Kallanta Umme tayi tace sake hada mata madaran ki kawo mugani.

Ficewa tayi dakin da Amnah tana jijjigawa cikin kulawa da kauna.

Rintse idanuwa Benazir tayi sbd kanta Dayake Neman daukan zafi.

Madaran ta hada ta tsaya dakin ta rasa ina zata dosa sbd Bata Saba wannan free rayuwan dasuke tinanin tayi a gidan ba.

Zeenah ce ta kalleta bayan ta saka doguwan riga mara nauyi tace

“Follow me.” Gaba tayi tana latsa wayarta data kunna lokacin benazir ta biyota a baya kaman mara lafiya sbd rashin kuzari da sanyin jiki.

Wani mahaukacin palon Daya gama Jin komai na Jin Dadin da kake buqata a zaman duniya suka fito komai da koina yagama daukan sanyi da qamshin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Duk inda ta saka tafin kafarta sanyi ya shigeta sai ta rintse idanuwa ahankali tana qanqame madaran Amnah Dayake hannunta.

Dakin Umme Zeenah ta Isa da ita ta Bude suke shiga Benazir din ta tsaya daga kofa

Zeenah kuwa gurin Ummen ta nufa tana Kiran sunan Amnah dake Kuka har lokacin.

Dagowa Umme tayi ta Kalli benazir din tace

“Qaraso kawo abata mugani idan ba Wani abin yake damunta.”

Takowa tayi ahankali ta qaraso ta tsaya daga gefe ta miqawa Zeenah madaran Umme ta amsa tafara Bata cikin sa’a kuwa ta amsa tanasha da sauri.

Gama Bata Akai Umme ta gyara mata jikinta da kanta ta Kwantar da ita take tayi bacci tana sauke ajiyar zuciya ahankali.

Kusan dukkaninsu ajiyar zuciya suka saukar Suma kafin benazir ta silale ta fito ta Maida kanta dakin Zeenah ta zauna qasa a darare zuciyarta ba Dadi Dan batasan Tayaya zatai rayuwa a Nan dinba Kuma,

Duk da alqawarin data daukanwa Anne na zata Kwantar da hankalinta tayi rayuwa me nutsuwa to Amma ta Ina? Tayaya?.

Chapter 47

47

Neman Nisa takeyi cikin tinani da damuwa Akai knocking kofar kafin aka Bude aka shigo.

Masu aiki ne guda biyu suka shigo a tare kowannensu dauke da fararen trays masu kyau dauke da breakfast dinta.

Cikin girmamawa Mai tsananin gaske sukai qasa da kansu suka gaidata.

Shiru tayi Bata dago ba sbd batasan da ita suke ba Dan haka Bata dagoba itama kaman yanda Suma Basu dagoba suka sake gaidata wannan Karan suna Dan dagowa.

Zeenah ce data shigo ta amsa musu tana cewa su Daya a cikinsu yaje ya kawo mata lemon zata ci abinci dashi.

Dayar ce ta fara Jere abincin a gaban Benazir da sai alokacin ta Dan dago ta Gane tin farko da ita suke.

Sake gaidata sukai ta amsa tana Maida musu da gaisuwa itama a sanyaye.

Ana kawowa Zeenah Abinda tace suka fice ta zauna tana kallan benazir data kasa kallan kayan da aka Jere a gabanta qamshinsu na cika hancinta zuwa cikinta.

Chips ne da ketchup da scotch eggs se pepper soup na Kazan da aka cirewa qashi dakuma tea mara Madara me qamshi da zafi sosai.

Bata dauka ita aka kawowa wannan abincin ba saida Zeenah ta sakata cinsa tareda Tayata zuba komai cikin wasu irin plates da suka saka benazir din hankalinta na Neman tashi da wannan rayuwar data samu kanta aciki alhalin mahaifiyarta na can cikin zafaffiyar rayuwa.

Duk yanda Zeenah taso Benazir ta sake taci abincin Bata iya cinsa sosai ba sbd ba cimarta bane irin wannan abincin Dan haka sama sama taci komai taji ya isheta.

Tattara kayan Akai aka fice dasu Mai Aiki ta shigo ta sake gyara dakin ta Kuna humidifier ta fice.

Umme da Zeenah ma shiryawa sukai suka fice zuwa Asibiti dubo dd babba.

Ita kadai aka bari sai Amnah da masu aiki.

Da Rana ma haka masu aiki suka kawo mata abinci aka jera mata

Daqyar ta iya cin kadan tace ta koshi suka dawo suka kwashe.

Kaman mara lafiya haka ta wuni a daki jigum tana renon Amnah duk a sanyaye ba kuzari.

Sai magrib suka dawo har lokacin tana daki zaune ba motsin kirki.

Shigewa sukai kowa yayi wanka suka Dan huta kafin suka fito cin abinci wannan Karan haka aka sakata fitowa zuwa dining Wanda har Akai aka gama Bata iya Sakin jiki ta zauna ko daidaiba bare iya cin abinci a cikinsu.

Dole aka maidata daki aka Kai mata Wani abincin acan Shima Bata iya ci ba saida Umme da kanta ta shigo tace taci.

Yau dinma hakuri Umme ta Bata akan su sake kwana dakin Zeenah kafin gobe.

Wanka sukai kaman yanda Zeenah ta sakata ta shirya ta shirya Amnah suka kwanta.

Yau ma kaman jiya sai kusan hudu ta samu bacci ya Dan dauketa.

Washe garin ranar tana daki masu aiki suka zo aka cire tsadaddin furnitures na dakin dake maqale Dana Zeenah da basuyi komaiba aka saka komai sabo a dakin tareda tsarin abubuwan dakin babys.

Me Aiki aka kawo ranar sabuwa wadda hidiman laluran benazir da Amnah ne kawai aikinta da haka ita aka saka ta Jere kayan lefen Benazir tsaf a closet hakama tarin kayan da aka siyawa Amnah duk ta Jere komai

Duk da babu inda yakeda Wani Abu me suna datti ko qura a dakin Amma Saida Nafisat me aikin ta tsaftace koina ta wanke toilet din da a ranar Shima aka zuba mata toiletries da komai na buqatanta Dana Amnah.

Ac aka kunna tareda qamshin masu Dadi Zeenah ta kawota dakin ta fice sbd wayan da zatayi.

Tinda ta baro gidansu babu Abinda ta dago tayiwa kallan ko sakan uku bare kallan tsaf sai dakin.

Turkish Royal bed ne da set dinsa na komai tareda Wani mahaukacin Katan mirror Daya ci kusan Rabin bangon gefe Daya.

Komai na dakin Ashe ne da fari aka saka sai daukan Idon nuna kudin Dayake cikin siyansa,

A gefen makeken gadon daga qurya gadon Amnah ne fari Mai kyau da tsadan gske Shima hakama da kayan qasan baby a jikinsa,.

Ko beddings dake shimfide a gadon fari ne hakama pillows Akai kusan guda 8 dasuka sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta na mutuwa sosai.

Carpet da table dasu stools harma da sauran kayan dakin kusan tsoro suka Bata saidai batada mafita ko tudun dafawa a wannan rayuwar data tsinci kanta aciki Dan haka ta Tako ahankali ta Kwantar da Amnah ta nufi inda take tinanin toilet ne ta shiga Nan Wani firgicin Yakuma cikata ta ringa saukar da hawaye masu zafin tonowa da Annenta tinanin anan ake nufin zatayi rayuwa Annenta na can cikin halin qaqanikayi.

Sosai tayi Kuka jikinta na sake mutuwa kafin tayo alwala ta fito ta tayarda sallah.

Tana idarwa taga har lokacin Amnah na bacci Dan haka ta koma toilet tayo wanka sbd tinanin al’adar da Dokan gidan ne wanka kafin kwanciya musamman ganin wannan gadan tasan bama zai yiyu ta hau musu gadon ba.

Tana fitowa ta dauko kaya inda Zeenah tace mata ta ringa daukowa ta saka doguwar Rigar jallabiya sbd a kwana Biyun datai dakin Zeenah cikin mawuyacin hali tayi su sbd kayan datake Bata tana sakawa Riga da wando.

Tana gama shiryawa Zeenah ta shigo ta zauna tana Tayata bawa Amnah data farka Madara.

Bayan sun gama Zeenah anan ta kwanta Saida Amnah tayi bacci kafin ta fice musu bayan ta nunawa benazir inda zata Kuna wutar dakin da kashewa kokuma rage hasken.

Zeenah ce ta sakata Hawa gadon kafin ta fice Dan haka tinda ta hau take shiru kaman wadda tayi bacci Amma zuciyarta cike take da tinanin inda ta samu kanta a yanzu.

Baby Amnah kaman tasan sunyi dakin kansu ranar bacci tayi sosai har safe ko madaran Bata farka ta Sha ba.

Suna yin sallar Asuba benazir ta gyara gadan ta sauko da Amnah suka zauna kan tattausan carpet din dake gefen gadon suna gyangyadi.

A gurin bacci ya sake dauketa sai kusan karfe Tara Nafisat ta shigo tafara kokarin gyara dakin ita Kuma benazir tayi toilet da Amnah Dan Yi mata wanka.

Yau ma a jiqe suka gama wankan ta kawota daki ta Kwantar Takoma itama tayo ta fito suka shirya suka zauna jiran tsammani kaman kullum.

Breakfast din na yau a dining aka kirawota a dosane tayisa cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.

Suna gamawa ta silale Takoma daki sukuma suka sake ficewa zuwa Asibiti sbd dd babba da zaa wuce dashi Zurich yaga likitan DD.

Dayake tafiyan tareda Dawood din harma da dad kaante zaayi sai Basu Wani tsaya Bata time ba cikin kwanaki 10 aka gama komai suka wuce Kuma tin ranar da aka tafi da dd babba asibiti Dawood Bai dawo kaantes ba sbd kullum a Asibiti yake haduwa da ummensa harma da dad kaante.

******Bayan tafiyarsu dd babba Umme ta samu nutsuwan dawo da hankalinta da kulawanta kan benazir data fara sabo da zaman daki da rayuwar kadaici data sake samun rayuwarta aciki duk da Zeenah na iya kokarinta gurin ganin tana debe mata kewa da Bata kulawa tareda nuna mata wasu abubuwan.

Wata sabuwar meyiwa Amnah wanka aka dauko dattijuwa wadda ita Kuma aikinta kawai na yiwa Amnah wanka ne sbd mura data fara shigarta na ruwan wanka da kullum saita shaqa sbd benazir Bata iya mata wanka toilet.

A jiki Umme tafara Jan benazir sbd lura da akwai tsoron mutane da rashin sabo da mutane sosai a tattare da Bena din,

Mum Khadija ma da bata cika son mutane ba tana ‘dan kaunar Bena din sbd fahimtar zatayi biyayya makan baiwa ita Kuma Daman tanasan Wanda zai Basu girma da biyayya ya nuna su dinne a sama.

Zaman daki da qarfi da yaji Umme da Zeenah suke Hana Bena kullum indai zasu fito sai ankirata ta fito.

A dosane take zama cikinsu Bata iya magana idan ba tambayarta ummen tayiba ko Zeenah.

Ahankali mura Mai qarfi ta shigeta ita da Amnah sbd sanyi da wankan Datake musu so biyu kullum tinda tazo sbd tsoron shafawa Wani Abu ko gidan datti ganin masu gidan da gidan kaman saika wanke hannu zaka taba su.

Boye zazzabinta Mai tsananin karfi tayi ta danne Bata bari ansaniba tinda haka Suka Saba gida,

Na Amnah ne yakasa dannuwa sbd rigimar Datakeyi ba sassauci.,

Ta Dena baccin dare sbd ciwon Amnah ga nata ciwon ga rigimar Amnah ga kadaici ga damuwar mahaifiyarta sai kawai tafara Neman zauncewa ciwo ya Kwantar da ita gadan gadan harda Kuma Qarin sauyin cima da muhalli.

Hankali tashe aka kirawo likita har gida yazo ya dubata aka duba Amnah itama.

Wannan ciwon da sukai ya saka jikinta yin sanyi sbd kauna me tsananin dataga Umme nayi mata itada Amnah sai Hakan ya taba zuciyarta akan yaudarar ummen takeyi a matsayin wadda Bilal dinta ke tsananin so.

Wannan tinanin ya sanyayar da zuciyarta daga bushewan da tayi batajin kowane feeling a gidan da mutanen gidan.

Idan zatayiwa Umme adalci Bata cancanta wannan yaudarar da ake mata ba Amma Kuma itama Batada zabi sbd ba itace ta zabarwa kanta wannan rayuwar ba.

A haka dole ta fara sakewa dasu Dan faranta ran Umme Dan Zeenah dasuke nuna mata asalin kauna da kulawa.

Da farko kokarin cin cimar da duk aka Bata tafara tareda daurewa tana cin abincin taredasu a dining kowane lokaci.

Hakama takan daure da kanta ta fito Koda dakin Zeenah ne taje,

Kullum da safe da kanta take zuwa dakin Umme ya gaisheta ta dena Jira sai an Aiko kiranta ta fito.

Hakan data fara ba qaramin faranta ran Umme yafara ba Dan haka suka sake dagewa sosai gurin kulawa da benazir din.

*****dd babba ya samu sauki sosai Amma Dawood ya hanasa dawowa sai ya huta daga tashe tashen hankalin da  akaita samu a baya Dan haka sukai zamansu sbd shi Dawood din yanada abubuwan da zaiyi a qasar Kuma ahakan yaqi barin ko so Daya Safnah ta gansa Kuma data kira yace Bai aminta ta samesa ba ta zauna inda take zai nemeta da Kansa.

Wata daya suka share harda sati uku kafin suka fara Shirin dawowa shi dad kaante Daman tini ya dawowarsa yabarsu acan.

*****Acikin wannan watan da satikan rayuwar Benazir a Kaantes ta fara amsa Wani sunan da matsayi na sauyi data fara samu,

Dukiya gaskia ce,hakama rayuwar hutu da daula gaskia ce,

Benazir ta fara samun sauyi na rayuwa Dana fata,

Skin dinta brown ne lafiyayye tin asali,

Su ba maabota yawo bane kullum sune kulle cikin kejin gidansu ahakan suka taso suka girma,

Fara jamiar su kullum jikinsu a rufe yake sbd rashin sitarar arzki da Horan da suka samu

 Dan haka fatarta na fara samun hutun kaantes da tsadaddiyar luxury rayuwar da ake Bata yasaka sauyinta fara bayyana a kankanin lokacin.

Cikowar jiki Kuma Daman ita din bamai jikin qiba bace Dan haka bata sauya ba tanan siririyarta Saidai murmurewan data samu.

Umme ta Siya mata waya itada Annenta aka aika mata driver yakai mata Dan haka tana magana da ita idan Ababa Yana gida ya Bata wayar tayi tagama a miqo masa ya aje.

Shima shirun da yayi ya daga qafa ne sbd sanin dd babba da Dawood din Basa qasar shiyasa yayi shiru sai sun dawo an nitsa yafara sanin matsayarsa.

******Qarfe uku na yamma jirginsu ya sauka Abbakar ne yaje daukosu

Shikuma DD Naseer ne yaje ya daukosa daga airport gidansa Kai tsaye ya wuce saiya huta zaizo kaantes din.

Yana Isa wanka yayi yayi sallah baya buqatan cin komai sai ya huta tukuna Dan haka kwantawa yayi baccin yamma sai 5 da Rabi ya tashi yasake Yin wanka ya fito Kai tsaye yayi kaantes.

Koda ya Isa zaayi sallan magrib Dan haka tareda dd babba suka shiga sallar suna gamawa ya fito Abbakar na biye dashi Yana sake masa barka da dawowa suka nufo ciko.

Sashen ummensa ya nufa Kai tsaye Shima Abbakar ya koma.

Zaune suke a Palo dukkaninsu daga ummen har Zeenah da benazir dake gefen Zeenah suna bawa Amnah Madara a tare yauma rigimar takeyi.

Qamshinsa yayiwa palon dip Dan haka a tare Umme da Zeenah suka dago kallan kofar daidai shigowansa

Sanye da black Balmain three quarter jean da hoodie sweatshirt hasken qafafunsa dake bayyane na daukan idanuwansu kaman koyaushe fatarsa kaman ta sabon baby sbd hutu da luxury rayuwar daya taso aciki yake aciki.

Chapter 48

48

Kukan Baby Amnah ne ya sakasa Dora fararen idanuwansa a gurinsu Zeenah din ya saukar dasu kan Amnah dake jikin benazir tana sake Kai madarar bakinta fuskarta a sanyaye da rashin sanin me zatayi Amnah ta Dena rigiman sbd rigiman Amnah daga rikitar da ita yakeyi Sam Bata San Abinda zai saka Amnah din Kuka.

Qarasowa yayi cikin palon har lokacin idanuwansa akan Amnah batareda ya Kalli wadda ke riqe da Amnah din ba.

Umme kuwa nata idanuwan akan dagayen fararen lafiyayyun qafafuwansa dake bayyane sike duk da tasan sune best kayan dayafi sakawa idan Yana gida Sam baya wahalarda Kansa da kaya masu nauyi ko takura.

Zaunawa yayi gefen ummen a hankali cikin nutsuwarsa ya gaidata batareda wainda ke palon sunji maganarsa sbd rashin daga muryan.

Zeenah dake kokarin gaidasa ne cikin farin cikin ganinsa maganarsa ta katseta kaman daga sama Benazir taji magana daga bayanta cikin sautin kamewa da nutsuwar murya.

“Baby Amnah ce??”

Benazir da maganar ta daketa Kai tsaye sbd Bata lura da shigowar kowa ba hannuwanta rawa suka fara ahankali batareda ta juyoba Dan Bata ma gane meya fada ba sbd nutsuwan muryan.

Zeenah ce ta daga baby Amnah din tana goge mata baki da lallaunsa pink baby hanky ta taso ta nufosa tana cewa

“Sannu da dawowa Yaya DD.”

Babyn yake kalla harta iso gabansa tana sake cewa

“Baby Amnah ga daddy ya dawo ki Dena rigiman haka.”

Sai alokacin ya juyo ya Kalli ummensa da idanuwansa dasukai Wani Dan shigewa da alaman “da gaske Amnah ce wanna?”

Murmush Mai yalwa Umme ta saki tana karban Amnah din daga hannun Zeenah tana sake goge mata Dan qaramin bakinta na mahaifinta data dauko Zak da Zak ta gyada masa Kai tana cewa

“Eh Amnah ce,gatanan duk ta ruda mummynta sbd rigimanta.”

Numfashi ya sauke a hankali mara sauti Yana kallanta daga hannun ummen Yana son daukanta Amma Bai San ya zai daukota ba sbd shi ba maabocin daukan Yara bane,

Bayama daukan Yara Sam Amma Kuma wannan tasa ce Yana Jin buqatan daukanta kaman yanda kowane Uba yake daukan ‘dansa idan an Haifa masa.

Dariya Umme ke masa da Zeenah lokacinda Umme ke kokarin Dora masa Amnah a hannuwansa Dayake Jin kaman zaa Dora masa farin cikin rayuwarsa ne kaf.

Ita kanta Amnah din kaman tasan gurin waye zata je dan haka tayi shiru idanuwanta a Bude.

Lokacin da Umme ta gama Dora masa ita ta janye hannuwanta suka barsa da ita ajiyan zuciya ya sake saukewa a Karo na biyu yanajin tsaftatacciyar kaunarta me qarfi da sanyi na sake kama zuciyansa,.

Yanzu shine uban wannan kyakyawan babyn ta hannunsa,

Daman haka feeling na zama Uba yake da sanyin nutsuwa?

Meyafi wannan kyakyawan babyn ta hannunsa a rayuwarsa yanzu??

Dagota yayi ahankali ya Karanto mata addua a natse cikin qaramin sautin da babu Wanda yaji tukuna ya miqe tsaye da ita a kafadansa ya fice zuwa palon dad kaante yana tafiya kaman bayason jijjigata hakama Bai Wani iya riqeta sosai ba sbd Bai iya dinba.

Yana fita Benazir data kasa motsi bare juyowa ta miqe tsaye a hankali cikin nutsuwa ta dauki kayan madarar tayi kitchen ta miqawa Nafisat Dan da tsaftacesu ita Kuma ta nufi daki hannuwanta na rawa bugun zuciyarta Datake ta riqewa sbd bugawan Dayake da qarfi Yana qaruwa.

Bedroom dinta ta nufa ta shige tareda qarasawa kan sofa ta zauna ahankali tana damqe hannuwanta dake Dan rawa.

Babu Wani tinanin Dayake ranta bayan na firgicin data shiga duk da tanada dauriya da nutsuwan danne firgicinta.

Zaunawa tayi a dakin shiru Bata fita ba tanata daidaita kanta Daga tsoro da fargaban data shiga har tsawon lokaci kafin ta tashi ta fada toilet tayo alwala ta tayarda sallar ishai tayi ta gama.

Tana tashi daga dadduman sallah mayarwa tayi ta nufi toilet Dan Yin wanka.

Tana shiga Bata Wani jima ba ta fito ta shafa Mai sama sama tayi duk Abinda zatayi ta saka doguwan Slianche free gown black da fari kadan a ciko har qasa tana kokarin daukan wayanta tagani ko zata samu magana da Anne Nafisat ta shigo ta sanar da ita lokacin dinner yayi.

Sauke numfashi Mai dumi tayi ahankali tareda ajiye wayar 

 Jikinta na mutuwa kafin ta miqe ta fito.

Tana fitowa Zeenah na fitowa daga nata bedroom din sanye cikin Riga da wandon Fendi masu Dan kauri ta shaqi qamshin Benazir din Mai sanyi Dayake Dan tashi jikinta tace

“Muci abinci muje mu duba dd babba tareda masa barka da dawowa.”

Gyada Kai benazir din tayi tana qarawa da cewa to.

Suna doso dining din Yana sake shigowa palon a Karo na biyu rungume da Amnah datai bacci a jikinsa.

Da nutsuwa yace

“Zeenah karbeta I think ta gaji or may be she’s hungry or something tana son farkawa kaman.”

Benazir data kasa gaba ko baya ta tsaya bayan Zeenah kanta a sunkuye shikuwa Yana bawa Zeenah Amnah ya nufi dining gurin ummensa.

Qarasawan da Benazir bataiba kenan ta juya dauketa Amnah Takoma daki batareda itama ta iya Koda tsautsayi daga Kai ta kallesa ba kaman yanda shi bai ma yi noticing nata ba.

A daki taci abincinta bayan tagama shirya Amnah tayi bacci sai tabarwa Nafisat ita suka fita zuwa sashen dd babba.

Dan mayafin Dayake kanta yasakata kakkame jikinta sbd gabaki Daya babu mayafin kirki a kayan da aka Siya mata Tin daga kan na lefe har Wanda aka sake sissiya mata bayan auren.

Da sallama suka shigo Zeenah ce a gaba sai Benazir din bayanta kaman yau aka kawota gidan.

Idanuwan dd babba akan Benazir tin shigowansu Kuma acikin mintina qalilan ya Karanto nutsuwa a tattare da ita Kai tsaye Dan haka ajiyar zuciya ya sake saukewa a Karo na biyu tareda amsa gaisuwar datai masa kanta qasa cikin tsananin girmamawa da ladabi.

Numfashi ya sauke tareda sakar mata a fuska cikin kauna da kulawa ya tambayeta Yaya baquncin sabon guri.

Kanta ta sake yin qasa dashi cikin sanyin murya da nutsuwa tace lafiya kalau.

Amnah ya tambaya itama tace lafiyan kalau.

Cikin hikima da nutsuwa yayita yan mata tambayoyi har akan karatunta yaji inda ta tsaya take ya yanke shawarar zata koma makarantarta tinda ashema hutun ya qare tin last 3 weeks.

Tariga ta cire tsammani daga komawa makaranta Dan haka tana Jin zancen nasa ta dago ahankali Amma Bata iya kallansa ba tayi godia cikin sanyin jikin yanda zatayi karatu da Amnah,

Kwatsam mutane su ganta da haihuwa ba aure.

Dd babba hanata tafiya yayi Saida yayi mata tambayoyin Daya gamsu da tafara samun sabo da kwanciyar hankali a Kaantes Dan haka ya sallameta ta tafi.

A Karan farko itama data samu nutsuwa da sanyin kwanciyar hankali da Wani Kai tsaye a cikin Kaantes din bayan Zeenah da Umme.

Jin tayi kaman ta samu Wani sabuwar nutsuwa da yanda dd babba ya mata nasiha tareda Bata tabbacin ta Kwantar da hankalinta a qarqashinsa babu Wani Abu dazai sameta ko Annenta duk da Bai fito ya nuna mata yasan komai ba.

Tana dawowa tini Zeenah ta shige hakama umme Bata ma sashen tana gurin dad kaante Dan haka itama shigewa tayi tayi Shirin bacci ta sallami Nafisat ta tafi sashen masu aiki ita Kuma ta shige bargo da Amnah dake bacci sosai har lokacin.

Washe gari suna cikin breakfast hajar me aikin Umme ta shigo har dining room ta sanar dasu Abbakar ya Aiko cewan Bena ta shirya za’a kaita makaranta.

Daga Umme har Zeenah sosai sukai farin ciki da Hakan Dan haka sama sama ta qarasa breakfast din ta miqe taje ta shiryo ta fito cikin wata Kuwait jallabiya me tsadan gaske maroon Bada mayafi bare hijab Dan haka dole kaman yanda Zeenah ta fada mayafin rigar ta Tayata nadowa suka fito gabanta na tsananta duka sbd yanda zataje school da ‘ya Amma Kuma hankalinta zai rabu biyu bazata taba samun nutsuwan karatun ba matiqar ba da Amnah taje ba Dan haka tini ta shiryata fes cikin designer kayan babies masu taushi da rashin ado aka nadota a pink shawl sai qamshi takeyi suka fito Nafisat na bayanta dauke da baby bag dinsu ta kayan Madara da komai na buqata da amfanin Amnah din.

Daga takalmin qafarta har chanel handbag din Dayake hannunta batasan kudinsaba Amma a yanda nutsuwarta yake Zaka dauka komai na jikinta ta San kudinsa Jan ajine takeyi Amma ha Hakan bane.

Bayan kwallin cikin fararen idanuwanta babu komai a fuskarta sai facemask Wanda Zeenah ta Koya mata amfani dashi ko acikin gida wasu lokutan,

Ita kuma Zeenah ta dauki dabi’an ne Daya yayan nata da babu inda zashi Bai sakasa sbd baya San ana yawan kallansa sai gashi Allah yayi masa wata irin haiba da kwarjinin da duk inda yaje zaa kallesa din sbd Wani nutsatsan kyau da ajin kamewa ne dashi.

Har mota Zeenah ta Rakata Driver ne sabo aka kawo yau din sbd kawai Kai Bena makaranta Kuma a Daya daga cikin motocin dd babba ya ware mata Dan kaita kawai da daukota.

Driver na ganin isowarsu ya fito da sauri ya budewa benazir din mota Yana mata barka da fitowa.

A mutunce cikin fargaba da tsoro ta amsa har Saida Zeenah a ta Bata qwarin gwiwa ita fa kaante ce yanzu ba buqatan Jin fargaba ko Jin nauyin girman da zaa ringa Bata.

Nafisat a gaba ta zauna Dan haka benazir din ce kawai a baya ita kadai sai Amnah dake jikinta.

Wayarta ta fidda tana son Kiran wayar Anne Amma tasan wayar na hannun Ababa lokacin Amma tinda ance driver ya biya da ita ta dauki takardun makarantar Datake ganin tana buqata wainda duka ta baro gida sai takejin gabanta na tsananta faduwa duk suka qara kusanci da Isa gidan.

Tsoro ne da rawa hannuwanta keyi sosai na Ababa Daya dasa musu a cikin ransu da har abada bazasu iya goge wannan tsoron ba.

Id card dinta kawai take buqata daga takardun makarantar data bari gidan Amma zuwan nata Sam Badan Id card din zatayisa ba sbd buqatan ganin Annenta ne da suka Dade Basu ga juna ba saidai a waya.

A kofar gidansu lafiyayyar motar tayi parking sai Data sauke ajiyan zuciya da numfashi a Jere kusan ba adadi zuciyarta na bugawa da qarfi cikin tsananin tsoro da shiga tashin hankali.

Tana cikin wannan firgicin ne Driver ya Bude mata kofa bata ma saniba Saida ya kira sunanta cikin girmamawa da a nutse.

Fitowa tayi qafafunta na Dan rawa tana damqe hannuwanta dake rungume da Amnah.

Kai tsaye kofar shiga ta nufa Nafisat na bayanta kaman jela dauke da jakar kayan madarar Amnah.

Chapter 49

49

Daqyar sallamarta ta fito daga maqoshinta lokacinda ta shigo tsakiyar gidan sbd tsoron da zuciyarta take ciki.

Duk da ba Wani sosai ta saka tirare ba Amma tsadansa ya sakashi sauya iskan tsakan gidan ahankali da sanyin qamshi hande dake daki bataji sallamar ba qamshin taji iska ya Dan kado mata shi daga waje take ta fito sbd tasan dole baqine suka shigo gidan.

Anne kuwa zaune take tsakar gidan tana Yanke farcenta da wata tsohuwar Reza wadda da benazir dince ta Saba Yanke mata farcen

Har cikin tsakiyan zuciyarta sallamar benazir din ta ratsa sbd take tasan Bena dinta ce Dan haka ahankali ta dago jikinta na sanyi da mutuwa wasu hawaye masu zafi suka ciko idanuwanta dake bushe tana kokarin maidasu kada Benazir ta gani.

Benazir kuwa ganin Annenta kadai tsakar gidan ya sanyata qarasowa da wuri ta nufeta qafafunta na rawa Basu tsaya janye Amnah a tsakaninsu ba Benazir ta rungume mahaifiyarta tana Jin dukkanin qarfin zuciyarta na karyewa.

Hande data fito salati me qarfi ta sake ganin su a Hakan Wanda ya saka Ababa Dayake shirin fitowa fitowan da sauri Yana cewa hande saita kashesa wata Rana da wainnan salatin nata masu daga hankali.

Yana fitowa idanuwansa akan Anne ya fara sauka Saida ya duba dakyau ya tantance Benazir ce

Gyaran murya yayi suka saki juna ahankali suna tsayawa gefen juna kan benazir qasa tana hadiye yawun zuciyarta dake bugawa da karfi.

Da sanyin murya me taushin data fara samu na nutsuwan rayuwar data fara samu ta Bude baki muryarta na Dan rawa ta gaidasa.

Bai amsa ba ya Tako ya qaraso gabansu ya tsaya cikin sake tsuke fuska ya miqa hannu ta miqo masa Amnah dake bacci ya karbeta.

Kallan babyn yake Yana Jin farin cikin  ganinta,

Bai taba kaunar ko nasa ‘yayan ba Amma ita cikin ransa yake jinta sbd ta zama silar arzikinsa da ‘yayansa suka kasa zama sanadin.

Dagowa yayi ya kalli Benazir murya a zafafe ya tambayeta metazo Yi

Shiru tayi kanta a qasa

Cikin zafi ya sake cewa

“Me na fada Miki?

“Babu ziyara matiqar ba nine na buqata zuwan naki ba Kuma ba yanzu zan buqata Hakan ba sai kin zaunu cikin Kaantes kin jiqu yanda ya yakamata,

Annenki zata biya duk Wani hukuncin laifin ki wlh sbd bansan hakuri ko asara ba.

Rufe idanuwanta tayi ahankali kanta na sake Yin qasa hannuwanta na Dan tsananta rawa.

Ahankali ta Bude baki ta sanar dashi Abinda akace tazo dauka makaranta zata.

Gyara tsayuwa yayi cikin Jin Wani lissafin na Hawa Kansa Jin anfara considering dinta as kaante itama tinda aka ware mata mota da drivern kanta.

Hana farin cikin fara samun Abinda yake Neman yayi ya Dan daure murya yace taje ta dauko ta fice daga gidan.

Juyawa tayi qafafunta na Dan rawa da  sanyin jiki ta nufi dakinsu ta shige Anne na bayanta.

Suna shiga ta dakata tareda juyowa ta Kalli Annenta da itama ita take Kallo zuciyarta na wadata da sanyin ganinta tareda farin cikin ganin dd babba ya dauko hanyar inganta rayuwar Bena dinta kaman yanda yayi mata alqawari Dan haka itama zata qara juriya da hakurin kowace irin ukuba da wahalar gidan har lokacin da dd babba zai gama bincikensa akan rasuwar su sumayyah tukuna ya dauki mataki akan Ababan da dalili.

Hannuwanta ta daga ahankali ta zaunar da Anne qasan tsakiyar dakin da tini aka dauke katifar ciki.

Rezan sake hannun Annen ta karba ta durqusa ta Yanke mata duka farcenta cikin kulawa da sauri.

Tana gamawa suka miqe tare Anne da kanta ta dauko mata id card dinta inda yake ta kama hannunta ta saka mata cikin murya Mai bayyanarda jarumta da kauna tace

“Karki sake dawowa Nan ki zauna gidanki kiyi ingantacciyar rayuwa,

Ki nutsu kiyi karatunki ki inganta kanki ki samu Daman Gina taki rayuwar da Zaki samu Daman samun ‘yancinki,

Inshallah zanyi dauriya nayi juriya Zamu tsira da yardar Allah,

A baya Banda qarfin zuciyan fatan rayuwa me nutsuwa Amma a yanzu inadashi sbd ke Bena Dan haka kije na yafe karki dawo Nan din saikin Gina rayuwarki me kyau Allah ya sadaki da dukkanin Alkhairi da farin cikin gidan ki.

Duk Wani gabar jikin benazir Saida yayi sanyi ya sake da maganar Annenta hawaye ya ciko idanuwanta Amma ya kasa saukowa sbd Wani irin sanyin jiki Dana zuciya da zantikan suka sakar mata tare Kuma da qwarin gwiwa.

Sake rungume Annenta batareda ta iya cewa komaiba sbd zasu iya fashewa da kuka su dukan idan ta Bude baki Dan haka ita kadai ta fito Anne tayi zamanta daki.

Hande na daki tana jiran shigowar benazir din dakin har ta fice bata saniba a waje ta tadda Ababa Yana lissafin motar da aka bawa benazir din zata fi miliyan Dari.

Tana fitowa driver ya Bude mata motar ta shige ya rufe.

Ababa da Kansa ya Kwantar da Amnah gefen benazir ya rife kofar motar Yana Jin zuciyarsa fal haske da lissafi.

Suna barin kofar gidan Benazir ta lumshe idanuwanta ahankali hawayen Datake riqewa suka gangaro mata ta Ciro handkerchief me taushi daga Jakarta ta share fuskarta ahankali tana Jin zuciyarta na sanyaya da rabata da mahaifiyarta da Akai Wanda takejin zatayi karatu inshallah tuquri ta inganta rayuwarta ba iya zaman kaantes ba tana buqatan yiwa kanta nata sunan bayan na kaantes Dan samun iKon karban mahaifiyarta,

Zatai karatun da zata Tara arzikin da zata Siya mahaifiyarta daga mahaifinta ko nawa ne inshallah.

Sake share hawayenta tayi tana sauke numfashi Mai zafi da ajiyar zuciya.

Kai tsaye jamia suka Isa hankalinta na kwantawa daga tinanin duk Wanda zai ganta da baby,

Basa muamala da mutane ko a baya Dan haka babu damuwanta ga duk Wanda zai ganta da babynta.

Parking driver yayi Bata Jira ya Bude mata ba ta Bude ta fito rungume da Amnah ta wuce Nafisat na bayanta suka nufi inda zata samo tabbacin komai na hutun da aka dawo su timetable da lectures da Akai da sauransu.

Cikin sa’a yau din sunata lectures in the next 20 min masu zuwa Dan haka taje duba results dinta na last semester data San ba lallai ma taci ko Daya.

A sa’arta taci courses uku ta fadi sauran 5 Dan haka Bata Wani damu ba tinda tasan yanzune zata dage tayi karatun Kaiwa matsayawa.

Da zasu shiga lectures Nafisat ta goyawa Amnah bayan ta Bata Madara Tasha Takoma bacci.

Mota Nafisat suka koma sbd babu inda driver ya tafi Yana Nan saita gama idan dare zata Kai zai Jira tinda aikinsa kawai shikuma na ta ne.

Suna fitowa 12 to 2 kai tsaye mota ta nufo tana Isa wayarta dake jaka kira ya shigo

Cikin Wani irin sanyi ta Ciro wayar sbd bayan Su Anne babu Wanda take magana dashi a wayar.

Sunan Umme tagani ahankali ta sauke ajiyan zuciya sbd wannan shine Karo na farko data fito kaantes tin kaita shiyasa ummen duk ta Dan damu sbd Amnah da Bata fita Rana.

Daukan wayar tayi cikin nutsuwa da sanyin murya tace

“Umme Ina wuni”

Ajiyan zuciya ummen ta sauke daga can bangaren tana cewa

“Bena Yaya makarantan?

Akwai Rana da yawo ko?

Ga Amnah tanata rigima Kila ko?

Ajiyan zuciya Bena ta sauke tana lumshe fararen idanuwanta zuciyarta na na’am da kaunar Umme akansu Dari bisa dari Dan haka tayi kokarin gwada Sakin murmushi me sauti tace

“Amnah a mota na barsu tin dazu Nima yanzu na fito daga lectures din Amma zamu sake shiga 2 zuwa 4.”

Ajiyan zuciya ummen ta saki tana cewa “ok ki kula da kanki da Amnah akwai Rana sosai,saikin dawo.”

Ahankali ta iya Bude bakinta dayayi nauyi sbd mutuwar jikinta ta furta “Nagode Umme Allah ya saka da Alkhairi.”

Murmush kawai ummen tayi tareda kashe wayar daidai shigowan DD palonta Yana amsa wayan Safnah da kusan kullum take kiransa ahankali,ita wannan dake gabansa baimayi noticing nata ba hakama Bai taba tambayar ta ba sbd baisan Tayaya zai fara kulawa ko Neman matan yayansa daya rasu tinda dai Amnah dinsa zai ringa ganin babynsa Hakan ma is ok.

Sallah Bena tayi a mosque na mata

Ta bawa Amnah Madara ta canja mata diaper da kaya zuwa Versace overall marasa nauyi da qamshi kafin suka koma ta shiga lectures suka zauna mota.

Sai 4 har da Rabi suka baro makarantan suka nufi gida.

Suna Isa driver yayi mata Saida safe ta wuce Nafisat na biye da ita gajiye duk da Bata ciki yunwa sbd akwai biscuits da drink da Umme ta sako musu cikin jakar kayan Amnah.

A gajiye suke sbd sabon da suka fara samu daga ita har Nafisat me aikin nata na zama guri Daya cikin hutu.

Babu kowa a palon Dan haka Kai tsaye dakinta ta wuce ta tube ta fada toilet Saida tayiwa Amnah wankan tayi tayo alwala ta fito ta shirya cikin Riga da straight skirt na atampar super wainda kusan duka atampopinta babu qarama bare laces da baa maganar kudadensu.

Sallah tafara Yi kafin ta shirya Amnah cikin guntayen overall blue da safa Mai taushi itama suka fito zuwa dakin Umme Dan gaidata.

Suna zuwa tayi knocking ahankali ta Bude ta shiga ahankali ummen na zaune tana amsa waya cikin nutsuwa.

Tana ganinsu ta sake fuskarta da farin ciki tana miqa hannu ta karbi Amnah din tana ci gaba da wayarta.

Bena kuwa ficewa tayi ta nufi dakin Zeenah batanan Dan haka ta fito ta nufi kitchen acan taci Brown spaghetti da aka dafa Dan ita kawai da yamman.

Sama sama taci ta koshi sbd Sam batada cin abinci sosai hanjinsu sun Dade da tsukewa daga Horan da Akai musu tin tasowansu.

Ruwan sanyi Tasha kadan kafin ta kamawa su Madam beba aikin abincin dasuke Yi na dare.

Tuwon semovita sukai da Miya kala biyu sbd banbancin raayi kowa yaci wadda yakeso.

Ita tayi miyan fresh veggies da Alayyahu sai uban Naman Kazan da babu qashi da nikakken nama

Madam beba kuwa miyan yauqi sukai da kifi da Naman rago.

Suna gamawa Zeenah na dawowa ta Kalli benazir din tana tambayarta me takeyi a kitchen.

Murmush kawai tayi ta sanar da ita Aiki sukai na abinci.

Sallar magrib tayi Bata fito ba sai bayan datai ishai dinta ta miqe ta fito.

Tana saka qafarta tsakiyar palon hancinta ya shaqar mata qamshin Daya sakata dakatawa sbd sanin Yana kusa kokuma Yana cikin palon Dan haka ta silale Takoma daki.

Koda aka Aiko kiranta cin abinci cewa tayi ta Kasho Bata Dade da cin spaghetti ba.

Kyaleta sukai sukaci abincinsu batasan DD baya part din ba shigowa yayi Kuma ya fita da Amnah.

Saida ta tabbatarda sun gama cin abinci ta fito Zeenah ta Rakata gurin dd babba gaidasa da masa godian komawarta makaranta.

Sun shiga Zeenah ko qarasawa batayiba ta juya sbd Kiran Daya shigo wayarta Dan haka ita kadai qafafunta na Dan rawa ta qararasa cikin palon da sallama a natse cikin siririyan muryanta me sanyi kanta a qasa.

Kallan Dawood da Bai dagoba dd babba yafara Yi kafin ya amsa sallamarta tareda Kiran sunanta

“BENAZIR? Qaraso ki zauna kinji.

Sunan da dd babba ya ambata ya saka DD dakatawa daga kallan datakewa Amnah cikin nutsuwa da tsananin kauna Amma Bai dagoba duk da sunan ya tabbatar masa da Mummyn Amnah dince ake nufi.

Itama Bata dago ba bare ta iya kallansu batama San waye da waye a palon ba Dan haka kanta a qasa ta zauna natse kaman yanda dd babba ya umarceta.

Chapter 50

50

Bude baki tayi nutsuwar muryanta a bayyane ta gaida dd babba cikin ladabi da sanyi.

Murmushi me sanyi dd babba ya sake cikin kulawa ya amsa tareda tambayarta Yaya school.

Sake Dan qasa tayi da kanta tana damqe hannuwanta dake Dan rawa cikin nutsuwa tace “lafiya kalau.”

Dawood da kaman baya gurin dd babba ya kalla kafin ya Maida kallansa kan benazir din da ita Kuma batasan ma da waye a gurin ba ya Dan sauke numfashi Mai sanyi da kulawa sosai yace

“Benazir ga mijinki Nan a zaune ki gaidasa.”

Faduwa Mai tsanani gabanta yayi kirjinta ya fara bugawa da qarfi ahankali ta Dan karkata gefensa batareda ta dago ba kanta a qasa ta Bude baki muryarta na Dan rawa sbd sanyi tace

“Ina wuni.”

Shi Kansa DD din shiru yayi na seconds sbd kalman dd babba ta cewan ga mijinta a zaune yasa ya Tina da auren mata biyu ne a hannunsa wainda babu wadda yasan ta inda zai iya sakata a mizanin lissafin rayuwarsa harma da matsayi na matar da ake tinanin yayi rayuwar Jin dadi kwanciyar hankali da nutsuwa da ita.

Batareda ya juya ya kalleta ba ya amsa Kai tsaye tareda miqewa ya fice Yana Ciro wayarsa da kiran Lizz ya shigo.

Bayan fitarsa dd babba ajiyan zuciya ya sauke tareda numfashi kafin ya saki qayataccen murmushi mara sauti ahankali Yana jinjina Kai.

Benazir data kasa motsi ya kalla yace

“Jeki benazir ki saki jiki kiyi karatunki ki qarasa wannan session din a gwada sauya Miki gurin karatun “

Godiya ta sake masa cikin sanyi tareda masa fatan Qarin lafiya tai masa seda safe ta fice.

Ita kadai ta Isa sashensu Dan haka tana Isa babu kowa a palon tana dap da Isa dakinta taji kukan Amnah ta juyo Kai tsaye sbd mantawa a hannunwa Amnah din take tintini.

Juyowanta yayi daidai da shigowansa palon Shima Yana kokarin riqe Amnah din dakyau sbd kaman zata Fadi da motsin kukan datakeyi.

A kyakyawan farar fuskarsa idanuwanta suka sauka gabansa a yayi mummunan faduwan Daya saka hannuwanta rawa da fitan numfashi da sauri tayi saurin dauke idanuwanta zata shige daki taji muryarsa me nutsuwa da kamewa yace

“Karbeta.”

Saida ta damqe hannuwanta ta tattara nutsuwanta guri Daya kafin ta iya dago qafafunta ahankali ta iso gabansa ta tsaya

Ya dago Amnah ya miqa mata tasaka hannuwanta dake Dan rawa ta karbeta tareda juyawa Kai tsaye tayi bedroom dinsu ta shige

Shi Daman tin kafin ta juya ya juya Yana cigaba da amsa cikin rashin daga hayaniya.

Bayan shigarta daki Hana kanta zama tayi bare dadewa acikin rawar hannuwanta da faduwan gaba ta hau kintsa Amnah hannuwanta na Dan rawa har lokacin.

Tana gama shirya Amnah itama tayi Shirin kwanciyar ta kwanta tareda rintse idanuwanta.

***Washe gari morning lectures take dashi Dan haka da wuri ta shirya tayi breakfast a dining tareda Umme da itace ta hada musu kaya a jaka yau ma Zeenah Kuma tana bacci suka fice yauma cikin wata tsadaddiyar Noriea Abaya ash da Rolling.

Sai yamma ko yau din ta dawo a gajiye sosai,

Sallah magrib tayi tayi wanka tea kawai Tasha ta kwanta bacci ya dauketa tabar Amnah a can gurinsu Umme

sallar ishai ma sai cikin dare ta farka tayi taga Amnah kwance gefenta an Kwantar mata tasan Umme ce ko Zeenah suka kawo mata ita.

******Ahankali rayuwar makarantan da Amnah ta sabo da ita tin tana Jin stress da gajiyan Hakan harta Saba Bata Jin komai yanzu musamman Mai aikinta Nafisat na kokari sosai gurin kulawa da Amnah Bata wasa da lamarin Amnah ko kadan,. hakama drivernta Ahmed Yana mata biyayya kaman Bai girmeta nesa ba kusa ba Amma sbd a qarqashinta yake biyayyarsa tayi mata yawa take Gani.

Rayuwar gidan ta Saba a yanzu da ita kusan ta ko Ina,

Dd babba kauna me tsanani da kulawa yake nuna mata Wanda kusan kowa ya fara shedar da Hakan musamman da yanzu takai komai nata kaman ba lissafi ake Siya mata har Abinda Bata buqata sosai Dan haka itama a zuciyarta matsayin dd babba da Umme a ranta daban suke,

Tana Jin su kaman zata iya iya komai dominsu kaman yanda zata iya komai domin Annenta idan Bai Saba sharia da musulunci ba,

Wannan ya sakata Sake kokarin Sakin jikinta tana sabawa dasu sosai.

Har lokacin Bata sake haduwa da DD kaante ba sbd kusan duk lokutan Dayake zuwa gidan Bata Nan kokuma ta shige Dan haka Sam Basa haduwa hakama bisa ga umarnin dd babba babu Wanda yayi wa Dawood din maganar yanada mata a gidan kaman yanda Shima ya nuna ya manta kokuma Daman auren Dan karban Amnah ne yayisa.

Kullum sbd Amnah yake zuwa gidan ya dauketa sai idan zai tafi zai dawo da ita,.Hakan yasaka yanzu benazir barinta wasu lokutan idan zata tafi makaranta.

***Lokaci ya Dan ja ahakan har sukai exam suka sake samun hutu Kuma alhmdllh wannan Karan karatun me nutsuwa da kwanciyar hankali takeyi.

Ababa Bai taba kiranta ba sbd kudin da dd babba ke Basa Yana dakatar dashi daga Neman Benazir sbd ta samu nutsuwan karatunta ba tsoro ko firgicinsa,

Annenta kuwa a yanzu dd babba da Kansa yake saka Abbakar Yana kaiwa Ababa ziyara Akai Akai ana dubo lafiyarta tin komai sai ahankali ake tafiyar da rayuwar.

Ababa da ake Kaiwa ziyara Akai Akai ta sakon kudi Kuma baa tura masa ta bank a hannu ake Kai masa dole ya ringa inganta rayuwar Anne sbd duk Abbakar yazo ya ringa kame kamen kada ya Gane Annen na cikin tsananin ukuba da wahala ga ciwonta ya tashi babu Wanda ya sani

Dan haka dolensa ya ringa inganta Annen da abinci da kulawa sbd yawan zuwan da ake masa.

Koda dd babba ya tabbatarda sun samarwa Anne sauki ta Hakan sai ya bawa benazir tabbacin Annenta yanzu tana cikin Aminci inshallah Dan saita Kwantar da hankalinta tayi Abinda Annen kesan tayi.

******Benazir Ababa kaante take amfani dashi a yanzu da rayuwarta ta samu sauyi Kwata kwata,

Kamanninta sun sauya sosai sbd lafiyan jiki Dana fatan dayake bayyane a tattare da ita,

Ta ciko koina Amma har lokacin batai qiba ba,

Jikinta na cikakkiyar mace a yanzu bayyane yake sbd hutu Daya ratsata ba laifi kam sosai.

Tsakaninta dasu Umme kauna da kulawa ce sosai shi kuwa dd babba baa ma fadan kaunarta Dayake a bayyane kusan bayan DD a cikin ransa yanzu ita din ce gata da Wani irin ilimi dayakesan ace ‘yayan family dinsa suna dashi shiyasa yafi son Dawood tin asali sbd iliminsa da babu me shi ko a cikin iyayensa sai gashi matarsa ma ta kasance cikin masu irin baiwarsa.

Amnah da ayanzu tayi wayo tasan Daddynta kaman me sbd shine Wanda yafi Santa fiye da kowa a rayuwarsa yanzu.,

Duk Abinda takeyi idan taji muryansa  zata taka ahankali da tafiyarta da batai qwari ba taje gurinsa.

Duk Wani Abu na Amnah a yanzu shine ya siyesa,.komai nata daga fari sai black kaman yanda su kadai ne kalan Dayake sakawa hakama ‘yarsa su kadai ne kusan kalan dayake Siya mata,Dayake fara ce tas kaman shine ya haifeta sai kalolin na mata kyau.

Duk wannan tsawon lokacin Basa haduwa,.daga shi har ita babu me buqatan ganin Dan uwansa Dan haka suke kaucewa haduwa da juna

Shi a nasa bangaren ma kaman har lokacin baiyi noticing nata ba.

Duk da tsawon lokacin da Basu taba haduwa suka tsaya gaban juna ha Abu dayan Daya hadasu shine kowannensu ya San qamshin Dan uwansa ko acikin qamshi nawa zasu shiga suna Gane na juna sbd Amnah.

Duk daukan dayakewa Amnah idan ta dawo hannunta qamshinsa a kame yake jikin Amnah da kayanta na turaren Caron poivre Mai Wani irin qamshi me sanyi da nutsuwa kuma duk qamshin Datake ji a mutane Bata taba Jin me irin qamshin wannan tiraren ba ko a familyn kaantes din kuwa Datake cude a cikinsu yanzu.

A nasa bangaren duk yanda baya bawa Abinda Bai shafesa mahimmanci ba Saida qamshinta dake jikin Amnah koyaushe samun shigewa Kansa Dan kuwa A jikin Amnah ne kawai yake samun wannan qamshin nata na aqua di parma da dd babba ne ya tsaya mata take amfanin da abubuwan da tsadansu bama gaskia bane a rayuwarta.

Wannan shine Wani communication da yake tsakaninsu kawai bayanshi babu Abinda yake hadasu da juna.

A bangaren Safnah kuwa tinda ta samu labarin yanada wata matar bayan ita ta daga hankalinta

Ita da mummynta suka dagawa hajiya da Daddynta harma da Umme hankalin akan Safnah ta fasa bataso Saidai ita a saketa kokuma a saki waccar dayar matar.

Umme da Alh basheer hankalinsu tashi yayi Amma suka ringa lallabata kada ma Dawood din yaji a take zai saketan ba Batawa Kai lokaci.

Da suka ga abin yaqi sauki sai dad dinta ya hanata dawowa yace tayi zamanta sai ansamu mafita.

Itama Umme amincewa tayi da Safnah din tayi zamanta tukuna su shawo kan Dawood din,

Ta Wani bangaren Kuma ita ummen tafison Safnah tayi zamanta acan kafin Dawood yafara noticing Benazir da ayanzu tafi Jin ta a zuciyarta matsayin matan Dawood akan Safnah duk da itama tana kaunar nata sosai.

Dd babba kuwa shiru yayi musu akan zancen safnah din da akace shakara Daya ya rage mata a karatu ta gama ta dawo ta tare Amma tsaban Rena hankalin mutane har shekaran ta wuce ba dawowan Safnah wadda itama ko sunan dawowanta Nigeria din bataso tafison DD din ya ringa zuwar mata can yafi mata.

Benazir ce matar Dawood a zuciyarsa Dan haka kaman yanda iyayen Safnah sukai biris da zancen dawowanta Shima yayi musu biris

Abinda ya sani Dawood tinda ya auresu su Biyun to saiya zauna dasu.

******Benazir na gama final exams dinta taje ta dubo Annenta wadda a yanzu tana zuwa dubota Akai Akai Kuma ba laifi Annen na cikin Aminci sbd kudin da dd babba ke bawa Ababa yaha hanasa Kiran Benazir akan saita gama karatu.

Hutun sati uku tayi sukai tafiya ita da Umme da Zeenah zuwa India dad kaante yaga likita harma da Ummen daga can suka wuce Costa Rica.

Watansu biyu suka dawo Benazir Bata rufa watanni biyar ba dd babba ya turata Cairo Wani business course na shekara Daya da wata biyar Kuma ita kadai ta tafi ba da Amnah ba dan haka take cikin kewan ‘yarta sosai.

******Dd babba da Kansa yaje bikin kammala business course dinta har Cairo tareda Umme hakama Zeenah data gama nata karatun a Zurich gurin DD Daya jima da komawa Shima tare suka dawo Nigeria

Motocin dasuka je daukosu suna harda Abbakar Wanda yayi farin cikin dawowarta sosai sbd kaunar Dayake mata Shima kaman shine ya haifeta.

Amnah na ganin mummynta tazo da gudu cikin farin ciki ta maqale ta tana  cewa

“Mummy” cikin muryanta na Yara.

Rungumeta benazir tayi tana sake kyakyawan murmushin Daya qayatar da kyakyawan fuskarta ahankali cikin tsananin kaunarta tace

“Oh my, I missd my baby so much”

Dariya Amnan tayi tana sake maqale mummyn tata tana cewa

“Where’s my daddy?”

Murmushi Benazir ta sake tana shafa fuskarta tace

“Baki ga Aunt Zeenah ba tana kallanki tayi missing naki sosai itama.”

Gurin Zeenah din tayi da gudu ta fada jikinta tana mata oyoyo itama.

Umme dake dariyarsu tini tayi hanyar bedroom dinta a Dan gajiye tana cewa

“Daddynta kawai take tambaya yarinyar Nan”

Dakunansu da aka gama gyarawa suna sanyin qamshin suka nufa kowa yayi nasa

Amnah na biye da Mummynta cikin tsananin farin cikin ganinta.

Ta sauya skin products nata zuwa Aesop Dan haka su ta fitar cikin kayanta ta Jere toilet kafin ta tube tayo wanka ta fito daure da blue towel   Brown skin dinta na daukan idon sheqin hutu da lafiya.

Mai Tai shafa sama sama ta fesa spray na turarenta ta saka pyjamas farare tayi sallan magrib da Akai a daki tasaka Nafisat ta kawo mata abinci taba fito ba tanayin ishai ta kwanta bacci.

Washe gari dukkaninsu kowa a daki yayi breakfast suna gamawa ita Kuma ta fita taje gurin dd babba daga can da kanta taja mota zuwa gidansu.

Ba laifi Bata samu Annenta cikin wahala ba Dan haka ta samu nutsuwa a can suka wuni ita da Amnah sai yamma suka dawo.

Tana parking suka fito kafin ta rufe motar Amnah ta saki hannunta da gudu ta nufi bayanta tana Kiran

“Daddy”

Ya Riga ya kawo bayan kaman yanda Shima ya Riga iso hanyar Dan haka tana juyowa akan fuskarsa idanuwanta suka sauka ta dauke Ido ahankali sbd kullum fatarsa qara daukan Ido takeyi.

Juyawa tayi zata bar gurin sbd Amnah tace

“Mummy ga daddynah ya dawo”

Cak ta tsaya tareda damqe handbag din dake hannunta ta juyo ahankali cikin nutsuwa da muryarta me taushi tace

“Sannu da dawowa.”

Bai taba dagowa ya kalleta ba sai ranar sbd ranar ne yafara Jin qamshin aqua di parma a daga jikin nata direct ba daga jikin Amnah ba.

Kallan da yayi mata ya sakata Dan daga qafa zata bar gurin Amnah ta sake kiranta tana cewa tadawo kar tabarsu itada Daddynta a baya.

Chapter 51

51

Cak ta dakata ta tsaya tana kasa juyowa sbd kaman tana Jin idanuwansa akanta Wanda suka hanata motsawa hakama ta kasa juyowa saidai bugun zuciyarta Daya Dan qaru.

Qamshinsa taji ahankali kaman Yana qaruwa a iskan dake shiga hancinta ta tabbatarda tahowa ne sukeyi Dan haka tana Jin takunsa gap da ita sai ta daga qafafunta taci gaba da tafiyarta cikin nutsuwa.

Amnah datakesan jinta tsakiyan iyayen nata hannu ta miqa zata kamo Benazir din tana Kiran sunanta

hannunta Bai Isa gurin Mummyn tata da batasan da ita ba tayi gaba cikin tsautsayi Amnah din ta subuce daga hannunsa tayi qasa

dagashi har Bena dataji ajikinta ta juyo da sauri a tare hannuwansu suka tarota tafin hannunta na sauka kan bayan tattausan hannunsa.

Amnah kuwa qanqame daddynta tareda riqe hannun Bena Daya tana kokarin fasa Kuka a tare suka ambaci sunanta cikin muryoyinsu masu nutsuwa da taushi.

Hannunsa da nata yake Kai ta kama ahankali zatai magana ya dago fararen idanuwansa ya zuba mata Wani Kallon Daya sakata Neman rikicewa tana sake kama hannun batareda tasan hannunsa take kamawa tinaninta na Amnah ne da rudewa tasakata kasa tantance girman hannun sbd taushinsa kaman na baby Amnah din.

Wani kallan ya sake zuba mata lokacinda ta sake damqe hannun da tafin hannunta da itama yakeda laushi,

Wanna Karan hannuwan nasu ya kalla Yana kame fuskarsa da ita firgitata kyawunta da tsananin kwarjininsa keyi..

Sai alokacin ta ankara da sauri Janye hannunta hannuwanta na Dan rawa da sanyin murya mara karfi ta furta  “Sorry” ta juya da sauri tayi gaba a Dan rude ko gabanta Bata Gani Allah yasa flat Hermes shoes ne qafarta shi ya hanata faduwa.

Tana shiga Palo Bata tsaya ba gaida Umme tayi ta wuce dakinta ta shige.

Tana shigewa ya shigo da Amnah fuskarsa freshe as always kananun guntayen kaya ne jikinsa idan dai fitan Shan iska ce zaiyi.

Kallansa Umme tayi cikin farin cikin ganinsa ta miqa masa hannu tana masa sannu da dawowa.

Kama hannunta yayi da hannunsa Daya yana sake mata qayataccen murmushin farin cikin ganinta Shima.

Amnah dake jikinsa ta shafa fuskarsa tana Jan dogon hancinsa tace

“Daddy muje na nuna maka kayan da mummy ta siyo mun data dawo kaji.”

Tashi daddy muje ka Gani please….

Saukowa tayi jikinsa ta tsaya ta kama hannunsa Daya da ‘yan qananun hannuwanta biyu tana jansa.

Kallansa Umme tayi tana dariya tace

“Kaje ka Gani tukuna mayi magana hankali kwance sbd Amnah idan bakaga kayan Nan nata ba bazata bari kowa yayi magana da daddynta ba.

Miqewa tsaye yayi ahankali Yana daukanta batareda tinanin har lokacin dakinta Daya da mummynta ba tinda yasan ko uban siyayya Dayake Aiko mata dashi dakin ta ma bazai daukaba sai ana rage wasu bare ace daki Daya take da mummynta da itama tanada kayanta Dan haka ya dosa dakin Datake nuna masan suje.

Bude dakin yayi Kai tsaye suka shigo ya tura kofar ya rufe Yana juyowa ya tsaya cak Yana kallan dakin dake cike da qamshin Mummynta Daya gama kama dakin da sanyin Acn Daya dada sanyayasa.

White clovia bra dinta dake yashe kan lafiyayyan gadon dakin idanuwansa suka sauka ya dauke idanuwansa daga gefen Yana juyawa zai fice Amnah ta taresa da cewa

“Ga mummy Nan ma ta fito ta dauko ma ka Gani Daddy.”

Benazir data fito Kai tsaye daga toilet daga ita sai short sleeveless gown me kwantawa ajiki wanka ta shiga Yi Amma ta kasa sbd Jin ana Kiran sallah sai tayi sallah tukuna Dan haka alwala tayo ta fito Daman ta cire doguwan rigarta da bra Daya dameta.

Maganar Amnah ta ankarar da ita suna dakin da sauri ta dago tana dubo gurin kofar daidai Yana dauke Kansa daga kallan fuskansa a fuske yaso juyawa Amnah ta hanasa shikuma Daman bazai batawa Amnah din ba Dan haka kaman baima San da wanzuwarta ba a dakin suka nufi kujera ya zaunar da Amnah din kafin yayi magana Benazir tini Takoma cikin toilet din tana Jin Amnah nata kiranta tayi kaman bataji ba.

Jansa Amnah takuma Yi har kan gadonsu ta ringa dauko masa duk Abinda takeson ya Gani Yana sauraranta kawai batareda ya iya magana me tsayi ba Daman sauraran surutun kawai Yana Basa nutsuwa da farin ciki.

Da kanta ta gaji Amnah din suka fito ba Dan Hakan ba shi zai iya zama taita masa surutun har kowane lokacin zasu Kai ba damuwansa bane.

Suna fita Benazir ta fito Dan tini tayi wankan data fasa.

Sallah tayi Shima lokacin an tada sallah tini ya fice zuwa masallaci.

Tana idar da sallah ta dauki wayarta tana duba sakonnin emails na yan ayyukan da dd babba yasa aka fara Bata Dan gwada zurfin hankalin ilimin data yo akan harkan business gashi akwai acct sosai cikin kanta kaman me.

Aje wayan tayi ta miqe tareda zare abayan sallarta ta fito jikinta sanye da Celine English  straight gown da Hula mara nauyi akanta riqe da hannun Amnah Da itama tai mata wanka ta shiryata cikin black pyjamas na Yara masu tsantsi tana hammar bacci gashi Bataci abincin dare ba.

Gurin su Umme dake Palo zaune ta barta ta nufi kitchen da kanta Dan hado mata tea Dan yawanci idan taci abinci me nauyi da dare baya Bata lafiya sosai shiyasa da daddare an sabar mata baa Bata Abu me nauyi se light.

Chocolate custard ta damo mata da kanta ta zuba madaran sosai aciki Bata saka sugar ba ta fito riqe da cup din tana Dan juyawa a hankali ta dawo.

Zaunawa tayi gefen Zeenah tana sake juyawa sbd ya huce.

Sallamarsa ta sanyata kasa dagowa taci gaba da hurawa se gashi baima zauna ba yayiwa ummensa goodnight ya fice.

Tana gama bawa Amnah custard din ta kira Nafisat ta dauketa ta tafi sake gyarata Ta Kwantar da ita sukuma suka nufi dining cin abinci.

Tana gamawa taje ta Sako babbar jallabiya akan rigarta ta nufi gurin dd babba kaman yanda ta Saba duk dare kafin shigewa saita je ta gansa.

Bata Wani jima ba kaman yanda ta Dan Saba jimawa har dai idan takai masa abincinsa da kanta ne sbd mafi yawan lokutan idan tana gida itace ke masa girkinsa na musamman me qara lafiya da inganci.

Tana dawowa babu Bata time ta kwanta take bacci ya dauketa itama.

Washe gari zata fara zuwa office ganin Wani aikin da dd babba yasakata duk da bawai bar mata aikin yayi ba gabaki Daya ya sakata joining fahat kaante ne babban yayan Siyam din Mum Khadija.

Dayake da ‘yar gaban goshin dd babba akafi saninta Dan haka ta samu tarba da respect sosai daga wainda suka samun ganinta Dan company din nada girman da kowa Yana can gurin sabgar gabansa ba kowa zai ganka ba harka tafi ka Gamo ka fito.

Fahat kaante yaji Dadin ideas dinta da wasu suggestions data Bada tareda Yaba nata ilimin Dan haka sosai yaji Dadin Aiki da ita a wunin sai yamma suka fito tare ta wuce kaantes Shima Yana biye da ita suna isowa shi ta gate din baya Wanda acan nasu bangaren yake ita Kuma ta shigo ta gate din gaba a Dan gajiye.

Tin a gurin parking taga Rolls-Royce black haraban gidan ta fahimci Daddyn Amnah na gidan Dan haka ta shigo a Dan natse cikin sa’a baya part dinsu Dan haka Kai tsaye ta wuce bedroom dinta.

Ko da tashiga tana waya Dan haka tana shiga Bata Kalli inda gadanta yake ba ta nufi closet tana ajiye handbag nata da key na mota tafara zuge zip din gaban doguwar jallabiyanta.

Rufe kofar dakin taji a juyo tana kallan kofar tana kashe wayarta cikin mamaki,

Bata ga kowa ba Kuma tabbas rufe kofar taji anyi,

Dawo da kallanta kan gadonta tayi ga mamakinta sai taga Amnah kwance tana bacci.

To waye ya bude dakin?

Shigowa Akai ko fita?

Numfashi ta sauke ta koma ta qarasa tubewa ta shige toilet kawai.

Bayan tayi wanka gajiyanta ya sake tayi sallah ta tashi ta nufi Amnah zata tada ita sbd baccin magrib zaisa ta kasa baccin dare.

Tana taba ta taji jikinta da zafi sosai

 da sauri ta Kalli fuskatarta tana sake taba wuyanta zuwa goban kanta taji zafi sosai.

Mummunan faduwa gabanta yayi ta janyota jikinta tana Kiran sunanta ahankali cikin tsananin damuwa da kulawa tace

“Meya samu my baby.”

Motsawa Amnah din tayi ahankali tareda Dan Bude idanuwanta tana ganin mummynta ta sake shigewa jikinta tana lafewa ahankali tareda Dan Kiran sunan Mummyn.

Rungumeta Bena tayi tana cewa

“Baby zazzabi kikeyi?

“Meyake Miki ciwo?

“Kinsha ruwan sanyi sosai kokuma qasan ruwa right?

Numfashi ta sauke tareda saukowa gadon ta mayar da Amnah din ta Kwantar ta fito Kai tsaye kitchen ta nufa inda maganinsu suke cikin Wani Dan qaramin fridge Daya da aka ware a kitchen kawai sbd saka maganin Amnah.

Paracetamol ta dauko ta Kalli Nafisat dake kokarin jera kayan da aka wanke tace ta hadowa Amnah white indomie ta kawo mata.

Daki ta koma tana shiga ta zauna bakin gadon tareda janyo Amnah jikinta ta rungume duk ranta na dagulewa sbd Amnah itace kuzari da farin cikinta bayan Annenta,.

Hankalinta ba qaramin tashi yake ba idan Amnah tafara zazzabi sbd komai qanqantar ciwo jigatar da ita yakeyi sosai taita wahala Dan haka hankalinta ke Neman tashi.

Maganin ta bata cikin kulawa da lallabawa kafin ta goge mata fuskarta da tissue tana ajiyewa sai ga Nafisat ta kawo mata Abinda tace din.

Zaunar da ita tayi jikinta cikin lallabawa da kulawa ta fara Bata indomie din Nafisat kuwa ta tattara kayan maganin da tissue zata fita dasu.

Kawar da Kai Amnah din keyi tana girgizawa tace

“No mummy banaso na koshi.”

No please sweety kici kadan ok???

Sake girgiza Kai tayi tana lafewa jikinta tace “No I don’t want”

Kallan Nafisat tayi ta miqa mata plate din jiki ba qwari tace

“Ki hado mata tea mara zafi sosai”

Karba Nafisat tayi tana cewa to ta fice da sauri.

Bayan fitan Nafisat shafa kanta Bena tayi cikin kulawa kaman zata hadiyeta tace

“Sweetyn mummy me kikeson kici to?

Zaki Sha warm yoghurt?

Girgiza Kai Amnah tayi a hankali

Bena tace “but baby you have to take or eat something before going to bed ga Kuma magani kinsha”

Kuka Amnah ta fashe dashi ahankali tana cewa

“No mummy ni banason abinci,bana Jin yunwa.”

Numfashi me dumi Bena ta sauke tana rarrashinta zuciyarta ba dadi.

Nafisat ce ta kawo tea din ta karba ta saka Amnah Shan nasa dole cikin tausasawa Yana gama shiga tafara Amai sukai toilet.

Aman datayi ya saka Dan kuzarinta tafiya tareda tsananta zazzabin ta fara Kuka daqyar Bena tai mata wanka da ruwa me zafi ta dawo da ita ta shirya ta Kwantar tini Nafisat Daman ta sake gyara dakin ta sauya zanin gado sabo duk da aman be taba ba Amma sbd tsafta da kiyayewa.

Rage sanyin Acn tayi sosai kafin ta fice daga dakin.

Itama Bena din Saida ta sake wanka tea kawai Nafisat ta kawo mata Tasha ta kwanta Batama iya fitowa ba.

Chapter 52

52

Kasa bacci tayi sbd zafin jikin Amnah datakejin Yana shigarta ahankali Yana  dumama nata jikin,

Umme ce tashigo jinta shiru ta tadda cikin wannan halin itama cikin damuwa tace ko Akira likita cikin dare.

Cikin nutsuwa da sanyin jiki Bena tace

“Kodai a bari zuwa da safe Umme sbd dare yayi Kuma ta samu bacci may b kafin da safen ta warware inshallah.”

Ok Allah yasa Hakan Amma dazu fa Rana tana tareda daddynta har yamma har fita sukai suka dawo

Shima inaga Bai San zazzabin ya shigeta ba harya wuce.

Numfashi kawai Bena ta sauke sbd gwara da Bai sani din ba Dan dole dayansu zai kasance da Amnah din ita Kuma idan Amnah na ciwo Bata iya barinta sbd damuwa da susucewan datakeyi.

Bayan fitan Ummen Zeenah tashigo ta hawo gadon Tana shafa Amnah din daga Nan bacci ya daukesu su duka anan Zeenah ta kwana dasu.

Washe gari da safe jikin nata da Dan sauki ba laifi,.

Kaman bazata iya fita tabarta haka ta ringa tarairayarta har kusan 10 kafin ta shirya ta fice zuwa office bayan taje gurin dd babba suyi magana.

A office yau hankalinta ya Dan rabu biyu so Bata Wani jimaba taba gama aikinta ta juyo gida tareda fahat Daya baro motarsa office suka dawo tare.

Ta gate din gaba suka shigo sbd yace zai duba Amnah din da babu lafiya.

Tare suka fito motar Yana kallan yanda duk batada kuzari ya saki Dan murmushi me sanyi Yana mamakin soyayyar datakewa Amnah duk kawaicinta akan komai Banda Amnah.

Itace a gaba gurin shigowa palon kafin shi a kan Amnah dake jikin daddynta idanuwanta suka sauka Shima Kallo Daya yayi musu ya dauke Kai Yana cigaba da wayar Dayake Yi da likitan dazaizo ya duba Amnah jikinta ya sake rikicewa da yamman.

Tana ganin mummynta ta miqa mata hannu Daya tana fara hawaye da Kiran sunanta ahankali.

Qarasowa Bena tayi ta kama hannun Amnah din wadda ta janyota ta zauna ba shiri tana kokarin matsawa ba dama sbd riqetan da Amnah din tayi tana hawaye cikin zafin ciwo.

Jikinta dake gugan nasa sbd kusancin da yayi yawa yasa ta Dan kallan gefen Umme dake gaisawa da fahat

Shi kuwa har lokacin Bai motsaba barema ya nuna yasan da Wani ya zauna gefensa.

Ahankali daqyar ta iya Bude baki murya a sanye tace

“Amnah muje daki naji Yaya jikin naki,

Na sake baki magani.

Lafewa tayi jikin daddynta tana Dan girgiza Kai ahankali Bata iya magana.

Fahat Daya gama gaisawa da Umme dawo da kallansa kan DD yayi ya masa magana suka Dan gaisa sama sama sbd Dawood din da hankalinsa ke kan Amnah.

Miqewa yayi ya tafi bayan duba Amnah itama Bena data kasa nutsuwa da zaman nasu ahakan ta zame hannunta daga na Amnah ta miqe ta bar palon.

Daki ta Isa tana sauke ajiyan zuciya a boye kafin ta wuce tayo alwalan sallar laasar data wuceta ta fito tayi.

Tana idarwa ta fito sbd takasa samun nutsuwan jikin Amnah.

Ko da ta fito likita yazo yana duba Amnah din.

Gefen Umme ta silalo ta zauna a hankali tana sauraran Abinda likita ke fadawa DD.

“Sanyi ne kawai yake son Dan shigarta sai a kiyaye barinta wasa da ruwa gaskia”

Juyawa yayi ya Kalli Bena dake bayan Umme likitan yace

“Madam ai last time na fada Miki Hakan please a sake lura sosai a kiyaye.”

Ajiyan zuciya ta sauke tana gyada masa Kai ahankali.

Magani yace zai Aikowa Amnah din yayi musu sallama ya wuce.

Bayan fitansa bacci ne ya dauke Amnah din har lokacin tana jikinsa.

Shima zazzabin yakejin Yana Neman kamasa sbd zafin jikinta da tin dazu yake shiga jikinsa Kuma shi fatansa batada Wani karfi da wuri wasu abubun ke saurin shigesa.

Abincin dole Bena ta miqe taje dining taci tana gamawa tayi dakin Zeenah Datake ta fama da nata aikin kwana biyu sbd itama zatai joining kamfanin Amma Kuma tana buqatan attending wasu online classes na sati uku ga service dasuke Shirin zuwa wannan Karan inshallah itada Bena din.

A dakin suka zauna itace ta ringa fahimtar da Zeenah din wasu abubuwan na course nata datai attending Wanda ya banbanta dana online da Zeenah keyi Kuma gashi Wanda Bena tayi dama ce da sai Dace ake samunta yanzu bazaa sake course din ha sai after like 3 years.

Har kusan 9:40 tana dakin kafin ta fito Takoma dakinta tana mamakin Ina Amnah ko tana dakin Umme.

Bedroom dinta ta Bude ta shiga Kai tsaye..

Ac din Dayake kashe ya saka mahaukacin qamshinsa yiwa dakin Wani irin gaurayar data sakata kallan gado Kai tsaye.

Zaune yake bakin gadon har lokacin Amnah na maqale dashi taqi yarda ya tafi yabarta.

Idanuwansa Wani laushi sukai da suka sakata rikicewa tana rudewa da kallansu tafara kokarin juyawa a hankali cikin Wani lazy sauti yace

“Kinsan meye time kuwa?”like kinsan ana duba time kuwa??

Dakatawa tayi tareda kasa fita tana daidaita numfashinta dake Dan fita da qarfi ta juyo ahankali batareda ta kallesa ba ta Kalli Amnah wadda da alama tana Jin zazzabin sosai har lokacin sai taji jikinta ya mutu ahankali ta Dan dago tanasan kallansa Amma ta kasa iya sake kallan idanuwansa ta Bude baki ahankali ta furta “sorry na bari kayi having time naka da ita ne”

Bai iya cewa komai ba sai kallan da yayi mata na minti Daya kafin ya Dan sauke numfashi Mai dumi da zazzabin dake cinsa Shima yakai hannu zai Zame Amnah ta sake qanqamesa cikin bacci da radadin ciwo tareda ambatan sunansa cikin bacci da qaraman muryanta me taushi.

Shiru sukai dukkaninsu suna kallanta  shi Kuma zuwa lokacin zazzabin yakeji sosai Yana buqatan zuwa gida sosai.

Lumshe idanuwansa dasuka sake saka Bena Neman rudewa ga ciwon Amnah da riqesan da Amnah tayi ga idanuwansa da duk ya motsa su saita ji tana Neman rudewa.

Ahankali ya dago ya Kalli Bena din jinta shiru takasa qarasowa ta karbi Amnah din daga jikinsa.

Ganin kallan da yayi mata ya sakata takowa ahankali ta iso gurin hannuwanta na Dan rawa ta ranqwafo takai hannuwanta cikin sanyi ta Dora akan na Amnah dake qanqame da jikinsa.

Dumin numfashinsa Mai zafi ne ya sauka wuyanta zuwa cikin rigarta ahankali take rawar hannunta ya qaru ahankali ta Dan rintse idanuwanta tana Kai hannunta Daya zata Ciro Amnah numfashin nasa Mai dumi ya sake saukar mata a fatan wuya ta Bude idanuwanta dake rintse ta kallesa daidai Shima ita din ya kalla ganin hannuwanta na rawa ahankali.

Kallansa tamkar wata fitina ce ga duk Wanda yayiwa irin wannan kallan na cikin tsakiyan Ido Dan haka haduwan idanuwansu ya sakata miqewa ahankali daga raqwafan da tai tana cika masa hanci da qamshinta Daya sake tsananta zazzabinsa.

Hannunsa Daya taji akan nata daidai lokacinda taso matsawa baya zata bar gurin sbd saukan dumin numfashinsa fatan jikinta zazzabin itama zai saukan mata.

Tinda take rayuwanta yau ne ranar farko da namiji yayi mata irin wannan rikon Dan haka Saida bugun zuciyarta ya tsaya cak ta rufe idanuwanta ahankali kafin tayi Wani motsi ya Dora hannunta kan Amnah ya Zame a hankali ya miqe ya fice daga dakin yabar dakin da fitinanniyar qamshinsa.

Kasa motsawa tayi tsawon seconds tukuna ta iya motsawa ta silale ta zauna bakin gadon inda ya tashi har lokacin tana sake Jin saukan dumin numfashinsa akan fatarta.

Gyarawa Amnah kwanciya tayi kafin ta miqe ta shiga toilet Bata Wani jima ba ta fito ta saka pyjamas masu tsantsi ta hau gadon ta kwanta tareda hade kanta dana Amnah pillow Daya tana Jin qamshinsa na shiga hancinta a duk numfashin da zata ja.

Qarfe 3 na dare jikin Amnah din ya sake tsananta zafi ko Kuka da rigima Bata iyawa Wanda ya saka hankalin Bena mummunan tashi ta fara hawaye tana shafa Amnah din.

Magani ta sauko ta sake Bata ko gamawa batai ba Amnah ta amayo sa jikinta na sakewa Dan haka hankali tashe ta janyo wayarta ta kira Nafisat daga bangaren masu aiki saiga Nafisat din tana wartsakewa daga bacci.

Motsin shigowan Nafisat sashen ya saka zeenah fitowa itama sbd Bata jima da kwantawa ba itama karatu ta kwana Yi.

Ganin halinda Amnah ke ciki ya saka Zeenah dauko wayarta ta kira DD sbd Umme na sashen dad.

Bena kuwa toilet ta shiga tayo Wani wanka sbd Amai dake jikinta ta fito daure da towel purple,lokacin Nafisat ta sake sauya zanin gado ta gyara dakin duk da tsakiyan dare ne Amma dole tayi aikinta.

Amnah ma tini aka goge mata jikinta aka saka mata wasu kayan baccin jikinta na Dan fisga sbd zafin zazzabi da qarfinsa.

Zeenah data sake Kiran DD Dan tanada tabbacin Kila Yana kaantes zai kwana sbd jikin Amnah bazai barshi ya tafi ba.

Koda kiran Zeenah keta shigowa wayansa Yana bacci ne sbd zazzabin Daya kamasa Shima Dan haka Bai ganiba sai asubata Daya farka Yayi sallah yaga misscalls nata.

Time datai kiran yafara kalla a natse yaga 3:36am.

Kai tsaye yasan jikin Amnah ne kawai dole zaisa tayi masa kira wannan time din Dan haka ya fito da Kansa yaja mota zuwa kaantes.

Koda ya Isa securities sunyi mamakin ganinsa lokacin suka Bude masa gate ya shige Kai tsaye sashen Umme ya nufa Koda ya Isa Zeenah ce ta Bude masa kofa sbd akwai sauran duhun Asuba Kuma lokacin masu aiki Basu isa shigowa ba.

Tana Bude masa tayi dakinta sbd baccin dake cike da idanuwanta daqyar sukai sallar Asuba kowannensu bacci yakeji musamman Bena data kasa rintsawa tin farkon dare har qarshensa.

Kai tsaye bedroom dinta ya nufa ya Bude ya shigo babu haske a dakin sosai sbd rage wutan datai sosai.

Kwance take daga ita sai silk kayan baccinta datafi sakawa sun maqale jikinta musamman da AC yake kashe Basuyi rufa ba Amnah na kan jikinta bacci sike cikin galabaituwa daga rashin baccin da Basu samuba da dare.

Qarasowa yayi Bai damu da tsayawa kare mata Kallo ba Amnah kawai yakai hannunsa ya taba fuskanta yaji zafin jikinta ya sauka Dan haka ya juya juya zuwa window ya Ciro wayarsa ya kira likita ya sake masa bayanin ko zai sake dawowa duba Amnah din.

Yana kashe wayarsa Amnah ta Bude idanuwanta Jin muryansa ahankali ta Bude baki ta kira sunansa cikin sanyi.

Juyowa yayi Yana kallanta cikeda kauna da kewanta ya Tako zuwa inda take Yana dauke idanuwansa daga kallan Bena Datake bacci cikin wata irin nutsuwa kaman baby itama ga idanuwanta datasha kukan ciwon Amnah din sun Dan kumbura kadan.

Tashi zaune Amnah tayi tareda miqa masa hannuwanta tana cewa ya dauko da ita gadon.

Cirota yayi ya fito dakin Kai tsaye sbd baida nutsuwan jira cikin dakin Daman.

Suna fitowa Palo Nafisat ta koma da ita tayo mata brush da yan wasu abubuwan ta sake canja mata kaya kafin ta dawo gurin daddynta lokacin Umme ta shigo ganinsa ya sakata mamaki.

Gaisawa kawai yayi da Umme ya fice da Amnah suka tafiyarsu gidansa.

Bena Bata farka ba sai 10 lokacin itama kaman zatai zazzabin takeji Amma Dayake tasamu baccin kirki ta Dan sake.

Umme ce ta fada mata yazo ya fita da Amnah dan haka breakfast sukai itada Zeenah suka tafi gurin dd babba ta jima tana magana dashi kafin suka fita sbd dole a satin zasu wuce Camp.

Amnah Bata dawo ba sai yamma sosai itada daddynta ya ajeta ya wuce sbd Shima yanada tafiya a satin zuwa Lagos Wanda suma acan zasuyi service Amma baimasani ba Saida dd babba ya sanar dashi a gidansa zasu zauna dake can Dan haka ya shirya zama dasu kafin ya gama nasa aikin ya dawo ya barosu.

burin dd babba a yanzu na ganin ya saka Bena cikin business dinsu ne sosai sbd ta tsaya cak anata future din Dayake san ta samu Dan yanta kanta da mahaifiyarta har abada daga mahaifinta Dan haka yafara sakata cikin ayyukan office kafin service nata da sai yanzu zasuyi itada Zeenah wadda itama takesan shiga family business dinta.

Chapter 53

53

Amnah ta samu sauki sosai ta warware Dan haka yanzu Bena ta samu nutsuwa da kwanciyar hankalin aikin office Datake Dan leqawa hakama tana samun time sosai yanzu na zaunawa da dd babbanta suna maganganu na businesses sbd kusan matsayin da Bilal ya rasu ya bari ne yake son Maidata Akai sbd Shima Bilal din yanada Saar iya gudanar da kowane irin business ya qulla sai an samu Abinda akeso 100 percent.

Umme Sam batason suje Lagos service nasu Amma Kuma kaman raayi da buqatan dd babba ne suje can din Dan haka dole ta hakura gashi anan zaa bar mata Amnah sai Mummynta ta gama ta dawo Kuma.

Lokacinda tafiyansu ya qarato Amnah harda ciwon kewan mummynta da zatayi ta kwanta daqyar Bena ta iya danne zuciyarta ta tafi tabarta Allah ma ya saka daddynta Yana Nan shi Dan haka kewan da zai ringa debe mata daban ne musamman wasu lokutan gurinsa take kwana sun Saba.

****Sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da hutawa suka fara a Lagos sbd Sam ba Wani wahala ko gwagwarmayar dasuke fama da ita sbd tini suka gama komai suka fara bautan qasansu a natse.

Wani 2 bedroom duplex ne dake Ikeja suke ciki na DD Wanda babu Abinda gidan ya rasa na Jin dadi da tsadan rayuwa,

Komai na gidan bisa ga tsari da yanda yake buqata yake hakama komai na a tsare yake kaman gidansa na Zurich da can gida.

Bedroom Daya suke amfani dashi sbd dayan bedroom din nasa ne basuma San Ina key dinsa yake ba bare Yaya yake.

Zeenah datai missing rayuwarta na turai suna zuwa Lagos din ta koma baturiyarta suka goge abinsu suna zuba life daidai yanda tayi musu.

Dayake service din nasu na yayan manya ne akwai ranakun da bama sa zuwa Dan a sati baifi suje so biyu ba gabaki Daya Zeenah ta zarar da Bena wadda itama Daman rayuwarta ta zurfafa sosai a rayuwan hutu da wayewa kawai tanada kawaici ne dakuma kalan rashin sakewanta da mutane sosai Daya zama kaman Wani Jan ajinta ne,

Amma a rayuwar da suka samu Kansu ta garin taji Dadin garin sosai fiye da wasu qasashen turawan Dataje Dan haka ta sake tana rayuwanta hankali kwance.

Kullum tana waya da video call da Amnah matiqar tana gida saidai ranakun Datake gurin daddynta to wannan shine Bata samun ganinta a waya sai ranar data dawo.

Ahakan suka dauki lokaci Dan har suna maganan wata biyu a garin Basu koma gida sbd dd babba yace su zauna su kammala gabaki Daya tukuna tinda a gida suke.

***Yau Zeenah ce kawai ta fita ita kadaice a gida

Itama Bata fita bane sbd yau Bata buqatan fita koina hutawa takesan Yi sbd jiya har dare sosai Basu dawo gida ba.

Baccin Rana tayi sai yamma ta tashi tayi wanka ta fito ta nufi kitchen,

Ruwa tafara Bude fridge ta dauko roba ta Bude Tasha kafin ta nufi kitchen island ta janyo kayan tea dake Kai ta hada warm tea Tasha sbd batasan Abu me zafi sosai ita.

Tana gamawa ta fito tana duba sakonnin wayarta har Dana Zeenah dake sanar da ita zata jima Bata dawoba.

Palo ta zauna tareda janyo laptop ta Bude zata fara Wani Aiki taji ana taba kofan shigowa palonsu.

Juyawa tayi ta Kalli kofar Rabin hankalinta na kan laptop din sbd ta kunna.

Password din kofansu taji ana sakawa Dan haka ta dawo da kanta kan Abinda takeyi sbd tasan bayan ita da Zeenah babu Wanda yasan password nasu so definitely Zeenah ce.

Maida hankalinta kan Abinda takeyi tayi tana Dan Dan girgiza qafanta ahankali.

Harta fara Abinda takeyi taki shiru ba hayaniyan shigowan Zeenah din batareda ta juyoba da muryanta me shegen nutsuwa da Wani aji irin class irin na ‘yayan hutu da wayewa tace

“Zee, kikace you’re not coming back early¿ Ko Zak…….  Cak ta tsaya da maganarta tana kasa qarasawa tareda dakawata daga Abinda takeyi bugun zuciyarta ya Dan tsananta sakamakon qamshin Daya shiga hancinta da sauri ta juyo daidai qarasowansa cikin palon sallamansa a makoshi.

Kallansa takeyi batareda tasan tana Hakan ba sbd mamaki da rudewa.

Kallanta dayaji akansa ya sakasa dakatawa ya zuba mata nasa idanuwan dasuka sanyata sake shiga Wani yanayi na bugawan zuciya da sauri.

Kaman daga sama taji muryarsa me wuyan ji

“Kin San ana amsa sallama right?”

Dauke kallanta tayi daga Kansa tareda Bude baki ta amsa sallamansa tana Dan tahowa gurinsa tace

“Barka da zuwa”

Tana tinkarosa ya Dan dauke Kansa daga gefen Yana wucewa zuwa hanyar bedroom dinsa sbd kayan dake jikinta da itama ta manta short free size Balenciaga sweet shirt ne kawai jikinta.

A Palo yabar luggage dinsa wadda Naseer ya ajiye masa bakin kofa ya juya batareda ya shigo ba.

Wucewa yayi yabarta palon tana Dan sauke numfashi kadan tanajin kanta na sarawa ma sbd bazata iya zaman palon bama Kuma.

Laptop dinta ta dauka zata tafi daki sai Kuma ta Tina cajan laptop din Yana palon Kuma Sam Bata taba ciresa bama tinda ta saka sa gurin Dan haka tayi zamanta gashi yariga ya shige tasan ba lallai ya fito yanzu ba Shima.

Zaunawa tayi taci gaba da Abinda takeyi hankalinta kwance cikin nutsuwa.

Wayarta ce tayi ringing a Dan kasalance sbd tafara gajiya ta duba taga Umme ce Kuma vidcall take taji zuciyarta tayi sanyi sbd sanin Amnah ce Dan haka ta dauka tana Sakin kyakyawan murmushin farin ciki tana cewa

“Oh my, ya Akai my baby tasan mummynta is Missing her like crazy da yamman nan?”

Dariyan farin ciki Amnah ta saki har tana kwantawa kan gadon Umme data Bata wayar ta fice duba baqin dake jiranta Palo.

Amnah na tsananin son iyayenta su ringa fada mata yanda suke tsananin sonta shiyasa dukkaninsu dasuka San halinta suke yawan fada mata ire iren Hakan sbd tana nuna Jin dadinta sosai.

Murmushi Bena ta sake saki tana sake cewa

“Baby na tayi missing mummy nata kuwa?

Naga kinyi Wani kumatu bayan mummy duk ta rame sbd kewanki,

Daddynki Yana baki more chocolates right??

Dariya Amnah ta sake Yi tana cewa

“Mummy Nima fa sosai nake missing naki and my daddy ma yayi tafiya yau yace he’s coming to you and…..

Fitowan Daddyn nata ne ya saka Zeenah Dan kallan gefe batareda ta juya ba shikuma luggage dinsa ya fito dauka harya tube daga shi sai black towel daya dauro qugunsa kaman yanda yake daura towelsa kaman zasu Fadi Amma yau din ya daure da kyau sbd sanin akwai Wani gidan bayansa,

Da ire iren wainnan sabon nasa yasaka baya iya hada muhalli da kowa sbd shi mutum ne me tsananin son yin komai nasa yanda yakeso ba takura ko wane kame kame.

Amnah ce idanuwanta suka hango mata shi da qarfi tana tsalle tace

“Daddy,daddy..”

Dakatawa yayi ya Kalli wayar hannun Bena yaga fuskar babynsa tana tsallen murnan ganin iyayenta tare tace

“Zo daddy kaima inata son ganinka Ina kewanka.”

Ta bayan Bena yazo ya tsaya ahankali tareda ranqwafowa Yana kallan Amnah ya saki Wani fitanannen murmushin Daya saka ruwan jikinsa na wanka da Bai goge ba sbd Yana buqatan sabbin towels dazai iya goge jikinsa da bedroom din sun jima aje bazai iya sakawa jikinsa ba.

Ahankali ruwan ya digo kan wuyan Bena ya gangara cikin rigarta

Numfashinta ya kusa tsayawa kafin ta iya janyosa ahankali kirjinta na Dan yin sama Wanda yasashi Dan motsawa sakamakon motsin ruwan ya sake digar mata a wuya wannan Karan rintse idanuwanta tayi ahankali

Amnah data Gani tace

“Daddy ka digawa mummy na ruwan wanka fa Kuma ya mata sanyi tace Kuma ruwa ajikin mutum idan ba wanka zaiyiba ko alwala Yana saka mutum yayi rashin lafiya ka goge mata banason mummyna tayi rashin lafiya.

Maganar Amnah ya saka Bena kallan wayar shikuma ahankali ya juyo idanuwanta kan wuyanta da daidai lokacin wasu suka sake digar mata suka gangarowa ahankali zasuyi cikin  rigarta ba tsammani Bena taji saukan tattausan tafin hannunsa kan wuyanta,Saura kadan Numfashinta yabar jikinta ba zato ta Dora hannunta Daya akan nasa ta tsayar hannunsa ta hanasa goge inda ruwan suka bi.

Yanda ta Dafe hannunsa da nata ya sakasa karkato da fuskansa kadan ya zuba mata idanuwansa da suka sake tsananta bugawan kirjinta dake sama yana qasa.

Duk kirjinta yayi sama saiya shafi hannunsa dake kusa da gurin

Ya sake zuba mata lazy eyes nasa zaiyi magana Amnah datake kan waya har lokacin ta kira sunansu da qarfi tana cewa

“Daddy kanata sake zubawa mummy ruwa fa nidai daddy ka goge mata Dan Allah.” Kuka take Neman Yi masa Dan haka a hankali yakai hannunsa Daya ya kife wayan ahankali tareda birkito Bena data kasa motsi yana kallan fatan wuyanta da santsinta ya saka ruwan Yana diga yake gangarawa ya sauko.

Kasa Bude idanuwa Bena tayi tana qanqame hannuwanta sbd kusancin dasuka samu yayi kusa sosai gashi jikinsa babu Riga qamshin shower gel dinsa Mai shegiyar qamshi da tsada sai shiga hancinta yakeyi direct.

Saukan hannunsa kan wuyanta a Karo na biyu ya sakasata sake riqe hannunsa a Karo na biyu itama saidai kafin tayi Wani motsi ya bi ruwan zai goge ba shiri ta qanqame hannunsa tareda Bude idanuwanta ahankali ta dago ta kallesa Shima ita ya zubawa idanuwansa.

Baki takeson budewa tayi magana Amma ta kasa sbd dumin da jikinta ke dauka na shigar zazzabi a take.

Shikuma ahankali ya janye hannunsa data riqe ya gangara da idanuwansa zuwa wuyanta a Karo na biyu ahankali ya Bude baki sbd cikin qaramin sauti me kashe jikin Wanda yake sauraro yace

“Bantaba kasa yiwa Angel Dina Abinda takeso ba.”

Juyawa yayi kaman ba shine yayi maganar ba yaja kayan Daya fito dauka ya koma bedroom dinsa ya shige yabarta tsaye numfashinta na kasa daidaituwa hakama mamaki fal cikin ranta,

Tasan ko me Amnah tace masa tana so Bai taba kasa Yi mata shi ba ko menene,to Amma Bata taba tinanin hadda irin Hakan ba zai iya Dan Amnah ta sakasa Kuma ko ajikinsa.

Silalewa tayi a hankali ta jingina jikin kujeran Datake Kai tana kokarin daidaita nutsuwanta kafin ta dauki wayar Daya kife ga mamakinta har lokacin Amnah na riqe da wayar tana jiransu,tana ganin mummynta ta washe baki tana cewa

“Mummy Ina daddy?”

Kasa amsata Bena tayi saidai da hannu ta nuna mata bayanta alaman Yana daki.

Daqyar ta tattara nutsuwanta suka qarasa firan da Amnah tayi mata sallama ta kashe wayarta tareda miqewa ta nufi bedroom ta sake samun nutsuwa kafin tayi alwala tazo ta tayarda sallar magrib da lokacinta yayi.

Koda ta idar Bata fito ba daki tayi zamanta sai datai ishai kafin ta fito ta nufi kitchen ta dafa tea me Dan zafi Tasha da biscuits bayan ta shafesa da Nutella.

A dining take zaune tana Sha ahankali sai gashi ya fito daga bedroom nasa sanye cikin black guntun three quarter da black free size shirt qafansa da slippers black Suma.

Dining din ya nufo Kai tsaye Yana Dan kallan Abinda take ci murya a hankali yace

“Whats this?

Dan dagowa tayi ahankali ta kallesa Amma Bata Kalli fuskarsa ba ta dawo da kallanta kan Abinda take ci cikin nutsuwa.

“I don’t eat wainnan abubuwan for dinner.”  Ya fada fuskarsa ba sakewa Kansa tsaye sbd Yana buqatan abinci and bayada patience na jiran order yanzu sbd inda yakecin abincinsu sunada Nisa da Nan inda yake kafin akawo zai iya kamuwa da ciwon ciki yunwa yakeji sosai.

Chapter 54

54

Kasa cewa komai tayi sai kawai ta miqe ahankali tareda dauke qaramin tray din dake daukeda abubuwan Datake ci din ta nufi kitchen.

Basu da wasu kayan abinci a gidan sbd Basa girki kullum order sukeyi kokuma yawon zuwa manyan 5star restaurants cin abinci se daidaikun ranakun da suke girkin a gida Shima baya wuce simple simple girki.

Junk foods kawai ne suke dasu a kitchen Dan haka Indomie ta dafa masa tareda egg da sausage ta Sako a wani qaramin white plate ta doro a tray tareda ruwa mara sanyi sosai da lemon drink tinda tasan ba lallai yasha sauran drinks dake gidan ba.

A dining ta ajiye ta qaraso palon Yana zaune Yana waya ahankali cikin nutsuwa gabaki Daya ya rikita palon da qamshinsa data jima Bata ji ba.

Bai ajiye wayar ba ya Dan dago ya zuba mata idanuwansa ta dauke Ido a hankali ta furta masa ga abincin a dining.

Bai dauke idanuwansa akanta ba Bai Kuma Bata amsaba hakama Bai Dena wayan Dayake yiba.

Kasa tsayuwa taji tana Neman Yi Dan haka ta juya tabar gurin ta shige dakinsu tareda rufo kofa Kai tsaye toilet taje tayo brush ta saka blush pink satin night suits marasa tsayi ta Haye gado tana kokarin Kiran Zeenah sai gata ta shigo bedroom din tana Amsa waya.

Saurin kashe wayan tayi tana qarasowa tsakiyan dakin tace

“D yazo gidan Nan right????

Ajiye wayarta Bena tayi tana kallanta dakyau tace

“Kinsan Hakan kike tambaya na Kuma”

Murmushi Zeenah tayi tana cewa

“Ina shigo na ji Hakan Amma ban tabbatar ba sbd ban gansa ba inaga ya shige ko ya fita.”

Basar da zancensa Bena tayi ta tambayar Yaya inda taje.

Numfashi ta sauke tana zare kayan jikinta ta jefar tace

“Komai yaje daidai inshallah zan samu attending meetings din Koda so biyu ne ma is ok zan dauki Abinda nakeson dauka.

Allah yasa” Bena ta fada tana fatan Hakan itama.

Toilet Zeenah ta fada daganan Bena ta shige lallausan duvet din gadon tana lumshe idanuwanta sbd bacci takeson lokacin baccinta yayi.

Washe gari babu me tashi gidan da wuri dukkaninsu bare yanzu da Mai gidan yake gidan,

Basu farka ba sai 10 har da mintina,

Benazir ce tayi brush tafara fitowa cikin kayan baccinta ta nufi kitchen shaf ta Manta da me gidan yazo gidansa.

Tea mara zafi hado da cookies ta fito kenan yafito daga bedroom dinsa a shrye cikin tsadadden Navy blue cashmere kaftan da hular qube sai qafafunsa dake sanye da Berluti demesure leather oxfords.

Qamshinsa kawai me sanyi tafara ji kafin ta dago daga kokarin zaman Datake Yi sukai Ido biyu daidai Yana qarasa fitowa palon Yana kallan agogo sbd yakusa latti a Abinda zaije Yi.

Yana dosota ta ajiye mug din hannunta ahankali sbd kada ya subuce mata ta dauke hannunta daga ajiye cup din Yana Dora nasa ya dauka ahankali yakai bakinsa baice mata komaiba bare amsa gaisuwan datai masa muryarta na yankewa da mamaki cikin qaramin sautin Daya sakasa jefa mata Kallo bakinsa na cup din Yana Dan Shan tea din.

 Gashi sunzo kusa daf sosai Kai tsaye hancinta babu Abinda yake shaqa bayan qamshinsa tafara Jin zuciyarta na bugawa a ranta tana tinanin me yakeyi ne Hakan?

Kadan ya buqaci Abu me dumi acikinsa Dan haka kadan yasha ya ajiye cup din tareda daukan tissue ya goge lips dinsa da Dan zafin ruwan tea din suka qara musu ja.

Wani numfashi Bena taja ahankali tareda dauke idanuwanta daga kallansa gabaki Daya sbd tsoransa datakeji Kuma Yana Neman kamata.

Juyawa yayi yabar gurin bayan ya sake Dan kallan kayan jikinta dasuka sakata zama yar sweet16.

Harya fice Bata iya motsawa ba Saida Zeenah ta Bude kofan bedroom dinsu ta fito cikin nata kayan baccin dasuka Fi na Bena zama guntayen tana shafa cikinta sbd itama yunwa takeji.

A sace Bena ta saci kallan jikinta dayayiwa Wani Kallo kafin ficewa

Taga bataga komai ba face kayan datake Jin rashin kyautawan fitowa dasu sbd ta manta dashi a gidan.

Dan Tari ta saki tana zaunawa ahankali ta dauki cup din Daya ajiye takai bakinta tafara Shan tea din tana Amsa maganar Zeenah sama Sama.

Zeenah da Batasan meya faruba tea din ta hado tazo ta zauna tana daga wayarta ta saka kiransa sukai magana ya sanar mata ya fita yanada meeting me mahimmanci sosai da wasu abokan business nasa Wanda Bana kaantes ba.

Tana sauraron wayar da Zeenah keyi dashi Yana magana a natse ba Wani sauri ko rawan murya bare hayaniya.

Zeenah kuwa suna gamawa tace yau ita bazata fita ba zata Jira gida tayi musu girki tinda ita Bena yau dole zata fita akwai itama aikin dazata leqa.

Suna gamawa sukai wanka kowannensu ya shirya suka fito tare Zeenah zata ajiyeta ta tafi da motan siyayyan abubuwan da zata buqata na girkin.

Zeenah kasuwa ta wuce bayan ta ajiye Bena tayi siyayyan fresh veggies da dasu frozen chicken da duk Abinda take buqata duk a supermarket ta dawo gida.

Koda ta dawo me musu Aiki kullum tazo harta gyake koina harma da dakin DD da babu Wanda ya taba shiga sai ranar aka gyarasa gashi yafi dakinsu girma sosai sbd yanason daki me space sosai bama ya iya zama a dakin da babu space me yawa.

Koina na gidan qamshi yakeyi Dan haka ta dakatar da Sima din ta Tayata aikin girkin.

****Se 6 na yamma Bena ta dawo har lokacin Zeenah ce kawai a gidan tana daki tana karatu a laptop.

Ko zama Bena batayiba Saida tai sallan laasar kafin ta tube tanason tayi wanka Amma ta bari sai after magrib.

Abinci ta fito taci kadan sbd yajin da yayi sosai itama Kuma Bata son yaji sosai.

Pepsi Tasha Daya ta qarasa koshi ta dawo dakin lokacin ake sallan magrib.

Suna gama sallah suka bige da waya da Umme da Amnah.

Shikuwa sai dayayi sallan magrib ya dawo

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa wanka yafara ya samu nutsuwa sosai yajisa fresh kafin ya kunna wayarsa Daya kashe Shima ummen yafara kira yayi magana da Amnah yakira dd babba ma sukai magana kafin yayi sallan ishai

Ya sake magana da Naseer dake hotel kafin ya kashe wayarsa gaba daya ya fito sanye da gajeran Nike da armless da slippers na Salvatore F ya fito fatan jikinsa kaman baby ya nufi dining daidai Zeenah na fitowa da farin ciki ta qarasa ta gurinsa tana masa sannu da zuwa sbd Basu hadun ba tin jiyan dayazo sai alokacin.

Tare suka qarasa dining da kanta ta zuba masa abinci ta dauko masa ruwa mara sanyi Takoma Palo ta zauna tana daukan laptop din Bena dake Palon zata duba Wani Abu.

Abincin ya kalla yaga brown vegetable basmati ce da qananun Naman Kaza aciki,

Ya Dan sake kallan abincin sbd bayason abinci me nauyi sosai da dare Shima Amma haka ya Dan daure yaci sbd Yana Jin yunwa.

Emilian spoon din dake aje ya dauka ahankali yasaka yafara cin abincin a natse.

Da farko baiji yajin sosai ba Saida yaci gaba daci yaji Wani azababben yajin daya sakasa sarkewa gumi na tsatsafo masa a farar fatarsa.

Ruwa ya dauka ya Sha fuskarsa na yin ja take sbd masifar da Bai taba ji ba a rayuwarsa sbd tinda Allah ya haliccesa Bai taba cin yaji haka ba

Baima San yaya masifansa yake ba.

Ruwan Daya Sha ya qarasa tsananta masa yajin dayakeyi har cikin kunnuwansa da cikin Kansa take Wani irin Tari ya sarkesa Yana Jin Kansa na Neman juyewa.

Ganin mummunan halinda ya shiga Yana Tari ya saka Zeenah tasowa da sauri ta dauki ruwa ta miqa masa ya dakatar da ita da hannuwansa Yana sake Tari idanuwansa na sauyawa gabaki Daya,

Idan akace asalin Dan gidan hutu ajebo to DD shine kalman in form of mutum,

Baisan yaji ba,Bai taba cinsa ba,baisan gigicewansa ba tinda duka abincinsa simple abubuwa marasa yaji yakeci,

gidansu Sam baa cin yaji bare shi Da Rabin rayuwarsa a turai ne

Dan haka gabaki Daya ya birkice musu Yana Neman rasa numfashinsa.

Hankali tashe Zeenah ta dauko masa ruwan sanyi tana miqa masa Amma Sam bazai iya Sha ba.

Abinci Ta dauki spoon taci kadan take ta saki ihu itama tana Shan ruwa da sauri ta kallesa tana rasa ya zatayi sbd Sima mayya dai kashesa zatai da yajin ta zuba a abincin Wanda Zeenah Bataci ba sai lokacin,

Batasan Hakan yake ba da bama zata aje masa ba sbd sanin ko kashesa wannan yajin zai iya Yi.

Ihun Kiran sunansa da Zeenah keyi yasaka Bena fito da sauri Bata tsaya saka sauran bottoms na saman guntuwan rigarta ta bacci ba Datake sakawa.

Cikeda mamaki da tsoro take kallansu

Idanuwansa da fuskarsa sunyi jajir ya sauya take sbd azaban da be taba ji ba.

Jikin Zeenah na rawa ta sake dauko ruwa me sanyi sosai ta zuba a cup zata Basa Bena data fahimci meyake kokarin illatasa ta nufi kitchen da sauri itama hannuwanta na rawa ta dauko Nutella ta Bude Bata tsaya saka spoon ba tsaban rudewa ta saka finger dinta Daya ta lakato me yawa ta nufi bakinsa dashi ta saka masa Bai Bai gama shigewa bakinsa ba ya riqe hannun nata ya janyota gabaki Daya ta fado Kansa ya Dora bakinsa da Nutella din akan bakinta ya hade Yana tsotsan Nutella din idanuwansa a rufe jikinsa na Dan rawan masifan Dayake Neman yanka harshensa.

Chapter 55

55

A kan qafafunsa ya zaunar da ita hannunsa Daya na zagayo qugunta hannun Daya na riqe da

kanta ya ringa tsotsan Nutella din tareda yawun bakinta Dan shi tsaban azaba bayajin ma yanada sauran yawun bakin dazai iya Shan Nutella din

sauran yawun bakin dazai iya Shan Nutella din.

      A yanda yake Janyo yawunta Yana juyasu da harshensa tareda Nutella din acikin bakinsu su dukan yasaka Bena samun attack sbd mutuwan zaune tayi a jikin nasa tareda rufe idanuwanta tana Neman somewa.

Halinda take ciki Bai bari ta qarar da feeling ko Daya ba na yanayin data samu kanta ayau hannun namiji Rana ta farko a rayuwarta.

Shi Kansa idanuwansa a rufe suke Yana sake Dan matseta jikinsa da hannun dake zagayen da ita ahankali,

Tsantsin kayan baccin jikinta da yanda yake matse da ita da lallaunsa hannunsa ya saka rigarta janyewa daga qasa cikinta da cibiyanta na bayyana batareda dukkaninsu sun saniba.

Baitaba sanin azaban yaji haka yake ba a rayuwansa,

Bai taba sanin yaji Yana kisa ba sai a ranar sbd shi dai yasan zaa iya kashesa da yaji Kai tsaye.

Ahankali tafin hannunsa ya sauka kan fatar cikinta Daya bayyana a take taja Wani wahalallan

numfashin Daya sake sumar da ita jikinsa tana sake rintse idanuwanta,

Shi kuwa hannun nasa na sauka fatanta sake zagayeta yayi da duka hannuwansa Yana qarasa

shanye Abinda yake Sha kafin ya sauke numfashi ahankali tareda zare harshensa daga cikin bakinta Yana sake sauke numfashi Mara qarfi tukuna batareda ya saketa ba ya Bude idanuwansa dasukai jajir ahankali ya Kalli idanuwanta dake rintse gam Wanda data Bude idanuwanta ta ga idanuwansa a wannan halin zata iya somewan gasken wannan Karan Dan haka kaman ta sani ta kasa Bude idanuwanta saima sake rintse su tayi jikinta na rawa hakama kirjinta na Hawa da saukan bugawar da zuciyanta keyi sosai.

Iskan bakinsa dayafi komai azabtar dashi ya sakar mata a fuska ahankali Wanda ya sakata sake rintse idanuwanta ahankali tana qanqame rigarsa.

Shi Kansa bai gama dawowa cikin cikakken hayyacinsa ba idanuwansa ya Dan rintse ya sake budewa har lokacin fuskarsu na hade duk da ya saki bakinta Amma lips nasu suna shafan juna shiyasa direct numfashin juna sike shaqa babu Wanda ya motsa.

      Jin shiru yasaka Bena hadiye Wani yawu zuwa maqoshinta daqyar kafin ta Bude idanuwanta dasuka Dan sauya itama

Acikin idanuwansa dasukai ja nata idanuwan suka fada sbd fuskansu dake hade.

Kokarin Maida idanuwanta ta sake rufewa tayi Amma motsinta ya saka lips dinsu sake shafan juna atake a ja numfashi daqyar kirjinta yayi sama ya qara mannuwa da nasa take ya rintse idanuwansa ahankali tareda janye fuskarsa daga tata ahankali Yana Bude idanuwa ya janye hannuwansa dake zagaye da ita manne jikinsa.

Kafin yayi kokarin miqar da ita daga jikinsa ta rigasa fizgo kuzarinta ta miqe da sauri hannuwanta dake Dan rawa sune rufe gaban rigarta da sauran bottoms din suka qarasa cirewa Allah yasa rigar Bata janye daga saman ba iya cikinta da cibiyanta kawai ya Gani ya dauke Kai tareda miqewa yabar gurin Kai tsaye batareda ya waiwayo ba.

Yana barin gurin qafafuwanta suka sake ta kasa tsayuwa ta dafa dining din rawar hannuwanta na qaruwa.

Rintse idanuwanta tayi tana kokarin daidaito numfashinta Dayake Neman fasa mata kirji ta ringa danne numfashin har Saida bugun zuciyarta ya dan dawo daidai.

Itama bedroom dinsu ta nufa da Dan sauri tana Hana qafafunta sanyi.

Tana shiga dakin ta rufe kofar tana juyowa sukai Ido biyu da Zeenah dake zaune tana da waya a hannunta da alama wayar takeson Yi kokuma ta gama.

Dauke Kai tayi tana saka botiran rigarta tareda kokarin daidaita kanta ta fuske zata shige toilet Zeenah da ko ajikinta Abinda tagani din Kuma tana ganin Hakan ta tahowarta daki ta basu guri sbd ganin kalan french kiss da Bata taba ganiba tace

“Kiyi wanka kawai daga can sbd Nutella din is All over your face.”

Kasa tsayawa tayi ta fada toilet din tareda rufewa ta jingina jikin kofa tana Dafe goshinta.

Mirror ta kalla taga yanda zagayen bakinta yayi kasa kasa da Nutella din hakama Shima ya Dan San mata yajin bakinsa a nata bakin sbd tana Dan Jin yajin kadan.

San mata yajin bakinsa a nata bakin sbd tana Dan Jin yajin kadan.

      Batayi wankan ba sbd fitowanta kenan ta fita palon Dan haka fuskarta kawai ta wanke da kyau ta fito bayan ta goge fuskar da towel qarami me taushi Bata iya tsayawa ko fira da Zeenah ba ta Haye gado ta Kwanta ta shige bargo tareda rufe idanuwanta tana yiwa Zeenah din saida safe.

Zeenah kuwa Sam ita Bata Wani damu ko Jin kunyar Hakan ha tinda ai Hakan is more than okay

ma garesu sbd su din maaurata ne,

Ita Bata San suna buqatan Hakan ba sai yanzu data wannan incident din ya faru sai take tinawa

da aure ne fa akan Bena din na yayanta gashi Young billionaire me class da zafin Kai da yawa mata shine namiji Dari bisa dari dasuke buqatan samu Dan haka gaskia ya kamata Bena tayiwa kanta fighting matsayinta tin kan baturiyar matarsa Daya ta dawo gata jininsu ce bazasu gujeta ba duk yanda suke tsananin kaunar Bena din kuwa.

Washe gari tinda safe Zeenah ta fice gidan lokacin Bena Bata farka ba haka Shima Bai fito ba.

Sai 9:30 Bena ta farka tayo brush ta fito tana kokarin saka kira a wayanta ta nufi kitchen ta dafa white Instant noodles da half done eggs guda biyu tana zaunawa Yana fitowa cikin free size kayan baccinsa farare Kal masu santsi gaban rigar a Bude gabaki Daya fatan cikinsa Wani daukan Ido takeyi sbd lafiya,hutu da murdewan Naman cikinsa maana abs nasa.

Ruwan tea din Dayake bakinta ta hadiye ahankali tareda Dan dauke idanuwanta daga tinkaro dining din da yayi.

Yana qarasowa fuskarsa babu walwala ko sakewa ya Dan kalleta kadan ya Bude baki a natse yace Yana buqatan co�ee kawai.

Juyawa yayi ba ya koma Palo kan kejeran Datake ta zamansa ce duk Yana gidan ya zauna a natse tareda crossing legs a hankali kafin ya dauki remote ya kunna TV yayi qasa da murya sosai Dan bayason murya sosai ko a qasa qasan Yana Dan ji,.aje remote din yayi ya dauki wayarsa ya Nemo

numbern Naseer ya kirasa

Cikin tausasshiyar murya mara qarfi sosai Kai tsaye Yana dauka yace

“Ina buqatan doctor I think papper ya tabamin kirji ko zuciya,just find a doctor Dayake kusa ka kawomin.”

Kashe wayan yayi ya ajiye daidai lokacin ta qaraso dauke da co�ee din ta ajiye masa kan table tareda Dan kallansa kadan tace

“Good morning”

Juyowa yayi ya zuba mata idanuwansa da sukai laushi da rashin kuzari sbd zazzabin Daya kwana dashi na azaban jiyan.

Dauke kallan nasa yayi akanta ahankali kafin ya amsa cikin qaramin sautin da nutsuwa tukuna ya dauki cup din yakai bakinsa cikin nutsuwa.

Juyawa tayi tabar gurin itama ta koma dining acan ta zauna tana qarasa Shan tea dinta sbd Instant Noodles din Kuma ta fita ranta bazata iya ci ba ya huce.

Tattara dining din tayi Takoma kitchen tana ajiye kayan Sima na knocking.

Fitowa tayi tana kallan time tasan Sima dince Dan haka Kai tsaye ta Bude mata ta shigo.

Tana ganin DD a palon tayi saurin yin qasa da Kai tana masa barka da safiya ta silale ta wuce kitchen.

Bena Kuma cup Daya gama dashi ta dauka ta Kai kitchen Takoma daki ta shiga wanka sbd yau itama zata fita.

Tana fitowa wanka ta shirya karfe goma Sha Daya da mintina ta fito cikin classy Alexander McQueen long pencil skirt golden yellow da farar laced shi�on long sleeve cikinta a shafe kaman

wadda batacin abinci hakama shape dinta daidai yafito sosai a shigar bawai matsewaba,

Silk scarf ne a kanta me Dan girma ta zagaye kanta dashi daga handbag sai wayarta a hannunta

ta fito key din motan ma Yana Palo tana fitowa ta dauka ta fice sbd baya palon ma ya shige Shima sbd motsin Sima me Aiki Yana damunsa.

Bayan fitarta a harabar gidan ta hadu da Naseer zai shigo kasa kallan juna sukai sbd yanda tasa zuciyar ke bugawa da sonta har lokacin ita Kuma batasan metakeji ba Amma dai bazata iya

ygjy

 kallansa ba sbd tinawa da kalman so ya taba shiga tsakaninsa da kanta. Buga mota tayi ta fice daga gidan gabaki Daya tana saukar da numfashi.

Daga gurin aikinta karfe 5 na yamma ta baro ta biya ta dauki Zeenah daga Nan suka wuce shopping Wanda kusan Zeenah ce duk tayi sayayya ita Bata buqatan komai kawai pyjamas ta sake Dan Siyawa kanta da Amnah sai undies da Bata gajiya da siyansu designers masu shegiyan tsada.

Sai gab da magrib suka dawo gida Koda suka shigo Yana Palo zaune cikin black Armani’s marasa nauyi Yana waya a hankali har lokacin Bai dawo daidainsa ba Dan ciwon ciki Kuma yajin jiya ya sakar masa Dan haka wunin ranar koina ma Bai fita ba Yana gidan.

Itace ta fara gaidasa cikin sanyi da nutsuwa kafin ta wuce ciki batareda taji ya amsaba sbd muryansa da bayason dagawa.

Zeenah kuwa zaunawa tayi gefensa tana gaidasa cikin kulawa da tambayan jikinsa.

Idanuwansa masu haske ya Dan waiwayo ya zuba mata kafin ya dauke Kai cikin nutsuwan harshe ya amsa mata Yana cewa

“A wannan time kuke dawowa from work normally or….”

Fasa qarasawa yayi kawai sbd baimasan meye dalilin tambayar tasa ba.

Itama Zeenah data so fahimtar tambayar dabai qarasa din ba sai tace

“Muna buqatan abubuwa da Dan yawa shine muka biya muka Siya bayan munbar o�ice.” Bai kalleta ba ya gyada Kai ahankali kawai.

Miqewa tayi ta nufi bedroom din itama ta shige lokacin har Bena ta tube tashige toilet.

Tana fitowa daga wanka sallar magrib tayi ta fito zuwa kitchen sanye da pencil jean Daya lafe a siraran cinyoyinta da hip nata hakama rigar jikinta White vest ce Kuma Bata Dan haka bra din

 jikinta ta zama strapless bra.

     Abincin da Sima tayi ta jera a dining ta fara budewa taga fried spaghetti da veggies,

Daga qamshinta kawai ta tabbatarda zatayi yaji Dan haka kadan ta saka fork ta Dan diba kadan takai bakinta taci.

Ajiyewa tayi tareda daukan ruwan dake kan dining din ta Bude Tasha tana satar kallan inda yake taga ko waiwayowa baiyiba.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda kwashe kayan tayi kitchen dasu sbd itama bazata bari yaci abincin ba sbd akwai yaji sosai yauma.

Chapter 56

56

Simple chicken macaroni salad ta hada musu da zallan pineapples drink mara sanyi sosai sbd

dukkaninsu babu me son Abu me sanyi sosai.

 Jerawa tayi a dining ta iso palon cikin nutsuwa ta sanar masa

     Juyowa yayi ya Dan kalleta kafin ya saukar da idanuwansa kan dagayen cinyoyinta da jeans din ya lafe.

Dauke idanuwansa yayi tareda Dan kallan time ya Bude baki a hankali yace

“Bana buqatan abinci irin na jiyan”

Numfashi ta Dan sauke ahankali tareda kauke Kai daga kallansa a natse itama tace “Light Abinda zaka iya ci ne”

Gyada Kai yayi batareda ya juyo ya sake kallanta ba.

Juyawa tayi ta bar gurin zata koma kitchen Zeenah ta fito tareda Janta suka nufi dining din dole

ta zauna

Shima tasowa yayi a hankali ya zauna tareda kallan Bena din da kasalallun idanuwansa

kaman mara gaskia haka Ta taso ta zuba masa ta koma ta zauna itama ta zuba suka fara a natse babu me magana.

Kadan yaci yasha drink din sosai kafin ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar dining din.

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa

Suma suna gamawa suka tattara gurin suka shige.

Sallar ishai tai kafin tayi brush tai Shirin bacci ta kwanta.

Da daddare ciwon ciki sosai ya hanasa bacci bayan zufa babu Abinda yake hadawa duk da ba kaya jikinsa dogon silk wandon pyjamas dinsa ne kawai jikin nasa.

Sosai yakejin azaban ciwon cikin Dan haka ya qarawa AC din dakin qarfi tareda tashi zaune ya jingina Kansa jikin kan gado Yana rufe idanuwansa da suka sauya sbd ciwo a hankali.

Ruwan sanyi yakejin Yana buqata Dan Sha su shiga cikinsa ko zai rage zafin Dayake ji cikinsa.

 Hannu yakai ahankali ya dauko wayarsa dake kashe bedside dinsa tareda kunna wutan gefen gadansa.

Kunna wayan yayi Bai tsaya duba time ba ya saka Kiran Zeenah sbd shi ya Saba komai Yi masa akeyi ruwan ba bayajin zai iya miqewa yaje ya dauko gefen cikinsa ya riqe sosai.

Bena ce tafara Jin ringing wayar cikin bacci Dan haka ta Dan Bude idanuwanta dake cike da bacci tafara lalaban wayar ta dago ta duba sunan waye ke kira sbd ta dauka wayarta ce ma.

D” taga an rubuta Kai tsaye ta Gane waye Dan haka baccin ya Dan saketa ta miqa hannunta Daya tana taba Zeenah din wadda Baa tadata idan tana bacci Sam Bata san Hakan.

Ganin Zeenah din taqi tashi ya saka Wani Kiran na Kuma shigowa ta daga wayar a hankali tareda cewa “hello” cikin muryan bacci.

Bai tsaya Jin Ba Zeenah din bace Kai tsaye da muryarsa Shima da bata fita yace “Ina buqatan cold water yanzu”

Yanada fada ya kashe wayan tareda ajewa Yana rintse Ido zufansa na qaruwa. Bena kuwa Ras ta Bude idanuwanta gabanta na faduwan.

Tashi tayi zaune ahankali tana kallan wayar hannunta kaman Bata Gane Abinda ya fada ba sbd qasa qasan muryansa Amma Kuma bazatai karyaba taji Abinda ya fada din.

Numfashi ta Dan sauke ahankali tareda ajiye wayar ta yaye bargon jikinta ta ziro qafafunta qasa ta Sauko tareda zira slippers dinta na masu laushi gashin dayake jikinsu.

Fitowa tayi ta nufi kitchen ta kunna wuta ta nufi fridge ta Bude tareda dauko ruwan me sanyi sosai guda Daya ta dauko Daya marasa sanyi tareda glass cup ta jerasu a trey ta kashe wuta ta fito.

Bedroom dinsa ta nufa Kai tsaye tareda tsaya bakin kofar tayi knocking ahankali hannuwanta na Dan rawa hakama zuciyanta.

      Shiru babu alaman yajita Amma batai saurin sake knocking din ba ta Dan Jira Wani mintin Daya kafin ta sake Dan buga kofan a hankali.

Ahankali ya Bude idanuwansa a Dan galabaice ya Kalli kofan cikin qaramin sautin da baiyi tinanin taji ba yace

“Shigo”

Numfashi taja kirjinta na sake bugawa kafin ta Dora hannunta a handle na kofan ta Bude ahankali tareda turawa Wani sanyi da qamshinsa Dayake kame da dakin suka sauka fuskanta da

hancinta taji kirjinta na tsananta duka

Ta Maida kofan ta rufe ahankali ta juyo babu haske sosai a dakin da yawa Amma tana iya ganin

komai.

Ahankali yakai hannu ya qarawa wutan dakin haske sai alokacin tagansa zaune jingine da gadon

jikinsa ba kaya

Kiris ya rage ta Sako ruwan hannunta Amma ta qanqame trey din tana dago qafafuwanta da qyar

ta nufosa kanta a qasa.

Ahankali ya Bude idanuwansa Shima sai alokacin yaga itace ba Zeenah ba Dan haka ya Maida idanuwansa ya Dan rufe tareda miqa hannu cikin nutsuwa yace ta Basa ruwan.

Ajiye kayan tayi akan Wani luxury table dake tsakiyar makeken dakin tukuna ta dauko robar ruwan me sanyi ta miqa masa.

Yana karba ya Bude ruwan Kai tsaye tareda dorawa bakinsa yafara Sha a hankali.

Juyawa tayi zata fice Bata Isa kofa ba ruwan ya dawo masa ta hanyar Amai me qarfin gaske sbd ruwan sanyin Kansa ba abin shansa bane.

Toilet ya nufa Kai tsaye tanajin Yana zuba aman take ta fahimci baida lafiya Dan haka sai ta kasa ficewa ta juyo ahankali ta Kalli ruwan daya aje din ko rufewa baiyiba ta dawo ahankali ta dauka ta rufe ruwan ta Maida kan trey ta dauke pillow dake jikinsa ya fado qasa gurin saukowansa ta durqusa ta dauka tareda mayarwa kan gadon tana gama sauya masa Wani so� luxury beddings

Yana fitowa daga toilet daure da towel jikinsa na tsiyayan ruwa da gumin Dayake Yi har lokacin

Yana fitowa daga toilet daure da towel jikinsa na tsiyayan ruwa da gumin Dayake Yi har lokacin

  na zafin cikinsa.

    Kallanta yayi ahankali tareda qarasawa kan gadon ya zauna ahankali batareda ya kalleta ba yace ta dauko Wani ruwan me sanyi.

Kallansa tayi cikin sanyi zatai magana Amma ta kasa ta juya take ta dauko Wani ruwan me sanyi Koda ta dawo ya kwanta jikinsa na fidda Wani tiririn zafi.

Ajiye ruwan tayi tareda kallansa taga idanuwansa rufe Dan haka batada zabin Daya wuce juyawa taje ta tada Zeenah ko zasu kira masa likita ne.

Tana fita dakin dakinsu ta koma tayita kokarin tada Zeenah Amma Zeenah din tace Mata kanta na ciwo Bata buqatan tashi yanzu.

Jin haka sai batama tsaya fada mata DD din ne baida lafiya ba ta juyo ta dawo Palo tana kallan kofar bedroom dinsa batasan mekuma zatai ba.

Samun kanta tayi da zaunawa a palon tareda shiga tinani har bacci ya ringa Dan fizgarta kadan.

Tashi tayi zata koma dakinsu taji Bude kofan bedroom dinsa ahankali ta juyo daidai yanason fitowa ganinta yasakasa komawa Yana cewa ta qaro ruwan sanyi.

Wannan Karan Daya ta qaro ta koma dakin tana shiga ta taddasa kaman yanda ta taddasa farko zaune tsakiyan gadan ya jingina bayansa da kan gadan.

Qarasowa tayi Bata ajiye ruwan ba ahankali ta Bude baki cikin sanyi tace “Shan ruwan sanyin zai kawo wata illar”

Bude idanuwansa dasukai jajir yayi ya kalleta cikin gajeran sauti yace a cikinsa yake buqatan ruwan ta zuba masa ahankali.

Bazata iya zuba masa ruwan Kai tsaye ba dan haka ta fita taje ta dauko sabon Dan qaramin towel me qaranci sosai ta jiqasa da ruwan sanyin sosai ta hadiye Wani numfashi daqyar kirjinta na dokawa ta hau gadon ahankali matsawa inda yake hannuwanta na Dan rawa ta Dora towel din

 kan fatar cikinsa da babu kaya jikinsa ruwan sanyin ya sauka cikinsa tareda gangarawa jikinsa ahankali ya bude idanuwansa take numfashinsa na Neman daukewa.

Saukan mayun idanuwansa akanta yasa Bena hannunta ya tsananta rawar data saka tafin hannunta sauka kan qasan cikinsa ta shafi cibiyansa a take dukkaninsu suka Kalli juna.

Saurin janye hannunta tayi tana goga masa sanyin a Dan rude shikuma ahankali relief ya fara saukan masa sbd zafi ne sosai cikinsa keyi Amma sanyin ya taimaka masa.

Saida ta sake saka wasu ruwan sanyin jikin towel din ta sake rage masa zafin cikin tsawon lokaci kafin ya samu dawowa hayyacinsa ahankali ya dago ya kalleta itama Jin idansa akanta ya sakata dagowa idanuwansu suka shiga na juna a hankali tayi saurin janye nata har lokacin tana Jin nasa akanta.

Rudewa tafara Yi da Jin idanuwansa akanta ba tsammani tsaban rudewa ta sake Sakin towel din tattausan tafin hannunta ya sauka kan fatarsa wannan Karan riqe hannunta yayi da hannunsa tareda dagowa Yana sake kallanta tsikan jikinsa gabaki Daya suna miqewa.

Hannunta Daya riqe yasata rasa balance nata a zaune sbd a hannun ne qarfinta na zaman yake Dan haka ba tsammani ta fada jikinsa ahankali kirjinta da nasa suna mannuwa da juna wannan Karan rintse idanuwansa yayi ahankali sanyin AC da rigar baccinta ta kama Yana sauka kan fatar jikinsa Yana sake sanyaya masa jikin Dan haka batai tsammani ba taji hannuwansa ya zagayota kirjinta na qarasa mannewa da nasa ita kanta Saida ta rintse idanuwan.

Babu komai akanta Dan haka qamshin Olay dake cikin gashinta yafara shiga hancinsa tareda asalin nata qamshin Daya sani suka ringa shiga hancinsa Kai tsaye suna Neman dawo da zazzabinsa Daya sauka.

Ahankali ta daga hannuwanta ta sauke kan bayansa zata janye jikinta Amma ta kasa Hakan sbd mutuwar da jikinsu yayi su dukan.

Shiru sukai kowannensu idanuwansa a rufe numfashinsu ne Kawai ke sauka jikin junansu,nasa yana sauka cikin wuyanta ahankali da nutsuwa ita Kuma nata na sauka kan kirjinsa da babu kaya tana tayar da tsigan jikinsa da duk saukan dumin numfashin nata.

      Shi bacci yafara daukewa ahakan cikin sanyi da gabalaitan da yayi daga jiya zuwa yau din,

Ita kuma sai daga baya nata baccin ya dauketa tana jira ya saketa ta tafi sai kasalanta ta saka baccin dake idonta tun farko dawowa ya dauketa.

Da Asuba Zeenah na tashi sallah taga babu Bena,

Fitowa Palo tayi nanma Bata ganta ba Takoma daki ta duba wayarta taga wayarta ajiye.

Toilet ta shiga nanma bata Nan Dan haka tayo alwala ta fito Bata tada sallah ba Saida ta sake fitowa ta nufi dakin yayan nata zata sanar dashi Bena fa bata gidan tana Kaiwa kofar bedroom din ta dakata sbd tinanin ko Bena din tana ciki,to Amma Tayaya?yaushe?

Danne zuciyarta tayi ta Hana kanta bugawa Takoma daki ta tayarda sallah tayi tagama har lokacin tana cikin yar shakku da fargaban inda Bena din zata tafi cikin dare tinda tare sukai bacci Tama rigata yin bacci Kuma ita Tama kasa Tina Bena din ta tayar da ita da daddare.

Har kusan 7 na safe babu Bena ba labarinta Dan haka 7 din na wucewa ta tashi ta fito tareda musu ordern breakfast daga Wani one of the best restaurants dake Lagos.

Bena kuwa cikin kasala ta motsa ahankali tareda Bude idanuwanta dake da sauran bacci har lokacin ta samu idonta cikin nasa yana Mata Wani irin Kallon data kusan somewa sbd tsayawar bugun zuciyanta.

Tashi tayi da Dan sauri daga jikinsa Datake kwance kaman baby.

Shikuwa har lokacin kallanta yakeyi da idanuwansa dasuka koma yanda suke suke gigitata mutane da kwarjininsa kyansu tareda haskensu.

Chapter 57

57

Kasa kallan fuskarsa tayi ta sauko gadon ahankali tareda zira slippers nata masu laushi qafarta

tana kokarin juyawa ta fice batareda ta iya ko furta kalma Daya ba

Tana Kaiwa kofa ahankali taji muryarsa me taushi da nutsuwa a sakalance yace

jyy

      “Idan kinyi sallah I need co�ee irin na jiya.”

Gyada Kai tayi ahankali batareda ta juyo ba ta Bude dakin ta fice tana gyara rigarta datake qamshin jikinsa gabaki Daya….

Daidai fitowan Zeenah daga kitchen ta tsaya tana kallan Bena din dake gyaran rigan baccinta tana fitowa daga hanyar bedroom din DD.

Kunyace me tsananin gaske take son kama dabaibaiye Bena din Amma taqi yarda da Hakan sbd wahala zatasha gurin Zeenah da tsokana Dan haka ta fuske ta nufi bedroom nasu tana qin sauraran Zeenan data biyota tana Kiran sunanta da sauri.

Tana shiga daki toilet ta wuce Kai tsaye ta rufo sai alokacin ta saki ajiyan zuciya Mai sanyi tana rintse idanuwanta.

Yanayin lattin sallan da sukai yasakata kasa tsayawa tinani da daidaita nutsuwanta tayo brush da alwala ta fito ta saka kayan sallah ta tayar.

Bayan ta idar tayi istighfar da adduointa ta miqe ta sauya kaya sbd duk motsinta qamshinsa takeji ajikinta Yana tashi Yana dawo mata da dumin fatarsa a jikinta.

Fararen Dior sweatshirt da slim trouser ta saka ta fito da qaraman hulan da Bata gama rufe gashin kanta ba ta nufi kitchen.

Co�ee ta fara kunna masa kafin ta soya masa chips da farin soyayyan kwai.

A farin kyakyawan trey ta jera masa su harda co�ee din ta fito ta ajiye masa a dining tana juyowa Yana fitowa Shikuma cikin black Ralph Lauren sleeveless sweatshirt da quarter trouser.

Fuskarsa pale Amma so fresh Da kallo Daya zakai masa ka Dan fahimci yayi kasalan ciwo.

Dining din ya nufo Kai tsaye idanuwansa akanta

Ita Kuma ta Dan Yi qasa da Kai tana Bude baki da sanyin murya tace masa

“Good morning”

      Saida ya zauna ahankali kafin ya dago ya kalleta ya Bude baki a gajarce Shima ya amsa Yana tambayanta Zeenah.

Kafin ta Basa amsa Zeenah din ta fito daga bedroom sbd breakfast datai order da aka kawo.

Da mamaki da shagwaba a fuskanta tace musu tafa Yi ordern breakfast.

Bai kalleta ba Bena din ya Dan kalla Yana daukan cup din co�ee yakai bakinsa ya kurba a hankali.

Ganin soyayyan farin egg din ya Basa tabbacin babu pepper a ciki Dan haka yaci breakfast din cikin nutsuwa sbd shi yanzu ko abinci me kala bayasan gani a gabansa.

Junk food ne ma kusan duka Abinda Zeenah tayi order Dan haka anan dining din Suka zauna tareda shi sukai breakfast.

Suna gamawa Dayake sunyi lattin tashi duka gidan saiga Sima tahau aikinta.

Bena Bata fita ba yau Zeenah ce kawai ta fita Dan haka daga ita sai shi suka wuni gidan Amma kaman ma baya gidan Dan tinda ya shige Bai fitoba.

White couscous da kidney sauce Mai hade da veggies tayi masa batareda ta saka yaji ko kadan ba.

Tana gamawa ta wuce daki tayi sallan azahar tareda sake wanka ta saka kayan marasa nauyi ta kwanta Dan baccin ko awa Daya ne ta huta.

Sai 4 ta tashi tayi alwala tayi sallan laasar tana idarwa ta fito tana waya da Amnah cikin kasala sbd baccin Rana kashe mata jiki yakeyi.

Dining ta nufa ta zauna taga baa taba abincin ba ta juya ahankali ta Kalli kofan dakinsa kafin ta dawo da hankinta kan wayar datakeyi a natse tace

“Baby kinyi waya da daddynki yau?”

   Eh,yanzuma dashi na gama waya kafin ke.”

   Numfashi ta sauke ahankali tace

“Ok bacci yakeyi ne ko me?”

Aa Ya tashi bacci fa tin dazu.”

“Ok baby ki sake kiransa kice ya fito ga abincinsa a dining” Shiru Amnah tayi har Mummyn tata ta gam bayani tace

“Mummy kina fushi ne da Daddy? Shine Zaki saka na kirasa?

Meyayi kike fushi dashi?

Nidai mummy ki shirya da daddynah.

Saurin dakatar da ita Bena tayi tana cewa

“Ya Isa haka naji,jeki gurin Nafisat ko Umme zan kira anjima.”

Kashe wayarta tayi tana ajiyewa kan dining din ta miqe ta nufi kitchen Dan dauko drink me Dan sanyi.

Tana fitowa ta taddasa yana zasu ne a natse idanuwansa kan wayarta dake ringing. Da sauri ta qaraso ta ajiye drink din tana duba wayar sunan Fahad kaante ne Akai.

Daukan wayar tayi daga gabansa batareda ta dauka ba ta ajiyewa dayan gefen tana masa barka da fitowa.

Bai dago ya kalleta ba ya gyada Kai ya Dora da cewa

“Bana buqatan spicy food you Already know so idan akwai pepper karki zuba I will order Wani abin.”

 Qarasa zuba masa tayi tareda Dan dagowa Bata Kalli fuskarsa ba tace “Abincin is not spicy ko kadan”

Janyewa tayi daga gurin bayan ya Dan deba spoon Daya yaci kadan yaji ba yajin ko kadan tukuna ya Dan sauke ajiyan zuciya ahankali mara sauti yafara cin abincin a hankali cikin nutsuwa.

Itama abincin takeci ahankali batareda ta dago tana kallansa ba.

Ta rigasa gamawa duk da sanyinta sbd kadan taci ta koshi,

Miqewa tayi ta dauke plate da sauran kayan ta mayar kitchen ta tsaya gyara kitchen din Bata

dawoba tanaji wayarta na ringing taqi fitowa sai Daya gama yabar gurin.

Fitowa tayi ta qarasa kwashe kayan ta gyara gurin Shima Takoma kitchen ta qarasa aikin gyara can din ta wanke hannuwanta ta goge da tsafatataccen Daya daga cikin towels qanana dake kitchen din Jere ta fito.

Wayarta dake dining ta dauka tana dubawa duka misscalls fin Fahad kaante ne Dan haka ta wuce daki zata kirasa Zeenah ta dawo Dan haka ta fasa Kiran tana kallanta da murmushi kan fuskarta tai mata Barka da dawowa suka shige daki sbd lokacin Me girma DD din ya samu fita daga gidan.

Suna shiga ta kira Fahad ta zauna kan qaramar couch dake dakin tana wayar cikin nutsuwa da sakewar datai dashi.

Har Zeenah ta shiga ta fito suna wayar sai daga baya ta kashe tana kallan Zeenah dake zaunawa gaban mirror tace

“Yaya dai Zee kaante?”

Gajeran dariya mara sauti Zeenah ta sake tana fara shafawa jikinta body cream me kyau da tsadan gaske tace

“Ki shirya mu fita akwai inda zan kaiki to show you Wani Abu.”

Cikin Jin Hakan yayi mata Bena tace ok sbd tana buqatan refreshing kanta itama.

Sai bayan sallan magrib suka fita Wani mahaukacin mall suka tafi me dauke da duk abubuwan dasuke buqata designers na waje masu tsadan gaske suka fara kashe kudi batareda Jin zafinsu

ba.

Suna gamawa Wani 5star Res sukai branching suka ci abubuwa kala kala kowannensu Yana waya hankali kwance.

Basu dawo gida ba sai 10 harda mintina lokacin Shima DD ya dawo suna parking motarsa na parking da Dan mamaki ya Kalli Zeenah Data fara fitowa motan kafin Bena da itace tayo driving ta fito daga ita se blue slim jeans da christian Dior free size shirt me tsayi.

Naseer Daya kawo DD a mota Shima fitowa yayi ahankali Yana Satan kallan Bena din wadda ta kasa kallansa DD da idanuwansa ke kanta ta Dan kalla jikinta na sanyi tayi masa sannu da dawowa ko amsata baiyiba ya wuce gaba Naseer na kokarin biyo bayansa ya datakar dashi da cewa yaje saida safe kawai.

Yana shiga palon Zeenah dake bayansa ta shigo ta wuce bedroom dinsu ta shige Bena na shigowa ta rufe kofar itama ta shige bedroom din.

Wanka sukai dukkaninsu sukai Shirin bacci take Zeenah ta fada gado se bacci Dayake ta rigata wanka.

Sallah ta fara ita kafin tayi wankan ta fito ta saka Riga da wando na bacci masu santsi gajeru ta hau gadon itama zata kashe wuta ta duba Bata shigo da ruwa ba Dan tana Shan ruwan dare sumtimes Dan haka ta sauko da qafafunta ta miqe tareda zira slippers ta fito ta nufi cikin Dan duhu sbd wutan koina a kashe lokacin 12 har ta Dan wuce da mintina.

Tana shiga kitchen ta Bude fridge ta dauko Daya jikinta na qwari sbd baccin Datake ji

Tana rufewa taji motsi bayanta ta juyo da Dan sauri daidai isowansa gurin fridge din Shima

ahankali yazo yana buqatan ruwan sanyin a kusa dashi Incase.

Da qarfi kirjinta ya doka da ganinsa sbd Bata taba tinanin Ganin nasa ba a lokacin gashi jikinsa ba kaya daga shi sai towel a qugunsa da kaman be dauru ba ana tabawa zai kunce da alama shi sai a time din yayi wanka.

 Dauke kallanta tayi ahankali daga Kansa sbd haske da kyan fatarsa tareda murdewan jikinsa da kullum yana geamin ya yasa bugun zuciyarta Dan tsananta.

Fuskarsa a Dan kame ya dakata Bai iso fridge din ba a hankali yace ta dauko masa biyu ta kawo masa.

Juyawa yayi ya fita

Tana ganin Hakan ta dauko ruwan da sauri ta biyo bayansa Dan Basa basai taje har cikin

bedroom dinsa ta Kai masa Dan haka da sauri sauri ta biyo bayansa ta cimmasa a Palo Yana daf da shigewa Jin tahowarta bayansa ya sakashi juyowa ahankali daidai ta iso Bata saka ran juyowan tasa ba kirjinsu yayi Wani irin haduwan da yasakashi loosing balance nasa a take yayi saurin dafa bango da ita a kirjinsa Dan haka itace jikin bangon shikuma yana Dafe da bangon har lokacin kirjinsu a manne.

Matse sosai yake da ita a bangon Yana kokarin dawo da balance dinsu itama Kuma tsananta bugawa kirjinta yayi har yanajin sama da qasan da Kirjinta sukeyi kan nasa kirjin.

Kasa motsi sukai dukkaninsu ta fizgo Wani boyayyan numfashinta dake Neman barin kirjinta da qarfi Wanda Hakan ya sakata kirjinta da babu bra yimasa Wani irin suka take tsikar jikinsa suka miqe ba zato ya Bude idanuwansa dasukai Wani iri take ya zuba mata tareda sake manneta da jikin bangon daqyar ya iya Bude baki cikin Wani Mayen sauti mara tashi ko kadan ya Dora bakinsa kan kunnenta Saida numfashinsa me dumi ya fara saukan mata ya furta

“Stop”

Saukan lips nasa kan fatan kunnenta da saukan muryarsa cikin tareda dumin numfashinsa ya sakata rikicewa gabaki Daya kirjinta ya sake Wani mummunan bugawan ta sake saka tsinin

kirjinta suka sokesa

Rintse idanuwansa yayi da qarfi tareda soka Kansa cikin wuyanta yayiwa qamshinta wata irin

shaqa hannuwansana zagaye qugunta take ta saki duka ruwan hannunta tana qanqame towel dinsa dataji Yana Neman kuncewa ya Fadi.

Chapter 58

58

Saukan hannunta kan towel dinsa ya sakashi dube idanuwansa dasukai nauyi ahankali yayi mata Wani irin Kallon kasala da Yana sake saka Kansa wuyanta ahankali fatar fuskansa na gogan fatan wuyanta zuwa kirjinta tana sake qanqamesa daga qugu.

Qamshinta Dayake shaqa ya saka idanuwansa qara nauyi Yana son janye kirjinta daga nasa dake Neman kashesa da zafin jiki Amma ya kasa motsawa sbd idan ya motsa a lakacin shi Kansa yasan towel din nasa zai iya kuncewa.

Yanda fuskansa ke gogan wuyanta ya saka jikinta mutuwa tayi shiru tsigan jikinta na tashi itama qamshinsa gabaki Daya na Jo Malone body wash dinsa ya cika mata iskar Datake shaqa a tsakiyansa gashi duk numfashinta Daya saiya daga kirjinta ya sake gogan nasa dakyau

Jin Yana Neman rasa Kansa gabaki Daya ya sakashi qarasa zagayota da hannuwansa ya manneta sosai da kirjinsa ta Yana rintse Ido ta yanda bazata ringa numfashi tana gogansa ba zafin jikinsa na tsanantuwa.

Tafin hannunta Daya ta dago ta Dora tsakiyan bayansa zata Zame dayan hannun na qugunsa Dafe da towel din datake tsananin tsoron ya Fadi.

Saukan tafin hannunta bayansa da babu kaya ajiki ya sanyashi qara cusa Kai cikin wuyanta ya sake Bude baki da muryan data sata qanqamesa da duka hannuwanta biyu cikin kunnenta yace

“Don’t do that again”

Batasan lokacinda ta lumshe idanuwanta ta ba tana langabar da kanta gefe sbd dayan gefen Dayake shinshina wuyanta zuwa kirjinta idanuwansa a rufe.

Yanda yake shinshinata Yana hada fatarsa da tata yasa dukkaninsu mantawa da su waye su din dakuma inda suke tsaye suna aikin.

Rigarta data yaye hannunsa ya sauka kan cikinta ta ja numfashinta Daya so barinta da qarfi tareda Bude idanuwanta ahankali daidai Shima ya Bude nasa idanuwan suka Kalli juna tayi qasa da nata idanuwan tana shikuma ahankali ya sake Kai bakinsa kunnenta cikin sauti mara fita sosai yace

“Wannan ruwan ya huce Ina buqatan Wanda yafi zama colder”

Yana fadan Hakan ya zare hannunsa daga fatar cikinta ahankali tana rintse idanuwanta sbd yanda yake dauke hannun.

Juyawa tayi da sauri kaman zata Fadi tabar gurin tana Isa kitchen hannuwanta na Dan rawa ta dauko ruwan sanyin sosai ko nata Bata tsaya dauka ba ta fito baya palon Dan haka dakinsa ta Isa Kai tsaye tayi knocking ta shiga baya dakin Yana toilet ta ajiye ruwan da sauri ta fito ta koma dakinsu ta fada toilet itama.

Fuskarta dake Dan tsatsafo gumi ta wanke tana sauke numfashi ahankali ahankali har ta samu ta Dan dawo daidai ta fito jiki ba qwari tahau gadon ta kwanta ruwan ma Bata daukoba hakanan taji ta Dena Jin kishirwan Dan bazata iya sake fita ba.

Ta Dan jima kafin bacci ya dauketa Bata farka ba sai Asuba.

Tare sukai sallah da Zeenah suna gamawa Zeenah ta koma ta kwanta ita Kuma akwai aikin kamfanin kaantes da zatai Wanda Fahad ya tura mata Dan haka shi ta fito Palo ta zauna tahau Yi cikin pink kaya masu Dan kauri sbd sanyi da safa a qafanta.

Har kusan 7 na safe tana Aikin tana Kiran Fahad din a Wani abin.

8:30 Zeenah ta tashi ta fito ganin Bena na aikin ya sakata Yi musu breakfast da kanta gasashen chocolate and coconut bread da fries tayi musu se hot milk tea.

Shima yau yanada meeting na qarshe da zaiyi Dan haka 9 ya fito sanye cikin native wear yau dinma na blue cashmere da wula kaman Wanda yau ne daurin aurensa da matar Dayake so Dan Kansa da raayinsa bana wainda yake aure na umarni da cika burin iyayeba.

Waya takeyi da Fahad Koda ya fito shigar jikinta ta kayan loro Piana ya kalla kaman Amnah Takoma ga tea da Zeenah da miqo mata da chocolate coconut bread takeci ahankali tana cigaba da amsa wayar idanuwanta na kan laptop dake kan qafafunta.

Qamshin Caron poivre Daya fara gauraya palon a hankali ya sakata kasa dagowa tana hadiye tea din bakinta a hankali sbd Jin idanuwansa sun sauka akanta.

Zeenah ce ta washe baki cikin kulawa tayi masa Good morning ya Tako ahankali Yana amsawa.

Bena na ganin ya tinkaro tayi saurin ajiye cup din hannunta ahankali tareda Dan dagowa tana kasa kallansa tace “good morning” ahankali itama.

Yana isowa Bai amsaba cup din data ajiye na tea dinta ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha kadan ya sake Sha har so uku kafin ya ajiye ya amsa gaisuwan Shima ahankali ya juya ya fice Zeenah data kasa gasgata Abinda yayi din ta miqe ta biyo bayansa suka fice tare suna magana.

Suna ficewa Bena ta dago ahankali ta zubawa cup din idanuwanta tanajin jikinta na mutuwa takai hannu ahankali ta dauki cup din itama takai bakinta taci gaba da Shan tea din zuciyarta na sanyi.

Koda Zeenah ta dawo Bena har lokacin Bata gama Shan tea din ba sbd gabaki Daya kuzarinta takejin kaman ta rasa.

Zeenah na zuwa taso maganar Abinda DD din yayi Amma Bena ta fuske tana basarwa.

Qarasa aikinta tayi guraren 11 tukuna ta miqe Takoma daki tayi wanka ta kwanta bacci sbd tana buqatansa Kona mintina arbain ne.

Sai Data tashi bacci tayi girkin Rana Takoma tayi sallah tukuna tayi wanka ta fita itama.

Dukkaninsu su ukun kusan lokaci Daya suka dawo Zeenah ce tafara dawowa kafin shi tukuna ita daga baya.

Kowannensu wanka yayi yayi sallar laasar suka fito dining gabaki dayansu suka ci abinci babu Wanda ya iya kallan Wani tsakanin shi da ita har aka gama kowa ya tashi.

Bayan magrib shi da Zeenah suka fita Basu dawo gidan ba sai after 12 lokacin tayi bacci Dan haka Saida safe na tasan time dasuka dawo.

Dayake ya gama Abinda ya kawosa sai ya fara Shirin kowama A Daren ranar da zai tafi ya bawa Zeenah card dinsa Daya suka fita shopping sukaiwa kudi wulaqanci haka yasa akaiwa Amnah siyayyan abubuwan da ma wasu tanadasu sunfi nawa duk baa fara amfani dasu ban.

Bayan sun dawo sunyi wanka sun huta sunci abinci suna gamawa Amnah ta kira daddynta tace sai taga mummynta sunata Kiran wayarta Bata dauka dayake tabar wayar daki.

Dan dagowa yayi da idanuwansa yayiwa Bena dake Jin Abinda Amnah ke fada Kallo Daya itama shi ta saci Kallo daidai time din.

Idanuwansa rudata sukeyi Dan haka ta janye kallanta tareda qarasa shanye ruwan dake glass cup din hannunta ta jiye.

Kallan Daya sake mata ya sata tasowa suka dawo Palo suna zaunawa kan kujera Daya tana kokarin Hana bugawan kirjinta fita sbd Amnah dake kallansu hakama Zeenah.

Qaqalo murmushi tayi cikin kulawa sosai da kauna tace

“Baby me kike Jira bakiyi bacci ba haryanzu? Akwai school gobe fa”

Dariya Amnah tayi tana cewa

“Bazan iya bacci da wuri ba yau sbd murna my daddy is coming back tomorrow, right daddy?

Wani qayataccen murmushin da Bena Bata taba ganinsa yayi ba ya sake a natse

Saura kiris ta kasa dauke kallanta daga Kansa ta samu ta dauke idanuwanta ta maidawa kan Amnah.

Cikin nutsuwa da kulawa hankali kwance yace

“Gobe Inshallah Daddynki ne zai dauko angel dinsa from school.”

Tsalle tafara tana murna da cewa

“Daddy na matsu gobe yayi,

Mommy please ki dawo tareda Daddy I miss you both inason na zauna tareda mommy na da Daddy na kaman sauran yara kaman,

Kaji daddy? Please bring mommy with you.

Ahankali ya juyo ya Kalli Bena wadda ta kasa cewa komai.

Kallan Dayake mata ya sakata yar rudewa tana Hana kanta bayyanarda rudewan ta Dan basar ta hanyar kallan Amnah din tace

“Baby ni zan dawo daga baya ba na fada Miki nakusa dawowa ba?”

Bata fuska Amnah tayi tareda marairaicewa tana kallansu su duka biyun idanuwanta na cikowa da hawaye tace

“Ba ance matan daddy na ta dawo yau Nigeria ba naji Umme na waya tana fada nidai Daddy mommy na ce kawai zata dawo gida”

Tsit sukai dukkaninsu harda Zeenah data zauna lokacin

Benazir kuwa hannuwanta ne suka Dan dauki rawa tayi saurin boyewa ahankali kada ya Gani zuciyarta na harbawa da qarfi.

Shi kuwa Bena din ya Dan kalla kafin ya Maida kallansa kan Amnah yace

“Ok Angel je ki kwanta da wuri sbd gobe ki samu karfin yiwa Daddy oyoyo,ok?”

Gyada Kai tayi ahankali tareda kallan Bena tace “goodnight mommy”

Ahankali Bena ta furta “goodnight baby…..Bata qarasa kira ya shigo wayarsa dauke da sunan SBB baro baro ajiki.

Miqewa Bena tayi ahankali tareda barin gurin ta koma dining Dan tattarawa taga Zeenah tini ta gyara komai Dan haka Kai tsaye bedroom dinsu ta wuce batareda ta juyo ba bayan tanajin idanuwansa akanta.

Bai dauki wayar ba tana katsewa Kiran ummensa na shigowa a natse ya dauka cikin nutsuwa yace

“Hello Umme barka da dare”

“Barka” ta amsa tareda cewa

“Safnah ta sauka a Lagos yau itama gobe zata qarasa porthacort inaga yakamata ka wuce can daga Nan sbd daddynta ya kira su dd babba maganar saka ranar biki da tarewanta.

Kashe wayarsa yayi bayan yacewa ummen to kawai sbd baisan me zai fada ba akan aurenda har aransa ya manta dashi.

Barin palon yayi Zeenah ma miqewa tayi ta nufi bedroom dinsu tana shiga Kiran Safnah na shigowa wayarta sbd DD Bai dauki nata ba Kuma ance suna tare.

Chapter 59

**********

Zaunawa Zeenah tayi kan couch Ahankali tana Dan kallan Bena datake zaune kan gado tana duba wayarta Dan kawar da Abinda takejin Yana Neman saka zuciyarta nauyi.

Wayar safnah Zeenah ta dauka ahankali tareda miqewa ta nufi Kofa sbd taji bazata iya daga wayan Safnah din gaban Bena ba.

Palo ta dawo ta zauna ahankali tareda daga wayan.

Cikin sautin nutsuwa da bayyanarda damuwa da rashin hakuri Safnah tace

“Ina buqatan address na gidan D zanzo Ina buqatan ganinsa I’ve been calling Him Amma baya dagawa.”

Cikin nutsuwa Zeenah tace

“Bamu gaisa ba ai tukuna ko?”

Qaramin tsoki Safnah ta sake a boye kafin a fili ta Dan sauke numfashi Mai sanyi tana sassauta dacin zuciyarta tace

“Sorry Sis na manta ne sbd hankalina Yana kan D gaba Daya Ina san ganinsa sosai kafin na bar Lagos din gobe,ya kike?

Ya service?

Nima inshallah next year Dani zaayi.”

“Fine Alhmdllh,barka da dawowa to.” Zeenah ta fada tana Jin zuciyarta batajin Safnah da yayanta tafi jinta a ‘yar uwarta kawai.

Sake tambayarta address Safnah tayi Zeenah din datasan bazai yiyuba ta Bata address na Nan gidan bayan Bena na gidan Dan haka ta Zame taqi fada mata qarshe ma ta sanar da ita gobe zai tafi so babu buqatan sanin address Kuma ‘dayan matarsa na gidan.

Kalaman Zeenah sun sosa zuciyar Safnah sosai Dan haka cikin baqin ciki da radadin zuciya ta daure sukai sallama kawai tayi jifa da wayarta tana Jin kanta na daukan zafin wai matar D din na gidansa tareda shi.

Tsoki taja Mai qarfi tareda daukan wayarta ta fasa kwana garin take tasa Akai mata booking ticket na tafiya cikin Daren.

*Bena kuwa bayan ficewan Zeenah daga dakin numfashi ta sauke ahankali sbd ta Dade da mantawa ba ita kadai bace matarda aka aurowa DD ba,

So Daya taji zancen ta sani Kuma tin daga ita har waccan din babu wadda ke gabansa yasaka ita kanta mantawa takeyi da akwai aurensa akanta bare wadda Baa Gani.

Dawowan matar tasa na nufin zai zama magidancin gidansa Dan haka dole tana buqatan kame kanta tinda waccan yar uwarsa ce ta jini ita kuwa tasani darajan Amnah takeci wadda itama duk ranarda ya gano ba itace ta haifeta ba tsanarta zaiyi ita.

Tashi tayi tashiga toilet tayo Abinda zatai ta fito ta shirya cikin kayan bacci masu Dan kauri sbd sanyi tayi kwanciyarta tareda rufe idanuwanta ahankali tana jiran bacci.

Zeenah kuwa bayan gama waya da Safnah da DD ta tsaya palon sukai magana sama sama akan yawan yawonsu da Daren dasuke Kaiwa a waje yace su Dena.

Duk da Bai fito ya fada ba tasan Kila akan Bena ya fada Hakan sbd ita yasan ta Saba a can foreign countries tana dare sosai a waje bakuma komai bane tinda ko saurayi batada shi bare ayi tinanin akwai Abinda yake shiga tsakaninsu.

Bayan sunyi sallama ta shige Shima ya Danyi mintina yana kallan kofan bedroom din nasu kafin ya Dan dauke Kai ya miqe ya shige.

Wanka ya tube yayi kafin ya shirya cikin white Balmain pyjamas ya jikinsa na tashin sanyin qamshinsa ya Kwanta.

Washe gari flight din 10 zai bi Dan haka 8 ya fito a shirye cikin D&G black shirt da Balmain slim jeans sai Fcap din flexfit me tsadan gaske.

Zeenah ce ta hada masa simple light breakfast ya zauna Yana cikin ci ahankali cikin nutsuwan

Bena ta Bude kofan bedroom dinsu ta fito fuskarta fresh sanye cikin kayan baccinta Riga da wando da suka bayyanarda shafewan cikinta kanta ko hula babu slippers ne kawai a qafarta ta nufo dining din cinyoyinta na daukan ido sbd lafiyan brown skin dinta.

Saida ta iso daf da dining din idanuwanta suka gansa zaune Yana jifanta da Wani irin Kallon da mayun idanuwansa.

Cak ta tsaya sbd duka tinaninta yaje akan ya Riga ya tafi.

Kasa juyawa tayi ta Dan dago ahankali ta Bude baki tace

“Good morning”

Sai Daya dago yayi mata kallan seconds kafin ya Dan dauke kallansa akanta ya amsa Yana cigaba da Shan tea dinsa.

Kokarin juyawa takeyi tabar gurin taji muryansa a natse yace

“Zaki bini zuwa gida yau din….

Dakatawa tayi daga tafiyan datakeyi ta juyo ahankali cikin mamaki da sanyi tace

“Yau??

Tasowa yayi daga dining din sbd ya gama ya ratsata ya wuce qamshinta na Dan shiga hancinsa ya nufi kujera ya zauna Yana duba agogon bighead Bottega veneta dake daure a hannunsa.

Rasa abin fada Bena tayi sbd mamaki da fargaba ga Kuma taro me mahimmanci da dd babba ya sakata halarta yau a matsayin me wakiltan department na account din kamfanin  kaantes ita da Fahad Yana Nan zuwa Lagos din yau ma,

Yanzu gashi Daddyn Amnah na fadan haka Daman tasan zai iya faruwa Hakan tinda Amnah tayi maganar tanason zuwanta.

Cikin sanyi ta Tako ta iso gurinsa tana sake Dan shiga sanyin jiki a natse tace

“Akwai serious business meeting na kaantes da zanje tareda Fahad Yana hanya and gobe ne Ina buqatan tsayawa please.”

Ambatan sunan Fahad datai ya sakasa Dan waiwayowa ya Kalli gefenta Kai tsaye yace

“Flight na 10 zamu bi.”

Yana fadan Hakan ya miqe yayi bedroom dinsa ya shige.

Zeenah dake zaune tana jinsu kallan Bena tayi cikin kulawa tace

“Kije ki sake rokansa kina buqatan tsawa gaskia wannan meeting din,

Babban opportunity ne karki wasa da Hakan and dd babba zaiyi fushi idan kika koma batareda attending haduwan ba,

Kije ki sake Basa hakuri dole Zaki tsaya gaskia.”

Jin tayi jikinta ya sake mutuwa sosai Sam itama Bata fatan ta tafi tabar wannan aikin datai kusan sati tana wuni da Raba dare aikinsa.

Numfashi ta sauke ahankali tareda nufan dakin tana Isa tayi knocking Ahankali.

Jin shiru ya sakata Bude kofar da hannunta ta tura ta shiga a hankali

Yana zaune Yana amsa waya ahankali cikin rashin hayaniya

Ganinta ya sakasa sallama da Safnah din a hankali tareda ajiye wayar ita kuwa Jin tayi kirjinta yayi nauyi tana Neman kasa mgn sbd fahimtar da matarsa yake wayan.

Boyayyan numfashi ta sauke ahankali tareda daidaita kanta ta dago Bata kallesaba ta fara rokansa akan yabarta din.

Kame fuska yayi sbd baya buqatan Jin zancen nata.

Ganin yaqi ko kallanta ya sakata sake qarasowa daf da shi zatai magana ya dago ya zuba mata fararen idanuwansa

Take ta rude tafara kokarin magana wayarsa tayi ringing.

A tare suka duba wayan sunan Nass ta Gani ta fahimci Naseer ne Kuma tafiyan zasuyi kenan.

Daukan wayar yayi ya Dora a kunnensa cikin nutsuwa yace ok kawai ya kashe wayan ya ajiye.

Miqewa yayi zai wuceta take idanuwanta sukai narai narai sai hawayen data manta Yaya ake tsiyayosu ma.

Dakatawa yayi tareda kallan hawayen nata ahankali ya Kalli fuskanta datai qasa da Kai.

“Meye wannan?

Ya fada Yana kallan hawayenta.

“Shi wannan din Kuka ne ko meye?”

Shiru tayi takasa dagowa

Ajiyan zuciya ya sauke me sanyi kafin ya rabata ya fice daga dakin a sukwane ta biyo bayansa ta fito itama

Yana fitowa Palo ya tadda Naseer ya shigo Dan Haka ya juya ahankali ya koma Dan dakatar da ita daga fitowan sbd kayan jikinta

Yana dowowa tana Sako Kai Dan haka sukai Wani irin hadewan data sakata yin baya ya riqota zuwa jikin bangon kofan Yana zagaye da ita ahankali.

Numfashi me Dan qargi ta hau saukewa tareda kasa dagowa sbd yanayinda suke.

Jin jikinsu manne da juna ya sanyata Bude bakin kasalance batareda ta dago ba ta furta “please kabarni na tsaya”

Qamshin mouthwash dinta ne ya shiga hancinsa tareda numfashinta sbd kusancinsu Dan haka ya juyo da idanuwansa ya Kalli bakin nata tana sake motsasa ahankali gurin rokansa.

Zare hannuwansa yayi daga jikinta tareda janyewa sbd zafin dayaji Yana shigarsa.

Bai waiwayo ba ya gyada mata Kai kawai tareda ficewa daga dakin.

Kafin ta sauke numfashi da ajiyan zuciya ta fito tini suka fice shi da Naseer Dan haka Koda ta fito sun fice.

Ajiyan zuciya da numfashi ta sake saukewa tana godewa Allah cikin ranta sbd babu Abinda yakeda mahimmanci agunta yanxu ta bangaren cimma buri irin kammala komai ta koma ta tsayu da qafafunta tareda taka matakin nasarar da zata Siya yancin mahaifiyarta da kudinta ta dawo hannunta.

Breakfast tayi sama sama sbd Jin duk jikinta yayi sanyi Kuma.

Tana gamawa ta shige wanka ta shirya ta fita Aiki sbd yanzu kam bazata ringa fashi ba a yanda takeso tinda sun kusa gamawa su tattara su koma gida.

Chapter 61

60

Dulkaninsu ranar sal yamma suka dawo kowa a

gajiye Dan haka order abinci sukal Koda aka kano

sunyi wank da salloli abincin kawai sukaci Bena ta

fara Wani aikin a laptop Zeenah ma kusan alkin

tafara du da Rabi wayoyi ne takeyi.

Sal dare sosai Bena ta gama taje ta kwanta kanta na

tananin chwo,

Washe gari da kanta tal

I dauko Fahad

daga airport Dayake sun latti Kal tsaye gurin meeting

din suka wuce,

Duk yanda Bana take tinanin lamarin ya wuce Nan

sbd Manyan mutane ne da lyakacinta jinsu da

ganinsu a media,

80

Su uku ne kawai mata Kuma ita Daya ce yarinya Mai

-sauran lokaci Amma sauran matan duka manyan

/mata he da shekarunsu suka Dan ja sai wadda batai

shekarun nasu ba ita Kuma zata girmeta sosai.

Hakama a kawai fararen fata har guda hudu Suma

Wanda dagani daga wata qasar suka zo.

Asalin turanci da wayewa tareda zurfafa a harkan

businesses da juya kudi ne yake tashi a gurin.

Da farko da zatai presenting nata bayanin rudewa

taso Yi Amma qarfin gwiwan da dd babba yake Bata

kullum tareda Dora duka hopes dinsa a kanta akan

cewan zata zamewa business din kaante lucky

charm inshallah akan sa’a da nasarorinsu zata ninka

musu yake fata.

Hakan ne ya sakata sauke numfashi tareda ajiyan

zuciya cikin nutsuwa da nata fresh ilimin da fasaha ta

fara Koro bayanai da nata turancin da itama ta qware

cikinsa.

17

80

Scanned with CamScanner

RA

Kai tsaye suka fara accepting ideas nata tareda

sabuwar fasahar data kawo harma da fashewan wata

•sabuwar hányar da kusan zasuce ta course din datai

‘ne Kuma tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.

Wannan shine Karo na uku a rayuwar Kaantes da

suka samu nasarar janyo manyan Tycoons,

billionaires da Wainda baa taba tsammani ba shigo

da mutum 9 a lokaci daya su zama shareholders a

cikin kaantes.

Dd babba ne da Kansa mutum na farko Daya taba

Hakan sai DD da Kansa Daya shigo musu da wasu

shareholders daga nasa business din sai Kuma Bena

yanzu,

Bilal na ya taba wanna nasarar Amma nasa mutum

8 ne Dan haka ana gama Fahad ne yayi presenting

sauran bayanin in documents aka garasa meeting

din suka fito manyan motaci da securities sai tsaro

na musamman ake Bawa gurin har kowannensu ya

fice daga gurin,

7:12

60

9

RA

Lokacinda dd babba ya fara samun Tabarin daga

media ne da Akai musu hotúna bayan fitowarsu tini

aka fara yada zancén na kaantes sun sake samun

damar qwatnushe manyan Tycoons a matsayin yan

‘saka hannun jarinsu.

Farin ciki yayi mara sosai hakama dad kaante farin

ciki ne fal a ransa sbd dole zaa ce matar ‘dansa ce.

Dinner sukai having ita da Fahad da Zeenah ta farin

cikin a Wani muhaukacin luxury restaurant suna can

dai 12 Saura suka baro suka ajiye Fahad tsadaddan

hotel din Daya sauka suka wuce gida.

Wanka kawai Bena tay Dayake sunyi sallah ta fada

gado ko wayarta Bata iya kunnawa ba tin bayan

wayarta da dd babba da Annenta dasuka gaisa,

Washe gari Bata iya fita ba sbd bacci da gajiyan

dararrakun data ta Hana kanta bacci sbal wannan

aikin Dan haka Zeenah ce taje takai Fahad airport

daga can ta wuce Aiki,

“Itama sai 11 ta farka tayi breakfast ta shirya ta wuce

aikin.

Bayan komawar Fahad take aka celebrating wanann

babban sabuwar nasarar data gara daga daraja da

girma tareda habbakar arzikin kaantes da bayama

faduwa,

Bena Bata Nan Amma haka aka ringa kiranta anai

mata barka tareda mata adduar fatan nasara me

dorewa.

Dawowanta kawai ake Jira ta fara aikinta me matsayi

babba a Kaantes

Shi Kansa Fahad yanajin Dadin Aiki da ita sosai

hakama dad kaante yanzu yasan zai samu Wanda zai

maye masa gurbin Bilal a bangaren Aiki Mai cikeda

nasarori sbd tin bayan rasuwar Bilal basu samu

Wanda ya cike musu gurbinsa ba a fagen nasara shi

DD Yana nasa business din daban baya cikin family

business bare ya kawo musu tarin nasa nasarorin da

maye masa gurbin Bilal a bangaren Alki Mal cikeda

nasaröri sbd tin bayan rasuwar Bilal basu samu

Wanda ya cike musu gurbinsa ba a fagen nasara shi

DD Yana ‘nasa business din daban baya cikin family

/büsiness bare ya kawo musu tarin nasa nasarorin da

Allah yay masa baiwa,

******Bayan sati uku da wannan samun Abinda

akeso din suka kammala service nasu Akai duk

abubuwan da zaayi suka fara Shirin dawowa.

Yau gabaki Daya baa gida suka wuni ba sai yamma

suka daw kowannensu a gajiye Dan haka wanka

sukai da sallah sai alokacin sukaji sun sake.

Snacks sukaci sbd ba sosal suke Jin yunwa ba

Suna zaune a Palo suna fira suna taba wayoyinsu

wayan video call din Amnah ya shigo wayan Bena.

Cikin farin ciki ta dauka fuskarta cike da murmushi

saidai ca ta tsaya tana Neman rudewa da Abinda

Cikin farin ciki ta dauka fuskarta ciké da murmushi

saidai cak ta tsaya tana Neman rudewa da Abinda

tayi niyar fada sbd ‘ganin Amnah din jikin daddynta

sanye da jersey pyjamas na Ralph Lauren navy blue

fuskánsa da skin dinsa sun qara haske sosai kaman

Wanda tinda yakoma baya fita hutawa yakeyi,

Qafansa Daya na kan Daya Amnah na jikinsa kwance

rige da iPad din.

Neman gagara iya magana takeyi Amma Amnah ta

kira sunanta tana cewa

“Mummy bakice komai ba fa”

Dan numfashi ta sauke a boye tareda Dan sale

murmushi Mai sanyi tana cewa

“Kema baki gaida mummy ba shiyasa”

Dariya Amnah din tayi irin ta Yara  tace *Ok ok sorry” datse Kiran tayi ta sake saka Wani

Bena din na dauka tace

“Mummy Ina Wuni?”

Wani murmushin me sanyi Bena ta sake tana

amsawa cikin kulawa zatai magana Amnah ta Riga da

cewa

“Mummy kema baki gaida Daddy ba”

Tsit Bena tayi tareda kasa kallan screen din wayarta

std Jin mayun idanuwansa akanta duk da Bai furta

komaiba tinda Kiran na Amnah da mummynta ne

babu shigarsa aciki.

Maganar Amnah din ta sakasa juyowa ya Kalli Bena

din itama Jin idanuwansa ya sakata Dan hadiye

Maganar Amnah din ta sakasa juyowa ya Kalli Bena

din itama Jin idanuwansa ya sakata Dan hadiye

numfashi ahankali ta dago ta kallesa kadan cikin

“sanyl tace

“Ina wuni?barka da dare”

Ahankali ya Bude baki ya amsa yana Dan dauke

idanuwansa daga kan iPad din sbd singlet ce jikin

Bena din blush pink ta kwanta jikinta sbd taushi da

tsadanta Kuma da alama babu bra jikinta iya singlet

dince kawai sbd yanda kirjinta shape dinsu yake

nunawa sosai sabanin idan akwai bra bazasu nuna

sosai din ba.

Ita kanta batai tsammanin Yana tareda Amnah ba da

bazata daga Kiran ba saita sakawa jikinta Wani abin.

Surutu Amnah ke mata tana amsawa a Dan kunyace

sama sama sbd duk ta motsa babu Abinda yake sake

bayyana kaman shape din kirjinta dasuke sakasa

dauke nasa idanuwan Shima.

Surutu ‘Ämnah ke mata tana amsawa a Dan kunyace

sama sama sbd duk ta mots babu Àbinda yake sake

bayyana kaman shape din kirjinta dasuke sakasa

duke nasa idanuwian Shima,

Cikin surutun Amnah tace

“Mummy kina dawowa karki koma gida gurinsu dd

babba da Umme ki dawo Nan ki zauna damu da

daddy na kullum mu zauna tare.”

Shiru Bena tayi tareda dagowa kadan ta Dan kallesa

shi kuwa idanuwansa ya zuba mata Yana Jin Abinda

Amnah ta fada Yana jiran amsarta.

“Kinji mummy?-

Murmushi ta sake tace

“Akwai school gobe ki kwanta idan nadawo sal muyi

maganar,

Ki kula kinji Rabin ran mummynta,

I love you, goodnight.”

Dagowa tayl ta kall

wansa na

lokacin Yana sake rud

ta furta “goodnight*’ ta kashe wayar ti

sauke ajlyar zuciya a hankall

Tana kashe wayar Wani murmushin gefen baki ya

sake ahankali sod gain yanda ta rude da maganar

Amnah.

Shi Kansa baisan Amnah zata furta Hakan ba Dan

haka zancen ya Dan sakashi murmushin gain tashin

Shi Kansa baisan Amnah zata furta Hakan ba Dan

haka zancen ya Dan sakashi murmushin gain tashin

“hankalin da zancen kawai ya sakata,

Daga lokacin Amnah zata buqaci Hakan daga garesa

babu Wanda ya Isa ya hanasa Bata Abinda takeson

Dan haka kawai Mummy nata tayi fatan kada Angel

dinsa tace masa tanason su dawo gidansa a ranar ko

kwana daya Bena ba zatai a Lagos ba ko kaantes.

*****Bayan kwana biyu da maganarta da wannan

suka tattaro suka dawo gida yayi daidai da saka

lokacin bikin Daddy Amnah din da matarsa wata

biyu masu zuwa kaman yanda mahaifiyarta ta bugata

Dan samun Daman shirinsu Daya kamacesu,

Bayan dawowarta ta tarar da sabuwar rayuwar

Datake jiranta ta daukaka da cigaban da Bata taba

tsammata ba,

Dd babba ya zama Wani irin gata da zuciyarta Dan

kuwa yanda take jinsa a duniyarta kat yanzu daga

12:49

al LTE

80

RA

Dd babba ya zama Wani irin gata da zuciyarta Dan

kuwa yanda take jinsa a duniyarta kaf yanzu daga

Anne sai Amnah dashi ne wainda takejin zata iya

komai akansu hakama bazata iyaba idan babu su

din.

Shi Kansa dd babba Bai taba tinanin akwai ranar da

zai kaunaci Wani gauna me garfi ba irin wadda

yakewa Bena bayan Dawood a cikin jikokinsa.

Cikin tarin nasara ta karbi babban matsayinta na fara

Aiki a Kaantes tareda sabuwar tsadaddiyar motar

data saka lissafin Ababa kuncewa Dan haka ya fara

birkice mata akan ko kudi kokuma Annenta Takoma

inda ta fito.

Zeenah ma ta fara Aiki da babban matsayi ita Kuma a

DDs sunan babban kamfanin DD kenan.

Fara aikinta yazo mata da nasarori Dan kuwa Aiki

takeyi da gaske cikin awarewa da wayewa tareda

nutsuwa,

12:50

60

Fara aikinta yazo mata da nasarori Dan kuwa Aiki

takeyi da gaske cikin qwarewa da wäyewa tareda

nutsuwa,

RA

Acikin qanqanin lokaci ta qara daga darajar kaantes

Dan haka ta tabbata Nasarar kaantes da dd babba

yake kiranta.

Dad kaante sosai yake Yaba mata Shima sbd

shigewarta kaantes ana samun yanda akeso daman

babban burin kaantes su zama sune a sama babu

tamikarsu bare Daman babu me ja dasu sai DDs

Shima Bada baqin cikin da Company din sbd tamka

nasu ne tinda na DD dinsu ne.

****Tinda ta dawo aka saka lokacin tarewan matarsa

Bata bari ko a hanya sun haduwa kullum office take

fita tayi busy sosai gidansu ma so biyu Ababa ya bari

taga Annenta Shima Sai data Basa 100k a duk

kowane ganin,

**Daga office Kai tsaye shahararren DDs company ta

biya Dan daukan Zeenah su koma gida tare bd yau

drivor yakaita Bata fita da mota ba Kuma yanzu Bata

bugatan yazo ya dauketa shiyasa takira Ben akan

‘idlan ta tashi ta biyo ta dauketa su wuce gide tare.

Suna baro DDs wayar Zeenah tayi ringing tana

dubawa taga D dinne Dan haka a tsanake ta dauka.

“Idan ki tashi Aiki kizo ki tafi da Amnah gida kalina na

ciwo zan huta

Kashe wayar yayi ita Kuma ta juyo ta Kalli Bena dake

driving tana waya a natse.

Kallan da Zeenah ke mata ya sakata sallama ta kashe

wayar tana cewa

“Yaya dai?

D yace na biya na dauki Amnah bayajin Dadi,

Ajiyar zuciya Bena ta sauke ahankali sbd itama

Daman tayi kewan ‘yarta kwana Biyun Dan haka tayi

parking Zeenah datasan gidan nasa ta karbi tugin

zuciyarta na Dan tsinkewa sbd batasan haduwa

dashi,

Chapter 61

******

Tinda suka kama hanyar zuwa gidan nasa tayi shiru Bata sake magana ba saidai idan Zeenah tayi mata ta Dan amsa ahankali tana Hana zuciyarsa bugawa ba daidaiba.

Tsaro da tsarin anguwar ya saka Bena mamakin wainda suke rayuwa a cikinta,

Main gate na shiga gidajensu DD din sai ka nuna Id card naka anshigar da sunanka,

Sunan kaantes dake qarshen sunayensu ya saka securities fahimtar gidan DD kaante suka zo Dan haka aka Bude musu suka wuce.

Daga ka shigo baka horn har saika fita Dan haka ahankali suke tafiya da motan har suka Isa gate na gidan DD Shima akwai security Daya agurin ya Bude musu gate suka shigo madaidaiciyan harabar gidan sukai parking.

Fitowa Zeenah tayi tana kallan Bena da batai niyar fitowa ba tace

“Waye zai iya rarraso baby Amnah ta yarda ta bar daddynta idan bake din ba,kinsan sarai bazata yarda tabar daddynta ba saida dubaru.

Ajiyan zuciya ta Dan sauke tareda ajiye wayarta cikin motar ta Bude ta ziro qafafunta ta fito tareda rufe motan suka nufi ciki Kai tsaye bugun zuciyarta na Dan qaruwa tareda Jin rashin sakewa.

Gioconda door din shiga main sitting room na gidan suka Bude Kai tsaye suka shigo sbd sanin password dinsa na shiga da Zeenah tayi.

Zeenah din ce a gaba kafin Bena wadda sanyin AC da qamshinsa da babu inda babusa a gidan nasa ya sata Dan lumshe rintse idanuwanta tana budesu ahankali.

Komai na rayuwarsa daban yake tin daga kan inda yake rayuwarsa da yanda yake gudanar da ita,

Palonsa babu Abinda yakeda wata kalan bayan fari milk da gold.

Bayason kaloli a komai shiyasa ko kayansa daga black sai fari sai Kuma navy blue Shima kalan Dan tanada duhu ne.

Baiji shigowansu ba sbd Yana can master bedroom dinsa a kwance Amnah Kuma tana palon cikin bedroom dinsa tana rubuce rubuce da kallan cartoon.

Waya Zeenah ta Ciro ta kirasa tana nufar kitchen dinsa Dan Shan ruwa.

A natse cikin sanyi ya dauka yaji ta iso yace ta dauko Amnah din kawai su wuce.

Har cikin palonsa ta Isa tareda Bena

Amnah na ganinsa ta taso da gudu ta fada jikin mamanta tana Kiran sunanta cikin farin ciki sosai.

Itama sake murmushi tayi cikin farin ciki tana daukanta jikinta tace

“Ohhh I miss my baby so much, please kizo muje gida daukanki nazo Yi”

Zaunar da Mummyn tata tayi ta hau jikinta tana taba dogon hancinta tace

“Aa mummy bazanje ba kema bazaki tafi ba Daddyna bayada lafiya ki zauna mu kula dashi idan ya warke saimu koma gurin su Umme tare,

Aunt Z Takoma ita Daya”

Dariya Zeenah tayi tana Jan hancin Amnah din itama tace

“Amnah din Aunt z ta girma tasan yakamata a kula da daddynta bayada lfy.”

Bena kuwa Wani murmushin ta qaqalo tana cewa

“Daddynki bayason hayaniyan kowa shiyasa zamu tafi gidan idan yaji sauki sai akula dashi din,.oya tashi muje gida Umme na jiranki Kuma ga Arabic uncle dinki nata zuwa bakyanan,kinason karatun Arabi naki ya Dena gudu?

Girgiza Kai tayi tana Bata fuska tace

“Banason ya Dena gudu Amma mummy nidai banason Abar Daddy shi Daya dazu yayi Amai fa Kuma Uncle Naseer ya kawo doctor yayi masa allura,

Cikowa idanuwanta sukai da hawaye taci gaba da cewa

“Nidai mummy to ki tsaya anan naje ayimun karatun Arabic Dina yau da gobe saina dawo ke ki tafi”

Shiru Bena tayi tareda matse fuska tace

“Banason Jin kowane magana tashi mu tafi idan na sake Jin maganar Wani ya tafi Wani ya jira I will slap your mouth.”

Fashewa Amnah tayi da kuka Wanda ya saka Zeenah janyota jikinta tana kallan Bena tace

“Meye Hakan?

Gaskia ta fada idan har baida lafiya haka sosai kaman yanda ta fada Wani zai tsaya tareda shi gaskia and it has to be you sbd ita almost 5 days Bata gida karatunta Yana rawa.

Kukan Amnah keyi sosai tareda zarewa daga jikin Zeenah tayi hanyar dakin daddynta da gudu ta shige tana qarawa kukanta qarfi.

Numfashi me zafi Bena ta sauke ranta na Dan Baci da yanda suka lalata ‘yar tasu Amma Kuma bazasu iya hanata Abinda takeso ba koyaushe daga su iyayenta musamman Daddyn nata har kakanninta su Umme shi dad kaante ma Badan daddynta da baya iya kwana biyu baizo ya tafi da itaba Shima kullum itace abokiyan firarsa idan Yana gida kokuma tana gurin dd babba Shima ta ishesa da surutunta.

Kasa cewa komai Bena tayi ta waiwayo ta Kalli Zeenah wadda itama ita ta kalla tace

“Kinsan bazan shiga bedroom dinsa ba dauko ta right??

Kece matarsa kece Zaki iya shiga so please je ki fito da ita mu tafi inada abin Yi gida da sauri.”

Kallan hanyar dakin tayi ta Dan sauke Kai taja numfashi tareda dagowa ta sake kallan Zeenah tace “ko Zaki kira wayansa ne”

Zeenah na ganin Hakan ta miqe ta nufi Kofa zata fice Bena tayi saurin riqota zatai magana suka Jiyo takunsa ahankali tareda Amnah ya fito daga bedroom din zuwa palon.

Zeenah ce ta fara juyowa tana kallansa cikin kulawa tai masa ya jiki kafin ta sake magana ya katsesu da cewan

“Meyake faruwa anan?”

“Amnah na Kuka me ya faru?”

Sai alokacin Bena ta juyo a hankali cikin nutsuwa ta Dan dago ta kallesa daga ita har shi lokaci Daya zuciyoyinsu sukai nauyi ya dauke Kai Yana sake maimaita tambayansa.

Cikin sanyi Bena tace masa “Ina wuni”

Amsawa yayi a gajarce Yana kallan Amnah Dake jikinsa ta lafe yace

“Angel kije gida zanzo gobe na dawo dake,ok??

Maqale kafada tayi tareda sake kwantawa jikinsa cikin kunnensa qasa qasa tace

“Daddy kace mummy ta tsaya anan to”

Idanuwansa ya jefawa Bena wadda tana ganin Hakan tasan me Amnah ta fada ta Maida kallanta kan Amnah zatai magana ya gyadawa Amnah Kai ahankali tareda miqawa Zeenah ita yace “kuje gobe zanzo na tafi da ita.”

Bena na ganin Hakan tayi saurin yin gaba zata wuce Amnah tayi saurin juyowa ta Kalli daddynta

Hannu Daya ya saka ya zagayo shafaffen cikin Bena yayo baya da ita ta jingina da kirjinsa.

Wani murmushin Dadi Amnah ta sake  suna ficewa tace

“Mummy ki kula da daddy fa kafin nadawo gobe”

Suna ficewa ta Zame da sauri tana waiwayowa ta kallesa tace “zan bisu”

Bai kalleta ba ya juya ya koma bedroom dinsa Yana cewa

“Ki Jira sai goben da Amnah tace”

Da sauri tabi bayansa zatai magana sbd suna wucewa batada yanda zaayi ta fita anguwan sbd securities bazasu bari ba

Bata ankara ba ta bisa har cikin bedroom dinsa tana masa magana suna Kaiwa tsakiyan dakin ya juyo daidai ita Kuma ta zo daf dashi suka tsaya da sauri tana kallan Dan mitsitsin space din Daya rage kirjinsu ya hade.

Shima mayun idanuwansa ya Kai ya Kalli space din Wanda ko fadin batir bazai shiga ba hakama dasun hade din akwai yiyuwan zazzabinsa ya qaru.

Wani siririn yawu ta hadiye tana dago da idanuwanta sama ta kallesa tareda Dan yin baya ahankali ta janye bayan sun shagi numfashin juna.

Juyawa tayi ya fice daga dakin ta koma Palo ya zauna sai alokacin ta Tina da wayarta na mota da handbag dinta Dan haka dai tana tsaka me wuya.

Zaune take shiru a palon daga ita sai makekiyan flat screen tv dake Aiki ba murya sosai can qasa qasa Kuma cartoons ne keta playing Wani bayan Wani a Netflix.

Time na sallan magrib ya sakata miqewa ta rasa ina zata alwala ta taga Wani kofan bedroom din ta Bude ta shiga ta fada toilet tayo alwala Dayake akwai direction na alkiblah sai kawai ta tayarda sallanta.

Koda ta gama qin fitowa tayi tayi zamanta tana tinanin Abinda zata fadawa su Umme da dd babbanta idan takoma bayan ta kwana daya anan.

Saida time na ishai yayi ta miqe tayi abarta tana idarwa ta fito sbd Yunwa yakeji Kuma bazata iya takura kanta da yunwar ba.

Ga mamakinta abinci ne a dining din Jere da alama order dinsa Akai Amma ganin tsadaddun food wormers na gida ya sata tinanin daga KAANTES ne Kuma Zeenah ce ko Umme ta Aiko da abincin.

Zaunawa tayi ta zuba abincin

Tana fara ci taji yaji a abincin take ta miqe tabarsa ta nufi kitchen tana tabbatarda girkin Zeenah ce tayisa sbd har lokacin Bata iya girki ba kokuma a ankaw sabuwar me Aiki gidan wadda batasan baa cin yaji Sam a abincin gidan ba bare wannan baturen gidan da aka kawowa.

Ruwa me sanyi Tasha a kitchen din Dayake ita bawai yaji Yana damunta bane sosai ko rikitata kawai dai Bata taso inda ma zataci abinci me Dadin da har zaa saka musu yajin bane to Kuma tana shigowa kaantes itama dabi’an rashin cinsa da sonsa kwata kwata ta shigeta.

Tana Shan ruwan dauko fresh orange drink da chocolates drinks dake cike da double door fridge din da duk aka cika sbd Amnah sbd ta tabbatarda bashine yake shansu ba.

Fresh orange drink din Tasha da cookies masu shegiyan tsada taci ta koshi ta koma dakin data fito sbd bazata iya zama palon ba Wani irin rashin sakewa da bugawan zuciya takeji.

Shiru shiru taga har 9 tayi Dan haka batada zabin bayan shiga toilet ta Saba da wanka data dawo Aiki Dan haka a takure take tin dazu.

Toilet din akwai komai duk da alaman baa amfani da dakin saidai kullum me aikinsa yazo ya gyare koina ya tafi.

Da Jo Malone body wash dinsa dake toilet din tayi wanka tareda wanke baki da mouth wash dinsa ta Ciro towel din gidan dasuke duk manya ne irin na Maza ta dauro ta fito tana kallan doguwan rigarta datake tinanin yanda zata mayar da ita jikinta ta kwanta.

Kofan dakin taji an Bude ta juyo da sauri tana Dafe towel din da yayi mata nauyi ta Kallo kofar tagansa Dafe da kirji Yana Tari ahankali idanuwansa jajir Yana nuna mata tazo ta duba kitchen dinsa idan akwai taimakon da zata iya Basa duk da wannan yajin baiyi azabar wancan ba Amma tsoron azaba irin wancan tasa hankalinsa ya tashi sosai.

Faduwa gabanta yayi tana Dafe kanta sbd tayi niyar dauke abincin sbd kada ya ci Amma ta manta shaf.

Nufosa tayi da sauri ta fito yabiyo bayanta Yana Dafe da kirjinsa kunnuwansa na juyawa kaman zasu tsinke da azaba.

Chapter 62

62

Babu Nutella a gidan kokuma Wani liquid Abu me Dan zaqin dazai kashe masa yajin Dan haka ta dauko orange drink me Dan sanyi ta kawo masa ta zuba a cup da sauri ta Kai masa bakinsa ya karba ya shanye duka baiji komai ya ragu ba take Wani tarin ya taso masa idanuwansa na sake rikicewa pepper na gigita rayuwansa cikin seconds da mintina,

Yanada allergic to yaji ma kwata kwata.

Ruwan sanyi ta dauko jikinta na Dan rawa da sauri ta kawo ta Basa Shima yaji kaman harshensa zai yanko daga bakinsa ya ture.

A cikin fridge ta samo Wani diary chocolate din Amnah ta kawo da sauri a azabce ya girgiza Kai bayacin chocolate shi.

Ganin Yana Neman some mata gashi batada waya jiki na rawa ta rasa abinyi sai kawai ta Bude chocolate din Dayake hannunta ta saka bakinta ta fara taunawa tukuna ta tsaya gabansa ahankali tareda ranqwafowa ta zira hannuwanta cikin sanyi ta kamo Kansa ta hade bakinsu cikin nutsuwa ta zira harshenta tareda chocolate din Dayake Kai cikin bakinsa.

Sanyin harshenta dana chocolate din data tauna masa ya sakashi qarasa hanyota kan qafafunsa Dayake zaune kan dining din Yana zagayota dakyau Yana tsotsan bakinta da duka Abinda yake cikinsa.

Rufe idanuwanta tayi ahankali sbd yanda yake tsotsan harshenta tareda chocolate din Yana sake shigo da ita jikinsa ya saka jikinta mutuwa sai kirjinta dake harbawa sosai kaman zai Faso.

Ahankali ya shanye yajin bayajinsa sai Wani irin yanayin Dayake Jin ya samu Kansa aciki ya Bude jajayen idanuwansa dasuka Sha wuya ahankali ya Kalli idanuwanta dake rufe Bai cire bakinsa ba anata yaci gaba da yiwa bakin Wani irin tsotsan Daya sakata Bude nata idanuwan itama tana qanqamesa da hannuwanta ahankali.

Babu Riga jikinsa dagashi sai dogon wandon kayan baccinsa masu santsi da tsadan gaske Dan haka saukan tafin hannuwanta a fatarsa ya saka numfashinsa skipping na seconds kafin ya Bude sakalallun idanuwansa ya kalleta sbd ya fada mata kiyaye yimasa Hakan a irin wannan haduwan tasu.

Miqewa yayi da ita ajikinsa har lokacin bakinsa na cikin nasa ya nufi bedroom dinsa da ita a karo na biyu kenan da wata mace ta sake taba shigowa dakin baccinsa,

Itace ta farko data shiga a bedroom dinsa na Lagos sai yanzu data shigo na Nan din Amma duk rayuwar dayayi a turai da Nigeria babu macen data taba shiga bedroom dinsa ko na Ina ne sai ita.

Batasan sun shigo dakinsa ba Saida ya sauketa tsakiyan dakin tareda zare bakinsa daga nata ya zuqo qamshin wuyanta zuwa kirjinta dake harbawa Yana Hawa da sauka.

Tsayar da idanuwansa yayi kan kirjinta nata dake Hawa Yana saukowa cikin towel fatan saman kirjinta tana daukan Idon hutu da lafiya.

Ya goga fuskansa ahankali cikin tayar da tsigan jikinsu gabaki Daya ya shafi kirjinta zuwa wuyanta

Atake gabanta yayi mummunan bugawan Daya saka towel dinta kuncewa ba zato ta fada jikinsa ta rungumesa sbd kada ya Samu Daman ganinta.

Idan akwai Abinda yafi dauke wuta shine ya samesa a lokacin daqyar ya iya bude kasalallun idanuwansa akanta yana Jin zaiyi gadon asthmar ummensa a take…

Tsigan jikinsa ahankali duk suka miqe yaji Kansa na daukan zafi ahankali ya shafo wuyanta zuwa tsakiyan bayanta ahankali Yana sake kokarin riqe numfashinsa da nutsuwansa.

Dagota yayi sbd kirjinta gap suke da illata kirjinsa Yana dagota sama yayi da ita zuwa lafiyayyan gadonsa da Wani zai hau masa akaro na farko bayan Amnansa.

Ahankali ya Kwantar da ita tayi saurin rufe idanuwanta tsoranta na qaruwa.

Saukan hannunsa ahan kan cikinta ya sakata Jan numfashin data kusa rasawa tayi saurin qanqamesa

Hakan datai ya sakashi qarasa kasa riqe Kansa ya ya Dora bakinsa ahankali kan nata Yana qarasa zuqo sauran zagin Dayake bakin,

Wuyanta yake shinshina Yana sauke lips dinsa Akai Yana sake matseta jikinsa harya gangaro kirjinta

Yana Dora lips dinsa wasu hawaye masu dumi na mutuwan jiki suka gangaro mata shikuwa kasa riqe Kansa yayi Yana sauke kisses dinsa masu dumi da kashe jiki a fatan wuyanta da Kirjinta..

Duk inda ya sauke lips a jikinsa sai tsigan ta sun miqe numfashinta ya kusa fita

Ahaka yagama sauke lips dinsa koina jikinta yana daf na birkicewa zuwa Wani matakin kwata kwata yaji Kansa da tinaninsa sun tsaya cak zuciyarsa na mummunan bugawa da tinaninsa daya dawo masa cewan ita din matar da ‘dan uwansa ya fara kusantuwa da itace.

Dakatawa yayi tareda zamewa daga jikinta Yana saukowa gadon ya fada toilet ya rufo kofan.

Kasa Bude idanuwanta da sukai tsananin nauyi tayi tana fidda numfashi da bugawan zuciya tsawon mintina kafin ta iya tashi zaune daga gadon ta sauko ahankali ta dauki towel dinta dake yashe qasa ta fice da sauri daga dakin.

Can dakin ta koma tana Isa gado ta Haye tareda shigewa bargo jikinta na Dan rawa bugun zuciyanta Bai gama dawowa daidaiba.

Rintse idanuwa tayi sbd har lokacin Jin dumin lips dinsa takeyi a koina dayayi kissing jikinta.

Shi Kansa ya jima a toilet din kafin yayi wanka ya fito idanuwansa ciki ciki ya shirya tareda saka wasu kayan baccin ya kwanta tareda rintse idanuwansa Kansa na daukan Wani irin zafi da ciwo.

Karfe 9 na safe tin kafin ya fito tana fitowa driver ya kawo breakfast daga kaantes ta bisa batareda yasaniba ta tafiyanta.

Suna Isa kaantes lokacin ma daga Zeenah har Amnah babu Wanda ya tashi Dayake weekend ne Umme kuwa Daman tana sashen dad kaante itama daki ta wucewarta ta tube ta saka kaya marasa nauyi ta kwanta sai alokacin ta samu baccin data kwana bataiba ya dauketa.

Sai 11 ta tashi lokacin kowa ya ganta babu Wanda ya tambayeta itama batace komaiba suka cigaba da alamuransu.

Wunin gabaki Daya a gida sukaisa babu Wanda ya fita

Da daddare suna zaune kan dining zasu fara cin abinci ya shigo

Da qamshinsa suka fara ankara da zuwansa dukkaninsu suka juyo suna kallansa Banda Bena data qi juyowa ta zuba tuwon semo da Akai kadan tafara ci da spoon a hankali.

Ummensa ce ta nuna masa kujera ya zauna ahankali gefen Bena Dina suka shaqi qamshin juna ta Dan rintse idanuwanta tareda budewa ta dago kadan ta kallesa Yana cikin fararen Fendi sweatshirt da sweatpant kaman matashin bature a natse murya ba qara tace

“Sannu da zuwa”

Shima Bai Wani kalleta ba ya amsa ahankali Yana Maida hankalinsa kan Amnah data dawo kejeran dayan gefensa.

Har akaci aka gama Baici ba shi fruit salad kawai yasha kadan sbd baya Jin yunwa.

A takure Bena taci abincin ta gama ta a miqe tabar gurin ta shige bedroom Kai tsaye Bata sake fitowa ba harya tafi.

Wani wasan buyan suka Kuma farawa har akazo aka fara shirye shiryen fara bikinsa da komai,

Invitations card ma na musamman dasuke nuni da Bikin manya ne zaayi.

Sosai ta Maida hankalinta kan aikinta ta sake zama busy haka dd babba ya ringa kutsata cikin manyan ayyukan da zasu qara daukakata Dan haka radadi da ciwon da zuciyarta take ciki yake samun dannuwa.

Ranar farko Dataje gurin Annenta da zancen sbd zuciyarta ta kasa daukan radadin ita Daya.

Annenta shiru tayi sbd batasan me zata fada mata ba tinda yanzu Rabi hankali Rabi daidai take.

Haka ta gama ta tattaro ta dawo gida.

Gabaki Daya ta Dena yarda su hadu office take wuni dai yamma sosai ta dawo tana dawowa take shigewarta.

Umme da Zeenah ta Wani bangare Sam zuciyarsu a sanyaye take da Jin yanayin Bena din duk da Bata nuna damuwa ko qunci ba Sam a shaanin auren da aketa fama kaman yanzu ne zaa daura auren.

Ana fara shagalin bikin ta wuce Australia tareda dd babba da Abbakar da Amnah raka dd babba ganin likita Wanda shikuma ya dauketa ne sbd a gama hidimar bikin.

Ta bangaren gidansu amarya Safnah kuwa kakarta hajiyarsu Umme da mummynta sun dawo Nan garin gabaki Daya sbd Daman Nan ne asalinsu hajiyan

Yanzu da Safnah zatai rayuwar aure garin sun dawo sauran matan daddynta biyu Kuma suna can porthacort sai yazama yanzu yanada mata biyu acan yanada Daya anan wato mummynta.

Mummyn Safnah din kuwa bakomai ya sakata Yanke shawarar dawowa Nan ba Sai Dan dole tana buqatan su kasance guri Daya da Safnah sbd Koda matsala ta samu bullowa tana kusa ta tosheta ta kowane hali me kyau ko mummuna.

Chapter 63

63

Tinda suka tafi Bena ta kashe wayarta Bata waya da kowa sbd tasan Amnah dole zata ce a kira mata daddynta haka Shima tasan zai iya Neman numbernta Dan kawai magana da yarsa Amma Kuma ita Bata bugatan komai ya sake hadata dashi a yanzu dayake shirin tarewa da matarsa.

Dd babba ma Daya fahimci Bata bugatan communicating da kowa dake Nigeria sai Bai takurata ba Shima sai dace ake samun tasa wayar Dan haka kusan can gida sai hidimar bikin ta rage armashi sbd rashin Jinsu a waya

Akai Akai ita Bena kwata kwata tinda ta tafi babu Wanda ta sameta bare ayi magana da

ita.

Daddyn Amnah din da Kansa ya karbi numbernta yayi kira yayi sakon ‘yana bugatan magana da ‘yarsa Amma duka shiru Dan haka

Shima gabaki Daya hankalinsa ya bar komai ya koma kan buqatan Jin ‘yarsa.

Shirin tafiya Australia ya fara dayaga duna kokarin share sati babu labari ba zancen komal.

Dad kaante ne da ummensa suka dakatar da tafiyarsa sbd bikinsa akeyi bazai yiyuba ya tsallake ya tafiyarsa.

Hakanan ya fasa tafiyan Ya zauna Amma ba

Dan ya fasa ba matigar suka wuce sati uku

Basu dawoba zaije yaga lafiyan yarsa ya dawo.

Bikin da Akai na kece Reni da sa’a tareda

Barnar dukiyar gaske kafin aka gyara part din

Bilal tareda Maida part din sabo fil komai aka sauya daidai Amarya yar gata masu arziki.

Tafiyar su Bena da sati biyu cif aka kammala bikin Amarya ta tare cikin kaantes a part din

Bilal da yanzu yake nata.

Batada was qawaye sbd mummynta itace qawarta Kuma abokiyan shawararta da duk

Wani Abinda zatai tare sukeyin abinsu,qawarta

Daya Kuma bama bahaushiya bace ‘yar Wani minister abokin daddynta Dan haka daga ita sai Mummynta da qawarta Rumah suka kawota sai Ummen DD din da Zeenah dakuma mum Khadija,Siyam Bata jeba sbd tanayin

Bena sosai Dan bayan Zeenah Bena batada

Kawa kaman Siyam din,itama Zeenah taje ne sbd zamanta dole Amma duk da haka da Bena na Nan ko tana dole bazata je ba gaskia zata zauna da ita ta rage mata radadin zuciya Koda

Bata nunawa ita Bena din.

Bayan Kai Amarya aka watse mummynta kafin su wuce ta tsaya sukai magana tsakaninsu

Mai Dan tsayi kafin ta fito suka bar kaantes kowa ya watse aka bar Safnah din ita Daya lokacin DD Yana wancan gidan nasa Yana hutawarsa sbd bayason ajiye kowace mace a wancan gidan shiyasa yace a gyara mata ta zauna cikin kaantes.

Bai dawo kaantes ba sai after 11 ya shigo da motarsa da kaf kaantes babu irinta yayi parking ya fito sanye cikin guntayen kayansa

Daya Saba sakawa Kai tsaye ya wuce sashen

Bilal din Yana shiga a Palo ya taddata

Tana ganinsa ta miqe tsaye tana ajiye wayarta data amfani da ita ta kallesa tare da masa sannu da zuwa batareda damuwa da time din

Daya shigo dinba dama kayan jikinsa dake bayyanarda daga hutawa ya fito.

Amsa gaisuwanta yayi tareda yimata barka da zuwa kafin ya Dora da yimata Saida safe ya nufi hanyar dayasan Nan ne bedroom dinsa anan ya shige.

Bata ji komaiba Dan tasan waye Dawood din game da zafin Kai da ajinsa Dan haka ta sauke Dan garamin numfashi tareda daukan wayarta ta nufi bedroom dinta itama ta shige tana wurgi da wayar kan gado ta wurgar da mayafinta Shima tana sake qaramin tsoki tace “Yana nufin haka zan kwana bayan duk

Abinda mummy ta dirka min Nasha?

Mitss”

A tsakiyan dakin ta tube kayanta ta jefar ta wuce toilet ta wanke duk makeup na fuskarta tayo wanka tanata fama tsoki a hankali sbd

Sam batada hakuri.

Tana fitowa wanka kayan bacci kawai ta saka ta fito dauka dakin ta nufi bedroom dinsa ga mamakinta dakin baya budewa sai an Bude maka daga ciki idan daga waje ne sai da password.

Wani qaramin tsokin ta Kuma ja mara sauti tareda Dan knocking kofar

A daidai wannan lokacin shikuma yana toilet

Yana wanka cikin ruwan dumi a natse Dan haka har tayita knocking ta gaji ta koma dakinta Baijiba.

Yana fitowa yayi Shirin baccinsa bayan yagama shafa tirarika da body oil kadan ya kwanta tareda lumshe idanuwansa da gabaki.

Daya babu Abinda suke bugata da son Gani kaman ‘yarsa.

Washe gari daga gurinsu Umme aka kawo breakfast daga shi har ita babu Wanda ya tashi daga bacci sai 10,

Shine ya fara shiryawa ya fito cikin Giorgio

Armani classy suits navy blue da Alexander

McQueen shoes take gamshinsa ya cike palon da inda ya fito,

Bai tsaya breakfast ba ya fice sbd yau meeting dinsa nada mahimmanci sosai a office.

Bayan fitarta sai daga baya itama ta fito sanye da kayan baccin brush kawai tayi ta fito ta zauna kan dining zata fara cin Abinda Mai aikin da aka bar mata daga cikin masu aikin

Umme ta shigo a natse kanta a qasa ta gaida

Safnah din.

Bata amsaba ta fara cin abinci ahankali tana latsa wayarta Dan Kiran mummynta tace

“‘Ina dayan matan D take zaune??”

Dan shiru Salma tayi kafin ahankali tace

“Tinda aka Akai auren a bangaren Umme take zaune da Amnah”

Shiru Safnah tayi sai a lokacin take tinawa da matar tasa nada shegiyar ‘ya wadda aka samu

ba aure.

“Tafi naji” tafada tana cigaba da cin abincin a hankali.

Aiki Salma ta wuce zata fara duk da babu inda

yakeda alaman buqatan Wani gyara koina fes

Amma dole hakanan ta hau goge kaya tana

Shirin shara da mopping before wadata koina

da qamshi.

Ita kuwa Safnah tana gamawa wanka taje tayi

ta shirya ta nufi gurinsu Umme tayi zamanta

acan Dan maitan son ganin wadda take amsa

sunan kishiyarts a baki kawai.

*****Bena sosai ta danne ta Hana duk Wani

azaban da zuciyarta take ciki ta sake suka

ringa samun hutu da nishadi tareda kulawa

da dd babba sosai Dan kusan itace ke Basa

maganinsa da lokaci yayi maganinsa da lokaci yayi

Hakama shi Kansa dd babban duk Kiran da

DD ke masa Sam yaqi nuna masa suna gida

Daya ma da Bena Dan haka Bai taba kwatanta cewan a Basa ‘yarsa ba bare Bena.

Amnah kullum sai tayi rigiman son magana da daddynta shi ya saka Bena dagewa ta danne

Abinda yake cin ranta ta saki jiki tana bawa

‘yarta nishadi suna Jin Dadin qasar yanda ya kamata.

Ta bangare Daya Kuma aikinta na office Bai dakata ba tana exchanging emails sosai da

Fahad gameda ayyukan office Dan haka take sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa.

Bata saka ranar dawowa a kusa ba San Dan karatun Amnah da hutun ta yake kokarin qarewa Dan haka sbd Amnah kawai zata koma idan lokaci yayi.

****Acan Nigeria kuwa Safnah kullum a bangarensu Umme take wuni duk da ta samu sanin Bena Bata qasar da ‘yarta,

DD kuwa kusan kullum baida time na zama gida Yana dawowa yaci abinci ya shige shikenan babu Wani Abu na kusanci da juna koma fira haka ta kauna da kulawa data taba shiga tsakaninsu kullum baya Wani zama sbd ko baya office yafi zama gidansa dake highbridge, yafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali acan

Ya kasa sabawa da zama kullum kullum da mutum a guri Daya shiyasa duk inda yake tin asali baya zama cikin familynsa yafison yaje inda zai zauna shi Daya yayi rayuwan dayakeso gashi matiqan Yana cikin gidansa ba maabocin saka kaya masu nauyi ko tsayi bane

Dan Hakan yake zaban zama gidansa shi Daya yayi rayuwansa ba takura ba damuwa.

Safnah hakurinta Yana qarewa gameda zaman

Datakeyi da mutumin da takejin zuciyarta idan

Bata samesa ba komai zai iya faruwa, Zafi da bagin ciki sosai takeyi da irin zaman dasukeyi

Babu ranar da Bata Kai kanta dakinsa Amma

Bai taba barinta ko shigaba Bare ta samu

Daman Jan raayinsa ya kwana da ita Dan a yanzu tafi buqatan suyi kwanciyar aure akan komai sbd vanda yake fitowa daga shi sai dogayen wandina ba Riga kokuma guntayen wandina ba Riga jikinsa ya sakata qara mutuwa akansa sbd ita ko a turawanta datai ravuwa cikinsu DD kaante daban yake,

Komai nasa me aji da Jan hankali ne tareda daukan Ido.

Ahaka suka shafe sati biyar babu Wani gaba bare baya Dan haka itama ta rage zama gida kusan kullum saita fita sunfita da Mummynta sbd lamarin ya fara qundurarsu gashi hakanan

Safnah takejin Bata gaunar matarsa ta dawo

Bata gama samun Kansa ko hankalinsa akanta ba Dan haka daga ita har mummynta hankalinsu ya tashi suka kasa zama suka kasa tsayi. ******Watansu Bena 2 cif suka fara Shirin dawowa lokacin suna barin Australia Umrah suka wuce suka qara sati biyu kafin suka diro

Nigeria,

Jirginsu da Asuba ya sauka Dan haka Fahad ne ma yaje da Kansa da lafiyayyan motarsa ya daukosu,

Kallo Daya yayiwa Bena ya dauke idanuwansa

Yana kore shedan daga zuciyarsa sbd yanda kyanta ya daki kirjinsa,

Tafiyan wata biyu kokuma yace uku Amma komai nata ya qaru,

Kyau, lafiyan fata,hutu,nutsuwa,aji da burgewa duk komai ta garo hakama harda cikowa tayi kaman wadda babu Abinda taje tayo sai hutawa. Dd babba ma ya gara samun qarfi da lafiya sosai harma da kwanciyar hankali sbd kulawa da Bena ke Basa da yanda ya bar gida da hayaniyarsu yaje ya huta Abinsa.

Abbakar kuwa gibarsa yayo abarsa lafiya kalau ta hutu da cima me kyau duk da Baya Wani son abincinsu acan Amma cinsa yakeyi ya koshi Abinsa ya huta ya fita yawon Shan iska yaci Dadi San ransa

Amnah ma sosai tayi jikinta da haske data garo Daman ita ba skin din mamanta ta daukoba na baban Dan haka take fara tas kaman DD.

Koda suka shigo kaantes an shiga sallan

Asuba Dan haka babu Wanda yasan ma sun iso, sai a lokacin ta Ciro wayarta jaka ta kunna ta kira Nafisat, Nafisat ce ta kwasar musu kayansu zuwa ciki shikuma dd babba Abbakar ne ya shiga nasa kayan bangarensa kafin suka wuce masallaci sallah sbd alokacin ne aka tayar.

Suna shiga Kai tsaye bedroom din Zeenan suka shige Nafisat Kuma cikin duhun Asuban ta hau gyara dakin Bena din.

Sun shiga Zeenah Bata ma tashi sallan Asuba ba motsinsu da shigowansu dakin ya tayar da ita ta tashi zaune ahankali ta miga hannu tana kunna wutan dakin taga Bena tsaye tana ajiye handbag nata Amnah kuwa gadon ta fada sbd bacci ne sosai a idonta.

Da sauri Zeenah ta sauko gadon bacci na

Sakin idanuwanta gabaki Daya ta nufo Bena suka rungume juna tana cewa “Oh ya Allah finally Bena kin dawo.”

Murmushi Bena ta sake ahankali tareda rungumeta itama tana cewa

“Kin dauka bazan dawo bane?”

Mintsininta Zeenah tayi tana janyewa daga jikinta tace

“Kinsa me kikai kuwa?

Meyasa Zaki Kashe waya ki Hana kowa Jinki for more than 2months,

Kin kusa sakawa kowa heart attack da rashin

Jinku.

Wani murmushin me sauti ta Kuma sakewa tana cewa

“Ba gashi na dawo ba”

1

Kayanta tahau cirewa ta fada toilet tayo alwala batai wanka ba ta fito ta saka Riga da wandon bacci tayi sallah ta fada gadon Zeenah din ta shige bargo take baccin dake cinta da gajiya ya dauketa.

Chapter 64

64

Zeenah ma sallan tayi Amma farin ciki ya hanata komawa bacci Dan haka karatun

Qur’an tayi a iPad kafin tana gamawa ta miqe ta hau Aiki a laptop Kuma.

Zata fita office 9 yau Dan haka time nayi ta shirya dole tabarsu suyi baccin hutu tukuna

8:30 nayi na fice.

Amnah ce ta fara tashi ta sauko gadon ta fito dakin ta nufi kitchen gurin Nafisat wadda sai alokacin ta samu ganin Amnah ta rungumeta cikin murnar dawowansu sbd lokacinda suka dawo da Asuba Amnah din na jikin mummynta sod bacci.

Itama Amnah sosai tayi kewan Nafisat din Dan haka ta Haye jikinta suka dawo zuwa bedroom din mummynta.

Dakin Nafisat tai masa Wani irin gyaran tsafta da kyau koina sai qamshi da sanyi ke tashi tareda ni’iman tsafna.

Toilet suka wuce Kai tsaye Nafisat ta taimaka mata tayi brush kafin Akai fitsari da alwala suka fito ta saka mata abayan sallah tayi sallah duk Nafisat na tsaye tana jiranta.

Tana gama sallan nata da zaa ce Allah ya

Bada Lada

Nafisat ta dauke kayan sallan ta sake gyara toilet da dakin kafin suka wuce kitchen Nafisat na cewa Bara na hado Miki breakfast naki yanzun Nan.

Cikin tsalle Amnah ta fara cewa

“a ba breakfast nakeso yanzu ba Ina iPad

Dina ki dauko ki sakamun charge inason Kiran Daddyna nayi missing nashi sosai sosai sosai Gyaran muryansa taji daga bayanta ahankali ya furta

“I miss my angel too sosai sosai.

Da Wani irin gudu ta nufosa tin Bai garasaba ta fada Kansa ya dauketa yayi sama da ita Vana

Jin zuciyarsa na samun sanyin da tinda suka tafi ya rasa shi.

Dariya sosai Amnah keyi tana farin cikin ganinsa shi Kansa murmushi yake mata

Wanda ya saka Nafisat silalewa ta kama hanyar kitchen Dan hado Abinda tasan dashi

Amnah ke breakfast wato chocolate custard fa soyayyan farin kwai da tomatoes kawai. Umme ma dariya da ihun Amnah ya sakata fitowa Daman dad kaante ya fada mata sun dawo sbd kowa a masallaci sallan Asuba

Kawai akaga dd babba da Abbakar, Shi Kansa Daddyn Amnah din a masallaci ya gansu ya tabbatarda dawowan ‘yarsa.

Amnah na ganin Umme ta sake shiga farin ciki itama tayi kanta ta rungume tana cewa tayi missing nata.

Daga jikin Umme ficewa tayi da gudu zuwa palon dad kaante Yana zaune Yana amsa waya yajita Kansa ta fado dole yayi sallama da

Wanda yake wayar Yana cewa

“Zaki karyawa dad din daddynki wuya ai da

wannan kibar da kika qaro acan.

Dariya tayi masa tana cewa “Wuyanta baze karye ba ai yanada qarfi sosai kaman na Daddyna”

Murmushi yayi Yana zagayo da ita gabansa yace

” Wannan wuyan na Daddynki ai yafi na kowa garfi.”

Shigowan daddynta palon ya sakata barin jikin dad kaante ta koma gurinsa ya dauketa Yana garasowa ciki ya gaida dad din kafin suka juya suka fice.

Palon Umme suka koma lokacin Nafisat ta gama hadowa Amnah din komai Suma sauran masu gidan angama nasu breakfast din an

Jere a dining. A dining din ya zauna shi da Amnah suna magana Yana amsa mata a hankali Nafisat na kokarin qarasa shirya mata breakfast din a gun

Daidai lokacin 9:40 ta buga aka Bude kofan bedroom din Zeenah Bena ta fito ahankali tana

Dan shafa wuyanta dataji yasamu sakewan datakeso sbd samun isashen bacci.

Kayan baccin jikinta masu tsantsi me da yanayin sanyi ya Dan sakasu lafewa jikinta tana fitowa Kai tsaye dining ta nufo tana Dan

Kiran sunan Nafisat sbd ta kawo mata tea me zafi sosai yau takesan Sha.

Tinda ta tinkaro dining din ya dago fararen idanuwansa ya zuba mata bata ankara da

Hakan ba Saida ta qaraso daf ta tsaya cak

Wani irin sanyi da bugawan zuciya na samunta lokaci Daya.

Dagashi har ita kowannensu yaga sauyi sosai a tattare da dayansu,

Kowannensu ya qara sauyawa da samun hutu da kyan yanayi musamman ita da komai na

Qarin data samu a bayyane yake.

Ahankali ta dauke kallanta da gunsa zuciyarta na Dan gara tsananta bugawa.

Juyawa take kokarin Yi Takoma Amnah tai caraf tace

“Daddy bakaiwa mummy oyoyo ba gatanan ta fito.”

Bena na Jin haka ta juyo da sauri ta kallesa

Shima ita yayiwa Wani Kallo da mayun idanuwansa

Tana ganin Hakan ta daga qafa da sauri zata gudu saidai ko taku daya Bata qarasa ba ya miga hannu daga zaunen Dayake ya riqo hannunta Daya ya dawo da ita baya ta fado kansu shida Amnah Dake jikinsa.

Nafisat na ganin Hakan tayi saurin barin gurin kanta gasa

Hade fuska Bena tayi tana kokarin cire jikinta

Dana nasu Amnah tace

“Mummy ki tsaya mana oyoyo kawai zai Miki kin manta munce muni missing nasa sosai fa.”

Rintse idanuwa tayi ta budesu akan Amnah cikin takaici zatai magana Amnah ta sauka daga jikinsa tana cewa

Bari na dauko iPad dina nayi muku hot kanawa mummy oyoyo.

Amnah na barin gurin ta kallesa a hankali tareda Bude baki tace

“Ina bugatan tashi ka sakeni”

Cikin idanuwanta ya zuba nasa ahankali take ta rufe nata tana kokarin Hana bugawan kirjinta Dayake fara Hawa yana sauka.

Magana ta sake Bude baki zatayi taji hannuwansa sun qara zagayeta ahankali tareda zaunar da ita da kyau kan qafafunsa suna fuskan juna.

Yanayin zaman ya sakata dagowa ta kallesa zatal magana tana Bude baki ya kamo kanta ahankali ya hade da nasa tareda zira harshensa cikin bakinta.

Batai tsammanin Hakan ba ko a mafarkinta

Dan haka ta qangamesa tana rintse idanuwanta kafin yanda yake kissing cikin bakinta ya sakata lumshe idanuwa tana Jin zuciyarta na Neman sanyi da narkewa.

Motsin dawowan Amnah ne ya sakasa Sakin bakinta ahankali tareda Ciro nasa ya jingina bayansa da kujeran dining din Yana kallanta da kasalallun idanuwansa kaman babu Abinda yayi.

Itama kasa dagowa tayi ta kallesa bare

Amnah hakama ta kasa tashi daga jikin nasa

Saida Amnah tace su shirya tai musu hoton tukuna ya Dan dago bayansa ahankali tareda daukan Amnah din ya saka tsakiyansu Akai hoton tukuna Bena ta iya migewa daga jikinsa ahankali jikinta a mace. Umme ce ta garaso itama fuskarta cikeda

farin ganin Bena din Mai tsanani tana zuwa

Bena ta rungumeta tana cewa

“Ummenah nayi kewanki sosai”

Cikin farin ciki Umme tace

“Mu da kika cinnawa hauka Bena,

Kika Hana kowa Jinki,

Amma dai koba komai kinyi kishi me tsafta

Allah ya qara Miki hakuri…

Kasa amsawa tayi tareda Satan kallansa

Shima itan ya kalla Jin kishi ne ya korata ta

Hana kowa jinta.

Kunya da nauyin maganar Umme ya sata zaunawa a Dan fuske tana basar da zancen suka fara breakfast harda ummen duk da ta

Dan ci breakfast tareda dad kaante a nasa palan.

A hankali take cin abincin batareda ta dago ba sbd idanuwansa na hanata walwala a gun.

Sama sama Shima yaci abincin Umme ta kallesa tace

“Matarka na can na jiranka kuyi breakfast kazo kayi anan.

Tsit gurin yayi har da ita ummen sbd sai datai maganar ta Tina da Bena dake gurin,.

Shima Bena din ya Dan kalla, Bena kuwa ruwan tea din dake bakinta ta hadiye ahankali sbd Neman gagara wucewa da sukai Bata dago ga ta dauki tissue fuskarta babu Wani sauyi ta goge bakinta ta dago ta

Kalli Umme cikin sakewan fuska tace

“Umme inaga yau zan koma office akwai pending ayyika sosai suna jirana,zan biya na dubo Anne kafin na tafi.

Murmushi Umme ta sake tana waskewa itama ganin Bena din Bata nuna damuwa ba tace

“Ok ba damuwa ki gaida Annen Taki tareda

Ababa Shima duk Muna gaidasu.”

Bata kallesa ba ta mige daga dining din ta wuce tana Jin idanuwansa akanta har ta shige bedroom.

Tana shigewa ta tube kayan baccin jikinta ta daura towel din Amnah da yayi mata qarami sosai ko dauruwa bayayi saidai ta riqe

Nata duk Nafisat ta kwashe da safen ta wanke sbd bazata iya daurawa sai an kwanke tin Bata

Nan sun kwana biya a ajiye

Na Amnah kuwa sabo ne ta fasa yanzun ta daura itama tana bugatan shopping din sababbi da wasu daga cikin toiletries nata.

Kofan dakinta aka Bude Kai tsaye aka shigo tareda rufewa Bata juyoba tana duba undies nata strapless bra zata dauko sbd tinanin

Amnah ce sai dataii shiru ta dakata sai a okacin taji qamshinsa ya shiga hancinta sai kawai ta qi juyowa tareda fasa dauko bra din ta nufi hanyar toilet zata shige yace

“‘Na dakatar na zuwa Aiki da fitanki gaba Daya.” Cak ta tsaya tareda juyowa Bata shirya ba sbd rashin fahimtar zancen da kyau.

Kallanta yakeyi fuskansa ba sakewa yace

“Yes you hard me right.”

Dawowa tayi zatai magana Bai tsaya sauraranta ba ya juya ya fice daga dakin fuskansa a hade sbd Bai dauka Yana zaune zata fadawa Umme fitanta da Abinda ya yankewa kanta ba batareda ko kallansa ba

Yana matsayin Wanda shine yakeda ikon da

Damar badawa din.

Wani irin bagin ciki ne me nauyi ya danne zuciyarta takasa ko motsawa daga inda take tsaye.

Ta jima a gurin tsaye kafin ta iya shiga toilet jikin na zafi da zazzabin bacin Rai Daya saukan mata a take.

Wankan ma ba acikin Dadin Rai tayosa ba ta fito ta shirya cikin Riga da skirt da coffee brown lace Mai tsananin tsadan tsiya ta Kira

Zeenah ta turo mata numbernsa a Karo na farko data taba samun numbernsa bare kiransa a wayanta.

Kira uku tavi Bai daga ba da alama yasan numbern tata Dan haka itama aje wayar tayi tana cire maganar daga ranta.

Gurin dd babba taie tai masa bayanin zancen murmushi kawai yayi yace

“Ki shirya kije ki dubo Annenki kawai karki je aikin bari sai kinsake magana dashi, Bazan masa magana ba kiyi magana

Dashi zuwa gobe ko anjima idan kin dawo daga gurin Annenki ki samesa gidansa na highbridge kuyi magana.”

To kawai tace Amma bataso Hakan ba hasalima bazata sake nemansa ba.

Shiryawa tayi itada Amnah da Nafisat dake kulawa da ko saka talkalmin Amnah suka fita.

Shopping sosai suka fara yiwa Anne kafin suka wuce gidan saidai murnarta komawa ciki tayi sbd tararda yau din jikin Annen ya tashi

Sam bata Wani hankalinta sosai ganinsu ne ma ta Dan Yi kaman ta dawo daidai sbd Bena cikin tsakiyan ranta take.

Hande duk Abinda zuka zo dashi karbewa tayi tace sai Ababa ya dawo abasa kafin ya bawa

Annen Abinda zai Bata da Kansa Bena Bata damu ba Dan haka ta zauna ta yankewa Annenta farce dasukai tsayi,

Ta kunce mata Kai ta wanke mata tas tareda taimaka mata da kanta tayi mata wanka tas

Nafisat kuwa dakin ta sakata ta gyara tayiwa

Annen wanki duk da sun siyo mata sabbin kaya Amma duk hande ta karbe sai Ababa ya dawo.

Abincin lafiyayyan dasuka zo dashi Daman sbd Annen suka fara barinsa mota Bena ta saka Nafisat ta dauko hande na ganin babban basket zata amsa Bena tace Mata abincin

Amnah ne Batacin komai sai shi.

Dole hande ta bari sbd duk masifar Ababa ya

Hana a taba Amnah wadda itama ta Dan yinsa sbd Yana sonta.

Chapter 65

65

Pepper soup na qatan catfish ne da Kuma white rice da aka dafa tareda veggies sai sauce na kidney qanana aciki,

A cikin dakin suka zauna Amnah na jikin

Nafisat tana Bata da spoon abaki ahankali ita

Kuma Bena tana bawa Annenta cikin tsananin kulawa da soyayyan mahaifiyarta me tsanani.

Saida ta tabbatarda Annen ta Koshi kafin ta

Bata fruit drink me mara sanyi Tasha tukuna

Nafisat ta tattara kayan ta mayar basket ta

Maida mota.

Har yamma tana gidan tana jiran dawowan

Ababa taso rokonsa yabata Daman kai Annen taga likita Amma har magrib Bai dawoba Dan haka Suka tafi Annenta na kallanta kaman zatai Kuka, Itama Saida tayi hawayen kafin ta iya tafiya tabar Annenta.

Gida suka koma Kai tsaye daki ta shige sbd ranta ya gajule da yanayin Annenta Kuma gashi dd babba Yanata tausanta sbd matigar ba asirin kafin da Ababa yai mata a karya ba ko sace ta Akai kokuma akai dole aka dauketa zata iya ransa ranta sbd Hakan Sai Kuma idan shine da Kansa Ababan yace ta tafi yayi freeing dinta.

Data shige daki bayan tayi sallan magrib kasa rige kukan Datake dannewa tin a gaban Anne tayi ta fasa kukan a hankali tareda cusa kanta cikin qafafunta.

Amnah data shigo ta taddata tana Kukan qarasowa tayi ahankali ta shiga jikinta ta lafeta tareda yin shiru sbd Bata taba ganin Mummyn nata na Kuka ba. Saida Bena tayi kukanta me isanta hardana DD

Daya da Abinda yayi mata da radadin kishinsa

Datake ta dannewa duk sai datai kukansu

Daman suna ranta danqare.

Wata alwalan tayo tareda wanka tazo tayi sallan ishai tana gamawa a daki Nafisat ya kawo mata yoghurt a glass cup Tasha ya isheta ta kwanta tareda cewa batada lafiya

Zazzabi takeji sbd tasan Hakan ne kawai zai saka abarta taji da Abinda yake cin ranta da ruhi.

Daga Zeenah har Umme sin shiga damuwan rashin laflyan nata Amnah kuwa sukuku tayi sbd Daddyn da Mummynta sune walwanta,farin cikinta da rayuwanta.

Da daddare Shima Bai shigoba sbd Bai sauko ba,

Washe gari ma Bai shigoba ya tafiyarsa office.

Safnah gantalinta Bai bari tasan Bena ta dawo ba sai data kwana biyu tukuna sbd kullum

Bata wuni gida idan ta fita sai dare.

Dd babba taje ta gaida harda yimasa girki na musamman

Baya cin girkin kowa yanzu saina Bena Amma

Bai nunawa Safnah din ba ya saka mata albarka tareda godia.

Qin zuwa sashen Umme tayi tinda taji Bena ta dawo Dan haka ta sake haukacewa tareda mayar da hankali ga Jan hankalin mijinta

Wanda haryanzu suke yanda suke.

Bena kuwa cikin kwana biyu ta shiga Wani mummunan halin sanyi da damuwa, Sam ta

Dena zaman Palo sai ta tabbatarda lokacinda bazai shigoba take fitowa ta zauna cikinsu

Umme Zeenah ma aikinta baya barinta zama gida sosai itama Kuma.

Amnah halinda mummynta take ciki itama ya taba ta Sam ta Dena walwala da Hayaniyan yarinta Datake sosai ta sauya.

Shi Kansa a kwanakin gabaki Daya ya sauya baya cikin walwala ko sakewan, koyaushe ransa ba Dadi a hade fuskansa take

Duk sai abin ya sake taba Amnah Takoma kaman iyayenta ba walwalan.

Shine yafara kokarin dawowa daidai sbd

Amnah data fara harda rashin lafiya sbd Bata

Saba da qunci ba batama San Saba.

Duk yanda ya sauya Yana shigowa yanzu kullum Bena Bata taba yarda ya ganta ba gabaki Daya ta kaucewa duk Abinda zai hadasu. Amnah idan zatai vidcall dashi barin dakin takeyi hakama idan har taji alaman Yana bangaren Bata fitowa saiya tafi.

Babban Oarin kame kanta ma harda matarsa

Bata shaawan haduwa da ita Sam bare shi.

A haka suka share kusan sati biyu

Duk lokacinda matarsa akace ta shigo Bata fita sai ta fice hakama Shima duk akace

Yananan Bata fitowa din.

Dd babba idanuwa ya zuba musu hakama umme sbd batasan meke damunsu ba kowannensu Kansa ya dauki zafi,dad kaante kuwa baimasan meyake faruwa ba.

Yau Zeenah bazata office ba hutawa zatayi

Dan haka Suka shirya itada Bena din suka fita outing ko kansu duka zai sake. Sunyi shopping sosai sunci tsadaddiyar abinci a restaurant na kaantes hotels and suites daga Nan sukas shiga VIP saloon and beauty parlor dake cikin kaantes hotels and suites din.

Ba Wani gyara dasuke bugata sbd kusan duk sati zuwa sati biyu saisunzo gyaran Amma tinda sun shigo Basu fitaba saida suka sake shiga Akai musu manicure and pedicure dasu

gyaran Kai da sauransu.

Suna fitowa Bena tace Zeenah ta ajiyeta

gidansu zata duba Annenta

Bayan sun Isa Bata bari Zeenah ta shiga ba tace ta tafi kawai idan ta gama zata kira

Abbakar ya turo driver ya dauketa.

Hakanan Zeenah ta barta ta wuce Amma taso duba Annen itama Amma Bena da dubara ta hanata sbd Bata son a ga Annenta cikin halin Datake ciki.

Yau dinma Bata tadda Ababa ba Dan haka gyara Annenta tayi fes ta sake tsaftace mata dakinta tsakan gidan kaman bola sbd babu me shara sai Anne ta Dan dawo daidai tayi musu shara

Shi girki kuwa yanzu Ababa kusan kullum na

Siya yakeci lafiyayye hande ma wataran na

Siya wataran Anne keyi idan tana daidai, Annen ce kawai kusan yunwa tafara shigowa cikin ciwon nata sbd saisun rage suke Bata.

Ganin Hakan sai Bena ta kawo Mai Aiki gidan ta ringa shara da wanki da girki Amma wahala tasaka me aikin kwana daya tayi ta gudu,

Bayan ita wata ta sake kawowa itama kwananta biyu ta yiwa Ababa Satan da Saida

Bena din tayi masa ranko Kuma ya Yanke babu me aikin da zata Kuma kawo masa gidansa daga lokacin.

Ana gama sallan magrib akazo daukanta ta koma gida.

Wanka tayi ta saka straight pencil Sisley doguwan Riga me laushi data kwanta jikinta gabaki Daya bawai matsewa ba.

Qaraman hula ta saka tareda ziro slippers tana fitowa palon Yana shigowa Shima sanye cikin black Ralphs da slippers na chanel fuskansa fresh Yana fidda Wani kwarjinin da sirrin kyau

Bata dakata ba ta juya kawai zata nufi hanyar kitchen babu tsammani ya riqota sbd ya kasa

Hana kansa barin ta tafi.

Baya ya dawo da ita bayanta ya jingina da kiriinsa gamshinta ya shiga hancinsa take ya rufe Ido Yana son magana ta kwace iikinta a hankali tareda yin gaba ya rigota kenan

Amnah ta shigo palon daga dakin Zeenah tana Ana gama sallan magrib akazo daukanta ta koma gida.

Wanka tayi ta saka straight pencil Sisley doguwan Riga me laushi data kwanta jikinta gabaki Daya bawai matsewa ba.

Qaraman hula ta saka tareda ziro slippers tana fitowa palon Yana shigowa Shima sanye cikin black Ralphs da slippers na chanel fuskansa fresh Yana fidda Wani kwarjinin da sirrin kyau

Bata dakata ba ta juya kawai zata nufi hanyar kitchen babu tsammani ya riqota sbd ya kasa

Hana kansa barin ta tafi.

Baya ya dawo da ita bayanta ya jingina da kiriinsa gamshinta ya shiga hancinsa take ya rufe Ido Yana son magana ta kwace iikinta a hankali tareda yin gaba ya rigota kenan

Amnah ta shigo palon daga dakin Zeenah tana Owacewa Bena ta hau Yi fuskarta ba walwala

Bai ce mata komaiba ya dagata cak zuwa bedroom dinta ya Bude ya shiga tareda tura kofan kafin ya jiyeta tareda jinginar da ita jikin kofan yayi manneta da kirjinsa ahankali.

Idanuwanta dasuka qi kallansa ya kalla tareda

Kai bakinsa kan fatan kunnenta cikin qaramin sautin Daya saka gashin jikinta gabaki Daya migewa yace

“Kukan me kikeyi kullum?”

Dumin numfashin bakinsa ya sauke direct cikin kunnenta tareda maganarsa Dan haka gafafunta sukai Neman saki zatai qasa ya zagayeta da hannunsa Daya tareda matseta da kyau jikinsa Yana lumshe fararen idanuwansa tareda zira Kansa wuyanta ahankali ya Shaqi qamshinta da qarfi.

Da gyar ta iya Bude baki muryanta ba sauti sosai itama ta furta

“Ka sake ni please”

Kansa dake cikin wuyanta yasaka maganarta shiga kunnensa Shima direct tareda dumin numfashinta Dana haka gabaki Daya ta qarasa kunnasa ya dago a kasalance ya Kalli fuskarsa tareda gangarawa da idanuwansa bakinta zuwa wuyanta da Kirjinta da rigar ta kwanta ta lafe.

Kunnenta ya fara sakar kiss me sanyi ahankali kafin ya sakarwa wuyanta tukuna ya dago ahankali ya kama bakinta da nasa wannan

Karan tare suka fara kissing juna cikin sanyi ba da zafi ba.

Baa taba kissing nasa ba sai yau din sbd duk kisses din dasuka taba Yi shine yake kissing nata Bata taba kissing nasa back ba sai yau

Dan haka kissing din na yau yafi kowanne shigarsu da tsimasu.

Ita kanta batasan tafara kissing din nasa ba sbd daga ita har shi sunyi kewan juna sosai batareda sun San Hakan.

Sake matseta yayi jikinsa tareda daukanta suka nufi couch har lokacin bakinsu na hade tini wayarta da hularta suka watsar jikin kofa

Ya zauna tana kan gafafunsa Yana Jin notin

Kansa suna kuncewa Daya bayan Daya,

Rigar jikinta ya Zame Daga sama zuwa ilkinta

Takoma daga ita sai hot red strapless bra data sake gigitasa ya shafo cikinta Yana zuwa kiriinta Yana Jin bazai rige Kansa ba.

Kirjinta ya dawo da Kansa da baki ya fizge bra din Daman Ba hannuwa ne da ita ba bare Wani qarfi sbd bras masu tsada basuda Wani qarfinauyi bare takurawa.

Jikinsa ta shige sbd rabata da bra da yayi shikuma Hakan ya kunce masa last notin

Kansa Daya rake Dan haka ya ringa kissing fatar jikinta Yana cakuda ta.

Bai taba samun Kansa a cikin wannan halin ba shi dayayi rayuwar turai da yanda yakeso bare ita data taso a killace cikin Cage Dan haka cikin zazzafan shauqi suka samu kansu da Wani irin crazy romance Daya kaisu wata rayuwar ta tsakanin so da kaunar juna batareda baki ya furta ba.

Migewa yayi tsaye da ita zai nufi lafiyayyan gadan dakin ta fizgo nutsuwanta tana sauke numfashi ahankali ta Bude idanuwanta dasukai nauyi ta kallesa tareda dakatar dashi tana nuna masa kofan da Akai knocking

Ahankali Wani irin zazzafan numfashi ya sauke me zafi kafin ya iya datakar da Kansa Yana kokarin daidaita Kansa ya saketa

Ta sauka jikinsa ahankali tareda Maida rigarta ta tana kasa kallansa ta nufi Kofa ta dauki wayarta da hulanta dake gurin tana juyowa ya taso ahankali idanuwansa jajir ya fice daga dakin.

Zeenah dake buga dakin sbd Daman tinanin

Yana ciki Dan Amnah tace daddynta na bangaren

Kasa binsa da Kallo tayi sbd ganin yanda ya fita fuskansa a hade.

Shigowa tayi dakin tana kallan Bena data kasa kallanta itama tana kokarin danna wayarta.

Akan bra din Benan dake qasa yashe idanuwanta suka sauka tana ganin Hakan ta Hana murmushinta fita tayi kaman Bata ganiba tafara tambayan Bena Abinda ya kawota Kasa amsata da kyau Bena tayi Zeenah na

ganin Hakan taji haushin kanta dataxo daidai

wannan lokacin da Bena dinta zata samu

Karne Virginity din DD kaante.

Zeenah na fita toilet Bena ya shiga tayi wanka

ta fito tayi sallan ishai da Kai tin dazu Basu

saniba

Daqyar ta iya fitowa cin abinci sbd har lokacin

jikinta a mace yake suna gamawa ta koma

daki ta Kwanta.

Washe gari da sakonsa ta farka na cewa

Takoma Aiki Dan haka cikin murna ta da farin

ciki tayi Shirin office ta fice.

Acan ya wuni gaf da magrib ta dawo sbd tarin aikin data tarar office dinta.

Tana yin parking harabar gidan ta fito mota daidai lokacin Safnah itama motarta ta shigo

tayi parking me aikinta na bayanta ta fito

idanuwanta suka sauka akan Bena data wuce

batareda ta tsaya kallanta.

##MAMUH#

#DBENA

#LOVE

#ROMANCE

#TOO HOT

Arewabooks@Mamuhgee_*

66

Dummmmm kunnuwan Safnah sukai mata jinsu na daukewa ahankali tana Jin maganar

Rabi me aikinta Sama sama dake tambayanta ko lafiyanta kalau.

Bata iya Jin me take fada daidai Saida garamin jiri me juyar da Kai ya dibeta Rabin tayi saurin tareta tana kallanta cikin tsoro da mamakin meya sameta a take.

Idanuwanta dake Neman hada mata hadari hadari ta sake budewa da kyau akan Bena wadda ko mutuwa tayi aka binneta ta kwana kabari aka fitar zata Gane itace wlh,

Benazir ‘yar uwarta jininta ce ta Gani takuma tabbatarda ita din ce idanuwanta har Wani rawa rawa sukeyi gurin kallanta harta shige

Take Wani jiri me qarfin gaske ya kuma dibanta gafafunta na kakkarwa ta kasa dagawa da Kanta kaman makauniya Rabi ta kama hannunta zuwa bangarenta.

Suna shiga Palo ta tsaya sbd Bata ganin komai sai duhu duhu ganinta Yana rawa cikin masifa da tashin hankalin da Bata taba saninsa ba a rayuwanta..

Harshenta karyewa yayi tana son tambayar

Rabi wacece wadda suka Gani din Amma batada hali sbd karshenta dake sake karyewa hannuwanta duka na jujjiga ta Ciro wayarta

Bata Gani sosai daqyar ta iya Gane numbern

Momynta ta saka kira sai alokacin ta zamu qarfin halin fizgo magana bakinta da cewa

“‘Waye,waye…wadda.muka.gani”

Ko gama rufe baki bataiba da kalaman data kasa hadawan

Rabi cikin tashin hankalin da tsoron meyake

faruwa ta katseta da Bata amsan cewa

“Aunty Bena ce,dayan Matan Sir DD,maman

Amnah ‘yar marigayi Sir Bial.”

Sankarew Safnah tayi a gurin komai nata na tsayawa cak harda numfashinta da gyar ta iya kemo Kalmar “bana Gane komai me kika fada?”

Cikin tsoro da gara shiga firgici Rabi ta Bude baki ta sake maimaita mata bayanin tana gama maimaitawa

Duhu ne ya rufe idanuwan Safnah gabaki

Daya sai ganinta Rabi tayi ta Yanke jiki ta Fadi a gurin Sume babu inda yake motsi a jikinta

Kuma daidai lokacin Momynta ta daga Kiran

Safnah din Daya shigo wayarta tafara Kiran sunanta sbd Jin ba magana.

hun Kuka Rabi ta sake jikinta na daukan rawan toro itama tafara Kiran sunan Safnah din cikin fargaba da rashin sanin meyake faruwa.

Jin Rabi na Kiran sunan Safnah cikin Kuka da tashin hankali ya saka momyn kashe wayar cikin faduwar gaba da shiga nata firgicin.

Kiran wayar tayi tareda micewa daga zaunen datake palonta ta shige bedroom dinta tareda rufe kofar

Rabi na daga wayar cikin masifa tace

“Ke banasan hauka da jahilci ki nutsu ki fadan meyake faruwa ne?”

Hadiye toro Rabi tayi cikin Dan daidaita kanta tace

“Aunty Safnah ne ta Suma Kuma Bata motsi

Sam harda numfashi ma batayi.”

Wani mummunan yawun tashin hankali momy ta sauke tareda Jin itama nata jikin na Neman daukan rawa idan Safnah ta mutu yanzu ai ita Kuma ta shiga uku da sauran bugatoci da burikan da Bata cimmawaba.

Migewa tayi daga zaman datai bakin gado tace

“Akwai Wanda yasan halinda take ciki ne?”

“Ah ah” Rabi ta amsa tana waiwayawa duk da palon a rufe yake.

“Ki Jata ki Kai daki kada DD ya dawo ya sameku a Hakan karki bari kowa ya sani ganinan zuwa yanzun Nan.”

Kashe wayar tayi tareda daukan key din motarta da mayafi ko handbag Bata tsaya dauka ba ta fito hajiya Bata sani ba ta fice daga gidan tana Hana kanta daukan duk Wani negative tinani.

Cikin mintina qalilan ta Isa kaantes sbd gudun data zabgo Amma tana shigowa anguwar ta rage gudun kwata kwata a natse ta shigo da motarta har ta iso gate aka Bude mata ta shige tinda ansan mahaifiyar Amaryar Sir DD ce

A natse tayi parking harabar gidan ta farko sbd duk bako baya wucewa da motarsa gate na biyu saidai ya ajeta a na farko masu gidan ne kawai ke wucewa gate na biyu suyi parking motocinsu acan.

Bayan tayi parking hakanan ta tilastawa Kanta nutsuwa da kamun kan dole tana Amsa gaisuwan securities harta shige gate na biyu ta wuce zuwa bangaren dazai kaita bangaren

Safnah.

Tana Isa ko knocking bataiba ta Bude kofar ta shigo Kai tsaye dakin Safnah ta wuce ta taddata har lokacin Bata farfadoba da alama idan baa taimaka mata da gaggawa ba zata iya macewa ma Kila a Hakan.

Ruwa ta fada toilet da kanta ta debo tana fitowa ta zuba mata su tana Kiran sunanta cikin mamakin Abinda yake faruwa da zai sakata shiga wannan halin.

Cikin mummunan hali ta sauke ajiyan zuciya a fizge tareda Bude idanuwanta idanuwanta da sukai jajir take sbd mummunan tashin hankali da masifar datafi mata rayuwar gidan Ababa.

Kasa motsawa tayi tana Neman sake somewa a Karo na biyu momy ta saka hannu biyu tayi mata wata irin jujigawa tana cewa

“Ke kimun bayanin meya faru ne kina Neman sakamun hawan jini da wasi wasi da firgici”

Rabi momyn ta kalla tace ta fice daga dakin ta dawo da kallanta kan Safnah dake magana ita Daya kaman ta zauce a rikice tana sake tsinkewa da lamarin ta sake jijigata ta kira sunan cikin tsawa da babban tsoro tace

“WIh zan taflyata na barki koma wace masifar kika debo ta tsaya kanki.”

Kuka Safnah ke nema ta fasa ko Abinda ya danne kirjinta zai fada Amma ta rasa Dan haka ta dago idanuwanta dasukai jajir ta Kalli momy bakinta na rawar fita hayyaci tace “Momy Bena matar D itace Benazir yar uwata, uwa Daya ta haifemu,

Uba Daya ya haifemu,Nono Daya muka

Sha…itace matar Dawood, itace wadda aka fara daura masa aure da ita, itace uwar Amnah yar Bilal dasuka Haifa ba aure.……Somewa ta sake Yi a Karo na biyu momy da tayi mutuwar zaune itama kusan somewan take Neman Yi Saida Rabi tashigo Jin shiru ta debo ruwa ta zuba musu hankalinta na sake tashi tareda shiga tsoron lamarin Dayake faruwan.

Suna farfadowa sai alokacin Safnah ta Dora hannu Akai zata fasa ihu da kukan balai da masifar Datake ji cikin zuciyarta

Momy da itama duka jikinta rawa yakeyi ta rufe mata baki da hannuwanta biyu tana jijigata cikin bushewan zuciya da tattaro nutsuwa tace

“Ki dawo hankalinki ki nutsu ki tabbatarda benazir ‘yar uwarki ce kika Gani ba gizo ba.

Wallahi tallahi Benazir din Dana sani ce,

Wallahi tallahi itace,

Rayuwata tazo karshe,

Komai nawa yazo karshe,

Identity Dina zai bayyana,.

Daddy zai San ni wacece, zai tsaneni, haiia zata tsaneni, ummen D da shi Kansa zasu tsaneni idan sukasan ni wacece dakuma yanda na wulaqanta mahaifiyata na baro gida,ban taba walwayansu ba,

Yaya aurena da D zai qare?

Qanqame hannuwan momyn tayi jikinta na rawa da fizga cikin mummunan tashin hankali tace

“Momy Dan Allah kiyi Wani Abu akan

Hakan banason na rasa Sunana da matsayina a matsayin Safnah basheer bulama,

Bazan iya barwa Bena D ba wlh, bazan iya rayuwa a yanzu ba a Safnah bulama Dina ba,

Bazan iya barin D ba, Karki bari asan Koni wacece sbd zan rasa

komai Dan Allah momy kiyi Wani Dan Allah.

Yanda jikinta ke rawa tana maganganun cikin

ficewan ‘hayyaci da mummunar tashin hankali

vasaka momy sake jijigata da qarfin gaske

tana cewa

“Ke kiyi shiru babu Abinda zai faru a abubuwan da kika fada,

Babu wata Safnah Ababa a dunia yanzu se

Safnah bulama,

Babu wata macen da Dawood kaante zai

zauna da ita sai Safnah bulama,

Waye benazir?

Matar data gama budewa Dan uwansa qafa ya

gama Abinda yake da ita itace zata warware

mana aikin shekara da shekaru??

Wallahi ko Wanda ya tsaya mata bazai

warware mana aikinmu ba, Kina maganar asirinki ya tonu Zaki rasa komai kin manta tonuwar asirinki shine tonuwar

nawa?

Wallahi Bena bazata lalata mana Aiki ba Koda

Hakan na nufin kawar da ita ne.

A razane Safnah ta dago tana sake jiqewa cikin mummunan zufan dake garawa jikinta

rawa.

A zafafe momy tace

“Kinada Wani tsarin ne bayan na kawar da Bena sbd itace mukullin buduwan sirrinmu,

Idan ta kauce babu Wanda zai haramta aurenki da D,hakama babu Wanda zai ganki

anan bare yasan asalin ke wacece.

Girgiza Kai Safnah tayi tana kallan momyn har lokacin cikin tashin hankali tace

“Momy kawar da Bena a yanzu ba shine

Abinda zamuyi na farko ba,

Bena D Yana aurenta tsawon shekarun Nan batareda ta tare ba hakama tin zuwana na samu tabbacin babu Abinda ya taba sniga tsakaninta dashi na aure Kinga kuwa inada

Chance,

Munada wata Daman.

Cikin tinani momy ta Kalli Safnah tana migewa tsaye tana Dan zagayawa kadan kafin ta tsava gaban Safnah din suna kallan juna tace

“Duk tsanani duk wuya kada ki bari ta taba ganinki,

A yanzu babban abin bugata da burinmu shine D yafara kusantarki kafin Bena din Dan idan bamu samu nasarar kauda ita ba aka Samu akasin ta ganki to tabbas sharia zatayi amfani da wadda ya kusanta a cikinku itace matarsa(inshallah),

Amma duk tsanani duk wuya Muna buqatan bacewan Bena idan har munason cigaba da rayuwa baa gidan yari ba.

Shiru Safnah tayi sbd itama duk tsanani duk wuya bazata yarda tayi rayuwar ukuba ba bayan wadda tayi a baya idan kawar da

Bena shine key din tabbatuwarta zama matar

Dawood kaante da zamanta Safnah bulama to tabbas ta shirya Hakan Koda zasu rasa komai sai ta tabbatarda ita D zai fara sani a mace.

Da wannan kudirin suka samu dawowa hayyacinsu Badan hankalinsu ya kwanta ba

Dan Kuma yanzu basuda kwanciyan hankali matiqar ba ganin sukai sun cimma sabon burin nasu na zamanta wadda ita zata amshe sunan matarsa ta gaskia ko a gaban shiria sbd idan ta rasa identity dinta na Safnah bulama zata amsa sabon identity na matar Dawood kaante.

Dagyar suka Dan seta kansu sbd kowannensu dai vana cikin rashin nutsuwan zuciya hakanan suka fito Palo momy ta Kalli Safnah

Safnah din tayi gaba taje ta sakawa kofar shigowa palon key ta dago tareda cakumo

Rabi wadda idanuwanta suka fito take jikinta

Yana daukan kakkarwa.

Cikin Riga momy ta saka hannu ta zaro wata garamar pistol data saka Rabi fara Sakin fitsari jikinta na sake daukan rawa safnah ta sake shago rigarta momy Kuma ta Dora pistol din a saitin kirjinta ta danna mata ita da karfi har

Saida Rabin ta kusa somewa tace

“‘Wallahi tallahi duk ranar da tsautsayi ya aikeki kika fada ko a toilet ne ke Daya kikai maganar

Abinda ya faru anan saina fasa kanki da kiriinki da wannan Abar.”Kasa ko gyada Kai Rabi tayi sai zubewa datai qasa tana kama kafar Momyn tana cewa wlh zata mutu da wannan maganar babu me ji daga gareta.

Sakinta Safnah tayi sbd duk jikinta har lokacin rawa yake Bata cikakken hayyacinta

Sam zuciyarta ta kasa nutsuwa Jin takeyi kaman kanta zai kama da wuta ta haukacr ga

Wani radadi da zuciyarta keyi na Jin idan Bata cika burinta ba na mallaka D zata iya mutuwa ko rasa hankalinta.

Chapter 67

67

Bayan tafiyan momy kasa zama Safnah tayi ta shige daki ta rufe kanta sai alokacin ta samu ta fasa Kuka tana Dora hannu Akai zuciyarta kaman ma a fashe da balai da masifa da taurin zuciya.

Itama Rabi bayan ficewan momy dakinta dake kofan baya ta kitchen din bangaren ta qarasa ta fada iikinta na rawa tana Neman tinawa kanta Abinda ya faru na wannan mummunan kaddarar.

DD yau Daya dawo ya tarar da palon tsit ba alamarta ba motsinta Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya shige sbd sallan ishai yayo ya shige kawai sbd ciwon Kai dake Dan Jin Yana damunsa kaman zaiyi masa qarfi ma. Tinda ta shige Bata fitoba sai washe gari data kwatanci karfe goma Bena ta Isa fitowa zuwa

Aiki ta fito tareda dage curtain na makeken windon Palo ta zubawa Bena din idanuwanta dasukai jajir ta kwana a zaune tana sakawa da wararwa.

Har Bena ta gama tahowa cikin Wani irin nutsuwa da aji tareda burgewa ta Bude motarta ta shiga ta tayar tabar harabar kaantes din akan Idanuwanta.

Jikinta na Neman sake daukan rawa ta saki curtain din da bin bango ta koma dakinta sbd ko gani sosai batayi sbd baqin cikin Dayake cin wuta sosal a zuciyarta.

*****Bangaren Bena kuwa da safen tana barin gidan da motarta office ta wuce Kai tsaye yau meeting ne dasu Mai mahimmanci Kuma da DDs company Dan haka take Dan sauke ajiyan zuciya Akai akai duk da tasan ba lallai shine zaizo meeting din ba Zeenah ce da directors da sauran manyan company din mutum uku ko hudu zasu wakilta.

Tana Isa lift tahau zuwa sama can inda office nasu na masu company din yake,tana Isa ta shige tareda ajiye handbag dinta Bata zauna ba ta zaro wayarta ta saka Kiran Fahad Dan

Jin ko ya samu isowa kaantes din sbd 10 harta wuce Sosai Kuma 11 ne meeting din.

Ko data gama waya secretary dinta ya shigo ya ajiye mata documents na meeting din kan desk yafara Koro mata bayani cikin turanci yanda aka tsara komai sbd ba bahaushe bane ko hausa sosai bayaji

Dan duka takardun tayi sama sama tana duba wayarta har time yayi ya shigo ya sanar mata time na shiganta meeting din yayi hakama bagin sun iso.

Ajiye wayarta tayi tareda sakata silent ta miqe tsaya tareda daukan documents din da kanta ta fice daga office dinta.

Qayataccen dakin meeting dinsu na

Company na kaantes ta nufa Wanda yake

Nan sama Basa meeting cikinsa sai Wanda zasuyi da manyan masu kudi sanannun da sukeda hannun jari a cikin kamfanin nasu.

Nan zasuyi wannan Taran sbd DDs nada babban share a gurinsu Dan haka tana Isa

Secretaryn Fahad dake kofa ya Bude mata kofar ta shiga lokacin tini Dad kaante da Fahad tareda sauran manyan kamfanin suna ciki itama a natse taje ta nemi guri ta zauna sbd tsaruwan meeting room din kana shiga bazaka ma gane a inda kake ba.

Saida suka share mintina uku kafin DDs suka shigo da sauri aka Bude masa kofar shine a gaba kafin Naseer da sauran manyan DDs gaba kafin Naseer da sauran manyan DDs guda uku suka shigo cikin girmamawa da

Basu tarba me kyau aka tashi tareda miqawa juna hannuwa aka gaisa Yana gama gaisawa da kowa Dora idanuwansa akanta yay ya mata Wani irin kallan Daya sakata Dan dauke

Kai daga kallansa tana Maida kanta kan

Abinda ya kawosu.

Duk Wani motsinta mayun idanuwansa akanta suke suna gigita nutsuwarta tana jinsu suna yawa akanta,

Kasa dagowa takeyi ta kallesa sbd mutanen dake tareda dasu zasu iya fahimtar Wani ga dad kaante a gurin da Wainda ma duk sun haifeta Dan irin wannan matsayin ma Bata Isa ace ta kaisaba ko shekara nawa zatai a Aiki

Amma sbd kamfanin nasu ne ya saka take matsayin da Sam yafi qarfin mace ma.

Kusan awa daya da mintina masu yawa aka share ana meeting din zuwa lokacin tini zazzabi ya Dan kamata jikinta yayi Dan zafi sbd dukan idanuwansa,

Daqyar taga Angama ta kowa ya watse ta fito ahankali Takoma office dinta Kai tsaye.

Tana shiga wayarta ta jefar kan tsadaddiyar desk din office din ko juyowa bataiba taji anbude kofan office din tareda rufewa Jin an saka key ya sakata juyowa da sauri sukai Ido biyu dashi Yana tahowa inda take.

Bata motsaba sbd Daman jikinta a kashe yake kallansa takeyi duka zuciyanta na narkewa sauran kuzarinta na tsiyayewa sbd a yanzu iya ganinsa kawai narkar da zuciyarta yake.

Isowa yayi gabanta ya tsaya Yana kallan cikin idanuwanta dake Tona asirin zuciyarta ya saki Wani gayataccen murmushin da Bai taba sakar mata ba zaiyi magana ta nemi zube masa a gurin sd murmushin Daya mata ya kusan suman da ita.

Tarota yayi jikinta tareda daukanta da hannuwansa biyu ya zaunar kan desk dinta ya tsaya gabanta tareda shige mata sosai suka matse.

Rangwafowa yayi yakai hannunsa Daya ya shafa wuyanta cikin Wani irin sanyi Daya sakata lumshe idanuwa yakai bakinsa ya Dora kan kunnenta Saida ya saki numfashi me dumi a ciki kafin ya a hankali qasa qasa yace

“Daga yau idan Zaki office na kashe saka irin wannan rigan”.

“..va garasa fada Yana zira

hannunsa cikin rigar wadda dohuwar Kuwait jallabiya ce Amma wuyanta Turtleneck ne sai yake ganin ya fidda asalin tsayayun well shaped boobs nata duk da rigan is free size gown har gasa Amma gefe da gefen a tsage yake tin daga qasa har gurin cikinta sai Akai mata slim trouser da ake sakawa aciki.

Ta yankan ya sake zira hannunsa ciki ya shafo shafaffen cikinta da yau yake mata Dan ciwon mara na period dayazo Maya yau din.

Bude idanuwanta tayi ahankali tareda kallansa kaman me koyan magana itama qasa qasa tace masa “ok”

Maganarta ta sakashi Jin jikinsa na zafin

Shima sbd a duk lokacin da zatai magana irin wannan gasa qasa jefasa yanayin zafin jiki takeyi.

Ciro Kansa Dana kunnenta yayi ya sake kallan idanuwanta tayi qasa da idon tana Hana kanta kallansa, ya gangara da idanuwan kan bakinta

Daya Dan sake motsawa ahankali tace

“Zaka yi latti.”

Boyayyan numfashi ya sake tareda Dan ragewa idanuwansa girma Shima qasa qasa yace

“Late for wat?

Kasa dagowa tayi bare Basa amsa Sai dataji hannunsa dake cikin rigarta kan cikin ya motsa zuwa sama a hankali

Ta dago tareda kallansa a kasalance tana

Hana numfashinta Dayake rikicewa fitowa..

Kallanta ya sakasa cigaba da yin sama da hannunsa zuwa saman

Jin zai rabata da numfashinta sbd yanda yake tafiya da hannun a hankali da laushin fatarsa da Dan sanyin da hannunsa yake dashi na Ac Daya dauka take taji tana Neman shidewa ta

Kai hannuwanta biyu ta qanqamesa tana Jan Wani shegen numfashin Daya sake kashesa.

Ranqwafowa yasake Yi Yana sake maimaita mata tambayansa ahankali Yana dosan bakinsa zuwa nata Saida ya Shaqi numfashinta me dumi cikin hancinsa tareda qamshinta kafin ya Dan lumshe idanuwansa dake shiga kasala ya hade bakinsu,saida yayi mata Wani sanyayyan tsotsa na minti Daya kafin ta fara kissing nasa Shima Yana sake matseta jikinsa suna zubar da Rabin kayan kan desk din qasa.

Duk yanda yanda yaso kada ya yamutsa Kansa

Saida Hakan ta faru kusan mintina shida a kan dsk din suna duk Abinda yasan zai Basa Jin dadi da zafin jiki kafin tayi jarumtar dakatar dashi suka dakata kowannensu zuciyarsa kaman zata Faso sbd tsananin Abinda yakeji a zuciyarsa game da dayansa.

Da Kansa ya saukar da ita daga dsk din ya kamo hannunta suka zauna kan couch Ya lumshe fararen idanuwansa dasuka Dan sauya

Yana daidaita nutsuwansa.

Itama shiru tayi tareda Hana tata bugatan nutsuwan bayyana ta kanne kaman babu

Abinda ya faru da ita a mintinan.

Miqewa tayi ahankali cikin nutsuwa ta nufi inda fridge yake ta Bude tareda dauko ruwa mara sanyi sosai ta dawo ta kawo masa.

Bai karbi ruwan ba ita ya juvo ya zubawa idanuwansa yanajin Kansa na daukan zafi sai kawai ya mige tsaye tareda karban ruwan a natse ya Dan sake kallanta yayi mata bye ya fice daga office din.

Yana fita Kai tsaye ya shige lift ya sauka ya fice

Yana Isa mota Naseer ya Bude masa ya shiga ya rufe suka bar kaantes din gaba Daya.

Highbridge yace kawai a wuce dashi sbd

Kansa Daya dauko ciwo kawai.

Suna Isa yace Naseer ya koma office shi zai huta anan idan yagama zai koma gida da

Kansa.

Itama can Yana ficewa daga office din ta zube kan kuiera tareda Dafe kirjinta da zuciyarta ke bugawa da sauri sai alokacin tafara kokarin daidaita nata numfashin itama Daya gama yamutsa.

Da yamma Koda ta koma gida itama ciwon

Kai takeji da zazzabi ga ciwon mara Dan haka wanka kawai tayi Tasha green tea me zafi sosai ya taimaka ya rage mata ciwon marar ta kwanta bacci da wuri.

Shima sai dare ya dawo Yana dawowa ya shige ya kwanta sbd ciwon Kai dakuma tafiyan data kamasa dole a jibi duk akan meeting din dayayi da Kaantes company.

Safnah ma kusan itama ciwon kan me tsanani dana zuciya take fama dashi sod tinda ta shige daki ko palo Bata fitoba gabaki Daya firgice take a tsorace da kaante villa din gabaki

Daya sbd ganin takeyi Bena zata iya ganinta,.

Jin takeyi gaba Daya gidan ya fita ranta so take tabarsa Takoma inda babu ko inuwan Bena

Bare sunanta,

A daki take Kuma a bangarenta da yayi Nisa sosai danasu umme Amma ko waya zatayi

Bata iya daga murya sbd Neman zautuwa

Datake batason aji muryan kada mummunan kaddarar tsautsayi ta afko mata.

Haka ta Kuma kwana a zaune ko kaftawan Ido babu bare Wani bacci,.

Tinanikan dake cikin Kai da zucivarta tini suka saka idanuwanta firfitowa zagayensu yayi duhu cikin kwana biyu sbd rashin rintsawa,

Bayan ruwa Datake Sha Suma hannuwanta na kakkarwa babu Abinda take iya ci,

Duk wannan masifar da balain da tashin hankalin akan Bena,

Shin menene amfanin Bena din a rayuwarta tinda ta zama mukullin buduwan sirrinta da komawa rayuwar dataci alwashin kome zata iya Yi da ta koma wannan rayuwar,

Idan tin farko har zata iya amfani da mahaifiyar data haifeta Dan guduwa daga wannan rayuwar to zata iya aikata komai ga koma waye Dan Hana kanta komawa baya.

Da wannan tinanin ta sake busar da zuciyarta dan cimma mummunan burinsu.

Dan haka ta shirya boye Kanta da Hana haduwanta da Bena duk tsanani duk wuya haduwanta da Bena duk tsanani duk wuya har sai cikin biyu sun samu Daya ko kawar da Bena daga doran duniya ko samun zama cikakkiyar matar da DD zai fara kusanta a tsakaninsu.

Chapter 68

68

Yau ciwon Mararta Bai barta ta samu iya zuwa office ba Dan haka ko fitowa bataiba a daki

Nafisat takai mata breakfast dinta Amnah

Kuma yanzu school yasa Bata zama gida sosai.

Zeenah kafin ta fita office sai data zo dubata cikin kulawa da kauna sosai kafin ta fice, Umme ma haka ta ringa yawon dubata a dakin tana mata sannu

Wanka tayi taci abinci kadan ta kwanta bayan

Tasha magani bacci ya Dan dauketa sama sama sbd ko ta fara idan ta Murda zai ta farka.

Ahaka tayi wunin wayarta ma kashewa tayi sbd Bata bugatan kira, Daqyar tai yinin duk bayan 2 hours saita tashi ta lallaba ta canja pad da pants harta samu da yamma ta iya sake wanka ta shirya sai alokacin ta Umme ta takurata dole taci Tuna macaroni salad tasha ginger mara sanyi ta

Dan fito Palo ta zauna ko zatafi Jin jikin ya sake.

Amnah ganin mummynta ba lafiya tinda ta dawo Nafisat nata dawainiyanta har Arabic teacher dinta yazo Nafisat ta kamata suka tafi

Daman baa barinta ita Daya da Nafisat ake karatun Dan haka suna can sai kusan magrib time na tafuyarsa yayi ya wuce suka dawo.

Ana gama sallan magrib jikinta Yakuma yin dumi sosai taji ta gaji da zaman ta miqe ahankali ta koma dakin tasake wanka da Shirin bacci ta Haye gado tana Dan rufe Ido sbd jikin lokacin har anyi sallan ishal.

Amnah da Nafisat ke Tayata karatun Arabic dinta dakin Zeenah suka koma sbd kada su dameta ganin tana Dan Jin jikin

acan bacci ya dauke Amnah sai kawai Zeenah tace Nafisat tabarta anan taje ta dauko mata kayan bacci ta shiryata ta fice musu daga dakin.

Daidai lokacin Shima ya samu wartsakewa daga ciwon kan Dayake fama dashi tin jiya

Dan haka Koda ya shigo palon babu kowa duk suna dakunansu kowa na Abinda yakeyi

Nafisat ce kawai ta gansa tana fitowa dakin

Zeenah tayi gasa da kanta tareda tausasa murya cikeda girmamawa ta gaidasa.

A taqaice ya amsa a gajarce

Zeenah data Jiyosa ta miqe daga alkin datakeyi a laptop tareda ajiyewa gefe ta zira slippers ta fito palon sanye cikin kayan bacci tana gaidasa da tambayan yaya kan nasa.

Amsawa yayi a hankali cikin sanyi kafin ya Kalli kofan dakin Bena da lazy eyes dinsa

Zeenah na ganin Hakan tayi saurin cewa

“Tin jiya itama batada Ify yau ko office Bata iya zuwaba.”

Kanta ya dawo da lazy eyes din yayi mata kallan tambayan meyake damunta.

Kallansa tasan me yake nufi sbd tasan Dan uwan nata dakyau Dan taka Kai tsaye tace

“Menstrual cramps”

Wani kallan Yakuma sakar mata cikin kasala da mamaki sbd baisan me take nufi ba sosai.

Murmushi ta sake sbd tasan Bai sani din ba tace

“Period, monthly bleeding na mata,haila in Arabic.”

Shiru yayi sbd sai alokacin ya fahimta ya Kuma

Gane.

Ahankali ya gyada mata Kai Yana cewa

“Tana Ina?”

Hannunta ta nuna masa bedroom din tace

“tana ciki, Amnah Kuma tana gurina zata kwana acan.”

Wucewa yayi dakin Kai tsaye ita Kuma ta koma nata dakin.

Yana shiga dakin nata babu haske sosai sanyin da qamshinta duk ya gauraya dakin tana kwance sanye cikin kayan bacci Riga da wando guntaye cinyoyinta masu lafiyan fata da kyan Kallo sai daukan idanuwa sukeyi.

A kasalance ya qarasa gadon Ya tsaya akanta kafin yakai hannu ahankali ya Dan qara hasken wutar dakin ya sake kallanta ganin yanda ta kwanta ta Dan dungule kaman baby Amnah.

Tausayinta ne ya sakasa lumshe idanuwansa tareda zaunawa bakin gadon a hankali ya Kai hannunsa kan hannunta dake kan Mararta ya janye ya Dora nasa a hankali.

Ajiyan zuciya suka sauke ahankali tare,

Shafa marar yayi ahankali Jin jikinta da dumi

Ita Kuma shafan da yakewa marar ya sakata farkawa ta Bude idanuwanta ahankali batareda da motsaba sbd qamshinsa Daya mamayeta yasata Gane shine a tareda ita.

Jin ta farka ya saka shi janyo bayanta ya hadata da kiriinsa suka lumshe idanuwansu a tareda tareda sake sauke ajiyan zuciya kowannensu a boye.

Babu Wanda yayi magana a cikinsu shiru sukai kowannensu na Jin dumin jikin Dan uwansa hannunsa na kan Mararta ya Dena shafawa

Amma dumin tafin hannuwansa Daya hadu da fatan marar nata ya sakata Jin tana samun relief da nutsuwa.

Ahakan shikuma yake shaqan qamshinta da dumin jikinta tareda taushin fatan Mararta ya sakasa lumshe idanuwansa yabarsu a rufe ita

Kuma ahankali bacci ya dauketa a Hakan.

Saida baccinta yayi Nisa sosai ya zameta jikinsa tareda gyara mata kwanciya ya rufeta da lallausan duvet cover ya fice daga dakin lokacin kusan karfe Daya na dare yayi.

Koda ya koma bangarensa Daman baiyi tinanin samun Safnah ba wadda kwana Biyun ta Dena zuwa dakinsa Sam ba kaman baya ba da kusan kullum saita Kai kanta.

Tin daga futarsa Safnah take zaune bakin window na dakinta tana Kallo ya shige bangaren su ummen Kuma Bata motsa a gurin ba duk tsawon awannin har lokacinda ya fito, ta Kalli agogo da idanuwanta dasukai

Wani irin ia na tafasar zuciya da baqin cikin datakeji kaman zai fasa zuciyarta ya kasheta take.

Barin ilkin window din tayi tana dafa bango sbd gafafunta dasukai mummunan rigewa sbd tsayuwa.

Wani masifaffen yaji da radadi idanuwanta ke mata tareda zuciyarta harma da qafafunta.

Tabbas bazata bari ta rayu acikin wannan mummunan halinba zuciyarta ko wata bazatayi a haka ba wIh bugawa zatayi ta mutu dole ta tsaya ta busar da zuciyarta a komai

Amma dai yau taba buqatan tabbatarda babu

Abinda ya shiga tsakaninsa da Bena sbd ma a yanzu kam ko wane abun ya shiga tsakaninsu to kenan ta tabbata sunan Bena din a gurguje zai fita cikin tsari su kawar da itan.

Washe gari ne zaiyi tafiya Dan haka Bena yafara kira a waya yace ta shirya likita zaizo ya dubata.

Cikin nutsuwa da yar basarwa tace masa taji sauki sosai ba laifi.

Shiru yayi sai Kuma yace ta shirya kawai dai likitan zatazo ta dubata.

Taji saukin da gaske ba laifi Dan hakama kusan ita ta taimaka Amnah tayi Shirin school

Abbakar ya tafi kaita.

Wanka tayi itama ta saka kaya marasa takura, pencil jean Daya lafe jikin siraran cinyoyinta sai black sweatshirt din blackpink.

Gashin kanta kaman baby haka ta dauresa tsakiyan Kai ta cusa cikin band ta fito Umme ta hada mata tea da kanta ta Bata ta karba tana Sha a hankalin sai ga Dr Ashley ta shigo

Nafisat datai mata iso tana bayanta

Dayake Umme sun Santa a asibitinsu take Aiki

Dan haka a sake suka gaisa aka zaunar da ita lokacin Zeenah na bedroom Bata fito ba ita

Kuma Umme tana gama gaisawa da ita tace

Nafisat ta kirawo Bena.

Qarasa Shan tea Bena tayi ta ajiye cup din ta taso daga dining ta nufo Palon daidai lokacin Dr Ashley ta dago ta zubawa Bena din idanuwanta sosai tana kallanta ta cikin farin cat eye glasses din dake fuskarta tana kokarin tantance kamanninta.

Bena ma Bata ankara da dr Ashley dinba Saida ta kawo tsakiyar palon sukai arba da juna.

Wani irin sarawa kanta yayi lokacinda taga Dr

Ashley likitar dake duba sumayyah yawanci idan Bilal yakaisu Asibitin kaantes, itace likitar data fara sanar dasu sakamakon cikin Amnah jikin sumayyah.

Neman dakatawa daga bugawa zuciyarta keyi Wani jiri ya debeta idanuwanta na duhu duhu tana Neman zubewa taji ya tarota da kirjinsa ta bayanta tareda rige zagayo cikinta da hannuwansa Yana kallanta cikin kulawa da mamakin Abinda ya sameta.

Tana gain Hakan sai kawai ta qarasa zubewa jikinsa zuciyarta na bugawa a mummunan yanayi.

Umme na gain Hakan hankalinta ya Dan tashi tana cewa

“Subhnallh,jikin ne Kuma? Yanzu fa take da sauki sauki sosai.”

Dr Ashley dataketa tinanin inda tasan Bena din ganin halinda ta shiga yasata dole watsar da tinaninta ta miqe tabi bayan D din dayayi gaba da Bena dauke ilkinsa kaman ya dauki Amnah.

Dubata Dr Ashley tayi babu Bata lokaci sbd ba Wani ciwon damuwa bane kawai dai

Dan su ummen da D din sun bawa ciwon mahimmanci sosai.

Fitowa sukai daga dakin sai alokacin Bena ta

Bude idanuwanta dasuke Neman cikowa da

hawaye zuciyarta na harbawa hannuwanta na

Dan daukan rawa sbd idan Dr Ashley ta tinata

to tabbas akwai yiyuwar mukullin Bude nasu

sirrin ya bayyana sbd itace tasan sumayyah ce

Bilal ke so Kuma itace ta dauki cikinsa ba ita

ba.

Zufa ne ya fara karyo mata sbd sai yanzu ta

Tina da bayyanar wannan gaskiyar zata saka

mutane da yawa tsanarta ciki harda yarta

Amnah da daddynta.

Bayan fitarsu dr Ashley D ta kalla tareda Umme

Kanta tsaye tace

“Ciwonta ba Wani serious abin daga hankali

sosai Akai bane,

Normally wasu matan haka suke fama every

month,wasu Kuma bako da yaushe suke

samun Hakan ba sai sun fara motsawan shaawansu ga wainda Basu taba motsata ba kenan so inaga daga ranar data fara harkan

Aure da mijinta zata Dena tinda Daman bawai ta saba ciwon maran bane.”

Shiru yayi har tayi sallama ta fice Bai furta komaiba

Ita Kuma Umme tausayin Bena din taji da wannan auren da dd babba yaqi cewa komai akansa ya zira musu Ido.

Juyawa yayi yakoma cikin dakin sai kusan bayan mintina arbain ya fito yayi sallama da

Umme ya fice sbd lokacin tafiyansa yayi kusa dole ya isa airport.

Rabi datazo bangaren a kunnenta taji Abinda

Dr Ashley ta fadawa su ummen Dan haka kaman yanda Safnah ta sakata kawo mata duk Wani zancen da zataji Daya shafi Bena haka ta tafi jiki na rawa da sakon munafurcin da Safnah tayi mata alqawarin kudade masu yawa ga kowane Sako me mahimmanci Saida D din yayi mata bankwana itama ya wuce airport kafin Rabi ta isar mata da sakon jikinta ya dauki barin farin ciki da murna Kai tsaye sai a ranar taji ta samu qarfinta ya dawo ta shirya tareda saka facemask da qaton sunglasses ta fito ko bangaren Umme Bata kalla ba sbd kada Wanda ya hangota ta sa motarta ta fada tareda Rabi suka bar gidan tareda kayanta a qaramar lv luggage bag sod bazata iya zama gidaba a tsorace take zata koma gurin mommynta kafin D ya dawo su samu tsayar da shirinsu yanda kota halin Yaya bazaa samu matsala ba.

Chapter 69

69

Safnah na fitowa kaantes Kai tsaye gidan ubanta basheer bulama ta nufa tana tuga motanta tana jujiga qafafunta cikin matsuwa data Isa gidan sbd ganin takeyi kaman zata hadu da Bena a hanya,

Tinda taga Bena a vanzu batada nutsuwan ruhi da zuciyarta,

Kowane sekan,minti ko daqiga datakeyi Bena barazanar rayuwarta ce.

Bazata iva daukan okaci a cikin wannan boye boyenba.

Shin Tayaya ma Bena ta hadu da Bilal ne yayi mata ciki tin farko?

Ababa ya mutu ne kokuwa ya haukace ne da

Bena har tayi ciki a gidansa Kuma take yawo a Raye haryanzu Dan kuwa idan Ababansu na

Raye batajin akwai kudi ko mugamin da zai hanasa daukan matakin rashin Imani akan

Kawo cikin shege gidansa.

Tana Isa gidan aka wangale mata qaton gate din ta shige Mai gadi na mata barka da zuwa ko kallansa bataiba ta wuce ciki Rabi na bayanta suka wuce sashen momy batareda ta biya sashen hajiyarsu ba.

Kai tsaye bedroom din momyn ta wuce lokacin tana waya da yayanta dake can asalin garinsu

Niger akan akwai yiyuwar tazo kusa idan abubuwanta suka fara rauni sbd tareda shi suke yawon dajin bin bokaye.

Safnah na Jin wayar da momy keyi ta zauna kan kujerar dakin tareda rafka mugun tagumi tana tafasan zuciya.

Gama wayar momy tayi ta kalleta tace

“Ki Kwantar da hankalinki na fada Miki ko zamu rasa komai muyi yawo tsirara bazamu bari asirinmu ya tonu ba,

Ke kina tinanin daula kawai zamu rasa Amma ba rasa daulan ne yafi firgita ba Abinda zai biyo baya.

Shiru Safnah tayi sbd azabar zafin dake cin zuciyarta ya hanata iya furta komai.

****Bena sukuku ta wuni a ranar sbd Abu biyu

Daya tsaya ranta ya gajule farin cikinta da walwanta.

Na farko zuwan Dr Ashley ya tinatar da ita tareda tabbatar mata ba lallai gaskiyar haihuwar Amnah na cewan itace ta haifetaba ya boyu har abada,

Tayaya kowa zai karbi wannan gaskiyar?,

Tayaya lamarin zai zo mata?

Ita kanta Amnah idan taji ba itace ta haifeta ba wane halin zata shiga,Kuma kaman batai mata adalci ba sbd ko adduarta iyayenta da suka rasu Basa samu duk da kasancewarta yarinya qarama.

Duka jamaar kaantes dasuke so da kaunarta batasan da wane idon zata kallesu ba.

Numfashi ta sauke tareda rufe idanuwanta ta

Bude ahankali tana sauko gadon da rigarta

Daya cire mata kafin ya tafi.

Canja kaya kawai tayi ta lallaba ta fito ta zauna Palo tareda fara Kallo Dan hana kanta tsananta tinanin da batasan amsar duk Abinda take tambayan kanta ba.

Fruits gananu yanka Nafisat ta kawo mata a bowl me kyau da Dan sanyi kadan tafara ci ahankali tana Dan Kallo sama sama batama

Wani Ganewa sbd hankinta cikakke baya kan Kallon.

Tana Palo aka aka dawo da Amnah daga school

Da kanta taje tayi hidimanta yau sbd Jin takeyi tsananin son yarta ya qaru cikin ranta sbd fargaban ranar bayyanar gaskia ga Amnah dinta tasan ba itace ta haifeta ba.

Gabaki Daya Sauran wunin tareda Amnah a jikinta ta garasa shi ita kanta Amnah din saita tace Mata yau mummy kin qara sona ko?.

Murmushi kawai tayi tana sake shafa bayanta tace “Rabin Raina kullum gara sonki nakeyi koyaushe”

Sai dare ta kunna wayarta sbd Tama manta da wayar kashe take Dan haka tana kunnawa kira na shigowa fitowanta wanka kenan daga ita sai qaramin towel din Amnah da Bata rabo da daurawa wasu lokutan.

Batada niyar duba Kiran sai tagama shiryawa taga waye me kira a Time din.

Amnah Dake kan gado ta Kalli wayar taga ba sunan Amma take ta Gane number daddynta ne sbd duka Numbers dinsa ta haddace su a kanta da farin ciki ta dauki wayar Kai tsaye ta daga tana washe baki da farin cikin ganinsa sd Vidcall ne.

“Daddy shine kayi tafiya Ina school ko”

Ajiyan zuciya ya sauke a hankali tareda kallan

Amnah din yanajin nutsuwa nashigarsa sbd ganinta kawai farin ciki da nutsuwa yake sakasa.

Cikin nutsuwa yace

“Angel ta yafewa Daddy next time zai

kiyaye,kina lafiya right?

Murmushi tayi tana cewa “ok na yafe Amma

nxt time bazan yarda ba, lafiya na kalau”

Ajiyan zuciya ya sake a salihance kafin ya

Danyi shiru na sakanni tukuna ya Bude baki

cikin nutsuwa yace

“Mummynki fa?tana lafiya right?I mean taji

sauki ta Dena ciwo da kukan ciwo??”

Amnah dariya tayi tareda juya cameran

zuwa ta baya Dan yaga mummyn tata dake

zaune gaban mirror kan kujera tana shiryawa

cinyoyinta dake bayyane suna daukan Ido ta

gama shafawa tsadaddan body oil da Dan body spray a jikinta.

Zubawa Bena din idanuwansa da sukai laushi

tinda yazo yayi yanajin sauran nutsuwan da

baigama samuba tana qarasa shigarsa kaman

Wanda Akewa caji haka yaji energy dinsa na

dawowa daidai.

Ganin yanda yayi shiru ya zubawa mummy

dinta idanuwa Yana kallanta cikin nutsuwa

batareda yace komaiba.

Kallan mummyn nata itama tayi ta dawo da kallanta kan daddyn tace

“‘Daddy zakayi Kuka ne sbd mummy ba lafiya??

Taji sauki fa,ta warke gashinan tana komai da

kanta lafiya kalau”

Sai alokacin Bena ta juyo ahankali ta kalli

Amnah din sbd batasan camera din baya na

Aiki akanta bane

Hannunta Daya ta dada ta Dora kan baki tayi mata alaman tayi shiru.

Shi kuwa Hakan datai ya sakasa sakin murmushin da baiyi Niya ba na maganar

Amnah da ita kanta Abinda tayi din.

Amnah ma dariya tayi zatayi magana

‘Daddynta yayi mata alaman shima tayi shirun karta fadawa Mummy din Yana camera na kanta.

Gyada Kai Amnah tayi tana dariya tareda gyadawa daddynta Kai.

Ya jima a Hakan Yana kallanta sbd iya kallan ma a yanzu dayake nesa ya ishesa.

Bena datake Jin kaman idanuwansa na kanta sbd aduk lokacinda yake kallanta tana Jin kallansa kanta,

Da zata saka kaya hakanan taji Bata sakeba sai kawai ta koma closet na kayansu ta shiryo a can ya fito sanye da Riga da wandon bacci guntaye iri Daya Dana Amnah ta garaso gadon lokacin Amnah tafara gyangyadi Kuma har lokacin Kiran Bai Yanke ba.

Cire wayar tayi daga hannun Amnah ta gyara mata kwanciya kafin ta hau gadon ta rufe

Rabin jikinta ta dauki wayar ahankali zata duba

Abu sai ganinsa tayi zaune sanyeda gananun kayansa dayafi sakawa Yana Shan Abu a cup ahankali da alama ko coffee ko wani abin me zafi sbd Dan tiririn Dayake Yi.

Hankalinsa baya kan wayar Shima Saida ya Dan juyo sai yaganta zaune itama tana kallansa ta Dan dauke Kai ahankali sbd batai niyar barin yaganta tana kallansa ba jikinta duk na mutuwa.

Kallan da yayi mata ya sakata sauke Kai ahankali kafin ta Dan dago kadan tace

“Barka da Isa Ify”

Bai amsaba Saida ya kurbi Abinda yake hannunsa a natse kafin ya kalleta ya amsa

Yana cewa

“Yaya jikinki?”

Kallan juna ta dago sukai kafin ta amsa tana

Dan narkar da idanuwa sd hakanan taji tana tinawa da yanda ta ringa Jin azabar marar kwana Biyun.

Duk yanda yaso suyi fira ko magana sosai

Basuyi ba sbd baisan me zai ringa cewa ba,shi

Idanuwansa ne maganarsa,zai iya wuni Yana kallanta da idanuwansa masu shegen kashe jiki da gigitata Amma bazai iya jero kalmomiba

Dan baisan mezaita fada dinba.

Da kanta ta fahimci baisan me ake fada ba kokuma baisan me zai fada din ba Dan haka tayi masa goodnight ahankali tareda katse

Kiran ta ajiye wayar tana Dan dafa kirjinta saitin zuciyarta ahankali tanaiin wannan Karan bugawan datakeyi cikin sanyi da nutsuwa da Wani irin so Mai tsananin gaske na nutsuwa.

Zamewa tayi ta kwanta daidai tareda Jan rufarta har zuwa kirjinta tana lumshe idanuwanta da shi kawai suke bugatan Gani zahiran a wuni Daya kawai Jin takeyi kaman yabarsu kenan itada Amnah dinta.

Shi Kansa a can bangaren ajiyan zuciyan ya sauke me Dan sanyi tareda ajiye cup din hannunsa Yana rufe Ido sbd Jin kaman Kansa bazai iya daukan gudanar da har sati biyu a tafiyan ba.

*****Washe gari Bena bayan tafiyan Amnah school itama shiryawa tayi Dan tafiya office sbd zuwa office dinne zai hanata zama cikin tinaninsa da jiya zuwa yau yake Neman sauya mata nutsuwa.

Breakfast sukai dukkaninsu tare a dining tanaji

Umme na tambayar Safnah kwana biyu Bata shigowa ko lafiya Kuma Bata kirata a waya ba.

A bakin Zeenah sukaii wai ta tafi gida sai D ya

dawo.

Da mamaki Umme tace

” To shine bazata kira ni ta fadamun ba?

Ni banma San ta tafi gidan ba Dan ko

Momynta Bata fadamun ba hakama hajiya munyi magana da ita jiya Bata fadan ba,

Ke waye ya fada Miki? Batareda Zeenah ta Dena cin soyayyar doya da egg tareda chicken sauce din gabanta ba tace

“Umme meye na damuwa bafa yarinya bace, Lokacinda tabar kaantes na hadu da motanta nikuma na dawo ta waya take sanarmun gida zata kafin D ya dawo.”

Shiru Umme tayi tana mamakin Safnah din ta yanda koba itace ta haifi Dawood miinta ba ai ita mamanta ne tinda ganwar mahaifinta ce

Amma Bata fada mata ba babu Wanda ya sani ta bar kaantes ta tafiyanta,

Da zaman ne ita Daya bazata iya ba da sai itama ta dawo Nan bangarensu harya dawo tinda akwai isasun bedrooms lafiyayyi anan din.

Bena dai Bata dago ba bare nuna tasan ma me ake magana Akai bare Kuma saka baki sbd har cikin ranta mantawa takeyi was lokutan da yanada wata matar sbd ita tin farko ba guri

Daya suke ba so koya koma gurin matarsa

Bata tinawa.

Breakfast dinta tagara cikin nutsuwa kafin ta miqe tayiwa Umme sai ta dawo

Cikin kulawa itama ummen tayi mata adduan dawowa lafiya.

Tareda Zeenah suka fito ita Saida ta biya gurin dd babba ta share kusan 30 min acan kafin ta fito lokacin Zeenah ta jima da wucewa itama motarta ta nufa ta Bude ta shiga ta fice daga kaantes din.

A office dukkaninsu suka wuni sai yamma suka dawo kowa da gajiyansa Da aikin gabansa Dan haka kusan kowannensu ma a dakinsa yayi dinner Bena ce ma Bata Wani jima tana duba abubuwa ba bacci ya dauketa

Dan haka Koda ya kira Amnah ce ta daga ta nuna masa Bena din datai bacci Sai dayayi mata kallan mintina shida kafin ya kashe wayar Amnah ma lokacin baccinta yayi ya kwanta jikin mummynta tareda shige mata magalqaleta tukuna bacci ya dauketa.

**Safnah da momy gabaki Daya acikin kwana biyun sun haukace Basa cikin nutsuwa da kwancivar hankali sbd ta tabbata bokan momy ya mutu inji ganinta Daya fara zuwa dubo mata bayan sunyi waya sbd baa shiga dajin

Kai tsaye sai andubo Maka sbd hadarinsa.

Tinda labarin nutsuwarsa yazo musu suke

Neman zaucewa sbd duk garyarsu da burinsu akansa yake,

Koda suke maganar kashe Bena kisan da bazaa Gane sune sukai ba zasuyi mata Amma yanzu da alama ‘danyar kisa zasu mata ta jininta a hannuwansu.

Chapter 70

Mutuwar bokan Jin sukai gwara ace Wani jininsu ne ya mutu,

Safnah tawar jiki ta ringa zubawa tana Neman kamuwa da ciwon zuciya Dana qwaqwalwa.

Wuni biyu da kwana daya sukai babu me cikakken hankalin kama Wani tinanin duk da sun San komai rintsi dole Wani hanyar zasu

Kuma samowa tinda ba tsayawa zasuyiba su rissina.

Cikin baqin ciki Safnah dake zaune palo ta Kalli momy idanuwanta jajir tace

“Momy dole cikin gaggawa fa zamu San abin

Yi,

Ina cikin hadarinda kowane lokaci wlh Bena zata iya ganina,

Tsawon shekarun Nan Muna auren miji Daya nida ita, Nazo na tare gida Daya nida ita tsawon lokaci

Muna guri Daya Muna rayuwa rabo da Sa’a yasa bamu taba ganin juna ba sbd Allah Yana

Sona yasa ko a yanxu din nice na ganta Bata

Ganni ba,bansan tsawon Wani lokaci Saar Nan zata bini ba,

Kada sa’a ta tayanke batareda munyi Shirin hakanba,

A baya banajin komai nake rayuwata sbd tinanin suna can cikin rayuwar Dana barsu acikinta bantaba tinanin ko a masu aikin irin dunivarsu Kaantes zan samu Daya daga cikin yan uwanaba shiyasa na sake bana shayin komai Dan nasan duniya biyu mabanbanta muke rayuwa ni da su,

Momy wIh tallahi asalina na bayyana Ababa salya mun ratayar da bazan mutu ba bazan rayu ba,

Momy sunan Ababa kawai idan na Tina bana iya Jan numfashi batareda azabtacciyar tsoro da tashin hankali ba..

Cikin tata masifar data addabi zuciyarta momy ta katseta da jajayen idanuwanta itama tana cewa “So nawa zan fada Miki ki Dena Kira mana ranar tonuwar asiri?

Kin manta inda dukkanmu muka fito?

Ni kaina anfada Miki ko rayuwar Dana fito a baya Ina bugatan tinawa bare fatan komawa

Wallahi bazan yarda na koma ba,

Asirin da kike magana akansa idan ya Toni nice zan fara kwabewa nabi hanya da hauka kafin ke,

Mutuwar Bashara ba snine karshenmu ba,yanzu ne zamu tashi tsaye muyi Aiki da qwaqwalwa da qarfin zuciyarmu,

Waye Benazir da zata kashemu da ranmu tsaye?

WIh ba Bena ba ko ‘yarta sai mun janye sbd kada ta tafi ta barmana baya da qura sbd yanda Dawood Bai iya hada komai da kowa da yar.

Cikin Dan Jin sassaucin zafin dake cinta

Safnah tace “Daman Banda niyar a bar ‘yar,tabi uwarta su tafi sbd barinta na nufin inada sauran alaga da dangina na baya”

Cikin zurfafa tinani sosai da tabbatarda cikin biyu bazasu yarda su rasa duka ba momy ta sake juyawa ta juya tinaninta tace

“Ko zamu rasa komai na bulama bazamu yarda mu rasa DD ba sbd idan muka rigesa ta

– hanyarsa zamu tsira daga sauran tonan asirin

Cikin bagin ciki sabo Safnan tace

“Tayaya bayan kallan namiji yakemun,

Wata na nawa a gidan Bai taba barin ko kalan gadon Dayake dakinsa na sani ba bare shiga,.

Wallahi wannan tafiyar da yayi dole kafin ya dawo muyi shirinda babu Abinda zai hanasa bani matsayin matsarsa. Jiniina Kai momy tayi tana cewa

“Wannan matsalar na gama da ita sbd sakonmi Yana hanya,

Idan kika ga ya dawo Bai mayar dake matarsa ba to wih ba namiji bane mace ne kokuma

•babu mazakuta a jikinta,

Maganin biyu ne dayan na bulama ne zamu aje Incase,

Idan asirin gaskiyarmu na ke ba jininsu bace ya kusa bayyana aikasa kawai zamuyi batareda sanin kowa ba ko Ganewa kowa a gama zaman gaisuwa a raba gado a kwashe

Rabi a baki matsayin yarsa qwalli Daya mu San da Benazir din zamuii mu huta.

Sai alokacin Safnah taji sanyin ranta ta sauke ajiyan zuciya da numfashi a tare tana Jin sauran hope da nutsuwa na shigarta ta saki dariyan Jin dadi da farin ciki zatayi magana idanuwanta ya sauka kan hajiyarsu dake kofa tsaye kaman ta Suma tana kallansu hannunta riqe da wayar data gama da Umme akan safnah Bata sanar dasu zata koma gida ba ta taso tazo Dan yiwa safnan fada kunnuwanta suka Jiyo mata Abinda yafi karfin rayuwarta da tsufanta.

Ganin kallan da Safnah kewa kofa idanuwanta na Neman fadowa qasa jikinta duka Yana

• daukan rawa ya saka momy hadiye tata dariyar ta juya taga hajiya tsaye tana kallansu.

Hawaye ne kawai suka gangarowa tsohuwar ta Kalli momy bakinta na rawa zuciyarta na radadi tace

“Me kunnuwa na suka jiyemun Nuratu?

Balain da masifar da muke ciki kenan bamu sani ba a hannunku.

Kallan juna sukai tareda nufota Safnah na

cewa “Hajiya bakiji daidai bane ba…

IIA

Wani gigitaccen Mari ta saukarwa Safnah din

Daya sakata kifewa qasa ta dago idanuwanta nayin ja ta Kalli hajiyar zatayi magana momy tace

“Yanzu da kikaje hajiya to me zakiyi?

A zafafe ta Kalli momy tace

“Zakiga Abinda zanyi”

Juyawa tayi tana Bude wayarta Dan saka kira ko taku biyu batayi ba momy ta dauko garamin glass stool din dake palon me shegen nauyi ta daga da qarfi ta kwada mata bayan kanta

Saida glass din ya fashe duk nauyinsa. Cak hajiya ta tsaya kaman Bata daku ba ta Dan motsa kadan wayar hannunta na faduwa qasa jini ya fara zuba da garfi ta Yanke jiki a gurin ko waiwayowa batai ba.

Da sauri jiki na rawa Safnah ta tashi tana kallan hajiyar kafin ta Kalli momy muryanta da-jikinta na rawa ta ce

“Momy idan Bata mutu ba zata fadawa dady da kowa gaskiyar Abinda taji,. Kuma ya zamuyi yanzu da ita Idan aka sameta anan haka zaa ce mun kashe,innalillahi,momy wlh banason zuwa prison,momy Bena zata samu DD ni Ina prison, Dan Allah momy ki.

Tsawa momy ta daka mata tana cewa

“Haukarki zata saka asan munyi Wani abin ki nutsu babu Abinda zai faru damu.”

Safnah na Jin Hakan tayi shiru suka kama hajiyar zuwa bakin kofar shigowa palon suna ajiyeta kwance kanta daidai kaifin stairs.

Wayarta Safnah ta dauko da sauri bayan ta saka hannunta leda kadama Wani abin ya biyo

baya a ga hannunta a jiki.

Cikin hannunta suka Bude suka saka mata wayar.

A tare suka koma palon suka share glass din cikin sauri bayan sun share Sabon towels uku suka dauko suka goge jinin Daya zuba suka zuba tirarika da kayan qamshi sosai.

Glass din dasuka kwashe toilet sukaje sukai floshin nasa towels din Kuma a cikin toilet momy tahau konesu itama Safnah ta fito ta tsaya kan hajiyar ta kwada Wani irin ihun Daya saka masu aikin gidan kaf fitowa tafara ihu tana cewa hajiya ta Fadi a stairs da sauri aka fara salati ana ihun Kiran sunan hajiyan.

Momy kuwa a cikin toilet kaman hayagi zai kasheta haka ta Kone towels din tsaf ta Bude window hayaqi ya fita ta wanke toilet din tas da kanta ta fesa tirarika ta fito

Lokacin tini driver da Safnah dake Kuka suka kwashi hajiyan zuwa Asibiti.

Hankali tashe masu aiki sukaiwa mom data tambayi meke faruwa taji hayaniya tana toilet.

Tanajin haka itama hankalinta ya tashi ta zari mota ta bisu Asibitin tana saka Kiran bulama ta sanar masa hajiya ta Fadi a stairs bayan kanta ya bugu anyi asibiti da ita.

Hankalinsa tashi yayi sosai gashi Yana porthacort Dan haka Shima Umme ya kira ya sanar mata.

Koda aka Isa asibiti da hajiya ko dubata baa fara Yi ba Rai yayi halinsa take Safnah ta ringa

Kuka tana rusa ihu,

Momy ma haka ta ringa kukan tana Kiran sunayen Allah a baki.

Umm Koda ta iso Asibitin tareda Zeenah hajiyan ta Riga ta rasu Dan haka sai kawai ta

Yanke jiki ta Fadi.

Daukanta Akai aka shiga emergency da ita

Bata taimakon gaggawa.

Su Safnah kuwa shiga taitayinsu sukai suna

Kuka suna waige waige sod fargaba da sanin akwai yiyuwan zuwan Bena dole Asibitin sbd

Umme.

Rasuwar hajiyan yasaka baa tsaya Wani kwaie kwaie ba da sauransu tana rasuwar aka lullubeta ana jiran lokacin daukan gawanta.

Cikin ganqanin lokaci Rasuwan hajiyan ta zaga dangi da abokan arziki.

Alh basheer bulama kuwa a ranar da yamma

•yayi Siya ticket shida sauran matansa na

tahowa.

Rashin nutsuwan da Safnah ke ciki na tsoron haduwa da Bena ya sakata somewan qarya momy ta kwasheta suka koma gida takaita ita Kuma ta dawo sbd kada a ga sun tafi du dukan.

Daga momy har Safnah Kuka suka ringa yi ba tsayawa har sai da idanuwansu sukai sintim,

Bena itama tini ta iso Asibitin Basu Wani jima ba aka sauyawa Umme Asibitin zuwa ta kaantes.

Cikin dare Alh basheer ya iso a cikin dare Akai komai aka Basu gawan hajiya da har lokacin kanta na Dan tsiyayan jini.

Duk girma da shekarunsa sai dayayi Kuka

sosai gaban gawar mahaifiyarsa

Umme ma dake asibiti kusan a cikin tsananin

hali kukan takeyi sosai na rashin uwa da ita

Daya ta rage musu.

Bena ce a tareda da ita asibiti Zeenah Kuma

tana gidansu Safnah din sbd zaman gaisuwa.

Anyi janaizarta da safe karfe Tara aka kaita

makwancinta aka dawo

Haka aka ringa karban gaisuwar daga manyan mutane da mokata da abokan Hulda.

Familyn kaantes kusan duka na kusa da nesa

sunzo sunyi gaisuwa dad kaante kuwa sai

dayayi kwana uku a Jere Yana zuwa kullum ya

sake musu gaisuwan tinda sirikarsa ce Shima

ya rasa.

Jinyan momy kwana biyu ya saka Bena Bata

taba leqa gidan gaisuwan ba har Saida Akai adduan uku aka watse zaman gaisuwar ranar

Kuma aka sallami Umme Dan haka Kai tsaye can gidan Zeenah ta wuce da ita

Bena Kuma Dayake ranar Zeenan ta rigata shiryawa sai ta wuce Asibitin tinda Angama zaman karban gaisuwa tanajin an sallami ummen gasunan dawowa saita Jira su dawo din Bata bisu ba bare tasan zasu biya can gidansu Alh basheer din.

Bayan sunyi gaisuwa da kukan rashin da sukai itada Alh basheer ta dawo gida Shima sauran matansa washe gari suka koma tinda Angama zaman shi zai sake kwana biyu a garin kafin ya koma can ma yayi karban gaisuwan wainda

Basu samu zuwa Nan din ba sbd Nisa.

Tinda Umme ta dawo suke kulawa da ita sosai kaman ‘varsu sbd tausayin damuwan data shiga na rasuwar sosai,

Taji radadin rashin hajiya fiyeda yanda tayi tinanin zasu iya jure rashinta.

DD ma kullum saiya kirata a waya ya ringa nuna mata kulawa sosai tareda Bata hakuri akan juriya.

Da haka ta Dan sake sbd ganin ta saka yaran cikin damuwa.

Chapter 71

71

Saida Umme ta warware sosai ta fara komawa daidai suka koma zuwa office daga Bena har

Zeenah Kuma har lokacin Safnah Bata dawo ba tana gidansu dad dinta ya koma duniyarsu ta dawo sabuwa a gidan ba hajiya yanzu sune komai da kowa tareda iKon dukiyarsa ta Nan da kadarorinsa na Nan Dan haka tini burinsu da zuciyarsu ta gara qarfafa a yanzu dukkanin shirinsu akan Dawood yake dawowarsa kawai suke bugata.

Bayan hankula sun kwanta sati biyu cif da rasuwar hajiyan daga Umme,dad kaante da dd babba har Safnah da Bena suna tsammanin dawowar D Amma shiru taflyan tasa ta gara kwanaki Amma tinda ana jinsa kalau sai kowa

Bai damu ba sai Safnah data matsu ya dawon sbd abubuwan dasuka haukace tanasha baji ba Gani.

Bena itace wadda tafi kowa kewansa haka

Kuma itace wadda tafi kowa boye hakan,

Kullum kusan a office take wuni sai yamma ta dawo tana dawowa Bata Wani zama sosai da dare yayi ya kwantawa bacci da wuri.

Wasu lokutan Kuma gurin Annenta take zuwa ta wuni ta dawo Saida Kuma a hankali hakurin Ababa ya fara qarewa sbd gabaki

Daya ya dawo Ababansa kullum Rena masa hankali kaantes keyi da cewan ya jira Bena ta karatu ta fara Aiki zaa yanka masa kudin albashin da duk wata zaa ringa Basa gashi ta gama karatun kusan tun shekaru Amma babu

Abinda yaji ko ya Gani,

Annenta Dayake ragawa sbd kada ya Bata rawarsa da tsalle a gaban kaantes din tini ya dawo da dokokinsa a cikin haukanta ma aikin gidan ake sakata tuquru. Duk Abinda Bena ta Tara nata na kanta ta tattara ta Basa kudi masu yawan gaske Dan ya Bata Anne ta nema mata lafiya Amma ya hanata Kuma ya karbe kudin.

***Abubuwan da Safnah takesha sukai mata yawa tareda sakar mata ciwon ciki me tsanani da Amai Dan haka Koda tai wunin ranar da zazzabi da ciwon cikin ta wuni me Dan tsanani.

Su Umme na ji Umme taje ta dubota lokacin su Bena na office Dan haka da duka dawo da dare Umme ta fada musu sbd Zeenah ta samu taie ta dubota.

Yau da safe very late ta iso office sbd sai data aje Zeenah gidan Alh basheer bulama din kafin ta wuce office da niyar idan ta tashi zata biya ta dauketa su wuce gida sbd yau bazata lega office ba zata Dan wuni gidansu Safnah din.

tana zaunawa ta dauko wayarta zata saka silent kira ya shigo wayar ta duba a hankali sai taga sunan Ababa.

Faduwa gabanta yayi hannuwanta na Neman daukan rawa ahankali sbd har gobe babu ranar da zasu hadu da Ababa Basu shiga wannan halinba,

Tsoransa Daya dasa musu a cikin jininsu yake har abada bazasu Dena ba idan ba Wani miracle din ya suka ba duk Abinda zasu zama kuwa.

Daga wayar tayi bugun zuciyarta na qaruwa cikin tsoro da fargaba.

A natse ta gaidasa kafin ta garasa baya bugatan gaisuwar yace “Kizo da motarki yanzu a nemi uwarki haukarta ta tashi tabi hanya.”

Yana gama fadan Hakan ya kashe wayarsa zuciyarsa na tafasa sbd ba garamin azaba zaiwa Annen ba idan ya kamata wannan

Karan,

Haukarta ta ishesa.

Gaba Daya ita kanta ta zamar masa lalurar da kashinsa yafi masa daraja akanta,

Barin da yayi mata a gidansu da Bai saketa yakaita bola da Kansaba sbd idan tana hannunsa ne zai juya Bena yanda yakeso tayi duk Abinda yace babu haufi.

Amma ko yanzu zai nuna musu su dukan

Yana Nan Ababansa babu Abinda ya sauya.

Bena cikin tsananin damuwa da tsoro ta miqe ta dauki wayarta takira Zeenah tace bazata samu zuwa daukanta ba gidansu zata

Annenta ba lafiya sosai

Bata Jira amsan Zeenah dinba ta kashe wayarta tana kokarin barin office din.

Zeenah dake tareda Safnah da momy duk sunji Abinda ta fada Dan haka Safnah taji ta warware sbd tafi kowa sanin Anne itace weakness din Bena me qarfin gaske.

Daki momy ta wuce tana Amsa wayan da babu kira bayan tashige ta qwalo Kiran Safnah wadda itama Abinda momyn ke tinani itama shi take tinani wato samun Saar Bena a daidai wannan gabar.

Zeenah data kasa nutsuwa sod sanin yanda duniyar Bena takeso takeji dashi kaman

Annenta Dan haka key din motar Safnah ta karba ta kama hanyar office Dan cimma Bena su tafi tare.

Tana ficewa Safnah ta karbi key din motar momy suka fito tareda momyn sbd hanyar gidansu zuwa gidan Ababa zasu Riga Bena da zata fito daga office Isa express titin na bavan gari Wanda babu mutane kwata kwata yanda ya kamata sbd dama tin farko kaman daji ne haka Ababa ya zabi zama gurin sukai rayuwa anan.

Yanda Safnah ke tuqi kaman hannuwanta na rawa da qafafunta sbd titin zuwa gidan Ababa. da suka kama Wanda shekarun baya suka ringa dawowa mata zuciyarta na bugawa kaman zata fado.

Dishi dishi take Gani a idanuwanta sbd mummunan tsoron Dayake cikin jininta Daya taso na Ababa.

Fuskan Ababan take Gani akan duka titin

Datake tafiyan

Rawa motan ta faravi dasu sbd hayyacinta

Datake Neman

Bata ankaraba tayi sama da Anne data hawo titin Kai tsaye tana kalle kalle da Kiran sunan Benazir data kusa kawowa tana hango

Annenta tana qara gudun motarta ta kawo gurinta akan idonta motar tayi sama da Annen ta watsar gefen titin

Take Wani duhu ya mamaye idanuwanta ta saki tata motar itama tana kokarin Yi daji

Momy na ganin haka ta jijiga Safnah da batasan waye ta Kade ba sukai kan motar

Bena da tasu motar suka daka da qarfi suka qarasa tura dajin da gudu sosai yanda abin zaiyi munin da wuya a rayu.

Basu bi takan Anne ba Safnah da kanta ke juyawa sosai da abubuwa da yawa kaman zata haukace take ji ita bayan motar Bena tabi da gudu sbd tabbatarda ta tafi kada su bar baya da qura.

Momy kuwa kan Anne tayi ta Gani ko ta mutu ko tana Raye ga mamakinta sai taga matar ta tashi gefen kanta na jini tana kokarin tafiyarta. Baya momy tayi da sauri sbd Gane mahaukaciya ce suka kade sbd alamunta sun nuna.

Safnah kuwa kan motar Bena dake tsananin hayaqi ta nufa ta ta fara kokarin Bude motar

Dan dubawa.

Sama sama Bena ke Jin iska da motsin abubuwan duniya ta Bude idanuwanta daqyar ahankali tana ganin dishi dishi duhu duhu jini na fita hancinta da fuskarta duk Daya Bata jinin.

Murfin kofar motar da aka Bude ya saka haske shiga cikin idanuwanta tafara ganin fuskar

Safnah ahankali tana bayyanar mata. Cikin mummunan hali take kanta na juyawa

Amma Kuma idanuwanta dasuka nuna mata Safnah sake shigar da ita mawuyacin hali sukai motsawa takeson Yi ta kira sunan

Safnah Amma ta kasa.

Safnah na ganinta cikin wannan halin taji toro da bugawan zuciyarta na tsananta ta juya da sauri zata gudu takira momy sbd ita bazata iya garasa Bena din da hannuwanta ba saidai momy ta qarasata.

Tana juyawa Bena tayi Wani garfin halin rigo hannunta Daya da hannunta dakeda jini sosai a wahale ta kira sunanta tana cewa

“Safnah kece???

Safnah, Safnah kece safnan Anne??

Wasu hawaye masu tsananin zafi ne suka gangarowa safnan ta kasa juyowa ta Kalli

Bena din.

Sake Kiran sunanta Bena tayi tana cewa

“Safnah ki taimaki Anne,

Ki taimaketa ki duba Wani ya kadeta Dan Allah idan kece kiyi magana naji”

Juyowa Safnah tayi hawayen da yamutsin zuciyarta na qaruwa ta kasa magana sai hawaye ta gyada Kai ahankali tace

“Nice Safnah Amma ba safnan Anne ba”

Wasu hawayen azaba da Fita hayyaci masu zafi suka gangarowa Bena ta Bude baki tace “Ni kadai na ragewa Anne Dan Allah idan Wani

Abu ya sameni Safnah ki kula da Anne tana

bugatan taimako da kulawa..

Jin Hakan ya saka Safnah kallan Bena din da

mamaki ta dawo da sauri tareda tarota jikinta

tana girgizata tace

“Ina sumayyah?

Ta rasu gurin haihuwan Amnah…

Wani irin zufa ne ya karyowa Safnah tana

kallan Bena hankalinta na Neman kasa

fahimta Amma Kuma tana bugatan fahimtar

komai kafin Bena din ta mutu,

Meya hada haihuwan Amnah da sumayyah

Kuma. “Ni kadai na ragewa Anne Dan Allah idan Wani

Abu ya sameni Safnah ki kula da Anne tana

bugatan taimako da kulawa..

Jin Hakan ya saka Safnah kallan Bena din da

mamaki ta dawo da sauri tareda tarota jikinta

tana girgizata tace

“Ina sumayyah?

Ta rasu gurin haihuwan Amnah…

Wani irin zufa ne ya karyowa Safnah tana

kallan Bena hankalinta na Neman kasa

fahimta Amma Kuma tana bugatan fahimtar

komai kafin Bena din ta mutu,

Meya hada haihuwan Amnah da sumayyah

Kuma. “Ni kadai na ragewa Anne Dan Allah idan Wani

Abu ya sameni Safnah ki kula da Anne tana

bugatan taimako da kulawa..

Jin Hakan ya saka Safnah kallan Bena din da

mamaki ta dawo da sauri tareda tarota jikinta

tana girgizata tace

“Ina sumayyah?

Ta rasu gurin haihuwan Amnah…

Wani irin zufa ne ya karyowa Safnah tana

kallan Bena hankalinta na Neman kasa

fahimta Amma Kuma tana bugatan fahimtar

komai kafin Bena din ta mutu,

Meya hada haihuwan Amnah da sumayyah

Kuma. Kuka ta fasa Mai taba zuciya da bayyanarda kewa da kaunarsu me tsanani ta rungume

Bena din tana cewa

“Bena karki tafi Dan Allah kibarni da Anne tinda kince sumayyan ta mutu,

Na dawo gareku yanzu bayan gwagwarmayar danasha Dan Tara Abinda zanzo na fansheku na tararda wannan mugun ganin”

Kuka Bena ke son Yi Amma azabar datakeji ta hanata cikin wahala.

Kaman daga sama aka jeho Anne gurin tana ganinsu ta qaraso gurin Benazir da gudu saidai kafin ta tabbata tayi Ido biyu da Safnah wadda itama ita take Kallo jikinta na wata irin rawa. Cikinta Anne tayi ta qanqameta tana Kiran sunanta Dana sumayyah Dana samirah duk lokaci Daya sbd ta manta waye acikinsu take gabanta.

Safnah na ganin haka ta janye da gudu zata bar gurin Anne ta bita lokacin tini Bena ta

Sume a gurin.

Cakumota Anne tayi tana Kiran sunayensu su ukun Banda Bena.

Momy dataga Annen zata saka a cimmusu gurin Jan Safnah da Annen taqi saki tayi dukkaninsu ta tura mota suka bar gurin sbd hayaqin motar Bena Daya fara yawa.

Suna barin gurin Zeenah na isowa da motarta kaman ance ta duba gefen hanya ta hango mota na hayaqi da sauri tayi parking tana yiwa wata motan data kawo hannnu suka tsaye ana gangarowa aka duba taga motan Bena da ita

Ciki

Hankali tashe aka fidda Bena din mutane tini hayaqi yayi alerting nasu suka taru.

Ana cire Bena motan tafara kamawa Dan haka jikin Zeenah har Wani mazari yake da jüjiga sbd tashin hankali.

Momy da Safnah kuwa Nisa sukai sosai da gurin Safnah ta Kalli Anne tana kokarin

Kwantar mata da hankali cikin dubara har

Annen ta sauko ta nutsu tana kallan Safnah din ahankali kaman yarinya qarama.

Numfashi Safnah ta sauke hannuwanta na rawa bakinta ma Yana rawa tace

“Anne samirah ce ni ba sumayyah ba ba

Safnah ba.

Gyada Kai Anne tayi ahankali.

Cikin kokarin sake Hana rawar jikinta bayyana tace

“Anne Ina sumayyah?

Meva sameta?

Waye ya haifi Amnah tsakanin sumayyah da

Bena?

Ya Akai Bena ta hadu da Bilal tayi aure a

Chapter 72

72

Shiru motan yayi tsit dukkaninsu kowa na jiran amsan Annen zuciyoyinsu na tsalle da harbawa da karfi,

Ita kanta Anne shiru tayi kanta na juyawa tambayoyin na jiya hankalinta da haukanta tareda dawo mata da abubuwa da dama cikin Kai da zuciya na radadi ko acikin hali na hauka.

Rawa hannuwanta suka fara kafin dukkanin jikinta ya dauki rawar Wani irin tsoro da wuta na cin tikinta gidan Ababa kawai takeson komai sbd balain datakeji Yana tafarasa cikin namanta da jininta.

Ganin haka Safnah ta fahimci kafin Ababa ne da baya barin Annen nesa da gidansa ko kadan Dan haka ta jijiga Annen da Dan qarfi tana cewa “Anne baki fadamun meya sameta ba?

Ya Akai aka haifi Amnah a gidan Ababa?.

Murya na rawa baa cikin hayyaci ba Anne tafara cewa

“Sumayyah ne ta samu cikin Amnah

Ta mutu ta barni gurin haihuwa,

Ta tafi tabar mana Amnah

Ababa ya siyar da Amnah da Bena gurin dangin Bilal,

Ya hanamu fada yace zan mutu idan na fada, Yace Kasheni ya kashe Bena idan na fada,

Yace Bena zata ringa kawo masa kudin dangin

Bilal,

Nikuma naje na fadawa kakan Bilal gskia ba

Bena bace ta haihu sumayyah ne,

Yace zai kula da Bena da Amnah bazasu bawa

Ababa komai ba,

Ababa Bai saniba Benata ta tafi kenan bazata dawo ba, bazan bari ta dawoba, banason ta dawo,inason ta zauna acan ta mutu acan

Amma idan zata musu acan tazo mu tafi tafi karta barni yanda sumayyah da sameerah suka barni, Safnah guduwa tayi ta barni Amma Bena tace indena fadan haka wai itama mutuwa tayi kawai ba guduwa ba,Amma

Amma Amma…

Karyewa harshenta ke Neman Yi sbd yanda jikinta ke rawa da jijiga Dan haka da sauri

Safnah tace momy ta juya da motan su koma su ajeta sbd idan tana cigaba da nesa da gidan Ababa zata iya rasa ranta.

Cikin tashin hankali ma masifa momy tace

Idan muka mayar da ita bayan ta ganki fa ta fadawa Ababan.

Bazata iya fada ba bakiga yanda take ba batada lafiyan hankali fa,

Juya muje mu ajeta Dan Allah momy.

Juya motan momy tayi tana ajiye wayarta datai recording din duk Abinda Anne ta fada tana dagawa Safnah wayar tace

Wannan maganar bansaniba Amma dai zata mana amfani gurin ankarar da Ababa ya dawo bangarenmu sbd kaantes kenan sunsan komai babu Abinda zai samu tarko sukai masa.

Kasa magana Safnah tayi sbd a lokacin Bata

Gane komai har suka Isa nesa da gidan Ababa kadan suka aie Anne Safnah na Kallo ta shige gidan batareda an nuna mata inda zata shiga ba.

Tana shigewa suka bar gurin da mugun gudu suka koma gida kaman babu inda sukaje suna jiran labarin mutuwan Bena.

*****cikin gaggawa Akai Asibitin Kaantes da

Bena kafin a Isa da ita tini labarin ya Isa ga dd babba da sauran family cikin qanganin lokaci kusan kaantes suka cika Asibitin sbd kusan a yanzu Bena itace bugun kirjinsu musamman dd babbanta da shine uwarta,ubanta,kakanta

Kuma abokin shawaranta sbd komai nata shine yake Bata shawara.

Umme da Zeenah kuwa harda Kuka sukeyi sosai sbd Jin motar datai hadarin da ita ta

Kone duk tinaninsu itama ta Kone dinne.

Hana media taji zancen ko kadan akanta sbd kada DD yaji baa son ya sani zaa boye masa hakama Amnah Dake gida an gargadi masu aikin da kada su bari ta sani ance mata

Mummy dinta tayo tafiyan kwana biyo zata dawo inshallah.

Kwana Bena tayi batasan inda kanta yake ba bayan Angama dubata cikin babbar saa aka ga babu inda ta samu matsala buguwan

Kai ne ta samu sosoi Daya fasa hancinta sai goshinta Daya fashe sai Kuma hannunta daya

Dan juji ciwo ya yanke sbd glass na mota.

Hankalinsu kaf sai alokacin ya kwanta Dan haka ake fatan farkawarta koina data ji ciwo anyi dressing nasa an sauya mata kava zuwa

Riga da wando masu laushi da kauri.

Su Safnah kwana sukai jiran mugun labarin daga kaantes Amma Sam babu hakama media dasuke ta jiran suji ana yada masifar data samu kaantes shiru ba komai Dan haka

Suka Dan shiga wasi wasi da tashin hankali

Amma dai sun lafe suna Jira basu motsaba

Dan kila Bena din ta Kone kurmus da motarta baa samu sani ba.

Zeenah ce me jinyarta a Wani muhaukacin luxury Amenity room dake can sama Asibitin

Wanda sai iya kaantes dinne masu Asibitin ake kwantarwa acan sai Kuma manyan masu qasa.

Umme kullum itama sai tazo da daddare ta dubata hakama dad kaante duk yabar office saiya biya ya dubata kafin ya wuce gida.

Dd babba kuwa Shima da daddare kullum sai

Abbakar ya kawosa sun dubata.

Ta farfado tin washegarin ranar data samu mummunan hadarin Amma Kuma tinda ta farfado takasa komawa kanta,

Kanta ya juye gabaki Daya

Tinani da radadi zuciyarta keyi sbd Abinda ya faru da ita bayan hadarin Dayake dawo mata,

Shin da gaske ne Safnah din data Gani kokuwa gizon mummunan hadarin data samu ne?

Meyasa zataga Safnah idanma gizo ne?

Sumayyahnta ya kamata tayi gizo idan har buguwan datai matacci takeson nuna mata,

Safnah ce tabbas ta Gani kuma tai magana da ita Amma shin wa zata tambaya taji gaskiyar,

Ta tambayi Zeenah baa samu kowa tareda itaba inda aka sameta an Bata tabbacin babu

Wanda aka Gani.

Wainnan tinanin ne ke cin ranta da dagula zuciyarta Amma idan ta Tina ansanar mata

Annenta na Nan lafiya Kalau sai taji zuciyarta ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa.

Sedai ta Wani bangaren Kuma a yanzu mahaifiyarta take buqata a tareda ita fiyeda komai, Annenta takeso idan Kuma bazata sametaba to Ina zata iya zabar Annenta Takoma inda take komai zata iya hakura dasni.

Data kasa Kwantar da hankalinta Umme da kanta ta aika driver har gida aka dauko Anne bayan Ababa ya saka hande tayi mata wanka da a shiryata da kanta sun rufe iikinta da yayiwa mummunan duka bayan ta dawo da kanta din.

Dukan dayayi mata yasakata kwanciya cIwo itama Wanda ya Dan dawo da ita hankalinta

Dan haka tana zuwa Asibiti tayi Ido biyu da

Bena sai kawai ta fashe da Wani irin kukan

Daya saka Bena kasa dagowa ta kalleta

Daman su biyu ne a dakin da zata shigo aka fita aka Basu guri.

Kuka Anne keyi zuciyarta cikeda Wani irin qunci da bagin rayuwarta.

Bena hawayen ta gangaro dasu masu zafin gaske ta riqo hannuwan Annenta tana yaye mata hijabinta taga yanda gabaki Daya jikinta suke a fashe da shatin bulalan igiyar daure shanunsa. Bata iya cewa komaiba ta rungume Annen tana cewa

“Insha Allah Anne komai yakusa zuwa karshe,zan daukeki na tafi Dake inda zakiyi rayuwa kaman mutane da yardar Allah.”

Girgiza mata Kai Annen tayi tana cewa

“Ko ahakan bana cikin bagin ciki Bena tinda kina cikin walwala da kwanciyar hankali ke.”

Batadai iya cewa komaiba sbd idan tace maganar zatayi Kuka zasu taru suyita Yi gasu

Umme na palon dakin suna jinsu

Cikin nutsuwa tace

“Anne meya faru bayan barinki gida?

Ya Akai kika koma gida bayan nagani da idona mota ta Kade ki??

Bakiga kowa ba a ranar????

Shiru Annen tayi tana Dan shiga nazari kafin ta girgiza Kai tana cewa Bata ga kowaba Bata

Tina komaiba.

Ajiyan zuciya a boye Bena ta sake tareda barin zancen sbd kada ta juyar da kan Annen.

Gida aka Maida Annen daga Nan ita Kuma ta

Dan samu sakewa sbd taga mahaifiyarta.

****** Jinyar sati Daya tayi ta warware sosai aka sallameta ta dawo gida saida tayi kusan kwana uku da dawowa harta fara zuwa office alokacin Amnah tasan accident Mummynta tayi tsoro ya kama yarinyar sosai da daddare Ya Akai kika koma gida bayan nagani da idona mota ta Kade ki??

Bakiga kowa ba a ranar????

Shiru Annen tayi tana Dan shiga nazari kafin ta girgiza Kai tana cewa Bata ga kowaba Bata

Tina komaiba.

Ajiyan zuciya a boye Bena ta sake tareda barin zancen sbd kada ta juyar da kan Annen.

Gida aka Maida Annen daga Nan ita Kuma ta

Dan samu sakewa sbd taga mahaifiyarta.

****** Jinyar sati Daya tayi ta warware sosai aka sallameta ta dawo gida saida tayi kusan kwana uku da dawowa harta fara zuwa office alokacin Amnah tasan accident Mummynta tayi tsoro ya kama yarinyar sosai da daddare kuwa tana kiran daddynta video call ta fada

masa yayi shiru tsawon mintina bayan Jin

Abinda Amnah din ta fada Bai ce komaiba

sai daga baya ya Dan sauke numfashi kadan

yayi mata Saida safe yace ta kwanta ya kashe wayar.

Safnah da mommy a cikin satin kiris ya rage

likitan qwaqwalwa Bai dubasu ba su dukan

sbd samun tabbacin Bena dai ta rayu Kuma ta warke fes,

Abinda ya Hana Safnah zaucewa shine sanin

koda Bena ta Tina cewan ta ganta to batasan

a Ina take ba Kuma waye miiinta Dan haka a

yanzu zabi Daya ya rage musu ko a mutu ko

ayi Rai D yafara kwanciyar aure da ita aurensa

da Bena ya haramtu.

****Yau very late tagama Shirin office ta

fito sanyeda Riga da slim skirt na Wani

tsadaddivar lace milk and coffee brown Da

tsadansa take a bayyane sai qaramin veil mara nauyi ta shiga mota ta ajiye handbag dinta a gefenta ta tayar da motan ta bar kaantes.

Tana Isa office ko zaman awa Daya bataiba ta fita ta shiga meeting acan suka Dan Dade tana fitowa Kai tsaye office dinta ta nufa ta tura kofan kafanta Daya ta Sako ta dakata sbd zuciyarta data tsaya cak da qamshin da hancinta ya shaqar mata cikin office din.

Wayarta dake hannunta ta Dan riqe da garfi sbd subucewan data so Yi.

Sai Data sauke numfashi Mai sanyi ahankali kafin ta qarasa shigo ta tura kofar tana rufewa kafin ta juyo taji anrungumota ta bayanta tareda saka Kansa wuyanta ahankali yana lumshe fararen idanuwansa dasuka gama jigata kafin isowansa daga jiya zuwa yau din.

Ita kanta boyayyan numfashi ta sauke ahankali tareda lumshe idanuwanta idanuwanta na

Dan cikowa da hawayen radadin da zuciyarta

ta shiga duk tsawon wannan lokacin da baya

Nan.

Jin jima a Hakan shiru kafin ya saketa a

hankali ya juyo da ita suka fuskanci juna Yana

mata Wani irin Kallo bakinsa baisan me zai

furta ba sbd baisan Yava zai iero zancen ya

fadesu ba

Itama Jin shiru ya sakata dagowa ta kallesa

cikin nutsuwa da da sanyi ta Bude baki zatai

masa barka da dawowa ya kasa hakuri ya

dagaya sama tareda Dora bakinsa kan nata

Yana shigar da harshensa cikin bakinta.

Lokaci Daya suka tsotsa bakin juna suka

Kalli juna a tare ta shige jikinsa kawai tareda

zagyesa da hannuwanta Hakan ya sakasa iya

Bude baki ya jero kalman “Kina lafiya kuwa?

“Since when kuka fara boyemin Abinda yake faruwa?

Yaushe ne kika samu accident din?

And how did it happen??

Tambayoyinsa a jere idanuwansa na cika da

Abinda Bata taba tsammata ba wato kaman ruwan hawaye yasata kasa riqe kanta ta jefar da wayarta da documents din hannunta masu mahimmanci ta Kai hannuwanta masu taushi ta kama fuskarsa ta Dora bakinta kan nasa tayi masa Wani irin kiss Daya saka hawayen cikin idonsa zubowa Bai tabbatarda hawayen bane sai Daya shafasu yaji sune ya kalleta Dan tabbatarwa da Kansa ta gama da rayuwansa shi kenan.

Matseta yayi jikinta tareda karban kissing din Yana zuge duk was albarkatun bakinta dasuke sake kashesa.

Wannan karon shafa da lasan Dayake mata tafara wuce control dinsa

Ya dauke ya zaunar kan dsk na office din nata tareda saka harshe ya lashi fatan kunnenta zuwa wuyanta komai nata na rabasa da hankalinsa.

Rigarta yake Neman yagaga da bakinsa tayi saurin dakatar dashi ta nanyar gangamesa ta nanasa suka fara sauke numfasni a hankali a boye sbd sai lokacin ya Tina a inda suke.

Rungumeta yayi jikinsa suka zauna kan sofa tana jikinsa tsawon lokaci kowanne najin bugun zuciyan Dan uwansa suna debe kewan juna da sukai.

Sun jima a Hakan kafin ya dagota sai alokacin ta iya Bude baki cikin sanyi na nutsuwa tace

“Barka da dawowa.”

Ajiyan zuciya ya sauke Shima kafin ya sake jero mata tambayoyinsa na dazu.

Cikin sanyi ta fada masa a hanvarta ta zuwa dubo Annenta ba lafiya shine ta samu accident din motarta ta Kone.

Shiru yayi Wani Abu me kama da tsananin tsoro na shigarsa na da Wani abin ya sameta.

Jin yayi ya yankewa zuciyansa bazata qara bi hanyarba kwata kwata zai Bawa Annenta gidan da zata zauna kusa da kaantes sbd basai taje titin bayan gari na ganin mahaifiyarta.

Time ya kalla yace Mata ta tashi zai tafi da ita gida kawai.

Kallansa tayi sbd Basu gama meeting din da zasuyi Dan haka tace masa yaje kawai zatazo.

Bayason yawan magana Dan haka ya kalleta yace ta shirya data gama Nan da 1 hour zuwa

2 hours zai Aiko Naseer ya dauketa.

Gyada Kai tayi ahankali qayataccen murmushinta na bayyana.

Shima Wani Kallo ya Mata sbd baida niyar ma kowa yasan ko a dawo bare komawa kaantes yau din.

Yana barin company din highbridge Nasser ya nufa dashi ya aje.

Naseer na fitowa Kiran Safnah na shigowa wayarsa sbd tin jiya take Kiran D din Bata samu shiyasa ta kirasa.

Kai tsaye ba tinanin komai ya sanar make a ya dawo Yana gidansa na highbridge tana Jin haka batace komaiba suka a kashe wayar qafafunta da hannuwanta na rawa.

Momy ta fadawa take momy ta saka shirywa ta samesa can.

Cikin mintina galilan ta shirya cikin wata fitanannivar shigan alfarma da wasu crzy kayan bacci ko awa Daya Bata dauka ba ta figi mota a natse ta nufi highbridge din.

Koda ta Isa yayi ordern abinci ankawo daga

Wani matsiyacin tsadaddiyar restaurant kusan cin mutum biyu. Da mamaki ta Kalli komai a tsarin abincin sbd bawai lallai cin mutum Daya bane.

Tasan password Dan haka Kai tsaye ta Bude kofar ta shigo ta rufe tana toilet gurin wanka ta ajiye abincin ta Bude lafiyayyan Chicken macaroni salad din da aka hado dasu ta Bude. maganin data zo dashi Wanda aka hada mugayen qwayoyin juyar da qwaqwalwa masu tsananin qarfin gaske.

Kadan momy tace ya saka Amma sbd tana bugatan yayi mata saduwan da kowa zai sheda ya sadu da ita sai ta juya duka ta juye sauran a ruwan sanyi dake kan dining Daya gama Sha.

Yana bedroom dinsa yagama wanka ya shirya cikin qananu gajerun kaya qamshinsa me Dadi da sanyi na tashi ya fito daidai zata nufi hanyar bedroom din nasa.

Ganinsa ya sakasa Dan mamaki da kallan time kafin ya Dan kame fuska Yana amsa gaisuwanta.

Dining ya nufa ta biyo bayansa tana masa sannu da zuwa cikin farin ciki da bayyanarda murnarta.

Zama sukai farin cikinta na garuwa take da dauko plates da kanta tayi serving nasa zata zauna yace ta tafi gida baya bugatan kowa anan hutawa zaiyi zai dawo gidan.

Magana zatai wayarta tayi ringing tana dubawa taga Momynta ce tace

“Kiyi sauri ki dawo ki baki dauki dayan maganin ba da zaisha qwayoyin su sakesa batareda ansan mugayen qwayoyin da aka basaba,Yi sauri ki zo ki karba ki koma kada a Samu matsala sbd zaa iya ganin drugs dinnan a jininsa.

Wani takaicin mantuwar ya soki zuciyanta Dan haka ta Dan saki qaramin tsoki a boye ta miqe tana daukan wayarta da handbag dinta ta nufi

Kofa tana ce masa zataje ta dawo mommynta bataiin dadi.

Bai amsata ba har ta fice ya fara cin abincinsa yaci ya koshi yaji Kansa na Dan sarawa kafin ya fara juyawa ahankali.,

Migewa yayi ya nufi bedroom dinsa yana kokarin cire rigarsa da Wani irin zafin gaske

Dayake ji Yana taso masa.

Mace yake buqata sosai da gaske,

Bugatan mace yakeji wadda ko Bena batazo highbridge dinba zai iya samunta kaantes to Amma bayajin ko fita zai iyayi a halinda yake ciki. Safnah data fice gidance ta fado masa arai yaji Kansa na qara juyawa zafin dayakeji jikinsa

Yana garuwa.

Bena bayan fitarta Batama Wani Jira meeting din ba ta wuce gida Kai tsaye taci abinci tayi wanka kenan Naseer ya kirata ya sanar da ita

2 hours din sun cika tace ya sameta Kaantes.

Yana zuwa ya dauketa suna barin kaantes ya tsaya hanya yace ta garasa da motar shi yasauka ya tafi gida sbd dagashi har ita a takure suke a motan.

Bayan ya fita zagayowa tayi ta shiga motar ta ja zuwa highbridge.

Chapter 73

73

Tana shigowa gate na highbridge ta Kalli time taga magrib ma ta kusa Saura kadan

Dan haka ta saka wayarta silent musamman data fahimci babu Wanda ya San ya dawo din hakama babu Wanda yasan fitowanta bayan

Nafisat data fadawa ta kula da Amnah idan lokacin baccinta yayi kafin ta dawo.

Ka a can harabar gidan securities ne kawai sukasan waye ya zo ya dauketa ta fita.

Parking tayi harabar gidansa dake cikin highbridge din tana Jin gabanta na Dan faduwa sbd sai yanzu ne ma tafara tinanin mema to zatavi anan da bazai bari ya dawo kaantes ba idan magana ce ko Wani abin.

Bude motan tayi ta fito a natse daga ita sai wayarta ta fito sai Kuma key na motan Dayake hannunta yanxu.

Kofan shiga palon ya Isa ahankali ta saka password data sani a bakin Amnah cewa date of birth dinta ya saka.

Kofan na budewa ta shiga tareda rufe kofan tayo cikin main palon tana kallan dining taga baya Nan sai abincin Dayaci yabarsu a kan dining din.

Hanyar kofar bedroom dinsa ta kalla tana ajiye wayarta da key din motan dake hannunta tanason nufar hanyar tanajin rashin sakewa da

Hakan.

Dayan dakin data taba kwana a gidan ta nufa tareda Bude kofan dakin ta leqa baya Nan

Daman Kuma tasan ba lallai Yana ciki ba

Wanda baya iya amfani da ko toilet din sauran dakunan gidansa idan bana asalin bedroom dinsaba.

Tana fitowa bedroom din taji kaman nishinsa me garfi Yana tashi tareda kaman yunqurin

Amai me garfin gaske.

Kallan hanyar dakin nasa tayi tareda nufar dakin Kai tsaye bugun zuciyarta na qaruwa tana Isa Kai tsaye ta saka password ta Bude tareda tura kofan ta shigo tana kallan dakin baya ciki.

Mayar da kofan tayi ta rufe ta nufi tareda karasa shigowa bedroom din nasa tana kallan kofan toilet dinsa Datake Jiyosa Yana Wani irin

Amai me qarfin gaske.

Jin aman nasa ya kasa tsayuwa Kuma da yanda take jiyosa batajin alaman Wani abin

Yana fitowa daga cikinsa kaman ma kakaro aman yake da Kansa.

Kasa hakuri tayi ta fada toilet din ta nufi gurinsa da sauri cikin damuwa tana Isa gabansa kafin tace komai ya janyota jikinsa da qarfi ya gangame Yana rawar jiki sosai baa cikin hankalin Kansaba.

Yanda yake rawar jiki Mai hade da jijiga ya sakata shiga toro da firgici sosai tayo kokarin zamewa Amma ya sake qanqameta cikin tsananin masifaffen balain davakeji ya girgiza mata Kai da garfi sbd tana barin jikinsa ya kalleta zai iya kasa controlling Kansa dayakejinsa kaman Doki idan ya sadu da ita a

Hakan zai iya kasheta ma Kila yakeji.

Tin suna tsaye a tsakiyan toilet din har qafafunsa suka Gaza daukansa ya zube gasa da ita gangame jilkinsa idanuwansa na Neman

Juyewa muguwar bugata da shaawa zasu kashesa Amma ya zabi ya mutu akan yayi mata Abinda zai illatata ya tsani Kansa.

Kasa riqe zuciyarta tayi ta fara hawaye masu zafi tana ta kokarin sake qwace kanta Dan tagani tasamu Daman sanin meya samesa,

Abincin Dayake kan dining takeson zuwa ta dubo idan Akai yaji ko shine ya sakasa wannan halin Amma yaqi sakinta Dan haka sai ta jansa da gyar suka Isa qarqashin shower ta miqa hannunta Daya dagyar ta kunna ruwa akansu jikinta na rawa sbd ko Hakan zai taimaka masa ya dawo hayyacinsa sod lamarin ya koma abin tsoro sosal.

Saukan ruwan a jikinsu ya sakashi sake gangameta Yana jijiga jikinsa na fidda Wani irin tiririn jininsa dake quna Yana dahuwa da balain drugs din da suka hada na balai suka

Basa,

Bai taba Shan ko maganin mura ba tinda ya girma duk ciwonsa yafi son allurarsa idan akwai,dan haka Sam baya Wani Shan magani ko na ciwon Kai bare qwayoyin shayeshayen dake juyar da qwaqwalwa an hadasu dana desires bama Daya ba kaloli masu qarfin gaske da ake Bawa dokuna idan ana son suyi

Abinda zasu samarda ciki. Zafi jikinsa ke sake dauka sosai har Yana fita duk da ruwan data sakar masa Akai,

Tashi hankalinta yayi sosai batasan lokacinda ta sake fashewa da kuka me sauti ba maimakon hawayen datakeyi a take ya fice hayyacinsa gabaki Daya gashi tanason qwacewa ta dauko wayarta ta kira Naseer yazo suje Asibiti ko ayi gaggawan kawo likita

Amma ya rigeta gam kaman zai ballata har gashinta tanaji suna amsawa sod matsewan dayayi mata.

Kuka takeyi sosai tana Kiransa Amma gaba

Daya baya hayyacinsa kafin ta sake wani yunqurin ya sake daukan jijiga Yana birkicewa gaba Daya.

Zuwa wannan lokacin Kukan a yayi tsananin gaske Dan haka ko azabar matsewan da yayi mata Bata ii shi take Jin zuciyarta ya azabtiwa da mummunan halin Davake ciki kaman me farfadiya.

Suna cikin wannan halin har tsawon lokaci har Akai sallar magrib aka fito da dadewa Bai

Dena jijigaba tayi duk yanda zatai ta kwace ta kasa qwacewa Dan haka ta ringa Kuka a jikinsa suna jijigan tare har abin yazo yafara lafa masa a ahankali ahankali ya Dena ya lafe jikinta.

Itama lafewan tayi tana Dena Kuka tareda daga hannuwanta dayayiwa mummunan matsewa har Wani ciwo suke mata ta sake sakar musu ruwan zafi daqyar.

Sai alokacin ya fara jero ajiyan zuciya masu qarfi a jejere Yana saketa daga mugun rigon da yayi mata.

Sai data ga ya nutsu ya Dena komai ya Bude idanuwansa dasukai Wani mugun ja ya kalleta tareda Jin zallan buqatanta,

Jin yakeyi kaman zai hadiyeta sbd zazzafan sonta da bugatanta dake azalzalan zuciyarsa.

Miqewa tsaye tayi dagyar tareda Kamasa kaman yaro ta migar idanuwansa na kanta kaman zai cinyeta dasu.

Ruwan dake sauce kanta suna gangarawa fatan wuyanta zuwa kirjinta suna shigewa rigarta suna sake jiga doguwar rigar jikinta tana lafewa jikinta shape din kirjinta suna sake bayyanar masa yake kalla

Ya kasa hakuri duk da jikinsa ba qarfi sosai ya saka hannuwansa biyu ya kamo kugunta ya matsota jikinsa tareda hade mararsu guri Daya

Yana lumshe idanuwansa cikin azababbiyar kasala.

Ita kanta rintse idanuwanta tayi ahankali tareda hadiye Wani bugawan zuciya tana Dan gangamesa.

Ajiyan zuciya ya sake saukewa shi kadai yasan masifan Dayake ji cikin jiki da jininsa.

Ahaka ma Saida suka jima gashi ko magrib

Basu yiba Saida ya sake daidaituwa ta kashe musu ruwan da kanta ta fara Zame kanta Yana kokarin sake rigeta ta kallesa da sanyin murya tace Basuyi sallah ba.

Ita tafara alwala ta zare kayanta gabaki Daya dake digan ruwa ta ajiye tareda dauro towel ta fito yabita da Kallo kaman maye.

Tana ficewa yayi saurin Dafe bango sbd dauriya kawai yakeyi Amma Yana cikin azababbiyar azaban da baisan ana jinta bama,

Dagyar ya iya alwalan ya fito Shima daure da towel

Har lokacin tana tsaye tana jiran ya fito ya Bata

Abinda zata saka. Da hannu ya iya nuna mata closet dinsa ta garasa ahankali ta dauko musu kaya ga mamakinta kusan sabbin kaya ne aka jera a closet din Wanda suke duk yawanci couples set ne wasu Kuma set din Kuma hardasu da

‘yarsu Amnah.

Yanayin dasuke ciki yasa Bata iya tsayawa

Wani dube duben ba ta dauko musu wasu black Balmain sweatshirt da sweatpant.

Babu inda zata iya tafiya canja kaya Dan haka hakanan ta saka kayan gabansa tinda babu undies nata duka sun jiqe.

Bayan ta saka ko data juyo ya saka nasa sabon towel me girma ta dauko dashi ta nade kanta tayi rolling nasa sukai sallah sbd kayan jikinsu Daman masu girma ne free size ba masu kama jiki na ko kadan.

Cikin lallabawa yayi sallan magrib da ishai din ita Kuma cikin ‘yar nutsuwa tayi ta kammala tana gama addua ta juyo ta kallesa taga Shima ya gama adduan zufa yake Dan Yi duk da sanyin AC a dakin ya kama koina.

Migewa tayi tareda nufar qaramin fridge

Dayake dakin cikin bedside a hade kaman ba Fridge ba ta Bude ta dauko apple dink me

Dan sanyi kadan ta kawo masa Dan yasha ita

Kuma ta samu Daman zuwa ta dauko wayarta a Palo takira ko Naseer ko Umme ko Zeenah asan halinda yake ciki na rashin lafiya.

Bai karba drink din ba hannunta ya kama tareda janyota ta fado Kansa Daman ya koma kan kujerar dakin zaune.

Kan gafafunsa ta fado ya karbi drink din hannunta ya jefar gefensu ahankali ya da dawo da idanuwansa kanta Yana mata Wani kallan maita da zalama, Faduwa gabanta yayi ta dago ta kallesa ganin irin kallan Dayake mata kafin tayi wata magana ya sake Janta cikinsa sosai akan gafafun nasa sukai kyakyawan hadewa suna fuskantan juna kirjinsu a hade.

Bugawan zuciyarta yasake gigita tinaninsa ya zagayota da hannuwansa Yana saka Kansa wuyanta Yana Jan numfashi me qarfin gaske

Daya sakata Jin tana sake samun bugawan zuciya da garfi hakama numfashinsa me dumi yake sauka fatan wuyan nata tini suka tayar da tsigan jikinta.

Babu tsammani ya Ciro Kansa daga wuyan nata ya kama rigar jikinta ya daga tareda zare mata ita gaba Daya take ya saki Wani mahaukacin numfashi gain lafiyayyan suran jikinta

Tasa rigar ya zare kafin ya janyota da kanta cikin sanyi ta hade kirjinsu,Saura kiris ya rasa numfashi da bugawan zuciyarsa akan Hakan datai masa sbd yanda komai nata na kirji ba kaya ajiki ya sauka kan nasa kirjin ba kaya ajiki Shima.

Yanda yakeji bazai iya cigaba da hakuri ba Dan haka ya dagota Yana kallan cikin idanuwanta dagyar ya iya furta “| love you”. .. Bai iya Jira ya garasaba ya hade bakinsa da nata itama sbd shiga matsanancin mamakin Abinda ya fada Bata gama mamakin ba taji bakinsa a nata Dan haka cikin tsananin tsananin sonsa dake Neman zauta zuciyarta ta zagayesa da hannuwanta tana sake Basa Daman jinta da kyau suna yiwa juna Wani irin french kiss

Kaman zai cinyeta

A kirjinta zuwa bayanta da Mararta ya ringa yawo da hannunsa cikin wata irin Abu Dayake

Jin kaman zai fasa Kansa.

Kashe wuyanta yahau Yi da harshensa zuwa kirjinta Da Yana Kai harshensa ta bangare masa taba Neman somewa sbd Wani Abu ne dabai taba faruwa da ita ba.

Tin tana iya control na halinda take ciki tini ta kasa tafara wasu irin hawaye tana banqare a jikinsa tana kokarin sakar masa Kuka sbd kanta juyewa yake Neman Yi.

Shi Kansa tini ya juye, notikan Kansa suka kunce ya rasa control gabaki Daya lasheta yakeyi Tako ina Yana sake gigitasu.

Hawaye takeyi Shima hawayen yakeyi gabaki

Daya dakin ya rikice da numfashinsa me garfin gaske Dayake sake dumama jikin Bena.

Bata sake Neman sumewa ba Sai Daya miqe da ita a jikinsa suka nufi lafiyayyan gadonsa ya

Kwantar da ita tareda Yi mata rumfa Yana son yay romancing nata dakyau Amma bugatarsa taci karfinsa Dan Hakan Kai tsaye ya qarasa rabasu da kayan jilkinsu Yana dagota jikinta tareda sake hade bakinsu guri Daya

Batasan me yake Shirin Yi ba Dan haka take kissing dinsa back suna cigaba da shafe shafensu da latse latse. Abinda taji ne ya sakata saurin Dena kissing dinsa Amma shi bai Dena ba baikima saketaba hakama Bai fasa Abinda yayi Niya ba kafin tayi Wani yunquri ya dauki harama.

Chapter 74

Kukan ‘dan Umme ya fasa me qarfin gaske lokacinda ya samu Kansa a duniyan da baisan

Yaya take ba,

Pillon da kanta yake Kai ya saka hakoransa ya kanne Akai ya fizgesa tini pillon ya fashe lallausan gashin ciki Yana zubowa da tashi sama cikin Dan hasken da dakin yakeda shi.

Kukansa ya Hana nata fita sbd ita batada lafiya ko garfin da zata iya fidda nata kukan yayi sauti Dan haka dakin ya kauraye da kuka kawai Kuma ahakan Bai sauraraba tsawon lokaci kaman zai mutu yakejin Kansa sbd abubuwa da yawa.

A daidai lokacin da ya samu Kansa daga shi har ita lokaci Daya suka sume babu Wanda yasan halin da Dan uwansa yake ciki. *******Safnah a lokacin da ta fice daga gidan cikin dauriya ta ringa Jan motarta a hankali cikin highbridge sbd dokansu ne baa gudu da mota a cikin gurin hakama baa horn,duk

Abinda zaiyi qara ko Bada hayaniya baa yinsa a ciki har sai ka fice Dan haka zuciyarta kaman zatayi tsallake ta fito sbd sauri da takaici ta lallaba ta samu ta fito highbridge din tayi yar tafiya tayi nesa da gate din shiga gurin ta samu tabau Wani titin ta take motarta cikin tsananin gudu tana Jin zuciyarta na sake daukan rawa da azamar gaggawa.

Ko data Isa gida Momynta ta kasa hakuri har ta fito da mayafi a hannu da key din mota zata bita takai mata itama zuciyarta na tsalle cikin rashin hakurin jiya da gaggawa sbd matiqar

Basu Basa wannan yasha ba bayan biyan bugata drugs din ba sakinsa zasuyiba ana zuwa Asibiti zaa iya gano meyasa Wanda ba asibiti kawai ba gasarma gaba Daya kamasu zatayi idan aka kamsu da wainnan qwayoyin sun bawa Wani,waninma Dan gaban goshin familyn kaantes.

A harabar gidan suka hadu batama fito mota ba momy ta fasa shiga motarta ta nufota tana sauke ajiyan zuciya da washe baki tace

“Wai barkanmu da arziki,harna fito sbd na kasa nutsuwa da Abinda zai kawo matsala,

Karbi bama sai kin fito motar ba Maza koma kada ya shiga halinda zai kasa komai ma.

Itama Safnah ajiyan zuciya ta sauke ranta na sanyaya tas da farin ciki ta karba tareda kokarin juya kan motar tayi reverse tana cewa

“Momy da wuri Zaki kira Naseer ki San yanda zakiyi ki turasa can yaje asamu kaimu asibiti

Amma ki fara kirana sai kin tabbatarda na

Basa magananin hannuna.”

Hankali kwance momy tace kije kawai da kaina zanzo kaiki Asibitin sbd tabbatarda babu Wani Abinda zaisa a Gane meyasha,

Kafin komai kina Isa ki tattara abincin Dayaci ki zubar karki bari a tadda abincin.”

Gyada kai kawai Safnah tayi tana ficewa cikin sauri sbd a matse take Data koma din,bayan cikar burinta na zama matarsa cike take da zallan kwadayinsa da bugatarsa sod ta tabbatarda DD kaante Bai taba sanin ya ya mace take ba a bangaren kwanciya Dan haka duk macen datai sa’ar budesa a leda zata zama sanyin zuciyarsa

Duk seconds din dake tafiya a hanyarta ta komawa highbridge akan Idanuwanta suke tafiva Dan haka hankalinta Sam baya kan hanya Yana kan agogon motar tana Jin kaman kanta zai kama da wuta sbd azarbabi.

Bata ankara ba tayi cikin wata motar data saka right signal na sauka titi Wani mugun buguwa sukai wanda ya saka kanta buguwa da steering mota taji kaman kan ya fashe.

Mintina tayi a motar batareda ta iya daga kanta ba sbd tsananin azaban dayake mata har sai da me motar gabanta ya fito Yana Dan buga glass na motar ta Yana mata hannu ta sauke glass.

Sai alokacin ta Dan dawo daidai tana Dafe kanta ta sauke glass tana kallansa cikin kokarin sake dawowa daidai ta Bude baki tana Basa hakuri kawai sbd batason Abinda zai tsayar da ita ya Bata lokacinta na Isa highbridge.

Ganin halinda take ciki Kuma da ganinta mace ya sakasa Shima juyawa kawai ya kyaleta Yana tsoki ransa a bace.

Girgiza kanta dake Dan juyawa tahau Yi tsawon mintina kafin ta dawo daidai Amma har lokacin kanta na Dan sarawa ta tada motar tabar gurin tana cigaba da tafiya sedai wannan

Karan bazata iya gudu ba idan har tanason kanta a Raye sbd kanta dake Yi Yana sarawa idan tace tayi gudu mummunan hadari ne zai iya faruwa da rayuwarta:

Lokaci mai Dan tsayi ya Jata kafin ta iso highbridge sbd Badan fitarta ba ta sani da yanzu komai yagama wakana tsakaninta dashi.

Tsoki tasake Dan ja lokacinda ta shigo highbridge din tanason tayi masifaffen gudu ta

Isa Amma ba Daman Hakan.

Ko data Iso tayi parking ta dauki maganin ta saka handbag dinta ta fito tareda rufe motar tayi ciki da sauri sai alokacin taji sanyi da farin cikinta ya dawo.

Password na kofan ta saka ta shiga ta mayarda kofan ta rufe tana dubawa palon baya Nan.

Hanyar zuwa bedroom dinsa ta kalla Amma

Bata nufa ba sai ta nufi dining da sauri tafara kokarin tattara abincin dining din tas ta kwashesu takai motarta ta zuba su baya jikinta na rawa ta sake tada motar kaman yar wahala da sauri ta sake fita daga highbridge din taje nesa da anguwan kadan ta zubar da komai a

Wani refuge ta dawo.

Securities din highbridge Suma ranar Saida sukai mamakin kaida kawon datakeyi a Dan haka Suka Yanke daga wannan fitan nata idan ta dawo ta sake fita bazata sake dawowa ba sbd in and out dinta na ranar ya cike kaidojin

Kai kawon baqinsu na wunin sbd tsaro.

Tana dawowa Sai data ganta a palonsa tsaye ta sauke ajiyan zuciya guda hudu a Jere kafin ta nufi bedroom dinsa ta Murda kofan tareda turawa Amma kofan Taki buduwa.

23 RA

Da sauri ta Kalli kofar sai alokacin taga itama

Saida password idan bana ciki bane zai Bude maka ka shigaba.

Wani azababben zufa taji yana kokarin karyo mata ta sake Murda kofan da qarfi tana turawa kaman wadda take Neman zaucewa.

Bubbuga kofan tahau Yi da Dan karfi har tana

Kiran sunansa tana cewa itace ta dawo ya

Bude mata kofan shikuma daga ciki daidai wannan lokacin ne bayaji baya Gani baya Gane komai bare Kuma Bena datake cikin karban azabar rayuwarta da Bata taba tsammani ba.

Dukan kofar takeyi nata magananin datasha

Yana taso mata gadan gadan itama shi take bugata kaman zatayi fitsari a wandonta tana ihun Kiran sunansa da karfi.

Watsi tayi da Jakarta da wayarta tana Bada himman buga kofa da turawa da garfi ko zata iya balla kofa.

Haukacewa take Neman Yi a palon ita Daya

Dan tini takejin ayau Yana Bude kofan wh Ko fyade ne saita masa.

Tana cikin masifaffen tashin hankalin kunnuwanta sukai mugun Jin data kasa fahimtar menene.

Dakatawa tayi hannuwanta da jikinta na mugun rawa sosai ta Dora kunnenta jikin kofar ahankali taii kaman ihunsa da kukansa takeji

Yana Kiran sunaye kala kala Wani mugun yanayl.

Yankewa gafafuwan sukai ta zube qasa

Amma Bata yarda ba da Abinda taji din ta sake kwantawa qasa ta Dora kunnanta iikin kofar Amma Bata Jin komai gwara ta saman Dan haka ta sake migewa jiki na tsananin fizga ta

Dora kunne.

Kuka ne yakeyi sosal,

Kuka ne bana ciwo ba bana azaba ba bana qunci ba,

To kukan me yake?

Sunan uban waye taji kaman Yana kira?

Wani mummunan busashen yawu ta hadiye dagyar ta makoshinta jiri da duhu suna Neman rufe idanuwanta.

Rawar da jikinta ya sake dauka wuta na cin jininta Yana tafasa ta rarrafa ta Nemo wayarta inda ta jefar ta Nemo numbern momy hannuwanta na kasa riqe wayar da kyau sbd rawar da suke daidai momy na daukan wayar itama wayan Bena data bari palon ta kawo haske alaman shigowan kira sai akan idon

Safnah taga sunan My Zee kaante baro baro jikin wayar da Annensu tana zaune batama

San anyi mata hotonba.

“Beeenaaaaa”…tafada sunan cikin kakkaryewan kalamai da mafi girman tashin hankalin rayuwarta.

Momy dataji yanda ta ambaci sunan Bena din take ta shiga rudani murya a rikice tace

“Wace Benar Kuma?

Meya kawo sunanta yanzu?

Ke sanar Dani meyake faruwa nei

Sakin wayar hannunta Safnah tayi tareda

Dora hannu Akai tanason fasa ihun dazai Tara mutane Amma Bata samu Damar Hakan ba ta

Yanke jiki ta Fadi gurin a sume.

lhun Kiran sunanta momy tafará Yi a waya tana tambayar lafiya Amma shiru ba magana ba motsi.

Rawa jikinta y dauka itama ta miqe tsaye tana sake Kiran sunan Safnah din Amma ba alamar akwai me Rai ma a kusa.

Wani zufan ne itama ya fara tsatsafo mata tana Neman tsinkewa sbd tagano dai yanzu kullum sabuwar masifa ce take bullo musu wata bayan wata

Kashe wayar tayi ta sake saka Kiran Safnah din tafara ringing harta katse baa dagaba,

Sake kira tayi har so biyu Amma baa daga ba tini tafara kaida kawo tana shiga fargaba da zafin zuciyar idan ba Wani abin ne yafaru ba,

Tsawon lokaci tanata sake Kiran Safnah baa dagawa gashi dare ya fara sosai Dan haka taji bazata iya Jira masifa ta sauko musu ba gwara taje ta dubo kada a Samu matsala.

Jallabiyar bacci ma ce a jikinta ta saka mayafi

Akai ta zari mukulli ta fito ta fada mota ta fice.

Cikin gudu sosai ta Isa highbridge da farko sbd lokacin snigarsu ya wuce dare yayi sosai kusan 1 na dare Dan haka Suka hanata shiga.

Cikin magiya ta nuna musu ‘yarta matar D kaante tana ciki tanata Kiran wayarsu Basa dauka tana son duba ko lafiya.

Wayarsu securityn dake duty ya daga ya kira gidan DD kaante Wanda kowane gida Dayake ciki akwai numbern dasuke kiransu da ita landline,

Ringing wayar keyi sosai Amma babu Wanda ya dauka, Sake kira yayi har so hudu babu Wanda ya daga Dan haka ya karbi id card dinta ya duba tareda shigar da information dinta aka Bude mata gate din ta shige.

Tana Isa gidan tafara kokawan saka password kala kala Amma bata saniba.

Sharkaf take da zufa iya zufa cikin tashin hankali,.

Canke tafara na password din Amma duk baiyiba sai kawai ta hau tinanin ranar haihuwan Amnah kokuma ranar da Mahaifin

Amnah din ya rasu wato Bilal.

Tana fara saka na Amnah ya Bude a gigice ta fada tana legawa kada ta fada tarkon da batasan Yaya yake ha tinda batasan meya samu Safnah ba tajita shiru.

Cikin mummunan sa’arta da Safnah tafara cin karo a palon kwance ba Rai a tareda ita kaman ta mutu.

Ihu taso fasawa tayi saurin rufe bakinta ta zube gabanta tana jijigata da karfin gaske tana Kiran sunanta ahankali.

Ganin alaman da Rai jikinta yasakata nufar dining tana Neman hanyar kitchen a gigice ta samo ruwan sanyi a fridge ta zubawa Safnah wadda itama a gigice ta farka tana Neman rusa ihu momy tayi saurin rufe mata baki.

Kallan momyn takeyi jikinta na dawowa da rawa hankalinta na gushewa tace

“Momy Bena ce a cikin Daki da D,

Bena ce take kwance a kan gadon DD Yana mayar da ita mace,

Momy wIh bazan iya yarda ba kashesu zanyi duka kowa ya huta Momy bazan iya…..Bata qarasaba kanta ya sake juyewa ta Kuma sumewa tsabar masifa da balain Datake cikinsa.

Momy data shiga mummunan tashin hankali da tafasar zuciya itama batasan lokacinda ta fara ganin duhu duhu ba kanta na juyawa.

Me kenan ya faru?

Biyu babu zasuyi ko me?

Cabdijam,wIh bazai yiyuba idan har sun rasa

D to ko zaa mutu bazasu rasa bulama ba Dan haka bazata taba yarda asan asalin Safnah ba.

Kitchen ta nufa ta kunna oven batareda komai a cikinsa ba takai zafinsa qarshe ta fito ta dauki ruwa ta zubawa Safnah tana farfadowa ta figeta suka nufi hanyar fita tana cewa

“Maza muje wlh na banka musu wuta daga duniyar dasuka sai lahira”

Safnah da Bata hayyacinta tanajin Hakan ta

Kalli momy da sauri kafin tayi magana momy ta Nuna mata motarta tana cewa ki shiga kija motarki mu wuce gwara ko ya rasa tinda Mika rasa.

Wartsakewa Safnah tai da gyar take ganin gabanta suka ja motocinsu suka bar highbridge din.

Basuyi tafiya me nisaba Safnah ta kasa tuqi sbd yanayin Datake ciki zata iya samun hadari

Dan Bata ganin komai bayan duhu.

Chapter 75

75

Hankali tashe momy tayi parking motarta ta fito gashi dare ne sosai ba wasu motaci dake wucewa bare mutane Dan haka kamata tayi tareda rufe motan Safnah din ta barsa anan ta Jata zuwa tata ta shigar taja motar suka

qarasa gida.

Maigadin gidan yayi mamaki da tsoron ganinsu wannan lokacin Amma hakanan ya Bude musu gate suka shiga momy tayi parking suka fito tareda nufar kofan qarasawa

ciki suka shige.

A Palo suka zube dukkaninsu kowannensu gafafunsa da hannuwansa na rawa kaman yanda zuciyoyinsu ke harbawa da rawa tareda

zafi me tiririn gaske.

Babu Wanda yake iya magana acikinsu sbd kowa ta zuci na can na cinsa,.

Safnah Wani irin zufa take fesowa tana tsiyaya sbd tsananin quna da tafasar da Kirjinta yakeyi

Amma jikinta kaf baya iya ko doguwar motsi sbd somewan datai tayi tsabar shock da bugawar da kanta ke Neman Yi.

Momy kuwa kaida kawo take yi itama Bata iya cewa komaiba tana fatan kafin safe DD da

Bena sun gone kurmus ko soyayyan jikinsu kar asamu sbd idan suka rayu su suna ruwa kwance,

Safnah dai aure tsakaninta da DD kaante ya haramta har abada matiqar Bena tana da Rai,

Idan Bena ta tabbata matar Dawood kaante to dole Safnah zata barsa sbd bazasu cigaba da boyewa haduwarta da Bena ba har abadaidan anie Neman dalilin barin aurenta da DD dole sai Anji cewan uwa Daya Uba Daya suke, To idan akaji Hakan aka Kuma San Hakan kenan Safnah ba jinin bulama bace daganan Kuma sunyi Tara babu,

Ba auren DD kaante ba zamansu qarqashin bulama sbd zai San safnan ba yarsa bace,

To daga Nan menene makomarsu????

Wannan shine zancen da momy keyi tana kaida kawo cikin palon kaman zata zauce sbd tinani na lissafi

Kallan Safnah tayi da jajajen idanuwanta tareda zaunawa suka fuskanci juna murya a qage tace

“Meya yakai Bena gidan bayan kince shi Daya ne a gidan Kuma babu Wanda yasan ya Dawo?

Ya akai ita ta sani?

Garin Yaya?

Meyasa Zaki bari duk tsanani duk rintsi Hakan ta faru? Safnah data koma kaman kurba bayan rawa babu Abinda hannuwanta keyi da qafa

Ta Kalli momy da jajayen idanuwanta da sukai jajir tanason tayi magana ta kasa sai alokacin

Wani irin kukan bagin cikin gaske me tsananin nauyi da azaba ya kufce mat ta fasa shi tana zube qasa kan tiles daga kujerar Datake Kai.

Duk da dare ne Safnah kasa riqe kanta tayi ta ringa Kuka Mai tsananin radadi da baqin ciki tana Jin kaman zata mutu sbd baqin ciki.

Kukanta ya saka momy sake shiga baqin ciki da takaici me tsanani itama zuciyarta na sake bushewa da fatan mutuwar DD da Bena tana cikin wannan daren.

Bata rarrashi Safnah ba sbd itama Daman tata zuciyar quna take tana sake shiga lissafi da zurfafa tinani sbd rashin mutuwar su DD Wani binciken zai tsananta akan qwayar Dake jikinsa wadda lefin kama mutum da ita kawai shekara 50 gidan yari ne bare a kama ka da ita kana amfani.

Dole idan DD ya rayu zaa San akwai wannan

kwayar a jikinsa Dan haka taji tana sake jiquwa

cikin zufa da tsananta fatan mutuwar su DD

din tana wannan daren.

******Zeenah data kasa bacci sbd sake Kiran

Bena data samun tabbaci a bakin Nafisat

cewan yaran Daddyn Amnah ne yazo ya

dauketa

Hakan na nufin DD ya dawo kenan tabbas to Amma ko yayane ya kamata Ce Bena ta

kirasu Dan bata taba iya bacci batai magana

da Amnah ba hakama Shima DD din Amma

dukkaninsu babu Wanda ya kira.

Umme dataji Bena din na highbridge ta

tabbatarda DD ya dawo Bai fadawa kowa bane Dan haka tace a kyalesu su huta Dan Allah kafin ya dawo Kaantes.

Kowa ya shige,Zeenah na bedroom dinta tana

Aiki a laptop har kusan 12 na dare kafin ta daure ta kashe tareda daukan wayarta ta sake saka kiran Bena.

Rashin daga wayar Bena din ya sakata Dan shiga mamaki sbd tasan Bena ko acikin baccin tsakan dare sosai daga wayarta takeyi bare yanzu datasan Daren baiyi sosai irin hakanan ba.

Kwantawa tayi gadonta kafin ta a sake saka

Kiran Bena din wayar taci gaba da ringing baa dagawa.

Canjawa tayi ta kira wayar DD shikuma wayarsa a kashe ma gaba Daya, Bata hakura ba sbd ita tinda Bena ta samu accident din baya Shima kusan haka tayita kiranta Bata dauka karshe suka sameta a accident Dan haka Bata wasa Sam da kiranta taji Bata dauka to hankalinta baya kwanciya barema Amnah da tin yamma tayi Wani sukuku jikinta yayi zafi babu Kuma alaman ciwo a jikinta fatanta Allah yasa ba Wani Abu yarinyar taji a jikinta zai samu mummynta ba

Dan haka sai kawai ta nema numbern Naseer ta saka kiransa tana kallan time lokacin 1 daidai.

Shima baiyi bacci ba sbd Yana Aiki Daman wasu lokacin yana Kaiwa har fiyeda 1 dinma baiyi bacci ba.

Kiran Zeenah kaante na shigowa wayarsa da Dan mamaki ya Kalli sunan ya Dan Maida idansa kan time ya kalla yaga karfe dayan dare. Daukan wayar yayi cikin kasa boye mamakinsa da tinanin dole akwai Abinda ya faru sbd babu ta yanda Zeenah da ko da Rana Basa waya bare da irin wannan lokacin, Yana dauka Kai tsaye yace

“Hello Allah yasa lafiya dai”

Ajiyan zuciya ta sauke itama Bata Wani tsaya

Jan wata gaisuwar ba ko batawa juna lokaci ta tambayesa Abinda yasakata Kiran nasa tace

“Bena fa tinda ka dauketa ka tafi da ita baa samunta har yanzu idan aka kira Bata dauka shikuma D tasa ma Bata shiga.”

Shiru yayi tareda sake kallan time yace Shi D Daman wayarsa a kashe suke tin kafin na baro ya bugaci Hakan na kashe masa su,

Ita Kuma Bena din banajin zata qi daga wayar ba dalili gaskia.

“Abinda nake tinani kenan Nima shiyasa na kira, please ko zaka kira ka bincika ko securities na bakin gate din highbridge din zaka tintinba.”

Dan ajiyan zuciya ya sauke sbd Shima gameda lamarin da duk ya shafi DD baya wasa dashi

Dan haka idan har Zeenah tafara tinanin ko ba lafiya ba dole zaije ya duba sbd DD shine top priority nasa a yanzu.

Sallama sukai ya kashe wayar tareda sake kallan lokaci ya sauke laptop dake qafafunsa ya ajiye gefe ya miqe tsaye ya nufi bedroom dinsa Kai tsaye ya dauko key ko kayansa Bai

Wani tsaya canjawaba sbd gajeran wando ne me tsayi da Fadi sosai sai short sleeve shirt takarmi kawai ya zira ya fice.

Gidansa bayada Wani Nisa Sosai da

highbridge sbd DD Dan haka Yana fitowa

yahau titi ba Daman banka gudu tsakar dare ne a kamasa a dauka me lefi ne kafin a gama

gano gaskiyarsa an Bata masa lokaci Dan

haka ya taho a natse Yana Yi Yana duba time

har ya iso highbridge din.

Take aka Bude masa gate ya shige sbd sanin

shi waye sun masa farin sani ire irensu basuda

shamaki da shiga highbridge a ko yaushe suka

ZO.

Duka duka su Safnah Basu rufa 45 min da fita

highbridge dinba ya shigo

Kai tsaye gidan ya nufa yana Isa yayi parking

ya fito Kai tsaye ya dosa kofa ta saka

password Yana sake saka Kiran wayar Bena

datake shiga. Wani mummunan hagayi da qauri ne ya cike palon Wanda ya sakasa shiga mamaki da tsoro da gudu ya nufi hanyar kitchen din wuta yakeci sosai ga ruwa na zuba na kashe wutan sosai Amma Basa Kaiwa koina da wutar take tsabar rudewa ma shi saiya kasa tsayawa kashe wutar ya fito da sauri Yana sake saka

Kiran Bena yaji vibrating din wayar palon Yana dubawa yaga wayar ma dap take da mutuwa

Dan haka ya kashe wayarsa tareda nufar hanyar bedroom din DD Kai tsaye ya Isa da sauri cikin tashin hankali,

Kama kofar yayi zai saka password ya Bude sai ya dakata tinawa da D din ba shi kadai bane a ciki kaman yanda ya Saba akwai yiyuwar Bena ma tana ciki tinda tana gida.

Sakin hannun kofan yayi tareda fara bugawa da karfi sbd yasan ba lallai akejin bugun kofarba.

Yanda yake buga kofan babu alaman motsinsu aciki ya sake saka hankalinsa mummunan tashi Yana kokarin juyawa ya koma kitchen ko wutar ya garasa kashewa

Kiran Zeenah ya shigo wayarsa a rikice ya dauka ya sanar da ita tabbas ba lafiya ba ya tararda gidan wuta tana kokarin kamawa daga kitchen hakama suna ciki Yanata kiransu ba response.

“Ganinan zuwa Nima” Zeenah kawai ta fada masa tana kashe wayar.

Bata bari kowa ya saniba itama ta zari key dinta ta fito daga kaantes ta nufo highbridge itakam a mugun speed sbd Bata damu da

Wanda zai kamata ba tana nuna Id dinta sukaga kaantes zaa saketa batareda Bata lokaci ba.

Ko data iso highbridge securities duk da sunga id card dinta na kaantes daya nuna ita qanwar DD kaante ce Basu barta ya shiga ba sbd lokacin barin masu ziya su shigo ya wuce

Daman da 1 ta wuce duk Wanda ba acikin highbridge din yakeba Basa barin ya shiga. Ranta Baci yake Neman Yi ta kira Naseer dole shi ya kira gate din aka barta ta shigo.

Data shigo ne dole ta Hana kanta gudu da mota Saida ta Isa tayi parking ta fito Kai tsaye tayo cikin

Itama Tari ta fara toro na kamata sosai da ganin hayaqin ta nufi kitchen da mugun gudu ta tadda Naseer duk ya jiqe gurin taimakawa ruwan kashe wutar sbd kamar wutar asiri yakasa kasheta duk da Bata cika kitchen dinba iya inda oven din yake ne taqi mutuwa Kila salya gama cinyewa.

Zeenah fitowa tayi a rikice tayi hanyar bedroom dinsu tana Isa Bata tsaya komaiba ta saka password Kai tsaye ta bude dakin duhu babu haske sosai.

A kan gadonsa ta fara sauke idanuwanta takuma gansu duk su Biyun a kwance kan gadon rufe cikin bargo babu me numfashi a Ihu taso fadawa cikin tsoro da rawar jiki ganin tashigo babu Wanda ya motsa a cikinsu Dan haka da sauri iikinta duka Yana rawa ta zagaya gurin Bena data lura kaman babu kaya jikinta dukkanin hannuwanta rawa sukeyi ta dauki kayan data Gani qasa ta dawo jiki na rawa ta dagata daqyar ta iya saka mata su duk a rude tana gama saka mata ta qwala Kiran Naseer baiji ba ta fito da gudu ta kirasa yaje dakin ita

Kuma ta tsaya Palo tana sake shiga tashin hankali ya taimakawa D Daya Dan motsa alaman Yana yanada sauran Rai ajikinsa ya shirya dole Naseer ne ya dauki Bena yakaita mota ya dawo ya dauko D Shima Wanda yake

Bude Amma Basa buduwa sbd a lokacin ne asalin qwayoyin jikinsa na mummunan maye suke Aiki sbd na desire sun sauka tinda ya sauke bugatansa.

Chapter 76

76

Hankalin tashe cikin toro da firgici Naseer da

Zeenah din suka nufi Asibiti dasu ba tareda sun tsaya sanar da securities komai ba kawai dai Naseer yace musu akwai oven ya kama da wuta a gidan please suje su kashe shi asibiti

zaije.

Yana fada musu yaja motar ya fice da gudu yau Yana karya doka

Su Kuma securities din Kai tsaye gidan suka nufa tareda Isa kitchen suka kashe wutar

Basu tsaya bincika komaiba sbd batareda wata damuwa ko matsala ko zargin Wani abin ba yafada musu Dan haka Suka dauki Hakan a tsautsayi suka rufe gidan suka koma gate kawai. Asibitin kaantes ya nufa dasu cikin mugun gudu kankanin lokaci yakaisu Asibitin cikin gaggawa Aka fito aka karbesu su duka biyun aka shige emergency dasu ta sama.

Ana karbansu aka shige dasu Zeenah ta fidda wayarta cikin tashin hankali da tsoron Daya mamaye zuciyarta ta Nemo numbern Umme ta saka kira.

Harta katse Bata daga ba Dan haka sai Bata sake Kiran ba Kuma Bata nema kowa ba suka fara zarya ita da Naseer kowannensu cikin shiga tinanin da jiran tsammanin dayafi komai azaba sbd matsuwa suje menene matsalar.

Yawo suka ringa yi Zeenah ta kasa zama babban tashin hankalinta da tsoranta idan ba

Wani mummunan al’amarin ne ya samesu ba,

To Amma da alama dai love sukai making a

Karan farko duba da yanayin da aka samesu. Naseer babu Abinda yake ransa da qwaqwalwansa face Jin D ya farfado lafiya.

Ko su Bena dasuke ciki a kwance Basu Kai su

Zeenah din Shan azabar zuciyar ba sbd tashin hankalin Dayake ransu da tsoro yasa idanuwan

Zeenah har sun fara dark circles kanta sai sarawa yakeyi.

Karfe biyu da kusan arbain Umme ta farka shiga toilet kaman ance ta duba wayarta taga misscall din Zeenah,

Da mamaki ta Kalli time na Kiran taga kusan 2 na dare akai Kiran.

Dakatawa tayi daga shiga toilet din ta Kalli dad kaante dake kwance Yana bacci cikin lafiyayyan gadan dakin nasa sai kawai ta saka

Kiran Zeenah sbd taii idan ko jikin Amnah ne data ke da alaman zazzabi ya tashi. Ringing Daya Zeenah a ta cafki Kiran ta daga

Umme na Jin muryarta tasan Bata gida Kai tsaye tace

“Zeenah lafiya kuwa?

Ina kike?

Jikin Amnah ne?

Ya Akai??

Katse ummen tayi da sanar da ita Kai tsaye suna Asibiti da DD da Bena.

Tana fadar Hakan Umme ta Bude murya da kyau tace

“Dawood dai kike magana ko kuwa?

Bena ma?meya same su?

Yaushe?

Meyake faruwa ne? innalillahi.

Bude idanuwa Ras dad kaante yayi Jin Abinda ummen ke fada murya a sake.

Tashi zaune yayi bacci na sakinsa babu Wani sauran magagin bacci ya kalleta yana cewa

“Lafiya?

Meya faru?

Su waye a Asibitin??

Hankali tashe Umme ta juyo ta kallesa tace

“Dawood da Bena ne a asibiti basusan inda kansu yake ba.”

Agogo ya kalla da sauri kafin ya yaye rufar jilkinsa Yana saukowa kan gadon ya qaraso gabanta ya karbi wayar ya saka kunne ya sake tambayar Zeenah da kyau

Ta tabbatar masa da suna Asibiti dasu

Dawood din.

Kashe wayar yayi tareda komawa bedside ya dauki tasa wayar ya fito Palo Yana Neman numbern Abbakar.

Umme ma fitowa tayi ta koma bedroom dinta ta cania doguwar rigar baccinta zuwa doguwar Abaya da mayafi me Dan kauri sbd sanyin tsakar Daren da zasu fita.

Ko data fito dad kaante da Kansa zaiyi tuqi

Abbakar ma tini ya fito daga Dan sashensa dake bayan na Ubandakinsa dd babba Wanda

Shima tini Abbakar ya isar masa da sakon. Motar dad kaante tini tayi gaba tareda Umme shikuma dd babba Shima cewa yayi Abbakar ya fidda mota Suma suje Yana buqatan zuwa Asibitin jikokinsa biyu mafi soyuwa aransa suna Asibiti kwance Rai hannun Allah ana

cewa baa San meyake damunsu ba.

Qanqanin lokaci ya kawosu Asibitin suna isowa kowa Kuma hankalinsa ya Dan sake

shiga damuwa sbd Jin harda wuta aka tadda

a gidan tana ci da baa je da wuri da kilama

mugun labari zaa ji kawai.

A lafiyayyan palon jiran manyansu dake can saman Asibitin suka zazzauna kowa ta girgiza qafa cikin rashin nutsuwan zuciya bayani

kawai suke Jira.

Babu Wani bayani daya zo musu sai kusan karfe 4 Dr Ashley tafara fitowa ta Kalli Zeenah kafin ta Kalli Naseer sbd sune suka taso zuwa inda take da sauri, tanason magana tana kokarin daidaita iya Abinda zata iya fadawa familyn kaantes din a gaban Naseer sbd batasan waye shi ba.

Cikin zaquwa Zeenah tace

“Dr Ashley ki fada koma meye ne wannan din kaman familyn kaantes ne sd Shine kunnuwa da hannuwan DD harma da ganinsa a Alamuransa.

Ajiyan zuciya Dr Ashley ta sake tareda kallans dd babba da ba iya cewa komaiba bayanin Kai yake jira ya gyada mata Kai alaman ta fada kawai suka saurarenta

Ta tausasa murya tafara cewa

“Ita Bena nata ciwon ba komai bane face sex na farkon rayuwarta data samu yau,

Bai Wani je mata da sauki ba ya nuna mata karfi gaskia Dan haka ta jigata ta Kuma tasha wuya sbd na farko ne so rashin saukaka mata muke kyautata zaton ya sakata kasa dauka ta Suma,akwai stitches kadan da Akai mata Dan haka ita inshallah zata farko kowane time sai a fara kulawa da ita da dinkin.”

Shiru gurin ya dauka kowa yayi tsit Zeenah da Naseer suka Kalli juna sbd sune a kusa da juna lokaci Daya kansu na Neman juyawa da

Jin wai sex din farko ga wadda ke da ‘ya.

Umme ma duk rudanin Datake ciki Bai hanata kallan Dr Ashley da sauri ba kafin ta juyo ta

Kalli dad kaante da shi Kuma dd babba ya kalla Wanda Kallo Daya zakai masa kaga babu alaman shock ko mamaki a tareda shi

Basu gama fitowa daga mamakin maganar ba da dauke wuta dd babba ya sake buga kansun da kallan Dr Ashley Kai tsaye yace

“Mun San wannan tinda ita an samu shawo kan tata matsalar Allah ya Yi mata albarka ya Basu zuria dayyaba me albarka da zanyi alfahari dasu,

Shi Dawood din nawa meye matsalarsa???

Shiru Dr Ashley ta Dan Yi Suma suka dawo da kallansu kanta batareda mamakin dd babba yagama sakinsu ba.

Shirunta ya sakasu Jin suna sake shiga damuwa da fargaba.

Numfashi ta sauke jikinta na Dan sanyi ta

Bude baki a natse tace

“DD nasa matsalar kusan ba guda Daya bane gaskia,

Na farko dai Muna kyautata zaton Shima sauke desire me garfin gaske ne a Karan farko

Daya San mace ya sakasa somewa..

Dan shiru tayi ta Dan tauna Abinda zata fada kafin ta sake kallansu taci gaba da cewa

“To Amma Muna zargin akwai mugayen qwayoyin drugs a tareda shi,

Babban tsoronmu akwai kwayan da muke

Zargi wadda idan akwaita a jini take shiga

Nan take Dan haka Kila sai anfitar dashi babu kayan awonta anan,

Muna Koda siyo kayan awonta mukai anan

Muna Yi masa aka Gane zaa soke lasisin wannan Asibitin tamu gabaki Daya, Acan zaa dubata a jikinsa akwai kaman antidote nata da akesha shi kadai yake koneta a jikin mutum idan ba haka ba zai ringa yi ne

Yana taso masa wannan qwayar.

Tsit sukai gurin gabaki Daya sbd babu Wanda ma ya Gane taqamaimai me take nufi sbd rashin yarda da Abinda kunnuwan nasu ke ji musu. Meya hada DD da qwayoyin drugs Kuma?

Bai taba muamalantar su ba rayuwarsa,

Sam shi gyangyamin irin wainnan abubuwan ma yakeyi sbd lafiyarsa,

Yaii ma kaman zai kashesa yake masa bare qwaya,ta na wannan zancen ya fito?

Dd babba Daya kasa yarda ko fahimtar Dr

Ashley din sosai ya Dan gyara zama ya kalleta yace

“Yanzu dai baa tabbatar ba tinani kukeyi right??

Yes Sir” ta fada a natse tana fatan suka tinaninsu kada ya zama gaskia.

Gyada Kai yayi a natse yace

“A bari ya farfado zamuji meya samesa da sauran abubuwan da maganar gwajin ya biyo daga baya.”

Gyada Kai tayi itama tana sake Basu tabbacin inshallah zai farfado lafiya for now dal.

Juyawa tayi tayi sauka zuwa office dinta su

Kuma suka kwasa zuwa dakin DD din Zeenah da dd babba Kuma Bena suka nufi dakinta.

Sosai ta wahala Dan haka fuskarta tayi fayau kaman wadda ta wuni a ciwo bacci yakeyi na wahala da azaba ga zazzabin gaske a jikinta

Daya dauki dumi sosai.

Shiru sukai kowa da Abinda yake ransa yana tinani.

Zeenah kasa Dora zancen cikin Kansa a takeyi wai Bena Bata taba sanin kowane namili ba sai yau,

To ya Akai ta samu cikin Amnah har ta haifeta?

Bangaren su umme ma tinanin suka shiga da damuwa duk da kaf acikinsu babu Wanda ya kama maganar wai qwayoyin maye a jikin DD sod sunsan ba Abu me yiyuwa bane Dan haka

Basu damu da wannan ba sai fatan su farfado kawai su samu lafiya daga shi har Bena din wadda itama Umme tinani ne kala kala cikin kanta game da cewan Bena Bata taba sanin kowane namiji ba sai yau da DD ya sameta a macenta.

To meye Hakan yake nuft?

Idan ana fada musu wannan zancen kenan so ake a fada musu ba Bena ce ta Haifa Amnah ba kokuwa?

Duka kowa Tara tambayoyinsa yayi cikin zuciyarsa da Kansa ya danne har asamu lafiyar su Bena din a koma gida aji gaskiyar kowa daga bakinsa, dashi da ake cewan akwai maye a jininsa da ita da akace budurwace bayan babu wadda zata taba sanin namiii har ta haihu komai shekarun da zatayi Bata sake kwanciva da Wani namiiinba bazata taba hadewa ba kaman budurwar da Bata taba sanin namijinba kwata kwata.

Chapter 77

77

Koda gari ya waye labarin kwanciyar DD kaante da Bena Asibiti ya yadu a family din kaantes na kusa Dana nesa Dan haka wainda suke kusa tini suka fara zuwa dubasa.

Dd babba Yana komawa gida ya saka Abbakar a Hana labarin fita ko kadan sbd tinda Doctors suka fara maganar zargin qwaya a jininsa yan labarai suna ji zasu yada labarin mutincinsu da sunansu zai tabu hakama Shima DD din nasa mutincin da sunan zai iya lalacewa a idan mutane da Manyan gasa abokan huldarsa Dan haka a Hana ko kalma Daya fita ta cewan ma

Yana Asibitin kwance ba lafiya.

****Safnah da momy Suma kwanan zaune sukai a dare babu Wanda bacci ya gifta idanuwansa,

A zaune qyam suka kwana |do Bude cikin taraddadi,tashin hankali da zaquwa suka Kai har safe suja jiran ta inda labari zai dawo musu.

Babu Allah a cikin ransu suna zaune Akai sallar Asuba aka gama Basu tashi sunyi ba Safnah idanuwanta sunyi Wani jajir da kumbura sbd kukan baqin ciki da zuciyarta

Datake Jin ta qarasa bushewa Dan kuwa wallahi bazata yarda tayi biyu babu ba a yanzu da suka Kai wannan matsayin na Bena ta Riga halasta ga DD kaante.

Sai da gari yayi Shar har karfe 8 Saura basuji

Wani bayani ba suka tashi sukai sallah

Suna gamawa ko addua Basu tsaya Yi ba suka mige Safnah tafara kaida kawo hannuwanta na rawa zuciyarta na qara konewa da bushewa tareda daukan zafi tana rasa ta inda zasuji meyake faruwa.

Momy kuwa babban tashin hankalinta da zafin da kanta ya dauka har Wani hayaqi takeji kaman Yana fitowa kunnuwanta na Abinda zai iya biyowa baya idan su Bena Basu mutu ba.

Komai ya taru ya lalace musu a mummunan yanayi da hanya mara bullewa matiqar su

Bena suka rayu,.

Qarshensu ne zaizo a wulagance su rasa komai su qare inda basason garewan sbd komai a fili zai iya bayyana,

Na farko rashin mutuwar su na nufin zaa gano akwai qwayoyin drugs a jinin DD harma da cocaine suka hada duk suka zuba masa Dan haka akwai babbar matsala idan ya rayu,

Na biyu ma Bena idan ta rayu Hakan na nufin dole Safnah zata bar DD Wanda barinsa shine zai Tona ya bayyanarda ita din ba ‘yar bulama bace haka zalika mutuwar hajiyarsa zata iya dawowa sabuwa ga Rabi tasan sirrinsu suna bugatan itama aikata inda bazata zata tafi da sirrin a cikinta har abada ba dawowa.

(100

Dan haka rayuwar su Bena itace qarshen tasu rayuwar.

Wani mummunan zufa ta share tareda kallan

Safnah wadda itama momyn ta Kallo tinani da momyn takeyi shi takeyi sak.

Babu Wanda ya iya cewa komai sbd babu me nutsuwa ko hankalin furta kowace kalma saisun ji labarin halin da ake ciki.

Har kusan goma na safe ba labari Dan haka

Safnah data kasa zama tana tsaye Tim asubar ta dauki wayarta ta saka Kiran umme Kai tsaye zuciyarta na harbawa kaman zata fado. Momy na Jin ta saka kira ta sa a speaker tayi tsit ko numfashi batason ja sbd fargaban

Abinda zasu jl.

Sai da wayar ta kusa yankewa Umme ta dauka tareda sallama a natse cikin sanyi.

Wani busashen yawu Safnah ta hadiye tareda

Bude baki tana Dan dedeta muryanta dake kokarin yankewa tace

“Ina kwana Umme?

Ya gida yasu Zeenah?

“Lafiya kalau Safnah,ya gidan ya momynki?

Lafiya kalau Umme,Daman Umme nace D kunyi magana dashi kuwa?

Wayoyinsa duka Basa zuwa na kira Naseer

Shima tasa a kashe banajin nutsuwan zuciyata game da rashin samunsa Umme.

Numfashi me dumi Umme ta sauke sbd sai alokacin ta Tina ma Safnah ma nada haqgi akansa Daya kamata tasan meya samesa Dan haka ta Dan sake yin sanyi a natse tace

“Safnah wIh hankula ne suka dauku sbd tashin hankalin da aka shiga na Abinda ya samesa shiyasa aka Manta shaf baa nemeki an sanar dake ba,

Yana Asibiti Tim tsakar dare jiya shi da Bena

Basu da lafiya arziki sukai wuta ta so kama gidansa dake highbridge Kuma ba.

Umme Bata garasa ba Safnah ta Yanke jiki ta zube qasa idanuwanta na juyewa.

Momy ma zubewa qasan tayi tana Neman somewa Amma tayi qarfin halin daukan wayar da Safnah ta saki ta Dora a kunnenta muryarta na yankewa da qyar ta iya cewa

“Shock ya saka Safnah sumewa itama gatanan zuwa zata kawota Asibiti”

Ko amsata Umme bataiba ta kashe wayar tareda migewa tana Gani dishi dishi sbd tsabar tashin hankali ta nufi dakinta a rikice ta janyo drowan gefen gadonta ta Ciro wata allurar jininta Data ke Jin kaman ya Haye zuwa 200+ take tayi wa kanta tana zubewa qasa tana fidda numfashi da sauri sauri Dan dawowa daidai.

Kusan fiyeda Rabin awa ta dauka kafin ta dawo daidai ta tashi jikinta na fizga da tashin hankali da baqin ciki ta nufi Palo Kai tsaye kitchen ta nufa ta dauko ruw ta zubawa

Safnah wadda koyaushe ta some kaman wadda ta mutu take.

Safnah na farfadowa momy ta kalla itama momyn ita take kalla tana cewa

Tashi mu fara kokarin hada kan Abinda muka samu dole mu bace bat mubar qasar gaba

Daya wIh bazanje prison ba.

Cikin bagin ciki da rasa abin fada Safnah tace

“dan munie prison mun samu sassauci da sauki kenan,

Kin manta momy kisa fa mukal,

Hajiya fa muka kashe,

Kina tinanin Dad zai gyale mu ne?

Su kaantes kina ganin zasu bari ko prison din akaimu?

Wih kashemu zaayi kisan wulaqanci Kuma,

Bazan yarda naje prison ba yanzu bare lahira lokacina baiyib,

Muna guduwa ba wahalar bincike zaa Gane mune mukai komai muka gudu Dan haka wIh Neman mu bazai musu wuya ba.

Idan Bena sungi mutuwa to dole Bena tabarsa bari na har abada ta Hakan ne asalina zai rufu

Kuma ta Hakan ne DD da kaantes bazasu taba samun nutsuwar yin bincike sosaiba a komai zasu mayarda hankali gurin Nemanta da tinanin inda ta bace bat babuta ba labarinta har abada haka zalika DD dole nice zanci gaba da zama matarsa.

Jajayen idanuwan momy ta zubawa Safnah tana juya zancen cikin kanta to Amma ta

Yava zasu batar da Bena tinda shegiyar taqi mutuwa a Karo na biyu.

“Kasheta zamu sake Vi” inii Safnah da idanuwanta suka gama rufewa fiyeda kowane lokaci sbd yanzu sun Kai karshen karshe na idan suka rasa wannan Karan to sai lahira ko prison.

Katseta momy tayi cikin zurfafa nata tinanin tace “Bazamu kasheta ba sbd munyi na farko babu nasara,

Munyi na biyu ba nasara

munayin na ukun Nan to tabbas babu shakka kamamu zaayi a saukake.

Shiru Safnah tayi sbd kota yayane dai dole sai sun samowa kansu mafita kafin DD ya farfado duk da Kila zai iya kwana biyu Bai dawo daidaiba kuma zaiya farfadowa kowane lokacin Dan haka Basu da lokacin batawa har mummunan kaddararsu tazo ta samesu suna

zaune.

Tinani suka fada cikin tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya da gangar jiki kansu kaman zasu kama da wuta sbd tension.

Safnah ce tinanin da Abinda taketa gujewa yaketa dawo mata cikin Kai Wanda ko sunan ta fada cikin kanta bugawa kan yake Neman Yi sbd tsoro da firgici me tsananin gaske hakama zuciyarta sunansa kawai Neman tsayawa bugawa takeyi Dan duk yanda takai ta goge a duk Wani aikin rashin Imani har gobe Ababa tsoronsa da shakkarsa a cikin jininta yake ba ita kadaiba dukkaninsu yayansa.,

Ababa sunansa kadai jikinta rawa yake dauka idan ta Tino Amma Kuma tana ganin lokaci yayi da zata Kai Kanta gabansa,

‘Idan har zai iya sauya sumayyah data mutu da Benazir ya boye mutuwarta ya bayyanarda benazir matsayin wadda tayi cikin shege ta haihuwa duk akan kudi gashi kudin kaantes dinma dayake Jira ba samu zaiyiba sbd Anne data lalata masa komai Bai saniba tarko sukai masa da zai Kamasa a lokacinda baida gurin tsira.

Dan haka lokaci yayi dazai San Abinda su

Anne sukai masa,

Yasan babu Abinda zai same daga kaantes,

Zasu basa kudin da ko Basuyi yawan Wanda zai samu a Kaantes ba ta xasu kusa sbd ya hade a cikinsu ya tsaya tsam ya Hana bayyanar Safnah ‘yarsa ce kota halin Yaya.

Momy shiru tayi lokacin da tagama sauraran

Safnah da wanna sabon plan din nata da tabbas ko ita da batasan Ababan ba tana Jin tsigan jikinta tashi a duk lokacinda Safnah take fadar halayensa da taurin zuciyarsa cikin tsoro da kyarma.

Idan har yanda Safnah ke fadan Ababa Tim baya haka yake to shigowarsa cikinsu komai zai tafi musu a daidai sbd da alama zaifi su sanin hanyoyin kawowa Kansu nasara,idan ma dukiyar Bulama yakeson a raba daidai dashi bayan sun kammala qwashe komai zasu raba din matiqar xai fiddasu a cikin motsalan dasuke ciki dumu dumu,

Haka zalika shine kadai yakeda mukullin juya rayuwar Bena a duk yanda yaso sbd Annenta

Datake hannunsa wadda zata iya Koma akanta,haka zalika su Kuma kaantes yanzu

Bena ce mukullin dazai iya juya raywarsu da ita sbd tsananin son Dasuke mata hardai yanzu da zasusan ba itace ta haifi Amnah ba.

Momy da lamarin da tsarin sukai mata shegen

Dadi ta saki Wani dariyar samun sanyin zuciya tace

“Idan ba Bai yarda ya dawo cikinmu an samar da mafita ba to Shima watan tonuwar nasa asirin ne ya tsayu,

Daga lokacinda kaantes suka gama sanin ba

Bena ce ta haifi Amnah ba to alokacin zaayi tariyar zancen yanda yayi ha’incin sauyawa

Amnah mahaifiya Yakuma rusa rayuwar

Bena,haka zalika jinin sameerah a hannunsa yake Dan haka daki day zaa Bamu a prison.

Cikin zurfafa tinani da ‘dacin zuciya Safnah

tace

“Ababa babu Abinda bazai iyaba akan kudi,

Jin Abinda su Anne da Bena sukai masa zaisa ko bamu buqaci Basa kudi ya fiddamu a wannan halinba zai iya kashe mana Bena har lahira cikin sauki.

Amma a yanzu banason Bena ta mutu sbd

Anne,

Amma dole zata bar rayuwarmu data DD har abada.

Chapter 78

78

Guraren 11 Bena ta farfado ahankali jiki duk babu qwari hakama dumi ne a jikinta sosai.

Umme da Zeenah harma da Siyam da mum

Khadija ta Gani a dakin Dan haka ta fahimci a inda take wato Asibiti.

Abinda ya faru da rayuwarta a wanni kusan goma Sha Wani Abu da suka wuce ya sakata

Jin kanta na juyawa tareda jikinta dake sake daukan dumi na zazzabi da gabobin jikinta dake ciwo har okacin.

Mayar da idanuwanta tayi ta rufe ahankali tareda Jin hawaye masu dumi sun gangaro gefen idanuwanta Wanda Hakan ya saka su

Umme sanii ta farka Dan haka cikeda kulawa

Umme da Zeenah data taso suka fara Yi mata sanni kafin su mum Khadija Suma daga baya sukai mata suna tambayarta jikin nata.

Bata iya magana ba bare amsawa sbd kunya

da ciwon da jikinta keyi tareda azabar Dan

stitches dinta dake mata zafi sosai ya sata ko

kasa dagowa ta kallesu.

Ganin Hakan ya saka Umme kallan mum

Khadija tace bari su koma daga qaramin

Sitting room na dakin na nan Asibitin su Bata

Daman wanka da Dan gasa ilkinta ko zata sake.

Harda Siyam suka fice Zeenah kawai aka bari

ta taimaka mata tashi zaune jikinta zafi sosai.

Bayan tashinta zaune kasa daurewa tayi duk

da yanayin Datake tanason jin waye ya kawota

Asibiti sbd idan Bata manta ba Shima D baida

lafiya kafin tarayyarsu Duk da dai ya nuna

mata alamar lafiyarsa Kalau da wanna abin

dayayi mata.

Har zata tambayi Zeenah din sai Kuma ta kasa sbd harda itama yau kuniyarta takeji sbd

Bata saniba ko sunsan Abinda yayi sanadin zuwanta Asibitin.

Ahankali take tafiya jiri na Dan Neman dibarta dole Zeenah ta sake kamata ta Rakata har cikin toilet din ta hada mata ruwan zafi Dan gasa jikinta ya warware da kyau dakuma shiga cikin ruwan.

Fitowa Zeenah tayi ta barota cikin toilet din tareda janyo mata kofa.

Ruwan zafin da lallaba ta shiga tana rintse idanuwanta sbd radadin azaba da Kuma in datakeyi kaman kanta zai fashe sbd ciwo.

Shiga ruwan ta daure tayi tareda rufe idanuwanta tana kokarin Tina abubuwan dasuka farun Amma ita kanta da kanta kunyar tinawa takeyi Dan haka ta tattara tinanin ta danne a zuciyarta ta samu tayi wanka ta gasa ilkinta da kyau ta Dan ji jikin ya saki ta fito, babu kowa a dakin sai Zeenah wadda ta ajiye mata kayan da aka kawo mata daga gida kan gado tareda undies da body mist kawai me tsadan gaske.

Pant da halfvest data kama mata kirji ba sosai ba ta saka kawai sai doquwan free rigan

English material me tsada da rashin hayaniva ta saka tareda garamin hula sai alokacin tasamu sauke sallar Datake kanta da rashin sanin inda kanta yake yasa bataiba.

Tana idarwa tea kawai Zeenah ta hada mata lokacin su Umme suka dawo su Mum Khadiia zasu mata sallama su wuce.

Ya jiki suka sake mata kafin sukai sallama sika tafi. Daqyar take iya Shan tea din sbd cikinta dake matse batasan Shan komai ga Kuma zazzabin

Datake ji har Time din.

Bayan tea dagyar Umme ta sakata dole cin pepper soup din Naman rago daya dahu sosai yayi mugun laushi.

Tana gamawa ba jimawa ta amayar dashi tas

Wani sabon zazzabin na sake tsananta gareta.

Likita aka kirawo tayi mata wata allurar tareda daura mata ruwan da baa daura ba tin farko.

Rufeta Zeenah tayi cikin sanyin jiki da tausayawa suna murnar ta farfado sauki zaizo

Kuma sai gashi ta sake birkicewa

Umme ma zuwa yamma hankalinsu va tsananta tashi sbd dai har lokacin DD Bai farfado ba,

Suma likitocin Basu dauka zai Kai wannan lokacin Bai farfado ba Dan haka Suka hau dubaru da duba Abinda zaisa ya farfadon.

Can gida ma daga dd babba har dad kaante da sauran family hankalinsu ya fara tashi sbd rashin tashin DD din.

Haka aka hanye wunin tass aka kwana a tsaye babu alaman zai tashi tini Umme da Zeenah suka Sha Wani irin Kuka idanuwansu sukai luhu luhu sbd Kuka,

Shi Kansa dd babba ba garamin tsoro zuciyarta ta riska ba da wannan Lamarin dake

Shirin faruwa dasu,

Me Hakan ke nufi?

Daman ana samun haka ne daga kwanciyar aure? Bena dake fama da kanta boye mata Akai baa fada mata halinda ake ciki da DD din ba ita

Kuma ciwo da kunya ya hanata iya tambayar

Yana Ina.

Safnah tin Rana ta iso Asibitin itama Tasha kukan rashin tashin mijinta har sai dare Umme ta sakata tafiya gida dole sbd dd babba yace babu me kwana da DD din idan ba Naseer ba.

**Bayan komawar Safnah gida da daddare kasa zaune tayi ta kasa tsaye tana cikin toro da firgici tareda bugawan zuciya akan haduwar da zasuyi da Ababa washe gari,

A duk lokacinda ta Tina da goben zata tsaya gaban Wanda tasan baya yafiya sai taji toro na Neman gigitata,

Jin takeyi kaman zai mayar da ita kajin gidansa ya rufe,

Badan Abinda suke so din ba a ynzu shine last mafita da hope dinsu da har abada babu Abinda zai maidata ko hanyar gidan bare iya tsayuwa a gabansa da sunan magana.

Firgitata ma lamarin ke Yi duk bayan tinani.

Momy data ga irin mummunan tashin hankali da tsoron me tsanani Datake shiga akan tinawa kawai da Wanda zasu gurinsa ta ringa

Bata qwarin gwiwa akan cewa yanzu babu

Abinda Ababa zai iva Yi mata sbd ba Safnar baya bace baiwarsa Kuma dabbarsa,

A yanzu ita Safnah bulama ce, tana kudin da zata hanasa zaman lafiya da kwanciyar hankali idan taso Dan haka babu Abinda zai lyayi mata a yanzu.

Shiru kawai Safnah tayi tanason dilmiya a maganganun momy Amma zuciyarta na sake tsayar da ita waye Ababa,duk kudin da zasuyi tsoran takunsa kawai ma a cikin jininsu yake da bazasu taba iya gogewa. Amma dai Abu biyu ne a yanzu a rayuwarta,inma ta dake ta tinkaresa ta Siya yancin kanta daga garesa tareda bayyanar masa da bugatansu,

Inma Kuma su zauna Jira sunaji suna Gani su gama yawo qarshensu yazo, Dan haka ta zabarwa kanta tinkarar Ababa su fuskanci juna,

Zata fara Sivan ‘yancinta daga garesa kafin gabatar da komai.

Washe gari a matse dukkaninsu suka kwana suka tashi sbd rashin sukuni da fargaban ko

DD ya farka,

Matigar ya farka Basu samu mafitaba to fa sunansu matattu tinda komai ma bincika zaa fara Yi a gano.

Momy tafi Safnah matsuwar su hadu da

Ababa sbd tarin Abinda take hangowa Safnah

Bata hangosu matiqar Ba siyi gaggawan ganin

Ababa ta yanda idan Bai amince musu ba sunada sauran time na harhada abubuwansu su gudu.

Safnah kuwa har lokacin zuciyarta cike take da tsoro da fargaban mahaifinta.

Karfe goma daidai lafiyayyar motar Safnah tayi parking kofar gidan Ababa Wanda hannuwanta gabaki Daya rawa sukeyi sosai hakama zuciyarta Neman Faso kirjinta takeyi.

Kallanta momy ta juyo tayi a hankali tareda tsayar da idanuwanta kan Dan siririn zufan

Daya tsiyayo mata daga goshinta ya gangara zuwa wuyanta. Kasa juyowa tayi ta Kalli momy sbd babu

Abinda idanuwayke Gani sani mutuwar

sameerah da kusan koyaushe take Jin kaman

itada Ababa ne suka kasheta tinda tana Kallo

lokacinda sameerah ta manta tabar dakin

hande Bude Amma tagi fitowa daga inda take

kallanta ta fada mata har Saida sanyi da iska

suka tayarda hande bacci ta cimmata a kofar

gidan da batai nasarar budewaba da wuri.

Masifu da balai da ukubar dasuka taso ciki

suka tayi aciki take tinawa tana Gani ta ko Ina

tini rawar hannuwanta ta qaru har jikinta Yana

dauka zufanta na qaruwa sosai.

Tashi hankalin momy yayi tayi saurin kama

hannuwanta tana Dan jijjjigata tana Kiran

sunanta tace

“Karki yarda ki bari tsoron zuciyarki yayi nasara

akan Abinda muka zo Yi wlh halaka Zaki jefa

mu,

A halake muke ma bari ki sani Dan wlh kowanne lokaci Muna iya zama labari gwara ki nutsu mugani idan Ababan zai samar mana

hanya me bullewa,

Ke ni wlh ko duka sai mu mallaka masa

Abinda muka samu mu fita wannan masifar idan yado daga baya mun dasa sabuwar hanyar dawo da dukiyarmu hannunmu,

Ki nutsu idan Zaki nutsu ba lokacin shiga tsoro

bane da firgici.

Wani busashen yawu Safnah ta hadiye tareda zaran tissue dake motan ta share zufanta a hankali tana kokarin daidaita kanta faduwan gabanta na Neman tsananta tana kokarin

controlling nasa.

Facemask ta Ciro a hankali ta saka tareda qatan glass ta juyo ta Kallo momy

Momyn ma ita ta kalla suka sauke ajlyar zuciya a tare kafin momy ta Bude motar ahankali ta fito daukeda qatuwar handbag dinta dake cike

dam da bundles na kudi har Dana dollar.

Makeken Chanel sunglasses ne a fuskarta ta nufi kofar shiga gidan ta shiga sai data shigo da bakin tsakar gidan tayi sallama ahankali tana kallan gidan.

Hande na dakinta tana Shan redionta Anne ce a tsakar gidan tana wankin kayan shagonsa a natse kanta aqasa.

Bataji sallamar farko ba sbd kunnuwan sun gara tabarbarewa sbd Marika datake Sha da wahala,

Tinda ta gudu dinnan aka dawo da ita azabar rayuwar gidan ta dawo sabuwa FIL batada ranar da zatace tanada sauki gareta.

Saida momy ta sake sallama da qarfi kafin

Anne taji ta dauko ta Kalli momy Wanda take kallanta cikin Dan kokarin sake fuska Dan tasan halaka suka kawo mata idan Ababa yaji

Abinda suka kawo masa.

Cire hannuwa daga wanki Anne tayi tana kallan momy tana kokarin Tina inda ta ganta sbd tabbas tasan fuskar.

Kanta ne ya Dan ringa juyawa tafara Dan girgiza sa tana kallan momy idanuwanta a

waje.

Faduwa gaban momy yayi kada haukar matar

Nan ya tashi tayo cikinta fa batareda tayi

Abinda ya kawotaba.

Momy na ganin Anne tana yowa gurinta ta sake Bude baki da garfi tayi sallama kafin ta rufe baki Anne ta ambaci sunan Sameerah tana kallan momy,

Girgiza Kai tayi tana cibaga da bubbuga kanta tana maimaita sunan Sameerah sameerah sameerah…….tana haka Hande ta fito daidai lokacinda Anne ta girgiza Kai da karfi tace

“ba sameerah ba Safnah ce,

Safnah ce,Safnah.

Momy na Jin Hakan Wani zufa ya Dan yanko mata Hande ta qaraso gurin da sauri tana riqe

Anne cikin tsawa me qarfi zatai magana Anne ta fizgi hannunta tana cewa

“Safnah ce sameerah ba,kece da Safnah.

Hande na ganin Hakan tasan abin ne yake

Neman motsawa cikin daga murya ta hau

Kiran Ababa Dayake dakinsa ya fito fuskarsa a matigar hade ya kallesu kafin ya Kalli baquwar dake tsayen tana daf da juyawa ta bar gidan kada Anne ta Tara musu mutane Yana cewa

“Uban waye yake Kiran sunan Safnah a cikin gidana?”

“Uban waye yake Kiran sunan Safnah a cikin gidana?”

Anne da kanta ke Dan juyawa Yana kokarin dawo mata da Abinda ya faru ranar tasake ambatar sunan Safnah

Ababa ya kalleta Yana Hana kansa fasa bakinta sbd baquwar dake tsaye wadda ko baa fada ba yasan itama daga kaantes take Kila sbd komai na alamar kudi sun nuna a tareda ita.

Chapter 79

79

*****

Momy ce tafara Bude baki ta gaidasa cikin

Dan kamewa sbd ganin kallan Dayake mata,

Sam bayason baqi kowanne suna shigowa gidansa sbd baya San kowa na sakawa rayuwar Dayake gudanarwa cikin gidansa Ido.

Amsa gaisuwanta yayi Yana kallan hande yace tayi ciki da Anne

Fizgarta Anne tayi tana cewa

“Muie ni wannan masifa har Ina da tsufana anbarni da aikin kulawa da mahaukaciya,

‘yarki na can cikin daula tana hutawa da ‘yarta tabarni da aikin kulan mara da mahaukaciyar uwa ayi magana su miqawa Ababa kudi yace na Dena damunsa da zancen Ina dawainiva da mahaukaciyar.

Daki hande taja Anne suna shigewa momy ta juyo ahankali tareda sauke numfashi me dumi da ajiyan zuciya ta Kalli Ababa suka sake gaisawa Kai tsaye ya tambayeta daga ita ba walwala a fuskarsa.

Numfashi ta sake saukewa tareda Dan gyara tsayuwa ta Bude baki tace

“Magana ce me mahimmanci da girma ta kawoni…

Akan me kenan??”Ababa ya katseta sbd bayasan kwana kwana ko batawa Kai lokaci matiqar ba garkar samunsa bace.

Sake kallansa momy tayi itama Kai tsaye tace “Akan halinda kake ciki muma muke ciki,a taqaice dai akan safnah ‘yarka dakaji mahaifiyarta na fada…

Wani mummunan matsiyacin kallai ya dago idanuwansa yayiwa momy sauran annurin fuskarsa na daukewa gaba Daya ya juyo da kyau ya kalleta zaiyi magana ta Bude bakin

Jakarta nuna masa daurin kudaden dollar dake sama kafin na nairas a qasa.

Kudin ya kalla da kyau ya ga Basu kama da fake ba Dan haka ya dauke kallansa akansu ya dawo dashi kan momy suka Kalli juna ta gyada masa Kai alamar zasu iya magana yanzu.

Wani numfashi ya sauke sbd mamakin matar datasan kudi sune Abinda ke karkatasa ga wata lanqwasar,

To Amma idan Safnah data ambata tana nufin safnan data gudu daga gidansa ce tsawon shekaru masu yawa wh wannan kudin bazai fidda ita daga hannunsa ba.

Ta dawo da kanta ne a daidai lokacin da yake

Neman ‘ya ko ta sata ce ya migawa yan drugs din Daya ci kudadensu sama da miliyoya

Dan haka babu Abinda zai hanasa hukunta rayuwarta mafi munin hukunci kuwa.

Palonsa suka garasa Yana gaba taba bayansa har cikin palon ya zauna a natse tareda Nuna mata guri ta zauna itama a natse tareda ajiye

Jakarta gefenta.

Numfashi ta sake saukewa a Karo na uku da ajiyan zuciya kafin ta kallesa dakyau ta tattara hankali da tinaninta guri Daya tafara da cewa

“Sunana hai Nuratu matar Alh basheer bulama,.

Kallanta Ababa ya sake Yi da sauri sbd baya mantuwa ga duk Abinda yakeso ko ya tsana ko lissafinsa ya sauka Akai,

Alh basheer bulama shine ‘yarsa ta auri DD kaante Rana Daya da Benazir.

Wani tinani ne kawai yafara zuwa Kansa a take kafin ta qarasa bayanin na kishin ‘yarsu ya kawosu akan tasa ‘yar Amma zai gama Jin Abinda taxo dashi da inda sunan Safnah ya shiga bakinta.

Ci gaba da bayani momy tayi da cewa

“Nice momy din matar Dawood kaante Daya wadda aka daura masa aure da ita Rana Daya da Bena Kuma nice marigiyar ‘yarka Safnah data bar gida a baya.

Shiru Ababa yayi Kansa na daukan caji da maganganun data fada din.

Kallanta yayi da kyau Yana Dan gyara zama yace

“Bangane marigiyar ‘yata ba Kuma mahaifiyar

Matar Dawood?

Ke menene sunan Taki yar matar Dawood din??

“Safnah basheer bulama” ta fada Kai tsaye.

Ni tawa yar Datake hannunki da wane sunan take amfani yanzu?

“Safnah basheer bulama” ta sake fada Kai tsaye.

Shiru Ababa yayi ahankali ahankali zafin kansa na tashi sbd Jin sabon zancen kaman bana hankali ba, Safnah basheer bulama har so biyu a gida

Daya??

Zare hular Kansa yayi ya ajiye gefe sbd zufan da Kansa ya a Dan fara hadawa ya kalleta yace

“I dan sunan yarki Safnah bulama,tawa ma

Safnah bulama a cikinsu da waye aka daurawa

DD aure da ita??

Sake sauke numfashi momy tayi tareda gyara zama Dan Yi masa gwari gwarin zancen Dalla

Dalla tace

“Safnah ‘yarka da ita aka daurawa DD kaante aure,Kuma Nima itace ‘yar tawa ‘yar Alh basheer bulama.,

Bayan barinta gida nice na tsinceta Kuma nice na bayyanar da ita ga Alh basheer bulama a matsayin ‘yar Dana Haifa masa,

Safnah ‘yarka itace ‘yar basheer bulama..

Shiru Ababa yayi zuwa lokacin zafin kansa sosai yake ci ya Bude baki cikin tsananin mamaki da tiririn Kai yace

“Benazir da Safnah miji Daya suke aure kenan?

Safnan tawa yar itace Kuma ta koma ‘yar Alh basheer bulama wadda aketa ikirarin babu

Abinda yakeso Sama da ita,

Auren mi Daya a tsakanin ‘yaya biyu to na waye ya haramta acikinsu yanzu??

Momy da Nan takeson Akai tace

“Aurensa da Safnah ya Riga ya haramta sbd

Bena yanzu haka tana Asibiti kwance ita ya fara mayarwa matarsa.”

Sai alokacin Ababa ya dago ya Kalli momy

Yana share zufansa sbd tsaka me wuyan da zasu sakasa idan akace na Bena ne zai haramta Dan kuwa shi ita Kai tsaye yake bugata a Kaantes,

Ko sumayyah ta dawo duniya yanzu akace ya zabi wadda zata zauna aciki Bena zai tsaya ta zaunu a ciki sbd itace saarsa.

Kai tsaye momy ya kalla Yace “Ina Safnah?

Girgiza masa Kai tayi tace

Ka nutsu kaji asalin Abinda ya kawoni.

Wani mugun Kallo yayi mata sbd a yanzu

Safnah yake buqatan Gani gabansa kawai yaga inda ta samu zarra da qarfin zuciyan iya barin Wani ya tinkaresa da zancensa bayan tana kusa dasu Ashe.

Zafi zuciyarsa ta dauka sosai sbd gabaki Daya zancen tafasa jininsa yayi duk Wani zafin kansa da zafin zuciyarsa suka taso.

Momy data ga yanda lamarin zai lalace batareda sunyi maganar datazo da ita ba ta fidda wayarta kawai ta Nemo recording din maganar Anne ta kunna masa tareda ajiyewa gabansa muryan Anne na fita cikin kyakyawan sauti tana fadan vanda Ababan yayi komai da yanda ya canja Bena da sumayyah dakuma gaskiyar sumayyah ce ta haifi Amnah da yanda ta fadawa dd babba komai da alqawarin da dd babba yayi make na ganin qarshen

Ababa.

Tsit palon yayi har recording din yagama playing bayan numfashinsa dake fita babu

Abinda yake motsawa a jikin Ababa, Sake kunnawa yayi ya sake saurara,Yana qarewa ya sake kunnawa har so hudu ya tabbatarda muryan Anne ce da kanta take maganar,

daidai Nan Kuma Safnah ta shigo palon Kai tsaye ta kofar waje dake kawoka cikin palon direct.

491 a

1 101

Daqyar take iya daga kowane takunta tana garasowa cikin tsakiyar palon.

Bugawan zuciyarta har ta saman kayanta ake ganinsa sbd tsananin tsoro da firgicin Dayake cikinta,

Tsayawa tayi a inda take gafafuwanta da hannuwanta na rawa ta dame hannuwanta sbd rawarsu ta tsananta.

Bata iya dagowa ta Kalli Ababa sbd Shima Wani horo ne da har abada Kila bazasu iya denawa ba saidai Nan gaba Kila idan ya shiga

cikinsu.

Tinda ta shigo ta tsaya Kallo Daya Ababa yayi mata da idanuwansa dasuka kada sukai jajir lokaci Daya da Wani irin mummunan tashin hankali bagin ciki tafasar jini da zuciya.

2 PA

Sharkaf ya jige da zufan da baimasan meyake akai Dan Adam keda irin wannan ruwan me yawa cikin jikinsa sbd har Wani tsiyaya yakeyi.

A tsawon shekarunsa baa taba Yi masa

Abinda ya jijiga duniyarsa da tinaninsa irin wannanba,

• A tsawon shekarun Nan Ashe kallansa ake tsaf Angama sanin komai gameda shirinsa,

Tarko aka hada masa mummunan da baisaniba Bai zataba saidai kawai yajisa aciki,

Duk wahala da gararin Daya ringa yi Yana kashe Kansa da lissafi da tinanin ya gama samun Abinda yakeso ranar kawai yake jira

Ashe babu ranar zuwan wanna ranar bare ya

Gani.

Lallai Anne ta demo Abinda kanta bazai iya dauka ba,

Benazir ma ta debo Abinda kanta bazai dauki nata ba bare na uwarta.

Safnah datake tsaye ya dago itama ya sake kalla da jajayen idanuwansa ya miqe tsaye ya nufeta

Take rawar hannuwanta tsananta sbd dukkaninsu da uwarsu wIh babu Wanda zai fita Basu he gasa tare ba.

Tsayuwarsa gabanta ya sakata dagowa ahankali tana fidda Wani irin zufa ta kallesa ko gama sauke idanuwanta akansa bataiba ya sauke mata Wani mummunan Marin bayan hannun Daya sakata zubewa qasa gefen bakinta Yana zubarda jini

Qafa ya saka yayi mata mugun Harbin data gangara gefe tana Dafe cikinta hannuwanta na tsananta rawa Kuma har lokacin ta kasa Bude baki tayi ihu ko Kuka, Jajir kawai idanuwanta sukai Wanda yake nuna tabbacin taurin zuciyar Datake dashi da bushewa ya saka qafarsa Daya ya take wuyanta daidai magoshinta tini tafara Shure

Shure tana Neman rasa ranta ga bakinta lokacin ya sake zubarda jini sosai sbd ba qaramin muni Marin Daya saukar mata yayi ba.

Momy dataga masifar rashin Imani Dayake

Neman daidai da nata koma fin nata sbd su a tsorace cikin rawar jiki suke komai Ababa kuwa hankalinsa kwance yake Neman kasheta har lahira babu toro ko rawar iiki a tareda shi.

Da sauri tazo gabansa tana kokarin cire

Safnah daga garqashin kafafunsa tana rokan ya saketa zata mutu.

Bai saurara Saida ya Bude baki yace

“Idan ma ta mutu ke kinada bagin ciki ne?

Tafi kowa sanin waye ni Amma har ta lya dawowa bayan ta gudu daga gareni tazo ta tsaya gabana Kuna tinanin na amsheta hannu biyu ne?

Somewa Safnah tai sai alokacin ya dauke kafarsa daga wuyanta zuciyarsa na tafasa da tsananin zafi da jininsa dake quna ya nufi cikin gida Kai tsaye dakin Anne ya nufa hande na ganin wucewarsa ta fito daga dakinta tana tambayar lafiya.

Yana shiga dakin wuyanta ya fara shagowa Bai tsaya komaiba ya janyota kaman ba mutum ba ya fito da ita har cikin palonsa ya jefar da ita gasa sai alokacin idanuwanta suka Bude cikin wahala ta Kalli gabanta tayi arba da fuskar Safnah kwance a some itama bakinta na zubar da jini.

Rufe idanuwa Anne tayi jikinta mace ta Bude ahankali ta sake dubawa dakyau taga Safnah dinta ce,

Wani nauyi zuciyarta yayi sbd idan har lafiyanta kalau ba cikin hali ne na hauka take ba idanuwanta ke nuna mata Safnah to tabbas

‘yarta ce take Gani gabanta.

Kokarin tashi tayi Dan sake Gani dakyau

Amma Ababa ya shaqota tareda fizgo wayar momy ya kunna make a maganarta taji.

Tinda tafara sauraran recording din ta fahimci itace Kuma shikenan Ababa yasan Abinda komai zai iva lalacewa Bena dinta.

Duk Abinda ya shafi Bena a yanzu kaman rayuwarta yake Dan haka jikinta ya dauki rawa idanuwanta suka fara sauyawa zuwa ia sbd

Abinda ya taso daga zuciyarta na tsananin fargaba da tashin hankali.

Chapter 80

80

Rawa bakin Anne keyi kaman yanda duka jikinta ya dauki rawa ta Bude baki zatayi magana ya dauketa lafiyayyan Marin bayan hannun daya sakar mata habo itama a take.

Bata damu da jinin dake zubo mata ba ta sake dagowa zatai magana ya shagota cikin Kansa dake Neman juyewa sbd bagin ciki da masifar dake cin jininsa da Kansa.

Hande data shigo tana sake ihun tambayar lafiya kan Safnah idanuwanta suka fara sauka ta tsaya ta duba dakyau dakyau ta tabbatarda

Safnah ce sbd kamannin Basu sauyaba duk da girma da sauyin rayuwar data samu.

Bata bi takan Anne dake Neman mutuwa hannun Ababa ba tayi kan Safnah da momy ke Neman ruwan zuba mata ta farfado a rikice take cewa “Waye wannan kamar baqar ‘yar can Safnah data tsallake uwarta ta gudu ta fada duniya.”

Ababa kuwa baimasan me hande ke fada ba

Jin yake baqin cikinsa na ninkin ninkuwa akan

Anne da duka Abinda ta Haifa masa babu

Abinda suka qaresa dashi sai baqin ciki da asara kan asara.

Wato ita yanxu Nan acikin hauka harta samu

Daman ganin dd babba tafada masa komai bayan algawarin dayayi na hallaka duk Wanda ya fitarda zancen Nan har Abada,

Wato shi wahalar banza ma yakeyi ya sharewa

Bena guri ya samar mata gun shiga da zama a

Kaantes qarshensa kawai suke Jira.

Tabbas da Badan Anne dake hannunsa ba da tini sun Dade da aikasa inda Bai taba tinaniba. Wane babban balai da masifar ne wannan?

Sannan yanzu wannan shedaniyar da sabuwar uwarta suna Karanto masa zancen miji Daya

Bena da safnan ke aure kenan dai a daidai Nan kowa alalensa ta kwabe masa,

Idan har tasa Alalan ta kwabe to wlh ta kowama kwabewa zatayi ta Hakan zai samu tasa mafitar fita da wannan zagayen da Akai masa sbd a yanzu kam zagaye yake baida tudin tsira.

Sakin Anne yayi tareda jefar da ita gefe ta zube tana kasa sakin ko tarin azaba sbd wahala ko fita bayayi.

Magana hande ta hau Yi tana tsinewa Safnah da gudunta da dawowanta Wanda yake sake qular da zuciyar Ababa ya kasa rige Kansa ya hada da Annen da Safnah yayi musu shegen duka Yana fatan ace Bena na gurin ya hada da ita Dan kuwa a yanzu dukkaninsu babu me amfani a gurinsa rayuwarsu da mutuwarsu duka Daya ce a gunsa Amma ko ta halin yayane sai ya samar da amfanin garshe daga gurinsu kafin gamawa da rayuwarsu.

Momy tin Datake Bata taba shiga mamaki da tsoron ganin me aikata barna irin haka babu ko shakka bare tsoro a tareda shi kaman

Ababa ba,

Su tsautsayi ne ma ya sakasu kisa Amma sun

– kasa samun kwanciyar hankali tin ranar har yau din Amma ga Ababa Yana taka wuyan mutane kaman dabbobi ko ajikinsa idanma zasu mutu rufesu zaiyi babu Wanda zai sani

Kuma yaci gaba da rayuwarsa hankali kwance.

Hande ce ta janyo Anne da kanta ya juye ta fito da ita tsakar gidan ta wucewarta dakinta,

Itama momy jiki na rawa da tashin hankali da toro ta fito da Safnah tsakar gidan ta debo ruwa daga Anne har Safnah din ta ringa zubawa a tare kowannensu na sauke ajiyan zuciya suna motsawa ahankali.

Tana ganin sun farfado tayi kan Safnah dake tashi zaune ahankali tana kasa iya juyowa ta

Kalli mahaifiyarta dake Jin jiki sbd bazata iya hada Ido da itaba.

Anne da Bata hankalinta batama tsaya kallan su Safnah din ba ta tashi zaune tana Sosa bakinta Daya fashe ta nufi dakinta Dayake a hargitse kaman na mahaukaciya ta shigewarta tana shiga ta zauna tana qanqame jikinta sunan Bena kawai take kira.

Safnah kuwa momy kamata tayi hande na zaginsu da tambayar gidan ubanwa ita

Safnah zata koma Kuma?Amma ko kallanta momy bataiba sbd Jin takeyi kaman ta fasa kan shegiyar tsohuwar da garamar pistol din

Jakarta.

A bayan mota ta saka Safnah dake Jin Wani radadin zuciya da zafi,

Ko radadin jikinta bataji saina zuciyarta dake tafasa,

Wih bazata ci wannan dukan a banza ba batareda sun samu Abinda takeso ba,

Idan har ta rasa DD to sai Bena ta rasa DD itama.

Koda suka Isa gida ko dressing din ciwonta gin bari tayi a kira likita yayi mata zafi sosai zuciyarta ke mata tanajin qunci.

Momy kuwa Jin tayi lamarin Ababa ya Bata toro sbd wannan ko su zai iya kashewa akan zafin zuciyarsa da nasa buqatan.

Har dare yayi zuciyar Safnah Bata Dena radadi ba gashi tanason zuwa Asibiti gurin DD Amma ba Daman zuwa sbd raunikan dukan Ababa da zaa fahimci duka ne take bare tace accident.

Dan haka dole karya tayiwa Umme cewan batada lafiya sosai itama a kwance take sai gobe zata sake dawowa Asibitin.

****Familyn kaantes kuwa duk inda hankalinsu yake ya tashi suna cikin mummunan tsaka me wuya da tashin hankali da damuwa,

DD dai Yana cikin Wani mummunan hali Dan kuwa Bai farfado ba Kuma an rasa Abinda ya hanasa farfadowa,ko motsi babu Abinda keyi a jikinsa,haka sai Wani irin fayau yakeyi sosal kaman Wanda ake zuge jininsa kullum.

Ba Umme da zeeyba ko Bena da ake boyewa tini ta fahimci ahalinsa ake ciki sbd rashin ganinsa dakuma Kuka da damuwan Umme da

Zeenah Daya kasa boyuwa.

Taji sauki ita sai Dan Abinda bazaa rasa ba na dinkinta da Bai warkeba sai zazzabin Dayake sakar make idan tayi kaida kawo,

Ita kanta gabaki Daya zuciyarta cikin mummunan hali take game da Abinda babu

Wanda yasan meya samesa.

Ko data lallaba har dakin Dayake ta dubosa hawayen dakeson tsiyayo mata ta danne sbd su Umme da dad kaante zuciyarta suka koma tareda Kona duk Wani nutsuwa da kwanciyar hankalinta.

Tana dawowa dakinta Bata zaunaba a sanyaye ta shiga toilet ta rufo kofar tareda Sako wasu hawaye masu tsananin zafi.

Ta jima aciki kafin ta fito idanuwanta jajir

Amma taqi yadda su Umme su Gane ta dawo kan gadonta takwanta ahankali tareda rufe jikinta.

Da daddare harta kwanta Amma batai bacci ba Zeenah na zaune kan sofar dake dakin me laushi tana waya da Naseer Daya kirata Dan sune suke jinyar a tare,shi na DD ita Kuma ta

Bena.

Dd babba ne ya shigo dakin Abbakar na bayansa.

Zeenah kashe wayarta tayi tareda gaidasu tanawa dd babban sannu barka da zuwa.

Amsawa yayi tareda Maida hankalinsa kan

Bena data Bude idanuwanta Jin shigowansa tana kokarin tashi zaune.

Zeenah datasan da babba idan zaiyi magana da Wainda yake ji dasu baya bugatan kowa ta miqe ta fice daga dakin zuwa na DD gurin

Naseer.

Kallanta dd babba yayi cikin kulawa ya tambaya Yaya jikin nata.

Amsawa tayi cikin sanyin jiki sbd ganinsa ya sakata sakin kukanta Datake ta riqewa.

Yasan Daman tana bugatan Wanda zata fasa kukan ciwon ranta gabansa shiyasa ya kawo ziyarar dakuma abubuwan Dayake son ji daga gareta.

Sai datai kukan ta gaji dd babba ya kalleta bayan yasa Abbakar ya miqa mata tissue ta goge idanuwanta yace

“Bena,fadamun meya faru bayan zuwanki highbridge,

Da kikaje wa kika tarar?

Dago idanuwanta dasukai laushi tayi ta kallesa tareda Dan girgiza Kai ahankali tace

“Babu Wanda na tarar”

Shiru yayi kafin yace

“Bayan kin Isa matarsa Safnah Bata zo ba?

Sake girgiza Kai tayi ahankali tace

“Aa”

Dan sake kallanta yay yace

“To Amma securities sun tabbatarda bayan shigarsa baiyi baqi ko Daya Ba sai ku Biyun daga ke sai matarsa data dawo gidan har so biyu.”

Shiru Bena tayi tana sake tabbatarda tinaninta na ranar babu Wanda yazo bayan zuwanta.

Abbakar ya kalla Yace “kasa su tura maka footage na Time da Safnah ta shiga da fitarta ita da mahaifiyarta ko zata Tina Wani abin Kila shock ko ciwo yasa kin manta.”

Banason bincike me girma sosai akan case din sbd kada media su sani inason komai a sirrance sbd son sanin ya Akai aka samu irin wannan mugayen qwayoyin masu iya kashe mutum ma a jikin DD.

Gayada Kai Abbakar yayi Yana cewa

“Inshallah”

Shiru Bena tayi sbd Bata fahimci me dd babba ke nufi ba da maganar qwayoyi a tareda D.

Sallama sukai suka fice suka barta cikin shiga tinani da mamaki harma da tsoron me Hakan ke nufi,

Ana nufin drugs ne na maye masu muni D yasha ko me?

Cikin tinani da fargaba tareda rashin nutsuwan zuciya ta kwana itama Wanda ta kasa tantance na menene Amma zuciyarta Wani nauyi tayi mata da rashin sukuni.

Yawanci irin wannan yanayin tana jinsane a duk lokacinda Annenta zata kasance cikin matsala ko tsananin Neman agaji,

Jin tayi hankalinta ya sake tashi akan Wanda take ciki Dan haka ko rintsawa bataiba yanda taga dare haka taga safiya cikin tinani da radadin zuciya.

****Yanda Bena ta kwana haka Safnah da

momy suka kwana hakama Kaantes suka

kwana,

Ababa ma a zaune ya kwana har safe ko

ringinginawa baiyiba,

Dagyar yaga saflyar ta waye masa sbd tinani

da lissafin rayuwar Daya samu Kansa a ciki

lokaci Daya ba shiri,

Tako wane bangaren ya duba yaga mafitarsa

tana kunshe da rige kowannensu a tafin

hannunsa ne,

Bashida Rabo a Kaantes dai ta tabbata to Dan

haka Shima idan Yana son mafita da tsira to

dole ya samarwa Kansa hanyar bullewa Shima

kafin DD kaante ya farfado kaantes su dawo

hayyacinsu.

Ko sun dawo hayyacinsu idan yanason tsira

da mummunan Shirin dd babba da baisan

ya yake ba to dole. ya batar da Wainda zasu bayarda tabbacin gaskiyar magana akansa wato Bena da Anne,

Idan bazai ci dukiyar kaantes ba bayan duk gama wahala da gwagwarmayar dayayi akan shigarsa cikinsu to Bena ma wlh bazataci ba hakama uwarta,

Shima dd babba bazai samu yanda yakeso ba kaman yanda Suma su Safnah bazasu samu yanda sukeso ba bayan ya karbi dukkanin

Abinda suka Tara prison ze aikasu Dan dole a wannan masifar mutum Daya ne zai tsira Dan haka gwara shi ya tsira tinda yaga hanyar.

Chapter 81

81

Washe gari dole aka fara Shirin fita da DD qasar waje cikin gaggawa babu Bata lokaci

Bena Kuma har lokacin Bata Isa sallama ba

Dan haka bada ita zaa ba zata samesu daga baya daga dd babba sai dad kaante da Zeenah wadda Bena tace taje kawai sbd tana bugatan

Wanda zata kira taji Yaya yake din kafin taji sauki itama.

Safnah Dayake tana gidansu ko ta kanta babu

Wanda yabi sukai Shirin tafiyarsu suka wuce cikin kwana biyu ba Bata lokaci.

****Babban Abinda ya bawa momy da Safnah mamaki shine zuwan Ababa har babban mahaukacin gidan Alh basheer bulama.

Da farko kasa yarda sukai da Abinda me gadi yazo ya sanar musu na cewan anyi bako yace a sanar dasu Ababa ne

Dukkaninsu suna Jin Hakan sukasan komai yazo musu a sauko kenan Dan haka aka ce ya shigo dashi palon baqi.

Ababa da aka shigo dashi karewa gidan Kallo yayi Yana tinanin wannan duk ya Dena Basa tsoro ko daga masa hankali tinda Suma masu kudin sun iya boyayyan mugunta,

Ba garamin ciwo da radadin Abinda dd babba ya shirya masa yaji ba,

Anne tayi masa Abinda ko kasheta yayi Bai cire bagin cikinta ba shiyasa idan tayi Hakan ne

Dan ‘yarta ta dauwama a Kaantes to shikenan kowa ya rasa.

Ko Daya zauna bai Kalli duk Abinda masu aiki suka zo aka Jere masa ba sbd shi abinda ya kawosa lissafi kawai.

Bai wani ima ba momy ta shigo palon Safnah na bayanta idanuwanta a abushe kaman yanda zuciyoyinsu suke,

Kallanta Ababa yayi Yana sake tabbatarda kafurcinta itama bane sauke bane,

Amma koma yayane shi yanzu baida bugatan ta idan har zata fanshi kanta da dukiyar

Bulama,

Baima da alaga a aynzu da ita bayan wadda zasu kulla yanzu ta kowa ya samu Saar Wani tasa ta fisshesa.

Zaman sukai babu Wanda ya gaida Wani a cikinsu sai Safnah data Bude baki zata gaishesa ya daga mata hannu Yana cewa

“Me kukeso Dani da kuka sameni da duka maganganun jiya??

Ajiyan zuciya suka sauke tare sbd yanzu ne

Akazo daidai inda sukeso.

Safnah ce ta mige ya koma ciki tareda fitowa da wata babbar jaka baqa ta ajiye gabansa momy tace

“Matsayinka na Wanda ya haifi Safnah nakeson siyewa har abada Kai ba ubanta

bane.

Wani shegen murmushi Ababa ya sake Yana kallansu sbd ko Basu siyaba har abada shi ba uban nata zai zama ba,to Amma idan zasu

Siya matsayinsa da Sunansa na ubanta da wanann jakar uban kudin to kenan Alh basheer bulama nawa zai Basa ya siyar masa da gaskiyar Safnah ba yarsa bace,RIBA BIYU ta farko kenan,

Take wannan lissafin Ababa a hau masa ya sake kallansu ya janyo jakar kudin gefensa yace

“Taje na barwa duniva ita har abada.”

Bayan shi sai me?

Zama Safnah tayi wanna Karan itace ta Bude baki sbd a yanzu ta Siya yancin ta daga

Ababan ta kallesa tace

“Zan baka duka kasona na duk abinda na mallaka ka raba auren Benazir da DD..

Wani murmushin takaicin Ababa ya saki sbd da alama dai ba lissafin komai akansu,

Koda su ko Bada su ba baida niyar barin Bena da Anne su samu zaman lafiya..

Katsesa momy tayi da cewa

“Nasan dama ba barinsu zakayi ba Amma hukuncin da mukeso ka dauka shine batar da Bena ta fita rayuwar kaantes gaba Daya har

Abada.”

Kai tsaye ya katseta Shima da cewa

“Bayason kaso kason dukiyar da ake cewa zaa

Basa rabawa biyu zasuyi daidai su Basa Rabi su dauka Rabi su biyu idan suka Basa yayi musu alkawarin Bena tabar rayuwar kaantes kenan har Abada barema asan asalin Safnah

Dan haka zata tabbata Safnah bulama har abada

Amincewa sukai babu ja,

Shima nasa sharadin ya bayar na duk abinda kaantes suke ciki gameda Abinda da babba zaiyi da duk Wani motsinta Safnah ta sanar dashi haka zalika a fili baida alaqar komai

dasu.

Wannan lamarin ya saka zuciyoyinsu duk gamsuwa da Abinda suke so shikuwa Ababa baqin cikinsa ne ya qare,

Dukiyar Daya rasa hannun kaantes ta dawo masa ta gidan bulama saidai Kuma tabbas

Rabin dukiyar bazata ishesa ba idan ya gama dasu Bena kodai su Basa sauran dukiyar ko

Alh basheer bulama ya Basa da Kansa idan yakai masa ziyara me kyau har porthacort.

Dag wanna driver akasa ya mayar da Ababan gida Wanda gabaki Daya yakejin duniyarsa ta fara dawowa daidai yanzu

****Bena kuwa Nafisat ce tazo jinyarta Dan haka tasaka akazo mata da Amnah Amma baa barta ba Abbakar ya mayar da ita gida.

Bayan tafiyar Amnah Bena wayarta ta dauko da aka kawo mata ta kunna sai alokacin sakon

Abbakar ya shigo na footage din da dd babba yace a tura mata ta duba.

Gabanta har faduwa yakeyi sbd Bata taba ganin matar D ba sai yau din Dan haka taji zuciyarta Bata cikin nutsuwa.

Bude video din tayi tafara dubawa na shigowan Safnah highbridge da fitarta.

Bata Wani ganeta ba sbd fuskarta ba sosai ya fito ba sai lokacinda Safnah din ta tsaya kofan shiga tana saka password din kofan shiga

Wanda daganan babu cameras a cikin Palo da dakunan gidan sbd privacy.

Dawo da footage din baya tayi ta sake kalla hannuwanta na rawa wayar na Neman kasa tsayuwa a hannunta.

Nafisat dake kallanta cikin mamaki da fargaban Abinda ya sameta ta kalla muryarta na sarkewa tace “Kinsan matar Daddyn Amnah?

Kin taba ganinta?

22 PA

Gyada Kai Nafisat tayi tana cewa “eh”

Da sauri Bena ta nuna mata wyaar tana cewa

“itace wannan??

Kallo Nafisat tayi tace “eh

Kasa yarda da Abinda take Gani tayi jikinta na rawa ta shiga Google tayi searching Safnah basheer bulama take hotinan Safnah suka bayyana har Dana aurenta da D.

Yawu Bena ke neman rasawa na hadiyewa ta dauko gadonta da sauri qafafunta na rawa ko taku biyu bataiba ta Yanke jiki ta Fadi gurin sbd ko mutuwa tayi ta dawo duniya tasan wannan Safnah dinsu ce.

81

A rikice Nafisat ta fito ta kirawo likita tana

Neman hawaye sbd batasan meya same Bena din ba.

Ciki gaggawa aka dauketa tareda mayar da ita gadonta aka Kwantar tareda dubata aka gano mummunan shock ne ya shiga.

Kusan awa Daya tayi kafin ta dawo daidai ta Bude idanuwanta dasukai mata Wani masifaffen nauyi hankalinta tashe ta janyo wayarta Kai tsaye Abbakar ta kira Bata tsava masa bavani ba tace ya tura mata numbern

Safnah matar DD.

Hannuwanta rawa duke kaman yanda zuciyarta ke rawa da matsuwa a turo numbern tafara Jin muryar wannan Safnah din ta sake tabbatarda Safnah dinsu ce,.

Sakon numbern ne ya shigo mata da sauri ta

Bude Kai tsaye ta saka Kiran numbern tahau ringing.

Ringing wayar takeyi har ta kusa tsinkewa

Safnah dake zaune tana cin abincin datai kwanaki Bata iya ci ba sbd tashin hankali sai yau datasan idan Ababa yaso Abu to tabbas yasan yanda zaiyi Koda masifa ya samo mafitarsa Dan haka su yanzu sun samu madafa.

“‘Hello” ta furta Kai tsaye tareda cewa

“Who’s speaking??”

Murya na yankewa Bena ta ambaci sunata Kai tsaye itama tana cewa

“Safnah,kece kuwa? Safnah kece matar DD???

Safnah dake cin abinci take ya dawo mata har ta hanci ta saki wavar tana Neman ruwa Tasha kada ta mutu Dan abincin yayi cikin kanta da hancinta.

Yanda take barin kayan abincin dake kan dining Jere gurin Neman ruwan Sha ya saka momy fitowa tana mamaki da cewa

“Ke lafiya Kuma?

Meya faru?

Ruwa Safnah ta samu ta Sha a gigice idanuwanta na ja ko daidai Bata gama dawowa ba tace

81

11⅝110

Q2 PA

“Bena ce,Bena ta Gane Miji Daya muke aure

Bena ta ganoni.. shikenan komai Zai lalace.

Momy cikin rikicewa tace

“Banganeba,garin Yaya?

Ya Akai ta Gane?

Meya faru wal.

Kasa amsawa Safnah tayi ta koma inda ta yar da wayarta da gudu ta dauko tana Neman numbern Ababa hankali tashe.

Ababa na gama Jin Abinda Safnah ta fada

Shima hankalinsa ya tashi sbd idan Bena ta

Fadawa Kaantes uwa Daya Uba Daya take da matar DD Daya Shima nasa wasan ya qare yanzu tin Bai fara ba sbd asirin su Safnah na tonuwa Shima tasa ta qare sbd dd babba

Daman hanyar garasa tarkesa yake,haka

Kuma shi hanyar samun kudi tazo masa Yana kwance saidai su sato su Basa bazai yarda komai ya samu wannan hanyar tasa ba,ko waye ya so kawo masa wasa wlh baddashi zaiyi bare su su Safnah dasuka Saba kisan.

A Asibiti kuwa Bena Neman zaucewa takeyi ta saka Kiran da babba wayarsa bata shiga sbd

Basu Isa sauka bama.

Rudewa tayi sai kawai ta tattara kayanta tacewa Nafisat su tafi gida bazata iya jiran ko driver yazo daukansu ba tana bugatan Isa gida asan babban masifan dasuke ciki na auren miji

Daya itada yar uwarta.

Babu likitan dayasan da ta fice daga Asibitin a Karo na farko data Tari abin hawan haya tin bayan shekarun baya.

Kai tsaye kaantes ta nufa suna Isa babban gate din farko aka ajesu ta zira kafarta Daya , zata fito napep din Datake ciki jikinta na tsananta rawa.

Wayarta ce tayi ringing Bata tsaya dubawa ba ta fito ta nufi gate aka Bude mata zata shige kenan Kiran ya sake shigowa ko dubawa bataiba ta daga.

“Idan kika gara taku daya daga inda kike bak

Zo yanzun Nan kin sameni ba kisani daga yau kinyi bankwana da Annenki har abada wih”

Cak ta tsaya idanuwanta na qafewa daga hawayen dasuka cikasu.

Kallanta securities sukai gain yanda ta tsaya kaman wadda komai na jikinta ya dauke wuta.

Nafisat ce ta dawo baya zatai mata magana

Bata ma tsaya Jin komaiba ta juya Kai tsaye ta fada napep din data fito securities Basu gama sallamansa ba tace ya juya da ita.

Lafiya suke kokarin tambaya Amma babu

Daman Hakan sbd jajir da idanuwanta sukai take.

Gudun gaske tasaka Akai da ita zuciyarta na

Neman Dena bugawa da tinanin idan Wani

Abu ya same Annenta

Koda suka iso ko Gani sosai batayi sbd nauyin zuciyarta cikin gidan kawai ta sauko ta shige.

A tsakar gidan ta tadda Annenta yashe a qasa gabaki Daya kamanninta sun sauya tana rakube ko hankalinta bata ciko.

Da gudu benazir tayi kanta ta rungumeta tareda Sako wasu irin hawaye masu tsananin zafin gaske.

Bata gama sauko da hawayenta ba taji muryar

Ababa a kanta yace

“Zan baki mahaifiyarki a yau ki tafi da ita har abada na sauwake mata tareda karya kafi na akanta Amma kema Kuma Zaki bace daga rayuwar kaantes gabaki Daya ku tafi inda babu

Wanda ya sanku idan ba haka ba wlh daga yau bazaki sake ganinta ba kema har Abada

Cikin Wani mummunan yanayi na firgici da tsoro tareda mummunan bugawan zuciya ta juyo ta kallesa ko bakinta ta kasa lya motsawa bare magana.

81

ll Bis

Q Ад

Safnah da momy ne suka shigo gidan Kai tsaye kowannensu hankalinsa tashe Dan Basu dauka Bena ta iso gidanba.

Tana ganinsu ta miqe tsaye jikinta de mutuwa

Yana garasa sakewa gaba Daya zata nuna

Safnah da yatsa tayi magana Safnah din ta juya baya ahankali sbd bazata iya kallansu ko hada idanuwanta dasu ba ita da Anne.

Ababa ne ya katse mata Dan sauran hanklin

Daya rage jikinta na fahimta da cewa

“Idan kin amince ga mahaifiyarki Nan ki dauka

ki tafi na sallameta.

Benazir kasa daukan zancen kunnenta yayi ta zube qasa gurin tana Neman sumewa Safnah tayi saurin tarota jikinta tana jujigawa tace

“Karkiyi gardama Bena sbd Anne Zaki yarda da Hakan ku tafi kuyi rayuwa cikin sauki da kwanciyar hankali”

Tashin hankali da firgicin kalmomin Safnah suka saka Bena kasa sumewa ta zubawa

Safnah din Ido kenan da alama sunsan miji

Daya suke aure.

Muryarta na rawa tace

“Safnah kinsan miji Daya muke aure??

Sakinta Safnah tayi tareda miqewa tana cewa

“Nasani shivasa nace akace ki dauki Anne Ku taflyarku Dan Allah,

Kece kawai Zaki kula da Anne yanda ya kamata Dan Allah ki dauketa ku tafi”

Wasu hawaye da Bena Bata taba fidda masu zafinsu ba tinda take a rayuwarta suka zubo mata tana Jin kanta na juyawa.

Anne da batasan me ake fada ba Jin a raffafo ta kama Bena tareda riqe hannuwanta gar tan kallanta alaman karta barta.

Wace nannauyar qaddarar ce wanna ta afko mata?

Bata tashi sanin miji Daya suke aure ba da

‘yar uwarta Sai bayan da sukai kwanciyar aure bayan shekaru da aurensu.

Ta bangare Daya Kuma batajin a yau din zata bar mahaifiyarta a Nan din Koda Hakan na nufin zatai nesa da DD kaman yanda suka bugata.

Miqewa tsaye kawai tayi da Annenta a hannunta Bata iya furta kalma ko Daya ba ta wuce tana daga qafafunta da qyar.

Ababa Data kusa ficewa tabbaci ya Bata akan duk ranarda ta dawo ko Neman Daya daga cikin yan kaantes to tabbas ba fashi aikin dake kan Annenta daga ranar zai karye Kuma karyewansa na nufin rasa rayuwarta.

Bata iya waiwayowa ba ta garasa ficewa

Annenta na gangameta cikin tsananin tsoro.

Fitarsu gidan Anne ta sake wani ajiyan zuciyan da batasan ma da a sauke ba ko waiwayo babu Wanda yayi acikinsu suka nufi babban titin bayan garin Kai tsaye.

Tafiya sukeyi babu Wanda yake hayyacinsa a cikinsu har sukai Nisan Daya kusa fiddasu gari gaba Daya.

Wata Black beymach ce tayi parking gabansu tareda Bude musu motar aka ambaci sunata

Ta dakata daga ita har Anne suna juyowa a tare

Itace tafara ganin Wanda yake cikin motar ko bugawa zuciyarta Bata samu Daman Vi ba ta

Yanke jiki ta Fadi gurin a some.

fitowa yayi daga motar ahankali tareda zagayowa ya dauketa ya saka motar ya kama hannun Anne itama ya saka motar ya rufe yaja da mugun speed duka kama hanyar barin garin gabaki Daya.

82

Hanyar barin gari sosai ya dauka Yana waiwayowa ahankali ahankali Yana kallan fuskan Bena din wadda itama Anne Bena din take kalla tana tabata tana Kiran sunanta ahankali kaman batason Wanda yake tareda su din yaji hakama jikinta gabaki Daya ma ya mutu zuciyarta ta narke Dan kuwa ko a halin rashin hankali Bena dinta daban take da komai bata son ko hadewan fuskanta da damuwa bare Kuka ko hali irin wannan.

Shi kuwa time din motar ya kalla yaga lokacinda ya kamata ya koma Yana sake qaratowa Dan haka yake sake buga motar sosai yana sake daukan hanya.

Tin suna tafiya Yana Dan waiwayowa cikin kulawa me tsanani da damuwa Yana kallan Bena harya Dena waiwayowa ya mayar da hankali sosai a tuqin.

Tafiyar awa uku cif sukai kafin Bena ta fara motsawa a hankali tana kokarin Bude idanuwanta ga kanta kaman zai fashe sbd nauyi da tsananin ciwo.

Sosai ta Bude idanuwanta suka Bude daidai ta tashi daga jikin Anne tana kallan Annen taga lafiyarta kalau ta mayar da kallanta cikin tsananin bugawan zuciya kirjinta har amsa sauti yakeyi sbd mummunan tsoro da firgicin Daya cika zuciyarta.

Tsoron leqa fuskarsa takeyi ta kalla sbd takasa yarda da Abinda idanuwanta ke ganar mata.

“Ya…yaa BILAL”…..Ta furta cikin yayyankewan kalamai da tsoron Dayake Neman juya kanta da cikinta Daya kulle waje Daya take ta sake zubewa jikin Anne ta sume a Karo na biyu sbd Tama rasa Gane inane take tsakanin duniya da lahira.

Bai tsayaba sake waiwayowa yayi ya kalleta Yana ci gaba da tuqi sbd komin dare Abuja yakeson Isa a ranar.

Zuwa wannan lokacin Anne hankalinta Neman sake juyewa yakeyi sbd ganin Bena na mutuwa tana tashi ahakan itama bacci ya dauketa abinka da Wanda ba cikakke.

Tafiyar awanni ce ta wuni Daya ta kaisu Abuja sai Daya gansa cikin garin Abuja dasu ya sauke numfashi tararda ajiyan zuciya me qarfin gaske kafin ya tinkari anguwar Daya sauka bayan dawowarsa Nigeria kwana uku dasuka wuce.

Wani gida ne me kyan gaske da tsari sosai irin ginin turawa me kyau sosai Amma ba mahaukacin girma sosai.

4 bedroom apartment ne Dayake cikin estate Amma still kowa da gate dinsa da harabar ajiye motacinsa kaman biyu haka.

Parking yayi ya sake sauke ajiyan zuciya tareda hamdala da adduar isowansa lafiya dasu Annen.

Bude kofan baya yayi daidai lokacin Anne ta farka itama Bena lokacin ta sake Bude idanuwanta ta kallesa idanuwanta na Neman sake shiga mummunan hali yayi saurin Kiran sunanta tareda matsawa baya Dan taga tsayinsa da kyau shi din ba fatalwa bane

Shine a Raye gabanta.

Tana ganin Hakan jikinta ya dauki mummunan rawa zuciyarta na kokarin Faso kirjinta idanuwanta na sake rinewa zuwa jajir ta fito motar rawar qafafunta na qaruwa bakinta cikeda tsoro da fargaba tareda tashin hankalin amsar tambayar Datake bakinta tana son furtawa tsoron amsar na Neman gigita kwakwalwanta.

Bude bakin tayi tana sake damqe hannuwanta dake kakkarwa tana kallansa ta furta

“Ina….su..mayyahhnmu?

Itama…tana..ray…..

Maganarta Bata gama fitowa ba aka Bude kofar qayataccen palon sumayyah ta fito da gudu wata ‘yar dattijuwa na bayanta da sauri tana Kiran sunanta,

Bata tsaya koina ba sai jikin Bilal din ta maqalqalesa tana dariyar farin cikin ganinsa kyakyawan fuskarta na Wani irin sheqin Hutu da zallan farin cikin asalin kyakyawar rayuwa.

Rungumeta yayi da kyau jikinsa Yana juyowa zai Kalli benazir da Anne sai yaga babu ko dayansu

Da sauri ya Maida kallansa qasa sai kawai yagansu a qasan duka sume.

Cikin sauri da tashin hankali ya Kalli dattijuwar data biyo sumayyah yace

“Momyn Abdul riqeta Jata ki mayar da ita ciki kada tashiga tsoro ko firgici zanji dasu idan sun samu kansu sai akawota ta gansu.”

Gyada Kai momyn Abdul tayi tareda kamo hannun sumayyah zata Jata sumayyahn ta maqalesa tana girgiza Kai alaman bazataje ba.

Shaf fuskarta yayi tareda hura mata iska a fuska ahankali take ta lumshe idanuwanta ta sake sa momyn Abdul ta kama ta sukai ciki batareda tama lura da Wainda ke gurinba tinda ba cikakkiyar lafiyar hankali ne da itaba.

Suna shigewa ya su kuya ya fara daukan Bena yakai ciki kafin ya dawo momyn Abdul ta dauko masa Anne wadda batada jiki ko Wani nauyi da zaa rasa iya daukanta.

Kai tsaye daya daga cikin dakunansu dake gidan suka nufa dasu suka Kwantar ita Bena Yana ajeta tana farkawa a gigice ta tashi zaune jikinta na sake daukan rawa da fizga ta sauko gadon tana kallansa hawayen na bushe mata Basa iya fitowa da rawan baki ta sake maimaita ambatan sunan sumayyah tana rarraba idanuwanta inda zata ganta.

Ganin halinda take ciki bayan an sanar dashi batada lafiya sosai Daman can ya sakashi saka momyn Abdul rirriqeta Yana kokarin Kwantar mata da hankali suyi magana a tsanaken Amma Sam ta fita hayyacinta Neman zaucewa tayi sbd ayau mummunan ranar baqin cikin rayuwarta,

Ta Gane miji Daya suke aure itada sister dinta tsawon shekaru da Basu ganta ba har sun cire Rai daga rayuwarta tini, a ayau din ma an rabota da Zuciya da ruhinta Amnah da dadynta sannan ta fito babu Abinda idanuwanta ke Gani sai matattun da suka Fi shekaru da rasuwa,.Tayaya hankalinta zai dauki wannan lamarin duka a lokaci Daya Rana daya.

Sosai jikinta ke jijjiga tana girgiza Kai tareda rintse idanuwanta gam tana qin budewa sbd kanta bazai dauka ba zafi qwaqwalwanta keyi, zaucewa takejin tana Neman Yi.

Ganin mummunan halin data shiga ya sakashi sakinta yabarwa momyn Abdul ita ta riqe da kyau yaje har bedroom dinsa inda ya wuce sumayyah a palonsa zaune tana kallan cartoon harya wuce ya fito Bata dago ta kallesaba sbd idan tana kallan cartoon babu Abinda take sake iya kalla sai an kashe tv din.

Yana fitowa dakin da Bena din take ya nufa da sauri cikin alluran Sumayyah ne da itama duk ranarda ta dawo hayyacinta haka take rikice musu da tambaya da son komawa gurin Bena da Annensu taka zata fara jijjiga tana Neman mace masa sai yayi mata allurar take kwantawa duk jikinta ya sake tayi bacci tana tashi shikenan zata tashi kalau Saidai lafiyarta dataqi dawowa daidai duk yawan Da yayi da ita na qasashe a tsawon shekarun ya kasa samun cikakkiyar lafiyarta ta dawo lafiyayyar sumayyahnta ta baya.

Yana Isa yayiwa Bena alluran wadda take bana cutatarwa bane take jikinta ya saki tayi sanyi ta silale a kan gadon a hankali take bacci ya dauketa.

Ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke shi da momyn Abdul.

Mayar da kallansa yayi kan Anne da itama Sam ko matso jikinta bayayi yace momyn Abdul ta tsaftace ta zai kira likita yanzu yazo ya dubata ita.

Ficewa yayi daga dakin Yana sake sauke ajiyan zuciya sai alokacin ya samu Kansa ya wuce dakinsa Kai tsaye yanajin gajiya ma tana Dan taso masa sbd tsawon rayuwarsa a jirgi yake yawo Bai iya Tina wen last yayi tuqi me tsayi irin wannan din sbd ko yau din Daya Isa jirgi ya hau ya Isa can sai Kuma gashi ya juyo baiyi Shirin juyowa a yau din ba sbd abubuwa da dama dasuka kawosa.

Yana shigowa sumayyah dake Kallo har lokacin ya kalla ya qarasa gurinta tareda sauke ajiyan zuciya ahankali ya rankwafo yayi kissing forehead nata ahankali,.dagowa tayi tareda Dan juyowa ta kallesa ta saki murmushi me kyau Daya sake qarawa fuskarta kyau Shima murmushin ya sakar mata ya Dora bakinsa kan lips nata Suma yayi kissing ahankali kafin ya miqe ya juya ya nufi bedroom dinsa yanajin koyaushe son sumayyahnsa sabo yake koma a ransa fatansa dai Allah ya Bata lafiya suji Dadi kaman kowanne ma’aurata da suke rayuwa duk da ahakan ma son juna sukeyi sosai,shi kadai ne Wanda ta sani matsayin uwa,Uba,miji,Dan uwa,aboki hakama masoyi.

Sam Bata yarda Yana barinta sai daqyar da dubara yake fita kullum tinda suka samu kansu a rayuwar kwanciyar hankali ta iya su Biyun yake kulawa da ita sbd tinda ta farfado bayan tsawon lokacin data dauka a coma,

Ta jima sosai kusan shekara a coma kafin Allah yasa zata tashi ta tashi saidai ba acikin hankali isasheba haka suke rayuwar har yanzu dasuka dawo Nan din.

Yana shiga bedroom wanka ya fara tubewa yayi da ruwan dumi kafin ya fito ya goge jikinsa da towel jikinsa ya Dan sake sosai daga gajiya Dan haka Yana shiryawa cikin qananun designers kaya marasa nauyi ya fito palonsa yayi sallah tareda sumayyah wadda bataiba,

Magrib da ishai da baisamu Yi ba kan time yayi suna idarwa yayi adduoinsa sumayyah nayin duk Abinda yayi tana murmushi sai da suka gama ya janyota jikinsa tareda zare mata hijabin sallanta ahankali Yana kallan fuskarta itama shi take kalla tana murmushi tace

“Kaima kana Jin yunwa ko?

Ni dai inason zanci abinci da yawa.”

Ajiyan zuciya ya sauke tareda Jan hancinta ahankali Yana shafan fuskarta dake sake kashesa da sonta kullum yayi kissing gefen fuskarta ahankali cikin nutsuwa da sanyin sauti yace

“Zaki ci abinci?

Me kikeso momyn Abdul ta kawo Miki?

Kin Tina sunan Bena da Anne???

Shiru tayi Jin sunayen a cikin kunnuwanta sun Bata Wani sautin Daya Isa harga zuciyarta ta dago ta kallesa tana lafewa jikinsa batareda ta iya cewa komaiba.

Shima shiru yayi kafin ya dagota daga jikinsa suna miqewa tsaye ya kama hannunta cikin nasa suka fito main sitting room na gidan ya nufi dining da ita suka zauna.

Sai alokacin jikinta da yayi sanyi ya hau murna ganin Abinda takeso ne duka su snacks sai pasta wadda takewa cin shedana har ta Koya masa matiqar zasuci spaghetti to Rabin cin duk lalata ne.

Cin abincin suka hau Yi sai a lokacin Dr din Daya kira yace masa ya iso.

Momyn Abdul ce ta shigo dashi tai masa jagora har dakin da Anne take kwance kan gado bayan ta Dan gyarata.

Dubata sosai likitan yayi ya tabbatarda zuciyarta da komai nata Yana Aiki kawai dai shock be dayayi mata yawa ya sakata Suma.

Ruwa ya daura mata Dan taimakawa saurin farfadowanta kafin yabar maganin da zaa sakawa raunikan jikinta Daya Gani wainda na mummunan dukan da Ababa yayi mata ne na bankwana.

Bayan tafiyarsa daga Anne har Bena kowanne na daki daban daban gyara musu kwanciya momyn Abdul tayi ta rufe kowanne kafin ta jawo musu dakunan ta fito ta nufi nata sbd dare da yayi sosai.

Sumayyah da Bilal kuwa tini suka wuce dakinsa Wanda yake nasu su Biyun sai Daya taimaka mata gurin wanka Dan Daman shine kullum yake taimaka mata da wanka sbd Bata iya Yi da kanta jiqo jikinta takeyi har kanta da kayan jikinta shiyasa tinda sukai auren tsawon shekarun shine yake mata wanka da komai sai idan zai fita Aiki momyn Abdul ta kula da ita wadda itama Momyn Abdul din sun Dade sosai tareda ita sulaiman ne Mai napep dinsa yakai masa ita qanwar mahaifiyarsa ce Kuma mahaifiyar Nafisat Nanny din Amnah anintacciyar me aikin Bena.

83

Kwanciyarsu sukai hankalinsa na kwanciya da dawowan su Bena rayuwarsa da sumayyah sbd idan har yanda wasu likitocin suka fada ne dawowar wainda ta rasa rayuwarta zai iya dawo mata da hankalinta daidai cikin qanqanin lokaci koma lokaci Daya yasaka yake Jin damuwarsu da quncinsa na rashin lafiyarta tsawon lokacin Dan haka a yanzu kam yakejin lokacin warkewar matarsa yayi.

Gyara mata kwanciya yayi a jikinsa kafin ya miqa hannu ya kashe musu wutan dakin Yana lumshe idanuwansa tareda kokarin Tina gwarwarmayar daya Sha a baya daga lokacinda ya bar gida.

Babu wanda ya farka a cikinsu kaf wainda sike gidan sai da safiya tayi sosai,

Bena ce tafara farkawa ta Bude idanuwanta dasukai mata nauyi sosai tana Jin kanta na Dan juyawa ta dafa ta tashi zaune daga kwancen datake tana kallan inda take.

Lumshe idanuwanta da sukai nauyi da ja tayi tana kokarin motsawa ta sauko Amma jikinta gabaki Daya ya mutu batajin karfinsa ko kadan kaman wadda akaiwa duka ko Wani allura.

Qafafunta ta zira qasa ta saukar tareda kokarin miqewa tsaye ta daddafa bango ta Isa bakin kofar dakin ta Bude ahankali ta fito tana tafiya kanta da Dan juyawa.

Motsin dataji a hanyar dining ta nufa batareda tasan inane take nufar ba.

Sumayyah ce da momyn Abdul ke zubawa ruwan tea Dan baa barin tana hada tea da kanta sbd ruwan zafin kada ya mata illa dokan Bilal ne.

Sumayyah dataji motsi tahowa itama dago kanta tayi ta Kalli hanyar idanuwanta a Bude hakama fuskarta dauke da murmushi da farin ciki duk tinanin Bilal ne ya fito.

A cikin idanuwan junansu idon kowaccensu ya sauka,

Cak Bena ta tsaya rawan qafafunta na qaruwa kaman yanda bugun zuciyarta ya tsaya cak wannan lokacin.

Sumayyah kuwa kafe idanuwanta tayi kan Bena tana Dafe kirjinta ahankali dataji Yana harbawa kadan kadan yana qaruwa.

Bena na ganin Hakan take ta fahimci halinda sumayyah take ciki sbd a duniya ita kadaice tafi kowa Gane lafiyan sumayyah da Anne hakama rashin lafiyansu.

Wasu zazzafan hawaye ne da tinda masifun rayuwarta suka fara saukan mata jiya Bata samu ko digon hawaye sun zo mata ba sbd radadin masifun sai wannan Karan dataji suna gangarowa daga idanuwanta tana rasa Gane wane yanayi ne a cikin zuciyarta,

Zallan farin ciki ne ko tsoro da fargaba ne¿

Takowa ta ringa yi ahankali tana nufo sumayyahn wadda hawayen Bena suka sauya buguwan zuciyarta kwata kwata sbd tini kanta ya fara juyawa fuskar Bena na dawo mata cikin Kai da hawaye kala kala da kukansu na baya.

Benazir na qarasowa Bata tsaya komaiba ta rungume sumayyahn data miqe itama tana kallan Bena har lokacin kanta na juyawa sosai.

Cikin tsananin Kukan Daya tarwatsa zuciyarta me qunci da tsima Rai ta ambaci sunan sumayyahn Wanda yayi daidai da fitowan Anne itama daga dakin tana dafa bango ahankali ganin inda take da Neman Bena.

Ganinsu ya sakata tsayawa cak itama tareda tsirawa fuskar sumayyah idanuwanta tana tinanin kenan jiya a hankalinta da gaske taga sumayyah,

Ta dauka cikin haukarta ne taga sumayyahn na mata gizo kaman yanda taga Safnah tai mata gizo shekaran jiya da jiya a gidan Ababa.

Sumayyah Datake rawan jiki sosai tana Neman rikicewa da runguman da Bena tayi mata tana ambatan sunanta suna hada Ido da Anne ta qarasa rikicewa gabaki Daya tafara jijjjiga tana kafe idanuwanta akan Anne benazir na Jin Hakan itama nata jikin ya hau rawa, Anne data farka cikin hayyacinta itama kansu tayo tana Taya Bena taro sumayyahn jikinta sbd zubewan Datake Neman yi.

Fitowan Bilal ya ga Abinda yake faruwa da sauri ya qaraso tareda daukan sumayyah wadda ta zube jikinsu kaman ba Rai jikinta idanuwanta a rufe koina jikinta na rawa sosai.

Kai tsaye dakin dake kusa Wanda Anne ta kwana ciki ya nufa da ita ya Kwantar sai alokacin ya lura da yanda jikinta ke rawa sosai da sauri ya fara girgiza ta Yana Kiran sunanta da karfi Yana cewa ta Bude idanuwanta.

Momyn Abdul dataga halinda sumayyahn take cikin damuwa da tashin hankali ta kallesa tace yayi mata alluranta mana.

Girgiza Kai yayi Yana kallan Bena da Anne da Suma suke cikin girmamammen tashin hankali da tsoron Abinda yake faruwa yace bazai mata ba yau tinda wainda take shiga wannan halin sbd su yau din suna tareda ita Yana fatan qarshen wahalansu ne yazo yau din.

Benazir ce ta hawo gadan itama ta kamo fuskan sumayyahn tana Kiran sunanta da qarfi muryanta na rawa,

Anne gabaki Daya ta kasa yarda da duniyar dasuka tsinci kansu a yanzu,

Shin duniya suke kokuwa lahira suka hade dasu sumayyahn,

Ita dai a halin yanxu data ganta tareda yaranta biyu a gabanta ko lahirar ne batada damuwa bare baqin ciki Dan kuwa rayuwarsu ta duniya sai dai suce Allah ya Basu ladan Ibadan daukan qaddarorin da sukaita Yi.

Bilal da duka zuciyarsa da kirjinsa suke tsalle Yana kallansu Yana jira da fatan daga yau idan ta gansu kada hankalinta ya sake juyewa ya tsaya daidai Dan bazai sake mata allura ba inshallah ahaka yakeson ta samu sauki da ganinsu.

Anne ma hannu takai ahankali ta dafa sumayyahn tareda Jin hawaye sun gangaro daga idanuwanta na farin ciki da tausayin kansu batasan lokacinda ta zube jikin sumayyahn ba ta rungumeta da qarfi ta qanqameta tareda fashewa da kuka me sauti tana Jin tsananin so da kaunar ‘yarta na dawo mata sabo fil sbd sun cire Rai daga rayuwarta tintini.

Kukan Anne ya saka sumayyah bude jajayen idanuwanta da suka sauya take ta Kalli Anne hawayen nason ciko idanuwanta Wanda ya saka Bilal Jin zuciyarsa na Neman bugawa sbd fargaba da matsuwan son ganin reaction nata sbd tsawon shekarun Bata taba Kuka ba bare hawaye Wanda Hakan ke nuni da Bata hankalin nata Amma yau ganin hawayenta na Neman sakasa Kuka Kai tsaye.

Momyn Abdul ma ganin hawaye idanuwan sumayyah ya sakata fashewa da kuka kawai tana kallan Bilal Wanda hawayensa ke gab da gangarowa.

Benazir ma datake Gane sumayyah ta dawo daidai tin Abaya idan taga hawaye a fuskarta ne tana ganin hawayen ta batasan lokacinda itama ta fashe da kuka ba Wanda ya saka sumayyah fashewa da kuka take itama tana kallansu har lokacin Bata gama dawowa daidaiba Amma tabbas Bena da Annenta ko da can ko a halin ciwonta Bata mantasu Bata Dena sonsu Bata Dena jinsu tsakiyan ranta.

Fashewan kukan sumayyah ya saka Bilal fashewa da kuka mara sauti Wanda ya saka momyn Abdul zuwa gurinsa ta dafasa tana Dan bubbugasa alaman rarrashi da taya murnar farin cikin wannan Rana me dinbin tarihi a  rayuwarsa sbd soyayyan sumayyah a ransa Wani Abu ne da momyn Abdul Bata taba Gani ba, mutumin dazai iya baro gida,iyaye da danginsa da gata da daulansu ya zo ya Gina tasa rayuwar daban sbd kawai kulawa da macen dayakeso Kuma duk shekarun Nan a cikin rashin cikakken hankalinta.

Duk Wanda ke dakin Kuka yakeyi tsawon lokaci kowa baya iya magana suna kukan rage baqin ciki da quncin rayukansu na baya tareda farin cikin rayuwar dazasu sake ginawa a tare yanzu.

Sumayyahn ce tafara shiru daga kukanta jikinta na Neman sakewa sai alokacin suka saketa suna kallan Bilal Wanda ya fita ya dauko mata Wani magani da sauri ya dawo ya saka mata bakinta tareda zuba mata ruwa daqyar ya samu ta hadiye maganin ta silale jikinsa idanuwanta na rufewa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu a tare kowa idanuwansa na kanta cike da so da kauna da kulawa.

Bayan tayi baccin sai alokacin suka zazzauna jigum jigum kafin Bena da qyar ta lallaba ta shiga toilet din dakin tayi wanka sbd ciwo da tsamin da gabobinta sukai na wahala Dan haka tana shiga toilet din ta sakarwa kanta ruwa ta fashe da sabon kukan Datake riqewa cikin ranta na tata quncin zuciyan.

Wane tsaka me wuya ta samu kanta aciki?

Menene makomar tata rayuwar data auren Dayake kanta?

Ta Ina zata fara tinanin kowace iriyar rayuwa batareda shi da Amnah a cikinta ba?

Wannan sabuwar qaddarar tata me nauyin gaske ce data hadata auren miji Daya da Safnah,

Gashi idan ta lissafa daidai itace ta haramta garesa Koda su Safnah da Ababa Basu koreta ba sbd ta tabbatarda zamansa da Safnah bayan tarewan bikinsu sunyita samun muanalan aure….

Rintse idanuwanta tayi tana durqusawa qasa kukanta mara sauti da tsananin qunci na qaruwa.

Ta jima a cikin toilet din kafin ta fito tana sakawa ranta cewa dole ne yanzu tayi kokarin yakicesa daga zuciyarsa sbd yariga ya haramta gareta matiqar ‘yar uwarta na Raye.

Bayan fitowanta Anne datai zugum itama cikin Nisan tinani dagowa tayi ta Kalli benazir din wadda taqi barin Annen taga fuskarta sbd yanda yanzu take daidai zata iya Gane quncin Datake ciki me tsananin gaske Wanda zata buqaci Jin dalili wanda idan har hankalin Anne ya manta da Abinda ya faru Bata fatan tinatar da ita ko sanar da ita Safnah da Abinda sukai din na korarsu akan suna auren miji Daya,abarsa akan Annen ta Dade da dangana da sakawa ranta cewan Safnah ta mutu,

Gwara ta zauna akan maganar Safnah bata Raye datasan Abinda yar tata takoma abin ya zo ya taba zuciyarta dasuke fatan samun sabuwar rayuwar aminci a yanzu matiqan suna tareda junansu.

Sallah tayi wadda duka Basu samu sunyi ba sbd ficewa hayyaci.

Itama Anne wanka tayi momyn Abdul ce ta kawo musu kayan sawa masu kyau duka acikin tarin kayan sumayyah dake cike da closets na kusan dakinsa Dana dayan bedroom din Dayake matsayin nata duk sitirar Dayake Siya mata ne kala kala baya damuwa da wasu ma bata sakaba yake siyo wasu.

Bayan sun shirya sunyi sallah abinci aka kawo musu har dakin Dayake babu sauran qunci bayan Wanda Bena ta danne cikin ranta haka sukaci abincin sama sama suka gama aka tattara gurin sai suka sake komawa zaman jigum jigum suna jiran farkawar sumayyah

Itakuma Bena kebe kanta tayi dayan dakin tareda zaunawa qasa ta cusa kanta cikin qafafunta zuciyarta na mata Wani irin ciwo da radadin datakejin kaman ba bazata iya rayuwaba ahakan.

Har yamma Bata fito daga dakin ba ko abinci takasa ci Annenta hankalinta yayi mummunan tashi Nan tafara tambayarta Yaya mijinta da Amnah.

Wannan tambayar ta Anne ta saka Bena kasa riqe kukanta Datake ta riqewa idanuwanta sunyi jajir da nauyi ta fasa kukan Mai ciwo tana fadawa jikin Anne.

#MAMUH#

_Masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek’e masge kwarkwatar idanunsu, da san kwakwale damuwarsu, da sanya bak’in cikin su facewa, su kwamaso sink’i-sink’in dariya, annashuwa da sassanyan murmushi kan fuskarsu, su antayawa ruhinsu salama, su sanbad’awa zuciyarsu yalwa, masu san farin ciki wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik’a, fasihiyar, mai san kasancewar ku cikin annuri, wacce ta saba kawo muku nagartattun litttattafanta masu dad’i, wacce ta kware wajen rubuta dad’ad’an labaru tun daga kan wanda ya k’unshi nadama, kuku,tausayi, cin amana, da nagartacciyar soyayya mai yalwa mai sanya tsoho ko tsuhuwa su tuna da jiya samartakarsu da ‘yan matancinsu ya motsa,_

84

Rawa jikin Anne ke kokarin dauka sbd Idan akwai abinda duka yake gigitasu to kukan Bena ne,

Bena Bata Kuka sai Abinda yafi karfin zuciyarta ta riqesa,

Rungumeta tayi tana son tambayar ta Abinda yake faruwa Amma tana kasa magana itama sbd itama bugawa zuciyar Tata keyi.

Kuka Bena keyi sosai Amma babu Wani sauki ko sasssuci Datake ji a zuciyarta na Abinda ke cinta.

Shiru Anne tayi tana Bata Daman yin kukan yanda takeso ko ta samu sassauci.

Suna cikin wannan yanayin aka Bude kofan Dakin aka turo ahankali Anne ce kawai ta dago taga momyn Abdul ce ta kawo musu abincinsu anan na dare ta ajiye ta juya ta fice.

Babu Wanda ya Kalli abincin suna zaune cikin sanyi da mutuwar jiki har dare yayi sosai kafin Anne ta saka Bena taci abincin dole tayi sallan ishai ta kwanta.

Kasa barinta Anne tayi itama tayi sallah taci abincin kafin ta kwanta bayan Bena din tana dafata da hannu Daya sbd tayi tsananin kewan kwana guri Daya da Bena dinta.

Sanin sumayyah nada Bilal a me kulawa da ita fiyema dasu ya saka Anne Maida kulawanta akan Bena data fahimci tana cikin Wani mummunan quncin Datake boye mata.

Washe gari cikin iKon ubangiji da falalarsa sumayyah na tashi ta tashi da ‘yar lafiyan hankalinta kaman baya yanda suke rayuwa gidan Ababa lafiyar tana zuwa idan sabon depression ya shigo ta koma sama sama.

Bilal Daya rasa inda zai saka Kansa rungumeta yayi cikin tsananin farin ciki da Bai taba shigaba ya fara hawaye Yana qanqameta jikinsa.

Ita kanta Wani sanyin farin ciki ne a zuciyarta Daya sakata hawaye tana sake shigewa jikinsa tana Jin zuciyarta kaman zata faso da tsananin sonsa Dana Annenta da Bena dinsu.

Rungume da ita ya fito Yana Kiran momyn Abdul wadda itama rungume sumayyahn tayi tana fashewa da kuka sbd itama taci baqar wuya a jinya da kulawa da sumayyahn na shekarun Nan.

Bena da tin datai sallan Asuba take zaune shiru nade a cikin hijab din datai sallah tayi Nisa sosai a tinani idanuwanta sunyi jajir sun kumbura sosai sbd kukan data kwana Yi tsakar dare wadda Anne tana jinta itama hawayen ta ringa yi sbd batasan quncin Dayake cin Bena dinta ba gashi ita ba cikakkiyar lafiyayyar datasan Yaya iyaye keyiwa yayansu acikin damuwa ba bare tayi tasan damuwan yarta,.Abinda kawai ta sani damuwan Bena damuwarta ce tin farko basai ta saniba tana ganinta a qunci itama take shiga qunci,hakama tana ganinta a walwala itama take shiga walwala da farin ciki.

Shiru suke zaune dakin Anne tayi shiru cikin tsananin damuwa tana rasa abin Yi ko fada ko tambaya,

Ita Kuma Bena datai Nisa a tinani idanuwanta a rufe batamasan me Annen keyiba.

Bude dakin sumayyah tayi cikin sanyi da mutuwar jiki da zuciyarta dake sanyaya tana sanyi ta zubawa mahaifiyarta idanuwanta tana kallanta komai na rayuwarsu dasuka sha fama Yana dawo mata tsaf cikin Kai da zuci.

Takowa tayi ahankali idanuwanta na tsiyayan hawaye ta nufi Annen wadda sai alokacin ta lura da shigowarta sbd hankalinta dake kan Bena cikeda damuwa da mutuwar jiki.

Ganin sumayyah ya saka Wani bangare na zuciyarta sanyaya ta zubawa sumayyahn idanuwanta itama sumayyah ta qaraso da sauri ta fada jikinta ta rungumeta tana Kiran sunanta a Karo na farko bayan shekaru.

“Anne, Anne” take furtawa dukkanin jikinta na mutuwa da Wani irin dacin zuciya ja rabuwarsu.

Ita kanta Anne hawayen takeyi tana Jin dumin ‘yarta data Dade da yarda da ta tafi lahira ta barsu.

Sun jima a Hakan Bena bata motsa daga yanda take ba sbd Bata hayyacinta Sam.

Sumayyah ce ta sake Anne tayi kan Bena din itama ta rungumeta tana kiran sunata tsananin son ‘yar uwarta na motsa mata gaba Daya.

Ahankali Bena ta Bude idanuwanta jikinta ba qwari kaman yanda zuciyarta take ba qwari ta kasa ko motsawa a yanda take sai hawaye sirara da suka gangaro mata,

A Karo na biyu na Wani matakin raywarsu zata sake danne qunci tabarwa zuciyarta ita kadai taci azabarta ita kadai batareda ta sanar musu ba Dan hanasu shiga damuwa da baqin cikin rayuwar dasuka samu me nutsuwa da kwanciyar hankali.

Babu magana dake tashi a dakin nasu bayan ajiyar zuciya da hawaye dake sauka a tsakaninsu.

Ahaka suka dauki tsawon lokaci su kadai har azahar sai alokacin suka ci abinci sukai wanka kowannensu yafito fes zuciyoyinsu cikeda nutsuwa da kwanciyar hankali Banda Bena da dauriya kawai takeyi Amma duk dauriyarta Basu Dade da gama cin abincin da sukaci ba zazzabi me qarfin gaske ya rufeta musamman kanta dake tsananin ciwonda takejin kaman zai tarwatse.

Rikicewan jikinta ya saka hankalinsu tashi Basu tsaya Kiran Wani likita ba dole Akai asibiti da ita sbd har Amai takeyi jikinta ya sake gabaki Daya.

Suna Isa asibiti aka Bata gado dukkaninsu kin komawa gida sukai suka zauna Asibitin zaman Jira zuciyoyinsu ba Dadi.

**********

AUis special care Zurich.

Kwanansu biyi da Isa Saida suka gama samun nutsuwa da ganin komai ya shiga daidai inda ya kamata ya shiga na Neman lafiyan DD din tukuna suka samu Daman kunna wayoyinsu Dan samun Daman magana da Wainda suka baro Nigeria.

Dd babba ne ya fara samun labarin batan Bena daga bakin Abbakar Dan haka yayi shiru cikin matsanancin mamaki da tashin hankalin Daya sake tabbatar masa da tabbas akwai abinda yake faruwa wanda suke zargi tin farko.

Wani Dan zufa ya share da tissue me laushi Yana jefarwa sbd tinanin Abinda zai biyo bayan batan Nan nata idan DD ya farka,

Ta bangare Daya ga familynsa Dama suna cikin rudanin Bena data kasance ba mahaifiyar data haifi Amnah ba, lafiyar DD kawai kowa ke Jira ayi magana dole kowa yasan menene asalin Abinda yake faruwa.

Labarin batan Bena kaante shi zai bawa duk Wanda yakeda hannu a batan nata Daman yin koma menene manufarsa na Hakan Dan haka take dd babba ya sanar da Abbakar kada kowa yasan Bena kaante ta Bata baa ganta ba,

Ayi duk bincike da zaayi me tsananin gaske daga boye kada abari kowa ya San Bata Nan,Abar kowa da sanin ta biyosu Nan Zurich gurin jinyar mijinta.

Wanna umarnin na dd babba ya saka hankalin Umme sake tashi Amma Kuma hakanan ta daure take danne tashin hankalinta cikin mutane tana nuna Bena din na can tareda su DD a Zurich.

Amnah ma Hakan Umme ta fada mata Dan haka yarinyar ta Maida hankali akan yiwa iyayenta adduar Allah yabawa daddynta lafiya ya dawo shi da mummy dinta su koma highbridge tare tinda tasan aranar da kafin ciwon daddynta mummy dinta a highbridge ta kwana.

Nafisat ma sosai ta dage gurin cigaba da kulawa da Amnah cikin so da kauna tana sake debe mata kewan iyayenta.

Ahakan cikin tashin hankali da matsanancin tsoro da tsaka me wuya familyn kaantes suke,

Zargi da bincikensu ya qarfafa musamman Daya kasance ace lokaci Daya ansamu D a wannan halin hakama kawai a wayi gari babu Bena babu labarinta.

Abbakar da Kansa yaje gidan Ababa suka gaisa kaman yanda ya Saba ya Ciro kudi me yawa ya miqa masa.

Wani murmushi Ababa yasaki Yana kallan kudin yace

“Sakon dd babba ne ko na Benazir?”

Shima Abbakar murmushin yayi Yana cewa

“Sakon Bena ne sbd tafiyan gaggawa ya kamata zuwa can Zurich gu……

Bai qarasaba Ababa ya Dan sake wata dariyar takaici kafin yace

“Ita Bena din?akace batada lafiya Kuma shine harta warke zata iya tafiya.”

Murmushi Abbakar ya sake sakewa yace

“Acan zaa dubata itama,gobe Inshallah zata wuce”

Shiru Ababa yayi zuwa lokacin sbd zuciyarsa data Dan fara shiga wasi wasi da shakka,

Shin da gaske Abbakar yake Bena na kaantes gobe zata wuce Zurich din? Kokuwa dai fada kawai yakeyi?

Idan Kuma da gaske ne Bena Bata wuce ba to ai ba kudi ya kamata a akawo masa ba da hukuma ya kamata  yagani.

Ta Wani bangaren Kuma yasan dd babba zai iya komai a sirrance har a kamasa sbd kada sunan kaantes ya lalace.

Tinani da lissafi yake Neman shiga Abbakar ya qare masa Kallo kafin ya Danyi gyaran murya sukai sallama ya miqa masa kudin ya wuce.

Yana barin gurin da mota Ababa ya saka kudin hannunsa aljihunsa Yana wucewa gaba batareda ya koma cikin gida ba Kai tsaye gidan Alh basheer bulama ya nufa.

Abbakar na barin kofar gidan Kai tsaye office din babban Jami’in da case din ke hannunsa ya nufa Yana Isa ya sanar dashi yanda sukai da Ababa.

Sallamarsa Sir Ashir bello yayi Yana Kiran wayar dd babba.

Bayan dd babba ya gama sauraransa Shima numfashi ya sauke ahankali yace,

“Saura matarsa da mahaifiyarta dasukaita kaida kawo a gidan ranar da abin ya faru,

Suma a sirrance zaayi binciken banason Abinda zai jawo mana bacin suna da shiga headlines na labarin da ba ci gaba ko wata daukaka muka sake samu ba”

Haka a ranar da abin yafaru a footage na anguwan bayan anfito highbridge matar Dawood din bayan fitowanta sunga Wani me napep daya ringa binta a baya a hankali har suka bacewa anguwar gaba Daya Dan haka Shima a Yi kokarin tsananta bincike a gano napep dinsa a gano ko waye ko akwai abinda zasu Gane ta gurinsa sbd kusan duka shigowarta anguwar da fitarta sun duba dakyau sunga Yana bibiyarta daga nesa sosai Dan haka dole Shima akwai Wani Abinda yasa yake Hakan ko Kila tare suke.

Gyada Kai sir Ashir bello yayi Yana sake bawa dd babba tabbacin komai zai tafi yanda suke so zasu Gane komai a tsanake cikin sirri batareda sunyi alerting Wanda yake da hannun duk wannan abubuwan ba.,

Su anasu bangaren ma wanda miyagun qwayoyin jikin DD suka fito hannunsu suke da tsananin buqatan sani sbd hukuncinsu 40years ne gidan yari kawai.

*****Ababa hankalinsa na rabuwa biyu ya kusa Kaiwa gidansu momy Amma Kuma sai tinaninsa ya hanasa sbd idan ya fada musu zasu ankare da wuri so Dan haka idanma tarko ne aka hada masa su zasu iya kaucewa daga tarkon Dan haka ya fasa fada musu ya juyo ya dawo gida.

Yana isowa gida Bai fadawa hande komai ba ya shige daki yana sake shiga tinani da lissafi,

Babu ta yanda dd babba zaiga Bena da Anne tare ace besan Abinda ya faru Ba,Dan haka tabbas akwai abinda ake shiryawa a boye,

Idan bazai Gane ko menene ba dole ya danawa su Safnah tarkon da sune zasu fada tarkon dd babba bashi ba Dan kuwa shi nasa laifin na canjan sumayyah da Bena ne

Su kuwa hardana kisa a cikin nasu lefukan,

Idan yaji tsit din yayi yawa dole yayi Abinda zaa San waye ya kashe hajiyar su Alh basheer bulama sai tashin hankalin ya karkata ya koma can yayi amfani da wannan Daman yasan nayi sbd yasan yanzu duk Ido da tsaro na Kansa,

Allah dai ya Isa tsakaninsa da dd babba da zuriar kaantes gabaki Daya wlh.

_

85

Qarfe ukun Daren ranar aka samu nasarar yiwa DD allurar qarshe cikin guda ukun daya kamata ayi masa duk bayan kwana biyu ake daya sbd ba qaramin qarfin gaske qwayoyin sukaiwa jikinsaba hakama duk allura Daya kudinta ba qaramin firgici zaka shiga ba na jinsu Dan haka sai ranar su dd babba suka dawo hayyacinsu yanda ya kamata suna fatan farfadowansa kowane lokaci,

Ta bangare Daya Kuma suna cikin fargaba da tashin hankalin ta inda zaa fara masa bayanin uwar ‘varsa ta Bata baa ganta ba tsawon kwanaki biyu.

Zeenah gabaki Daya ta jeme a iya kwanakin biyu sbd tashin hankali da damuwa,

Ga batan Bena ga D a kwance ga Amnah can gida kullum kira takeyi tace a Bata mummynta suyi magana basuda mafita dai kame kame suke mata kullum sbd maganar ma yarinyar abari tasan ba’asan inda mummy dinta take ba Bata taso ba Dan kuwa zata iya shiga mugun halin da basusan ya zasuyi da ita ba.

Karfe 5 na Asuba daidai DD ya budewa idanuwansa dasukai nauyi ahankali batareda ya motsaba sbd jikinsa da yayi Wani irin nauyi na kwanciyar kwanaki,

Ahankali cikin kasala da rashin kuzari ya sauke sanyayyan numfashi ahankali tareda lumshe idanuwansa va sake budesu anankali

Abu na farko Daya fara zuwar masa Akai shine sunan Bena Wanda shi kansa baisan wane hali zuciyarsa take ciki ba a yanzu kanta dama shi

Kansa.

Dakin Dayake ya juya Kansa ahankali ya kalla ya mayarda idanuwansa kan sauran kayan monitoring heartbeat dinsa da sauransu ya tabbatarda a Asibiti yake Kuma tabbas Bata Nigeria bane musamman duba da blue kayan

patients din dake jikinsa.

Babu kowa a dakin Dan haka ya sake rufe idanuwansa Yana sauke numfashi ahankali

ahankali a Jere Yana son fara calming

numfashinsa kafin yafara kokarin tashi zaune tini alerm na dakin ya fara qara me sauti daidai

misali na Kiran nurse zuwa ga dakin.

Yana tashi zaune ana Bude kofan Dakin nurse ce ta shigo sai Naseer a bayanta da sauri suka shigo Naseer na wuce nurse din ya Riga Isa ga DD din Yana Jin Wani farin cikin ganinsa zaune.

Bai tsaya komaiba Yana Isa ya rungumesa sbd da Bai tashi yau dinba shikenan baa San ranar tashinsa ba har shekara zai iyayi a kwancen

Amma Allah ya amsa adduar su ya tashi.

D baida Wani qarfi ko Dadin zuciya Dan haka

idanuwansa ya mayar kawai ya lumshe yana

kasa motsawa daga zaunen har nurse ta

duddubasa taje ya kirawo likita har guda

biyu da Wani nurse Daya namiji aka taru aka

dubasa dakyau aka sake diban jininsa Akai

gurin awo dashi Dan duba idan sauran drugs

din dake jinin nasa allurar ta qarasa qona su.

Barka da tashi likitocin sukai masa cikin

kulawa da farin ciki kafin suka fice daga dakin

suna sake tattauna maganar ciwon nasa

Suna ficewa ya Bude idanuwansa dake rufe

ya Dan Kalli Naseer dake cikeda farin ciki sai

kokarin Kiran su dd babba yakeyi a waya.

Magana yaso Yi Amma bayason ko Bude

bakinsa nauyin komai na jikinsa yakeji Dan

haka ya Dan ziro gafafunsa qasa ahankali

Amma yakasa miqewa tsaye sbd sunyi nauyin

da bazai iya tafiya da Kansaba Kai tsaye a yanzu daga tashinsa.

Yana Nan zaune Naseer ya kira su dd babba ya sanar musu take kowannensu yahau sujjada Yana godewa Allah sbd su kadai suka

Dan mummunan tashin hankali da fargaban dasuke ciki akan wannan halin Dayake.

Bayan ya gama waya dasu Naseer din dawowa yayi ya sake kallansa cikin kasa boye farin cikinsa yace “zan shirya Maka toilet yanzu ka Dan gasa jikinka kanl sake kafin zuwansu dad kaante”

Yana fadan Hakan ya nufi bathroom din da sauri ya shige kaman bana asibiti ba kaman a hotel Dan haka komai tsaf yanda DD din ke bugatan toilet hakama kullum sai anwanke an sake tsaftace komai na toilet din duk da babu me shiga Amma sbd suna jiran farfadowansa kowane lokaci shiyasa koyaushe ake cikin

Shirin duk Abinda zai buqata bayan tashin nasa.

Fitowa yayi da Kansa ya kama DD din Wanda baya iya tafiya haka Suka lallaba ya shiga toilet din dashi yakaisa har bakin bathtub Daya hada ruwan dumi sosai ya kawo masa komai Dazai bugata ya Jere masa harda sabbin towels guda biyu dasu toothpaste da toothbrush na wainda yasan asalin dasu DD ke amfani.

Zare rigar patient din dake jikinsa yayi ahankali tareda sakinta qasa tareda short din Dayake jikinsa ya shige bathtub din ahankali tareda kwantawa Yana rufe idanuwansa.

Shiru yayi cikin ruwan tsawon lokaci seda ya ji jikinsa ya Dan sake sake sbd ruwan zafin dake ratsasa sosai suka sakar masa da jiki tsawon lokaci kafin ya fito cikin ruwan duk acikin sanyi ya dauki brush ya tsaya yayi brush tareda wanke bakinsa da mouth wash kafin ya koma qarqashin shower ya sakarwa Kansa ruwan zafin sai alokacin ya sake sauke ajiyan zuciya.

Yanda ruwan yake sauka jikinsa ahankali ya sakashi ahankali ya fara dawo da tinanin halinda suka samu kansu a ciki kafin shigarsa wannan halin da baisan meya samesa ba har lokacin.,

Bai iya Tino wahalar dayasha ba kafin kasancewa da Bena a yanzu iya nutsuwa da yanayin duniyar da suka kasance a tare yake

Jin feelings din da dumin numfashinsu Daya ringa fita Yana sauka a lokacin harma da

Wani girmamammen lamari Daya risketa aciki

Wanda ya sakasa sallama mata duniyarsa gabaki Daya sune yake tinawa suna dawo masa acikin Kansa,

Bai taba kusantan kowace mace ba Dan haka baisan ya ake nufin Virgin ta kasanceba Amma dai a iya abinda yaji Yakuma tarar Bena din ta sake komawa Virgin bayan haihuwan ne? kokuma bata Haifa Amnah da kanta ba?

Idanma Cs Akai mata to ya akayi Bai taba Jin dinki a Mararta ba sbd yasha shafa Mararta tin kafin su zama Abu daya yanzu din.

Meyake faruwa ne?

Shine baisan komaiba akan wainnan abubuwan kenan kokuwa dai akwai abinda ya kamata y sani dinne Bai saniba?

Wainnan tinanin sune suka cika Kansa kafin na tashin hankalin da mamaki suka biyo baya sbd sai alokacin yake tinanin meya samesa ya shiga halinda ya shiga,

Idan ya Tina daidai mutuwa yaji yakusa yi da mummunan desire da zai kira da dark desire ma sbd a lokacin da Bena batazo ba zai iya afkawa duk macen Daya samu Wanda zai iya kashe Kansa idan Hakan ba a faru bayan ya dawo hayyacinsa sbd tsananin gyanqyaminsa da raayinsa na macen Dayake so ne har cikin zuciyarsa da ruhinsa kawai zai iya kwanciya da ita shiyasa bazai taba iya kwanciya da dayan matarsaba sbd zai cutatar da ita matigar ya kwana da ita babu digon sonta cikin ransa,

Yabarta ne idan yaga bazai iya adalci ba zai sallameta taje da budurcinta ta samu Wanda yake sonta har Zuciya.

Ya jima sosai Yana San jikinsa ya Dan samu karfi kafin ya gama ya fito daureda towel a qugu ya ratayo dayan a wuyansa Yana tafiya ahankali fatarsa ta sake haske sbd kwanciyar dayayi kwana biyu yayi fayau kaman mace me sabon shigan juna Biyu.

Ko Daya fito tini Naseer ya ajiye masa kaya da underwear sabbi na sunspel masu tsada.

Jikinsa ya goge a hankali da sauran rashin kuzarinsa ya gama ya saka underwears din da saka short wando me Dan tsayi kadan da black rugbay shirt sai alokacin yayi salloli

Yana gamawa yayi adduoinsa Yana tashi ko gadonsa Bai qarasaba su dd babba suka shigo dakin kowannensu a tsanake cikin jallabiya

Dan lokacin 7 harta wuce.

Dd babba ne ya fara ware hannu cikin farin ciki me tsananin gaske ya rungumesa tareda Dan bubbuga bayansa Yana kiransa da “my champ”

Shima dad kaante cikin farin cikin ya Dan rungumesa Yana Jin zuciyarsa na sanyi sbd

Daya rasa DD Shima kaman yanda ya rasa

Bilal da shikenan baisan ya rayuwarsa zata kasanceba.

Zeenah data shigo daga baya da gudu ta garaso ta fada jikinsa tareda rungumesa

Shima rungumeta yayi ahankali Yana Dan Jin sassaucin nauyin zuciyarsa dake azabtiwa da rashin ganin wadda yakamata ya fara Gani farko farko.

Hawaye Zeenah ta ringa yi Wanda ya sakasa

Bude bakinsa dole yayi mata magana da

cewan

“Meyesa kike Kuka?

Kin dauka zan mutu ne?

Wa zan barwa ‘yata da..

. Shiru yayi tareda

kasa qarasawa Yana dagowa ya Kalli su dad kaante Kai tsaye dd babba ya kalla Yace

“Bata zo bane?

Lafiyanta kalau right??

Zeenah na Jin Hakan ta dakata da hawayenta tana zamewa daga jikinsa tana Satan kallan dd babba dayace kar Wanda ya sanar masa halinda ake ciki.

Dd babba fuskewa yayi cikin basar da zancen da kulawa yace

‘tama kasan batajin dadi so tana Nigera sai ta warke sosai zata iya zuwa daga baya kokuma idan mun koma shikenan.”

Yanda yayi maganar yasaka DD Kai tsaye

Shima ba Wani shakka ko Wani Abu kunya yace

“Sosai ne batada lafiya??

Nayi forcing kaina sosai ne akanta har haka?

Did I really f… cikin Wani irin Jin nauyi dad kaante ya katsesa da cewa

“Rashin lafiya ne kawai Kuma ta warware inshallah.”

Naseer ma Kansa qasa yayi sbd nauyin maganar DD din Wanda Sam shi bai ji Wani komaiba sbd yasan tabbas ya nuna mata qarfi tinda Bai dauka zai sameta a yanda ya sameta din ba,and baitaba dauka haka ake samun

Kai acikin wannan rayuwarba shiyasa ya kasa controlling Kansa Dan haka idan har shine ya sakata a wannan halin Yana bugatan komawa

Nigeria cikin ganganin lokaci sbd yaga yanayin jikin nata kada tanacan tana Jin jiki sosai Bai saniba.

Dd Babba Kuwa bai damuba da zancen  dinba sbd yasan shi Dan Kai tsaye Daman musamman ga wadda yake Jin yanxu bazai iya controlling Kansa akan Yanda yakeji a zuciyarsa ba shikuma Daman Hakan shine fatansa.

Yanayin yanda DD yayi shiru ne Kauai ya saka dd babba Dan shiga nazari sbd idan Basu nuna masa taji sauki da gaske ba ba lallai ya zauna anan din dasuke son ya zauna ba har su fara zuwa su samu mafitan nema Bena din da qaske sbd dole zasu masa dubara abarsa

Nan su koma su kadai.

Shima DD din a natse cikin sanyi ya karanci yanayinsu Daya bayan Daya Amma Bai kawo tinanin komai a ransa ba bayan na sosai ya nunawa matarsa qarfin Daya illatata may be.

Kowanne fuskewa yayi suka danne suna sake bayyanarda farin cikin tashinsa Dan haka tini suma yan Nigeria aka sanar dasu suka samu farin cikin farfadowansa Kuma ana sake shiga fargaban bayyanarda maganar batan Bena.

Shi Kansa bai sake nuna damuwa ko Wani yanayi ba gameda maganar Bena din saima ya

Dan ringa daurewa Yana nuna jarumtar qarfin jikin Dayake samu.

Har yamma suna Asibitin anata nuna masa kulawa kaman zasu hadiyesa shi dai Bai Wani sake sosai ba sbd zuciyarsa data kasa samun cikakkiyar nutsuwa,

Hakanan yakejin Sam hankalinsa ba kwantawa zaiyiba matigar ba Bena din yaji ba.

Washe gari ahaka suka sake wuni results dinsa sun fito babu sauran drugs din a jininsa

Amma sun Basu takardar Asibiti data hukuma

Datake bayyanarda bashine yasha da Kansa ba Basa Akai Bada saninsa ba Dan haka hukuman gasar ta Bada takardarta akan idan sun koma gida Nigeria Akai binciken gano komai zasu shiga cikin zancen Wanda zaa kama da qwayoyin.

86

Wannan bayanin da Akai tas a gaban DD lokacinda suke office din hukumar Zurich din sai alokacin yasan haqiqanin meyake faruwa,

Wato Wani ne ya saka masa mugayen qwayoyi, to Amma a Ina?

Idan tinaninsa yazo daidai a ranar tinda gari ya waye babu Abinda ya sakawa cikinsa hatta ruwa Bai Sha ba sbd damuwa da bacin ran labarin accident din Bena haka ya tashi ta biyo jirgi baici komaiba harya sauka,

Daga airport office dinta ya fara tsayawa

Kuma anan ma baici komaiba haka ya Isa highbridge baici komaiba Saida yayi ordern abinci Wanda ya Saba cin abincinsu Daman bawai yanzune yafara ci ba,

Bayan wannan abincin baici komaiba a ranar

Kuma tabbas Yana gama cin abincin Nan yasamu Kansa a mawuyacin halin da babu

Abinda yake tinawa sai azabar daya ringa Sha a jininsa Daya ringa quna Yana babbaka, Zuwan Bena shine yabasa Iko da Daman yaqar ciwon da azabar sbd sonta Mai tsananin gaske da baimasan akwaisa a ransa hakanba shine yafi garfin azabarsa ya iya dannewa.

Shiru yayi a bayan motar shida dd babba

Wanda Shima tinanin yakeyi Yana Jin a jikinsa ko menene matar DD din Daya tanada alaga da wannan Lamarin.

Shi kuwa DD tinani ya ringayi tsakanin ordern abincinsa da kawo abincin babu Wanda yazo gidan bayan Safnah sai Bena daga baya.

Bena ta fita Sam a zancen ya cireta sbd Koda ta iso Yana gap da rasa ransa ma gaba Daya

Dan haka koma menene a tsakanin zuwan

Safnah da Wanda ya kawo abincin ne.

Batareda ya juyo ya Kalli dd babba ya Bude baki a natse yace

“‘Me binciken da akeyi ya bayar?

Ansan waye ne?

Akwai Wanda zargi ya nuna?

Menene ainihin dalilin Daya Hana Mummyn

Amnah tahowa?

Shiru dd babba yayi tareda sauke numfashi

Shima Bai Kalli DD dinba yace

“Bayan matanka biyu a ranar babu Wanda yaje gidanka,

Su Biyun ne kawai suka shiga a dai time din da ake zargin daga lokacin ne koma menene ya sameka.”

Sai alokacin D ya juyo ya Dan Kalli dd babba da idanuwansa dasuka qara haske sosai ya Bude baki Kai tsaye yace

“Kai ne ka Bada Daman a Dorawa BENAZIR alaman tambaya akan wanna maganar kokuwa su masu binciken ne??

Shima dd babba sai alokacin ya juyo ya Kalli

Dawood din da kwariininsa Shima ya cika masa Ido musamman da babu Annuri ko Daya a fuskarsa.

Wani lalataccen murmushi dd babba yayi kafin ya dauke idanuwansa akan DD din yace

“Kanada huija ko shedan fiddata daga zargin kenan?

“Ko menene acikin abincin danaci a ranar ko ruwan danasha suke,

Dan haka a lokacinda aka tafi gidana a in in

Dayake kan dining shine Abu na farko Daya kamata a dauka Dan aunawa.”

“Kana tinanin baayi Hakan bane?

Babu abincin da aka Samu ko abinsha a dining ko kitchen koma duka dakunan gidan Dayake nuni da kasha Wani Abu ma kafin shigarka halin daka shiga.

Numfashin takaici DD ya sauke sbd Abinda ya kamata ayi bashi akeyi dinba a nasa ganin Dan haka yace

“Naci abinci a ranar Wanda nakeda tabbacin shine ya bamu wannan matsalan Dan haka zan kira securities na highbridge zasu turo footage na sake dubawa,

Idan har babu komai Dayake nuna naci abinci a gidan har shara idan an duba to tabbas fitar da abincin Akai Dan haka Wanda ya fitar da abincin shi kawai ake bugatan Gani asan inda zaa fara sauran binciken

, “

Wanna maganar tasa ta saka dd babba yin shiru Yana shiga nazari tabbas dole idan yaci abinci to meyasa zaa kawar da komai agi barin ko spoon Dayaci abincin dashi Kuma ko a sharar gidan babu inda aka zubar da komai da alama gidan aka bari dasu kenan gaba Daya.

Ajiyan zuciya ya sauke tareda kallan DD yace karya kira securities da Kansa tinda Bai gama warkewaba ya bari Ashir bello zai nemesu ya sake duba footage din dakyau ya duba Wanda ya fita da Wani Abu Dayake nuni da kayan abincin ne.

Hakan da dd babba yayi shikuma shine ya sake jefa zuciyarsa cikin zargin akwai abinda ba’a son ya sani shiyasa baa San ya shiga zancen bayan shine sosai a cikin zancen.

Shiru kawai yayiwa dd babba din har suka

Isa gidansa aka saukesu su Kuma suka Isa masaukinsu.

Baibu waya a tareda shi sbd bashine ya kawo

Kansa qasar ba kawosa Akai Dan haka da daddare har ya kwanta ya kira Naseer a wayar gidansa yace ya kawo masa waya ko iPad

Yana son magana da Amnah.

Hakan dayace ya saka Naseer fita ba jimawa ya kawo masa tasa iPad din Dan yayi amfani da ita.

A daidai wannan lokacin Amnah na tareda

Nafisat tana gyara mata kanta cikin kulawa

Kiran ya shigo.

Amnah na ganin numbers din na waje ta San daddynta ne da sauri ta tashi daga jikin Nafisat tana murna ta dauki wayar.

Kyakyawar fuskar daddynta ce ta bayyanar mata cikin tsananin farin ciki ta ambaci sunansa tana cewa

“Daddy na ya warke Allah ya karbi addua na danakeyi kullum yehhhh”

Wani sanyi ne ya shiga zuciyarsa ya Dan lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta yace

“Angel din daddy nayi kewanki”

Zaunawa tayi daga tsallan da take tana marairaice fuska tace

“Daddy nayi missing naku kaida mummy kullum bana iya bacci da daddare sbd mummy

Bata Nan,

Nidai Dan Allah ku dawo,kace mummy na ta dawo….hawaye ne suka fara gangaro mata sbd a kwanakin ba garamin kewa da guncin rashin mahaifiyarta takeji ba dagyar take iya bacci kullum haka Nan take Jin wata irin kewan mamanta tana cinta kusan kullum da zazzabin dare take kwana haka Nafisat ke kulawa da ita Sosai kaman jininta.

Shiru yayi tareda zubawa Amnah din idanuwansa dasuka saka yarinyar sake tsinkewa da hawaye tana sake ambatar sunan mummynta jiki a sanyaye.

Wani Abu ya Dan hadiye daga maqoshinsa

Daya tsaya kafin ya Dan diadaita Kansa batareda Abinda yake zuciyarsa ya sauka kan fuskarsa ba cikin nutsuwa da kulawa yace

“Angel,Ina mummynki taje ne??

Dagowa tayi ta kallesa tana sake tsiyayo

hawaye tace

“Mummy ba tana gurinka ba inji su Umme da

dad kaante hakama aunt Z tace mummy tazo

gurinka itama batada lafiya zasu warke ku

dawo tare”

Shiru yayi tsawon mintina yana shigar

da zancen Kansa kafin ya sake kallanta

da idanuwansa da zuwa lokacin sun fara

sauyawa ya sake tausasa murya cikin nutsuwa

yace

“Tinda ta taho gurina Kuma bakiyi waya da ita bane?

Girgiza Kai tayi tana cewa “kullum idan nakirata bana samu Kuma idan nace aunt Z ta bani mummy na muyi magana sai tacemun tana bacci kokuma tana sallah”

Shiru sukai dagashi har Amnah din tsawon mintina kafin ya dago ya kalleta yace ta miga

Nafisat din waya taie ta dauko littafin karatunta na Arabic ta nuna masa.

Migawa Nafisat din iPad din hannunta tayi tareda migewa tabar dakin zuwa dakin mummy dinta da gudu Dan dauko littafinta.

Tana ficewa Bai tsaya komai ba Kai tsaye cikin kamewan murya yace ta fada masa ina Bena take.

Shiru Nafisat tayi gabanta na faduwa hakama tana kasa dagowa ta Kalli wayar sbd tsoro da kwarjininsa.

Cikin Dan daga murya ya qara maimaita tambayar bacin ransa Dayake controlling Yana

Dan bayyanuwa.

Rawa hannuwanta suka Dan fara Yi murya na rawa tace

“Bata Nan”

“Tana Ina??

“Bansaniba,Amma ance wa Amnah tana tareda ku”

Shiru yayi kawai daidai lokacin Amnah ta kawo littafinta ta ringa masa bayani yana sauraranta kawai da amsa mata Amma kwata kwata hankalinsa da nutsuwansa baya Akai.

Yana gama magana da Amnah Kai tsaye

Ummensa ya kira Yana kiranta cikin murna

tahau gaisawa dashi tana Jin Dadin iinsa kaman daga sama taji yace ta Basa Bena yanason magana da ita.

Murmushin qarfin hali tayi tana cewa

“Yanzu ta kwanta bacci sbd ilkin nata Bai

gama warwareba kasan Kuma tana bugatan

samun isashen hutu Dan haka kabari

lokacinda take farke sai a kiraka.

Numfashi kawai ya sake tareda cewa shikenan ya kashe wayar.

Yana kashe wayar saukowa yayi daga

gadonsa ya zira slippers ya fito da keys na

motarsa Daya dake qasar Yana fita ya fada

motar yaja ya fice batareda Naseer da Zeenah

dake gidan ba sunsan futarsa.

Kai tsaye gurin dd babba ya nufa sbd baya bugatan Wani kwana kwana ko boye boye a sanar dashi Abinda yake faruwa bayason kayan ciwon Kai da haukan dasuke Neman manna masa Dan tini Kansa ya fara daukan zafi da nauyi.

Koda ya Isa yasan room numbers nasu Dan haka Kai tsaye na dd babba ya nufa Yana

Isa ya tadda room service zata fito Dan haka dakin Yana Bude ne Kai tsaye ya shige tana taresa ko sauraranta beyiba ya wuce zuwa quryan bedroom din sbd babban daki ne na masu kudin gaske Wanda zakaji kaman kana gidanka ne a sake.

Daidai kofar bedroom din Yana Isa ya sakata cak Jin Abinda dd babban ke magana Akai cikin waya Dayake Yi da Sir Ashir bello babban

Jami’in binciken sirri.

Bayanin Ababa da asalin komai Sir Ashir bello ya buqaci ji komai da komai sbd yanzu binciken ya shigo da mutane cikin zargi da yawa,

Matar Dawood din Safnah da mahaifiyarta na ciki dumu dumu hakama Ababa da ake zargin batan Bena dashi Kuma idan har yanada saka hannu a batan Bena shi to tabbas akwai alaqan batanta da Abinda ya samu DD.

Hakama ta Wani bangaren dole itama Bena din da Naseer zasu shigo binciken sbd Bena kadai ce ta samesa tagansa a halinda ya shiga dalilin gwayoyin.

Ajiyan zuciya dd babba yayi yafara yiwa sir

Ashir bello bayanin komai Daya bayan Daya na asalin rayuwar dasu Bena da mahaifiyarsu suka taso ciki da asalin Rabin kwakwalwan da mahaiflyarsu da sumayyah wadda itace Asalin budurwar Bilal Kuma mahaiflyar Amnah tareda yanda kaddara ta samar da cikin da renansa da yanda Ababa yarinta musu barazana a fakaice cikin dubara har suka aminta da auren sumayyah tazo ta rasu a gun haihuwar yayi canjen sumayyah da Bena tareda boye musu cewan sumayyah Bilal ne yazo ya sace gawarta da haryanzu basusan inda gawar suke ba wand yakeda tabbacin Shima wannan zancen akwai abinda yake boye cikinsa Basu saniba.

Kudin Daya ringa bawa Ababa da yanda yaketa bincike da Neman hanyar karbe mahaifiyar

Bena daga hannunsa duk ya hada ya fadawa sir Ashir bello din Yana dorawa da cewa

“Ina zarginsa da batan Bena kaman yanda nake zargin matar Dawood da saka hannu a kan duka lamarin biyu sbd kishinta hakama

Ina zargin akwai Wanda yasan me suke aikatawa idan ma suna aikawatan sbd yanda duk Abinda muke Gani akwai me bibiyab safnah din.

Idan akwai abinda DD ya taba ji a rayuwarsa

Wanda ya buga zuciyarsa Nan take yaji Yana Neman kamuwa da heart attack to wannan abubuwan Dayake ji ne a yanzu a bakin dd babba Wanda idan a gurin Wani yajisu bazai taba yarda da Hakan na faruwa a duniya ba.

87

Kansa kasa yarda yayi da Abinda yaji Dan haka ko ganin gabansa bayayi ya juyo yabar dakin ya fito jiri na juya Kansa sosai ya sauko qasa kaman Wanda yake cikin maye haka ya Isa motarsa ya shiga ya zauna zufa na feso masa Tako ina yanajinsa a wata duniyar ta daban,

Kansa ba zafi yakeyi ba wuta yakeci sosai da sosai,

Bena dinsa ce ake fadan ta taso a wannan rayuwar dayakejinta kaman duniyar wasu dabbobin ce ake fada?

Bena dince ta taso tana wankin wasu qattin Maza?

Bena dinsa ce ake maganar da yanzu tana hannun yan drugs?

Bena dinsa ce ake maganar ta taso cikin yunwa da wahala irin wannan da ko karensa bazai iya bari ya Rabi irin wannan wahalar ba bare ace Macen datayi nasarar da Saar shiga inda babu wata mace a duniya data shigar masa wannan gurbin,

Bena dinsa ce ake fadan ba ita bace asalin macen da ‘dan uwansa ya so ba,ya muaamalantu da ita suka samu ciki ya haifi Amnah ba….

Bilal da sumayyah ana nufin tare suka  Kone a motan Bilal?

Idan haka ne meyasa gawa Daya aka Gani?

Hakan na nufin dayansu na Raye?

Waye cikinsu a Raye?

Innalillahi wainna ilaihi rajiun”

Wannan mutumin daya haifi su Bena mutum ne kuwa kokuwa wani dabban ne Allah yayi da suffan mutane?

Antaba Kaisa Asibiti antabbatar da lafiyansa kuwa?sbd wasu mutanen ana zaune dasu ne kawai batareda ansan mahaukata bane masu asalin Abinda ake kira hauka.

Wata rawa jikinsa keyi sosai zufansa na qaruwa sbd Wani mummunan zazzabin tashin hankalin Abinda Bai taba ji ba ko tsammata a rayuwar ba Daya rufar masa a take.

Hannuwansa na rawa ta tayarda motar Yaja Yana fitowa daga parking lot din gurin Yana daukan iPad din Naseer dake hannunsa ya nema Naseer din Kai tsaye ya sanar dashi ya Siya masa ticket din komawa Nigeria yau din Nan komai tsakan dare.

Naseer na samun sakon ya miqe daga kwancen Dayake cikin mamaki da tsoro da fargaban ko DD din yaji maganar Bena ne.

Fitowa yayi yaje har bedroom dinsa ya dubo yaga baya gidan ya fita yaje ya duba motarsa ma Bata gidan take yasan yasan komai na maganar rashin sanin inda Bena din take Dan haka baida zabi bayan cika umarnin DD din.

Take yayi contacting Wanda zai Siya musu ticket da komai take sukai sa’a akawai jirgin dazai tashi zuwa Nigeria cikin Daren Dan haka dole ya hau hada musu kayansu ba tareda ko Zeenah ta saniba sbd tayi bacci na gajiya da rashin nutsuwar zuciya dasuke ciki musamman ita da kullum Kuka takeyi sbd shakuwa da kaunar dake tsakaninta da Bena ga tsananin tausayinta da kaunarta data qaru a ransu me tsananin gaske bayan da dd babba ya fada musu komai gameda raywarsu Bena din wadda hatta Umme data ji sai data kwana tana Kuka itada Zeenah,dad kaante kuwa Jin yakeyi da shine yasan da Hakan tini da bazai iya bin komai a hankali dinba kama Ababan zaayi a batar dashi gabaki Daya Annen Kuka ai insha Allah aikin zai karye ko baya Nan.

Koda DD ya iso gidan Yana shigowa bedroom dinsa kawai ya nufa ya a sauya kayansa daga na bacci Daya fita dasu baa cikin nutsuwa ba zuwa Riga da wando marasa tsayi ya saka facemask da Fcap ya fito Kai tsaye ya fito

tini Naseer ya saka kayansu a mota Dazata kaisu airport suka wuce.

Har lokacin cikin Wani irin mummunan hali yake sbd zazzabin dabai taba shiga bane a jikinsa hakama zuciyarsa Wani irin wuta take ci dashi tana qarawa jikinsa zafi da zufa.

Maganar ma rashin ganin Bena ganganci ne ake fada bayan ansan yanda tayi rayuwa hannun mutumin dayake amsa sunan ya haifesu Dan haka shine na farkon zargi ma akan batanta,

Fatansa dai yanzu yafara zuwa ya tsaya gabansa suyi magana ta billions tinda itace yarin dayafi Ganewa akan komai.

Idan kudine matsalansa to zai nuna masa kudinsa ko uwarsa ce calculator saiyayi batan lissafin da zai Basa shikuma Abinda yakeso daga garesa na Ina Bena take.

Hakama zai ninka masa ninkin su ya siyar masa da yancin Annen Bena ko nawa ne ya fada zai Basa daganan zai aikasa inda yakamata ace tini an Dade da aikasa sbd Bai yarda shi din me hankali bane.

Suna Isa airport ko awa Daya Basu rufa ba jirginsu ya daga zuwa Nigeria.

Dagawansu baifi da awa Daya ba Zeenah ta ankara da cewan ita kadaice a gidan take tahau Neman wayar Naseer Bata samu sai ga sakonsa Daya tura mata tin kafin su tashi ya shigo a lokacin na cewan D ya sakasu komawa Nigeria a Daren.

Tana ganin sakon hankalinta yayi mummunan tashi gigice ta kira dad dinsu ta fada masa.

Shima tashi hankalins yayi sbd yasan zafin kan DD bazai bari a tsaya ana komai a nuku nuku a boye ba sbd kada sunan family ya lalace akan Benan Nan ya fahimci yafison kowama ya sani sunan Kaantes ya dade Bai Baci ba.

Da Kansa ya fito dakinsa zuwa dakin dd babba ya sanar dashi halinda ake ciki.

Shiru dd babba yayi Shima baiso Hakan ba dan haka yace suma ba amfanin zamansu a nema musu jirgi gobe su koma.

Dad kaante na ficewa wayarsa ya daga ya kira Abbakar ya sanar dashi a sake budewa Ababa wuta harma dasu Safnah din asake Bude musu wuta ta yanda Wanda yakeda hannu acikin batan Bena zai iya yin Abinda zaa ganesa da wuri kafin DD ya iso zafin abin zai iya baci sosai.

Yana gama waya da Abbakar baccin dake idanuwansa ya kaurace gabaki Daya sbd baisan me Dame DD ya saniba a cikin Daren dazai iya barin qasar a take.

Umme ma hankalinsu tashi yayi data samu labarin abinda yake faruwa na tahowar DD Dan haka ta kasa samun nutsuwa kwata kwata.

************

Ababa a Karo na biyu Abbakar ya sake kawo masa kudi tareda buqatan son gaisawa da Anne wai Bena zatayi magana da ita a waya.

Shiru yayi wannan Karan qin karban kudin yayi ya Dan dake ya koma cikin gida ya jima kadan ya fito ya Kalli Abbakar yace batajin dadi bazata iya fitowa ba ta kira ni zuwa anjima zan hadata da Annen.

Hakan Daya fada ya saka Abbakar cewa shikenan sukai sallama ya miqa masa kudin dayazo dasu baiyi Niya ba Amma sbd kada a Gane komai saiya amsa kudin kawai Yana washe bakin qarfin hali sbd lamarin yafara isarsa.

Abbakar na wucewa yakoma cikin gida Yana hada zufan tashin hankali da tsoro sbd ya tabbatarda akwai abinda yake faruwa,

Wai shi wace qaddarar ce ma ta Kaisa hadewa dasu Safnah?

A baya duk barnarsa dayake abarsa cikin rufin asiri da lumana,

Tafiyar Bena zir na Neman janyo masa masifu kala kala Dan haka wlh bazai yarda su jefasa masifar datafi wadda yake ciki ba ta sanin gaskiyarsa da kaantes sukai akane haihuwar Amnah.

Hande data ga Yana hada zufa ransa bace Yana Neman recorder dinsa da yayiwa mummunan boye wadda duk Abinda su haj Nuratu bulama da Safnah suka tattauna dashi akan abubuwan dasuke buqata.

Hakama abinda Basu saniba a ranar da suka Basa kudin Nan Bai baro gidan ba Saida ya qyalla Ido akan me aikinsu Rabi Daya ga yanda suke maganar komai a gabanta bayan takawo masa kayan Sha

Hakan ya tabbatarda masa da tasan dukkanin sirrinsu.

Ranar Daya tabbatarda Basa gida saidaya koma ya samu ganin Rabin Kallo Daya yayi mata maganin Dayake mata dashi ya kamata take ya bayyanar mata da buqatansa ta zai raba duk Abinda ya samu da ita Amma ta sanar dashi duka motsinsu sbd ya tabbatarda zasu iya munafurtansa.

Rabi data San halinsu ciki da waje Kuma taga yanda suke tsoran shedancin Ababa dayafi nasu take ta amince da buqatansa sbd ganin Suma sun yarfada da nasa balain yafi nasu Dan haka Rabi tasan sai tafi zama safe idan tana tareda Ababa Dan haka cikin qanqanin lokaci yagama sanin sirrinsu a gurin Rabi hatta video din yanda suka kashe hajiyar Alh basheer bulama tana dashi duka suna hannunsa.

Bayan ya samu video dinne ma yayi baqin cikin shiga lamarinsu sbd yasan zasu iya Shafa masa kashin kaji Dan haka kafin ta lalace masa tasu zai lalata ya samu Daman silalewa kafin adawo Kansa.

Kayan Daya dauka dauka ya fitane yasaka hande binsa tana Kiran sunansa Amma Sam Bai tsayaba ya fice hande ta tsaya kallan iKon Allah tana tsinewa Anne da zuriarta sbd sun zautar masa da ‘da,

Sauran duk sun tafi ynzu wannan data dawo zata haukatar mata dashi.

Bayan fitarsa wayarsa ya fidda tareda Kiran Rabi yace ta shirya ta gudu ta koma gidan kaantes sbd Tona asirin su Safnah zaiyi porthacort zashi da sassafiyar washe gari daga can bazai dawoba.

Tana Jin Hakan tace maganar kudin dasukai zasu raba Kuma fa?

Cikin masifa da takaici yace ” au baki gode na barki ba zan zareki acikin su shine kike maganar kudi bayan kinsan kema ba fita zakiyiba idan zancen ya fita,

Abinda yasa na barki ki koma Kaantes ki nuna barazanar kasheki sukeyi kika gudo sbd so neke Suma ki ringa sanar Dani halinda ake ciki har na samu na gudu tukuna,idan ha haka ha ai kema inada shedan dake suke kulla komai har kisan dake Akai tinda kingani kikai shiru harda video kinada Amma kikai shiru.”

Motsin da Rabi taji a bayanta ya sakata juyowa da sauri tana sakin wayarta ganin Safnah bayanta tsaye.

Wani irin zufane ya karyowa Rabin tayi saurin matsawa baya zatai magana Safnah ta sakar mata murmushi hankila kwance tana cewa

“Ruwan tea zakiso ki dafamun fita zanyi Yi sauri.”

Kallanta Rabi tayi gabanta na tsananta faduwa Amma ganin yanayinta ya sakata Jin sanyin Safnah din bataji komai a wayar datakeyi ba.

Ajiyan zuciya ta sake a boye tareda cewa to.

Wucewa yayi a sanyaye ta nufi kitchen ita Kuma Safnah bayanta tabi da Kallo tana Jin zuciyarta na Neman kamawa da wutan tashin hankali da baqin ciki Amma bayyanarda fushin ba amfani a yanzu dasuke gab da haukacewa a cikin masifar dake faruwa.

Ko ruwan Bata Dora ba Safnah tace ta barshi.

Daki ta koma ta sanarwa momy komai babu jimawa momy ta fito ta bawa Rabi kudi tace taje ta siyo mata katin dubu biyu a layin bayansu.

Karba Rabi tayi jikinta na rawa sbd hanyar tserewa gidan take nema komai Bata dauka ba ta fito da niyar idan taje Siyan katin bazata dawoba guduwa zatayi.

Tana fitowa tayi bayan layin nasu da babu mutane sai titi tafara sauri tana waiwaye taga babu kowa tafara gudu gudu sauri sauri.

Tana wannan gudun da sauri Bata Ankara ba mota tazo a mugun guje tayi sama da ita ta watsar kan titin a kakkarye ba Rai jikinta jini na fitowa ta koina.

Motar Bata tsayaba saima gudu data qara suka hau titi daidai da kyau suka nufi gidan Ababa kai tsaye babu Wanda zuciyarsa Bata rawa sbd idan Ababa ya Isa porthacort komai ya qare gwara Shima yau ayita ta qare momy a shirye take data kashesa ayau Shima batada baqin ciki da asara.

Safnah kuwa itadai babban burinta a tsayar dashi daga zuwa gurin dad bulama kada duniyarsu ta tsaya suyi mummunan karshe.

Suna Isa gidan hankali tashe suka fada gidan Kai tsaye dakinsa suka nufa babu wata wata suka hau dubasa bayanan Safnah tace

“Momy wlh shikenan ya tafi zai Tona mana asiri,

Yasan mune Muna kashe hajiyarsu Dad,

Yasan mune muka sakawa D wannan qwayoyin,

Yasan komai akanmu fa munshiga uku mun lalace,me zamuyi yansu mu datakar dashi…

Cikin tashin hankali momy tace “wlh bazamu bari ya isaba hanya Zamubi yanda muka taka Rabi da mota yanzu haka zamu take kansa da mota Shima mu aikasa inda ya kamata…..

Daga bayansu hande cikin daga murya da tashin hankali da mamaki tace

“Me nakeji?

Ababan ne zaa take kansa da mota??

Ke Safnah uban naki kuke maganar a taka Kansa da mota?

Me kika zama?

Kisa kukeyi yanzu,wace hajiyar Kuka kashe??

Momy dake cike da zallan baqin ciki da tashin hankali na masifa a zafafe ta harbi handen da qafa Daman takiacin tsohuwar takeyi.

Safnah ma data rasa abinyi jakar dake hannunta ta Bude sauran gari qwayoyin dasuka bawa DD suna Jakarta su ta Ciro ko ruwa Basu sakasu ba ta zazzagewa hande a baki momy ta dauki kofin ruwan dake gurin da sauran ruwan da qadangaru suka gama Sha ta zubawa bakin handen take qwayoyin sukai mata cikin ciki jikinta take ya dauko jijjiga sbd jininta na tsufa baiyi karfin na DD ba Dayake matashi Kuma namiji.

Sakinta sukai yashe a tsakar gidan jikinta na wata irin jijjiga kaman ba mutum ba suka fice.

Suna ficewa Ababa na dawowa gidan yayi mantuwa ya tadda hande tsakar gidan a yashe kaman gawa hancinta da bakinta duk jini.

Rawa jikinsa ya dauka da Wani irin mugun zufan tashin hankali Yana kallanta Yana tsoron tabata hannuwansa su fito jikinta Dan haka ya juya da gudu yaje dakinsa ya dauki passport dinsa Daya manta Wanda yayi kwanaki Dan irin Hakan Yana dauka ya fito daga dakin Yana kallan gawar hande dake yashe Yana Jin radadin da Bai taba jinsa a zuciyarsa ba Kuma yasan aikin waye Dan haka zasusan wa suka taba daga yau wasan kowa yazo karshe.

Ledan robar dasuka yar tsakar gidan ta qwayoyin dasuka durawa Annen ya nufa ya dauka da hannunsa bayan ya sakasa a leda ya daure ya dauki ledan roban ya saka cikin wata babban ledan ya daure Kai tsaye ya ajiye gefen hande ya dauko wuta ya babbakawa gidan sbd kada a tararda gawar hande da wainnan qwayoyin a gidansa su sake sakasa cikin masifar Dayake ciki Dan kuwa hukuncin qwayoyin kawai rayuwarsa bazata dauka ba.

Yana gama babbakawa gidan wuta ya fito da sauri lokacin duhun magrib ya wuce Yana fitowa daidai Naseer na parking mota a kofar gidan.

D ne yafara fitowa Kai tsaye cikin gidan da wutar ke ci sosai da a nufa ya fada sbd dubo Annen Bena Yana shiga yaga hande kwance a yashe da leda gefenta.

Wuyanta ya taba dakyau yaji akwai sauran Rai atareda ita Dan haka Kai tsaye ya sunkuceta sbd tinanin itace Annen Bena ya dauko ledan dake gefenta ya fito da ita da sauri.

Ababa kuwa DD na shigewa gidan Naseer bugu Daya yayiwa wuyansa me kyau na maji qarfin matashi take Ababa idanuwansa suka juye zai zube agurin some Naseer ya cirasa sama ya Bude boot din motarsu ya sakasa ya rufe D na fitowa da hande suka saka bayan mota ya shiga suka bar gurin take zuwa Asibiti.

88

Suna barin kofar gidan da mota gidan wutar gidan ta sake kamawa sosai yan anguwa da tsirarru wainda ke kusa suka fara ankara da gobarar gidan Amma da yawa suka qi tahowa kawo dauki sbd Ababa da baya mutinci ko gaisuwar mutunci ma bayayi da mutane,hakama baka Isa ya Rabi ko katangar gidansa ba sai yace kana leqa masa ta da ‘yaya akan wannan kawai sai yakai qararka acika tarar kudade ba dalili tsaban zalinci da mugunta,

Hakama Sam baya muamala da kowa bakuma yabari ayi da iyalinsa.

Wannan yasa da yawa suna ganin wutar suka fara nesa da gidan Dan kallan iKon Allah.

Kukan dabbobinsa ne Daya fara tashi sosai sbd zafin wutar Dayake kokarin Kai musu Dan haka sbd dabbobin gidan kawai yasaka mutane Kai dauki suka shiga aka Sako dabbobin tareda gargadosu waje sunata fitowa da gudu suna Kuka.

Raguna ne sosai da Shanu harma da akuyoyi da kaji masu yawan gaske.

Duk dahun magrib da yayi ana iya ganin yawansu Dan haka tini jamaa suka ringa taruwa Dan kawo dauki dakuma samun rabonsu.

Wainda sukasan halin Ababa sune suka Tara masa kan dabbobinsa guri Daya akai nesa dasu can Wani gidan da baa gamaba aka barsu Nan kafin ya iso.

Wainda basusan halinsa ba kuwa haka Suka ringa Satan kaji da raguna cikin hayaniyar da Taron mutanen suna guduwa dasu.

Naseer kuwa Kai tsaye Asibitin Kaantes ya nufa da motar Dayake ja cikin Wani shegen gudu sbd rayuwar hande dake cikin mummunan hadari Dan jini ne sosai yake fita ta hancinta sbd ita Kai tsaye qwayoyin sukai cikin kanta Dan jininta bazai iya daukaba,hakama kan nata bazai iya daukaba Dan haka Suka Huda jijiyoyinta Kai tsaye tana fidda jini sosai.

Suna Isa sbd DD ne da Kansa ya saka Kai tsaye dole aka amsheta Akai sama da ita sbd Bata taimakon gaggawa Dan Muni abin yake dada Yi.

Ana karbanta aka tabbatarwa DD cewan zaa dubata da kyau komai zaije daidai Kila.

Da wannan ya Dan samu Daman Jin Kansa dake tsananin juyawa ya Dan rage Dan haka Kai tsaye Asibitin suka bari suna kama hanyar zuwa highbridge.

Suna Isa bayan Naseer yayi parking juyowa yayi ya Kalli DD zaiyi magana D din ya katsesa da Bude baki cikin danyan Kai yace masa ya hada masa dakin kudi yanzu a cikin gidan.

Murmushin mugunta Naseer yayi tareda gyada Kai Yana Bude motar ya fito Yana nade hannuwan rigarsa Datake long sleeve.

Kai tsaye cikin gidan ya nufa Bai tsaya Palo ba ya wuce babban store Room din Dayake kitchen take ya hau fitarda kayan dasuke ciki Daman ba wasu masu yawa bane.

Yana gama fitarwa dakin yakoma zallan fili fes babu qazanta Amma duk da Hakan Saida ya Kuma tsaftacesa tsaf ya fito ya nufi dakin DD cikin closet inda wata mahaukaciyan katuwar boyayyar safe locker take cikin bango baa ma ganinta sai Wanda yasan da ita.

Password ya saka ya Bude take wasu mahaukatan kudi suka bayyana a Jere masu shegen yawan gaske tin daga kan nairsa har dollars da pounds akwai.

Haka Naseer yafara fiddosu Yana zuwa qatuwar jaka Yana Kaiwa storeroom din Yana dawowa Yana sake diban wasu Yana Kaiwa.

Saida yakai kudi me yawan gaske kafin ya dakata akwai rechargeable fans kusan guda uku manya manya acikin kayan Daya cire daga store din Dan haka ya daukosu gabaki Daya ukun ya kunna tareda bin kudin Nan Yana zazzagewa wasu suna Yana fasa bunch nasu wasu Yana barinsu a daurensu,

Babu tsoffi acikin kudin suka sabbi ne fil Dan haka tini fankokin suka fara daga kudin sama cikin dakin take dakin yakoma kaman ana ruwan kudi sbd gudun fankokin dakuma yawan kudin dake watse.

Ajiyan zuciya Naseer ya sauke bayan yagama wannan aikin kafin ya fito Kai tsaye mota ya nufa ya Bude Booth yaga har lokacin Ababa a some yake Dan haka kaman Wani Barawo haka ya cakumosa ya cirosa daga motar ya nufi cikin gida dashi.

DD dake Palo zaune Yana amsa waya daga Asibitin juyowa yayi yaiwa Ababan Wani mummunan Kallo sbd Jin Abinda ake sanar dashi daga Asibitin cewan irin munanan qwayoyin da aka samu a jininsa sune a jinin Hande Kuma nata jinin bazai dauka ba ko kadan han haka akwai yiyuwar Wani mummunan Abu ya sameta.

Kashe wayar yayi zuciyarsa na qara daukan nauyin Abinda aka fada din sbd idan mahaifiyar Bena ta rasu duniyar Bena dinsa zata tsaya ne.

Shin Ina ta hadu da wannan qwayoyin?

Waye ya Bata?

Ta Ina aka samesu?

Meya hada gidan Ababa da wainndan qwayoyin?

Tin farko ma meyasa ya fito ze gudu bayan daga cikin gidan ya fito yaga wuta naci hakama yaga halinda Annen take ciki,

Idan ze gudu ne to tabbas shine ya Bata wainnan qwayoyin,

Idan ma ba shi bane tabbas yasan inda suka fito Kuma idan yasan inda suka fito to yasan Shima waye ya Basa wainda yasha Shima.

Naseer Kai tsaye dakin ya nufa da Ababa Yana Isa ya Bude store din Daya koma dakin ruwan kudi ya tsaya daga kofa ya daga Ababan sama ya Jefasa cikin dakin kan kudade

Mummunan jefawan da Akai masa ya sakasa farfadowa agigice cikin azababbiyar azaban qafarsa Daya data Kaye take

Cikin radadi da taurin Rai ya Bude idanuwansa da tini sukai ja sbd tashin hankali da mamakin Ina yake?

Kudi yaga suna yawo a saman dakin da koina cikin dakin suna tashi sosai.

Da sauri ya sake rufe idanuwansa ya Budesu Yana Jin azabar qafarsa har lokacin da fara kallan dakin yaga koina kude a kwance da masu tashi kan iska,

Hannuwansa dake Dafe da qara ya kalla yana juyawa da Kansa Yana kallan inda yake kwance.,

Daloli ne da pounds da Bema sansu ba yan dubu dubu yake kwance akansu kaman shimfa.

Sake rintse idanuwansa sosai yayi wannan Karan ya Budesu da kyau ga tabbatarda kudine yake kwance Akai,

Tashi zaune ya sake Yi Yana kallan Naseer dake kofa zuciyarsa na mummunan bugawa sbd wainnan kudin Bai taba ganinsu ba a ruyuwarsa hakama baisan dalilinsu na Daukosa ba su kawosa gurin wannan kudin,

Sake kallan Naseer yayi zaiyi magana Naseer ya katsesa da cewa

“Kudin da duk kake buqata a rayuwarka har karshenta wainnan zasu isheka,

Bakasu zaayi,babu duka ba zagi ba komai zasu zama naka ka gudu inda kayi niyar guduwa kayi rayuwarka babu ruwanmu da abubuwan daka aikata ko kake aikatawa,

Duka wannan kudin zaa baka su ne a sirrance babu Wanda ya sani ko zai sani,

Duka duka Abu biyu mukeso daga gareka Wanda kana bamu su shikenan ka kwashi kudin Nan ka tafiyarka,Amma sharadin mu na farko shine duk tsanani kada dd babba ko kowa yasan min hadu dakai har munyi Wani boyayyan Hulda,.ka yarda da Hakan?????

Duk da Ababan na cikin radadin kafarsa hakama zuciyarta na cikeda tsoro,mamaki,shakka, fargaba da wasi wasi akan komai Dayake faruwa a Nan din Amma Jin cewan basason dd babba ya sani ya sakashi Jin shiga tinanin idan har basason dd babban ya sani to kenan da gaske boyayyan Hulda zasuyi dashi da gasken.

Lissafi yahau Yi akan yariga ya rasa komai,

Hande ta mutu,

Baida ‘yaya ko mata,

Ya rasa dukiyarsa suna can suna ci da wuta dabbobinsa da gidansa da Dan sauran arzikinsa dake gidan duk yasan ya rasa,

Yanzu Kuma gashi ya shiga hannun wainnan majiya qarfin dayasan ko dukan DD bazai iya dauka ba shi da yake da jikin Hutu kaman na Yara bare na Naseer Dayake kaman basamude ya tsane ruwan jikinsa tsam.

Dan haka babban fatansa da burinsa a yanzu ya samu Abinda zai gudu Yana tserewa komai da kowa,

Amma tinda boyayyan Hulda sukeso dashi zai risga dasu yasamu tserewa kafin asan meya kashe hande qaryarsa ta qare Dan kuwa ta tabbata su Safnah suyi galaba akansa kenan,

Da gangan suka yarda ledan robar qwayoyin gidansa Dan kawai su jaza masa masifar da shi duk taadancinsa baitaba sanin ya qwayoyin suke ba bare inda ake siyarwa Amma wlh bazai yarda ba mutuwar kasko zasuyi idan ma kamawa tayi Amma dai yanzu bari yaga yanda sukuma wainnan zasuyi dashi.

Gyada Kai yayi Yana kallan Naseer yace ya amince.

Ajiyan zuciya Naseer ya sake tareda Dan waiwayawa ya Kalli DD dake zaune Yana jinsu sai alokacin D din ya taso yazo gabansa ya tsaya Yana dauke kallansa daga Kansa sbd zuciyarsa zafi da radadi takeyi idan Yana kallan fuskan mutumin Daya haifi Bena Kuma mutumin Daya lalata rayuwarta ya reneta a gidansa kaman Dabba,

Da ba shine ya haifi Bena ba wlh da tin a jiyan zasu jefa shege cikin wutar dayaso barin Anne ta kama a ciki ko Rabin jikinsa ne ya kama kafin su fiddosa su miqawa jamaa shi akaisa Asibiti.

Tsanar kallan fuskansa yakeyi Dan haka Kai tsaye cikin kamewan murya da rashin Annuri ko kadan yace

“Duka wannan kudin zan baka inda Bena take kawai nakeson ji,

Kana fadamun bazaka fadawa kowa ka ganni ba bazan fadawa kowa na ganka ba.”

Dagowa Ababa yayi da sauri ya Kalli DD din sbd Jin tambayan da baimayi zatan ji daga Bakinsa ba sbd kenan tintini da Abbakar ke ce masa Bena tana Zurich tareda DD din qarya ake masa sbd ya kawo Kansa,

Kenan suma basusan inda take ba??

Da gasken kenan ta shiga duniya ta tafi???

Wani irin sanyi ne ya mamaye ransa sbd damarsa ta Kai su Safnah qasa ta dawo hannunsa,hakama kenan babu tabbacin shine ya kawar da Bena da Annenta zarginsa kawai akeyi hujja ake nema,

Hmmmnnn tabbas zai Bada hujja kuwa me kyau.

Dagowa yayi ya Kalli DD cikin marairaice fuska yace

“Daman Bena Bata tareda ku acan?

Nima zargin danakeyi tin ranarda Annenta ta bace na cewa Bena ta dauketa sun gudu Ashe gaskia ne…..

Wani Kallo DD da Naseer sukai masa lokaci Daya Jin Annenta ta Bata,

Naseer ne yayi saurin katsesa da cewa

“Wacece wadda muka sama a gidan to idan Annen Bata Nan??

“Hande ce, mahaifiyata,kakarsu Bena me tsananin kaunarsu,nayi kokarin cetan ta Amma nakasa sbd wutan shine na fito Neman taimakon masu kashe wuta asamu a fiddota shine Kuka taho Dani,

Meyasa Kuka taho Dani bayan mahaifiyata na cikin hadari”

Tsoki mara sauti DD yayi tareda gyara tsayuwa yace

“Ina Bena take?

Ina Annenta take?

Me ka sani game da tafiyanta da Annen tata?

Magana Ababa zaiyi sbd anzo inda yakeso yau Safnah zatasan shine uban ubanta a duk shedancin dasukeyi itada Nuratu, wayar DD ce tayi qara cewan yayi gaggawan zuwa Asibiti yanzun Nan.

Kashe wayar yayi tareda kallan Ababa yace

“Kudin gabanka basai na fada mata nawa bane Amma ka nutsu ka qirga miliyin Dari biyu ka ajiye mana sauran gefe,amsar da zaka bayar itace zata baka Daman daukan kudin ka tafiyarka”

Yana gama fadan Hakan ya juya ya fice

Naseer ma kofan dakin da Ababan yake ciki ya janyo ya rufe tareda saka key din kofar datake da masifaffen nauyi da qarfin masifa.

Suna rufesa gidan suka bari da sauri zuwa Asibiti.

Koda suka Isa Hande tayi Nisa bayan sunan Safnah da Ababa a bakinta babu Abinda take fizgota tana fada,

Wani jijjiga da wasu yawu masu jini jini take fitarwa.

Sunan Safnah datake fada ya saka DD da Naseer yin shiru sbd basusan waye Safnah din ba.

Babu Abinda zasu iya mata Dan haka DD ya karbi report na awon qwayoyin jininta ya fice daga Asibitin.

Suma manyan Asibitin ganin Hakan suka kira dd babba da tinda suka iso yake Kiran wayoyin DD baya samu hakama anje gidansa bayanan daga shi har Naseer Dan haka Jin Abinda Asibitin suka kira suka fada yasashi shiga mamaki da sabon fargaba yace abar Asibitin da matar Dan haka ba Bata lokaci suka tattarata suka mayar da ita Asibitin gwamnati sbd kada matsalan qwayoyin ta taba sunan Asibitinsu.

DD kuwa ledan dake motarsa ya hada da report din ya nufi office din Sir Ashir bello dasu sbd dole yanzu kam tinda ansamu ledan qwayoyin zaa iya samun fingerprints na duk Wanda yakeda hannu a samar da qwayoyin.

89

Koda su DD suka Isa office din Sir Ashir Shima Kansa ya dauki zafi sbd dd babba Dayake office din suna duba footage na Wanda ya fitar da abincin ranar da abin ya samu DD babu Wanda suka Gani bayan Safnah matarsa,

Basu sake shiga rudu ba Saida same lokaci bayan ta zuba abincin a refuge same me napep dasuka ga Yana bibiyarta bayan tafiyarta Saida ya fito ya Isa sharar ya saka hannunsa ya dauki ledan kayan abincin ya koma napep da ita Yana duba menene yake ciki yabar gurin.

Basu nunawa D Abinda suka Gani dinba bare sanar masa sbd sai sun gama Tara komai tukuna,

Saidai ledan Daya ajiyewa Sir Ashir gabansa tareda report na Asibitin hande ya saka Sir Ashir kallan dd babba Shima kallan DD yayi take aka dauki ledan Dan gudanar da binciken gaggawa akanta.

Report din kan table dake gurin idanuwan DD ya sauka yaga sunan Safnah a sama kafin yayi Wani motsi dd babba ya janye tareda miqewa yace su tafi kafin report din ya fito.

Suna baro office din Sir Ashir Kai tsaye kaantes suka nufa sbd babu Wanda ya zauna ya huta tinda suka dawo suke yawo.

Suna Isa Amnah da gudu tazo ta fada jikin dadynta ya dagata sama Yana sake Jin tsananin so da kaunarta cikin zuciyarsa sbd sai yanzu ne ya tabbatarda yarinyar marainiyace gaba da baya Ashe bayan rashin Uba harda mahaifiyarta ta rasa,Amma ko yayane dai yasan bazata taba maraicin ba bare tasan ma ba sune suka haifetaba.

Gurin Umme suka nufa suka gaisa itama Umme cikeda farin ciki da tsananin son danta ta rungumesa tana hawaye sbd masifun Nan sun fara musu yawa daga anfita wannan Se wannan.

Kofan dakin Bena ya sauke idanuwansa zuciyansa na Wani irin yankawa Dan haka ya miqe yabar sashen ya nufi nasa.

Baiyi mamakin rashin tadda Safnah ba Dan haka Bai Wani damu ba ya wuce bedroom dinsa wanka yafara Yi ya samu Dan qarfin jiki ya fito ya shirya cikin black Balmain Riga da wando yayi sallah

Yana idarwa Nafisat da Amnah suka kawo masa light abinci da Umme ta dafa masa da kanta.

Bazai iya cin komai ba dan babu Abinda yake masa daidai a jiki da Zuciya harma da bakin.

Amnah a gurinsa ta kwana bayan tayita tambayan Ina mummy dinta shi baisan me zai fada mata ba sbd Shima kaman zaiyi hawayen ne kaman yanda itama takeyi,riqe Kansa kawai yakeyi sbd kada taga hawayensa ta daga hankalinta kokuma tasan Wani Abu ya samu mummy din nata.

Har gari ya waye Bai iya rintsawa ba Dan haka zazzabi zazzabi ke Neman shigarsa sbd Bai Saba da qunci da damuwa ba bare wahalan tinani.

Daga shi har Amnah kusan zazzabin suka kwana dashi suka tashi dashi Dan Daman ita matiqar mummy dinta Bata tareda ita kusan kullum zazzabin dare takeyi sbd ta Saba shigewa jikin mummynta tayi bacci cikin tsananin so da kulawan Mummyn.

Hakanan Kansa na ciwo yayi sallar Asuba suna idarwa kusan dukkaninsu a tare suka jima masallacin Saida gari yayi haske kafin suka fito ko ciki Basu qarasa ba Kiran Sir Ashir bello ya shigo wayar dd babban dake hannun Abbakar Kuma shine ya dauka yaji sakon Sir Ashir din Wanda Shima Bai rintsaba ko kadan shi da yaransa kwana sukai Aiki da bincike tareda zuwa gidan DD na highbridge suka duba fingerprints na Safnah dake gidan wanda yazo daidai da Wanda yaje jikin ledan da DD yakai musu hakama same fingerprints ne dake jikin motan da Bena tayi accident da ita kwanakin baya da ake bincike Akai itama a boye da dd babab ya saka.

Shiru Abbakar yayi bayan kashe wayar Sir Ashir bello din Yana Rasa ta yanda zai isar da bayanin da Neman da Sir Ashir din ke musu.

Dukkaninsu musamman DD da idanuwansa sukafi na iyayen nasa kaifin kwarjini suka zuba masa suna jiran Abinda zai fada shikuwa so yeke iya dd babba zai isarwa sakon.

DD da ransa ya Baci ya hade fuska dakyau tareda kallan Abbakar cikin kamewa da Bata Rai yace

“Banajin akwai sauran Abinda ake boyewa Wanda bansaniba,idanma akwai zan sani ayau din,.ka fada me Sir Ashir bello din yace,Ina sauraronka.”

Shiru Abbakar yayi kafin ya Kalli dd babba Wanda Shima yanzu sakon kawai yake buqatan sani shikuwa dad kaante kallan mamaki duka yake musu sbd baisan binciken me duk suke jiran sakamakonsa har haka cikin daga hankali ba.

Numfashi Abbakar ya sake Yana San kasa kallan DD yace

“Sir Ashir Yana buqatan ganinka acan sbd kace baka buqatan zuwansa Nan koyaushe kawo report sbd kada a ankarar da yan jarida Amma yace Yana buqatan zuwanka sbd sakamakonsa komai ya fita na qwayoyin da aka shayar da DD da Wanda aka shayar da kakarsu Bena harma da sakamakon binciken accident din Bena…..

Wani irin Kallo DD yayiwa dd babba cikin matsanancin mamaki da zuciyarsa dake daukan Wani nauyi da harbawa ba daidaiba sbd Bai taba sanin accident din Bena bana Allah bane akwai zargin da akeyi akan Hakan shine aka boye masa akwai Wanda ke bibiyab matarsa da Wani sharri,

Meyasa zaa boye masa dan kuwa da tini zai fara Bata kariyar da ko Kansa bai sametaba.

Shi Kansa dad kaante mamakin ya shiga sosai Yafara rarraba idanuwa cikin firgicin meyake faruwa da familyn nasu wai.

Dd babba kuwa Kai tsaye Bai iya cewa kowa komaiba ya wuce gaba Abbakar na bayansa ya je ya dauko key din motarsa da sauri.

Shima DD Kai tsaye Naseer ya kira Wanda Shima ranar a cikin Kaantes ya kwana take ya fito cikin qananun guntayen kaya Shima ya tada motar DD din Suma suka rufawa dd babba baya

Dad kaante na kasa tsayawa yayi Dan andena barinsa Baya tinda Shima babba ne a familyn ya dauko key da Kansa Bai tsaya Kiran driver dinsa ba yaja ya mara musu baya.

dd babba ne yafara Isa yau Yana fatan komai yazo karshe sbd zarginsa da hankalinsa Daya kasa kwanciya akan matar DD Dan haka baya cewa komai har suka Isa

Suma DD a cikin motarsa babu me iya magana sai nauyi da tafasan da zuciyarsa keyi akan Abinda zasu tarar na duk Wanda yakeda saka hannu akan accident din Bena,

Bai damu da Wanda ya shayar dashi mugayen drugs dinba shi ayanzu wanda yake son hallaka matarsa yake son Gani.

Suna isowa Kai tsaye suka fito daga shi har Naseer tare suka nufi ciki daidai lokacin da Sir Ashir da idanuwansa sukai Wani luhu luhu sbd rashin bacci da aiki tuquri na azaba dasukai acikin daren.

Miqawa dd babba report din yayi Wanda Kai tsaye DD ne ya fara saka hannu ya karba Dan ganin suna Neman Bata lokaci gurin bayani da boye boye.

Yana budewa yafara bin rubutun ahankali da reports din Yana karantawa.

Shiru yayi tsawon seconds Yana kokarin Dora zancen cikin Kansa a daidai.

Kallan Sir Ashir bello yayi fuskarsa a matiqar hade da yanayin wulaqanta yace

“Waye Safnah din?

Daga Sir Ashir har dd babba da Naseer kallansa suka dago sukai cikeda sanyin jiki da mamaki,

Naseer ya kalla ganin alaman duk sun Santa da idanuwansa ya kafe Naseer Yana jiran amsa

Naseer ya Dan matso gefensa kadan cikin sanyin murya yace

“Second wife Dinka,’yar uncle Dinka Alh basheer bulama, Safnah basheer bulama”

Cikin Wani irin mummunan yanayi yace “kana nufin SSB??

Shiru Naseer yayi sbd bazai iya Basa wannan amsan kai tsayeba Dan kada suyi breaking zuciyarsa bayan tsananin baqin cikin da zai samu Kansa a ciki na Jin matarsa ce tayi wainnan ayyukan.

Kallansu yayi Daya bayan daya kafin ya tsaida kallansa kan dd babba Yana cewa

“Meye ne??

Kunyi shiru ne Kuna tausayin waye ne?

Kuna kunya ko baqin cikin ace matatace tayi wannan aikin??

Like seriously??

Kallan Naseer yayi Kai tsaye yayi wurgi da takardun Yana juyawa yace

“Kira manyan hukumar yan drugs dake Lagos wainda case din nawa yake hannunsu wainda zasu miqata hukumar Zurich dake Neman inda qwayoyin suka fito sune zasu San abinyi da ita Amma kafin Nan muje naji meye hadin wancan mutumin da ita dataje gidansa ta bawa mahaifiyarsa qwayoyin hakama meyasa mahaifiyar tasa babu Abinda take kira sai sunansu su Biyun dole akwai Wani abin da basu saniba hakama idan Safnah ce ta batar da Bena da saka hannunsa tinda yayi niyar guduwa.

Kansa Wani tiriri yakeyi Yana daukan zafin gaske sbd yanzu ne ya tabbatarda Bena na cikin hadarin gaske Jin abubuwan dake faruwa.

Suna ficewa dd babba ya Kalli Sir Ashir ya sauke numfashi cikin nutsuwa yace

“Yanzu da akeda shedu da tabbacin itace zayi wannan ayyukan zaku iya kamota a shigar da case din hannun manyan hukuman yan drugs a fara tambaya da bincikenta yanda ya kamata ta hanyar da kuka Saba ji da irinsu.

Angama” sir Ashir ya fada sbd Daman Jira suke sosai dasu samu ta shiga hannunsu Dan kuwa wainnan qwayoyin ba qaramin zancen bane a gurinsu Dan yanzu akan Hakan shi wata hanyar samun Qarin girmansa tazo musamman manyan hukuman yan drugs da zata shigo ciki basuda Imani ba sani ba sabo Dan kuwa da tin farko hannunsu zancen ya shiga da babu Abinda zaa tsaya yiwa boye boye da tini Safnah anrufe bayaninta na Wani ake.

Dd babba na barin office din Shima Sir Ashir ya Bada umarnin a buga takarda a aika Lagos ta email yau a bugo musu stamp a dawo da ita su fitar ta tabbacin zaman samun qwayoyin dasuka Fi Muni a tareda Safnah din.

DD da Kansa yake tuqin motar Wanda ya saka Naseer yin shiru kawai Yana jiran su Isa Shima.

Koda suka Isa highbridge dokarsu da baa taba takawaba yau duka Saida DD ya takasu Wani mahaukacin horn yake musu jiki na rawa aka Bude masa da matsiyacin gudu ya shige Kai tsaye ya nufi gidansa ko parking daidai baiyiba ya tsayar da motar ya fito.

Naseer ne ya fito Shima da sauri ya rufe motar ya biyo bayansa suka qarasa ciki.

Hanyar kitchen suka nufa Kai tsaye tareda nufar store din da sauri Naseer yayi gaba ya Ciro key din inda ya ajiyesa ya Bude kofar tareda turawa ta Bude gabaki Daya.

Ababa dake zaune gabaki Daya karfinsa ya qare kaf babu sauran kuzari a jikinsa ko kadan sbd azabar kwana zaune dayayi Yana kirgan kudin da lisassafinsa gabaki Daya ya kunce,

Idanuwansa gabaki Daya sunyi luhu luhu sun fito sunyi jajir zagayen idanuwansa su Yi baqi sosai sbd azabar rashin rashin rintsasu da yayi ko kadan be rintsasu ba kudine yaketa Daman kirgawa ya kasa hada ko miliyan Ashirin tin dare har safiyar,

Idanuwansa Basu taba haduwa da azaba irin ta yau din ba,

Fankokin sunqi mutuwa sai daga kudin sukeyi koya hada ya aje,

Yayi yayi ya kasa kashesu,

Ya kasa hakura sbd taurin zuciya da naci da kwadayi da Neman mafitan dayakeyi.

Babu iskan ventilation a dakin Wanda ya sake azabar dashi da numfashinsa sbd tsananin qamshin kudin Daya cika dakin babu inda window yake yasaka ko iskan fankar bayaji zufan jikinsa kusan ya qare Dan kuwa tin Daren yake tsiyayan zufa me yawa har safiya,

Ruwan jikinsu sun qare daqyar yake iya daga hannunsa Yana cigaba da taba kudin Amma lissafin tini ya kunce masa babu Abinda yake so kawai a budesa ya fita iskan Allah ya dakesa ko baa basa ko sisi ba abarsa ya tafi sbd qamshin kudin kashesa zaiyi ya masa yawa aciki ya zamar masa cuta.

Kallansa sukai a wulaqance suna kallan idanuwansa da basa Gani sosai sbd kumburi da Jan dasukai,

Shi Kansa dagowa yayi ya kallesu dishi dishi yake ganinsu ko magana baiya iya Yi sbd azaban nauyin da Kansa yayi da azabar ciwo.

DD ne ya matso gabansa ya tsaya sai dayayi shiru ya hadiye tafasa da zafin da zuciyarsa keyi ya Bude baki Kai tsaye ya jefa masa tambayar waye ya Akai yasan Safnah bulama hartaje gidansa ta durawa mahaifiyarsa qwayoyi.

A yanda yake cikin matsananciyar azaba da wahala Yana Jin tambayar ya dago ya sake Bude idanuwansa dasukai masa zanen na Panda ya Kalli DD dakyar ya Bude baki yace

“Safnah ce ta Kori Bena da Annensu,

Safnah ce ta biya kudin gaske me yawa suka bawa hande bana Nan hande ta Basu Anne da Annen sukai amfani suka Kori Bena ta tafi sun shiga duniya.”

Naseer ne ya shigo dakin tareda cakumo Ababan ya fito dashi daga dakin ya jehosa harabar gidan inda zai samu iska ya Dan dawo daidai yayi bayani da kyau.

Sake maimaita Abinda ya fada yayi DD ya Kalli Naseer yace sakashi booth muje inda zeyi magana.

Ababa na Jin Hakan ya zare idanuwansa na Panda Yana cewa

“Safnah ce da haj Nuratu sukai komai yanada duka shedu da komai da zai bayar”

Naseer be sauraresa ba ya shaqosa wannan Karan idonsa biyu ya Bude Booth ya Jefasa ciki Ababa na Neman siqewa suka rufe Booth din suka shiga motar.

Kai tsaye office din Sir Ashir Suka nufa suna Isa aka Bude both Wani marar Imani cikin yaran Sir Ashir bello din ya saka hannu Daya ya Ciro Ababan Wanda tini yafara Neman somewa a Booth din sbd azabar zafi da rashin numfashi.

90

Idanuwan Ababa Basu gama budewa ba aka jefasa cikin Wani daki me masifaffen duhu da baka ganin komai se dai Kaji murya.

Zare idanuwansa ya fara Yana Neman ganin inda zaiga Dan haske komai qanqantarsa Amma babu cikin murya Mai tsananin bacin ran gaske DD ya sake jefa masa tambayar ya Akai yasan Safnah??

Rawar baki ya fara zaiyi magana yaji saukan Wani masifaffen Marin bayan hannun qato daya sakasa kifewa qasa kunnuwansa na dauke ji diff.

Rarrafawa ya fara Yana Neman inda zai dafa ya tashi aka sake jeho masa wata tambayar wadda kunnuwansa dasuke dauke ji Basu ji ba Dan haka ba amsa take aka sake kifa masa Wani Marin Daya dawo da jinsa take cikin gigicewa da murya me qarfin gaske yace

“yata ce nine na haifeta…

Shiru gurin ya dauka dukkaninsu shiru sukai musamman DD Daya kasa fahimtan me zancen ke nufi,

Shi Kansa dd babba dake kan waya Yana Jin komai sbd yace Sir Ashir bello ya barsa Yana buqatan Jin komai.

Shaqosa officer din yayi cikin qarfi da rashin Imani yace

“Wacece yar taka??

Safnah bulama ake magana.

Shaqar data kusan raba Ababan da numfashinsa yasanyi shi kusan sakin fitsari Yana bubbuga hannun dake wuyansa sai Daya kusa mutuwa officer din ya sakesa lokacin Naseer ya shigo dakin sanyeda glasses din dake saka suna Gani cikin hudun ya kama Ababa ya daga sama tareda mannasa da bango a karon karshe ya sake tambayar gaskiyar Safnah da inda Bena take.

Yana Jin muryansa Naseer ya Bude bakinsa da muryarsa ta shaqe sbd wuyansa Dasha shaqa be dawo daidai ba yace

“Nine na haifi Safnah basheer bulama,

Safnah da Benazir uwarsa Daya ubansu Daya wllahi,

Nine na haifesu duka Kuma Annen Benazir ce ta haifesu duka,

Su hudu ne, Sumayyah,sameerah, Bena da Safnah”

Kallan DD sukai dukkaninsu sbd zuwa lokacin kan kowa ya sake daurewa,

Ababa yace shine ya haifi Safnah,to Kuma Safnah a matsayin ‘yar basheer bulama aka Santa.

dd babba ne yayi shiru cikin zurfafa tinanin tabbas Anne ta sanar dashi yayanta hudu, Sumayyah, sameerah, Bena da Safnah.,

Safnah itace wadda ta gudu tabar gida,

Safnah itace yar Anne Ababa yake nufi kenan?

Safnah da Bena suna auren miji Daya kenan ko me??

Dukan wahala Naseer dake cikeda takaicinsa sukaiwa Ababa shida officer din Amma still Abu Daya yake fada cewan shine ya asalin uban Safnah ba bulama ba.

Ganin taurin ransa yayi yawa ya saka su Basa Daman kawo shedan dayace zai kawo akan Hakan.

Ta bangare Daya kuwa takardarsu suketa Jira cikin matsuwa ta dawo ta email dinsu sbd su kame Safnah wadda sunancan Suma cikin matsananciyar tashin hankalin rashin ganin Ababa da inda yake ga labarin gidansa Daya Kone kurmus ya sakasu sake shiga baqin ciki sbd sunso ne a kamasa da wainnan qwayoyin a gidansa.

Da motar office aka tafi da Ababa har shagon wankinsa inda ya boye jakar kayansa da komai Daya dauka na tafiya porthacort.

Ciro kayan yayi aka karba ana kokarin budewa yaga hankalinsu na Kai ya juya da matsanancin gudu zai tsare cikin rashin wasa da lamarin ba Bata lokaci aka harbe qarasa Daya wadda Bata karye dinba take ya zube a gurin Yana zunduma Wani mummunan ihun azabar daya sakasa somewa take jini na zuba sosai a qafar.

Kaman yankakken rago haka aka washesa aka saka mota Akai asibiti dashi.

Ana zuwa Asibiti bayan ana karbesa anyi ciki dashi bullet akwai aka buqaci Asibitin ta cire a nadesa hakanan a dawo musu dashi suka tafi aka barsa da jamian tsaro biyu suyi gadinsa.

A can office bayan an Bude komai na kayan Ababan anan aka samu duka Wani Abinda Daya saka DD kasa tsayuwa Saida Naseer yayi saurin tareda aka kawo masa kujera ya zauna ana qarawa AC din office din qarfi sbd Bai taba Gani ko Jin tashin hankali ba a ruyuwarsa irin wannan,

Shine duk acikin irin wannan abubuwan da Bai taba ji ba ko a labarai,bare drama ko film sbd bayama kallansu,

Shine yake auren mata biyu dasuke uwa Daya Uba Daya.

Babban Abinda yake sake saka jikinsa daukan rawa da shiga matsanancin tashin hankali shine da mummunan qaddara ta sakasa Wani Abu ya shiga tsakaninsa da Safnah kafin Bena da Bena ana nufin ta haramta garesa kenan har abada???

Zai rabu da ita kenan bashi ba ita har abada??

Shikenan zata rabu dashi taje ta auri Wani namijin???…….Bai qarasa wannan mummunan tinanin ba zuciyarsa ta kasa dauka take numfashinsa ya fara daukewa Kansa na Neman tarwatsewa..

Da sauri akayo Kansa Amma kafin kowane motsi tini ya fice hayyacinsa sbd balain yayi masa yawa da masifa yake ya rasa numfashinsa dole aka kwashesa zuwa Asibiti.

Naseer ma dole yabarwa Abbakar harkar hukumar shikuma ya koma jinyar ubangidansa.

Kafin takardarsu ta dawo daga office Nan suka kira Alh basheer bulama Kai tsaye suka buqaci ganinsa batareda Yi masa Dan taqaitaccen bayanin Abinda yake faruwa.

Shima acan take jininsa yayi mummunan Hawan da dole saida akai gaggawar Nemo likita ya dubasa sbd Dakar zuciyarsa da abin yayi.

Hankalin iyalin Alh basheer din ba qaramin tashi yayiba da halin Daya shiga Kuma cikin rashin sa’a Koda Akai masa Kiran Yana tareda matarsa Daya da me aikinta tana jera musu abincin a dining Dan haka komai a kunnen me aikin akaisa.

Tana ganin halinda Alh basheer din ya shiga ta silale ta koma dakinsu na masu aiki ta shige toilet ta kunna famfon ruwa ta fidda waya ta Nemo numbern momy datake Aiki gidan sbd ita Dan kawai sbd ita,

Tin jiya momyn ke kirana akan idan taga zuwan baqo gidan kowane iri ne gurin Alh basheer bulama ta sanar make dan ta tanadi wainda zasu kawar mata da Ababan Yana Isa batareda ya isar da Abinda yaje fada ba.

Ganin babu baqon dayazo sai Kuma ga wannan mugun sakon wayar ya saka shahida me aikin Kiran momy cikin bayani a natse Dalla dalla tayiwa momy bayanin Kiran da Kuma Abinda akace ankama ‘yarsa ta bogi Safnah bulama dashi wato wasu qwayoyin.

Shiru momy tayi wadda sukafi kwanaki nawa Basu rintsaba sbd tashin hankali da baqin ciki me tsananin gaske tareda rashin sanin madafa.

Kashe wayar shahida momy tayi tana miqewa daga zaunen datake bakin gado shiru tafara kaida kawo hannuwanta na tsananin rawa kaman yanda zuciyarta ke harbawa da matsanancin tashin hankalin da baa saka masa raba ba.

Idan yanda Shahida ta fada ne ance Safnah bulama kawai ne ita baa ambaci sunanta ba Hakan na nufin baa San da itaba aciki ne kokum lissafin be zo kanta bane…

Ta faru ta qare musu kenan,

Yau rana ta batar musu.

Wace qaddararriyar masifar ce ta kaisu Sako Ababa a rayuwarsu suna komai a tsanake hankali kwance yanzu komai ya lalace,

Jinin Rai na kisan mutum nawa ne a hannunsu?

Ita na hajiya Dana Rabi ne a hannunta saina Wanda ta taba yi a bayan aurenta da bulama ya mutu.,

Safnah kuwa jinin ran Wanda tafara kashewa na farko shine Wanda bayan barinta gida ya kamata yaso yimata fyade ta kashesa har lahira Wanda akan Hakan momyn ta hadu da ita ta taimaka mata suka boye gawar daganan suka zama uwa da ‘ya,

Sai Kuma jinin Hande da itace ta kasheta tinda itace ta dura mata qwayoyin a baki.

Idan har baa ambaci sunanta ba to tabbas nata asirin da sauransa Dan haka bazata sanar da Safnah ba silalewa zatayi ta gudu kafin Azo kamasu tabar Safnah a sameta ita Daya.

Sauran qwayoyin karshe dasuka rage musu ta dauko jikinta na tsananin rawa zata Bude ta zubasu a bakinta tashanye itama ta shiga mummunan halinda zaa dauka Safnah durata mata itama tayi Dan ta kasheta idan yaso kafin ta warke dai lokaci yaja case din ya mutu ita ta tsira.

Harta zuba a bakinta taji Bazata iyaba tayi saurin fito dashi tana gobe bakinta ta mayar dashi leda ta jefar tsakiyar dakin tana shiga Sabon tashin hankalin Neman mafita Dan haka gwara dai ta gudu inda zata tsira da rayuwarta.

Gurin drawer na aje kudinsu ta nufa ta Bude jikinta na wata irin rawa tahau diban kudi ta cika qatuwar handbag dinta babba ta dauki passport dinta ta saka tareda sauran id cards nata.

Tana fitowa Safnah dake dakin itama nata idanuwan kaman na Panda duk sun fito sunyi baki sbd tashin hankali da rashin rintsawa ta fito sukai Karo a palon.

Kallan juna sukai ta kalli momyn a tsanake itama momyn ita ta kalla tana boye tashin hankalinta ta kalleta tana  Dan bayyanarda kulawa tace

“Bari naje na dawo yanzun Nan nayi Miki bayanin Wani abin mamakin kiji.”

Gaba tayi tana Hana yanayinta bayyana.

Harta fice Safnah batace mata komaiba sai jakar hannunta data hango kudi masu tarin yawa aciki musamman daloli.

Mamaki ne ya kamata Dan haka ta Bude dakin momyn ta shiga ta nufi inda suke ajiye kudi taga babu komai se yan canja,

Passport din momyn ta duba Bata gansa ba nata kawai ta Gani Dan haka ta sake shiga matsanancin mamaki da tashin hankali.

Juyawa tayi zata fice ta hango ledan robar qwayoyin dasukai amfani dasu tsakiyar dakin take ta fahimci akwai babban Abinda yake faruwa.

Fitowa tayi da sauri daga Palo ta nufi harabar gidan har momyn ta kusa ficewa da kota ta tsayar da ita ta qarasa gurinta tayi qasa da glass Safnah tace

“Momy nesa ne zakije??

Cikin girgiza Kai tace “aa yanzu fa zan dawo,Dana dawo zakiji komai fa.”

Jan motar tayi ta wuce Safnah ta bita da Kallo tana goge hannunta daga ledan qwayoyin data sakawa momyn bayan motarta batareda ta saniba.

Momyn na ficewa itama motarta ta dauka ta fito da sauri tabi bayan momyn.

Sun ficewa motacin jamiaan tsaro gudu uku suka iso gidan maigadi ne ya nuna musu motocin su Safnah dasuka fice yanzu Dan haka take suka bi bayansu Suma.

Hanyar barin gari momyn ta kaman tana kallan madubinta ta lura da motar Safnah dake binta Abaya.

Wani mummunan faduwan gaba da zufa ne ya keto mata sbd Safnah taci gaba da binta akwai babbar matsala zaa iya kamasu duka tare Dan haka suna sake ficewa daga mutane ta tsayar da motarta tana kallan motan Safnah datai parking bayanta.

Fitowa mota Safnah tayi cikin tsananin baqin ciki da takaici tareda tafasan zuciya sbd har lokacin ta kasa Gane me momyn ke Shirin aikatawa.

Tana tahowa momy sai dataga ta fito motar ta nufota kafin tayi gaba kadan da motarta tayo reverse cikin Wani mummunan gudu ta taka Safnah din da motarta Bata tsayaba ta buga da mugun speed tayi gaba tana Hawa titi sosai da gudu.

Cikin mummunan yanayi na karywar qafarta Daya da fita fit a take jamian tsaron suka iso kan Safnah wadda ke cikin halin Rai ko mutuwa Dan hatta fuskar kusan tayi dameji suka kwasheta sauran motacin kuwa suka bi bayan momy.

Asibitin da aka Kai Ababa Wanda tini Shima gurin cire bullet an qarasa lalata qafar acan aka kaita itama da qafarta Daya Bata hayyacinta sbd fuskarta datai damage.

Momy gudu takeyi sosai tana qarawa hankalinta na tashi tana waya da qaninta dazai Siya mata ticket a Daren ta wuce Lagos daganan zata Bema visa tabar qasar gaba Daya.

Checking point na sojoji ne suka tsayar da ita ganin yanda take gudu sosai tana mace.

Jakar kudin dake qarqashin qafafunta suka fara gani take suka buqaci tayi parking.

Parking tayi tana Dan kame kame tana murmushin karfin hali kafin tafara magana saiga ledan qwayoyin abayan motarta.

Koda jamian dasuka biyo motarta suka iso gabaki Daya kamanninta sun sauya daga hannun sojojin Dan haka take case dinta ya girmama aka fara daukanta hotina mutane ana korarsu sbd harda bindiga a Jakarta.

Kamata Akai babu tausayin halinda take ciki da mummunan dukan datasha da kan bindiga a hannun sojojin aka saka mota ko tafiya Basu fara ba itama ta sume kaman matacciya hancinta da bakinta suna jini hakama idonta Daya ya tsiyaye.

Same Asibitin itama aka kaita inda su Ababa da Safnah suke babu Wanda yasan inda Kansa yake haka itama aka Bata gadon batasan inda kanta yakeba jininta na tsiyayewa.

saisun farka su samu Daman karban hukuncinsu.

91

Familyn Kaantes sai alokacin da sukaji Safnah da momy na hannu Daman shi Ababa tini yana hannun hankalinsu ya Dan kwanta suka dawo da sabuwar damuwarsu akan ta inda zaa fara Neman Bena da Anne yanzu.

Ta bangaren Umme kuwa da alh Bulama rasuwar hajiya sabuwa ta dawo musu sbd ganin yanda su Safnah suka kasheta cikin rashin Imani da tausayi.

Kowa ya shiga jimami tashin hankalin Jin wannan masifar,

Umme tayi Kuka fiyeda lokacinda suka rasa hajiyar,

Alh Bulama kuwa bayan ciwo da baqin cikin rayuwar dasuka samu kansu aciki harda baqin ciki da radadin rasa ‘ya dayayi sbd Safnah tashiga cikin tsakiyan zuciyansa fiyeda yanda ake tinani ashe ita din ba tsatsonsa bace.

Umme itace ta ringa tausan Dan uwanta tana Jin radadin sa na rashin ‘ya ko ‘dan Kansa.

Matansa kuwa murna da Jin dadi suka hau Yi sbd har ga Allah sun azabtu da Safnah sbd itace take jiya rayuwar Alh Bulama din da matansa yanda takeso haka akeyi babu wanda ya Hana.

DD kwana daya da wuni Daya yayi a Asibiti kafin ya Dan warware ya dawo gida lokacin labarin rasuwar hande yazo musu babu Wanda yaji komai akan Hakan saidai suka bita da Allah yaji qanta tinda musulma ce Kuma mutuwa na kan kowa hakama kowa Yana fatan idan ya rasu ya sadu da malaikun rahama.

Bayan dawowarsa daga Asibiti Kai tsaye kaantes ya koma sbd highbridge din ana gyara na sauya komai na gidan Daya buqata.

Zuwa wannan lokacin Amnah ta fahimci mummy dinta batanan baa San inda take ba Dan haka ta kwanta rashin lafiya sbd rigima da kukan data ringa yi musu ba kakkautawa.

Shi Kansa Daddyn nata Dake Neman yin kukan Sam qin yadda tayi da rarrashinsa Dan haka Shima kusan Neman komawa kwance jinyar yakeyi sbd Yana gab da rikicewa gaba Daya Shima idan ba gano inda matarsa take akai ba.

Cikin tashin hankalin Rigima da ciwon Amnah sukai kwana biyu Shima a lallabawa kawai yakeyi sbd baida lafiyan,

Bincike kuwa tini aka bazama babu kama hannun yaro dukiya me yawa ake zubarwa Dan tsananta binciken Amma shiru.

*******Nafisat dake kwance tareda Amnah tana shafa kanta datai bacci jikinta da zafi sosai sbd rigima data gama kafin baccin.

Wayarta ce tayi haske alaman shigowan kira Dan haka ta Zame Daga jikinta ahankali tareda nufar toilet ta shige ta kunna ruwa ta dauki wayar cikin nutsuwa da sanyi tace

“Hello Ina wuni Yaya sulaiman?”

“Lfy kalau alhmdllh,kina jina ko Nafisat?,Yaya Amnah?ya jikinta?”

Numfashi Nafisat ta sauke ahankali tareda Dan zaunawa gefen bathtub tana cewa

“Lafiya kalau,Amma ta kasa yarda da rashin Anty Bena ko yanzu rashin lafiya ce sosai a jikinta.

Shiru sulaiman yayi kafin ya Dan gyara zamansa cikin napep din da yanzu Janta kawai yakeyi sbd batar da tinanin mutane da kamanni yace

“Inshallah ta kusa kasancewa tareda mahaifiyarta Amma dai yanzu Mummyn tata batada lafiya duk lokacin Nan fama akeyi da ita Dan haka yanzu Abinda mukeso dake passport dinta da id cards dinta duka Zaki tattara guri Daya ki samu yanda zakiyi ki fitomin dasu anjima idan anshiga sallan ishai masallacin kaantes.

Shiru Nafisat tayi tareda Dan Nazari duk da Bata taba musawa duk Abinda yace kaman yanda Shima Bai taba musawa Bilal Abinda yace ba Dan haka tace

“Zanyi kokarin yin Hakan anjima Amma Dan Allah Yaya sulaiman kada ku bari Amnah ta Dade a Hakan babu mamanta wlh zata iya kamuwa da Wani ciwon,yarinyar nada qawa zucin mamanta sosai,

Dan shiru tayi na sakanni kafin ta qara da cewa

“Shima daddynta Yana cikin mummunan halin”

Gyada Kai sulaiman yayi Yana cewa ” wanna duk sai yanda Sir Bilal yafada zaayi”

Sallama sukai ya kashe wayar itama ta kashe tana kashe ruwan tareda fitowa daga toilet din.

Tana fitowa ganin DD a dakin ya sakata rudewa sbd Bata taba tsammanin shigowarsa ba Dan haka tai saurin qasa da Kai tana gaidasa a girmame.

Kaman bazai kalletaba qafafunta kawai idanuwansa suka kalla zai nufi ‘yarsa dake kwance kan kujeran dakin Bena din zai dauka sai yaga babu alaman ruwa ko kadan a qafafunta bayan daga toilet ta fito.

Mayun idanuwansa da duk suka fada a kwanakin na rashin matarsa ya dago ya zuba mata Yana kallan hannuwanta Suma ya gansu a bushe tsaf babu ruwa ba alamansu bayan yaji qarar ruwa shigowarsa a toilet din.

Fuskarta ya kalla itama ruwa sai ya Dan Kalli wayar hannunta take ya tabbatarda waya tayi ta sirri idan har babu ruwa hannuwanta da qafafunta da fuskarta Kuma ta kunna ruwa to Hakan na nufin tabbas waya tayi.

Bai furta komaiba ko gaisuwanta be amsa ba ya dauki Amnah din ya fice daga dakin.

Kai tsaye dakin Zeenah ya kaita Dan fasa tafiya yayi da ita ya fita Yana fidda wayarsa ya kira Naseer sbd shi yanzu kowa baya yarda dashi akan duk Abinda ya shafi Bena da ‘yarsa Dan haka take yace Naseer ya saka qaqqarfan bincike akan me aikin Bena Kuma Nanny din Amnah.

Naseer na Jin Hakan yafara kokarin bincikar masu aikin gidan ma gabaki Daya.

DD gaba Daya yanzu ko mutane bayason shiga bayason suna nemansa Kuma,

Kadaice Kansa yakeyi sbd baya buqatan kowa atareda shi matiqan ba matarsa ce ya dawo qarqashinsa ba.

Ranar ma haka ya wuni cikin tsananin zafin jiki da ciwon Kai Dana kirji me tsananin gaske Wanda ya saka hankalin dd babba ma nasa hankalin b kwance yakeba da batan Benan,

Wainda dake asibiti kaf acikinsu babu me sauran amfanin da zai iya magana bare yasani ko ma ya fada inda Bena ta tafi.

Safnah ma dai har tsawon kwanakin Bata farfado ba sbd ba qaramar buguwa kanta yayi ba.

Ababa duka qafafunsa biyu babu me Aiki dayan bullet ya lalata dayar itace ta karye tin gidan DD babban baqin rayuwarsa da quncin Daya dabaibaiye rayuwarsa shine yau ko qafafun da zai iya daga Kansa tsaye baida,

Hande ta mutu ta bar duniya,

Ga hukuma na jiran su warke ayi gidan yari dasu ita momy ma da Safnah akwai yiyuwar ratayesu zaayi da ransu suna ji suna Gani su mutu Subar duniyar,shi kalan nasa hukuncin kuwa Kila life in prison ne sbd dumu dumu ansaka sunansa cikin tare suka maumalan qwayoyin da aka kama momy dasu Dan haka shi tasa mummunan qaddarar ta qarew yari ce har mutuwa da qafafu biyu babu ko Daya.

Daya Tina Hakan Wani irin Kuka yake fasawa wanda ke saka jikinsa daukan rawa Yana Rasa ta yanda wannan mummunan kaddarar ta samesa,Jin yake dama shine ya mutu ba hande ba ya huta da wannan biyu babun.

*********Koda Akai sallan magrib Saida likita yazo ya duba DD sbd jikinsa dake tsanani,

Bayan tafiyan likita daqyar Anne ta sakasa yaci abinci yasha magani.

Hakanan ya daure ya fita sallan magrib masallaci daga can Bai jiraba kaman yanda dd babba keyi wasu lokutan na tsayawa jiran sai anyi ishai ya baro masallacin gaba Daya.

Bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye ya tube tareda sakarwa Kansa ruwan sanyi sbd ciwon Kansa ya rage ya samu Jin sassauci.

Ya jima Yana cikin ruwan kafin ya gama ya fito daure da towel fatar jikinsa tana Wani irin kyallin daukan Ido sbd duk yanda yake cikin tsananin damuwa da quncin zuciya fatarsa da kyansa suna Nan saima daukan Ido Dayake qarawa sbd rashin fita.

Yau jallabiya ya saka da hula ya Kalli time yaga lokacin sallan ishai yayi har na fara ya fito a natse cikin kamewa Yana nufar hanyar fita.

Yana kawowa sashen ummensa da a hango fitar Nafisat daga sashen tana nufar gate zata fice.

Kallawa yayi a natse ya Gane ita din ce Dan haka wayarsa ya fitar Kai tsaye ya kira Naseer yace yabi Nafisat gatanan ta fita Kaantes.

Naseer alwala yayo zashi masallacin Amma ya juya ya nufi hanyar babban gate na fita Kaantes

Yana fita ya hanga har tayi Dan nisa Dan haka bicycle din securities na gidan da ake zagayen gidan da ita da daddare sbd tsaro ya janyo ya hau yabi bayanta Yana kafe idanuwansa akan inda tabi.

Dap da zai cimmata can nesa da kaantes ta baya yaga napep tazo gabanta ta tsaya sukai kaman sunyi magana inda ze kaita cinikin beyiba ta jefa masa jakar dake hannunta a bayan napep din yaja y wuce ita Kuma sai datai tsayuwar mintina kusan biyar kafin ta juya ta dawo gida.

Naseer bayan napep din ya ringa bi da Keke Yana hanasa Gane ana binsa.

Dagowan tafiya sukai har sulaiman ya Isa gidansa yayi parking din napep dinsa ya fito ya shiga baya ya Ciro jakar da Nafisat ta jefa masa tambayar ta passport din Bena ya shige gida dasu.

Naseer da ba qaraman gajiya yayi ba da tuqin keken tini ya hada uban zufa guri ya nema a nesa da gidan ya ajiye kekan ya fara sauke numfashi tsawon lokaci kafin ya dawo daidai ya fidda wayarsa tukuna ya turawa DD sakon inda yake kawai.

Yana gama tura masa sakon ya saka wayar aljihunsa ya nufi masallacin anguwar ya sake alwala yashiga sallan da beyiba.

Kaman Wanda yayi gudun fitar Rai Yana sallame sallah DD ya iso gurin Dan haka Shima motan ya shiga suka zauna suna gadin gidan sbd koma menene Nafisat ta bawa me napep din dole akwai inda ze Kaisa sbd nan gidan Daya shiga matarsa da ‘yayansa biyu ne a ciki a yanda Naseer ya tambaya cikin masallacin.

Kaman ma barayi haka Suka dasa zaman Jira a motar ga zazzabi sosai a jikin DD Dan haka dole Naseer ya mayardashi gida ya dawo shi ya dasa zaman Jira.

Har asuba Yana gurin a gabansa sulaiman ya fito sallan Asuba Shima ya fito suka shiga masallaci a tare sukai sallah da zasu fito ne sulaiman ya fidda wayarsa yakira Wani yaronsa Dayake napep yace yazo ya karbi napep dinsa yakaisa Tasha zaiyi tafiya zuwa Abuja yau.

Naseer na Jin Hakan ya dakata cikin masallacin Saida sulaiman ya shige gidansa.

Kallan man Dayake cikin motarsa yayi yaga tabbas ze Kaisa Abuja Dan haka wayarsa kawai ya dauka ya turawa DD sakon zaibi Naseer din Abuja tukana yaga wane abune Nafisat ta Basa kuma waye zaa Kaiwa.

*****Qarfe 7 sulaiman ya fito daga gidansa rataye da jakar matafiya tareda matarsa data biyosa har waje tayi masa Allah ya tsare hanya ta koma Shima ya shiga napep saurayin Daya kira yazo suka shiga napep din ya jasa zuwa Tasha.

Sai dasukai Nisa sosai Naseer ya tada motarsa yabi bayansu har cikin Tasha Yana kallo ba jimawa motan da sulaiman ya shiga ta cika ta tashi ta fito zuwa Abuja.

Naseer Kansa ya manta yaushe rabonsa da tuqin doguwar tafiya sbd jirgin dasuke Hawa sai yau din.

Sosai yake tattare da gajiya sbd ga kwanan mota ga tukin keken da yayi hakama ga doguwar tafiyar

Dan haka Koda suka Isa Abuja yamma tayi hakama ya matiqar gaskiya sosai Shima kaman zazzabin yake ji Amma haka yayi karfin halin bin motar har ta sauka passengers duka firfito harda sulaiman ya dauki drop ya kama hanyar gidan Bilal.

Saida Naseer yaga har gidan da sulaiman yayi ringing kofa ba jimawa aka Bude Wanda ya Gani je ya sakasa kusan somewa a motan Daman ga yanayin Dayake Dan haka da qyar ya Ciro wayarsa ko Gani bayayi sosai ya turawa DD address da house number na gida tareda saka sunan Bilal kawai karshe.

DD da tinda ya samu sakon Naseer yake kiransa baya samunsa har yamma tayi Jin yakeyi kaman zai qarasa zaucewa

Yana fitowa sallan magrib sakon Naseer na qarshe ya shigo masa dakatawa yayi cak da inda yake tareda qara Karanta sakon kusan so uku kafin ya juya kawai ya nufi sashensa ya dauko Abinda zai dauka ya fito da Kansa yakai Kansa airport ya Siya ticket cikin dare Saida ya Bata kusan awa biyar zuwa shiga a airport din kafin ya samu jirgin zuwa Abuja.

Duk yanda yaso Bai samuba sai qarfe 7 na safe Shima ya samu iso masaukin Naseer Wanda ya kwana cikin matsanancin halin zazzabi me qarfin gaske Amma ba laifi lokacin ya warware.

Qaramar tsadaddiyar luggage dinsa ya ajiye a dakin Naseer din alwala da sallah kawai yai bugun zuciyansa na qaruwa sbd har lokacin be Gane sakon Naseer ba sosai hakama babu Wanda yasake maganar komai acikinsu Yana idarwa karfe 8 suka fito Kai tsaye da mota Naseer ya nufi gidan.

*******Jikinta yayi Dan sauki sosai akan jinyar datasha ta kwanakin,jinyar jiki data zuciya wadda har yanzu ta kasa cirewa ko kasa tinaninsa a zuciyarta sbd mutuwace kawai tasan zatayi yafita ranta.

Anne da sumayyah harma da Bilal duk Wani kulawa da tattalin dasuke Bata Basu iya cirota daga damuwa da radadin zuciya ba saidai suna iya kokarinsu gurin ganin sun kula da ita din musamman sumayyah data San duk Abinda ya faru Bena ta fada mata Dan haka Suka taru suka boyewa Anne maganar Safnah din Dan gwara abarta akan yarda da Safnah ta Dade da mutuwa kawai akan baqin cikin dazata shiga idan taji Abinda yake faruwa.

Shikuwa Bilal ya yanke shawarar su tattara su dukan su koma Canada ne sbd tashin hankalin rikice rikicen da aketa Yi a Kaantes kafin hankali ya kwanta Bena din ko zata samu sassaucin halin Datake ciki shiyasa ya buqaci passport dinta.

Da safen sumayyah da momyn Abdul ne kawai a palon suna hada dining se Anne data fito da Bena wadda tayi fari fayau ta Dan rame Sosai,

Sanye take da Riga da wandon bacci masu tsantsi da hula qarama akanta Anne ta kamota cikin kulawa riqe da hannunta ta fita da ita Dan ta daure tayi breakfast tareda su sbd tsoron kada yunwa Kuma tai mata illa.

Knocking kofar Akai kafin momyn Abdul taje ta Bude Kai tsaye aka Murda kofan aka Bude Kai tsaye daidai fitowan Bena da Annenta daga bedroom din Dayake na Bena din yanzu.

Akanta idanuwansa suka fara sauka ita kuwa abinda ya Saba sanar mata da wanzuwarsa a guri ya shiga hancinta cikin Wani mummunan sanyin jiki ta juya ta Kalli kofan idanuwanta suka sauka kansa.

Shikam tsaban Abinda zuciyarsa ta kasa riqewa bare yarda dashi ya Tako cikin rufewan idanuwa batareda damuwa da duk Wanda yake gurinba Kai tsaye yana isowa ya kamota ya hade fuskarsa da tata cikin tsananin budewa da fallasa zuciyarsa ya hade bakinsa na nata hawayen Daya kasa riqewa kaman Wani baby suka fara gangaro matsa.

Daga Anne har su sumayyah da Momyn Abdul din dake palon mummunan tsoro ne ya kamasu ganin Abinda Basu taba ganiba.

92

********

Yanda yayi mata kyakyawan rungumar da yanda ya hade fuskansu da yanda yake kissing nata hawayensa na gangarowa daga cikin kyawawan idanuwansa tini ta kasa hanata Kansa ko kwacewa daga garesa sbd ita kanta ganinsa ya zo mata ne kaman a mafarkin da Bata taba kawowa a kusa ba,

Ta Riga ta cire Rai daga ganinsa har abada sbd tinanin ya haramta gareta,

Ganinsa da jinsa a jikinta yanzu ya tabbatarwa da zuciyarta bazata taba iya rayuwa babusa ba a ynzu shi din wani tsoka ce a kirjinta da bazata taba iya fitaba.

Ita kanta hawayen ne masu sanyi suka gangaro mata idanuwanta na rufewa ahankali hakama jikinta na sakewa gaba Daya a jikinsa sbd kasa yarda da ganinsa ya taho gareta.

Sake rungumeta jikinsa yayi dakyau Yana qanqameta tareda zare bakinsa daga nata Yana sake qanqameta dakyau Yana jero ajiyoyin zuciya hawayensa na kasa tsayuwa sbd sai alokacin ykejin kaman zai tsaga kirjinsa ya mayar da ita cikinsa gaba Daya ya boye ya Hana kowa da komai ko taba ta bare a sake rabasa da ita.

Shiru palon ya dauka babu Wanda ya iya magana babu Wanda ya iya motsawa Anne dake gefenta tsaya tini ta saki hannun Bena din dayake riqe a hannunta tareda matsawa gefe kadan sbd kaman bema lura da kowa a palon ba bare ita Datake riqe da Bena din,

Sumayyah da momyn Abdul Kallo dai sukai masa tin Sako Kansa palon suka fahimci shine DD qanin Bilal sbd kamarsu datai yawa.

Naseer daga kofar ya tsaya bayan shigewarsu Yana tura kofar palon ya rufe ya tsaya Yana Dan dauke Kansa daga kansu Bena din sbd Daman yasan zaayi Hakan sbd DD shi Sam baisan Yaya akeyi ko control na Kai akan lamarin da duk ya shafi Bena.

Ita kanta Bena din sai da suka jima a Hakan tsaye kafin ta Tina da akwai mutane palon ta Dan bude idanuwanta da sukai jajir tana zamewa daga jikinsa ta dago ta kallesa gabaki Daya idanuwansa dasukai laushin rashinta ya zuba mata tareda sake Kai bakinsa yayi kissing idanuwanta ahankali kafin ya dawo yayi kissing hancinta da kumatunta duk a hankali daga qarshe ya sake mayar da ita jikinsa ya rungume Yana Bude baki cikin Wani raunannan sauti yace

“Karki sake barina ko me Wani zai fada Miki,zan baki kariya ke da Annen ki, please karki sake barina,I love you,I love you”

Kasa motsawa tayi sbd kalmominsa dasuka shigeta jikinta ya sake mutuwa ta dago hannuwanta ta zagayesa dasu tareda qanqamesa tana  sake shigewa jikinsa.

Kaman daga sama Bilal ya fito daga hanyar bedroom dinsa sanye cikin jallabiya fara da wayarsa a hannunsa Yana qarasowa cikin palon Abinda ya fara girgiza zuciyarsa shine qamshin da babu Wanda ya sani dashi sai mutum Daya a rayuwarsa shine DD kaante,shine ya fara shiga hancinsa shigowansa palon tareda girgiza masa zuciya a tsanake ya qarasa cikin palon ya tsaya cak daga inda yake Yana zubawa DD idanuwansa da tini suka sauya zuciyarsa na mummunan harbawa da bugawa.

Naseer Daya fara lura da Bilal din Shima kusan wutace ta daukewa jikinsa sbd jiya ya kasa yarda da cewan da gasken Bilal ne ya Gani,

Ya dauka idanuwansa ne,kenan tabbas shine,

Bilal kaante na Raye kenan?

Da sauri cikin tashin hankali ya Maida kallansa kan DD Wanda yasan zai iya samun bugawan zuciya ya sume idan yaga Dan uwansa Bilal a gabansa a Raye Dan haka ya Dan Tako kadan ya matso kusa da DD din Dan Incase kafin ya Dan Bude murya dake rawa ya danyi gyaran muryar daqyar tana yankewa ya Bude baki cikin yayyankewan kalamai ya ambaci sunan D din ya nuna nuna masa bayansa.

Budewa idanuwa DD yayi tareda dagowa batareda ya saki Bena ba hannunta na cikin nasa qanqame ya juya ya Kalli inda Naseer yake nuna masa  idanuwansa suka dauka cikin na Bilal kaante dake tsaye bayansa Yana kallansa cikin firgici da tsananin so da kaunar Dan uwansa me tsananin gaske tareda Kuma tsananin mamaki da tsoron ya Akai yasan Nan din har yazo.

DD kuwa da farko dakatawa yayi dakyau Yana kallan mutumin dayake tsayen a gabansa idan Bilal ne kokuwa shine yake ganin Hakan,

Hannunsa dake riqe Dana Bena sakewa yayi ya rasa kuzarin kama komai bare iya riqewa Nan take,

Lumshe idanuwansa yayi ya sake budesu akan Bilal Wanda hawaye suka cika idanuwansa dakyau sbd yasan yanzu DD zai iya somewa idan ya tabbatarda shine sbd Kansa baya daukan shock masu girma be sababa da tashin hankali.

Motsawan Bilal ahankali tareda yowan taku daya Yana kokarin nufo DD tareda Bude baki zai kira sunan D din take DD ya fahimci tabbas Bilal ne a gabansa,

Daqyar ya iya waiwayowa ya Kalli Naseer dake gefensa Yana kokarin ganin DD din Bai shiga shock da yawa ba,

Gyada masa Kai Naseer yayi da alaman “yes Bilal dinne a gabansa Shima yana ganinsa.

Kasa riqe Kansa DD yayi Kansa yayi Wani irin sarawa qafafuwansa suka sare lokaci Daya Naseer da Bilal dasukasan zaayi Hakan dama suka taresa batareda ya Kai qasa ba

Bilal ne Kai tsaye da kansa ya cirasa da qarfi yayi kan kujera dashi Naseer na gyara masa pillows na doguwar 3 seater Turkish sofa set din aka Kwantar dashi.

Momyn Abdul kuwa na ganin Hakan tayi kitchen da sauri ta dauko ruwa me sanyi ta kawowa Bilal ta miqa masa karba yayi tareda ajiyewa gefe sbd sunyi sanyi ko babu sanyi ana saka masa su yanzu sai ya tashi da shiga Wani ciwon kan kokuma Wani abin Kuma Dan haka Naseer ne ya kalleta yace ruwan dumi zata kawo.

Bena datasan itama Daman zai iya shiga firgicin ya shiga wannan halin hawayen dake idanuwanta ne suka gangaro kan fuskarta ahankali taji qafafunta na qasa daukanta

da sauri sumayyah da Anne dasuke kallan iKon Allah sukai saurin riqota a tare suma sumayyah na rungumeta jikinta Anne Kuma na riqe da hannunta Daya tana Dan shafa bayanta da hannun Daya.

Daki sukai da ita suka zaunar bakin gado Anne ta Kalli sumayyahn tace taje ta kawowa Bena din ruwan dumi na tea itama Tasha da sauri Dan zata iya Amai da wanna firgicin sbd babu komai a cikinta.

Sumayyah kan Bena ta shafa cikeda kulawa kafin ta miqe ta fito daga bedroom din ta nufi dining ta fara kokarin hada mata tea sukuwa su Bilal na kan Dan Umme har lokacin.

Tana gama hadawa Bena din tea ta nufi dakin da sauri itama sbd Suma kokarin taimakawa tasu sukeyi.

Tana Kaiwa Anne ta karba tafara bawa Bena din wadda ta girgiza Kai tana cewa bazata iya saka komai acikintaba batajin buqatan Hakan.

Tilastata Anne tayi tareda sumayyahn suna rarrashin Tasha tea din sai alokacin sumayyah da Anne suka Kalli juna sumayyah ta zauna kan kyakyawan kujeran Dayake dakin ta Kalli Bena cikin kulawa sosai da tausasa murya tace

“Shine DD kaante din???

Anne ma shiru tayi tana jiran amsar da Bena din zata bayar sbd kansu na duhu da ganin wannan Dan madarar mara qarfin jini.

Numfashi ta fara saukewa kafin ta Dan dago ta Kalli Anne da itama ita take Kallo Dayake sun Saba ahaka suka taso basuda Wani abokai ko qawaye bayan Annensu da junansu.

Gyada Kai tayi a kasalance tareda bude baki ta furta “eh shine” ahankali tareda rufe idanuwanta hankalinta baya kanta Yana palo kan Wanda zuciyarta ke tsakanin bugawa a lokacin akansa.

Numfashi Anne da sumayyah suka sake lokaci Daya sai alokacin Anne taji kanta yayi Wani irin qato da sanyin jiki sbd kunyar kasancewarta a Palo lokacinda wannan abin ya faru,

Data sani Tim farko Hakan ze faru da yau bazata fita daga Dakinta ba zata zauna ta kame kanta acikinsa, Daman Bilal ne keta ganin Basu takura ba ko kame Kai sun saki jiki sun Saba dashi sosai yakeso sbd su zama ahali me kusanci da shaquwa da jina sosai.

Sumayyah kuwa shiru tayi sbd itama kunyar abin ne ya rufeta lokacin sbd da farkon lamarin duka shock ya hanasu Gane komai bare tinanin komai sai yanzu ne kunya da takaicin suna gurin ya shigo ke dabaibaiyesu.

Ita kanta Bena Jin yanda sukai tsit kowannensu Kansa a qasa yasata Jin kunyar komai Daya faru sbd harga Allah Bata tsammaci ganinsa ko a mafarkinta ba yanzu,hakama tasani kome zatayi a daidai wannan lokacin ko waye a gurin zai iya aikata Abinda ya aikata batareda yaji komaiba sbd Bai dauka baayin hakan ba a gaban mutanen.

A Palo Naseer ne yayi dubarunsa da ruwan dumi Yana saka qaramin sabon towel da yanzu aka fasashi Dan bazai yiyu a saka masa Wanda ba sabon ba zai iya Basa matsa a skin ya ringa sakawa a cikin ruwan zafin Yana matsewa kadan da sauran ruwan yan goga masa a tafin qafarsa da tafin hannuwansa.

Cikin zafin jikin Daya kamasa take ya Bude idanuwansa ahankali Yana kallan fuskar Bilal dake gabansa Yana shafe masa yan qananun zufan dasuka firfito daga lafiyayyar farar fatar fuskarsa.

Qurawa Bilal din idanuwansa yayi ya kasa ko qyaftawa tsawon lokaci Yana shiga tinani da abubuwa kala kala na yanda rasuwar Bilal din ta kasance da yanda daga baya yake sanin akwai yiyuwar ba gawar Bilal bace Daman aka samu a mota Ashe.

A yanzu Neman hawayensa yayi ya rasa idanuwansa sukai jajir Yana kallan bilal har lokacin ya kasa tashi daga kwancen Dayake Saida Bilal yaga shock da nauyin zuciyan na Neman yiwa DD din yawa ya ajiye tissue din hannunsa tareda Kai hannunsa biyu ya dago DD din zaune ya rungumesa jikinsa atake suka qanqame juna da qarfi kaman mata wannan Karan Bilal ne ya fara hawayen kewan Dan uwansa da yayi fiyeda yanda yayi tsammanin zuciyarsa zata riqe.

Shi DD kuwa Wani nauyi da radadin rashin Bilal da yayi tsawon shekarun ne suka danne kirjinsa idanuwansa sukai jajir baya iya ko hawayen farin cikin ganinsa sbd Wani abin busar da hawaye yakeyi.

Naseer ajiye towel din hannunsa yayi ya miqawa momyn Abdul robar yace takai kitchen tabasu guri.

Tana barin gurin Shima wayarsa ya fidda daga aljihunsa Yana nufar kofa sbd yakamata yayi magana da Zeenah Dan babu Wanda yasan sun Abuja gashi yasan tayita kiransa jiyan Bata samu sbd kashe wayarsa da yayi.

Yana fitowa daga palon tana daga Kiran nasa cikin sanyin murya da mutuwar jiki sallama kawai tayi masa tayi shiru sbd fushin datakeyi akan kashe wayarsa da yayi batareda ya nemeta ba.

Yanajin muryanta sauke ajiyan zuciya ya fara Yi sbd nutsuwar Daya samu tareda Jin kaman zazzabin kewanta zai kamasa saidai yasan Kuma muryan nata akwai fushi aciki dan haka tausasa muryarsa yayi tareda Bude mota ya zauna ciki ahankali yafara rarrashinta cikin tasa kalan soyayyar da kusan irin ta ubangidansa ce Dan kuwa tinda ya fara soyayya da Zeenah daga zaman jinyar da sukai ya mace gaba Daya akanta kallanta kawai kashe masa dukkanin jiki yakeyi.

**********

DD da Bilal su kadai ne a Palo zaune bayan sun jima rungume da juna cikin yanayinda baya fasaltuwa na tsananin kewa da kaunar juna kafin DD ya kallesa da idanuwansa dasukai laushi har lokacin ya kasa hawaye ma bare,

Da taushin murya me sanyi da nutsuwa yace

“Meyasa ka boye kanka daga familynka bayan kasan Muna cikeda da radadin rashinka??

Meyasa??

“Kasan irin gwagwarmayar da Akai before life ya kawo mu inda mike a yanzu?

Rayuwana ya shiga Wani mugun hali ni banma San yazan fada Maka ba Amma dai meyasa ka zabi Hakan??”

Numfashi Bilal ya sauke ahankali tareda Dan sauke Kansa yayi shiru tsawon mintina tukuna ya dago ya Kalli DD dayayi Wani Kalan tausayi cikin qanqanin lokaci ya Bude baki a hankali cikin nutsuwa yace

“Na zabi boye Kai ne na Dan Wani lokacin bawai na har abadaba,

Zuciyarta tana tsananin son sumayyah da bazan taba iya komawa da ita gida a halinda take ciki kafin ta warke sbd nasan family na bazasu taba karbanta su barmu tare ba,

Nine asalin dalilin rusa yar rayuwar da suke lallabawa da ita a hannun mahaifinsu Tayaya zan barsu a cikin wannan halin bayan nasan a wancan lokacin ba karban sumayyah din zaayiba da Abinda zata Haifa anfada ne kawai Da wata manufar da bansan mecece ba,

Ban baro kaantes ba a wancan da niyar tafiya nabar gida kwata kwata ba Amma a halinda na Tarar da sumayyah din aciki lokacinda na Isa gidansu ban yarda Dana barta ahakan ba shiyasa na dauketa da niyar tafiya nesa da ita Dan nemar mata lafiya,

A halinda na fito da ita ni kaina ban dauka a kwai sauran Rai a jikinta ba Dan haka Kai tsaye Wani private hospital dake hanyar fita gari sosai nakaita Kuma aka karbeta cikin gaggawa aka tabbatarda Bata mutu ba da ranta sedai tana mummunan hali.

A wannan lokacin na shiga mafi munin tashin hankali sbd ban dauka zata rayu ba,na dauka rasata zanyi.

Ta dayan bangaren Ina ganin Kiran dukkaninku a wayata Dan haka na sakawa Raina maganar dd babba ce akan kada na taba dawowa kaantes Dan haka a cikin wannan halin na kira driver Dina nace aikasa yake kaantes ya dauko mun password da duka sauran id cards Dina da cards Dina da wasu abubuwan da zan buqata batareda sanin kowaba sbd banason Umme ta shiga damuwa da tashin hankalin bazan dawo kaantes ba.

A cikin Daren na karbi komai hannunsa nace ya mayar da motar kaantes.

Mun rabu dashi bansan sun a akaiba da safe Abinda na fara cin Karo dashi a labarai shine labarin rasuwata daya yadu cikin qanqanin lokaci,

Driver na yayi accident ya rasu an dauka nine Dan haka babu Abinda yazo Raina kawai bayan na tafiyata inda zan samu nutsuwan jinyar sumayyah Dan samar mata lafiya tinda har Hakan ta Riga ta faru.

Boyon kaina na fara tareda taimakon sulaiman me napep din Dayake kaisu makaranta,

A gidansa muka koma bayan sumayyah taji sauki kusan kwana ashirin Muna jinya,

Acikin kwanaki ne na samu labarin aurenka da Bena,

Banyi mamakin Hakan ba sbd yanda Ababa bai fidda zancen yarsa ta rasu ba ga kowa bare batan gawarta.

Sanin daga Kai har Bena zaku zama iyayen da kusan zasu Fi mu son ‘yar da aka Haifa dakuma ganin Bena ta samu Damar da zata fita daga hannun mahaifinsu da tsananin quncin rayuwarta ya sakani Yanke shawarar dauke sumayyah mutafi inda zan nema mata lafiya sbd bayyanarmu zai dakatar da aurenka da ita Ta tabbata a gidan Ababa hakama nasan bazaa taba karban sumayyah a halinda take ciki ba na rashin cikakken hankalin.

Da kaina nayiwa Nafisat hanya a sirrance ta hanyar Bata complimentary card Dina nafada mata Wanda zata Kaiwa wadda yake da iKon Kai ma’aikatan kaantes Kuma cikin iKon Allah ya dauketa sbd tausayin nayi alqawarin inganta rayuwarta kafin rasuwata Dan haka aka miqata cikin sa’a a matsayin nanny Kuma me aikin Bena.

Sulaiman ne ya rakoni har Abuja da sumayyah tareda momyn Abdul wadda itace take yiwa sumayyah wanka da sauransu.

Dawowanmu Abuja da farko Badan Sha fama da gwagwarmaya sbd yanayin sumayyahn dayake da wahala da wuyan shaani Dan haka muka na Nema malamai aka daura mana aure.

Bayan aurena da ita ko watanni bamu rufa ba muka bar qasar na koma Canada da ita.

Acan na fara Aiki Kuma Ina kulawa da ita Kuma Muna ganin likitoci kan matsalarta Akai Akai.

Bana tareda kowa Amma na Samu nutsuwa da farin cikin rayuwar Dana Dade bansamuba a cikin family na,

Sumayyah itace nutsuwa da farin cikin rayuwata,

Batada kowa sai ni,batasan kowaba sai ni,

Nine uwa,Uba,aboki,miji da komai nata.

Aikina Yana sake daukan tsanani da buqatan mayar da hankali sosai Dan haka na tura komai sulaiman ya turo min da momyn Abdul sbd ta taimaka gurin kulamin da sumayyah.

Sumayyah ta sake sumun ciki so Daya Tasha wahalarsa sosai wanda kusan yaso qara juyar mata da Kai Dan haka muka ciresa babu sake samun Wani ba na aje maganar haihuwa sai lokacinda ta samu dawowa daidai,

Duk Abinda yake faruwa kaantes ina sane Ina ji Kuma Ina farin ciki sbd ganin kunsamu kwanciyar hankali,

Munfara bibiyan Safnah ne batareda munsan ita din asalin yar uwar Bena bace sai lokacinda ta Kade Anne Kuma suka so kashe Bena Wanda sulaiman yagansu Kuma shine yafara Kaiwa Bena Doki kafin Zeenah ta iso ta Tara mutane,

Daga wannan lokacin sulaiman yafara bibiyarta,

Ranar data zubarda Abinda sulaiman ya dauko muka duna muka Gane Abinda suka baka se washe gari mukaji Ashe Kai suka bawa wainnan qwayoyin shine dalilin Daya sakanin dawowa qasar tareda Sumayyah da momyn Abdul Kuma a ranar na barsu Abuja na wuto sbd kunbar qasar a wannan lokacin nasan komai zasu iya aikawata Bena tinda ba kowa.

Kai tsaye Asibiti na Isa ta tararda Bena tabar Asibitin Koda muka kira Nafisat itace ta sanar damu Bena din Takoma da napep da alama gidansu zata tafi Dan Nafisat taji maganar Ababan ta waya.

Kafin na Isa sulaiman ya rigani Isa gidan Kuma ya leqa ya tabbatarda suna ciki Kuma duk Abinda suka fada yaji komai Dan haka bayan fitowarsu Bena shine ya nuna inda suka bi Ina Isa kuwa na samesu a hanyar na daukesu na taho dasu sbd hadarin Safnah da matar Alh basheer bulama yanada yawan gaske da zasu iya sake canja hanyar kawar da ita matiqar Bata bar garinba kwata kwata na lokaci.

A yanzu dinma rashin lafiya take fama dashi tinda ta baro ta kasa cire tinani da damuwa a ranta Wanda tana buqatan cirewan kada Wani ciwon ya shigeta shiyasa na buqaci passport dinta Dan fita da ita na Dan lokaci.

Shiru DD yayi Bai iya cewa komaiba sai ja da idanuwansa suka qara tsananin ciwo da nauyin Kansa na qaruwa,

Shidai irin wainnan abubuwan jirkita Kansa sukeyi,baya daukan Hakan,

Bai sababa,

Duka wannan abubuwan akan sumayyah da tsananin son da Bilal din ke mta yayisu?

Idan shi Bilal zai iya Hakan akan sumayyah shi dayafi Bilal din Jin mafiyin wannan son akan Bena to Yaya zeyi idan Wani Abu ya samu Bena,

Yaya zaiyi idan da sun samu fita qasar da Bena batareda ya gano inda suke ba,

Da haka zai zauna babuta?

Tayaya zai iya dauka?

Zuciyarsa bazata iya daukaba.

Juyawa yayi ka Kalli koina cikin palon yana Neman inda zai ganta ko zuciyarsa zata dawo saitin daidai sbd wannan tinanin ya sakasa da zuciyarsa cikin tsananin rashin nutsuwa.

Ajiyan zuciya bilal ya sake Yi sbd yasan Shima kalan halinda zuciyarsa take shiga akan soyayyar ‘yar gidan Anne,ga Kuma DD Wanda da alama shi Kansa bazai iya dauka ba sbd baisababa haka Bai iya boye Abinda yake zuciyarsa ba game da komai.

Sarawa kan DD yakeyi sosai da duka Abinda yaji Dan tausayi da tsananin son Dan uwansa sabo fil ya dawo masa Yana Kuma farin cikin dawowarsa rayuwarsu sbd babu Wanda ya Isa ya raba Bilal da sumayyah a yanzu Dan ko shi bazai bari a rabasu ba yanda yasan Yaya akeji dinnan.

Sake rungume juna sukai zuwa lokacin tsananin ciwon kan DD din yayi yawa sbd ga rikice rikice, ga abinci Daya dena ci,ga damuwa, ya abubuwan Dayake taji da yakasa yarda da suna faruwa a duniyar Dan haka abin yayi masa yawa,

Bilal ne ya miqe da sauri ya dauko wayarsa ya kirawo likitansa Wanda yake Kuma kaman aboki hakama a cikin estate din nasu yake Shima Dan haka cikin qanqanin lokaci sai gashi ya iso.

Naseer na ganin shigowar likita yayi sallama da Zeenah Yana nufo ciki batareda ya fada mata komaiba gameda Bilal dasuka Gani sbd sai DD ya Bada umarnin abari kowa ya sani tukuna.

Dubasa likita yayi babu Wani Abu face damuwa da gigita datai masa yawa cikin Kai so Hutu kawai yake buqata da isashen bacci zai samu Kansa ya sake inshallah.

Bayan tafiyan Dr kallan sumayyah yayi wadda hankalinsu ya Dan tashi sun dauka Wani abin ne Kuma ya samesa

Yace ta hadowa DD din simple breakfast yaji kafin ya samu hutawan Daya kamata.

Kallan sumayyahn yayi kafin ya mayar da kallansa kan Bilal har lokacin Kansa na sarawa yace Bena yakeson Gani.

Shiru sumayyah tayi tana juyawa ta Kalli kofar dakin da Bena take ciki tareda Anne Yana ganin Hakan ya miqe a hankali zai nufi dakin Bilal ya riqosa cikin Dan basarwa yace masa Anne na ciki fa.

Kallan Bilal din yayi kafin ya girgiza Kansa a hankali yace ok a kirata ita tasan Abinda yake iya ci.

Murmushin da sumayyah batasan yazo mata bane ya subuce mata take shikuma Bilal jikinsa ya mutu da Hakan Dan haka ya saki DD yabarwa Naseer shi yabi bayan sumayyah zuwa kitchen Yana saka Kai yaga momyn Abdul tana Kitchen din Dan haka ya juyo Ya dawo Yana Dan fuskewa.

Gaba Daya hankalin DD na kan kofar dakin da Bena ke ciki basarwa kawai yayi Yana daurewa sbd Bilal da Naseer sunce baa shiga idan mahaifiyar mata ne aciki Amma shi ko Umme na Nan ai Yana shiga.

Simple instant noodles da boiled eggs da sausage sumayyah ta dafo ta ajiye a dining Daman already akwai kayan breakfast dake Jere Wanda babu Wanda yayi breakfast din a cikinsu Dan haka cikin kulawa Bilal ya Dan tilastawa DD yayi breakfast din kafin ya tafi masaukinsu ya huta,

Sam bayajin cin komai tinda ba Bena zai ganiba kawai baya buqatan cin komai sai ya dawo anjima din Amma dole Bilal yai masa.

Zaunawa sukai a dining din harda Naseer,

Sumayyah ce tayi serving nasu ta koma kitchen ta dauko musu ruwa marasa sanyi sosai ta ajiye.

Abincin DD ya kalla yana Dan ya mutsa fuska kadan sbd ganin kayan veggies aciki sosai.

Naseer dayaga abincin gashi kalan yan gayu Amma ganin kayan Miya sosai aciki ya sakashi fara diban abincin yaji ko da akwai yaji.

Shima D ahankali ya diba abincin da fork ya Kai bakinsa cokali Daya abincin ya shiga bakinsa ya tauna ahankali yayi shiru sbd Abinda yaji yafara gauraya bakinsa.

Cikin Wani yanayi na qarfin hali ya hadiye abincin tareda sake dubowa yaci sbd ya faranta ran Dan uwansa,

A cokali na uku daqyar ya hadiye zufan dayake hadewa Yana sake tsitsifo masa tini ya saki spoon din kunnuwansa na daukan Wani masifaffen yajin Daya kasa daurewa ya dago jajayen idanuwansa Yana kallan Naseer dayayi daurin dauko ruwa zai Basa Amma Sam Neman gigicewa DD din keyi

Take hankalin Bilal da sumayyah ya tashi sukayo Kansa suna Kiran sunanda da Dan qarfi.

94

********

Tashi hankalinsu yayi musamman Naseer da Bilal Daya manta Sam DD is mugun allergic to yaji kwata kwata bare cinsa,

Ruwa sumayyah ta sake zubawa da sauri masu sanyi tana miqawa Bilal ya Basa

Da sauri ya amsa ya nufi bakinsa da ruwan a rikice ya amsa yakai bakinsa idanuwansa na sake rinewa yasha Amma take yaji kaman azaban Yana tsananin qaruwa ne ya miqa musu cup din da sauri Yana Dafe kirjinsa farar fuskarsa na qarasa rinewa zuwa jajir zufansa sai qariwa yakeyi Yana feso masa.

Juice sumayyah ta sake zubawa a rude tana miqawa Amma Sam ya ture ya kasa amsa take hankalinsu ya sake tashi.

Da sauri sumayyah ta ajiye cup din hannunta ta nufi dakinda su Bena suke akwai rechargeable fan me girma ta nufa zata dauko tana sanar dasu halinda DD yake ciki ta fice da fan din da sauri takawo gefensa ta  ajiye tareda kunna masa iska na hura masa sbd zufan dayake hadawa.

Bena shiru tayi bugun kirjinta na tsananta da Jin Abinda sumayyah ta fada sbd tafi kowa sanin halinda yake shiga na tashin hankali da masifa akan yaji.

Daurewa takeyi tana son Hana kanta a fita sbd tsoro da gudun Abinda zai iya faruwa idan take din Amma Kuma zuciyarta ta kasa nutsuwa da yarda day a barsa a halinda tasan wuya yakesha Kuma daga qarshe ciwo zai iya biyowa baya.

Batada Wani kuzari me qarfi sbd rashin laifiyarta Data kasa warwarewa yanda ya kamata itama duk da Hakan kasa daurewa tayi ta tashi daga jikin Annenta tareda kasa kallan Annen ta miqe tsaye tana zira takarminta masu taushi na yawon daki tana cewa Annen bari ta dubo Abu a kitchen.

Kofa ta nufa ta fice tabar Anne na bin bayanta da kallo sbd batasan me zata Nemo ba ko dubowa a Kitchen.

Tana fitowa daidai momyn Abdul ta fito kitchen ita Kuma riqe da qaramin bowl ta zubo manja a ciki me kyau akan abasa a gani Yana taimakawa yaji fita.

Kitchen din ta shige Kai tsaye cikin rashin kuzari da Dan sauri ta dudduba basuda Nutella bare chocolate tinda ba Yara a gidan Dan haka ta a dauko glass cup me kyau ta hada masa ice tea me kaurin gaske da qanqara aciki ta fito ta nufosu.

Da jajayen idanuwansa ya hangota tafe da cup cikin sauri da galabaita ya daga hannu ya miqa mata sbd yasan ta samo abinda zai taimaka masa ne.

Tana qarasowa momyn Abdul ta koma kitchen da manjanta dayaqi Sha ganin yake mutuwa zaiyi yana shansa,

Daga Naseer har Bilal kowa aje cup din hannunsa yayi na ruwa da juice din dasuketa yaqi da kokawan Basa ya samu saukin.

Tana qarasowa Kai tsaye miqa masa cup din tayi tana kokarin janye abincin daga gabansa.

Sumayyah ce ta amsa abincin ta juya tayi kitchen dashi Dan mayarwa.

Naseer kuwa barin gurin yayi Yana share gumin da Suma suka hada na tashin hankaln DD din kawai.

Bilal ne kawai ya rage a gun Dan haka ta sake miqa DD din ya karba hannunsa na Dan rawa yakai cup din bakinsa yafara Sha Yanajin kaman Shima bazai taimakesa ba ya aje cup din kafin ya dauke hannunsa Akai ta Dora hannunta kan nasa ahankali tareda dagowa ta kallesa cikeda kulawa da sanyin jiki ta girgiza masa Kai akan yasha din ze taimaka masa.

Kasawa yayi Yana Neman miqewa tsaye zufansa har lokacin qaruwa yakeyi.

Sake riqe hannunsa tayi ta hanasa miqewa

Bilal na ganin Hakan ya juya yabar gurin Yana cewa bari a kira likita ma.

Yana barin gurin palon ya koma ba kowa Dan haka ta zauna gefensa ahankali tareda daukan cup din ta nufi bakinsa dashi tana Basa ahankali.

Sha yakeyi ahankali Yana rintse idanuwansa sbd zuciyarsa dayake Jin kaman tana zafin yajin itama.

Da bakinta tai masa alaman ya Bude bakinsa ta Gani.

Budewa yayi kaman Wani babu Yana kallanta a Dan wahalce.

Matsowa tayi da bakinta a hankali daidai nasa bakin gadon a Bude bakinta ahankali cikin Wani irin sanyi da tsananin kulawa ta fara hura masa iskan bakinta ahankali cikin nasa.

Wani irin yummm yaji saukan iskan bakinta me tafe da qamshi da yajin mint flavor mouthwash dinta me tsada zuwa cikin bakinsa har maqoshinsa yaji saukan iskan.

Rintse idanuwansa yayi babu shiru kafin ya Budesu akanta itama ta Bude nata Dana lumshe ta kallesa tareda Kai cup din bakinsa ta Basa ya kurba ahankali

Ta sake hura masa iska a bakin tana ganin yanda harshesa yayi ja.

Sake Basa ice tea din tayi tana hura masa bakin a hankali

Bai San ya akaiba sai yaji yafara Jin yajin na raguwa Yana sauka ahankali hakama zufansa na raguwa saidai cikinsa kam dayaji yana masa Dan zafi a ciki alamar yajin yayi cikinsa.

Yanda take masa din kaman baby ya sake sakasa Jin jikinsa gabaki Daya ya mutu babu Abinda yakeso a lokacin bayan yaji saukan ruwan sanyi a jikinsa Dan haka ya kalleta a galabaice da kasala ahankali ba kuzari yace ta bisa su tafi please.

Kasa tayi da kanta a hankali tareda Dan narke fuska sbd batasan Tayaya zata iya binsa ba Annenta na Nan hakama Bilal sbd kunyarsu takeji.

Hannunsa ya Dora kan nata hannun a hankali Yana kallanta itama shi take kalla cikin sanyi da kulawa ta sake Kai cup din bakinsa hannuwansu na tare ta Basa yasha ahankali ta sake matsawa da bakinta ta ringa hura masa bakin tana Yana lumshe idanuwansa dasuke sake laushi bayan Jan dasukai.

Kasa hakuri yayi cikin nutsuwa ya janyo hannunta dake hade da nasa ya dawo da ita kan qafafunsa tana son tashi cikin tsananin kunya da fargaban kada Wani ya fito ya samesu Hakan Amma yakasa sakinta saima girgiza mata Kai yayi ahankali Yana mata nunin data Dena motsawa.

Kallan idanuwanta yayi da nasa idanuwan Yana zagayeta da hannuwansa tareda Dan matseta jikinta ahankali suka manne sosai da juna ya Bude baki zeyi magana ta Bude bakinta ta sake hura masa iska a bakin sbd tasan Abinda zai fada bazai wuce ta bisa ba.

Saukan sanyin iskan bakinta cikin nasa ya sake dumama jikinsa dake Neman kamuwa da zazzabin dole na wahalan dayasha.

Cikin qaramin sautin Da baya fita sosai ya Kai bakinsa kan kunnenta lips dinsa suna gogan fatar kunnenta murya a qasa qasa cikin sanyi yace

“Idan bazani dake ba Nima zan kwana anan.”

Bude idanuwanta dake rufe tayi tareda motsawa zata dago daga jikinsa tayi magana Amma Bai saketaba Dan haka dole itama kunnensa dake setin nata bakin zatai magana lips nata suka gogesa a gefen fuska Wani irin dumi hakan ya qarawa jikinsa ya rufe idanuwansa