Kanwar Maza Hausa Novels

Kanwar Maza Chapter 6

P6

Iya ƙarfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.

Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya ɗago ya kallesu ya ce “Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?”

Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi”Mama tana nan?”

“Eh tana nan” Aliyu ya bashi amsa.

Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.

Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba’asi.

“Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?”.

Mama ta ɗan yi sororo ta ce “Wace irin sikila kuma?”

“To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ƙi sai a bayana na goyota”

Yaya Umar ya kalleta ya ce “Ke meya sameki?”

Cikin in da in da ta ce “Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata ‘yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita”.

“Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?” Yayi maganar cikin tsare gida.

Cikin kuka ta ɗage ƙafar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce “Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi ni ba zan iya makarantar nan ba, wai ban iya karatu ba shi ne aka yi mini wannan dukan, ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ga duka ga karatu mai yawa, da wanne zan ji?”

Cikin tsawa Yaya Umar ya ce “Wuce mu je makarantar, sai kin ci ubanki yau, ai dama karatu aka turaki ba wasa ba”

A karo na farko ta yi wa yaya Umar gardama tana kuka, ta riƙe hannun Huzaifa, ta ɓuya a bayansa.

“Ni nake miki magana ki ke ɓuya a bayansa, ba zaki fito ki wuce ba”

“Dan girman Allah kayi haƙuri, wallahi idan suka san ƙarya nake, sai sun kusa kashe ni, wallahi duka ake na tashin hankali a makarantar nan” kuka take wiwi kamar wadda aka yiwa mutuwa, mama dai ta kasa magana.

Huzaifa kuwa janyota ya yi daga bayansa, ya ce Wallahi ba zai kareta ba sai dai ayi mata duk abin da za ayi mata.

Yaya Sadik ne ya fito daga ɗakinsu, yana zuwa ya ture Umar, ya kamo hannun Rumaisa, ya wuce da ita ɗakin su.

Suna shiga ya zaunar da ita, shima ya zauna ya ɗan ƙura mata ido sannan ya ce “Auta, meke damunki ne, kullum sai an yi rigima dake an ce ba kya ji, ke ko haushi ba kya ji?”

Ta girgiza kai ta ce “Wallahi ina jin haushin yadda aka tsane ni kullum ace bana ji”

“To yanzu meyafaru, har aka dake ki ki ke cewa sikila ce dake? Kin san sikila kuwa meyasa ki ke fatan wannan ciwon?”

“Gani nayi za a kashe ni da duka, ni bana son a dake ni”.

“Gaskiya ba ka kyautawa, dan me yarinya za ta yi laifi ka hana a hukunta ta, me kake ƙoƙarin koya mata ne?” Umar yayi maganar a mugun fusace.

Yaya Sadik ya waiwayo ya kalli Hussainin na sa, ya haɗa hannayensa alamar ban haƙuri ya ce “Tuba muke, zan wa tufkar hanci in sha Allah, on behalf of her, ayi haƙuri gobe in Allah ya kaimu da kaina zan mayar da ita makarantar in basu haƙuri” gajeren tsaki Umar yayi yai waje, babu wanda yake masa katsalandan kamar yadda Abubakar yake yi masa, ya fuskanci idan aka biyewa Yayan nasa ruma tsiyarta zata tsula ba tare da an kwaɓeta ba, da tayi laifi sai ya ce ƙuruciya ce.

Wunin ranar kowa share ruma yayi, yaya Sadik ne kawai yake kulata, Huzaifa da yasir suka ƙare mata zagi tsaf suka tsangwameta.

Ko a jikinta, tun da Allah ya sa ba a mayar da ita makarantar an ce ƙarya take ba, hankalinta ya kwanta.

Washegari Yaya Abubakar da kansa ya rakata makarantar, aka dinga yi mata sannu ana mata ya jiki, ta basar ta dinga amsawa.

************

Sanye yake da fararen kaya ƙal, fuskarsa sanye da fari siririn glashi, taku yake cike da ƙasaita ya biyo wata doguwar baranda.

Sannu a hankali ya ƙarasa gaban wata ƙatuwar ƙofa, ya sa hannu ya murɗata a hankali. A take ta buɗe wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinsa.

Da sallama ya shiga ya mayar da ƙofar ya kulle, babu kowa a falon sai wata matashiyar budurwa tana saka turaren wuta.

Amsa masa tayi tare da faɗin “Sannu da zuwa”.

“Yauwwa ‘yar aikin Ammi, ina ma’aikatan ne ki ke aikin da kan ki?”

Ta ɗan kalle shi sannan ta ce “Nima ‘yar aikin ce ai” yayi murmushi ya ce “Sorry idan haushi ki ka ji, ina Ammi?”.

“Bacci take” ta bashi amsa lokacin da take cigaba da saka turaren wuta.

“Ba kowa kenan?”

Cikin ƙosawa da tambayoyinsa ta ce “Duk sun tafi makaranta”.

“Ke me ya hana ki je makarantar?”

“Ohh God, uncle J am sick shi ya sa ban je ba, Ammi idan kana son ganinta ka dawo an jima, ina fatan zan iya tafiya na gama amsa tambayoyin ka?”

Ya girgiza kai ya ce “No, saura ɗaya ina yayan ku?”

Tayi murmushi ta ce”Wannan tambayar ai kai yakamata a yiwa, i don’t know ” daga haka ta bi wata hanya ta bar falon.

Ya girgiza kai a hankali ya ce “Wannan yarinyar ta fi mai kora shafawa, izzarki tayi yawa”

Wayarsa ce ta fara ringing, ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar.

“Ke nifa kin isheni, ni kaina ban san in da yake ba, anjima kuma kilisa zan fita, zan neme ki amma” daga haka ya kashe wayar, ya saka a aljihunsa ya fice.

*********

Ruma ta sha kashedi a wurin su Huzaifa, a kan ta shiga hankalinta a makarantar nan, dan ba ƙaramin girmansu ake gani ba, halinta ba zai sa mutuncinsu ya zube ba.

Ta cigaba da zuwa makaranta, amma ba ta gane komai, idan Yasir ya zaunar da ita zai koya mata kuma, sai ta ce ita ta gaji ba ta so.

Ranar wata juma’a da yamma, Abdallah yana ta haɗa kayan miya, za a kai markaɗe, Yasir ya kalleshi ya ce “Abdallah kyanta na ɗau hotonka kana haɗa kayan miyar nan, na je na nunawa yarinyar nan mai awara”.

Haɗe rai Abdallah ya yi ya ce “A’a mai wake zaka nunawa ba mai awara ba”

Yasir ya yi dariya ya ce “Zaka ga mai wake, wallahi yarinyar nan ta mato a kan ka, kawai ka nutsu ku daidaita, wallahi shar da kai awararka zaka yi ta ci”

“Na rantse idan ba ka yi mini shiru ba sai na ɓarar da kai”

Yasir ya ce “Yaya ba zan ƙoƙari na tayata kafa gwamnatin ta ba, kullum sai ta kyauta mini”.

Buut Ruma ta fito daga ɗaki ta ce “Yasir yakamata muje ka gabatar mata da ni, na dinga biyawa idan zan je makaranta”.

Tsaki Yasir ya yi “To munafuka waye ya sako dake, na zaci ma bacci take wallahi “

Abdallah ya ce “Wallahi ko da wasa ki ka je, sai na kakkarya ki”.

“To ni ce maka ma nayi zan je?”

“Ke dai ki ka sani gulayya” Yasir yayi maganar yana hararta.

“Wallahi ni ba gulayya ba ce” shareta suka yi suka cigaba da hirarsu, yayin da Ruma ta koma gefe tana naɗar abin da suke faɗa.

Kamar yadda a islamiyya ruma ba wani ja take ba, haka ma makarantar boko ba uwar da take ganewa sai wasa.

Ta na cikin top 10 na marasa ganewa a aji, sannan ta farko a sahun marasa ji.

Yau bayan an taso daga makarantar boko, ta biyo ta hanyar da lambun mai unguwa yake. Ƙaton lambu ne da ya kasance mallakin wani a babba masarautar Kano, wanda yake ƙarƙashin kulawar mai unguwa, ba kowa ya san da hakan ba sai ɗaiɗaikun mutane.

Gaba ɗaya hanyar ba ta cikin jerin hanyoyin da zata bi su sada ta da gida, amma tun da ta ji ‘yan ajinsu suna labarin mangwaron lambun ya fito yayi kyau, tayi alwashin bi ta hanyar dan ganewa idonta abin da suka gaya mata.

Aikuwa babu ƙarya, lambun ƙato ne na gaske, wani wurin an kewaye shi da katangar bulo, wanu wurin kuma aka ƙarasa kewaye shi da waya.

Akwai bishiyoyi kala-kala a ciki, wasu duk sun yi ‘ya’ya kasancewar lokaci ne na damuna.

Mangwaron nan yayi ‘ya’ya sosai gwanin ban sha’awa.

Ƙatuwar ƙofar shiga wurin ta gani, babu kowa a wurin, dan haka kai tsaye ta kutsa a gaban wata ƙatuwar bishiyar mangwaro ta tsaya, yanayin wurin yayi mata kyau sosai da sosai.

Ta samu dutse, ta dinga jifan bishiyar, suna faɗowa tana ɗiba, ta tara ta cika jakarta, sannan ta nufo hanyar fitowa.

Tana fitowa wani matashi yayi caraf ya danƙeta yana faɗin “Alhamdilillah, shegiya ɓarauniya ashe ku ne masu shiga lambun nan suna ƙurguma mana sata”.

“Ban gane ba wace iri ɓarauniya me nayi maka?”

“Zaki ga me ki ka yi mini, gidan mai unguwa zan kai ki, ke saboda ƙwarewa ma, da ki ka sata sai ki ka biyo ta ƙofa zaki fita, kina ‘ya mace kina sata”

Cikin rashin kunya Ruma ta ce “Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, ta ƙofar nan fa na shiga, ba wanda ya haura gida ne ɓarawo ba?”

“To da ki ka bi ta ƙofar, wa ki ka tambaya ki ka shiga ki ka ɗebo abibda ba naki ba?”

“A’a, to ni wa na gani a wurin, kuma ma naga ai bishiyar ta Allah ce, Allah ne ya fito da ita, kuma sai ace sai an tambayi wani sannan za a ɗau abin da Allah ne ya fito da shi, kai iskar da ka ke shaƙa wa ka tambaya ka ke shaƙarta?” Saroro ya bi ruma da kallo, wata ‘yar cukul da ita sai shegen surutun tsiya.

“Zaki yi bayani, sai na kai ki gaban mai unguwa”

“Daɗinta shi mai unguwar ba shi da wutar da zai sakani, kuma duk in da za a je ai bishiyar Allah ce, kuma ka sakar mini hijjabi dan ni ba ‘yar iska bace ba.

Bai ko saurareta ba, ya figi hijjabinta ya fara janta.

“Ka dai na ja na haka kamar wata akuya, ba ƙaramin aikina bane na cire maka hijjabin nan na ƙara gaba.

Mama sai kallon agogo take yi, tana kallon hanyar shigowa, amma babu ruma babu alamunta.

Tsakar gida ta fito tana kiran Usman, kasancewar shikaɗai ne a gidan, ya dawo da wuri bashi da lectures.

“Ka ga haryanzu yarinyar nan shiru ba ta dawo ba”

Usman Ya ce “wataƙila tana can tana rashin hankali a titi da ƙawayenta, amma maybe ki ganta yanzu”.

“A’a zunnuraini, shi biyu da rabi fa take dawowa amma kalli yanzu ƙarfe ɗaya da rabi, hankalina ya kasa kwanciya”

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Kuma fa kamar ma ga ‘yan makarantar su lokacin da nake hanyar dawowa, amma bari na je makarantar ta su” yana rufe bakinsa, suka ji ana ƙwala sallama a waje.

Usman ya amsa, ya nufi ƙofar gidan, aikuwa yana zuwa ya tarar da an riƙo ruma, tana rungume da jakar makarantar ta, sai kumbura baki take, tana cika tana batsewa.

Kallon matashin saurayin yayi, ya ce “Bawan Allah lafiya, ya zaka riƙo yarinya haka kamar ka riƙo ɓarauniya?”

Matashin ya ce “To kusan hakan ne, karɓi jakarta ka duba ka gani”

“Ka saketa mana” yayi maganar a fusace yana fincike hannun matashin daga hijjabinta.

“Me tayi maka haka?”.

“Nan matashin ya kwashe komai ya gayawa Usman”

“Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, tun da ta ƙofar wurin na shiga kuma ban ga kowa ba, ai ba haurawa na yi ba”

Usman ya fizgi jakar ruma, ya buɗe ya ga mangwaro ya kai takwas a ciki manya, nunannu da ɗanyu, sai goba guda huɗu.

Ya kalli ruma, sannan ya kalli matashin ya ce “Yanzu kai a kan wannan zaka danƙota ka keto layi da ita haka? Ka taɓa kamata ta shiga ta ɗaukar muku abu ne?”

Matashin ya ce “Ban taɓa kamata ba, amma ana haura mana, ayi sata”

“To kuma sai aka ce maka nice nake yi, ni wallahi ban taɓa shiga ba sai yau”.

Usman ya zura hannu a aljihunsa, ya ɗauko dubu ɗaya, ya miƙawa matashin ya ce “Na san dai abin da ta ɗauka, bai kai na hakan ba, gashi nan na biya, kuma kar ka sake kiranta ɓarauniya Please, ba halinta bane ba ba ta taɓa yi ba, dan ka ci sa’a da na biyewa zuciya sai na kifar da kai, saboda yadda ka riƙo mata hijjabi, ka keto unguwa da ita, saboda ɗanyen mangwaro”

Yana gama maganar, ya ingiza ƙeyar ruma zuwa cikin gidan, suna shiga gidan ya danƙota ya ƙwace jakarta, ya durƙusar da ita ya ce “Oya tsallen kwaɗo maza”

Waiwayo ruma tayi, ta kalleshi cikin mamaki, amma taga babu alamar wasa a tare da shi, cikin tsawa ya kuma cewa tayi tsallen kwaɗo.

Mama ta fito tana faɗin “Lafiya, me aka ce tayi, sallamar da ake kenan?”

Usman ya ce “Ƙyaleni da ita mama” nan ruma ta kama tsallen kwanɗo.

Duk yadda mama tayi a kan Usman ya gaya mata me aka ce ruman tayi, amma yaƙi, sai dai ruma ta ci ƙwal ubanta, dan ko miƙewa kasa wa tayi.

Duk yadda mama ta kaɗa ta raya, amma bai gaya mata ba, kuma babu wanda ya gayawa abin da ta aikata.

****

Islamiyyar su ruma, sanya mata ido suka yi, dan ba ta iya karatu balle kawo hadda, ko karatun aka zo sai dai a tsallake ta, dan ba iyawa take yi ba.

Malamin ajin ko sabgarta ba ya shiga, tun daga ranar da ya dake ta ta ce ita sikila ce. Yau dai ya kasa jurewa yace mata “Wai ke ba kya jin haushi yadda ‘yan ajin ku suke karatu, amma ke ba kya iya wa?”

“To malam karatun yayi mini yawa, yaya zan yi?”

“Su sauran da suke iyawa, da me suka fiki?”

Ita kanta ruma gaba ɗaya malamin bai yi mata ba, dan bai fi sa’an Abdallah ba, shi ma ɗalibi ne a makarantar, amma ya dinga takura mata.

Tayi masa banza tana kallon wani gefen daban.

“Magana fa nake miki?”

“To ya sayyadi me zance maka? Ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ni fa tun farko ba son makarantar nake ba, kawai dan yayana ya kawo ni ne”.

Ita gaba ɗaya kanta tsaye take faɗar magana, ko tayi maka daɗi ko kar ta yi maka kai ta shafa.

Tsaki yayi ya ce “Daƙiƙiya mara zuciya”

Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce “Malam wannan ba halin musulmi nagari bane ba, ba koyarwar addinin Musulunci bace. Saboda bana iya karatu dama duk ka bi ka tsaneni Allah ya buɗa mini ƙwaƙwalwata nima. Zuwa zan yi a canza mini aji” ta tashi ta ɗau jakarta ta bar ajin, ba tare da ko izini ta nema ba.

Ta bala’in jin haushin cin mutuncin da ya yi mata a gaban ‘yan ajinsu, wai daƙiƙiya mara zuciya.

Ofishin shugaban makarantar ta nufa, dan ta sanar masa a canza mata aji, malaminsu ya tsaneta, amma ta tarar baya nan.

Azuzuwa ta shiga dubawa, aikuwa ta ganshi a ajin su Yasir yana yi musu karatu.

A ƙofar ajin ta tsaya ta ce “Headmaster ina wuni?”

Ya ɗago ya kalleta, ba wanda yake ce masa wani head master sai yau a bakinta.

Ya ce “Lafiya lau”

“Malam zuwa na yi ka canza mini aji, ni na gajj da ajin nan, malamin ya tsaneni”

Dariya ‘yan ajin suka fara yi, Yasir kuwa ya sunkuyar da kai ƙasa.

Yayi murmushi ya ce “To shikenan, ki je ki jirani, idan an tashi sai mu yi magana”

“To, Yasir in jiraka idan an tashi mu tafi tare?”

Wani mugun kallo ya yi mata ya ce “Da tare muka zo”

Murguɗa baki tayi, ta koma kan barandar ajin ta zauna, shiru-shiru ta gaji basu tashi ba, ta kaɗa kai tayi tafiyarta gida.

A hanya ta biyo ta filin ball ɗin su Yaya Aliyu, maza sun yi cincirindo, ana kallon ball, ta tsaya tana leƙawa ko zata hango yaya Aliyu.

Kutsawa ta dinga yi, sai gata ita ɗaya a cikin maza.

“Ruma me ki ke yi a nan?” Ta ɗaga kai ta kalli mai maganar, abokin Aliyu ne.

“Yaya Aliyu nake nema”

“To ai yana cikin fili, ball yake”

“To ai na sani, kallonsa zan yi”

Ya jinjina kai ya ce “To ai shikenan”

Kamar daga sama ya ji ana kiran sunansa, da ‘yar siriryar muryarta.

Duk da yadda ya taso ball ɗin a gaba, amma sai da ya tsaya ya waiwaya.

Ruma ya hango a gaban garada, tana ɗago masa hannu.

Waro ido ya yi, ya nufi in da ruma take.

Coach ɗin su Aliyu ya fara masifa, dan ajiye ball ɗin da ya yi, ya waiwaya aka ci su ɗaya.

“Ke me ki ke yi a nan?”

“Wucewa zan na ce bari na zo na ganka”

Ya dafe kai ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ki wuce ki tafi gida”

“Dan Allah ka bari na gani”

Hankalinsa na kan ruma, coach kuma na ta masifa.

“Kai dalla wacece wannan, ku koreta daga wurin nan”.

“Wallahi ba inda zani, ai wurin yayana na zo”.

Aliyu ya kalli abokinsa ya cewa “Aminu, dan Allah jire mini yarinyar nan” ya koma cikin filin yana waiwayenta.

Aminu ya bata wata ƙatuwar jaka ta zauna a kai, ita kaɗai mace a cikin maza.

Yana ball ɗin amma hankalinsa yana kanta.

Ta dinga yi masa tafi tana bashi ƙwarin gwiwa, kusan duk hankali ya dawo kanta, gaba ɗaya ta bawa wasu dariya a wurin.

Da yaya Aliyu ya ci ball kuwa, ta dinga tsalle tana murna, ya ci ball biyu.

Da aka tashi har hoto aka yi mata, ita da Aliyu ta riƙe kofin da suka ci, kasancewar ball ce ta cikin unguwa.

Ba a tashi daga ball ɗin ba, sai ana kiran sallar magariba, mama tana can ta sa an yi sahu ya kai uku a makarantar su, ana nemanta.

Suna tafe a hanya tana yabawa yaya Aliyu, abokansa sai tsokanarsa suke yi a kan ruma.

“Yaya Aliyu, akwai wani wanda kuna ball ɗin, ya dakar maka ƙafa, na ji haushi idan na ganshi sai na buga masa dutse wallahi”.

“Ni ban saki ba, kuma baki ga an bamu pk ba da ref ya gani”

“Oho ni na san wani pk, amma da ka tsaya ja masa duka ka rama, daga wasa sai cin zali”

Haka suka ƙarasa gida, mama na tsaye da carbi a tsakar gida, tana tunanin ta ina ruma zata dawo.

Sai gata ita da Aliyu, yana riƙe da hannunta.

Mama ta kalleta ta ce “Ke daga ina?”

Sai a yanzu ta tuna daga islamiyya ko gida ba ta zo ba, ta kalli ya ya Aliyu ya kalleta.

“A ina ka ganta?” Mama ta tambaye shi tana kallon ruma.

Aliyu ya ce “wallahi mama nima kawai ganinta na yi a filinmu, ban san ina za ta tsaya ba idan na ce ta taho, shi ya sanya na ce ta tsaya”

“Kina mace uban me ya kai ki filin ball?” Huzaifa yayi maganar a ƙufiule, dan takalminsa har tsinkewa ya yi saboda nemanta.

Hararsa tayi ta sake noƙewa a jikin Aliyu.

Duka Huzaifa ya kawo mata, Aliyu ya tare ta, ya ce laifina ne duk Allah ya baku haƙuri.

Mama ta fara tunanin anya ba zata kai ruma wurin malaman ruƙiyya ba, abin na ta ya fara bawa mama tsoro sosai da sosai.

Kamar yadda ruma ta saba kwatsa zance, bayan kowa ya halarra, haka yau ma sai da kowa ya halarran, an gama cin abinci sannan ta gyara murya ta ce “Yasir, wai yaushe ku gama karatun ɗazu da naje ajinku”.

“Ban sani ba” ya bata amsa.

“Mhmm ai dama ba zaka sani ba, nifa gaba ɗaya mutuncin malamin nan ya zube a idona, wallahi mama idan kin ji me yake gaya musu sai kin riƙe baki, duk da wani abun bana ganewa, duk basu san daga waje ina jiyowa ba, kuma maimakon Yasir ya fito daga ajin nan, amma ina yana zaune ana koya musu abin da bai kamata ba.

Saroro yasir ya yi, ya ji me aka koya musu da bai kamata ba, suna haɗa ido da ruma, ya tuna karatun da aka yi musu, kan ya kai ga ɗaukar mataki ta ce “Ina ji ai yana ce muku, wai ko idan mutum ya rungume mace alwalarsa ba ta karye ba, ko kiss, dan Allah wannan mama ba iskanci bane da ɓata tarbiyya, nan idan muna kallo aka nuno kiss ɗauke tashar ake yi, amma wai malaminsu yake gaya musu.

Kuma naga ai turawa ne kawai suke rungume-rungume da kiss, mu wannan ba ɗabi’ar mu ba ce amma yake gaya musu, wallahi makarantar nan ɓata tarbiyya ake yi”.

“DANƘARI!!”

GODIYA GA TARIN MASOYA MASU BIBIYAR LITTAFIN ƘANWAR MAZA, COMMENT ƊIN KU NA SANYA NI NISHAƊI, KAR A MANTA DA SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊIN MU DOMIN SAMUN DAƊAƊAN LITATTFAN HAUSA NA SAURARO.

P7

Dafe goshi Yasir ya yi yana murzawa a hankali, ruma ‘yar bala’i ce, ba zata tashi yi maka hansfree ba a cikin jama’a sai kowa ya hallara kamar mai sanar da wani abu mai muhimmanci, in da ya gode wa Allah da ya kasance, a makaranta ta ji ana koya musu, da bai san da wasu kalaman zai amfani wurin kare kansa ba.

Ita kuwa ta zaƙalƙale tana ta jawabi, babu wanda ya tanka mata, karo da idanun Umar ne ya sanya mata aya a jawaban da take kwarowa babu ƙaƙƙautawa.

“Zo nan” yayi maganar cikin bada umarni.

Kamar mara gaskiya haka ta tashi ta je gabansa ta durƙusa.

“Je ki ɗauko mini jakarki ta makarantar boko da ta islamiyya”

“Dummm ta ji gabanta ya faɗi, har gara jakar islamiyyar ta ma, tun da ba a daɗe da sakata ba litattafan da mutuncinsu, amma ta makarantar boko dai kam sai dai Allah ya kyauta.

Jiki babu ƙwari ta je ta kwaso jakunkunan, ta zo gabansa ta ajiye su.

Ya kalli jakarta ta makarantar boko, duk ta ci ubanta da jagwalgwalon biro, har da zanen ‘yan aljanu a jiki da su ABCD a jikin jakar, sunan ‘yan gidan nan kuwa babu wanda ba ta rubuta a jiki bs. Tun daga nan ya san cikin jakar ma ba za ayi abin arziki ba.

“Oyaa zazzage litattafan na gani”

Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji’un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar ɓera ya ci rage mata. Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nannaɗe su tayi, wasu ta ninka su biyu, a taƙaice kai ka ce bolar wani office ɗin ce. Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar ƙasa da sauran goriba duk a ciki.

Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba.

“Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?” Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Ya sanya hannu ya ɗau littafi ɗaya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi ɗaya sai ta yi duk subject ɗin da ta ga dama a ciki.

A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject ɗaya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta faɗuwa shine maths.

Yayi ajiyar zuciya ya ɗaga kai ya kalleta ya ce “Ashe asarar kuɗin tara kawai ake a banza ko? A biya miki kuɗin makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza faɗi ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?”

Ta girgiza masa kai alamar a’a.

“Ƙarya na yi miki kenan? To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result ɗin da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating “

Ras! Gaban ruma ya faɗi “Na shiga uku, dan Allah ka yi haƙuri, zan daina surutun in dinga karatu”.

“Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da daƙiƙanci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko? Oya buɗe Alqur’ani nuna mini a surar da ku ke”

Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke ɗin ba.

Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi ƙafa dubu.

Da haka yaya umar ya ƙwaci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara ɗaukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a ƙafa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai ƙyaleta ta kwanta ba sai wurin ƙarfe ɗaya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.

Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji.

Ya bata litattafan, yayi mata kashedi tare da jadadda mata, idan har ta cigaba da daƙiƙanci, sai ya sa an yi mata repeating.

*********

Zaune take a kan makeken gadonta, ɗakin cike da kayan alatu kai da gani ka sam mai ɗakin ‘yar gata ce.

Ta dunƙule wuri guda a kan gadon, idanunta sun yi jawurr alamar ta sha kuka.

Daga ita sai doguwar riga ‘yar kanti, kanta babu ɗan kwali, kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin matsananciyar damuwa.

Turo ƙofar ɗakin aka yi, wata babbar mace ce ta shigo ɗakin, idonta sanye da farin gilashi, hannunta riƙe da tray da cup.

Cikin tausayawa ta kalli yarinyar, ta ɗan girgiza kai, ta ƙarasa ta ajiye trayn, ta rungumota tana faɗin “Haba Iman ɗina, shikenan rayuwa bawa ba zai jurewa ƙaddara ba? So ki ke ciwona nima ya tashi?”

Iman ta girgiza kai, hawaye na cika idanunta.

“To Meyasa zaki takura kan ki, haka Allah ya so dama, ai dama tun farko biyayya ce zaki yi mini, kuma Allah bai yi yiwuwar abun ba, amma ki yi haƙuri kin ji babyna”

Ta jinjina kai lokacin da take sake kwantar da kanta a jikin matar.

Ta ɗakko tea a kofa tana bawa Iman a baki, tana sha tana share hawaye, kai da gani ka san akwai tsantsar soyayya da ƙauna a tsakanin su. Ta gama bata tea a baki, ta dinga shafa gashin ta, tana yi mata nasiha.

**********

Mama ta mayar da hankali sosai a kan ibada, mutane na ta shirin zuwan watan ramadan, mama tana ta azumi ita da su yayyen ruma, amma ban da hajiya ruma da cin abincinta ne kawai ya dameta.

Yanzu haka ta cinye taliya, ba ta ƙoshi ba, ta kwaɗa garin kwaki ta zauna tana ci.

Yasir sai masifa yake mata, wai shegen ci ne da ita kamar akuyar ƙauye, ko saurarensa ba ta yi ba ta cigaba da tura abincinta.

Mama ta kalleta ta ce “Wai ke ruma, ko zuciya ba zaki yi ba, azumin nan da kowa yake yi na neman lada ko guda ɗaya ki gwada ba?”

Ɗan ɓata fuska tayi ta ce “Mama ni sai Allah ya kaimu watan ramadan, idan na fara azumi tun yanzu, ai ramewa zan yi kan salla”

“Ke ta ramewa ki ke, dan ubanki ina nuna miki ibada amma ke ba kya so”

Shiru ta yiwa mama tana cigaba da danƙarar garin kwakinta, dan ba ta ji za ta iya wannan azumin ba, idan na du gari ya zo dai ta jarraba.

Bisa ga jajircewar yaya Umar, aka samu ruma take ɗan taɓuka abin arziki a makarantar islamiyya, shima ba wani sosai ba, dan sam ba ta bayar da hadda, tana iya ƙoƙarin ta ko ba duka ba, ta ɗan iya karatun da aka biya musu, saboda idan yaya umar ya titsiyeya ta ɗan samu abin karanta masa dan ya bari ta yi barci, idan kuwa ba baka ba ta san sauran.

Yau ana can ana sallar la’asar, ruma tana zaune tana shan mangwaron ta, tuni ta yi sallarta a cewarta ba za ta iya bin jam’in nan ba, tun tana tsayuwa sai jiri ya fara kwasarta ba za ayi a idar ba.

Ta gama shan mangwaronta, ta tafi wurin alwala wanke hannu.

A wurin alwalar akwai yaran da suma ba sa sallar, suke ta wasan su.

Babu tsammani, ruma ta ji an zuba mata bulala. Tamkar wadda ta fita hayyacinta, haka ta tashi a gigice, tana duba wanda yayi mata wannan ɗanyen aiki haka.

Wani prefect ta hango, bayan ya zuba mata bulalar ya tafi kora sauran yaran da bulala.

Cikin kiɗimewa, ta ɗauki ƙatuwar buta guda ɗaya, ta bishi a guje tana ihu, ta dinga watsa masa ruwan. Ya waiwayo ya tsaya yana kallonta, ta ga hakan bai mata ba ta dinga ƙwala masa butar, daga ƙarshe ta durƙusa ta ɗibi ƙasa tana watsa masa tana kuka.

Tamkar soko, haka ya tsaya yana kallonta, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya kasa, balle ya kare kansa.

An idar da salla kenan, hankali ya fara dawowa kan in da kukan rumaisa ke tashi, bayan ta gama ɓata masa jiki da ruwa da ƙasa a gogaggen uniform ɗin sa, ta haɗa hannayenta biyu tana yakushinsa gami da kai masa duka.

Da ƙyar wani malami ya ɓanɓareta daga jikin matashin yaron, wanda ba dan ya girmeta ba, kuma babu dutse to babu abin da zai hana ta fasa masa kai da dutse, dan ba ta ga laifin da ta aikata zai zuba mata wannan bulalar ba.

Malamin ya dubi ruma ya ce “Meyasa ki ka yi masa haka? Meye haka ki ka yi?”

Cikin kuka ta ce “Dukana ya yi babu abin da na yi masa, wanke hannuna kawai nake yi shine ya dake ni, kuma wallahi ban yafe ba”. Har ta gama maganar kuka take yi, jikinta yana rawa.

Yayin da hankalin ɗaliban duk ya dawo kan su ruma, da jikin Auwal da ruma ta duƙunƙuna masa kamar ya faɗa taɓo.

Haƙuri malamin ya bashi, ya ce ya je ya wanke jikinsa.

Kuka ne kawai auwal bai yi ba, amma ya ji zafin abin da ruma ta yi masa ba kaɗan ba.

Auwal ɗan ajin su Yasir ne, ya san ƙanwar yasir ce, sai dai sam bai taɓa shiga sabgar ruma ba, kuma shi bai ma san ita ce a durƙushe a wurin ba, yayi mamakin ƙarfin hali da kuma tsaurin ido irin na ruma.

Ko da labarin abin da ruma ta aikata ya kai kunnen yasir, haƙuri yayi ta bashi, auwal ya nuna ba komai, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya ƙyale ruma ba sai ya ɗau mataki a kanta.

Babu yadda Yasir bai yi da ita a kan ta ba wa auwal haƙuri, amma mursisi ta ce sai dai ya mutu idan har sai ta bashi haƙuri.

Tun da ruma ta yiwa auwal wannan haukan, sauran prefect ɗin ma tsoron taɓata suke yi, dan sun fi yadda da aljanu ne da ita, saboda tsaurin idonta yayi yawa sosai.

*********

Gaba ɗaya ruma ba ta wani ɗokin zuwan salla, saboda ta san ba ta da kayan salla, mama da gaske ba zata ƙara mata komai na kayan salla ba, ko kayan ado da ake saya mama taƙi sai mata, a cewar mama wannan shine hukuncinta na ƙin jin magana. Ta ji haushi sosai amma ta danne ta cigaba da zuba ido, dan kuwa sallar akwai sauran lokaci.

Yau ta shigo gida daga makarantar boko, da wata takarda a hannunta sai yashe baki take yi.

“Deluwa, murmushin me ki ke yi ne haka, takardar meye a hannunki?”

Kallon banza ta yiwa Huzaifa ta ce “Na gaya maka bana son sunan amma ka ƙi daina gaya mini, sai na maka rashin kunya ace bana ji”

Huzaifa ya ce “Yi mini rashin kunyar, ki gani idan ba ɓarar da ke ba”.

“Hmm haƙuri halin abin ƙaunar mu Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shi ya sa ba zan kula ka ba” girgiza kai yayi yana murmushi, ta cire takalmanta ta shiga ɗakin mama.

Mama ce da Abdallah a zaune a falonta suna hira, yana guga.

Mama ta dubi ruma ta ce “Murmushin me ki ke yi ne?”

Ruma ta ɗagowa mama takarda ta ce “Presentation zan yi a makarantar mu, kowa aka bashi, ni ba a bani ba, na dinga kuka da ƙarfi nace idan ba a bani ba, na daina zuwa makarantar, shi ne fa Headmaster ya ce nima sai an bani, spelling b ne zamu haddace words ɗin nan ɗari biyu da hamsin, zamu yi mu da ‘yan wata makaranta”

“Ai fa kai ba hankali, wai ki ka dinga kuka da ƙarfi ko kunya ba ki ji ba” Abdallah ya faɗa a hasale.

“To ai da ban yi hakan ba, ba zasu bani ba” tayi maganar cikin taɓara.

Mama ta ce “amma dai ba su san ta nawa ki ke zuwa ba ko da suka baki?”

Ruma ta tsuke fuska ta ce “Wato mama ke ma dai daƙiƙiyar zaki ce mini ko?”

Abdallah ya ce “To mecece idan ba daƙiƙiyar ba” gaba ɗaya haushi ya kamata, ba ta kuma kulasu ba ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo ta ce masa an bata spelling b sai su ce ai ba ci za ta yi ba, kada makarantar za ta yi.

Babu wanda ya bata ƙwarin gwiwa, ga yaya Abubakar ya koma makaranta, dama dai yana nan ne shine zai biye mata.

Zaune yake a cikin chemist ɗin, yana jiran mai chemist ya sallame shi, kamar daga sama ta shigo chemist ɗin ta ce “Gashi ka bawa mama maganin ciwon kai” na zai manta wannan muryar ba, ko a mafarki ya ji ta, yana ɗaga kai suka haɗa ido.

Murmushi ta yi masa ta ce “Yaya auwal ina wuni” juyawa ya yi ko da wani take ba da shi ba.

“Baka da lafiya ne?” Tayi maganar tana kallon allurar da mai chemist ɗin yake zuƙewa.

A hankali ya ce “lafiya lau, ya su yasir?”

“Suna nan lafiya, ya jiki?”

Da sauƙi ya bata amsa, yana tuna yadda ta damalmala masa kaya a islamiyya, da yadda yayanta ya rutsata ta bashi haƙuri amma ta ce sai dai ya mutu, ba zata bayar ba, idan suka haɗu a makaranta, sai ta tsaya ta harare shi, har da murguɗa baki, amma wai yau take gaishe shi, har da su yaya bayan ko yayan nata yasir ba ta ce masa yaya.

“Deluwa wannan hamsin ɗin taki za ta karɓuwa kuwa?” Cewar mai chemist.

“Awaisu mai chemist, duk ranar da na tashi jajjaga maka rashin mutunci, a kan kirana da deluwa, sai ka yi kuka” ta faɗa very serious.

Dariya ya yi ya ce “Ke, ai ko ban kai sa’an ‘yan biyun gidanku ba, na san na girmi Aliyu, amma ni zaki saka kuka?”

“To shikenan, ka cigaba zaka gani, bani maganina na tafi”

Bayan ya bata maganin ta kalli auwal ta ce “Yaya auwal, Allah ya ƙara lafiya” tana gama maganar ya fita tana tsalle kamar kwaɗuwa.

Tun da ga ranar da suka haɗu da auwal a chemist, kullum ta ganshi a makaranta sai ta gaishe shi, duk da baya sakar mata fuska idan zai amsa, amma bai sanya ta daina ba.

****

Ɗaya ga watan ramadan, bayan gari ya ɗauka an ga wata, mutane na ta shirin ɗaukar azumi, da asuba mama ta tashi kowa sahur, amma da ƙyar ruma ta tashi ta yi sahur, saboda nauyin bacci.

Ranar ɗaya ga azumin ya kama asabar ce, ruma ta ce gaskiya ba zata iya zuwa islamiyya ba, tun ƙarfe goma take jin kamar zata mutu.

Wajen ƙarfe sha biyu na rana, ta dinga yiwa mama kuka tana burgima wai hanjinta na gutsutstsurewa ita fa mutuwa zata yi.

Aliyu ya ce ‘mama dan Allah ki ƙyake yarinyar nan, tun da ba zata yi ba ta je ta ƙarata”.

“Aikuwa sai ta yi, idan ya wajaba a kan ta wa zai mata?”

“Mama ki bari ua wajaban sai ta yi, kalli fa kamar zata rasu”

Mama ta ce ruma ba zata karya azumi ba, mama tana can tana salla, ya kandamowa ruma ruwa ta sha ta karya azumi.

Sai da mama tayi kamar ta zane Aliyu dan takaici, a ganinta sangartar ruma ta yi yawa.

Abu kamar wasa, ruma taƙi yin azumi, idan ma ta ɗauka ta ji wuya, sai ta karya abin ta, idan aka sha ruwa kuwa tafi uban kowa zaƙewa, daƙyar ska samu ta yi shida, shima Usman ya ce bai yarda da ingancinsu ba. idan aka ce ta je sallar asham kuwa sai ta ce ita wallahi gajiya taje yi da tsaiwa, ƙafafuwanta sai sun fara suɗewa ake ruku’u, nan ma sai bayanta ya kusa karyewa ake ɗagowa ba zata iya ba. mama kuwa ta gaji ta kamata ta zaneta da mafici.

Idan kuwa aka matsa ta je sallar asham, wataran a can cikin yara ake tsintowa mama ruma tana tsalle -tsalle ko dambe a maimakon salla, tilas mama ta hanata zuwa take titsiyeta su yi a gida.

Sai da salla ta gabato, ruma ta sake da tabattar da mama ba zata yi mata wani ɗinkin ba, ta dinga yi wa mama magiya, a kan ta yi mata wasu kayan, amma mama ta ce ba zata yi ba, lokaci ne da zata rama rashin jin da ruman take yi mata.

Gaba daya ɗokin sallar ya fita daga kanta, saboda ba ta son kayan da aka sai mata, gashi sallar bana ko arzikin takalmi da jaka bata samu ba, dan haka ta ce ba zata yi ko kitson salla ba.

Mama ta bata kuɗi ta ce taje ayi mata lalle, dan ba zata yi salla haka ba.

Ruma ta tafi ƙunshi tun safe, sai bayan la’asar ta dawo.

Mama ta kalli lallen nan babu kyan gani, kamar ana saka shi aka ɗauraye.

Kafin mama tayi magana mai lallai ta kira mama, suka gaisa.

Mai lalle ta ce “Mama, wallahi kar ki ga lallen ruma bai yi kyau ba, ana saka mata wai sai an cire ba ta so ta gaji, da na ƙi cire mata, ta cire abinta wai kashi take ji”

Mama ta ce “To shikenan, kar ki damu na gode sosai” ta kalli in da ruma ta tsaya ta ci magani kawai ta jinjina kai ba ta ce mata komai ba.

Tun magariba, ruma taga mama ta kwaɓa lalle kaya guda, ba ta kawo komai a ranta ba, ta cigaba da harkokinta.

Sunanta da mama take kirane, ya sanya ta san asuba ta yi, ta yinƙura zata tashi, ta ji motsin leda a ƙafarta, ta tashi zaune amma ta ga hannunta da ƙafarta duk leda.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, mama me ya sameni?”

“A ina?”

“Wannan ledar mecece?”

Mama ta ce “Ahh, ruma ai ba ke kaɗai ki ka san ta kan tsiya ba, na sai miki kaya ba godiya ki ka raina, na biya kuɗi ayi miki lalle ki ka ƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kina wannan shegen baccin na yi miki dungulmi da shi zaki yi sallar, tsohuwa ta faɗa kwata ba, irin wanda nake yi, kuma kitso ma gidan Hanne zan saka Huzaifa ya kai ki, tayi miki zane huɗu ba dai ba kya ji ba, ai daidai nake da ke, ina sane nake kawar miki da kai”.

Ruma ta kalli yadda aka ƙunshe mata ƙafa har ƙwauri, ga hannayenta kuma ana batun ayi mata zanen Hausa guda huɗu a ka tayi salla, ta tuna uwar rigar da zata saka a matsayin kayan ssllarta, ta ɗora hannu a ka ta zunduma ihu.

DAN ALLAH MASU NEMA DAGA FARKO KU DINGA TAMBAYA A GROUP KO DUBA WATPAD KO AREWABOOKS NA GODE

*TAƘABBALALLAHU MINNA WA MINKUM, INA TAYA AL’UMMAR MUSULMI BARKA DA BABBAR SALLA, UBANGIJI ALLAH YA KARƁI IBADUNMU YA MAIMAITA MANA*

P8

Da rige-rige Usman da Abdallah suka shigo ɗakin, suna tambayar meyafaru da ruma take wannan uban ihun.

Kallonta Usman ya yi, ya kalli mama ya ce “Mama meya sameta ne?”

Mama ta ce “Ku tambayeta mana, ba gata nan a zaune ba”

Abdallah ya ce “Ke menene?”

Nuna masa hannunta ta yi, tana sake fashewa da wani uban kukan.

“Wannan ledar ta meye haka a hannunki, kamar wata miskiniya”

Ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka iya ƙarfinta.

“Dalla ki rufewa mutane baki, kiyi mana bayanin menene?” Usman ya daka mata tsawa.

“Ba mama ce ba”

“Me maman tayi?”

“Ta yi mini lallen tsofaffi wai tsohuwa ta faɗa kwata ina bacci, wallahi dariya za ayi mini idan aka ganni da shi”.

“Kuma saboda baki da mutunci, ki ke mana wannan uban ihun da Asubar nan, ke dai ba zaki yi hankali ba ko?”

“Wallahi mama ba ta sona, ban san meyasa ta tsaneni ba, wayyo Allah na”

Abdallah ya ce “Allah ya ƙara, a wannan shegen baccin naki, har aka yi miki lallen baki sani ba”.

Mama ta ce “Ki tashi ki kwance lallen nan kiyi salla”.

Ko motsi ruma ba ta yi ba balle ta tashi.

Abdallah ya ce “Wai wane irin lalle ne tsohuwa ta faɗa kwatar ne?”

Cikin kuka ruma ta ce “Irin fa wanda mama take yi a ƙafarta”

Dariya ce ta ƙwacewa Abdallah, ya ce “Haba mama, ya zaki yi mana haka?”

Mama ta ce “Hukunta ta nayi, duk rashin jin da take yi ba ta zaci ina da hanyar hukunta ta ba, na bada kuɗi ayi mata abin arziki na zamani, amma taƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kuma ajima da kaina zan kai ki kitso zane huɗu za ayi miki”.

Sosai ruma take kuka, Usman kuwa ficewa yayi ya cigaba da sabgarsa, Abdallah ne ya kaita bakin rariya, ya tayata ya cire ta wanke, aikuwa hannunnan yayi jawur, lalle ya kwanta ɗoɗar hannunta da ƙafarta.

Da gari yayi haske kuwa, Huzaifa ya ga lallen rumaisa, ya zauna ya sakata a gaba ya dinga yi mata dariya, har da kifawa, wai hannunta kamar kuturwa.

Ko Abincin safe ruma ba ta ci ba, sai kuka da goge hawaye, wajen ƙarfe goma na safe, mama ta sakata a gaba zuwa gidan kitso.

Kamar yadda mama ta faɗa, kitson hannu biyu aka yiwa ruma, gashi ta sha azaba a wurin mai kitson, saboda da ta ƙi tsayawa, mama na dukanta, matar kuma ta matse mata kai a tsakanin cinyoyinta, ga kitson azabar zafi tamkar za a zaro ƙwaƙwalwarta saboda yadda matar ke jan gashin.

Ko da aka gama kitson, ruma ta haɗa gumi ga hawaye da majina saboda azabar zafi, mama ta sakata a gaba suka tafi gida.

Ruma da ta kalli hannunta ranta yake ɓaci, saboda hannun ganinsa take kamar ba nata ba.

Har ana gobe salla ruma bata farin ciki, ji take ina ma ace an fasa sallar idi wannan shekarar, saboda wannan yankan ƙauna da mama tayi mata.

Har bata son a aiketa, dan idan ta fita ta ga yara sun sha kitso da ƙunshi, sai ta yi kuka, saboda yadda ta ƙarfi ita aka mayar da ita zamanin mutanen da.

Yanzu haka tana tafe a hanya, zuwa aiken da mama tayi mata, ta gaji da tafiya ga ɓacin rai, ta samu wuri tayi zamanta a kan wata baranda, tana share hawaye.

“‘Kukan me ki ke yi ne haka, ba aiken ki aka yi ba?”

Ta ɗaga kai taga mai maganar, Auwal ne, na makarantar islamiyya da ta yiwa bori rannan.

Shiru tayi masa tana tura baki.

“Meyasa ki ke kuka?”

Miƙewa ta yi tsaye tana faɗin ‘Babu komai”

Ya ɗan girgiza kai ya ce “Ina Yasir?”

Cikin ƙunƙuni ta ce masa bata sani ba, tayi wucewarta.

Mamaki ne ya kama shi, duk in da ta ganshi ko ba zai kulata ba, sai ta yi masa magana, amma yau tayi masa wulaƙanci.

Aiken da bai fi tayi shi a mintuna ashirin ba, sai da ta shafe awa biyu da rabi, ta koma gida Aliyu sai da ya murɗe mata kunne, saboda yadda ta je ta daɗe.

Da safiyar salla kuwa, an kai ruwa rana da hajiya ruma kafin tayi wanka, dan cewa ta yi ba zata je idi ba.

Huzaifa kuwa musamman ya ƙi shiri da wuri, sai ya ga shigar da ruma zata yi yayi mata dariya.

Ta na kuka, mama ta watso mata wannan atamfa da ta zauna ta dinga kushewa.

“Mama dan girman Allah ki barni na saka tsofaffin kayana, wallahi bana son kayan nan”.

“Ni ki ke gayawa ba kya son kayan nan, zaki saka ki wuce ko kuwa?”

Za ta tsaya gardama Aliyu ya yi mata tsawa, ya ce ta ɗau kayan ta saka su wuce sallar idi.

Ga lalle dungulmi, ga kaya ɗinkin mutanen farko, ga kai babu kitso mai kyau, ba yari ba sarƙa  koma kamar ‘yar ƙauye.

Huzaifa kamar ya shiɗe don dariya.

“Yarinya kin yi kyau kamar bafulatanar ƙauye” Yasir ya yi maganar yana dariya.

“Babu ruwanka da ni Yasir, zan maka rashin mutunci wallahi”.

“Na kuma jin bakin ki sai na ɓarara da ke, maza wuce mu tafi” Aliyu yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.

Usman ne ya miƙo mata sabon hijjabi ya ce “Gashi nan ba dan hakinki ba”.

Ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai hijjabin zai taimaka mata ta rufe wannan buhun ɗinkin, tun da hijjabin dogo ne.

Karɓa tayi tana yi masa godiya, ta saka suka tafi idi.

********

“Masha Allah, looking take away my beautiful angel” Ammi ta faɗa tana kallon Iman.

Murmushi iman tayi ta ce “Ammina, an yi salla lafiya”

“Alhamdilillah my dear, ina fatan dai an yi mini Addu’a”

Murmushi ta yi ta ce “Ba dole ba Ammina”

Wata matashiyar budurwa da ke zaune a kan kujera, ta ɗago ta ce “Wai mu Ammi baki ganmu bane?”

“Na ganku mana”

“Ai shikenan Ammi, wannan wariyar launin fata tayi yawa, mu shikenan ba za ki dinga kallanmu ba, sai wannan mai kama da bafulatanar dajin” cewar ɗaya yarinyar.

Ammi ta ce “Kun dai ji kunya, da ku ke kishi da ƙanwarku”

Iman tayi musu gwalo ta ce “Iya wuya dai, nice ta gaban goshin Ammina”

‘Ta mayar da ke ciki, ko a saka ki a zanin goyo a baki Nono, ƙarshen ƙauna”

Ammi ta girgiza kai ta ce”Allah ya shirye ku, Iman ki je ki shirya direba zai kai ki gidan zinariyar Galadima, ki kai musu Abincin salla”.

Ɓata fuska Iman tayi ta ce “Ammi”

Kan ta ƙarasa maganar, Ammi ta ɗora yatsanta a kan lips ɗin ta ta ce “Shhhh, bana son musu, tana ta complain ba kya zuwa” Ɗan gyaɗa kai Iman tayi ta ce “Shikenan Ammi, bari na shirya”

*****

“Ke ba zaki ta so ki fara kai tuwon nan ba”

Ruma ta kwaɓe fuska ta ce “Dan Allah mama ki yi haƙuri, ki bawa su huzaifa su kai wallahi idan na fita dariya za ayi mini”

“Ni nake aiken ki, ki ke cewa na aiki wani ruma, ni ko ruma?”

“A’a mama ba haka bane ba, wallahi dariya yara suke yi mini” tayi maganar hawaye na taruwa a idonta”.

“Tashi ki wuce ki je aiken da aka yi miki” Usman ya daka mata tsawa.

Jiki na rawa ta tashi, ta ɗau kwanukan da mama ta zuba tuwo, ta fara kai wa.

A hanya ta haɗu da wasu ‘yan makarantar bokon su, cikin fara’a ɗayar ta ce “Laa ruma, ya ki ke ina kayan sallar ki?”

Ruma ta kalleta ta ce “Ji masifa, to ba ni da su, ba a ɗinka mini ba”

“Daga tambaya sai masifa?”

“Eh, ina ruwanki da ina kayan salla na, tsirara ki ka ganni?” tayi maganar tana saye hannun ta a cikin hijjabi.

“Kutmelesi, ruma meye wannan a ƙafarki?” Gaba ɗaya suka kalli ƙafar ruma, da take sanye da silifas ɗan madina, ga ƙafa tayi maroon da lalle, kasancewar ruma ba  iya ɗaurin zani ta yi ba, zanin ya ɗage har ƙwaurinta, kuma hijjabin bai gama rufe ƙafar ba.

“Kutmelesi, wane irin lalle aka yi miki, lallai mai lallen nan ta cuceki, kut kamar ƙafar tsohuwa”

Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake leƙa ƙafarta.

Cikin takaici, ta juya zata tafi, amma wata zaƙaƙurar yarinya, ta biyo ruma tana ɗage mata zani.

Mai jiran ƙiris ya samu a sarari, tuni ruma ta yi watsi da kwanuka, ta fara sana’ar ta ta dambe.

Kasancewar a ƙule take dama, ta rasa in da zata sauke fushinta, dan haka ta zage ta kama yarinyar nan ta dinga jibagarta kamar Allah ya aikota.

Suna cikin damben Allah ya bawa yarinyar sa’ar ketawa ruma hijjabi, hakan ya ƙara tunzura ruman, ta danne yarinyar tana duka.

“Wannan yarinya an yi jarababbiya, duk in da ta tsuguna sai dambe, sai ka ce annoba” cewar wani mai awo a gefe, da bai raba su ba sai zance.

Ɗagowa ta yi cikin masifa ta ce “Wallahi ni ba annoba bace ba”

Ta duƙa ta cigaba da dambenta.  ji tayi an yi sama da ita, ta fara kokowar ƙwacewa tana kai duka.

“Zaki nutsu ko sai na kakkarya ki” yaya Aliyu ne ya tsare ta da ido.

“Dama abin da ta aiko ki kenan?” Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai.

“wuce mu tafi, dage uwar faɗa”

Haka ta kwashi kwanukan, da yagaggen hijjabinta a hannu ya tasa ta a gaba, zuwa gida.

Mama na ganin ruma ta shigo tare da Aliyu, a yadda ta shigo kawai mama ta gane halin ta je ta gwada a waje.

“Damben ki ka je ki ka yi kenan ko, mara kintsi?”

Wage baki ruma tayi zata fara yiwa mama bayani, amma mama ta katseta ta ce “Ban tambayeki ba ruma, ki je ji yi tayi, bakin mutane kawai ya ishe ki”

Gefe ta koma ta zauna, tana jin yadda ba ta gamsu da dukan da ta yiwa Hauwwa ba, saboda dariyar da suka yi mata.

Yaya Umar ne ya fito daga ɗakin su, cikin wata dakakkiyar shadda dark blue, ya karya hula sai ƙamshi yake zubawa.

Tsuruu ruma ta yi da ido, tana jiran ya sauke mata masifa, tun da ya ji ance ta yi dambe.

Nufota ya yi, ita kuma ta ƙura masa ido ko ƙiftawa ba ta yi.

Ya kalleta ya ce “Na canza miki ne?”

Ta girgiza kai ta ce “A’a ka yi kyau ne”

Murmushi ya yi, ya miƙa mata leda ya ce “Je ki ka gwada wannan” da sauri ta tashi, ba tare da sanin meye a ciki ba ta karɓa ta shiga ɗaki.

Doguwar riga ce ta shadda kalar kayansa, da mayafi da sabon takalmi da yari da sarƙa.

Ko da ta saka ta fito ba ƙaramin kyau ta yi ba.

“Mama kin ganni, na yi kyau”

Aliyu ya ce “Saboda son kai, shine ku ka yi kaya iri ɗaya babu ko labari”

Cikin tsananin farin ciki ta ce “Yaya Ussy, kalleni dan Allah na yi kyau?”

“Eh to, babu laifi sai ki ka zama kamar budurwa, duk da ƙwaila ce”.

Cikin tsananin farin ciki, ta faɗa jikin yaya Umar tana murna “Yaya na gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi ya sa ka gama da duniya lafiya”

Ganin yadda take murna ya sanya shi yin murmushi na gefen baki ya ce “Allah ya sa ki daina rashin ji”.

“Iyee, lallai mai sunan Baba, ni sai ka haɗani da atamfa kala uku, amma kai da ƙanwarka ka yi muku kaya iri ɗaya, wato an fi son ta a kaina” mama tayi maganar cikin sigar wasa.

Murmushi ya yi, dan ya san halin mama da barkwanci wasu lokutan.

Mama ta shiga ɗaki, ta fito da wata ƙatuwar leda, ta miƙawa ruma ta ce “Gashi nan, ba dan halinki ba, kayayakin da suka yi miki ne, na wannan sallar naƙi nuna miki dan in hora ki”

Rikicewa ruma tayi, dama suna yi mata ɗinke-ɗinke, amma sallar bana bata san sun yi mata ba, dan a ƙalla ta tashi da kaya ku san dozen, banda hijjabai da abun hannu da sauransu.

“Wayyo Allahna, dama kuna so na haka? Duk nawa ne wannan mama kin ga fa duk nawa ne”

Gaba daya suka kewaye ta suna murmushi, ganin yadda ta rikice tana murna.

Bin su ta dinga yi ɗaya bayan ɗaya tana yi musu godiya, tana zuwa kan Huzaifa ya wani maze ya ce ‘Kar ki damu, wannan fa bakomai bane ba, idan har zaki dinga biyayya”.

“Ba zan yi biyayyar ba, na san ma ba uwar da ka saya mini, duk gidan nan waye ya kai ka talauci da son banza?”

“Laaaa, ke fa ba a abin arziki da ke ko?”

“A’a yi haƙuri mama, shi ɗin ne zai ɓata mini rai, yanzu a cigaba da zuzzuba tuwon ina kaiwa, amma wallahi duk in da na san ba za a bani kuɗi ba, sai dai Yasir ko Huzaifa su kai”

Haka tayi ta rabon Abinci cikin annashuwa, gidan da aka bata kuɗi tayi ta murna, idan ba a baya ba tayi ta jin haushi.

********

Ba zata iya ƙayyade rabonta da gidan nan ba, dan haka ta ɗaga kai take ta na kallon sauye-sauyen da aka yi a gidan.

Ya ƙawatu, duk da ginin yana nan a yadda yake, amma an yi wa gidan gyara sosai.

Da haka ta ƙarasa cikin ƙaton falon da ke cikin gidan.

Hadimai ne ke ta kaiwa suna komowa a cikin tangamemen falon, suna aikace-aikace.

Ɗaya daga cikin hadiman ce ta kalli Iman da fara’a ta ce “Maraba da zuwa”.

Iman ta ce “Yauwwa sannunku da aiki, Ummma fa?”.

“Tana cikin turaka, bari ayi miki iso”

Babu jimawa hadimar ta fito, ta kalli Iman ta ce “Bisimillah, ta ce ki shiga”

Bayan hadimar Iman ta bi, zuwa turakar Ummma.

Shigarsu ɗakin ke da wuya, gaban Iman ya faɗi, bisa tozali da mutanen da ba ta son ko haɗa hanya da su, ba dan jinin Ummma bane su, to tabbas da kai tsaye zata iya cewa mutanen da ba ta ƙauna.

Faɗaɗa murmushi Ummma tayi ta ce “Masha Allah, Iman dama talaka na ganinki?”

Murmushin yaƙe iman ta ƙaƙalo, ta durƙusa a kan gwiwoyinta tana gaida Ummma.

Cikin mutuntawa Ummma ta amaa mata, tare da tambayarta ya Ammi.

“Hajiya Iman, manya manyan ‘ya’ya a gidan Galadima, ya kike ya school?” cewar wata matashiya da ke zaune a gefen Ummma.

Ko ba a gaya mata ba, ta san da biyu budurwar ta yi wannan maganar, ta dake ta ce “Lafiya lau Anty Soafy, an yi salla lafiya?”

“Hmm lafiya lau, irin wannan ado haka, Ummma wannan leshin kamar irin sa Khairiyya ta saka ranar kamunta ko?” Tayi maganar tana ƙarewa Iman kallo.

Umma ta ce “Eh irinsa ne”

“Wow, it worth 120k fa, lallai autar gidan Galadima, kin riƙe wuta”.

Iman jin ta take tamkar a kan wuta, dan haka a gurguje ta ce “Ummma dama abincin salla ne, Ammi ta ce na kawo miki, kuma nazo mu gaisa, bari na tafi”.

“Kai Iman tun da wur haka, ke dai ba kya son mutane, shikenan bari na baki barka da salla”.

“A’a Umma, ai na girma da barka da salla” iman tayi maganar tana miƙewa .

“Ƙaniyarki, tsaya ki karɓa mana” girgiza kai iman tayi, ta fice daga ɗakin da sauri.

Har ta kai tsakiyar falon, ta ji an riƙe mata jaka.

Ta waiwayo tana kallon wadda ta riƙeta.

“Duk na san kin ci kin ta da kai, Ammi tana ji dake, na san kina da kuɗi baki rasa komai ba, amma yakamata ki karɓa tun da kin san baki da gado a cikin dukiyar gidan Galadima?”

Cikin rauni Iman ta ce “Anty Soafy me kuma ya kawo wannan maganar?”

Cikin ko in kula Soafy ta ce “Yau aka fara gaya miki irin wannan maganar ne, ai gara a dinga yi ana tuna miki, ko ba haka ba?” Ta fizgi jakar iman, ta saka mata kuɗin, ta saƙala mata jakar a kafaɗarta ta koma ciki.

Gwiwa a saɓule, iman ta nufi fita daga falon, tuni idanunta suka cika da hawaye, sai dai tana fitowa ya sha gabanta, ya ƙureta da idanuwansa.

Ƙoƙarin ratsewa take ta wuce, amma ya ce “Me ta ce miki ne, har ta saka ki kuka?”

Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.

Yayi murmushin gefen baki ya ce “Anyway, kin yi kyau sosai a outfit ɗin nan, ashe yayanki yana Saudiyya babu ko sallama?”.

“Uncle J, am sorry sauri nake, Ammi na jirana” daga haka ta wuce ta bar shi a wurin a tsaye.

**********

Zuwa yamma mama ta saka ruma a gaba sai sa ta cire shaddar nan, dan idan ta bar ruma da ita sai shaddar ta fita daga hayyacinta.

Kwanukan da aka ɓata, Yasir ya tattara yana wankewa, mama ta ce “Ke, shiga ɗakinsu ki dudduba mini idan da kwanukana, cokula ko kofi, duk ki fito mini da su, dan na san hali, sai a kai mini kwano ɗaki a ƙi fito da shi”

Ruma ta tashi ta nufi ɗakin samarin nan, ba tare da ko sallama ba.

Usman ne a kwance yana waya, kuma da alama da mace yake wayar.

Buɗe baki tayi, ta tsaya tana kallonsa. Zumbur ya tashi zaune, ya katse wayar ya ajiye ya haɗe rai ya ce “Zo nan” ba musu ta ƙarasa in da yake.

“Me ki ka ji?”

Ta ce “A ina?”

“Ina tambayarki kina tambayata? Nace me ki ka ji?”

“Wallahi ban ji komai ba, kawai dai na ji ka ce…..” Sai kuma ta yi shiru.

“Ba zaki faɗa ba sai na taka ki?”

Ta tura baki sannan ta ce “Na ji ka ce, wai kwalliyar ta tayi kyau, kamar farin wata”.

“Sai kuma me?”

“Shikenan na ji wallahi “

“To na rantse da girman Allah, idan ki ka sake ki ka faɗa, wallahi sai na yi miki dukan tsiya, ƙanwar abokina ce ba wata ba”

“To ai ni dama ban ce zan faɗa ba, mama ce ta aikoni” daga haka ta shiga duddubawa mama kwanukanta.

Aikuwa ruma ta fito da kwanuka a hannuta tana faɗin mama “Kin ga kofin ki, an sha fura a ciki sha zumamu ya siɗe miki kofi tas, har ɓera ya fara ci. Kin ga plate ɗin ki har da sauran alalar da ki ka yi tun sati biyu da suka wuce”.

Yasir ya ce “To munafuka, uban waye ya saka ki wannan sharhin?”

Mama ta ce”Ai ba ƙarya ta yi ba, ku yi ta kwasar mini kwanuka kuna kaiwa ɗakin ku, sai na bi na tsinto abina, ƙazaman banza kawai”

Mama na tsaka da mitar sai ga Aliyu ya shigo, ya ce “Ina ruma”

Ta ce “Gani”

“Yo sauri, abokaina ne na filin ball suke tambayata kina ina, shi ne suka biyo ku gaisa, saura kiyi wani haukan da zaki zubar mini da mutunci “.

Murmushi ta yi ta ce”A’a ba zan zubar maka da mutunci ba, bari na sako gyalena”

Yana maganar ya fice, Huzaifa ya ce “Mama ke ba a zo gaishe ki ba, sai wannan yarinyar lallai ruma”.

Ta fito daga ɗakin mama da sauri, ta kalli Huzaifa ta ce “Ka yi mini Addu6, Allah ya sa su bani kuɗi” tana gaya masa ta kwasa da gudu ta fita waje.

Da fari gaishe su tayi kamar nutsatsiya, suka amsa mata cikin mutuntawa.

“Ya makaranta ya rikici2?”

Ta ce “Makaranta lafiya ƙalau, amma ni bana rikici” suka din ga jan ruma da hira ita kuma tana zuba, Aliyu sai hararta yake amma ta cigaba da zuba.

Dariya suka dinga yi mata, suka babbata barka da salla, ko ɗan cewa ba zata karɓa ɗin nan ba tayi ba, zuruf ta miƙa hannu ta karɓe tana godiya.

Wani mugun kallo yake wa ruma, amma ko saurararsa ba tayi ba.

Ta duba a cikin kuɗin da aka bata, akwai ɗari biyu da ta tsufa sosai, ta kalli wanda ya bata ya ce “Ɗan uwanmu ɗan canza mini wannan, ba zata karɓu ba” buɗe baki Aliyu ya yi yana bin ruma da kallo.

Aikuwa ya karɓa ya canza mata wata, ta ce ta gode ta shige gida.

“Mama kin ga abokan yaya Aliyu sun bani, kuma sun ce suna gaishe ki”

Mama ta ce “To madalla”

“Mama gashi ki ajiye mini, ki ɗora da lissafi, idan kin manta ni ina sane da lissafin, dan Allah mama kar na zo karɓar kuɗina ki fara ce mini, abubuwan da ki ke mini ba da kuɗina ki ke yi mini ba, wallahi mama da za ayi lissafi ban san iya adadin kuɗin da nake bin ki ba”

Cikin gatse mama ta ce “To Anty ruma, ki zauna ki lissafa duk kuɗin da ki ke bina, na biyaki”

“Dan Allah mama da gaske ki ke?”

“Eh mana” murna ta dinga yi tana cewa ‘Ai mama kuɗin da nake binki, sai ma zauna musamman na yi lissafi, tsaf sai na zama attajira da kuɗin nan, unguwar da muke zuwa a bani kuɗi ai da yawa”

Yasir ya ce “Ba zaki taɓa hankali ba”.

Aliyu ne ya shigo rai a ɓace yana hararar ruma.

Kawar da kanta tayi gefe taƙi kallonsa.

“Dole ki kawar da kai mana, yarinyar nan ana bata kuɗi ta karɓe, wai har da cewa wai wata ba zata karɓu ba, da yake ke ki ka basu ajiya”

“Yaya ba kyau mayar da hannun kyauta baya fa”

“Zaki mini shiru, ko sai na mareki, mara kai kawai”

A ranta ta ce “Ohoo dai, tun da Allah ya sa na karɓa”.

Bayan sallar isha’i yaya Umar ya dawo, duk sun daddawo suna gida, ana ta hira.

Ruma tayi gyaran murya, ta kalli Yaya Usman ta ce “Mama kin san me?”

Mama ta ce “A’a”.

Usman ya zubo mata ido, kowa ya yi shiru yana sauraron wani shirmen zata faɗa.

P9

Wani irin kallo Usman yake mata, amma ta basar ta ce “Mama kin san me yaya Usman ya yi?”

Mama ta ce “A a sai kin faɗa”

Usman ya ce”Haka muka yi da ke ruma?”

“Oho ni dai bana munafurci da rashin gaskiya, duk abin da aka yi mama bata nan sai na gaya mata, ba zan ga ana ba dai-dai ba mama bata sani ba na yi shiru”.

Kamar ya yi kuka ya ce”Amma haka muka yi da ke?”

Mama ta ce “Gaya mini ina jin ki”

Ruma ta kalli Usman ta ce “Sai dai ka yi haƙuri fa, amma wallahi sai na faɗa a gaban kowa da kowa, ba zan zuba ido ana abin da ba dai-dai ba”

Ba dan ya san idan ya yinƙura zai yi mata wani abu mama zata hana ba, da sai ya kife Ruma da mari, ya san idan ta ɗaga maganar nan akwai damuwa, zai sha faɗa da mita.

Uwa uba ga Yaya Umar a zaune a wurin, kuma ba shi da tabbacin iya abin da ruma ta gaya masa ta ji, shi kaɗai ɗin ta ji, dan kawai ɗaga kai ya yi ya ganta a tsaye lokacin da yake wayar.

Ta gyara zamanta sannan ta ce “Ɗazu, da ki ka aikeni kai tuwo gidan mai ƙuli, na ganshi a ƙofar gidan su wannan abokin nasa Yahaya, shi da abokansa sun dawo daga idi, ko gida ba su zo ba, ya zauna an fito da abinci sun haɗu suna ci, kuma kin hana hakan”

Ajiyar zuciya ya yi, yana hamdala da ba wancan zancen ta yi ba.

Mama ta ce “To wannan abun ne ki ke ta zuzutawa, ai shima ya zo ya ɗau abinci ya fita da shi sun ci tare”

“To mama sai aka ce ya je ya zauna a ƙofar gida yana cin abinci ai rashin kamun kai ne, kuma ke ki ka ce rashin kamun kai ne fa”.

Mama ta ce “To shikenan, za a yi masa faɗa”.

“To mama kiyi masa faɗan mana yanzu”

A fusace ya ce “Ke wai ni sa’an ki ne?”

Umar ya ce “Maganinku kenan da ku ke wasa da ita”

Can ta sake gyara zama ta kalli mama ta ce “Mama, kin san wani abu?”

“Ke na gaji da wannan shirmen naki fa” mama ta faɗa cikin ƙosawa.

“Mama ba shirme zan ba, ɗazu na ga Habiba a masallacin idi, da tsofaffin kaya na ganta”.

“To ina ruwanki? Kin ga ina rabaki da sabgar munafurci amma ba zaki dai na ba ko?”

Jiki a sanyaye ruma ta girgiza kai ta ce “Mama so nake a bata kaya ɗaya a cikin kayana” gaba ɗaya juyowa suka yi suna kallon ta jin abin da ta ce.

Huzaifa ya ce “Kina da hankali kuwa?”

“Amma dai ka san tun da nake ni ba mahaukaciya ba ce ko? Mama dan Allah a bata ita ma ta saka sabon kaya”

“Rufewa mutane baki, mara zuciya nan babarta ta zo ta ciwa mutane mutunci, amma ki ka cigaba da shishshige mata, ba za a bayar ba ɗin” Aliyu ya faɗa yana zaro ido.

Mama ta girgiza masa kai, ta dubi ruma ta ce “Allah ya kaimu gobe, sai ki zaɓi wanda zaki batan”

Murmushi ruma ta yi ta ce “Na gode mama, Allah ya saka da alkhairi, to zaki ɗan zuba mini naman kazar ita ma na kai mata ta ci, na san su basu yanka kaza ba”.

Yasir ya ce “Dama ta yaya zasu yanka, wannan babar ta su tana kiwon kaji kamar su kasheta, amma ba zata yanka su ci ba, bayan talauci har da son zuciya”

“Ka daina zagar mini babar ƙawa dan Allah”

Mama ta ce “Kin ga, tashi ki wuce ki je ki kwanta”

Ta miƙe ta shige ɗaki, mama ta mayar da idonta kan Aliyu ta ce “Aliyu, kar ku hora yarinyar nan a kan halin rowa, duk rashin jin ta tana da tausayi da son taimako, idan har abin da za ta yi bai saɓawa shari’a ba ku ƙyaleta”

Aliyu ya jinjina kai. Ruma kuwa ji take kamar ta janyo washegari, ta kai wa habiba wannan kayan, ita ma ta saka ta ji daɗi.

Washegari da wuri ruma ta yi wanka, ta yi kwalliyar salla da ɗaya daga cikin kayanta, ta zauna ta ɗaukarwa Habiba set ɗaya na atamfa har da ribbon da abin hannu.

Mama bata hanata ba, ta ƙulle mata nama ta bata ta kai wa Habiban.

Har zata ɗauka ta fita, ta tsaya ta ce “Mama, dan Allah idan ta yi kwalliyar zamu je gidan ‘yan ajinmu mu yi wasa”.

Mama ta ɗan ɓata fuska ta ce “Amma dai kin san babna son wannan abun ko, ba na son yawace-yawace”

Ta ɗan marairaice ta ce “Dan Allah mama, kin san bana yawo, daga aike sai makaranta, yanzu fa salla ce”.

“Shikenan, na ji, saura kuma ki je ki zauna sai an nemo ki, ina da ina zaku je?”

Ruma ta lissafa mata, mama ta yi ajiyar zuciya ta ce”Yanzu ƙarfe goma da rabi, kar ki wuce sha biyu, idan ki ka wuce abin da zai zo biyo baya ba zai yi miki daɗi ba”.

Cikin murna ta ce “Mama da wuri zan dawo in sha Allah ” ta yi waje ta na murmushi.

Kai tsaye gidansu Habiba ta nufa, ko da ta je ta yi ta sallama, shiru ba a amsa ba.

Tsayawa ta yi a tsakar gidan ta cigaba da sallama.

Sani ne ya leƙo yana amsawa, yana ganin ruma yayi saroro ya ce “Ke uban me ki ka zo yi mana a gida?”

Hararsa ta yi ta ce “To ina ruwanka ai ba wurinka na zo ba, ba yayana yayi maka tsakani da ni ba, babu ni babu ba, ko kuma na kira shi, ya zo ya ƙara kumbura maka fuska”

Tana tsaka da maganar, sai ga babar Habiba ta fito daga banɗaki, tana ganin ruma ta tsuke fuska ta ce”Ke me ki ka zo yi mini a gida?”

“Gurin Habiba na zo”

“Da izinin wa ki ka zo wurin Habiban?”

Habiba ce ta fito daga ɗaki, hannunta riƙe da kwanon tuwo da miyar kuka, tana ganin ruma ta ce “Laaa ruma, kin dai na zuwa makarantar allo “

Ruma ta ce “Ba na ganki a masallacin idi ba ki ka ƙi kulani”

Habiba ta ce “Wallahi ruma ban ganki bane ba? Ya salla?”

“Lafiya lau, wurin ki na zo, zo ki ji?”

Mamaki ya cika babar su Habiba, ta riƙe haɓa ta ce “Habiba, wato cigaba da shiga sabgar yarinyar nan ki ka yi ko?”

Habiba ta girgiza kai ta ce “Wallahi Ummanmu ba kulata nake yi ba, na daɗe ma bamu haɗu ba”.

Ruma ta miƙowa Habiba leda ta ce “Kawo miki na yi, ki zo ki karɓa ki gani”

Babu musu ta ƙarasa ta karɓi ledar, taga ɗinkakkiyar atamfa ga abin hannu da ribbon, sai kuma ƙullin nama.

Habiba ta ce “Ruma wannan na waye?”

“Naki ne, in gaya miki, kayan salla na  kala goma sha biyu da hijjabai, har da abin hannu da sarƙa, shine na ce bari na kawo miki ɗaya, ki saka mu je yawon salla”.

Babar su Habiba ta ce “Ba ta so ba zata karɓa ba, bana son shishshigi, ba ta kayanta ce muku aka yi tana buƙata? Ita ma tana da kayan salla”

Idon Habiba ya cika da hawaye ta ce “Wallahi Umma bani da kayan salla, ina son kayan dan Allah ki bar ni na saka”.

Ruma ta ce “Dan Allah Umma ki bari ta saka, mun shirya ai mun dai na faɗa, dan Allah ki bari ta saka”

Umma ta kalli yadda Habiba ta rungume kaya tana kuka, wai tana so, haka ta ƙyaleta. Habiba ta shiga ɗaki ta saka kayan, aikuwa tamkar dan ita aka ɗinka su suka yi mata kyau.

Sani ya din ga ce wa habiba mara zuciya.

Abin ka da ƙuruciya, tuni habiba ta shirya a cikin kayan, duk da babar Habiba na jin haushin ruma, hakan bai hanata rawar jiki wurin raba naman kazar da ruma ta kawo ba, fan kuwa an daɗe ba a haɗu ba.

Daga haka suka fita nasu yawo.

Tamkar awakai haka suka dinga yawo, kusfa kusfa gidajen ƙawayensu, wasu a haɗu a rabu da su ƙalau, wasu kuma a ƙare da faɗa. Ruma ba ta tashi tuna kashedin mama ba, sai bayan azahar tana ta gararanbarta a gari.

A suwkane ta nufo gida, tana ta tunanin yadda za ta kare kanta a wurin mama, dan ta san zuwa yanzu ana can ana nemanta kamar kuɗin guziri.

Yaya Usman ta hango a tsaye a jikin wata mota, ya sha kwalliya, shi da abokansa, da alama fita za su yi.

Da gudu ta ƙarasa in da yake tsaye ta ce “Yaya ussy, me ka ke yi a nan?”

“Ban sani ba, wuce ki tafi gida, ki kai aiken da aka yi miki” abin da ya faɗa ne ya sanya ta fuskanci kamar mama ba ta neme ta ba, dan haka ta ce “Dan Allah ina zaka?”.

“Zamu ɗan fita chilling ne”

“Meye chilling kuma?”

Ya haɗe rai ya ce “Cewa na yi fa ki tafi gida ko?”

“Dan Allah ka yi haƙuri, zan bika dan Allah”

“Ke wai ni sa’an wasanki ne? Ba zaki wuce ki tafi gida ba?”

Ta sake marairaice wa ta ce “Dan Allah Yaya”

Riƙe rigarsa tayi tana kallonsa kamar za ta yi kuka. Tunawa ya yi da haushin ƙin tafiya da ita zai iya sanyawa ta tona masa asiri.

Yayi ƙasa da murya ya ce “To ki je ki tambayo mama, idan ta yarda sai mu tafi”

“Wallahi na san idan na tafi, tafiya zaka yi”

“Shegiya sai ka ce mayya, idan na tafi da ke a ina zan saka ki motar ba space” yayi maganar a ƙule.

“Sai na zauna a cinyarka” duk yadda ya so ya yakice ruma, taƙi ta nace, gashi ya san zai sha kunya, idan har ruma ta tona masa asirin yana waya da budurwa, dan ya san sai dai ya kasheta bayan ta faɗa zare idonsa ba zai hanata faɗar abin da ta yi niyya ba.

Haka ya sakata a motar, dama ta abokinsu ce, ita kaɗai a cikin maza, sai zaginta yake, amma ko a jikinta, ya sakata a gefensa.

Abokansa sai dariya suke masa, suna “Ka ga Ƙanwar maza, suke mulkin amma dole a biki ko ba a so” ba wanda ta kula a cikinsu suka tafi.

Wurin shaƙatawa suka je, duk abin da suka ci sai da suka sayawa ruma ita ma ta ci, da ta ji ta ƙoshi ta kalli Usman ta ce “Yaya ussy, a samo leda a ɗaure mini sauran na tafi da shi gida”

“Saboda kowa ma bashi da hankali kamar ke? Wallahi baki isa ba” ba dan ya ji daɗin fitar ba, ya azalzali abokansa suka koma gida, saboda yadda ruman ke ta zubar masa da mutunci a idon abokansa.

Ko da suka je gida, mama a kiɗime take, tun sha biyu ake nemanta ba a ganta ba.

Bin su da kallo mama ta yi, ta dubi Usman ta ce “A ina ka ganota?”

“Nima a hanya na ganta bayan la’asar, zamu fita da abokaina, ta nace sai ta bini, na kira Aliyu a waya na gaya masa muka tafi da ita”.

“Ku ka je ina?”

“Wurin wani cin abinci ne, ni da su Isma’il ne”

“Kuma ita kaɗai a cikin maza Usman, ka san tun yaushe yarinyar nan ba ta gidan nan, ka ga tashin hankalin da na shiga kuwa? Wallahi yau sai kin ci ubanki”

Abdallah ya ce “Wallahi mama ko ba ki daketa ba, sai na zaneta yau, ki yi mata bugun shekararriyar dawa, yarinyar nan ta ci a bata gado a Asibitin mahaukata”.

Mama a tsananin fusace ta janyo ruma, ta din ga turjewa tana ihu, mama ta zaro bulugari ta dinga bugunta da shi tana kurma ihu tana neman taimako.

Mama ba ta saba tarbiyya da duka ba, amma idan ta kai bango jikin mutum yana gaya masa, sai da Usman ya ƙwaci ruma da ƙyar a hannun mama.

Tun daga ranar, mama ta ce ba zata bata sauran kayan sallar baz gashi an aiko mata da kayan salla daga can garin su, ga dangin mahaifin su ma, sun ɗinko mata kaya, sun aiko mata da su, duk mama ta ce ba zata sake sakawa ba ta gama kwalliyar salla.

Washegari ta na ji ta na gani mama ta shirya, ta tafi cikin gari, ta bar ruma a gida.

Gidan duk ya yi mata babu daɗi, sai faɗace-faɗace take da su Yasir.

Suka gama suka fice suka bar ta a gidan. Ta ji babu daɗi rashin tafiya da ita da mama ba ta yi ba, gaji da zama ta tashi tana neman abun yi.

Ɗakin ‘yan mazan ta shiga, ta fara gyara musu ta ci karo da shaddar yaya Umar ya saƙaleta.

Wani tunani ta yi, ta kwaso shaddar ta fito da ita tsakar gida. Ta zuba ruwa a bokiti ta tuttula omo ta zunduma shaddar nan a ciki, ta koma ta cigaba aikin gyaran ɗakin.

A ƙalla shaddar nan ta kai awa biyu a ruwa, ruma ta fito ta jagwalgwala ta shanya. Ai kuwa shaddar nan gaba ɗaya ta daina wannan shining ɗin da take yi saboda azabar omo.

Aka jima, ya haɗa wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.

Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta duƙufa tana guga.

Ya tsaya yana ƙoƙarin gane me take gogewa.

“Wai meye wannan ki ke gogewa haka?”

Ta ɗago ta kalleshi ta ce “Kayan yaya Umar ne, na ga ya saƙale su a ɗaki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa”.

Abdallah ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?”

“To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?”

“Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?” Ai suna cikin maganar ruma ta ƙone gaban rigar.

Dafe kai ta yi ta ce “Innalillahi, na shiga uku, Abdallah ya zan yi na ƙona masa shadda?”

Abdallah ya ce “Maganinki shegen karambani, kya san mai zaki gaya masa”

Hannu ruma ta ɗora a ka ta dinga kuka, dan ta san yau kashinta ya bushe, sai yadda Allah ya yi da ita.

Haka mama ta dawo ta tarar da ita, tana ta uban kuka, Abdallah ya gaya mata abin da ta aikata.

Cikin kuka ruma ta ce “Dan Allah mama ki bashi haƙuri, yau na san na mutu wallahi, dan Allah mama kar ki bari ya dakeni ko ya saka ni punishing”.

“Ba ruwana, ai nima ba jin maganata ki ke yi ba”.

Abu kamar wasa, har bayan la’asar ruma ba ta ci ko Abincin rana ba, sai kuka take yi.

Huzaifa ya ce “Ni ne mutum na farko da zai sanar da mai sunan Baba wannan taɓargaza da ki ka aikata masa”

Duk da mama a ƙule take da ita a kan laifin da ta yi mata jiya, amma hakan bai hanata saka ruma ta ci abinci ba, amma ruma taƙi ci sai aikin kuka. Ita kanta mama na tausayawa ruma hukuncin da zata fuskanta a wurin Umar idan ya dawo ya tarar da ɓarna da ta aikata masa, sai dai ita ta janyo kanta, rashin jin ta ya yi yawa.

Mai sunan Baba bai dawo ba sai bayan sallar magariba, tun da ya shigo ta sake takurewa tana uban kuka.

Ya dube ta, cikin kakkausar muryarsa ya ce “Kukan me ki ke yi?”

Huzaifa ya gyara zama, ya wassafa masa ɓarnar da ta aikata.

Duk da babu isasshen haske a tsakar gidan, ta tsorata da kallon da ya yi mata.

“Dan Allah yaya ka yi haƙuri, ba a son raina na aikata hakan ba, wallahi kawai niyyata na baka mamaki, na wanke maka na goge maka ban san haka abin zai zama ba”

Kalmar ta bashi mamaki sai da ta saka Aliyu dariya, ya ce “Lallai kin bashi mamaki kam”

Yadda ta firgice ne, ya sanya Yasir ya ce “Dan Allah yaya ka yi haƙuri, kuskure ne, tun da tsautsayin nan ya faru ba ta ci Abinci ba”

“Zaka ɗau hukuncin da zan yi mata kenan?” Yayi maganar ba tare da ya kalli Yasir ba.

Yasir ya ce “Eh ni ka hukunta ni a madadinta, a tsorace take”

A ɗan tsawace ya ce “Tashi ki ɗauko mini kayan na gani”

Sumi-sumi ta tashi ta je ta ɗauko kayan, ta miƙa masa.

Ya karɓa ya duba, gaba ɗaya kayan sun tashi daga aiki, jikinta sai rawa yake yi.

“Tun da ki ke na taɓa saka ki wanki?” Ta girgiza kai.

“To Meyasa ki ka wanke nawa kayan?”

“So nake nima na yi abin arziki, ban zaci zai zama na tsiya ba”

Ya girgiza kai ya ce “Zubo mini Abinci” ta tashi tana ta tsuma, ta je ta zubo abinci ta kawo masa tana kallonsa.

Ya karɓi Abincin, ya ajiye a gabanta ya ce “Ci Abinci”

Fuska duk hawaye ta ce “Dan Allah ba zaka saka ni kama kunne ba?”

Ya girgiza mata kai ya ce “Ba zan saka ki ba” yayi maganar yana ɗebo Abincin ya kai bakinta.

“To ka haƙura?” Ya jinjina mata kai alamar eh.

“To dan Allah ka yi haƙuri, tsautsayi ne”

“To, ci abinci” sai a lokacin ta ji ranta ya yi sanyi, har ta fara cin abinci, babu wanda bai yi mamakin yadda mai sunan Baba ya ƙyale ruma ba, basu taɓa kawo zai rabu da ita ba.

Sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta ce “Me sunan Baba”

“Na’am”

‘Dan Allah ka yi haƙuri, zan karɓi kuɗina na wurin mama sai na saya maka wata “murmushin gefen baki ya yi ya ce ‘To Shikenan”.

Bayan yaya Umar ya fita, Huzaifa ya lallaɓa ya bi ruma ɗaki yana cewa “Ruma, wace addu’a ki ka yiwa mai sunan Baba ya ƙyale ki ne? Zo ki gaya mini”

Usman ya ce “Wallahi nima na yi mamaki duk ɓarnar nan da ta yi masa ya ƙyaleta”

Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.

Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ƙi zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu ɗan mai makarantar ta liƙewa, duk ajin da za shi ya yi ƙari sai ta bishi, gashi ta maƙalewa Auwal, yaya sama yaya ƙasa haka take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.

Yanzu ma ‘yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ƙarin Alqur’ani, sai ga shi ya shigo shi da ruma.

Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata zuwa ajinsu, amma sai gata.

Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu kamar gaske aka yi ƙarin nan aka idar.

Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi ‘Inyee ashe ka na ja, hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na faɗa a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba”

Dariya ‘yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.

Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce “Malam nima zan karanta”

Ya ce “To bisimillah”

Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai shafi guda, ba ƙaramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.

Ɗari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja ba.

Da ya kammala ƙarin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya haɗe rai ta ce “Malam ni ka bar ni a nan ajin”

Malam Habibu ya ce “To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba ruwan kowa da ita kar a takura mata”

Suka ce to.

Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata taɓa zama shiru ba.

Ruma ta shige cikin ‘yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ƙasarta, amma duk tana jin me suke faɗa.

Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.

Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ƙofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta bata farar ƙasa kyauta.

Duk shegen son kuɗi irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ƙasarar nan, saboda shegen surutun ta da nacin tsiya.

Ta karɓi farar ƙasarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ƙawaye, a cewarta ɗaliban ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su ɗaliban sa’aninta kowanne ya mayar da hankali a kan karatunsa ne, ita kuwa ruma ‘yar abi yarima a sha kiɗa ce.

Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, “Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa ya hallara zan faɗi me aka yi mini” jin kowa ya shareta ya ƙi kulata ya sanya ta ce “Mama yanzu dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?”

“Da aka yi miki me?”

“Mama a gabanki ‘ya’yanki suke ce mini ƙwaila, amma baki taɓa hana su ba”

Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce “To ba ƙwailar bace ba?”

Ruma ta buɗe baki ta ce “Au mama har da ke?”

Aliyu ya ce “To meye dan an ce miki ƙwaila, ai ƙwailar ce”

Ruma ta ce “Kutt, ƙwaila fa wadda ba ta da nono kenan?”

Aliyu ya ce “Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa”

Mama ta ce “ke waye ya gaya miki haka?”

“‘yan ajin su Yasir ne suke faɗa, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin su”

Mama ta ce “To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ƙwaila ba?”

“Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon, na zo na ƙulla a leda na dinga sakawa” cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ƙyaƙyata dariya yake ƙasa-ƙasa lamarin ƙanwar nan ta su sai Addu’a kawai.

Aliyu ya ce”Ke da ki ke ƙanwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai kin fi kyau”

Ta ce “Kuma fa haka ne” ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa “Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji tana ɗan warin nan da ƙamashin turare “

“Fitar mini daga ɗaki dan ubanki, shashasha mara alƙibla fita ki bar mini ɗaki”.

10

Ɗan tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce “Mama wai me na yi to?”

“Ban sani ba fitar mini daga ɗaki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an canza mini ‘ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan gado irin naki?”

Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta.

“Ba zaki fita ki bar mini ɗaki ba, sai na taso kan ki?”

Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.

Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce “Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?”

Ta murguɗa baki ta ce “Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo”

“To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?”

Huzaifa ya yi caraf ya ce “Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo ɗin ta gani”

Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.

Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga ɗakin mama ya ɗau jakarta.

Ruma ta ɗaga murya ta ce “Mama, ga Huzaifa nan ya ɗaukar miki jaka”

Ya ce “To munafuka”

“Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki kuɗi”

Huzaifa ya ce “Mama aron naira ɗari zan ɗauka”

Mama ta ce “Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka ɗaukar mini kuɗi ba bani ka ke ba”

“Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi”

Daga kitchen mama ta ce “Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo ɗakin nan?”

“Mama wallahi bai ajiye miki ba”

A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka ya fice.

Ruma ta ce “Dana sani na bar shi ya ɗauka, nawa nake bin mama ba biyana take ba”

***

Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma.

Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B.

Malamin ya ce “Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi”.

Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi magana.

Ƙarshe dai ruma ce ta taimaki ‘yan ajinsu, gaba ɗaya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da ɗaliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi, tsabar naci ne ya sanya a ka bata.

Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki a saboda harkar karatu.

Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.

Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya niƙi-niƙi.

“Ke wannan kayan na menene?”

Ruma ta zubewa mama kayan ta ce “Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani”

“Meyasa aka baki?”

“Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ƙi koya mini, na je na yi ta yi da kaina, shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar”

Mama ta ce “Hmm, ai shikenan”

“Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?”

“Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa”

Cikin rashin fahimta ruma ta ce “Mama wace gurguwar kuma?”

Cikin gajiya da halin ruma mama ta ce “Ki tashi ki cire uniform ki yi wanka”

Ruma ta tashi ta cire kayanta, ta ɗebi ruwa ta shiga wanka. Ta na tsaka da wankan, ta jiyo muryar Usman ya shigo, daga banɗakin ta buɗe murya ta ce “Yaya Usyy Albishirin ka”

“Ruma ban hanaki surutu a banɗaki ba?”

Ta ce ‘yi haƙuri mama”

Ba dan ta gama wankan ba, cikin zumuɗi ta fito daga wankan ‘Yaya usman, bari na nuna maka wani abun mamaki”

Ba ta san a ya ta fito daga banɗakin ba, sai da mama ta daka mata tsawa, daga ita sai pant ta fito. Ta koma ta ɗauko zani, sannan ta kwaso kyaututtukanta ta nunawa Usman.

Ya kalli ruma sannan ya kalli kayan ya ce “Ruma ban yarda da ke ba”

Ta ce “Saboda me?”

“Ina ki ka ga kwanyar da zaki yi wani abun arziki ke?” Tsuke fuska ta yi tana kallonsa ta ce “To me ka ke nufi?”

“Ɗauko takardar da aka baki, na yi miki tambayoyi” ta miƙe ta je ta ɗauko masa takardar ta miƙa masa.

Ga mamakinsa duk abin da ya tambayi ruma, sai ta bashi amsa daidai ko gyaranta ba ya ci.

Ya ajiye takardar, ya kalli ruma ya ce “Ni fa haryanzu mamaki nake, matar da take zuwa ta kusa da ta ƙarshen aji, ita ta yi wannan ƙoƙarin”

Ruma ta yi murmushi sannan ta ce “Ikon Allah kenan, baku san haushin da nake ji idan aka ce mini daƙiƙiya ba, shi ya sa na dage na je na iya”

“Congratulations, ina ma zaki cigaba da dagewa da kin ga cigaba a rayuwarki”

Ta taɓe baki ta ce “A’a da wahala gaskiya, ka san baƙar wahalar da na sha kan na iya wannan abun, dan a dai na ce mini daƙiƙiya daga wannan ba zan kuma ɗaukar dala ba gammo ba”

Usman ya yi murmushi ya dafa kafaɗarta ya ce “Haba ƘANWAR MAZA, rayuwa ce fa, kuma idan da rai da lafiya yanzu aka fara, kar ki sake ɗarsawa ranki cewa akwai wani abu da zai gagareki komai wahalar sa, rayuwa sai da gwagwarmaya da faɗi tashi, musamman ga ɗan talaka. Kar wani abu ya ƙara razana ki, ko ki yadda ke daƙiƙiya ce zaki iya komai kema”

Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce “Dan Allah da gaske Yaya Ussy?”

Ya jinjina mata kai ya ce “Sosai makuwa, ki dubi rayuwarmu a cikin gidan nan, tun baki da wayo, har zuwa yanzu a cikin gwagwarmaya muke, farincikinmu kawai ki ke gani, amma kowa akwai kalar ƙalubalen da yake fuskanta, ki kalli mama ba ta yi karatu mai zurfi ba, amma ta cancanci a kirata jarumar uwa, ba lallai ki fuskanci me nake nufi ba a yanzu, amma ki saka maganganun nan a ranki akwai ranar da za su yi miki amfani. Amma ki tsaya a kan ƙafafuwanki, ki fuskanci abin da yake baki tsoro, ke fa jaruma ce, bai kamata sunan daƙiƙiya ya biki ba”

Ruma ta ɗan yi shiru sannan ta kalli Usman ta ce “Yaya Usy, in sha Allah zan dinga mayar da hankali na yi karatu sosai na daina wasa”

“Yauwwa ko ke fa, ai hakan ya fi deluwa”

“Kuma zan cigaba da ƙoƙari, in zama mai ƙarfi sosai, duk wanda ya tsokane ni, in yi masa dukan tsiya in farfasa masa baki da hanci, in kakkarya mutum”

Mama da take jin su ta ce “Ke kuma ba kya fatan ki girma ki yi hankali, sai rashin hankali ke ba kya fatan Allah ya shiryeki ki daina faɗace-faɗacen banzan man a matsayinki na mace, faɗa ba na ‘ya mace bane”

Ruma ta ce “A’a mama, gara ki bar ni na koyi ƙarfi sosai”

“Sai kuma ki yi ai”.

Usman ya kuma murmusawa ya ce “Ba irin wannan ƙarfin ake magana ba, ƙarfin zuciya da kaifin basira wurin sarrafa duk wata Matsala da za ta tinkaro ki, kar ki bari matsalolin ki su razana ki, ko sau ɗaya kar ki bada wannan damar, ki turje ki dake ƙalubale duk girmansa, ki yi gaba da gaba da shi”

Ruma ta ce “Mhmm, gashi dai hausa ka ke yi, amma bana gane me ka ke faɗa, sai na ji kamar ma wani yaren ka ke daban, ban wani gane me ka ke nufi ba”

“Ni ma na san ba zaki gane a yanzu ba shekarunki da hankalinki babu lallai ya kai, saboda ke a yanzu ba ki sa wata damuwa ko matsala. Tashi ki zubo mana Abinci mu ci” Ruma ta miƙe ta tafi kitchen.

Mama ta ce “Kai ma banda abinka, wannan zaka zaunar ka na wani gayawa wannan bayanan, me zata gane a ciki? Ita ban da wautarta da tambayoyin ta na rashin kan gado me ta sani?”

Usman ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Haka kurum mama ina jin tausayin yarinyar nan, jikina na bani za ta yi gwagwarmaya a rayuwa, gwagwarmaya a bugiren da ba zamu iya tsaya mata ba, ko yi mata wani taimako ba, gwagwarmayar da take buƙatar ta tsaya da ƙafarta ta cimma nasara”

Mama ta ce “Tooo ikon Allah, to koma dai menene, ni dai addu’a kullum cikin yi muku ita nake, ba ku kaɗai ba, dukkan ‘ya’yan muslmai baki daya, Ubangiji Allah ya shiga lamarinku, ya tsare gabanku da bayanku, ya kula da rayuwar ku”

“Amin mama, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana uwa ma bada mama”

“Amin ya rabb”

A ranar duk wanda ya shigo, sai ruma ta nuna masa kyaututtukan da aka bata, har a waya sai da aka kira mata yaya Abubakar ta gaya masa, tun ana tayata murna da Allah ya sanya albarka har ta fara ƙular da mutanen gidan. Dan hatta maƙwabta sai da ta shiga ta gaya musu ai tayi ƙoƙari a makaranta an bata kyauta.

Da ta je Islamiyya kuwa, har ofishin shugaban makaranta ta je, shi ma ta gaya masa, ya tayata murna tare da sanya mata albarka, ta ƙarasa staff room bayan sun gaisa da malaman suma ta gaya musu ai a makarantar boko tayi ƙoƙari an bata kyaututtuka. Nan suka yi ta mata fatan alkhairi, ji take a duniya yau ta ƙure daɗi tayi abin da ba ta taɓa ba.

“Malam to idan an idar da salla dan Allah a sanar”

Wani malami ya kalleta ya ce “A sanar da me?”

“Na yi ƙoƙari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ɗari biyu da hamsin fa na haddace yadda ake spelling ɗin su”

“To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a sanar wa ɗalibai”

Ruma ta ce “A’a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini daƙiƙiya su san ƙwaƙwalwata na aiki, wataran zan bayar da mamaki”.

Malam Habibu ya yi caraf ya ce “Ƙwarai kuwa, dole a sanar da ɗalibai wannan namijin ƙoƙari da ki ka yi, nima ba rannan na yi ƙari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu” cikin jin daɗi ruma ta ce “Yauwwa malam na gode”

Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce “Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah kaɗai ya san wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka faɗa ɗin, za ta ji daɗi da ƙara samun ƙwarin gwiwa”.

Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ƙofar masallacin maza, ta leƙa ta ce “Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a faɗa ba”.

Malam Habibu ya ce “To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka”

Haka malam Habibu ya tashi ya ce “‘yan uwa ɗalibai da malamai, a taya ‘yar uwa murna, wato ‘ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu’a, Allah ya ƙaro nasarori”

Daɗi kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.

Huzaifa da suka yi salla sahu ɗaya da Yasir ya ce “Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi ko?”

“Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ƙona banzayen litattafan da aka bata, kowa ma ya huta”.

Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida.

Da sauri ruma ta nufi dattijuwar ta faɗa jikinta ta ce “Gwaggo Atine, yaushe rabon da na ganki?”

Dattijuwar ta washe baki ta ce “Dama ina zaki ganni, nayi-nayi da babarki ta din ga kai mini ke ina ganinki, amma ta ƙi saboda ina ƙauye”.

Mama ta ce “Haba Yaya Atine, wallahi ba haka bane ba, kin san yanayin makaranta kuma ruma ba ta ji idan aka kai miki ita sai ta gallabe ku”

Ruma ta haye kan cinyar matar cikin jin daɗi ta zauna.

Matar ta ɗora da cewa “Ba wani rashin ji, a kawo mini ita a hakan ina son ta, duk rashin jin ta. Ɗan uwana ya ƙallafa rai a kan ta yana son ta, nima ina matuƙar ƙaunarta da na ganta shi nake tunawa amma ba za a kawo mini ita ba, sai wannan ƙartin ne kawai suke zuwa in da nake” ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Mama cewa take “Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda za a dinga kawota”.

Ruma kuwa ta kalli Gwaggo ta ƙyal-ƙyale da dariya ta ce “Dan Allah Gwaggo ki daina wannan kukan, ni wallahi fuskarki dariya take bani idan ki na yi, kin ga yadda ki ke yamutsa kuwa?”

Yaya Aliyu ya ce “Ai gara ta fara gwada miki halin”

Gwaggo ta tsaya da kukan ta ce “Rumaisatu, kukan nawa ne yake baki dariya?”

Ruma ta ce “Eh mana, amma ki daina ce mini wata rumaisatu, sai ka ce wata masara, kowa aka saka masa suna mai daɗi a gidan nan, amma aka saka mini wata Rumaisa kamar masa”

Gwaggo ta jinjina kai ta ce “Ikon Allah”

“Gwaggo wai ina wannan ‘yar ta ki, mai kamar ni ɗin nan?”

Jin ruma ta tambayi ‘yar autarta ya sanya Gwaggo yin murmushi ta ce “Au Lawisa tana nan ƙalau, ta na ta a gaishe ki, ita ana biki sun tafi da tuni tare zamu zo”

Ruma ta yi dariya ta ce “Wai Lawisa, ai har gara nawa sunan ma da nata, wata lawisa kamar za ace lawashi, ta fini girma yanzu?”

“A’a zaku yi tsayi ɗaya da ita”

Ruma ta yi murmushi tana kaɗa ƙafa.

Abubakar ya ce “Ruma ɗaga mata ƙafa mana”

“A’a ƙyaleta, ai haryanzu yarinya ce, Allah dai ya kai ni auranku ke da Lawisa”

Ruma ta ce “Amin, ki yi mini Addu’a, Allah ya sa na yi tsawo na isa aure, kuma Allah ya sa na auri kyakykyawa mai kuɗi sosai”

Mama ta riƙe haɓa ta ce “Ruma, ƙanƙanuwarki da ke, har kin san wani miji mai kyau mai kuɗi?”.

Gwaggo ta ce wa mama “Wai ke ina ruwanki da mu ne, muna hira kina saka mana baki” ta mayar da hankali kan ruma ta ce “Amin ‘yar albarka, Allah ya kai ki in da zaki huta, mu ci mu sha mu yi wadaƙa”.

“Amin, kuma Allah ya sa na auri me kyau”.

Aliyu ya ce”Da wannan shegen hancin naki kamar na aladae zaki auri me kyau?”

Gwaggo ta ce “Ƙarya ka ke dan ubanka, wallahi kamar ta ɗaya da babanku, kuma hanci ne da shi har baka, in Allah ya yarda sirikina kyakykyawa ne kuma mai abin hannu, tun da ‘ya ta ba daga nan ba”

“Gwaggo kin san wa nake so na aura?”

“A’a sai kin faɗa”

“Kina kallon wrestling?”

Gwaggo ta ce”A’a ni ban san shi ba”

‘To ball fa?”

“Ni ina zan ga wannan shirmen”

Ruma ta ce “Da kina kallo, da na gaya miki wanda zan aura a cikin su”.

Cikin son katse surutun da ruma ke yi ba kunya ba tsoro mama ta ce “Ruma tashi ki canza kaya, zan aike ki” ruma ta miƙe daga cinyar Gwaggo ta tafi sauya uniform.

Tun da Allah ya sa Gwaggo ta zo gidan nan, ruma taɓara ta ƙaru, don ko me ruma za ta yi ba zata bari a yi mata faɗa ba, gashi kullum cikin faɗa take da mai sunan Baba, dan kome za ta yi idan ruma tayi laifi hukunta ta yake yi.

“Wannan yaro da fuska kamar bajimin sa, ba ka da imani, wannan ‘yar tatsitsiyar yarinyar guda nawa take, da zaka dinga azabtar da ita wallahi Hauwa wannan ɗan naki mugu ne”

Gaba ɗaya ruma da Gwaggo suka gallabi gidan nan, ruma kuwa aka samu tikitin rashin ji dan ma tana tsoron mai sunan Baba.

Yau Malam Habibu yana babban aji, ruma tana tare da shi, yayi musu ƙari, tana ta wasanninta da ciye-ciye, sai da ya kammala yana amsa tambayoyi sannan ruma ta ce “Malam ka ce idan mace tayi mafarkin namiji sai ta yi wanka zata yi salla, to ni kuma kullum sai na yi mafarkin yayyena, Kuma ni sai zan tafi makaranta nake wanka watarana kuma mama ta ce bana fita tayi mini wanka, to yan…..

Kan ta ƙarasa ‘yan ajin suka hau dariya, dan ba zaka taɓa cewa hankalinta na kan abin da yake koyarwa ba.

Malam Habibu ya ce ” ‘ya ta ta kaina, ai wankan da mama take yi miki ya wadatar, duk ɗayane”

Ta ce “Au ho, na gane”

Tana dawowa daga islamiyya ta turke Abubakar ta ce “Yaya Sadik yau ka san meyafaru a makarantar islamiyya ?”

Sadik ya ce “A’a”

“Ka san na canza aji a islamiyya, saboda malaminmu baya ƙaunata, Ajin su Yasir kuma ya ce idan na ƙara zuwar musu aji sai ya dakeni, sai na koma ajin malam Habibu gaba ɗaya ajin ‘yan sauka”

Abubakar ya ce “To ban da abinki kin taɓa ganin an fara gini daga roofing, ai daga tushe ake farawa”

“Oho dai koma yane, wani karatu aka yi nake son na tambayeka, da zan tambayi malam Habibu na manta”

“To ina jin ki”

” ‘yan ajin ne da su da wasu na ga wataran ba sa salla fa, ko su ƙi zuwa da Alqur’ani izifi sittin wai Haila suke yi. Na tambayesu sai suka ce mini wai ai mata ba kullum suke salla ba, idan ba su yi salla ba haila suke yi ko biƙi. Aikuwa nima na ƙi yin salla, wata prefect ta ce me yasa ba na salla nima na ce biƙi nake”

Gwaggo da ta idar da salla ta ce “Subhanallahi” jin maganar ruman kamar saukar aradu.

Ita kuwa ko a jikinta, ta cigaba “Shi ne ta ce dan ubana ni na isa in yi biƙi, na ce ba dai ubana ba sai dai na ta, kuma tun da nima biƙi nake ba zan salla ba, ashe wataran mata ba sa salla amma ni kullum mama sai ta ce sai na yi”

Abubakar ya ce”To, wannan zancenku ne ke da maman ita zata baki amsa”.

Ruma ta ce “Mama…..”

Mama ta katseta ta hanyar cewa “Rufe mini baki, kar ki sake ki yi mini shirme, kuma ki tashi ki yi sallar da ki ka ce baki yi ba dan ubanki”

“To mama ai idan ana biƙi ba a salla”

“Biƙin ubanki, ke kin san meye biƙin ne?”

“To meye biƙin?”

“Ba zaki tashi ki yi sallar ba, sai na zane ki da bulugarin nan?”

Ta kalli Gwaggo ta ce “To ke gaya mini”

Kamar wadda ta tambayi meye wani babban zunubi Gwaggo ta ce “A’a ni babu ruwana, ga uwarki nan ta baki amsa ni zaki tambaya wannan babban al’amari ba a bakina ba, ‘ya’yan binki wayewar ku ta yi yawa”.

“Ohh ni ruma, komai na yi laifi ne, ai shikenan”

Tun daga lokacin ba ta kuma kula kowa ba, ta koma tayi shiru wai ita ta ji haushi.

Har zuwa sallar magariba, ba ta sake kula kowa ba, Gwaggo ma ta gaji da yi mata hirar, amma Ruma taƙi saurarata.

Yaya Sadik ne yayi gyaran murya ya ce “Ruma, wai ni kuwa idan kin girma me ki ke son ki zama ne? Da na je taron PTA ɗin ku an ce da kun shiga primary 6, za’a fara shirin common entrance, shi ne na ce idan kin shiga Sakandire me ki ke sha’awa Art zaki yi ko science?”

Ta kalle shi ta ce”Wai in din ga drawing?”

“Wane irin drawing kuma?”

“To ai ji na yi ka ce Art, Art ba drawing ba kenan?”

“A’a ba wannan ba”

“Ni dai kawai sana’ar da zan samu kuɗi nake so, ko kuma in zama ‘yar sanda, in dinga tsayawa a titi ina bada hannu masu mota suna bani kuɗi, ko kuma a buɗe mini kanti, ko na zama mawaƙiya ko ‘yar film!”

P11

Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.

“Yaya ya na ji kuma kayi shiru?”

“To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?”

“To wai me na faɗa ba dai-dai ba?”

“Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin taɓa ganin mace a titi tana bada hannu a ƙasar hausa?”

Ta ɗan yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce “A’a, to mawaƙiya fa ko film?”

Abubakar ya ce “Ba kushe sana’ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban”

“To ba sai a buɗe mini kanti ba”

“Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?”

Ta yi farat ta ce “Ga maman Olu beyerabiya”

“To ke bayerabiya ce?”

“A’a amma dai…..”

“Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan” ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.

Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da faɗa da azabar saka ido.

Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.

Amma kullum cikin surutu takewa mama “Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga ƙauye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi’

Mama ta ce “Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu haɗa talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai ƙwaƙwarar sana’a sai ƙarfin hali, idan suka ɗauko aure da yaya za su riƙe?”

“Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya ɗau abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara’a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara’a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama”

Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.

Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa’an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.

“Umaru da kai fa nake” A hankali ya ɗago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.

“To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka ƙarata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.

A hankali yasir ya ce “Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona”

A rikice ruma ta ce “Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba”.

Huzaifa ya yi ƙasa da murya ya cewa Abdallah”Ji munafukar ‘yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?”

Abdallah ya ce “Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta haɗa yaƙin duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi”‘

Kamar wasa ruma har da kuka, wai kar Gwaggo ta tafi, ji suka yi kamar su yi wa ruma taron dangi su zaneta.

Ganin ruma na kuka, ya sanya Gwaggo ta ce ba zata tafi yanzu ba, saboda ruma.

*****

Sauri-sauri take yi, tana tafe tana duba agogon hannunta, tana daf da makara zuwa wurin da zata.

Tana ƙarasawa harabar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce “Gali, gani na fito zo mu je na makara”

Cikin girmamawa da murmushi Gali ya taso ya ce “Allah ya taimaki ‘yar gaban goshi, Allah ya ƙara miki lafiya uwar ɗakina, ai tun ɗazu ke nake jira, tun da tun huɗu ki ka ce mini”

“Kai dai bari, na tsaya na yiwa Ammi girkin dare, kar na je ban dawo da wuri ba ka san ba komai take ci ba”

Ya ce “Haka ne, bari na fito da motar” ya yi gaba ita kuma ta tsaya.

‘yan mata ne su huɗu, suka fito ta ƙofar wani sashi na cikin gidan, suka tunkaro in da take wajen harabar gidan, hakan ya yi dai-dai da fito da motar da Gali ya yi.

Kai tsaye suka tinkari motar ba tare da sun kulata ba, suna ƙoƙarin buɗewa su shiga.

Da sauri Iman ta ce “Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne”

Ɗaya daga cikin su ta kalleta ta ce “Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?”

Iman ta ce “A’a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tuƙi ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa”

Cikin tsawa ɗaya daga cikin su ta ce “Shut up! Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?”

“Me ku ke yi haka a tsatstsaye?” Gaba ɗaya suka waiwaya suka kalli mai maganar.

Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.

Fauziyya ta cire glass ɗin fuskarta ta ce “Bro, wannan ƙanwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita”

Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce “Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko? Sa’anninki ne su?”

Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.

“Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl”

Gaba ɗaya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.

“Ke zo nan” ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.

Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.

“Ina zaki?”

“Napep zan je na hau”

“Wuce ki koma, ba zaki fita ba” yayi maganar cikin bayar da umarni. Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga ta bar gidan. Ba ta ce masa ƙala ba, ta koma sashin su, sai dai duk yadda ta so ta riƙe hawayenta abin ya faskara, tuni hawayen suka wanke mata fuska.

“Subhanallah, abar ƙaunata ya haka? Meyafaru? ya baki tafi ba?” Ammi ta yi mata tambayoyin a jejjare cikin ruɗewa bayan ganinta ta na kuka.

Iman ta share hawayenta ta ce “Bakomai Ammi, kawai fasawa na yi”

No ban yarda ba, gaya mini”

“Ammi su Fauziyya ne da Yaya Mahmud”.

Nan da nan Annurin fuskar Ammi ya ɗauke gaba ɗaya ta ce “Mahmud again? Tura fa ta fara kaiwa bango, meya yi miki?”

Iman ta share hawayenta ta ce “Ammi dan Allah ki bar maganar, kar ranki ya ɓaci, bana son ki damu”

Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Na ji, amma me suka yi miki?”

“Dan Allah kar ki damu Ammi, bakomai ki yi haƙuri”

Jinjina kai Ammi ta yi sannan ta ce “Yanzu shikenan, kin fasa fitar kenan?”

Iman ta ɗaga mata kai alamar eh. Ta ja hannun Iman suka bar falon.

****

Cikin rarrashi mama take magana, “Ruma, aiken ki nake son yi, amma bana son ki je ki yi mini shirme, ko ki tsaya a in da ban aike ki ba”

“In sha Allah mama, ba zan tsaya a ko ina ba, fiii zan ware dogayen ƙafafuwana da bala’in gudu na je na dawo”

Mama ta ce “Wane irin gudu kuma? Kalen ki watasar mini da kayan aiken, ki tafi a hankali, ki yi sauri ki je ki dawo”

“In sha Allah zan yi sauri, na je na dawo”

Mama ta gaya mata in da take so ta je, tare da abin da za ta kai, ruma ta sauya kaya ta saka hijjabi, ta fita yi wa mama aike, ta ƙuduri aniyar za ta je ta yi sauri ta dawo ko dan ta farantawa maman.

Tashin farko ta bi ta cikin unguwa, tana tafe tana kalle-kallenta, duk wani lungu da saƙo idan ta bi sai an kira sunanta, dan kusan kowa ya santa.

A ƙofar wani shagon aski ta ga keken Huzaifa, hakan ya tabattar mata da yana cikin shagon.

Murmushi ta yi ta nufi ƙofar shagon askin, da sallama ta buɗe ta shiga cikin shagon.

Duk maza ne a ciki, ga Huzaifa ya zauna a kan kujera za ayi masa aski, jin sallamar mace ya sanya dukkansu suka juya suna kallonta.

“Ohh Huzaifa yau Allah ya yi zaka cire wannan sumar kenan? Kuma wallahi aka yi maka askin ‘yan iska kai da mai sunan Baba”

A ƙule Huzaifa ya ce “Ke uban me ya kawo ki nan? Ba ki ga shagon aski bane?”

“To ni ina ruwana da wani shagon aski, ba dai mutane ne a ciki ba, keken ka na gani a waje na san kana nan, na ce bari na leƙo na ganka”

“To na ji na gode, fita ki bar wurin nan”

“To sai ka tsaya na gama kallon kalandar askin nan, sai na tafi ” tayi maganar tana riƙe ƙugu, tare da zubawa kalandar ido.

“Ni wannan yarinyar ba ke na taɓa rabaku faɗa da wasu yara ba, kun dawo daga makaranta?” Cewar wani da yake zaune shima yana jiran askin.

“Eh nice, me na yi kuma?”

Ya ce “A’a gane ki kawai na yi”

“To yanzu da ka gane ni lada nawa aka baka?”

Mai aski ya ce “Deluwa, dan Allah ki yi haƙuri, wurin nan duk maza ne, ki je aiken da aka yi miki, ko kuma in saka a riƙe mini ke na yi miki aski”

“Aikuwa da sai ka kasa zaman Ɗorayi, sai na saka yayyena sun kakkaryaka sun zubar, ni zaka yiwa aski?”

Huzaifa ya miƙe tsaye rai a ɓace ya ce “Bi ƙofar da ki ka shigo ki fita”

Ta ɗan kwaɓe baki ta ce “Huzaifa ba ayi maka gwaninta, daga ziyara?”

“Ki fita na ce, wallahi na zo in da ki ke sai na gwara kan ki” ja ta yi ta tsaya cike da taurin kai tana kallon idonsa, hakan ya ƙara tunzura shi, yayi kanta amma suka riƙe shi, ta fita da gudu daga shagon.

Tana fita ta yi ƙwafa, ta tura keken sa ta ji bai rufe ba, keken ya fi ƙarfinta, amma ta haye ta yi gaba.

Wani ya leƙa shagon askin ya ce “Huzaifa ƙanwarka ta ɗau keken ka fa ta tafi”

Da sauri ya miƙe ya leƙo, ai tuni ta kusa ƙarshen layin, ya san ko da ya bita ba zai cimma ta ba.

Kawai yayi tsaki ya koma ya zauna, zuciyarsa na tafasa, ‘yan cikin shagon suka din ga dariya, kowa na tofa albarkacin sa a kan halayar ruma.

Haka nan tun da ruma ta fita, mama ta kasa nutsuwa, kawai dai gata nan ne dai, ta fara dana sanin dalilin ma da ya sanya ta aiketa.

Tun tana saka ran ta ga ta ina za ta shigo gidan, har ta fara fidda rai, yanzu ba ta fiye ɗaga hankalinta ba, idan ruma ta fita makaranta ko aike ba ta dawo da wuri ba, sai dai fargabar mai za azo ace mata ruman ta aikata.

Aikuwa ilai, tana cikin wasi-wasi sai ga sallamar wata matashiyar budurwa da wata yarinya, yarinyar bakinta a fashe, jikinta duk kwata ga fasashshiyar roba, da sauran gari a cikin ta, yarinyar sai kuka take, yawu da jini yana zuba daga bakinta.

Cikin kaɗuwa mama suka gaisa da matashiyar yarinyar, mama ta hau tambayar ba’asi.

Babbar ta ce “Dama cewa aka yi na zo gidan su na faɗa, ruma ce ta taho a kan wani ƙaton keke kashe gardi, ta taho da gudu, ƙanwata ta karɓo niƙa, ta bugeta da keken ta faɗa kwata, ita ma ta faɗi a gefe, ta tashi ta karkaɗe jikinta ta hau keken ta gudu, kuma ba iya ƙanwata ta buge ba, tun da tana tafe tana faɗuwa a kan keken”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ya Allah kai ka jarrabeni, Allah ka dube ni, ka bani ikon cin wannan jarrabawa” mama ta kamo hannun yarinyar da aka jefa kwatar, ta wanke mata jiki, ta basu dubu ɗaya tare da basu haƙuri ta ce zata zo har gida ta basu haƙuri.

Gwaggo kuwa ta hau masifa “Wallahi mutanen maraya ba ku da kara a kan ɗa, yanzu saboda wannan ɗin aka wani aiko yawon kan ƙara, ai ɗa na kowa ne, kuma fitinar maraya ai daban take”

Kamar mama za ta yi kuka ta ce “Ba wnai fitinar maraya, dama can haka ake fama da ita, a ina ta samu keken da ta hau ni da na aiketa wuri daban, kullum sai ruma ta sakani asarar kuɗi da yawon ban haƙuri, nan gaba idan ba ayi wasa ba, sai wasu sun kai ƙararmu ga hukuma”

“A’uzubil’ahi kina uwa ba zaki faɗi alkhairi a kan yarinyar ki ba, ƙuruciya ce, kowa da irin ta sa” mama ba ta kuma cewa komai ba, idan ta biyewa zuciya, za ta iya musayar yawu da Gwaggo, wanda ba za ta so hakan ba.

Huzaifa ya shigo a kumbure yana bala’i “Mama! Ina ruma take wallahi yau sai na tattakata, sai na ci mutuncinta”

Mama da take a ƙule ta kalle shi ta ce “A ina ka ganta?”

“Mama shagon aski fa ta bini, na koreta shi ne ta ɗauke keke na ta gudu, ni sa’an wasanta ne ita duk wani halin zubar da mutunci ta iya”

Mama ta safe kai ta ce “A ina da ta samu keken kenan? Za ta gane ba ta da wayo da Baba zan haɗata bari ta dawo”

“A’a ke wace irin uwa ce, wannan mugun ɗan na ki, haka kawai ya kassarata a’a ban lamunta ba “

Huzaifa ya harari Gwaggo ya ce “Wallahi ko ba a gaya masa ba, da hannun nawa zan ci ubanta, sai na girgiza ƙashin haƙarƙarinta “

Har gefin magariba babu ruma babu alamarta, tun mama tana jurewa, har ta saka aje a nemo mata ruma.

Aliyu Allah ya bawa sa’a, ya ganota a wata tawagar ‘yan d.j, ana biki an kunna d.j, ta shige tsakiyar manyan mata, ana rawar sabada, ta gantsare sai rawa take, tana wani juye-juye sai ka ce an saka mata batir, ga ta a shafe ba gaba ba baya ama sai karkaɗa jiki take.

Cikin ‘ya’yan Mama, Aliyu Ustaz ne, ba shi da ra’ayin wannan abubuwan, amma yau a saboda ruma, sai gashi a tsakiyar mata, ya samu bayan ruma da take ta juyi, ya tsula mata tsumagiya.

A zafafe ta ƙandare ta juyo, a zaton ta yaron mai D.J ne ya daketa, dan dama yana ta korar yara daga cikin filin rawar taƙi tafiya. Ba kuma rawar kawai take yi ba, har da satar kuɗin liƙi tana sakawa a cikin hijjabinta, sai ta gantsare tana rawa idan aka liƙo sai ta wayance ta ɗauke kuɗin.

Cak ta tsaya tana kallon Aliyu, ta ɗaga kai ta kalli yadda gari ya yi duhu.

“Sannu ‘yar makaɗa, aike da aka yi miki kenan ko? Fita ki wuce mu tafi”

Kasa magana tayi, a take tayi saranda, da jin za ta iya ɗaukar kowane hukunci, saboda ita kanta ta san ta tafka ta’asa.

Ta janyo keken Huzaifa, da Allah ya sa ba a sace ba, ta hau turawa, Aliyu ya haske keken, tayoyi duk sun sace, dan ɗayar ma fashewa ta yi, ga kaca ta zube keken duk wani gurin ya lotse, adon fitulun da ya yiwa keken kuwa, suma wasu duk sun fashe.

Yana tafe yana kallon ruma, yana tunanin anya ruma mutum ce, fitinarta ko su da suna kamarta ba su yi haka ba, su dai akwai dambe kamar zakaru, kamar su cinye juna, amma rashin ji a gida, rashin ji a unguwa rashin ji a makaranta wannan sai Ruma ƘANWAR MAZA.

A ƙofar gida suka tarar da Uamar, yana tsaye yana waya, tana ganinsa ta fara kuka, tana cewa “Kashina ya bushe”

Aliyu ya ingiza ƙeyarta zuwa cikin gidan, da sauri Huzaifa ya taso, dan ta kekenaa yake yi, sai dai yana kallon keken ya san ko a wurin ‘yan gwan-gwan wannan keke ba zai daraja ba, kamar yayi shekara da shekaru.

A ka rasa wanda zai ce mata komai, duk suka zubo mata ido.

Mama ta ce “A ina ka ganota?”

“Ga ta nan ku tambayeta”

Cikin muryarsa mai razanata musamman idan ba ta da gaskiya ya ce “Daga ina ki ke?”

Jikinta ya hau rawa ta ce “Dan Allah mai sunan Baba……

“Daga ina ki ke fa kawai na ce?”

Gwaggo ta ce”Ya zaka razanata da wannan muryar ta ka, ka tambaye ta cikin nutsuwa mana”

Huzaifa ya daɗe bai ji abin da yake shirin sanya shi kuka ba irin yau, ya kasa ko tari tun bayan tozali da kekensa.

Rarraba ido kawai take tana kokowa da numfashi, ganin yadda kowa ita yake kallo yana jiran amsarta.

Wata irin gigitacciyar danƙa Uamar ya yiwa kunnenta, ta kurma ihu, ya janyota har tsakiyar tsakar gidan, ya dungurar da ita, ya naɗe hannun rigarsa cikin tsawa ya ce”Ina ki ka je da aka aike ki?”

Cikin kiɗima da razani, ruma ta wassafa komai, ba ta ɓoye ba ciki har da zuwa wurin aski da yadda ta ɗau keke tana tafe tana faɗuwa, duk ta gurje gwiwa, da yadda bayan ta dawo daga aike ta tsaya wurin ‘yan bikin da ba ta san suwaye ba ma, tana rawa tana satar kuɗin liƙi.

Sai a lokacin ta faɗi har faɗa suka yi da yaron dj yana ce mata shegiya ɓarauniya.

“Yanzu ina kuɗin da ki ka ɗebo ɗin?” Yayi maganar yana miƙa mata hannu.

Aikuwa ta zura hannu a rigarta, sai ga kuɗi, a ƙalla idan aka ƙirga sun kai dubu uku da ɗoriya.

12

Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce “Sata ki ka koma yi kenan ko?”

Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.

“Ba zaki buɗe baki ki yi mini magana ba?”

“A’a Yaya wallahi ba sata nake yi ba”

“To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?” Ta girgiza masa kai.

Ya ce “Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki”

Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce “Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo”

Gwaggo ta ce “Ku dai din ga haƙuri yarinya ce, ƙuruciya ce kawai take damunta”

Huzaifa ya yi ƙwafa ya ce “Ba ƙuriciya da yarinta ba, Allah ya sa ɗanyar ƙwaƙwalwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali”

Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguɗawa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.

Daga shiga banɗaki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta ɓata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta ɗau hijjabi ta tayar da salla.

Ita kanta ba ta san adadin raka’ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ƙarshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu ɗaya nazari kawai take.

Haka ta idar ta saka addu’a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faɗa sannan take zaman yin addu’a.

Ganin taƙi sallame addu’a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu’a ta tashi.

Ya ce “Oya, kamun kunne”

Cikin marairaicewa ta ce “Dan girman Allah Yaya…..

“Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?”

Jiki a sanyaye, ta durƙusa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.

Gwaggo ta ce “Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?”

Ruma ta ce “A’a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi haƙuri”

Mai sunan Baba yayi shiru, ya ƙi kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce “Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?”

Mama ta ce “Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam” ƙarshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba ɗaya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi haƙuri ya ce in tashi”

“Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waɗanda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana”

“Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur’ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan”

Yasir ya ce “Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun”

Gwaggo ta ce”Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin ƙi, ni babu abin da ya ƙular da ni, irin wannan goho da ya saki kina ‘ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin ƙi”.

Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.

Cike da ƙuluwa Yaya Aliyu ya ce”Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba” haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka ƙasa-ƙasa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.

Har mai sunan Baba ya dawo ruma tana nan tana aikin kamun kunne, tana yi tana faɗuwa tana tashi.

Sai da ya dawo sannan ya ce ta tashi, kuma ya ce mata washegari za su gauraya.

Tana miƙewa tsaye jiri ya kwasheta sai amai, Gwaggo ta fito da sauri ta kama ruma, kanta sai juyawa yake saboda azabar wahala.

A zaune ta yi alwala tayi sallar isha’i, ko abinci ba ta nema ba, ta kwanta saboda galabaita, cinyoyinta sai azabar ciwo suke yi mata, dama da fari suna ciwo saboda hawan keke, gwiwoyinta na raɗaɗi saboda duk ta ƙuje su saboda keke, yanzu kuma ga kamun kunne, jikinta kamar an mata duka haka take jin ta, a take wani irin wahalallen bacci ya kwasheta.

Sai dai kwana ta yi da wani irin zazzafan zazzaɓi, wanda ita kanta ba ta san ya hau ta ba, jin surutan ta ya yi yawa a baccin ne ya sanya mama zuwa ta taɓa jikinta, ta ji da zafi sosai.

Duk da mama a ƙule take da ruma, haka ta fita ta ɗebo ruwa ta sanya ɗan ƙaramin towel, ta din ga shafawa ruma ruwa a jikinta.

Tun asubar fari kuwa, ruma amai ne ya tasheta, saboda har a lokacin jiri take yi.

Yanzu ma a zaune ta yi sallar asuba, ta nemi wuri ta kwanta.

Tun mama na basar da ita, har kuma ta fara damuwa, Gwaggo kuwa ta samu wuri ɗaya ta zauna sai mita take na masifa a kan mama tana gani aka bawa ruma gwale-gwale amma ba ta ce komai ba.

Bayan gari ya gama wayewa, Gwaggo ta karya ta yi haramar tafiya, sai dai a lokacin ruma ta samu bacci, dan a galabaice take. Gwaggo ta ce kar a tasheta, Abdallah ya tafi rakata tasha, suna ta murna zasu huta, dan dama Gwaggon ta ishe su,  ruma ce kawai take son zamanta a gidan.

Mama ta tashi ruma, ta matsa mata a kan lallai ta ci Abinci, ta na ci tana kuka ta ɗan sha tea kaɗan ta kuma kwanciya, sai dai ko mintuna goma ba ayi da cin Abincin na ta ba, ta tashi ta cigaba da amai.

Ba shiri mama ta ce Aliyu ya zo ya kai ruma chemist a dubata.

Da ƙyar take iya tafiya, suna tafe tana kuka, har sai da ran Aliyu ya fara ɓaci, amma ya shareta suka cigaba da tafiya a hankali. Cikin sa’a kuwa suka tarar ya fito, kasancewar asabar ce, ranar ba ya zuwa aiki.

Ya na ganinsu cikin kulawa ya ce “Subhanallah, ‘yar gidan mama yau ke ce ba lafiya?” Ita dai ba ta iya magana ba ta nemi wuri ta zauna. Aliyu ya zauna ya rungumeta, saboda ƙoƙarin faɗuwa take yi.

“Meya sameta haka?”

Aliyu ya ce “Ina ga zazzaɓi ne dai, da amai ta fara jiya”

Bakinta bai mutu ba, ta ce “Kamun kunne aka sakani, kusan awa goma shine ya sani rashin lafiya”

“Subhanallah, waye ya saki kamun kunne kuma?”

“Mai sunan Baba ne”

“To ki yi haƙuri, yanzu dai zan ɗibi jininki na yi miki gwaji, in duba meye ya haddasa zazzaɓin”

Ɗiban jinin da za’a yiwa ruma, tamkar za a cire mata ido, ta dinga kurma ihu, tana fizge-fizge, ga ta da shegen ƙarfi, da ƙyar Aliyu ya riƙeta aka ɗebi jinin nan.

Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.

Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce “Malaria ce ke damunta, dan haka akwai buƙatar ayi mata allurai, da kuma magunguna”

Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.

Ya haɗa alluransa ya nufo ta, ta miƙe tsaye.

“Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba”

“To a ina za ayi mini allurar?”

Mai chemist ya ce “Ai a baya ake yin ta”

“Wai bayana” tayi maganar tana nuna bayanta.

Nasiru mai chemist ta ce “A’a a mazaunai”

“Suwaye mazaunan?”

Aliyu ya haɗe rai ya ce “Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi”.

Ta riƙe skirt ɗin ta gam ta ce “Ni wallahi ba zai ganni ba”

Aliyu ya fizgota, ya riƙeta da ƙyar suka danneta suka yi mata, Aikuwa ta din ga zunduma ihu, kamar sun mata wani abu.

Haka aka gama yi mata treatment, suka taho gida, ban da uban kuka babu abin da take yi.

“To subhanallah, ko me aka yi mata kuma take wannan uban kukan haka oho” mama ta yi maganar tana fitowa tsakar gida.

Aikuwa suna shigowa, ta nufi mama tana kuka.

“Meye haka, kukan me ki ke haka,ki ke ɓare baki?”

“Mama yaya Aliyu ne da Nasiru mai chemist”

“Suka yi miki me?”

“Bayan ya ɗibar mini jini, kuma suka buɗe mini tsiraici na aka yi mini allura”

Mama ta ce “Subhanallah”

“Mama ba ke ki ka ce ɗuwawu tsiraici bane ba, amma har da Yaya Aliyu ya riƙe ni, Nasiru mai chemist ya ganni, wallahi ban yafe ba”

Mama ta girgiza kai, ta ƙiftawa Aliyu ido sannan ta ce “Haba Haidara, ya zaka yi mini haka, dan me za’a buɗe mata jiki ayi mata allura?”

Aliyu ya ce “To mama ai larura ce, ko a addinance ba haramun bane”.

Cikin masifa ta ce “To shi yayana ne da zai ganni? Har da taɓani ya yi mini allura a wurin”

Aliyu ya ce “Sa’anki ne ni, uban me za a kalla a jikin naki?”

“Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, Allah ya jijjigo bala’in duniya da lahira ya ɗora masa, tun da ya ganan mini tsiraici na”

Mama ta ce”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wace irin Addu’a ce haka, kar in kuma ji, baki san larura ba?”

Aliyu ya ce “Sakarya, kamar ba tsairaicin ki ka je kina kaɗawa a gaban mutane ba jiya”

Umar ya shigo ɗakin mama, suna magana, bai kula ruma ba amma dan ya duba jikinta ya shigo.

Tana kwance ga zafin ciwo, ga na takaicin allurar da aka yi mata, zafin allaurar bai dameta kamar ganinta da mai chemist ya yi.

Sai da yamma mama ta sakata ta yi wanka, ta canza kaya ta ɗan ji ƙwarin jikinta.

Sai da ta kwana uku tana fama, sannan ta ware gaba ɗaya, sai dai rashin lafiyar da tayi ya sanya aka mance da laifin da ta tafka, kowa sai lallaɓata yake, ban da Huzaifa.

Ta ware sarai har ta koma makaranta, kullum mama cikin nasiha take yi mata, tare da yi mata addu’a da fatan shiriya.

Tun daga ranar ruma ta daina bi ta hanyar chemist ɗin Nasiru, idan kuwa ta ganshi ko kallonsa ba ta yi, balle ta gaishe shi, a cewarta ɗan iska ne tsairaicin ta ya kalla.

“Mama wai yaushe zaki haihu ne, babannin ‘yan ajinmu sai haihuwa suke yi, amma ke ban taɓa ganin kin haihu ba”

Mama ta ce “Ikon Allah, ba gaki na haife ki ba, ai ke ce auta ha zan kuma haihuwa ba, sai dai in kin girma kin haifa na ɗauka”

“To ni yaushe zan haihun?”

“Sai kin girma kin yi aure”

Ruma ta ɗan yi jimm sannan ta ce “To ni so nake na haihu, ina son ƙani ko ƙanwa da zan din ga wasa da su”

“Ruma ki ka haihu yanzu ai a nemi tsari, sai an yi aure ake haihuwa”

“To gaskiya mama ni so nake na haihu yanzu”

Usman da yake jin hirar ta su ya ce “Ke, idan ki ka haihu ba aure tsanarki za ayi, a kore ki daga gidan nan da unguwar ma gaba ɗaya, shi ya sa ba a wasa da maza, ki ka bari namiji ya taɓa ki to ciki zaki ki haihu, kuma korar ki za mu yi”

Waro ido ruma tayi ta ce “Amma ku kuke taɓani?”

“Ai mu yayyenki ne, muharramanki ne mu”

Ruma ta dafe ƙirji ta ce “Allah ya rufa mini asiri, ai da ban sani ba, taɓ idan aka koreni ina zani?”

“Oho miki dai, wannan damben da ki ke da maza ma, idan ba ki daina ba, sai dai ki ga kin haihu, kuma sai kin bar mana gida”

Ta yi ajiyar zuciya ta ce “In sha Allah hakan ma ba zata faru ba, ai ni ban san hakan abin yake ba, Allah ya sa na yi tsawo na auri kyakykyawa mai kuɗi”.

Mama ta ce “Ke zan ci ubanki ke da kyakykyawa mai kuɗin nan, miji na gari ake roƙon Allah, fitsararriya”

“Ni dai gaskiya bana son mummuna, mai kyau nake so”

“Ke dalla ware, da wannan munin za ki auri kyakykyawa?”

“Ni dai yaya Ussy, ka yi mini Addu’a, ka san wa zan aura a cikin ‘yan ball”.

Miƙewa ya yi ya ce “Ba ni da lokacin jij wannan shirmen na ki”.

Tun daga wannan lokacin, ruma take kaffa-kaffa, da gudun kar wani namiji ya taɓa ta, saboda kar ta haihu a koreta ta shiga uku, kuma ta san idan aka koreta ba kuɗin mota za a bata ba, balle ta tafi ko ƙauye ne wurin Gwaggo.

Yau gaba ɗaya mama ta kasa gane kan ruma, tun da ta dawo daga makaranta yanayinta ya nuna kamar tana cikin damuwa.

Ba irin tambayar da mama ba ta yi mata ba, amma ta ƙi gayawa maman dalilin damuwarta ta, ta ce cikinta ne yake yi mata ciwo kawai

Mama ta aiki ruma sayen maganin sauro, ta je ta sayo, ta dawo ta tsaya a soro tana kuka.

Huzaifa ne ya sameta a soron tana kuka, dan sai da ya ɗan tsorota.

“Ke me ki ke yi a nan?”

Cikin kuka ta kira sunansa “Huzaifa”

“Na’am” ya amsa.

“Ka san wani abu?”

“A’a sai kin faɗa”

“Yaya Usyy ne ya ce mini idan namiji ya taɓani, zan yi ciki in haihu, kuma korata za ayi daga gidan nan, sai malam ya aikeni karɓo masa chalk, da na kawo masa hannunsa ya taɓa nawa. Na tambayi ‘yan babban aji na gaya musu abin da yaya ussy ya gaya mini, suka ce eh haka ne wai ciki ne da ni, ka ga cikina ma ya fara kumbura yanzu ya zan yi bana son a koreni dan Allah ya zan yi” ta yi maganar har cikin zuciyarta tana rushewa da kuka.

Huzaifa a ransa ya ce ‘Alhamdilillah, na samo maganinki’

“Tabbas Deluwa kin kwaso mana abin kunya, yanzu abin da zai faru shi ne, ki haɗa kayanki a ɓoye, cikin dare na kai ki tasha ki bar gidan nan, dan idan mai sunan Baba ya sani sai ya jefa ki a rijiya”

Sake rushewa ta yi da kuka har da majina, ya yi saurin cewa “Sai mama ta jiyo kina kuka asirinki ya tonu ko?”

Ta goge hawanyeta ta ce “To ya zan yi?”

“Shikenan, zan rufa miki asiri, amma zaki din ga yi mini wankin uniform”.

“Eh na yadda, amma dan Allah kar ka faɗawa mama, bana son a koreni dan Allah”

Huzaifa ya yi wani murmushi cikin mugunta ya ce “To na ji, goge hawayen ba zan tona miki asiri ba”

Abu kamar wasa, ruma ko abinci ba ta iya ci, gashi kullum sai ta wanke wa Huzaifa kayan uniform.

Mama ta gaji ta ritsa ruma, har da bulala sannan ta zauna ta yiwa mama bayanin abin da yake damunta.

Mama ta yi salati ta sanar da Ubangiji, gaba ɗaya ruma ba ta da wayo, ga shegiyar tambaya idan kuma ka yi mata bayani yadda za ta fahimta, nan ma ta yi wata kwaɓar.

Sai da mama ta yi da gaske, sannan Ruma ta yadda ba ta da ciki, dan har da nunawa mama cikinta wai ya kumbura ɗa ne a ciki.

******

Ta na zaune a kan sallaya ta idar da salla, sai dai ta lula duniyar tunani, ba lazamin take yi ba.

Kamar daga sama ta ji ana kiran sunanta, ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

“Ohh Nusaiba, an gama girkin daren ne?”

Nusaiba cikin damuwa ta dubi Ammi sannan ta ce, “Ammi, tunanin me ki ke yi haka ne? kin san fa ba ki da cikakkiyar lafiya”

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Nusaiba tunanin nan na dole ne, shi yake yin kansa, abubuwa sun yi mini yawa, bana son na nuna gazawata amma ni na san na gaza na kasa shawo kan komai, al’amura na ta ƙara dagule mini”

“Me kuma ya faru ne?”

“Mahmud, lamarinsa yana damuna, ga kuma yadda aka addabawa yarinyar nan a cikin gidan nan, haƙurina ya fara ƙarewa, duk wanda ya taɓa Iman ni ya taɓa raina ya na ɓaci fiye da tunaninki”

Nusaiba ta gyara zamanta ta ce “Ammi, kin san wannan duk shirin Mummy ne, so take ki magantu ku raba abin faɗa a cikin garin nan, ita take buga miki wannan wasan, ki ƙyaketa kuma ki yi haƙuri ki ɗauke kan ki daga Mahmud, ba ga takawa nan ba, mu da shi mun isheki rayuwa su je su ƙarata mana”

Ammi ta girgiza kai ta ce “Nusaiba kenan, ba zaki gane ba, tashi maza ki je ki tabattar an gama komai, sannan ki kira mini Iman, ba na son zamanta ita kaɗai”

Nusaiba ta ce “To shikenan Ammi, bari na je”.

Sannu a hankali yake tafiya, tamkar ya na tausayawa ƙasar da yake takawa, har wani rangaji yake kamar wanda ake yiwa kiɗa.

Fuskar nan a murtuke babu annuri, in da ya sa a gaba kawai yake kallo, yake burin cinmma. Babu tsammani suka yi kiciɓis a baranda, ba tare da ɗaya ya san ɗaya ya taho ba, kuma aka rasa wanda zai bawa wani hanya ya wuce.

Kallon-kallo suka yi na wani ɗan lokaci, sannan ya lumshe idonsa a hankali ya buɗe. “Banihanya”

Kallonsa ya yi irin kallon ba ka isa ba ya ce “Ni da kai waye ya tarewa wani hanya?”

Cikin tsawa da zafin zuciya ya ce “Ka bani hanya na ce”

Murmushin gefen baki yayi, tare da rausayar da kai, yayi taku biyu ya koma gefe ya bashi hanya.

Sai da ya ƙare masa kallo, kamar ba zai wuce ba, sannan ya cigaba da takawa sannu a hankali ya wuce.

Ya waiwaya ya bi bayansa da kallo, yayi wani murmushi sannan ya ce “Zamu ga wanda ya fi iya buga wasan sa”

(A mini afuwa ban editing ba)

P13

Kwanci tashi asarar mai rai, ruma ta kammala primary school za ta shiga sakandare, sai murna take yi, sai dai babu abin da ya sauya a halayenta na rashin ji, ta hanasu sakat,a gidan, da an jima sai ta buga tsalle ta ce “Wooo ni zan shiga sakanni in dire”

Yasir ya ce “Ji banza, me aka yi da maza meye wata sakandare, ai yanzu aka fara”

“A’a bar ni na yi tsalle, na samu cigaba a rayuwa ta, Sakandire fa, zan shiga jss1 ai girma ya zo, yanzu ni ma zan yi tsayi tun da zan shiga Sakandire”

Usman ne ya miƙo mata kuɗi ya ce “Yi sauri ki je wurin mai shayi, ki karɓo mini madara zan karya”

Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce “Mama fa ta hana ni zuwa wurin mai shayi, da mai kifi da mai nama”

“Za ki wuce ki je ko sai na zo kan ki?”

Ba dan ta na son aiken ba, ta karɓa ta saka hijjabi ta fita, tama tafe tana shan farar ƙasa, bakinta yayi fari tas, kai ka ce akuya ce ta dumbuji dusa.

Ko da ta isa rumfar, dandzon matasa ne a ciki, sun cika kuma galibi abokan yayyenta ne, ba wanda ta kula a cikinsu ta miƙa kuɗi a bata madara.

“Rumaisa, ina Dambele?” Cewar wani matashi da yake ƙoƙarin kai lomar indomie.

Ta kalleshi ta ce “waye kuma dambele?”

“Ussy mana, na gidanku”

“Sai ka ce mini wani dambele kuma, kamar sunan rago, yana gida ya aka yi?”

“A’a ba komai, kawai na tambayeki ne, kin san Usman dambele wani ɗan ball ne, shi ma haka ake ce masa a filin ball”.

“Ni zaka gayawa dambele ɗan ball me, ai sai dai na baka labari”

Kan kace me, aka ɓarke da hirar ball a teburin mai shayi tare da ruma, yadda take bayanin ball ya isa ka gane ƙanwar maza ce, gaba ɗaya ta manta da aike da aka yi mata, ta tsaya ana sharhi da ita.

A ƙalla ta kai mintuna arba’in a wurin, ta manta da aiken gaba ɗaya, ga wurin shayin a ƙofar gidan su yaje, ya ci ace ta je ta dawo, amma babu ruma babu dalilinta.

Ba shiri Usman ya sanya riga, ya fito nemanta, ‘yar muryarta kawai yake jiyowa, tana bayani, har da dukan teburin mai shayi tana mayar da yadda aka yi.

“Ke! Meye haka?” Firgigit ta waiwaya, ta ga Usman a tsaye a bayanta.

“Aiken da na yi miki kenan?”

Kame-kame ta tsaya yi, dan har ga Allah ta manta da wani aike, musun ball na ɗibarta a rumfar mai shayi.

“Dambele yanzu nake tambayar ruma kai, ashe kana gidan ma, yarinyar nan ta burgeni, ta san ta kan ball abin mamaki, gaskiya na yarda ƙanwar maza ce”

A ƙule ya ce “Kai dilla ware, wannan ai hauka ne, kawai kun saka yarinya a gaba, kuna wani surutu, meye alaƙarku da ita?”

“Haba Usman, Ruma ai ƙanwarmu ce”

“Ba wani ƙanwarku, baku haɗa alaƙar komai da ita ba, ke kuma wuce kan na saka ƙafata, na kifa ki a wurin” sumi-sumi ta bar rumfar mai shayin ta nufi gida.

Ya bita gidan, ya dinga yi mata masifa, kamar zai cinye ta ɗanya.

*****

“Hutawarki lafiya uwar ɗakina ta kai na, jirgin sama maƙurar tafiya komai nisan ta”

Gyara zama ta yi ta dubeta ta ce “Bani labari, me ake ciki ne?”

“A’a, labarin bai gama nuna ba, amma ki bari ya ƙarasa tukuna, amma fa gida ya ƙara hargitsewa, ina ta gwara kawuna ta ko ina, na hanata sukuni, kusan tun bayan da Mahmud ya sa ƙafa yayi fatali da ƙudurinta”

“Hajiya Jamila, idan har muka tafi a kan tsarin da muka yi da farko, to tabbas zamu cimma buri, sarautar ta bar gidanku har abada”

Hajiya Jamila ta yi murmushi ta ce “Ai hakan na fi so, gara ai ayi biyu babu, sai na yi mata kassarawar da zata bar gidan nan da ƙafafuwanta, tun da dai na fuskanci asiri ba ya cin ta, gara ayi mutuwar kasko”

Dariya suka yi a tare, suna tafawa cike da duniyanci, tare da cigaba da tattaunawa a kan cikar muradansu.

****

Tamkar mai shirin zarewa, haka yake kai gwauro, ya kai mari a cikin katafaren falon, da ya sha ado da kayan alatu kamar ba za a bar duniyar ba.

Gefe guda wani babban mutum ne, zaune a ɗaya daga cikin jerin kujerun da suke falon, hannunsa riƙe da wani kwagiri, fuskarsa ɗauke damuwa.

Matashin ya daki teburi ya ce “Daddy meye abin yi ne? Ka na zaune ba ka ce komai ba?”

Dattijon ya numfasa sannan ya ce “Ka bini a hankali, ina tunanin wani abu ne”

“Daddy ba mu da isasshen lokaci fa, you know am following your footsteps, idan aka ɓata siyasarka, zai shafeni, mutum mai girma da daraja, kamar kai wannan ɗan ƙaramin alhakin zai kawowa barazana, gaba ɗaya gidajen jaridu, da dandalin sada zumunta, an buga labarin nan, kamar kai ka cancanci haka a ƙasar nan”

Murmushi mutumin ya yi ya ce “Easy Khalifa, ai ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin yaƙi ne, haka zalika yaro bai san wuta ba sai ya taka, ka ƙyale shi, a yanzu ba ta tasa ma nake yi ba, na zuba ido ne in ga wani mataki za a ɗauka a kansa. Saboda idan ya matsa sai ya fasa ƙwai, to ba ni kaɗai za ta shafa ba, zata shafi manyan ƙasar nan da dama, yaron tone-tonensa ya yiwa, amma yana daf da tona wuƙar da za ta yi ajalinsa”

“Ohh my God, Daddy sai wasu irin maganganu ka ke yi, amma haryanzu ba ka gaya mini menene mafita ba”

Alama ya yiwa Khalifa da ya je, Khalifa ya ƙarasa gabansa ya durƙusa. Ya tallafo kan Khalifa ya yi masa raɗa a kunne.

A take damuwar kan fuskarsa ta gushe, murmushi ya mamaye fuskar ta sa ya yiwa mahaifin na sa alamar jinjina da hannunsa.

****

Sati biyu kenan da fara zuwan ruma makarantar sakandare, kullum sai ta yi gugar kaya, wai kar ta je da ƙazanta kamar ba ‘yar sakandare ba, amma idan ta tashi dawowa tamkar ta yi dambe da kura, kayan nan duƙun-duƙun haka take dawowa da su.

Haka kawai yau zuciyarta ta raya mata, ta bi ta hanyar gidan mai unguwa, kasancewar a hanyar makarantar da take gidan yake.

A layin gidan mai unguwar, ta ga manyan motoci a fake, da alama wani abun ake yi. Hankalinta na kan lambun da ta taɓa zuwa ta ɗebo mangwaro mai gadi ya ce mata ɓarauniya, dan haka ba ta tsaya jin me ake a layin gidan mai unguwar ba.

Sai dai ko da ta ƙarasa layin lambun, wasu manyan motoci ta tarar guda uku a ƙofar lambun.

Lelleƙawa ta shiga yi, ta na haɗiyar yawu, saboda yadda take iya hango cincirindon bishiyoyin mangwaro da yadda  suka yi ‘ya’ya, ban da sauran ‘ya’yan itatuwa.

“Ke uban me ki ke yi a nan wurin?”

Da sauri ta waiwaya, ta ga waye yake yi mata tsawa haka.

Ɗan gidan mai unguwa ne dai, da ya taɓa kamata.

“Taɓ dama kana nan?”

“Eh ina nan, yau ma satar ki ka zo yi?”

Ta tsuke ɗan bakinta ta ce “Ba yayana ya ce kar ka sake ce mini ɓarauniya ba?”

“Oho miki dai, ai ɗiba ki ka yi ba a baki ba”

“Eh amma ai dai ya biya”

Cikin hanzari ya ce “Wai me ma ki ke yi a nan wurin ne?”

Ruma ta ɗan riƙe haɓa ta ce “Hmmm, ashe haryanzu ka na nan, ba ka cigaba ba, ni gashi har na gama primary na shiga sakandare”

“Ke dalla ware, tun kan a haife ki na yi sakandare na gama, fitsararriya wai wani ban cigaba ba, ɓace ki bar nan wuri muna da baƙi”

Ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce “Wai su waye suka zo, na ga ƙofar gidanku ma da mutane”

“Ban sani ba, ba zaki wuce ba sai na zane ki?”

“Dan Allah ɗan uwanmu mangwaro zaka san mini, ka ga dai yau ba sata na yi ba ko?”

Dariya ya kwashe da ita ya ce “A ina na zama ɗan uwanku?”

“Ai kai ɗan uwanmu ne na Musulunci”

Girgiza kai ya yi, zai wuce ta ya shiga cikin lambun, amma ta biyo shi.

“Wai ke baki da hankali ne, na ce miki muna da manyan baƙi masu wurin ne suka zo”

Cikin ko in kula ta ce “To ni ina ruwana, koma suwaye ai mutane ne ba mala’iku ba, dan Allah in biyoka ka san mini, ni sai na je na tambayo mai unguwa ma, na san shi zai ce ka bani”

Ya ƙarewa ruma kallo tsaf, a rashin hankalinta, tsaf za ta aikata abin da ta faɗa, na zuwa tambayo mahaifinsa, gashi yana tare da baƙi, ya dubeta ya ce “Yanzu abin da za ayi, ki zauna ki jirani, bari baƙin su tafi sai na baki”

“To, bari na je na zauna, kuma idan baka fito ba, biyoka zan yi”

“Wallahi ki ka shigo, zane miki jikinki za su yi”

“Su waye wai?” Ta yi maganar tana sake leƙa lambun.

“Kin ga tsaya, bari na je na samo miki” ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin lambun.

Dandamalin wani gida ta samu, ta ajiye jakarta, ta ɗebi duwatsu ta hau ‘yar carafke.

Tun ‘yar carafken na ɗauke mata hankali, har ta gaji da jiran ɗan gidan mai unguwa. Ta zube duwatsun ta tashi, ta je ƙofar shiga lambun ta tsaya, ta ɗaga murya ta ce “Ka cika alƙawari, zan shigo fa” magana ta fara ji ƙasa-ƙasa na mutane, alamar za a fito, ba ta yi niyyar matsawa daga bakin ƙofar ba, sai da ta hango akuya na shirin watso mata litattafanta, ta ci, ta nufi wurin jakarta, ta ɗau jakar ta na zagin akuyar, har da kiranta mayya mayuwanciya kamar tana magana da mutum.

Tana waiwayo wa, taga mutanen sun fito, sai dai kusan duk sun yi rawani, sai mutum ɗaya da suke takewa baya, shi kuma suit ce ma a jikinsa.

Da gudu ruma ta kwaso, ta tsaya daga baya ta ce “Laaa sarki ne wannan?” Jin ‘yar shilar muryarta ya yi, tamkar busar wata ‘yar sarewa a kunnensa, duk da akwai dandazon yara da suke wurin, galibi suna zuwa idan har ya zo, saboda ya kan basu kuɗi. Har ya ɗan juyo, zai waiwayo ya ga wacece a cikin yaran, bai juyo gaba ɗaya ba, dogon hancinsa kawai ta iya ganowa, ya ɗauke kansa ya shige motar da aka buɗe masa.

“Sarki ka ganni, ka juyo ka kalleni, ko dai ba sarki bane ba, na ga sarki ba ya saka ƙananan kaya ai”

“Ke! Hattara yarinya ‘yar talakawa, ba a yiwa takawa karan tsaye”

Shiru ta ɗan yi ta dube shi ta ce “‘yar talakawa kuma, to wallahi gidanmu akwai abinci, mu ba talakawa bane ba, kuma ba gara ni ba ma, Idan mu ka je kallon hawa mandawari, mama ta ce mini masu irin kayanka bayi ne, sayar da su ake yi zamanin baya a karɓi kuɗi”

Kowa waiwayowa ya yi yana kallon ruma, ya yin da dogarin ya zabura ya yo kan ruma, aikuwa ta kwasa da gudu ta tayar da uwar ƙura, shi kuma ya bita yana a tare ta.

Da ƙyar ruma ta kai gida afujajan, ta na ta haki kamar numfashinta zai ɗauke, ta shige ɗakin mama ta ƙule ta na ta sauke numfashi.

Mama ta biyo ta ɗakin ta na faɗin “Ke!ke ruma ke da waye haka? Yanzun ma tsokanar ki ka yo ko? Tun yashe aka tashi ‘yan makarantar ku, amma Allah bai nufe ki da shigowa ba sai yanzu ko? Ba zaki fito ba ina yi miki magana?”

Sumi-sumi ta fito, tana waige-waige sannan ta mayar da idonta kan mama.

“Daga ina ki ke?”

Ruma ta ɗan ɓata fuska ta ce “Mama ba ko ina fa”

“Zaki gaya mini ko na bari sai ya shigo?” Cikin kiɗima ruma ta ce “A’a, dan Allah kar ki yi mini haka, wallahi kallon sarki na tsaya, a lambun mai unguwa, shi ne wani bawa ya ce mini ‘yar talakawa, shi ne” sai kuma ta yi shiru.

“Shi ne me?”

“Cewa na yi, ai gara ni ba baiwa ba ce, shi fa kayan bayi ne a jikinsa, wanda ki ka gaya mini ɗin nan ranar da muka je cikin gari kallon hawa, shi ne ya biyo ni da gudu”

Tafa hannu mama ta shiga yi tana faɗin “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dama can na aike ki, na ce idan an tashi ki dinga zuwa wani wur?” Ta girgiza kai.

“Saboda tsabar rashin kunya da rashin hankali, ki ka tsaya kina cewa babban mutum bawa, daga yi miki bayani ranar, ke ba zaki taɓa hankali ba ko? Ina ma ya kama ki ya yi miki dukan tsiya, na gaji da halinki ruma, ki na girma ki na sake shiga dawa, gaba ɗaya babu alamar hankali balle nutsuwa a tare da ke. Ki je ki cigaba da abin da Allah ya nufe ki da yi, Allah ya gani na yi iya yi na, ban yi miki irin wannan tarbiyyar ba Allah ya shiryeki”

Ruma ta yi shiru, tana sunkuyar da kai kamar gaske.

A ɓangaren karatu, an samu sassauci daga halin ruma, kullum Usman ya na ba ta ƙwarin gwiwa, a kan kar abin da ya bata tsoro, duk wani abu da wani zai yi, ita ma za ta iya.

A makarantar islamiyya kuwa, tun da malam Habibu ya taɓa hannunta garin karɓar bulala ta daina bin sa, sai dai yau ta zauna a ajinsu, gobe ka ganta a wani ajin, ɗaukar magana kuwa ba ta fasa ba. Dan saboda tsaurin ido, har manyan ‘yan matan nan haka take zagewa ta yi musu rashin kunya, ba abin da ya yi mata zafi. Kuma ku san ko yaushe ta na cikinsu, ba ta yawo da sa’aninta.

****

“Allah ya taimake ki Hajjaju Mummy”

Murmushi ta yi cikin isa da izza ta ce “Abin ƙauna, ka yi breakfast ɗin ne?”

“Eh, na yi” ya yi maganar ya na zama a kusa da ita.

Ta saka hannu ta shafi sumar kansa ta ce “Mahmud, ya kamata a rage sumar nan”

Yayi murmushi ya ce “Haba Mummy, wannan sumar yadda ki ka ganta ki bar ta kawai”

“Hmm to ai shikenan, ya shirye shiryen komawa school?”

“Alhamdilillah, ina nan ina yi, very soon zan koma”

Fauziyya ce ta fito falon riƙe kofin shayi, ta kalli Mahmud ta ce “Yaya Mahmud, barka da safiya”

“Yauwwa, ina Ruky, ban ganta ba?”

Ta nemi wuri ta zauna ta ce “Ba ta tash ba, bacci take yi” ya kalli agogon hannunsa ya ce “By this time?”

Mummy ta ce “Ka san ta na karatun dare, dole ta yi bacci da safe”

Ya jinjina kai ya ce “Haka ne”.

“Amm Yaya Mahmud, takawa ya dawo fa, yakamata ku haɗu kan ka koma, kun daɗe baku haɗu ba” tsuke fuska ya yi, ya kalli Fauziyya ya ce “Yaushe ki ka fara tsara mini abin da zan yi a rayuwata? Ubana ne shi da lallai sai na ganshi? Na gan shi jiya mana so what?”

Mummy ce ta katse hirar, ganin Mahmud har ya ɗau zafi ta ce “Is ok, ya isa haka, ku dai idan ya shigo ku je ku yi masa sannu da zuwa, bana son ƙananun maganganu irin na gidan nan”.

Sannu a hankali yake danna system ɗin da ke gabansa, kamar ya na tausayaa mata, hannunsa ɗaya kuma riƙe da cup ya na shan tea, idan ba ka kalleshi sosai ba, zaka ɗauka Mahmud ne a zaune.

Muryarta ce take dawo masa kunnesa, kamar a yanzu take magana *laa sarki ne wannan? Sarki ka juyo ka kalleni* ya tuna ƙarfin hali da ta dubi ɗaya daga dogarinsa, ta ce masa bawa, koma dai wacece a muryarta ya ji akwai yarinta da kuma tsananin tsaurin ido, idan sarkin ne shi a haka zata yi masa magana kenan, ba girmamawa?

Iman ce ta fito daga sashin Ammi, hakan ya kaste masa tunaninsa, ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi ta ce “Barka da hutawa ranka ya daɗe” tun ɗazu Nusaiba take falon, tun da suka gaisa ta ja bakinta ta tsuke, ta kasa ce masa komai, shi ma kuma bai kulata ba, amma Iman na fitowa ya yi murmushi.

“Barkanki dai auta ta Ammi, kin tashi kenan?” Ta jinjina masa kai sannan ta ce “Once again Ya hanya, ya kuma ibada?”

“Alhamdilillah, ya karatun?”

“Ina nan ina ta yi Yaya, ka yi mini Addu’a kuwa da ka je?”

Ya jinjina kai ya ce mata “Sosai, ban yiwa kai na Addu’a da na yi miki ba, na so mu tafi tare da ke, amma na san Ammi ba lallai ta yadda, sai dai ku je umarar azumi ke da ita”

Iman ta yi murmushi ta ce “Nima ina yi maka addu’a sosai yaya, Allah ya kawo abin da Ammi take ta fata”

Nusaiba ta jinjina kai, da wani ne ya tsare Yaya da wannan maganar da ya shiga uku, to wa ma ya ga fuskar hakan, ai sai Iman ɗin.

“Iman, ai kuma zaku iya samarwa Ami abin da take burin, ku fito mana da tsayayyu, a wuce wurin kawai”

Iman ta ɗan rausayar da kai ta ce “Sai dai Anty Nusaiba, amma ni dai kam sai a hankali ” tayi maganar jiki a sanyaye.

Alama ya yi mata da hannu da ta zo.

Ta tashi ta tafi in da yake ta zauna, ya matsa kusa da ita, yayi ƙasa da muryarsa ya ce “Na ji abin da ya faru lokacin ina Saudiyya, abin bai yi mini daɗi ba sam, da Ammi ta yi shawara da ni, ba za ta yanke wannan hukuncin ba, ai Allah ke da rayuwar kowanne bawa. Ki ɗau abin da ya faru a matsayin Mafi alkhairi, Allah ya tanadar miki mafi alkhairi, ni kai na example ne a gareki, dan haka mu cigaba da Addu’a gaba ɗaya” ta jinjina masa kai ta na share hawaye.

*******

Usman ne a zaune ya gama cin abinci, ya kalli Abdallah ya ce “Kai ka san wani hau da wannan Anas ɗin yayi mini yau?”

Abdallah ya ce “Sai ka faɗa”

“Wai ni zai tara ya ce mini ya na son ruma, yarinyar da ko ciwon kan ta ba ta sani ba, ni kuwa na ci ubansa, sai kaɗan na kikkifa masa mari”

Abdallah ya yi dariya ya ce “Ba abokin ka bane ba, na ga filin ball ɗin ku ɗaya ma”

“Dan abokina ne, sai ya ce yana son ƙanwata, mahaukacin ina ne shi?”

“Amma wallahi yaya Usy ba ka kyauta mini ba, ‘yan ajinmu na Islamiyya su yi ta labarin saurayi, ni kuma ba ni da saurayi, duk wadda ba ta da saurayi fa wai baƙin jini ne da ita, sai an kai ta wurin malamai sun yi mata Addu’a “

Abdallah ya ce “Saurayin uban wa? Ke ya zaki yi da wani saurayi, ko yake shi Anas ɗin ne ma mara hankali, shi ma irinki ne ai mara kan gado perfect match”

Ɗan saroro ta yi ta ce “Wai Anas ɗin gidan mai taya?”

Abdallah ya ce “Ƙwarai kuwa”

Ta ce “Taɓ, Astagfirullah Allah ba irin wannan ba, kenan addu’a ta ba ta karɓu ba, ina ta Addu’a Allah ya bani saurayi mai kyau, mai kuɗi, mai ƙarfi sosai wanda zai din ga goyani kamar girman brownstrawman na wrestling, kawai sai wani Anas ya ce yana so na, wata uwar ƙeyarsa kamar sirdin keken baban su Ade, gashi siriri da kaɗan ya fi taliya. Ina ga sai na ƙara dagewa da Addu’a “.

Usman ya ce”Ke, kina halitta ne da zaki din ga kushe wasu? Kin ga ki shiga hankalinki, ba ke ce baki da kamun kai ba, dole kowa ma ya ce zai ce yana son ki, kuma wallahi idan ba ki shiga hankalinki ba, sai na bashi ke”

“Allah ya kiyaye, wallahi ba zan aure shi ba, gashi baƙi ƙirin kamar an rina shi”.

“Ke zan ci ubanki na kuma jin kina kunshewa wani halitta, ke kyan ne da ke. Ni kullum fatana Allah ya baki miji na gari ko ya fi biri muni” mama ta yi maganar a hasale.

“Mama biri kuma, ba amin ba gaskiya, dan Allah idan irin wannan addu’a ki yi mini ki daina, ni wallahi kyakykyawa na ke so”

“Kyan banza da na wofi, kyan ɗan maciji ki auri kyan ya din ga gasaki ba gara mummuna na gari ba”

Ruma kamar za ta yi kuka ta ce “Ina wani abin arziki a muni”

Mama ta hau ruma da faɗa, ruma ta yi shiru, amma a duk sa’ar da mama ta ce Allah ya bata miji nagari duk muninsa a zuciyarta za ta ce ba Amin ba.

Yau ruma Alla-Alla take gari ya waye, sai murmushi take ita kaɗai.

Yasir ne ya lura da ta na fara’a, dan haka ya ce “Wai ke murmushin me ki ke yi ne haka?”

Ta gyara zama ta ce “Ka san tun da na shiga sakandare, ban yi faɗa da kowa ba, so nake na zama ‘yan mata, in din ga tsayawa a cacar baki, to ni cacar baki ba ta biya mini buƙata, na fi son na haɗawa yarinya malaman jikinta, muka yi faɗa da wata yarinya, ka san ni ba na zagi, ta dinga zagina in gaya maka, amma ban yi kuka ba.

Kawai yau na ga babarta ta zo makarantar mu, da ƙyar ta shiga ofishin principal saboda girmanta, ina ga ta yi rabin bangon ɗakin mama.

Kai ina ga fa ta yi yakuzuna na jikin receiver girma, koma ta fishi, shi ya sa nake son Allah ya kaimu gobe, za ta gane ba ta da wayo, ba dai har da cewa babata tsohuwa ba ce, wallahi a jikin allo zan zana babarsu.

14

Buɗe baki Abdallah ya yi ya na kallon ruma, bil haƙƙi take maganar har cikin zuciyarta.

“Ke fa hankali bai wadaci ƙaramar ƙwaƙwalwarki ba, sai ki je allo ki zana babar wasu, idan aka zana taki zaki ji daɗi?”

“Ai ni na yi alƙawarin na daina dambe, ta zageni na kasa ramawa, saboda ashar take yi, ni kuma bana zagi, gaba ɗaya ta cuceni ta ɓata mini rai, ni kuwa ba ta san ba a taɓani a ci bulus ba, wallahi sai ta gane kurenta”

Abdallah ya girgiza kai ya ce “No, ki nemi wata hanyar dai, amma ban da iyaye, ba abin wasa bane”

“Iyaye ba abin wasa bane, ta ce mini mara tarbiyya babata tsohuwa, sai na ci buhun ubanta, ranar ma a sanyi ta sameni, da sai na tayar mata da aljanu na yi mata dukan tsiya, to bana som daga shigata makarantar a tsaneni ne, ayi mini mummunar shaida”. Duk yadda Abdallah ya so nusar da ruma, ta yi biris ta ƙi fahimta ta yi alwashin ramuwar gayya a kan abin da aka yi mata.

*****

Nasihar da takawa yake yi mata, a hankali ta ji ta ratsata sosai da sosai, daga ita har shi suna fuskantar jarrabawa daban-daban, wanda hakan yake jefa Ammi cikin damuwa.

Nusaiba ta kalli Takawa da Iman ta ce “Iman ‘yar gidan yaya, Ammi ta ki yayan ma naki”

Murmushi iman ta yi tana sake gyara zamanta.

Turo ƙofar falon aka yi, suka ɗaga kai gaba ɗayansu suka kalli ƙofar. Jabir ne ya shigo, da sallama a bakinsa. Suka amsa masa gaba ɗaya, hankalinsa ya na kan Iman ya na ƙare mata kallo. Hakan ya sanya ta haɗe rai tana ɗan kawar da kai gefe.

Yayi murmushi ya kalli Adam ya ce “Ni zaka yiwa haka, ka dawo amma sai dai na ji a gari ko ka neme ni”

Takawa yayi murmushin gefen baki ya ce “Ai idan ka san na dawo, zaka dameni ne ka sani yawo a gari, shi ya sa na yi shiru so nake sai na huta, shi ya sanya ma ban zauna a gidana ba, na yo nan”

Nusaiba ta ce “Uncle J, ina wuni?”

“Lafiya lau Nussy, Iman ba magana ne? ‘yar rigima”

Ba dan ta so ba ta ce gaishe shi, gaba ɗaya kwanan nan ba ta son abubuwan da Jabir yake mata, wanda ta kasa gane kan su.

Suna tsaka da hirar sai ga sallamar su Fauziyya da Ruƙayya, tare da Samha suka shigo falon.

Gaban Iman ya faɗi da ta ga Samha, musamman wani irin kallo da take bin ta da shi, da Iman ɗin ta kasa gane wane irin kallo ne.

Jabir suka fara gaisarwa, sannan cikin girmamawa suka gaida Takawa. Cikin halinsa na ko in kula da kuma tsare gida ya amsa musu.

Fauziyya ce ta gyara zama ta ce “Yaya ashe ka dawo, bamu san ka dawo ba, sai ɗazu Mummy ta ce mana, ai ka dawo”

“Eh na dawo” ya faɗa a taƙaice.

“Masha Allah, ya ibada?”

Ya amsa da “Alhamdilillah”

“To Allah ya sa an yi karɓaɓiyya”.

Samha ta gyara zama, ta na yiwa Adam wani irin shu’umin kallo, ta ɗan murmusa sannan ta ce “Takawa, ni fa kwance jaka na zo yi, daga zuwa wurin su Fauziyy, na ji suna cewa za su shigo yi maka sannu da zuwa, na ce bari na biyo su in yi sannu da zuwa, kuma a bani tawa tsarabar”

A hankali ya ɗago idonsa, ya kalli Samha, ya ɗan yi murmushi tare da girgiza kai amma bai ce komai ba.

Jabir ya dubi Iman ya ce “Iman, duk kin maƙalƙale mana shi, kamar ke kaɗai ki ka yi kewarsa, ki barmu mu ma mu gana da shi sosai mana” yayi maganar da sigar wasa.

Noƙe kafaɗa ta yi kamar ƙaramar yarinya, sai dai suna haɗa ido da Samha, samhan ta sake yi mata wani mugun kallo, da ya tilasta mata sunkuyar da kai.

“Jama’a ya shirin bikin Jamilu Turaki, Takawa akwai kilisa fa ranar Juma’a”

Adam ya girgiza kai ya ce”Kai, ƙyaleni da wata kilisa, duk na gaji, ni ban so ku ka san na dawo ba ma, ina buƙatar hutu sosai “

“Amma ba dai ka na nufin, ba zaka yi hawan ba, Jamil ɗin guda?”

“Sai na yi tunani tukuna, idan ina da time”

Jabir ya ce”Ba ruwana, kai da shi”

Tsarguwa da rashin sukunin da idanun Samha suka sanya Iman ne ya sanya ta miƙe ta ce “Ni dai sai an jimanku, zan je na huta”

Samha ma ta miƙe ta ce “Mu je, ina son na gaida Ammi kan na tafi ” jikin Iman ya yi sanyi, dan ta san akwai wani abu a ran Samha data ce za ta bita ta gaida Ammi.

Suna shiga ƙofar da zata sada su da sashin Ammi, Samha ta riƙo hannun Iman, ta tsayar da ita suna fuskanta juna.

Cikin raunaniyyar muryarta kamar mai shirin yin kuka Iman ta ce “Me na yi miki?”

Samha ta ƙarewa Iman kallo, sannan ta ce “Wai wace irin yarinya ce ke, kin manta kashedin da na yi miki ko sai na sake nanata miki?”

Iman ta ɗan ɓata fuska, ta aro jarumta ta ɓoye tsoron ta ta ce “Anty Samha, ni babu komai a tsakanina da takawa, ki yarda da ni mana, ina jin sa kamar wanda muka fito daga ciki ɗaya, ni ba zan iya aurensa ba”

Samha ta ce “Ƙarya ki ke yi, ba wani ki na jin sa kamar wanda ku ka kwanta ciki ɗaya, ai ba ki da kimar da zaki kwanta mahaifa ɗaya da Adam, ko kin manta wacece ke?”

Iman ta girgiza kai ta ce “Ban manta ba, ‘yar karere ce ni, wadda ba ta da gado a gidan Galadima, wadda aka taimakawa aka riƙe, ina sane ba sai kin tuna mini ba”.

Samha ta yi wani murmushi sannan ya kuma duban Iman ta ce “Ƙwarai kuwa kina sane, ban da Ammi ta nace da a cikin barorin gidan nan ya dace ki tashi ba ‘yan gida ba, dan haka ki kiyayi shiga gonata”

“Amma ta yaya, a tare muka tashi da takawa, ta yaya za ki ce sai na nesanta da shi?”

Ta ɗage kafaɗa ta ce “Wannan matsalar ki ce, ba tawa ba, dan na ga alamar tun da ba ki samu wancan ba, wannan zaki hara ki shiga hankalinki”.

Iman ta girgiza kai ta ce “Ni babu abin da ki ke tunani tsakanina da takawa, amma ke ma Anty Samha bana tunanin zaki samu abin da ki ke so, akwai katangar ƙarfe a gabanki, kuma kin san takawa kin san halin sa sarai, ki bi a sannu” daga haka tayi gaba ta bar Samha a tsaye.

*****

Kamar yadda ruma ta yi alwashi, haka ta yi, ta je ajinsu ta zana wata shirgegiyar mata a kan allo, ta yi labelling ɗin ta. Gefe kuma ta zana ƙarama wadda ba ta kai matar ba, ta yi labelling ta rubuta Asiya shu’aibu.

‘yan ajin suka dinga tuntsira dariya, saboda yadda zanen ya yi.

Ita kuwa Asiya ba ta san me aka yi ba, sai dai tana shigowa ta ga ‘yan aji suna kallonta suna dariya.

Saroro ta yi, tana son gane me suke yiwa dariya, ba ta kula ba ta je ta zauna, sai dai ta na zaman idonta ya sauka a kan allon, ta ga ta’asar da ruma ta yi.

A firgice ta tashi tsaye, tana zazzare ido “Uban waye ya yi mini wannan rashin mutuncin”

Ruma ta miƙe ta ce “I am madam”

“Saboda tsabar kin raina wa kan ki hankali, kina nufin wannan babata ki ka zana?”

“An zanata ɗin, ni ba cewa ki ka yi babata tsohuwa ce ba, ashe ma babata ta fi taki kyau”

Kan ruma ta farga, Asiya ta diro gaban ruma ta shaƙe ruma da hijjabinta. Kan ruma ta farga Asiya ta rufeta da duka, ta kaita ƙasa saboda ta rufe mata fuska da hijjabi. Kan ruma tayi wani yinƙuri, Asiya tayi mata duka.

Da ƙyar aka kirawo wani malami, ya janye Asiya daga kan ruma.

Malamin ya tasa su a gaba zuwa ofishin malamai, dan hukunta su, ruma ta shafa bakinta ta ji jini, tun da take a rayuwarta ko da za ta yi dambe a fitar mata da jini, to tabbas a duba wanda suka yi damben ta lallasa shi shi ma.

Gaba ɗaya Wani irin baƙin ciki ya mamaye ruma, gaba ɗaya ta rasa abin da yake mata daɗi, tun da take ba a taɓa galaba a kanta ba sai yau.

Ko da aka je staff room ana mayar da yadda aka yi, ruma taƙi magana, sai idonta da ya yi jawur, aka yo caaa a kan ruma, malamai suka din ga yi mata faɗa a kan bata kyauta ba zana babar Asiya da ta yi, suna kiranta mara ɗa’a.

Haryanzu malaman basu san wacece ruma ba, dan tun da Allah ya sanya ta zo makarantar ba ta taɓa gwada musu halinta ba.

Aka ce sai ruma ta bawa Asiya haƙuri, sannan za ta yi wankin banɗaki na sati guda, ita kuma Asiya zata yi sharar aji na kwana uku, saboda ɗaukar mataki da ta yi suka yi dambe da ruma.

Juyin duniya ruma ta yi magana taƙi, ƙememe taƙi bayar da haƙuri, dan haka aka sakata Kneel down har aka tashi a rana.

Babu abin da take tunani sai abin da za ta yiwa Asiya ta huce daga wannan baƙin cikin.

Ko da aka kaɗa ƙararrawa, ruma ba ta jira malaman su sallameta ba, ta tashi ta tafi aji ta ɗauko jakarta, Asiya ta din ga yi mata dariya har da gwalo. Wata nutsuwa ce ta shigi ruma a lokacin, dan a lokacin ji take da da wani abin dukan a kusa da ita, to tabbas sai ta illata Asiya.

Ta ɗau jakarta ta fice, har ta je gida kamar zararriya jikinta a sanyaye.

Tun da mama ta ga ruma ta shigo babu ko sallama, ga uniform ɗin ruma a duƙunƙune ga busashshen jini a gefen bakin ta, ta san yau ta yi halin na dambe, ga takalminta da jakarta a hannu ta shigo da su, gwiwar wandonta ta yi kaca-kaca da ƙasa.

Ta zubar da su a tsakar gida ta shige ɗakin mama kawai ta nemi wuri ta kwanta.

Ba ta tashi ba sai bayan azahar, ta tashi ta yi wanka, ta yi alwala ta yi sallar azahar, ta kuma neman wuri ta zauna a tsakar gida.

“Mutuniyar, wai ya aka yi ne? Zo ki sayo mana kifi mu ci Abinci, tun da na dawo nake cigiyarki” yayi maganar yana leƙa fuskarta.

Maimakon ta amsa masa kawai ya ga hawaye a fuskarta.

“Ke, menene mama ce?”

“Yaya Usy”

“Na’am rumaisa”

“Ni za a daka a hana kuka? Zuciyata zata fashe” tayi maganar tana sake fashewa da kuka.

Rarrashinta ya shiga yi, yadda ya ga tana neman ta shiɗe, idanunta duk suka yi ja.

Ya din ga lallaɓata ta gaya masa abin da ya faru.

Mama da take jin su ta ce “Allah ya ƙara miki, Allah ya sa yau da ki ka samu wadda ta zane ki, ba zaki sake dambe ba, dama ban da iskanci meye na zana uwar wani, idan ke aka zana taki uwar zaki ji daɗi?”

“Mama cewa fa ta yi babata tsohuwa”

“To sai me? Tsufa ai arziki ne, ruma ita duniya ‘yar siyasa ce, ba komai ƙarfi yake baka ba, amma kin kasa gane hakan”

Wani irin kallo take yi wa mama, wato ita mama ko a jikinta kenan.

Usman ya kawar da fuskar ruma daga kallon mama. Abu ne mawuyaci ruma ta yi fushi, ko an ɓata mata rai sai dai ta yi kuka, idan ta gama kuma shikenan ya wuce sai a shirya, amma yadda idanunta suka yi yau ya tabattar masa da ta kai maƙura a ɓacin rai, ba a taɓa defeating ɗin ta ba sai yau. Irin zuciyar mai sunan baba ce da ita, idan rai ya ɓaci silently suke fushi, sai dai suna shiga mawuyacin hali, har gara shi Umar yana shouting wasu lokutan, amma ruma gaba ɗaya kasa komai take idan tana cikin matsanancin ɓacin rai. Wata irin ajiyar zuciya kawai take yi.

“Yaya ni raguwa ce ko? Aka zageni, a kan gaskiyata kuma aka hukunta ni, ni ko?”

Usman ya yi ƙasa da muryarsa ya ce “Ke ba raguwa ba ce, kowa shaida ne, kamar yadda nake gaya miki, ki fuskanci duk wani abin da yake baki tsoro, gaba da gaba na tsaya miki”

Ta ɗaga kai ta kalli Usman, ya jinjina mata kai alamar ƙwarin gwiwa, ta jinjina kai ta mayar da kai ta kwanta a jikinsa, tana cigaba da ajiyar zuciya.

Duk wanda ya shigo ya ga ruma a haka, sai ya tambayi ba’asin meyafaru, ko ba ta da lafiya ne?

Mama ta ce “Ina fa, lafiyarta ƙalau, yau bori ne ya kar boka, ta tsokano wadda ta fi ƙarfinta, aka naɗa mata duka, shi ne take nema ta suma ki cigaba kar ki fasa halinki”

Aliyu ya tsaya a kan ruma ya ce “Ke, ki na wani sokwancin ki ka yadda aka dake ki har ki ke wa mutane kuka?” Ruma ta yi shiru ba ta amsa ba.

“Ina fatan dai ba a gaban wadda ta dake kin ki ka yi kukan ba? Wallahi da ina gidan nan sai kin fita kin rama, dan ubanki yaushe ki ka koma shashasha har aka dakeki aka fitar miki da jini, ‘yar uban waye da baki taka mini ita ba”

Buɗe baki mama ta yi, ta kalli Aliyu ta ce “Gadanga, maimakon ku tayani yi mata faɗa, ku ke mara mata baya? Ba sai ku ce Allah ya sa hakan ya zama silar shiriyarta ba”

Aliyu ya girgiza kai ya ce “A’a Addu’a ce kawai za ta shiryata, amma ba a daketa a waje ta tsaya tana kuka ba, babu rago a gidan nan, ko ɗan uban waye ta daka zamu bada haƙuri, amma wallahi aka kuma dukanki a waje, ki ka zo mana gida ki na kuka, sai na ƙara miki wallahi, idan mazane kawai ban yadda ki yi faɗa da maza ba, ki zo ki gaya mini, amma mace dai ‘yar uwakki, ki tattaka mini kowacece”

Aikuwa mama ta haɗasu gaba ɗaya ta din ga faɗa kamar ta ari baki.

“Kaf cikinku babu wanda na sha wahalr rainonsa kamar ruma, amma kuna zigata ta ɗauko magana, rainonta dai-dai yake da rainon fitinannun yara maza huɗu, maimakon ku tayani dawo da ita hanya, amma ku ke ingizata”

Gaba daya suka yi wa mama shiru, ta yi ta banbaminta ta yi ta gama.

*****

Karkarwa jikinsa yake yi, tamkar zai hau bori, jikinsa sai wani ƙaƙƙamewa yake yi, tamkar ba jikin ɗan Adam ba.

Wata matashiyar mace ce zaune a kan gadon, tana kallonsa, ido fal hawaye, ya yin da shi kuma ya cigaba da tunkararta.

Girgiza masa kai take yi, amma ta kasa motsawa balle ta gudu.

Yana zuwa ya zauna a gabanta ya tsura mata ido, ya miƙa hannunsa kan cikinta, take jikinta ya hau rawa ta rintse idanuwanta, tana zubar da hawaye. Sautin muryarta ne ya dakatar da shi ga aikata abin da yake ƙoƙarin yi

*Sarki ka ganni, ya na ga sarki da ƙananan kaya, sarki ka kalleni* tamkar a zahiri haka yake jin muryartata a cikin kunnuwansa, a hankali ya buɗe ido ya na ƙarewa ɗakinsa kallo. Sai a lokacin ya gane mafarki yake yi, ba zahiri bane.

A hankali ya tashi ya zauna, ya yaye bargon da ya rufa da shi, ya kalli agogon da ke kafe a jikin bangon ɗakin. Ƙarfe tara da rabi.

Ɗan guntun tsaki ya ja, me yasa yake yawan jin muryarta ne? Anya ba aljana ba ce ita ma?. Gabansa ne ya faɗi da yayi wannan tunanin, da kuma tuna matsalar da yake ciki, yake ta neman mafita a kanta.

Saurin girgiza kai ya yi, ya sauka daga kan gadon, ya wuce banɗaki.

****

Cikin matsanancin razani ta ƙwala ihu “Wayyo Allah mama” a gigice mama tayi kanta tana faɗin “Ke lafiyar ki kuwa?”

Tashi ta yi zaune ta na rarraba ido, tana kallon ɗakin.

“Lafiya menene?”

“Mafarki na yi na tsorata”

Mama ta ja tsaki ta ce “Ba dole ki dinga mafarki kina tsorata ba, tun da ba kya Addu’a kwanciya bacci”.

“Wallahi mama na yi”

“Ke ki ka sani dai, ko a garin neman maganar ki ruma, kya tsokano abin da zai dinga tsorata ki, ya hana ki bacci tashi ki je ki yo alwala, yanzu za a kira sallar asuba.

Haka nan jiki babu ƙwari, ta tashi ta yi alwala ta gabatar da raka’atanul fajr, sannan ta yi sallar asuba.

Jikinta duk yayi sanyi da mafarkin da ta yi, amma ta kasa tuna me ta gani a mafarkin ya tsorata ta.

Babu wanda Ruma ta kula a ajinsu, ta nemi wuri ta yi zamanta ta yi shiru, tana ta takura ƙwaƙwalwarta, ta tuna mafarkin da ta yi ya bata tsoro, amma ta kasa har aka kusa tashi, hankalinta baya tare da ita.

Asiya ce ta zo kan ruma ta tsaya, ta riƙe ƙugu ta ce “Ki je ki wanke banɗakin da aka saka ki, ko na je na faɗa” tamkar ruma na jin tsoron Asiya, haka ta tashi jiki na rawa zata fita daga ajin, sai dai ta yi burki a gaban allo, ta ɗaukko chalk a aljihun rigarta, ta sake zana wata shirgegiyar matar, wadda tafi ta jiya, ta yi labelling ɗin ta.

Ta waiwayo kuma tana kallon Asiya, tare da jiran ko ta kwana.

Aikuwa kamar ruma ta san a rina, Asiya ta kuma nufo ruma, tana zuba ashar, kan ta ƙaraso ruma ta yi ciki da ita, suka faɗa kan wasu ɗalibai.

Hannun Asiya ɗaya ta samu, ta din ga duka kamar ta samu ɓarawo, sai da ta tabattar da ba zata iya kai duka da hannun ba, sannan ta koma fuskarta.

An kai ruwa rana kan a ƙwaci Asiya daga hannun ruma, sai a lokacin ruma ta ji hankalinta ya kwanta, baƙin cikin da ya tokare mata zuciya ya sauka.

Babu wata-wata, malamin su ruma ya saka su kneeldown a rana, ba tare da ya tsaya ya ji ba’asin ma meyafaru ba.

Tun a lokacin Asiya ta ji ba ta iya motsa hannun da ruma ta din ga jibga, ta din ga jin kamar ba a jikinta yake ba.

Suna Kneeldown ruma ta riƙe ƙugu ta ce “Ke kin isa ki dakeni na ƙyaleki, hmm baki sanni bane, kuma wallahi ban huce ba, zaki ga abin da zan yi miki, ki dakeni ki zageni, sannan ki zaci kin ci bulus, ai faɗa ni da ke daga yau har ranar busa ƙaho, ba dai uwata ce tsohuwar banza ba sai ka ce babata sa’arki ce ba? Ai ki yi mini komai ban da taɓa uwata, ban taɓa zagin uwar wani ba, kema babarki  jibgegiyar bayerabiya masu kashi a leda”

Gigicewa Asiya ta yi, tana kuka tana son kaiwa ruma duka, amma ta kasa sarrafa hannunta ga ciwon da jikinta yake yi mata.

Ruma ta durƙusa ta dinga dumbuzar ƙasa hannu bibbiyu tana watsawa Asiya a fuska. Ban da kuka babu abin da Asiya take yi.

Ranar ma sai da aka tashi sannan aka sallame su, aka ce gobe da safe za su cigaba da punishment.

Rumaisa ta riga Asiya tafiya, ta je ta samu hanya, ta tattara duwatsu, ta tara su a cikin jakarta. Ta kuma datsar Asiya a hanya, ta dinga kabbara tana jifanta. “Sheɗaniya gara na jefeki na huta, na ga haka ake yi idan an je makka a jefi sheiɗan, gobe ko cewa aka yi ki kalleni, ba zaki sake ba balle ki dakeni”

Sai da ruma ta gama abin da Allah ya nufeta da yi, sannan ta wuce gida. Yau kam bakinta har kunne, jin ta take wasai ba ta da wata damuwa ko banza ta rama abin da aka yi mata har da riba, malamai kuwa ko zasu kwaɗata su cinye bai dameta ba.

Abdallah ne yake ta shiri, ruma sai tambayarsa take ina zashi?.

“Ke wai kin aikeni ne?”

“A’a, amma dan Allah ka gaya mini”

“Cikin gari zani ziyara”

Ta haɗa hannayenta biyu ta ce “Dan annabin rahama ka tafi da ni” hararta ya yi ya cigaba da shirinsa.

Ta dinga bin sa tana lallaɓa shi, har ya amince zai tafi da ita.

Mama ta ce “Hmm in dai ruma ce zata baka kunya, Allah ya sa kar ta ɗauko maka magana”

“Ta ɗauko ma, dakuwa zata yi wallahi”

Ruma ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta a cikin gari cikin ‘yan uwa, akwai ‘yan uwan mama sosai a cikin gari, sai dai mama ba ta zuwa da ita, saboda ta din ga neman magana da dukan ‘ya’yan mutane kenan.

Akwai wata ‘yar cousin ɗin mama, da rashin jin su ya kusa zuwa ɗaya da na ruma, duk da ruma ta fita. Ta ce “Ruma, zo mu je yakasai, akwai ƙawata a gidan Turakin Kano, jikarsa ce biki ake a gidan, kuma za ayi kilisa, kan Abdallah ya dawo mun je mun dawo, mu je mu ciyo banza”

Ruma ta ce “yauwwa hauwwaliya, yi sauri ki shirya mu tafi kan ya dawo ya hana ni zuwa”

“Ke har da babbar leda zan ɗauko, idan mun ci mu ƙullo sauran”

Haka suka shirya, suka yi sallama a kan zasu je biki su dawo.

Suna tafe a hanya suka sai masara, suna tafe suna ci suna hira.

Tabbas idan ka ji wane ba ƙarya ba, gidan ya tsaru yayi kyau sosai da sosai, gini ne na sarauta da aka ƙawata da kayan alatu, ruma sai rarraba ido take yi.

Ƙawar hawwaliya ta din ga murna da ta gansu, ta kai su wani falo suka zauna.

Ruma kuwa hankalinta na kan wata mata, da ta sha ado sai kai wa take tana komowa tana wani hura hanci, tana dakawa mutane tsawa.

Ruma ta ce “Taɓ, wai wacece waccan?”

Yarinyar ta kalli wadda Ruma ta nuna ta ce “Laa Anty Samha ce, ƙanwar mama ce, ba mata bace ba ta da aure”.

Ruma ta ce “too na ganta wata gwabjejiya, sai masifa take yiwa mutane, ni na zaci matar sarki ce ma, yakamata a samu mai kwaɗeta ya zata din ga hantarar mutane?”

Hauwwaliya ta daki cinyar ruma ta ce “Ke, ƙanwar mamanta cefa”

Yarinyar ta yi murmushin yaƙe ta ce “Bari a kawo muku Abinci, sai mu je wurin kiɗan ƙwarya da kilisa”

Ruma ta miƙe ta ce “Hauwwaliya, ni dai zan je wurin da na ga an ɗaure dokuna na kallesu, idan an kawo Abincin ki ƙulle mini nawa a ledar da ki ka zo da ita” buɗe baki Hauwwaliya ta yi, da jin hansfreen da ruma ta yi musu.

Kai tsaye ruma ta fito tana cigaba da kallon gidan, da yadda manyan mata ke shiga suna fita, da shiga kala-kala.

“Ke ba kya gani ne, meye haka?” Ruma ta ɗaga kai ta kalli wadda ta daka mata tsawar. Matar da take ta hantarar mutane ce.

“Eh bana gani, sandata na fito nema, ke da ki ke gani meya hana ki kauce?” Ruma ta yi maganar tana tsare Samha da ido.

Wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Samha, da ta yi tozali da idanun ruma, ga ta ƙarama amma wani abu mai kaifi ne a idanun ruma.

Ruma ta raɓata ta wuce abinta. Da sauri Samha ta bi bayan ruma, amma ta nemeta ta rasa.

Kai tsaye burgar dawakin da suka wuce ta je ta tsaya. Ta tarar da wani dogari yana basu Abinci.

“Sannu da aiki”

Ya kalli ruma ya ce “Yauwwa sannunki”

“Dan Allah ina dokin sarki a nan?” Yayi murmushi ya ce “Nan babu dokin sarki, na ‘ya’yan sarki da manyan Hakiman fada ne”

“Dan Allah ka cewa sarki ya bani doki ɗaya”

Yayi dariya ya ce “Ke idan aka baki doki ya zaki yi da shi?”

“Hawa zan din ga yi mana” ruma ta din ga yiwa dogarin nan surutu, sai da ya gaji sannan ya ce “To ai Shikenan, yanzu dai fita za ayi da su, za ayi kilisar angwaye”

Ta jinjina masa kai, ta koma gefe ta tsaya, tana kallo aka shirya dawakan, aka yi musu kwalliya sannan aka fita da su.

Hauwwaliya ce ta fito ita da ƙawar ta ta tana faɗin “Ke ruma, tun ɗazu jira nake ki dawo, amma ki ka ƙi komawa”

“Ke ƙyaleni, kallon dokuna nake”

Ƙawar hawwaliya wadda suke da Turaki, ta ce “Mu je to, sai mu kalli kilisar”

Suka fita daga cikin gidan gaba ɗayansu, kan barandar wani gida suka je suka tsaya, suna tsumayin a fara kilisar.

Abin yana burge ruma sosai da sosai, duk wanda ya zo wucewa sai ta ɗaga masa hannu tana tsalle.Tun da suke wucewa babu wanda ta kira sarki, sai da ya zo wucewa tare da ango.

“Sarki mai koriyar alkyabba, a dawo lafiya, dan Allah ka bani kyautar doki, ko kuma ka ɗanani a kan dokinka!!!”

(Wannan ‘ya ni kaina tana bani ciwon kai 😒 in kun ji ni shiru ku dinga yi mini addu’a, Allah ya ƙara mini lafiya 🙏)

Mai nema daga farko, ya duba watpad Please 🙏

P 15

Gaba ɗaya aka juyo ana kallon ruma, mutanen wurin suka hau dariya.

Shi kansa Jamil da yake ango, da sauri ya ƙara rufe fuksarsa da rawani yana murmushi, dan saura ƙiris dariya ta ƙwace masa.

Adam kuwa sake tsare gida yayi, kasancewar dama can ba mai yawan fara’a bane ba, jin muryar ruman yake a wani abu daban, anya mutum ce?. Kamar zai juya domin ganin fuskarta, sai kuma ya fasa ya sake rufe fuskarsa da rawaninsa, yayi gaba.

Ƙawar Hauwwaliya kuwa ɗan zaro ido ta yi ta ce “Ke kin san waye wannan kuwa?”

Ruma ta ce “Ba shine sarki ba?”

“Ba sarki bane ba ai, ɗan gidan marigayi Galadima ne da ya rasu, sunan sarki ne da shi, Takawa ake ce masa, wallahi ki ka bari ya kamo ki, sai kin gayawa mutanen garinku, ba ki san yadda muke jin tsoronsa ko a family ba, hmmm su Ummanmu sun girme shi amma tsoronsa suke ji, ba ya wasa da mutane”

Bayan gama jin jawabin da aka yi mat, ta taɓe baki ta ce “Taɓ, na gama yaya umar, ni gani nake kamar na taɓa ganinsa ma, ko a ina oho mini dai na manta, so nake na ga fuskar sa”

Dariya yarinyar ta yi ta ce “Ki zo wataran mu je gidansa, ko gidansu sai ki ga fuskar sa amma daga baya zan laɓe ke ki shiga” ruma ta kwashe da dariya ta ce “Ke da wasa nake miki, amma dai zan zo wataran a ɗanani a doki”

Yarinyar ta dubi Hauwwaliya ta ce “To yaushe zaku kuma zuwa?”

“Ke, ita fa ruma ba a nan unguwar take ba, zuwa ta yi yau zata koma gida, a ɗorayi take fa”

“Haba, idan mun zo hawan salla wataran, sai na zo gidanku”

Ruma ta yi murmushi ta ce “Allah ya kawo ki, amma baki gaya mini sunanki ba”

“Sunana Jannah, ke kuma ruma ko?” Ruma ta jinjina mata kai alamar eh.

Ta miƙowa ruma ledar viba ta ce “Ga saƙonki” ruma ta karɓi ledar ta yiwa Jannah godiya, suka tafi gida.

Allah ya taimaketa, Abdallah bai dawo ba sai bayan salla magariba, sannan ya ɗauketa suka tafi gida.

Tun a hanya yake tambayarta meye a ledar hannunta, amma tayi mursisi ta rungume ledarta taƙi nuna masa, har suka je gida.

Mama sai da tayi mita “Abdallah ka ɗaukar mini ‘ya ka tafi da ita, tun ɗazu nake zuba ido in ga ta ina zaku dawo, ka san da wuri take bacci, kun je kun yi dare”.

Abdallah ya ce “Mama wai dama kina son yarinyar nan?”

Mama ta buɗe baki, tare da yin murmushi ta ce “Dan ƙaniyarka in haifi ‘yar a cikina ka ce dama ina son ta, ni duk cikinku waye bana so, ai banda hali irin na ruma son da nake yi mata daban ne, kasancewar ta mace ɗaya tilo a cikinku, amma sanin halinta ya sa wasu lokutan nake kamar bana son ta, idan ba haka taɓarar da zata yi sai Allah”

Ruma ta ce “Kai ban taɓa jin kin ce kina sona ba, ashe idan na mutu zaki yi kuka”

Mama ta ce “Ke rabani da shiririta, tashi ki yi sallar isha’i ki zo ki ci Abincin dare ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta”.

Ruma ta tashi ta ce “Ai ni yau ba abincinki zan ci ba, na gidan sarauta zan ci” mama ba ta ɗau maganarta da muhimmanci ba, sai da ta idar da salla, ta janyo viva, tana firfito da Abinci.

Mama ta matsata da tambaya, ta bawa mama labarin abin da ya faru.

Abdallah ya ce “Wallahi mama ban ma san ta je ba, na ƙarasa na gaisa da abokaina na tsohuwar unguwarmu, shi ne ta samu ta tafi, yanzu da doki ya takaki ki ce me?”

“Doki bai takani ba, sai abin arziki da na samo, kun ga gidan sarautar nan, wai gidan Turaki, gaskiya suna da kuɗi, mama kalli kaza guda ta sako mini, kalli kayan gara, ya ma sunan wannan dunƙulellen abun mai kamar kashi?” Ta yi maganar tana nunowa mama Alkaki, gaba ɗaya ko a jikinta, dan ita ba ta ji a jikinta ta yi laifi ba.

Mama zurru kawai ta yi da ido ta na kallon ruma, mama ta gaji da faɗa a kan halin ruma, dan haka ta yi shiru ta na faɗin Allah ya shirya.

******

Yanayinsa ne ya nuna wa Ammi cewar ya na cikin damuwa.

“Takawar ka lafiya babban mutum, basarake kuma jinin sarakai, me yake faruwa ne?”

Adam ya yi murmushi ya ce “Bakomai Ammi, gajiyar bikin nan ce ta Jamil, kuma kwana biyu ban hau doki ba yau na hau doki, duk jikina ciwo yake”

Ammi ta yi murmushi, a dole wai sai ya ɓoye mata akwai abin da yake damunsa, dan haka ta yi murmushi ta ce “Shikenan, ka je ka ɗan watsa ruwa ka kwanta ka samu ka huta” ya jinjina mata kai, yana shirin tashi ta ce “Yauwwa Takawa, ni ko tun da ka dawo, ka je ka gaida babarka?”

Take ɗan ragowar annurin fuskarsa ya ɗauke, ya ɗan ɓata fuska tare da girgiza kai alamar a’a.

“To ka san dai yakamata ka yi hakan, bana son ƙananan maganganu, tun da yanzu a gajiye ka ke, kuma kana gidan nan yakamata in an jima ko da safe dai, ka je ku gaisa ka ce mata ka dawo”

“To” ya amsa a taƙaice.

*****

Mama sai fama take da ruma a kan shirin makaranta, sai laƙai-laƙai take yi, sai ta fara shiri, sai ta tafi banɗaki yawon kashi, saboda ciye-ciye da ta yi, ya ɓata mata ciki. Mama ta kai matuƙar ƙuluwa sai faɗa take yi, ruma kuwa ko a jikinta.

Har ta ɗau jaka, sai ga kira a wayar mama.

Mama ta ɗaga tare da yin sallama.

“Da ga makarantar su Rumaisa ne, dan Allah idan za ta taho, a haɗota da wani babba daga gida”

A ɗan ruɗe mama ta ce “Lafiya, wani abun ta yi?”

“A’a, a dai haɗota da wani babba, ko babanta ko wakili”

“To shikenan, babu laifi, za ta taho in sha Allah” mama ta ajiye wayar ta kalli ruma. “Ruma, me ki ka yi a makaranta?”

“Ni kuma? Ni babu abin da na yi”

“Ki gaya mini tun kan raina da na ki su ɓaci”

“Wallahi mama ni babu abin da na yi”

“Amma aka ce ki je ke da wani babba, anya ruma ke fa ba gaskiya ki ka cika ba”

Ruma ta ce “Ni dai wallahi na san babu abin da na yi”

Mama ya gyaɗa kai ta ce “Ai shikenan, zamu gani”.

Ta ƙarasa ƙofar ɗakin ‘yan mazan, ta ce “Waye ba zai fita ba yau a cikin ku? Wani ya zo ya je mini makarantar su yarinyar nan, an kira ni an ce ta je ita da wani”

Yaya Aliyu ya ce “Mai sunan Baba dai ya tafi makaranta, ni ma ina da lectures ƙarfe goma sha biyu, amma bari na zo mu je na ji menene”

Ita kanta ruma tunani take Meyasa ake neman wani a gidansu a makaranta?

Suna tafe a hanya da Aliyu yana mita “Ke, kawai kin sa an katse mini bacci na, Allah ya sa na ji wani rashin jin ki ka yi, na samu abin duka na zane ki”

Ta tura baki ta ce “Ni dai na san ban yi komai ba, wataƙila ma wani abun arzikin na yi ake nemanku, amma kowa ba ya kyautata mini zato”

“Ruma ai ke abin arziki  bai karɓe ki ba, sanin halinki ne ya sanya ake tsoron lamarinki”

Suna tafe a hanya, yara da manya mata da maza kusan kowa ya san ruma, suna tafe ana kiranta ta na ɗaga wa mutane hannu, har suka isa makarantar.

Ofishin Headmaster suka je, ruma sai rarraba ido take tana ‘yan ciye-ciyen ta.

Aliyu suka gaisa da Headmaster, ruma ma ta gaida Headmaster ta koma gefen Aliyu ta tsaya.

Headmaster ya kalli ruma ya ce “Waye ya sallameki jiya ki ka tafi?”

Ruma ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba.

Headmaster ya dubi Aliyu ya ce “To, a gaskiya ƙanwarka ce ko ‘yar ka ba ta jin magana, sun samu saɓani da abokiyar karatunta, an yi musu sulhu amma ba ta ji ba, sun kuma faɗa jiya, ta karyata a hannu, kuma ta bita hanya ta din ga jifanta da dutse wai jifan shaiɗaniya. To uwar yarinyar nan ta ce ba zata yadda ba, yanzu haka tana division ta kai ƙara, suna jiran mu, ka san ƙabilu wasu lokutan basu da tawakalli ba su san ƙaddara ba”.

Aliyu ya ce”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ke dan ubanki a garin yaya ki ka karya ‘yar mutane, kuma baki faɗa ba?”

Ruma ta zare ido ta ce “Kaii Innalillahi, wannan ɗan dukan da na yi mata ne ta karye, zagina fa tayi ta zagi mama, ta dakeni shekaranjiya waccan, amma aka bani rashin…….”

Cikin tsawa Aliyu ya ce”Rufe wa mutane baki, sai ki tashi mu tafi idan kulle ki za su yi ke ki ka jiyo, tashi mu tafi”

Ai ruma ko a jikinta, ta turɓune fuska.

Haka suka tasa ruma a gaba, zuwa police station. Mama sai kiran waya take ta na tambayar meyafaru, Aliyu ya na ce mata babu komai.

Ko da suka je police station, suka tarar da Asiya, an naɗe hannu, ga fuskarta duk a kumbure. Ruma ta kalli babar Asiya, kujera ba ta ɗauketa ba, sai wani benci aka saka mata ta zauna, fuskarta ta sha uban tsagu kwaya-kwaya.

Ruma ta sunkuyar da kai ta na so ta yi dariya.

Suka nemi wuri suka zauna, wani ɗan sanda ya kalli ruma ya ce “Yanzu wannan ce ta karya ta?”

Cikin gurɓatacciyar hausa, babar Asiya ta ce “shi ne ya karya ɗana wannan, ke ni ki ka zana a allo, ban fi babarka kyau ba? Ka zana katuwar mace wai ni ne, kuma ka karya mini ɗa, wallahi ba zan yarda ba, yaro ba tarbiyya”

Ruma ta ce “Ni fa mace ce ba namiji ba, kuma ita ta cewa babata tsohuwa, kuma wallahi mama ta fi kyau”

Ɗan sandan ya dakawa ruma tsawa, amma ko gezau ta tsatstsare shi da ido.

Ta tsuke baki, tana cigaba da zazzago madara a hannunta tana sha.

Aliyu ya yi ajiyar zuciya ya yi ƙasa da murya ya ce “Wallahi idan ba ki nutsu ba, sai na bar ki a wurin nan, su yi miki duk abin da suka ga dama, kuma wallahi matar nan ta zauna a kan ki sai dai buzunki”

Ta waro ido ta ce “Kai dan Allah ka bata haƙuri, ai sai na mutu idan ta zauna a kaina”

Aliyu ya gyara murya, ya dubi ɗan sandan ya ce “Dan Allah Yallaɓai, a yi maganar nan a kasheta a yanzu”.

Ɗan sandan ya ce “A’a, case ɗin a hannun DPO yake, sai kun jira ya zo”

Aliyu  da Headmaster sai bada haƙuri suke, Headmaster sai  cewa yake a samu a rufa maganar nan, a rufe case ɗin tun da abu ne na yara. Amma babar Asiya ta ce ba ta san zancen ba, sai an biwa ‘yar ta hakkinta.

Aliyu suka ɗan fara hira da ɗan sandan da yake wurin, ruma kuwa da sun haɗa ido da Asiya, sai ruma ta zare mata ido. Aikuwa suka haɗa ido da babar ruma, tana zarewa Asiya ido. Aikuwa ta taso tana tafe da ƙyar tana bala’i, ta yo kan ruma.

Ruma ta zabura ta miƙe, ta haye bayan Aliyu ta na ihu.

“Wanna yaron ba shi da mutunci, ba shi da tarbiyya wallahi sai na yi shari’a da baban shi, ya karya mini ɗa kuma yana zare masa ido”

Aliyu ya janyo ruma daga bayansa, ya tankaɗata gaban babar Asiya, ya ce “Ga ta nan ci ubanta tun da ba ta da kan gado”

Ruma ta din ga kurma ihu tana “Na shiga uku, dan girman Allah kiyi haƙuri, ki yi mini rai babarmu” babu kunya babar Asiya ta taso tana ƙoƙarin make ruma.

Ganin rashin dacewar abin da babar Asiya ke shirin yi ne ya sanya, ɗan sandan shiga tsakani yana bawa babar Asiya haƙuri.

Ta hau ta din ga bala’i a kan ko sisi ba zata yafe ba, sai an biya kuɗin maganin da suka kashe.

Aliyu cewa yake “Dan Allah Yallaɓai ka bari ta jibgeta, yadda gobe ba zata ƙara ba”

“A’a gara dai a bata haƙurin, kar karyayyun su zama biyu”

Ihu ruma take yi tana faɗin “Dan Allah babarmu ki yi haƙuri, wallahi ba zan ƙara ba”

DPO ne ya yi sallama, gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan sa.

Nan ɗan sandan ya ƙame tare da sarawa DPO.

DPO ya ƙare musu kallo, sannan ya ce “Sannunku”

Aliyu ya ce “Yauwwa Yallaɓai sannu da zuwa”

Ruma ta durƙusa har ƙasa ta ce “Ina kwana”

“Lafiya lau Baby girl, me ki ke yi a nan ba ki tafi school ba, na ganki da uniform?”

Ƙarasowa babar Asiya ta yi, tinkis-tinkis “Yallaɓai, shi ne yaro da ya gaya maka jiya, ya karya mini yaro a school”

Buɗe baki ya yi, ya na kallon ruma ya ce “Ke, ke ki ka karya musu ‘ya Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ku shigo daga ciki mu yi magana “.

Suka shiga ofishin DPO, ruma sai maƙalewa Aliyu take yi, tana sunkuyar da kai kar su haɗa ido, da babar Asiya.

Tun da suka shiga babar Asiya take mayar da yadda aka yi tana masifa, DPO mamaki yake yadda aka yi ruma ta iya karya wata, ba da abin duka ba da hannunta. Sai da ta gama banbamin bala’inta, sannan ya dubi ruma ya ce “Yarinyar kirki, zo nan”

“Dan Allah ka yi haƙuri kar ka kai ni prison” Ruma tayi maganar tana tauna kwakwa a bakinta.

Yayi murmushi ya ce “Ai ba prison zan kai ki ba, magana za mu yi”

“To rantse” kallon ruma suka yi gaba ɗaya, wai DPO take cewa ya rantse.

Aliyu ya ce”Yallaɓai, dan Allah ka yi haƙuri yarinyar ba ta da cikakken hankali, magani ake nema mata”

Ta yi farat ta ce “Wallahi lafiyata ƙalau”

Aliyu ya kai mata duka ya ce “Ni ne nake yi miki ƙaryar?”

DPO Ya ce “Na fuskanta, zo ki ji kin ji baby girl, magana za mu yi” Ruma ta ɗan matsa gaban teburinsa, amma taƙi ƙarasawa in da yake.

“Garin yaya ki ka iya karya mata hannu?”

Ruma ta ce “Ka na kallon wrestling?”

Ya ce “Sosai makuwa”

“To a nan na koyi ƙarfi, kuma yayyena fa maza ne, su bakwai ne ni ce ‘yar auta a gidanmu, ina da ƙarfi sosai, irin yadda shemaus yake yi a wrestling na gwada ban zaci ana karyewa ba wallahi “

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, kun ga kaɗan daga rashin fa’idar kallon irin wannan abubuwan ga yara kenan. to meya haɗaki da ita ki ka karya mata hannu?”

“Zane ta yi mini a littafina, na yi mata magana ta yaga min  littafi, na rama, shi ne ta din ga zagina, tana yi mini ashar ni kuma bana zagi, ta ce wai babata tsohuwa, shi ne ni kuma na zana babarsu a allo, ta dakeni kuma aka bani rashin gaskiya, ni kuma washegari na rama, ina ga aljanuna ne suka tashi, na yi mata irin na ‘yan wrestling, amma wallahi ban san za ta karye ba, raina ne ya ɓaci sosai”

Headmaster da tun da aka zo bai ce komai ba, sai girgiza kai kawai da yake yi, dan ya rasa me ma zai ce, bai taɓa zaton haka rumaisa take ba.

Headmaster ya numfasa ya ce “Yanzu dai tun da sabga ce ta yara, ayi ƙoƙari a sulhunta kowa ya yi haƙuri”

Babar Asiya kuwa kallon ruma kawai take, yadda take bayani da confidence, tana ciye-ciye kuma aka rasa mai tsawatar mata, sai ma nema ake a goyi bayan ruman.

DPO ya kuma kallon ruma ya ce “Matso nan kusa da ni ‘ya ta, magana za mu yi”

“A’a, ba na zama a kusa da maza, Huzaifa ya ce idan ina zama a kusa da maza haihuwa zan yi, kuma korata za ayi daga gidanmu, idan aka koreni kuma ban san in da zani ba, rannan ma Allah ne ya taimakeni, da malam Habibu ya taɓa mini hannu ban haihu ba, mama ta ce lafiyata ƙalau ba ni da ciki”.

ba ƙaramin dariya ruma ta basu ba, Aliyu ya dafe kai ya sunkuyar ƙasa, ita ruma ba ta san rufi ba, ko zaka kasheta za ta faɗi gaskiya ne”.

Duk yadda aka so yin sulhu, babar Asiya taƙi yarda.

DPO ya ce “Yanzu Madam, so ki ke a kai ku kotu ke da wannan yarinyar jikarki ko kuwa?”

Aliyu ya ce”Yallaɓai, ta ƙirga abin data kashe, in sha Allah ba zai gagara ba sai a biyata”

Sai da ta ji haka hankalinta ya ɗan kwanta, ta lissafa kuɗi dubu talatin da biyar ta ce a biyata.

Aliyu ya ce”Yallaɓai a nema mana sassauci, wallahi yarinyar nan marainiya ce, kuma na gaya maka, tana da matsalar ƙwaƙwalwa, ana kai ta shan magani, ana ta abin da za a ci ga karatun ta, ga rashin lafiya abun da yawa”

“Wallahi lafiyata ƙalau, ni bana rashin lafiya sai zazzaɓi, ko gudawa, amma dai wataran idan raina ya ɓaci sai na ji aljanuna sun tashi, ƙarfina ya ƙaru, idan na kama mutum na dunƙule hannu na dinga dukansa ko hmmm ba a magana, da na ce na daina dambe saboda mama ta daina fushi, ita Asiyar ce ta janyo muka yi faɗa”.

Aliyu ya ce “Dalla rufewa mutane baki, Yallaɓai ba ta da cikakkiyar lafiya”

Headmaster ya ce “Amma ai mu da ku ka kawota makarantar baku gaya mana ba”

Babar Asiya ta dage, ba zata rage ko sisi ba, DPO ya ce zai biya dubu ashirin a aljihunsa, su ruma su biya dubu goma “.

Aliyu ‘yan kuɗin registration ɗin sa ne da yake tarawa, haka ya biya, suka din ga bada haƙuri shi da ruma.

Duk da wannan abu, babar Asiya ba ta huce ba, dan ta so a zane ruma, sai dai bisa ga mamakinta yarinyar sa’ace da ita, babu wanda ya daketa, sai ma nasiha da DPO ya yi mata, yana cewa Aliyu “Ka ga irin wannan yaran, idan aka yi haƙuri, suna da ɓoyayyiyar baiwa da Allah ya yi musu, da al’umma za iya amafana, ku yi haƙuri ku cigaba da kai ta Asibiti tana ganin likita, da sauƙi tun da har tana iya zuwa makaranta, sannan ku kiyaye abin da zata din ga kallo”.

“Kaii wallahi ni babu wani likita da nake gani, nifa lafiyata ƙalau, wato Yaya Aliyu kana nufin ni mahaukaciya ce?” Harar ya watsa mata yana yi mata daƙuwa suka cigaba da magana da DPO.

bayan sun fita daga ofishin, Headmaster ya ce ruma ta zauna a gida, sai wani satin sa duba su gani idan zasu iya bari ta cigaba da zuwa makarantar.

Tsalle ta yi tana faɗin Alhamdilillah.

Aliyu ya girgiza kai ya ce “Mara hankali kawai”

******

“Takawarka lafiya magajin galadima, Allah ya baka yawan rai, ya ja kwanan hajiya” ɗaya daga cikin hadiman Mummy kenan, da ta ware maƙogwaro, take ta zabga wa Adam kirari kamar za ta dungura, maƙogwaronta ko zafi ba ya yi mata.

Hannu ya ɗaga mata, ya cigaba da tafiya zuwa cikin falon.

Sanyi A.C ya cika ɗakin, ga ƙamshin turare da ya haɗu ya gauraye falon.

Risunawa ma’aikatan da ke cikin falon suke yi a gareshi, tamkar sun ga sarki.

Jinjina musu kai ya yi, ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon. Ya shafe a ƙalla mintuna takwas, sannan ta fito cikin wata haɗaɗiyar shadda sai ɗaukar ido take yi.

Ta na ganin Adam, ta yalwata murmushin fuskarta ta ce “Hutawarka lafiya takawa, fatan ana lafiya? Kuma ina fatan ba a gaji da jirana ba, ina shiryawa ne”

Girgiza mata kai yayi ya ce “Barka da wannan lokacin”

“Yauwwa barka dai, an dawo lafiya ya ibada?”

“Alhamdilillah”

Ta sake yin murmushi sannan ta ce ‘Ai har na fara shirin zuwa da kaina na kwashi gaisuwa, na ji labarin ka dawo, amma ba ka zo mun gaisa ba, kuma har aka yi bikin gidan Turaki aka gama ban ganka ba, ko jikin ne?”

Ya ɗaga idanuwansa ya kalleta, amma bai bata amsa ba.

“Well, kun haɗu da Mahmud kuwa?, yazo gari shima ya kusa komawa ma, ya dawo lokacin kana saudiyya”

“Dama zuwa na yi na gaishe ki, and a gayawa su Fauziyya ba na son yawan fitar nan” yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe, ya fara takawa sannu a hankali.

Murmushi ta yi ta bi bayansa da kallo. “A zahiri mutum har mutum, amma baɗini ba wanda ya san cikakken waye, kamar bil adama kamar kuma wani abu daban, da ni ki ke zancen Binta, sai na rabaki da komai sai na tabattar da na huce a kam abin da kk ka yi mini” ta yi maganar a hankali tana bin bayan takawa da kallo.

Ya kai tsakiyar falon, Mahmud ya buɗe ƙofar ya shigo, ganin junansu ya sanya suka yi turus, suna musayar kallo, kamar abokan gaban da suka yi shekara da shekaru ba su haɗu ba sai yau.

LITATTAFAN DA NA RUBUTA SUN HAƊA DA.

ABDULJALAL (FREE BOOK)

AƘIDATA (BOOK1 FREE 2 PAID)

WATA KISSAR SAI MATA (FREE)

WUTA A MASAƘA (FREE)

RUƊIN ƘURUCIYA (BOOK1 FREE 2 PAID)

GABA DA GABANTA (1FREE 2 PAID)

ƘANWAR MAZA (1FREE 2 PAID)

Page 16

Kallon-kallo suka shiga yi wa juna, aka rasa wanda zai bawa wani hanya, Mahmud ne ya fara janye nasa idon ya wuce yana wani irin taku cike da rainin hankali, ya bawa Adam hanya.

Cikin hanzari Adam ya bar falon, yana jin wani abu yana tsikarar zuciyarsa.

Adam na fita, Mummy ta taso ta na faɗin “Mahmud ya haka, meyasa ba zaka tsaya ku gaisa ba, kamar ba ɗan uwanka ba?”

Mahmud ya ce “Mummy, ni baki ga abin da ya yi mini ba? Lokacin da ya sauke girman kai ya duƙa mini, wataƙila na fara saurarasa”

“Haba Mahmud, shi ne fa gaba da kai, ya zaka ce haka? ni fa bana son ace ina ziga ka, kuma ko ba komai ya ci sunan mai martaba, ya cancanci ka girmama shi, kuma idan Allah ya sanya sarautarmu ta dawo gidan nan, ka san shi ne magajin babanku, shi zai zama galadima tun da shi ne babba”

Ya dubi Mummy ya ce “Ni wata sarauta ko wani abu makamancin haka bai dameni ba, a naɗashi sarki ma gaba ɗaya, wannan shi ta shafa, look Mummy, a bar wannan zancen ni bani da lokacinsa, bari na je na karya”  yana gama maganar ya wuceta, ya na bada baya, Mummy ta yi murmushi ta ce “Haryanzu ina wasana yadda nake so, Mahmud dole na ɗarsa maka zaƙin mulki da ƙaunar sarauta, sannan kuma azo a rasa sarautar gaba ɗaya mu je zuwa”.

****

Aliyu suna tafe a hanya, yana ta yiwa ruma faɗa.

“Dan ubanki kuɗin makaranta na, na registration na fara tarawa, yanzu kin saka na kwashe na bayar a banza, ban ci ba ban sha ba, dan ma Allah ya sanya DPO ya biya mafi yawa daga kuɗin. Saboda ba ki da mutunci ina kareki ki na ƙaryata ni, ni dama na ƙyaleta ta yi miki shegen duka”.

Ta waro ido ta ce “Kaii, idan ta sumar da ni fa?”

“Ai gara ta sumar da ke ɗin, tun da ke dai har abada ba kya hankali, wai ki ka karya ‘yar mutane saboda tsabar kanki ba daɗi”

“To ba kai ne ka ce mini mahaukaciya ba, wai ana kai ni asibiti”

“To meye marabarki da mara hankalin? Zaki gane kurenki ne, bari mu je gidan sai na daki kuɗina” har suka isa gida, ruma ba ta sake cewa komai ba.

Mama na ganin Aliyu tare da ruma sun dawo, ta fito daga ɗaki ta na tambayar ko lafiya?

Ruma ta ɗan sosa kai tana kallon Aliyu.

“Zaki dai na kallona ko sai na tsokane idon? Sai ki yi mata bayanin abin da ki ka yi ai”.

Ruma ta kalli mama, kamar zata yi kuka ta ce “Wallahi mama tsautsayi ne”

“Tsautsayin me? Me ki ka aikata kuma?” Ruma ta yi tsilla-tsilla da ido.

“Ba zaki gaya mata ba”

“Mama, da wasa fa na gwada irin na wrestling ɗin nan, shi ne wata ta karye”

A ɗan hasale mama ta ce “Kai ka gaya mini abin da ta yi mana, ka tsaya ka na mini wasa da hankali”.

Aliyu ya yiwa mama bayanin abin da ruma ta aikata, da yadda suka yi, zuwansu police station yanzu.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Allah ka shiga lamarina, Allah ka dubeni a kan halin wannan yarinyar”.

“Mama dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba, ita ta fara tsokanata na rama, ban san zata karye ba wallahi”

Mama ta dube ta ta ce “In dai kece, ba zaki canza hali ba, yanzu ruma har ta kai ki ga zuwa police station ruma, kaf yaran nan yayyenki babu wanda ya taɓa zuwa wurin ‘yan sanda, sai ke ruma ko? Allah ya yi miki magani, ki je ki yi ta yi kar ki fasa” mama na gama maganar ta shige ɗaki ta bar ruma a wurin.

Ruma ta kalli Aliyu ta ce “Kai baka da rufin asiri, wallahi da yaya usy ne zai rufa mini asiri, amma na fuskanci da kai da Yasir, da Huzaifa baku taɓa rufa mini asiri ba, ƙiris ku ke jira …..

“Dalla rufe mini baki, tun ban daki kuɗina a jikinki ba, dubu gomar nan ta tsaye mini, ni Wallahi da ma ƙyaleki na yi su yi miki duk abin da suka ga dama” ɓata fuska ta yi, ta bi bayan mama, sai dai mama sam taƙi kulata, wanda hakan ba ƙaramin tayar wa ruma hankali yake ba.

Wunin yau gaba ɗaya aka rasa mai saurara ruma, duk wanda ta yiwa magana sai ya hantareta gaba ɗaya haushin abin da ta yi suke ji.

“Hmm huzaifa ni fa Allah ne ya taimake ni, da matar cewa ta yi sai ta dakeni, ka ganta kuwa, ƙatuwace sosai da sosai fa, a kan benci ta zauna, kaga hannun ta a cure da nama, idan ta dakeni ai ji zan kamar an buga mini guduma”

Usman ya ce “Sai na zubar da haƙoranki, ba zaki nutsu ba ko?, ki ke cigaba sa kwatanta yadda take, ina ma Alin ya bar ta ci ubanki, ke ban da rashin kan gado, kawai ki je ki karya ‘yar mutane saboda tsabar wauta ta yi miki yawa, sai ka ce wata rainon gaɓa-gaɓa?”

Aliyu ya ce “Kai ba ka san abin takaicin ba ma, har da wani cewa ai aljanunta ne suka tashi, ba a hayyacinta ta daki yarinyar ba, tsabar cin kai”

Mama ta ce “Ba ku ne ku ke zigata ta ɗauko magana, ku ka ce kun tsaya mata, dole ta yi abin da ta ga dama ai, kuma daga yau duk wasu tashoshi na wrestling a gidan nan sai an sauke mini su, an daina kallon sa a gidan nan, kai kallon ma sai an daina”

Ruma ta waro ido ta ce “Mama, shikenan sai na daina ganin saurayina na wrestling”

Usman ya ce “Au ke har wani saurayi ne da ke a wrestling ɗin?”

“Eh mana, ba ka san shi bane, Huzaifa ya ma sunan sa, ɗan tuna mini, idan na ganshi har wani daɗi nake ji”.

Huzaifa ya ce “Ke ki ka san shi ni ban san shi ba”

Yasir yayi tsaki ya ce “Wallahi Mama mi bamu go ahead, mu yi wa yarinyar nan ruƙiyya ni da Huzaifa, mu samo tsumangiya in cuɗa mata jikinta in haɗa da ayar Allah wallahi dolen aljanun na ta su magantu”

“Wallahi ni ba ni da aljanu sai raina ya ɓaci, kuma na sha tabara da ayatul kursiyyu, na fi ƙarfin aljani da makiri ko tsunburbura na fi ƙarfinta”

“Ke dalla ware, ai ke kin fi tsunburburar ma rashin ji” suka din ga caccakar ruka kamar zasu daketa.

Ita damuwarta a kan mai sunana Baba ne, hukuncin da zai ɗauka a kan ta, na abin da ta aikata, sai ta ji bai ce komai ba ma, yayi shiru kamar bai san me aka yi ba.

***

Tsaye yake a bakin wardrobe ɗin, yana ƙarewa kayan ciki kallo kamar ba nasa ba, ya saka hannu da nufin ya ɗauko kaya, hannunsa a sauka a kan koriyar alkyabbarsa.

Kamar ya na jin tsoron Alkyabbar, ya zarota ya na kallonta.

*Sarki mai koriyar alkyabba a dawo lafiya, ka ɗanani a kan dokinka ko ka bani kyautar doki*

Shiru ya ɗan yi ya na tunani, ta yaya zai ji murya ɗaya a mabanbantan wurare, kuma haryanzu bai kai ga ganin fuskar wacece ba, gashi a duk lokacin da zai ji muryar, sai ta kira shi da sarki!.

Ajiye Alkyabbar ya yi, ya ɗauko wata dark blue ɗin suit, ya shirya a cikinsu ya ɗauki jakarsa ya fita.

A ɗaki ya tarar da Ammi tana sallar walaha, ya zauna ya jira ta idar.

Ta idar ta kammala Adduointa, sannan ta kalli Adam ta ce “Barka da wannan lokaci takawa”.

Yayi murmushi ya ce “Barkanki Ammi, zan wuce ne”

Cikin tausayawa ta kalleshi ta ce “Ka na ganin babu matsala, zaka iya zuwa aikin?”

“Babu wata matsala in sha Allah”

“To matso na yi maka addu’a” ba musu ya matsa kusa sa Ammi, ya durƙuso mata da kansa, ta ɗora hannunta na dama a kan nasa, ta dinga kwararo masa Adduoi.

Wata irin nutsuwa ya din ga ji ta na ratsa shi, ya lumshe idonsa, sai da ta idar, sannan ya riƙe hannun ya sumbaci hannun ya ce “Allah ya ja zamanin giwar Galadima, ya baki yawan rai, Allah ya jiƙan Galadima”

Murmushi ta yi, tare da jin maganar har cikin ran ta ta ce “Amin takawa, Ubangiji Allah ya tsare” ya miƙe yana faɗin Amin, ya bar ɗakin.

***

Tun da abin nan ya faru, an kai ruwa rana sosai, kan malaman su ruma su yarda ta cigaba da zuwa makarantar, bisa sharuɗai sannan ruma ta cigaba da zuwa makarantar.

Tun baya da aka yi sulhu a police station, duk ranar juma’a sai mama ta aika wani ya tasa ruma a gaba sun je duba Asiya, sun kai wani abu, amma kullum babar Asiya babu godiyar Allah, kullum suka je sai ta yi complain, ita kuma ruma kan su taho, sai ta aikata wani abun da za ta sake tunzarata tayi ta masifa.

A haka duk suka ce sun daina zuwa, yau mama ta ce dan Allah mai sunan Baba ya saka ruma a gaba su je.

Tun da Allah ya sa babar Asiya ta yi arba da fuskar mai sunan baba, ta shiga hankalinta, ko maganar kirki ta kasa sai kame-kame.

Tun da suka gaisa, ya bata abin da zai bata, ya ce ruma ta tashi su tafi, ko yaya mai jiki bai ce ba balle ya ce Allah ya kyauta.

suka taho hanya, ruma a nutse take babu tsokana da hauma-hauma, saboda kura ta san gidan mai babban sanda.

da suka zo bakin layin su, cikin girmamawa ruma ta kalli mai sunan Baba ta ce “Mai sunan Baba, mama ta ce na taho mata da kayan miya a wurin Hudu”

Ya kalleta ya ce “Idan kin ga dama, ki tsaya hauma-hauma da neman magana a hanya, zaki zo ki sameni”.

“In sha Allah ba zan yi ba”

Ganin da mutane a wurin Hudu, ya sanya ruma ta tsaya ta na jira, sai dai kan ya kawo kanta, ta ɗau wuƙa ta din ga daddatsa masa kabewa bai sani ba.

Da ta gaji ta ce “Malam hudu ka sallameni mana”

Ya ce “Yi haƙuri na fara sallamar matan aure, su da zasu ɗora girki”

Ruma ta yamutsa fuska ta ce “To da me matan auren suka fini? Nima fa watarana matar auren nan ce”

Yayi murmushi ya ce “Eh, amma dai yanzu ƙwaila ce, Allah ya nuna mana kin zama matar aure ruma”

Ta haɗe rai ta ce “Gaskiya malam Hudu ka daina gaya mini wannan kalmar ta watsewa, ƙwaila fa iskanci ne”

Ɗan buɗe baki yayi ya na kallonta, sai kuma ya ce “To Allah ya baki haƙuri” sai da ta bawa mutanen wurin dariya.

Can ta kalli Hudu, ta kalli lafcecen billensa kamar an yi masa da gatari ta ce  “Malam Hudu, na daɗe da tambayar nan a zuciyata wai meyasa aka yi maka bille?”

Yayi murmushi ya ce “Delu billen mahauta ne”

“To amma dai da wuƙa aka yi maka ko?”

Ya ce “A’a, aska ce, billen gado ne na mahauta”

“To kai baka gaji kuɗi ba sai bille, da babanku ya mutu sai aka raba muku billen?”

“Ke na gaji da wannan wulaƙancin naki, mai zan baki?” Ruma ta miƙa masa kuɗi, ta yi masa bayanin abun da zai bata, ya sallameta ta tafi gida.

Da ta je gida, ta haɗa kayan miyan, ta gyara su ta tafi kai markaɗe.

****

Tsaye take a harabar Hotel, tana sanye da doguwar riga ja, ta naɗe kanta da jan mayafi, fuskarta sanye da tabarau da kuma takunkumin fuska, dan haka idan ba wanda yayi mata cikakken sani ba, ba yadda za ayi ka ganeta.

Wayarta ta ɗauko ta kira wata lamba, ta kara a kunnenta, a ɗan hasake ta ce “Gani nazo ka na ina?”

“Room A7, Vip” ta ajiye wayara, ta shiga cikin hotel ɗin, babu wanda ta tambaya da kanta ta gano ɗakin, ta tsaya a bakin ƙofa, ta kuma kiran wayar “Gani a ƙofar ɗakin” ta faɗa a taƙaice.

Wani mutum ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya leƙo ya ce “Ke ce baƙuwar yallaɓai?”

“Kai ka san wani Yallaɓai, ka je ka gaya masa gani na zo”

“Ok, to dama cewa ya yi a shigo da ke”

“Ba zan shigo ba, idan ya matsu ya fito idan kuma ba a matse yake ba zan yi tafiyata, bana son jira”.

Ya ɗan yi jimm ya ce “Amma kamar maganar ki ta yi tsauri”

A fusace ta ce “Kai ka san wacece ni kuwa? Na yi mai wuyar ai da na zo nan, idan ba zai fito ba zan tafi”

Juyawa mutumin ya yi ya koma cikin ɗakin, babu daɗewa sai ga wani mutumin ya fito, shi ma fuskarsa rufe da takunkumi.

“Ki shigo mana, zuwa bai yi miki wahala ba sai shigowa?”

“Ba zan shigo ba, ka gaya mini koma menene a nan ina jin ka”

Ya ce “Well, mu je ƙasa to, sai mu yi magana”

Tare suka sauka ƙasa, suka samu wuri suka zauna, ya dubeta ya ce “To sauke takunkumin mana”

“Ba zan sauke ba, wai tukuna kai wayene naga kamar ka na ƙoƙarin raina mini hankali”

Murmushi ya yi, ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce “Khalifa senator usman, na san kin sanni kuma kina jin sunana, kuma kin san me nake nema”

Ajiyar zuciya ta yi, ta sauke na ta takunkumin ta ce “Dama kai ne? To Meyasa ka ke nema na?”

“Samha kenan, kin san ita kasuwar muradi babu in da ba ta kai mutum, ba wani abu ne ya sa nake neman ki ba, sai dan mu haɗa hannu na taimake ki, ki taimake ni. Ban sani ba ko baki sani ba, amma na san kin san Adam, Adam ya na barazana ga mutunci da rayuwar mahaifina, da kuma ni kaina da career ta, dan haka nake son ki taimakeni na kai shi ƙasa, zan baki kuɗi ko nawa ki ke bukata” yayi maganar yana tsareta da ido.

Ta cire gilashin fuskarta, ta dube shi ta ce “Da ka tashi binciken ba ka binciko da cewa, Adam ba ɗan uwana ne ba kawai, shi ne mutumin da nake so, kuma nake muradin aure”

Ɗan waro ido ya yi ya ce “Kuma!”

“Ƙwarai kuwa, sannan kar ka manta, ni ‘ya ce da na fito daga gidan sarauta mafi daraja a nahiyar Afirka, sarautar Kano, dan haka kar ka yi zaton zaka ruɗeni da kuɗi, kuma kar ka sake nemana”

Khalifa ya ce “A’a Samha, kar ki yi gaggawa, ki yi tunani dai”

“Babu wani tunani da zan yi” ta tashi ta mayar da tabaranta, ta na ƙoƙarin tafiya, Khalifa ya sha gabanta ya ce”Samha ki na abu kamar ba wayayyiya ba, ki rubuta ki ajiye, za ki neme ni da kanki a nan gaba”

Ba ta kuma tanka masa ba, ta raɓa shi ta wuce.

***

Abdallah ya na ta wanke kayan mama tare da na ruma, mama kuma tana aikace-aikacenta, ruma tana ta yanka salak, sai ta ajiye wuƙar ta riƙe haɓa ta ce “Mama, kin san wani abu?”

“A’a”

“Ba kin ce mini mutane ta baki suke haihuwa ba?”

Mama ta ce “Eh”

“To wallahi akuyoyi ta ɗuwawu suke haihuwa, ta wurin kashinsu in gaya miki, ɗazu da na kai markaɗe na gani a gidan”

Abdallah ya ce “An zo wurin”

Mama ta yi tsuru ta rasa me zata gaya wa ruma.

“Wallahi mama da gaske nake, ta wurin kashi suke haihuwa, akuyar ta din ga kuka, baki ga abin ƙyama ba, na tsura mata ido, ta bani tausayi, Allah ya taimaki mutane ta baki suke haihuwa, idan ka haihu ta wurin kashi, ai idan ka na ji kashi sai dai ya zubo, dan wurin ba zai rufu ba”

Mama ta share ruma, ba ta ce mata uffan ba, hakan bai sanya ruman ta gaji ba ta kuma cewa “Mama kaji ma fa ta wurin kashinsu suke yin ƙwai, to Meyasa mutane suke haihuwa ta baki, na ga dai baki ƙarami ne”.

A ƙule mama ta ce “Ke ki ƙyaleni, idan na kuma aiken ki kai markaɗe, ki ka kai gidan sai na zane miki jikinki, ita ma saboda wauta ta bari ki ke kallon haihuwar akuya”

Ruma ta yi shiru ta sunkuyar da kai, Abdallah kuwa kamar ya bushe da dariya, ganin yadda mama ta hasala, gashi ba abin kayi wa ruma bayani ba, ka na gaya mata abin da kan ta bai ɗauka ba, zata kuma gangamo maka wata maganar.

Ko da dare yayi, ruma ta na shirin kwanciya barci, ta ce “Mama, dan Allah ki tasheni na yi sallar dare, zan roƙi Allah abubuwa da yawa”

Mama ta ce “To, Allah ya sa silar shiriyar kenan”

Ruma ta kwanta ta ji daɗin katifar, bacci ya fara ɗaukarta, ta ce “Mama ko na baki sallahun Addu’ar ne, ina ga ba yau ba, ba zan iya tashi ba, ki yi mini addu’a Allah ya sa na samu saurayi nima na din ga zance, ‘yan ajinmu na islamiyya su yi ta bayar da labari, ni kuma ban san me ake ji a zancen nan ba, amma dan Allah kar ki roƙo mini mummuna mama”

Mama kawai ta cigaba da abin da take, ruma ta gama surutanta, bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe kowa yana ta azamar ya kammala abin da zai yi da wuri ya fita, ruma kuwa sai cin abinci take sannu a hankali ta na murmushi.

Abdallah ya kalleta ya ce “Ke lafiyarki kuwa?”

Ta yi murmushi ta ce “Mama jiya kin yi mini addu’ar da na baki sallahu kuwa?”

“Ruma addu’a, ai kullum cikin yi muku nake”

Ruma ta sake murmushi ta ce “Abdallah ka san mafarkin me na yi yau?”

“A’a”

“Mafarki na yi wai ana bikina, kai ka ga angon mai kyau, kai Allah dai ya sa na yi tsayi ayi mini aure, dama Hudu mai kayan miya jiya yaƙi sallamata, wai ni ba matar aure bace ba, ba ka ga angon ba, sai so nake na ɗago na kalleshi ina ta irin sunkuyar da kan nan na amare, ina…… Shiru ta yi da idonta ya sauka a cikin na mai sunan Baba a tsaye, ya naɗe hnnayensa ya na kallonta.

P 17

Shiru ta yi ta kasa cigaba da maganar, ta zuba masa ido ta na jiran ta ji mai zai ce.

Ya tako a hankali ya zo gabanta ya tsuguna, ya na kallon idonta. Cikin sauri ta sunkuyar da kan ta ƙasa, tana jin yadda abincin da ta ci ya tsaya mata a ƙirji, ga wani irin ƙugi da cikinta yake yi mata saboda tsoro.

“Aure ko, shi ki ke so?” Da sauri ta girgiza masa kai alamar a’a.

“Ki je ki dawo daga makarantar, za mu yi magana in dai aure ne baki da matsala, za’a aurar da ke tun da shi ki ke so” da sauri ta ɗago, ta kalleshi za ta yi magana, amma ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce “Shhh, tashi ki wuce ki tafi makaranta”

Kamar wadda aka gayawa mummunan saƙo, jiki babu ƙwari ta bar gidan ta tafi makaranta, sai dai kamar ta faɗi a hanya, dan jefa ƙafarta kawai take yi, maganar mai sunan Baba ta tsaya mata da yawa.

***

Samha ce zaune a kan gado, hannunta riƙe da waya, ɗaya hannun kuma tana wasa da gashin kanta, amma hankalinta ba a kan wayar ba, zancen zuci take yi.

Ƙarar buɗe ɗakin ne ya dawo da ita hayyacinta.

Fauziyya ce ta shigo, ta ajiye jakarta ta zauna a kan gadon, ta dubi Samha ta ce “Ke jiya ki ka shanya ni ina jiranki, amma ki ka ƙi zuwa”

Samha ta ɗan lumshe ido, ta buɗe tare da ajiyar zuciya.

“Ke wai meye haka ne?”

“Ke bari kawai”

“Ban gane in bari ba, kin san ba ma ‘yar haka da ke, explain kawai madam”

Samha ta dubi Fauziyya ta ce “Jiya na je mun haɗu da gayen nan fa”

Fauziyya ta waro ido wace ta ce “Ki na da hankali kuwa? Mutumin da baki sani ba ki ka je wurin sa?”

“Eh tare da security na je, sai dai ban bari ya sani ba, kin san waye ma tukuna?”

“A’a, sai kin faɗa”

“Khalifa Usman wakili”

“Meye haɗinki da shi? Ko ya na ciki ne?”

Samha ta yi tsaki ta ce “Ke ba wannan ba, wai yayi bincike a kaina, so yake na taimaka masa ya kai takawa ƙasa, saboda yana barazana ga feature ɗin sa, da mahaifinsa”

Fauziyya ta zaro ido ta ce “Yaya Adam dai?”

“Shi fa”

“To me ki ka ce masa?”

“Fauza, kin san ina son Adam, ba zan goyi bayan a cutar da shi ba, dan haka nace masa ba zan iya ba, kar kuma ya sake nemana”

“To meyasa?”

“Fauza yayanki ne fa, kuma kin san abin da yake zuciyata game da takawa”

Fauziyya ta jinjina kai ta ce “Na san yayana ne, amma ke yanzu haryanzu ki na nan a kan bakanki kina son sa, ana barin halak dan kunya fa”

“Ke ki ka san ta, ita halak ɗin, bari na shiga wanka” ta yi maganar tana miƙewa.

Ɗan shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci ‘wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani’ da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga ɗakin.

***

Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.

Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.

Gabanta ne ya faɗi da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.

Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.

Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.

Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai.

“Ɗago ki kalleni” ya faɗa a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

“Aure ki ke so ko?” Nan ma ba magana sai girgiza kai.

“Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura ɗin, ranar juma’a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta”

Da sauri ta ɗago ta kalleshi, “Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba”

“Ƙarya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so”

“Wallahi a’a, ban san batsa nake tambaya ba”

“Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma’a za a ɗaura miki aure”

“Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba”

“A ina saurayin naki yake?”

“A cikin tv nake ganinsa, ɗan wrestling ne, amma ban san a ina yake ba”

Mai sunan Baba ya kalleta ya ce “To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to saƙonki ya isa za ayi abin da ki ke so”

“Wallahi yaya ba haka nake nufi ba”

“To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu’a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?”

Cikin kuka ta ce “Wallahi ban sani ba”

Ya sake tsuke fuska ya ce “Ƙarya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan”

“Wallahi ban sani ba, ‘yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa”

“Wace irin soyayya?”

“Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da daɗi, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba”.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce “Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma’a ɗaurin aure”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan girman Allah ka yi haƙuri, manya ake yiwa aure ban da yara”

Cikin zafin rai ya ce “Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri” jiki na rawa ta tafi ɗaki, tare da fashewa da kuka.

Gaban mama ta je tana kuka ta ce “Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini”

“To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya zaɓa miki shikenan”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi”

Mama ta ce “Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya”

Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ƙarshe a nan wurin bacci ya kwasheta.

Da safe kuwa wasan ɓuya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, taƙi yadda su haɗu, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

Ruma fa gaba ɗaya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.

Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta ɓuya sai kuka, duk ta rasa sukuni.

Mama ta shiga banɗaki ta lallaɓa ta ɗau wayarta, ta kira Abubakar.

Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya faɗi “Ruma, menene? Meyafaru?”

“Yaya, mai sunan baba ne”

“Me ya same shi, me ya yi miki?”

“Wai aure zai yi mini, dan Allah ka yi masa magana, mama taƙi hana shi, dan Allah ka ce masa ni yarinya ce, dan Allah kar ayi mini auren nan bana so”

Cikin rashin fahimta ya ce “Wani irin aure kuma?”

“Haka ya ce wai ranar friday zai mini aure da wani, dan Allah ka hana shi”

“Kwantar da hankalin ki ‘yar gudaliyar, zan kirashi in sha Allah, ki daina damuwa”

“A’a ba zan iya dainawa ba, ka kirashi yanzu kawai”

“To an gama, kiyi haƙuri babu mai yi miki wani aure yanzu”.

Ya yi ta kwantar mata da hankali, har ta samu ta ɗan nutsu.

***

Yana zaune a falo, yana duba labarai a wayarsa, Mummy na gefe tana shan fruit, ta kalli yadda ya sha fararen kaya, da shuɗiyar alkyabba hannunsa ya sha zobbunan azurfa, sai kaɗa ƙafa yake a hankali.

Ta yi murmushi ta ce “Ka ga kyan da ka yi kuwa? Sai ka fito a basaraken ka na asali jinin galadima, Allah ya kawo gingimemiyar kujera”

Bai kalleta ba ya ce “wace irin kujera ce gingimemiyar?”

“Ka gaji Galadima mana, ko ma kujerar garin gaba ɗaya”

Mahmud ya ce “Mummy you are funny, ni fa sabgar sarautar nan ba ta dameni ba, ki bar ni da karatuna, na kammala na samu aikina period, shi dai da yake ta zazzare ido, na san bai wuce a kan sarautar ba, sai ya je yayi ta yi”

Cikin mamaki ta kalli Mahmud ta ce “Mahmud, wai kai meyasa ba ka da kishin zuci ne, sarautar nan fa taku ce, ta mahaifinku ce gaba ɗaya a ka ɗauka aka kai wani gidan, kuma muna saka ran za ta dawo mana, tun da galadiman yanzu shi ma yana can babu lafiya, kuma da zarar ya mutu babu batun wani ya gaje shi, tun da duk ‘ya’yansa mata ne, Jabir kuma bai isa ya saka rai ba, dole gidan nan za ta dawo. Dan haka ba zan zuba ido a bawa Adam sarauta bayan ga ka ba, kai ma ɗan galadima ne, dan haka kai ma ka cancanci ka gaji sarauta”.

Mahmud ya ɗan yi shiru ya na tunani, amma bai ce komai ba.

“Mahmud, kar ka watsa mini ƙasa a ido, idan ba haka ba, haka fa zamu cigaba da zama Giwar Galadima ta mamaye komai, ta cigaba da juyamu yadda take so, yaka ke gani idan sarauta ta dawo Adam ya samu, kai menene naka, a wani babin ka tashi?”

Ajiyar zuciya Mahmud ya yi, ya fesar da iska daga bakinsa, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta ya ce “Mummy, zan je salla daga nan zan ɗan shiga gari, sai na dawo” yana gama maganar ya miƙe a hankali ya bar falon.

Fauziyya da ke laɓe take jin su ta fito, ta nufi wurin Mummy ta zauna tana murmushi ta ce “Hajiya Mummy, mai abubuwan ban mamaki, irin wannan famfo haka?”

Mummy ta yi murmushi ta ce “Ai ba ayi komai ba ma tukuna, dole sai na sakawa Mahmud ƙawazucin kujerar nan, yaron nan akwai baƙin taurin kai, ɗan uwan ɗayan ne a taurin kai, tun da ƙuruciya nake kwaɗaita masa daɗin mulki, amma yaƙi ganewa, amma zan cigaba da gwada masa fa’idar ace mulki yana hannunsa, in sake rura wutar ƙiyayya a tsakaninsa da Adam, kuma in toshe kafar da sarautar za ta dawo gidan nan, dan ita ma Hajiya Lubabatu kwaɗayi take na ta ɗan ya gaji sarautar idan mahaifinsa ya mutu”

Fauziyya ta jinjina kai ta ce “Mummy kenan, akwai lissafi, na zo miki da wani labari ne mai daɗi”

“Wani labarin kenan?”

“Khalifa Usman wakili, kin san case ɗin su da takawa, kusan shi ne yake trending a media yanzu”

Mummy ta jinjina mata kai.

“To dai in gaya miki shi ne ya gayyaci Samha, wai yana son su haɗa kai, su kawo ƙarshen yaya Adam, ita kuma ta ce bata yadda ba, kin san son shi take yi”

“Eh, na sani, ai itama Samha wata makami ce da nake amfani da shi ta ƙarƙashin ƙasa, amma labarin nan yayi mini daɗi sosai, ke dai ku cigaba da baza kunnuwa, duk abin da ku ka ji, ko kuka gani kawai ku sanar da ni”

“In sha Allah Mummy, Allah ya ida nufi”

Suka yi murmushi gaba ɗaya.

Takawa ne zaune a wani ƙaton falo, mai ɗauke da kayan ado na gidan sarauta, gefe gud kuma tarin litattafai ne a jere a cikin wata drower.

Ya sanya system a gaba, yana dannawa yana ɗan juyi a jan kujerar da yake kai.

Jabir na zaune a kan kujera yana facing ɗin sa. Jabir ya tattara nutsuwartsa a kan Adam ya ce “Takawa, kana bibiyar shafukan sada zumunta kuwa?”

“Meyafaru?”

“To ai gani na yi ka yi burus, kamar baka bibiyar meke faruwa”

“Shi ya sanya na tamabayeka, meyafaru?”

“Tone-tonen da ka ke ƙoƙarin yiwa Senator usman wakili, akwai ƙura fa sosai da sosai”

Ya ɗan ɗago ya kalli Jabir ya ce “Ai ni ƙurar nake son ta tashi, ta hana kowa nutsuwa, saboda haka nake wannan aikin”

“Duk da haka, ko dan tsaron kannka da lafiyarka, yakamata ka san yadda zaka din ga gudanar da ayyukan ka, taɓa manyan nan ba abu bane ba sauƙi ba fa”

Adam ya yi murmushi ya ce “Na fahimce ka mutumina, kar ka wani damu, ka tayani da addu’a kawai, amma dole mu yi wa ƙasarmu hidima”

Jabir ya jinjina kai ya ce “Haka ne”.

***

Bil haƙƙi mai sunan Baba ya nunawa ruma aure zai yi mata, ya je ya a sayo sabuwar katifa ta ‘yan makaranta, ya ce wa mama gata nan a ajiye ta ruma ce, ya sayo kwano da kofin silba mai murfi da sabuwar buta, shi ma ya ce na ta ne.

Hakan ya ƙara dugunzuma hankalinta, cikin dare mama ta na bacci ta ga ruma tana shimfiɗa sallaya tana kuka.

Mama ta ce “Ke lafiyarki kuwa?”

“Sallar dare zan yi, na roƙi Allah a kan mai sunan Baba, tun da kin ƙi ki hana shi, an rasa wanda zai hana shi yi mini aure”.

Mama ta yi murmushi ta ce “Ke fa ki ka ce kin ji kin gani, ki yi addu’a kawai Allah ya baki zaman lafiya da ke da wanda zai aura mikin”

Zaman dirshan ruma tayi, ta ɗora hannu a ka tana kuka, mama ta rufe fuska tana yi mata dariya ba tare da ta sani ba.

Ruma ta daɗe a sujjada tana addu’a, sannan ta koma ta kwanta.

A islamiyya kuwa, malamin ajin da take ne, ya lura yana ƙari tana kuka, dan yanzu a ɗan samu cigaba, ta daina guje-gujen aji, a babban aji da ajin su Yasir take zama, kuma yanzu tana iya karatu ba kamar da ba.

Sai da ya kammala ƙarin Alqur’ani, sannan ya kira ruma yana tambayarta me ya sa take kuka?

Ba ta gaya masa ba, ta ce mai babu komai, ƙarshe sai ƙyaleta yayi.

Ranar juma’a kuwa da farar safiya da kuka ta tashi, dan yau ne kwanakin da mai sunan baba ya ɗibar mata suka cika, ba tare da ta samu wanda za ta kawo ba, a matsayin wanda take so, to ita wa ma take da shi.

Mama sai fama take da ita ta shirya ta tafi makaranta, amma ta rungume uniform ɗin tana kuka.

Umar ya fito fuska a haɗe ya daka mata tsawa, cikin tsuma ta hau saka kayan ba tare da ta yi ko wanka ba.

“Ki fice ki tafi makaranta, idan kin je can sai ki yi musu kukan, shi ne ki ka gayawa ɗan uwa wai zan yi miki aure ko? To shi ma bai isa ya hanani abin da na yi niyya ba, ai ke ki ka nuna ki na son auren, wuce ki bawa mutane wuri”

Kamar korarriya, ta ɗau jakarta ta tafi makaranta.

Bayan fitarta, mama ta kalleshi ta ce “Babana, a sassauta mata ta horu haka, kwanaki uku kenan ba ta ko cin abinci, ayi mata afuwa babana”

“Ƙyaleni da ita, horata kawai nake, amma yau zan ƙyaleta in sha Allah”

Ƙin shiga makarantar ta yi, ta tsaya a waje tana kuka, mai gadi ne ya ganta, ya ja ta ya kaita ofishin Headmaster, ya sanar masa da a waje ya ganota ta tsaya ta na kuka.

Headmaster ya ce “Ai ni rigimar yarinyar nan nake tsoro, ke me aka yi miki?”

“Yayana ne ya ce zai yi mini aure yau”

Waro ido ya yi ya ce “Aure kuma? Waye zai kwasa? Ke bana son wasa”

“Wallahi haka ya ce”

Headmaster ya kalli ruma, sai ya kawo ko rashin hanklin ruman ne ya motsa, dan haka ya ce “To shikenan, ki yi haƙuri ki tafi aji, zan kira gidan na ku mu yi magana da su” yayi ta lallaɓa ruma ya kaita aji.

Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba, sai da ta dawo gida ta tarar mama tayi tuwon shinkafa da miyar taushe, da wainar masa wai azo a kai maƙwabta ace na auren ruma ne, mai sunan Baba ya ci farar shadda ya fito tsakar gida ya ce “Mama, idan an idar da sallar juma’a za a ɗaura mata aure, sai ayi mata addu’a”

“Na shiga uku, mama wai da gaske ne? Mama ku yi mini rai ban isa aure ba wallahi”

Wani mugun kallo ya yi mata, ta shige ɗaki da gudu tana kuka, ya fice ya bar gidan.

Dariya Huzaifa ya din ga yi mata yana “Ruma, Allah ya sanya alkhairi zan kawo miki goron ɗaurin aurenki har gida ki tauna, dan mijin naki ma tsoho ne, malam labaran ladan ne”

Ruma sam ba ta shiri da malam labaran ladan, saboda ya taɓa tsula mata carbi, wataran yana kiran salla, ta taɓa tsayawa a ƙofar masallaci tana  kiransa da ƙarfi, wai saboda muryarta ta fito a sufika, ya idar ya kamata ya zane ta da carbi, gashi tsoho sosai.

Mama ta shiga ɗaki ta tarar da ruma sai rizgar kuka take.

“Haba amarya, ya da kuka kuma kamar ba amarya ba?”

“Dan Allah mama ki bani kuɗin mota na gudu”

Mama ta kwashe dariya ta ce “Dama ruma akwai abin da zai baki tsoro haka?”

Rungume mama tayi cikin kuka ta ke faɗin “Dan Allah mama kar ayi mini aure, wallahi na daina rashin ji, ina sonki sosai, bana son na rabu da ku, mama zaki yadda a aura mini wanda ya dakeni dan Allah mama ki hana shi aurar da ni”

Rungumeta mama ta yi tana murmushi, tausayin ruma ne ya kamata, dan har ramar dole ta yi, saboda damuwa.

Mama ta zubo mata abinci, ta zaunar da ita ta bata, amma ruma taƙi ci.

Mai sunan Baba suka yi sallama, duk suka shigo a tare daga sallar juma’a, duk sun sha kwalliya.

Aliyu ya ce “Amarya kin sha kuka, to Allah ya sanya alkhairi” ta rirriƙe mama tana girgiza kai tana zubar da hawaye.

Mama ta kalli mai sunan Baba ta ce “Tuba muke babana, Allah ya bada haƙuri duk ta rame, ayi haƙuri”

Yasir ya ce “Haba mama, ya zaki yi mana haka?”

Mama ta yi masa daƙuwa tana harararsa.

Umar ya ƙarasa gaban ruma da ta takure a jikin mama, tana share hawaye.

“Kalleni” yayi maganar yana tsareta da ido.

Ta ɗago a hankali ta kalleshi, idanunta sun yi jawur.

“Daga rana mai kamar irin ta yau, idan na sake jin ki aikata wani abu na rashin mutunci, ko wannan shegen surutun naki, to ki tabattar aure babu fashi, kin ji na gaya miki?” Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume mama.

Mama ta ce “To madalla godiya muke, Allah ya rayaki, ya kaimu auren ki na gaske, da miji na gari ko?”

“Ni ba zan aure ba, bana so da ma da wasa nake, kuma ba zan auren ba”

Mama ta ce “Tashi ki yi godiya, tun da dai ya janye maganarsa”

“Na gode” tayi maganar tana ɓoye fuskarta.

Tashi yayi ya bar ɗakin ba tare da ya ce mata komai ba, ta din ga sauke ajiyar zuciya ta ce “Amma an shiga hakkina, Allah zai sakawa marainiya”

Yana tsaye a bakin ƙofa, karaf maganarta a kunnensa.

P 18

Sarai ya ji abin da ruma ta ce, amma ya share kawai ya tafi, dan idan ka biye mata babu abin da zai hana ta saka maka hawan jini.

Sai a lokacin ta samu zarafin dirarwa wainar da mama ta yi, ta fara ci ta na ajiyar zuciya, dan a kwanaki ukun nan Allah kaɗai ya san tsananin damuwar da ta shiga.

Yasir ya ce “Na so auren nan aka yi miki, mu ga ta tsiya, kowa ma ya huta da halinki”

“Ta Allah ba taka ba, bakinka ya sari ɗanyen kashi, na asuba mai tururi”

Mama ta ce “Meye haka, ki na cin abinci kina zancen ƙazanta”

“To mama ba sune suke tsokanata ba”

“Ina ruwanki da su, wato har kin samu kanki za ki ɗora daga in da ki ka tsaya ko?”.

Ta girgiza kai ta ce “A’a, ai na shiryu ba zan ƙara ba”

“Kima cigaba, wallahi kin san idan ya zuciya da halinki, zai aikata abun  da ya ce”

Sallamar Abubakar da suka ji ne, ya sanya ruma yin wani zillo, ta daka tsalle ta yi waje, maƙalƙale shi tayi tana murmushi tana faɗin “Oyoyo yaya”

“Amarya ba kya laifi, kar dai har an ɗaura auren ban samu ɗaurin auren ba?”

Ta ɓata fuska ta ce “Yaya har da kai ko?”

“A’a, nima fa kirana aka yi a waya, aka ce mini yau ɗaurin aure”

Waiwaya ta yi, ta kalli mai sunan Baba da ya shimfiɗa tabarma ya baje litattafai yana dubawa, ta kalli Abubakar, ta kai bakinta kunnensa ta ce “Wallahi hussaininka ya ɗau hakkina, ba dan yayana bane ba ko? Hmmm”

Ya kalli mai sunan Baba ya yi murmushi ya ce “Kai, a wani dalilin ya sa ka ɗaga mana hankali haka fisabilillahi?” Ko ɗagowa bai yi ba, balle ya kallesu. Ruma ta kama hannunsa suka shiga ɗakin mama.

Mama ta ce “Ta barka ka ƙaraso in ganka kenan? Na ga ta je ta tsareka da zance, kamar ba yanzu ta gama kuka da neman taimako ba”

Abubakar ya yi murmushi, ya zauna ya ce “Sannu da gida Hajiya mama, uwar ‘yan maza da ‘yar budurwa, na sameku lafiya?”

Mama ta yi murmushi ta ce “Lafiya lau Alhamdilillah, amma ba ka da lafiya ne?”

Ya ɗan kalli jikinsa sannan ya ce “Me ki ka gani?”

“To ai ganinka nayi wuri-wuri duk ka rame Saddiƙu”

Ya shafi sumar kansa da taru sosai ya ce “Mama wannan karatun namu, ai ba sauƙi ne da shi ba, pressure ce kawai, ruma zubo mini abinci” miƙewa ruma ta yi, ta fita ta kawo masa kulolin abincin ta dire masa, ta zauna ta saka shi a gaba, tana ta zuba masa surutu, mama kuwa kallon yadda yake zira abincin nan yake babu ji babu gani, kai da ganin yadda yake cin abincin ka san akwai yunwa a tare da shi, ba dai ta ce komai ba suka cigaba da hira.

Da la’asar shi da mai sunan Baba suka tafi masallaci, bayan sun dawo kuma suka zauna a tsakar gida suna hira.

Ruma so take ta zauna da Yaya Abubakar, ta yi masa hira sosai dan ya fi kowa tsayawa ya saurareta, amma ta ga hankalinsa yana kan ɗan uwansa.

Ganin ta zauna daga nesa tana ta kallonsu, ya sanya yaya Abubakar cewa “Ruma, ɗauko comb ki zo mu yi tsifa, na ga kitson kanki ya tsufa” ta jinjina masa kai, ta shiga ɗaki ta ɗauko comb da kibiya ta kawo masa, ta zauna a kusa da shi, tana yi tana kallon fuskar Umar, dan kar ya hantareta ko ya koreta.

Yaya Abubakar ya karɓi kayan tsifar, ya kwantar da kanta a kan cinyarsa, ya fara tsfefe mata kai.

Rai a haɗe mai sunan Baba ya ce “Amma dai ka san bana son ƙazanta ko?”

“Ƙazantar me kuma?”

“Dan me zaka zo kusa da ni kana aikin gashi, ko ƙyanƙyami ba ka ji”

Abubakar ya yi murmushi ya ce “Kayi karatunka ka ƙyalemu mu yi tsifar mu” a hankali ruma ta fara lumshe ido, bacci yana ɗibarta, cikin gyangyaɗinta ta ji Abubakar yana cewa mai sunan Baba “Ka ga ƙoshin nan da na yi cikina har wani ciwo yake yi”

Mai sunan Baba ya kalle shi ya ce “Kamar yaya, da ba ka ƙoshi ne?”

“Wallahi Akhi rabona da Abinci kusan kwana biyu yau, a ƙafa fa na taho tasha, na samu mota na taho gida shi ma daga tasha na ninko, Allah ya haɗani da wani ɗan unguwar nan ya goyoni a babur”

Cikin mamaki Umar ya ce “Garin yaya?”

“Wallahi kamfanin ‘yan chinan da muke yiwa aiki ne suka koremu, suka kawo mutanensu. Ni kuma na ga ban aiko da komai gidan nan ba, ta yaya zan bugo na faɗi matsala, na sayar da wayata na sai ƙarama ina ta fama, gashi mun kusa exam, shiyasa ban zo gida ba, shekaranjiya garrin kwaki na ci ko jiƙawa ban yi ba, na wahala a semester nan wallahi”

Umar yayi tsaki ya ce “Akhi kana da matsala, amma ko baka gaya wa mama ba, ni mai ya hana ka gaya mini, sai ka je ka kashe kan ka da yunwa, idan ba abinci ta yaya karatu zai yiwu?”

“Kai ba fa ban gaya maka ne dan ka yi mini masifa ba, ko nima ƙaninka ne?. Na tafi na barku kuma kuna ta fama da yadda zaku yi, ni ban muku ba, kuma na ɗoro muku matsala, gashi na yiwa yarinyar nan alƙawarin sabuwar jakar makaranta ban samu saya mata ba, har kunyarta nake ji wallahi”.

Mai sunan Baba ya numfasa ya ce “Dole mu din ga gaya wa juna matsalolinmu, watarana sai labari, ni kaina abubuwan sai a hankali, na saya wa yarinyar nan sabuwar katifa kusan dubu talatin,  ta ta ta lalace, da so nake na sauya mata makaranta, makarantar gwamnatin nan ba ta iya komai, an ce mini registration dubu Arba’in, duk term kuma dubu Ashirin da biyar, gashi muma an yi mana ƙarin kuɗin makaranta, ga komai ya yi tsada, rayuwar ƙasar nan sai dai Allah ya sassauta mana, ina jin su Huzaifa ma suna zancen zasu yi sauka, suma kusan dubu sittin ake nema su biyu, ga garin a tsaye yake cak, sai dai Allah ya iya mana kawai, ita kanta mama ba ƙaramin ƙoƙari take ba, yakamata ace zuwa yanzu ta fara hutawa, ta sha wahala domin mu rayu mu zama mutane”.

Abubakar ya ce “Haka ne, amma komai lokaci ne, daga cikin godiyar da nake yiwa Allah shi ne kasancewar dukkaninmu Allah sa babu wani wanda yake fita ya ɗauko mata magana a waje, ko ba komai hankalinta a kwance yake “

“Sai wannan abar” mai sunan Baba yayi maganar yana nuna ruma, da tayi pretending kamar bacci take.

“Ba wani ɗaukar magana, guda nawa take”

“Kai ba zaka gane ba, da ta je ta karya ‘yar mutane a makaranta, sai da aka kusa korarta, har wurin ‘yan sanda aka kaita”

Abubakar ya waro ido ya ce “Autar”

“Hmm kai ba ka nan, ba ka san wainar da ake toyawa ba kawai, wannan yarinyar ba ta da kai sam, kullum cikin nemo magana take ana ta abin da za a ci”

“To a daina faɗa, gara ayi ta mata addu’a “

Mai sunan Baba ya ce “Ai Addu’ar ce kamar ba ta kamata, duk gidan nan babu mai ibada kamar mama, kuma babu wanda zai yi mata addu’a ta karɓu sama da wadda take mata, amma haryanzu shiru, kullum rashin jin ta gaba yake yi, ni tausayi take bani wasu lokutan, tana da zaɓe-zaɓen abinci, and we can’t provide what she wants, kuma ba ta san babu ba, sai ta zauna tana kuka, wai an bata kunu ba suga, ko ba za ta ci tuwo ba, could you imagine?”

Abubakar yayi murmushi ya ce”Allah dai ya yassare mana, in sha Allah za su huta, ita da mama”

Ruma da ta yi bakamm ta na jin su, wani irin tausayinsu ne ya kama ta, wato duk wannan zare idon da hantarar da mai sunan Baba yake yi mata, yana son ta har yana tausayinta haka.

Tana wannan tunane-tunanen har baccin gaske ya yi awon gaba da ita, sai magariba ta tashi, Yaya Abubakar ya tsefe mata kai tas ya taje, dama ya saba yi mata tsifa idan har yana gari.

Duk in da suka gilma sai tayi ta kallonsu cike da jin tausayinsu, tabbas tun da ta buɗi ido a duniya, yayyen nan na ta maza kowa ƙoƙarinsa ya ga ya kawo abin da za a rufa kai asiri, haka mama kullum cikin faɗi tashi take.

Ta zubo abincin dare ta zauna tana kallon yadda kowa ke ta walwala kamar ba su da wata damuwa, ta zubawa su Mai sunan Baba ido, da suka zuba Abinci kwano ɗaya, tausayin Abubakar ya kamata, da tuna yadda yake gaya wa ɗan uwansa ya kwan biyu bai ci abinci ba, kuma ya sha garri ba ruwa balle suga, kuma ba wanda ya gayawa.

Ta kalli Abincin gabanta, Usman ya sayo kifi ya ɗora mata a kan abinci, kifin da shi bai ci ba, bai kuma bawa kowa ba sai ita, gefe ga ƙullin lemon fata da Aliyu ya shigo da shi, shi ma bai sha ba ita ya bawa.

A hankali ta ture abincin, ta shiga ɗaki ta zauna tayi shiru, sai kuka wani irin ƙauna da tausayin yayyen nata ya kamata.

Babu tsammani ta ga mama ta hasketa da fitila.

“Kukan me ki ke yi a duhu haka, ga abincin ki ba ki ci ba?”

Da sauri ta girgiza kai ta ce “Ba kuka nake ba”

“To me ki ke yi idan ba kuka ba, ƙarya nake kenan?”

“A’a mama ni fa ba kuka nake yi ba”

“To meya hana ki cin abinci ki ka dawo ɗaki ki na kuka?”

Ta girgiza kai ta ce “ba komai”

“Wai ba ance miki batun auren nan wasa bane ba, shi ne ki ka cigaba da takura kanki, ba zaki tashi ki je ki ci abincin ba?”

“Ba magana ake yi miki ba, ko sai na zo kan ki?” Ta jiyo muryar Yaya Umar daga tsakar gida. Jiki na rawa ta taso ta fito.

Cikin haɗe rai ya ce “zauna ki cinye abincin nan, sai wani ciwon ya kama ki ki cazawa mutane”

Ƙoƙarin kai abincin bakinta take, amma ta kasa kuka ya kuma ƙwace mata.

Aliyu ne ya dubeta ya ce “Ko Abincin ne ba kya so, ki ke yiwa mutane kuka? Me zaki ci?”

“A’a zan ci”

“To kukan me ki ke yi?”

“Ku ƙyaleni dan Allah, na ƙoshi ne” tayi maganar tana share hawaye.

Abubakar ya ce “Ikon Allah, taso dawo nan kusa da ni, zo ki saka hannu mu ci namu abincin tare” ba ta son ɓata masa rai, dan haka ta tashi ta je kusa da shi ta zauna, ya dinga ɗebo abincin yana bata a baki tana karɓa yana rarrashinta ba tare da sanin dalilin kukan nata ba, sai dai ba rarrashin da yake yi mata ne ya sanya ta yi shiru ba, hararar da mai sunan Baba ya jefeta da ita ne, ta sanyata haɗiye kukan da take yi.

Haka ya dinga lallaɓa ruma, da kansa ya gyara mata wurin da zata kwanta, ya saka mata net, har da yi mata addu’a, hakan ya ƙara sanya tsananin tausayinsa a ranta.

Sai da ya tabattar ta ɗan nutsu, sannan ya tashi ya fita, Mai sunan baba kuwa sai tsaki yake yi, yana hararar Abubakar, ya san da ya yi wani yinƙuri na yiwa ruma tsawa, zasu yi faɗa.

Mama har ta manta da batun ruma, ta na shirin kwanciya, ta sake jin sheshsheƙar ruman a cikin net ɗinta.

Mama ta kuma haskta da fitila ta ce “Ke dan ubanki fito daga cikin net ɗin nan, ki zo ki gaya mini abin da aka yi miki?”

Ruma tayi saurin goge fuskarta tayi kamar bacci take yi.

A hasale mama ta ce “Ba zaki fito ba sai na zo?” Ruma ta janyo jikinta ta fito, ta zo gaban mama ta zauna, amma ta kasa magana.

“Gaya mini menene kuma? Ko wani ne yayi miki wani abun?”

Ruma ta girgiza kai, “to kukan me ki ke yi wa mutane, ki gaya mini ko na leƙa na kira miki dodon naki”

“Kiyi haƙuri, zan gaya miki amma kar ki ce na gaya miki”

Mama ta ce “Ina jinki” nan ruma ta kwashe komai ta gaya wa mama, sannan ta ɗora da cewa “Mama Allah ya bamu kuɗi, ya horewa su Yaya ya sa kar su daina zuwa makaranta, kuma ni ba sai an canza mini makaranta ba, Allah ya bamu kuɗi su daina shan wahala, yayana ya kwana biyu bai ci abinci ba mama, wai an kore shi daga kamfani bai gaya miki ba” ta ƙarasa maganar tana kuka.

Jikin mama yayi sanyi ainun, duk wauta sa rashin tunani irin na ruma ashe ta na da hankali wasu lokutan, biri ya yi kama da mutum, Abubakar ya rame amam yaƙi gaya mata meke faruwa.

Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce “Ruma, kin ga wannan yana ɗaya daga dalilan da yasa nake miki faɗa a kan nutsuwa, ke gaki a gida amma sai abin da ki ke so shi zaki ci, kin ga yadda suke ta wahala da ƙoƙarin faranta mana, dan Allah ki daina rashin ji kin ji, ki yi ta yi muku addu’a, nima ina yi, yanzu ki je ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu kin san zaki tahfiz”. Ruma ta jima ta kwanta, sai dai bayan kwanciyarta mama ta kasa barci, sai tunanin yadda za ta ɓullowa al’amuran.

*****

Kirarin da ɗaya daga cikin hadiman Ammi ke ta rangaɗawa ne, wadda suke kira da Baba uwani, ya tabattar wa da su Iman da ke zazzaune a falo, takawa zai shigo, nan suka din ga kintsawa, ban da Iman da ta rashe a jikin Ammi, suna hira.

Sai dai Adam tare da Jabir suka shigo, hakan ya sanya Iman jan mayafi ta rufe kan ta.

Cikin girmamawa suka gaida Ammi, Jabir ya kalli Iman ya ce “Ke ba ki san girma ya zo ba ne?, Look at you, you are now a big girl duk kin bi kin danne mana Ammi”

“To idan ba ta danne ni ba wa zata danne? Ƙyaleta ‘yar auta ce ai”

Jabir ya yi wani murmushi sannan ya ce “Ammi, biyo takawa na yi, na kawo miki ƙararsa, ko ke zai ji maganar ki”

Adam ya harari Jabir, amma Jabir ya maze ya cigaba da magana.

“Ammi kin san halin ƙasarmu sarai, kin san yadda abubuwa ke gudana, duk da kasancewar sa shima wani ne, amma gaba da gabanta ta yaya zai sako Senator wakili da mutanensa a gaba, ai duk wanda ya kwana ya tashi, ya san mutane ne masu ɗaurin gindi, dan me zai tsananta?”

Ammi ta ɗan numfasa ta ce “Ban ƙi ta taka ba Jabir, amma abin nan na ga duk sabgar aikinku ce, ni ba komai nake ganewa ba, amma nima ina yawan yi masa magana a kan ya san in da zai din ga kai kansa”

“Yanzu haka Ammi, wai akwa ibom zai je, na rasa abin da zai kai shi wata akwa ibom”

Ammi ta kalli takawa, da ya kashingiɗa ya lumshe ido, kamar ba a kansa ake tattaunawa ba, ta yi murmushi ta ce “Rabu da shi Jabir, zan yi magana da shi”

“Ai gara dai Ammi” ya mayar da kallonsa kan Iman ya ce “Iman, ɗan sama mini abin sha mai sanyi mana, zan je garden in ɗan yi wani aiki”

Haushi ne ya kama Iman, ga masu aiki amma bai saka kowa aikin ba sai ita, ga Ammi a zaune balle ta ce ba zata yi ba.

Haka ta tashi ta tafi kitchen dan haɗa masa wani abun.

Adam kuwa ɗakinsa ya wuce, ya je ya nemi wuri ya kwanta, dan ya ji kansa ya fara yi masa ciwo, tun wayewar garin yau.

A garden ta tarar da Jabir, tun da ta ɓullo ya kafeta da idanunsa, da hakan sai da ya ƙona mata rai, ta yi tsaki.

Tana zuwa ta dire masa jug da kofi, za ta juya.

“Ɗan tsaya mana” ta tsaya cak, sannan ta waiwayo ta kalle shi.

“A tunaninki haka kawai na ce ki zo ki sameni a garden, magana zamu yi”.

Cikin yanayinta mai kama da shagwaɓa ta ce “Ni uncle J karatu fa zan yi, ina da exams”

Tashi yayi ya zagaya kusa da ita yana kallonta.

“Maganata ba ta da muhimmanci kenan?”

Ta ɗan ja da baya ta ce “To ina jin ka”

“Iman me na yi miki ne ki ka tsaneni, ki ke guduna kwanan nan?” Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba. Sai gani yayi kamar ta ɗan razana tana kallon wuri ɗaya.

Waiwaya ya yi domin ya ga mai take kallo, Mahmud ya gani a tsaye yana kallonta, gaba ɗaya ta ruɗe.

“Zo nan” Mahmud ya faɗa cikin isa yana kallonta.

Jabir ya ce “Kamar yaya ta zo, haka ake yi?”

“Ban saka da kai ba, kar ka ɓata mini rai”

Jiki na tsuma, Iman ta sunkuyar da kai ta nufi in da Mahmud ya ke.

“Amma Mahmud kamar ba ka ikon nuna wa iman wannan isar, tun da dai ba wani abu a tsakanin ku”

“Jabir, kafi kowa sanin waye ni, idan ba ka kiyayeni ba, za a ji kaina da kai, ba ruwana da abin da ku ka laɓe a lambu kuna yi, abin da ya dameni shi zan yi”

Waro ido Iman ta yi, jin abin da Mahmud ya faɗa, sai dai ko kusa ba ta ga fuskar da zata kare kanta ba, haka zalika ba ta da zaɓin da ya wuce ta bi umarnin Mahmud.

Ya tasata a gaba har sashin su na Mummy, da Mummy da Fuziyya da ruƙayya duk suna falon sai kuma Samha da dama tun tasowarta kusan kullum tana gidan su.

“On your knees” yayi maganar cikin tsawa. Cikin mamaki iman ta yi abin da ya ce, tana son jin laifin da ta yi.

“Ke saboda baki da mutunci, Mummy ta aika a kiraki amma ki ce ba zaki zo ba aiki ki ke yi wa Ammi, Mummy sa’arki ce?”

Cikin rashin fahimta iman ta ce “Ni kuma? Wallahi ba wanda ya zo ya kirani”

Mummy ta ce “Au iman ruƙayya ƙarya za ta yi miki kenan, ai da ka ƙyaleta, dama ta daɗe tana nuna mini ba ni na haifeta ba, dama ba wani abun ne ya sa na ce a kirata ba, dogwayen riguna ne na saya musu, nace ta zo ta karɓi nata”.

“Wallahi Mummy ban haɗu da Ruƙayya ba jiya, ruƙayya a ina muka haɗu?”

Ruƙayya ta ce “Ni zaki rainawa hankali, kina falo fa kina kallo a lokacin ki ka ce mini ba zaki zo ba”

Samha ta girgiza kai ta ce “Yaya Mahmud, ta ina zaka yi tsammanin tarbiyya a wurin ‘yar da ba jinin sarauta ba, ‘yar karere ‘yar riƙo”

Haka suka din ga jifan iman da miyagun maganganu.

Tun da ta taso, ta buɗi ido a gidan Galadima, take fuskantar ƙalubale sharri gami da makircin hajiya Jamila wato Mummy, makira ce ta gaske.

Suka ƙare mata cin mutunci, Fauziyya ta watso mata dogwayen rigunan a jiki, Mahmud ya ce ta yi godiya ta ɗauka ta bar sashen.

Ba yadda ta iya, ta aikata abin da ya ce ta tashi ta fita gwiwa a sanyaye.

Mummy tayi murmushi, a ranta ta ce bari mu gani, yarinyar nan zata gayawa wancan mahaukacin ne ya zo yayi hayagaga ko kuwa? Idan har ya zo yayi mana tashin hankali, zan tabattarwa da Samha akwai alaƙa a tsakanin iman da Adam, ko kuma in cigaba da amfani da wannan damar, wurin rura wutar ƙiyayya tsakanin Mahmud da shi, ina baƙantawa matar nan.

*****

Mama tayi ta faɗi tashi, ta tarawa Abubakar kayan abinci na komawa makaranta, wanda sam shi bai san ma tana yi ba, tun da ya dawo yake ta buga-buga yana tara ɗan abin da zai tafi da shi, ranar da zai koma mama ta tambaye shi babu wata matsala, ya ce mata eh ai yana da komai.

Mama ta yi murmushi, ta nuna masa watto bagco ta ce ya ɗauko, ya duba. Ya ɗauko ya duba, kayan abinci ne da ta tara masa.

Ya ce “Mama na gaya miki fa ina da komai, Meyasa zaki takura kan ki?”

“A’a ni ban takura kaina ba, Ubangiji Allah ya bada sa’a ya taimaka” yayi ta yiwa mama godiya, mai sunan Baba ya raka shi tasha, ya bashi dubu biyar, amma sai da suka kai ruwa rana Sannan ya karɓa.

Ruma ce ta fito daga wanka, ta tsaya a gaban mudubi daga ita sai pant, tana kallon kanta.

Mama ta kalleta ta ce “Meye haka ne ki ke tsaye tsirara ki nemi kaya ki saka”

Ruma ta juyo ta kalli mama cikin damuwa ta ce “Mama kalleni”

“Na ganki meyafaru?”

“To ba abin da ki ka gani?”

“Ni banga komai ba”

“Mama wai baki ga ƙirjina kamar ya kumbura ba?”

Mama tayi murmushi ta ce “Na gani”

“Mama to ya kike dariya, ba alamomin ciwon Cancer bane?”

Mama ta ce “A’uzubil’ahi, ba wannan bane ƙirga dangi ki ka fara”

Cikin rashin fahimta ruma ta ce “Wane dangin na ƙirga, ni ina zan iya ƙirga danginmu?”

“Ba wannan ake nufi ba, girma ki ka fara zaki zama budurwa, fitowa za su yi”

Ruma ta haɗe rai ta ce “Ni bana son su fito”

Mama tayi dariya ta ce ‘Saboda me?”

“Da nace ina son su fito a daina ce mini ƙwaila, Yaya Aliyu ya ce gara na yi zamana a haka, ai suma basu da shi”

“To ke namiji ce, da zaki zauna a haka nan gaba da kanki zaki zo kina nema daga baya, ke da a da ki ka ce zaki sayo na sayarwa ki saka”

“To ai yanzu na fasa, gara kar ya fito, idan ya fito fa ba zan din ga yawo ba riga ba”

Mama ta ƙarewa ruma kallo, alamomin girma duk sun fara bayyana a jikinta, mama ta numfasa ta ce “Yanzun ma ai na hanaki yawo babu riga”

Ruma ta ɗau vest ɗin ta ta saka, ta ce “Mama kalli fa, kalli yadda vest ɗin fa tayi mini, to wai tsayi zai cigaba da yi? Ko kuwa?”

“Nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito, sai ki ga yadda za su yi, ki dai kula da kanki, ban da wasan banza da maza ko mace, duk wanda yayi miki wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki, idan kin zo ki gaya mini, wannan wurin ba wurin wasa bane, gaba ɗaya jikinki ma al’aura ne abin alkintawa ne”.

“Ni mutum ya taɓani ma, ba sai na sumar da shi ba”

“Ni dai bana son rashin hankali, ki kula da kanki, zuwa gaba in ga mai yakamata ayi, idan rigar mama yakamata a saya, sai a sayo ki farawa sakawa”.

Ruma ta ce “Taɓ, haka kurum a din ga yi mini kallon ‘yar iska”

Mama zata yi magana, usman  yayi sallama ya shigo, ba ta amsa sallamar ba ta ce “Yaya usy, kalleni me ka gani?”

Ya ce “A ina?”

“Au dan ubanki gaya masa zaki kin fara nono, ni yau na ga ta kaina, Innalillahi wa Innalillahi raji’un”

Jin abin da mama ta ce ya sanya Usman ja da baya ya bar ɗakin.

P 19

“Wai ke duk yadda mutum ya so ya kwaɓeki ya nuna miki rayuwa ruma ba kya ganewa, sai ka ce rainon daji, yanzu usman ɗin zaki gayawa kin fara ƙirgar dangi, abin da ake ɓoyewa a tattala?, kai wannan yarinya kune yaran ƙarshen zamani”

“To mama ai gani na yi yayana ne, kuma bana ɓoye musu komai”

“Eh ba kya ɓoye musu komai, kuma aka ce miki ciki har da tsairaicin ki ko? Ɗauki kaya ki saka ni ki fice ki bani wuri, kan na taso kanki.”

Ruma ta durƙusa ta ɗau kayanta ta saka, dama mama ce za ta aiketa.

Mama ta kalleta ta ce “Ruma wai ke komai naki butsu-butsu babu kintsi, haka ake ɗaura zanin ma, dama a dama ake ɗaura zani, kalli ƙwaurinki duk a waje kamar zaki tsallaka wuta”

Kamar ruma za ta yi kuka ta ce “Mama ni ya zan yi, ni wallahi bana son zanin nan, idan ina tafiya a hanya ji nake yi, kamar na kwance shi na riƙe a hannu, harɗe mini ƙafa yake, ni nafi son wando ko doguwar riga”

“Aikuwa kin daina saka su, dole ki koyi ɗaurin zani ki na ‘ya mace, matsonan na ɗaura miki”

Ruma ta ƙarasa fuskar ta a haɗe, dan har ga Allah ba ta ƙaunar zani sam.

Mama ta ɗaura mata sannan ta kalleta ta ce “Ga farar hoda can a kan mudubi, ki ɗan shafa sannan ki saka kwalli”

“Mama farar hoda kuma kamar wata ‘yar tashe, ni ki bar mini fuskata a haka kawai, bana son shafa mata komai, kwallin nan ma idan na saka zazzagowa yake fuskata ta koma kamar ta boka”

Mama ta miƙe ta danƙi hannun ruma, ta ja ta zuwa gaban mudubi ta ce “Wallahi sai kin saka kwalli, ba zaki fita da ido kamar jan nama ba” ruma har da kuka mama ta gwale idonta ta saka mata kwalli, ita ruma a rayuwarta duk wani abu ma shafe-shafen kwalliya na mata, bai dameta ba ba tayi, dan basa burgeta. Ta sha zagi wurin mama kan ta tafi aiken nan.

***

Takawa kuwa lokacin da ya shiga ɗaki, kan sa ciwo yake yi masa sosai, dan bacci ma yake ji a lokacin.

Kwanciyarsa babu daɗewa bacci mai nauyi ya fara ɗaukarsa, sai dai baccin bai je ko ina ba ya fara jin wannan muryar a kunnensa tamkar ana yi masa raɗa “Sarki mai koriyar alkyabba” a hankali ya buɗe idonsa, ya hau dube-dube a ɗakin, amma babu kowa.

Kawai sai ya ji ba ya son kwanciyar, dan haka ya tashi da sauri ya fito daga ɗakin.

Iman kuwa sai da ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta shiga sashen Ammi.

Ammi tana nan a in da suka bar ta a falo ba ta tashi ba, Iman ta ƙaraso cikin yaƙe ta ce “Ammi, kin ga Mummy ce ta kirani ta bani”

Cikin mamaki Ammi ta ce “Ke da ki ka fita kaiwa Jabir lemo, me kuma ya kai ki sashin su? Kin san bana son zuwanki in da suke”

Iman cikin dakiya da ƙoƙarin danne hawayenta ta ce “Yaya Mahmud ne ya kirani, ya ce Mummy na nemana shi ne ta bani, bari na je na gwada” ta na gama maganar ta yi gaba, dan kar Ammi ta fahimci wani abu.

Takawa na tsaye a falon, har Iman ta yi gaba, ta ji ya janyota ya dawo da ita, ya ɗan ƙura mata ido.

“Me suka yi miki?”

“Wai ni? Babu komai fa, kaya kawai ta bani”

“Me suka yi miki?” Ya kuma maimaitawa.

Tunanin ƙaryar da zata yi masa ta hau yi, amma kan ta kai ga furta komai ya daka mata tsawa, hakan ya sanya jikinta fara rawa. Cikin razani ta gaya masa abin da ya faru.

“Wuce ki tafi” ya faɗa yana nufar ƙofar fita daga falon.

Ammi ce ta tare shi ta ce “Ban lamunta ba, kar ka kuskura ka je in da suke, da gayya suka yi, ka ƙyale su kawai”

“Ammi, ba saboda Iman kawai nake wannan abun ba, na san a duk lokacin da aka taɓata, kai tsaye ka aka yiwa, Ammi ko tausayin yarinyar nan ba sa ji?”

Ita kanta Nusaiba da ke zaune tana cin abinci, al’amuran gidan sun fara isarta, tana tausayin Iman sosai da sosai.

Ammi ta ce “Na fahimce ka takawa, amma tun da ka ga ina kawar da kai, to kai ma ka dinga haɗawa da haƙuri, ka koyi kawaici ba a komai zaka yi magana ba, kar ka kula su”.

Baba Uwani da ke ‘yan kaye-kaye a falon ta ce “Ayi haƙuri uban gidana, ban san ka da yawan hasala ba, Allah ya huci zuciyar magajin Galadima, ayi haƙuri”

Da ƙyar Adam ya haƙura, ya nemi wuri ya zauna, ya na jin yadda zuciyarsa ke tafasa,  shi dama ba ta Mummy yake ba, Mahmud kawai yake son ya yiwa kashedi a kan rayuwarsu.

Nusaiba tsam ta miƙe, ta nufi ɗakin Iman, ta tarar da Iman ɗin zaune ta zuba uban tagumi, tana kallon kayan da aka yi amfani da damar bata, aka ci zarafinta, kayan da basu wuce ta yi kyauta da ninkin su ba.

Nusaiba ta dafata ta ce “Masoyiya”

Iman ta kalli Nusaiba ta ce “Na’am Anty Nusyna”

Kallon idon Iman Nusaiba ta yi, idonta ya nuna ta yi kuka sosai.

“Be brave iman, kiyi haƙuri, ban san yadda zan fasalta miki abin da nake ji ba, idan aka cutar da ke ba, muna sonki sosai Iman, kin san yanayin halin da ki ke ciki, dan Allah ki daina damuwa ko ɓata ranki”

Iman ta yi murmushi ta ce “Kar ki wani damu, yayata ai na ma riga na saba”

Nusaiba ta zauna sosai ta ɗora da cewa “And yakamata ki daina nuna ki na jin tsoron su, musamman yaya Mahmud kamar mara tunani, abin da aka gaya masa kawai da shi yake amfani, ai gara ma yayi ya koma in da yake karatu mu huta masifaffen banza”

Iman ta toshe baki ta ce “Sai na gaya masa abin da ki ka ce, babu ruwana” tayi maganar tana dariya.

Ajiyar zuciya Nusaiba tayi tana murmushi, ganin yadda murmushi ya bayyana a kyakkyawar fuskar Iman.

***

“Ohh ni rumaisa sai girma nake, mama, ta bakin naki kwanci tashi asarar mai rai, na shiga jss2 fa”

“Aikuwa dai, kina ta girma amma babu nutsuwa ba”

“Kai mama, Allah ya nuna mini lokacin da zaki yabeni, ke kullum bana abin arziki a wurinki mamancy”

Mama ta girgiza kai ta ce “Ai ke gaba ɗaya abin tsiyarki ya ninka na arzikin yawa”

“Mama”

“Ina jinki”

“To ɗan kalleni mana”

Mama ba ta kalli ruma ba ta ce “Sai kuma kiyi ai”

“Dan Allah ki sai mini shayi da indomie, kin san bana son tuwon nan “

“Rumaisa ai ni ce ma Indomien, zo ki gutsiri in da ki ke so ki ci, tuwo kuma ban yi miki dole ba, ki barni da kayana”

“Allah ya jiƙan matar da ta ƙirƙiro tuwo idan musulma ce, amma ta cuceni zuciyata tafi raya mini a zamanin tsunburbura ta zo”

Ruma ta ƙaraci soki burutsunta, da gwasalewa mama tuwo, mama taƙi kulata.

Hankalin ruma ne ya tsaya a kan rediyon da mama take ji, wata mata tura wasiƙa, tana son a bata maganin da zata sha, tun da tayi yaye ƙirjinta ya zube kullum mijinta cikin yi mata gori yake.

“Kan uba, amma wallahi maza basu da kai, dan Allah meye haɗinsa da kallonta?” Mama ta ja rediyon ta kashe.

“Mama ya zaki kashe, ki bari mu ji mana, nifa bana son harkar watsewa, wallahi ka gaya mini maganar banza sai na tafi gidanmu, wannan ai rashin tarbiyya ne, ya ya zai din ga yi mata kallon ƙurilla, kuma mama ba kin ce mini ɓoyewa ake yi ba? Ita ma har da ita”

Mama dai ta basar, tayi mata shiru, can ta kuma cewa “Hmm kin san Allah mama, nima na gani fa, ‘yan ajinmu na islamiyya suka ce, wai idan mace tana tafiya ba ta saka hannu a hijjabinta, maza kallonta suke yi, haka ma idan ta juya bayanta, jiya da na je gidan Asabe ban samo gawayi ba na je titi, daga nan na tsaya sayen mai, kin san riga da skirt na saka, sai mayafin abayat, wani mutum ya tsurawa gurin zamana ido, ai ban sani ba, ina waiwayawa muka haɗa ido, na ce malam kalli gabanka mana, baki ganshi ba babba da shi na saka hannu na kare abina har na zo gida”.

Abdallah ya ce “Sannu jikar faisal, duk ‘yan matan da suke kaiwa suna komowa a wurin, ba wadda ya kalla sai ke ƙwaila, wani ɗan abu kamar falanki, saboda asara ke zai tsaya kallo”

“Wallahi ni ba ƙwaila bace ba, kuma ka je ka tambayi kowa na wurin ka ji, kallona yake yi, ni kuwa na saka hannu na rufe”

Mama ta ce “Ya isa haka, kuma saboda tsabar rashin sanin ciwon kai ki tafi har titi da ɗan ƙaramin mayafin da bai fi ayi kallabi da shi ba, duk ranar da Allah ya nuna mini, sai na zane ki. Kuma zan saka bababana ya je islamiyyar lallai a raba muku aji da wannan yaron, dan sun fi ƙarfin tunanin ki”

Da sauri ruma ta ce “Ki yiwa Allah da ma’aikinsa, kar ki aika mai sunan Baba, kin san yanzu ƙiris yake jira yayi mini aure”.

“Aikuwa ina daf da gaya masan, idan har baki nutsu ba, kin daina wannan rashin kan gadon ba, gara ya aurar da ke na huta”

Ruma ta saka hannu ta kama laɓɓanta ta ce “Na daina da yardar Allah”

***

“Takawa, wai yaushe zaka je ka ɗauko yarinyar nan ne?”

Ya ɗan lumshe idonsa ya buɗe sannan ya ce “Zan ɗaukota ne, gara ta ɗan huta ta nutsu tukuna, visarta har yanzu da saura”

Ammi ta ce “To shikenan, yauwwa ya maganar tafiyar da na ji Jabir ya ce zaka yi? Meye gaskiyar maganar?”

“Ammi ki manta da shi kawai, ɗan rainin hankali ne a wurin aiki ne za a tura mu wani bincike”.

Ammi ta numfasa sannan ta ce “To, Allah ya yi jagora, amma dai duk da haka kamar yadda ya ce ka din ga kula takawa, ka san currently a ƙadamin da kake, kar ka janyo mana wata wahalar wadda muke ciki ba ta ƙare ba, dan Allah ka dinga komai a sannu, sannan ka riƙe addu’a kamar yadda nake jaddada maka”

“In sha Allah Ammi, kar ki damu ina iya ƙoƙarina wurin yin Addu’a”.

“Haka ake so, Allah ya yi maka jagora”

“Amin Ammi”.

Daga haka ya ɗauko wayarsa yana duddubawa, yana tsaka da duba wayar, Ammi ta kuma cewa “Ko yaushe Mahmud zai koma makaranta, na ga kamar lokacin komawarsa yayi, kuma ance mini haryanzu ana ganin gilmawarsa a gidan nan”

Takawa ya sauke wayar, ya dubi Ammi ya ce “Ammi, ba babarsa tana kallo bai koma ɗin ba ta zira masa ido, dan Allah ki daina damuwa da abin da ya shafe su, ki din ga ɗagawa kan ki hankali”.

Ammi ta girgiza kai ta ce “Da kai da su ni duk abu ɗaya ne a wurina, ba zan so rayuwar wani daga cikinku ta samu tangarɗa ba”.

“To Ammi tun da ba sa yi da ke, ai mu mun isheki rayuwa, dan Allah ki manta da su”

Ajiyar zuciya Ammi ta yi, ba ta sake cewa komai ba.

***

Yau kamar korarriya haka ruma ta shigo gida, sai cika take tana batsewa, ba ta kula kowa ba ta cire uniform ta yi wanka, ta zubo abincin ta ta fara ci.

Kamar wadda aka tsikara ta ce “Yaya Aliyu, wai ina ce makarantar ‘ya’yan gwamna ne?”

Yayi murmushi ya ce “Mai yafaru?”

“A’a tambaya kawai nake yi”

“A manyan makarantu suke, wasu a turai ma”

“Suna zama a ƙasa, ajinsu babu abin zama?”

Yayi dariya ya ce “Amma kin ci kai, ‘ya’yan gwamna ne zasu zauna a ƙasa? Zama a ƙasa a makaranta wannan ai sai ɗan talaka”

“To meye banbancin mu da su? Dukkanin mu ba mutane bane, kuma muma ba ‘ya’ya bane?”

“Kuna da bambanci mai tazarar gaske, dukkaninku mutane ne, kuma ‘ya’ya ne, amma iyayensu ke riƙe da madafun iko, abin da zaku yi ku taimaki kanku a matsayin yaran talakawa shi ne, kuyi karatu komai wahala, idan ba haka ba kuwa ku ƙare a bayinsu da ‘ya’yansu”

Tamkar ruma zata fashe da kuka ta ce “To wallahi zan yi Allah ya isa, aka ce duk ‘yan ƙasa ɗaya muke, bencinmu ya karye, dama wasu a ƙasa suke zama, kullum sai kayana sun yi datti, uniform ɗina duk sun fara koɗewa. Ga malaman namu ma sai a hankali, wallahi malamin English ɗin mu bai iya turanci ba kame-kame yake yi, malamin math ɗin mu kuma Arabic yayi ba uwar da muke ganewa, ga ajinmu azababben zafi window ɗaya ce, bana gane komai a makarantar kamar na daina karatun. Kuma jiya nake ji a radion mama uban kuɗin da ake saiwa  wasu manyan motoci sai ka ce motar aljanna, ko meye sunansu oho na manta, to wallahi duk wanda aka raba da haƙƙina ya cinye ban yafe ba, zama a ƙasan da nake a matsayina na ‘yar ƙasa”

Mama ta ce “Ruma wa ki ke yi wa Allah ya isa, ban hanaki wannan ɗabi’ar ba ruma?”

“Mama ba zaki gane halin da muke ciki ba, ga rashin abin zama, ga zafi ga rashin malamai ga duka kamar an samu jakai, har noma ake sakamu fatanya a makaranta, gaba ɗaya makarantar mu ‘ya’yan talakawa ne, shikenan mu ba mutane bane”.

Ruma kenan, gaba ɗaya tunaninta da maganganunta sun shallake shekarunta, wataƙila hakan yana da alaƙa da yawan jin radion da mama take yi, da yawan tattauna matsalolin da ƙasa ke ciki da yayyenta suke yi.

Babu wanda ya kuma tanka mata, tayi bambaminta ta gama, dan ta wani fannin tabbas Ruma tana da gaskiya, amma babu yadda za ayi a gaya mata tana da tazarar da waɗanda take hange take kamanta kanta da su ta gane.

Haka ta ƙare cin abincin tana mita, kuma bil haƙƙi har cikin ranta, take faɗar yadda abin yake yi mata ciwo.

Kasancewar yau Alhamis babu makarantar islamiyya, Huzaifa da Yasir duk suna gida.

Huzaifa ya nutsu yana ta kallon tiktok a wayarsa, ruma ta lallaɓa ta zira kanta tana kallo.

Huzaifa ya ɗauke wayarsa ya kalli ruma ya ce “sai ka ce mayya, mara zuciya kawai”

“Eh na ji, ni kunna dai mu gani”

“Ba zan kunna ba, ke ki ke saya mini data?”

“A’a, amma ɗan kunna gani kawai zan” ya haɗe rai ya ce “Ba zan kunna ba, bar nan wurin ko na dakeki”

Ta tashi tana zumɓura baki ta ce “Mutum dai idan tsiya tana bin sa, ko ka raɓeshi haushin ka yake ji?”

“Ni ne tsiya take bi ko? Wallahi ki ka bari na zo kanki, saina kwaɗa miki mari”

Cikin tsiwa da rashin kunya ta ce “To kar ka barni da rai ma mana, idan da rai nima zan yi wayar nan” Jin yadda take ɗaga murya ya san idan ya biye mata, faɗa za su yi, ran mama ya zo yana ɓaci, kawai ya shareta ya cigaba da danna wayarsa.

A hankali ta lallaɓa ta koma wurin Yasir, shi kuma Yasir Instagram yake kallo, dan haka sai ka ce dole ta ɗan maƙale tana leƙawa dan kar shi ma ya koreta.

Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce “Dawo ta nan ki kalla, madam no heart”

“Ai in dai zaka barni na kalla, to babu damuwa kafi wancan tsiyar muka rako duniya”. Yasir ya yi murmushi bai ce komai ba.

Sai dai tamkar zata shige cikin wayar, ko ta ƙwace masa wayar.

Duk hoton ko videon da ta gani sai ta tsaya ta yi liking. Ƙarshe sai sakar mata wayar ya yi, ya tashi ya bata wuri.

Sai da mama ta tashi ruma ta aiketa, sannan ta tashi daga kallon wayar.

Ɗaukar niƙa mama ta aiketa a can titi, ta ɗauki kayan saƙarta ta tafi da su, tana tafe a hanya tana saƙa, ta ɗauko niƙa ta taho gida, sai dai niƙan da nauyi.

Ba tsammani ta ji an ce “Sannu ko” ta ɗaga kai ta kalli mai maganar, ba ta amsa masa ba ta cigaba da tafiya. Biyota ya yi ya ce “Daga ina haka?”

Ruma ta tsaya ta kalleshi ta ce “Ba dan ka kusa sa’an yaya Usy ba, da sai na ce maka kai ka aike ni da zaka tsareni da tambaya?”

Ya girgiza kai ya ce “No, yi haƙuri kawo na tayaki ɗaukar kayan”

Ruma ta ce “Yauwwa, kamar ka san na gaji kuwa” ta ajiye masa niƙan ya ɗaukar mata.

Suna tafe yana yi mata tambayoyi, ita kuma hankalinta yana kan saƙarta.

Babu zato babu tsammani sai ganin Yaya Aliyu ta yi a gabansu, gabanta ya faɗi ta ce “Yaya”

Rai a haɗe ya ce “Waye wannan?”

Ta kalli mutumin ta ce “Oho kawai ganinsa na yi”

Mutumin ya yi murmushi ya ce “Ashe yayanmu ne, barka da yamma”

Aliyu bai amsa ba ya ce “Malam meye haɗinka da ita?”

“A’a babu komai, kawai dai na tayata ɗaukar niƙan ne, sannan dan Allah idan babu damuwa, ni dai ina son ta ne, dama na biyo ta ne domin na ga…..

“Haba bawan Allah, ina kai ina wannan yarinyar ‘yar cikinka, meye wani abin soyayya a wurinta ban da salon ɓata tarbiyyar yarinya”

Ruka kuwa ta buɗe baki ta ce “wai sona ka ke ka zama saurayina, taɓ to ai ni ba zan yi aure ba”

Yayi murmushi ya ce “Eh mana, yayanmu ni zan jirata ko nan da shekara nawa ne idan muna raye zan jirata”

Aliyu ya sake tsuke fuska ya kalli ruma ya ce “Wuce ki tafi gida”

Ruma tayi gaba tana ɓata rai, ya ce “Zo ki karɓi kayan naki”

Ruma ta ce “Ka ajiye wa Yaya Aliyu ya taho da su”

Aliyu ya ce “Ni ne zan taho miki da aiken”

Kwasa ta yi da gudu, ko waiwayowa ba ta yi ba, dan kar ma ya ce sai ta ɗauko niƙan dan ta gaji.

Kamar korarriya mama ta ga ruma a cikin gidan, tana ta sauke numfashi.

“Lafiya ina aiken? Ko faɗan ki ka je ki ka yi?”

Ta girgiza kai.

“To menene, ina aiken?” Ruma ta sake tura baki.

“Ke magana nake miki kin shareni”

Kan tayi magana Aliyu ya shigo, da niƙan Mama.

Ya dire niƙan yayo kan Ruma, ta zura da gudu ta shige bayan mama.

“Wai meyene, lafiya?”

Aliyu ya ce “Ita ta san me tayi ai, wani bagidajen gaye ne, da wani tattararren ƙafar wandonsa, wai wannan bagidajiyar yarinyar ya biyo wai yana son ta, sai da na kusa ɗuɗɗura masa ashar, banda son lalata tarbiyyar yarinya, uwar me yake nema a wurin wannan yarinyar mai rabi hankali rabi hauka?”

Mama ta ce “Aliyu, ba ina sukar matakin da ka ɗauka bane ba, amma wanda ya ce yana son naka ai ba maƙiyinka bane, duk abin ku fa ko kuna so, ko ba kwa so dole watarana sai kun aurawa wani ta bar gidan nan, ku daina wulaƙanta mutane Sabo sun ce suna son ‘yar uwarku”.

“Ni bana son shi, ƙafarsa busu-busu ko mai bai shafa ba, kuma sai warin rana yake”

Hannu mama ta saka, ta mako ruma daga bayanta, ta din ga yi mata faɗa.

Duk da ita ruma ko faɗan ka yi mata ba ganewa take yi ba.

***

Iman ce ta shiga sashen Ammi da sauri, sai dai Ammi ta ɗan razana ta ce “Lafiya kuwa?”

Iman ta ce “Ammi, ina ga yaya Mahmud ne zai koma makaranta, na gansu a haraba kamar airport Mummy za ta kai shi”.

Da sauri Ammi ta tashi, ta zaga ta ventilation ɗin ta, ta leƙa ta window, ta hangi Mahmud ya buɗe bayan mota ya shiga, Mummy ma ta shiga an kunna motar sun yi gaba.

Jiki a sanyaye Ammi ta saki labulen, ta shiga ambaton sunan Allah, Iman ta rungumota ta na faɗin “Ammi kina lafiya? Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki fa, kar ciwonki ya tashi” sai dai kan Ammin ta yi wata magana numfashinta ya fara sama-sama.

P20

*Page ɗin sukutum guda naki ne masoyiyya Zainab kumurya, idan kin ga dama ki yayyaga shi ki zubar ko ki kashe Ruma, tun da naki ne😂. Ke kuma marubuciyar mijin malama Nimcy ki ji tsoron Allah, wallahi ana ta ƙorafi kin sako jaruma da masifu amma kin yi burus da mutane, zan karɓe rubutun mijin malamar nan fa😂 wanda bai karanta ba ya garzaya mijin malama an gama book1 labari mai tsayawa a zuciya*

A gigice Iman ta riƙo Ammi tana jera mata sannu, jinjina mata kai kawai Ammin ke iya yi, amma ta kasa magana.

Iman ta rungumota ta zaunar da ita a kan gado, cikin damuwa ta ce “Ammina, dan Allah ki yi haƙuri, ban nuna miki dan na tayar miki da hankali ba”

“Kar ki damu Iman, ba ki tayar mini da hankali ba, kawai dai tari ne ya taso mini, kawo mini ruwa a fridge mai sanyi na sha.

Cikin rawar jiki Iman ta tafi ta kawowa Ammi ruwa, ta karɓa ta sha, sannan ta ɗan kwanta ta lumshe idonta. A take ƙwaƙwalwaarta ta shiga tariyo mata abin da suka wakana a shekarun baya, daga kafuwar gidan zuwa yanzu, abubuwa da dama sun faru masu matuƙar wahalar mantawa da kuma ruɗani, wanda haryanzu a haka ake, komai sake dagulewa yake yi. A hankali ta gyara kwanciyarta tana son ta kawar da tunanin daga zuciyarta, amma sai kaiwa da komowa abubuwa suke a ƙwaƙwalwarta suka hanata sukuni.

***

Ruma kuwa a ‘yan kwanakin nan ta addabawa Yasir, kusan kullum tana liƙe da shi tana kallon waya, idan anjima ta ɗau wayar Usman ta fara game, ya zo yayi ta zaginta ya ƙwace, sai ta koma gefe ta ɗau wayar mama, ta yi ta yi wa ƙawayenta fulashin, wasu su biyo wasu kuma suma su yi ta mata fulashin, babban abin da yake ƙonawa mama rai fulashin, wataran wayar haske kawai take yi, ko sai ta fara ringing ta zo ɗagawa ta katse, mama ta yi ta masifa ta ce “Idan baki kiyayeni ba, da ke da ƙawayen naki sai na saɓa muku, gayyar rashin hankali”.

Yasir yana ɗan taɓa gyaran wayoyi, ya iya harkar jagwal, shine gyaran waya, system da sauran kayan electronics.

Wata waya ya samu, ta sha jiki, ya sayo layin data, ya saka a wayar, ya bawa ruma ya ce “Gashi nan, ki dinga kalle-kallen ki a wannan ki ƙyale mini wayata, kuma ki daina ɗaukar wayar mama kina fulashin, ki yi da wannan, saura ki lalata kuma akwai lokacin da zan dinga karɓa, dan ba bar miki na yi ba. Na buɗe miki account amma ban saka sunanki ba, ƙanwar maza na saka na ɗora miki hoton flower a dp kar a gano mu”.

Ruma tamkar ta goya Yasir dan murna da farin ciki, ta gurfana ta dinga yi masa godiya, tare da sanya masa albarka.

“Amma ki ja bakinki ki yi shiru, kar ki gayawa kowa”

“In Allah ya yarda ba zan gaya wa kowa ba, bakina ƙanin ƙafata, amma me yasa ba zaka saka mini sunana ba da hotuna na nima?”

“Dan ubanki gidanku kuna da background ɗin da zaki dinga hoto ne? Kuma ni ban baki dan ki saka hotunanki ba, dan wallahi kin san idan suka gano kashinmu ya bushe, idan kin san ba zaki bi abin da nace ba, to tun wuri na karɓe kowa ma ya huta”

“A’a Allah ya baka haƙuri, da wasa nake maka nima, idan bana komai sai ka dinga bani ina ganin duniya nima, a daina hantarata dan na leƙa waya”.

Tun da Yasir ya bata wayar nan, aka samu sauƙin neman magana a cikin gida, kusan koda yaushe tana kan wannan jagwal ɗin wayar, kuma Yasir abubuwan karatu yayi mata following, dan haka su tafi gani, kuma sosai suke ɗauke mata hankali, ya fi bata da daddare idan ya tabattar ta gama ayyukanta, da assignment, sai ya bata ta zauna a kusa da shi ta kalla, da lokacin kwanciya ya yi ya ƙwace wayar ya korata ta kwanta.

***

Zuwa la’asar Ammi ta ɗan samu nutsuwa, sai dai kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa.

Takawa ya fuskanci damuwa ƙarara a fuskar ta, sai dai ganin yadda take basarwa ba ta son magana, ya sanya shi yin shiru bai yi ƙoƙarin tilasta mata jin abin da yake damunta ba.

Wurin Jabir ya tafi, domin samun sauƙin wasu damuwoyin da suke damunsa, kasancewar sa ɗan uwa ɗaya tilo da ya fi yarda da shi.

Jabir na ganinsa ya ce “Sarkin matsala, tun kafin ka yi magana, fuskarka ta nuna akwai damuwa, yau kuma menene?”

Takawa ya ɗan yi shiru, sannan ya ce “Khalifa Usman wakili”

Jabir ya tsuke fuska ya ce “Ba zaka rabu da sabgar wannan yaron da ahalinsa ba ko?”

A hankali Adam ya ɗan lumshe idonsa, ba ya son yin dogon jawabi da ga Jabir, tun da shi jabir haryanzu ya kasa gane abin da yake nufi game da khalifa, dan haka kawai yayi shiru ya cigaba da tunani.

“Ina Ammi?”

Adam ya buɗe idonsa ya kalli jabir, amma bai yi magana ba, so yake yayi masa zancen muryar nan da yake ji, wadda haryanzu ya kasa daina jinta a kunnuwansa, amma ya san da ya ɗago zancen Jabir zai yi masa wata fassarar. Bai gama fahimtar mai Jabir ya cigaba da cewa ba, sai jin sunan Iman da yayi Jabir ya furta.

Ya ce “Me ka ce ne?”

“Ni fa matsalata da kai wulaƙanci, duk surutun da nake ba ka ma gane me nace ba?”

“Sorry” ya faɗa a taƙaice yana tsare Jabir da ido alamar yana son ya maimaita masa me ya ce.

Jabir ya ce “Well, cewa na yi, wai me ƙaninka yake nufi da Iman ne, yana takura mata da yawa fa”

“And so…?”

“Kana nufin ba ka damu ba kenan?”

“Kaga ni ka ƙyaleni da sabgar gidan nan, bana iya tunanin komai a kai, ko na fara ma kaina ciwo yake yi, gaba ɗaya bana son yin tunani a kan matsalolin gidan nan “.

Jabir ya yi ajiyar zuciya ya ce “Haka ne, ni auren Iman nake son ku bani, ka wuce mini gaba zuwa wurin Ammi mana”.

Wani irin kallo Adam ya yiwa Jabir ya ce “Ba ka da hankali ne?”

“Ban gane ba ni da hankali ba?”

“Amma ka san ba abu ne da zai yiwu ba ko?”

Jabir ya ce “Saboda me, wai ni ko dai kai ne ka ke son ta ne?”

Tsaki Adam ya yi ya tashi ya ce “Ka san idan har zan auri Iman, zan iya auren su Nusaiba ko Fauziyya, kai ma ka san ba zan bari ka auri Iman ba, kuma ka san dalili”.

“Amma a tunanina wannan bai kai hujjar da za a hanani aure ba”

A ɗan hasalae takawa ya ce “A ganinka ba”

“Amma…..” Bai jira jabir ya gama maganar ba, ya fice ya bar Jabir.

****

Ruma ce a tsakar gida, ta zage tana ta dakan ƙuli-ƙuli, zata yiwa Yasir kafi kaza, dan ya ƙara samun ƙwarin gwiwar bata waya tana jagwalgwalo, dan wayar ta fara shiga ranta sosai, ga cacar kuɗin data yana yi mata, da na caji wasu lokutan, tayi kiran ƙawayenta a wayar iyayesu su yi ta shashashanci ta daina ɗaukar ta mama.

Mama tana ganin wayar a hannun ruma, tana mitar ba ta son yawan duba wayar nan da take yi, a zatonta wayar Yasir ce kawai yake bata ta yi game da wasanta ta bashi kayarsa.

Mai sunan Baba ya nutsu ya tattara hankalinsa a kan litattafansa, sai dai hankalinsa ba a kan litattafan yake ba, damuwa da tunani ne fal a ransa, zuwa yanzu yakamata a sake aikawa da Abubakar kuɗi ko babu yawa ne, dan har zuwa yanzu ya ce masa bai samu wani aikin ba, leburanci ne ya kan shiga cikin gari ya nema idan ba shi da lectures, kuma gashi ɗan abin da za a baka na leburancin nan, bashi da wani yawa ga wuni ana aikin ƙarfi.

Ga kuɗin saukar su Yasir, ga kuɗin Necon su, dan dai suma yaran suna da ƙoƙarin neman na kai, da karambani Yasir ya koyi gyaran fitila, da wayoyi gashi ya san kan computer sosai, yanzu zai kashe wata wayar  ya tashi wata yana da kai a wannan fannin.

Shi kuma Huzaifa big boy ne, shi baya tanadi, idan ya samu kuɗi kawai ya kashe su, a huta. Sai dai bashi da rowa, yana zuwa shagon ɗinki da na aski, amma mugun mashiririci ne na gaske.

Sallamar da aka yi ne, ta dawo da mai sunan Baba daga tunanin da ya tafi.

Wata yarinya ce sa’ar ruma, sai kuma wata ‘yar budurwa suka yi sallamar.

Fuskarsu kawai ya kalla, ya san da ƙuyar idan ba ruma ce, ta yi wata tsiyar ba.

Suka gaida mama cikin ladabi, shi kuma ya mayar da hankali a kan littafin gabansa kamar bai san da zuwansu ba.

Zumbur ruma ta miƙe, za ta janye su, mama ta ce musu yaya aka yi, saboda ita mama a tarbiyyar ta ƙawaye ba sa biyo ruma gida, idan ba wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ya kawo su ba.

‘yar babbar ta ce “Kuɗin da ƙanwata take bin ruma, muka zo karɓa”.

Cikin mamaki Mama ta ce “wane kuɗi kuma?”

Yarinyar ta ce “Ranar an aiki ƙanwata, suka haɗu da ruma, shi ne a canjin mamanmu, ruma ta ranci naira ɗari biyu ta bawa wani  tsoho almajiri, wai  ya bata tausayi da ga gani yunwa yake ji, wai zata bata kuɗin kuma haryanzu ba ta bayar ba, mamanmu kuma so take ta yi amfani da kuɗinta”

Mama ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ita ruman? Uban waye ya ce ki karɓar musu kuɗi kiyi sadaka da su?”

“Wallahi mama tausayi ya bani, cewa yayi na taimaka masa, kuma idan na bayar da kuɗinki zaki yi mini faɗa, shi ne na ranci canjin babarsu, kuma malam ne ya ce mana sadaka maganin masifa ce”

“Ke a cikin wace masifar ki ke? Ko da yake akwai masifar da ta wuce ɗauko mini magana da ki ke yi ba yau ba gobe, baki yi sadaka da kuɗin uwarki ba sai na uwar wasu, saboda tsabar rashin ji?”

Abdallah ya ce “Wallahi mama yarinyar nan da ƙyar idan ba ta da taɓin hankali”.

Mama rasa me zata yiwa ruma ta huce ta yi, saboda yadda take caza mata kai abin ya wuce hankali, sai ƙifta ido take kamar an kwashewa karya ‘ya’ya, gefe ɗaya kuma tana hararar yaran.

Mai sunan baba ya kalli Ruma, ya ga tana yiwa yarinyar alamar idan suka haɗu sai ta yankata.

gashi yau Mama ba ta da wani kuɗin kirki, ga ruma zata ja mata fitar naira ɗari biyu ba dalili.

Mai sunan Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ɗari biyu ya ajiye ya kalli yaran ya ce “zo ki ɗauka”

Cikin fargaba da tsoro yarinyar ta tafi ɗaukar kuɗin, dan fuskarsa ma kawai abar tsoro ce saboda kwarjini.

Har ta durƙusa ta ɗau ɗarin, ya kalleta sai da hantar cikinta ta kaɗa, ta dakata da ɗaukar kuɗin.

“Ke shashashar ina ce da wata za ta ce ki bata aron kuɗin babarki, ki bata ta bayar kina tsaye san sokwanci”

Jiki na rawa ta ce “Idan ban bata ba zata iya dukana”

“Idan ta dakekin ba zaki iya ramawa ba, ko ƙarfinki ta fi? Daga yau idan kuka kuma bata wani abinku, ku ka biyota gida kawo ƙara, da ku da ita zan haɗa na zane, ɗauki ki tashi ki bani wuri”

Kamar mai shirin ɗauko wani abu a wuta, haka ta miƙa hannu ta ɗauko kuɗin, ta tashi suka fice da sauri.

“Ke kuma zo nan” yayi ya yana kallon inda ruma take.

Jikinta har wata tsuma yake, ta taso ta zo in da yake ta durƙusa.

Ya ƙare mata kallo ya ce ‘har kin manta sharaɗinmu ko?” Ta girgiza kai.

“Da kyau, nan da gobe in Allah ya ki nemo kuɗina da na bayar ki biyani, dan ba zan ɗau asara ba, kuma ban yarda ki tambayi wani a gidan nan ya baki ba, kuma ki ka je waje ki ka ɗauko magana sai na takaki a gidan nan, mara kan gado tashi ki bani wuri” da sauri ta zabura ta bar gabansa tana tsuma, ita yanzu a gidan uban wa za ta samo kuɗin da zata biya shi?.

Haka ta koma tayi zuruuu, kamar ruwa ya jiƙa mage, tana ji a ranta idan ta kama yarinyar nan sai ta daku, saboda ja mata damuwa da ta yi.

****

Samha ce zaune a falo, tana shan twa da biscuit tana yi tana kallon tv, tare da kaɗa ƙafa.

Wayarta ce ta fara ringing, dan haka ta ajiye kofin tean, ta ɗau wayar ta kara a kunnenta.

“Samha” ya kira sunanta a taƙaice.

“Waye?” Tayi maganar cikin ƙosawa.

“Khalifa Usman wakili”

“Wai meye haɗina da kai ne? Me ka ke so kuma?”

“Easy mana, a kan maganarmu ne dai da muka fara”

Samha ta ja tsaki ta ce “Wai kai baka ganewa ne? Ba mun gama wannan maganar da kai bane ba?”

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Ina ƙara baki lokaci ne, gudun kar ki dawo kina cizon yatsa daga baya, kin fi kowa sanin halin sa da taurin kai, ke a tunaninki ta ina burinki zai cika, kina daga zaune kina shashashanci lokaci na ƙure miki? Kiyi abin da ya dace ki samu burinki ya cika, ganin bayan Adam baya na nufin yi masa illar da ba zai amfanu a gareki bane ba, amma ganin bayan nasa shi ne samun damarki na biyan taki buƙatar. Idan so nake na kawar da Adam, abu ne mai sauƙi a gareni, amma ni ba hakan nake buƙata ba, haɗin kanki kawai kiyi tunani amma”.

Bai tsaya jin amsarta ba, ya katse wayar, Samha ta bi wayar da kallo, tamkar za ta ga Khalifa a ciki. A hankali ta ajiye wayar ta yi shiru tana jujjuya maganar sa, sai dai ta kasa gano cikakkiyar mafita a kan lamarin.

“Samha, me ki ke tunani ne?”

Samha ta kalli mai maganar ta girgiza kai ta ce “Babu komai”

“Ki yi sauri ki je ki duba kayan nan, bana son sai an fitar mutane sun gama zaɓa tukuna”

Samha ta ce “Shikenan” sai dai hankalinta da nutsuwarta sam ba sa tare da ita.

***

Sam ruma ta rasa sukuni, gaba ɗaya sallolinta addu’a take a kan Allah ya sa mai sunan baba ya huce, idan bai huce ba bata san in da zata samo ɗari biyun nan ba, gashi ya ce kar ta sake ta tambayi kowa a gidan.

Gashi har wayewar garin yau ba ta samu kuɗin ba, wunin ranar bai kulata ba, bai kuma ce ta bashi kuɗin ba, sai da dare yayi, ta rasa dalilin da ya sanya yake son hukunta ta da daddare ya hanata bacci.

Tana zaune zuruu ta takure, tana zancen zuci ta ga ƙafafuwan sa, tana ɗaga ido suka yi ido huɗu.

Take ta rikice ya fara “Wallahi yaya ban samo kuɗin nan ba, ban san a in da zan samo su ba, kayi mini rai dan Allah”.

“Kin san ba ki da inda zaki samo kuɗin kika arar mata kuɗi, da uban wa zaki biyata da? Wato sata ki ke kenan”

Cikin kururuwa ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wallahi ban taɓa ɗaukar kayan wani ba. Wallahi dama niyyata na tara mata, sai na biyata amma wallahi bani da kuɗin da zan biyaka dan Allah kayi haƙuri”

Cikin kaushin murya ya ce “Sai fa kin nemo kuɗina kin biyani, ko a ina ne”

“Wallahi sai dai in kayana za a sayar a biyaka, amma wallahi bani da su”

“Wallahi da kin samo kuɗin nan kin bani, sai na taka kanki, ta tabatta sata ki ke yi, ko a gida ko a waje, amma sai Allah ya ƙwace ki, kin yi sa’a da kin gane shayi ruwa ne, sai na sakaki a mari na kulle, kuma ki cigaba da abin da ki ke yi kar ki fasa, idan ki ka kaini bango sai dai ki ji an ɗaura auranki da malam Ladan, ko na sakaki a mari” jikin Ruma har ɓari yake, saboda wannan taratsin da yake yi mata kamar ta yi fitsari haka take ji. Ba ta samu damar shaƙar isashiyar iska ba, sai da ya bar ɗakin ta dinga ajiyar zuciya.

Mama kuwa sam ba ta tanka musu ba, dan a yanzu kowane hukunci mai sunan Baba zai ɗauka a kan ruma, ba zata nema mata sassauci ba, saboda ruma babu alamar shiriya a tare da ita.

Sai da wannan ƙurar ta lafa, sannan ruma ta samu nutsuwa, ta cigaba da harkokinta.

Kamar mai ɗaukar karatu, haka ta nutsu a kan waya, tana kallo a Instagram wani abun ta yi dariya wani tayi tsaki.

Kan wani hoto taje, wani kyakkyawan mutum, ya sha kayan graduation, yanayinsa bai yi yanayin fara’a ba, amma ya ɗan geɓare baki yayi murmushi, har za ta yi liking saboda a rayuwarta tana son ta ga mutanen da suka yi nasara, musamman ta kammala karatu.

Kawai sai ta sake wurgawa, ta ga wani hoton nasa a cikin turawa, ta dinga dubawa, sauran hotunan duk a cikin turawa, da kuma aji na karatu, ajin tamkar ofishin wani shugaban ƙasar.

Haushi ne ya kama ruma da tuno yadda ajinsu yake, sheranjiya da aka yi ruwan sama, suka je suka tarar ruwa ya cika ajinsu, murfin kwano ya yaye, sai haɗesu suka yi a wani ajin.

Ai babu tunani ta shiga comment section ta ce An ɗibi haramun an je karatu, Allah ya isa kuɗin talakawa, ɓarayin kuɗin mutane, bamu yafe ba muna fama ajinmu ko rufi babu.  daga haka ta ƙara gaba, ta cigaba da kallonta.

Ta gama abin da take, ta ajiye waya ta shiga nata shagali.

Sai da daddare ta dawo, ta sake ɗaukar waya, ta ga an yi mata reply a message, ta yi ta murna yau an kulata a Instagram, dan ganin mutanen Instagram ɗin take wasu mutane daban.

Sai dai tana dubawa ta ga wani yayi mata replying da ‘Ya aka yi ki ka san da kuɗin talakawa ya yi karatun’

Cikin zafin rai ta rubuta ‘Idan gaskiya ne meyasa ya tafi ƙasar waje karatun, su yi a Nigeria mana” ta rufe datar ta ajiye tana huci, tare da ɗan jin releif a ranta, dan ta daɗe tana son samun damar da zata isarwa irin wannan mutanen abin da yake ranta.

Yanzu take jin kallon waya yayi mata rana, da ta ƙi yin zuciya har ta iya yadda ake amfani da irin wannan abubuwan.

***

Takawa ne riƙe da waya a hannunsa, Jabir sai surutu yake yi masa, amma kasancewar suna da banbancin hali shi da Jabir, ya sanya Jabir bai damu da rashin amsawar Takawa ba, saboda shi mutum ne ba mai yawan magana ba.

Can Adam ya ɗago rai a haɗe ya ce “Kai, wai ban hanaka ɗora hotuna na a social media ba?”

Jabir ya yi dariya ya ce “Tuna baya ne, ya sanya na ɗora gashi ka yi kasuwa ‘yan mata sai comment suke yi, waɗanda kuma suka sanka, suna yabawa tare da jinjina maka”

Adam ya yi guntun tsaki ya ce “Kana da matsala” har ya wuce account ɗin Jabir, kawai ya koma ya shiga comment section yana dudduba abin da aka ce.

Sai dai lokaci ɗaya annurin fuskarsa ya ɗauke, har wata zufar ɓacin rai ta fara tsatstsafo masa a goshinsa, duk kusan ko yaushe a cikin damuwa yake, amma ya daɗe bai ci karo da abin da ya daki zuciyarsa kamar wannan ba.

Ya ɗaga ido yana kallon Jabir, Jabir ya ce “Ya dai, ya na ga kana kallona?”

Riƙe wayar yayi, ya cigaba da kallon Jabir, Jabir ya miƙe ya duba wayar, ya yi tozali da abin da ya sanya Adam ɓacin rai.

Jikinsa ne yayi sanyi, dan sam bai san an yi wannan comment ɗin ba. Yana ƙoƙarin yin magana takawa ya ce “Kira mini Sidi a waya, ayi mini tracking ɗin account ɗin nan”

                      P21

Jabir ya ɗan yi gyaran murya ya ce “Ka ga dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka san ba a rasa irin waɗan nan a social media yaran talakawa ne kawai marasa tarbiyya amma dan Allah kawai ka share”

Takawa ya kalli Jabir ya ce “Ka kira mini Sidi na ce”

Jabir ya girgiza kai, wasu lokutan takawa akwai kafiya da gardama, da ga ganin comment ɗin mace ce, kuma koma menene ba zai huce ba tun da ta riga ta yi.

Ya lalubo lambar sidi, ya kira masa shi, ya bashi wayar.

Cikin zafin zuciya ya karɓi wayar, ya yi wa sidi bayanin abin da yake son ayi masa.

Yana gama wayar, ya jefa wa Jabir wayar, ya fice daga ɗakin gaba ɗaya.

Sosai samha ta ɓata lokaci wurin yin kwalliya, kasancewarta ‘yar ƙwalisa, sai dai babbar matsalarta ta ƙware a iya shigar banza, tun da garin Allah ya waye, bayan sun kammala waya da khalifa ta ji ta na son ganin takawa, dan haka da la’asar ta shirya ta tafi gidan, domin ganinsa.

Sai dai cikin sa’a, da ta shigo kan ta kai sashin Ammi, ta ga takawa ya taho fiuuu. Yanayinsa na rashin walwala bai sanya ta damu ba, balle ta saurara da abin da ta yi niyya.

Kai tsaye ta tunkari in da yake, ta fara yi masa magana, ko kallon in da take bai yi ba, yayi gaba abin sa, mamaki ne ya cikata, amma ba ta haƙura ba ta bi bayansa zuwa sashin Ammi, sai dai a sashin Ammi ma bai tsaya a falo ba, ya wuce ciki. Gaba ɗaya zuciyarsa a cunkushe take, an daɗe ba a gaya masa abin da ya ƙona masa rai kamar wannan comment ɗin ba, danganta shi da sata ba.

Samha kuwa gani tayi da kunya ta bi bayan takawa.

Nusaiba ce ta fito cikin shiri, da alama fita za ta yi, tayi arba da Samha a falo a tsaye.

“Ya dai na ganki a nan a tsaye, ko zama baki yi ba?” ‘yan kame-kame Samha ta hau yi “Amm, dama takawa yana nan ne?”

“Ban sani ba, amma meyasa ki ke nemansa?”

Tsuke fuska Samha ta yi ta ce “Ina ruwanki da dalilin da ya sanya nake nemansa, ba abin da ya shafe ki bane”

“Haka ne, amma kamar yayi banbarakwai da yawa, ko kin manta waye shi a wurinki, Anty Samha ai ana barin halak dan kunya”

“Shut up! Na ce miki akwai wani abu ne a tsakaninmu, kin san bana son raini ko? Kuma ko ba komai ai takawa ɗan uwana ne” Nusaiba ta ce “Haka ne, Allah ya taimaka” ta wuce ta bar Samha a falon.

Samha ta damu ta ga Adam sosai da sosai, domin samun ƙwarin gwiwar yanke hukunci a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi.

Fitar Nusaiba babu daɗewa, Samha na tsaye na ta tunani, ma’aikatan sashin Ammi babu wanda ya tanka mata tun bayan gaisuwa, saboda sun san halinta na dizgi da wulaƙanta mutane da cin zarafi.

Iman ce tayi sallama a cikin falon, kamar kullum tana ganin Samha gabanta ya faɗi.

Salo-salo kamar mara lafiya iman ta ƙaraso cikin falon, ta kalli Samha ta ce “Anty Samha ina wuni?”

Samha ta ɗago kai ta kalli iman, ta yamutsa fuska, ta tsani iman fiye da yadda ta tsani ‘yar uwatta. Ta ko ina iman kyakywar ce, ko da kwalliya babu, ko a wani yanayi yarinyar kyau ne da ita, ko kuka ko dariya, ko fushi ko fara’a komai kyau yake mata, ga tsananin kusanci da yake tsakaninta da takawa, bayan ɗaya katangar da ta yi mata shamaki da cimma burinta da take ta ƙoƙarin rusheta, iman ma wata babbar matsala ce a gare ta, dan duk tsanani akwai aure a tsakanin ta da takawa. Ba ta sake tabattar da Iman matsala ce a gare ta ba, sai da samarin ‘yan matan gidan suke zamewa su ce suna son iman, sai da su Fauziyya suka yi da gaske, wurin damɓara mata mummunan fenti, da yayi mugun taka rawa wurin rusa farincikin rayuwar iman sannan suka samu sauƙi, ga yarinyar sumi-sumi kamar munafuka, tana da sanyin hali, nutsuwa da kuma girmama mutane, shiya sanya kowa yake sonta, ban da yanzu ma da ake janye jiki daga gare ta.

“Anty Samha, wai ya na ga kina ta kallona? Me na yi kuma?”

Wani mugun kallo ta yiwa iman ta ce “Zan yi maganinki ne, magani na har abada, idan har baki bar sabgar takawa ba” iman na shirin magana, Ammi ta fito da sauri daga sashenta tana ƙwalawa iman kira.

Ganin Ammi a ruɗe ya sanya iman bin Ammi da sauri, ba tare da tunnin komai ba, Samha ma ta rufa musu baya.

A ɗakin Ammi suka tarar da takawa a sheme a ƙasa.

Cikin ruɗu Ammi ta ce “Iman ina maganin sa”

Cikin rawar jiki iman ta ce “Ammi me aka yi masa kuma ciwon ya tashi?”

“Ban sani ba, kawai yana shigowa ya faɗi yi sauri ki ɗauko”.

“Kin san ya daɗe ciwon bai tashi ba, sai na binciko shi a in da na ɓoye, bari na ɗauko”

Samha ta ce “Ammi meya same shi ne?”

“Bashi da lafiya ne” Ammi ta bata amsa a taƙaice.

Iman ta ɗan jima sannan ta kawo maganin, wani mai ne a doguwar kwalba ta zo da shi, ta buɗe tana shafawa takawa a goshinsa, jikinsa sai wani irin rawa yake yana ƙamewa kamar mai farfaɗiya.

Iman ta dinga shafa masa tana karanto adduoi daban-daban, kusan mintuna goma sannan ya daina abin da yake yi, da kansa ya tashi ba tare da ya cewa kowa komai ba, ya je ya hau kan gadon Ammi ya kwanta ya rufe idonsa.

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce “Ammi bari na tafi, dama mama ce ta aiko ni wurin Mummy, na biyo na gaishe ki, bari na tafi Allah ya ƙara lafiya”.

Har samha zata fita, Ammi ta kirata, Samha ta dawo gaban Ammi.

Ammi ta riƙo hannun Samha ta ce “Dan Allah Samha kar ki gayawa kowa takawa bashi da lafiya, waɗanda suka san yana da wannan rashin lafiyar sun zata tuni ya warke, dan Allah ki rufa mini asiri, ki yi shiru da bakinki” Ammi tayi maganar kamar zata yi kuka.

Cikin kulawa Samha ta ce “Ammina, kar ki damu, babu wanda zan gayawa in sha Allah, rufin asirinki ai namu ne, ba wanda zai ji in sha Allah “

Ammi ta jinjina kai, ta yiwa Samha godiya, iman kuwa tausayin Ammi yakamata, ammi haryanzu ba ta san halin samha ba, ko da yake ba wanda zai yadda da samha fuska biyu ce da ita.

Jiki a sanyaye Samha ta wuce sashin Mummy, sai dai sashin na ta shiru babu kowa. Kai tsaye ta nufi ɗakin Mummy.

Ta tarar da mummyn na waya, ta samu wuri ta zauna tana jiran ta kammala wayar.

Mummy ta kammala wayar ta dubi Samha ta ce “Samha ‘yar ƙwalisa, ya aka yi ne, na ga duk jikinki a sanyaye?”

Samha ta dubeta ta ce “Mummy, wai dan Allah baki da masaniya a kan rashin lafiyar Adam?”

“Wace rashin lafiya kuma?”

“Rashin lafiyar da ake cewa yana da ita, yau na gani da idona”

Mummy ta waro ido waje ta ce “Ki na nufin bai warke ba dama?”

“Eh, mahaifiyarsa ta nemi na yi shiru da bakina, amma na kasa jurewa, sai da na ga iman tana ta shafa masa wani abu a fuska, sannan ya tashi, anya Mummy babu hannunki a ciki?”

Mummy ta yi wani murmushi sannan ta ce “Samha kenan, ke idan da hannuna a ciki zan kasa gaya miki ne, ai da ko a wurin mahaifiyarku zaki ji, babu ruwana a cikin lamarin nan, ni ban ma san haryanzu yana da wannan ciwon ba, a zatona tuni ya warke”

Samha ta rausayar da kai, sannan ta miƙe tsaye ta ce “Na tafi, dama sauri nake” bayanta mummy ta bi da kallo, sannan tayi wani irin murmushi ta ce

“Yarinya man kaza, wannan labari yayi mini daɗi da ki ka zo mini da shi, dama na daɗe ban ji labari mai daɗin wannan ba. Zan cigaba da amfani da wawancinki ina ruftaki, dole in je gidan Galadima, sai Hajiya Luba ta ji wannan zancen”

****

Ruma kuwa tuni ta manta abin da ta yi, dan ba ta ɗauki abin da tayin wani abu mai muhimmanci ba, sabgoginta ta cigaba da yi, sai dai tana iya ƙoƙarinta yanzu a kan kar ta yi wani abun da zai kuma haɗata da mai sunan Baba, dan karonsu babu daɗi sam.

***

Kamar ko yaushe, haka yanzu ma muryarta ta yake ji a kunnuwansa, a hankali ya buɗe idonsa, yana son tabattar da a ina yake, abin da ya iya tunawa shine ya shigo cikin gidan sashin Ammi, amma daga haka bai iya tuna komai ba.

A hankali kunnuwansa suka jiyo masa muryar Ammi tana karatun Alqur’ani.

Ya juya, ya kalli Ammi, ta na sanye da hijjabi, iman kuma ta ziro masa ido tana kallonsa.

Da sauri iman ta ce “Ammi ya farka”

Cikin kulawa Ammi ta dube shi, ta ɗora hannunta a goshinsa tana yi masa sannu.

Ya jinjina kai, Iman ma ta shiga jero masa sannu yana jinjina kai.

“Takawa, duk da na san ba ka so, amma ya zama dole ka yi haƙuri mu cigaba da neman magani, a baya abu ya lafa amma Kwatsam yau sai gashi ka faɗi, dole mu yi wani abu a kai kafin a farga a samu abin faɗa.

Shiruu Adam ya yi yana sauraron Ammi, ba tare da ya iya cewa komai ba.

Ammi ta kalli iman ta ce “Auta, duk da bani da matsala da ke, amma ke ma ki yi shiru, ko waccan ruɗaɗɗiyar Nusaiba kar ki gayawa”

Iman ta ce “In sha Allah Ammi, bari na je na mayar da maganin”.

Zuwa washegari takawa ya ware, kamar ba shi ba,  ya cigaba da azalzala a kan a nemo masa mamallakin account ɗin nan da aka ce masa ɓarawo da shi.

A washegari Mummy ta shirya ta tafi gidan Galadima mai ci a yanzu, wato gidan su Jabir.

Hajiya Lubabatu na ganinta suka yi wata shewa, tare da gaisawa da junansu.

Hajiya Lubabatu ta ce “Ya akwai labari ne?”

“Da ɗumi-ɗuminsa ma kuwa, mu shiga daga bedroom.

Cikin ɗaki suka shiga, Mummy ta ce “Ya jikin Galadima ne?”

Hajiya Lubabatu ta ce “To ni me ma zance miki ne, a ƙarshen watan nan dai nake son ko ni ko jabir wani ya je, ance dai da sauƙi”

“To Allah ya ƙara afuwa, amma gaskiya Yakamata ki miƙe ki ɓata alaƙar da ke tsakanin Adam da Jabir, kin san idan babansu ya rasu sarauta gidanmu za ta dawo, ke sai ki zuba ido shikenan babu makoma, idan sarauta ta dawo hannun Adam waya san lokacin da zai mutu balle Jabir ɗin ma yayi sarautar, duk da ina ta ƙoƙarin ƙara rura wutar gaba tsakaninsa da Mahmud, sai dai Mahmud wawa ne, ya ƙi mayar da hankali a kan Sarautar, ba ta gabansa “.

Hajiya Lubabatu ta yi murmushi ta ce “Jamila kenan, ai kema kin san ba a zaune nake ba, kuma da sannu dukkaninmu zamu yi nasara, ai ke dama ba kya burin sarautar ta dawo gidanku”

“Ƙwarai kuwa, shiyasa nake ta son komai ya ɓaci, ko kin san ashe Adam bai warke daga wannan larurar da yayi ba yana yaro, mai kamar farfaɗiyae nan ba?”

“Haba dai, ya aka yi ki ka sani?”

“Samha ce ta zo ta titsiyeni, wai ta gani a sashin su, wai ko ina da hannu a rashin lafiyar ta sa, na ce mata ni babu ruwana, da ciwonsa na ganshi”

Hajiya Lubabatu ta ce “Kai samha ma akwai bin ƙwaƙwƙwafi, shareta kawai ai aiki yana kyau sosai”

“Haaa ke dai bari, idan har ina raye ko zan tafi tsirara sai Binta ta ɗanɗana kuɗarta in Allah ya yarda sai ciwon nan ya zame masa hauka tuburan, na kaɗa sauran yaran nata tare da wannan shegiyar yarinyar mai kama da larabawa”

Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce “Shi dai wannan ɗa abu ya zame masa goma da ashirin, da hauka ko in ce farfaɗiya, ga kuma maita duk shikaɗai”

“Hmm ke dai bari, ina jiran lokacin da zan kwatsa zancen nan a cikin masarautar Kano, ɗan da suke ji da shi maye ne, da ya sha a nonon uwarsa, ta ta ba ta baiyyana ba sai ta shi”

Cike da rashin imani suke ƙyaƙyace dariya, kamar ba za su bar duniya ba.

Cikin dare da misalin ƙarfe biyu da rabi, Baba uwani ce ke sanɗa kamar ‘yar fashi, ta buɗe babbar ƙofar sashen Ammi ta fita, kai tsaye ta nufi sashen Mummy, tana tura ƙofar sashin ta buɗe, ta kutsa tana waige-waige.

Hanyar kitchen ta bi, ta tarar da Mummy a wani ɗaki a zaune tana jiranta.

Baba uwani ta duƙa ta gaida Mummy, Bata amsa ba ta dubeta ta ce “Kin san dalilin da ya sanya na nemekk?”

Ta girgiza kai alamar a’a.

“An ce mini ɗan uwar ɗakinki Adam, haryanzu bai warke ba, ciwon nan da yayi da yarinta yana nan yana fama, jiya ma ya tashi haka ne?”

Baba uwani ta ce “Wallahi ban sani ba uwar ɗakina, jiya ta aikeni, kuma ina tunanin babu wanda ya sani, saboda da na dawo ban ji labari ba”.

“Ba tambayarki nake dogon labari ba, ance mini akwai wani abu da aka shafa masa, ya tashi da wuri, wannan abin nake son ki sanya ido ki ɗauko mini”

“Ranki ya daɗe, ai ban san a in sa suke ajiyewa ba, ba ta sanya ni a sabgar neman maganin sa ba”

“Bai shafeni ba uwani, ki aikata abin da na ce kawai, tashi ki bani wuri”

Haka baba uwani ta taso, tana tunanin ta in da zata fara aiwatar da wannan aiki mai mugun hatsari.

****

Yau ruma fakar idon Yasir ta yi, ta ɗauki wayar nan ta jefa a jakar makarantar ta, ta yiwa mama sallama ta tafi makaranta. Sai dai da ta je makarantar babu wanda ta iya nunawa wayar, gudun kar yaran su tona mata asiri a ƙwace wayar, sai dai ta na jin kanta riƙe wayar nan da take yi, duk da ba wayar kirki ba ce ba.

Yau mama ba ta nan, ta je cikin gari za su kai wani kayan lefe na wani ɗansu, dan haka ruma sai lissafi take a kan ba zata islamiyya ba, ƙulewa za ta yi a ɗaki ta yi kallo a waya, kuma ta sha baccinta.

Ta tsaya ta sai gyaɗa a hanya, tana tafe tana ci, kamar ba ɗiya mace ba, dan ruma duk wani abu na jan aji na mata ruma ba ta iya ba, haka nan take rayuwarta kamar namiji.

Ƙarar mota ta ji a bayanta, sai dai kan ta kauce, ta ga an sha gabanta da motar, wasu ƙarti ne suka fito suka ce “Shiga mota”

“In shiga aje ina kamar a film ɗin indiya”

Cikin tsawa ɗayan ya ce “Ki shiga mota na ce”

Ruma ta cake ta riƙe ƙugu  ta ce “Wai saboda me, in shiga ka kai ni ina?”

“Kai dalla dannota kawai, za ta ɓata mana lokaci” sau ɗaya ya tankaɗa ƙeyar ruma, ta hantsila cikin motar.

Aikuwa ta din ga kurma ihu “Al’ummar ɗorayi an saceni, dan Allah ku kawo mini agaji” rufe motar suka yi, suka ja dama motar tint ce, sai dai ruma ta cika musu kunne da kururuwa.

“Ke, kin ishemu, zamu yanka ki da da wuƙa a motar nan”

“Wallahi ba zan yi shiru ba, kun satoni kun sakani a tsakiyarku bayan ku ba muharramaina bane ba”.

Wanda yake tuƙa motar, ya dubi na kusa da shi, cikin harshen turanci ya ce “Anya kana ganin wannan yarinyar ce kuwa?”

“Oho, mu kai masa ita dai, shi zai tantance “.

“To ai gani na yi yarinya ce sosai, yaushe wannan zata iya wannan abu?”

“Kai wannan sai ta aikata, ji yadda take wa mutane ihu, dan ya ce ban da cin zarafi da sai na sakata a silent yanzun nan”.

“Wallahi idan baku buɗe mini motar nan na fita ba, sai na tara muku jama’a, ashe ma ku ƙananan ‘yan kidnapping ne, da kuka sace ni, to wallahi ni ƙanwar maza ce, idan yayyena suka gano ku, sai kun raina kanku” babu wanda ya kulata cikinsu, har suka isa in da zasu je, ba ta yi shiru ba ko na mintuna. Haka zalika idan za a kasheta ba ta san ta in da aka bi ba, saboda baƙin glass ne a motar.

Ita dai ta ji an tsaya, aka buɗe mota aka ce ta fito. Fitowa ta yi tana kallon harabar da aka paker motar.

Ingiza ruma suka yi, ta ƙanƙame jakarta tana kalle-kalle.

Wani falo aka shiga da ita, suna shiga wani irin sanyi ya daketa, ta ce “Wayyo sanyi” duk sai da suka kalleta kamar wata ‘yar ƙauye.

Ita ba kawotan ne ya dameta ba, tsaruwar gidan da yadda aka narka masa dukiya ne ya burgeta take ta kallo.

Sanyin Ac ne ya fara damunta, saboda haryanzu babu wanda ya ce mata komai, tunani ta fara yi, idan mama ta dawo ta tarar bata nan fa, gaba ɗaya hankalinta ya tashi yayi gida, a yadda take jin labarin kidnapping dai ba haka ake yin sa ba, ko da yake dai ai babu maraba.

Miƙewa tayi ta dubi mutumin da yake zaune a bakin ƙofa ta ce “Bawan Allah dan Allah ku zo ku sallameni, kar babata ta dawo ta ga bana gida”

“Wuce ki zauna, kafin na fasa kanki da harsashi”

“A’a da bom zaka fasa mini kai, ni me na yi muku ne?”

“Wallahi ki ka cigaba da yi mana hayaniya, sai na saka igiya na ɗaureki”

“Kamar ya ya ka ɗaureni da igiya, sai ka ce ragon layya? Dan Allah ku zo ku mayar da ni”

Cikin tsawa ya ce “Ki koma ki zauna na ce”.

Tsaki ta ja ta koma ta zauna, bin ruma ya yi da kallo jin yadda ta yi masa tsaki.

Zama ta yi ta ɗauko gyaɗarta ta cigaba da ci, tana ɓata wurin, mai gadin na ta kallonta yake, ita kamar ma ba ta damu da ɗaukotan nan da suka yi ba, gaba ɗaya ba ta da wata damuwa.

Ta gama cin gyɗarta, ta buɗe jakarta ta ɗauko rake. Duk ta ɓata wurin, ta gama ta gaji tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Surutan mutane suka ji, alamar za a shigo. A cikin mutanen da suka shigo su uku, tana yiwa ɗaya kallon sani, sai dai ta manta a ina ma ta sanshi.

“Tana ina?” Ya faɗa a taƙaice.

“Gata nan a gabanka sir, ita muka samo, kuma ta faɗi wasu abubuwa da ya sake tabattar da ita ce” cewar ɗaya daga cikin wanda suka kawo ruma.

Mamaki ne ya kama shi, ta ina ƙaramar yarinya kamar wannan, ta samu waya, har ta iya yi masa wannan comment ɗin.

Ya zauna ya na ƙare mata kallo, sai wani haɗe rai take tana basarwa, tana harare-harare ta gefen ido.

Jabir ya ce “ka bi komai a sannu Please, ka ga ƙarshen abin ma ashe yarinya ce, dama haƙura kai kamar yadda na gaya maka da farko”.

“Me na yi miki ki ka kirani da ɓarawo?” Yayi maganar yana tsareta da ido.

Mamaki ne ya kama ruma, ita a ina ta sanshi da zata kira shi da ɓarawo. Ya sake maimaita maganar amma tayi banza taƙi magana.

Jabir ya ɗauko wayarsa, ya shiga account ɗin da ruma tayi comment da shi ya nuna mata, ya ce “ke ki ka yi wannan comment ɗin?” Ta zubawa Jabir ido, shima ta ƙi kulashi, sai dai a yanzu ta gane in da ta taɓa ganin Adam, a Instagram taga hotonsa tayi comment.

“Wai kurma ce ne?”

“Sir wallahi ba kurma bace, yanzu ta gama magana iskanci ne, ka bari a casata kawai”.

“Am talking to you, me na yi miki ki ka ci mutuncina, wai na saci kuɗin talakawa, ance miki ni ɗan siyasa ne?”

Jabir ya ce “Easy Adam, yarinya ce ƙarama, ki na ji ki san abin da zaki din ga rubutawa a social media, wanda ya baki waya ma shi ne babban mai laifi, da ya bawa under age waya. Babban mutum ne sannane, ɗan gidan marigayi Galadiman Kano ne, bashi da alaƙa da siyasa, amma kin yi masa ƙazafi shi mahaifinsa basarake ne, kuma ɗan kasuwa ba kuɗin tal…..

“Shut up Jabir, na meye zaka din ga yi mata wani bayani”

“A’a ka yi haƙuri, kin ga bashi haƙuri komai ya wuce” wani kallon zaka bushe ruma tayi masa, ta ƙara gyara jakarta ta ɗauke kanta gefe guda.

Mamaki ne ya cika Adam, shi da yake dodo ko a cikin manyan mutane, amma shi wannan ‘yar shilar ke rainawa hankali, yana yi mata magana amma ta mayar da shi ɗan iska.

Jabir ya jinjina kai ya ce “Lallai gaba da gabanta, anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace ba?”

Kallon Jabir tayi ta galla masa harara, haka kawai tana ganinsa ta ji ta tsaneshi, wani mugun haushinsa ya kamata, ya fiye shishshigi.

Adam rasa abin yi ma yayi, dama wata babbace he knows how to deals with her, amma wannan ya hukunta ta ya ce ya yiwa wa?.

Ruma ta miƙe tsaye da jakarta, tana kallon wanda suka kawota, jinjina kai kawai suke, da ganin namijin ƙoƙarin da ubangidansu yayi.

Cikin ƙunƙuni ta ce “Ni a mayar da ni in da aka ɗauko ni” tayi maganar tana nufar ƙofar fita.

“Ku kamata ku ɗaure mini ita, sannan a nemo mini waye ubanta, in nuna wa babanta banbancin arziki da tsiya, shine dai-dai yi na, dan na fuskanci bayan talauci har da rashin tarbiyya a tare da ita.

Ba tare da ta waiwayo ba ta tsaya, dan ma kar ta kalleshi ya yi mata kwarjini ta ce “Shi baban nawa sai ka bishi kabari ka nuna masa ka fishi kuɗi, kuma Alhamdilillah ni dai an yi mini tarbiyya dai-dai gwargwado, kuma wallahi sai na saka yayyena sun yi maka bugun sakwara, har DPO na unguwarmu sai na gaya masa, ba sunanka Adam ba ɗan galadima ko wambai to wallahi sai na faɗa ka saceni ka kawoni cikin maza” tuni ya daskare a wurin, jikinsa ya hau tsuma, ga zafin maganganu da fitsarar Ruma, ga razani na jin muryar da take ta addabar kunnuwansa.

Cikin azama ya fizgota, ya juyo da ita gabansa, ya riƙe hijjabinta tare da rigar uniform ɗin ta. Kallon hannun takawa tayi, da ya sanya wani agogo mai kyawun gaske, amma babban abin da ya razana ruma, yadda ya riƙota ta wuya hannun ƙaton namiji a jikinta kan ƙirjinta, abin da aka ce ta ɓoye ta tattala, kar wani ya kai hannu wurin, idan ba haka ba za tayi ciki, amma hannun wani ƙato a wurin !!!

                      P22

Wani mugun ɓacin rai ne ya kama ruma, kamar za ta yi kuka ta ce “Malam meye haka? Meyasa zaka taɓani ka cikani”

Cikin tsananin mamaki, da rashin abin yi yake sake sauraren muryar ruma “Da..d…dama kece, meyasa ki ke bibiyata mai na yi miki ne?”

“Ni yaushe na sanka ma? Ka cikani kafin na yi maka hauka da tijarar da zaka yi dana sani, ka sakar mini hijjabi”

Tsananta riƙon da yayi wa ruma ya yi, yana sake bin ta da kallo, yana jin tamkar ba shi bane ba, anya mutum ce yarinyar nan, ko kuma dai muryar ce ke cigaba da yi masa gizo.

Ganin yadda duk ya gigice kamar zai fita hayyacinsa, ya sanya Jabir ƙoƙarin cire hannun takawa daga jikin ruma.

“Takawa, dan Allah ka kula mana, yarinya ce fa ƙarama ba sa’arka ba, dan Allah ka saketa, sannan kamar yaya tana bibiyarka?”

Hankaɗe ruma yayi, ya koma gefe ya zauna, yana dafe goshinsa.

Kuka ruma take wiwi, ta ɗauki jakarta.

Jabir ya kalli wanda suka kawo ruma ya ce “Sidi ku mayar da ita”.

Suka tasa ruma a gaba, ta waiwayo ta kalli takawa ta ce “Wallahi ban yafe ba ku…..”

“Ke wuce mu tafi, kin samu an ƙyaleki kuma kina yi wa mutane iskanci, mara tarbiyya”

Cikin dakiya ta ce “Eh bani da tarbiyyar, ku tarbiyyar ce ta saka kuka ɗauko ni ba da sanin iyayena ba ku ka kawo ni nan, cikin maza Allah sai ya saka mini”

Jabir ya ce “Kar ka kuma tankawa yarinyar nan, mayar da ita”

Jabir ya zauna a kusa da takawa ya ce “Takawa, wa me yake faruwa ne, ka san ta ne?”

Adam yayi shiru bai motsa ba, kuma bai ce komai ba, Jabir ya yi masa tambayoyi har ya gaji, amma bai amsa masa ba.

Ruma kuwa suna zuwa unguwar su, suka ajiyeta suka tafi, ta samu wani borehole ta wanke fuskarta, sannan ta tafi gida.

A tsakar gida ta tarar da Yaya Aliyu, ya kalleta ya ce “daga ina ki ke?”

“Makaranta” ta bashi amsa tana ɓata rai.

“Ba jarrabawa ku ke yi ba?”

“Laifi muka yi aka saka mu punishment” ta bashi amsar tana tsoron kar ya ganota.

“Haka dai ki ka iya, kullum cikin laifi kamar ke kaɗaice ɗaliba a makarantar”

Ganin bai ganota ba, ya sanya ta shiga ɗaki, ta ajiye jakarta ta tafi gaban mudubi ta tsaya, ta ƙarewa kanta kallo, ta tuna yadda takawa ya shaƙeta hannunsa har yana taɓo ƙirjinta.

Wasu hawayen ne suka shiga ziraro mata. “Wallahi sai ka gane baka da wayo, ka zunguro sama da kara, ni za a ciwa mutunci? Wallahi sai na kuma rubutawa, zaka gane ba ka da wayo, ai talauci ba hauka bane, mai kyan banza” haka ta tsaya a gaban mudubi, ta cigaba da kuka.

Kamar zararriya ta ɗauko jakarta, ta ɗauko wayar ta kuma komawa kan account ɗin da Jabir ya saka hoton takawa, ta sake rubuta “Wallahi Allah ban yafe ba, sai na kai ƙararka wurin ‘yan sanda, zaka san da ni kake yi” ta ajiye wayar tana fatan Allah ya sa kar idan mama ta dawo ta fuskanci wani abu.

****

Baba uwani ce ta shiga kitchen ta tarar da iman tana faten dankali.

“A’a mutuniyar ba kya gajiya da aiki, Ammin ake yiwa girki ne?”

Iman ta yi murmushi ta ce “A’a baba uwani, nice zan ci”

“Au yau ba za a ci abincin namu ba ne?”

Iman ta yi murmushi ta ce “Ba haka bane, kawai da wannan ɗin nake sha’awa bana son takura muku ne”

“A’a ai da kin faɗa ma babu wani abu, sai ayi miki, ni kuwa na ce takawa lafiya ƙalau kuwa yake?”

Cikin rashin fahimta iman ta ce “Me ki ka gani?”

“Ganinsa na yi duk wani iri”

“A’a lafiyarsa ƙalau, ina ga hakan ya na da alaƙa da yanayin aikinsa, kin san abubuwa su kan yi masa yawa”

Baba uwani ta ce “haka ne wallahi, ina tausayawa takawa yadda al’amura suke shan kansa Allah ya yi masa jagora”

Iman ta ce “Amin” a dai-dai lokacin ta juye dankalin a plate ta ɗauka ta fice.

Baba uwani ta yi tsaki ta ce “Kai wannan yarinyar kininabbiya ce ba wani abu da zaka samu daga wurinta”.

Takawa fa abubuwa suka sake rikice masa, tun bayan haɗuwarsa da ruma, da ya ji muryarta da take masa yawo a kunne, yana ta tuntuntuni, mutum ce ko akasin haka, dan iya ƙwarin gwiwar ta, da rashin kunya da ayar tambaya a kanta.

Yau gaba ɗaya bai koma gida ba, ya wuce gidansa ya tura wa Ammi message a kan ba zai shigo gida ba, a gidansa zai kwana.

Bayan ya turawa Ammi saƙon, ya kuma komawa Instagram, ya duba comment ɗin da ruma ta yi a kansa, kawai ya ci karo da sabon saƙonta, ya tabatta kenan ita ɗin ce dai ta yi comment ɗin farko.

Kiran Ammi ne ya shigo wayarsa, ya saita nutsuwarsa ya ɗaga tare da yin sallama.

Ammi ta amsa sanna ta ce “Yanzu na ga saƙonka, ka sam yadda yanayin jikinka yake, amma ka ce zaka kwana a gidanka kai kaɗai, kar wani abu ya sameka fa”

“Ammi kar ki damu, babu abin da zai sameni in sha Allah, ina son gabatar da wani aiki ne”

“To shikenan, amma dai da ka ji wani abu ka kirani a waya”.

Ya jinjina kai ya ce “To shikenan, in sha Allah sai da safe” suka yi sallama ya katse kiran.

Ya rintse ido, yana jin muryar ruma na sake amsa kuwwa a kunnuwansa, ya tuna yadda ta danganta shi da sata, take ya ji ya tsani yarinyar, kuma daga uniform ɗin jikinta zaka gane ‘yar talakwa ce, amma sai ƙarfin hali da rashin mutunci, to yayi faɗa da wannan ‘yar ma ya ce ya yi da wa? Wani uban tsaki ya ja, ya koma ya kwanta yana ƙwafa. Ya kuma komawa ya na duba comment ɗin ruma, amma ya tarar Jabir ya goge posting ɗin gaba ɗaya.

***

Ko da mama ta dawo, ta tarar gaba ɗaya ruma ba ta da walwala, duk tayi wani iri, mama ta tambayeta ko ba ta da lafiya, ta ce ita lafiyarta ƙalau kan ta me yake ciwo, mama kuwa ta ƙayleta, amma ta cigaba da monitoring ɗin ta.

Yau ko wannan uban surutun da take kamar an jefeta a ka, babu ta yi shiru sai tunane-tunane take a ranta, a kan me za ta yi wa wannan ɗan tahalikin ta huce, gashi ita ba ta san a ina ma za ta sake ganinsa ba, balle ta gaggaya masa magana ta huce da abin da yayi mata.

Mama suna ta hira suna tsara yadda bikin saukar su Yasir zata kasance, ruma ta koma kusa sa Abdallah ta ɗan yi ƙasa da muryarta ta ce “Yaya Abdallah, dan Allah waye galadiman Kano?”

Ya dubeta ya ce “Basarake ne a Kano, ba shi ne aka ce yana Germany ba bashi da lafiya, meyasa ki ke tambaya?”

“Babu komai kawai tamabaya na yi, amma ba ya mutu ba?”

“Anya, gaskiya ban sani ba, na ji dai an ce yana Germany babu lafiya”

Ɗan shiru ta yi ta na tunani, a wurin Hauwwaliya kawai za ta samu abin da take so, dan haka ta sake gyara zama ta ce “Yaya dan Allah ranar juma’a mu je cikin gari”

“Ba zani ba, ina da abin yi ranar”

“Dan Allah, na ji mama tana waya da mamansu, an ce Hauwwaliya babu lafiya dan Allah ka kaini na ganta”

“Ke na ce miki ina da abin yi ranar”

“Ai Allah na ce, ka taimaka” ta yi maganar cikin magiya.

Abdallah ya ɗan yi tsaki ya ce “Zan yi tunani”

Ta ce “Dan Allah ka kaini”

Bai sake kulata ba, saboda baya son magiya, ruma kuwa ta ƙware a kanta.

***

Kamar wasa Samha ta kira Khalifa a waya, kamar dama jiran kiranta yaje, tana kira ya ɗaga.

“Adon gari ya kike?”

“Ba dogon surutu ba, ina son sanin deal ɗin da kake son mu yi, na gani idan zan iya”

Murmushi ya yi, tare da kashe sigarin hannunsa ya ce “Kin yi tunani kin ga ni ke da mafita dai kenan? Sai dai kin so ki makara dan na samu wanda ya kawo tayin shiga deal ɗin, ban sani ba ko ta wurnki aka samu bayani, amma duk da haka kema akwai role ɗin da zaki taka, a ina zamu haɗu?”

Cikin mamaki Samha ta ce “Amma waye haka, da har ka ke tunani ta hanyata ya ji labarin deal ɗin nan?”.

“Kar ki damu da sanin waye, mu haɗu a hotel ɗin da muka haɗu last”

Ta girgiza kai ta ce “No, kar ka manta ni ‘yar babban gida ce, ba zai yiwu ma din ga yawon hotel ba, ka sama mana wani wurin kawai”.

“To Shikenan, zan turo miki wani address ɗin, ki huta lafiya” ta sauke wayar daga kunnenta, tana tunanin anya ba ta yi garaje ba wurin amincewa da Khalifa ba tare da ta san aikin sa za ta yi masa ba?.

***

Ranar juma’a ana tashi daga makaranta ruma ta taho gida, saboda ta tirke Abdallah ya cika mata alƙawarin kai ta cikin gari, dan tuni ta tambayi mama, mama ta barta Abdallah ya kaita, musamman da ta ji ta ce Hauwwaliya zata duba.

Ƙasan zuciyarta kuwa, so take ta sake haɗuwa da takawa, ta yi rashin kunya ko ta huce abin da ya yi mata.

Duk wani hoton Adam yake kan account ɗin Jabir, sai da Jabir ya sauke shi, ƙarshe ma yayi blocking ɗin ruma, bayan yayi reporting account ɗin ta an rufe mata shi.

Abdallah ya ce “Sai dai ruma ta yi haƙuri, dan wani wurin za shi, amma mama ta ce ya daure ya kaita, dan ruma a zahiri damuwa ta nuna da rashin lafiyar Hauwwaliya.

Ba dan ya so ba ya tasa ruma a gaba zuwa mandawari, Hauwwaliyarma ta samu sauƙi, bayan sun gaisa da mutanen gidan, Abdallah ya ce da yamma zai zo ya ɗau ruma.

Hauwwaliya ta yi ta murna da ganin ruma, dan rabon da su haɗu tun wancan zuwan.

Bayan ruma ta ɗan jima, ta fara ƙoƙarin aiwatar da abin da ya kawota.

“Hauwwaliya, ina ne gidan Galadima ne?”

Hauwwaliya ta ce “Wai makaranta?”

Ruma ta yi tsaki ta ce “Galadiman kano”

“Wanne?”

“Au biyu ne?”

Hauwwaliya ta ce “Ai akwai Galadima na yanzu, wanda ba shi da lafiya yana Germany, sannan akwai gidan Galadiman kano wanda ya rasu”

Ruma ta ce “Wanda ya mutun”

Hauwwaliya ta yi dariya ta ce “Ke ai wan baban su Janna ne, jikar turakin nan da muka je gidan su biki ta bamu kaya, kuma yayan Galadiman kano na yanzu ne duk fa ‘yan uwa ne, sarautar ba a rabawa a bawa bare dole sai su”

Ruma ta yi tsaki ta ce “Ni fa ba nasaba na tambayeki ba, ina ne gidan na sa”

Hauwwaliya ta ce “Shi wa?”

“Ke wai ya ina magana kina raina mini hankali, maganar wa muke ne?”

“To ke meye alaƙarki da su da ki ke tambayata?”

Ruma ta ce “Assignment aka bamu a makaranta”

“Aka ce me?” Ruma ta ɓata fuska ta ce “Hauwwaliya, ni zaki wulaƙanta?”.

Hauwwaliya ta kwashe da dariya ta ce “Yi haƙuri, Galadiman da ya rasu gidansa a bayan gidan sarki yake, wani ƙaton gida gari guda, baki ga katangar gidan ba, doguwa sosai a nan dai gidan yake”

“To kin san ‘ya’yan gidan?”

“To meye alaƙata sa su da zan san ‘ya’yan gidan, suma ‘ya’yan gidan duk a cikin assignment ɗin suke?”

Ruma ta yi murmushi ta ce “A’a dan Allah in anjima mu je, ina son in ga dokuna”

Haka ruma ta din ga lallaɓa Hauwwaliya, suka tafi yakasai, har family house ɗin su Takawa.

Ruma ta yi mamakin girman gidan, ya fi na Turaki da suka je rannan, suka gama yawonsu suka koma gida.

Yau ma sai magariba sannan Abdallah ya ɗauketa, suka koma gida, sai dai tun da suka koma gida, ruma take tunanin ta ina za ta ga Takawa, dan ta ƙudirce a ranta ba zata haƙura ba.

Sai dai gate ɗin gidan na su kawai girmansa abin mamaki ne, babu wata ‘yar kafa da za ta bi ta shiga, ga masu gadi a zaune a ƙofar gidan, da alama shiga gidan ba zai zama abu mai sauƙi ba.

***

Tun da Samha ta koma gida, take tunani a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi, dan ba abu ne mai sauƙi ba. Amma duk tunanin da ya kamata ta yi ta yi, shikaɗai me mafitar da ya rage mata, dan takawa hankalinsa sam ba ya kanta, idan har ba kawar da alaƙar nan ta yi ba, to ita da Adam sai dai kallo daga nesa, haka zalika sai ta yi ƙoƙari wurin takawa su Hajiya Jamila burki a wasu ɓangarorin dan idan suka nakasta shi, to ita suka yi wa.

***

Mama ta zauna ta tattauna da yaranta, a ƙarshe suka amince da a sayar gonar mahaifinsu ta can katsina  a garin Ƙanƙara, domin yin hidimomin da suke gabansu, masu registration ayi musu, masu exam a biya musu, masu buƙatar jari duk ayi musu. Sannan still akwai filinsu da aikin gwamnati ya bi ta kai, za a basu diyya.

Sai dai mama ta ce ita tsoron garin nan take ji, kawai ayi waya su sayar ɗan abin da ya samu da na diyyar a aiko musu, can dangin babansu suka hau mitar cewa mama ta mallake yaran ba ga son su je in da suje, ƙarshe aka yanke Aliyu zai je.

Yaya Abubakar ya ce “Dan Allah mama idan zai je, ya kai musu ruma, tun da dama exam za su yi, su yi hutu, ko a samu su daina surutun nan da suke yi na rashin zumunci, rabon da aje da ita garin fa tun yaye, rannan da na je baki ga mita da faɗan da suka din ga yi ba, wai kin fiye son ‘ya’ya, wayar da muka yi da baba Habu shekaranjiya a kan biyan diyyar nan shi ma ba ki ji faɗan da ya yi ba”.

Mama ta ce “Ba ƙi nake ba, ka san halin rashin jin yarinyar nan shi nake tsoro, ga yanayin garin babu lafiya”.

“Mama ai a cikin ido ake tsawurya, in Allah ya yadda babu abin da zai faru sai alkhairi”

Mama ta ce “To, Allah ya sa”

Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe ɗaya ta fi son sai ta tafkawa takawa ɓarna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.

***

Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare, ƙamshi duk ya gauraye ɗakin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.

“Mutum kwalliya sai ka ce aljana” dariya ta yi har sai da dimples ɗin ta suka lotsa, ta ce “To idan ban kwalliya ba me zan yi?”

Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce “Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai” ɓata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana faɗin “My Chubby girl”.

***

Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da yake garin.

Gaba ɗaya Instagram sun yi banning account ɗin ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram ɗin sam.

Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.

Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.

Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.

A ƙofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga? Cikin dakiya ta tunkari ƙofar gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.

Gadan-gadan ta nufi shiga, wani ɗan sanda yayi mata tsawa ya ce “Ke wurin wa ki ka zo?”

Ta ɗan yi jimm sannan ta ce “Wurin wani”

“Waye wanin?”.

“Sunanshi Adamu”

Wado ido suka yi gaba ɗaya suna kallon ruma “Ke! Baki da hankali?” Saroro ta yi tana tunanin me ta yi kuma?

“Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki faɗi wannan sunan haka? Zaki bar wurin nan ko sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki”

“Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga”

“Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga”.

“To a wurin wa zan nemi iznin?”

Ɗaya daga cikin su ya ce “Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar ‘ya da baki fil-fil kamar robot”

Ta kalleshi ta ce “Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina” tayi maganar idonta ƙyar a cikin nasa.

Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya jiƙawa yarinyar nan jikinta.

Ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana kallon hanya. Suka kunna sigari suna sha, ruma ta kallesu ta taɓe baki a hankali ta ce “An yi asara”

“Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?”

“Ni dai ba a kanku nake ba, ku ƙyaleni mana” ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu naɗi.

Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara’arsu suka fara mata magana “Baba Sabuwa, kin dawo?”

“Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?”

Suka amsa mata da Alhamdilillah.

Ruma ce ta taso da sauri tana faɗin “Baba” baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce “Yarinya ya aka yi?”

“Dan Allah gidan nan zaki shiga?”

Ta ce “Eh, a gidan nake aiki”

“Kin san wani Adamu a cikin gidan?” Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da fatan Allah ya sa wani bai ji ba.

“Ke ‘ya ta ai ba a faɗar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san shi”

Ruma ta yi ƙasa da muryarta ta ce “Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata”

Baba uwani ta ce “To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?”

“Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi “

Baba sabuwa ta ce “to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda”.

“Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku”

“Zo mu baki sigari ” ɗayan ya faɗa cikin iya shege.

“Sai dai uwar sigari” ta faɗa a hankali.

Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.

Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a ɓangaren Mummy, kuma tana ɗaya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan.

Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar ɗakinta takardar su fara dubawa ko kuwa? Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a ɗan tofinta, ta cigaba da ayyukanta.

Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da faɗa, dan babu wanda ya san ta fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin saƙonta zai je in da take so, sai Addu’a take Allah ya sa baba Sabuwa ta bayar da saƙonta. Aliyu ya tasa ta a gaba zuwa gida, suna tafe yana ƙare mata zagi.

Wajen ƙarfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa gidan ba sai yanzu.

A gate jami’an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.

Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya ce “Kira mini Baba sabuwa” ta miƙe tana tunanin me yasa yake neman Baba sabuwa a yammacin nan?.

Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya miƙa mata hannu ya ce “Bani saƙona” babu musu ta fito da takarda ta miƙa masa. Ya juya ya fice.

Fauziyya ta ce “Sabuwa, takardar mecece?”

“Wallahi wata yarinya ce ta tsareni a ƙofa, ta ce a bashi ban san yarinyar ba ma”

“To meye a ciki?”

“Ai kin san ba iya karatu na yi ba”

“Kuma da baki iya karatun ba, mai ya hana ki kawo mini, tashi dalla usless” Sabuwa ta tashi cike da haushin tsawar da Fauziyya ta yi mata, duk da ba yau ta fara ba.

Bai tsaya duba takardar ba, ya jefata a cikin jakarsa ya tafi wurin Ammi.

Gaba daya ya manta da takarda, sai washegari da daddare yana neman wasu takardu, takardar ta faɗo.

Ya buɗe takardar wasu ‘yan ƙananan rubutu ne, marasa kan gado a cikin takardar, bai yi zaton rubutun zai karantu ba sai da ya fara karantawa, duk an gwamutsa Capital da small latter’s.

*Da farko dai zan fara da yi maka Allah ya isa, dan da alama baka da ƙanne mata shi ya sa ka yi mini abin da ka yi mini. Kamar yadda ka saka aka nemo ni, nima sai da na gano gidanku. Ka saka aka ɗauko ni, ka zageni kuma ka ci mini zarafi, to wallahi ban yafe maka ba taɓa mini nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka shaƙoni hannunka yana taɓa wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya taɓa shi ciki yake yi, to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na faɗa an saci kuɗin talakawa an je karatu ƙasar waje. Mu zuba mu gani daga maƙiyiyarka  RUMAISA MAHMUD ƘANƘARA ƊORAYI TUNGA ƘANWAR MAZA Kazo ka kasheni*

Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ƙirjinta ranar da aka kai masa ita.

Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta da ƙuruciya.

“Zan ƙure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen” ya maimaita wasiƙar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ƙular da shi irin wai ya taɓa mata nono, duk da bai riƙe cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.

Mama ta haɗawa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ƙarshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta taɓa nisa da ita na kwanaki ba, ga kuma rashin ji irin na ruman.

Uniform ɗin ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya ɗoɗar Abdallah ne ya goge mata su, sai ƙamshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye.

Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta, ƙazantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta buɗe idonta, dan ta ga wani mara mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?

A hankali ya sauke glass ɗin motar, suka yi ido huɗu da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma kasa magana gaba ɗaya.

Buɗe motar ya yi ya fito yana ƙare mata kallo.

“Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na ga saƙonki, abin da ki ka ce na taɓa ɗin ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba in gani ko akwai”.

“Wai kai ɗan iska ne?” Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar Takawa, saboda ya kaita bango.

Maganar ta dake shi, amma ya ce “Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke taƙama da su, sai na kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya”.

Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.

“Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka” tayi maganar har da dukan ƙirjinta.

Girgiza kai ya yi, ya buɗe motarsa ya shiga, ta durƙusa ta ɗebi taɓon wurin ta fara watsa wa motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da taɓon wurin ya tafi.

(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALAƘARSA DA MAITA DA HAJIYA JAMILA TA FAƊA? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ƊAN UWANSA. ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU KO KUWA? KAR

Cikin damuwa Huzaifa ya dube shi ya ce “To me ka gani da ba ka yarda da shi ɗin ba?”

Cikin sanyin jiki Yasir ya ce “Wallahi kawai, ni mutanen cikin motar ne ba su yi mini ba”

Tsaki Huzaifa ya yi ya ce “Ka fiye matsala wallahi, dan Allah kar ma muje gida ka yi wannan zancen ka ɗaga mata hankali” Yasir bai kuma cewa komai ba, suka tafi gida, sai dai shikaɗai ya san abin da yake ji a jikinsa.

Ruma kuwa da suka tafi, sai kallon hanya take, tana murmushi dan tun da take, ba ta taɓa tafiya mai nisa ba, kuma ta yi sa’a a wurin taga take, dan haka take ta leƙe tana murmushi. Sai dai tun shigarsu, Aliyu ya lura da Mutanen da suke zaune a  gaban su, tun da suka hau motar mutanen suke waya da wani yare, wayar taƙi ci taƙi cinyewa, gashi ba mai iya fahimtar abin da suke faɗa a wayar.

Ruma kuwa sai surutu take wa Aliyu, kamar an jefeta a ka, ta ce wannan ta ce wancan. Aliyu dai bai tanka mata ba, sai Adduoi yake yi yana cigaba da kallon mutanen da tsarguwa da wayar da suke ta yi.

Ruma ta ɗauko wayar nan ta wurin Yasir, ta din ga ɗaukar kanta a hoto, ga wayar duk a ragargaje amma sai ɗagawa take tana hoto, har da hoton hanya ɗauka take, ta hau yin videon cikin motar tana ɗaukar mutane.

Ko da suka bar gari suka shiga jeji, sai wannan mutane suka ce wa direba ya sauka daga kan kwalta, ya tafi ta gefen titi kan burji, ba tare da musu ba kuwa direban ya bi umarninsu, kuma aka rasa wanda zai yi magana a kan hakan kowa yayi shiru.

“Wai ya na ga ana bin gefen titi, ga kwalta ɗoɗar a lailaye?” Ruma ta yi maganar har sai da kowa ya waiwayo yana kallonta. Ɗaya daga cikin mutanen ya yi murmushi amma ba wanda ya kulata.

“Ke uban wa ki ka ji yayi magana, sai ke haziƙa mazaruƙs, kar na sake jin bakinki ko na make ki” Aliyu yayi mata maganar cikin kashedi. Tura baki ta yi ta kawar da kanta gefe. Sai dai ba aje ko ina ba, ruma ta fara cewa Aliyu ita fa wannan zaman motar ya isheta.

“Wallahi idan baki kiyayeni ba sai na zane miki jikinki, ni na yi dana sanin tahowa da ke, babu wanda ake jin bakinsa sai ke? Ki rufe mini baki na gaya miki”

Kamar zata yi kuka ta ce “To ni fa na gaji ne, kuma yunwa nake ji, su wannan mutanen na gaba, ba tun da muka taho suke waya ba suke surutunsu, babu wanda ya damesu sai ni zaka ce na ishi mutane, ni wallahi yunwa nake ji ulcer ta zata tashi”

Riƙe kunnenta Aliyu ya yi ya ce “Yi mini shiru, a gidan uban wa ki ke da ulcer?”

“Cikina ne ya fara ciwo, yunwa nake ji”

“Wallahi zan zaneki idan baki shiru ba” haka ruma tayi shiru tana ƙoƙarin goge hawaye.

Sai da suka zo wani ƙaramin ƙauye, mutanen nan suka ce a tsaya, nan ma direban ya bi umarninsu ya tsaya, kowa yana son yin magana amma yana tsoro.

Aliyu ne ya fara fusata ya ce “Direba ya na ga an tsaya? Mu da muke sauri?”

Direban ya ce “Dan Allah ku yi haƙuri, wani saƙo za su karɓa mu wuce, yanzun nan ba daɗewa zamu yi ba in sha Allah”

Aliyu ya ce “Amma ai ba a haka, sai a nemi alfarmar na mota ba a tsaya kawai ba, wannan shiga hakki ne ai”

Sai da Aliyu ya yi magana, sannan sauran mutanen cikin motar suma suka fara ƙorafi a kan abin da aka yi.

Yayin da mutanen suka yi shiru ba su kula kowa ba.

Sun kai mintuna sha biyar, sannan wasu mutane suka ratso cikin dajin  a babura, mutanen suka sauka, suka karɓo wata uwar jaka, sannan suka dawo motar. Ɗaya daga cikin su ya dubi ruma cikin gurɓatacciyar hausar sa ya ce “Ke ki ka ce ki na jin yunwa ko?” Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya bata wata baƙar leda, ta karɓa ta ce “Na gode” Aliyu ya bi ruma da kallo dan ya rasa me yakamata yayi mata, kawai ba ta san mutum ba ya bata abu ta karɓe.

Gasashshiyar kaza ce a ciki, da ruwan roba, ta waro ido ta ce “Laa yaya kaza ce”

Ya harareta ya ce “Mayya, tun da baki taɓa cin kaza ba, idan ki ka ci sai na miki dukan tsiya”

Ta ɓata fuska ta ce “To in mayar masa, in ce ka hanani ci?” Banza yayi mata, ganin bai kulata ba ya sanya ta saka hannu ta hau cin abarta.

Da ta ci ta ƙoshi ta ɗaure sauran, ta kwanta a jikin Aliyu ta hau bacci.

****

Lafiya Adam ya sauka a Abuja, ya sauka a hotel ɗin da zai zauna na kwanaki biyu, dan ba ya son a san da zuwansa, shi ya sanya ya sauka a hotel, sai dai gabansa ya tsananta faɗuwa ya rasa dalili, ya kira Ammi ya kai sau uku, amma ta ce masa komai lafiya babu wata matsala.

Da yamma ya shirya ya ce bari ya ɗan fita ya je wurin abokansa, ko ya ɗan rage damuwar da ya rasa meya haddasa masa ita.

Sai dai yana fita harabar hotel ɗin, ya ji kansa ya wani sara, yayi ƙoƙarin basarwa  ya fita, amma ya kasa ƙafarsa ta yi masa nauyi ya ji yana nema ya faɗi, a hankali ya juya ya koma ɗakin da ya sauka, ya nemi wuri ya kwanta, saboda yadda yanayin jikinsa ya sauya tamkar zai fita hayyacinsa.

***

Ruma na farkawa daga baccin da ta yi, ta cewa Aliyu kashi take ji, shi kuma ya ce sai dai ta riƙe kayanta sai sun sauka, don ko zata yi hauka ba zai saka a tsaya ba, ba zai bari ma ta yi kashi a daji ba.

Ta din ga matse ƙafa tana nema ta yi masa kuka, har sai da ta fara janyo hankalin mutanen da ke motar.

“Wai kai ba ka ga yarinya bace ne? A tsaya ta yi mana” cewar ɗaya daga cikin mutanen da Aliyu ya kasa yarda da su.

Aliyu ya ce “A’a ba zata yi ba, idan mun je in da zamu ta yi” ya bawa mutumin amsa yana tsuke fuska. Ai bayan batun kashi ta cigaba da kuka, ita fa zai zubo, kuma ta gaji da zaman motar nan. Kan Aliyu ya yi magana motarsu ta yi faci, a tsakiyar jeji.

Fasinjoji suka din ga tsaki suna mita, masu ruwa suka ɗaura alwala kasancewar azahar ta yi, suka yi salla.

Wanda ya bawa ruma kaza ya kalli Aliyu ya ce  “Abokina tun da an tsaya gyara motar, ka shiga da ita ta samu wuri ta biya buƙata mana”.

“Ɗan uwa ai na gaya maka ba abin da zata yi sai mun je, ƙyaleta ƙarya ma take ba wani kashi da zata yi”

Kowa yayi salla amma banda wannan mutanen, ana ta fafutukar sauya taya, tabbas da a gari motar nan ta lalace, da ba abin da zai hana Aliyu ya canza musu mota, saboda bai yadda da mutanen nan ba, shi ya san me ya gani, kuma yana tsoro yayi magana su cutar da su.

Aliyu yana salla, ruma ta tsaya tana ta ƙarewa dajin kallo tana ɗaukar hoto da akwalar wayarta kamar abin da ta fito yi kenan.

“Ɗan uwanmu ku ba kwa sallar ne?” Ruma tayi maganar tana zama ɗan nesa kaɗan da ɗaya daga cikin mutanen.

Ya kalleta ya ce “Sai mun je gida zamu yi”

“To wai Meyasa kuke ta sawa ana tsayawa a hanya ne? Duk ku ka ja muka daɗe fa”

Ya ce “Saƙo muka karɓa a wurin ‘yan uwanmu”

Ruma ta jinjina kai ta ce “Sune suka baku kaza ku bani na ci?”

Ya waiwaya ya kalli wanda ya bawa ruma kazar ya ce “Tun da ki ka cewa yayanki yunwa ki ke ji, yayi wa ‘yan uwanmu waya, ya ce su sayo kazar, dama zamu karɓi saƙo a wurinsu, shine ya karɓo miki ya baki”

Ta yi murmushi ta ce “Allah sarki, kuna da kirki, to ku baku da gida, ‘yan uwan na ku a daji suke ba gida ba?Na ga daga daji suka fito kuma babu gida a cikin daji ai”

“Eh, bamu da gida a daji muke rayuwarmu”.

Cikin mamaki ta ce “Kai sai ka ce wasu kuraye, ku wane yarene to?”

Ya haɗe rai ya ce “Ke kin isheni fa, bar nan gurin”

Ruma ta ce “Yi haƙuri, dama ko a gida haka ake cewa na fiye tambaya, na daina, ina son sanin abubuwan da ban sani bane”.

Bayan ta yi shiru, sai ta hau tattaɓa jakar hannunsa ta ce “Wai kai ba zaka ajiye kayan nan ka huta ba, ba ka jin nauyi”

Saurin janye jakar yayi yayi mata shiru.

“Na ji kamar wasu ƙarafa, kayan gwan-gwan ne a ciki? Su kuma kna zaka kai su”

A fusace ya ce “Ke tashi ki bar nan wurin kan na illata ki?” Yayi mata maganar cikin tsawa, ko girgiza ba ta yi ba, sai ma tsare shi da ta yi da ido, wata lamba ce a jikin jakar, wannan jaka dai ba za ace kaya ne a ciki ba, sai dai lambobin jikin jakar sun ɗau hankalinta sosai.

Aliyu ne ya figo hannunta yana zaginta.

“Yarinya ce, ka daina dukanta mana babu kyau yarinya ce ƙarama” yayi wa Aliyu maganar yana riƙe hannun Aliyu.

Aliyu ya rasa haɗin mutumin nan da rumaisa, da ya yi mata faɗa sai ya hau ce masa ya ƙyaleta yarinya ce, ko ina ruwansa oho.

Haka ya haƙura ya ƙyale ruma, tun da mama ta kira ya ce mata haryanzu basu isa ba, ya sanya mama shiga cikin damuwa, saboda ya ci ace sun je, amma ta ji suna hanya.

A haka aka gyara motar suka hau suka cigaba da tafiya. Ruma ta durƙusa ta taɓa wata jaka da kuma buhu da ke ƙarƙashin kujerar da take kai.

“Wai dan Allah kayan waye wannan da ba za a saka masa su a ƙasan kujerarsa ba sai ta mu, ni fa sun isheni na yi kawaicin na gaji, sun addaba mini”.

Mutumin nan dai ya waiwayo ya ce wa ruma “Yi haƙuri, mun kusa sauka ma, namu ne zamu ɗauke”.

“Wallahi ɗan uwanmu ba dan naka bane ba, sai an cire mini su, da na wannan mai jakar ne da ya hantareni sai ya kwashe kayansa ya mayar da su wurinsa, ɗazu daga tambaya ya yi mini tsawa”.

“To kiyi haƙuri” ɗayan ya waiwayo ya kalli ruma, ruma ta zaro masa ido kamar tana kallon yaro.

Aliyu dai ya sunkuyar da kai yana cigaba da addu’a, shi ba abin yayi wa ruma magana ba ko ya rufeta da duka ba.

Sun shiga katsina, a wani ƙaramin ƙauye suka tsaya zasu sauka, mai jakar nan ya kalli ruma ya ce “Ke sauko, zamu ɗauki bindigoginmu”.

Tsit kowa ya yi, ruma ta ce “Wace irin bindigogi kuma?”

“Zaki sauko ko sai bomb ɗin ciki ya tashi da ke?”

Tankaɗata Aliyu yayi suka sauka, aka ɗaga musu kujera, aka fara fito da jaka.

“Dan Allah da gaske bindiga ce a ciki?”

Yayi murmushi, ya zugewa ruma jakar, ƙananan bindigu ne, ƙirar pistol.

Ya ce “Waccan jakar kuma da kike tambaya meye a ciki ɗazu, bullet ne a ciki”

Ta ɗan waro ido ta ce “Kashe mutane ku ke yi kenan, tun da dai na ga ku ba ‘yan sanda bane kuma ba sojoji ba?”

Ya girgiza wa ruma kai ya ce “A’a ‘ya ta, aikin Allah muke yi ake biyanmu”

“Aikin Allah ai ba a biyan mutum, Allah ne zai biya mutum da lada”

Yayi murmushi ya ce “Ba zaki gane ba, Ubangiji Allah ya yi miki albarka ya rayaki, da ‘ya ta na raye da ta yi kamar ke”

“To ta na ina yanzu ‘yar ta ka?”

“An kasheta ita da babarta, Allah ya rayaki” ya kalli Aliyu ya ce “A lallaɓata dan Allah, sai wataran ‘ya ta” yayi maganar yana ɗagawa ruma hannu.

Wata narkekiyar mota ce ta yi parking, mai kyan gaske aka ɗora kayan bindigar a ciki, suka shiga motar aka ja suka tafi.

Ruma ta ɗauko wayarta ta fara dannawa.

Aikuwa Aliyu ya dinga zaginta, har da zagin da bai san iya shi ba, dan ruma ta kai shi maƙura yau, gaba ɗaya ruma ba ta da hankali ba ta san ciwon kanta ba, shi tun da suka hau motar, suka yi nisa ya gane bindigogi ne a buhun da ke ƙasan kujerarsa, kuma yana fuskantar yaren da suke yi kaɗan-kaɗan, ‘yan ta’adda ne mutanen, amma ruma sai hauka take zubawa da wauta saura ƙiris ya karɓi shegiyar wayar nan ya jefa ta ta window. Sai dai yana tsoron yin hakan dan ya ga mutumin nan ya zaƙe a kan ruma kar yayi masa wani abu idan ya taɓata.

Direban ya ce “Wallahi bawan Allah Yarinyar nan mai sa’a ce, dan ni na zaci ma da zasu sauka tasa ta zasu yi a gaba su tafi da ita, ko su kasheta surutunta yayi yawa, ba a yi wa wannan mutanen haka”

Aliyu ya ce “Eh kaima ai azzalumin ne, da ka ɗauko mu mota ɗaya da wannan mutanen”.

“Megida ba laifina bane ba fa, kullum akwai irinsu da suke shige da fice zuwa garuruwa, ba su fiye cutarwa ba sai in kun musu rawar kai, mu ma abincinmu da rayukanmu muke karewa”.

“Amma jami’an tsaro na garin nan, ga su a tasha, amma ake safarar makamai a tsakanin garuruwa suna gani?”

“Lallai ɗan samari zancen ka ke so, lamarin ƙasar nan ta mu ai sai dai Innalillahi wa Innalillahi raji’un, idan ka matsa sai ka kwana a ciki amma manyanmu sun san komai”

Aliyu ya girgiza kai ya ce “Allah ya kyauta”.

Sai bayan la’asar sannan suka sauka, Ruma ta sha mita, kamar Aliyu ya ari baki, tayi masa shiru ta ƙi kulashi.

Sai da mama ta kira ta ji sun sauka sannan hankalinta ya kwanta.

Gidan da suka je babban gida ne, mak ɗauke da part-part, galibi Ruma ta san su, dan suna zuwa gidansu dan haka ba ta ga wani abu na musamman a a wurinsu ba, sai dai yanayin garin yayi mata kyau.

A sashin Gwaggo suka sauka, Gwaggo Atine har da hawayen murna, ta rungume ruma tana yi musu maraba.

‘yar autar Gwaggo lawisa, sai kallon ruma take, da yake za su yi sa’anni da ruma, sai kallon ruma take yi.

Ruma kuwa jikinta ne duk ya mutu, saboda uwar tafiyar da suka yi, ba ta taɓa tafiya mai nisan ta yau ba.

Aliyu ya yi alwala, ya ce ita ma ta tashi ta yi salla.

A kan sallayar da ta yi salla, ta nemi wuri ta kwanta, nan da nan jikokin Gwaggo suka fara zuwa ganin ruma.

Ruma a ranta ta ce “Ji bala’i, kamar an ajiye musu buranya, sai kallona suke” ta dunƙule a cikin hijjabinta ta ɓoye fuskarta.

Gwaggo tamkar zata goya ruma, su Aliyu su kan zo, shi ma sai a shekara wani daga cikinsu bai je ba.

Nan da nan ta ɗorawa ruma.

“Auta taso ki zo ki yi wanka, zaki ji daɗin jikinki sosai”

Ruma kamar ta ce ba zata yi ba yamma ta yi, amma ta ga kar ta watsawa gwaggon ƙasa a ido, daga zuwanta, ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan zafin.

Bayan ta fito ta tarar da lafiyayyiyar alala ta sha manja.

Ruma haryanzu a ƙoshe take da kazar da ta ci, dan haka ta ci kaɗan ta ce ta ƙoshi.

Lawisa kuwa so take ta yi wa ruma magana, amma ruman sai wani basarwa take tana haɗe rai, gaba ɗaya jikinta a ciwo yake, saboda wannan wahalalliyar tafiyar da suka yi, ga wani ɓacin rai da take ji da ba ta san dalilinsa ba.

Ganin ruma ba zata kulata bane, ya sanya ta fara ƙoƙarin yin abin da zata burge ruman, sai ƙoƙarin shishshige mata take yi.

“Ba ki ci alalar da yawa ba, zaki sha fura?”

“Na ƙoshi” ruma ta bata amsa a taƙaice.

Lawisa ta yi murmushi ta ce “To rama fa”

“Baiwar Allah cikina ne a cike fa, na ƙoshi, ko haɗama ki ke so in yi?”

“A’a, ko in ɗauko miki fulo ki kwanta”.

Ruma ta ce “Eh, dama na gaji sosai”

Lawisa ta je ta ɗauko fulo, ta kawo wa ruma, ruma ta kwanta babu jimawa ta hau bacci.

***

Nema yake ya fita daga hayyacinsa, duk Addu’a da ta zo bakinsa yi yake yi, amma kansa kamar ana buga masa wani abu, ga wayarsa na ta ringing amma ba zai iya ɗagawa ba, ya lumshe idanunsa, ya jin yadda cikin naman jikinsa ke wani irin zafi, idanunsa kamar za su fito saboda ciwon kai, ya dafe kan yana karanta alƙur’ani a fili, a hankali wani mawuyacin bacci ya kwashe shi.

Rumaisa ya gani a kan wani dutse a zaune tana kuka. Hayaƙi na ta tashi a wurin, amma yana iya gane fuskarta.

*Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka* kamar yadda ta gaya masa a haɗuwarsu ta ƙarshe, haka ma a yanzu take sake maimaita masa, ya buɗe idonsa a hankali a cikin dodon kunnensa yake cigaba da jin sautin muryarta.

Ruma ma da bacci ya kwasheta, a razane ta yi wata ‘yar ƙaramar ƙara ta farka, tana haki kamar wadda ta sha gudu, a lokacin duhun magariba ya rufa! Gaba daya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya?.

Tamkar wadda aka tsamo da ga kwata haka ruma ta juya ta koma gida tana kuka, mutane a hanya wasu na tambayarta ko lafiya? wasu kuma suna mata dariya, yara sa’aninta kuma suna dariya ta kamo kifi soyayye, saboda yadda ta yi tsumu-tsumu da taɓo.

Takawa kuwa tafiya yayi yana jinjina taurin kai da tsagwaron tsageranci gami da rashin tsoro irin na Rumaisa.

Ya daɗe bai ga abin da ya bashi mamaki kamar rumaisa ba, amma babu mamaki kamar yadda ya sanya aka masa bincike an tabattar masa da a cikin maza bakwai ta tashi, har halinta na rashin ji sai da aka gaya masa, tare da makarantar da take zuwa, a nan ya tabattar da muryarta da yake ji tabbas ta ta ce, tun da gidan gonarsu a unguwar su yake. Amma ya aka yi ta san gidansu har ta bishi can.

Ya tsaya da mamakin ne a lokacin da ya tuna ɓarawo da ta laƙanta masa, a take ransa ya ɓaci, ya sake ƙudurar aniyar sai ya ladabtar da ruma ta hanyar da ta dace.

Idan ya tuna sharrin da ta sake liƙa masa, wai ya taɓa mata nono, sai ya rasa me ma zai yi, mamaki ko dariya?.

Mama ce ta kalli ruma ta ce “Meye haka, meya same ki?”

Cikin kuka ruma ta ce “Wani bugagge ne ya wanke ni da ruwan kwata, wallahi ba zan yafe masa Allah ya tattaro masifar duniya da ta gabasa da yamma kudu da arewa….

“Rufe mini baki? Ban hana ki yi wa mutum irin wannan addu’a ba? Wataƙila bai sani ba”

“Mama kalli jikina fa, ya na sane yayi mini, wallahi ba zan yafe ba, kuma in Allah ya yarda sai an sace motar, sai na yi masa tijarar da bai taɓa ganinta ba idan na kuma haɗuwa da shi, kuma sai an sace motar na ga ta tsiya”

“Wane mahaukacin ne yayi miki haka? Makaho ne shi?” Usman ya faɗa yana ƙarewa uniform ɗin ruma kallo, da suka jagalgale da taɓo.

Mama ta ce “A’a, kar ka zigata dan Allah, wuce ki je ji cire kayan, tsautsayi ne, kuma Allah yana tare da masu haƙuri”

Usman cikin takaici ya ce “Haba mama, kalli jikinta fa wallahi wannan da iskanci yayi mata, waye shi a ina yake? Kin gane shi? A nan unguwar yake?” Ya jero mata tambayoyin.

Ɗan shiru tayi ta tuna furucin takawa, na zai kama yayyenta ya rufe su, ya saka a rushe musu gida. Nan da nan ta ce ni ban san shi ba, zuwa ya yi wucewa, yayi mini haka, to wallahi Allah ya isa na”

Huzaifa ya ce “Ƙaraso na tayaki ki wanke jikinki” ta ƙarasa, Huzaifa ya ɗebo ruwa a rijiya ya hau sheƙawa ruma, sai da ta kusa shiɗewa, mama ta din ga yi masa faɗa, ƙarshe dai ruma ba ta je makarantar ba ranar, ba ta yi jarrabawar ba, wunin ranar kuka ta din ga yi, tare da janyo wa takawa jafa’i iri-iri.

A daren da yakamata washegari su ruma su tafi katsina, ta fara ciwon kai da ciwon ciki, har zuwa wayewar gari, dan haka mama ta ce sai dai a ɗaga tafiyar zuwa kwanaki biyu idan ruma ta warke.

Har zuwa azahar ruma tana kwance tana fama da ciwon ciki, Yasir ya ce “Shegen ciye-ciyenki na masifa ne yake janyo miki ciwon ciki, kece ci wannan ci wancan a islamiyya kullum cikin tauna kamar tunkiya” ruma ba ta yasir take ba, ta kanta take yi dan haka bata kula shi ba. Aka kai ruma chemist aka sayo mata magunguna.

Mama aka yi wa waya daga cikin gari,  babur ya buge Hauwwaliya ta karye a ƙafa, dan haka babu shiri mama ta shirya cikin tashin hankali ta tafi.

Ruma sai kuka take, ga karayar hauwwaliya, ga zafin ciwo kuma wai mama ba zata tafi ta barta ba. Mama ba ta saurareta ba, ta shirya ta yi ficewarta.

Burgima ta din ga yi a tsakar falon mama tana kuka, kamar wata yarinyar goye, sai gunji take “Wayyo cikina”

“Ke!” Ta ji tsawar mai sunan Baba daga ƙofar ɗakin. Take ta nutsu ta yi shiru.

“Mara hankalin ina ce ke? Dan baki da lafiya sai ki ishi mutane, ba zaki yi addu’a ba?”

Shiru ta yi tana kuka ƙasa-ƙasa dan ita kaɗai ta san abin da take ji.

Aka jima kuma sai amai, ga jikinta ya ɗau zafi sosai. In da ta yi aman a nan ta zauna ta kasa tashi. Sai Aliyu ne ya wanke mata baki ya ɗagata ya mayar da ita ɗaki, ya wanke wurin.

Har bayan azahar mama ba ta dawo ba, ga ruma jiki yaƙi daɗi, Aliyu ya ce zai samo abin hawa ya kaita asibiti. Usman ya ce a fara ba ta abinci ta ci tukuna.

Cikin ruma ya sake ƙullewa, har cikin ƙafafuwan ta, ta tashi da ƙyar, ta tafi toilet yin fitsari.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, na shiga uku dan Allah ku taimake ni ” suka jiyo ihun ruma a toilet.

Mai sunan Baba ne ya tafi da gudu ya buɗe banɗakin a razane, dan duba meya sameta, suma sauran suka rufa masa baya, amma suka tsaya a waje saboda ya na bakin ƙofar.

Ruma ce a tsaye, ta gama fitsarin ta miƙe tsaye tana kallon yadda fitsarin na ta ya gauraya da jini, duk da ba wani mai yawa bane ba.

“Meye haka?”

Cikin rawar jiki ta nuna masa ta ce “Mai sunan baba ka ga, fitsarin jini nake, mutuwa zan yi” tayi maganar idonta na cika da hawaye.

“Yaushe ki ka fara irin wannan fitsarin?”

“Yanzu kawai na gani” tayi maganar tana dafa bango, saboda jirin da take ji.

Ya waiwayo ya kalli Yasir ya ce “Ɗauko mata zanin mama” Yasir shima jiki na rawa ya tafi ɗakin mama, dan hankalinsa ya tashi sosai.

Ya sake duban Usman ya ce “Ɗan ɗora mata ruwa ya yi zafi, ta yi wanka” cikin damuwa Usman ya ce “To meya sameta?”

Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce “May be is her fisrt period”

A razane Aliyu ya ce “What! Rumaisan? How old is she? Yarinya ce fa sosai”

Usman ya ce “Ikon Allah”

Mai sunan Baba ya miƙa mata zani ya ce ta ɗaura ta fito. Ta ɗaura ta fito ya bata kujera ta zauna, Usman ya zuba ruwa ya wanke banɗakin. Ruma kuwa jikinta sai rawa yake yi tana tunanin ƙarshenta ne ya zo.

Usman ne ya fita sayo pad, sai dai babu wanda ya san ya ake amfani da ita.

Gaba ɗayansu suka diririce, musamman ganin yadda ruma ke kuka, Huzaifa kamar ya tayata kukan, ita sam ba ta san menene ya sameta ba, mai sunan Baba ne kawai yake ta wani basarwa.

Aka kai mata ruwa tayi wanka, usman ya tattare kayan da ta cire, ya zuba a bokiti ya zuba musu ruwa.

Gaba ɗaya mai sunan Baba ya rasa ta ina ma zai fara, gaba ɗaya baya manta lokacin da aka haifi ruma, kamar jiya aka haifeta haka yake gani, wai ita ce yau period ya zo, yarinyar da ko ciwon kanta ba ta sani ba, ban da tarin rashin hankali da rashin kunya ba abin da ta sani, duk wani abu da ya shafi rayuwa ba saninsa ta yi ba.

Sai da yayi browsing, sannan ya ga yadda ake amfani da pad, ya nuna mata, har zuwa yadda ake discarding ɗin ta, ta karɓa ta saka, sannan ta saka kaya.

Ya kalli su Usman ya ce “Su basu wuri, za su yi magana” ba musu duk suka fita.

Ya kalli ruma ya ce “Kalleni nan” ta ɗaga kai ta kalleshi.

“Ko akwai wani abu da ya haɗaki da wani?”

Ta ce “Eh” gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa ya ce “Menene?kuma waye shi?”

“Wani mutumi ne, ruwan kwata ya watsa mini da motarsa jiya da safe”.

“Ba wannan nake nufi ba, ko akwai wani wanda yayi miki abin da bai dace ba, ko wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki?”

Tunowa ta yi da takawa, yadda ya cakumota, amma tayaya za ta fara yi wa mai sunan Baba wannan bayanin, ai kan a kai ga takawa, ita zai fara tattakawa, a karon farko da ta yi masa ƙarya ta ce “Babu kowa”

“To idan ma akwai ki ka ƙi faɗa, idan na gano sai na yankaki na zuba a rijiya, kuma wannan yanayi da ki ka shiga, duk wanda ki ka bari ya taɓaki ko yayi miki wasan banza, ciki zaki yi kuma mutuwa zaki yi” gaban ruma ne yayi mummunan faɗuwa, meye makomar taɓata da takawa yayi? Ta yi ciki kenan?.

Haka suka shimfiɗa tabarma a tsakar gida, suka kewaye ruma, yau har masu zuwa ball ba wanda ya fita, suna ta jera mata sannu, ban da masu fifita da masu ba ta abinci.

A haka mama ta dawo ta tarar da su, cikin mamaki ta dube su ta ce  “Wai har yanzu jikin ne?”

Usman ya ce “Tun da ki ka fita a haka take”

Mama ta ce “To Allah ya ƙara afuwa, wallahi ina can muna fama, da ƙyar aka samu aka ɗora yarinyar nan, tana jin jiki, sannu ‘yar auta” ruma dai ba ta amsawa mama ba, ta sake lafewa a cinyar Aliyu.

Mai sunan Baba kuma yana gefe kamar mai gadi, yana kallonsu.

Mama ta kalli kayan ruma da suke shanye, gidan ko ina tsaf, amma ko girkin dare ba su ɗora ba.

Mama ta ce “Yasir, tashi ka ɗora mana ko taliya ce a ci da daddare” gaba ɗaya basu da walwala kamar wadda aka ce musu ruman mutuwa ta yi.

Cikin damuwa mama ta ce “Wai me yake faruwa ne duk na ga kun yi jugum-jugum? Duk dan ba ta da lafiya ne ku ka zo ku ka tare a wuri ɗaya haka, ba an sayo mata magunguna ba?”

Duk shiru suka yi, suna sunkuyar da kai aka rasa mai iya yi wa mama bayani.

“Mama fitsarin jini fa nake yi ” Ruma ta yi maganar daga kwance.

“Wane irin fitsarin jini kuma? A garin yaya?” Mama ta yi maganar a tsorace.

Usman ya ɗan yi gyaran murya ya ce “Wato ainihin, muna tunanin, wato ko.. abin nan na mata da suke duk wata, wato haila shi ta fara” waro ido waje mama ta yi ta ce “Ban gane ba”

Mai sunan Baba ne ya karɓa yayi wa mama cikakken bayanin abin da yake faruwa.

Mama ta yi salati tare da tafa hannu ta ce “Ruma haila, iko sai Allah girma ya riga hankali zuwa, a yanayin jikinta ban taɓa kawo zuwan wannan abun yanzun ba, ikon Allah”

“Mama wai menene ya sameni?”

“Girma ki ka yi” mama ta bata amsa.

Mama ta sake kallon igiya da kayanta a kan igiya, ta jinjina kai ta ce “Lallai ƙanwar maza, yanzu har ɗan kamfan ma ku kuka wanke mata? Iko sai Allah to Allah ya shiga lamarin, amma akwai badaƙala”.

“Mama wai mutuwa zan yi?”

“Ba mutuwa zaki yi ba, abin da yake hana ‘yan makarantar ku salla shi ne ya zo kanki”. A gaban su Yasir mama ta zauna tana yi mata bayanin komai, sai a yanzu ta gane wasu daga cikin karatun da aka yi musu a Islamiyya in da suka dosa.

Gaba ɗaya jikin ruma yayi sanyi, babu babban abin da ya tsorata ruma, sai cewa da mama ta yi ita ma yanzu za a din ga rubuta mata zunubi idan ta yi saɓo.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, na shiga uku, dan Allah kar a rubuta mini zunubi”.

Aliyu da ta kwanta a kan cinyarsa ya ce “Wallahi sai an rubuta miki, gara tun wuri ki nutsu ki shiga hankalinki”

“Astagfirullah, dan Allah mama kar a rubuta mini zunubi, ba na jin magana, dan Allah mama kar a din ga rubuta mini zunubi bana son na mutu yanzu. Wayyo Allahna”

Mama ta ce “Iko sai Allah, na ga yadda za ayi wannan lamari da wannan yarinyar mara kan gado”.

Har zuwa washegari aka samu zazzaɓi ya sauka, amma jikinta babu ƙwari, mama da kanta ta kaita banɗaki za ta yi mata wanka, sai dai pad ɗin jikinta ba ta ɓaci ba, mama tana yi mata wanka ruma tana ɓoye ƙirjinta.

Mama kawai ta yi dariya ta cigaba da silleta.

Da ta fito da ita kuwa, tuni sun haɗa mata tea, Yasir ya ɗauko mata kayan sawa, har da pad ɗin da zata saka.

Mama kawai girgiza kai ta yi, gaba ɗaya sun wani nutsu sun damu, duk saboda ƙanwarsu.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce “Ni ba zan saka wannan abar ba, damuna take yi?”

Mama ta ce “A haka zaki zauna?”

Ruma ta ɗaga kai alamar eh.

“Aikuwa kya ɓata jikinki, a haka jininki ya ƙare, ni babu ruwana” mama kan ta mazewa take yi, amma lamarin ya zo mata a bazata, ba ta taɓa kawo wannan abu nan kusa a kan ruma ba.

Da ƙyar ruma ta yadda ta saka pad ɗin nan, duk nasihar da mama tayi mata, tare da bayani, lokacin salla na yi ta ɗau buta ta ce ita alwala za ta yi.

“Wai ke wace irin yarinya ce ne haka? Ba na yi miki bayanin babu salla, babu azumi, ga duk wadda take haila ba”.

“To ni mama da wanne zan ji, kin ce mini za a din ga rubuta mini zunubi,. Yanzu kuma kin ce ba zan salla ba, in shiga wuta kenan?”

“Wai ke Meyasa duk bayanin da za ayi miki, ba zaki tsaya ki fuskanta ba sai dai ki yi ta wauta, Allah ne ya ɗauke miki, sai kin yi tsarki zaki yi salla” Aliyu yayi Maganar a fusace dan ya fara gajiya da halin ruman, ana mata bayani tana bauɗewa.

Tun ranar da ya ɗan zubo ɗin nan, bai sake zubowa ba, ruma ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, ga pad ta isheta gaba ɗaya abin duniya ya isheta.

Tun daga kwana ɗayan nan ya ɗauke, mama da kanta ta kaita banɗaki ta koya mata yadda ake wanka, babu babban abin da yake cigaba da ɗagawa ruma hankali, cewa da mama ta yi, ita ma za a fara rubuta mata zunubi.

Ta tattara laifin kacokan ta ɗora shi a kan takawa, wanda a dalilinsa duk haka ta sameta, dan daga watsa mata taɓo ya sa ta fara rashin lafiya, wannan abun ya zo mata.

Mama ta ce a bar tafiyar su katsina, sai bayan ruma ta gama warwarewa zuwa wani satin.

***

Takawa kuwa har zuwa yanzu, bai daina jin muryar ruma ta na zuwar masa ba, abin har mamaki yake bashi. Wasu lokutan a zahiri yake jin muryar tana yi masa gizo, gashi tun daga ranar yau kwanaki huɗu kenan, bai sake arba da wani abu da ya shafe ta ba.

Haryanzu zuciyarsa ta kasa nutsuwa da cewar ruma mutum ce, duk da sidi ya tabbatar masa da binciken da ya yi a kan ta da makarantar da take zuwa, wanda makarantar yayi niyyar zuwa, amma suka haɗu a hanya.

Tunawar da ya yi cewa yana da tafiya Abuja jibi zai je wata ganawa ta musamman da wasu lawyoyi, tuna hakan ya sanya shi dawowa nutuswarsa, ya bar tunanin ruma ya tashi ya fice.

Gidansu ya tafi, ya je ya samu Ammi dan sanar mata da batun tafiyar sa. Cikin damuwa Ammi ta ce “Ina fatan ba a kan mutanen ne zaka yi tafiyar ba, ka je ka cigaba da bin diddiginsu su illataka ba?”

Takawa ya ce “A’a Ammi, tattaunawa ce da wasu lauyoyi, kwanaki uku kawai zan yi na dawo”

“To Allah ya kaimu, ka kula sosai takawa, ka riƙe azkar sannan ka sanya Allah a ranka, kar saboda kana da matsala da wani ka sako shi a gaba da niyyar fansa, ka saka Allah a cikin lamuranka”

“In sha Allah ammi”

“Allah Ubangiji ya tsare, zaka ci Abincin dare a nan ne, ko kuma gida zaka tafi?”

“Ina da ayyuka a gida Ammi, ku ci abincinku kawai”.

“To Shikenan, Allah ya tsare”

Ya amsa da Amin, ya tashi ya fita.

Yana daf da kaiwa in da motarsa take, motar Mummy ta yi parking. Ta buɗe ƙofar motar ta fito ta nufi Adam tana wani irin murmushi.

“Manya gatan wasa, a gidan ka wuni ashe, kwana biyu ba ka shigowa mu gaisa”

“Na yi busy ne” ya bata amsa a taƙaice.

“Ashe Abuja za ka tafi, to Allah ya tsare”

Ɗan turus ya yi yana tunani, ya aka yi ta sani? Amma kasancewar ba ya son yin doguwar magana, mussaman da ita, ya sanya bai tsaya bin diddiginta ba, ya buɗe motarsa ya shiga.

***

Sarai ruma ta warke, mama ta sake haɗa mata kayanta, sai dai dare ya raba, ruma ta na cikin net ɗin ta tana ta bacci, mama kuma ta zubawa jakar da ta haɗawa ruma kayanta, haka nan ta ji ba ta son tafiyar da ruma za ta yi, kuma ba ta ji za ta iya hana tafiyar ba, ba ta taɓa rabuwa da ruma na lokaci mai tsawo ba sai wannan karon, gaba ɗaya jikin mama a sanyaye yake, ba ta da wani kuzari, zuciyarta na raya mata ko ta hana tafiyar da ruma, amma daga ƙasan zuciyarta ba ta ji ta yarda da wannan shawarar ba.

Tun asuba ruma ta fesa wanka, sai murna take ba ta taɓa tafiya mai nisa da wayonta ba, mussaman barin Kano, mama dai jiki a sanyaye take taya ruma shiryawa, tana yi tana mata nasiha, a kan ta nutsu har su je su dawo, ban da gantali da neman magana.

Ƙarfe goma na safe, suka kammala shiryawa, Aliyu ya ɗau jakar kayan, suka tafi, ruma sai ɗagawa mama hannu take tana murmushi, yayin da mama ko murmushin ta kasa, ruma ta ɗauko wayarta ta wurin Yasir, ta saka a jakarta.

Gaba ɗaya su kansu sauran yayyen na ta, jikinsu a sanyaye yake, kamar su ce a fasa tafiyar da ita, daga ƙarshe da ta gallabe su, suka ce Allah ya raka taki gona.

Ɓangaren takawa ma, yau ta kasance ranar da zai tafi Abuja, ya biya gida ya yi wa Ammi sallama, sannan ya ɗauki mai kaishi airport, ya dawo da motar. Sai dai tun a daren jiya yake jin ba ya son tafiyar, duk da ba yau ya fara tafiye-tafiye ba, amma yana jin sa wani iri, kamar akwai wani abu mai muhimmanci da zai yi nesa da shi, yana tsaye yana gyara agogon hannunsa, Ammi sai kallonsa take yi.

Ya kalleta ya ce “Ammi, ya dai na ga kina ta kallona?”

“Haka kawai bana son ka tafi ne, ji na yi kamar na ce ka fasa”.

Murmushi ya yi ya ce “Ammi kenan, sai ka ce zan bar gari, saudiyya fa sai da ns kwana ashirin da takwas, kwanaki uku fa zan yi kacal na dawo, ki yi mini addu’a, idan su Nusaiba sun dawo daga makaranta, ace musu na tafi”

Ammi ta jinjina kai ta ce “Allah ya tsare” ya ɗau jakarsa ya fice.

Huzaifa da Yasir, sai da suka raka su Aliyu tasha, suka hau mota, Ruma sai ɗaga musu hannu take, ta na yi musu gwalo, wai ba za a tafi da su ba.

Tun da suka baro tashar suka nufo gida, jikin Yasir yake a sanyaye, Huzaifa na ta magana, amma ya kasa amsa masa.

“Wai lafiya na ji ka yi shiru?”

“Huzaifa, ji na yi ban yarda da motar nan da su ruma suka hau ba”

Ya kalli Yasir cikin mamaki ya ce “Saboda me?”

“Mutanen da suke cikin motar ne ba su yi mini ba sam, ni duk wani iri nake ji a jikina!!!

Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Aliyu ya ce “Magana ake miki, ihun me ki ke yi wa mutane?”

Ta ɗan ɗago ta kalleshi, idanunta sun yi ja saboda gajiyar tafiya ga bacci da bai isheta ba ga kuma razana da ta yi.

“Mafarki na yi na tsorata”

“Kuma shine ba zaki yi addu’a ba,waye ma ya ce ki kwanta ki yi bacci da la’asar ɗin nan?”

Gwaggo ta ce “Daina yi mata faɗa, wannan ba laifin kowa bane laifin babarku ne, bana tunanin ta na nemawa yarinyar nan maganin tsari, wataƙila aljanu ne ko kuma mayu suka tsorata ta, bana raba ɗaya biyu suke bibiyarta”

Ruma ta waro ido ta ce “Mayu kuma, ni fa wani mutum nake gani, ki daina tsorata ni”

“Ahaf sai kuma ki yi, ko dai maye ne, ko kuma aljani shi ya sa ki ke ganinsa, kurwarki ya ke son lashews” shiru ruma ta yi tana tunani a kan mafarkin da ta yi.

“Aikuwa sai dai ya ci kansa, ba dai ni ba”

“Tashi kiyi sallar magariba, a samo mini gaushi, na turara miki tsakin kuka da tazargade haɗi da turaren mayu, koma menene zai barki, ai kaf zuriyarmu kurwarmu tafi ƙarfin maye, aljan kuwa sai dai yayi ya barmu”

Aliyu ya girgiza kai mutanen karkara sun yarda da camfi, kuma ba ka isa ka sauya musu ra’ayinsu ba.

Takawa kuwa a hankali ya gama watstsakewa a kan gadon ba tare da ya motsa ba, a hankali ya furta “Wai me na yi miki ne haka ki ka sakani a gaba, wace irin jaraba ce wannan duk in da na motsa yarinya ɗaya nake gani, wannan idan har ba aljana ba wataƙila tana da wani mugun nufi a kaina, Allah ya shiga tsakanina da ke”.

Rurin da wayarsa ke yi ne, ya sanya ya miƙa hannu a hankali ya janyo wayarsa ya duba, magariba ta riga ta yi, ya tarar da missed call rututu, wanda na Ammi duk ya fi yawa sai na Jabir.

Ammi ya fara kira, bugu ɗaya ta ɗaga cikin damuwa ta ce “Ina ka shiga ka ajiye wayarka nake ta nemanka ba ka ɗagawa?”

Ya ɗan gyara muryarsa ya ce “Ammi na ajiye duka wayoyin ne na fita, shi ya sa”.

“Amma bai kamata ka ajiye wayoyi ka fita ba, ka saka hankalina ya ɗaga sosai, amma ya na ji muryarka a haka, ba ka da lafiya ne?”

Yayi Murmushin ƙarfin hali ya ce “Haba Ammi, lafiyata ƙalau mura ce ta kamani, da na motsa sai ki ce bani da lafiya?”

“To ai dole sai ina yi ina bin diddigi, tun da ba cikakkiyar lafiya gareka ba, Ubangiji Allah ya tsare”

“Amin Ammi, na gode” ya katse wayarz ya tashi a hankali, ya ji jikin da sauƙi yanzu ba kamar ɗazu ba, ya lallaɓa ya shiga banɗaki yayi alwala, ya dawo ya yi salla.

***

Har zuwa dare, ruma ta ƙi sakin jikinta, kamar ba ita ce mai shegen surutun nan ba ta bi ta takure a wuri ɗaya kamar mara kuzari, gaba ɗaya ji take jikinta babu ƙwari. Yaya Aliyu ne suke ta hira da Gwaggo, da wasu daga cikin samarin gidan da suka shigo, duk yadda suka so su yi wa ruma wasa ta kulasu taƙi, ta koma gefe ta takure ta sha kunu.

Cikin damuwa Gwaggo ta ce “Rumaisatuna, wai menene gaba ɗaya kin ƙi sakin jikinki sai ka ce wata baƙuwa, me yake faruwa ne?”

Sheshsheƙa ruma ta fara sheshsheƙar kuka.

Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanta.

“Menene, me ki ke so?” Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Aliyu ya ce “Ba magana ake miki ba?”

“Gida” ta faɗa tana rushewa da kuka.

“To dan ubanki nan a titi kike ba a gida ba?” Aliyu yayi Maganar a hasale dan daga tahowarsu zuwa yanzu, ruma ta kai shi bango.

“Ni mama nake son gani, ka kira mini ita a waya”. Gwaggo ta ce “To shikenan, yi shiru a kira miki ita. Ka ga illolin rashin zumunci ko? Yanzu da ana zuwa da ita, yaushe zata yi kuka dan tana cikinmu, ai duk abu ɗaya ne, amma kalli yanzu kallon baƙi take yi mana, yi maza ka kira mata ita ko ta daina kukan”.

Takaici ya rufe Aliyu, kamar ya tashi ya naɗawa ruma duka, sai iskanci take kamar wadda aka kawo yaye, ya kira mama a wayarsa, ya jefawa ruma jikinta.

Mama na ɗaga wayar ruma ta saka kuka, cikin kiɗima mama ta ce “Lafiya kuwa ruma, menene?”

“Mama gida, ni ba zan iya bacci ba”

Mama ta ce “Haba ruma, ai sai ki ɗaga mini hankali, ba kun sauka lafiya ba ko wani abun aka yi miki?”

“Ba ayi mini komai ba, ni kawai gida a kusa da ke zan kwana, kuma ina son in ga su Yasir da Abdallah da yaya usy”.

“Ke dai ki na da shirme, to da aure aka yi miki fa, dangin mahaifinku ne fa nan ma gida ne ruma, duk abin da ki ke so za su yi miki, dan Allah ki daina ɗaga musu hankali”

“To ni gaskiya ki ce a dawo da ni gida gobe, ni so nake na ganki dan Allah”.

Mama ta ce “Ke ki mayar da hankalin ki, bana son sakarci fa, meye haka ne ruma, kawai daga zuwa baƙunta ki tayar musu da hankali, ko sai na haɗaki da babana?”

Da sauri ruma ta ce “A’a”.

“To ki nutsu ki daina yi musu kuka”

Ruma tana share hawaye, wasu na gangarowa ta ce “To, na daina”.

“Yauwwa, sannan ki yi fitsari kan ki kwanta, kar ki yi musu fitsarin kwance kin san dai kashedin da na yi miki ko?”

“Eh”

“To ki nutsu, sai da safe ki gaida gwaggon”

Usman ya karɓi wayar a hannun mama ya ce “Ke ruma, maman nono za ta baki da zaki din ga kuka ke mama, to idan ma shayar da ke take yau an yayeki”

Cikin shagwaɓa ta ce “Yaya ussy”.

Ya amsa da”Na’am ƙanwar maza”.

“Yaya usy ina son in ganka”.

“To idan kin gannin lada za a baki? Zan gayawa Ali, idan kin samu miji a nan mun bar musu ke, su aurar da ke”.

Aliyu ya fizge wayarsa ya ce “Ba katin banza ne da ni ba, kar Allah ya sa ki daina kukan, dama akwai karnuka da suke yawo a garin da daddare, idan baki nutsu ba, a ƙofar gida zaki kwana”.

Gwaggo ce kawai ta din ga rarrashin ruma, ta gyara mata kan gadonta na ƙarfe ta kwanta.

Tsananin gajiyar mota, da baƙunta ya sanya bacci kwashe ruma.

Ɓangaren mama ma, hakan take, kewar ruma take sosai, tun yamma su Huzaifa suka fuskanci hakan suke tsokanar mama suna mata dariya, wai yau an ɗauke mama ‘yar gudaliyar ifrituwarta, duk ta damu.

Mama ta din ga basarwa, irin ko a jikinta ɗin nan, amma tun da ta ji kukan ruma hankalinta ya ƙara tashi, cikin dare kuwa kasa bacci tayi, sai kallon wurin shimfiɗar ruma take yi. Sai yanzu take jin ina ma ba ta bayar da ruma an tafi da ita ba, dan gaba ɗaya hankalinta ya ƙi kwanciya.

***

Samha ce zaune a wani katafaren office, tare da Khalifa wakili, sai juyi yake a kan kujera yana kallonta yana mata murmushi, ita kuwa ta yi tsuru-tsuru kamar ɓera ya kwan a gadon kyanwa.

“Ki kwantar da hankalinki mana, babu wani abun damuwa a ciki fa”

“Khalifa, dan Allah kamar yadda muka yi yarjejeniya, tare da yin alƙawari a fari, dan Allah kar ka cutar da Adam, ni yanzu haka ma fa a tsorace nake”

Yayi wata makirar dariya ya ce “Lallai kin damu da shi da yawa, kar ki ji komai fa, kin fara naki ɓangaren, saura ɗaya ɓangaren suma za su yi nasu role ɗin “

“Amma haryanzu ba ka gaya mini su waye ɗaya ɓangaren ba, kuma aikin me zasu yi ba su, bayan da fari ce mini kai deal ɗin ni da kaine kawai”.

“Saken da ki ka yi na rashin ba da amsa da wuri ya sanya third party joining deal ɗin, kuma na ga za su taimaka sosai, shi ya sa na haɗaku ku duka a tafiyar, amma ki kwantar da hankalinki ba wata matsala”

Ta yi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan, ni zan wuce sai ka ji ni”.

Ya ce “To a sauka lafiya, zamu yi magana” bayan fitar Samha Khalifa yayi wata uwar dariya ya ce “Yaro man kaza, zaki gane baki da wayo”

Ɓangaren samha ma bayan fitarta jinjina kai ta yi ta ce “Yaro bai san wuta ba sai ya taka, da na yi achieving abin da nake so, zan nuna maka wacece mace, zaka gane ba ka da wayo, kuma zan gano wanda ka sako a cikin sabgar nan bayan ni, zan baka mamaki”.

****

Ko da garin Allah ya waye ma, aka yi alwala aka yi salla, ruma ta gaida wanda ta ga zata iya gaisarwa, ta koma ta yi shiru abun ta.

Lawisa ta dubi ruma ta ce “Sannu, kina buƙatar wani abun ne?”

Ruma a ranta ta ce “Wannan yarinyar kin isheni wlh” a zahiri kuwa ruma ta shareta, dan ita ji take kamar a kan wuta take, ba ta son zaman gidan nan.

Aka yi abin karin kumallo, kunun tsamiya da wainar gero, ga kunun na daka ne, sai ƙamshi yake, sai dai tun da Aliyu ya ga an kawo kunu, kuma kunun babu suga yake kallon ruma ya ga, wani action za ta yi, za ta sha ne ta yi kara ko halin za ta nuna.

Ta kalli kofin kunun, ta kalli Aliyu, amma ya kawar da kansa, ya na shan nasa.

Lawalli da yake yayan lawisa ya ce “Rumaisa ki sha kunun mana”

“Bana shan kunu” ta faɗa a raunace.

Ya ce “Au mutan birni ba cimarku ba ce ba, Gwaggo dafa mata shayi, bari na sayo madara a shago, a sayo miki burodi”

Dariya ruma ta yi ta ce “Meye kuma burodi, buredi ake cewa ai” karo na farko da tun da ta zo ta yi dariya, gaba ɗaya hausar ta su wani iri take jin ta.

Shima ya yi dariyar ya ce “To shikenan buredi bakanuwa”.

Ta ce “Banda buredi, shayin kawai zan ci wainar geron”

Aliyu ya galla mata harara, ta basar kamar ba ya ganshi ba.

Haka kuwa aka yi, sai da aka samo shayi sannan ruma ta karya.

Gwaggo ta ce lawisa ta zagaya da ruma sashen matan yayyenta su gaisa, su ga ruma.

Jiki na rawa lawisa ta amsa, ta jagoranci ruma zuwa ɓangarorin gidan.

Ruma ta sha mamakin waɗanda ta din ga gani a matsayin ma’aurata, duk yara da su.

Sai dai Mutanen gidan akwai su da kirki, hannu bibbiyu suka din ga karɓar ruma, suna yi mata barka da zuwa.

A hanyar komawarsu sashen gwaggo ruma ta ce wa lawisa “Wai duk wannan sirikan gwaggo ne?”

Cikin jin daɗin ruma ta kulata lawisa ta ce “Eh” ruma ta jinjina kai.

Bayan sun koma sashin gwaggo, lawisa ta ɗau niƙa za ta kai, ruma ta ce za ta bita. Suna tafe a hankali ruma ta fara sakin jiki da lawisa, ta din ga kallon garin, yayi kyau sosai, ‘yan garin ma’abota noma ne.

Duk wanda ya ga Lawisa da ruma sai ya tambaye ta wacece ruma, ta ce musu ‘yar uwatta ce. Abin yayi ta bawa ruma mamaki, ita a gida unguwarsu wa ma ya damu da wani, da za a din ga tambayarka waye wannan.

Ko da suka dawo gida ma, ruma a hankali take sakin jiki da lawisa, suka fara aiki tare suna ɗan taɓa hira.

Wajen sha ɗaya na safe, lawalli ya ɗauki Aliyu a babur ɗin sa suka tafi can wani ƙauye, in da a nan wasu daga cikin gonakin nasu suke, wurin gidan wani kawunsu da suke kira da baba Habu.

Ruma ta zazzage kayan da ta zo da su tana sake ninkewa, bayan ta gama ta ɗauko wayar nan ta ta, ta fara kallon hotunan ta.

Lawisa ta zauna a kusa da ita tana leƙawa. Gwaggo ce ta kira lawisa, ta tashi ita kuma ruma ta cigaba da kallon wayar.

Hotuna ne da videos da ta din ga yi ciki har da wani sashe na wannan jakar ta bullet da ɗaya daga cikin mutanen nan ya rataya, sannan a hotunan akwai in da gefen fuskar ɗaya daga cikinsu ta fito.

Ruma ya ajiye wayar tana tunin wasu abubuwa da suka dabai baye mata kai ta kasa gane kansu.

Bindiga dai jami’an tsaro ne suke ta’amalli da ita, amma ta yaya za ayi ace da saninsu ana shiga da fita da su ba tare da sun tsawatar ba?’ ajiye wayar ta yi, tana son ƙara nutsawa cikin tunani, amma kwanyarta ta gaza bata komai.

“Ruma zaki je rafi, muje ki ga ruwa da duwatsu”.

Gwaggo ta ce “Ke kar ki kaita ki wahalar da ita mana”

Ruma ta ce “A’a gwaggo zan je” tayi maganar tana miƙewa tsaye, ta saka hijjabi suka sake fita.

Wani ɗan madaidaicin rafi suka je, ‘yan mata wasu na wanki a gefe, wasu kuma suna ɗiban ruwa. Ruma ta samu na yi, ta din ga ɗaukar hoto, ta din ga tsalle-tsalle a wurin, yanayin ya burgeta.

Kan wani ɗan dutse ta hau, can nesa ta hango wani wuri baƙiƙirin kamar an yi gobara. Ta kalli lawisa ta ce “Lawisa, can gobara suka yi ne?”

Lawisa ta ce “Wallahi wasu fulani ne suka kafa sansani a wurin, cikin dare aka kawo hari, aka ƙona musu shanunsu, suka ce manoma ne suka yi musu ake ta rigima, da ƙyar abin ya lafa”

“Kaii aka ƙona musu shanunsu, kuma da gaske manoman ne suka yi musu?”

Lawisa ta kai bakinta kunnen Ruma ta ce “Ke ‘yan ta’adda ne fa suka yi musu, amma aka ce faɗan fulani da manoma ne, amma kar ki ɗaga hankalinki fa, mu nan haka lafiya lau muke zaune, an fi tashin hankalin a wuraren su Baba habu”.

Ruma ta yi ajiyar zuciya ta ce “To kuma ba a gayawa ‘yan sanda ba?”

Lawisa ta ƙwalo ido ta ce “‘yan sanda, a ina zamu ga ‘yan sandan ko sun zo me zasu yi, wataran dai sojoji na zuwa ayi ta harbe-harbe abin tsoro”

“Zo mu je wurin, in ga wurin sosai da sosai “

“Ke, Aikuwa tsaf fulanin nan zasu illata mu, yadda suke a ƙule zo mu tafi gida, na cewa Gwaggo ba zamu daɗe ba”

“Ke ki tafi, ni ba yanzu zan taho ba”.

“To ai baki san hanya ba”

Ruma ta ce “Idan na ɓata na tambayi hanyar, ni wurin can nake son zuwa ” tsoro ne ya kuma kama Lawisa ta cewa ruma “Ki zo yanzu mu koma gida, akwai hanya mai sauƙi da zan bi da ke muje wurin “.

Ruma ta ɗan rausayar da kai ta ce “Ina fatan ba ƙarya ki ke yi mini ba, ina son in ɗauki hotunan wurin in ɗau komai, yadda zan ji daɗin bayar da labari, kuma idan na bayar a yadda tunda ina da hoto”.

Lawisa ta yi murmushi ta ce”Haka ne, karki damu” ta lallaɓa ruma suka koma gida.

Sai dai a washegari ruma ta faki idon mutanen gidan ta fice, kai tsaye wurin da aka yi wa fulanin nan ƙone-ƙone ta je. Sai dai tafiyar da nisa sosai, wurin shiru ba kowa sai ragowar abubuwan da aka ƙona, da tsirarun bukkoki a can gaba kaɗan, wurin kamar an yi wata annoba.

“Ke wace wannan me ki ke yi a wurin nan?” A hankali ta waiwaya taga wani dattijo a tsaye s bayanta, hannunsa riƙe jallon ruwa.

“Sannu baba” ya amsa da yauwwa.

Yana cigaba da ƙarewa ruma kallo.

“Baba gidan ‘yan uwanmu mu ka zo, na hau wani dutse na hango nan shine na ce bari na zo na gani, Allah ya mayar da alkhairi amma kun gayawa ‘yan sanda abin da ya faru?”

Kallon ruma yake, yadda take magana fiye da shekarunta.

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Gidan wa ki ka zo a garin nan?”

“Gidan dagaci ne, ɗan uwan babanmu ne” ya jinjina mata kai ya ce “To mun gode da jajen da ki ka yi mana, amma maza ki tafi kar sauran mutanen rigar nan su ganki”.

“To in sun ganni mai zai faru me na yi musu?”

“Kasheki za su yi, dan haka muje na raka ki hanya” babu musu ya saka ruma a gaba har zuwa cikin gari, suna tafe suna hira ruma tana addaba masa da tambayoyinta da ba sa ƙarewa”

A hanya suka yi sallama, ya koma ita kuma ta ƙarasa gida.

Gwaggo duk ta tashi hankalinta rashin ganin ruma, ita kuwa ko a jikinta ta ce kallon gari ta fita yi.

Sai dai a tattaunawar ta da dattijon nan ya gaya mata wasu abubuwa da suka sake ɗaure tunaninta.

****

Hajiya Lubabatu ce ta tsaya a tsakiyar ɗakinta, tana kallon hoton Galadima mai ci a yanzu, wands ya kasance mijinta da yake can ƙasar Germany yana jinya, ta ɗan lanƙwasa yatsan hannunta ɗaya sannan ta furta “Ka yi haƙuri ranka ya daɗe, bani da isasshen lokacin da zan cigaba da ɓatawa a kan ka, goben ɗana ita ce a gabana yanzu ” ta yi maganar tamkar na cikin hoton yana jinta.

Khalifa ne zaune a kan kujerar da take kallon wadda mahaifinsa yake, mahaifinsa sai murmushi yake sannan ya nisa ya ce “Ina jinka Khalifa”.

“Yauwwa daddy, kamar yadda nayi maka bayani, na tsara komai kuma ina da yaƙinin komai zai tafi dai-dai da yardar Allah”.

“Haka ne, banƙi ta taka ba, na kuma yabawa ƙoƙarin da kake yi, amma gani nake komai zamu yi wa yaron nan ba zamu huce ba, yanzu haka bayanai sun zo mini yana garin Abuja, sai dai ban san wurin wa yaje ba, idan har ya cigaba da abin nan EFCC zata bincike ni, kuma daga haka ya ɓata siyasata, ya ci mutuncina kuma ya ɓata gobenka”.

Khalifa ya gyara zama ya ce “Daddy, ai shiyasa nake ta ƙoƙarin aikin nan ya tabatta, ta yadda zan kau da hankalinsa a kan komai, ya tattarashi a wuri ɗaya, ka harda dani, abin nan zai yiwu daddy, kuma akwai nasara a ciki”.

Senator wakili ya yi murmushi ya ce “To shikenan, ina saurarenka, sannan duk abin da kake buƙata, i will make sure that I provide it”.

“To Shikenan Daddy, godiya nake “

Yayi murmushi tare da jinjina masa.

***

Kwanakin su ruma uku, ta saki jikinta, duk da kullum sai sun yi waya da mama, yawo kuwa kamar ta ci ƙafar kare, har gona suke zuwa ita da Lawisa, har ta saba da sirikan gwaggo da yaran maƙwabta.

Sai dai gona ɗaya aka samu aka sayar, a gonakin baban nasu, kuma shima dubu ɗari bakwai kawai aka samu, saboda yanayin in da gonar take babu tsaro sosai.

Ana i gobe zasu dawo kano, Gwaggo ta shirya ruma, ta haɗata da lawisa lawalli ya kai su can wani ƙauye, gidan wani ƙanin mahaifinsu, wai su gaishe su.

Aliyu sai mita yake yana tambarat gwaggo yaushe su ruma za su dawo, saboda da sassafe yake son su kama hanya, gwaggo ta ce kar ya damu, gobe da safe zasu dawo.

Har washegari da safe su ruma ba su dawo ba, Aliyu ya ce “Gwaggo, wai haryanzu su ruma ba zasu dawo ba, tafiya fa zamu yi, bana son rana tayi mana”.

Gwaggo ta ce “Gadanga, sai dai kayi tafiyarka kai kaɗai, ina sane na tura ruma can, sai za a koma makaranta zan dawo da ita da kaina, yanayi ya nuna mini babu isasshen tsari a jikinta, kuma akwai buƙatar ta zaga ta san dangin mahaifinta suma su santa”

Aliyu ya ce “Amma gwaggo ba mu yi haka da mama ba, dan Allah kar ki yi mini haka”.

Gwaggo ta ce “Mhmm, sai kuma ka yi, na gama magana”

Saroro Aliyu ya yi ya ma rasa mai zaice, ya ciro wayarsa ya kira mama a waya.

Yana kira mama ta ɗaga ta yi sallama.

“Mama, gwaggo fa ta tura ruma wani ƙauye, wai ba zamu taho tare ba sai an koma makaranta zata da wo da ita”.

Gwaggo ta ɗan ɗaga murya ta ce”Eh, ni na ce ba zata dawo yanzu ba, sai na gama nema mata tsarin jiki, sannan kuma ta san dangin mahaifinta, tunda ba zuwa take ba”

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce “Aliyu ka taho kawai, idan ka tsaya zai zama abin magana, ƙyaleta taho”

“Amma mama…

“Kar ka ce komai, in dai ruma ce, da kansu za su tattaro su dawo da ita, ka taho ka barsu”.

Abin da gwaggo ta yi ba ƙaramin ɓatawa Aliyu rai yayi ba, da ya san haka ne da ba zai taɓa bari ta saka a kai ruma ko ina ba, daga zuwa ziyara kawai ta riƙe ‘ya wai sai wani lokaci.

Ya sake duban gwaggo ya ce “Gwaggo, ruma fa ba zata yarda ta zauna a garin nan ba, rigima za ta yi miki idan ta dawo ta tarar na tafi na barta”.

Gwaggo ta ce “Babu komai, na san yadda zan shawo kan kayata, amma a yanzu dai ba in da zata”.

Takaici ya ishi Aliyu, ya bi gwaggo da kallo.

“Gadanga ko dukana zaka yi ne? Na gama yanke hukunci, idan kuma kaima zaka zauna ne ni haka nake so, sai mu zauna idan lokacin yayi sai ku tafi duka”.

Tabbas ba dan gobe yana da test mai muhimmanci a makaranta ba zama zai yi, ya saka lawalli a gaba sai ya kai shi ya ɗauko ruma, amma ba yadda iya ya ɗauki jakarsa ya fice.

****

Har Adam yayi kwanakinsa uku a birnin tarayya, bai iya aikata komai ba, saboda da ya fita da niyyar zuwa wani wuri, sai jiki ya hau rawa kai ya hau ciwo, ga ruma da ta addabawa rayuwarsa ya kasa mantawa da ita, komai yake yi sai ya din ga ganinta.

Bayan ya cika kwanaki huɗu, ya kira Ammi yayi mata ƙaryar bai gama abin da yake yi bane, sai dai tattaunawar haka aka yi ta babu shi, duk da halartarsa tattaunawar na da matuƙar muhimmanci.

A kwana na biyar ya kira direbansa a waya, ya ce ya zo da mota ya same shi a hotel ɗin da yake.

Ƙarfe biyu direban ya sameshi, sai dai a wannan karon cikin ikon Allah tun da ya fito sau ɗaya kan ya sara, jiri ya ɗan ɗebe shi, amma  ya tattara nutsuwartsa, yana addu’a, ya nufi motar.

Suka gaisa da direban nasa, yayi masa ya hanya, daga nan ya ce ya gaya masa in da zai kai shi.

Mintuna ashirin ce ta kaisu, a harabar wata plaza suka yi parking, Adam ya buɗe motar ya fita.

Wani matashi ne zaune wanda zai yi sa’an Adam, yana danna computer, yana ganin Adam ya miƙe cikin girmamawa yana murmushi ya ce “Barka da zuwa”

Adam ya ƙarasa yana murmushi, ya miƙa masa hannu suka gaisa, sannan ya zauna.

Matashin ya kalli Adam ya ce “Adam, ya aka yi an shirya zama da kai, amma ba ka yi attending ba?, na din ga kiran wayarka ba ka ɗagawa, har wayar ma ta daina shiga gaba ɗaya?”

Adam ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa ya ce “Am sorry Habib, wata matsala aka samu, amma komai normal yanzu in sha Allah”.

Cikin kulawa Habib ya ce “Are you safe?”

Adam ya jinjina kai sannan ya ce “Me aka tattauna, wace matsaya aka cimma?”

Habib ya ɗan rausayar da kai ya ce “To, mun tattauna yadda yakamata, amma dai kamar yadda na yi maka bayani da farko, ko da ka fito ƙarara ka bayyana lamarin nan, ko an je kotu za a sake su, saboda haryanzu baka da wata cikakkiyar hujja ta zahiri da zaka kafa, yanzu ko kun yi wani abu a kai, ya riga ya gama shiri, da tattaunawa da lawyoyinsa, ya shirya tsaf da ka yi attacking zai yi depending, yanzu abin da yafi shine ka sake mayar da hankali sosai da kai da abokan aikinka, ku samo hujja ta gaske, ta zahiri da za ayi amfani da ita, nima zan shirya tsaf domin cimma nasara ni da tawagarmu”

Adam yayi ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa, ya sake ɗagowa ya kalli Habib ya ce “Duk wata hanya da zan bi domin neman hujjar kama mutumin nan an tosheta, kuma kullum kallon mutunci ake masa, ana sake bashi girma tare da shigar da shi cikin al’amuran ƙasar nan, bayan su ne babbar matsalar mu”

“Adam, tun da ka ga haka, ba shi kaɗai bane, ko dai an san me yake yi ake rufa masa asiri, ko kuma akwai wasu manyan da suke aikin tare “

“Haka ne, abin da nake tunani kenan nima, amma babu komai in sha Allah zamu yi nasara, zan cigaba da ƙoƙari, ina son magana da saifu ma, zan zauna a garin nan sai Allah ya kaimu monday zan koma kano”.

Habib ya ce “To shikenan, Allah ya yi jagora, gashi ko shayi ban baka ba”

Adam ya girgiza kai ya ce “Kar ka damu”

Daga haka Adam ya tashi ya fita, ya saka direbansa ya mayar da shi masauki. Sam ya ƙi yadda yaje gidan sa, saboda wani Dalili nasa.

***

Ƙauye ne sosai in da aka kai ruma, sai dai mutane masu matuƙar karamci da girmama ɗan Adam, tamkar za su goya ruma, dan wasunsu duk basu santa ba, sai dai sun san mahaifinta sosai tunda ɗa ne a wurinsu.

Garin sun yi noma sosai, sai dai an girbe an tare shi a cikin gonaki, ba a kwashe an kai gida ba, ga yanayin garin kamar yanayin garin da aka yi wata annoba.

Wani wurin a ƙone, wani wurin dai gashi nan.

Tun da safe ruma ta fara cewa ita azo a mayar da ita gidan gwaggo, yau zasu koma gida ita da yaya Aliyu, amma dattijon da ya kasance ƙanin kakanta ne ya ce “Ai jikata ba ke ba tafiya, sai hutun makarantar bokonku ya ƙare, kina nan tare da mu”

A ɗan razane ruma ta ce “Saboda me?”

“Haka gwaggonki ta ce”

“Ni gaskiya ba zan iya zama a garin nan ba, gida nake so na koma na ga mama, na gaji, ni ku mayar da ni gida” ta yi maganar tana kuka.

Matarsa da ake kira da iya ta ce “Haba rumaisa, muma fa duk iyayenki ne, muna ƙaunarki sosai, ki kwantar da hankalinki kin ji, za a mayar da ke, idan ki ka matsa zasu iya ƙwaceki gaba ɗaya, ‘yan kwanaki zaki yi a mayar da ke”

“Ni mama nake son na gani”.

“Ki yi haƙuri, za a mayar da ke in dai wurin mama ne” An kai ruwa rana sosai da ruma, kan ta daina koke-koke, sai dai ita ma ta haɗa musu aiki, ba komai take ci ba, tsirfar yau daban ta gobe daban.

In da ta ɗan ƙara samun sassauci, shine tana tare da lawisa, kuma a gidan akwai wata sa’ar tata zaliha, dan haka sukan ɗebe mata kewa.

***

Ba ƙaramin ɓacin rai ‘yan mazan mama suka shiga ba, tun bayan da Aliyu ya dawo musu babu ruma, tare da sanar da su hukuncin da gwaggo ta yanke ba.

Abdallah ya ce “Wallahi gwaggon nan tana da matsala, tsabar mugunta ta yi garkuwa da yarinya dan son zuciya daga kai mata ita a sada zumunci”.

Sai da suka yi dariya jin abin da ya ce, wai tayi garkuwa da ita.

Usman ya ce “Wane irin garkuwa kuma?”.

“To idan ba garkuwa ba, ta yaya zata saka a kai yarinya wani ƙauye a ɓoyeta, wai ba zata dawo yanzu ba, amma idan ta cika musu ciki da rashin ji, ai sa dawo da ita da kansu”

Suna cikin tattaunawar mai sunan Baba ya dawo, suka gaisa da Aliyu, ya tambaye shi ina ruma? Ya sanar masa da yadda suka yi da gwaggo.

Tsuke fuska yayi ya ce “Wane irin abu ne haka? Idan na gama exams ranar lahadi zan je na taho da ita, akan me zasu riƙe ta?”

Mama ta ce “A’a babana, tun da na haƙura dan Allah kuma ku yi haƙuri ku ƙyalesu, yanzu sai ace zigaku nake yi, su je su ƙarata, sati biyu ai kamar yau ne”

“Duk da haka, bai kamata ruma ta zauna a wurin nan ba, babu tsaro gaba ɗaya dole zan je na taho da ita, dan ba ta zuwa makarantar boko yanzu, islamiyya fa?” Sosai ya ɗau zafi, mama dai ta ce ba ta yadda wani yaje ya ce zai taho da ruma ba.

***

Gaba daya ta tattara hankalinta da nutsuwarta a kan litattafanta, gefe kuma ga calculator tana dannawa, tayi ɗai ɗai a ƙasan carfet, ta saki dogwayen kalbar da aka yi mata, ta zubo har kafaɗarta, duk da kalbar ta tsufa amma ta yi kyau sosai.

Nusaiba ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama.

Iman ta amsa mata, ta zuba mata ido tana kallonta.

“Sarkin littafi, me kuma ake yi?” Iman ta kalli litattafan ta yi murmushi ta ce “Boko nake ci masoyiyya, ta samu ne?”

Nusaiba ta zaune ta ce “Eh to, ba nace ba, uncle J ne ya zo, kuma da alama ke yake son gani, sai tmbayata yake kina ina?”

Tsaki iman tayi, ta gyara zamanta tana ƙoƙarin mayar da kanta kan litattafanta.

“Kai, uncle J ɗin ki ke yi wa tsaki, ya zo ya sakani a gaba sai tambayata yake kina ina?”

“Anty Nusaiba dan Allah ki ƙyaleni da sabgar mutumin nan, wai me zan yi masa ne dan Allah?”

“Nifa na kasa gane abin da kuke ɓoyewa, anya ba sonki yake yi ba?”

Da sauri iman ta girgiza kai ta ce “Dan Allah Anty Nusaiba kar ki ɗaga maganar nan, idan har Ammi ta ji za ta bayar goyon bayan hakan, ni kuma ba zan watsa mata ƙasa a ido ba, amma ni bana sha’awar duk wani wanda ya fito daga masarautar na, ke kin san me nake nufi”.

Nusaiba ta yi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan, na daina cigaba da aikin ki, zan je na ce masa bacci ki ke kawai”

Iman ta jinjina kai alamar to.

****

Tafe suke su uku, ruma na ta shan tsamiyar biri tana zubarwa a hanya, mayafinta a kafaɗa. Su fuskarsu duk da hoda da kwalli, ruma kuwa tata yadda take haka take kamar namiji, kunneta babu ko ɗan kunne.

“Kai ku tsaya” ruma tayi maganar tana kallon wata bishiyar mangwaro, ‘yar gajeriya amma tayi ‘ya’ya fal.

Suka kalli ruma suna son jin dalilin tsayar da su ɗin.

“Mangwaro zan tsinka”.

A ɗan razane Zaliha ta ce “A’a ruma, a garin nan fa bakomai ake taɓawa ba, baki ga gonaki duk an yi girbi ba, amma ba a ɗauka ba,masu garin ake jira su zo su yanke harajin da za a biya sannan a ɗebi amfanin gona, yanzu idan suka zo wucewa suka ganki, zaki saka mu a matsala.

“Suwaye masu garin?” Ta yi maganar cikin ko in kula.

Lawisa ta ce “Ke dai ki bari kawai ruma, ki bari idan muka je gida sai a saka a samo miki”

Ruma ta cire mayafinta, ta ɗorawa lawisa a kafaɗarta, ta nufi bishiyar nan, suna ƙwala mata kira, amma ba ta tsaya ba, ta kama bishiya ta haye kamar buranya, hawan katanga da bishiya ba abu ne mai wahala a wurin ruma ba.

Ta naɗe doguwar rigarta, ta tara mangwaron sannan ta saukko, su kuma suna ƙasa suna jiranta cikin tsoro suna cewa ta sauko.

Bayan ta sauko ta karɓi mayafinta ta zuba a ciki, ta saɓo abunta tayi gaba ta ƙyalesu.

Bin ruma suka yi da kallo, ta ci uwar ubansu a rashin ji, haka suka rufa mata baya suna kallonta.

Suna cikin tafiya suka ga ta saki hanya ta shiga wata gona, tarin masarar da aka jingine ta je ta fara ɗauka.

“Innalillahi, dan Allah ruma kar ki janyo mana masifa, dan Allah ki fito mu tafi, duk wanda aka gani a gona bayan girbi ba a biya haraji ba kashe shi za ayi”.

“Kisa kuma sai ka ce cinnaka, guda biyar kawai zan ɗauka gasawa  zan yi na ci”

Zaliha ta ce “Dan Allah ki fito kar su ganki”.

“Wai suwaye ne? In sun ganni ba ruwanku ni kaɗai na ɗauka” ta zuba masarar a mayafinta ta fito. Kamar suna tsoron ruma suka sake rufa mata baya suna zazzare ido.

Sun yi tafiya mai nisa sun kusa gida, suka ji ana musu magana “Ke daga ina ku ke?” Gaba ɗaya suka tsaya suka waiwaya, wani dogon mutum ne a tsaye, sanye da rawani hannunsa saye a cikin tsummar rigarsa, ya ma dai fi kama da mahaukaci.

Ruma ta ƙare masa kallo za ta yi gaba abinta.

“Ke ina magana zaki tafi?” Ya daka mata tsawa.

Cikin tsiwa da rainin hankali ruma ta ce “Haba babana ke fa ka ce mana, kuma na ga dai ba aikenmu ka yi…”

Da sauri zaliha ta riƙe hannun ruma ta ce wa mutumin “Dan Allah ka yi haƙuri, baƙuwa ce ne a garin”.

“Baƙuwa amma mara tarbiyya ko? Ba ta san nan ina ne ba? Kuma ba ta iya ladabin yin magana da manya ba, Meye wannan ta riƙo?”

Ruma ta ja da baya ta ce “Nifa ban gane ba, me na yi maka zaka ce mini mara tarbiyya? Mangwaro ne da masara” tayi maganar tana buɗe masa mayafin.

“Waye ya baki izinin ɗaukar masarar?”

Ruma da haushi ya fara kamata ta dake ta ce “Yi haƙuri ban san gonarka bace, idan yayana ya zo ɗaukata daga birni zai baka kuɗin masararka, ni na tafi sai kun taho” ta ɗau kayanta tayi gaba.

Su kuwa jiki na rawa suka tsaya suna sauraren mutumin.

“Lallai dagaci, wato har da kawo baƙi marasa ɗa’a ba tare da ya nemi izini ba, har su zo su karya mana doka, to zai gane kuskurensa da mu yake zancen, ku wuce ku tafi”.

Da gudu suka tafi gida domin sanar da abin da yake faruwa.

Suka tarar da iya na tuhumar ruma ina ta samo wannan kayan, amma tayi shiru ta ƙi magana.

Su zaliha ne suka kwashe komai suka gaya wa iya.

“Mun shiga uku ruma, ai mu garin nan ba a mana haka, a zaune muke ƙarƙashin umarnin ‘yan bindiga, suke da garin, ki daina haka ba ruwanki da kowa, duk wanda ki ka gani a garin nan girmamashi to ba ruwansu da ke, amma idan ki ka yi musu rashin kunya sai su yi miki illa”.

“To ku mayar da ni gidanmu mana, ni ba wanda ya isa yayi mini wani abu, dan ni ƙanwar maza ce zane mutum yayyena za su yi. Kawai sai ya ce mini mara tarbiyya shi tarbiyyar ce ta saka yake yi wa mutane magana a haka, ni a kano kowa ya san ina girmama mutane raini ne ban so, ni na zata ma mahaukaci ne”.

Iya ta kwantar da murya ta ce “To na ji, amma dai dan Allah ki kula, bari Alhaji ya shigo zai je ya basu haƙuri, ‘yan bindiga ne sai su illataki, muma bin umarninsu ne ya sanya muke zaune lafiya”

Ruma ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Wai iya su waye ‘yan bindigar nan?”

“‘yan tayar da ƙayar baya ne, Allah ne kawai ya san meye aƙidarsu”

Cikin rashin fahimta ruma ta ce “Meye ƙayar baya kuma, sai ka ce wasu kifaye?”

“Ba zaki gane ba ko na yi miki bayani, amma dai bisa umarnin su muke zaune, sai abin da suka ce muke yi”

“To suma shugabanni ne zaɓarsu ake yi, na ji kin ce ba kwa komai sai da izininsu, ko ‘yan sanda ne su?”

“Babu ɗaya ruma, kawai dai ku yi ta mana addu’a, muna zaune ne dan kawai mun san ko mun bar nan ba in da zamu je, bamu da wurin zuwa”

Ƙwaƙwalwa ruma ta shiga wani tunanin na daban, ba ta kuma cewa komai ba, ta shiga wata sabgar.

Tana missing ɗin gida sosai, ga wayarta ta mutu ba caji tama barota cikin kaya a gidan gwaggo.

Kullum da safe cikin bata rubutu da banka mata hayaƙi ake a gidan, wai maganin tsarin jiki na baki maita da aljanu.

Ruma kuwa ta ce ita ba zata sha wani rubutu ba, warin tawadar nan amai zai sakata. A kwanaki biyu kacal ruma ta fara buwayarsu, saboda sai ƙoƙari take sai ta aikata wani abu da zata tsokano mutanen nan.

Yau da yamma kasuwar ƙauyen take ci, dan haka suka shirya su uku zasu tafi kasuwa, iya tayi ta jawa ruma kunne a kan rashin ji da kuma yi wa mutane tsiwa, sannan ta basu kuɗi suka fita suka tafi.

Kasuwar ƙauye ce dai, amma ta burge ruma sosai da sosai, ga kayan gargajiya nan kala-kala.

Sai dai abin da ya bata mamaki, yadda ta kan ga wasu mutane masu rufaffiyar fuska suna kaiwa suna komowa, hannayensu saye a cikin rigunan su.

Shagon wani mai awo suka shiga suka zauna, za su sai wake, da alama su lawisa sun san shi, sai hira suke. Suna cikin hirar wani mutum yayi sallama suka amsa masa, ya shigo ya zauna, bai ce musu komai ba, suma kuma ba wanda ya tanka masa.

Ruma ta ce “Ni fa hausar nan taku dariya take bani”.

Mai awo ya ce “to  hausar mu tafi daɗi ai, na ji kamar hausar kanawa ki ke yi ko?”

“Eh mana, ni ‘yar kano ce, hausarmu mai daɗi, garinmu ma yafi naku kyau sosai da sosai”

Mai awon ya ce “Ai mu ma dan nan ƙauye ne, amma garinmu yana da daɗi da kyau”.

Ruma ta yi dariya ta ce “Ba wani nan, garin naku da baku da iko da komai, wai sai an baku umarni mutum da kayansa, kano kuwa ba haka bane, abu idan naka ne naka ne kawai. Kuma ku ba damar baƙo ya zo sai a din ga tuhuma waye wannan, kano kuwa ba a haka?. Haka wani zanƙalelen mutum kamar mahaukaci ya tsayar da mu yana tambaya wai wacece ni?”

Zaliha ta ɗan daki cinyar ruma tana ƙifta mata ido, amma ruma taƙi shiru.

“Wai me awo suwaye masu yawon nan da rufaffiyar fuska kamar munafukai” a tare suka kalli ruma, sannan suka kalli mutumin nan na zaune.

“Ya naga kuna kallona kamar an ritsa mara gaskiya? Bawan Allah ko kai ka san su?” Ta yi maganar tana kallon mutumin

Ya girgiza kai ya ce “A’a, amma ina ga ko sune masu garin da ake faɗa”.

“Wai sune ‘yan ta’addan?”

Ya rausayar da kai ya ce “Wataƙila”

Ruma ta ce “Amma kuwa ba su kyauta ba, ba su yi wa kansu adalci ba, su dinga ƙwacewa mutane kaya, nima fa da zamu zo garin nan a kan bindigogi na zo, ina ‘yan ta’addan ne a mota ɗaya muka hau da su”

Ya ɗan waro ido ya ce “Haba dai, baki ji tsoro ba?”

Kamar ya kunna ruma, ta gyatta zama ta ce “Ni ban ji tsoro ba, a cikinsu fa wani har kaza ya sai mini, yayi kalar masu kirki, amma ban san meyasa suke kashe mutane ba, kullum a rediyon mama sai an ce sun kashe mutane, abun tausayi, ku yi ta Addu’a kuna musu nasiha, ko zasu daina”.

Mutumin yayi murmushi ya ce “To shikenan, kuma kanawa ku tayamu da Addu’a, amma na yi mamaki da ki ka ce a kan bindigogi ki ka zo, kuma ba ki ji tsoro ba”

Ruma ta yi wani irin murmushi ta ce “Baka sanni bane ba, yayyena maza bakwai” ta yi maganar tana nuna masa da yatsunta.

Sannan ta ɗora da cewa “Ni ba komai ne yake bani tsoro ba, na ce musu dan Allah su buɗe mini in gani ko da gaske suke bindiga ce, kai ka ga yawan bindigar? Allah ya kyauta kawai” ta miƙe tsaye ta ce “Bari na je na sayo gyaɗa” tayi waje.

Lawisa ta yi ƙasa da murya ta ce “Zaliha tashi mu gudu kar yarinyar nan ta ja a harbemu a tsakiyar kasuwar nan”.

“Ya ya za ayi mu gudu mu barta?”.

Mai awo ya ce “Ranka ya daɗe ayi mata haƙuri baƙuwace kuma yarinya ce, ayi haƙuri dan Allah” mutumin bai ce komai ba ya cigaba da danna wata waya mai madannai.

Gaban mai gyaɗa marau ruma ta duƙa, tana saya wani mutum ya wuce tare da bigeta da wani abu, kuma ko waiwayowa bai yi ba yayi gaba abunsa.

Da gudu ta tashi ta bishi “Malam ka bugeni, ba ka ji ba na ce ka bugeni fa”

Ya waiwayo yana kallon ruma.

“Ba ka ji ka buga mini wani abu a bayana, kuma ba ka bani haƙuri ba”

Ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce “Ni ne zan baki haƙurin?”

“Eh mana, wani abu fa ka bugeni da shi a bayana, ai ka waiwayo ka bani haƙuri ko?”

Zai yinƙura kenan ya ji an danƙi hannunsa an ja shi. Wani mutum ne shima mai rufaffiyar fuska ya riƙe shi.

Cikin tsiwa ta ce “Bana yi wa manya Allah ya isa, amma wallahi ban yafe ba, Allah ya haɗaka da wanda yafi ƙarfinka kaima ya ci zalinka”

Idon kowa ya dawo kan ruma, ita kuwa ko a jikinta, ta koma ta sai gyaɗarta da ruwan leda, ta koma shagon mai awo.

Ko da ta koma, ta bi su ta  bawa kowa leda ɗaya ta gyɗa, har da wannan mutumin da ya shigo ya zauna.

Ta kalli mutumin ta ce “Ɗan uwanmu kana da ‘ya’ya?” Ya jinjina mata kai alamar eh.

Ta kuma bashi ɗauri biyu ta ce “To ka kai musu wannan, ga ruwa ma na baka. Ku kuma ku tashi mu tafi, ‘yan garin nan ba su da mutunci, wani ya bugeni da wani abu a baya, kuma yaƙi bani haƙuri ni kuwa na masa Allah ya isa, kuma wallahi na koma gida sai na je na gaya wa ‘yan sanda, abin da ske a  garin nan da abin da na gani ana yi! Sai na faɗi komai”

Ba ta ji ko ɗar ba da ta yi maganar, ta ɗau abubuwan da ta saya, mutumin nan ya bi ruma da kallo, har zata fita daga shagon ya ce “Ƙawata yaushe zan zo kano na kawo miki ziyara, in ga Kanon da ake cewa ta fi garinmu kyau?”

Murmushi ta yi ta ce “Idan ka zo kano ka ce wurina ka zo sai yayyena sun naɗa maka na jaki ni ma su karairayani, cewa za su yi kai saurayina ne, amma dai Kano tana da kyau sosai, sai watarana ɗan uwanmu”

Ta yi waje, su lawisa suka bita kamar munafukai.

Jerin babura ne suka din ga shigowa cikin kasuwar ko ta ko ina, suna ɗaukar mutanen nan masu rufaffiyar fuska suna barin cikin kasuwar.

Ruma ta ce “Zaliha wai wannan mutanen idan suka idan su ka bar nan ina suke tafiya a kan bauran nan?”

Jiki a sanyaye zaliha ta ce “Cikin daji suke tafiya, ruma mutumin nan fa na cikin rumfar nan shima fa sune, ɗan uwansu ne” waro ido ruma ta yi ta ce “Haba dai? Amma nake hira da shi?”.

“Shiyasa ake ce miki ki iya bakinki, kin zage sai zuba ki ke har da cewa zaki gaya wa ‘yan sanda”.

“To ba gara a gaya wa ‘yan sandan ba, tun da ku tsoronsu ku ke ba za ku iya ba, ai taimakonku zan yi, ke nifa DPO ɗin unguwarmu ma ya sanni, tun da na karya wata yarinya ya sanni, dan haka sai na je na gaya masa”.

Lawisa ta ce “Ke waye ya ce miki aikin ‘yan sanda ne?, sojoji ma fa ake turowa, amma haryanzu abu ya gagara mu samu tsaro “

Tunawa ta yi da batun da aka yi, na da sanin wasu daga jami’an tsaro ake zirga-zirga da makamai amma ba yadda suka iya.

Ƙarar wani abu ruma ta ji, da bata taɓa jin sauti irinsa ba, sai gani tayi mutane suna gudu, mutumin da yake tafiya a kusa da su ya faɗi cikin jini.

Aka buɗewa mutanen kasuwar wuta. Tuni ta nemi su lawisa ta rasa sun arta, ita kuwa ta kasa gudun, ta kasa gaba ta kasa baya, sai rungume kayan sayayyar ta da tayi tana rarraba ido, mutane sai faɗuwa suke cikin jini.

Ji ta yi an kama hannunta an ja ta da gudu, an bi ta bayan kasuwar da ita, ba ta san ko waye ba, sai da suka bar cikin kasuwar, sannan suka tsaya.

Mutumin da ya zauna a rumfar mai awo ne, sai dai shima a wannan karon fuskarsa a rufe take, da kayansa da kuma muryarsa ta gane shi ya ce mata “Yi sauri ki bar wurin nan, ki tafi gida” daga haka ya juya ya barta.

Ikon Allah ne ya kai ruma gida, dan ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar wannan ba, mutane kwance a cikin jini an kashe su.

Ko da ta je gidan babu kowa, ta zube kayan hannunta a tsakar gida ta zauna, ta yi shiru tana cigaba da jiyo ƙarar harbe-harbe sama-sama.

Ta yi kusan mintuna ashirin, sai ga iya da su lawisa sun shigo, da alama ita suka tafi nema.

A gigice iya ta ƙaraso in da ruma take tana faɗin “Rumaisa babu abin da ya sameki ko? Bari gobe in Allah ya kaimu da sassafe azo a mayar da ke, mutanen nan sun sake waiwayo mu, ina fatan babu abin da suka yi miki”

Ta kalli jikinta, ba abin da ya sameta sai dai jini duk ya taɓata. Iya ta saka ruma ta yi wanka ta canza kaya.

Sai dai ruma ta kasa magana, dan ta tsorata da abin da ta gani, gawar mutane kwance a cikin jini.

Da ƙyar ta iya cin abinci, ta nemi wuri ta kwanta, sai dai bacci ya gagari ruma sai tsananin zurfin tunani.

Ruma tana jiyo iya da sauran mutan gidan, suna mayar da zance da irin ɓarnar da aka yi a harin na yau, a nan ta ji irin masifu da tashin hankalin da suka fuskanta a baya, wanda haryanzu suna kai.

Tun da Allah ya sa ruma ta buɗi ido, ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar wannan ba.

****

Takawa jiki yayi kyau, ya daina jin abin da yake ji, ya cigaba da sabgoginsa a Abuja, sai dai duk yadda ya so ya gama abin da yake ya dawo kano abu ya gagara.

Tattaunawa ce ta musamman suka yi, ita ma tattaunawar sai dare suka yi ta, sai bayan sha biyun dare sannan suka gama, ya fito zai tafi masaukinsa, dan ko direban bai nema ba yau.

Ya biya wani restaurant ya ci abinci, sannan ya nufi makwanci. Tun safiyar yau yake fama da fargaba da ya rasa dalilinta. Yana tsaka da tuƙi gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa gabansa ya faɗi, ƙirjinsa yayi wani irin bugawa da sai da burki ya kusa ƙwace masa a tsakiyar titi. Da ƙyar yayi parkinh ya kifa kansa a kan sitiyari, ya dafe ƙirjinsa sa hannu ɗaya, yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugu.

***

Gari yayi tsit kamar an yi ruwa an shanye, duk wannan balahira da ta faru har aka yi aka gama, babu jami’in tsaro ko ɗaya da ya bayyana a wurin, sai da ƙura ta lafa waɗanda aka karkashe wa ‘yan uwa, suka je suka ɗebo gawarwaki, aka yi musu sutura ana jiran gari ya waye a sallacesu, wasu gawarwakin ma ba a samu ɗebo su ba saboda tsoro.

Dare ya tsala sosai, farin wata ya haske gari, ko ƙwaƙwƙwaran motsin wani abu ba ka ji, ciki har da ƙwari.

Idanunta tarwai, babu alamar bacci zai ɗauketa ko da kuwa ɓarawo ne. Daga can ƙasa-ƙasa ta fara jiyo jiniyar babura suna kusantowa. Ta runtse idanunta tana hango yadda a abubuwa suka faru ɗazu a kasuwa, sai dai ƙarar baburan suka cigaba da kusantowa yana cika mata kunne.

Hannu ta saka ta toshe kunnuwanta, tare da sake rintse idanuwanta. Dan ƙarar baburan na sake hasko mata abun da ya faru

Ba ta san iya adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, ta sauke hannuwanta, iface-iface ta din ga jiyowa ana salatuttuka, hayaniya ta yi yawa a ilahirin kewayen gidan.

Muryar mijin iya ta jiyo yana faɗin “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, mutanen nan sun sake dawowa, mai kuma suke nema da mu? Me suke buƙata?”

Iya ma cikin kuka take salati tana “Allah kana gani, Allah bamu da wani gata sai kai, Allah ka duba mu”.

Wani irin ihu da gurnani kunnuwan ruma suka jiyo mata, kai daga jin ihun ka san wadda take yi a cikin masifa take.

Muryar wani magidanci suka ji yana ta magiya “Dan girman Allah ku yi mini rai, ‘ya ta dan Allah ku rufa mini asiri”

Ƙarar harbi suka ji, daga nan basu sake jin muryar mutumin ba, sai kuka da ihun yarinyar. Wadda ruma sukan yi wasa tare.

Gaba ɗaya kururuwar mata da hargowar mutanen ta karaɗe ƙauyen, haɗi da harbe-harben bindiga.

Kan iya suyi wani yunƙuri, wasu irin zaratan maza su kusan huɗu sun afko cikin gidan.

Mijin iya ya tsaya ƙyam, babu tsoro a tare da shi ya ce ‘Haka muka yi da ku? Kun saɓa alƙawari mun yi duk abin da kuke so, amma bamu tsira ba, so kuke lallai sai mun fita mun bar muku garin, idan mun fita ina kuke son mu je?”

Cikin tsawa wani ya ce “Ba tuna mana alƙawari muka zo ka yi ba, aiki muka fito yi, kai ku kama shi ku ɗaure mana shi” aikuwa suka kama dattijon suka yi masa ɗaurin huhun goro, suka rufe masa baki,  sannan suka afko cikin ɗakin.

Lawisa da zaliha sai kyarma suke yi, ruma kuwa tayi zuruu da ido, tana ganin sarautar Allah, abin da take ji a radion mama yau gashi a zahiri ba labari ba.

Hargitse kayan ɗakin suka shiga yi, wasu kuma suka zaga suka kwance garken dabbobin da ake kiwo a gidan, suka yi waje da su.

Ɗaya daga cikin su, ya zo ya danƙi ruma ya fara janta.

Cikin kururuwa iya take faɗin “Ka yi wa Allah da ma’aikinsa ka ƙyale yarinyar nan, baƙuwace ‘yar amana ce, dan Allah karku cutar da ita”.

“Kai wuce da ita” ɗayan yayi umarni cikin tsawa. Iya ta yinƙura zata yi magana, ɗayan ya saka bakin bindiga ya buga mata a ka ta zube a ƙasa sumammiya.

Ruma ta zura silifas ɗin ta, ɗayan yayi waje da ita yana janta. Ko da suka fita ko waiwayowa ba sa yi, su Zaliha sai kuka suke suna kiran ruma, amma suka ce idan suka kuma magana sai sun harbesu.

Ko da suka fita tuni duk sun tattara waɗanda zasu tafi da su, a cikin daren suka ingiza su zuwa cikin daji, ciki har da ruma.

Tafiya suke tamkar suna kaɗa dabbobi, an tattaro mata manya da ƙanana sai maza ‘yan tsirari.

Tafiya suke a tsananin duhu, ba tare da sun san in da suke sanya ƙafafuwansu ba, ruma ganin abin take kamar a mafarki.

Tun suna tafiya ruma tana saka ran tafiya za ta ƙare, har ta sare ta fara galabaita ta gaji tiƙis, dan haka ta ja ta yi burki ta durƙusa tana hutawa.

Cikin tsawa wani ya ce “Ke! Tashi ki wuce mu tafi”

“Na gaji wallahi, ba zan iya tafiya ba”

“Ba zaki iya tafiya ba? Tashi kan na ɗauke kanki da harsashi”

“Wai ya ka ke so na yi, ba ka ga ni yarinya bace ba, wallahi sai dai ku kasheni, nace na gaji ni wallahi ban taɓa ganin bala’i irin wannan ba”

“Dalla kasheta mu wuce, ba zata ɓata mana lokaci ba” cewar ɗaya daga cikinsu.

“Tsaya in zauna daga nan, sai ku harbeni, ina zan iya wannan wahalar, Allah yasa idan na mutu na je a sa’a, na san mama za ta mini Addu’a” tayi maganar tana zama.

Waɗanda suke kan babura ne suka iso, wani yayi parking ya ce “Tsayuwar me kuke yi ne?, ku wuce mana”.

“Oga wai ta gaji, shine ta samu wuri zauna ta ce mu harbeta”

Hasketa na kan babur ɗin ya yi da fitila, ta saka hannu ta kare fuskarta tana mucincina ido, saboda hasken fitilar.

“Ke ‘yar gidan waye a garin nan?” Ya tambayeta.

“Nifa ba ‘yar garin nan bace, ziyara kawai na zo, gwaggo ta yaudareni aka kawo ni nan, wai sai zamu koma makaranta zata mayar da ni gida “

“Taso ki hau mu ƙarasa” yayi maganar yana nuna mata babur ɗin da yake kai.

Babu musu ko wani abu ta kama babur ta ɗane, ya ja suka tafi.

Aka cigaba da kaɗa sauran a ƙafa, tamkar shanu, a iya sanin ruma ita dai kawai sun yi tafiya mai nisan gaske, kafin su ƙaraso wani ƙaton wuri, bayan wani dutse tsakiyar daji sosai da sosai.

Wasu mutanen suka tarar riƙe da manyan makamai, ga wasu mutanen da aka kama duk a zube a ƙasa a zazzaune kamar fursunoni.

Ya karkata babur ɗin ya ce wa ruma ta saukko.

Ta cimimiye shi sannan ta sauka, tana kallon wurin, sai dai duk da hasken farin watan ba kowa take iya ganewa ba.

Ɗaga kai tayi ta kalli mutumin da ya kawota a babur. Da kayan jikinsa ta gane shi, mutumin ɗazu da duka haɗu a kasuwa.

Cikin mamaki ta ce “Kaii, kai ne?”

Ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce “Shhhhhh, wuce ki nemi wuri ki zauna”

Ta ƙarewa wurin kallo, sannan ta kalleshi “Wai a nan zan kwana? Akwai sanyi fa, kuma a wannan filin babu abin rufa ba katifa?”

Wani daga cikinsu ya gyara bindigarsa cikin tsawa ya ce “Zo ki wuce, au ke daɗi ma ki ke nema, zaki gane kuskurenki kuwa”.

Ba ta motsa ba ta sake duban wanda ya kawota, ya jinjina mata kai ya ce “Wuce ki zauna”

A hankali ta ja ƙafarta ta wuce ta zauna a in da aka nuna mata, wani irin sanyi take ji har cikin ƙashinta, ga bishiyoyin wurin sai rausayawa suke yi, ƙafafuwanta duk sun yi tsami ga ƙaya da ta taka.

Wasu daga mutanen suka koma gefe, suka kunna sigari suna sha.

“Allah mai iko, yau kuma nan Allah ya kawo ni” ta takure jikinta tayi shiru, da yanzu tana gida kusa da mama, mama tana lulluɓeta.

***

Da ƙyar Adam ya iya kai kansa hotel ɗin da yake, bai tsaya ko ina ba sai ɗakinsa, ya je ya buɗe ya kwanta a ruf da ciki, yana ta maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji’un.

Cikin wani abu mai kama da bacci da kuma gizo, yake jin sheshsheƙar kukan ruma, kamar dai kowane lokaci itan dai yake gani tana kuka.

Haka ya wanzu a wannan yanayin, da shi kansa bai iya tantance wane iri bane ba.

Alarm ɗin wayarsa ne ya buga, alamar asuba ta yi, hakan  ne ya sanya ya farka da kalmar shahada a bakinsa.

Ya tashi zaune ya ɗan yi shiru yana tunani, shi dai tun da Allah ya sanya ya taso da ƙuruciyarsa bai taɓa cikakkiyar lafiya ba, daga wannan sai wannan, bai taɓa tunanin zai kawo i yanzu ma a raye ba.

Ya yanke shawarar idan ya koma kano, zai kuma neman ruma ya ji meye matsalar sa da ita, da ta hana shi sukuni irin haka.

***

Har gari yayi haske, waɗanda aka ɗauko su ruma tare da su ba su ƙaraso ba, ruma ta kalli wani tsaye da bindiga ta ce masa “Zan yi sallar asuba”.

“To waye ya hanaki?”

“Ban gane ba, zan yi fitsari ne in yi alwala, a bani abin salla”

“Duk ciki waye ki ka ga yayi salla a nan, kar in sake jin bakin ki”.

Wani dattijo ya ce “Yarinya sai dai ki yi taimama ki juya ki kalli gabasa ki yi salla, amma babu mai baki wani ruwan alwala a nan” tsananin mamaki ya cika ƙwaƙwalwar ruma, ita haryanzu ma ba ta san dalilin da ya sanya a ka kawota nan ba.

Shawarar tsohon ta bi, ita kanta taimamar ba ta iya ba, haka nan ta batsaltsalata, ta yi salla.

Gari yayi haske sosai, sai ga waɗancan sun ƙaraso a mugun galabaice, wasu ƙafa sai jini take saboda taka ƙayoyi, wasu sai haki suke yi suna kuka, haka suma aka zube su a wurin gaba ɗaya.

Matan da suke ciki sai koke-koke suke, wani ƙato baƙi daga cikinsu yayi musu wata razananniyar ƙara “Ku rufe mana baki, ko tarwatsa ƙwaƙwalenku da harsashe”.

Ruma tayi zurruu da ido tana kallon mutumin.

“Ke kuma na yi kama da ubanki ne da ki ke kallona?”

Jin maganar ruma tayi a sama ba daɗin ji.

“A’a meya kawo zancen ubana kuma, ubana ko da ban san shi ba, yafi ka kyau” tayi maganar cikin ƙunƙuni.

“Me ki ke cewa?” Yayi maganar yana yo wa kan ruma.

Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Babu wanda ya sake bi ta kansu, aka bar su a wurin nan.

****

Gidan iya kuwa sai da gari ya waye maƙwabta suka shigo, aka yayyafawa iya ruwa, aka tafi da ita Asibiti da ita da mijinta, su lawisa kuwa sai koke-koke suke yi.

Maƙwabtansu kuwa an yi wa yarinyar gidan fyade an kashe babanta an tafi da matar gidan. Nan da nan labari ya cika gari.

Babu shiri gwaggo ta shirya ta sanya lawalli ya goyata a babur ya kaita garin su iya. A nan ta iske cewar an yi garkuwa da rumaisa. A take ita ma ta yanke jiki ta faɗi, ita ma aka yi asibiti da ita.

Iya tuni ta farka, gwaggo kuwa da ƙyar ta farfaɗo, tunda ta farko take koke-koke tana faɗin “Na shiga uku me zance wa uwar yarinyar nan, da na sani na basu ‘yar su, ƙaunar yarinyar nan ya sanya na riƙeta, da na san haka zata faru, da na barshi ya tafi da ita. Ni yanzu ina zan saka kaina”

Sai da ma’aikatan wurin suka taru suka yi ta rarrashin gwaggo suna bata haƙuri, amma cewa take “Ni dama tawan suka ɗauka suka bar ‘yar mutane, bawan Allah baƙuwace ‘yar wa na ce, ban san me zasu yi mata da suka tafi da ita, Allah ka fitar da yarinyar nan ni Shafa’atu ina zan saka kaina, ta ina zan yi wa uwar yarinyar nan bayani?”

Likitan ya ce “Ai uwar yarinyar na tabattar musulma ce, kuma tayi imani da ƙaddara, dan haka ko a gabanta ne za a iya sace yarinyar “

Girgiza kai gwaggo ta yi ta ce “Ba zaka gane ba”

A social media Abubakar ya fara ganin abin da ya faru, kuma ya san da batun an kai ruma katsina, ƙauyen da iya take, duk da yana makaranta.

Ba shiri ya kira Aliyu a waya ya sanar masa da a kan lallai ya bincika, su ji ya ruma take, sannan su gaggauta zuwa su ɗaukota.

Usman ma ya gani, dan haka a burkice ya ja Aliyu yake nuna masa abinda ya gani.

Aliyu ya ce “Yanzun nan Yaya yayi mini magana a waya, ina son na kirasu a waya amma tsoro nake ji, babban tashin hankalina kar mai sunan Baba ya ji balle mama, dama ya ce gobe in Allah ya kaimu zai je ya ɗauko ruma”.

Usman ya ce “Ka ga ba wannan ba, ka kiras lawalli a waya ka tambayeshi yaya rumaisa take?”

Aliyu ya girgiza kai ya ce “Usman gabana faɗuwa yake yi fa, ance an karkashe wasu an tafi da wasu, kai dai ka kirasu”

Usman ya kira wayar lawalli, amma taƙi shiga, dan haka ya kira ta ɗanlami babban ɗan gwaggo, dan tabattar da abin da yake faruwa.

Sai da ta kusa katsewa sannan ɗanlami ya ɗaga wayar.

Ba tare da sun gaisa ba, cikin zaƙuwa Usman ya ce “Yaya ɗan lami, ya ake ciki ne? Na ji ‘yan ta’adda sun kai hari garin su Iya, ya ake ciki ya ya ina ruma?”

Yaya ɗanlami ya ce “Wallahi kuwa, dan kaga gwaggo ma tana gadon asibiti, Baba kawai aka sallamo”

Aliyu ya karɓe wayar ya ce “To Allah ya kyauta, ya ya rumaisa, gobe in Allah ya kaimu yaya umar zai zo ya ɗauketa ya taho da ita, dan Allah a ɗaukota daga garin nan kan ya zo”.

“Aliyu sai dai fa mu tsananta addu’a, an samu matsala ‘yan bindiga sun tafi da rumaisa!!!”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, me ka ke cewa ne…?”

Usman ya girgiza Aliyu ya ce “Me ya ce maka ne?”

Kan Aliyu yayi magana, suka ga mai sunan Baba a tsaye yana kallonsu, Allah kaɗai ya san iya adadin lokacin da ya shafe a tsaye yana jin su ba tare sun sani ba.

Tsuru-tsuru suka yi suna kallon umar, sai dai yanayinsu ya nuna a razane suke, kuma aka rasa wanda zai yi magana.

Ƙarasawa yayi gabansu, ya karɓi wayar daga hannun Aliyu, ya yi dialing lambar ɗanlami, yana kira ya ɗaga tare da yin sallama. Sai dai ɗanlami na jin muryar mai sunan baba cikinsa ya kaɗa, dan ba ƙaramin tsoron tijarar mai sunan Baba suke ba.

Cikin kakkausar murya Umar ya ce “Me ka gaya musu? Ina ruma take?”

Ɗanlami ya ɗan rikice sannan ya ce “Malam umar a saka addu’a, amma Akwai damuwa, ka san shi lamarin ƙaddarar Ubangiji ba ayi mata shamaki”.

Cikin hasala ya kuma cewa”Ba nasiha na ce kayi mini ba, tambayata zaka amsa mini, damuwar me, ka yi mini bayani ina rumaisa take?”

Tamkar an ritsa ɗan lami da bindiga ya ce “Umar wallahi ‘yan bindiga sun tafi da rumaisa, kuma ba da ita kaɗai suka tafi ba, amma an sanar da jami’an tsaro za su yi ƙoƙari a kai, za abi bayansu”

Cikin tashin hankali ya ce “Ya isa haka ɗanlami, amma kun san garin nan babu cikakken tsaro kuka tura yarinyar nan? Babu yadda ba ayi ba a kan gwaggo ta bayar da yarinyar nan a dawo da ita gida amma taƙi, ta turata in da ta san babu tsaro, duk yadda ake ciki ku san yadda zaku yi, ni ban san wata magana ba kawai an haɗa baki da ku an yi garkuwa da yarinya ku san yadda zaku yi”.

Ɗanlami zai yi magana, mai sunan Baba ya kashe wayar ya cillar ya fice a fusace dan gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai da tashin hankali.

Mama ce ta fito tsakar gida ta na faɗin “Wai babana shi da wa yake ɗaga murya, me kuka yi masa ne yake ta magana sama-sama?”

Cikin sanyin jiki Usman ya ce “Saɓani ne aka samu, kin san halinsa da zuciya da saurin fushi”

Mama ta ce “A’a ai kuwa bai fiye yin magana ba, sai an ƙure shi, wani abun dai ku ka yi masa, ko kuma faɗa kuke a tsakanin ku” gani tayi sun jeru basu ce mata komai ba, sai dai fuskokinsu ɗauke da damuwa, kamar a firgice suke.

Ta dubi Aliyu da kyau ta ce “Gadanga wai menene, na ganku duk wani iri me yake faruwa ne, ko akwai wata matsala ne?”

Aliyu ya dake ya ce “Babu komai mama, ni bari na fita zan sayo omo na yi wanki”.

“Ban da omon da babana ya sayo shekaranjiya ya shigo da shi kaya guda, kusan kayan, wane omon kuma ka ke nema ko ka manta ne?”

Ya dafe kai ya ce “Ohh na manta, aski zani, ai na manta shaf da Oman ne, idan na dawo daga askin sai na yi wankin” yana yin maganar yayi waje, Usman ya rufa masa baya.

Gaba ɗaya mama ta kasa gane kansu, kuma ba wanda yayi mata bayanin wani abu. Kawai ta share ta cigaba da sabgoginta.

Duk yadda usman ya so dakewa abu ya gagara, a soro ya durƙusa ya fashe da kuka, shi ya riga ya karaya ya san ubangijin da ya halicci ruma ne kawai zai fitar da ita.

Aliyu ya rungumo shi ya ce “Haba usyy so ka ke sai mama ta gane ne? Dan Allah ka jure kan mu san abin yi, kar mu bari ta gano akwai matsala idam ta gane, ka san tana da hawan jini, yanzu zai iya tashi”

Usman ya ce “Wane abun yi da me zamu karɓota? Me muke da shi? Mutanen da ba imani ne da su ba, ‘ya mace ce fa, Allah kaɗai ya san me zasu yi mata, gara ace mutuwa ta yi ga gawarta da wannan tashin hankalin, wa zai kula da ita?”.

Aliyu da tasa zuciyar ma ke daf da karyewa ya ce “Na sani, amma addu’a ba ta bar komai ba Usman ita zamu dagewa, kayi haƙuri tashi ka daina kuka kar mama ta zo ta samemu” haka yayi ta rarrashin Usman.

Mai sunan baba kuwa ji yayi duniyar ta yi masa zafi, ina ma shi aka ɗauka aka bar ruma. Yaya mama za ta ji idan ta samu labarin an yi garkuwa da rumaisa?.

Zuciyarsa ta din ga zafi yana jin da zai ga gwaggo sai yayi mata rashin mutuncin da bata taɓa tunani ba, dan yana jin zai iya mangareta dan duk ita ta janyo wannan masifar, duk da tana ƙanwar mahaifinsu, cewar da aka yi tana gadon asibiti jininta ya hau bai dameshi ba, dan da jinin tasa uwar ya hau ko wani abu ya samu ruma, gara duk abin da zai faru ya faru.

***

Zuwan takawa a Abuja a wannan karon ya sanya ya samu abubuwa masu muhimmanci da bincikensa bai kai masa ba a baya, sai dai zuciyarsa na ta azalzalarsa a kan lallai ya koma gida, jinsa yake tamkar a kan wuta, idan bai bar garin ba kamar wani mummunan abu zai faru da shi, dan haka babu shiri, ya tattara kayansa ya taho Kano, dama ga Ammi na ta waya dan duk a tsorace take, saboda yanayin jikinsa, Jabir ma duk ya addabeshi a kan nan kano ma akwai aiki, dan haka ya haɗa kayansa ya koma kano.

Sai ka ce a wannan karon ya fara tafiye-tafiye, Ammi sai hamdala take a kan dawowarsa gida lafiya, dan ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da yayi tafiyar nan dan sam ji ta yi ba ta son tafiyar ta sa.

A gidan Turaki suka haɗu, da takawa, da Jabir da kuma Jamil da ya kasance wa ga Samha kuma cousin ɗin sa.

Hira suke yi sosai, suna tattaunawa a kan rayuwa.

Jamil ya zunguri Takawa ya ce “Kai, wai me kake nufi da ni ne, ba fa ka taka gidana ba, ranar da na tare ma ko rakiya ba ka yi mini ba, kuma ba ka zo ba sai harkokinka kawai kake”

Ɗan shiru Adam yayi, tun daga lokacin da ya ji muryar ruma a ranar ya rasa nutsuwarsa, kilisar ma da ƙyar aka ƙarasata da shi, tunani ya fara yi ko zuwa unguwar su zai yi.

‘Ka je ka yi mata me?’ wata zuciyar ta tambayeshi.

Tsaki yayi wanda ya fito fili bai sani ba.

“Tsakin me kake kuma?” Adam ya tambaye shi.

Girgiza kai yayi bai ce komai ba.

Jabir ya ce “Yauwwa Takawa, ina mutuniyarka kuwa wannan yarinyar?”

Haɗe rai Adam yayi tare da basarwa, Jamil ya ce “Wace yarinyar, budurwa yayi ne? Kai ka isa ka yi wa ƙanwata kishiya?”

Jabir ya ce “To bana ce ba, wata ‘yar figigiyar yarinya ce mai kama da bainu, ban taɓa ganin yarinya mara mutunci da rashin tsoro irinta ba”.

Adam a ransa ya ce “Ai ba ka san mara mutunci ba, sai ka ga wasiƙar da ta rubuta mini’ amma a zahiri yayi shiru kamar ba da shi suke hirar ba.

***

“Ina sonka Adam, so bana wasa ba, so mai tsananin gaske son da nake jin zan iya komai domin na mallake ka, duk da na rasa dalilin da ya sanya bana gabanka, ko da yake ba rasa dalili na yi ba, nafi kowa sanin dalilin da yasa bana gabanka, kuma ina daf da magance komai domin in samu miƙaƙƙiyar hanya ɗoɗar ta cimma muradina na rayuwa da kai, ko baka aureni ba ina son kasancewa da kai na rayu ƙarƙashin kulawarka. Ban sani ba ko zuwa nan gaba asirina ya tonu duk da bana tunanin faruwar hakan, amma idan ma ya farun ka yi mini uzuri soyayyar ka ce ta janyo mini hakan” tamkar taɓaɓɓiya haka samha ta saka hoton Adam a gaba ta na surutu, hoton yana sanye da kaya ne na sarauta, ya ɗan sauke rawaninsa yana murmushi, wanda aka ɗauka da hawan wata salla.

Sai da ta gama soki burutsunta, ta mayar da hoton ma’ajiyarsa, ta tashi ta ƙarasa shirinta ta fice.

Mummy ce tare da aminiyarta zaune a ƙuryar ɗakin Mummy suna tattaunawa.

“Wai hajiya Lubabatu babu wani zazzafan malami ne, abubuwa kamar sun tsaya mini, sun ƙi cigaba kamar yadda nake so”.

“Haba Jamila, ke kin san an daɗe muna haƙa rijiya, rijiyar da muke saka ran samun ruwa a kowane lokaci, mun shirin da idan balli ya tashi akwai rikici, ke dai mu cigaba da haƙuri”.

Mummy ta girgiza kai ta ce “Ya ci ace burina ya gama cika, nifa da dai da mintuna biyar bana son ruhin Binta ya kasance cikin kwanciyar hankali da farinciki, so nake ta dauwwama a baƙin ciki har ƙarshen rayuwarta”.

Dariya Hajiya Lubabatu ta yi ta ce “Haba Jamila, ai ko a haka kika barta wallahi ta yabawa aya zaƙinta, kuma ta ɗanɗana kuɗarta, amma ki cigaba da haƙuri ai mun ɗana tarko daban-daban”.

Mummy ta jinjina kai ta ce “Shikenan, bari mu ga zuwa yaushe, na cigaba da sanya musu ido, duk wani motsinsu uwani na gaya mini, kuma na ce lallai ta kawo mini maganin da waccan ‘yar tsintuwar ke shafa masa”.

“To shikenan, to bari mu ga yadda abubuwa zasu kaya”.

***

Har azahar babu wanda ya kula su ruma, masu kuka na yi masu addu’a na yi, ga yunwa ta addabeta a gida wataran ƙarfe bakwai ta karya, amma har bayan azahar babu wanda ya kulasu balle ya basu wani abu.

Tashi ruma ta yi ta samu ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ta ce “Bawan Allah yunwa nake ji, ku bani abinci na ci”

Wani mugun kallo ya yi wa ruma ya ce “Zo ki cinyeni, an gaya miki nan wurin hutu ne da jin daɗi?”.

“Ai ni ba mayya bace da zan cinyeka, idan ma cin ne ban ga abin ci a nan ba, idan ba za a bamu abinci ba meyasa zaku kawo mu nan?” Ta na rufe baki yana hankaɗeta sai dai faɗi ƙasa ya saita ta da bindiga “Idan ki ka yi mini hauka, yanzu na lahira zasu yi maraba da ke”.

Ruma ta kalli yadda ta faɗi ƙasa, wata irin zuciya ta harziƙota ta miƙe tsaye ta sake kallonsa ta ce “Na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, ai daɗinta idan ka kasheni ba a wuta zaka sakani ko aljanna ba, hisabi na Allah ne, to na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, harbeni maza kai kuma a ƙara maka kwanakinka a duniya”

Babu alamar tsoro ko shakka a tare da ruma, kowa sai da ya Zubo mata ido, saboda ƙarfin halinta.

A fusace ya tashi yayi kan ruma, amma wani ya riƙe shi, ya ce kar ka kuskura, ƙyaleta idan ka yi mata wani abun za’a iya samun matsala, ka bari oga ya zo ya faɗi ya za ayi”.

Huci ya din ga yi yaso ya tattaka ruma, ko ya keta mata haddi a gaban mutanen wurin, ya kawo ƙarshen harshenta.

“Ni baka kyauta mini ba da baka bari ya kasheni na huta ba”

“Wato ke dai bakinki ba zai mutu ba ko?”

“Idan har so ku ke na yi shiru, to ku kasheni ko ku mayar da ni gidanmu, wannan ai zalunci ne ni yunwa nake ji” tayi maganar tana share hawaye.

Dattijon nan ne dai na jiya ya ce “Yarinya ki yi shiru da bakinki, kar su citar da ke, wannan mutanen ba ayi musu haka”.

“To ni yunwa nake ji” tayi maganar har cikin zuciyarta.

Duk wani kurari da zare ido ruma taƙi yin shiru, kamar ma da gayya take yi dan ta tunzurasu su yi mata abin da za su yi mata.

***

Har dare mama ba ta san abin da ya faru ba, kuma an rasa wanda zai gaya mata, sai mita take musu cewar ita fa ta kasa haƙuri ta kira gwaggo idan an dawo da ruma ta haɗata da ita, amma wayar gwaggon ba ta shiga. Sun yi mamaki da duk jin rediyon mama ba ta ji batun kai harin ba.

Ganin tana ta surutu ita kaɗai ba wanda ya tanka mata, ya sanya ta magantu “Wai ba zaku gaya mini meke faruwa ba ne? Duk cikinku fa yau babu wanda ya ci abinci, kun ƙi walwala kun ƙi magana, kuma kun ƙi gaya mini menene?”

Usman ne ya tashi ya ce “Mama sai da safe, ni dai bana jin daɗi ne”.

Babu wanda ya bawa mama amsa, a hankali duk suka watse daga tsakar gidan, mama ta sha jinin jikinta ta fara tunanin menene ya faru haka, da basa son gaya mata?.

Babu wanda ya saurari su ruma sai bayan la’asar, aka zo da wasu kuloli a kan babur, aka rarraba musu wata busashshiyar gurasa, gaya guda ɗai-ɗai, sai pure water ɗaya tamkar mabarata.

Ruma ta kalli gurasar nan, duk uwar yunwar da take ji, amma a rasa me za a bata sai wannan takurarriyar abar a bushe, babu mai babu komai a jiki.

Gashi duk ta bushe kamar ƙanzo.

Ruma ta gasta ta fara ƙoƙarin haɗiya, amma ta kasa haɗiyewa, da ƙyar ta dannata da ruwa, daga gutsura ɗayar nan ba ta ƙara ba ta shanye ruwanta ta yar da ledar, sauran kuwa tuni kowa ya kama gurasar nan suka cinye.

***

Duk wata tattaunawa su Usman da sauran ‘yan uwansa sun yi, amma sun rasa ta ina zasu ɓullowa lamarin, duk in da zasu buga sun yi, amma babu wani labari game da in da su ruma suke, gashi da wani ya ce zai je katsinan mama za ta gano akwai abin da yake faruwa, dan a yanzu haka ma duk ta tsargu, mussaman yadda suka daina walwala ga kuma ta fara shiga damuwa rashin shigar wayar gwaggo.

Su huzaifa ma sun gano abin da yake faruwa, sai dai yanayin ruɗewa da Huzaifa da Yasir suka yi, ya sanya mama cigaba da jefa musu zargi da kuma kokwanto.

Yau ƙarfe tara na safe taga duk sun fito daga ɗakinsu sun jeru a tsakar gida, kamae kullum babu wanda yake walwala a cikinsu, kuma babu mai sunan Baba a cikinsu.

Mama ta girgiza kai ta ce “Koma menene Allah yayi muku maganinss, tunda ni dai ina tsakaninku ba zaku gaya mini ba”.

Ta fito daga banɗaki kenan, Abubakar yayi sallama ya shigo da jakarsa ta makaranta, sai dai kallo ɗaya tayi masa shima ta ga tsananin tashin hankali a fuskarsa.

Mama tayi saroro tana kallonsa, cikin ƙarfin hali ta ce masa “Kai kuma me ya dawo da kai yanzu?”

Suka haɗa ido da Aliyu, Aliyu ya sunkuyar da kai, Yasir kuma ya hau goge hawaye.

“Saddiƙu, dan Allah kai ka gaya mini menene? Ku daina ɓoye mini koma menene, na kasa nutsuwa sun ƙi su gaya mini abin da yake faruwa, na rasa gane kansu, dama har akwai abin da ban cancanci in sani ba?”

Abubakar ya ajiye jakarsa ya kamo hannun mama ya ce “Mu je ɗaki mama sai mu yi magana”

Mama ta buge hannunsa ta ce “Ba in da zani, ku yi ta riƙe abin ku a cikinku nima bana son ji, idan abin da bana ƙauna a rayuwata bai wuce ganin fuskokin da ba sa son damuwata in gansu cikin damuwa ba, ko ba zan maganta muku ba ai na yi addu’a” ta juya za ta wuce ɗakinta.

“Mama ruma ce” ya furta a hankali, cak mama ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, ta ji maganar ta sa kamar bai faɗeta dai-dai ba.

Ba tare da ta waiwayo ba ta ce “Mutuwa ta yi?”

“An yi garkuwa da ita, a garin su Iya, a cikin harin da aka kai ƙauyen har da ita aka ɗauka”.

Innalillahi wa Innalillahi raji’un, mama za ta iya cewa ko mutuwar iyayenta ba ta girgizata kamar wannan abu da ta ji yanzu ba, ji ta yi kamar ba a hayyacinta ta ji maganar ba, tamkar an mata yayyafin wuta, Rumaisa a hannun ‘yan biniga, gara ace kashe mata ita suka yi, ta tura a ɗauko mata gawarta, amma ruma ‘ya mace ƙarama a hannunsu a tsakiyar dajin Allah, Allah kaɗai ya san me za su yi mata, ga halin ruma da ta sani na rashin kunya da surutun tsiya, tsaf za su illata ta.

Jikin mama ne ya hau rawa, ta sake ƙare musu kallo, Huzaifa da Yasir suna ta kuka, Aliyu kuma ya sunkuyar da kai, haka Abdallah, Usmsn kuwa barin tsakar gidan ya yi, babu mai sunan Baba ko ba a gaya mata ba ya tafi katsinan ne.

Ta yinƙura da niyyar ɗaga ƙafarta, ta tafi luuu gaba ɗaya suka yi kanta suna kiran sunanta

Sosai suke girgiza mama, amma ko motsi ba ta yi, a gigice Abdallah ya ɗebo ruwa ya din ga shafa mata a fuskarta Usman ya ɗauko mafici yana yi mata fifita.

Aliyu ya kalli Usman ya c “Usman wani ya je ya samo napep mu kaita asibiti da sauri”.

Usman ya ce “Ko nan da zaure ba zan iya fita gani nake komai zai iya faruwa kan na dawo, sai dai ko su Yasir”.

Yasir da yake riƙe da hannun mama ya ƙara ƙanƙame hannun, ya ƙi tashi yana kuka.

A hankali mama ta yi tari, ta fara motsawa tana Innalillahi wa Innalillahi raji’un. Babban fatanta Allah ya sa idan ta buɗe idanunta ace mata mafarki take yi.

Sai dai tana buɗe ido ta kalli fuskokin su Huzaifa, hakan ya tabbatar mata a zahiri ne, ruma an yi garkuwa da ita.

Sannu suka din ga jerwa mama, amma ta kasa amsa musu, a hankali ta ce “Ku kira babana, dan Allah ya juyo gida kar ya je, mu bar wa Allah komai”.

“Amma mama meyasa?”

“Kar yaje ya tayar musu da hankali ko shi ma wani abun ya same shi, zuwan nasa babu abin da zai ƙara ku kira mini shi a waya, ya dawo gida dan Allah”.

Jiki a sanyaye Abubakar ya janyo wayarsa a aljihunsa ya kira lambar Umar.

Mai sunan Baba na ɗagawa Abubakar ya ce “Akhi mama ta ce ka dawo gida, bata yarda ka je ba?”

A hasale Umar ya ce “A kan me zaku gaya mata, kun san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba dan me za a gaya mata? Wannan ai ba yi ba ne, idan wani abu ya sameta fa?”

Shima Abubakar da zuciyarsa ke a kusa ya hayayyƙo masa “Kai saurara ni ka ke wa shouting? Da wanne zan ji ne? Har zuwa yaushe zamu cigaba da ɓoye mata. zamu dawo mata da rumaisa ne idan bamu gaya mata ba? zaka din ga yi mini hayaniya kai kaɗai kake cikin damuwar ne? Duk ta shiga damuwa ba mai cin abinci kowa baya walwala kuma an ƙi sanar mata abin da ke faruwa, zuwa yaushe za a cigaba da ɓoye mata, idan ka ga dama ka dawo idan ba ka ga dama ka je ka yi abin da ka ga dama”

Umar yayi wa ɗan uwansa uzuri, damuwa ce ta sanya ya sauke masa, dan Sadik ba dai haƙuri ba. Suna gama wayar Abubakar yayi cilli da wayar zai tashi mama ta riƙe shi.

Cikin tawakalli da ƙarfin hali ta ce “Yi haƙuri, kar ka yi fushi dan Allah, ka lallaɓo mini shi ya dawo ka san halinsa”

Abubakar yayi ajiyar zuciya zai yi magana wayar mama ta fara ringing a ɗaki, Yasir ya je ya ɗauko, mai sunan Baba ne yake kira.

Mama ta karɓa da sauri ta kara a kunnenta ta ce “Babana dan Allah ka dawo gida” tayi maganar muryarta na rawa.

“Ki yi haƙuri mama, daga sallar asuba na wuce, ina Katsina yanzu haka na kusa ƙarasawa ki yi haƙuri ba abin da za zan aikata, zan je wurin jami’an tsaro ne, ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta dawo lafiya “.

“To” kawai mama ta ce ta saki wayar, tana wata irin ajiyar zuciya, zuciyarta sai wani irin zafi take yi mata, amma idonta ya bushe babu hawaye.

Su ruma kuwa yau kwana na huɗu kenan suna hannun ‘yan bindiga, ba wanka ba wanki, ga azabar yunwa ruma ba ta iya cin abin da ake bata, ruwan nan ɗaya idan an basu da shi take sha idan tana jin fitsari ta yi. Duk azabar kashi irin na ruma, ta matse abin ta ba ta yi.

Tun da ruma take ba ta taɓa kawo tsintar kanta a irin wannan halin ba.

Ga duka da wasu lokutan ake yi wa wasu, duk da ita babu wanda ya taɓa dukanta, amma ana dukan wasu ciki har da mata, ‘yan bindiga su dake su su taka su da ƙafa.

Wani tarihi ruma ta tuna da aka taɓa basu a islamiyya, a rayuwarta tana son malaman da suke basu tarihi, dan duk abin da take zata nutsu ta saurara.

Akwai ranar da malamin yayi musu tarihin Annabi yunus da kifi ya haɗiye shi, ya karanta *La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*

Har ruma ta ce “Kai malam amma kifin da ya haɗiye annabi yunus, dai yayi girman duniyar nan?”

Malamin ya yi murmushi ya ce “Meyasa ki ka ce haka? Kin san girman duniya kuwa?”

“To ai malam kifin da inuwa mai kifi yake sayarwa, da wanda ake talla ko ɗan tsako ba zasu iya haɗiya ba, amma na ji ka ce kifi ya haɗiye mutum”

“Kifi ne dai babba ruma, amma ba kamar girman duniya ba, kuma ba a gaya mana girman kifin ba a Alqur’ani, abin da nake son ki riƙe yanzu shi ne, falalar wannan addu’a da annabi yunus Alaihissalam ya karanta, a duk lokacin da kika shiga wani mawuyacin hali, ko ki ka shiga hannun wasu azzalumai to kema ki karanta Addu’ar da Annabi yunus Alaihissalam ya karanta *La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*”

“To malam, in Allah ya yarda zan din ga yi, to wace addu’a zan yi idan na yi wa mama laifi kar ta yi mini faɗa ko ta saka mai sunan Baba ya sakani kama kunne?” Jik tambayar da ta yi, ya sanya ‘yan ajin suka kwashe da dariya.

“A’a ai dole idan ki ka yi laifi ayi miki faɗa ko a hukunta ki, amma a duk lokacin da kike fargabar haɗuwa da wani, mugu ko maƙiyi sai ki karanta *Allahumma inni as’aluka min nuhurihim, wa’auzubika min shuriruhim*”

Ko da ruma ta tuna da wannan tarihin da malaminsu ya yi musu sai ta fara nanata “*La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*”

Ihun wata mata ne ya sanya ruma waiwayawa taga ko dukan na ta ake, amma taga ɗaya daga cikin mutanen yana jan ta tana ihu, tana a taimaka mata. Babu wanda ya tanka mata mutumin yayi cikin dajin da ita.

Ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya ce “Ai gara hakan, tun da ‘yar matsiyata ce ba za su biyan kuɗin da aka ce su karɓeta ba”.

Kusan awa biyu mutumin ya dawo ba tare da ita ba.

Ta ji wasu a kusa da ita suna magana ƙasa-ƙasa “Innalillahi, ita ma sun mata fyaɗe sun kasheta” Ruma ji tayi kamar ta tambayesu meye fyaɗe, tunowa tayi lokacin da take tambayar mama meye fyaɗe su Aliyu suka din ga hantararta.

A take ta fashe da kuka, saboda yadda take kewar gida, duk suka juyo suka kalleta.

“Ke meye haka?”

“Mama” ta faɗa cikin kuka.

“Yi mana shiru ko in taka ruwan cikinki”

“Wallahi ba zan yi shiru ba, wayyo Allah mama yaya Aliyu yaya usy dan Allah ku zo ku ɗaukeni zan mutu, wayyo Allahna” kuka take sosai kamar wadda wani iftila’in ya afkawa.

Wata mata ce ta din ga rarrashin ruma tana bata haƙuri da ƙyar ta yi shiru, ta cigaba da nanata addu’ar nan.

Mai sunan Baba kuwa yadda yaje ya tarar da gwaggo ne ya sanya jikinsa yin sanyi, ya tarar iya ma tana asibitin ita da mijinta, gwaggo sai kuka take ba ta ko cin abinci, likitoci na ta fama jininta ya sauka abu ya gagara, saboda yadda ta addabi kanta.

Tana ganin mai sunan Baba ta sake rushewa da kuka, “Dan girman Allah ku yi haƙuri, ku yafe mini umaru ban zaci abin zai kasance a haka ba, tsananin ƙaunar da nake yi wa ɗan uwana ce na mayar kanku, ban yi hakan dan baƙanta muku ba, son da nake wa ruma ya sanya na hanata, da na san haka za ta faru da ba zan ce ma azo da ita ba, ku yafe mini dan Allah” gaba ɗaya suka fashe da kuka, har su iya da su Lawisa da aka sace ruma a gabansu.

Ganin yadda dattijuwar ke cikin tashin hankali ita da iyalanta ya sanya ya ji duk jikinsa yayi sanyi, idan ya ce zai ɗaga musu hankali bai yi musu adalci ba, tun da suma ba da son ransu hakan ya faru ba.

Ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon gwaggo sannan ya ce “Ki daina kuka, ko dan saboda a samu jininki ya sauka, yanzu ya ake ciki an sanar da jami’an tsaro ne ko kuwa ya ake ciki?”

Dagaci ya ce “Ka san garin namu, jami’an tsaro ba su fiye bamu agaji ba, mu da su mutanen muke yin sulhu, duk abin da muka saka jami’an tsaro wata ɓarnar suke yi mana, amma dai saboda ita rumaisan mun sanar da jami’an tsaro, amma sun ce mu jira abin da ‘yan bindigar suka ce sai a sanar musu, muna nan muna jira haryanzu dai ba su yi mana aike ba”.

Mai sunan Baba yayi shiru ya ma rasa abin da zai ce, ƙarshe ya yanke shawarar a kai shi wurin ‘yan sandan domin ya ji meye abin yi.

Ɗanlami ya ɗauki mai sunan Baba suka tafi, sai dai daga ƙauyen da aka sace su ruma zuwa wurin ‘yan sandan uwar tafiya ce mai zaman kanta, da ko menene zai samu ‘yan garin ba lallai su samu ɗaukin jami’an tsaro.

Ganin girma da kwarjini da kuma ganin cewa Umar ba ɗan garin bame ya sanya DPO garin tsayawa ya saurare shi.

“To ɗan uwa idan zan baka shawara ka koma gida kawai ku yi addu’a, bin bayan mutanen nan aikin sojoji ne bana ‘yan sanda ba, mu mun yi iya namu ƙoƙarin, sai dai mun bar sallahun idan sun yi wata magana a sanar mana, haryanzu dai ba su ce komai ba”

Shiru kawai mai sunan Baba yayi, ba zaka ƙara sanin lamarin tsaron ƙasarmu ya taɓarɓare ba sai wani iftila’i ya afka maka.

Ba tare da samo wata mafita ba, mai sunan Baba ya kamo hanyar kano.

Gidansu ruma kuwa tamkar an yi mutuwa, ko magana mai sauti ba sa iya yi, tun da mama ta ɗan samu ƙwarin jikinta ta hau sallaya, canza alwala ce kawai take ɗagata, yunwa kuwa ko jinta ba ta yi.

Ba yadda ba su yi da mama ba a kan ta ci abinci, ta ce su ƙyaleta kawai.

Ko da ta ji sallamar mai sunan Baba, ji ta yi kamar zai ce mata ga ruma nan ya dawo mata da ita, amma ko da ya shiga ɗakinta ta kalleshi ta ganshi shikaɗai, sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta ji zuciyarta ne neman karyewa.

Ya ƙarasa gaban mama ya zauna, su Abdallah duk suka zubo masa ido, amma ya rasa ta ina zai fara yi musu bayani.

Mama ta sake ɗaga kai ta kalli ta mai sunan Baba, ya girgiza mata kai ya ce “A dage a cigaba da Addu’a kawai”

Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mama ta sauke, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

Huzaifa ya fashe da kuka, Yasir ma ya taya shi.

Cikin dakiya mai sunan Baba ya haɗe rai ya ce “Meye haka kamar wanda ba su je islamiyya ba, ba ku yi imani da ƙaddara bane? Yanzu kuka ne ya kamace ku ko kuma addu’a?” Haka ya din ga yi musu faɗa alhalin shima da zai samu space kukan zai yi. Ya tashi fuuu ya tafi ɗakinsu, yana zuwa ya tarar da Abubakar a zaune yayi shiru ya lula duniyar tunani.

Mai sunan Baba ya zauna a kusa da shi, ya ce “Akhi na dawo?”

Banza yaya Abubakar ya yi masa bai kula shi ba.

“Na san na yi maka laifi, amma yakamata ka yi mini uzuri, ba a hayyacina nake ba, idan ka gama fushin sai mu yi magana” ya yinƙura zai tashi Abubakar ya ce “Yaya ku ka yi da ka je, an samu labarinsu?”

“Babu wani labari mai daɗin ji, sai ma kayan takaici, ance mu saurara idan sun kiramu sun ce mana wani abu shikenan sai mu sanar”.

“Idan kuma ba su kira ba a haka zata cigaba da zama a hannunsu?”

“I have no idea” mai sunan Baba ya faɗa cikin damuwa.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Aki meye abin yi?”

“Addu’a” ya bashi amsa a taƙaice.

Dare ya tsala, wasu daga cikin al’umma sun kwanta suna hutawa, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da iyalansu suke kwanan zaune, ciki har da mama da yaranta maza yayyen ruma gaba ɗaya mama ta manta da wani abu wai bacci a wannan halin da take ciki, a zaune take tamkar an dasata tun tana iya lazimin da addu’a har ta kasa ta rasa abin da ma zata ja.

Zuciyarta sai zafi take mata, da tunanin a wani hali ruma take ciki.

Wurin baccin ruma ta kalla, da yanzu tana nan mama tana faman gyara mata kwanciya ko tashinta fitsari, da yanzu ta yi ɗai-ɗai sauro na cizonta mama tana mita tana sake gyarata, ko ta ƙaro fanka idan ta fuskanci zafi yayi mata yawa, ko ta kashe fanka ta lulluɓeta idan sanyi yayi yawa.

“Ruma ko a wani hali kike? Ko kina raye? Ko kin ci abinci? Ya in da ki ke kwance? Sanin gaibu sai Allah, ya rabbilarshil azim, dan girmanka Allah ka tsare mini ‘ya ta da sauran ‘ya’yan musulmi, Allah ka dawo mini da ita cikin aminci” ta ƙarasa addu’ar kuka yana kufce mata, sai a lokacin ta ɗan ji nutsuwa da ta samu hawayen idonta ya zuba.

Ɗakin ‘yan mazan ma gaba ɗaya idonsu biyu, wasu da Alqur’ani wasu a kan sallaya, wasu suna kuka, dan basu taɓa tsintar kansu a cikin mummunan tashin hankali kamar wannan ba.

Ruma ta yi rigingine a filin Allah, wani irin sanyi yana ratsata ga cikinta kamar ya haɗe da bayanta saboda azabar yunwar da take ji, ga ƙaiƙayi da jikinta yake mata saboda rashin wanka, ga wani irin sauro na bala’i da ƙwari suna gasa mata cizo.

A hankali ta furta “Mama, mai sunan Baba” sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zirarowa ta gefen idonta.

Tana tsaka da tunanin, wurin yayi tsit, mutanen sai kewayasu suke yi da manyan bindigogi.

Wani irin sauti ruma ta din ga jiyowa na motoci ƙasa-ƙasa, daga bayan dutsen da ke nesa da su.

“Sha tara ga motocin smoke can suna aiki fa” cewar ɗaya daga cikin ‘yan bindigar.

” ‘yan wahala ba, ni mamaki nake yadda suke iya fitar da sabgar nan ba wata matsala” ɗayan ya bashi amsa.

“Haba, sun gama sai ta komai nake gaya maka, babu wanda ya isa ya tare musu hanya, babban controller na ƙasa ma fa nasu ne, kuma akwai na sa kason a ciki mu suka mayar ‘yan iska kawai”.

Sha tara ya ce “Aikuwa sai mu yi tawaye, ko dai su yi wani abu a kai ko mu bujure, haba ma’adanan nan fa da suke kwasa ba dan muna gyara musu aikin nan ba da ba zai yiwu ba, amma kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi”.

“Kai ni ba wannan ba ma, oga nake jira ya zo ayi wadda za ayi a san yadda za ayi da mutanen nan”

“Eh gobe zasu shigo ai”

Haka suka cigaba da hirarsu, amma kan ruma ya ɗaure, wasu ma’adanai ake kwasa meye ma ma’adanan?

“Zan yi fitsari” ta faɗa cikin rawar murya”.

“Yi a nan” ɗayan ya bata amsa.

“Ina jin yunwa ma”

“Idan ki ka kuma magana sai na taka ruwan cikinki”

Guntun tsaki ruma ta yi, tayi juyi wani abu da ba ta san menene ba gasa mata cizo, wata uwar ƙara ta saki, ta miƙe tana kuka.

“Wai wannan wace irin iblishiyar yarinya ce meye kuma?”

“Wani abu ne ya cijeni” ta yi maganar a gigice tana soshe-soshe.

“Nemi wuri ki zauna ki rufewa mutane baki, ni wallahi da oga ya zo da na daɗe da harbe wannan shegiyar yarinyar da ba ta rasa matsala”.

“To ku mayar da ni in da kuka ɗauko ni mana, meyasa zaku kawo ni nan” tayi maganar a sangarce

Hasketa ɗayan yayi da hasken fitila, ta saka hannu ta kare tana motsa baki, saukar wani abu ta ji a goshinta mai nauyin tsiya, daga haka ba ta sake sanin in da kanta yake ba.

Bayan sallar asuba, su Abdallah suka sanar da abin da yake faruwa a masallaci, tare da roƙon bayin Allah su taya su da addu’a, Allah ya fito da rumaisa cikin aminci da ƙoshin lafiya.

Mutane da yawa sun kaɗu da jin abun da ya samu ruma, dan ruma ta mutane ce, da yawan mutane sun santa, kan gari ya gama haske unguwar su ta cika da labarin yin garkuwa da ruma.

Gari na gama yin haske aka din ga sintirin zuwa yi wa mama jaje, tare da addu’ar Allah ya bayyana ta.

Mama duk yadda ta so ta jure, ta kasa haka ta dinga share hawaye, masu cewa ta daina kuka kuwa kallonsu kawai take yi, gani take ba su san a cikin tashin hankalin da take ba ne.

Hatta daga islamiyya su ruma haka aka yi tawaga guda, suks zo yi wa mama jaje suka gabatar da Adduoi, tare da yi wa mama alƙawarin za su cigaba da addu’a da karatun Alqur’ani har zuwa lokacin da Allah zai bayyana rumaisa.

Rumaisa kuwa a hankali ta motsa, ta fara ƙoƙarin buɗe idonta, amma ta ji goshinta yana mata zafi, a hankali ta kai hannu goshin ta ji ya kumbura, ga busashshen jini ta shafo.

Cikin ƙarfin hali ta tashi zaune, sai dai wani irin jiri ne yake ɗaukarta, saboda azabar yunwa, ga zafin dukan da aka mata da bakin bindiga.

Wani narkeken mutum ta gani, yana zagaya su, yana ƙare musu kallo.

“Ke a ina aka ɗaukko ki?” Yayi mata maganar cikin tsawa. Ba ta kai ga bashi amsa ba, ta ga mutumin da ta bawa gyaɗa a kasuwa.

Yayi saurin kawar da kansa da ga kallon ruma.

“Ke ya ina miki magana kin mini shiru?” Yayi maganar cikin muryarsa mara daɗin ji.

Gefe guda ta ja, ta tanƙwashe ƙafarta, tana jin yadda take jan numfashi da ƙyar.

A fusace ya saka hannu ya fizgo ruma, amma ta taƙarƙare iya ƙarfinta ta fizge hannunta ta ja da baya tana huci. Kallon kallo suka shiga yi, tsakanin shi da rumaisa.

Yinƙurawa yayi zai maketa, mutumin nan ya shiga tsakaninsu, ya ce “Yi haƙuri, yarinya ce”

“Ban gane yarinya ba, bani bindiga kasheta zan yi”

Ya girgiza masa kai ya ce “A’a, da alama ubanta wani ne, za a samu kuɗi a hannunsu, ka bari mu karɓa sai a kasheta”.

“Ni bani da uba” tayi maganar cikin ƙwarin gwiwa.

“Ina magana kina saka baki? Zan ƙyaleshi ya kashe ki” da ƙyar ya shawo kan mutumin ya ƙyale ruma.

Ya ɗauki wata leda ya jefa mata, buredi ne a ciki sai ruwan pure water. Tamkar ta shekara ba ta ci ba, haka ta dirarwa buredin nan, tana ci tana yinƙurin amai.

Tana zaune tana cin abincinta, tana kallon yadda ake karɓar lambobin waɗanda aka ɗauko su tare, ana cinikin nawa za a biya a karɓesu kamar wasu dealer kaya.

Mutumin nan dai na ɗazu, ya zo kan ruma ya ce “Bani lambar babanki”.

“Dama ana zuwa kabari da waya?”ta tambayeshi.

“Kamar yaya?”

“Na gaya maka bani da uba ya mutu ai”

“Bani lambar wani ɗan gidanku”

Rumaisa ta ce “Ka ga nifa gidanmu in dai kuɗi zaka ce musu su kawo, basu da shi,  sai dai ku yi mini abin da zaku yi mini”

Ya ƙare mata kallo ya ce “Haka ki ka ce?”

“Eh”

Ya miƙe tsaye ya ce “Biyoni”.

Gaba ɗaya suka bi ruma da kallo, ita kuma ta ƙare masa kallo ta ce “in biyo ka mu je ina?”.

“Cewa ki ka yi sai dai ayi miki duk abin da za ayi miki, abinda yakamatan zan miki ai”.

Ruma ta ce “Koma mene ka yi mini a nan ba in da zani”

Mutumin da yake ta ƙoƙarin bata kariya ya fara fusata ya ce “Wai ke wace irin yarinya ce?, duk yadda za ayi a kare mutuncinki a rabu lafiya ana yi, amma ke sai ka ce baki san ciwon kanki ba, ke kin san me zai miki ɗin ne ki ka tura baki kina cewa ayi miki koma menene?”.

Cikin kuka ta ce “Ta ina kake kare mutuncin nawa, da kuka haɗamu maza da mata kuka rabo ni da ‘yan uwana, yanzu ka gama cewa a kasheni, wallahi babu in da zani daga nan, koma me zaku yi mini ku yi mini ni na gaji”

Su kansu waɗanda aka kamo su tare da ruma mamaki suke yi, yadda take rashin mutuncinta yadda ta ga dama.

Ƙaton nan ya sanya ƙafarsa iya ƙarfinsa ya taka ƙafar Rumaisa, ta riƙe kanta ta yi wata irin ƙara, ba ta warke daga waccan azabar ba ga wata ana gana mata, ji ta yi kamar ya karyata, saboda azabar da ta ji, dan ƙato ne na gaske.

Mutumin da haryanzu ba ta san sunansa ba ya ce “Ina ga daga yanzu ba zan sake magana ba, su yi miki duk abin da zasu yi miki, akwai dalilan da yasa nake baki kariya, amma tun da ke na fuskanci baki da hali, duk abin da aka yi miki ke ki ka saya, idan baki nutsu ba haka zaki ta shan baƙar wahala, kina raye amma na lahira sai yafi ki jin daɗi, ki cigaba mara kunyar banza”.

Fuska duk hawaye cike da dakiya ta ce “Eh ayi mini ɗin, ku kasheni daga nan sai me?, wallahi ba zan daina magana ba sai kun gaji kun kasheni, kuma ba lambar wanda zan bayar a gidanmu, ku da Allah ba zan yafe muku ba, ba laifin da na yi muku kuke cutar da ni, Allah ya saka mini duniya da lahira”.

Buɗe baki yayi yana kallon rumaisa, ga fuska duk busashen jini, amma sai kwaroroto take ba tare da ta na tsoron ayi mata wani abu ba.

Aikuwa ƙaton nan ya dinga takata da ƙafarsa, yana dukanta tana ihu tana “La’ila ha illa anta, subhanaka inni kuntu mina zalimin” shine kawai abin da take maimaitawa, dan idan ya takata ji take kamar ana buga mata itace, ko wani nannauyan ƙarfe.

Ɗayan kuwa yana kallo bai kuma cewa komai ba, sai da ƙaton nan yayi mai isarsa ya ƙyale ruma, ba dan ta yi shiru da bakinta ba, sai dai ihun ma da ƙyar take iya yin sa saboda ta galabaita. Haka kowa ya zura mata ido yana kallonta, duk wurin ita ce ƙarama sauran duk da girmansu, amma tafi kowa baki da rashin mutunci.

A gigice mama ta dafe ƙirjinta, hawaye na zuba daga idonta, mutane na ta bata haƙuri, amma a zuciyarta take jin kamar wani na faruwa da rumaisa, mussaman da zuciyar ta ta ta tsananta bugawa.

Idan ka ga mama sai ka zata wani ciwon tayi, duk da ba mace ce mai ƙiba dama, amma ba ramammiya bace ba, tana da kumarinta, amma lokaci guda duk ta zube sai tsawo.

Ba ta iya cin abinci sai su Abubakar sun yi da gaske, da rarrashi da ban baki, ake samu ta ɗan sha abu mai ruwa-ruwa. Duk wata walwala da ake a gidan nan suka dainata, bacci kuwa sai dai ɓarawo, babu mai iya yin sa yadda yakamata a gidan.

‘yan uwa da abokan arziki ana ta shige da fice, ana yi wa mama jaje tare da addu’a Allah ya baiyyana ruma.

Habiba ce ta faɗo gidan su rumaisa a gigice, ta din ga kallon yayyen rumaisa da mutanen da suke zazzaune, can ta hango mama, ta ƙarasa wurinta da gudu, ta zube a kan gwiwoyinta “Mama, wai da gaske an sace ruma?”

Mama ta ƙura mata ido, amma ta kasa magana.

Maƙwabciyar su ruman ce ta ce “Eh da gaske ne, yanzu ku je ku yi ta yi mata addu’a, Allah ya bayyanata cikin aminci, ya tsareta a duk in da take”.

Rushewa da kuka habiba ta yi, tana wata irin sheshsheƙar kuka, gaba ɗaya ta gigice tana wani irin kuka.

A fusace mai sunan Baba ya ce. “Dalla ku fitar mana da mai ihun nan, da wane zamu ji?”

Aliyu yayi saurin cewa “A’a ba haka yakamata ayi ba, akwai shaƙuwa a tsakanin su, bai kamata a hantareta ba”

Aliyu ya fita ya je ya samu Habiba, ta haɗa hawaye da majina tana kuka, ya tuna faɗace-faɗacensu na ƙuruciya tsakaninta da rumaisa, kullum cikin sintirin kan ƙara ake, da yadda yake zaneta ita da yayanta a kan ruma, amma yau ta tayar da hankalinta saboda ɓatan ruma.

Hannunta ya kamo ya ja ta gefe yana rarrashinta, amma babu alamar za ta yi shiru, duk jijiyon kanta sun ɗaga idonta yayi jawur saboda kuka.

“Kiyi shiri kar kanki yayi ciwo, sannan addu’a zaki taya mu, Ubangiji Allah ya bayyana mana ita, ki daina kukan, mu je na raka ki gida”

“Allah ya sa kar a kasheta, Allah ya sa ta dawo gobe” ta faɗa tana sake fashewa da kuka.

Ƙwalla ce ta cika idon Aliyu, domin kuwa dauriya kawai suke yi, ya wayance ya ce “Amin ya Allah, dan idan kin yi salla ki din ga sakata a addu’a kin ji”

Habiba ta jinjina kai, tana cigaba da share hawaye. ya saka ta a gaba ya rakata gida, amma yanayin tashin hankalin da take ciki, zai tabbatar maka da ta kaɗu sosai da ɓatan ruma.

Hauwwaliya ma da take a zaune tana jinyar karayar da ta yi kafin tafiyar runa, ita ma haka ta burkice, dan da har tana mitar ruma ta tafi ba ta zo ta dubata ba balle su yi sallama, sai labarin an yi garkuwa da rumaisa suka ji.

Hatta malamansu ruma na makarantar islamiyya da take gallaba, gaba ɗaya suka shiga damuwa, makarantar kanta kamar ana zaman makoki, saboda babu wanda bai santa ba da halinta. Ita kanta tsohuwar da take sayar da kayan yara a makarantar, da suke yawan faɗa da ruma sai da ta yi kuka, dan wataran idan sun yi faɗa wata ran suna shiryawa, dan idan ruma ta zo da abinci wataran tare suke ci, duk rashin jin ta akwai shiga rai.

Takawa yana kwance a ƙaton falonsa a kan doguwar kujera, yayi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi, abubuwa da dama sun yi masa yawa, gaba ɗaya ya rasa wace matsalar yakamata ya fara tsayawa ya nemi mafita a kai, duk matsalar da ya tunkara, sai abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa.

Wani irin zazzafan zazzaɓi ne ya kama ruma, saboda wahalar da ta sha, ga azabar cizon sauro da kuma sanyi suka haddass mata zazzaɓin.

Babu wanda yake ta tata, balle ya taimaka mata, tuni wasu aka fara bayar da kuɗin fansarsu, idan sun ga dama su bayar da mutum, idan ba su ga dama ba su karɓi kuɗin sannan su kashe mutum su ja gawar zuwa bayan wani babban dutse da yake nesa kaɗan da in da suke ajiye mutanen su yar gawar ba tare da suturta gawar ba.

Ruma na kwance ta takure tana ta rawar sanyi, ga azabar ciwon jiki, saboda dukan da ta sha, wasu mutane suka zo a kan babur, wanda aka goyo hannunsa ɗauke da ƙatuwar jaka, ta ɗaga ido dan ta ga su waye, wa za ta gani, dattijon bafullacen nan, da ta haɗu da shi har ya rakota gida a garin su Gwaggo.

Kallonsa take, amma ya kawar da kai kamar bai taɓa ganin ruma ba, ya basu jakar, shima suka bashi wata jakar ya hau babur ɗin aka bar wurin da shi. Tunani ta shiga yi a kan abubuwan da ya gaya mata, da kuma tunanin meye alaƙarsa da wannan mutanen? Kenan duk shiri ne?” Idonta ya sauka a kan lambar dake jikin jakar, sak irin lambar jakar da aka nuna mata bullet a ciki lokacin da za su zo katsina!

Guntun tsaki ta ja, a lokacin da ihun wani mutum ya dawo da ita hayyacinta, kan ta gano dalilin da ya sanya mutumin yake ihun, sai ganin abu ta yi a jikinta kamar an watso ruwa, jinin mutumin ya ɓata su an kashe shi.

Gaban ruma ne ya tsananta faɗuwa, ta ma rasa wani halin yakamata ta shiga, tashin hankali ko kuma fargaba, ga jikinta babu daɗi, ta fara fidda rai da samun mafita.

A hankali ta tashi zaune, ta ƙarasa gaban wanda ya kashe mutumin, ta kalleshi ta ce “Dan Allah nima ka kasheni”

“Saboda me zan kasheki?”

“Na gaji da zaman wurin nan, dan Allah ku kasheni nima” tayi maganar cikin magiya.

Ya kwashe da dariya ya ce “Ai ke zaki yi mana amfani,  ko zamu kasheki sai mun koya miki hankali tukuna, dan ba zaki taɓa barin hannunmu ba, an jaddada mana mu kula da ke, bakinki ba shi da linzami, ko mun karɓi kuɗin fansarki kashe ki zamu yi”.

“Idan kuma baku karɓa ba fa?” Ta tambayeshi.

Ya bata amsa da “Nan ma kasheki zamu yi”

“To ku kashe ni, dan ba wanda zai baku kuɗin fansata, bamu da kuɗi talakawa ne mu”

Dariya yayi, ya cigaba da busa sigari, ya share ruma.

***

“Daddy, ina ganin kamar yadda nace ka bar komai a hannuna, komai ya kankama, kawai mu cigaba da abin da muka saka a gaba”

Senator usman wakili ya girgiza kai ya ce “Ni fa haryanzu a raina ban gama gamsuwa da shirin nan naka ba Khalifa”

Khalifa ya gyara zama ya ce “Please Daddy, ka yarda da ni, ba zan baka kunya ba kamar yadda na yi maka alƙawari zan cika, Ni dai na riga na saka rai, bana son damar ta wuce ni”.

“Ni kaina ba zan so damar ta wuce mu ba Khalifa, amma yaron nan yana da taurin kai da nacin tsiya, bana tunanin zai ƙyalemu, ina matuƙar jin tsoron kar ya tona mana asiri”

Khalifa ya ɗan girgiza kai ya ce “Amma daddy, sauran members ɗin naku ma sun san abin da ake ciki?”

“Sun sani sarai, abin da nake tunani, akwai masu bashi goyon baya da haɗin kai a kan ya kawo ƙarshena, ba wannan ne ya fi ɗaga mini hankali ba, ina tsoron ya bankaɗo mu, dan ko last week na ji yana Abuja ku san kwanansa bakwai a can”.

Cikin damuwa da tashin hankali Khalifa ya ce “To yanzu shikenan daddy, babu wani abun yi?”

Usman wakili ya kwashe da dariya ya ce “Abun yi kai, ka zuba ido kawai yaro, babu wani abu da zai iya, muna da wani shiri a ƙasa”.

“Allah daddy, shirin menene?”

“Kar ka damu, idan ya tabatta za ka gani, kaima ka je ka cigaba da naka ƙoƙarin zan gani idan zaka iya zama magajina”

Khalifa ya yi murmushi ya ce “To shikenan daddy, ba ka da matsala da ni”

***

Iman ce zaune a falo, an saka mata lalle ja, tana ta kwaɓe fuska za ta yi kuka, wai ita ta gaji ammi sai mita take ta ce “Aikuwa kina tashi sai ranki ya ɓaci, ku kamar ba mata ba mutum yayi ta fama da ku a kan ku dinga ado”.

“Ammi fitsari fa nake ji” tayi maganar a shagwaɓe.

“Yi a nan a wanke”.

“Mhmm ammi zan yi kuka fa ya matseni”.

“Ki bari na zo na sameki a wurin nan kin cire lallen nan, ki ga yadda zan yi da ke”.

Jabir ne yayi sallama, Ammi ta amsa ya ƙarasa cikin falon yana kallon iman.

Kan nan nata babu ɗan kwali, gashin kanta sai ɗaukar ido yake ya sha mai, ta tufke shi. Haɗe rai ta yi ta kawar da kai, ya zauna suka gaisa da Ammi, daga nan ya hau zuba kamar an kunna shi, amma hankalinsa ba akan hirar da suke take ba, a kan iman take da ta basar kamar ba ta san da zamansa a wurin ba.

Ganin ba shi da niyyar tashi ne ya sanya Iman tashi, dama a iya hannu aka saka mata lallen, ta wuce ɗakinta.

Ko da ta koma ɗakin zama tayi tai shiru, tana tunanin irin balahirar da jabir zai jefata a ciki muddin ya ce yana sonta, kuma yadda yake da ammi babu abin da zai hana ammin amsawa, dan kamar ɗa shima ta ɗauke shi.

Baba uwani ce ta yi wa ammi ƙarya a kan zata je ta dawo, ammi ta bata izinin fita.

Tana fita ba ta tsaya ko ina ba, sai harabar gidan ta tabbatar da babu wanda ya ganta ta yi wuf ta faɗa sashin Mummy, ta ɓarauniyar hanyar da ta saba bi.

A ɗaki ta iske Mummy, Mummy ta dubeta cikin mamaki ta ce “Uwani, me ki ka shigo yi nan da yammacin nan sai an ganki”.

“Allah ya huci zuciyarki uwar ɗakina, Allah ya baki yawan rai, wani labari ne nake tafe da shi, ban sani ba ko zai yi daidai da abin da ki ke son ji ba”.

Mummy ta numfasa ta ce “Ina jinki”.

“Dama wani al’amari nake ta sanyawa ido, in tabattar da shi, amma ina hasashena yana daf da zama gaske, Jabir naku na gidan Galadima mai ci a yanzu, kamar shi ne yake sinsina iman, akwai alamun yana daf da cewa yana sonta”.

Wani uban tsaki Mummy ta ja, “To ni ta ina hakan ya shafeni, ni abin da na saka ki ki yi mini kenan? Ki saka mini ido ki kawo mini labari a kan abin da ya shafi ahalin gidan nan kin kawo mini maganar bare wadda ko gashi ba ta da shi a cikin gidan nan, ni ina ruwana na saka ki aikin samo mini maganin da suke yi wa wancan uban ciwon Adam amfani da shi, amma haryanzu shiru kin tsaya kawo mini shirme”

Baba uwani ta duƙa ta ce “Tuba nake, Allah ya huci zuciyarki, Allah ya sanyaya ruhinki”.

“Tashi ki bani wuri, kar ki sake zuwa in da nake idan har baki kawo mini abun da na ce ba”.

“In Allah ya yarda ba zan dawo ba sai da saƙonki, tuba nake”.

Kwanki goma kenan da sace ruma, amma babu wani labari a kan ta, tun mai sunan Baba yana buga waya ko da wani labari, har mama ta ce yayi haƙuri ya daina kiran wayar.

Shi kansa dagaci ba yadda bai yi ba ayi sulhu, su faɗi abin da suke so a basu su sako wanda suka kama, amma suka ce ba zasu bayar ba, yayi musu maganar rumaisa amma suka ce su ba zasu iya gane wata yarinya da suka ɗauka a gidansa ba.

Ruma kuwa sai gwada musu halin take na azabar taurin kai da rashin kunya, wataran ta yi borin amma sun ƙi su kasheta kamar yadda take fata, sannan suka fara yi mata horon yunwa, basu cigaba da takurata a kan sai ta bayar da lambar wanda za a kira a gidansu ba, suka ƙyaleta sai dai tana ganin azaba, idan ta ishesu da rashin mutunci, da kan bindiga suke dukanta.

Duk jikinta yayi tsami, ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ga rashin lafiya da take ta fama, wasu ko ba a kashe su ba wahala ce take kashe su a wurin, ruma ta fara sanya ran ita ma wahalar ce zata yi ajalinta.

Tun ruma na iya addu’a har ta fara sarewa, tayi kukan ta kira maman har ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido.

Tana nan kwance kamar matacciya, ta ji wani irin ƙamshin turare mai daɗin gaske ya gauraye wurin.

Wata mata ce take kuka, amma kamar iyayi matar take a cikin kukan, ruma ta ɗago da ƙyar ta kalli matar.

Tsohon ciki ne a jikin matar, duk da ruma ba ta san kan ciki ba, amma yadda cikin matar yayi girma kana gani ka san ta kusa haihuwa, matar na sanye da wani irin farin leshi mai ɗaukar ido da hankali, mai ɗauke da golden a jiki, hannunta zuwa kunnenta duk gold ne. Kai da gani ka san ba a wahala take ba, gata fara sol kamar ba ta shiga rana, sai kuka take ƙafarta na ta zubar da jini tana haki.

“Rufe mana baki, ko mu harbeki a ciki” suka yi mata tsawa toshe bakinta ta yi da hannunta ta zauna tana kuka, tana ƙarewa wurin da taken kallo.

Tausayinta ne ya kama rumaisa, ita wannan ƙaton cikin na matar ne yafi ba ta tausayi. Ita kuma ko a ina suka ɗaukota oho?.

Fatar matar duk tayi burɗun-burɗun, tayi jaa, alamar ƙwari duk sun cijeta a hanya kan su ƙaraso.

Cikin ƙarfin hali da kuka, matar ta ce “Dan Allah ku yi haƙuri, ku tausaya mini halin da nake ciki, ku sallameni, ko dan halin da nake ciki, cikina saura kwanaki kaɗan na shiga wata tara, dan girman Allah ko nawa ku ke so ku kira gidanmu, za su baku ku sake ni”.

“Ke ki rufe mana baki, ke zaki gaya mana abin da zamu yi?”

“Ba abin da zaku yi nake gaya muku ba, taimaka mini zaku yi, dan Allah ku duba halin da nake ciki”

Banza suka yi da ita suka cigaba da abin da ya dame su.

Ruma tana fama da kanta, amma sai bin matar take da kallo, ƙarshen tausayi matar ta bata. Galibin waɗanda aka ɗauko ruma da su, da waɗanda ta tarar an sallami wasu, wasu kuma an kashe su, sannan kuma kusan kullum akwai wanda mutanen za su kawo.

“Ki yi haƙuri ki daina kuka, ki yi addu’a” ruma tayi maganar cikin sanyin jiki.

Matar ta kalli ruma ta share hawayenta, ta ce “To, Allah ya kuɓutar da mu, sun kashe mini direbana ma, ya iyalinsa za su ji?” Tayi maganar cikin kuka.

Ruma a ranta ta ce “Lallai wannan ‘yar gata ce, har direba ne da ke”

A haka dare yayi, matar nan na ta kuka, abinka da farar fata ta koma jawur saboda kuka.

Suna nan a  zube a wurin kamar shara, ga wata irin iska da ake yi mai sanyin gaske, ga yunwa na damun ruma ga ciwo, dare ya tsala ruma ta kwanta ta takure, saboda yadda sanyi ya takura mata. Matar nan kuwa tana zaune tana cigaba da aikin kuka, gaba ɗaya a tsorace take da wurin sai waige-waige take, ita ma tana sake dunƙule jikinta saboda sanyin da take ji.

Idon ruma biyu tana kallon matar, a hankali ta matsa kusa da ruma zata kwanta a ƙasa, saboda ta gaji da zaman ga ɗan cikinta ya dunƙule mata wuri guda, cikinta yayi mata babu daɗi, hannunta ne ya taɓa na ruma, ta ji yadda jikin ruma ya ɗau zafi sosai, ta sake kai hannunta goshin rumaisa ta ji kamar an kunna wuta. Ta ɗan jijjiga ruma amma ba ta motsa ba.

Ta cire ɗankwalin kanta ta rufawa ruma a jikinta, ta kwanta ta miƙe ƙafafuwanta, sai dai ba aje ko ina ba, matar ta fara tari da atishawa wanda hakan ba ya rasa nasaba da sanyin da yayi mata yawa.

***

Katafaren falo ne mai girman gaske, kai kace wata fadar ce, saboda girma da tsaruwar falon, Hajiya Jamila ce zaune a kan wani lallausan carfet a ƙasa, yayin da wani babban mutum ke zaune a kan kujera.

“Ina jinki Jamila, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce?”

Ta sake duƙawa ta ce “Allah ya ja kwanan mai girman wambai, matsala kam ba za a rasata ba”.

“To Ubangiji Allah ya warware mana, meke faruwa?”

“Allah ya taimake ka, tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ƙoƙi, ƙarar giwa na kawo maka” sai kuma ta yi shiru.

Ya ce “Ina jinki”.

“Allah ya baka yawan rai, na rasa gane in da ta dosa, ban san menene a ranta game da ni da yarana ba, ‘ya’yanta ne manya, nawa ƙanana ko da kishi a tsakanin mu, ai bai kamata zumuncin yaranmu ya taɓu ba, shikenan ina son ganin su Nusaiba amma ba sa zuwa in da nake, shi kansa mai babban suna sai ya shafe wata bai taka in da nake ba, wataran tamkar zai dakeni, na rasa irin wannan abu. yaranmu ai abu ɗaya ne a ganina, amma sam yaran nan ban san kallon me suke yi mini ba, gaisuwa sai sun ga dama suke yi mini, mussaman wannan buzuwar yarinyar ni na gaji da irin wannan zaman da muke yi” ta ƙarasa maganar cikin damuwa.

Wambai ransa ya ɓaci ya ce “Shi takawan da kansa yake wannan rashin albarkar? Aikuwa albasa ba ta yi halin ruwa ba, haka ya canza hali? Har galadima mai ci yana batun zai yi murabus, mun fara tattaunawa a kan akwai yiwuwar a dawo muku da sarautarku, tun da ya kawo ƙarfi, kuma shi galadima babu lafiya, ina daf da kai maganar ga mai martaba, to a haka za a bashi mulkin yana wannan rashin ɗa’ar?”

Gaban Mummy ne ya faɗi, jin batun wambai na cewa za a dawo da sarauta gidansu a bawa Adam.

“Allah ya baka yawan rai, ni ba ziga ba, kuma ba wai ina kushewa bane ba, amma takawa ai ba zai iya jagoranci ba, ya fiye zafin zuciya da saurin fushi, abu kaɗan idan su Fauziyya suka yi masa ba ka ga cin mutunci ba, kuma kar ka manta bashi da cikakkiyar lafiya, larurar nan da yayi tun yana yaro haryanzu fa tana tashi, ai gara a bawa mahamud duk da shi ma da sauran ƙuruciya a kansa, ko a barwa Jabir kawai”

Cikin mamaki wambai ya ce “Kina nufin haryanzu takawa bai warke ba, amma ta ja bakinta tayi shiru balle a cigaba da nema masa magani? Meke damun Binta ne?”

“To ban sani ba idan ka shiga lamarin ko a samu mafita, amma takawa bai dace da sarautar nan ba ba zai iya ba, gara Mahmud amma Mahmud haryanzu hankalinsa da saura, ai gara a bawa Jabir, idan yayi murabus shine yakamata ya gaje shi”

Wambai ya ce “Wannan ba huruminki bane ba, sai abin da muka yanke, tashi kije zamu san abun yi”.

Mummy ta duƙa ta ce “Allah ya baka yawan rai, a huta lafiya” ta tashi ta bar gidan.

***

Mai sunan Baba ne yayi rigingine yana kallon saman roofing, zuciyarsa sai bugawa take yi, yana ji a ransa da ya san direction ɗin da zai nufa ya tarar da in da aka kai ruma da sai yaje ko da zai mutu a can, babban fatansa kar a lalata rayuwar ruma, gashi tun yana buga waya ya ji ya ake ciki, har ya haƙura, dan babu wani labari mai daɗi an doshi sati na biyu.

A hankali ya tashi ya buɗe ƙofar ɗakin su ya fito tsakar gida, ya ga ƙwan ɗakin mama a kunne.

A hankali ya ƙarasa ya tsaya ta window ɗakinta ya leƙa, mama na zaune ta ɗaga hannayenta sama sai zubar da hawaye take yi.

Har ya shiga ɗakin ba ta sani ba, ga furar da ya kawo mata da magariba ko taɓawa ba ta yi ba.

Motsin da ta ji ne ya sanya tayi saurin goge hawayen ta ce “Babana ba ka yi bacci ba?” Ya zauna a gabanta ya ɗan kalleta ya ce “Ba ki sha furar ba, ki yi haƙuri ki daina zama da yunwa” ba ta iya ce masa komai ba sai kallonsa da take yi.

“In ɗauko miki kofi ki sha?” Yayi maganar a hankali.

Hawaye ne ya cika idonta, ya miƙa hannu ya ɗau kofin da ya kawo mata tun a lokacin, ya tsiyaya mata ya ce “Ki sha ko kaɗan ne”

“Ba zan iya ba, na san ruma ba ta sha kamar wannan ba, kar su lalata mini ‘ya babana na fara karaya” tayi maganar tana rushewa da kuka.

Kamar zai yi kukan shima, ya dake duk da yadda zuciyarsa take masa zafi.

Ya kai hannu yana goge mata hawayen ya ce “Duk abin da ya sameta dama Allah ya rubuta mata faruwar hakan, amma addu’armu tana tare da ita a duk in da take, damuwar ki kawai ta isa ta ƙara mana zullumi, ki kwanta ki huta ki cigaba da yi mata addu’ar.

Haka ya lallaɓa mama ta kwanta, ba dan yana saka ran zata yi barci ba, sai dan fatan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta su samu salama.

Ya tashi cikin sanyin jiki, ya tafi ɗakinsu, sai dai yana zuwa ya tarar da Huzaifa da Yasir sun haɗa kai da gwiwa suna ta uban kuka, Abubakar yana rarrashinsu, Abdallah ma ya haɗe kai da gwiwa usman kuwa ya zuba tagumi yana bin su da kallo, hannunsa riƙe da Alqur’ani, Aliyu ne kawai a kwance shima kuma ba bacci yake ba.

A hankali mai sunan Baba ya ja da baya, ya koma tsakar gida ya zauna, yama rasa ina zai saka kansa, shima da hali kukan zai yi, ya riga ya gama karaya.

Wayewar garin Allah, jikin ruma ya ƙara tsanani, sai rawar jiki take tana kwarara wani irin koren amai, ga kukan ciwon ciki da take yi duk ta fita hayyacinta.

Babu wanda ya damu da halin da take ciki, sai wannan matar, da a yanzu ba ta kanta take ba ta ruma take, saboda tausayin da take bata, sai sannu take yi mata, tun tana iya amsawa, har ta daina .

Cikin damuwa matar ta ce “Dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kai yarinyar nan asibiti, kar ta mutu a haka, wallahi tana jin jiki sosai”.

“Idan ta mutu meye naki? Ki ji da kanki mana uwar shishshigi” wani daga cikinsu ya bata amsa.

Cikin damuwa ta ce “Amma yarinya ce, dan Allah ku taimaka ko magani ku sai mata kar ta galabaita” banza suka yi mata suka cigaba da shaye-shayen su.

Kamar zata yi kuka, sai sannu take yi wa ruma tana dafa goshinta.

Ruma kuwa sai jujjuya kai take tana kiran sunan mama, duk ta fita kamar ta shekara tana ciwo.

Ko da rana ta ɗan ɗaga idon matar nan yayi ja, jikinta sai rawa yake saboda yunwa da take ji, ga ɗan cikinta sai motsi yake, ga mura da ta addaba mata, amma tafi tausayin halin da rumaisa take.

Mijin iya ne wato dagaci a tsaye a tare da wannan dogon mutumin da su ruma suka taɓa haɗuwa da shi.

“Dan Allah dogo ku taimaka dan zatin Allah ku sako yarinyar nan, ko ku faɗi abin da za a baku, ba ‘yar garin nan bace ba, a mayar da ita hannun ahalinta wallahi marainiya ce”.

Dogo ya ce “Ni ba ‘yan ƙungiyar mu ne suka kawo farmaki ba, kuma dama yarinyar na ga kanta yana rawa, tun da aka kai wannan lokacin ba su ce muku komai ba, wataƙila sun kasheta”.

Cikin kiɗima dattijon ya girgiza kai ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan girman Allah tun da baka tabattar ba ka duba mini, waɗanda suka sako suka dawo gida,  sun ce mana tana can a raye, dan girman Allah ka duba mini ka sanya baki a lamarin nan dan Allah”

“Ni ne zan saka bakin? Su sha tara ne fa suka yi aikin, ban maka wannan alƙawarin ba, zan dai je na duba maka ko tana nan”

Dagaci ya ce “To shikenan, hakan ma na gode sosai”

***

Mummy na barin gidan wambai ta tafi gidan aminiyarta Hajiya Lubabatu, domin fesa mata labarin da ta guntso a gidan wambai.

Sam labarin bai yi wa Hajiya Lubabatu daɗi ba.

Cikin hasala take cewa “Yanzu saboda tsabar wulaƙanci ace har yana shirin yin murabus amma ni ban sani ba”.

“To da baki sani ba ni ba gashi na gaya miki ba, kuma shi yana can Germany ke kina nan ta ina zaki sani?”

“Amma shima wannan wamban ƙasurgumin munafuki ne”

Waro ido mummy tayi ta ce “Rufa mana asiri kar wani ya ji mana, ke ai ba a wannan yakamata ki mayar da hankali ba, wai yana tunanin idan yayi murabus Adam za’a dawo wa da sarauta, sai dai na gyara miki hanya, dan na kunno mus wuta daga shi har uwarsa, dan sai da na tabattar da na fusata shi sosai a kansu. Yanzu dai ki nemi Jabir ku tattauna a kai, ku yi duk iya ƙoƙari kar a rabaku da sarautar nan, Jabir ya gaji ubansa”.

Hajiya Lubabatu ta ce “Ai faɗa ma ɓata baki ne, ai dan ubansa dole ya zo ya san abin yi, ya tare a gindin Adam sai ka ce ubansa”.

“To wallahi ku san abun yi”

“Kar ki damu zaki ji ni” daga haka suka cigaba da hirarrakin su.

****

Kamar a bayi haka aka fara rabawa su ruma abinci, gurasa ɗaya da ruwa ɗaya, haka ake basu kullum, sai ranar da Allah ya kawo wannan mutumin, ya kan kawo mata abinci.

Wannan matar kuwa ko magana ta kasa saboda a wahale take, ji take kamar yunwa za ta kasheta.

Ko da aka bata gurasar nan ba ta tsaya komai ba, ta yi loma uku da ita, saboda azabar yunwar da take ji.

Ruma ta miƙa mata tata ta ce “Gashi ki ƙara da tawa ni na ƙoshi”.

Matar ta girgiza kai ta ce “A’a, ke ce baki da lafiya, ki daure ki ci, sai ki ji ƙwarin jikinki” ruma ta girgiza mata kai alamar a’a.

Matar ta saka gefen zaninta, ta sharewa ruma gumin da ta fara yi, saboda zazzaɓin jikinta ya sauka.

Mutumin da ya tinkaro su, ruma ta tsaya ta zubawa ido, sarai ta gane shi, mutumin da ya tare su yana tambayar wacece ita?

Kenan duk rabin mutanen garin abu ɗaya suke yi kenan, satar mutane? Ta tanbayi kanta.

Suka gaisa da ‘yan bindigar da suke wurin, ya yi musu magana da yaren da ruma ba ta iya ji.

Suka amsa masa, sannan ya shiga duba mutanen wurin, can ya nuno ruma, ya ce “Waccan ce”.

Ƙaton da ya taɓa dukan ruma da bakin bindiga ya tashi ya je ya danƙo ruma, kamar an yi cinikin kaza za a sayar haka ya fizgota, cikin dakiya ta fizge hannunta tana haki.

“Bata da lafiya ka yi mata a hankali” cewar matar da haryanzu ruma ba ta san sunanta ba.

“Ke idan baki kiyayeni ba, da shiga abin da ba a saka ki ba, wannan cikin naki ba zai hana na keta miki haddi ba a gaban jama’a ba, ki shiga hankalinki” daga haka ya mayar da idonsa kan ruma ya ce “Wannan ka ce ko?”

Dogo ya ce “Eh ita, ya ce ku taimaka ku faɗi abin da za’a bayar ku bayar da ita”

Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce “Ai wannan ta zama tamu, ba zamu bayar da ita ba, ta ce sai da a kashe ta a wurin nan, dan haka muma muna so,  su yi haƙuri su mance da ita, ko su fansheta da ‘yan mata biyar, dan ni ba dan barde ya saka mini ido a kanta ba, da tuni ta zama yarinyata, kawai su je idan ubanta da sauransa yayi wani ƙoƙarin su haifi wata, wannan kuwa ba zamu bayar ba” yayi maganar yana ƙoƙarin rungumo ruma jikinsa.

Duk da yadda take a galaibaice, amma haka ta dunƙule hannu, ta ɗirka masa duka a ciki.

Sak suka yi gaba ɗaya suna kallonta, kamar wata zakanya, ta ja da baya ta dunƙule hannu “Wallahi idan ka kuma taɓani sai na yi maka duka, ni ba ‘yar iska bace ba, wane irin azzalumai ne ku? Ba kwa tausayinmu? Muma fa mutane ne kamar ku, kar Allah ya sa ku sake ni, ku kasheni ka kasheni idan kai ɗan halak ne, ni a duniyar nan bana tsoron kowa sai Allah La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin” cikin tsananin ƙwarin gwiwa take maganar ga jikinta yana tsuma.

Ƙare mata kallo ya yi, dudu tsayinta bai fi cikinsa ba, ko a shekaru baya tunanin tayi sha huɗu, ko maza surrender suke idan suka shigo hannu amma yarinya ƙarama ta tsaya a gabansa tana wannan maganar.

“Dan Allah ka kashe yarinyar nan mu huta, sun hana a taɓata sun ƙi bari a saketa duk ta gallabi mutane, barde yana da matsala, kalli yadda take rashin mutunci fa” ɗaya daga cikin mutanen yayi maganar yana gyara bindigarsa tare da saita ta a kan ruma.

“Kai kuma ban saka da kai ba, idan kuma na kasa da kai to ka kwashe, kuma in sha Allah ba zaku gama da duniya lafiya ba, sai kun ga abun da Allah zai yi muku”.

Murmushi ƙaton nan yayi cikin ƙarfin hali, da jin kunyar dizgin da ruma ta masa ya ce “Idan ka kasheta a yanzu ai ta ci bulus, bari in gwada mata tabon da zata tafi lahira da shi, yau ko ni ko barde amma sai na nunawa yarinyar nan iyakarta, ni ki ka ce zaki daka ko?”

Ruma ta sake gyara tsayuwa ta ce “Wallahi kana taɓani sai na ware ƙwanjina, na rama kai ka san wace ruma kuwa?”

Dogo kuwa kamar soko haka ya riƙe hannu yana kallon ikon Allah.

Cikin magiya da kuka matar nan ta fara “Dan girman Allah kayi haƙuri, kar ka yi mata wani abun zafin ciwo ne”

Ruma ta ce “Ba wani zafin ciwo, a hankalina nake, wallahi ya taɓani sai na rama, bana tsoron kowa a wurin nan”

Ya shammaci ruma ya danƙonta, zai fizge hijjabinta da yayi daƙal-daƙal saboda dauɗa, ta riƙe hijjabin ta shiga kai masa duka da hannu ɗaya tana wani gurnani da ihu kamar zakanya.

Ya saka kan bindiga ya ƙwala mata a ka, ihu ta yi ta durƙushe a wurin, sai ga jini ta hancinta.

Tasowa matar nan ta yi da ƙyar ta nufo su, sai dai kan ta ƙarasa ruma ta miƙe cikin tangaɗi ta saka hannu ta dintsi ƙasa da ciyayi, ta watsa masa a jikinsa, gaba ɗaya suka taso suka yo kan su.

Riƙe ruma matar ta yi ta shiga tsakiya, ta haɗa hannayenta biyu cikin magiya 🙏

Ba ta yi maganar ba ya hankaɗeta ƙasa, ta fasa ihu jin kamar a take ɗan cikinta zai faɗo, wani irin gigitaccen ciwo ya ɗaure mararta zuwa ƙafafuwanta.

Hankalin ruma ya koma kan matar, ta nufeta da sauri, amma mutumin nan ya kwarfeta, ya sanya bindiga ya dinga kwaɗa mata, yana takata da ƙafarsa, ihu take amma bakinta yaƙi mutuwa “Idan ka isa azzalumi ka kasheni, kuma in sha Allah yadda Allah ya kuɓutar da Annabi yunus a cikin kifi, ya kuɓutar da Annabi Ibrahim daga cikin wuta, sai Allah ya kuɓutar da mu, haka malamin mu ya ce mana mu yarda da Allah, in sha Allah zai saka mana” ya daka ya daka ya takata, ya sanya wani itace ya maka mata a baya. Wani irin ihu ta kuma yi, bakinta da hancinta na ta zubar da jini.

Tuni ta fara gani dishi-dishi, gadan gadan ya nufi ruma, ya durƙusa a kanta ya kama skirt ɗin jikinta ya fara ja.

Salati da salallami mutanen wurin suka fara yi, duk rashin imanin mutanen, idan suka so keta wa haddi, suna barin idon mutanen da su, amma yana nema ya keta ruma a gaban su.

Wasu kuwa gani suke ruma ita ta janyo wa kanta, tsananin ciwon da matar nan ke ji bai hanata jan jikinta zuwa in da suke ba, ta riƙe rigarsa tana kuka tana girgiza masa kai. Wani irin mari ya kwaɗa mata, da a take shatin yatsun sa suka bayyana a kan kuncinta.

Ɗaya daga cikinsu ya zo ya saka hannu ya dinga jan matar a ƙasa, ya wancakalar da ita a gefe.

Ya kuma danƙar skirt ɗin ruma, amma cikin ƙarfin hali ta riƙe.

Ji yayi an fincikoshi ta baya, an kwaɗa masa mari.

A gigice ya kalli wanda ya mare shi, barde ne wanda ruma ta bawa gyaɗa kuma yake kawo mata abinci wasu lokutan.

Wata irin ashar yayi masa, cikin ƙaraji ya ce “Me ka yi mata? Me na ce maka da aka kawo ta? Au har ka manta zaka karya yarjejeniyar?”

“Amma ai ka tsaya ka ji meyafaru kan kayi mini haka”

Cikin hasala barde ya ce “An maka ɗin, wallahi da ka aikata abin da ka yi niyya, da sai na yi gunduwa-gunduwa da namanka a wurin nan” cikin huci ya nufi kan ruma, jikinta duk shaidar duka.

Ya ɗagota ya girgiza ta, ta buɗe ido ta kalleshi, a hankali ta fizge hannunta daga nasa ta mirgina ta kwanta a gefe, tana kallon matar nan, da take ta sauke numfashi da ƙyar, kamar sumammiya.

Bai sake ƙoƙarin taɓa ruma ba, ya ja ƙaton nan yayi gefe da shi yana yi masa magana.

Ruma ba ta sake bi ta kansu ba, a hankali ta mirgina, ta ƙarasa in da matar nan take kwance, tana numfarfashi, ruma ta ɗora hannunta a kan na matar, a hankali ta ji matar ta riƙe hannunta, ta sake matsawa jikin matar ita ma tana mayar da numfashi ba tare da wani ya tankawa wani a tsakanin ita da ita ba.

Dagaci kuwa tun da suka yi magana da dogo, a kan zai je ya bincika masa ruma, ya kira Aliyu ya sanar masa domin hankalinsu ya ɗan kwanta, dan haka suka cigaba da dakon abin da dagacin zai ce masu, gashi Aliyu ya riga ya gaya musu yadda suka yi dagaci, dan haka mama kullum sai ta tambayi Aliyu, haryanzu dagaci bai yi magana ba?.

***

Kasancewa Adam ba a family house ya kwana ba, Kamar kullum bisa ga al’ada yana biyawa ya gaida Ammi, dan haka yau ma a cikin hanzari ya yake tafiya, ya ƙarasa sashinta.

A bedroom ya tarar da ita, sai dai saɓanin kodayaushe, ya tarar da fuskarta a haɗe, hakan ya tabattar masa da akwai damuwa.

Sai dai ya bari sun gama gaisawa, sannan ya ce “Allah ya baki yawan rai, lafiya na ga fuskar ki babu walwala?”

Ammi ta ce “A’a lafiya ƙalau, wambai ne ya bani saƙon cewa idan ka tashi daga aiki, yana nemanka” sak takawa yayi, ya dubi Ammi ya ce “Wani abu ne ya faru?”

“Ni ma ban sani ba, kawai dai ya ce yana nemanka?”

“Ko laifi na yi mass?” Adam ya sake tambaya.

“Ban sani ba takawa, ka je dai ka ji ko menene”

“Shikenan” ya faɗa a taƙaice, ya tashi ya ce “Na tafi”.

“Allah ya tsare” Ammi ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.

Har ya kai bakin ƙofa Ammi ta ce “Adam!” Sai da tsigar jikinsa ta tashi, dan abu ne mai wahalar gaske ta kira sunansa haka kai tsaye.

Ya tsaya ya waiwayo ya kalli Ammi.

“Idan ka je wurinsa, ko me zai ce maka ban yadda ka tofa ko ka yi ƙoƙarin kare kanka ba, ka bishi da to kawai”

Ɗan shiru yayi yana nazari, akwai wata a ƙasa kenan, a zahiri kuma ya ce “To, in sha Allah”.

A falo ya haɗu da Nusaiba, ta gaishe shi, bai iya amsawa ba sai jinjina mata kai kawai ya fice.

Yana tafe yana auna kashedin ammi da kiran da wambai yayi masa, saboda shi a yanzu tension ɗin da yake ciki ya ishe shi, ba sai an ƙara masa da wani ba.

Nusaiba ta shiga ɗakin Ammi, ta tarar da ita zsune a gefen gado, ta yi shiru.

“Ammi” Nusai ta yi maganar kamar tana tsoron wani abu.

Ammi ta kalleta ta ce “Na’am ya aka yi?”

“Amma dai baki gaya wa takawa yadda kuka yi da wambai ba ko, kar ya hasala?”

Ammi ta girgiza kai ta ce “Ta yaya zan gaya masa, ni babban fatana idan ya je kiran da yake masa, Allah ya sa kar yayi masa irin cin mutuncin da yayi mini, kin san halin yayan naku da zuciyar tsiya babu lallai ya jure, dan ma na taushe shi kan ya tafi”

Jiki a sanyaye Nusaiba ta ce “Ammi ni fa gaba ɗaya a maganganun da yayi, na kasa gane wane point yake son yayi magana a kai, sai kame-kame kawai yake yi yana faɗa na babu gaira babu dalili, ko dai Mummy ce ta je ta gaya masa wani abu?”

Ammi ta girgiza kai ta ce “Bana tunanin haka, kin san shi dai dama mutum ne mai zafi, a bar maganar kawai, ‘yar auta ta ba ta tashi bane?”

“Eh bacci take yi, kin san exams suke shirin farawa”.

Ammi ta jinjina kai, ta cigaba da jan carbinta.

****

Hatta masalattan unguwar su rumaisa, duk salla sai an yi addu’ar Allah ya bayyana rumaisa, saboda garkuwa da rumaisa abu ne da ya zo a bazata, kusan za a iya cewa ita ce yarinya ta farko da aka sace a unguwar, dan duk irin wannan abubuwan sai dai a ji su a nesa, amma yau gashi a cikin unguwa.

Kamar yadda dogo ya yi wa dagaci alƙawari, ya koma masa da maganar ruma.

Tun da dagaci ya ji dogo ne ya zo yake nemansa jiki na rawa ya tashi, ya fita tare da fatan Allah ya sa a dace a samu rumaisa.

Iya ma tashi tayi ta biyo bayansa, ya tsaya ya kalleta ya ce “Ke kuma ina zaki?”

Cikin rikicewa Iya ta ce “A ruɗe nake, ni dai mu je in ji me zai ce”

“Dan Allah ki koma, duk yadda muka yi da shi, idan na dawo zan sanar miki” da ƙyar ta yadda ta koma gida, amma ta ja ta tsaya a tsakar gida.

Cikin sauri ya fito ya iske dogo suka gaisa, cikin zaƙuwa ya ce “Ya ake ciki ka ganota?”

Dogo ya ce “Eh na ganota, tana rukunin su sha tara, sun ce ba zasu bayar da ita ba, ba sa buƙatar kuɗin fansarta, dan haka ku cigaba da addu’a, wannan yarinyar halinta zai iya sakawa su kasheta, halin na ta nema ya sanya suka ce ba zasu bayar da ita ba, dan haku ku cigaba da addu’a kawai.” Daga haka dogo bai kuma ce masa komai ba ya yi tafiyarsa.

Dagaci kuwa ya tsaya ya dinga nanata Innalillahi wa Innalillahi raji’un.

Jiki a sanyaye ya koma cikin gidan, iya ta tare shi tana faɗin “Ya ake ciki, me suka ce maka?”

Yayi shiru ya kasa magana. “Dan Allah ka yi magana mana, menene ya ake ciki ya ganota? Sun faɗi me za a basu?”

Ya girgiza mata kai ya ce “Tana nan a raye, amma sun ce ba sa buƙatar kuɗin fansa, ita ɗin suke so, halinta ya saka suka ce ba zasu bayar da ita ba ta zama ta su”

“Wayyo Allah na shiga uku, yarinyar mutane ta salwanta a dalilinmu, na shiga uku na lalace”.

“Meye haka ki ke yi kulu? Wannan ai rashin hankali ne”.

“Ƙyaleni na yi rashin hankalin, har abada uwar ‘yar nan ba zata mamta da ni da gwaggo ba na shiga uku, da na sani ban karɓi rumaisa ba, ban san haka zata faru ba, Allah ka shiga lamarin nan wayyo Allahna”

Haka dagaci yayi ta fama da iya tana kwarmato da ɓurari.

****

Rana ce ta take a kan su ruma, a hankali ta ja jikinta da yake mata ciwo, ta tashi zaune, jikinta babu abin da yayi saura sai tsabar ƙarfin hali da taurin kai.

Da wannan ƙaton ta fara tozali yana hararata, ita ma hararar ta watsa masa, ta mayar da idonta kan matar nan, ta fara tattaɓata. A hankali matar ta buɗe ido, ta kalli ruma, tana ganin fuskar rumaisa ta yi murmushi. Ita ma ruma murmushin ta yi mata sannan ta ce “Tashi koma waccan bishiyar, nan rana ta tarar da mu”.

Cikin ƙarfin hali ta ce wa ruma “Ba su yi miki komai ba ko?”

Ruma ta jinjina mata kai, da ƙyar matar ta tashi, da rarrafe suka canza wuri zuwa wata inuwa suka zauna.

“Yunwa ki ke ji ko?” Ruma tayi maganar tana kallon matar.

Ta girgiza wa ruma kai ta ce “A’a, ke nake so ma ki samu ki ci wani abu, baki da lafiya, dan Allah ki daina rigima kar su illata ki, ba zan ji daɗi ba”.

Ruma ta ce “Mhmm ki daina damuwa da ni, ni na saba da kasada, sonake su kasheni na huta na gaji”.

“A’a bana son a kashe ki, in sha Allah zaki fita lafiya ƙalau”.

“Ban ga alamar hakan ba, gara na tunzurasu su kasheni na huta, suma su huta amma wallahi in dai suka barni a raye na din ga tayar wa da uban kowa hankali kenan”.

Matar ta waro ido ta ce “Ke ba kya jin tsoro ne?”

“Taɓ, ai tsoro yayi yamma na yi gabas, ni fa ƙanwar maza ce guda bakwai, ko ‘yan unguwarmu sun sanni, dan ma na daina dambe da maza, yayyena sun hanani, duk wata kasada idan na ɗauko in tafi ƙarfina su suke shigar mini, ni fa har wata ‘ya na taɓa karyawa. Bindigogi ne fa kawai da su, to wallahi bana tsoron bindigar su kamar yadda nake tsoron mai sunan Baba”.

“Waye haka kuma?”

Ruma ta gyara zamanta ta ce “Yayana ne, sunanshi umar, hmmm ina tsoron Allah ina tsoron sa, nifa bana jin tsoron mama kamar yadda nake tsoron sa, kin san idan nayi laifi baya tashi hukuntani, sai cikin dare ina tsaka da bacci zan ji ni a sama, in zata ko raina aka zare kin san ance idan mumini ya mutu, to sama ake yi da ransa, to sai na ji an watsoni tsakar gida, sannan nake gane ai ina duniya, hukuncin ma sunan Baba ne, idan ya haɗe rai ya tattare girarsa sai na ji kamar in zawo a tsaye”.

Duk da halin da suke ciki, bai hana matar yin murmushi ba, dan ba ƙaramin dariya ruma ta bata ba.

Ruma ma Murmushin ta yi ta ce “Mai sunan baba dodon marasa hankali in ji mama, idan ya sakani kama kunne a daren nan, to wallahi da asuba a zaune zan salla saboda azaba, mai sunan Baba ya iya punishment”

“Ni kuwa zan so na ga mai sunan Baban nan da ki ke tsoro fiye da bindiga”.

“Kema idan ki ka ganshi sai ya baki tsoro, shi fa ba ya dariya, kullum fuskarsa a haɗe, wataran ko hararata yayi sai na kwana uku a nutse”.

Dariya suka yi tare, ruma ta ce “To baki gaya mini sunanki ba, ina mijinki da ‘yan gidanku?”

Matar ta yi murmushi ta ce “Suna na, sunana Aisha”.

“Anty Aisha, ke a wani garin ki ke?”

“Zan gaya miki, yanzu jikina babu daɗi na bugu, yaron cikina sai juya wa yake”.

Cikin damuwa ruma ta ce “Sannu, Allah ya sa su sake ki kan ki haihu, Allah ya sa ki amayo shi lafiya”

Cikin dariya ta ce “Me zan amayo?”

“Ɗan mana, ba ta baki ake yo aman jariri ba, haka mama ta ce mini, amma su fa akuyoyi to ta wurin kashin su suka haifo ɗa, daga yi wa mama tambaya ta ce idan na kuma wurinda akuya ta haihu sai ta zaneni” halin da Aisha ke ciki bai hanata yin dariya ba, ta riƙe cikinta, saboda dariyar ta ƙarfin hali ce.

“Ya naga kina dariya, ko ba ta nan ake haihuwar ba?”

“Ta nan ne mana, Allah ya sa na amayo shi lafiya”.

Ruma ta ce “Amin, ina zuwa” daga haka ruma ta miƙe ta nufi mutumin nan ta je ta tsaya masa a ka, ya ɗago ya kalleta ya ce “Me kuma ki ke nema?”

“Abinci, yunwa muke ji”

Ɗagowa yayi yana ƙarewa ruma kallo, ita ma ƙyar ta ƙure shi da nata idanuwan.

Wata leda ya ɗauka ya wurga mata ya ce “Gashi nan shegiya mayya, mayuwanciya” ta durƙusa ta ɗauka ta ce “Koma me zaka ce na ji, na dai fi ƙarfin ka, ba yadda zaka yi da ni”.

Tun mutanen wurin suna namakin ruma, har sun saba da halinta, kome zata yi sai dai ta ci duka, amma ban da haka ba wanda ya isa yayi mata wani abu.

Ta koma wurin Aisha ta zauna ta ce “Anty Aisha, tashi mu ci abinci” tayi maganar tana buɗe ledar.

Buredi ne a ciki da pure water.

“Matsiyata kullum daga gurasa sai buredi”.

Aisha ta ce “Ruma dan Allah ki din ga shiru, kin ga baki da lafiya, kar su sake dukanki”.

“Wai meyasa ki ka damu da ni haka ne? Dan Allah ki daina damuwa idan ba haka ba sai na koma baki haushi, haka nake, in dai ba gajiya zasu yi su kasheni ba, suna tare da wahala” ruma ta ƙarasa maganar tana miƙawa Aisha buredin a baki.

Murmushi ta yi ta karɓa, ba dan buredin na yi mata daɗi ba, sai dan rashin mafita.

****

Kwanaki kusan talatin kenan da sace ruma, babu wata tartibiyar magana a kan in da take ko yadda za a sameta, ga mama sai ciwo take a tsaye, ko ta sha maganin hawan jini, jinin baya sauka, ga ulcer ta yi mata mummunan kamu saboda rashin cin abinci.

Yanzu haka suna zaune duk sun kewayeta, amma babu iya cewa komai, sai ma ita ce cikin ƙarfin hali take musu faɗa, a kan rashin cin abinci.

Usman ya dubi Aliyu ya ce “Dan Allah ka sake kiran mijin iya, ka ce masa haryanzu muna jira bai ce mana komai ba, an samu an yi maganar da su kuwa?.

Usman bai yi musu ba, ya kira mijin iya, Abdallah ya ce “Ka saka mana a hansfree mu ji”.

Aliyu ya saka wayar a hansfree, suka gaisa da mijin gwaggo sannan ya ɗora da cewa “Baba haryanzu ba ka ce mana komai ba, an gano a in da taken, ko kuma sun faɗi abin da za a basu?”

“Aliyu zancen ne babu daɗin ji, shi ya sanya na yi muku shiru”.

“Sun kasheta ne?” Abdallah yayi maganar a kiɗime.

“A’a, ba kasheta suka yi ba, wanda muka tura ɗin ya dawo ya sanar da ni cewa sun ce ba sa buƙatar komai ba zasu bayar da ita ba, halinta ya sanya za su riƙeta ko kuma a fansheta da ‘yan mata biyar, duk iya ƙoƙarin da zan yi na yi abu ya faskara, sai dai mu cigaba da addu’a kawai”.

Gaba ɗaya aka rasa mai magana, sai mama da take ta “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Allah ya sa ba taurin kan take yi musu ba, Allah ka kuɓutar mini da yarinyar nan ka tsare mini ita” tayi maganar tana kuka

Abdallah ne ya rungume mama yana rarrashinta, yana goge mata hawaye.

***

Mintuna kusan talatin da takawa ya sanya aka yi masa iso wurin wambai, amma shiru bai fito ba gashi ya fara ƙoasawa da zaman, dan haka ya tashi da nufin ya tafi, dan akwai tarin ayyukan da suke gabansa ya yanke ya taho.

“Na sallameka ne zaka tafi, ko nima halin rashin ɗa’ar zaka gwada mini?” Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli wambai da ya shigo falon, sanye da jallabiya ba tare da naɗi ba.

“A’a ranka ya daɗe, na zaci ba zaka samu fitowa ba, na baro ayyuka da yawa na taho”

“Saboda ayyukan ka sun fi kirana muhimmanci ko, ashe abubuwan da ake gaya mini akan ka gaskiya ne ko Adamu?” Cikin mamaki Adam ya ke kallon wambai.

“Zaka nemi wuri ka zauna, ko kuma jera kafaɗa zamu yi sannan mu yi magana?”

Adam yayi ajiyar zuciya, ya samu wuri ya zauna a ƙasa yana tunanin laifin me yayi wa wambai haka har yake kiran sunansa haka.

“Dukkanin abin da ka ke yi ya sameni, kuma ka bani mamaki ka bani kunya, turbar da ka ɗauko ba ita ce turabar da mahaifinka ya ɗoraka a kai ba, dan haka ka shiga hankalinka idan ma uwarka ke zigaka kanka yake rawa gara ma tun wuri ka nutsu ka shiga hankalinka, kuma wallahi idan ba ka yi wasa ba, sarautar da kake jiran ba zata dawo gidanku ba, idan ma ta dawo ɗin sai dai a bawa ɗan uwaka tunda kai dai ba ka san abin da yake maka ciwo ba” maganar Ammi ce ta sanya shi yin shiru, gaba ɗaya ya rasa a kan me Wambai yake yi masa faɗa tare da ci masa zarafi, shi ce masa yayi yana jiran a bashi sarauta ne?.

Nan da nan jijiyoyin kan Adam suka ɗaga, saboda tsananin ɓacin rai, haka tsohon nan ya saka Adam a gaba ya zage shi tsaf ba tare da wata tartibiyar hujja ba.

Sai da yayi mai isarsa sannan ya tafi gida, da ƙyar ya kai kansa gida, yana shiga sashen Ammi ya tara da su Fauziyya da Samha a falon Ammi.

Wucewa yayi ciki yana ta huci, Ammi da take zaune tare da su a falon ba ta tashi ba, ta basar da shi. Cike da gulma Fauziyya ta ce “Ammi meya sami takawa ne?”

Ammi da tun daga shigowar su Fauziyya shashenta ta san akwai wani abu a ƙasa, dan rabonta da su anfi wata guda, kawai ta basar ne.

Ammi ta ce “Babu komai, ina ga aiki ne yayi masa yawa kawai”.

“Kin ga yadda idonsa yayi ja kuwa? Kamar ba shi da lafiya fa”.

Iman ce daga kitchen ta wuce ɗakinta, dan sam  a ta san abin da zai sanyata shiga shirgin su Fauziyya, tana zuwa ta tarar da takawa a tsaye a ɗakinta, tamkar zai fashe, ya watsarwa mata da kayan kan mudubinta, sai karkarwa yake.

Yana jin motsin iman, ya buɗe jajayen idanunsa yana kallonta.

Girgiza masa kai ta shiga yi, amma ta kasa gaba ta kasa baya.

“Zo nan ya faɗa a kausashe”.

“Dan Allah ka yi haƙuri, ba ni na ɓata maka rai ba” tayi maganar cikin rauni.

“A hayyacina nake iman, hannunki kawai zan riƙe”.

Cikin rawar murya ta ce “Amma ba zaka yi mini komai ba?”

“Na rasa abin da zan riƙe, kaina zai tarwatse ne, help me just your hands” cikin tsoro ta nufe shi, ta ƙarasa nesa kaɗan da shi ya kama hannunta ya riƙe tamkar zai ɓallata.

Ihu ta ƙwala jin yadda ya murɗa mata hannu, haƙoransa sai karkarwa suke yi.

Sama-sama suka jiyo ihun iman, suka tashi suka nufi ɗakin Iman.

Takawa suka tarar ya banƙare hannun Iman, hannu ɗaya kuma ya shaƙeta, rigar jikinta ta ɗage sai kokowa take da numfashi tana kakari.!!

Gaba ɗaya tsaya wa suka yi suna kallon su, Ammi ce kawai ta iya ƙarasawa tana ƙoƙarin ƙwace Iman “Me ka ke yi haka ne takawa, iman ce fa”

A hankali ya saki wuyan iman yana ƙare mata kallo, jikinta duk yayi ja saboda azabar wahalar da ta sha.

“Kalli fa ka gani, iman ce fa takawa”

Kamar wanda ya warke daga ciwon hauka, haka ya din ga bin Iman da kallo, kamar zai fashe da kuka ya ce “Iman yi haƙuri, ban san ke ba ce, hannunki kawai na ce zan riƙe, na ga kin koma wata mata zaki caka mini wani abu, yi haƙuri iman, Ammi ban san iman ba ce ki bata haƙuri”

Nusaiba ce ta kalli su Fauziyya da suka yi tsaye suna kallon abun da yake faruwa, ta ce “Anty Samha ba wani abu, zaku iya tafiya”.

Samha ta ce “Ba zamu tafin ba, a kan ki muke ko yayanki ne ke kaɗai”.

Ammi ta ɗago iman tana yi mata sannu, iman ta jinjina mata kai.

Ammi ta ce “Ina maganinsa yake? shegiyar gardama irin ta sa ɗauko in shafa masa” A hankali iman ta yinƙura, ta je ta saka mukulli, ta buɗe wata drower, ta ɗauko wata jarka cike da wani mai.

Ƙurii Fauziyya ta yi, tana kallon in da iman ta ɗauko maganin.

Adam yayi zuruu da ido yana bin su da kallo, can ya sauke idonsa a kan su samha, cikin tsawa ya ce “Get out” sai da suka razana, kan su yi wani yinƙuri ya sake daka musu wata tsawar, cikin rige-rige suka yi waje da gudu.

Ammi cikin damuwa ta ce “Takawa, meye ya ɓata maka rai haka ne?”

Kamar mai shirin zaucewa ya hau surutai, “Ni na ce ina son sarautarsu ne? Su barni in ji da abin da ya dameni mana, me na yi masa? Idan ya kuma takura mini zan kashe shi, zan shanye jininsa gara ma ki gargaɗe shi ya fita a hanyata”.

Cikin tsawa Ammi ta ce “Adam! Kar na sake jin ka furta wannan maganar, wan ubanka ne fa, ban hanaka zancen shan jinin nan ba, sai ka ce maye?”

Nusaiba ta ce “Ammi ba a hankalinsa yake faɗar shan jinin nan ba, ki yi masa a hankali”.

 iman  shammace shi, ta shafa masa maganin a fuska, a take ya yi atishawa, sai kuma a hankali ya sulale ya kwanta a ƙasa ya hau bacci.

Hawaye Ammi ta shiga zubarwa, iman da Nusaiba suka yo kanta gaba ɗaya “Haba Ammi, idan ki ka yi kuka mu kuma mu yi yaya, dan Allah ammi ki daina ki yi masa addu’a” Iman tayi maganar hawaye na cika idanunta.

“Iman, ciwon da nake tunanin ya rabu da shi, yana neman ya dawo daga rai ya ɓaci sai ya hau maganganu, ya fita hayyacinsa, ina zan saka kaina, saboda tsabar neman magani na fara tsoron kar in faɗa hannun mushirikai na rasa imanina, sanadin ciwon nan har jita-jita aka din ga yaɗawa wai maye ne fa, da wanne zan ji?”.

Nusaiba ta ce “Dan Allah ammi ki daina damuwa, Addu’arki fa ba ta tafiya a banza, zai warke in sha Allah “Astagfirullah, Allah ya yaye maka Adam, duk wani hope ɗina a kanka yake, ban ce wani ne ya yi maka bs, Allah ne ya ɗora maka, ina fatan ya yaye maka”

Suna tsaka da maganar ya fara surutai “Sidi, ku je ku dubo mini yarinyar nan, na gaji a kan me zata din ga zuwar mini a bacci ko in din ga jin kukan ta a kunnena, anya mutum ce? ku je ku duba mini ni bani da lokaci” kamar sun je cinema haka suka zuba masa ido, can kuma ya toshe kunne yana faɗin “Ki daina yi mini kuka, bana son kuka, meye alaƙata da ke ne?”

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin ammi da su Nusaiba.

A hankali nusaiba ta ce “Yaya maganar wa ka ke yi ne?”

Tun da Nusaiba ta yi magana bai sake cewa komai ba, yayi shiru bacci yayi awon gaba da shi.

***

Idan da sabo ruma ta saba, dan haka yanzu baccinta take cike da mafarkan su Mama da yayyenta, sai dai babban abin da yake addabarta bai wuce ganin mutumin nan da ta tsana a cikin mafarkinta ba, wanda hakan ba ƙaramin haushi yake bata.

Yanzu ma mafarki take yi, tana zaune tana kuka a cikin dajin nan, takawa ya ɓullo sanye da wasu baƙaƙen kaya, ya ratso mutanen da suke wurin, ba wanda yake iya ganinsa sai ita, ya zo ya tsaya a kanta, ya miƙa mata hannu ya ce “Taso mu tafi”

Ta waiwaya tana dubawa ko akwai wanda yake ganin sa, “ba zaki taso mu tafi ba kin tsaya kina kalle-kalle?”

Cikin tsiwa ta ce “Eh ba za’a taso ba ɗin ni na gayyace ka?” Tayi maganar a fili, tana buɗe ido, tsaki tayi tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta ta ce “Aikin banza, ko me yake kawo shi mafarki na oho, idan na kuma ganinka a baccina, sai na yi maka rashin mutunci, dan wallahi sai na rama abin da ka yi mini”

“Ke da waye ne baby rumaisa”ta ji muryar anty aisha.

Ruma ta sake buɗe ido ta ce “Ba kowa”.

“Haba dai ba kowa, tun ɗazu ki ke surutu fa kina masifa a cikin bacci, har wancan yake cewa zai taka ƙafarki ki tashi,”

Duk da duhu ne, Ruma ta zare ido ta ce “Haba dai, me nake cewa?”

Aisha ta ce “Ina ta fama da kaina ban riƙe ba, amma dai faɗa ki ke da wani a bacci”

Ruma tayi ajiyar zuciya ta ce “Wani mara kirki ne yake zuwar mini, taimako ɗaya Allah zai yi masa, shine na mutu a wurin nan, amma muddin na fita ko ni ko shi, sai ya gane bashi da wayo”

Anty Aisha ta ce “Subhanallah, me yayi zafi haka?”.

“Baki san rashin mutuncin da yayi mini ba, nonona ya taɓa mini, kuma mama ta ce duk wanda ya taɓa nan wurin na zama ‘yar iska cikin shege ne zai fito mini”

“Ya salam, ke ya aka yi ya kai hannunsa nan wurin?”

“Sa wa yayi aka ɗaukoni, wai zai yi mini warning, ya shaƙo hijjabina ya taɓa wurin, ni kuwa na din ga bin diddigi sai da na gano gidansu, na je na rubuta masa wasiƙar rashin mutunci na ce a bashi”

“Kai ruma lallai jan wuya ke ce, irin wannan ƙarfin hali haka?”

“Rabu da shi, ai wallahi ya bari na fita daga wurin nan zai gane kurensa, Anty Aisha wai ke a wani gari kike?”

“Zan gaya miki ruma, na san zuwa yanzu labari ya samu mijina da dangina abin da ya faru da ni, sai dai ban ga alamar kuɗin fansa suke so ba,. Tun da sun ƙi yin waya su faɗi abin da za s bayar idan…. Ba ta ƙarasa maganar ba ta riƙe ƙugunta ta ce “Washhh”

A ɗan rikice ruma ta ce “Sannu Anty Aisha, kwanta a kan cinyata ki miƙe ƙafar to”.

“A’a kar na hanaki bacci baby ruma, yi kwanciyarki”.

Ruma ta ce “A’a ai ba zan iya komawa ba kwanta”.

A hankali Aisha ta ja jikinta ta kwanta a kan ƙafafuwan rumaisa, Ruma ta ce “Bari na yi miki tsifa, kin san ni nake yi wa mama tsifa har kitso na iya” Aisha ba ta hana ruma ba, ta dinga jagwalgwala mata gashi, sai dai duk da mawuyacin halin da take ciki, ruma dariya take bata, dan sam ruma ba ta da rufi.

“Anty Aisha ina son in ga kina dariya, daɗi nake ji, tun da ki ka zo wurin nan na rage damuwa duk da ina missing ɗin gidanmu, in sha Allah idan Allah ya ƙaddara muka bar nan, ko a wane gari ki ke zan zo gidanki”.

Tayi murmushi ta ce “Nima haka ruma, tun da na zo wurin nan, kawai nake jin ki a raina, nake kuma sarawa jarumtarki, sai dai babu lallai na bar wurin nan a raye haka jikina yake bani”

“Ɗaga mini cinyata tun da ba zaki daina wannan maganar ba” ruma ta faɗa rai a ɓace.

“Haba ruma, ni ɗin ki tsaya ki ji mai zan gaya miki, idan ma na mutu lokacina ne yayi kuma zan yi shahada”. Ruma ta ture kan Aisha daga kan cinyarta ta tashi ta ce “Sai ki je ki yi ta shahadar ai, ba zan sake kulaki ba”

Kowa yayi bacci, sai masu gadi da su ruma ne idonsu biyu, da wani ne yake wannan surutun cikin daren nan, da yanzu ya sha tijara ƙila a haɗa masa da duka ma, amma kasancewar rumaisa ce take magana ba wanda ya kulata, dan yanzu da an taɓata zata hau kwarmato, idan kuma ba a isa ayu mata wani abun ba kamar tayi musu asiri.

Ɗayan ya kalli ruma da ta tashi zata canza wuri daga kusa da Aisha, ya ce “yau kun yi faɗa da uwar taki ne?”

“To meya dameka ne, ka cigaba da gadinka mana, sa ido sana’ar banza”.

“Ni ki ke cewa sa ido sana’ar banza, dan kin ga ana ƙyaleki?”

“Ai wallahi ko me zan yi, baku isa ku yi mini wani abu ba, addu’a nake banka muku ta ko ina, in gaya maka, ka san wani abu kuwa?”

“Bana son ji, wuce ki nemi wurin kwanciya”.

Ruma ta ƙarasa wurin da suke zaune sun kunna wuta, wasu suna shaye-shaye, ta zaune a gefansu ta ce ta yi ƙasa da muryarta ta ce”Ka san meya haɗani da anty aisha muka yi faɗa kuwa? Cewa take yi wai zata mutu ta tafi ta barni, shine ta bani haushi”

“To ina ruwana? Sauran da suka mutu meyasa baki damu ba?”

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Tana sona ne wallahi, nima kuma ina sonta, dan Allah ku saketa, ko ku kai ta asibiti ba ta da lafiya”

Ya ce “Wallahi na yadda addu’a ki ke yi mana, ko kuma daga can gidanku ake yi, ban da haka ba a taɓa kawo ɗan iskan mutum mara tsoro irin ki ba”.

“A’a nifa ba ‘yar iska bace, so nake ku kasheni, amma kun ƙi ya zan yi, kalli yadda na koma kamar ‘yar jari bola, wataran a gidamu mama sai ta yi mini wanka sau biyu a rana, amma yau ban san adadin kwanakin da na shafe ban yi wanka ba, tun ina warin har na daina”.

“To ai ko ni ma sai na yi miki wankan, akwai kogi a gaba”

Aisha tana daga can nesa, amma ko ƙifta ido ba ta yi a kan ruma, dan kar wani abu ya faru, ruma tayi zaman dirshen sai zuba take, duk da ba ta san mai ruman take cewa ba, amma hirarta kawai take yi da su hankali kwance.

Ba ta sake bi ta kan Anty Aisha ba, har aka yi sallar asuba, ruma ta yi salla tayi kwanciyarta bacci.

***

“Mummy, wallahi na san in da maganin nan yake, a ɗakin iman yake, kuma na sake tabattar da takawa yana nan da wannan ciwon mai kama da na aljanu, mai kuma kama da na hauka”

Mummy ta kalli Fauziyya a tsanake ta ce “Fauziyya, bana son shirme da ƙarya fa”.

“Haba mummy, kamar wata ƙaramar yarinya, kin ga yadda ya shaƙe iman a ɗakinta kuwa, ya ɗage mata riga baki ga ba”

Mummy ta yi murmushi ta ce “Kin tabattar kin ga in da maganin yake? Idan kin tabattar ina son gaya wa uwani ta kawo mini shi, dan da maganin wannan malamin yace zai mini aikin da zai kawo ƙarshen hankali a jikin adam, kin ga ba shi ba sarauta kenan”

“Wallahi mummy na gani, sai dai akwai mukulli a drower mudubinta ne”

“Fine, kafin nan, ina son ayi raising issue na cewar yayi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, wani sashin kuma ace an kama shi shi da ita, hakan zai ƙara ɓata sunansa, da yi wa zuriyar binta baƙin jini a cikin masarautar nan”

Fauziyya ta ɗan yi jimm sannan ta ce “Anya Mummy, decision ɗin nan naki bai yi tsauri ba kuwa?”

“Ban gane tsauri ba, duk wannan fafutukar ba dan ku nake yi ba, ki shiga hankalinki fa”

“Am sorry, ba zan sake ba duk hukuncin da ki ka yanke dai-dai ne”

Mummy ta yi ƙwafa ta tashi ta fice.

***

Habiba ƙawar ruma kullum sai ta je layinsu ruma, ta tambaya ko an ga rumaisa, dan tsoron zuwa gidan su ruma take saboda yayyen ruma, tsoro suke bata, ita a da can ma idan ba dole ba ba zuwa take yi ba, balle yanzu da suke cikin damuwa da tashin hankali.

A ƙofar gidan su ruma take tsaye tana leƙe.

“Me ki ke dubawa ne?” Ta ji muryar usman.

Da sauri ta waiwaya tana kallonsa.

“Me ki ke yi a nan?” Ya maimaita.

Habiba ta ce”So nake na ji ko zan ji yo muryar ruma ta dawo”

Cikin sanyin jiki usman ya ce “Ruma ba ta dawo ba Habiba, na san kina yi mata addu’a, to ki cigaba kar ki daina dan Allah”.

Hawaye ya cika idon habiba za ta yi kuka, usman ya ce “Kar ki yi kuka kin ji, maza tafi gida kar a neme ki kin ji”

Haka nan ta juya ta tafi gida.

***

Ruma kuwa sai da rana ta take, sannan ta tashi daga baccin da take yi,ta tashi zaune ta ɗaga kai suka yi ido huɗu da Aisha, amma rumaisa ta kawar da kanta gefe taƙi kula Aisha.

Sai dai a kallo ɗayan da ruma tayi mata, ta hango damuwa a fuskar aishan.

Gaishe da mutanen wurin tayi, ta koma gefe ta tattara duwatsu ta hau ‘yar carafke.

“Sannu rumaisa, ke rayuwarki baki da wata damuwa, yau ba kya jin yunwar ne?” Cewar wanda suke kira da sha tara.

“To kun bani abincin ne?”

“Ga abinci nan barde ya kawo miki kina bacci”

“Nifa na gaji da buredin nan ba yau ba gobe… Au ashe waina ce yau” tayi maganar tana murmushi, yayin da mutane suke kallon tsabar samun wuri da ruma ta yi.

Ta koma gefe da nufin ta fara ci, suka yi ido huɗu da Aisha ta zubo mata ido,haka nan ruma ta ji jikinta yayi sanyi, dan haka ta tashi ta je gaban Aisha ta zauna ta ce “zo mu ci”

Aisha taƙi magana, kawai ta zubawa ruma ido.

“Mu ci mana” ruma ta sake maganar tana kallon idon aisha, amma ga mamakinta taga hawaye a kwance a cikin idonta.

“To Meyasa kuma zaki yi kuka?” Ruma tayi maganar kamar ita ma ta yi kukan.

“Meyasa ki ke fushi da ni ruma? Na ji daɗin kwanciyar da na yi a kan ƙafafuwanki, har na ji ina son yin bacci, amma ki ka tashi ki ka barni” tayi maganar cikin damuwa.

Ita ma ruma cikin damuwar ta ce “Ba ke ce ki ke cewa zaki mutu ba, na gaya miki kuma bana so”.

“To na daina, amma ki matso kusa da ni in kwanta a kan ƙafarki, ko zan ɗan ji daɗin kwanciyar, kwana na yi ina ciwon baya da ciwon mara, ƙafafuwana kamar ana sara mini su”

“To mu ci wainar, sai ki kwanta”

Ta girgiza wa ruma kai, ta karkata da ƙyar ta kwanta a kan cinyar ruma, sannan ta kalli ruma ta ce “Har na ji daɗi, mu daina faɗa dan Allah ƙawata, gurin nan yana bani tsoro, da sakani cikin damuwa ke kaɗaice ƙwarin gwiwata, idan na ganki nake jin daɗi, kuma ko ina cikin damuwar barkwancinki na sakani nishaɗi”.

Murmushi ruma ta yi ta ce “Ni wallahi idan ki ka ce baby ruman nan, sai na ji kamar na fara rarrafe da shan hannu, kamar wata jaririyar zanin goyo, wai da mama baby take ce mini da har a yanzu sai na din ga fitsari a wando, zan zuba taɓar wallahi”.

Cikin dariya Aisha ta ce “Ki gauraya da mai sunan baba ba” tare suka cigaba da dariya, kamar babu abin da yake damunsu duk su biyun. Can aisha ta ce “Wai ina ɗan kunnenki, na ga kunnenki babu yari”.

Ruma ta haɗiye lomar wainar da ke bakinta ta ce “Ai ni ina ga sai salla salla nake saka ɗan kunne, nifa kamar su Huzaifa haka nake yawona, dan da za a barni, zan iya yawo da gajeren wando a cikin unguwa, in je ayi mini askina”

Aisha ta girgiza kai ta ce “Ruma idan na biye miki, sai ki saka na fara naƙuda yanzu” ta saka hannu ta ciro ɗan kunnayen kunnenta, ta sakawa ruma.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce “Ni fa bana son ɗan kunne, idan suka dameni tsaf zan ciresu na watsar”

“Ruma kin san kuɗin abin da na saka miki a kunnenki kuwa? Gold ne tafiyayye daga dubai, dan Allah kar ki yar”.

“To ni me zan da shi?” Ruma ta tambaye ta tana shafa kunnenta.

“Bar miki na yi, ga wannan ma, ta miƙawa ruma ɗan kwalin kayanta, ta ƙulle wani abu a ciki ta ce “Sarƙar ɗan kunnen ce, da zobuna da kuma sarƙar ƙafa”.

“To su kuma me za ayi da su?” Aisha ta ɗan yi shiru, daga bisani kuma ta ce  “Ajiya ce na baki, zan karɓa, idan kuma ban karɓa ba na bar miki”

“To ni yanzu wannan ajiyar taki, a kaina zan ɗaurata ko kuma ƙuguna zan ɗaurawa, dan tsaf zan manta ya kama gabansa na kama nawa”

“Amana ce fa, ki kula da su sosai” ruma ta takurawa aisha sai da ta ɗan ci wainar nan, amma kallo ɗaya zaka yi wa aisha ka san bata da lafiya, amma sai ƙarfin hali take tana biyewa rumaisa.

A ‘yan kwanakin nan kusan kullum, akwai kalar mutanen da suke zuwa wurin nan, wasu idan sun zo su ɗauki manyan jakunkuna.

Yau ma wasu ne suka zo a babura kusan huɗu, amma su waɗan nan sanye da baƙaƙen coat, suma fuskokinsu a rufe, ruma ba ta damu da su ba, ta mayar da hankalinta kan aisha, tana fatan kar ƙarar baburan nan nasu ya tasheta.

Bayan mutanen sun tattauna da waɗanda suka sace ruma, kai tsaye aka nuno musu in da su ruma ke zaune, suka tunkari su rumaisa.

Tsayawa ruma ta yi taga ikon Allah,wurin wa aka zo, wurinta ko kuma wurin Aisha….

Cigaba da tunkaro su ruma suka yi, ruma kuma ta tattara hankalinta ta ga me za ayi.

Suna zuwa suka kewaye su rumaisa, ɗaya daga cikin su ya sanya hannu zai ɗaga Aisha, amma ruma ta saka hannu ta kare, ta ce ‘Wai me zaka yi mata? Matar aure ce fa yaya zaka taɓa ta?”.

“Ke, ni ki ke yi wa wannan maganar?” Ya kuma kai hannu zai janyo Aisha, amma ruma ta riƙe hannunsa. Jin hayaniya ya sanya Aisha motsawa a hankali ta buɗe idonta, ta kalli mutanen da ke tsaye a kanta, ta yinƙura da ƙyar ta tashi zaune ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un Lafiya?”

A karo na uku, mutumin ya kai hannu ya danƙi Aisha, ya fara janta, ruma kuma ta miƙe zata bi bayansa, ɗaya daga cikinsu ya danƙo ruma, yayi jifa da ita a gefe ya saita ta da bindiga.

Da sauri sha tara ya ce “A’a kar ka kuskura ka yi mata wani abu, akwai yarjejeniya tsakaninmu da ƙungiyar su barde, mun yi yarjejeniya a kanta, muddin wani abu ya sameta zamu yaƙi juna, babu ruwanku da ita, zan riƙe muku ita, dan ba zata yarda ta bari ku yi aikinku ba”.

Yayi maganar tare da ƙarasawa ya danƙo ruma, aikuwa ta hau bori, tana kiran Anty Aisha, Aisha kuwa ta kasa magana, sai miƙawa ruma hannu take yi, mutumin nan kuwa babu imani sai janta yake yi.

Cikin gigita ruma ta ce “Dalla ka cikani, suwaye su me zasu yi mata?”

Sha tara ya ce “Ke a shegen shishshigin ki, zaki jawa kanki abun da ba shikenan ba” kan ruma ta kuma yin wata maganar, sha tara ya watsa wa ruma wani abu a fuska, ta silalale a wurin nan, tana gani sama-sama.

***

“Uwani ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, bana son a wannan karon a samu wata matsala, ki yi mini aikin nan yadda yakamata”

Baba uwani ta risuna ta ce “In Allah ya yarda ba zan bari a samu wani kuskure ba uwar ɗakina”.

“Yauwwa, aikin da na saka ki ki ka kasa, Fauziyya ta yi mini rabin aikin, dan haka ƙarashe ne zaki yi yanzu, Fauziyya ta tabattar mini da ta gano in da maganin nan yake, yana ɗakin iman, a cikin drowern mudubinta, dan haka duk yadda zaki yi, ki samo mukulli ki buɗe wardrobe ɗin nan, ki ɗauko mini, akwai wani aiki da za ayi mini, wanda lallai sai da shi”.

Baba uwani ta ɗan yi shiru tana nazarin yadda za ta ɗau wannan kasadar.

“Ya ki ka yi shiru ko ba zaki yi ba?”

“Wace ni? Ki ƙaddara an gama wannan aikin uwar ɗakina, zan yi da iznin Allah”.

“Ai na zata ba zaki yi bane, sai kuma abu na biyu, wata jita-jita nake son ki yaɗa mini a gidan nan, na san daga nan har masarauta kowa zai ji, dan duk wani mufurci ku hadimai kun iya shi. Ina son ki je ki yayata cewar, Adam ya yi shaye-shaye ya bugu ya tashi yinƙurin yi wa iman fyaɗe!”

Ras! Gaban baba uwani ya faɗi, ta gyara zamanta ta ce “Uwar ɗakina, fyaɗe kuma?”

“Eh, ko baki ji ba?”

“Allah ya baki yawan rai, na ji zan kuma aiwatar”

A wulaƙance “Mummy ta ce “Tashi ki je”

Jiki a sanyaye baba uwani ta tashi ta bar ɗakin.

A hanyar komawa sashinsu ta haɗu da baba sabuwa, sabuwa ta ƙure uwani da ido, uwani ta ce “Lafiya ki ke yi mini wannan kallon haka?”

“Lafiya lau, kawai ina tunanin ranar da dubunki ta cika ya zaki yi? Baiwar Allah can ta yarda da ke ta baki amanar kanta da ta ‘ya’yanta kina ci, duk wahalar da take yi miki”

A fusace baba uwani ta ce “To ina ruwanki, bana son saka ido fa, wallahi idan ba ki yi wasa ba, sai na gaya mata ta ɗau mataki a kan ta”.

“Wallahi ki ka gaya mata, kan ta ɗau mataki a kaina zan ɗauka a kanku, dan sai na ja abun da za’a ɗauremu duka, dan nima na san sirrinta tana sakani aiki, ni idan nayi mata babu laifi, dama hadimarta ce ni, ke kuwa fa? Ki dai ji tsoron Allah wallahi” ba ta jira me baba uwani za ta ce ba, ta tafi ta bar wurin.

Hajiya Jamila ɗawisu sarkin ado, sukari ba ka yi farin banza ba, gugar ƙarfe sha kwaramniya. Haka hadimanta suka shiga jera mata kirari, sai dai babu wanda ta kula ta cigaba da takunta ɗai-ɗai ta nufi sashin Ammi.

Ammi kuwa na zaune ita da Adam a ɗakinta, yana zaune a gabanta ya sunkuyar da kansa, sai dai duk ya rame, cikin nutsuwa da tawakalli Ammi ke yi masa nasiha.

“Har kullum Adam ba zan gaji jadadda maka batun yin addu’a ba, addu’a na da muhimmanci a rayuwarka, tun da na haifeka a cikin jarrabawa ka ke, ko in ce muke, ka ƙara haƙuri wannan ma zamu cinyeta da yardar Allah, ka yi haƙuri ka jure, na sani akwai ciwo amma ka sani, jarrabawa alamar soyayya Allah ce ga bawansa, kullum cikin Addu’a nake maka, har abada maƙiyanka fadawanka ne, waɗanda ka sani da wanda ba ka sani ba, Allah zai ije maka su in dai har kana Addu’a, ni dai fatana ka rage zafin zuciya adam, babu in da zuciya zata kai ka, ka din ga haƙuri da yanayin da duk zaka tsinci kan ka” wata hadimar Ammi ce ta nemi izini ta shiga, ta sanarwa da Ammi zuwan Mummy.

Sai da gaban Ammi ya faɗi, ba ta ƙaunar abin da zai haɗata da Mummy, dan ba ƙaramin fargaba take shiga ba, ƙarfin Addu’a ne yake sanya ta iya riƙe kanta.

Jiki a sanyaye ta tashi ta fita falo, ta tarar da Mummy a zaune a falon tana yi wa iman magana, sai dai ba ta kai ga jin abin da take cewa iman ɗin ba ta yi shiru.

Ita kanta iman ba ƙaramin tsoron Mummy take ji ba, saboda haɗuwarsu babu daɗi sam, ta tsaneta sosai da sosai.

Fuskar iman Ammi ta kalla, ta san akwai wani abu da Mummy ta gaya mata, da ya sanya Iman shiga ruɗi, dan fuskar iman kullum idan ba murmushi ba, to tabbas shagwaɓa, amma sai ta ga iman a razane.

Mummy kuwa na ganin Ammi ta faɗaɗa murmushin ta, ta risuna ta ce “Allah ya taimaki giwa, barka da fitowa”.

Ammi ta nemi wuri ta zauna, ta ce “Barkan ki dai, kuna lafiya?”

“Eh to, mun gode Allah sai dai ba na ce lau ba, yara babu wanda yake zuwa, duk sun ɗauke ƙafarsu”.

“Kin san yanayin makaranta, ba sa samun zama shi ne kawai”.

Mummy ta yi murmushi ta ce “Haka ne, dama yara ne suka zo mini da batun rashin lafiyar takawa, na ce bari na zo na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, amma gaskiya yakamata ki tashi ki nema masa magani, shi da ake sanya ran ya gaji mahaifinsa, amma ya din ga abu kamar mahaukaci, gaba ɗaya zance ya cika masarauta har kunnen manya”.

Kalmar mahaukacin da ta kira Adam da shi, ba ƙaramin dukan Ammi ya yi ba.

Amma ta maze ta ce “Ai shi lamari irin wannan, duk maganin da zaka nema, lafiya ta Allah ce, idan ka miƙa masa lamarinka kuma, sai ya kawo maka mafita, tun da shi ya halicci kowa”.

Mummy ta ɗan kaɗa ƙafa ta ce “Haka ne, akwai wasu ɗabi’unki da suke burgeni, wanda har nake koyi da su, ƙarfin hali da yarda da kai, bari mu gani idan yana da rabon warkewa, Allah ya bashi lafiya, na barki lafiya uwar masu jiran gado” ta miƙe tana wani irin shu’umin murmushi.

Kan iman Ammi ta mayar da idonta ta ce “Iman, me ta ce miki ne?”

Iman ta ƙaƙalo murmushi ta ce “Bakomai Ammi, tambayata take ya jikin Takawa” Ammi tayi shiru, dan ta san iman ƙarya tayi mata, ba ta takura sai ta ji ba, saboda kar ta ji abin da zai ƙara bata haushi.

***

A hankali ruma ta buɗe idonta, ta ji kanta kamar ba nata ba, yayi mata wani irin nauyi har yana nema ya rinjayeta, daga kwance nan ma jiri take yi.

Shiru ta yi tana ƙoƙarin tuna abin da ya faru, kan abun da aka watsa mata ya ɗauketa, ta tuna yadda ta ga ana jan Aisha, da ta ja ta tsaya saboda cikinta, ɗaya daga cikinsu wani ya tsinketa da mari, har sai da ta durƙushe saboda gigicewa, ɗaya daga cikinsu ya takata da ƙafarsa, ta saki ihu daga haka ruma ba ta san meya kuma faruwa ba.

A gigice ruma ta tashi, sai dai ta cigaba da tangaɗi, saboda abun bai saketa ba, Aisha ta hango a zaune jingine da bishiyar da suke kwana a ƙasanta da daddare.

Ruma ta nufeta, amma ta kasa sauri, da ta yi ƙoƙarin yin sauri, sai ta ji tana ƙoƙarin faɗuwa.

Tana zuwa ta tarar da Aisha a zaune, idonta ɗaya ya tara jini, fuskarta duk a kumbure, zaninta kuma na farin leshi, ya rine da jini, sai haki take yi.

“Anty Aisha menene? Me suka yi miki?” Ruma ta yi maganar da ƙyar.

Alama ta yi wa ruma da ta ƙaraso kusa da ita, ruma ta ƙarasa a hankali ta zauna a kusa da ita. Aisha ta miƙa hannu ta riƙo na ruma, ta ɗora a kan cikinta sannan ta ce “Rumaisa, takani suka yi a cikina, kin ji babyna ba ya motsi” tayi maganar tana fashewa da kuka.

Kuka ruma ta saka ta ce “Suwaye su? Me ki ka yi musu?”

“Ban sani ba, sun ce ba dan su karɓi kuɗin fansa suka ɗaukoni ba, dan su tozarta ni ne, ki yi mini Addu’a dan Allah, Allah ya sa babyna yana raye, na fara jin jiri, na zubar da jini da yawa”.

Ruma ta rasa abun yi, ta rungume Aisha suna kuka.

“Zaki iya tashi a rakaki wurin da zaki wanke jikinki?”

Barde yayi maganar yana kallon Aisha.

Ruma ta ce “Ba ta so, mugwaye azzalumai, marasa imani, me ta yi muku?”

Barde ya ce “ke! Ki daina ganin ina ɗaga miki ƙafa, wannan matar ba an ɗaukota ne dan ayi garkuwa da ita ba, mutanen da suka zo ɗazu su suka yi garkuwa da ita”.

“Wallahi ba zata je ba, ba ta so salon ku kuma yi mata wani abun”

“Shikenan, kun huta”.

Aisha ta ce “Rumaisa ki yi sallolin da suka wuce ki, sai ki sakamu a addu’a”

Ruma tayi taimama, ta miƙe ta kabarta salla, dan Anty Aisha ce ta koya mata yadda ake yin taimama, farillanta, da sunnoninta.

Da ta idar da sallar ma kusa da Aisha ta koma ta zauna, tana ta jera mata sannu.

****

Ammi na zaune a kan sallaya tana lazumi, Baba uwani ta faɗo dakinta a hargitse, da har sai da Ammi ta tsorata.

“Tuba nake ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, tuba nake ki yafe ni, na faɗo miki ɗaki babu neman iso, wani abu na jiyo da ya girgiza ni, na ga bai kamata na rufe miki ba”.

Cikin mamaki Ammi ta ce “Ke kuwa menene haka?”

“Allah ya baki yawan rai, kin san zance a cikin masarauta ba ya rufuwa, ban sani ba ko a hadiman sashin nan ne da basu san meke faruwa ba, ni kin san tun yaranki na ƙanana muke tare da ke, wani zance na ji yo da ya ɗaga mini hankali na ce dole na sanar miki”.

“Ina jinki, meyafaru?”

“Kin San rashin lafiyar nan ta takawa ba kowa ya san yana fama da ita ba, to jita-jita ta yaɗa gari wai shaye-shaye yake yi, yayi mankas yayi yinƙurin yi wa iman fyaɗe!”

Ras! Zuciyar Ammi ta yi wata irin mummunar bugawa, shaye-shaye ga kuma kalmar fyaɗe da aka jinginawa yaranta.

A kiɗime ta ce “Uwani, a ina ki ka jiyo wannan mummunan zancen?”

“Hadiman gidan turaki na ji suna faɗa, ammma suma wai-wai suke yi “.

“Kenan Samha ce ta je ta faɗi wannan maganar?”

Cikin inda-inda uwani ta ce “Amm…a..a’a ba na tunanin hakan, ban dai san yadda a kai zancen ya fasu a haka ba” Ammi ta ja wani irin numfashi ta ce “Shine, jeki kawai” daga haka ta kasa tofa komai, saboda tsananin tashin hankali.

***

Ɗan barcin da ya saci mama tana daga zaune, ta ji daɗinsa sosai, dan dama ba iya baccin take yi ba. Aliyu yana zaune ya na yi mata ninkin kaya, mai sunan Baba kuma yana gyara socket ɗin ɗakin.

A gigice mama ta farka daga baccin, ta miƙe tsaye zata fita, cikin zafin nama mai sunan baba ya tashi ya riƙota yana faɗin “Ina zaki je ne?”

“Rumaisa ce a waje tana ƙwanƙwasa ƙofa zan je na buɗe mata ne”.

“Haba, amma ya aka yi mu bamu ji bugun ba, ba kowa fa”.

“Kai umar ka sakeni, tana ƙofar gida tana bugawa, sai kuka take ni na ganta, kuma na ji bugun”. Umar zai iya ƙirga sau nawa mama ta kira sunansa da wayonsa.

Ya kwantar da murya ya ce “Mama, yau kuma umar ba baba ko mai sunan baba ba? Cewa fa ki ka yi kin ganta a waje tana kuka? Ta yaya ki ka ganta? bacci fa ki ke yi mafarki ne ba gaske ba?”

Sai kuma jikin mama yayi sanyi ta fashe da kuka ta ce “yi haƙuri babana, na zaci gaske ne, yi haƙuri na yi maka tsawa”.

Aliyu ya ce  “Mama, tun da ki ka fara mafarkin ruma a ƙofar gida tana buga gida, in sha Allah ta kusa dawowa, ina jin hakan a jikina, baki ga Adduoin fa da ake yi mata ba”.

Mama tayi murmushi ta ce “Ashe kai ma kana jin za ta dawo, na zaci nikaɗai nake ji, dan dai kar in dameku ne, ina ma san ranar da zata dawo”.

Mai sunan Baba ya girgiza kai ya ce “Shikenan, dama lokacin shan maganinki yayi, zauna in baki ki sha ki kwanta ki huta, Allah ya dawo mana da ita lafiya, ya tsare mana ita a duk in da take”.

Kamar ƙaranar yarinya mama ta ce “Kai ma kana kewarta ko babana?”

“Mama ƙanwata ce fa, duk halinta jininmu ɗaya ina kewarta, zauna to” haka ya zaunar da mama da ƙyar, ya bata magani, dan mama har likitan ƙwaƙwalwa liktanta ya bada shawar ta gani, saboda depression na neman kamata.

***

Tamkar ciwo jira yake dare yayi, ciwo ya tayar wa Aisha, sai dai ta daure ta ƙi nunawa saboda kar ruma ta tayar da hankalinta.

Ruma da hannunta ke kan cikin Aisha, ita kuma ta riƙe hannun ruma, ruma na kwance lamo ba bacci take ba, can ruma ta ce “Laaa, Anty Aisha wallahi jaririnki ya motsa, baki ji ba?”

Da ƙyar ta yi murmushi ta ce “Na ji ruma, yana raye Allah ya sa ina da rabon ganinsa”.

“Amin, bari in yi musu magana su kai ki asibiti “

Ta riƙe ruma ta ce “Ƙyalesu, ba zasu kai ni ba, na ji sauƙi ki zauna mu yi hira”

Ruma ta ce “Ni bana son hirar, so nake na ga kin koma kamar da”

Cikin dakiya ta din ga yi wa ruma hira, tana sakata dariya, amma a ƙasanta kuwa jini ne yake zuba sosai.

Jin tana cigaba da numfashi da ƙyar, ya sanya ruma ta tashi, ta tafi wurin ‘yan bindigar nan ta ce “Dan Allah sha tara ku kai ta Asibiti, bata da lafiya sosai wallahi”

Duk da duhu ne, ya kunna fitila ya haske in da Aisha take, sai jujjuya kai take, zaninta yayi sharkaf da jini.

A aljihunsa ya sanya hannu, ya ciro wayarsa, ya kira wata lamba.

“Oga, matar nan fa kar ta mace mana, ya ake ciki azo a fita da ita ko zuwa wayewar gari ne”

Ruma ta kasa kunne, sai dai ba ta jiyo me na cikin wayar yake cewa ba. Sha tara ya kashe wayar ya ce “Da safe za a kaita asibitin, tafi ki kwanta”

Ruma ta tashi ta koma wurin Aisha, tana gaya mata ai da safe zaa kaita asibiti.

Aisha ta jinjina kai, ruma ta ce “Anty Aisha, wai daga ina jinin nan yake fitowa, ko fitsarinsa ki ke yi ne?”

“A’a ruma, amma dan Allah matso in din ga jinki a kusa da ni, jiri nake ji”.

Ruma ta matsa ba tare da ƙyamar jinin ba, ta rungume Aisha.

“Rumaisa ina ɗan kwalina da na baki?”

“Yana ƙunguna na ɗaure shi, na baki ne?”

Ta ce “Yauwwa sannunki baby rumaisa, ina ƙaunarki sosai”

Ruma da kuka take ta ce “Nima ina sonki sosai Anty Aisha”.

“Idan na haifi mace sunanki zan saka mata, idan namiji ne kuma sunan wannan abokin naki da ya taɓa miki ƙirji, ya ma ki ka ce sunansa?” Ta yi maganar cike da zolaya, da son kunna ruma.

Aikuwa ruma ta ce “Wallahi ba za’a saka masa sunansa ba, ke me yayi miki zafi, zaki saka sunan ɗan iska, ba gara a saka sunan Barde ba, tun da dai yana bamu abinci”

Ta yi dariya ta ce “To a saka mai sunan Baba”

Ruma ta ce “Kaii, ban baki wannan shawarar ba, faɗansa kaɗai ya isheki”.

Aisha tayi wa ruma wani irin riƙo tana nishi, sannan ta ce “Kawo kunnenki ki ji wata magana”.

Gaba ɗaya jikin ruma yayi sanyi, bayan ta gama gaya mata abin da zata gaya mata, sai da ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, tana nazarin abun da ta gaya mata.

Haka suka wanzu, ba su rintsa ba a daren, sauran mutane sai dai wanda yayi juyi ya yi wa Aisha sannu. Lokaci lokaci kuma sai ta danƙi hannun ruma tana wani irin yinƙuri da kakari, ita kaɗai ta san abun da take ji, ruma kuwa sai dai tayi ta mata sannu da addu’a Allah ya bata lafiya. A haka har gari ya waye, ta ɗaga ruma ta ce ta je ta yi salla.

Da ƙyar ruma ta iya tashi, jikinta da jinin nan ta yi salla, dan ba ta da wasu kayan, kuma ba ta da ruwan wankewa, jikin ruma duk a sanyaye yake.

Tana idarwa ta nufo in da Aisha take, amma ta ga wasu daga cikin matan wurin sun kakkare Aisha, suka hana ruma ƙarasawa, sun kewayeta.

Ruma ta ɗan ƙare musu kallo ta ce “Wai me ku ke yi haka ne?, da can baku kulata ba ta kwana babu bacci, sai yanzu, ku bari na ganta mana meyasameta?” ɗayar ta ce ‘yi haƙuri, zaki ganta ne haihuwa za ta  yi “

“To shine zaku wani kareta, ba amayo shi kawai za ta yi ta bakinta ba, ku matsa dan Allah”

Kakarin Aisha ta jiyo tana salati, tana kiran sunaye daban-daban, ta shiga kiran sunan ruma.

Ruma ta gigice, sai dai matan suka cika mata ido ta kasa yi musu rashin kunya, dan duk da girmansu.

“Anty Aisha, kin ganni a nan sun hanani zuwa wurinki, meya same ki?”

Jin kukan jariri ruma ta yi ya karaɗe ko ina, sai hamdala Aisha take tana nishi sama-sama. Ba su farga ba, sai ganin ruma suka yi a tsakiyar su.

“Anty Aisha kin haihu? Sannu”

“Yauwwa ruma, kin gani ashe babyna bai mutu ba”

Sam hankalin ruma bai kai daga ina ɗan nan ya fito ba, ita dai ta ga jaririn a kan Aisha ta ce “Ai dama na gaya miki yana motsi, yana nan da ransa bai mutu ba” ruma ta mayar da hankalinta kan jagwalon da yaron yake ciki, ga jini face-face abun babu kyawun gani, yaron ƙato da shi sai tsala ihu yake, bakinsa yana karkarwa saboda sanyi.

Matan suka shiga laliben abin da za a yanke cibiya da shi.

Aisha kuwa ta riƙe hannun ruma sai murzawa take tana cigaba da salati.

Su kansu ‘yan bindigar rasa abun yi suka yi, tausayawa Aisha za su yi, ko yaya za su yi mata, basu taɓa kamo wadda ta haife musu a wuri ba, sai a wannan karon.

Ruma hijjabinta ta bayar, aka nannaɗe jaririn, sannan aka saka shi a mayafin Aisha, aka ɗora mata shi a jikinta.

Haka ta yi ƙoƙarin rungumeshi, amma ta kasa ɗaga hannunta, sai ruma ce ta riƙe mata shi, ta din ga kwarara masa Addu’a, tana saka masa albarka daga baya ta koma yi wa rumaisa Addu’a.

“Anty Aisha, to ki tashi zaune mana, idan barde ya zo ya kawo abinci sai ki ci, ki ba shi ya sha kuka yake”

“A’a ruma, ba zan iya tashi ba, ki yi masa addu’a kawai, na bar miki shi halak malak, na bar miki shi har abada, daga yau ke ce ummansa, ubangiji Allah ya raya miki shi da imani, ki saka masa duk sunan da ki ke so”

“Kar dai zafin ciwo ya sa ki ce kin bar mini shi, daga baya ki zo ki ce ba haka ba”

Ta yi murmushi ba ta ce komai ba, ɗaga kai ta kalli yadda jaririn yake ta motsi a cikin zani, ko arzikin wando bai samu ba.

Hawaye ya zubo daga idonta  ta ce “Allah ya rayaka, ka kula mini da baby rumaisa na”.

“Dan Allah anty aisha ki daina wannan maganganun, ni bana jin daɗi, tsigar jikina ma duk tashi take yi. Sun ce za su kai ki asibiti, yanzu jira zan in ga gudun ruwansu, idan basu zo sun kai ki ba, in je in tayar da tarzoma, in tayar wa da kowa hankali”.

Ta girgiza kai ta ce “Ba zaki canza hali ba ai” tayi maganar cikin ƙarfin hali tare da murmushi.

A hankali take salati tana juya kanta, ruma ta miƙe da jaririn ta bawa wata mata ta ce “Goya mini shi”. Matar ba ta yi wa ruma musu ba ta goya mata shi, dan kamar tsoron ruma suke ji, sun ga yadda su kansu mutanen ke lallaɓata, sun tsoron su ɓata mata rai, a kashe su.

Ta juya wa aisha bayanta ta ce “Ya ki ka ganshi a bayana?”

“Yayi miki kyau sosai, Allah ya raya miki, amma baki gaya mini sunan sa ba”

Ruma ta yi murmushi ta ce “Zan gaya miki, sai an kai ki asibiti tukuna”.

Ta ja numfashi ta ce “Dan Allah samo mini ruwa na sha ruma”.

Ruma ta tafi da sauri ta karɓo ruwa a wurin su sha tara, sai buga waya suke suna magana a kan Aisha”.

“Wai dan Allah yaushe za a kaita asibitin ne, tana shan wahala fa sosai “.

“Za’a kaita, mota muke jira a kawo” suka faɗa dan kwantar mata da hankali.

Ta dawo ta sake kallon jikin Aisha, tamkar an tsomata a bokitin jini, ta yi jalaf kamar an zuba mata.

Ruma ta ɗagota ta fara bata ruwan, maƙwarwa biyu kawai ta yi ta ce “Alhamdilillah” daga nan bata kuma magana ba.

Ruma ta ce “Masha Allah, ai gara ki yi baccin sai ki huta, Allah ya sa motar ta zo da wuri.

Ta ƙulle bakin ledar pure water, ta ajiye, ta gyara wa aisha kwanciyar kanta.

Ta koma tana ta zagayawa tana jijjiga jaririn da yake bayanta, sai dai yaron ya din ga tsala ihu, kamar ana tsoma shi a wuta.

Ruma ta koma wurin Aisha ta tattaɓata ta ce “Anty Aisha, ki tashi ki gwada shayar da shi, kin ga sai kuka yake yi” shiru Aisha ba ta motasa ba.

“Anty Aisha, har baccin naki yayi nauyi haka? Ki tashi kuka yake” taga matan da suka karɓi haihuwar suna kallon kallo, suna kallon ruma.

“Dan Allah ku zo ku tasheta mana” tayi maganar tana sake jijjiga Aisha.

Ɗaya daga cikinsu ta zo ta tattaɓa aisha, suka haɗa ido da ɗaya daga cikin ‘yan bindigar, mai dukan ruma wato sule, ta girgiza masa kai, yayi mata alamar ta yi shiru.

Ta kalli ruma ta ce “Ki ƙyaleta, bacci ne a kanta, ki bari ta huta kin ga haihuwa ta yi”.

“To ai ba ta da nauyin bacci, bari mu gani to zuwa anjima, bari na bashi ruwa, Allah sarki Anty Aisha ai gara ki huta, kin sha wahala”

Da haka suka rufe ruma, ta bawa jaririn nan ruwa sai da ya ƙoshi da ruwan pure water, sannan ta sa aka mayar mata da shi bayanta, ta cigaba da jijjiga shi a bayanta”.

****

Kusan mintuna biyu da shigowar Jamil ɗakin, amma takawa bai san ya shigo ba, saboda yadda yayi nisa a cikin tunani.

“Takawa, wai meye ne? Wannan wane irin tunani haka da ƙarancin shekarunka, ka tsaya tunani zai kassaraka”.

Adam bai motsa ba, da ido kawai ya kalli Jamil, ya mayar da idonsa ya lumshe, tabbas ba dan jarumta irin ta ɗa namiji ba, da kuka zai yi ko zai samu sassauci, komai ya dagule masa, abubuwan duk da ya sako gaba suna neman su gagare shi, ya kasa komai.

Jabir ne ya fito daga toilet, ya tarar da Jamil yana yi wa takawa mita.

Jabir ya gyaɗa kai ya ce “Wallahi Jamil tun kan ka shigo nake yi masa nasiha, a kan ya miƙa lamuransa ga Allah, tunani bawa wata cutar damar shigarsa ne, amma yaƙi ganewa”.

Idanun Adam suka yi jawur, ya kalle su cikin tsananin damuwa ya ce “Ya ku ke mini abu kamar wani wanda ya rasa imaninsa ne? Ina da hankali ina da imani, na yarda da ƙaddara, ina tunanin yadda zan shawo kan matsalolin da suke gabana ne, a wannan halin da nake ciki, wambai yake kirana yana ci mini mutunci, na rasa laifin me na yi masa, ba wannan ne ma ya dameni ba, wani rumors ne yake yawo wai na yi shaye-shaye na yi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, ƙanwata ko da ina haukacewa wasu lokutan amma na san iman ta haramta a gareni, ban san meyasa ƙaddarorinmu ke tafiya a kusan tare ba, ni idan sunana ya ɓaci normal ne, ba wannan ne karon farko ba, iman yarinya ce zuciyarta ta yi ƙanƙanta da duk wannan pressures ɗin, tun da maganar nan ta isketa, ta burkice ba lafiya, jikin Ammi na neman tashi, gashi kuma still wai wambai na nemana, ya ake so na yi ne?” Ya ƙarasa maganar cikin wani irin zazzafan huci mai cike da tsantsar damuwa da tashin hankali”.

Jamil ya dafa shi ya ce “Takawa, mun san komai amma ka sani, ita rayuwa haka take, yau fari gobe tsumma, ka cigaba da addu’a kawai”.

Jabir ya ce “Shiyasa na ce ka bani auren iman, ni zan jure duk wani ƙalubale, amma ka dage wai ba zaka bani ba, na rasa menene a zuciyarka”.

Cikin son sauke fushinsa ya kalli Jabir ya ce “Babu komai a raina, amma ba zaka auri iman ba”

“Kai zaka aureta kenan?”

“Eh” ya bashi amsa.

Jamil ya ce “Duk wannan ba ta taso ba, dan Allah ku yi haƙuri, ni tafiya ce ma ta kamani ta gaggawa, na zo ɗaukar system ɗina”

Jabir ya ce “Sarkin hijira, yau kana nan gobe kana can, kamar mara gaskiya”.

“Ni ne ma takawa, na san duk yawona ban kai shi ba, shi ne mara gaskiya lamba ɗaya” yayi maganar cikin zolaya, da son saka Adam murmushi, amma Adam ya tashi ya bar musu ɗakin gaba ɗaya.

***

Kusan har la’asar ta gabato, ruma ba ta ga aisha ta tashi ba, haƙurinta ya fara ƙarewa ta fara yi musu halin nata, a kan sai an kai aisha asibiti, haryanzu ba ta tashi daga bacci ba. Ta kai ta kawo ta duba aisha, ta cigaba da tsiwar azo a kai ta asibiti, su dai sauran mutanen da suka san mai ya faru, suka yi tsit aka rasa mai fahimtar da ita.

Sule ya fara ƙoƙarin zare mata ido, dan ta ishe su, amma ya tuna tashin hankali da barazana ba sa aiki a kan rumaisa.

Ta wannan surƙuƙin aka shigo da wata mota, ruma ta ce “Alhamdilillah” ta cigaba da jijjiga Aisha tana cewa “Anty Aisha tashi, ga motar da zata kai ki asibiti”.

Wasu mutane suka saukko, mutum biyu sun sanya farar PPE gown, sauran kuma mutanen da suka zo ne masu baƙaƙen kaya.

Suka ƙarso kan gawar Aisha, ruma ta ce “Ku bayin Allah da zaku zo kaita asibitin, amma baku zo da wuri ba duk ta galabaita tun ɗazu taƙi tashi daga bacci?”.

Basu kula ruma ba, hannayensu sanye da gloves, suka naɗe Aisha da zaninta, da yake kaca-kaca da jini da ƙazantar haihuwa, suka fito da wata leda, suka fara ƙoƙarin zura gawar a ciki.

A kiɗime ruma ta ce “Ya hakaz’? ya zaku sakata a leda kamar wani kifi, idan ta mutu fa?”

Ɗaya daga cikinsu ya ce “To uban waye ya ce miki tana da rai? Ta mutun ai” wata irin gigicewa ruma ta yi, ta danƙi gawar Aisha ta ce “Ƙarya ka ke yi, wallahi ba zaku sakata a leda ba, bama zaku kaita asibitin ba, ku ajiyeta zata tashi daga baccin nan da kanta”

Hankaɗeta suka yi, suka sanyata a ledar nan, suka sakata a mota, ɗayan ya ɗaga waya ya ce “Eh, ku jiramu a boda, da wannan motar zaku zo, sai ku karɓeta”

Bayan sun sakata a motar, ɗayan ya dubi bayan ruma da ta ga gama hargitsewa tana ta sambatu, ta kasa Addu’a, ya ga jariri a bayanta dan haka ya tunkareta, amma sule ya sha gabansa ya ce “me zaka yi mata?”.

“Jaririn nan zan karɓa”

Sule ya girgiza masa kai ya ce, ka ƙyalemu, da kaina zan karɓi yaron nan na kashe shi, yanzu idan kace zaka karɓe shi ta ƙarfi, sai dai ka kasheta ko yi mata illa, dan duk in da kake tunanin wata halitta mai azababben taurin kai da kafiyar masifa, aka samu wannan yarinyar an gama magana, idan kuma wani abu ya sameta, faɗa zai faru tsakaninmu da su barde, dan tana zaune ne bisa yarjejeniya, akwai yaranmu a wurinsu, idan ta cutu zasu kashe su, mu kuma ba zamu ƙyale ba”.

“Amma ka tabatta zaka kashe yaron? Muddin yaron nan ya rayu, asirinmu zai iya tonuwa, kuma ina fatan yarinyar nan ba zata bar wurin nan ba, da duk sauran wannan mutanen?”

Sule ya ce “Lokaci kawai muke jira, kar ku damu”

“To shikenan, muna kan tattaunawa da mijinta, zai kawo mana kuɗin fansarta, zuwa jibi zai kawo, idan ya kawo ku karɓa ku ajiye mana, sai a gaya masa ta mutu ita da ɗan cikinta”.

Sule ya jinjina masa kai, mutanen suka shiga cikin motar, suka kunna.

Ruma kuwa ta din ga kurma ihu tana “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, na fa bata ruwa ta sha, wallahi ba ta mutu ba, haba Anty Aishana, haka muka yi da ke, ba tare muka ce zamu tafi gida ba, har ki ka ce zaki zo gidanmu, haba Anty Aisha kin san fa na shaƙu da ke ina sonki, meyasa ki ka tafi ki barni da jaririnki, a ina zan gano danginki?”.

Sha tara ya ce “Ke rumaisa! Wai ke baki san ƙaddara ba, to sai ki bita in da ta tafi, tun da uwarki ce”.

“Eh zam bita, idan ka isa kai ɗan halak ne ka kasheni in bita, tun yaushe nake muku magiya, wataƙila da kun kasheni da ban santa na saba da ita ba. Ba zan yafe muku ba, Allah ya bi mana hakkinmu, kun sa an haifi jairiri a dajin nan babarsa ta mutu, wa zai shayar da shi? Kuna da imani kuwa, anya kun san Allah?”

“Idan baki rufe mana baki ba, wallahi sai na kashe jaririn nan kamar yadda na yi alƙawari” sule yayi maganar yana kallon ruma cikin takaici.

“Wallahi ka kashe yaron nan kai ma sai na kashe ka da hannuna, na shirya yin fito na fito da duk wanda ya taɓa mini ɗa, sai dai ku fara kasheni”

Sha tara ya ce “Ohh, barde ya barmu da bala’i, dan girman Allah ku bashi yarinyar nan kamar yadda ya buƙata mu huta da masifar wannan yarinya mai kama da tsaka”.

Ruma ba ta iya kuma cewa komai ba, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka, tun da mama ta haifeta ba ta taɓa jin wani abu mai raɗaɗi da ya daki zuciyarta irin mutuwar Aisha ba, tayi kuka tayi kuka, tun mutanen wurin suna rarrashinta suna sanya ran ta yi shiru, har suka gaji suka rabu da ita. Kan faɗuwr rana idonta suna kumbure, da ƙyar ka ke iya gani tsagar idonta saboda kumburi, ga yaron sai kuka yake, da yayi kuka sai ta tuttula masa pure water ta cigaba da rarrashinsa.

Gaba ɗaya haka suka ƙarasa wunin ranar cikin jimami, domin Aisha akwai kirki duk da rumaisa take sabgoginta, amma dai ta shiga ran Mutanen wurin, kuma sun ji mutuwarta sosai da sosai.

A haka har dare yayi, yaron ya fara karkarwa saboda jikinsa babu sutura, ga shi jikin masa duk busashshen jinin haihuwa, babu wanka babu wanki.

Ruma ta duƙunƙune shi a jikinta ta cigaba da kuka, ta shafi ƙirjinta da babu wani abun kirki a wurin sai ƙirgar dangi, balle ta bashi, to idan ma ta bashi mai zai zuƙo tun da dai ruwa ake sha a ciki, to ita nata guda nawa yake balle a ji wani ruwa a ciki.

“ƙila ma idan da ruwan, ba zai fi cokali ɗaya ba” ta bawa kanta amsa.

“Ke wallahi sai kin kawo yaron nan an kashe shi, uwar me zaki bashi duk ya cikawa mutane kunne?”

Duk da tana cikin matsananciyar damuwa, hakan bai hanata cikin ƙunƙuni cewa “uwarka zan bashi ba”.

Sule ne ya tako ya zo gaban rumaisa ya zauna, ya ce “Bani na ga jaririn”

Juya masa baya tayi, tana sake ƙanƙame yaron.

“Ganinsa kawai zan na baki, babu abin da zan yi masa”.

“Taɓ, ai Allah ɗaya ne kawai zaka ce mini na yarda da kai, wallahi ba zan bayar ba, na san kashe shi zaka yi”.

“Ke ki na ji na ko? Ki kawo yaron nan a basu, dan dole zasu dawo wurin nan, kuma kin ga za a ɗau hakkinsa, tun da dai uwarsa ta mutu, ki bani shi gobe sai a basu gawarsa kema ba iya raino zaki yi ba”

Share shi ta yi, ta cigaba jijjiga yaron a jikinta, cikin zafin nama ya danƙo ƙafafuwan yaron zai ɗaga shi, ruma ta danƙara masa cizo a hannun, zafin cizon ya sanya ya saka hannunsa ɗaya ya daki kanta.

Sai da ta daina ganewa na wucin gadi, kanta ya juye gaba ɗaya, amma hakan bai saka ta saki jaririn ba.

“Wallahi sai na kashe yarinyar nan, uban kowa ma ya huta, sai dai duk wadda zata faru ta faru”.

Sha tara ya ce “A’a sule, ka san yadda mu ka yi da su barde, ka ɗan ƙara haƙuri, bana son fitina ta shiga tsakaninmu da su ne”.

“Wallahi na tsani yarinyar nan, iskancinta yayi yawa, tun da na fara harkar nan ban taɓa haɗuwa da ɗan rainin hankalin da yake abin da ya ga dama ba irin ta”.

Banza ruma ta yi masa, kamar ba ta san me yake cewa ba, ta rungume jariri ta cigaba da kuka, ji take ina ma tun kan ta san Aisha suka kasheta, wani irin so da tausayin jaririn nan suka rufeta, haka yake tik jikinsa babu kaya.

Sule kuwa a ƙule ya ce “Yanzu haka zamu cigaba da zama wannan ɗan tayin yana cika mana kunnuwa, uban me zamu ba shi?”.

“To ba ita ta ga zata iya ba, sai ka ƙyaleta ai”.

“Amma mun riga mun yi da su a kan cewa zamu kashe yaron nan, yanzu me zamu ce musu?”.

Sha tara ya ce “Ai babu lallai su dawo, ko ma zasu dawo kan su dawo ɗin zamu san abin yi”

Sauran matan wurin babu yadda ba su yi ba, a kan ruma ta bayar da jaririn su tayata rarrashinsa, amma ta ce ba zata bayar ba, dan bata yarda da kowa ba, gashi ɗan ruwan da take ɗaɗɗaka masa ya ƙare.

Haka dare yayi, salla idan zata yi, sai ta bayar a goya mata shi, jaririn yana kuka ita ma tana kuka, gwanin ban tausayi.

Dare yayi sosai, amma ruma tana tsaye, tana aikin jijjiga yaron nan, sha tara ya kalleta ya ce “Wannan Yarinya da gani irin maita ce, kalli dan Allah dan bala’i yaro ya hanata bacci ya hana mutane sukuni, amma taƙi bari a kashe shi, sai wahala take yi, shegiya taurin kai kamar jinjirar jaka”.

Sule ya ce “Ko kuma kafuran farko ba, wallahi da ka barni da saina harbesu su duka, kowa ma ya huta”.

“Ƙyaleta dai tukuna, mu ga iya gudun ruwan barde”.

Haka ruma ta shafe awanni ta na fama da yaron nan, ta roƙi su sha tara su bata ruwa ta kuma bashi, amma suka ce ba zasu bayar ba.

Sai da yayi mai isarsa, sannan ya yi shiru, ta koma wajen bishiyar da Aisha ta mutu, ta jingina tayi shiru tana tuna yadda suka yi ta hira daren jiya, amma yanzu wai babu ita a doron duniya sai ɗan ta. A haka wani ɓarawon bacci ya kwashe rumaisa.

****

“Yaya Jamil, ya jikin takawa kuwa?” Samha ta yi maganar tare da tattara hankalinta a kan Jamil.

“Ya ji sauƙi”.

“Sauƙi sosai dai, ni fa na tsorata da yanayin da na ganshi a ciki, kaga abun da yayi wa iman kuwa?”

“Kenan kune ku ka je ku ka ce yayi shaye-shaye yayi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, kun sanya ‘yar mutane a wahala jikinta ya rikice”.

Waro ido samha ta yi ta ce “Mu kuma? Yaushe? Wallahi ni ban faɗa ba”.

“To yaya aka yi wannan banzan zancen mara ma’ana ya fita, ke kin san dai takawa ba ya shaye-shaye, idan ma kin yi haka ne dan cimma ƙudurinki, ba zai aureki ba, ke ma kin san ko da aure bai haramta a tsakaninku ba, amma a al’adance takawa ya haramta a gareki a yanzu dan haka tun wuri ki shiga hankalinki, kuma ki nemi wani a manemanki ki yi aure ki huta, ko kuma ki cigaba da dakon soyayyar sa a banza da babu abun da zata amfana miki”.

Shiru Samha ta yi, ta san babu tantama makircin Mummy ne da Fauziyya.

“Kun fara wuce gona da iri, ina bin ku ne don kawai na ga in da ku ka dosa, amma kina zaƙewa hajiya Jamila ” tayi maganar a zuciyarta.

“Ai kai Jamil wataƙila idan ka gaya mata ta ji, tun da ni ban isa na gaya mata ba, tun wuri na ce ki fita a sabgar yaron nan, komai ki ke yi ba kya gabansa, amma ki nace samha kamar shine autan maza, yaron nan bashi da mutunci ko kaɗan, ni kaina uwarku wani gani-gani yake mini, amma daga ke har Jamil sai wani shishshige masa ku ke yi”.

Jamil ya ce “Mama, kin san halinsa yana iya ƙoƙarin sa wurin mu’amalantar kowa yadda ya dace, amma tare muka taso, dan haka bashi da wasu abokai sai mu, tun da duk tsatso ɗaya muke, wannan yarinyar ce dai idan har bata shiga hankalinta a kan sa ba, zata cigaba da shan wahala ne”.

Zumɓura baki Samha ta yi, ta tashi ta bar ɗakin, dan babu mai gaya mata ta ji, in dai a kan takawa ne, son sa ma yanzu ta fara.

***

Da sallama takawa ya shiga ɗakin ammi, in da iman ke kwance a kan gadon ammi, ta rufe rabin jikinta da bargo, Nusaiba na ta jera mata sannu.

Yana shigowa suka ƙara nutsuwa suna gaishe shi, ya amsa musu sama-sama, ya ƙarasa gaban gadon ya ce “Iman, ya jiki?”

“Da sauƙi yaya” ta amsa a sassanyar muryarta.

Yayi ƙasa da murya ya ce “Am sorry, duk laifina ne abubuwa suke ta faruwa a haka, amma dan Allah ki yi haƙuri kin ji, bana son wani abu ya sameki, ba zamu iya jurewa ba, ki mayar da komai ba komai ba, sannan ki toshe kunnenki a kan duk abin da za a faɗa”.

Ta jinjina masa kai ta ce “Ina sha Allah yaya, kuma kar ka damu, in sha Allah komai zai wuce ne”.

Ya ce “Ina fatan hakan, ga jabir can yana son yayi miki sannu, taso mu je falon”.

Ji ta yi kamar ta ce a’a, amma ta san ba ta isa ta ce a’a ɗin ba, dan haka ta ɗau hijjabinta ta saka, Nusaiba ta rungumo iman suka fito falon tare.

Sai dai da suka fito, takawa ya tarar da Samha a falon a zaune.

Basarwa yayi bai ko nuna ya ga samha ba, Jabir kuwa ya kafe iman da ido kamar maye.

Samha ta gyara zamanta cikin iyayi ta ce “Yaya ya ƙarfin jiki?” Ya ɗago ya kalli Samha, ya ɗan ƙura mata ido, amma bai ce komai ba.

Nusaiba ta ce “Uncle J ina kwana?”.

“Lafiya lau, ya gida ya Ammi?”

“Ammi na lafiya, ta fita ne”.

Jabir ya mayar da idonsa kan Iman ya ce “Iman, ashe baki ji daɗi ba, ya jikin?”

Cikin yanayinta na rashin son magana da kuma ƙosawa ta ce “Da sauƙi”

“Allah ya baki lafiya autarmu, duk na kasa sukuni tun da aka ce mini jikinki ya motsa, amma na yi mamakin da na ganki a gida, takawa ba za a kaita asibiti ba?”.

“Eh na za a kaita ba, amma tun da ha ka ka zo, sai ka kaita?”.

“Kar ka gaya mini magana mana, daga tambaya, dole na tuhumi yadda ake nema ayi sake da lafiyar auta”. Haɗe rai iman ta kuma yi, ba ta ce komai ba, dan gaba ɗaya ta ƙosa da zaman.

Samha kuwa da zancen iman ya fara ƙular da ita, ta yi gyaran murya ta ce “Takawa duk ka rame wallahi”.

Jabir ya ce “Ba dole ba, ya sanya tunani da damuwar a ransa, gaba ɗaya ya koma wani iri”.

Samha ta din ga zubo zance, amma takawa ya ƙi kulata, ya kashingiɗa yayi musu shiru.

Iman ta ce “Ni dai zan koma ɗaki jiri nake ji, sai anjimanku”.

Takawa ya kalleta ya ce “Ko na mayar da ke ɗakin?”.

Samha ta yi zumbur ta tashi, ta nufi iman ta na faɗin “Haba dai, gani a zaune, bari na rakata tun da jiri take ji” sai da gaban iman ya faɗi, sam ba ta so haka ba, dan ta san da biyu ta ce zata kaita ɗaki.

Ta rungumi iman, ta nufi sashin Ammi da ita, iman ta ce “A’a ɗakina zan koma”.

Samha ta ce “Bakomai, bari na rakaki” tayi maganar kamar gaske.

Sai da suka shiga ɗakin iman, sannan ta taƙarƙare, ta hankaɗa Iman kan gadon, ba tare da tausayin halin da iman ɗin ke ciki ba.

Ta murtuke fuska ta ce “Ke ‘yar tsintuwa, kalleni da kyau, ya muka yi da ke?”.

“Anty Samha me na yi miki?”.

Cikin ƙulewa Samha ta ce “Ke fa tsohuwar munafuka ce, kullum na yi magana sai ki ce mini, ke babu komai a tsakanin ki da takawa, amma kullum cikin naniƙe masa ki ke, ko abun da ake faɗa ɗin gaske ne, kina kai masa kanki?”

Iman ta yi shiruu, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, amma ba ta da bakin magana, ‘yar tsintuwa ce kamar yadda Samha ta faɗa.

Maganar samha ce ta dawo da ita hayyacinta, “Wallahi idan ki ka cigaba da shishshige wa Adam, sai na sa kin yi dana sanin zuwanki duniyar nan, sai na mai da ke matacciya da rai, sai na yi miki illar da ba kya zato, ki kiyayi adam ki daina yi masa shishshigi idan ba haka ba zan aikata abin da na faɗa, banza mai kyan banza ‘yar tsintuwa, ke ban da abinki ma, har kina tunanin haɗa jiki da jinik sarauta ƙasƙantacciya irinki, da babu wanda yake da taabbcin ‘yar halak ce ke, ƙila ma ‘yar gaba da alfatiha ce”

Duk yadda Samha ta din ga yi wa iman baƙaƙen maganganu, ba ta tanka ba, tayi ta gama ta fita. Sai da ta fitan sannan iman ta bawa hawayen idonta damar zubowa.

Tana tsaka da kukan baba uwani ta shigo ɗakin ” ‘yar auta ya jikin naki?”.

Iman tayi maza ta rufe idonta kamar tana bacci.

Ta leƙa fuskar iman, ta ga idonta a rufe, cikin sanɗa ta koma gaban mudubin ɗakin iman, ta hau laluben mukullin drower mudubin iman.

A hankali iman ta buɗe ido tana kallon baba uwani, tare da tunanin binciken me take yi mata a ɗaki haka.

Tari tayi tare da ƙoƙarin gyara kwanciyarta, ta buɗe idonta tana kallonta, nan da nan baba uwani ta diririce, ta fara kame-kame “Amm..amm…’yar auta dama idonki biyu ne? Dama na ce bari na zo na yi miki sannu, sannan na ɗan tattare miki ɗakin”.

Iman ta ce “Bakomai baba uwani, ai gyaran ɗakina ba aikin ki bane ba, ke da ki ke a kitchen, kuma ga hadimai, an gyara ɗakin da safe karki damu”.

“To..to…toooo shikenan, Allah dai ya baki lafiya iman, Allah ya yaye miki ya baki lafiya, bari na koma kitchen ɗin” ita da iman ta bita da kallo, ba ta ga alamar gaskiya a tare da ita ba.

***

Cike da wata irin mummunar faɗuwar gaba, rumaisa ta farka daga baccin da ya ɗan ɗauketa, ta ga jaririn nan dai yana rungume a jikinta, idonsa biyu sai cin hannunsa yake, kai da gani babu tambaya ka san yunwa yake ji.

Tana ɗaga ido ta hango barde a kan babur shi da wani, sule na ganinsa ya ce “Yauwwa dama kai muke jira”.

Su ka yi parking ɗin baburin, barde ya sauka hannunsa riƙe da leda.

Ya ƙurawa rumaisa ido, ya nufi in da take, ya durƙusa a gabanta, ya saka hannu ya ɗaga zanin da jaririn ke ciki, ya kalli yaron. Bai yi magana ba ya ga ruma tana zubar da hawaye.

Bai ce mata komai ba, ya kwance mata ledar gabansa, koko ne da ƙosai a ciki, sai madarar peak guda biyar ya ce “Gashi nan, na ga da ki ka yi rashin lafiya kina ta amai, wataƙila har da ulcer, ga madara nan ga kuma abinci ki din ga kula da abinci, in anjima zan aiko yarona da abinci, ba a samo waina a in da ake sayo miki ba”.

Maimakon ta yi masa godiya cikin kuka ta ce “Aisha ta mutu fa, jaririnta ne wannan”.

“Na sani, ita tata ta ƙare, Allah ya karɓi shahadarta”.

“Shikenan haka zan ta zama a nan wurin sai wahala ta kasheni? Ku baku kasheni ba, ku baku sakeni ba”.

“Ke, ki mayar da hankali ki ci abinci na ce”.

“Ba zan ci ba, ka kwashe tsiyarka” kallonta ya yi a fusace ya ce “Ni ki ke gayawa haka?”

“Eh ɗin” sai kuma ta ɗan yi shiru ta ce “ka yi haƙuri dan Allah, na gaji ne ban san a halin da mama da yayyena suke ciki ba, na gaji da zaman wurin nan, dan Allah a tunaninka abin da ku ke yi ɗin nan kun yi mana adalci, kalli fa jaririn nan, ya rasa mamanshi an haife shi a tsakiyar daji, ko kaya babu a jikinsa fa, ga yunwa yana ji, kalli wurin kwananmu, yau a kashe wannan, gobe a wulaƙanta wancan ya kuke so mu yi? Galibinmu fa duk talakawa ne, ba ‘yan masu kuɗi ba”.

“Kin san meyasa nake ta baki kariya kar a kashe ki?” Ta girgiza masa kai.

Ya ce “Gyaɗar da ki ka bani a kasuwa, ki ka ce idan ina da ‘ya’ya in kai musu, na gaza samun tsaro a ƙasata, a kan idona na rasa iyayena, da ‘ya’yana biyu da yunwa ce ta kashe ɗaya, saboda hare-haren ‘yan ta’adda bana iya fita samo musu abun da zasu ci, aka sace ɗan uwana, sai da na sayar da komai nawa domin karɓo shi, aka kashe shi, shiyasa da aka yi mini tayin wannan harkar ban ji ko ɗar ba na karɓa na shiga, idan ya so duk ayi mutuwar kasko, kuma na samu ƙwarin gwiwa ne, tun bayan da na san iyayen gidanmu su ne tsaro a ƙasar nan….. Sule ne ya kaste barde ta hanyar cewa “Kai fa nake jira mu yi magana, ya za ayi ka karɓo mana jaririn nan mu kashe shi, mun riga mun yi wa mutanen smoke wannan alƙawarin, yarinyar nan ta ƙeƙashe ƙasa ta hana yaron nan, ina tsoron muyi mata illa, mu saɓa waccan yarjejeniya da ke tsakaninmu da ku”.

Barde ya kalli rumaisa, sannan ya kalli sule ya ce “Kar ka damu, gobe zamu kawo muku mutanenku, ku bamu ita, mai gida da kansa zai zo wurin nan”

Sule ya yi murmushi ya ce “To madalla, ai hakanma yayi”

Suka cigaba da tattaunawa, ruma kuwa ta samu wata ledar pure water, ta zuba kokon nan a ciki, ta zazzaga madara, ta dinga bawa jaririn nan.

Haka nan yaron nan ya din ga shan kokon da ruma ke ɗura masa, ba ta san ya ƙoshi ba, sai da ya din ga kwarara amai ta hanci ta baki.

“Rumaisa ya zaki bawa jaririn kwana biyu koko, ai sai ki ja masa wani abun” cewar wata dattijuwar mata.

“To baba ko in baki shi ki shayar da shi ne? Idan ban bashi koko ba mai zan bashi, da ma aka samu kokon, tausayinsa nake ji, da mamansa na nan, da ya samu sauƙin wani abun, ka yi haƙuri ka ji yarona, Allah ya kula mini da kai, ya jiƙan anty aisha” tayi maganar tana zubar da hawaye tana goge masa aman da yayi da zanin da yake ciki.

Bayan tafiyar barde, sule ya cewa ruma “Sai ki gode Allah, gobe zasu bamu mutanenmu dan su karɓeki, mu kuma a goben zamu kashe ki, ba zamu basu ke ba”.

Duk da tsiwar da ruma take yi musu, a kan su kasheta, sai da gabanta ya faɗi jin ya ce gobe zasu kashe ta, to yaya jaririn nan zai kasance kenan? A zahiri kuwa ko gezau ba ta yi ba, sai cigaba da gogewa jaririnta amai da ta cigaba da yi.

Azabar galabaita ta sanya yaron ko kukan kirki ya daina yi, sai dai yai kaɗan yayi shiru, ga wani irin numfashi da yake yi, iya ƙirjinsa kai da gani ka san ba shi da cikakkiyar lafiya.

Yau tun da garin Allah ya waye, bayan rumaisa ta yi sallar asuba, ta zubawa wurin da suke zama ita da aisha ido,, sai wasi-wasi take yi, tayaya jaririn nan zai rayu? Ance kasheta za ayi, waye zai kula da ɗan ta san dai ƙarshenta shi ma kashe shi za su yi, ga wata irin soyayyar yaron da ke ratsa zuciyar rumaisa.

Tana zaune a gefe, tana saƙawa taan warwarewa, ta ji tamkar ta tashi ta gudu, amma ta san da ta gudu zasu harbeta, sun ce yau za su kasheta, amma ta ga cikinsu babu wanda ya saurareta. Sha tara ne ma ya dubeta yana dariya ya ce “Duk shirin tafiyar ne na ga kin nutsu, sai ki bi masoyiyyar taki, ƙarshen ƙauna har ɗan naku ms zamu haɗa mu turo muku ku ci soyayya” tsaki tayi ta kawar da kanta gefe. Ya din ga ƙyaƙyata mata dariya.

Sai dai wunin ranar ya shuɗe barde bai dawo ba, balle ta san matsayarta, peak ɗin nan ta dinga zubawa a pure water tana ɗurawa jariri, sai dai duk girman nan nasa ya sace, fatarsa ta fara yamushewa, idanun jaririn suka yi yellow, ga zafi da jikinsa yake ɗauka, ga fatar jikinsa duk ta yi alamar ƙarancin jini da oxygen, idan jikin nan nasa yayi zafi, sai dai ta saka shi a gaba, tayi ta uban kuka, ba ta taɓa tsammanin cin karo da ƙalubale mai girgiza zuciya irin wannan ba.

A kwana na huɗu, tun safe sule yake masifa, ya ce idan har barde bai zo ba, sai ya kashe rumaisa, saboda ya riga ya sanar da mutanen smoke cewar ya kashe rumaisa da jaririn nan, babu babban abun da ya sake girgiza rumaisa, irin yadda suke commanding ɗin ‘yan uwan aisha su kawo musu kuɗi, kuma da alama masu hali ne, dan miliyan ashirin suka caza, kuma sun haɗata, suna ta yi musu kwatancen in da zasu kai kuɗin, gobe da yamma.

Rana ta karya ta kusa faɗuwa, rumaisa ta jiyo ƙarar babura da yawa, tare da harbe-harbe.

Duk da ba yau ta fara jin ƙarar bindiga ba, amma ta ɗan razana, take ‘yan bindiga suka zagaye su ruma, suka saita bindigoginsu, da shirin ko ta kwana suna saka ran idan jami’an tsaro ne, su kashe kowa a wurin.

A ƙalla sun kai babura goma duk sanye da kayan sojoji, sai dai fuskokinsu duk a rufe, sai manyan makamai da suke riƙe da su.

Suka yi parking baburan, suka sassako, sai a lokacin su sule suka nutsu, suka sauke makaman, kasancewar sun gane ko suwaye.

Barde ne ya fara buɗe fuskarsa ya ce “To yaya, kun shirya ayi musayar ko kuwa? Kun tattauna da iyayen gidan naku?”

Sule ya ce “Ai ba yau muka yi da ku ba, tun bayan kwanaki uku baya muka yi, amma ka saɓa alƙawari”.

Ɗaya daga cikin mutanen ne, ya tako a hankali zuwa gaban sule ya tsaya nesa kaɗan da shi ya ce “Rumaisa zaka bani kawai, maganar mutanenku, ma yi daga baya”.

Sule ya dube shi a fusace ya ce “Amma ka raina mini hankali, ba zan bayar da ita ba, kuma a yanzun nan zan kashe ta, yarjejeniyar ta watse, a cigaba da faɗan tsakaninmu, ko mu….

“Shhhhhh, ka san da wa ka ke magana kuwa?” Mutumin ya katse sule.

“Ban damu ba ko kai waye, yau zan kasheta kowa ya huta, na gaji da yi muku biyayya ina saɓawa iyayen gidana”. Ita rumaisa mamaki ne ya kamata, duk a kanta ake wannan taƙaddamar, shi kuma wannan mutumin ko a ina ya san sunanta oho.

Sule ya nufi ruma gadan-gadan, sai dai kan ya ƙaraso gawarsa ta faɗi a gaban rumaisa, tare da watsuwar jininsa a wurin mutumin nan ya harbe shi. Ware ido ruma ta yi jiki na rawa take kallon gawar. Kan kace kwabo, sun fara harbe-harbe a tsakanin su, sai dai mutanen sule na ta ƙoƙarin su harbe rumaisa kawai.

Sauran mutanen da suke tare da rumaisa, sai ihu suke yi, mutanen da suka zo a babur, suna kama su, suna ta ɗaurewa.

Mutumin da ya harbe Sule ya kalli ruma ya ce “Ɗauki yaron ki tashi ki tafi”.

“In tafi ina?”.

“Koma ina ne, ki tashi ki bar wurin nan kawai, saboda ke na zo” ya ƙarasa maganar yana sauke takunkumin fuskarsa, wa zata gani, mutumin nan da ya bata kaza a hanyar zuwansu katsina.

Kan tayi magana ta ga ya saka bindiga ya harbe Barde, ya furta ‘Kai ma amfaninka ya ƙare”

Sake gigicewa ta yi ta ce “Na shiga uku, meyasa zaka kashe barde, ya taimakeni sosai, meyasa zaka yi haka, ta nufi gawar barde tana kuka.

Fincikota mutumin yayi ya ce “Rumaisa, ki tafi na ce, mu a irin wannan aikin namu, babu tausayi ko sanayya, barde yana da alaƙa da iyayen gidan su sule, yarona ne, shi ya yi mini kwatancenki na ganeki, na shirya yadda zan kuɓutar da ke, da ya karɓeki kin zama mallakinss, ko kina so ki rayu da ɗan ta’adda babu aure?” Cikin tsuma ta girgiza masa kai.

“Dan haka maza ki bar wurin nan, na san yanzu za a kawo musu ɗauki, Allah ya tsare” tsyawa ta ɗan yi tana kallon gawar barde, da ke yashe a wurin da aisha ta mutu.

“Ki tafi ko in kasheki da hannuna!”

A hankali ta juya, ta ɗau hanya, hannunta rungume da jariri, ɗanyen goyo.

Da farko ta na yi tana waiwayowa, daga baya ta ƙule ta nausa cikin daji, kawai tafiya take yi, ba ta san ma in da take sanya ƙafarta ba, sai dai maimakon ta ganta a hanya sosai, sai gani ta yi tana kuma nausawa cikin surƙuƙin daji, daji ne na gaske da ya amsa sunansa daji, babban fatan ruma Allah ya sa ta gane hanyar da aka shigo da su, abun da ta manta shine, tafiyar da suka yi a kan babur ta awanni ce, a cikin duhun dare, kuma in da ta nufa ma ba ta nan hanyar aka shigo da su ba.tafiya kawai take yi, ga rana na ta tafiya gangara zata faɗi, gashi babu alamun ruma ta kusa hanya.

Duk addu’a da ta zo bakinta yin ta kawai take, ganin abun take tamkar mafarki, ta rasa ta ina ma yakamata ta bi, gashi yau jaririnta ko kukan kirki ba ya yi, amma ta ta’alaƙa hakan da yunwa yake ji, fatanta ta isa gari ta samu abun da za ta bashi ya ci kar ya mutu.

Lokaci guda mutuwar aisha da ta barde ta faɗo mata, aikuwa ta fashe da kuka, tana kuka tana faɗin “Anty Aisha ina ma tare muke tafiyar nan, ko ina suka kai gawarki oho, Allah ya yi miki rahama, kai kuma Barde ban sani ba ko Allah zai yafe maka, amma Allah ya baka ladan tausaya mini da ciyar da ni da ka din ga yi, ni dai na yafe maka duniya da lahira.

Ruma ba ta san jikinta babu ƙwari ba, sai da ta fara tafiyar nan, sannan ta gane ashe a galabaice take, jikinta babu ƙwari da ƙarfi kamar yadda take jin ta a da, gaba ɗaya ta gaji, ƙishirwa take ji, ga duhun magariba ya fara yi, kuma babu alamar samun hanya, ƙafafuwanta tuni suka yi tsami, gashi sai taka abubuwa take yi, kama daga ƙaya zuwa ƙananan duwatsu, amma zuciyarta ta cigaba da bata ƙwarin gwiwar ta tafi, tana jin zata iya fita hanya a kowane lokaci.

***

Takawa ne yake ta safa da marwa a ɗakinsa, yana daddana wayar hannunsa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san ya rame, duk yayi wani iri kamar mara lafiya.

Can ya kara wayar a kunnensa, cikin zaƙuwa ya ce “Ya ake ciki, me ka gano? Akwai wani labari ne?”.

“Easy mana Adam, wacce zan amsa maka cikin tambayoyin naka tukuna? Ka yi haƙuri wannan bayanin duk ba na waya bane ba, kana da time ka shigo abuja gobe in Allah ya kaimu?”.

Adam ya ce “Ni bani da wani time, am so much busy here, abubuwa sun yi mini yawa, koma menene kawai ka gaya mini ta waya, ina jin ka”.

“A’a ni babu abun za zan gaya maka ta waya, ka bari ni zan shigo kanon in sha Allah”

Adam ya yakice gumin da yake tsatstsafo masa, ya ce “Bashir, bani da wani isasshen lokaci da zan baka, kawai ka yi abun da na ce, koma menene ka gaya mini, kar aikin da nake yi ya koma baya”.

“Na fuskanci a rikice ka ke, idan ka sauko ma yi maganar, gaggawar ba ta da wani amfani ” kan adam ya kuma magana, ya kashe wayarsa. Ya yi jifa da wayar a kan gado, ya san tun da bashir ya ce masa ba zai gaya masa a yau ba ba zai faɗa ba.

“Bashir why, kana ƙoƙarin mayar mini da aiki baya fa, dole na zo na sameka, ba zan iya jiranka ba”.

Ya miƙe hannu ya ɗau waya ɗaya, ya sanya a aljihunsa, ya fita ya ɗau mota ya nufi family house ɗin su.

A sashen Ammi ya tarar da duk iyalan gidan ahalin marigayi Galadiman kano sun hallara, kama daga kan Mummy zuwa Fauziyya da ruƙayya, duk da ita ruƙayya ba ta fiye zama a gidan ba, tana can gidan yayar Mummy, ga kuma Ammi a zaune da iman da kuma Nusaiba, na gidan auren ne kawai ba sa nan. Takawa yayi turus yana kallonsu, wambai ya ƙure shi da ido, ya ƙaraso cikin falon yana sake tsuke fuska ya ɗam risuna ya ce “Barka da zuwa”

Wambai ya ƙi kulashi, shi kuma Adam bai tashi ba.

“Wato wuyanka har yayi kaurin da zan aika maka ka zo, ka yi burus da kirana ko?”

Yayi shiru bai ko motsa ba, sai ma alamun ɓacin rai da suka baiyyana a fuskar shi.

Da sauri Ammi ta ce “Allah ya taimake ka tuba yake yi, ayyuka ne suka sha masa kai, ga rashin lafiya da…..

“Ya isa binta, dama ke ki ke goya masa baya yake abun da ya ga dama, bai san darajar mutane ba sai zuciya ta banza da ta wofi, tabbas na fara gazgata jita-jitar da ake yi a kansa, na cewar yana shaye-shaye, duba da yanayin abubuwan da yake aikatawa, kalli yadda yake muzurai kamar zai kai mini duka, kalli yadda yake yawo a gari, kamar ba jinin sarauta ba, kalli ƙananan kayan da ke jikinsa, duk wani abu da ya shafi al’adar gidan nan nema yake ya watsr da ita, saboda kawai ya raina mutane.

Cikin dakiya Ammi ta sake cewa “Tuba yake, ayi masa afuwa”.

Adam a zuciyarsa kuwa ji yake yi tamkar ya tashi yayi tafiyarsa, don cigaba da sauraren wambai, na iya sanya wa ya ɗuɗɗura masa ashar ya huta, saboda takaici.

Wambai ya mayar da idonsa kan Ammi ya ce ‘Na san kina sane da maganar da take yawo a cikin masarautar nan, na yayi shaye-shaye yayi yimƙurin yi wa waccan yarinya fyaɗe, yayin da daga wata majiyar muka samu labarin ba fyaɗe bane ba, wani abu ne a tsakaninsu daban, to dukkaninku ku sani, ko da ɗan uwana baya raye, ba zan lamuncin mutunci da martabar gidan nan ta lalace ba, a hakan ka ke saka ran sarauta ta shiga hannunka, kana shaye-shaye ga kuma wannan mummunar maganar, ba zan lamunta ba, tun kan maganar nan ta je wurin mai martaba, zan yi wa tufkar hanci, ni na san abun yi. Ke binta ina mai baki umarni a kan lallai wannan yarinya ‘yar tsintuwa, ko dai ki nemi ahalinta ki mayar musu da ita, ko kuma ki nema mata miji ta tattara ta bar cikin gidan nan, na baki nan da abun da bai wuce watanni biyu ba, ta daina amfani da kyawunta tana barazana ga mutuncin gidan nan ba. Labarai suna zuwar mana, yadda ake ta samun akasin auren ‘ya’yan jamila saboda ita, to ki san abun yi tun kan ku kai ni bango “. Iman ta yi shiru ta sunkuyar da kai, ta riƙe yatsun Ammi tana wasa da su, tana ɗan murzawa da ƙarfi, saboda azabar ɓacin rai da damuwa.

Haka wambai ya ƙarewa Ammi cin mutunci ita da yaranta, a gaban Mummy, daga bisani ya sallame su.

Tun kan su gama watsewa daga falon, iman ta fashe da kuka, mussaman da ake ce wai ita ce ke barazana ga mutuncin gidan. Adam rasa abin da zai ce ya yi, bayan fitar wambai Mummy ta ce “Sai haƙuri fa binta, yaran yau me ka haifesu ba ka haifi halinsu, a zage a bawa yara tarbiyya, kan a samar mana da abun kunyar da zamu gagara kallon duniya, ko mu rasa sarautarmu gaba ɗaya”. Babu wanda ya tanka mata a cikin su, har Adam da yake zaune yana jin ta.

Bayan fitar Mummy Adam ya ce “Ammi, Allah fa bai ce in bi wan ubana ba, ke da marigayi kune yake wajibina na biku, dan haka babu ni babu wannan tsohon da zuriyarsa har gaban abada, ba zan ƙara zuwan kiran da zai yi mini ba, kuma ba zan sake zama a gabansa na yi masa kallon uba ba, ita kuma Mummy haryanzu kin hanani dama a kanta, shikenan idan har zamu cigaba da zuba mata ido, to fa zata cigaba da ƙoƙarin ganinmu a rana ne. Ni ban damu ba dama can ni ɗan iska ne mara mutunci a cikin masarautar nan, amma ba zan cigaba da lamuntar wulaƙanta iman ba, ko dan saboda ita yakamata ko sau ɗaya ki kareta” ya ƙarasa maganar a matuƙar zafafe, ya tashi ya bar falon.

Daga Nusaiba har iman saka Ammi suka yi a gaba suna yi mata kuka, ta rasa abun da zata yi, ta rungumesu duka a jikinta tana ajiyar zuciya.

Tabbas takawa yayi gaskiya, haƙuri da kawaicin da take nunawa a kan abubuwan da ake yi wa iman da ma iya kanta da yaranta, yayi yawa, sai dai ba tana yin hakan da wulaƙanta iman ko ‘ya’yanta ba, sai dan gudun kar ayi ƙoƙarin rabata da ita.

***

Ko arzikin ganin tafin hannunta rumaisa ba ta iya yi, saboda duhun da ya mamaye ilahirin dajin, sai kukan abubuwa daban daban da take ji, lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma ta ji shiru kamar babu wata halitta da ta wanzu a cikin dajin.

Sai yanzu ta gane a wurin ‘yan ta’addam nan a rahama take, ko ba komai tana jin motsin mutane, idan ta gaji kuma tana yi musu kuka ko da zasu hantareta,  wani irin sauro da kuma wasu irin ƙwari ne suke gasa mata cizo ko ta ko ina.

Ta yi iya ƙoƙarin ta ta nannaɗe jaririn, dan kar ƙwari su cije shi, sai numfashi yake sama-sama, jikinsa ya ɗau zafi, ita kanta rumaisan zazzaɓi ne a jikinta, ga wata irin azababbiyar ƙishirwa da kuma yunwa da take ji. A haka ta jingina a jikin bishiya tana addu’a tana kuka ƙasa-ƙasa, ba dan tana tausayin jaririn nan ba, da kuma tsoron wanda ya kashe kansa makomarsa wuta ba, to da babu abun da zai hanata ta kashe kanta.

A hankali take sauke numfashi tana soshe-soshe, babu alamar tana jin bacci a idonta.

Kamar wadda aka tsikara, ta tashi tana laluba hanya, tana tafiya a hankali, hannunta ɗauke da jariri. Hayaniya ta fara jiyowa sama-sama ana maganganu.

Dan haka ta din ga nufar in da sautin yake fitowa, tana nufar sautin tana hango hasken wuta yana ci, da alama dai mutane ne a wajen. A haka har ta cin musu, ta laɓe tana leƙawa, kusan zata iya cewa wata ƙaramar masan’anta ce ta sarrafa makamai iri iri, manya da ƙanana dan wasu ma ba ta san su ba, wasu suna shaye-shaye wasu suna ta shirya makamai, yayin da wasu ke ƙidaya kuɗi.

“Kai har labari ya cika gari artabun da aka yi a dajin nan, mutuwar su sha tara duk ta cika jaridu, kuma haryanzu babu wata ƙungiya da ta ɗau alhakin kai wa su sha tara hari” cewar wani da yake ta murza sigari.

“Kuma ba jami’an tsaro bane ba, a cikin mu ne dai, kuma an kwashe mutanen suka yi garkuwa da su ba” wani ya bashi amsa.

“Haka na ji, daga sama an bada umarnin abi sahunsu, akwai wani jariri da wata mata ta haifa, ana son a tabattar da baya raye, gobe akwai operation, dole a gano suwaye suka kai harin”.

“Haka ne, amma yanzu a gama ware kayan nan, su je su rarraba, da safe a bar gari da su, kai yellow, ku zo ku ɗinke kuɗin nan a cikin buhunhuna a kai su a daren nan, mutanen cikin bukkar nan kuwa duk wanda ba a kawo kuɗin fansar sa ba, ku ƙaddamar masa kawai”.

Hawaye ne suka ziraro a fuskar rumaisa, wato nan ma wata tawagar ce ta daban, atishawa jaririn hannunta yayi, hakan ya janyo hankalinsu in da take.

“Kai anya ba wani naman jejin ne a wurin ba, ku duba mana”.

Rumaisa kuwa tuni ta bar wurin, tana addu’a, amma yadda suka dalle wurin da fitila a ya tsorata ta, dan tuni ta saka ran an gansu, sai dai ta samu cikin ganyayyaki ta zauna tana mayar da numfashi.

“Ni yanzu ya zan yi, ya Allah ko ban kuɓuta ba ka kuɓutar mini da jairirin nan na karɓi amanar sa, Allah kar ka sa rayuwarsa ta salwanta” ta yi addu’ar a hankali.

Da ta ɗan ji dama-dama sai ta tashi ta cigaba da tafiya a hankali, tana shashafawa tana duba hanya, saboda babu haske kuma tana haɗawa da addu’a.

Jin gajiya tayi mata yawa, ga zazzaɓi ya kamata sosai da sosai, ya sanya ta nemi wuri ta zauna, ta haƙura da cigaba da tafiyar, ta tattaɓa ƙirjin yaron zuwa hancinsa, ta ji yana numfashi, amma a galabaice, ga jikinsa zafi sosai.

A haka ta takure da shi a jikinta. Ba ta sake sanin meyafaru ba, sai farkawa ta yi ta ga rana ta ɗaga sosai a kanta, ta duba jikinta duk fatarta tayi wani irin baƙi da kore-kore, ga ƙafarta tayi tsami, saboda ciwukan da ta ji, da hanzari take sake lalube jaririn nan, amma babu abun da ya same shi, sai galabaita. Ta sake kwantar da shi a gefenta, ta lulluɓe shi, tayi taimama ta yi sallar asuba da ta tsere mata.

Har ta nemi wuri ta zauna, saboda gajiya da rashin ƙwarin jiki, amma zuciyarta ta tunatar da ita idan ta cigaba da zama, yaron nan yana iya rasa ransa, dan haka ta tashi da ƙyar, tana tattara yawun bakinta ta haɗiye, saboda azabar ƙishirwa amma bakin nata a bushe yake, ta cigaba da bin hanya tare da fatan Allah ya fitar da su.

***

Tun da garin Allah ya waye mama a rikice take, kaiwa kawai take tana komowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa abun da yake yi mata daɗi.

“Mama, dan Allah ki nutsu ki kwantar da hankalinki, kin san fa jininki ya hau”.

Ta girgiza kai ta ce “Ƙyaleni Abdallah, zuciyata ce take ta bugawa, ko dai an kashe rumaisa, ko kuma tana cikin mawuyacin hali, na kasa samun nutsuwar zuciya”.

“A’a mama, kar ki yi wannan fatan, ko sakawa kanki wannan tunanin, sharrin zuciya me kawai, amma in sha Allah tana nan a cikin ƙoshin lafiya” Huzaifa ya yi maganar cikin damuwa.

“Ba zaku gane me nake ji ba, ku ƙyaleni kawai”.

Aliyu kuwa tafe yake a hanya, ya je shago ya sayo abu, sama-sama ya ji ana kiransa, sai ya ji kamar muryar rumaisa, nan da nan ya tsaya, ya waiwaya sai ya ga Habiba ce, tafe da kayan miya a hannunta, kan ta cim masa ta faɗi saboda sauri, ya ƙaraso wurinta da sauri yana “Faɗin sannu, kk bi a hankali kar ki ji ciwo” ba ta damu ba ta miƙe tsaye ta ce “Yaya Aliyu gidanku dama zan je, mafarki na yi rumaisa ta dawo, shi ne na ce Allah ya sa gaske ne, na taho in ganta”.

Shiru Aliyu yayi yana kallonta, yama rasa mai ze ce mata, a ransa ya ce ‘Haka mama ta yi irin wannan mafarkin, Allah ya sanya ya zama gaskiya’

A zahiri kuwa ya ce “Ki na ji na ko Habiba?”

Idonta ne ya tara hawaye ta ce “Dan Allah kar ka ce mini ba ta dawo ba”.

“Ki yi haƙuri kin ji, amma rumaisa ba ta dawo ba, muna ta addu’a dai”.

Kawai ta durƙusa a wurin, ta haɗa kai da gwiwa ta saka kuka.

A ɗan rikice ya ce “Tashi kar mutane su ce wani abun na yi miki”.

Ya riƙe hannunta ya ɗagata, sai kuka take yi.

Sai yanzu ya ƙara tabattar da soyayya da shaƙuwa da ke tsakanin rumaisa da Habiba, bayan duk saɓanin da suka din ga samu, amma taƙi nutsuwa saboda rashin rumaisa.

Ya kai mintuna ashirin yana rarrashinta, ba tare da ya ƙosa ba, saboda ƙaunar da ta nunawa rumaisa, ya sa yake jin kamar rumaisan ce take kuka.

***

Takawa kuwa ya shirya cikin wani farin yadi, yana ƙoƙarin saka hula, message ya shiga wayarsa.

*Adam ka ɗan yi mini uzuri, abu ya kamani zan je katsina, sai in Allah ya kaimu gobe zan shigo kano*

Wani takaici ne ya kama takawa, a ganinsa bashir ya gama raina masa hankali, cikin hasala ya kira wayar Bashir amma ya ji ta a kashe, ko uwar me zai je yi a Katsina oho.

Wata irin ƙwafa yayi, ya kwashi mukullin motarsa da wayoyinsa ya fita, yana jin zafin abun da Bashir yayi masa.

***

Rumaisa kuwa ita kanta ta san ta galabaita, dan ta fara fidda rai da rayuwa. Tsakankanin wasu ciyayi ta kutsa, kawai ta ganta a wani fili, ta tsaya cak tana kallon wurin, idonta ya sauka a kan wani mutum a tsaye ya gama fitsari gefe ga bindigarsa.

Yana waiwayowa suka yi ido huɗu da rumaisa “Ke wacece, me ki ke yi a nan?” Ja da baya ta fara yi, ya ɗauki bindigarsa ya nufeta. Ai ba ta san lokacin da wani kuzari ya zo mata ba, ta juya da gudu ta bar wurin, aikuwa ya bita, ɗan uwansa da yake cikin ciyayi, shi ma ya fito ya rufa musu baya.

Sosai take gudu tsakanin rayuwa da mutuwa, ta yi wa jariririn nan kyakykyawan riƙo, tana jin yadda numfashinta ke barazanar rabuwa da huhunta, ƙarfinta ya fara ƙarewa, amma ɗan ragowar hope ɗin da take da shi na samun damar yin rayuwa ko jaririn nan ya rayu, ya sanya ta cigaba da bawa kanta ƙwarin gwiwa, ba ta iya gane meye a gabanta, saboda azabar wahala dishi-dishi take gani, babu zato babu tsammani ta yi karo da wani nannauyan abu, mai ƙarfin gaske, ƙatuwar bishiyar kuka ce, da rumaisa ba ta ankara da ita ba, suka yi karo, a take ta silale ƙasa ƙeyarta ta bugu, jini ya fara zuba, jaririn ya faɗi a gefe ɗaya.

A harabar gida takawa yana shirin fita, suka kiciɓis da Jabir, jabir ya dube shi ya ce “Ina zaka ne haka? Na ga yau Saturday babu aiki?”.

Adam yayi ajiyar zuciya ya ce “Bashir ne yake yi mini yawo da hankali, sonake mu haɗu ayi wadda za ayi, amma sai raina mini hankali yake, na ce zan bishi Abuja ya ce na jira yazo kan da kansa, kawai sai kuma ganin message ɗin sa na gani, wai za shi katsina, uban me zai je yi a katsina?”

“To amma yanzu ina zaka je?”.

“Zan je na yi aikina da kaina ne” ya bashi amsa yana kallon agogon hannunsa.

Jabir ya gyara tsayuwarsa ya ce “Kayi aikinka ko ka ɓatawa kan ka lokaci, wata ƙila akwai dalilin da ya sanya yake yi maka yawo da hankali, ka yi haƙuri ka bi komai a hankali, ka bashi yau zuwa gobe in Allah ya kaimu mana”.

Adam ya girgiza masa kai ya ce “No, ba zan iya ba” ya juya zai nufi mota. Jabir ya riƙo shi ya dube shi ya ce “Bashir amintaccen ka ne, bana tunanin zai yi wani abu da zai yi maka yawo da hankali, ko ya cutar da kai, Please ka bashi ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne” da ƙyar jabir ya lallaɓa takawa dan ba laifi Adam akwai baƙin taurin kai”.

***

A hankali take motsawa, ta fara ƙoƙarin juyawa, dan gaba ɗaya a tunaninta bacci take yi, sai dai ta ji wani irin azabar raɗaɗi a ƙeyarta, zuwa kanta da wuyanta, a hankali ta tashi zaune tana waige-waige.

Jaririn yana nan in da ya faɗi, yana ta motsawa a hankali yana zura hannunsa a bakinsa, yana ta numfashi sama-sama. Rumaisa ta zuba masa ido hawaye na zuba daga idonta, haryanzu jikinsa da ƙazantar haihuwa, duk ya fita a hayyacinsa. Wani irin jiri take ji, ta kalli in da ta faɗi ta ga jini, na in da ta fasa ƙeya ta faɗi.

Ta kalli ƙugunta haryanzu tana ɗaure da ɗankwalin Anty Aisha da ta bata, ta ja jikinta zuwa kusa da jaririn, ta riƙe hannunsa tana kuka “Ka yi haƙuri yarona, na kasa baka kulawar da yakamata, kaga nima yarinya ce ban san me kake buƙata a matsayin ka na jariri na, na rasa yadda zan yi mu bar wurin nan, dan Allah kar ka mutu kamar yadda mamanka ta tafi ta barni” tayi maganar kamar tana yi da sa’anta.

A haka cike da tsananin muradin cigaba da rayuwa, ta sake ɗaukarsa ta miƙe cikin ƙarfin hali, ta cigaba da tafiya, sai dai ba ta je ko ina ba ta kasa, ta silale ta zauna a jikin wani dutse ta zubawa sarautar Allah ido.

Kamar a mafarki rumaisa ta ga wasu irin dandazon shanu sun cika wurin, ita dai ba ta san ta in da suka ɓullo ba, ta hangi mai kiwonsu, yana ta ratsawa ta cikinsu. A gefenta ta din ga ganin wata inuwa, ta ɗaga kai sai ta ga wata bafulatana, doguwa do jerin ƙorrai a kanta, ta kalli rumaisa ta ce “‘yar nan dan Allah taimaka mini na sauke ƙorran nan”.

Ruma ta harari matar ta kawar da kai, kamar ba ta ga a halin da take ciki ba, take cewa ta sauke mata wannan uban ƙwaryoyin, can matar ta kuma cewa “Rumaisa da ke fa nake” ruma ta kalli matar cikin mamaki za ta yi magana ta fasa, ta kwantar da yaron, ta miƙe ta kamawa matar suka sauke ƙorran.

Ta koma ta zauna ta na cigaba da kallon jaririnta, matar ta din ga auna nono, ba tare da kuma tankawa rumaisa ba, can rumaisa ta ce “Dan Allah baiwar Allah ki taimaka mini da ruwa da nono na bawa yaron nan, ni ko ba zaki bani ba, shi ki bashi dan Allah”.

Matar ta yi murmushi ta ce “Ai na zata ba zaki kulani ba, na tashi na yi tafiyata”.

Ta miƙawa rumaisa battar ruwa, ta karɓa ta ɗago jaririn za ta bashi, matar ta karɓe shi ta bashi ruwan, sannan ta buɗe wata ƙwarya ta tsiyayo madara fresh ba a daɗe da tasota ba, ta fara bashi, aikuwa duk da bashi da lafiya, haka ya din ga karɓa yana sha, kamar zai cinye da mazubin.

Rumaisa sai murmushi take, ganin ya samu ruwa da abun da zai ci.

Matar ta kalli ruma ta ce “Ba dan halinki ba bari na san miki ruwa ki sha, ruma manyan gari, ruma kaya da yani, gwagwarmaya na gaba ba ta zo ba kuma ba ta wuce ba”.

“Wai ke a ina ki sanni?” Ruma ta tambayi matar.

Matar ta yi murmushi ta ce “Ke waye bai sanki ba, karɓi ruwan ki sha, kar kuma ki manta ki kula da amanar da aka baki, Allah ya taimake ki baki mini rashin kunya ba, Kodayake jikin ta ƙaura yayi la’asar, wallahi da a dajin nan zan barki, amma ki ka taimaka mini, sha ruwan na rage miki hanya ” rumaisa ba ta gama gane me matar ke cewa ba, ta karɓi abun ruwa ta kafa kai, sai dai maƙwarwa biyu ruwan ya ƙare ba ta ƙoshi ba.

Lumshe ido rumaisa ta fara yi, tana jin yadda kanta yake ƙara nauyi, ta karɓi yaronta daga hannun matar ta rungume, sai sunkuyar da kai take, kamar ta yi shaye-shaye saboda ji take kamar zata fita daga hayyacinta.

“Ke!ke! Baiwar Allah me ki ke yi a gefen titi haka?” Rumaisa ji ta yi kamar ta farka daga bacci, ta buɗe idonta sosai, irin zaman da tayi ta rungume yaron a haka take, sai dai a wani wurin ta ganta daban, jeji ne wurin sai dai tana zaune a gefen titi, kwalta ɗoɗar.

“Me ki ke yi a nan, ina zaki je?”

Ta ɗaga kai ta kalleshi amma ta ba ta kula shi ba.

“Ko dai mahaukaciya ce ne? Wannan yaron na waye, ni da na zaci tsohuwa ce ashe yarinya ce, daga ina ki ke ɗan waye a hannunki?”

“Ɗana ne” ta bashi amsa.

Mutumin ya ce “A’a ba dai ɗanki ba, ina hijjabinki, ina ne gidanku?”.

“Kai dan Allah ka ƙyaleni haba” tayi maganar tana neman wurin kwanciya.

“Karki kwanta da jaririn nan a wurin nan, ki gaya mini in da zaki in kai ki”.

Ta kalleshi ta ce “Ka san ɗorayi?”.

“A’a wanne gari ne?”

“Tun da baka sani ba Shikenan, na gode sosai” gani yayi kamar maganar da rumaisa take yi, haukacewa ta yi ba a hayyacinta take ba. Wata danƙareriyar mota ce ta yi parking a wurin da mutumin yake tsaye a kan rumaisa, da tuni mutane suka fara taruwa a wurin.

“Bawan Allah lafiya, meyake faruwa ne?”.

Ya kalli na cikin motar ya ce “Wallahi kaga yanzu nake dawowa, na biyo hanya ns ga wannan yarinyar da jariri, ta ma dai ƙi bari na ga yaron, amma kamar dai mahaukaciya ce”.

“A’a dawanau ce ni ba mahaukaciya ba, kai haka ake tainako ƙishirwa nake ji, amma ko ruwa bai bani ba yake ce mini mahaukaciya”.

Na cikin motar ya ɗauko ruwan roba, ya fito ya bawa rumaisa, ta karɓa ta taƙarƙare ta shanye shi a maƙwarwa uku tayi jifa da jarkar.

Ya kalli rumaisa a tsanake ya ce “Na ji kin ambaci dawanau, ke ‘yar kano ce?”

“Eh, dawanau asibitin mahaukata ne, dan Allah idan ka san kano ka kaini, kar jaririna ya mutu, bashi da lafiya” tayi maganar cikin magiya.

Ya ce “Ok babu damuwa, amma Meyasa na ganki a haka? Ina hijjabinki kalleki futu-futu fa, ga raunuka a jikinki, kalli kanki yana zubar da jini, jikinki babu hijjabi, ƙafarki babu takalmi, dole ayi zaton ko baki da hankali”.

“Kwana kusan sittin fa a dajin nan, saceni aka yi, dan Allah ka tashi ka mayar da ni gida” salallami mutanen wurin suka ɗauka.

A take ya ciro id card ɗin sa, ya nunawa mutanen, shi jami’in tsaro ne, dan haka ya ce zai tafi da rumaisa babban asibiti na cikin garin katsina.

Rumaisa ta ce ita fa ba ta so a kaita ko ina sai gida, ya fuskanci yarinyar kafaffiya ce, dan haka ya ƙyaleta ya ce ta taso sai ya ɗauki wakilcin mutum ɗaya su tafi, su tsaya su yi reporting wa police, su wuce da ita asibiti.

Sai dai duk yadda rumaisa ta so ta tashi ta kasa, saboda ji ta yi ƙaffuwanta kamar ba nata ba, ƙarshe sai ɗaukarta aka yi aka saka a motar suka tafi.

Sai dai fa fafur ta hana kowa jaririn nan, yana ƙanƙame a jikinta, jin abubuwan take kamar a mafarki, Allah ya kuɓutar da su, ta din ga jera hamdala ga Ubangiji.

Sai dai rumaisa na sanya ran an kama hanyar kano ne, ta gansu a asibiti, aka zo da wheel chair, aka ɗorata a kai, nurses zasu karɓi jariri ta ce ba ta san zance ba.

Emergency aka shiga da su, aka yi ta lallaɓa rumaisa ta bayar da jariri ta ƙi, ta ce idan aka matsa mata, ko da rarrafe sai ta gudu daga asibitin.

Kasancewar mutumin da ya tsinceta shi ma ba ɗan gari bane ba, idanya barta babu wanda zai kula da ita, ya sanya a ka bawa rumaisa ɗan taimakon gaggawa, ya ɗau rumaisa tare da rakitar ‘yan sanda biyu, suka taho kano.

Suna tafe a hanya rumaisa tana ta surutai, masu kama da na fita a hayyaci, ta ce wanna ta ce wancan, ita dai gata nan kamar mai barci kuma kamar zautacciya.

Ba su suka iso kano ba sai bayan tara na dare, suka biya suka kuma report ga police na kano, aka yi rubuce-rubuce, sannan suka wuce da rumaisa asibiti.

Suna zuwa aka karɓi su rumaisa, da tuni hankalinta baya jikinta, tun a hanya aka sai abin ci aka bata, amma taƙi ci, ba ta ma da nutsuwar da zata ci Abincin.

Aka zare jaririn hannunta, da a yanzu numfashi ma yake neman ya gagare shi, da yawa sai da wasu suka yi hawaye, ganin halin da jaririn ɗanyen haihuwa yake ciki, cibiyarsa ta yaƙune tayi baƙi, jikinsa duk ƙazanta, aka samo kaya aka saka masa aka wice da shi nursery domin bashi taimakon gaggawa.

Ita kanta rumaisan sai ka kai zuciyarka nesa zaka iya taɓata, saboda yanayin da take ciki na ƙazanta da dauɗa, ba yadda ba su yi ba su kwance ɗan kwalin ƙugunta, amma aka kasa, ƙarshe suka ƙyaleta suka fara kokawar ceto rayuwarta, ita kanta sai da aka saka mata oxygen, saboda sama-sama take numfashi, aka ɗebi jininta aka tafi yi mata gwaje-gwaje.

***

Kusan mintuna uku tana zaune a dining tana ta juya cokali a cikin kofin shayin, amma ta kasa ɗagawa ta sha ko da sau ɗaya, sai zancen zuci take. Jin an dafa ta ne ya sanya ta ɗago a hankali ta kalli ammi, a take ta fara ƙaƙaro murmushin da bai wuce iya leɓenta ba.

Ammi ta ja kujerar kusa da ta iman, ta zauna ta ce “Autana, ko ban tambayeki ba na san abun da ki ke ji, kuma na san ke mai juriya ce, dan haka kar ki saka maganganun da wambai yayi a ranki, ki manta da komai, ki mayar da hankali a kan karatunki, da kin kamma sakandare, zan turaki Mexico wurin laila, ki nutsu ki yi karatunki a wurinta, kuma in sha Allah zan sama miki miji na gari, mai tsoron Allah wanda zai riƙe mini ke tsakani da Allah”

Iman ta rungume Ammi ta ce “Ni dai a’a ammi, zan zauna a tare da ke, bana son mu rabu, zan cigaba jure komai in rayu a kusa da ke”.

Ammi ta yi murmushi ta ce “Duk abun mutum dai dole sai aure ya rabamu, watarana sai mutum ya tafi gidan miji”

Iman ta ce “Sai mu tafi tare, duk wanda zai aureni, sai ya yi wa ammina nata ɗakin”.

Yana sanye da farar jallabiya, ya ɗora rigar saƙi ta sarauta, da farar hula, yana tsaye yana kallonsu, ya ɗan yi gyaran murya, hakan ya sa suka ɗago suna kallonsa.

Ammi ta ce “Ina zuwa haka?”

Ya gyara agogon hannunsa ya ce “Zan je gidan turaki ne in gaishe shi”.

“Amma ina fatan ba wani abun zaka je ka gaya masa ba, ka tayar masa da hankali?”

Takawa ya girgiza kai alamar a’a, iman ta ce “Yaya a dawo lafiya”.

“Allah ya sa, ki kula ki sha magungunan ki a kan lokaci”.

Ta jinjina kai ta ce “In sha Allah” daga haka ya fice daga falon.

“Ammina, bari na je na sha magani na ɗan kwanta”.

Ammi ta ce “To babu laifi, amma dan Allah kar a je a zauna ana tunani, idan na gani ba zan ji daɗi ba”.

Iman ta yi murmushi ta ce “Ba zan yi ba in sha Allah, in dai kina nan Ammi wane tunani zan yi?” Tayi maganar tana miƙewa tsaye tana yi wa Ammi murmushi.

Ko da ta je ɗakinta, ta tarar da baba uwani tana ta yi mata bincike bincike.

“Baba uwani” ta kira sunanta a razane ta waiwayo ta kalli iman ta ce “A’a uwar ɗakina kin shigo?”

Iman ta ce “Eh, amma me ki ke nema ne?”.

“A’a babu abun da nake nema, baki gani ba, gyara ɗakin nake yi, ke da ba lafiya ba, kaye-kaye nake yi miki ai”.

“Amma baba uwani na sha gaya miki, gyaran ɗaki ba aikinki bane ba, ya zaki din ga wahalar da kanki da yawa haka, kiyi wancan aiki kuma ki zo ki yi wannan”.

“To imanuwa idan ban yi miki ba wa zan yi wa, kuma gashi ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba, na san sai ki ce zaki yi da kanki ma”.

Iman ta girgiza kai ta ce “Kar ki damu baba uwani, ki yi tafiyarki kawai, za a gyara ɗakin ma ai babu datti, ina son in ɗan kwanta ne”.

“To Shikenan babu laifi, ki huta lafiya”

Iman ta bi bayanta da kallo, daga bisani kuma ta je ta nemi wuri ta kwanta.

***

Cikin ƙosawa take wayar, cikin yanayi mai kama da faɗa-faɗa “gaskiya Khalifa na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba, ai yakamata ace zuwa yanzu result ya fito”.

“Ke duk result ɗin da ki ka gani bai yi miki ba, wanne ki ke jira? Meyasa kin fiye wutar ciki ne?”

Samha ta ce “Au haka ma zaka ce, ni na kasa gane wannan yawon da hankali, ni fa na fara jin tsoro”.

Dariya Khalifa ya yi ya ce “Haba jaruma, wane irin tsoro kuma? Ai mun yi kaso mafi yawa na aikin, sauran ke zaki yi wa kanki fighting, ki bi komai a hankali, idan ki ka yi gaggawa aiki zai iya kwaɓe miki, dan ni babu ruwana. Nan ba da daɗewa ba, zaki ji labari mai ɗan karen daɗi”.

Ta yi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan, Allah ya sa”. Ta ajiye wayar ta yi shiru tana tunanin maganganunsa.

“Anty Samha, Anty Samha!”

Waiwayowa Samha ta yi ta kalli yarinyar a ɗan hasale ta ce “Lafiya ki ke yi mini wannan kiran haka?”

“Anty Samha kin gan mu, zuwa muka yi baki yi murna ba?”.

“Na ji, jeki wasanki, idan na fito ma gaisa”

Yarinyar ta ɗan ɓata fuska ta ce “Shikenan, naga uncle takawa ya zo, bari na je na gishe shi”.

Da sauri Samha ta ce “Jannah, bana son shirme da gaske ki ke yi ko kuwa?”.

“Wallahi da gaske, ga motarsa can da hadimansa, yana wurin Baba suna gaisawa”

“Shikenan, na ji jeki maza” janna na fita samha ta tashi ta canza kaya, ta hau feshe-feshen turare.

Takawa yana jin daɗin mu’amala da turaki, dattijon akwai nutsuwa da kuma dattaku, ba shi da hayaniya sam balle faɗa.

Sun daɗe suna hira, sai da takawa ya fara shirin tafiya sannan turaki ya ce “Amm..wato akwai maganganu da muka ji suna ta yawo a kanka, a cikin masarautar nan, sai dai bamu yanke maka hukunci ba. Maganganu ne marasa daɗi da maimaita su ma bashi da wata fa’ida, amma duk da haka zamu jadadda, a din ga kula a ƙara kiyaye martabar addini da kuma al’ada, ba zamu so zancen nan ya je kunnen mai martaba ba, mussaman yadda ake ji da kai, yake sonka, muna ta ƙoƙarin daƙile jita-jitar, mun sani shaye-shaye ba halinka bane ba, dan da kana yi, zamu gane, amma a cigaba da kiyayewa tare da riƙe addu’a”.

Adam yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya ɗan risuna ya ce “Za’a kiyaye in Allah ya yarda, Allah ya ƙara maka lafiya, zamu wuce”.

“To madalla, Allah ya tsare ka isar da gaisuwata ga mahaifiyarka, ka ce kwana biyu bamu ga aiken mutan daji ba ma’abota nagge” yayi maganar a nutse cikin sigar barkwanci.

Takawa ya ɗan murmusa, tare da duƙawa daga nan ya tashi ya fita.

A falo ya tarar ana ta shirya abinci, Janna ta ƙaraso gabansa ta risuna ta ce “Barka da wannan lokaci uncle”.

“Barkanki dai janna, kwana biyu bana ganinki, ya makaranta?”

“Lafiya ƙalau”

Ya ce “Masha Allah”. Yana ɗaga kai ya yi tozali da matar da ya tsana a duniya, mahaifiyar su Jamil, wato mama, bai san ya aka yi suka san ya zo ba, dan ta ƙofar baya ya shiga sashen turaki, ya nemi ayi masa iso.

Ta washe baki ta ce “Takawarka lafiya toron giwa, gaba salamun baya salamun, galadima magajin galadima, da haka za a wuce ban san an zo ba? Ai yakamata mu gaisa ko”.

“Ai ban zaci idonki biyu ba, barka da wannan lokaci” yayi maganar yana ɗan risunar da kansa ƙasa.

Kan ta amsa samha ta fito tana murmushi “Takawa, yau kai ne a gidan namu? Zaka tafi babu ko sallama da mun yi faɗa da kai kuwa” wasu irin matsatsun kaya ne a jikinta riga da skirt, ilahirin surar jikinta ko ina a matse.

“Ku yi mini afuwa, dama ina da niyyar shigowa”.

Mama ta ce ‘Amma na ga kamar kana shirin tafiya, da ka yi ɗan waken zagayen, ga abinci nan na saka a kawo maka ai”.

“Ayi mini afuwa sauri nake ne, ana jirana, zan sake yin zuwa na musamman na barku lafiya” bai ma tsaya ba balle ya ji mai za su sake cewa ba ya fice.

***

Ɗan ƙura mata ido yayi, bacci take kamar babu rai a jikinta, yanzu babban fatansa ya san daga in da take a nemo ‘yan uwanta, su zo su san abun yi a wanke mata wannan dattin na jikinta, ko ita ma ta samu ta ji daɗin jikin nata.

A hankali ta buɗe idonta, ta ɗan motsa jikinta da yake ta yi mata azabar ciwo.

Ya ce “Alhamdilillah, kin farka?”

Ta yi masa ƙuri da ido tana kallonsa.

Ya durƙusa a gaban gadon ya ce “Ki bani lambar wayar wani a gidanku, a sanar musu kin dawo”.

A hankali ta buɗe baki ta ce “Haka muka yi da kai?”

Ya ce “Me fa?”.

“Ina ɗana?” Ta tambaye shi.

“Yana sashin jarirai ana kulawa da shi, kin san ya galabaita”.

Rumaisa ta ce “Lallai baka sanni ba, ni fa a kan yaron nan, sai na tayarwa da kowa hankali, a bani ɗana”

Zai yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ciro wayar daga aljihunsa, ya kalli screen ɗin wayar ya ce “Jarababbe, na san na shiga uku da masifarka yau”.

Ya ɗaga wayar ya saka a kunnensa ya ce “Ya?”.

“Abun da ya kamata ka ce mini kenan?”.

Bashir ya ƙara nutsuwa ya ce “Sorry man, na san na yi maka laifi, am sorry for that, wani emmrgency case ne ya faru, na bayar da taimakon da zan iya, yanzu haka ina Asibiti wata yarinya na tsinto a katsina ta kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga”.

“Ina ruwana, ta ina hakan ya shafe ni? Ni abun da ka yi mini ka kyauta kenan? Na rantse da Allah muka haɗu sai ka gane baka da wayo”.

Ruma ta yi ƙuri da ido tana sauraren muryar da ko daga maye ta farfaɗo, ba ta manta mai ita ba.

Bashir ya san iya tijara zai sha ta a wurin takawa, dan haka ya shiryawa karɓar da duk wani hukunci da zai yi masa, ya kwantar da murya ya ce “Tuba nake, ka bari zan zo in sameka, na gaya maka ina Asibiti ne”.

“Kar ka sake ka zo in da nake, idan ka zo haɗuwarmu ba zata yi maka daɗi ba”

‘shi wannan kowa ma yi wa masifa yake yi?’ ta tambayi kanta, can kuma ta ce ‘Ƙila ma ba gaske bane mafarkin da na saba nake yi’.

Maganar Bashir ce ta dawo da ita hayyacinta “Haryanzu ba ki gaya mini ko sunanki ba, mun kawo ki unconscious, ki gaya mini sunanki, ki bani lambar wayar wani a gidanku, na kirasu ga abinci nan na kawo miki, yan sanda suna jirana na je na kai report”.

“Ina jaririna?” Shine abun da ya fito daga bakin rumaisa.

“Na gaya miki yana nursery, an saka mishi oxygen ana ƙoƙarin ceto ransa”.

“Idan wani abu ya same shi ba zan yafe maka ba, kuma wallahi sai na saka yayyena maza sun zane ka” ta yi maganar tana hawaye.

Bashir ya sake nutsuwa, yayi murmushi ya ce “ba zata kai mu ga haka ba,  babu abun da zai same shi sai abun da Allah ya ƙaddara masa, trust me, yanzu bani lambar wayar”.

Ta ɗan rausayar da kai ta ce “Allah ya sa ba mafarki nake yi ba, ni na manta lambar kowa, bari na baka ta Yasir, yayana ne ta sa na tuna.

Ya ce “Ok, gaya mini” yayi maganar yana riƙe wayarsa.

Ta gaya masa lambar cif, yayi saving ya ce “Tashi ki ci abinci, yayata zata zo ta zauna da ke, kan ‘yan gidanku su zo”.

Ta girgiza masa kai ta ce “Ni ba zan ci komai ba, sai na ga mama”.

Bashir ya ce “No, ba za ayi haka ba, ki daure ko kaɗan ne”

“Ni dai ka tashi ka kirawo mini ita kan na farka daga baccin da nake yi” tayi maganar tana kuka har da sheshsheƙa.

Ya ce “To shikenan, bari na je, yayar tawa zata zo, sunanta Asiya, za ta zauna da ke”

Ba ta ce masa komai ba ta cigaba da share hawayenta.

Mintuna talatin da fitarsa, sai ga yayarsa Asiya ta iso, ta tarar da rumaisa tana barcci, dan haka ta nemi wuri ta zauna tana jin tausayin yarinyar, mussaman yanayin da ta ganta a ciki.

***

Kasancewar yasir ya iya gyaran kayan Electronics sosai, ya sanya ya buɗe ɗan case da yake gyare-gyaren sa, ko yanzu da yake ta aiki yana yi ne ba dan yana jin daɗin aikin ba, sai don rage kewa da kuma damuwa.

Wayarsa ce ta fara vibrating, yana ji yayi banza sia da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga ya yi sallama.

“Wa’alaikum salam warahmatullah, ina magana da Yasir ne?”

Yasir ya ce “Eh ni ne”.

“Yauwwa, sunana Bashir kibiya, ni jami’in tsaro ne dan Allah idan ba zaka damu ba, ina son haɗuwa da kai a babbar headquarter ‘yan sanda ta bampai”

Waro ido Yasir yayi ya ce “Yallaɓai me na yi? Wallahi ni ban yi wani laifi ba”

“Na sani malam Yasir, ni yakamata na zo da kaina ma, amma wani abu ne ya riƙeni ka zo da gaggawa ka sameni”

Jiki a sanyaye Yasir ya kashe wayar,ya kwashe kayansa, yana tunanin wa zai jewa da wannan maganar, babu yadda za ayi a gayyaci mutum bamfai ace lafiya lau.

Ya tsaya a ƙofar gida ya kasa shiga gida, sai rarraba ido yake yi.

Abdallah ne ya fito daga cikin gidan, Yasir ya ce “Alhamdilillah, zo ka ji wani abu”.

Abdallah ya ce “Ya aka yi?”

Kamar Yasir zai fashe da kuka ya ce “Wani ne ya kirani, wai na je bamfai yana jirana kuma ni wallahi tsoro nake ji”

Abdallah ya ƙare masa kallo sannan ya ce “Kai, ka gaya mini idan wani abun ka aikata, Kodayake da ruma tana nan sai in ce ko ita ake nema, amma kuma ks tabattar ba ‘yan iskan gari bane ba, ko a cikin abokanka wani ke son raina maka hankali ba?”

Yasir ya ce “Bana tunanin hakan, mutumin muryarsa ba ta yi kama da haka ba”.

Abdallah ya ce “Bani lambar” Yasir ya bashi lambar ya saka a wayarss ya kira, yana kira Bashir ya ɗaga, suka gaisa Bashir ya ce “Bawan Allah, yayan yasir ne ni, ina son jin dalilin da ya sanya ake nemansa a bamfai?”

Bashir ya ce “Eh, abu ne mai muhimmanci, da laifi yayi gida zamu zo mu kama shi ai, ku hanzarta dan Allah”

Abdallah ya ce “To shikenan babu damuwa “.

Ya katse wayar ya kalli Yasir ya ce “Zancenka gaskiya ne, ka san wani abu? Kar mu gaya kowa, zo mu je mu ji koma menene, sa ji daga baya” Abdallah ya ƙwararawa Yasir gwiwa, suka kama hanya suka tafi.

***

Ammi ta fito babban falo, ta dubi ɗaya daga cikin barorinta ta ce “Maza je ki korawo mini iman” ta amsa mata cikin girmamawa, ta tafi.

Bai fi mintuna bakwai ba, sai ga Iman “Ammi gani, Allah ya sa ba laifi na yi ba?”.

“Ai laifin ki ka yi, na gaji da zaman ɗakin nan da ki ke yi, jikinki ai da sauƙi yanzu, ki shirya zamu je gidan Jamil, an ce matarsa tayi ɓari” ɗan ɓata fuska iman tayi kamar zata yi kuka.

“Menene ko ba zaki ba?” Ammi tayi maganar tana tsare iman da ido.

“A’a zan je, bana son na je na tarar da Anty samha ne” tayi maganar kamar ta rushe da ihu.

Ammi ta kalleta a tsanake ta ce “Meye tsakaninki da Samhan da ba kya son haɗuwa da ita?” Sai kuma ta sha jinin jikinta jin abun da ammin ta ce.

“Bakomai Ammi, bana son fita ne”

“Aikuwa sai kin fita, maza muje in shiryaki, kar ma ki ɓata mini lokaci” Nusaiba kuwa sai dariya take yi, ganin ammi ta saka iman a gaba wai ita zata shiryata. Hakan kuwa aka yi, Ammi na tsaye iman ta shirya cikin baƙar abaya, da ta karɓi kyakywar farar fatarta, sai ɗaukar ido take yi, ta ɗora mayafin a kan ta, sai dai kwantaccen gashinta sai da ya bayyana.

Tare suka fito da Ammi, tana janyo hannunta, ita kuma kamar ta fashe da kuka, sai tura baki take yi. Haka suka jera da Nusaiba da iman da ammi.

Nusaiba ta ce “Allah ammi kin shagwaɓa yarinyar nan da yawa, ji wata taɓara da take yi”.

Ammi ta ce “Bar ni da ita, sai na zaneta tukuna” haka suka fito harabar gidan a tare.

Tun daga nesa yake kallonsu, ya tattara nutsuwartsa a kan Iman, tamkar ba bugun Nigeria ba haka take.

“Ruky wannan ma ‘yar gidanku ce?”

Ruƙayya ta waiwaya ta hango su Ammi, a fusace ta dube shi ta ce “To ba ‘yar gidan nan ba ce, tsintota aka yi aka riƙeta a gidan nan, babu wanda ya san danginta ma, wataƙila ma ba ta da uba”

Maimakon ya fusata sai ya ce “Wow, amma dai a ƙasashen Larabawa kuka tsinto ta ko? Ko irin Afrika ta gabas ɗin nan”.

“A’a africa ta sama, aka tsinto ta aikin banza ” ta tashi fuu ta shiga ciki.

Tashi yayi yana kiran sunanta, amma bata ko sake waiwayo wa ba ta tafi.

“Wallahi na gaji, ni da gidan ubana saboda bala’i ban fiye zama ba, ko na kawo baƙina ba, da gayya idan bar zan yi baƙo mu zauna a harabar gidan nan, sai wannan banzar yarinyar ta fito, ita kuma ammi ta wani sako su a gaba riii kamar shanu, duk yadda na ƙallafa rai a kan gayen nan, yana ganinta ya hau wani surutu, ji nake kamar na zuba mata wuta a fuska uban kowa ya huta”.

Mummy da take jin ta tayi shiru ba ta yi mata magana ba, ta ƙaraci bala’inta ta gama, amma Mummy ta fara hasala, duk yadda suka kai ga ɓata iman, ba ya wani tasiri sam. Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce “daga yau idan kin yi baƙi, ku din ga shigowa falon waje, kuna zama, ku bsrni da ita, zamanta a gidan nan ya kusa expire ” haka ruƙayya ta zauna tana cigaba da huci.

***

Yasir da Abdallah basu saki jikinsu ba, sai bayan ganin kyakywar tarbar da Bashir yayi musu, ya kai su wani katafaren office, har da sanyawa a kawo musu ruwa da lemo.

Abdallah ya ce “Ranka ya daɗe mai ɗan uwana yayi ake nemansa ne? Hankalinmu ya kasa kwanciya, kar wani abu ne ya faru, mahaifiyar mu babu lafiya, ba wanda muka sanarwa ma a gida”

Bashir ya yi murmushi ya ce “Ɗan sanda ai abokin kowa ne, ba abun tashin hankali bane, ni na so mu zo har gida amma wani aiki nake yi wa uban gidana. Shekaranjiya aiki ya kaini jihar katsina, na kwana ɗaya a can, a kwana na biyu na kamo hanyar baro garin, na tsinci wata yarinya da jariri a gefen hanya, wani mutum yana tambayarta, so nayi amfani da id card ɗina, muka kaita asibiti da yaron, amma yarinyar ta kasa bamu haɗin kai saboda jaririn nan, so a jiyan muka taho kano, aka kwantar da ita a asibiti ita da yaron, ta ce mini dai ɗanta ne, na yi reporting wa abokan aikina, shine ta bani lambar wayar Yasir ta ce mini yayanta ne, suananta Rumaisa.

Miƙewa tsaye suka yi tsaye gaba ɗayansu, suna kallon Bashir, amma suka kasa magana.

Bashir ya miƙe ya ce lafiya kuwa?”

Tuni hawaye ya wanke fuskar Yasir ya ce “Yallaɓai ina ruma take, ƙanwarmu ce aka saceta a katsina, tafi wata biyu kusan watanta uku a hannun ‘yan bindiga, dan Allah tana ina”

Bashir ya dafa kafaɗar Yasir ya zaunar da shi ya ce “Calm down, tana nan ana kula da lafiyar ta, ku godewa Allah, duk da ba ta gaya mini meyafaru ba, amma dai gaskiya a galabaice take, ikon Allah ne ya fitar da ita, tana nan asibitin koyarwa na kano, zaku bamu bayanin yadda aka yi ta ɓata da komai da komai “. Daga Yasir har Abdalla aka rasa mai magana, dan Abdallah durƙusawa yayi yana kuka dan tuni suka fara fitar da rai.

Nan Bashir da abokan aikinsa, suka din ga rarrashin su, suka gaya musu iya abun da suka sani, daga tafiyar su ita da Aliyu zuwa yanzu, aka kuma duk wasu cike-cike da za ayi, aka ce zasu tafi Asibitin wurin rumaisa.

Abdallah ya gige hawaye ya ce “Yallaɓai zamu iya kiran gida mu sanar musu, mahaifiyarmu na nan ba yadda take saboda azabar tunani da damuwa”

“Eh ku kirata ku sanar musu”.

Yasir ya ce “Mai sunan baba zaka gayawa, shi zai san yadda zai ya sanar mata, kar ta gigice jininta ya kuma hawa”.

Haka kuwa aka yi, sai dai Umar bai ɗaga wayar ba, sai Aliyu aka samu, gaba ɗaya ya rikice da jin maganar, amma yayi iya ƙoƙarinsa ya saita kansa, mama ba ta gane ba, ya sanarwa Usman da Mai sunan baba.

Mai sunan  ya ce su yi gaba, zai taho da mama, ba tare da ya bari ta gane wani abu ba, su fara zuwa su duba idan da gaske ruman ce.

Tun da rumaisa ta ɗan farka, Yayar bashir ke fama da ita ta ci abinci, amma ta gardame ta ƙi ci, sai surutai kawai take marasa kan gado, tana kukan ita fa a kawo mata jaririnta. Sai da nurses suka ɗauko shi, an saka masa kaya, sai dai ya ɗan yi dama dama, an sanya masa robar hanci, ta nan ake ɗura masa madara.

Rumaisa ta zubawa jaririn ido a hannun Asiya, tana bashi madara ta sirinji, sai ta ga ta koma mata suffar Aisha.

“Anty Aisha, kin ga amanarki? Ashe nan suka kawo ki suka barmu a can?”.

Asiya ta ce “Asiya dai, sunana kenana ba Aisha ba” sai da ta yi magana, sannan rumaisa ta ga ta koma Asiyan.

Ita kanta ruman a yanzu bata iya banbance wacece ita, da kuma rayuwar da take yi.

Ƙofar ɗakin aka buɗe, rumaisa ta ɗaga kai, bashir ne a farko da wasu ‘yan sanda, Yasir ya ture su, ya rugo da gudu ya zo ya rungume rumaisa yana kuka.

Rumaisa ta kwantar da kanta sosai a jikinsa ta ce “Yasir, idan ka zo mafarkina ka daina tafiya, ka barni tsoro nake ji”. Bai san me ma take faɗa ba, Abdallah ma ya garzayo ya rungumesu gaba ɗaya, sai dai ruma ba ta da ƙwarin da zata iya rungumesu ita ma. Dan ita gaba ɗaya ta riga ta yadda da cewa mafarki take yi.

Abdallah ya kalleta, ‘yar da mama ke ta tattalawa tana kula da tsaftar ta da jikinta, sai gata duƙun-duƙun kamar ta warke daga ciwon hauka, koma dai wadda take cikin haukan tuburan

Su Usman ne suma suka banko ɗakin, suna addu’ar Allah ya sanya rumaisan ce.

Suna ganinta suma suke kewayeta suna kuka, kallo ɗaya zaka yi mata ka san ta sha azaba ta wahala.

“Dan Allah duk kar ku tafi ku barni, mu yi ta zama a cikin mafarkina” tayi maganar tana fashewa da kuka. Babu wanda ya rarrashe su, kai da ganin yadda zaratan samarin ke kuka, ka san sun shiga ɗimuwa da ɓatan ‘yar tahalikar.

Mai sunan Baba da ƙyar ya lallaɓo mama a kan zai kai ta ganin likita wani asibitin daban, ta ce ba zata ba, wani abun suke ɓoye mata kawai, sai da suka kai ruwa rana sannan ta yadda.

Ko da suka isa ɗakin da ruma take, kasancewar Usman ya tura masa message na sun ganta rumaisa ce, ya sanar masa ɗakin da take.

Ko da mama tayi ido huɗu da rumaisa ƙamewa tayi, sai ruwan hawaye.

Ruma ta hau miƙa mata hannu tana hawayen ita ma ta ce “Mama dan Allah ki zo in taɓaki kar na tashi daga baccin na ga kin tafi” Mama ta ƙarasa ta ƙanƙame rumaisa kamar ta mayar da ita ciki.

“Dan Allah mama kar ku tafi, kullum sai kun zo a mafarki na ganku, amma sai ku tafi ku barni a wannan dajin mukaɗai, dan Allah mama ki zauna da ni, Allah ya sa kar na tashi daga baccin nan, mamana tsoro nake ji kar ki bari na farka”

“Ruma nima ji nake kamar mafarkin ne, ina ta gaya musu kin dawo kina waje amma basu yadda ba, Allah Alhamdilillah” tayi maganar tana sake rungume rumaisa.

Wata nurse ta shigo da tray na magunguna ta ce “Gaskiya bayin Allah kun yi yawa a ɗakin nan ku ragu zan yi mata allurai, bacci muke son tayi ƙaaƙwalwarta ta huta” ta yi maganar tana ƙarasawa gaban gadon rumaisa.

Bashir ya ce “ki bi a hankali, watanni uku ba sa tare an saceta, ki bari ta ga ahalinta”

Nurse na ƙoƙarin ɗaga hannun ruma daga jikin mama ta yi mata allura, a zuciye rumaisa ta yi jifa da trayn “So ki ke dole na tashi daga baccin? Bana so ki ƙyaleni” ruma tayi maganar kamar mai shirin tayar da aljanu.

Sai a yanzu mai sunan baba ya ƙarasa, ya zauna a gefen gadon, ya ɗago rumaisa daga jikin mama, ya rungumeta a jikinsa, ya ɗago hannunta ya riƙe ya ce “Yi mata abun da ya kamata”

Ta yi lamo a jikinsa, sai kuma ta ce “Mai sunan baba”.

Ya ce “Na’am”

“Yau a mafarkin nawa ba zaka sakani kama kunne ba? Kullum idan ka zo sai ka sakani kamun kunne, amma ko zaka sakani kamun kunnen, ka zauna a mafarkina, tsoro nake ji bana son duhun nan” tayi maganar tana shirin fara fizge-fizge amma ya danneta a jikinsa ana gama allurar ta cigaba da bacci.

Bayan baccin ya ɗan ɗauketa, mama ta share hawayenta ta ce “Aliyu, ku je gida ku zo da ruwan zafi, ayi mata wanka, kan mutane su ji su fara zuwa”

Bashir ya ce “No, kar a taɓata tukuna sai zuwa dare, muna jiran result ɗin likita tukuna, sai ayi mata wankan, sannan akwai jariri da na tsince su tare, ta ce mini ɗanta ne, duk da ni ban ga alamar hakan a tare da ita ba”.

Mama ta ce “Jariri kuma?”

Asiya dake gefe ta miƙa musu jaririn ta ce “Gashi, bayan tafiyarka ta sanya rigima sai da aka ɗauko shi”.

Mama ta karɓi jaririn tana ƙare masa kallo, Bashir ya ce “Ikon Allah, ban yi zaton yaron nan zai rayu ba, amma cikin ikon Allah kun gan shi, har da sauran ƙazantar haihuwa a jikinsa na gansu”.

Usman ya ce “to a ina ta samu jariri?”

Aliyu ya ce “Oho, tubarkallah gashi ƙato mai kyau.

Ruma tana baccin nan, aka juyata ana wanke mata raunin da yake ƙeyarta, gashin kanta har da kwarkwata, ban da tarin datti da dauɗa.

Mama ta din ga yi wa Bashir godiya, rumaisa ba ta daɗe ba allurar ta saketa, sai dai ta kasa yadda ba mafarki take yi ba.

Kamar kullum Bashir ya din ga lallaɓata ta gaya masa, ina ta samu jariri, amma ta ce “Na gaya maka ɗana ne”.

Mama ta ce “Rumaisa, ki gaya mana ko hankalinmu zai kwanta, ina uwar ɗan take” rumaisa ta yi shiru tana tunani.

“Ba kya ji ne?” Mai sunan baba yayi maganar yana kallonta.

“Ɗan wata mata ne” ta basu amsa.

Nan ta gaya musu iya abun da ta sani, ta ɓoye musu wani abun.

Bashir na gama jin bayanin ruma, ya ce asibiti za a canza mata.

Suka shiga tambayarsa dalili, amma ya ce likita ne ya bada shawarar hakan.

Daf da magariba Bashir ya isa gidansu takawa, bayan yayi ta kiran lambarsa amma yaƙi ɗagawa.

A harabar gidan suka yi kiciɓis, Bashir ya tattara nutsuwartsa ya ce “Allah ya baka yawan rai, ina ta kiran lambarka ka ƙi ɗagawa”.

Ƙoƙarin tureshi Adam yake ya wuce, amma Bashir yaƙi matsawa ya ce “Tuba nake, amma ka tsaya ka saurareni, wallahi babban uzuri ne ya sameni, na gaya maka yarinya na tsinta, ta kuɓuto daga hannun ‘yan bindiga”

A fusace Adam ya ce “Ka je ka yi abun da kake so mana, ai ban yi maka magana ba, ambulance sarkin taimako ka je ka yi ta yi mana, tun da ni tawa buƙatar ba buƙata bace”.

Bashir ya ce “Dan Allah Adam ka saurareni ka ji”

“Ba zan ji ba, bana son ji” yayi maganar a fusace zai wuce.

“What if yarinyar tana da alaƙa da aikin da ka bani? Ka rage zafin zuciya ka dinga cin ribar rayuwa, ka zo mu je zuwanka ka ganta yana da muhimmanci, za a iya samun muhimman bayanai a tare da ita, yanzu haka Ammi na asibitin”. Cak Adam ya tsaya yana kallon Bashir.

“Ka zo mu je, ina tabattar maka da cewa, yarinyar nan za ta iya zama ita ce makarin abun da muke nema, ka yi haƙuri ka yadda mu je”.

“Amma meya kawo ammi cikin zancen nan”.

“Dole ce, dole ce ta shigo Ammi cikin lamarin nan, kuma har zuwa yaushe zamu cigaba da wannan ɓoye-ɓoyen? Ka zo mu je” Adam bai kuma cewa komai ba, ya bi Bashir motarsa.

Wani katafaren asibitin kuɗi Bashir ya sanya aka mayar da rumaisa, sai dai ba ta iya taka ƙafafuwanta, saboda raunukan da suke jiki, mama tana yi mata wanka tana kuka, haƙoranta sun yi yellow, gashi nan a cukurkuɗe, fatar rumaisa duk cizon ƙwari, haka zalika cikin kayanta duk ƙwari, Mama ta sanya almakashi ta ragewa rumaisa gashinta, saboda tana da cukurkuɗaɗɗen gashi mai tsayi.

Mama ta tsorata da ta ga uban gwal ɗin da yake cikin ɗan kwalin da yake ƙugun rumaisa, ko da mama ta matsa mata da tambaya, sai ta hau kuka.

Abinci ma da ƙyar ta ci kaɗan, ta kwanta ta cigaba da aikin bacci.

A hankali take motsawa, tana buɗe idonta da kaɗan-kaɗan, tana tsoron kar ta buɗe idonta ta ganta a duhun dajin nan, ko wurin su sule.

Ganinta ta yi a wani wuri na daban, dan har aka canza mata Asibiti mama tayi mata wanka, ba a hayyacinta take ba, ko ina farin tiles da farin ƙwai, ga sanyin ac da yake ratsata, a hankali ta fara shaƙar wani irin daddaɗan ƙamshin turare, ta din ga kallon mutanen ɗakin ɗaya bayan ɗaya, wata babbar mace ta gani a zaune tayi mata kama da wanda ta sani.

A hankali ta ga su Aliyu da Usman a wurin, ga wasu dogarai masu kaya kalar na bayi da mama ta ce mata.

Gabanta ne ya faɗi da ta yi tozali da Adam a kan gwiwoyinsa, rungume da jariri hawaye na zuba daga idonsa.

Cikin ihu ta ce “Wayyo Allah mama, kina ganinsa ko ni kaɗai nake ganinsa?”

Mama ta ce “Waye?”

“Wannan mugun mutumin” tayi maganar tana nuna Adam.

A rikice mama ta ce “Me yayi miki?”

Bashir ya ce “Rumaisa, ki kwantar da hankalinki, ba mugu bane ba, kwatancen da matar nan ta baki, shi na yi tracking, mutanen da ta gaya miki gidan sirikanta ne kuma iyayenta, Adam abokina kuma shi ne baban jaririnki, shi ne mijinta”.

Kamar sokuwa haka ruma ta bi bashir da kallo, daga bisani ta ja wani uban tsaki ta ce “Dan Allah ka daina raina mini hankali, wai komai nawa sai wannan mutumin ya shigo ciki, to wallahi ba shi bane ba, ɗana ne ba shi ne babansa ba”.  Ko cikin gushewar hankali takawa ba zai manta wannan muryar me shegen karaɗi da tsiwar tsiya ba. Shi kansa mamaki yake yadda aka yi rumaisa take shigowa cikin rayuwarsa a bazata. Ya ɗaga jajayen idanunsa ya na ƙare mata kallo.

Usman ya ce “Rumaisa, kin ga ki nutsu kin ji, shi a ina ki ka san shi?”

Ta kalli Bashir, sannan ta ɗan kalli takawa, ta girgiza kai ta ce “Ni ban san shi ba, ku karɓo ɗana ku bani, ba shine babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba”.

Bashir shima ya ƙarasa gaban rumaisa ya ce “Rumaisa, ba cewa ki ka yi tace miki ita ‘yar turakin kano ba ce? Ta ce miki giwar Galadima ce sirikarta ba, to ai ga giwar Galadima nan, Adam kuma ɗanta ne” ruma ta yi shiru ta tafi tunanin abun da ya faru ita da Aisha.

Lokacin da ta kammala bawa Aisha labarin abun da ya faru a tsakaninta da Adam, ta din ga yi mata dariya ta ce “Kamar na san mutumin nan da kike bani labari”.

Rumaisa ta ce “Taɓ, aikuwa idan ɗan uwanku ne sai dai ki yi haƙuri dan ba shi da mutunci, bama ki san shi ba anty aisha”.

Aisha ta kalli ruma ta ce “Ɗan gidan marigayi Galadiman Kano ki ka ce ko?”

“Oho masa, amma dai kamsr haka aka ce”

“Amma da ƙarfin hali kike ruma, dan ƙarfin hali babban mutum ki yi masa wannan rashin kunyar?”

Ruma ta taɓe baki ta ce “Ai ni Allah kaɗai nake tsoro”

Aisha ta yi murmushi ta ce “To ki yafe masa mana my baby rumaisa” ruma ta daki ƙasa ta ce “Ai ko shine zai zo gabana ya ce na yafe masa ba zan yafe masa ba, kin ga rashin muntucin da yayi mini, har da ce mini ‘yar talakawa, yanzu da ciki ya fito mini da ya taɓa mini nono fa, ina zan saka kaina?”

Tayi dariya ta ce “Ai bai fito ɗin ba, kuma gaskiya kar ki yi masa sharri dan kin tsane shi, you are still a baby, ina wani nono a nan banda sharrinki ruma? Ko kwatan nawa ba su kai ba fa, ko ganinsu ba ayi”

Rumaisa ta ce “Wallahi sun fara fitowa, mama ta ce duk wanda ya taɓa ciki zai fito mini, kuma korata za su yi daga gidan su, yanzu da ya sa an koreni fa, ni fa bana son ma su fito, idan ba haka ba mama zata hanani yawo ba riga, yanzu ma hanani take yi”

Aisha ta yi dariya ta ce. “gaskiya ki daina zaginsa tun da dai ba a korekin ba, kin yi masa sharri, ina wani abun taɓawa a nan” tayi maganar tana sake tuntsirewa ruma da dariya.

Ruma ta ce “Wallahi ya taɓa, kuma idan Allah ya sa na bar nan idona idonsa zai gane bashi da wayo, ana i gobe zan zo katsina, yayi mini wanka da kwata a tsakiyar layi, wai har da cewa na yi masa sharri da nace ya taɓani, wai zuwa yayi ya duba ya ga ko akwai wani abu a ƙirjina ki ji ɗan iska fa”

Aisha ta dafe ƙirji ta ce “Wayyo zuciyata, haba baby rumaisa sunan mijina adam, kar ki sa kishina ya tashi. Amma ni nawa Adam ɗin shima yana da zafin zuciya, baya son raini ga miskilanci, amma idan ki ka fahimce shi, mutumin kirki ne, mai son kulawaga iya soyayya, sai dai….” ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce “Ruma zaki auri Adam?”

Ruma ta waro ido ta ce “wane Adam ɗin? Ni da ban yi tsawo na girma ba za ayi mini aure?”.

“Adam da kuke faɗa, ki yafe masa ko dan albarkacin yana da sunan mijina”

Ruma ta turɓuna fuska ta ce “Ai wallahi ko yayanki ne ba zan yafe masa ba, da in auri Wannan gara na mutu ba aure, kuma ni miji kyakkyawa nake so, kuma mai kuɗi”

“In dai kuɗi ne akwai su ruma, kuma ai kyakykyawa ne”

Rumaisa ta dubeta ta ce “Ba fa mijinki ba, wannan da muke faɗa nake gaya miki, mai suffar mugwaye da wata banzar motarsa in sha Allah sai an sace motar ma”.

“In an saceta ma zai sai wata, kuma ya sai miki kema, banda faɗan rashin gaskiya ke fa ki ka fara zaginsa a social media, amma tsabar rigimarki kina ta zaginsa, kin ci sa’a da bai ɗaureki ba, ko ya sa a zaneki ba”.

“Oho ni dai ban yafe ba”

Tayi ajiyar zuciya ta ce “I love your confidence my dear, you can face the challenges. Jikina na bani wani abu game da ke, zaki iya ruma” tayi maganar tana jan kunatun rumaisa ta ce “Kamar haka mijina yake wasa da kumatuna”.

“Anty Aisha, yake taɓaki? Ba a wasa da maza fa” ba ta bawa ruma amsa ba, sai dariya da take yi mata, tana fatan Allah ya tabbatar da abun da take ji game da ruma.

Ranar da zata rasu bayan ta haihu, ta riƙe hannun rumaisa ta ce “Baby rumaisa, idan Allah ya sa kin kuɓuta, ni ‘yar gidan turakin kano ce, amma kar a nemi mahaifina kai tsaye a nemi sirikata, idan ba zaki iya riƙe jaririn nan ba, ki danƙa mata shi, Hajiya Binta giwar Galadima, uwar gidan galadiman kano, sirikata ce ita zaki danƙawa jaririn nan, ɗan ta shine mijina” a lokacin gaba ɗaya ruma ta manta da wani adam balle ta kawo shi a lissafi da aisha ta yi zancen galadima.

Ko da ruma ta zo nan a tunaninta sai ta tambayi kanta ‘Kenan da gaske shi ne mijinta?’ a zahiri kuwa ta fashe da kuka ta ce “Wallahi ba shi ne babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba” a bata iya tafiya ta fara ƙoƙarin dirowa daga kan gadon tana miƙa hannu ta ce “Ni ku bani jaririna, ba ɗansa bane ba, ni ba ta ce mini in bawa kowa ba, ku bani ɗana” mama tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Bashir ya miƙawa Adam hannu ya ce “Ka ga Adam, kawo yaron nan, gaba ɗaya a ruɗe take, kamar ba ta hayyacinta ne ma, kawo a bata shi kan muga yadda hali zai yi”.

“Bashir ka haukace ne? Taya ka ke cewa in baka ɗana ka bawa wani?”.

“Wallahi ba ɗansa bane ba, ku bani ɗana” ruma tayi maganar tana kuka.

Bashir ya karɓe yaron, ya miƙawa rumaisa, ta rungumeshi tana fashewa da kuka ta ce “Cewa ta yi idan ba zan iya riƙe shi ba, in bawa giwar Galadima ni ban santa ba ma, ban san a in da take ba, amma ni dai zan iya riƙe yarona, ai cewa ta yi ta bar mini shi har abada nice mamansa”. Gaba daya ɗakin aka zubawa sarautar Allah ido.

Ammi da tun ɗazu take zaune kamar an shukata, ta kasa magana sai tasbihi kawai da take yi, ta tashi sannu a hankali, ta je kusa da rumaisa suka matsa mata ta zauna.

Ta dafa kafaɗar rumaisa idonta fal hawaye ta ce “‘ya ta, nice giwar Galadiman kano mai rasuwa, Adam kuma ɗana ne, shine mahaifin wannan jaririn, kuma mijin Aisha”.

Ruma ta girgiza kai ta ce “A’a wallahi ba shi bane ba, ni fa ba zan bawa kowa ba, ni ta ce ta barwa shi”.

Ammi ta ce “To shikenan, na ji babu mai rabaki da yaronki, Ubangiji Allah ya baku lafiya gaba ɗaya, yanzu ki bayar da shi a mayar da shi sashen kula da yara”.

Rumaisa ta girgiza kai ta ce “Ba zan bayar da shi ba, haka kurum ya bishi ya sace shi, da in bashi ɗana gara na koma wurin ‘yan garkuwa da mutanen”.

Huzaifa ya ce “To fa ana wata ga wata”.

Ammi ta ce “To shikenan, rungume shi da kyau, kin ga bacci zai yi kema ki kwanta ki huta” a’a ba zan rufe idona in je ya gudu da shi ba.

Miƙewa Adam yayi jikinsa yana rawa, amma Ammi tayi masa wani irin kallo, tayi masa nuni da ya fita, yayi gaba ya tsaya ya waiwaya yana kallon rumaisa, da jaririnsa da yanzu ya shiga tunanin ina uwarsa? A wane hali kuma take ciki?”.

Suna tafe a hanya babu wanda ya iya cewa komai, sai Bashir da yake yi wa Adam nasiha “Adam dole sai mun bi yarinyar nan a hankali har yanzu a rikice take, kuma a cikin firgici ba ƙaramar azaba ta sha kan ta fito da yaron nan ba, kaga Yarinya ce ƙarama ikon Allah ne ya fito da su, dan ita ma ba gama sanin ciwon kanta tayi ba, a sannu zamu bita mu ji a ina ita Aishar take, sai mu zo mu yi shiri”.

Daga Ammi har takawa, babu wanda ya ce wani abu, kowa da abun da yake saƙawa a zuciyarsa, adam bai taɓa tunanin abubuwa su cukurkuɗe masa haka ba.

Suna zuwa gida ammi ta wuce part ɗinta, adam ma bai jira bashir ba, ya rufa mata baya.

A falo nusaiba ta tare ta tana tambayarta, “Ammi wai ina ki ka tafi haka, mun dawo daga islamiyya kawai muka tarar ba kya nan, kalli dare har ya fara yi fa” sai dai fuskar ammin ta nuna mata ba lafiya ba. Kan ta yi magana ta ga adam ya shigo ya bi bayan anmi, hakan ya sanya ta sha jinin jikinta.

A ɗaki ya tarar da ammi, ta ajiye carbin hannunta da mayafinta, hawaye tuni ya wanke mata fuska.

“Ammi dan Allah ki tsaya ki saurareni, kar ki yi mini haka”.

Ta kalli Adam ta ce “In saurareke ka gaya mini me adam, yanzu a duniya akwai abun da zaka iya ɓoye mini? Ta ina zamu kalli duniya mu fara bayanin abun da ya faru? Ta yaya duniya za ta yadda da cewar jaririn nan ɗanka ne? Da yaya zaka yi wa turaki bayanin abun da ya samu ‘yar sa, shikenan mun zama masu son kai kenan, idan maganar nan ta yaɗu ina zan saka kaina, ina ta ƙoƙarin toshe waccan kafar wannan ta ɓullo, adam kana me garin yaya haka ta faru ka ɓoye mini, ɗan da ba a san da cikinsa ba kawai mu ce ga ɗa meye shaidarmu ba ƙarya muke yi ba, ina ita Aishan?”

Adam da ya gama rikicewa ya ce “Dan Allah ammi ki fahimce ni, zan yi miki bayani bani da laifi, ba domin na ɓoye miki na yi duk abun da na yi ba”

Ammi ta katse shi ta hanyar cewa “To domin ka faranta mini ne? A tunaninka zan yi murna da hakan ne?”.

Ya girgiza kai tare da goge hawaye ya ce “A duniya bani da makusancin da ya fiki, daga ni har aisha, kin san komai Ammi, kamar yadda muke ta neman magani tsawon shekaru huɗu, aka dace cikin jikinta ya zauna, bayan ɓari da take ta yi babu ƙaƙƙautawa a dalilina, cikin nan  babu wanda ya san da shi, bayan ke sai mu, wanda hakan shawarar ki ce, har zuwa lokacin da kika bayar da shawarar ta je Saudiyya wurin ɗan uwanki kawu mahadi, ta zauna ta raini cikin a can, idan ya isa haihuwa ta dawo Nigeria, duk dan kaucewa hatsarin da ka iya faruwa da cikin, muka yi nesa da juna ni da ita.

Bayan na kai ta ta yi watanni huɗu, na sake komawa Saudiyya umara, na dubata, na dawo babu daɗewa ta ce mini ita ta gaji da zaman Saudiyya so take ta dawo gida. Ta ce mini wannan kakar ta ta, mariƙiyar mamanta babu lafiya, dan haka ita so take ta dawo ta je ta ganta, kar ta rasu basu gana ba. Gudun ɓacin ranki, ya sanya ta dawo babu wanda ya sani, sai dai a lokacin cikin yayi girma sosai ta sanya rigima a kan lallai sai ta je duba matar, an ce ba ta gane kowa, wankin ƙoda ake yi mata ma. Duk sauƙin kan Aisha, haka ta kafe a kan lallai sai ta je katsina duba matar, a daidai lokacin kuma ni tafiya Abuja ta kamani, bayan tafiyata ta sanya ɗaya daga yarana, masu tsaron lafiyarta ya kai ta katsina. Ta turo mini saƙo a waya tana bani haƙuri a kan ita fa ta tafi, ba zata iya jira na dawo ba, a tsorace take kar kakarta ta mutu. Bayan dawowata daga Abuja, sai samun saƙo na yi, an tsinci gawar yarona da motar, ita kuma ba a san in da take ba, tun da ga wannan lokacin nake ƙoƙarin gano in da take, har zuwa wannan lokaci, daga ni sai Bashir muke ta ƙoƙari, dan ko su Jabir basu sani ba, na san na yi laifi ammi amma ba da gayya na yi ba.

“Adam nika ɗai zan fuskanci wannan bayanin naka, duk mutane sun san da cewa tana Saudiyya, babu wanda ya san ta zo Nigeria haka zalika babu wanda ya san tana da cikin ma, kawai sai mu ce ga ɗa to ita tana ina, na gaya maka bana samunta a waya, amma ka yi ta yi mini ƙarairayi, dama akwai abun da zaka iya ɓoye mini Adam? Me zaka cewa Turaki?”.

A raunane Adam ya ce “Ko babu wata cikakkiyar shaida,ni na san da cewa ɗana ne, babu yadda za ayi yarinyar nan ta san wasu abubuwan idan ba gaya mata tayi ba, amma ammi ni yanzu ba abun da mutane zasu ce ne ya dameni ba, samo aisha ne ya dameni, babu wata hujja da nake jira yaron nan nawa ne, ko a fuskarsa kamanni na ne, sannan da kaina zan gayawa turaki komai, duk hukuncin da zai yi mini zan ɗauka”.

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Zan cigaba da yi maka Addu’a, Allah ya kawo mana mafita, amma yarinyar nan ka bita a hankali dan Allah, in sha Allah yadda jaririn ya kuɓuta, ita ma zata kuɓuta”.

Adam ya jinjina kai kawai, ya tashi ya fita daga ɗakin, su Nusaiba suna falo a tsaye cirko-cirko, adam ya zo ya fice.

Cikin rige-rige suka tafi ɗakin Ammi, amma suka tarar ta shiga toilet, ko da ta fito umarni ta basu, na su je su kwanta sai da safe, dan kar su bi diddigin abun da ya faru, sai dai a tsorace take da abun da ka iya faruwa idan zancen nan ya fasu.

A asibiti kuwa, Aliyu ne ya dubi rumaisa ya ce “Ke dai a rayuwarki ba a taɓa rasaki da matsala, an samo uban yaro kin ce ba shi ne ubansa ba, sai ki nuna mana waye ubansa?”

Usman ya ce “Ai ko da uban me ki ke yawo, sai an mayar musu da ɗan su”

Mama ta ce “Yanzu dai a bar wannan maganar, Allah ya dawo mana da ita, daga dawowarta sai a bari ta sarara kan a hau yi mata faɗa, Ali ku je gida haka, kwa sanar da mutane an ganta”

Mai sunan Baba ya ce “Eh amma kar su sanar da Asibitin da take, kar azo a takura mata, ko ayi ta surutu saboda jaririn nan, a bari komai ya daidaita”

Mama ta ce “To hakan ma babu laifi, kar ku gayawa Abubakar a daren nan tun da ba a samu wayarsa ba, ku bari sai da safe kar ya ce zai bsro dutse yanzu”

Usman ya ce “In sha Allah”

Mai sunan Baba ya saka hannu, ya karɓi jaririn da ga hannun rumaisa, sai bin sa take da ido, kar ya fita ya bawa Adam yaron, ya ƙarewa yaron kallo ya ce “Bari na bawa nurses ɗin nan, su mayar da shi ɗakin da ake kulawa da sh, mama gobe in Allah ya kaimu zan zo mu koma ki ga likitan ki”

Mama ta ce “Ga mara lafiya ni ina zani? Dama rashin lafiya tawa saboda ita ne”

Ya ce “Duk da hakan, yakamata ke sai da safe, ki nutsu ban da gardama da taurin kai ki yi addu’a ki kwanta ki huta”

Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce “Dan Allah mai sunan Baba kar ka bawa kowa shi, wallahi zan iya rasuwa idan aka rabani da shi” bai ko waiwayo ba ya fice daga ɗakin.

Mama ce ga rungumota tana rarrashinta ta ce ‘Ba wani zai bawa ba kin ji, ki yi haƙuri ɗakin da ake kula d shi zai kai shi” rumaisa ta yi lamo a jikin mama, can ta ce ‘Mama”

Mama ta amsa mata da na’am.

“Ba mafarki nake ba ko, ba zan kuma farkawa na ganni a dajin ba, na ga kun daɗe a wannan mafarkin nawa”.

Mama ta shafa bayanta ta ce “Ba mafarki bane ba, duk muna tare da ke”.

“Mama kin ga yadda ki ka rungumenin nan? Haka maman yaron nan take rungumeni tana rarrashina idan na tunaki ina kuka, sarƙarta da zobuna ne a cikin ɗankwalin nan, ɗan kunnen da ki ka cire a kunnena shi ma nata ne, mama ba zan manta da ita ba” rumaisa ta yi maganar cikin kuka.

“To ya isa, ita ma in sha Allah zata kuɓuta cikin amincin Allah” rumaisa ta cigaba da kuka, dan ba wanda ta gayawa aisha ta rasu.

Aliyu suna zuwa unguwarsu, ya wuce gidan su Habiba, lokacin kusan ƙarfe goma na dare, ya aika yaro ya ce yana sallama da Habiba.

Maimakon Habiba sai babarta ta fito tana masifa, wani watsatstsen ne ya zo neman habiba a wannan daren, yar habiban guda nawa take?

Tana ganin Aliyu ta yi sak, ta ce “Ya aka yi ne, ko laifin ta kuma yi maka, ko ƙanwar ta ka ta kuma duka ka zo rama mata, duk da ance an yi garkuwa da ita”

Ya ce “Ba ɗaya, wani abu zan gaya mata”.

“Wani abu ne kenan?”

Aliyu ya ce “Shikenan tun da na ga hankalinki bai kwanta ba”

Sai kuma ta ce “A’a, bari na taso ta” ta koma cikin gida, mintuna uku sai ga habiba ta fito tana mutsutsuka ido.

“Habiba” ya kira sunanta, ta kalleshi ta ce “Yaya Aliyu ina wuni”

“Albishirnki” yayi maganar cikin murmushi.

Ta ɗan yi saroro ta ce “Goro”.

“To zaki bani goron nan, Alhamdilillah addu’a ta karɓu, rumaisa ta kuɓuta yau, tana asibiti ma”

Gigicewa ta yi ta ce “Innalillahi, dan Allah da gaske, dan Allah kar ka ce da wasa kake yi, dan Allah mu je in ganta”.

“No, ba a zuwa wurinta yanzu, ba ta da lafiya, amma zan zo da kaina na kaiki ki ganta”

Hawaye ta fara matsewa tana “Allah sarki ƙawata, Alhamdilillah, Allah na gode maka”

Ya ce “Maza ki je ki cigaba da baccinki, Sai da safe”

“Dan Allah yaushe zaka zo ka kaini na ganta, gobe?”

“A’a zan zo dai, ki je ki cigaba da baccinki” yayi maganar yana ɗaga mata hannu ya tafi.

Ta shiga gida da gudu tana murna.

Adam kuwa yana zuwa ɗaki ya zauna ya fashe da kuka kamar yaron goye. Wai matarsa ce ta haihu a daji a hannun ‘yan bindiga, ko a yaya ta haihu oho, ko a wani hali take sanin gaibu sai Allah.

“Why aisha, meyasa ki kasa jira na dawo ki ka tafi? Duk yadda muka tssra rayuwa bayan kin haihu, ƙarshe a tsinto mini ɗana babu ke, haba aisha kin ga sakamakon rashin jin magana ko, matar da ki ke so ki je ki duba ita bata mutu ba, amma ke kin shiga wahala. Amma bakomai, Allah ya sa kina cikin ƙoshin lafiya, zan fito da ke ko da zan rasa rayuwata ne!

Haka Adam yayi ta surutai, kamar zai zauce.

Mama kuwa kwana tayi tana salloli tana miƙa godiyar ta ga Ubangiji, na bayyana mata rumaisa da yayi, idan aka jima sai ta je ta leƙa fuskar rumaisa, kasancewar ita da Abdallah ne a wurin ruma, Abdallah yana gefen  gadon rumaisa sai kallonta yake yi, shima ganin abun yake kamar wasa wai rumaiss ta dawo.

Mama tana tsaka da salla, ruma ta farka daga bacci tana cewa zata yi fitsari, Abdallah ya ɗagata cak ya kaita banɗaki, mama tana ta gyaran murya, amma ya kai ta tayi fitsarin, sannan ya mayar da ita kan gadon ya kwantar.

Ta kalleshi ta ce “Yaya Abdallah”

“Na’am rumaisa”.

“Kaga haryanzu ban tashi daga baccin ba”

Yayi murmushi ya ce “Ai a gaske ki ke ba bacci bane ba”.

Tayi ajiyar zuciya ta ce “Ai na kasa ganewa ne, wataran sai in ganni a dajin, wataran a nan amma dan Allah mai sunan Baba bai bashi jaririna ba ko?”.

“Bai bashi ba, yana can ɗakin yara”.

“Alhamdilillah, ina son yaron nan bana son a rabani da shi”

Abdallah ya ce “To maman boy”

“Abdallah ban zaci zan rayu ba, na sha wahala sosai, ranar da aka tafi da mu, na din ga kuka na gaji da tafiya, aka goyani a babur, aka kaini wurin”.

“Amma dai basu yi miki wani abun ba ko?”

“Wallahi sun yi mini, abubuwa ma da yawa, zan baka labari da safe, wannan ciwon na ƙeyata ne yake mini zafi, jikina ma duk babu daɗi, kwanana uku fa ina tafiya a daji”.

Gaban mama ne ya faɗi, jin rumaisa ta ce an yi mata abubuwa da yawa tana matuƙar tsoro da fargabar ace sun lalata rumaisa, gashi haryanzu likita bai faɗi sakamako bincikensa ba.

Da safe mama ta tashi rumaisa, ya yi salla, ta wanke mata baki, ta yi mata wanka, ta saka mata wata ‘yar riga domin ta samu ta sha iska, nurses suka shigo suka yi wa rumaisa dressing ɗin raunukan jikinta. Mama ta kalleta ta ce “Ko kina buƙatar wani abun? Ga kayan marmarin nan, wanne zan baki a ciki ki ci?”.

“Ba ko ɗaya, kawai ki zauna a kusa da ni in rungumeki in ji ɗuminki” mama tayi murmushi ta ƙarasa kusa da ruma, ta rungumeta.

Abdallah ya koma gefe ya ɗan samu bacci, saboda daren bai yi bacci ba saboda farinciki.

“Rumaisa” mama ta kira sunanta, ruma ta ɗaga kai ta kalli mama.

“Ina fatan babu abun da suka yi miki, lokacin da ki ke wurinsu?”

Ta mayar da kanta ta kwantar a jikin mama ta ce “Mama ni meye ma ba ayi mini ba, bana son tunowa tsoro nake ji, mama ki ɗauko jaririna shi ma ayi masa wanka”.

“Na ji, amma ina fatan…” Ba ta ƙarasa ba, ruma ta katseta ta hanyar cewa “Mama dan Allah ki daina tanbayata a kan mutanen nan, tsoro nake ji, dan Allah ki daina tuna mini” mama ta ce “To shikenan, bari in karɓo yaron”.

Mama ta je ta karɓo jaririn, har nurses suke gayawa mama a kowane lokaci zasu iya sallamar yaron, zuwa yanzu babu abun da yake damunsa, kuma gwaje-gwaje sun nuna malaria ke damunsa, sai kuma pneumonia, amma ba wata mai damuwa ba.

Mama ta ce “To masha Allah, Ubangiji Allah ya ƙara afuwa”.

Mama ta tafi da shi ɗakin da rumaisa take, ta karɓo pack ɗin da Bashir ya sayo na jaririn, da madararsa da komai.

Ta haɗa ruwa ta yi wa yaron wanka, ta shirya shi, ta haɗa madara ta bashi, ta miƙawa rumaisa shi. Ruma har da ajiyar zuciya ta zubawa yaron ido, sai ta fara hawaye.

Mama ta ce “To kukan na menene?”

“Mama tausayin yaron nan nake ji, mun sha wahala sosai da tuni an kashemu, ko shi an kashe shi, wasu mutane ne suka ce dole a kashe shi, kar ya rayu fa”.

Mama ta ce “Wasu mutane ne?”

“Nima ban san su ba, Allah ya baka lafiya yarona” tayi maganar tana shafa kan jaririn, tana murmushi shi kuma sai cin hannunsa yake yi, yana kallon ruma yana lumshe ido.

Mai sunan Baba ne yayi sallama, shi da Usman, hannunsu ɗauke da kayan abinci.

Duk suka gaida mama ta amsa musu, ruma ta ce “Mai sunan baba ina kwananku?”

“Lafiya lau ya jikin naku?”.

“Da sauƙi Alhamdilillah”

Umar ya ce “Allah ya ƙara afuwa, kai Abdallah tashi ka haɗa mata abun karyawa”

Abdallah ya haɗawa rumaisa shayi da uban ƙwai, ya bata da ƙyar ta sha shayin, ta ce ita bata son cin komai.

Mai sunan Baba ya sanya mama a gaba, a kan lallai sai ta tashi sun tafi gida, sai ta je ta huta ya kaita ganin likita, da ƙyar mama ta amince, ya sakata a gaba ya ce Abdallah ma ya tashi ya je gida ya huta ya dawo da yamma. Aka bar ta da ita da Usman, sai jaririnta da take ta shafa kansa tana murmushi.

Adam kuwa kwanan zaune yayi, yayi kuka kamar ya fita a hayyacinsa haka ya wayi gari, Ammi ma kusan a haka ta kwana, tunani kawai take yi a kan ina zasu samu mafita, ta ina za su fara.

Wajen ƙarfe goma na safe, Bashir ya je gidan su takawa, ya sa aka yi masa iso wurin Ammi, ta bayar da damar a shiga da shi, cikin girmamawa suka gaisa ya ce “Ammi dama na zo ne mu koma asibiti da Adam, muje mu ji ko akwai wani bayani da zamu samu daga bakinta yarinyar, tun da naga jikinta da sauƙi, amma na kira wayoyinsa a kashe na je can gidansa an ce bai kwana a can ba”.

Ammi ta ɗan dube shi ta ce “Malam bashir ban ji daɗin ɓoye mini abun da ke faruwa da ku ka yi ba, gaba ɗaya kun jagwalgwala al’amura, amma shikenan na san ba laifinka bane, shi ya fi kamata ya sanar da ni, bari na duba ko a gidan nan ya kwana ma”

Ko da Ammi ta je ɗakin Adam a zaune ta tarar da shi, babu alamar ya runtsa, idanunsa sun yi jawur sun kumbura.

Ammi ta ce “Ka yi sallar asuba kuwa?”

Ya jinjina mata kai alamar eh.

“Tashi ka yi wanka, ka karya ga Bashir can yana jiranka”

“Ammi dan Allah ya ƙyaleni, bana son jin komai, kaɗaici nake so”.

“Shi kaɗaicin me zai maganta maka bayan mai faruwa ta riga ta faru, so kake jama’a su fuskanci wani abu kafin mu kai ga samun mafita? Ka tashi ya ce so yake ku je ko akwai bayanan da zaku samu a bakin yarinyar”

Adam bai kums cewa komai ba ya tashi ya shiga banɗaki, bai san a yaya yayi wankan ba ma, ya fito, Ammi ta saka shi a gaba, ya ɗan zuƙi shayi kaɗan ya fita. A falo ya tarar da Bashir, su Iman suna gaishe shi, amma babu wadda ya amsawa haka ma barorin da suke wurin, ya ce wa bashir tashi mu tafi.

Ammi ta bi bayansu tana yi musu magana ƙasa-ƙasa.

Nusaiba ta yi wa iman kallon meyake faruwa ne, iman ta ɗan ɗage kafaɗa alamar ita ma ba ta sani ba.

A harabar gidan suna shirin hawa mota, sai ga motar Jabir ya shigo gidan, takawa bai tsaya ba ya shiga motar bashir, saboda baya son magana da kowa a halin yanzu, kuma ya san jabir ritsa shi zai yi da tanbayoyi masu ma’ana da marasa ma’ana.

Takawa suna tafe a hanya shi da bashir, babu mai cewa komai, can bashir ya ce ‘Adam ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi dai-dai ina kyautata zaton zamu samu duk wani information da zai iya taimaka mana a kan binciken mu”.

“Bashir, komai ya hargitse mini, ban san ta ina zan kuma sake fuskantar matsalolina ba, jiya kwana na yi ina tunani, yaya aka yi yarinyar nan ta kuɓuta da jariri ina Aisha take, wani irin tashin hankali da tozarci ne haka ace matarka ta haihu a hannun ‘yan ta’adda?” Yayi maganar cikin tsananin damuwa da zafin rai.

Bashir ya dafa shi ya ce “Calm down, ka bi komai a hankali, komai zai dai-dai ta in sha Allah”.

Baba uwani ta kasa zaune ta kas tsayez babban burinta shine ganin yadda za ta yi ta san meyake faruwa, ta samu ta kaiwa Mummy labari, domin a kan idonta Ammi da takawa suka shigo a daren jiya, haka zalika yanayin yadda ta ga fuskokinsu a wayewar garin yau ta sake tabattar da akwai wani abu da yake faruwa kuma da alama babban al’amari ne, amma babu wata hanya ko kafa aka bari balle ta ji labarin.

Bashir sai da ya tsaya a hanya ya sai carton carton na ruwa da maltina, suka ƙarasa Asibitin da rumaisa take.

Bashir ya sanya masinja ya ɗauko kayan da suka zo da su, ya biyo su.

Da sallama suka shiga ɗakin da rumaisa take, ba dan ƙarancin shekarunta ba, kai ka ce mai jego ce, saboda yadda take rungume da jariri a hannunta, usman ya amsa musu sallamar ruma kuma ta ɗago ta kallesu.

Bashir ya sallami masinjan nan, sannan suka zauna, suka gaisa da usman, suka tambaye shi mas jiki ya ce da sauƙi, wanda duk bashir ne yake yi, Adam ba ya iya magana.

“Rumaisa ba magana, ina kwana ya baby?”.

“Lafiya lau” ta faɗa tana satar kallon takawa da yayi zuru-zuru ta taɓe baki.

Mu ga babyn yayi maganar yana karɓar jaririn yayi murmushi ya ce “Alhamdilillah, kin ga babyn zai warke ya barki, gaskiya ki daina langwai” ita dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Bashir ya miƙawa adam yaron, ya kuma kallonta ya ce “To ya jikin naki?”

“Ba sauƙi” ta faɗa kai tsaye.

Usman ya ce “Ke fa daɗina da ke ƙarancin tunani, ba zaki godewa Allah ba ki ce da sauƙi, zaki ce ba sauƙi?”

Sai ta fara kuka ta ce “To ina sauƙi? Mama ta aske mini gashi, bana iya taka ƙafata ƙeyata ma ciwukan zafi suke yi mini, ga haƙarƙarina ciwo yake mini”.

Bashir ya ce “Ya salam, kin gayawa likita? Ko kin faɗi da wurin ne?”

Ta ce “A’a wani sule ne ƙato ya dinga takani da ƙafarsa a wurin, tun daga nan yake mini ciwo”

Bashir ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Adam ba shi jaririn a mayar da shi nursery dan Allah, dan na ji yana atishawa ko sanyin nan yayi masa yawa”.

Adam bai motsa ba, ya zubawa yaron ido yana jin wani irin tausayinsa da ƙaunsrsa na shiga ransa, ya karɓi jaririn ya bawa usman, usman ya fita mayar da shi ya rage daga takawa sai bashir da ruma a ɗakin.

Bashir ya kalli rumaisa ya ce “Rumaisa, kamar yadda dai na yi miki bayani da fari, Adam abokina ne, dukkaninmu jami’an tsaro ne na farin kaya, zai yi miki wasu tambayoyi ne dan Allah ki bamu haɗin kai”

Rumaisa ta kawar da kanta gefe, taƙi ko kallon in da Adam yake.

Adam ya numfasa ya ce “Ta yaya zaki tabattar mini wannan ɗan na Aisha ne, ita ta haife shi”

Rumaisa jin tambayar ta yi kamar da rainin hankali a ciki “To ai ba sai ka tabattar ba, tun da dai ni na san ɗanta ne, shiyasa na ce ba kaine babansa ba”.

Bashir ya ce “A’a ruma yi haƙuri, kin san komai a hankali muke bi tun daga tushe, ki bamu amsa Please”.

Ta ɗaga filon da take kai, ta janyo ɗankwalin aisha, da yake a ninke, ta wurgawa adam cinyarsa “Ni banda wannan ban san me zance maka ba”.

Ya saka hannu ya ɗau ɗan kwalin yana jujjuya shi, yana tuna wasu abubuwa da suka faru, tabbas ɗan kwalin aisha ne.

Ya ɗaga kai ya kalli Ruma ya ce “Ina aisha take yanzu? Ya aka yi ki ka kuɓita da jaririn? Ita tana ina?”

Tayi masa banza, dan ranar ƙarshe da ya wanketa da ruwan kwata ne ya faɗo mata.

“Ruma amsa mana, ina aishan take? Kar ki damu, adam ɗan sanda ne na farin kaya, ki yi masa bayanin komai”

Cikin tura baki ta ce “Saura na korayen kaya, ni ban san in da take ba”

“Kamar ya baki san in da take ba, ya ina magana kina shareni, ina Aisha take ina matata”

Ruma ta zaƙalƙale ta ce “Ka bita dajin ka ɗaukota, ka san kana sonta ka bari aka sace ta, ka ƙi zuwa ka fitar da ita, da ku ba gawara babu ba, ba da jami’an tsaro ake haɗa baki ba, haka aka ce da bakin su ‘yan bindigar suka faɗa, in so kuke ku ganta sai ku tafi dajin ai, kuma wallahi idan kuma kun sani aka sace mu kuka ƙi taimaka mana a fito da mu, sai Allah ya saka mana, dukan da na sha a wurin mutanen nan ma ya isheni, ka zo zaka dameni”

Gaba ɗaya ido suka zubawa rumaisa, tana kuka tana tsiwa.

Adam ya ce “Ni kike gayawa haka?”

“Tsoronka zan ji ne, wallahi bana tsoron kowa sai Allah subhanahu wata’ala, kuma wallahi tun da Allah ya sa na fito sai ka gane ba ka da wayo, sai na rama abun da kayi mini”

Kallon tuhuma Bashir ya shiga yi wa rumaisa da Adam, kenan sun san juna, akwai wani ɓoyayyen abu kenan a tsakaninsu.

Usman ne yayi sallama, ya tarar da rumaisa tana kuka, su kuma sun zuba mata ido.

Ya ce “Lafiya kuwa?”

“Ba wannan ne ya sakani a gaba yana zare mini ido ba, wai sai na gaya masa in da matarsa take, kuma ni ban san komai ba, likita ma fa ya ce kar a din ga takura mini amm yake hantarata”

Adam ya dafe goshinsa yana tunanin meya dawo da wannan jarababbyar yarinyar rayuwarsa, meyasa take liƙe da ƙaddararsa ne.

Shi kuwa bashir mamaki ne ya ishe shi, maganganun ta sun girmi shekrunta, ya kalli usman ya ce “Tambayoyi kawai muke mata, so muke mu yi ƙoƙarin ceto uwar yaron ita ma, ba wani abun aka yi mata ba”.

Usman ya kalleta ya ce “Ke ki gaya musu abin da ki ka sani mana”

“Ni ban san komai ba”

“Kamar yaya, ya aka yi ki ka karɓo jariri ki ka gudo, ina babarsa take?”

“Tana can” tayi maganar tana share hawaye.

“Ke ya aka yi ki ka fito?”

Sake ɓare baki tayi tana kuka ta ce “Wallahi likita ya ce a daina takura mini, da me zan ji kai baka san wahalar da na sha ba, kun haɗu kuna hantarata”

Usman ya ce “Ke fa rumaisa makira ce wasu lokutan, uba waye ya hantarekin?” Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kalli su Bashir ya ce “Tun da ba zata faɗa abubuwan da ake buƙata ba, ku ɗauke ɗanku ku tafi, kar ta sake ganinsa ma”

Ihu ta fara yi “Ni kar ku ɗaukar mini ɗana”.

“To ki yi musu bayanin abun da suka tambayeki*

“Ni ban san komai ba, ba ‘yan sanda bane su, su je dajin mana su duba, ni nace ba abun da na sani, ni duk na manta wasu abubuwan ma”.

Sarautar Allah bashir ya zubawa ido, bai taɓa zaton tana da baki haka ba, saboda yadda ya tsinto ta a galabaice.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi da ƙarfi, da duk sai da suka waiwaya domin ganin waye.

“Yaya Sadik ɗina” rumaisa ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana kuka”

Bashir ya kalli Usman ya ce “Abokina, wai har ku nawa ne yayyen nata ne?”

Usman ya yi murmushi ya ce “Mu bakwai ne, ita ce autar mu”

“Masha Allah, ba wanda zai ce mamanku ce ta haifeku, sam ba ta tsufa ba” yayi maganar yana murmushi.

Abubakar ya kalli Usman ya ce “Meyasa ba a gaya mini tun a jiya ba, sai yau da asuba Aliyu ya gaya mini”.

“Mama ce ta ce kar a gaya maka, kar ka ce zaka taho a jiya, ga wanda ya tsinto ta a katsina nan” yayi maganar yana nuna masa bashir.

Abubakar ya nufe shi ya miƙa masa hannu yana faɗin “Ɗan uwa, mu gode mun gode Allah ya saka maka da alkhairi, tun da aka ɗauki rumaisa muka rasa nutsuwa mun gode sosai Allah ya biya” ya sake komawa wurin ruma yana dubata ya ce “Allah sarki autarmu, haka ki ka koma duk kin rame ruma, kullum tunaninki muke yi”

“Nima kullum sai na yi tunaninku, sai na ganku a mafarkina” tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Bashir ya dubi Adam ya ce “Akwai buƙatar mu tafi, na san masu zuwa dubiya zasu yi ta zarya, mu ƙyaleta ta keɓe da ‘yan uwanta” takawa bai iya cewa komai ba, Bashir ya ja hannunsa suka fita.

Suna tafe a hanya Adam ya ce “Ka wuce da ni gidana, bana son komawa gida yanzu”.

Bashir ya ce “Shikenan, amma dan Allah kar ka je ka damu kanka, ko ka yi ta tunani, hakan ba wani amfani da zai yi maka” still dai Adam bai ce masa komai ba.

Can bashir ya kuma cewa “Amma it seems you know each other before kai da yarinyar nan, a ina ka santa?”

“Bashir, dan Allah ka ƙyaleni, ina cikin tsaka mai wuya, dole yarinyar nan ta yi magana, kan al’aamrin nan ya ƙara kwaɓewa” yayi ya a hasale.

Bashir ya ɗan gyaɗa kai ya ce “Haka ne, amma dole ka rage zafin zuciyar nan mu bi a hankali, dan yarinyar nan da alama gardamammiya ce ta fika taurin kai” ya cigaba da tuƙi, ba wanda ya kuma cewa komai.

Can gidansu Adam kuwa, su Iman suka ƙara shiga damuwa, ganin ammi ba ta fito karyawa ba, kuma sun je wurinta hadimarta ta tabattar musu da cewa ta ce kar wanda ya je wurinta, tana buƙatar kaɗaici.

Cikin damuwa Nusaiba ta ce “Iman, ko ke kin san wani abu ne da yake faruwa, why are they behaving like this? They all look strange today”

Cikin damuwa iman ta ce “Tare fa muka kwana muka tashi da ke, ban san komai ba, nima dai na shiga damuwa da mamaki, wani abu yana faruwa amma maybe ba sa son mu sani ne”.

“Amma ko menene wannan, abu ne mai girman gaske, tun da har ta kai ga ammi ta ce kar wanda ya je wurinta, ga takawa tunda suka fita da abokinsa bai dawo ba” suka koma suka zauna suna tattaunawa a falo.

Baba uwani ce ta same su ta ce “Yaran nan meya samu giwar Galadima ne yau, daga ita har ɗan gidana na kasa gane kansu yau, ko abinci ba ta bari an shigar mata da shi ba, shi kuma ina magana bai ko kalleni ba, duk da miskili ne amma ba ya shareni idan na gaishe shi”

Iman ta ce “Zancen da muke yi kenan, bamu san meyake faruwa ba”

“To Allah ya sa dai lafiya” tayi maganar ba tare da ta ji daɗin rashin samun wani bayani ba.

Ƙamsshin turarensa da ya daki hancinta ne ya sanya ta san shine, a take ta ƙara tsuke fuska.

“‘yan matan ammi, ya na ganku kun yi tsilli-tsilli da ido kamar marasa gaskiya ne?”

Nusaiba ce ta fara cewa “Uncle J ina wuni?”

“Lafiya lau” ya amsa yana ƙarewa iman kallo. Banza ta yi masa taƙi kulashi.

“Iman ba zaki kulani ba?” Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ja wata irin ajiyar zuciya ya ce “Ina ammi ne?”

Nusaiba ta ce “Tana hutawa ne, ta ce kar a dameta yau”

“Takawa fa, tun jiya rabona da shi, ga wayoyinsa ba sa shiga gaba ɗaya, a gidan nan ya kwana ne ko gidansa?”

“Eh a nan ya kwana, amma yanzu baya nan”

Ya ɗan yi shiru sannan ya kuma cewa “Ba ku san in da ya tafi ba?”

Nusaiba ta waro ido ta ce “Uncle J, takawa ne zai gaya mana wani wuri da za shi? Bamu sani ba”.

“Wai ya nake ganinku duk wani iri ne, ko akwai abun da ku ke ɓoye mini?”.

Nusaiba ta ce “A’a Bakomai”.

Miƙewa iman ta yi zata bar falon “Iman” ya kira sunanta.

Ta tsaya cak ta waiwayo tana jiran abun da zai ce.

“Zo ki zauna ina da magana da ke”

Ji ta yi tamakar ta ce ba zata dawo ba, amma ta nemi wuri ta zauna.

Yayi wa Nusaiba alama da ido, a kan ta basu wuri. Ba musu Nusaiba ta tashi ta bar falon.

Kujerar two seater da iman ke kai, ya zo ya zauna, ya ɗan tsura mata ido, amma ta takure jikinta, kamar yana motsawa zata zura da gudu.

“Iman” ya kira sunanta, ta ɗan ɗago amma ba ta kalleshi ba.

“Meyasa ki ka yi blocking ɗina a what’s app, da phone ɗinki gaba ɗaya?” Tayi shiru tana sauke numfashi.

“Am talking to you, or just because i ask for your pictures, you can deny it if you don’t want, meyasa zaki yi blocking ɗina, bari abun da ki ke ta gudun kar in faɗa, i love you, ina son ki iman, kuma zan bi ta in da na san zan samu abun da nake so kai tsaye, kin san tsarin gidan sarauta ai, so gara ki kwantar da hankalinki ki daina kaucewa” hawaye ne ya cika mata ido, amma ta yi ta ƙoƙarin kar su zubo. Ya gama surutansa ya tashi ya tafi.

Kamar zata kifa haka take sauri, yau ko bari ba ta yi daren yayi ba, saboda yadda maganar ke mimtsininta ji take idan ba ta je ta kai rahoton ba, wani zai rigata.

Sashin Mummy ta isa, ta nemi iso aka yi mata, mummy na ganin yadda baba uwani ta shigo jiki na rawa ta san akwai magana, dan haka ta sallami barorinta, ya rage daga ita sai baba uwani. Ta dubeta ta ce  “Meyasa ki ka shigo mini a yanzu? Sai kin saka an fara zargin mu, ina fatan dai abun da ki ka zo mini da shi, mai muhimmanci ne ba shirme ba?”

“Allah ya baki yawan rai, wani ƙwai ne yake gangarowa daga kan dutse, kuma da alama idan ya fashe zai yi warin da zai addabi kowa”.

Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce “Bani labari”.

“Alamu sun nuna akwai wani abu da giwa take ɓoyewa ita da ɗan ta, dan tun jiya sun kasa sukuni, sun gaza zaune sun gaza tsaye, dan ita yau ta hana kowa ya je in da take har ‘ya’yanta, shi ma kuma tun da ya fita shi da wani abokinsa bai kuma dawo ba, suna ta ƙumbiya-ƙumbiya, amma ina nan zan sanya ido, da na ji ƙyas zan kawo miki rahoto”

Mummy ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Ta kaɗaice ta hana kowa zuwa in da take, ciki har da ‘ya’yanta, lallai abun da yake cikin ƙwan nan, ba ƙarami bane ba, ki cigaba da sanya ido, ƙwan ya fashe a kan idonki, kuma da zarar ya fashe ina son ki riga kowa sani, ya kuma nice wadda za ta fara jin ko menene, ina nan ina jiranki, haka zalika nima zan sanya ido a nawa ɓangaren”

“Allah ya baki masara, in Allah ya yarda za ayi duk abun da ki ka ce, na barki lafiya” Mummy ta ɗaga mata hannu alamar zata iya tafiya.

Baba uwani ta tashi tana murnar yadda ta sanya farantawa uwar ɗakinta ta ɓoye.

Unguwar su ruma ta ɗauka cewar ta dawo, magana har islamiyyar su, gaba ɗaya unguwa ta ɗauka, aka din ga yi musu addu’a da tayasu murna.

Huzaifa ne yayi hankalin cewa a kira katsina a waya a sanar musu da anga rumaisa, dan gaba ɗaya ma sun manta da batun su.

Sai da mai sunan Baba ya kai mama ta ga nata likitan, sannan suka tafi Asibitin da rumaisa take.

Gaba ɗaya rumaisa ta kasa daina kuka, saboda farincikin ganin ‘yan uwanta gaba ɗaya a tare da ita, da ta motsa a tambayeta me take buƙata.

‘yan uwa da abokan arziki kuwa da maƙwabta tuni suka fara sintiri a asibitin, domin duba ruma, kowa yazo da ɗan abun alkhairinsa da zai bawa rumaisa.

‘yan uwansu na kano kuwa suma tuni suka cika asibitin, wannan su zo wannan su tafi, sai ga hauwwaliya ma sun zo da sandarta ta dogarawa, kasancewar tun karayar da ta yi kan a sace rumaisa ba ta warke ba. Suka rungume juna.

Ruma ta ce “Hauwwaliya gurguwa ki ka zama ne? Na ganki da sanduna”

Hauwwaliya ta ce “Ke ba gurguwa na zama ba, kin manta na karye ne?”

Ruma ta ce “Au haka ne fa, ban zo na ganki ba ma fa aka saceni”.

“Allah sarki rumaisa, kin ga idi, zaman hannun ‘yan bindiga an ce wahala ake sha fa”

Ruma ta yamutsa fuska ta ce”daina tuna mini dan Allah, wuya ko da magani babu daɗi”

Likita ne yayi sallama shi da nurse, mama ta yi musu sannu da zuwa, mai asibitin ne da kansa ya kalli ruma ya ce “Sai ka ce mun kwantar da shugaban ƙasa, ‘yan dubiya daga wannan sai wancan, kamar ba wani mara lafiya sai ke” ruma tayi murmushi tana kallon trolleyn da suka shigo da ita, tana fatan ba za ayi mata allura ba.

Yayi murmushi ya ce “To yaya jikin naki?”

“Da sauƙi, amma haƙarƙarina fa yana mini ciwo haryanzu”

Ya ce “Mu ga wurin, ya aka yi haƙarƙarin yake yi miki ciwo?”

“Sule ne ya takani a wurin, wani jibgege, nauyin ƙafarsa kamar tsauni”. Yayi murmushi yana ƙoƙarin miƙa hannunsa ya ɗaga rigarta ya duba, amma ta riƙe rigar ta tsareshi da ido.

“Dubawa zan yi na gani”

Aliyu ne ya taso, ya kama rigar tata zai ɗaga “Yaya Aliyu ni kar ka buɗe mini jiki a ganni”

Aliyu ya ce “Ke dallacan, ina tsintoki a ka yi kanki ko ɗan kwali babu, wa zaki yi wa iyayi? Ko shi wanda ya taka kin kin yi masa iyayin?”

Tana zumɓura baki ya ɗaga rigar, likitan ya danna haƙarƙarin, ta saki wani marayan kuka.

Ya ce “Is ok, zan rubuta muku hoto in sha Allah, ayi mini hoton wurin, da kuma kanki”.

“Wurin mai hoto za a kai ni? Ayi mini a waya mana, bana son motsawa ko ina ns jikina ciwo yake”

Ya girgiza mata kai ya ce “X-ray nake nufi, ba hoton passion ba, sauko yau ki taka ƙafar nan na gani” ta girgiza masa kai ta ce “Tana yi mini ciwo fa”

“Sai fa kin taka yau saukko, da yayi ki ka yi gudu ki ka fito daga daji?”.

Shiru ta yi sannan ta ce “Ikon Allah ne ya fito da ni” ta fara ƙoƙarin saukowa a hankali ta tsaya a kan ƙafarta. Likitan ya ce “Good, taka a hankali mu gani”. Tana ƙoƙarin ɗaga ƙafar, amma ji take kamar ba a jikinta take ba, dan haka ta kasa.

Likitan ya ce “Riƙe hannuna, ki ɗaga ƙafar a hankali, bana son ganinki a kwance kullum”

Noƙe kafaɗa tayi, ita ba zata riƙe hannunsa ba.

Ya saka hannu ya riƙo na ta hannun, ya ɗan ja ta sai da ta ɗaga ƙafar sai da ta yi ƙara saboda ciwon da ƙafar take yi.

Usman ne ya taso, ya cire hannun ruma da ga na likitan ya ce “Zamu zagaya da ita in sha Allah, in dai ƙafar ce zata din ga takata” murmushi yayi ya girgiza kai, ƙiri-ƙiri ba sa iya ɓoye kishinsu a kan ƙanwarsu, zai duba mata rauni, Aliyu ya taso ya buɗe masa da kansa, yanzu kuma Usman ya zare hannun ruma daga nasa.

Ya rubuta musu duk abun da yake so a kawo masa, ya fita daga ɗakin.

Hauwwaliya ta dogaro sandarta, Usman kuma yana riƙe da rumaisa suka fita zagaya asibiti.

A hankali rumaisa tana takawa, har suka je ɗakin da jaririnta ke kwance, nurses na kula da shi, sune suke yi masa komai. Ruma ta daɗe a wurinsa, sanann suka fito, a wurin komawa ɗakimta kuma ƙafa taƙi takuwa, ƙarshe sai Goyata Usman yayi ya mayar da ita ɗaki.

Ammi ba ta fito ba sai la’asar, shi ma da ta fito tea kawai ta saka a kai mata, shi kawai ta iya sha, kai da ka ganta ka san a tashin hankali take.

Wayar Adam take ta kira amma ba ta shiga.

Ta fito falo ta tambayi barorinta ko Adam ya shigo? Suka ce mata tun safe da ta raka shi ya fita, bai kuma dawowa ba.

Ammi ba ta samu wayar Adam ba sai magariba.

“Ina ka ajiye wayarka nake ta kira amma ba ta shiga?”.

“Ammi na kashe wayar ne, saboda bana son a dameni da kiran waya”.

“Wannan ba hujja bace, ka san dole zan neme ka ai, ya ake ciki akwai wani abu ne, ko yarinyar ta yi magana a kan Aisha?”

Kamar yana gaban Ammi, ya girgiza kai ya ce ‘Ta ƙi magana, ta ce bata san komai ba”.

Cikin rashin fahimta Ammi ta ce “Kamar yaya?”

“Haka dai ta ce”

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Ka zo ka sameni, asibitin zamu tafi yanzu “.

Ya sauke numfashi ya ce “To gani nan” ya ajiye wayar yana jin yadda kan sa ke sara masa, saboda damuwa da tunani.

Sai kusan ƙarfe tara na dare sannan Takawa ya zo tafiya da ammi, sai a lokacin su Iman suka samu damar ganin ammi.

Cikin damuwa Iman ta ce “Ammi ina zaki?, yau gaba ɗaya bamu ganki ba”

Cikin ƙarfin hali Ammi ta ce “Ku yi haƙuri, wata unguwa zamu je, yanzun nan zamu dawo ba daɗewa zamu yi ba” daga haka ta yi gaba ta bi bayan takawa suka fice.

Iman ta ce “Yaya Nusaiba, akwai matsala fa, Ammi suna ɓoye mana wani abu ba sa son mu sani”.

Nusaiba ta ce “Nima na gani, amma bari mu jira mu gani”.

Ita iman abubuwan sun yi mata yawa, ga maganganun wambai, ga zancen da yake yawo a kan su da takawa, ga abun da take gudu Jabir ya furta wai yana son ta.

Kamar kurame haka su Ammi suka ƙarasa Asibitin da rumaisa take.

‘Yan dubiya duk sun watse, sai Mama da Abdallah mai sunan baba suna ta shirin tafiya gida, Mama ta wanke jaririn nan tas, an haɗa madara an bashi, ya gama sha ruma tana rungume da shi, tana kallonsa tana tuna irin yadda suka sha gwagwarmaya kan su kuɓuta.

A hanyar barin asibitin, mai sunan Baba suka haɗu da Adam da Ammi, ɗan kallon kallo suka yi da shi da takawa, amma babu wanda ya kula wani, suka wuce.

Sallamar su Ammi ce ta dawo da rumaisa daga tunanin da take yi, ta ɗaga kai ta kallesu ba tare da ta amsa sallamar ba, Abdallah da mama suka amsa suna yi musu barka da zuwa.

Ruma ta ɗan ƙare musu kallo, fuskar takawa kamar ta mai amai da gudawa, duk yayi wani iri, mama ta basu wurin zama, suka gaggaisa ammi ta dubi ruma ta ce “Maman baby ba magana?”

“Ina wuni” Ammi ta ce “Lafiya lau, ya jiki ya baby kuma?”

“Lafiya lau”.

Ammi ta ce “To Alhamdilillah”

Mama ta ce “Jiki da sauƙi kam, domin yau har ta tattaka, gobe in Allah ya kaimu zamu je mu kaita hoton ƙafar da kai, da kuma haƙarƙari da take kuka da shi”.

Ammi ta ce “Allah sarki, karki damu, zan aiko s kaita”.

Mama ta ce “A’a kar ɗawainiyar ta yi yawa, zamu kaita in sha Allah”

Ammi ta ce “Ɗawainiya ta wuce tserato wa da ta yi da wannan jaririn, ai duk abun da muka yi mata bamu faɗi ba”.

Mama ta ce “Rumaisa kawo jaririn su ganshi mana”.

“Amma mama kar ki bashi ɗana”

Mama ta ce “Shi wa?”

“Wancan mutumin” tayi maganar ba tare da ta kalli Adam ba.

Guntun tsaki mama ta yi, ta karɓi jaririn, ta miƙawa Ammi shi, Ammi ta karɓe shi tana murmushi tana ƙare wa yaron kallo, kamannin adam ne sak yaron ya kwaso.

Ta dubi ruma ta ce “To maman baby, ba a saka masa suna ba haryanzu?”.

Ruma ta ce “Na saka masa suna, sunansa Mahmud!” A tare Ammi da Adam, suka ɗago suka kalli rumaisa, ita kuwa ta basar dan ba ta san me ta yi ba.

Ammi sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta dubi rumaisa ta ce “Ita aishan ce ta saka masa wannan sunan?”

Ruma ta ce “A’a, ni na saka masa, sunan babana ne, ina son sunan sosai”

“Ba shi ne sunan da na yi niyyar sakawa ɗana ba, ba zan saka wannan sunan ba” Takawa yayi maganar cike da iko, sai da mama ta ɗan ji babu daɗi, ko da zai canza sunan bai kamata ya faɗa a gaban ruma haka ba, ba za ta ji daɗi ba.

“Ka ga ba fa ɗanka bane ba, tun da ni ta ce ta barwa shi, ɗana ne Mahmud na saka masa, kuma ba zan canza ba” ta yi maganar tana yi masa kallon banza.

Ammi ta ce “Madalla, suna mai girma da karama, Ubangiji Allah ya raya Mahmud, ta zauna maman baby, mun karɓi sunan” kallon da Ammi ta yi wa takawa ne ya sanya shi haɗiye maganar da yayi niyyar yi.

Ammi ta dubi ruma ta ce “Rumaisa, Haryanzu baki gaya mana ya ki ka baro aisha ba? akwai buƙatar ki bawa Adam haɗin kai wurin amsa tambayoyin da zai yi miki, tun da shi ma jami’in tsaro ne. Yaya Aisha take? Ya aka yi ki ka fito da ke da jaririn babu ita?”

Rumaisa ta ɗan yi shiru tana wasa da gefen bedsheet ɗin da take kai, hawaye ya taru a idonta, sai dai babu tsammani ta yi ƙara tana kare fuskarta da hannunta, da sauri mama ta ƙarasa wurinta tana tambayarta ko lafiya?.

Jikin ruma sai rawa yake yi, ta rungume mama tana ɓoye fuskarta.

Mama ta ce “Rumaisa ki yi magana mana, menene?”

Ruma ta ɗago a hankali tana duba jikinta ta ce “Sha tara ne ya harbe wani mutum jininsa ya ɓata mini jiki”.

Jiki a sanyaye mama ta ce “A asibiti fa ki ke a tare da mu, duba ki gani, jikinki babu komai babu jini” mama tayi maganar tana nuna mata rigarta, sai dai duk da haka ruma sai haki take kamar ta yi gudu.

Ammi ta ce “Haryanzu akwai sauran razani a tare da ita, dole ta razana tun da ki ka ga haka, Allah kaɗai ya san abubuwan da ta gani. Bari mu tafi ta samu ta huta, sai dai duk da ban san zuwa yaushe za a salleme ku ba da yaron nan, zan roƙi alfarmar ku, ya ɗan zauna a wurinku kan a sallami rumaisa, muna ƙoƙarin shawo kan wata matsala ne, kan mu kai shi gida kowa ya sani” abun ya ɗan ɗaurewa mama kai, wace irin matsala kenan? Amma ba ta tambaya ba ta ce “A’a babu damuwa, Ubangiji Allah ya raya mana shi a bisa tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam”.

Ruma daga kwance ta ce “Ni fa ba wanda zan bawa ɗana, ɗana ne fa”.

Ammi ta ƙarasa gaban gadon ruma, ta shafi kanta ta ce “Dama naki ne, aro zaki bamu ai, Allah ya baki lafiya ya tsare gaba” ta yi maganar tana murmushi.

Ruma ta amsa da Amin, daga nan suka yi sallama suka tafi.

Suna tafe a hanya Ammi ta ce “Gaskiya akwai matsala, idan har yarinyar nan ba ta yi bayani ba, dole mu nemi yadda zamu yi”

Takawa ya ce “Ammi, ni fa na riga na gama shirin tarar kowane irin ƙalubale zan fuskanta, na san duk yadda muka kai ga ɓoye lamarin nan, nan kusa zai baiyyana, ko da a yanzu ma kalli a halin da nake ciki, kuma kar ki manta, da dogarai uku ki ka zo wurin nan, a gabansu aka faɗi komai, na san a kowane lokaci maganar nan zata watsu”.

Ammi ta ɗan yi jimm sannan ta ce “Lokacin da Abokin ka bashir ya yi mini waya, babu halin in fita nikaɗai, kuma ban san kiran me yayi mini ba, wannan dalilin ne ya sanya na tafi da su, kuma jiya na ja musu kunne a kan su yi shiru da bakinsu”.

Ya girgiza kai ya ce “Ammi, kin manta gidan nan ne, lokacin da aka fitar da zancen ina shaye-shaye na yi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, mutum nawa ne a wurn, wa zaki kama ki tuhuma ki ce shi ne? Haka wannan ɗin ma, dole zan matsa lamba yarinyar nan ta yi mini bayani, na san in da zan nemi mafita”

Ammi ta yi shiru, abubuwa sai sake cakuɗewa suke yi, ba a warware wannan ba wancan sai ya kunno kai.

“Ammi, meyasa ki ka amince da sakawa yaron nan Mahmud? Ni ba sunan da zan saka masa ba kenan, sunan Alhajinmu na so mayarwa, ni bana son sunan nan”

Ammai tayi murmushi mai ciwo ta ce “Haba babban mutum, ban ji daɗin jin wannan maganar daga bakinka ba, a bar wannan zancen dan Allah, ina roƙa mata alfarma, a bar mata wannan sunan tun da shi take so”.

Takawa ya ɗan duƙar da kai ya ce “Tuba nake”.

Bayan tafiyar su takawa kuwa Abdallah ne a ɗan hasale ya ce wa ruma “Dan ubanki ba a yi wa masu mulki magana yadda ki ke yi musu, gatse-gatse babu ɗa’a, wai ma ke kowa sa’anki ne da zaki din ga magana son ranki? Na fuskanci ba ki yi laushi ba haryanzu. To wallahi sai an basu ɗan su, ke gama rainonki aka yi da zaki janyo mana wani? Ki kuma cewa ɗanki ne ki ga yadda zan yi da ke” Jin Abdallah kawai take yi, amma gani take idan zasu mayar da ita ƙuli, babu wanda zai rabata da jaririn nan.

Washegari ‘yan Katsina su gwaggo da iya, da sassafe suka yi dirar mikiya a Kano, yayin da ‘yan uwa da abokan arziki, malaman islamiyya da makarantar bokonsu rumaisa, haka mutane daga lungu da saƙon unguwa, suka din ga zuwa dubiya gami da jajen abun da ya samu rumaisa, sai dai fa unguwarsu rumaisan ta ɗauka a kan jaririn da rumaisa ta dawo shi, nan da nan zantuka kala-kala suka hau zagaya cikin unguwa, masu daɗi da marasa daɗi a kan rumaisa.

Aliyu ya cika alƙawari, ya kawo Habiba har ɗakin da rumaisa take na jinya,ita da babarta, suka rungume juna suka din ga kukan farin ciki.

Gwaggo kuwa sai da ta yi kuka tana neman mama ta yafe mata da ta sanya a ka kai ruma aka ɓoye, ta ɗora alhakin faruwar komai a kan ta, har da su lawisa duk aka zo, rumaisa ta yi farincikin yadda mutane ke ta shiga suna fita duk saboda ita.

Sai dai duk rawar kan rumaisa taƙi sakin jiki ta basu labarin abun da ya faru a zamanta a hannun ‘yan ta’adda, ko zancen aka ɗauko sai ta haɗe rai ta hau kuka, gashi haryanzu lokaci zuwa lokaci tana razana, haka kurum tana zaune sai ta hau ihu, tana kiran sunayen ‘yan bindigar ta ce zasu yi mata wani abu, har sai da mai sunan Baba ya hana yi mata zancen gaba ɗaya.

Tun da aka rubutawa rumaisa hoto, mama ta aika Abubakar ya tambayo kuɗin hoton, aka ce masa dubu arba’in da uku, mama ta ɗan shiga damuwa, domin kuɗin da yawa, ba ta son yawan ɗorawa yaran ɗawainiya, dan ma kuɗin asibiti da na magani ba biya suke yi ba, an riga an ɗau nauyin lafiyar rumaisa a aljihun takawa, dan tun da bashir ya ji yaron nan na Adam ne, ya sanya aka canza musu asibiti zuwa babban asibitin kuɗi, domin samun kulawa ta musamman tun da ya san adam yana da kuɗin biya, ko magani likita ya rubutawa ruma, sai dai kawai a ɗauko a kawo musu, sai dai wanda babu su je waje su saya.

***

Tana zaune a kan katafaren gadonta, sai shirya mata kayanta mai aiki take a cikin akwati, dan ta ƙallafa ranta a kan tafiyarta Abuja nan, sai ba wa mai aikin umarni take cikin isa da kuma gadara gami da wulaƙanci.

Samha kenan akwai gayu da ƙwalisa, sai dai babu hali mai kyau, ɗaya daga cikin wayoyinta ta duba ba ta gani ba, ta js ɗan gajeren tsaki, ta fita ta tafi ɗakin mama.

Mama ta tarar tana ta ƙananan surutai tana mita. “Mama na bar Samsung ɗina a ɗakin nan ne?”.

“Ke ni rabu da ni da wata wayarki, turaki ya ɓata mini rai”.

Samha ta ce “Too ikon Allah, mai Baban kuma yayi miki?”

“Manta kawai, jirgin ƙarfe nawa zaki bi?”

Samha ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce “Ƙarfe biyar na yamma, amma ki din ga haƙuri mama, kin san tsufa yana taka muhimmiyar rawa a kansa yanzu, idan ki ka matsa zaki yi ta damuwa ne ranki yana ɓaci”.

Ɗan shiru mama tayi sannan ta ce “Abun nasa dai ba tsufa bane, ba wani tsufa kawai halinsa ne, ina yi masa maganar wani abun daban, amma yana nuna mini maganata ba ta da muhimmanci yana kawo mini nasa zancen da bai shafeni ba”.

Samha ta yi murmushi ta ɗau wayarta ta ce “Na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi, yakamata ace zuwa yanzu kin saba mama, ki yi haƙuri, bari na je na cigaba da shirina” daga haka ta fice ta koma ɗakinta.

***

Abubuwa suka cakuɗewa Adam gaba ɗaya, kallo ɗaya zaka yi masa ka san a cikin tashin hankali yake da matsananciyar damuwa, Ammi ta ce sam ba ta yarda ya je gidansa ya zauna shikaɗai ba, don tun da ya shiga damuwar nan take cikin fargaba, kar ciwonsa ya tashi abu ya ƙara haɗe musu.

Yau da safe Ammi da kanta ta je ta saka Adam a gaba a kan ya ci abinci amma ya kasa ci, sai da ya ga ta matsa sosai da sosai sannan ya ɗan cakali kaɗan ya bar shi.

Ammi ta dube shi a tsanake sannan ta ce “Takawa” ya ɗaga kai ya dubeta.

“Yanzu meye abun yi ne? Me ka yanke a kan lamarin nan, kuma ya ake ciki game da binciken?”

Ya ɗan yi jimm sannan ya ce “Dama Bashir ne incharge ɗin da case ɗin yake a hannunsa, sannan police ɗin da case ɗin yake hannunsu suna ta ƙoƙari, ina ga in anjima za su je asibitin da kansu, su yi mata tambayoyi”.

Ammi ta ɗan sauke numfashi sannan ta ce “Bana son a cigaba da yawan matsawa yarinyar ne a kan maganar, na ga haryanzu tana cikin razani, dole a bita a hankali”.

Adam a ransa ya ce “Babu wani razani, tsagwaron iskanci ne, kuma da ni take zancenta, ba zan lamunci iskancinta a kan rayuwar matata ba’

Amma a zahiri ya ce “Amma Ammi dole ta yi magana domin gaggauta ceto Aisha”.

“Eh haka ne, amma ita ma ‘ya ce, kuma yakamta a bita a sannu, saboda lafiyar ƙwaƙwalwarta, kana kallona gabanka jiya take ihu wai an harbe wani” Ammi ta dafe goshi ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu, dole yarinyar nan ta shiga ruɗu, ayi kisan kai a gaban yarinya ƙarama kamar wannan”

Shiru Adam yayi, yana ta addu’a Allah ya sa Aisha tana lafiya.

Ya kalli ammi ya miƙe tsaye ya ce “Ammi, bari na je asibitin nan da kaina”.

“A’a kar fa ka je ka nuna musu zafin zuciya da zafin kai, ka bi komai a hankali”.

Ya girgiza kai ya ce “Ba wani abun zan yi ba, kin san yau za’a kai ta x-ray, so nake na je na ga yaron, in kuma jarrabawa ko zata yi magana”.

“To shikenan, ka gaishe su, ni sai zuwa dare in Allah ya kaimu na je” ya jinjina wa ammi kai ya fice.

Likita ne a tsaye a kan rumaisa da take ta bacci, tun bayan da mama ta yi mata wanka, ta yi wa jaririn, ta kwantar da shi a kusa da rumaisa suke ta bacci, haka nan mama ma yaron ya shiga ranta, ga yaron da matuƙar haƙuri, idan yayi kuka ko dai ya gaji da kwanciya ko kuma yana jin yunwa, daga bacci sai cin hannu kawai yake yi, mama ba ta taɓa jin ta gaji da ɗawainiyar da take da ɗan da bata da alaƙa da shi ba, ji take yi hakkinta ne na uwa ta kula da shi, gefe guda kuma tana matsanancin jin tausayinsa tare da fatan Allah ya kuɓutar da mahaifiyar sa, ita kanta da ta ɗaukowa rumaisa zancen uwar yaron, sai ta hau zabure-zabure.

Likita yana duba file ɗin ruma yana kallonta, mama ta ce “Likita babu dai matsala ko?”.

Ya ce “Eh babu, duk wasu gwaje-gwaje da yakamata ayi mata mun yi mata, babu wani mummunan ciwo a tare da ita, sai dai zan rubuta wata allaura a sayo ayi mata, saboda ciwon haƙarƙarin da take kuka da shi, kan ku yo hoton”.

“Eh, in anjima za aje yin hoton in Allah ya yarda, dan sai daf da asuba ta samu bacci, da gari ya waye na tasheta, tana ta kuka da wurin”.

Ya ce “In sha Allah idan aka yi allurar, za ta samu releif, kan muga sakamakon”.

Mama ta ɗan nisa sannan ta ce “Amma likita ba su yi mata wani abu ba dai ko? Basu taɓa ta ba kun duba?”.

Ya jinjinawa mama kai ya ce “Ki kwantar da hankalinki, akwai report da police suka bamu, tun daga asibitin farko da aka kaita, da na biyu zuwa nan, muma da namu binciken, komai lafiya ƙalau”.

Mama so take ya bata amsa ƙarara, amma kamar bai fahimci me take nufi ba, ba ta son ya ga kamar ta matsa masa, dan haka ta ƙyale shi”.

Ganin yadda rumaisa ke kuka da ciwon haƙarƙarin nan ya sanya ta ce bari ta yi sauri ta je ta sayo allurar, gashi da wuri Abdallah ya tafi, yau yana da jarrabawa a makaranta, gwaggo kuma daga ita har iya suna fama da jikin girma, suma mama cewa tayi su tafi gida su huta, dan haka ganin ruman na barci ya sanya ya fito nursing station ta ce musu dan Allah ga rumaisa nan, za ta je sayo allura.

Mama na fita takawa ya iso asibitin, dan direba ya saka ya kawo shi, shi ba zai iya tuƙin ba.

Yana daf da shiga ɗakin da rumaisa take, likita ya fito daga ɗakin kusa da nata, suka tsaya suna gaisawa.

Takawa ya tambayi likitan ya jikin jaririnsa?.

Likita ya ce “Baby yana nan lafiya Alhamdilillah, shi ya samu sauƙi sosai Alhamdilillah, mamansa ce dai iya rigima haryanzu muna fama ba ta warware ba, muna jiran sakamakon hoton da zamu turata mu san abun yi na gaba”.

Adam ya ce “Haryanzu ta ƙi magana a kan in da mahaifiyar yaron nan take, da an yi maganar sai ta hau ihu, dan Allah hakan yana da nasaba da razani ko kuma iskanci ne kawai”

Sai da doctor yayi dariya ya ce “To kowanne ma zai iya kasancewa, amma razani kam tabbas tana cikinsa haryanzu, wasu lokutan tunanin ya kan ƙwace mata ta zaci tana hannunsu haryanzu, amma abi komai a hankali, sannan dan Allah idan ku ka tashi karɓar yaron nan, ku bita a hankali ta shaƙu da shi sosai, kar ku rabata da shi lokaci ɗaya”.

Bayanin likitan na yanzu ya shiga ta kunnen Adam na dama, ya fita na hangu, dan bai ji zai iya saurarawa ko ɗaga ƙafa wurin karɓar ɗansa ba, yanzu ma don yana cikin tashin hankali ne, da damuwa da son sanin in da matarsa take, ba dan haka ba, da tuni ya ɗauk ɗan sa.

“Thank you very much” ya faɗa a taƙaice ya shiga ɗakin rumaisa.

Sai dai yayi mamakin ganin babu kowa, baccinta take hankali a kwance, gefenta ga jaririn shi ma yana barci, kai ka ce uwarsa ce.

Ya ƙarasa gaban gadon ya tsaya ya ƙare mata kallo, a haka tana bacci looking so innocent, amma a zahiri halinta idan ba ka kai ziciyarka nesa ba, sai ta sa zuciyar mutum ta buga.

Ya kalli ƙafarta da aka rage bandejin da ake saka mata, saboda raunukan da suke ƙafar, ga wani yanka a ƙwaurinta, kai da gani ka san faɗuwa ta yi, ga tabo a gefen goshinta, kai ba sai an gaya maka iya wannan ya isa ya tabbatar wa mutum da ruma ta azabtu kan ta kuɓuta.

Hannunsa biyu ya saka a kan gadon, ya ƙurawa yaronsa ido da yake daga lungu, ya tuna irin yadda suka shirya rayuwa da shi da Aisha idan Allah ya sauketa lafiya, da irin budurin da suka shirya yi, da yadda take nanata masa sai dai su bawa mutane mamaki, ba wanda ya san da cikin sai dai su ce wa mutane ga babynsu, yau ga baby amma ita ba ta nan.

“Aisha why, meyasa a karon farko ki ka tsallake umarnina abun da baki taɓa yi ba, gashi kin sanya mu a wani hali” ya furta lokacin da hawayensa ya gangaro ya zuba a hannun rumaisa.

Juyi tayi zata gyara kwanciyarta, ya ga tana nema ta danne masa ɗa, dan haka cikin azama ya miƙa hannu zai ɗauke yaron. Caraf rumaisa ta riƙe hannunsa ta buɗe ido ta kalleshi.

“Wayyo Allah zai sace mini ɗa, mama kina ina” ta ware murya iya ƙarfinta tana ihu.

Ya nemi wuri ya zauna, ya ɗan tsurawa yaron ido, a hankali ya kai bakinsa kunnen yaron, yayi masa huɗuba da Mahmud kamar yadda ammi ta buƙata, ba kuma dan yayi niyyar sanya sunan ba.

Ya sauke yaron a hankali yana cigaba da kallonsa, ya ɗaga kai ya kalli rumaisa ya ce “A karo na babu adadi, ina sake tambayarki ina aisha take? Bana son ki kai ni bango, in yi miki abun da ba shikenan ba, ki bani amsar tambayoyin da nayi miki, matata na cikin hatsari dole na san in da take”

Kawar da kanta ta yi gefe, ta ƙi kallonsa.                                 

“Am talking to you” yayi maganar cikin tsawa ganin yadda take nema ta mayar da shi mahaukaci.

Sake kawar da kanta gefe ta yi, ta dafe kanta da hannayenta, tana ƙunƙuni.

“Da ke nake, ki bani amsa” ya sake maganar kamar zai kai mata duka.

“Wai dan Allah me kake so na ce maka, ni na san a in da take? Nima fa saceni a kai, ko garinmu ne da zan san ina ne, ka je da kanka mana ka duba, ni na san sunan wurin ne? Kuma wallahi kar sake yi mini tsawa bana so”

Ya yinƙura zai sake magana mama ta yi sallama. Ya haɗiye maganar ya waiwaya ya kalli in da mama take.

Cikin girmamawa suka gaisa, mama ta ce “Ashe ka zo, na je sayo mata magani ne a waje”

Adam ya ce “Eh na zo, ban jima ba, amma ku din ga kai takardar pharmacy zasu baku ba wani abu”.

Mama ta ce “A’a basu da shi ne, ai yakamata muma mu din ga taɓukawa, masu shagunan ne ma basu fito ba, saboda haƙarƙarin da take kuka da shi, ya sanya na fita dubawa”.

Adam ya karɓi takardar hannun mama, ya ɗau hotonta, ya kalli mama ya ce “In anjima Bashir zai zo, zai taho da maganin sannan ya kai ku wurin X-ray ɗin”.

Mama ta girgiza kai ta ce “A’a, mun gode ɗawainiyar ta yi yawa, hakan ma Allah ya saka da alkhairi yayi maka albarka, ka bari kawai wannan zamu yi ba zai gagara ba da yardar Allah”

“Nima ɗan ki ne, ba zan ji daɗi ba idan ki ka nuna ba kya son na yi muku abu”

Tsidik ruma ta sanya baki ta ce “A’a bama so, yaya Abubakar zai zo su kai ni, idan ma wayo kake yi mini na fika wayo in gaya maka” ta yi maganar tana harare-harare.

Da ido ɗaya yayi mata wani irin kallo, mama kuma ta yi mata daƙuwa ta ce “Ke bana ciki da rashin hankalinki, sa’anki ne ko wani ya saka baki da ke? Kin ma taɓa yi masa godiyar ɗawainiyar da yake da ke?”

Ruma ta yi shiru tana basarwa, kar mama ta cigaba da yi mata faɗa a gabansa ya rainata.

Huzaifa ne yayi sallama da kwandon kayan abinci, suka amsa masa bayansa kuma Gwaggo ce da lawisa.

Nan suka zauna suna gaggaisawa, Huzaifa ya ƙarasa ya karɓi Mahmud a hannun takawa ya riƙe hannun jaririn ya ce “Mai sunan babanmu, kana lafiya?” Yayi maganar kamar jaririn zai amsa masa.

Takawa kuwa bin su yake da ido, lawisa ma ta bi Huzaifa tana cewa ya bata ta ɗauke shi.

Adam ya tashi yayi musu sallama ya fice, tabbas ranar da zai karɓi jaririn nan akwai daru, mussaman a wurin uwar riƙonsa rumaisa, yarinyar da ta riga ta fara shi kai bango saboda halinta.

***

“Ammi kin yi shiru baki ce mana komai ba”

Ammi ta ce “To Nusaiba me zan ce muku?”

Iman ta ce “Ammi kina ɓoye mana abun da yake faruwa, amma gaba ɗaya yanayinki da na takawa a ‘yan kwanakin nan ya tabattar da akwai wani abu a ɓoye, bama jin daɗin yanayin nan sam”.

Nusaiba ta ce “Ni fa ina daf da sanarwa Anty laila, wataƙila ki gaya mata meke damunku ku ka ƙi gaya mana”

Ammi ta numfasa ta ce “Kar ki kuskura ki haɗa ni da laila, koma menene dole zaku ji, amma ba yanzu ba”

“Yanzu Ammi haka zamu cigaba da kallonku a haka, ba fa haka muka saba rayuwa a tsakaninku ba, taya zamu yi adopting hakan lokaci guda, ammi walwalarki ce fa tamu” Nusaiba tayi maganar kamar za ta yi kuka.

Iman kuwa tuni idonta ya tara hawaye ta ce ‘Ammi ko dai nice, idan saboda ni ne, ki kai ni Gombe can family house ɗin ku, zan zauna, kuma duk wanda ki ka zaɓa mini zan aure shi, amma dan Allah ki cigaba da walwala muna ganin murmushin ki”

Tausayin Iman ya kama Ammi, ya kamo hannun iman ta ce “Haba iman ɗina, ki na tunanin akwai wani ƙalubale da zai ta so na rabu da ke ne? Kar ki kuma wannan maganar, wani abu ne yake faruwa daban, amma komai zai daidaita in sha Allah”.

“Ammi wai muma ‘ya’yanki baki yadda da mu ba, muma munafukai ne kenan yaya takawa ne kawai mai iya riƙe sirrinki?” Nusaiba ta yi maganar har cikin zuciyarta.

Duk da halin da Ammi ke ciki, sai da Nusaiba ta bata dariya, ta girgiza kai ta ce “Ba abun da ku ke tunani bane ba Nusaiba, wata yarinya aka tsinto a katsina da jariri” sai kuma ta yi shiru.

“Ammi to meye haɗin hakan da damuwar da kuke ciki?”

Ammi ta ce “Ɗan takawa ne”

Nusaiba cikin rashin fahimta ta ce “Wane takawan? Ta ina za a tsinto yaro a katsina kuma ya zama ɗan sa?”

“Ɗan sa ne” Ammi ta basu amsa.

Iman ta ce ‘Amma Ammi, ta yaya?”

“Ɗan Aisha ne, ta kawo ɗan kwalinta da gwala-gwalanta”

Nusaiba ta ɗan dafe goshi a rikice ta ce “Ammi kin hargitsani ban gane ba, ta yaya Anty Aisha da take Saudiyya za’a tsinto ɗan ta da ɗan kwalinta a Nigeria kuma a katsina, anya ba ƙarya yarinyar take yi ba, ko wani abun ake shiryawa ba”

Hawaye ya cika idon ammi, ta ɗauki wayarta, ta buɗe ta nemo hoton jaririn ta miƙa musu.

Cikin tsananin mamaki suke kallon hoton, babu in da yaron ya bar Adam saboda kamanni.

Iman ta ce “Ammi, ni fa haryanzu ban gane ba, a ssudiyyan ta haihu ko kuma yaushe ta dawo Nigeria har aka tsinci jaririnta, ita tana ina?”

Nan Ammi ta warware musu komai, kamar yadda takawa yayi mata bayani.

Nusaiba ta dafe kai ta fashe da kuka ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Ammi yanzu mai za’a cewa mai girma turaki, tayaya za’a warware wannan lamari? Anty Aisha a hannun ‘yan bindiga tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani? Kuma Ammi ki ke ɓoyewa, idan zancen ya ɓullo ta wani wurin daban fa, kar ki manta ba’a san da cikin nan ba, kuma cewa aka yi zata ƙaro karatu, aka yi ta surutu a kai, tayaya za a dawo ace ba ƙaro karatu ta tafi ba, har ta je ta dawo an saceta ya haihu sai ɗa da ɗankwalinta da gwala-gwalanta, ana ma da tabbacin tana raye?”

Gaban Ammi ne ya sake faɗuwa, jin abubuwan da Nusaiba ta faɗa, take hawaye ya fara gangarowa daga cikin idon Ammi.

Iman ta ce “Anty Nusaiba, komai da muhallinsa, kan ƙalubalen ya zo, za a nema masa mafita, wannan maganganun naki zasu sake jefa ammi cikin damuwa”

Iman ta dubi Ammi a tsanake, ta fara goge mata hawayen fuskarta ta ce “Ammina, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, duk wani surutu da ƙazafi da zs ayi mana, ba zai kai wanda aka yi mana a baya ba, na san da tashin hankali, amma ammi ba zaki taɓa yanke hukuncin da zai cutar da wani ba balle mu. Ki na ji ammi ƙaddarar haihuwar yaron nan ce ya sanya anty aisha dawowa ƙasar nan, kuma suka ɓoye miki, duk da yadda suke biyayya ga umarninki, kar ki ɓata ranki ammi,  kin san addu’a da ki ke yi mana ce ta zama katanga daga dukkanin sharri. In sha Allah mai girma turaki zai fuskance ki. An tambayi yarinyar ina Anty Aisha take?”.

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Haryanzu fama ake ba ta yi magana ba tukuna”.

“To shikenan, in sha Allah za ta yi magana, Sai a bi komai a hankali Allah ya sa tana lafiya, shi kuma jaririn Allah ya raya shi” iman ta sake ɗaukar wayar Ammi, tana kallon hoton jaririn.

Nusaiba ta ce “Ba wai tayar muku da hankali zan yi ba, amma kar ku manta masarautar nan ba a iya samun bala’i ba, idan aka sako mutum a gaba da baki da surutu sai zaman garin nan ya nemi ya gagare shi”.

Iman ta ce “Haka ne, amma in sha Allah babu abun da ya gagari Allah, Addu’a zamu duƙufa babu dare babu rana. Amma Ammi yaushe zamu je asibitin mu ga yaron muma?”.

Ammi ta ce “Ba yanzu ba, ku ɗan bani lokaci, bana son mutanen gidan nan su fuskanci wani abu tukuna”

Haka suka cigaba da tattaunawa, sai dai Nusaiba ta kasa magana domin kuwa ta riga ta gama karaya.

****

Ƙaton katafaren office ne, mai ɗauke da duk wani kayan alatu na jin daɗi da more rayuwa, Senator Usman wakili na zauna a ɗaya daga jerin kujerun office ɗin, sai kuma baƙonsa da yake zaune a kan kujerar da take fuskantar sa.

“Kana ɗaya daga cikin makusantan wancan yaron, da ya dage kai da fata sai ya ga bayana, sai dai kuma kwana biyu na ji shi shiru, duk na gama duk wani shiri da zan yi maganinsa, ko kuma akwai wani abu da yake ƙullawa da ban kai ga sani ba, kar yayi mini bazata”.

“Ranka ya daɗe shi ɗain banza ja da ikon masu ƙasa? Ku ne fa ƙasar nan yadda ku ka dama haka ake sha, shi da duk masu goya masa bayan gayyar rashin sanin ciwon kai ce, dan tabbas manyan ƙasar nan akwai masu goya masa baya, wanda nake kyautata zaton ‘yan adawarka ne”.

Wakili yayi murmushi ya ce “Ba abokan adawata bane ba, domin abokan adawata muna aiki tare ne, mabiya kawai muke rainawa hankali”.

“Haka ne Yallaɓai, amma a yanzu haka dai, bana tunanin wani shiri yake yi, dan a ‘yan kwanakin nan akwai abun da ya ɗauke masa hankali, ko office bai fiye zuwa ba, ya ce bashi da lafiya, amma babu tabbas a maganar ta sa”

Wakili yayi murmushi ya ce “Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shikenan ka cigaba da sanya mini ido a kan sa, da kawo mini rahoton duk abun da yake ciki, sannan zamu cigaba da shirye-shiryen tsayar da khalifa takarar gwamna, shi ma ba zamu baro ya ɓata masa suna ba”.

“Amma ranka ya daɗe, na ji wancan satin majalisa ta naɗa kwamiti, domin bincikar gaskiyar abun da hukumar dss suke zarginka da shi, ya za’ayi da wannan”

Wata iri dariya wakili yayi ya ce “Duk saɓatta juyatta ne na siyasa, domin juya tunanin talaka baibai, ka san shi talakan Nigeria idan har zai ci ya ƙoshi, duk abun da zaka ɗora shi a kai zai bi a haka, babbar damuwar ɗan Nigeria ya ci ya ƙoshi ne, daga haka ba shi da wata damuwa da yadda abubuwa suke wakana, suma Dss ɗin muna nan zamu yi abun da ya dace a kan su”

Mutumin ya jinjina kai ya ce “Yanzu ranka ya daɗe wannan kwamitin da aka naɗa na binciken shi ma plan ne?”

Kamar mara imani haka wakili ya sake ƙyaƙyacewa da dariya ya ce “Ka je ka cigaba da yi mini aiki, nima zan yi amfani ƙarfin kujerata da faɗi a ji na ƙasar nan, na cika maka naka burin”.

Risunawa mutumin ya yi yana jinjinawa wakili yana faɗin “Allah ya ida nufi, wakili na kowa”

Yayi maganar yana kamabama wakili, yayin da shi kuma yake ta ɓaɓɓaka dariya.

***

Kamar yadda Adam ya faɗa, da azahar bashir ya zo, zai kai rumaisa wurin X-ray, amma mai sunan baba ya ce bai yarda ba, su zasu kaita kar son banzan na su yayi yawa.

Bashir cikin mutuntawa ya ce “Haba Yallaɓai, rumaisa fa ta zama ƙanwarmu mu ma, ko ma in ce maka ‘yar mu, duk abun da muka yi mata bamu faɗi ba, ka duba girman aikin alkhairin da ta yi mana, ai tafi ƙarfin abun da muke yi mata a wurin mu, dan Allah kar ka damu, wallahi ba son banza bane, idan dai har kuɗi ne, akwaisu adam ba shi da matsalar su, ku kwantar da hankalinku, dan Allah ka bari a kaita”.

Mai sunan baba ya ce “Wanda ku ke yi mana, da wanda ku ka riga ku ka yi mana ma mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, amma muma a matsayin mu na ahalinta yakamata mu tagaza”.

Bashir ya ɗan langaɓe kai ya ce “Zaku ja mini magana a wurin uban gidana, ga kuma uwa uba Ammi, ba za ta taɓa jin daɗi ba, sun ɗora ni a kan kula da komai, dan Allah ku yi haƙuri wallahi baku da wata damuwa a kan hakan, ɗaukar ɗawainiyarta ba yana nufin gazawarku bane ba, yana nufin nuna godiyarmu da jin daɗinmu ne a gareku, da yaba karamcinku, duk da mun san ba biyanku zamu yi ba”.

Abubakar ne ya ce “Shikenan ɗan uwa babu damuwa, Allah ya saka da alkhairi”.

Bashir ya ce “Yauwa ɗan uwa Amin, ku gama kintsawa sai a fito da ita ga mota can a waje” yana gama maganar ya fita.

Mai suanan baba ya ce “Malam wannan wane irin abu ne, shikenan sai mu zuba musu ido suna ɗawainiya da mu, bana son nan gaba su yi amfani da wannan damar, su ce zasu juyamu ka san ba zai yiwu ba”.

Abubakar ya ce “Haba dai, in sha Allah babu abun da zasu yi”.

Sai da rumaisa ta tabattar da mama ta goya Mahmud, wanda take wa laƙabi da Sabir, ta ce saboda haƙurin yaron take kiransa da sabir, tun da suka baro daji bai fiye kuka ba, ba kamar ɗan wata malamarsu ba jarababbe mai kukan masifa.

Suka ɗunguma suka tafi kai rumaisa x-ray, mama na ta fatan Ubangiji Allah ya sa lafiya babu wata matsala.

***

Adam ya idar da salla yana zaune a kan sallaya, yayi shiru ya rasa abun da yake yi masa daɗi, babu tsammani ya ji an turo ƙofar bedroom ɗin sa.

Jabir ya gani, ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

Ya amsa masa a ciki, yau ya manta bai yi wa masu gadi warning na kar su bar kowa ya shigo ba, koma yayi musu ya san basu isa su hana Jabir shigowa wurinsa ba.

“Adam, wai ina ka shiga ne a kwanakin nan, na zo gidan nan ba adadi, bana samunka idan na je can gida ma baka nan, ina ka shiga haka?”.

“Ina nan” ya faɗa a taƙaice.

“A’a, ɗan tsaya meyake faruwa ne, ka wani rame, ga fuskarka duk ta kumbura har idonka, menene?”

Tashi Adam yayi ya ninke sallayar, ba tare da ya kula Jabir ba.

“Adam magana fa nake yi maka, ka wani shareni, ni ne fa nake yi maka magana, meya sameka haka?”

“Idan ka tashi tafiya, ka sanarwa masu gadi, kar wanda ya sake zuwa wurina” yayi maganar yana ƙoƙarin hawa gadonsa ya kwanta.

Ture shi jabir yayi ya tsaya a gabansa ya kalleshi ya ce “Kalleni, da Jabir kake magana, har akwai wani abu da kake ɓoye mini a rayuwa? Muna ɓoyewa juna wani abu ne?”.

Adam ya dafe kansa ya zauna, yana ajiyar zuciya, ya dubi Jabir ya ce “J, gaya maka matsalata ba shi ne maganinta ba, ka yi mini addu’a kawai”.

“Mu kan tattauna abubuwan da suke damunmu a tsakanin mu, ko da bamu da mafita, sai dai hakan yana ƙara mana yarda da juna da jin matsalar ɗayanmu ta dukkaninmu ne, dan haka babu buƙatar ɓoye mini komai”.

Adam ya kama hannun Jabir, suka zauna a tare, ya kalli Jabir ya ce “Haƙiƙa ka tuna mini abun da na kusa mantawa, tabbas damuwar ɗayanmu, ta dukkaninmu ce, duk da ina ta ɓoye abun, ban bari kowa ya sani ba, amma a kowane lokaci na san dole komai zai fito, amma a yanzu ku ɗaga mini ƙafa please “.

Jabir ya jinjina kai ya ce “Shikenan” ya fice ya bar Adam, da ganin s yadda ya fita Adam ya san bai ji daɗin abun da yayi masa ba, sai dai shima dole ce babu yadda ya iya.

Sai daf da magariba sannan Bashir suka dawo da rumaisa daga wurin X-ray, yanzu tana iya taka ƙafafuwan ta sannu a hankali.

Sai bayan sallar magariba, sannan Bashir ya yi musu sallama, mama ta yi ta masa godiya da sanya albarka.

Daga nan asibitin bai wuce ko ina ba, sai gidan Adam, ya tarar da shi ya dawo daga masallaci sannan, lokacin an yi sallar isha’i.

Bayan sun gaisa Bashi ya ce “Yauwwa, mun je an yi mata hoton, likita zai ganta gobe in Allah ya kaimu, sannan ya duba idan da yiwuwar a sallameta”

Adam ya ɗago ya kalleshi ya ce “Babu in da za a sallameta sai ta faɗi in da matata take, ko na sanya a tsareta”

Bashir ya girgiza kai ya ce “No, Adams, a hankali zamu bi ta, duk da muna cigaba da ɓata lokaci, kuma can katsinan ma, babu wani cikakken bayani, dan haka na yanke shawarar zamu je da police, kai tun da ban san meye a tsakaninku ba, kamar wasu maƙiyan juna kai da ita, za mu je da masu uniform, wataƙila su ta yi musu bayani, yadda ake ciki sai mu san abun yi”.

“Zuwa yaushe kenan?”

‘Zan yi magana da Hassan, sai muje ko zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe ne”.

“Wannan shi ne chance na ƙarshe, idan har ba ta yi magana ba, zan saka ta yi ta ƙarfin tsiya!”.

Bashir ya ce “A’a, ba sai an kai ga amfani da ƙarfin tsiya ba, zata yi magana a hankali, ƙuriciya ke damunta, amma duk da haka kamar akwai wata ‘yar tsama tsakaninka da ita, yanayin abubuwan da take yi maka, kamar da gayyya take yi maka”.

Adam ya ɗan yi guntun tsaki ya ce “Manta da ita kawai, sai gobe in Allah ya kaimu, X-ray ɗin na ta babu wata matsala?”

Bashir ya ce “Ai na gaya maka sai gobe in Allah ya kaimu likitan zai duba”.

“Allah ya kaimu”

Bashir ya amsa da “Amin”.

**

Nusaiba tun da ta ji abun da yake faruwa, ta rasa nutsuwarta, ko abincin kirki ba ta iya ci. Yanzu haka tana tsaka da tunanin da ta saba ta ji Iman ta dafata “Anty Nusaiba” Nusaiba ta ɗan zabura sannan ta sauke numfashi ba tare da ta ce komai ba.

“Anty Nusaiba tunanin me ki ke yi haka ne?”

“Bari kawai Iman, tun da Ammi ta gaya mana zancen nan, na kasa nutsuwa ina tausaya mana idan zancen nan ya fita, kin san yadda aka samu a gaba da ma a masarautar nan, ƙiris ake jira wani abu ya faru, to ga wannan babbar magana gaba ɗaya na kasa nutsuwa, idan har ba Anty Aisha aka gano ba, wallahi muna cikin tashin hankali”.

“Haka ne, amma babu abun da ya gagari addu’a anty nusaiba, kuma babu ta yadda muka isa mu kaucewa ƙaddara, in sha Allah babu abun da zai faru”.

“Iman, na san kina dakewa ne kina ƙoƙarin kwantar mini da hankali, amma kar ki manta abun da aka gaya wa mutane a kan barinta ƙasar nan, kin san yadda aka sako yaya Adam a gaba, yanzu idan maganar nan ta fasu, babu irin sharrin da ba za ayi masa ba ba shi ba har Ammi da mu baki ɗaya. Shiyasa ni tun farko ban so hukuncin da ammi ta yanke ba, tun da komai muƙaddari ne” ta ƙarasa maganar tana kuka.

Iman ta rungumeta ita ma tana zubar da hawaye ta ce “Na sani Anty Nusaiba, amma Ammi uwa ce, duk abun da zata yi, tana yi ne dan bamu kariya da wanzuwar farincikinmu, kuma in sha Allah ƙoƙarin ta ba zai tafi a banza ba, komai zai zo ƙarshe da yardar Allah, ki daina damuwa, komai zsi zo da sauƙi, ai babu abun da ya gagari Allah” suka cigaba da kuka iman na rarrashin Nusaiba.

Baba uwani ce ta shigo tana sallama, tare da zuro kai. Da sauri suka gyara iman ta amsa mata.

Ta dubi iman ta ce “Uwar ɗakina lafiya kuwa?”.

Iman ta ƙaƙalo murmushi ta ce “Lafiya lau baba uwani, akwai wani abu ne?”

“Ni fa na kasa gane muku gaba ɗaya, giwa ta daina walwala, mai gida ma haka, kuma gashi na tarar kuna kuka, dan Allah me kuke ɓoyewa ne meyake faruwa haka? Gaba daya gidan babu daɗi, babu wata walwala saboda yanayin nan da ku ke ciki” Ta yi maganar tana neman fashewa da kuka.

Nusaiba ta ce “Baba Uwani babu wani abu kar ki damu”.

Cikin damuwa iman ta ce ‘Dan Allah kar ki yi kuka baba uwani, komai zai daidaita ba wani abun bane ba, Ammi jikinta ne ya ɗan tashi shiyasa bata walwala, kuma kin san walwalarta ce ta mu, kar ki yi kuka Please” baba Uwani ta matse ƙwalla ta ce “To shikenan, Allah ya bata lafiya, ya sanya komai lafiya, ya jishe mu alkhairi” tana gama maganar ta juya ta fice.

Iman ta ce “Allah sarki baba uwani, tana sonmu da yawa, bana son in ga masu shiga damuwar nan suna ƙara yawa, Allah ya bamu mafita, ina shirin gaya miki wani abu, wannan maganar ta kunno kai”.

Nusaiba ta dubeta ta ce “Wane abun?”

“Ki bari wannan matter ta yi settling, zan gaya miki”.

“No, kin san ba zan jure ba, ba zan iya jira ba, ki gaya mini yanzu kawai”.

Iman ta ja numfashi ta ce “Kin san me uncle J ya ce mini?”

Nusaiba ta girgiza kai ta ce “Sai kin faɗa”.

“Wai so na yake yi, kuma ko ban amince ba zai bi ta in da ya san za a bashi ni”

Nusaiba ta yi murmushi ta ce “Ni na san a rina ai, take-takensa duk ya gama nunawa, amma ke mai ya sa na ga kamar ba kya son shi ne? Mai uncle J ɗin ya yi?”

Iman ta ɗan murza zoben hannunta ta yi shiru.

“Do you still loves him?” Nusaiba ta yi maganar tana kallon fuskar Iman.

Iman ta ɗan waro ido ta ce “Who?”.

“Your recent ex, ɗan……”

“Shhhhh” iman ta katseta.

“Kar mu kai ga nan Please, mu bar maganar ma kawai”

Baba uwani kuwa da ke laɓe a ƙofar ɗakin, jin sun sauya hira ya sanya ta tafi tana tsaki “Aikin banza jarababbu, sun ƙi yin maganar gaba ɗaya, zancen da suka yi kuma, idan na kai mata ba so take yi ba, aikin kawai”.

***

Adam yana kwance ya ƙura wa roofing ido, sai ya tuna Jabir, abun da yayi masa ɗazu ya tuna, sai ya ji bai kyauta ba, jabir a komai yana tsaye a kan lamuransa, bai kamata ya yi masa haka ba, kuma jabir mutum ne mai kaifin tunani da hangen nesa, sanin ko ya so ko bai so ba zancen zai fit6, ya yanke shawarar ya yi wa jabir zancen, mussaman da suna tare Ruma ta yi masa abun da ta yi masa da farko, tare da saka ran Jabir zai iya samo masa mafita.

Da sauri ya tashi ya fita, ya ɗau mota ya tafi gidan Galadima mai ci.

Sai dai tun a hanya yake kiran wayar Jabir ya ƙi ɗagawa, ya je gida ya tarar Jabir baya nan, sarai ya san in da zai same shi, dan haka bai tsaya ko ina ba sai can.

Ko da Jabir ya ga Adam, ƙoƙarin share Adam ɗin ya yi amma ya kasa.

“Wurinka na zo” Adam yayi maganar yana duban idon Jabir.

“Ina jin ka” jabir yayi maganar yana basarwa.

Adam ya sanya hannu ya ɗago Jabir da kwalar rigarsa, ya ja shi suka fita waje.

“Wai meye haka ka ke yi?”.

Adam ya tsuke fuska ya ce “Yaya na zo wurinka in ce wurinka na zo, ka shareni ba ka fini mulki da jin kai ba, na san ka sani”.

Jabir ya kalli Adam ya ce “Har ka manta few hours ago abun da ka yi mini?”.

“Forget about it, just feel like to share it you”

“Ka riƙe sirrinka, tun da bai kamata na sani ba”.

Adam ya dafa kafaɗar Jabir ya ce “Kar ka yi mini yawa mana, yakamata ka saurareni”.

“Ina jin ka”

Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya gaya wa Jabir abun da yake faruwa.

Sak jabir yayi, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, wani irin gumi ya shiga tsatsfo masa ya ce “Takawa, wannan fa ba ƙaramar magana ba ce, case ne mai girman gaske, ni gaba ɗaya sarƙaƙiyar nan ta yi yawa, na kasa ganewa gaba ɗaya, an ce Aisha zata tafi ƙaro karatu, kuma tana Saudiyya rainon ciki, ta dawo ba wanda ya sani an yi garkuwa da ita, ta haihu jariri ya kuɓuta ita ba a san in da take ba, wannan zancen kamar film ko almara ni ban gane ba”.

Cikin matsananciyar damuwa Adam ya ce “Bar shi a baka gane ɗin ba, ka san wacece ta zo da yaron?”

Jabir ya girgiza kai, Adam ya ce “Wannan yarinyar da ta zageni a social media, da na yi niyyar hukuntawa ka hanani”.

Jabir ya waro ido kamar su faɗo ya ce “Again? Ita a ina ta samu jaririn naka?”

“Wai kai Jabir anya ka ci waec kuwa? Duk bayanin da nake baka ganewa, amma ni babban mamakina bai wuce yadda yarinyar nan take manne da ƙaddarata ba, ita ma an yi garkuwa da ita watannin baya, Bashir ne ya tsinceta a Katsina, a hanyar kai kuɗin fansar aisha, ta zo da ɗankwalin aisha wanda ya ƙara tabattar mini ba ƙarya take yi ba, sai dai duk yadda muka kaɗa muka raya taƙi faɗar komai a kak aisha, kamar tana amfani da hakan ta rama abun da na yi mata ne”.

Zamewa jabir yayi ya tsuguna yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Adam kuma yana tsaye yana murza yatsunsa ya na jin yadda hawaye ke cika masa ido.

Sai da Jabir ya gama salallaminsa, sannan ya tashi tsaye, ya dubi Adam ya ce “Yanzu ba lokacin tattauna wata magana ba ce, babu isasshen lokaci, dole a nemo in da aisha take kan kowa ya ji wannan zancen, gashi ka ce sun daina kiranka a kan kuɗin fansarta”.

Adam ya jinjina masa kai alamar eh.

“Ka ga, maza mu je mota, muje Asibitin”.

Haka Adam ya ɗauki Jabir suka tafi wurin rumaisa.

A can unguwa kuwa, mama na nan suna ta fama da jinyar rumaisa, amma maganar jaririn nan ta cika gari, kasancewar mama babu wanda suka yi wa bayanin in da rumaisa ta samo jariri, ko a ‘yan uwa ba kowane ya sani ba.

Wasu suka din ga cewa ciki rumaisa ta yi, shi ne aka kaita wani wurin ta haihu, dama wannan shegiyar fitinarta ta da rawar kai ta yi yawa, tsaf zata aikata, ba su yi la’akari da irin raunukan da suke jikinta ba, wasu ma cewa suke yi, ba wani saceta da aka yi, rainon ciki ta yi. Ya yin da wani sashen suke cewa gaba ɗaya rumaisa ba ta yi kama da wadda ta ɗau ciki ta haihu ba, dan a yadda take ɗin nan, idan ma cikin ne, abu ne mai wahalar gaske ace ta iya haihuwa da kanta, haka unguwa ta ɗauka, wasu suna sukarta, wasu suna bata kariya, sai dai su mama sam basu sani ba, dan ko a gari babu wanda ya iya tarar zaratan samarin nan ya yi musu zancen.

Yanzu ma mama na ta shirin su kwanta, ruma ta sha magungunan ta, tana ta shafa dogon gashin jaririnta, tana kallon dogon hancinsa.

“Meyasa ka yi kama da babanka, dama babarka ka yi kama, da ka fi haka kyau boy na” ta yi maganar tana kissing ɗin sa a goshinsa, tana murmushi da jin soyayyar Sabir na shiga zuciyarta.

Yaya Abubakar ya dubeta ya ce “Mama boy, zan tafi gida, gobe in Allah ya kaimu zan biyo mu yi sallama, zan koma school zamu fara exams”.

Ruma ta ɓata fuska ta ce “Dan Allah kar ka tafi, bana son ka tafi”.

“Ki hi haƙuri, exams ɗin nan ce zata saka na koma, ba dan haka ba a kusa da ke zan kasance in ta kallonki gudan jinina”

Ta yi murmushi ta ce “Allah ya bayar da sa’a”

Mama ta ce “Ka zo ka tafi kar ka yi dare”

“To mama, ban gaji da ganinku bane” kan mama ta yi magana Adam suka shigo.

Ruma ta kawar da kai tana faɗin “Innalillahi wa Innalillahi raji’un” domin ta gaji da ganin takawa, da kullum sai ya zo sau biyu, kuma duk zuwa sai ya ɗaga mata hankali a kan ta gaya masa in da Aisha take.

Ba ta ƙara haɗe rai ba sai da ta ga Jabir, sarai ta gane shi, da shi aka haɗa baki Adam ya ɗaukota yayi mata wulaƙanci.

Cikin girmamawa suka gaisa da ammi, yayin da jabir ya ƙurawa rumaisa ido, da ta haɗe rai.

Suka gaisa da Abubakar ma, da yake tsaye yana shirin tafiya.

Mama ta ce “Ana ta ɗawainiya da rumaisa fa, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ya shiga lamarin ka ya kareka da ga sharrin maƙiya”.

Adam ya ce “Bakomai mama, yi wa kai ne, ki daina godiya ma, addu’a muka fi buƙata”

Rumaisa a ranta ta ce “Ji shi, wai mama sai ka ce babarsu, dan tsabar kuturun iyayi, wallahi mamanmu ce kawai” ta yi maganar a zuciyarta.

Abubakar ya ce “Ruma baki iya gaisuwa bane?”

Ta ɗago ta ce ‘Au wai baƙi mama ta yi, sannunku”

“Ya jiki kuwa?” Jabir yayi maganar yana kallon ruma.

“Da sauƙi”.

“Ai da yake ban san meyafaru ba, sai yau, shiyasa bamu zo da shi na dubaki ba, mu ga jaririn”

Maimakon ta miƙo shi, sai saka hannu ta dafe shi, tana harare-harare.

Abubakar ya matsa ya ɗauko masa jaririn, ya bashi sannan ya fara yi wa ruma mita “Wai ke wace irin yarinya ce ne? Ke shikenan ba wanda zai taɓa yaron nan sai ke, ke da kece uwassa ban san yadda za’ayi ba”.

“To ai nice mamansa, ai dai bar mini shi ta yi”.

Ya ce “Ke tafi can, ke ma ɗin ai Haryanzu rainonki ake yi, mama bari na wuce na je gida na haɗa kayana”

“Yaya Sadik, sai da safe ka gaishe da su”

“Ba yanzu duk suka tafi ba, duk kuna tare sai da safe, ban da yi wa mama rigima dan Allah, a bari sai mun zo mu ayi mana” murmushi ta yi Abubakar ya kama hanya ya fita.

Jabir ya zubawa yaron ido, Adam da ke zaune a gefensa ma, ya zuba masa ido yana saƙa abubuwa daban daban a ransa.

Mama ta juya tana amsa waya, ruma ta lallaɓa a hankali ta sauko daga kan gadonta, ta saka hannu ta ɗauke jaririn daga hannun jabir, a gabansa ta ce “A’uzubi kalaimatillahi tammat” ta ƙarasa gadonta ta kwantar da jaririnta, ta hau gadon tana ta haɗe fuska.

Adam ya ɗan kalli jabir, kallon irin ka gani ko?.

Jabir ya girgiza kai ya ce “Rumaisa, na ji duk abun da ya faru, ina fatan Allah ya tsare gaba, amma yakamata ki bayar da haɗin kai wurin kuɓutar da maman yaron nan in dai kina ƙaunar ɗan ta da gaske, da haka zaki tabattar mana son gaskiya ki ke wa ɗan ta”.

A wulaƙance rumaisa ta kalli Jabir ta ce “An gaya maka ina abu dan na burge mutane ne? To kar Allah ya sa ku yadda ɗin mana ina ruwana, wataƙila shi sai in gaya masa kai ban gaya maka ba, mugwaye kawai, kuma ni ba dan ta bar mini jaririn nan ba, ba abun da zan yi da ɗan ku, dan ni bana ko ɗaukar yara, idan aka bani riƙon ɗa ma, mintsini yake sha da cizo, wannan kuwa ɗana ne, ba wanda ya isa ya ƙwace mini shi ehe” ta yi maganar tana fari da murguɗa baki”.

Jabir ya ce “Kan uba, haka ki ke?”

“Ai na fi haka ma, idan kun gama zaman kwa tafi, ko ku cigaba da zaman jirana in gaya muku in da take,  tun da ni na saceta” tana gama maganar ta juya ta kwanta.

Jabir ya riƙe haɓa yana jinjina kai, Adam kuwa tuni ya fusata ya tashi fuuuu ya bar ɗakin, a waje ya tarar da mama yayi mata sallama suka wuce.

A mota Jabir yake cewa Adam “Ban taɓa zaton azabar taurin kan yarinyar nan ya kai haka ba, ji yarinya ƙarama da iya shege”.

“Shawarar da bashir ya bayar, ita ce last option ɗina, idan taƙi ba da haɗin kai, zan yi abun da ba ta zato” a haka suka tafi gida suna tattaunawa.

Washegari da safe Ammi ta shirya, zata asibiti Nusaiba da Iman sun so bin ta, amma ta ce a’a su yi haƙuri ba yanzu ba, ta saka aka sheƙa girki, ta saka a mota, tana shirin shiga motar su tafi, ta ji yo muryar Mummy “Giwa, waye Babu lafiya ne na ganki da kulolin abinci da safiyar nan? Ko wani ne a cikin yaran amma ki ke ɓoye mini?”

Ammi mamaki ne ma yakamata, ya aka yi ta fito da sassafe haka, har ta ganta.

‘Ba ɗaya yara duk suna lafiya, wani abu ne mai muhimmanci” daga haka Ammi ta shige motar, ba tare da sake tanka Mummy ba.

Mummy ta riƙe ƙugu ta jinjina kai ta ce “Lallai ta tabbata akwai abun da ki ke ɓoyewa giwa, kuma da alama yana da muhimmanci a wurinki, bari mu ga idan na bankaɗo ko menene in da zaki saka kanki, zan saka a bi bayanki, domin ganin in da ki ke zuwa”

Rumaisa tana jin zuwan Ammi, suna ta hira ita da mama, amma ta yi bakam kamar bacci take yi, alhalin idonta biyu maganar ce kawai ba ta son yi.

Sai da likita ya shigo, sannan ta tashi suka gaisa da Ammi, likita ya duba X-ray ɗin ta ya ce babu wata matsala, haƙararin nata ma buguwa ce kawai, zai rubuta mata magani.

Mai sunan baba ma tuni sun zo, tare da Abubakar ya biyo yayi musu sallama zai koma makaranta.

Ammi take tambayar mama ko ‘yan biyu ne saboda kamanin da suke yi, ba ta gane su, kawai dai ta lura da ɗaya yana da fara’a ɗaya baya yi.

Mama ta ce “Eh ‘yan biyu ne, Abubakar da mai sunan babana, shi ne sa, ba ka dariya sai hamma”.

Ammi ta yi murmushi ta ce “Tubarkallah Allah ya ray miki, familynki sun burgeni sosai da sosai, rumaisa a yayyen nan naki ki bani biyu mana, na je na ƙara da nawa yaran mana, ni nawa duk rasuwa suke yi, saura uku a raye”

Mama ta ce “Allah sarki, Allah ya raya wanda suka rage, ya jiƙan wanda suka rasu”.

Ammi ta amsa da Amin.

Aka zubawa ruma abinci, Abubakar yana bata a baki, tana ta shagwaɓa.

Bashir yayi sallama, da shi da ‘yan sanda huɗu cikin uniform.

Ruma ta tsaya cak tana bin su da ido, nan suka gaggaisa da kowa, Ammi ta bi bashir da kallon ko lafiya.

“Maman Boy, ya jiki? Yau zaki ganni da police, su ne case ɗin binciken aisha yake hannunsu, dan haka za su yi miki tambayoyi ne” a take rumaisa ta haɗe rai, ta kawar da kanta gefe.

Ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya ce “Baby girl, ki amsa mana tambayoyinmu, zai taimaka mana ƙwarai wurin binciko wanda suka yi garkuwa da ku”.

Ruma ta zumɓura baki ta ce “Ni fa bana riƙe abubuwa, na manta komai, likita ya hana ayi mini zancensu”

“Ki yi haƙuri ki bamu haɗin kai, ba zancen su zamu yi miki ba, yaya aka yi aka sace ki? Yaya aka yi ki ka haɗu da aisha har ta baki jaririnta da ɗankwalinta?”.

“Ni kawai sace ni aka yi, muka gamu da ita, ta bani yaron, na taho” yanayin yadda ta yi maganar zaka san ƙarya take yi.

Ɗan sandan ya sake nutsuwa ya ce “Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, a ina kuka haɗun da ita?”

Kawar da kanta gefe ta yi, irin idan ka gaji ka tashi ɗin nan.

Duk yadda ya so lallaɓa rumaisa sai da ta fara hasala shi, rarrashin duniya amma fafur ta ce ba ta san komai ba.

Mama ta yi kanta da zagi, Abubakar yana lallaɓata amma ta yi mursisi tana hawaye, ta ce ba ta san komai ba ita ta manta.

Mai sunan baba da tun ɗazu yake jin su bai yi magana ba, sai yanzu ya tashi ya nufi gadonta, ya ture Abubakar shi ya zauna ya kalleta, ta sunkuyar da kai ƙasa, cikin muryarsa mai razanar da ita ya ce “Kalleni” ta ɗago da ƙyar ta kalleshi.

“Gaya musu abun da suka tambayeki” ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan ta mayar da idonta kansa  ta shiga girgiza masa kai.

Idonta ne ya cika da hawaye, amma ta kasa magana.

Mama ta ce “Ruma ba kya ji ana yi miki magana ne?”.

Ammi ta ce “Ku bita a hankali, kar ku tsoratata”.

“Ba zaki faɗa ba sai na saka sun saka miki sarƙa sun tafi da ke, ana magana kina kallon mutane” yadda mai sunan baba yayi mata maganar cikin hargowa sai da ta tsorata, jikinta ya hau rawa, tana girgiza masa kai.

Ya sake kafeta da ido ya ce “Faɗi, komai ɗacinsa da muninsa faɗi”

Cikin rauni idonta na zubar da hawaye ta ce “Bana son faɗa, bana son tunawa ne, labarin babu daɗin ji, kuma babu daɗin tunawa. Ta mutu!ta mutu! Ko sin ce sun kasheta? Ta mutu ne ba ta raye, kuma sun zo da mota sun ɗauke ta tun a can, bana son tunawa, mutuwar anty aisha abu ne da ba zan manta ba, ta mutu! Ta mutu!! Ta mutu ku rabu da ni dan Allah tun da na gaya muku” ta yi maganar cikin hargowa tare da watso piliown kan gadon tana wani irin kuka, da sai da mai sunan baba ya rungumeta jikinsa a matuƙar sanyaye.

Takawa ta gani a tsaye a ƙofar ɗakin, ya zuba mata ido da dukkanin nutsuwarsa, yana jin abun da take faɗa tamkar zubar dalma a tsakiyar zuciyarsa.

Lumshe idonta ta yi, hawaye na tsiyaya daga idonta, mai sunan baba yana jin yadda zuciyarta ke bugawa da saurin gaske.

Duk wanda yake ɗakin sai da yayi sak, cikin ammi ya kaɗa yayi wani irin ƙugi, take ta fara fatan Allah ya sanya mafarki take ba gaske bane ba.

A hankali takawa ya tako cikin ɗakin, sai a lokacin suka lura da zuwansa, ya ƙarasa gaban gadon rumaisa, da take kwance a jikin mai sunan baba, hannunta ya kama ya yi wa wani irin mugun riƙo ya dubeta ya ce ‘Ki ka ce matata ta mutu, ta yaya? Ya za ayi ki ce aisha ta mutu? Ke kin san mutuwa kuwa”.

Ba riƙon da yayi mata ne ya sakata a cikin tashin hankali ba, abun da take gani a tattare da shi ne ya ɗaga mata hankali, sai dai alamu sun nuna babu wanda yake ganin abun da take gani sai ita kaɗai.

Mai sunan baba ne ya shiga ƙoƙarin ƙwace hannun rumaisa daga na Adam, amma ya kasa ruma kuwa ta ƙura masa ido tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Ammi tamkar an dasata, ta ji maganar a bazata, ba ta taɓa tunanin abubuwa zasu cigaba da rikicewa haka ba.

Bashir ma ƙoƙarin ƙwace hannun rumaisa suke yi, amma riƙon da ya yi mata ba na wasa bane ba.

“Ki ka ce matata ta mutu? Ta mutu fa ki ka ce, ki tashi daga baccin da ki ke yi ki gaya mini gaskiya, ba Aisha ce ta mutu ba”.

Cikin kuka ta ce “Ka cikani kar ka ɓalla mini hannu, tun da na gaya maka abun da ka ke son ji” tayi maganar cikin kuka.

Bai iya cewa komai ba, sai ganinsa suka yi ya silale a ƙasa ya suma.

Sai a lokacin ammi ta samu hawayen idonta suka gangaro, mama da sauran mutanen wurin suka yi kan adam, sai dai ba ya motsi sam.

Da gudu Abubakar ya fita, sai gashi da likitoci sun biyo shi, suka yi umarni a kawo stretcher a ɗau adam a kai shi emmrgency.

Mai sunan baba kuwa bai motsa ba, sai ma rungume rumaisa da yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, saboda kukan da take yi, ruma kuwa da ta ga an kawo stretcher an ɗora adam a rikice ta ce “Wai shi ma mutuwa ya yi? Haka anty aisha fa ta yi ta daina motsi bayan ta yi ta fitsarin jini, jininta ya ƙare”

Mai sunan baba ya sanya hannunsa ya rufe mata ido ya ce “Bai mutu ba in sha Allah, ki yi ta Addu’a”.

Gaba daya ta kasa nutsuwa, mutuwar aisha ce ta dawo mata sabuwa fil a idonta, duk masifar mai sunan baba, tausayin rumaisa ya mamaye shi, yarinya ƙarama tana ta gamuwa da iftila’in ƙaddara.

Ammi kuwa kuka ta din ga yi, kamar babu gobe ta yi iya ƙoƙarin ta amma ta kasa tawakalli ta jure, abu ka da mata abu na ‘ya’ya, mama na son ta rarrasheta amma ita ma ta ɓuge da kukan, daga baya suka bi bayan su Bashir, domin jin halin da Adam yake ciki, Yaya Abubakar ya tare su a hanya ya ce “Mama, ku je ku zauna in sha Allah babu wani abu, ga likitoci can sun rufu a kansa, ba za su bari ma ku shiga ba, ku yi haƙuri ku je ku zauna, ayi masa addu’a.

Yadda ammi take kuka zai tabattar maka da ba iya mutuwar ce ta dake ta ba, akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, la’ila ha illa la Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam” sune abubuwan da ammi ke ta nanatawa.

Mai sunan baba ya numfasa ya ce “A duk lokacin da muka rasa abu mai muhimmanci a rayuwarmu, sai mu tuna Allah ne ya bamu, kuma Allahn da ya bamu yafi mu son abun, kuma ya fi mu sanin muna son abun, dan haka addu’a zaki yi ki daina kuka” da ruma yake maganar, amma a zahiri ba iya ruma yake yi wa nasihar ba, har da ammi.

“Mai sunan baba” ruma ta kira sunansa.

“Na’am”

“Ka ga laifina da naƙi faɗa tun da farko? Ka ga shi ma zai mutu ya bar jaririn ko?”

“Ke da ki ka ce ba shi ne babansa ba, Meyasa ba kya so ya mutu?”

“Mai sunan baba” ta kuma kiran sunansa.

“Na’am” ya amsa mata.

“Idan sabir ya girma sai ya ji duk a gabana iyayensa suka mutu, idan ya tsane ni fa? bana son tunawa da mutuwar anty aisha, idan na tuna ji nake kamar na kashe kaina, da tsohon cikin nan fa dukanta suke yi, idan zasu dakeni ta hanasu, tun da suka taka mata cikinta take rashin lafiya, idan barde ya kawo mini abinci, tare muke ci, wataran ta ce in cinye ni ‘yar baby ce ita ta ci girma. Mai sunan baba na yi ta yi musu magiya su kai ta asibiti suka ƙi, kuma sun san ba ta da lafiya, na yi ta kuka ina roƙonsu ita kuma tana musu magiyar su karɓi kuɗin fansata a wurin mijinta su sakeni ni yarinya ce. A hannuna ta mutu bayan na bata ruwa, babu wani ɗan sanda da ya zo kuɓutar da mu, kuma sai yanzu zasu zo su dameni wai sai na gaya musu tana ina? Me za su yi a kai bayan ta bar duniyar, na tsani duk wani jami’in tsaro tunda har anty aisha ta mutu ba wanda ya kawo mana agaji, sai wasu ‘yan ta’addan ne suka ƙwace mu, wallahi duk wanda ya kuma tambayata wani abu ba zan faɗa ba, dan babu abun da za su iya yi a kai” tayi maganar cikin ƙunar zuciya tana rirriƙe hannun mai sunan baba.

A hankali ya kwantar da ita, ya toshe mata bakinta, saboda kamar nema take ta fita hayyacinta, adduoi ya din ga yi mata, har ya samu ta yi shiru, amma maganganunta sun ɗaga masa hankalin, shi daga nesa ma masu ciki tausayi suke bashi, saboda dakon cikin ma kawai ya ishe su, balle ace a taka mace da tsohon ciki, abun da ban tausayi.

Daga mama har ammi kowa sai goge hawaye take yi, sabir ne ya motsa ya fara kuka, mai sunan baba ya sanya hannu ya ɗauke shi ya fita da shi waje.

Ya ƙurawa yaron ido, sunan mahaifinsu rumaisa ta saka masa, ya tuna irin faɗi tashi da sadaukarwa da mama take yi a kansu, tun suna yara har zuwa yanzu da suka zama mutane ba ta daina ba, amma shi wannan ɗan bai san wannan ba, hasali ma tasa uwar tana kawo shi duniya ta mutu ta bar shi a dokar daji a hannun yarinyar da ita kanta ba ta san ciwon kanta ba, ta yi kwanaki tana gararanba da shi a daji babu ko wando a jikinsa ga ƙazantar haihuwa.

Wani irin tausayin yaron ya kama shi, ya rungume shi a ƙirjinsa yana shafa bayansa, wata irin ƙwallar tausayin yaron ta cika masa ido.

Abubakar kuwa tamkar wani daga cikin ‘yan uwansa ne suka suma aka kwantar da su, sai kai wa yake yi yana komowa, sai da ya ga lokaci na neman ƙure masa sannan ya ɗau jakarsa ya tafi.

Ko da su Usman suka zo mamaki ne ya kama su, ganin halin da su mama suke ciki, fuskokinsu ɗauke da damuwa, idon mama yayi ja saboda kuka, ammi kuwa har a lokacin kuka take yi.

Aliyu ne ya fara maganatuwa ya ce “Mama lafiya kuwa? Meyafaru ne?”

Mama ta girgiza masa kai ta ce “Lafiya ƙalau, ya kuka baro gidan an gama komai?”.

Usman ya ce “Mama, ya zamu ga kuna kuka kuma ku ce lafiya ƙalau, meyafaru?”

“Baban yaron nan ne babu lafiya, ashe mahaifiyar sabir da ake ta fama da rumaisa a kan ta yi bayani taƙi, ashe rasuwa ta yi, a hannun’yan bindigar ta rasu”.

Dafe ƙirji Aliyu ya yi yana Innalillahi wa Innalillahi raji’un, usman kuwa sak yayi duk da bai san matar ba, amma tausayinta ya kama shi.

“Mama rumaisa kuwa na da hankali, kuma shine ake ta fama da ita ta yi mursisi taƙi faɗa, saboda tsabar rashin kan gado”

“To ka san halinta da baƙin taurin kai, yanzun ma babana ne ya sakaya a gaba ya zare mata ido, amma yan sandan da suka zo suma ƙin kula su ta yi”.

Cikin damuwa usman ya kalli Ammi ya ce “Dan Allah ku yi haƙuri, wallahi yarinyar nan haka take sai a hankali wasu lokutan, bai kamata ta ɓoye abu mai girma irin wannan ba, ku yi haƙuri Allah ya jiƙanta da rahama ya sanya ta huta”.

Ammi ta ce “Amin, ku daina ganin laifinta a kan gaskiyarta take, yanzu ihu ake bayan hari, kamata yayi a kai musu ɗauki tun suna hannun ‘yan bindigar. Ba ta yi mini komai ba, babu abun da zan ce wa rumaisa sai fatan Allah ya rayata, ya shiryata ya tsareta na gode sosai da sosai”. Ta kai maganar tana kuka.

Usman cikin damuwa yake duban Ammi ya ce “Ki yi haƙuri, sai a gode Allah da ya kuɓutar da ɗan ta, ko ba komai za a kalla ace ga ɗan Aisha, kuɓutar yaron nan kawai ya ishi a godewa Allah, duk da ya karɓi uwarsa, komai yayi daidai ne, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri Allah ya yafe mata, ya kula mana da jaririnta, ku yi haƙuri dan Allah kuka ba mafita bane, duk da dole ne jin zafi a duk lokacin da muka rasa makusanta mu da muke so, amma ayi haƙuri, duk jarrabawar da Allah ya yi wa bawa dai-dai ce”.

Duk da ba wasu shekaru ne da usaman ba, amma ammi har cikin zuciyarta ta ji daɗin yadda suka nuna damuwa a kan ta. Ta ce “Na gode Allah ya yi albarka”

Ƙasan zuciyar ammi kuwa, tashin hankali ne mai yawan gaske, dan al’umar sun yi dagulewar da ba ta san ta ina zata kamo bakin zaren ba.

Sai wajen azahar rumaisa ta farka, ji take kamar ba a gaske ta faɗa musu mutuwar Aisha ba, mai sunan baba ta gani zaune a gefen gadonta, yana juya Sabir yana murmushi gefen baki, mai sunan baba da kan ka ga dariyar sa aiki ne ja, ruma za ta iya cewa tun da ta buɗi ido a duniya ba ta taɓa ganin mai sunan baba ya ɗauki ɗan wani ba, wani irin daɗi ta ji da ta gan shi ɗauke da Sabir.

Ya dubi ruma ya ce “Sannu kin tashi?”

Ta jinjina masa kai alamar eh.

“Babu wata matsala dai ko?”

“Eh babu, baban mama kana son mai sunan babanmu ko?” Ya jinjina mata kai, a lokacin da yake gyarawa sabir kwanciyar sa a hannunsa, duk da ba wani ƙwarewa yayi a iya ɗaukar yara ba.

“Mai sunan baba dan Allah kar ku bari a rabani da shi, wallahi mamansa ta ce ta bar mini shi, da gaske nake ba wasa ba” kallonta kawai ya yi bai ce mata komai ba.

Ammi kuma na kan dadduma tana jin su, amma ba ta tanka ba.

Su Iman sun kira wayar ammi har sun gaji, dan ƙarshe ma kashe wayarta ta yi ma gaba ɗaya, dan ba ta san me za ta ce musu ba.

Adam kuwa ya shafe awanni a emergency ana fama, domin a ceto ransa, sam zuciyarsa ta ƙi bugawa yadda yakamata, bpn sa ma an kasa picking ɗin sa, ga numfashin sa ma yayi ƙasa fiye da yadda ake so, su kansu likitocin sun fara fidda rai, da ƙyar da taimakon Allah ya farfaɗo ya samu bacci, sai da ya yi baccin ne sannan aka fito da shi a ka bashi ɗaki.

Wunin ranar da su Aliyu aka yi ta sintiri a kan Adam, in an jima usman ya zauna ya yi ta yi wa ammi nasiha yana ba ta haƙuri. Sai da aka fito da shi, sannan aka ce ammi ta je ta ganshi.

Aka yi mata jagora har ɗakin da yake, dan har ta fara fitar da rai a kan sa, jin shiru-shiru ba a fito da shi ba, ta zaci ko shi ma ya rasun ne.

Ta tsaya tana ƙare masa kallo, ga robar ruwa nan a saƙale, shi kuma idonsa a rufe yana bacci.

Ta kama hannunsa a cikin nata, ta saka hannunta ɗaya tana shafa kansa ta ce “Na sani akwai wahala, amma ka ƙara jurewa, tun da na haifeka a kullum akwai fejin ƙaddara da kake buɗewa babi babi, da an wuce wannan sai wannan, na sani da wahala amma ka ƙara jurewa addu’a ta tana tare da kai yarona. Allah ya shiga lamarinka Adam, Allah ya cigaba da dafa maka ya baka ikon cin jarrabawa” tayi maganar tana rushewa da kuka.

Bashir ya ce “Ammi, addu’a nan dai, ita zaki cigaba, kar jininki ya hau fa, kuma yanzu mun gano bakin zaren, tun da ta tabatta ta rasu, sai mu san abun yi na gaba, Allah ya yi mata rahama”.

Aka din ga rarrashin ammi ana bata baki, daga bisani Bashir ya sallami direbanta, bayan magariba bashir ya ce zai mayar da ita gida, ya dawo ya zauna da Adam.

Mama ta ce “A’a, ita zata kwana a wurinsa”

Aliyu ya ce “Haba dai, saboda rashin kara ka wuni kana kaiwa da komowa, ita ma ta wuni a nan kuma ace ku kwana, ai ba wani abu, ko ni sai na zauna na kwana da shi”.

Ammi ta ce “Kar a ɗora muku ɗawainiya”

“Wallahi ba wata ɗawainiya, Allah ya bashi lafiya kawai”.

Daga gida har wurin adam kowanne tana son ta zauna, amma ya zama dole ta zaɓi tafiya gida, domin kuwa ba ta son kowa ya farga da abun da ya faru kan su sanar da kansu, ta san rashin zamanta a gidan, kan iya jefa zargi a wurin masu son ganin bayanta, dan haka a dole ta yarda Bashir ya ɗauketa ya mayar da ita gida.

Aikuwa a falo ta tarar da su Nusaiba a zazzaune fuskokinsu duk babu daɗi.

Nusai ce ta fara cewa “Ammi akwai matsala ne, tun safe mun kira wayarki ba kya ɗagawa hankalinmu duk ya tashi, yanzu uncle Jamil ya bar gidan nan yana nema ya ɗaga mana hankali wai ina takawa yake?”

Gaban Ammi ne ya faɗi, kar dai ya san wani abun ne, ta buɗe baki da ƙyar ta ce “Ya ce muku wani abun ne?”

“A’a kawai dai yana tambayar mu wai ina yake, baya samunsa a waya, ya je gidansa ma baya nan”

“Babu wani abu, ban zaci zan kai haka ba nima, amma ai gani na dawo”

Buutt baba uwani ta fito cikin girmamawa ta ce “Allah ya ja zamaninki, haƙiƙa yau mun wuni cikin zulumi da tashin hankali, mussaman da baki wuni a gida ba na tambayi su auta, sun ce ba su san in da ki ka tafi ba, ga wayarki ba ta shiga duk sun shiga damuwa kamar marayu”.

Ammi ta ce “Gani na dawo, uzuri ne ya riƙe ni, zan shiga in huta, kar wanda ya shigo mini”.

Iman ta ce “Ammina abinci fa?”.

“Na ci” ta faɗa a taƙaice ta wuce sashinta.

Nusaiba ta ja hannun iman, ta yi ƙasa da muryarta ta ce “Anya kuwa babu matsala?”.

Jiki a sanyaye Iman ta ce “Nima haka nake tunani, amma ta ce kar wanda ya je in da take balle mu ji”.

Nusaiba ta yi ajiyar zuciya ta ce “Bari mu jira zuwa Allah ya kaimu da safe mu gani”

Iman ta amsa da “Allah ya kaimu ya sa lafiya”

Tafiyar Ammi babu daɗewa Adam ya farka, Aliyu ya yi masa sannu, ya ɗan jinjina masa kai.

Ya yinƙura zai tashi, Aliyu ya taimaka masa ya tashi zaune, ya bashi ruwa ya sha.

Aliyu ya ce “Zaka ci wani abun ne?” Adam ya girgiza kai ya ce “Salla zan yi”.

Aliyu ya taimaka masa ya kai shi banɗaki yayi alwala, ya dawo da shi ya shimfiɗa masa abun salla, ya jero sallolin da suke kansa, sai dai bai tambayi Aliyu komai ba, can kamar an mintsine shi ya ce “Da gaske ƙanwarka take matata ta mutu ko?”

Jiki a sanyaye Aliyu ya ce “Haka ne, amma dan Allah ka karɓi ƙaddara ka yi haƙuri, ka ga da ƙyar likitoci suka ceto ranka, mahaifiyarka na cikin damuwa, kar ka sake sawa hankalinta ya tashi”.

Hawaye ne ya taru a idon Adam, ya haɗiye wani abu mai ɗaci, da sai da adams apple na maƙogwaronsa ya motsa sosai, cikin rawar murya ya ce “Jikina ya daɗe yana bani ta rasu, amma zuciyata ta ƙi aminta da hakan, ina jin zan sake ganinta, zan sake kallon fuskarta, ashe bankwana na yi da ita, na san ko gawarta bani da ikon gani, balle in binneta da hannuna ina yi mata addu’a da tuna biyayyarta da soyayarta, wayasani ma ko yar da gawarta suka yi ta lalace a haka, sun tozarta ni, sun tozarta iyalina. Amma ni musulmi ne, muslmi ne ni tabbas, dole na yi imani da ƙaddara. Ku rarrashi ƙanwarku, amma a gobe in Allah ya kaimu zan karɓi ɗana, zan je gaban sirikina, kuma uba a wurina, in sanar masa komai, ya ɗauki duk matakin da yake ganin ya dace da ni”.

Wani irin tausayinsa ne ya kama Aliyu, duk yadda adam ya so ɓoye hawayensa kasawa yayi, ya barsu suka din ga zuba son ransu.

Da ƙyar Aliyu ya ɗan yi gyaran murya ya ce “Kamar yadda ka ce kai musulmi ne ka yarda da ƙaddara, to Yakamata a ga hakan a aikace, ka yi haƙuri in sha Allah sirikinka zai fuskance ka, Allah ya yi mata rahama”.

Mama ce ta yi sallama a ɗakin tana faɗin “Aliyu ya tashi kuwa?”.

Ta tarar da su a zaune, mama ta ce “Alhamdilillah ala kulli halin, Allah mun gode maka, sannu ka ji?” Ya jinjina wa mama kai yana share hawaye.

“Ayi haƙuri, a fawallawa Allah, yaronka mahaifiyarka da sauran makusantanka suna buƙatar ka, ita tata ta ƙare ta yi shahada sai fatan Allah ya karɓi shahadarta, ayi haƙuri, Aliyu je ka ɗaki ka kawo ruwan shayi da abinci ya samu ya saka wani abu a cikin sa”.

Aliyu ya tashi ya fita, yana fita lokitan dare ya shigo, ya dudduba Adam aka bashi maganinsa na dare, likita ya jaddada masa ya kula da magani da dokokin da aka saka masa.

Sam Adam ba ya fahimtar abun da likitan yake faɗa, mama ta miƙa masa kofin shayi cikin kulawa ta ce “Daure ka sha, ka ga an baka magani, dole sai ka ci abinci” kallon mama kawai yake yi, wato duk in da uwa take uwa ce, yadda ta ke ta nuna kulawa a kansa sai ya ji daɗi, duk da tarin damuwar da yake ciki.

Duk da ba zai iya tantance manufar kulawar da mama take bashi ba, amma tun da ya taso kulawa ɗaya ce yake gani ta zahiri, wato kulawar ammi ban da haka galibi masu yi masa murmushi suna yin sa ne da biyu.

Da ƙyar ya karɓi kofin shayin, ya ɗan sha kaɗan ya ajiye, mama ta yi ta masa nasiha, da rarrashi cikin siga ta dattaku da manyance.

Ya ɗan murza zoben hannunsa ya ce “Da ke da iyalinki, babu abun da zan iya ce muku sai godiya, a rayuwata na daɗe ban ga mutane masu karamcinku ba. Amma dan Allah ku yi haƙuri da abun da zan faɗa, ina son zan karɓi yarona, dan Allah a rarrashi mamansa, na san zata tsaneni fiye da da, amma ni ba zan iya da rigimarta ba, a bata haƙuri zan ɗau yaron nan zan tafi da shi wurin kakansa, sai hukuncin da ya yanke a kanmu”.

A take mama ta ji babu daɗi, domin ita kanta ta shaƙu da jaririn ba kaɗan ba, ya shiga ranta.

A zahiri ta ce “Babu laifi, Ubangiji Allah ya raya shi bisa tafarkin addinin musulunci, ya jiƙan mahaifiyarsa. Amma ina fatan ba zaka rabamu da shi gaba ɗaya ba, dan a halin rumaisa bana jin za ta iya haƙura”.

Yayi murmushi ga hawaye na zuba daga idonsa ya ce “Za ta saba in sha Allah, ba zata damu sosai ba amma yarona yana buƙatar kariya ta musamman, ba zan manta soyayyar da ta nunawa gudan jinina ba”

Jiki a sanyaye mama ta ce “Babu laifi, Allah ya jiƙan mahaifiyarsa, kai kuma ya baka lafiya” da haka mama ta yi musu sallama ta koma ɗakin da rumaisa take. Ta kwanta tana facing ɗin Sabir, tana ta baccinta, ta saka hannu ta riƙe masa nasa hannun suna bacci.

Tausayinsu ne ya kama mama, amma babu yadda ta iya, haka ta shiga harhaɗa wa sabir kayansa, a daren ta haɗa komai cif a wuri ɗaya.

Suma ta haɗa musu nasu kayan, dan ta ji likitan yana cewa washegari zai sallami rumaisa, tun da ita ma ta warware sai abun da ba a rasa ba.

Sai da ta kammala, sannan ta yi alwala ta tayar da salla.

Da asubar fari, sabir ya tashi yana ‘yan koke-koke, mama ta ɗauke shi ta yi masa wanka, ta bashi madararsa, ita kanta mama tana matuƙar ƙaunar yaron da tausayinsa, ta ɗauke shi ta goya shi a bayanta, ta yi sallar asuba, ta tashi ruma ta yi salla sannan ta fita daga ɗakin.

Harabar asibitin ta koma ta kira mai sunan baba, tana shiga ya ɗaga, ya gaida mama, ta amsa masa sannan ta ce “Babana, dan Allah da gari yayi haske ka taho asibitin nan, yau za a sallami rumaisa, kuma yau za su karɓi ɗan su, ka san halinta sarai, jiya da daddare babansa da ya farfaɗo ya ce zai karɓi ɗan sa ya tafi da shi ya gabatar da shi a danginsa, sannan ya sanar da rasuwar uwar ɗan”.

Mai sunan baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce b”Babu laifi, zan shigo in sha Allah, amma a bita a hankali dan Allah, ko a bari na zo tukuna”

Mama ta ce “ai shi ya sa na ce sai ka zo ɗin”

Bayan sallar asuba, Adam ya karɓi wayarsa a hannun Aliyu, ya kira ammi, suka yi magana, ta ji daɗi sosai da jin muryarsa, tayi masa addu’a da fatan alkhairi.

Ya kira Bashir ma suka gaisa, tare da sanar da shi, ya je ya taho da Ammi.

Kiran jabir ne yake ta shigowa tun bayan da ya kunna wayar, kamar ya share sai kuma ya ɗaga.

“Wai ina ka shiga haka baka ɗaga wayata? Ya ake ciki ne akwai wani labari ne? Ko ka koma wurin yarinyar?”

“A’a ban koma ba, zan koma bacci yanzu zan zo gida in sameka anjima” bai ko tsaya saurarar mai jabir zai ce ba, ya kashe wayar ya ajiye, haryanzu ya kasa gazgata maganganun rumaisa, wai Aisha ta mutu, ganin abun yake kamar almara, sai yanzu ya gane ka rasa mutum ka ga gawarsa wata ni’ima ce, ba irin tunanin da bai zo masa a kan gawar Aisha ba.

Abun mamaki yau ruma taƙi komawa bacci, mama har tambayar ta ta yi ba zata koma bacci ba, ta ce ba ta ji.

Ta dubi in da mama ta haɗa kayansu ta ce “Mama wai tafiya zamu yi ne an sallame ni?”.

“Eh, in anjima za a sallame mu”

“Yeeee dama na gaji da zaman asibitin nan wallahi, yau sai gida, ga kayana ga na babyna nima na samu mai sunan babana, sai dai Allah ya sa kar yayi halin mai sunan kakanmu” tayi maganar da sigar tsokanar mama, amma mama ba ta tanka mata ba.

Har gari ya waye ruma idonta biyu, ta damu mama a kan ta bata sabir, amma mama ta hanata.

Wajen ƙarfe tara, Usman da mai sunan baba suka zo, ruma tana ta murna zata tafi gida, dan zumuɗi ta ce abincin ma sai ta je gida zata ci.

Usman ya din ga kwasar kayansu yana fitarwa, sai murna take yi yau ba kwanan asibiti, dan takardar sallama kawai suke jira daga likita.

Bashir ne ya shigo ɗakin rumaisa, ya kalleta yayi murmushi ya ce “Yau sai gida uwar rikici”

Ta yi murmushi ta ce “Ɗan uwanmu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, jin godiyar nake ma ta yi kaɗan a baki, amma zan din ga yi maka Addu’a idan na yi salla”..

Yayi murmushi ya ce “Kai masha Allah, amma na gode ƙwarai da gaske, sister na asiya ma tana gaishe ki, ita ma ba ta da lafiya ne. Amma kin je kin duba baban sabir kuwa?”

Ta ɗan yi turus tana kallon mama, mama ta ce ‘Yanzu zan sakata a gaba mu je ta duba shi, sai mu tafi”.

Bashir ya ce “Yauwwa mama, dama ga ammi can ma ta zo sai ku yi sallama, ai bai kamata ku tafi babu sallama ba”.

“To ai yaya Aliyu ya ce bai mutu ba, har ya tashi”

“Haba rumaisa, idan da kara yakamata ki je ki duba shi, ko dan albarkacin sabir ɗinki”.

Usman ya ce “Sai ka lallaɓata ma, wuce mu je, kuma saura mu je ki yi rashin kan gadon naki, ya saka dogarai su saita miki zama”.

Suka ɗunguma zuwa ɗakin da takawa yake, suka tarar ammi na zaune a kusa da shi, ta riƙe hannunsa, tana share masa hawaye.

Ammi na ganinsu tayi murmushi ta ce “Kun fito? Yau ban ƙaraso mun gaisa ba rumaisa, hankalina ne a tashe”

Ruma ta durƙusa ta gaisheta, ta amsa mata cikin girmamawa.

Usman ya ce “Ki yi masa sannu mana”ta dubi Adam za ta yi masa magana, amma gabanta ya faɗi, ganin gaba ɗaya idonsa ya koma baƙi, yana fitar da hayaƙi.

Mannewa ta yi bayan usman, tana leƙo shi, taga ita yake kallo, amma idonsa yana ta hayaƙi, kallonsu take yi, tana jiran ta ji wani yayi magana a kan idon takawa, amma ta ji babu wanda yayi magana da alama su ba sa gani.

“Ba zaki yi masa sannun ba?”

Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ɗan zuro kai ta ce “Sannu, Allah ya bada lada” tayi maganar a rikice dan a razane take, bata taɓa ganin idon mutum a haka ba.

Bashir ya ce “Ladan me kuma rumaisa, shi da ba shi da lafiya?”.

“Au ba lada ba, Allah ya warkar da shi”

Usman ya ce “Yau kuma meke damunki ne?”

Mama ce ta kwance Sabir daga bayanta, mai sunan baba ya karɓe shi,  ya ƙarasa gaban gadon Adam ya ce “Allah ya ƙara lafiya, ya jiƙan mamansa, kamar yadda ka buƙata ga yaronka, Allah ya raya shi, Allah ya biyaka ɗawainiyar da ka yi da ƙanwarmu”. Adam ya karɓi Sabir, yana ƙoƙarin mayar da hawayen idonsa.

A rikice ruma ta ce “Ban gane ga ɗan sa nan ba, da shi zan tafi ai, ni anty aisha ta bar wa shi” tayi maganar tana nufar Adam, amma mai sunan baba ya tare ta ya ce “Juya mu tafi” karo na farko da ta tsaya ta saka idonta a nasa ta ce “To ka karɓo mini ɗana”.

“Ni nake magana ki ke mayar mini?”.

“Haba mai sunan baba, ya za ayi a ƙwace mini yarona, dama abun da aka shirya kenan? Mama ki saka baki” ta dubi Ammi ta ce “Dan Allah ku bani yarona, na sha wahala kan mu tsira tare, idan aka ƙwace mini shi, mutuwa zan yi, wallahi ina son sa sosai, ɗan uwanmu yaya bashir, dan Allah ka karɓo mini ɗana”

Gaba ɗaya sai tausayin rumaisa ya kama su. Ammi ta ce “Kina ji ruma, ki kwantar da hankalinki, babu mai rabaki da yaronki, zamu je a kai shi cikin dangi ne, kuma in sha Allah za a din ga kawo miki shi ki ganshi”.

Rumaisa ta fashe da kuka ta ce “Da na san haka ne, gara na zauna mu mutu a dajin, da da wannan mutumin ya ce in tafi ba zan tafi ba, gara a harbeni, kwanana biyu ba ma bacci ni da sabir, saboda sanyi yana kuka, kwanana uku ina bulayin hanyar da zamu dawo, kuma a ƙwace mini shi bayan mun sha da ƙyar, ba anty aisha ba sabir ɗina. Dan an ga ni yarinya ce za a ƙwace mini ɗa” Mai saunan baba ya danƙi hannunta zai yi waje da ita, tana kuka tana miƙa hannu tana “Dan Allah ku bani sabir ɗina” tun da ruma ta fara kukan nan tana zuba, ko ɗaga kai Adam bai yi ba ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Kuka sosai rumaisa take yi, tamkar an ce mata mama ta mutu, bashir ya rakosu yana ƙoƙarin rarrashinta, amma mai sunan baba ya ce ya rabu da ita, ya buɗe mota ya sakata, amma sai miƙa hannu take taka kuka.

“Ki rufewa mutane baki, idan an baki ɗan ya zaki yi da shi, ke wace irin yarinya ce da ba a isa a gaya miki, ko ki rufe mini baki, ko na casaki a wurin nan” mai sunan baba yayi mata wata irin tsawa mai razanarwa.

A gigice ta ƙanƙame mama tana ƙoƙarin haɗiye kukanta, amma ta kusa ƙwarewa saboda kuka, ga hawaye ga majina har da yawu, saboda kuka.

Ammi na tsaye tana hango rumaisa yadda ake fama da ita, wani irin tausayinta ya kamata. Allah kenan ya karɓi uwar yaron, kuma ya sanya soyayyarsa mai tsanani a wata zuciyar.

A hankali ta juya ta koma ɗakin da adam yake, yana rungume da jaririnsa.

Ammi ya dube shi ta ce “To me ka yanke? A ganina mu bari nan da ko kwanaki biyu ne ka gama warwarewa”.

Adam ya girgiza kai ya ce “Ammi, ba zan taɓa warkewa ba, barin lamarin ina sake jinkirta loka8, abubuwa caɓewa za su cigaba da yi, daga nan gidan turaki zan wuce, zan je na sanar masa da laifina gaba ɗaya duk hukuncin da ya yanke a kaina shikenan”.

Cikin damuwa Ammi ta ce “Kana ganin hakan shine mafita?”.

“Ammi dole ita kaɗai ce mafita, na yi zaton aisha tana raye ne dama, shi ya sanya nake ta jinkirtawa, amma na yadda ta rasu yanzu, yanzu zan fara fuskantar mai girma turaki, daga baya kuma sai na fuskance ƙalubale na gaba”.

Ammi ta ɗan yi shiru yana kallon ƙasa, daga bisani ta yi ajiyar zuciya ta ce “Shin, Ubangiji Allah ya yi mana jagora baki ɗaya “

Ya amsa da amin.

Bashir suka shigo tare da likita, likitan ya dubi adam da yake rungume da jariri ya ce “Allah sarki rumaisa, gaskiya ta shaƙu da yaron nan, ba ka kyauya ba da ka ƙwace mata ɗa” Adam ya sunkuyar da kai ba tare da ya iya yin magana ba.

“To Yanzu me yake damunka, zan rubuta maka teses na yi reviewing file ɗin ka, na ga vitals ɗin ka duk normal”.

“Sallama nake so” ya faɗa a taƙaice.

“Meyasa zamu sallameka? Dole mu riƙe ka zuwa gobe in Allah ya kaimu mu ga abun da hali zai yi”.

“Ba zaku hana Allah zartar da hukuncin sa ba, ku yi haƙuri tafiya zan yi ” duk yadda likitan nan ya so lallaɓa adam ya ɗa zauna, amma yaƙi ammi ta ce ya basu sallama kawai, suna da issue a gida.

Haka kan likitan ya rubutawa adam sallama, da yayi tunanin ya kira jabir su tafi tare, sai ya ga babu wani amfani ma da jabir ɗin zai yi masa a halin yanzu, dan haka kawai ya share suka tafi.

Suna tafe a mota, yana kalon sabir da yake ta ƙamshin turare, yana wasa da hannunsa, har da farar hoda da kwalli mama ta shafa masa, ba ayi masa aski ba, dan haka suma ta cika masa kai, ga ta a cike baƙa siɗik, har ta ƙasan hularsa ta fito, ga gashin girarsa a hankali yana tofowa.

Ƙasan zuciyar Adam yana ta fargaba da tunanin, yadda zai fuskanci turaki.

Har gidan turaki bashir ya kai su, sai dai shi ya tsaya a mota, su kuma suka shiga.

Da fari ta ƙofar turakar turaki ta harabar gidan, Adam ya shawarci Ammi su shiga, amma sai suka tarar da ita a rufe, dan haka dole suka bi ta cikin gida.

Falon ba kowa sai hadimai, suna ganin Ammi tare da Adam, cikin rawar jiki suka gaishe su, aka tafi nema musu iso wurin matar gidan.

Ba su jima a zaune ba sai ga mama ta fito cikin taƙama, ta dubi Ammi ta yi murmushi ta ce “Giwa, yau ke ce a gidan namu?”

Ammi ta ce “Ni ce, kin san ɗaurowa take a ɗaure alƙali, ya gida ya iyali?”

“Alhamdilillah, takawa magajin takawa, dan kujerar galadima ta yi maka ƙanƙanta babbar kujera muke fata” tayi maganar tana kallon jaririn hannun Adam.

Ta sake cewa “Ina ku ka samo ɗa?”

Adam ya ce “Dan Allah idan babu damuwa, muna neman iso wurin mai girma turaki idan yana nan”

Ta ɗan jinjina kai ta ce “Yana nan, bari ayi masa magana”.

Ƙanwar Samha ce ta fito sumayya, ta gaida Ammi tare da takawa, ammi tambayeta ina samha, ta ce mata ta je abuja.

Mama ta fito ta ce “Bisimillah, ku shigo”

Ammi ta tashi, tana gaba adam na bin ta a baya, suka shiga falon turaki.

Yana zaune a falonsa, gefensa ga Alqur’ani a ajiye, da alama karatu ya idar.

Ya kallesu yayi murmushi ya ce “Maraba da manyan baƙi”.

Ammi ta risuna ta ce “Barkanmu da wannan lokaci”

“Barka dai, ya iyali ya kuma rayuwa”

Ammi ta amsa da Alhamdilillah, maimakon mama ta fita ta bar ɗakin, sai ta nemi wuri ta zauna.

Turaki ya kalli Adam ya ce “Takawarka lafiya, ana lafiya?”

Adam ya jinjina kai kawai, amma bai yi magana ba.

Ammi ta gyara zaman ta ta ce “Allah ya baka nasara, wata muhimmiyar magana ce ke tafe da mu, amma kan in ce komai, zan fara da neman afuwa sannan a sassauta mana hukunci”

“Babu laifi, ku muke sauraro”.

Adam ya tashi a hankali, ya tafi gaban turaki ya durƙusa, ya ɗora masa Mahmud a kan cinyarsa”.

Turaki ya rungumi sabir ya ce “Masha Allah, ina na samu ɗa, ɗan kyakykyawa Masha Allah?”.

“Ɗan wurin aisha ne” takawa ya faɗa jiki a sanyaye.

Turaki ya faɗaɗa fara’arsa ya ce “Ikon Allah, uwata yaushe ta haihu?, yaushe rabona da ita?”

“Allah ya baka yawan rai, haƙiƙa ni mai laifi ne, kuma a shirye nake da karɓar hukuncin da duk ka zartar a kaina. Wannan jaririn ɗan wurin aisha ne matata, kamar yadda aka kai ruwa rana da surutu a kan karatu da nace zata tafi. Duk ba wannan ba ma, maganar da nake maka, yanzu haka fulani ba ta duniya, ya rasu” Adam yayi maganar kansa a ƙasa hawaye na gangaro masa.

Haka suka cigaba da ƙulla mugunta kala-kala suna dariya.

Wunin yau Samha ba ta bi ta kan wayoyinta ba, sai yanzu ta nutsu, ta ɗau wayoyinta ta kunna, ta ajiye su a kan gado, ta shiga wanka. Daga shigarta wanka zuwa fitowar ta missed calls sun fi goma sha.

Mamaki ne ya kamata, tana shirin duba missed calls ɗin, kiran Fauziyya ya shigo wayarta. Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce “Wai lafiya ake yi mini wannan kiran kamar mara gaskiya?”.

Fauziyya ta ce “Ke dalla can, idan ma wani rabon ne har ya wuce ki baki ɗaga waya ba, kawai kin wani kashe wayoyi”.

“Ke karki ɗaga mini hankali, hutu na zo yi dan me za a dameni? Ina jin ki”

Fauziyya ta ce “To, ai ni zancen ne ma ban san ta ina zan yi miki shi ba, abun farinciki zan ce miki, ko kuma tashin hankali da jimami, ko kuma abun ɗaure kai?”

Samha ta ɗan juya idonta ta ce “Fauzi, zan kashe wayata fa”.

“Katangar da ta daɗe da tsaye miki, ta hanaki cikar burinki ta rushe”.

“Kamar yaya kenan?”.

“Ƙanwarki ce ta mutu”

Miƙewa Samha ta yi, ji ta yi kamar ba ta ji dai-dai ba, wai ƙanwarta ta mutu.

“Ƙanwata wacce? Wace ƙanwar tawa?”

“Ahh, wacece ta sha gabanki ta hana cikar burinki na auren yayanmu, aisha ɗazu aka ce wai ta rasu a wurin haihuwa, a garin da ta je karatu, amma an dawo da jaririnta, amma dai kamar akwai wani abu da ake ɓoyewa ba a son a sani”.

Wata iska samha ta fesar ta ce “I hope ba ƙarya ki ke yi mini ba?”.

Samha ta ce “Ana ƙarya da mutuwa ne? Ki tambayi wanda ba sa yi miki ƙarya sai ki tabattar”.

“Am sorry, ba haka nake nufi ba, zan kiraki” ta kashe wayar ta cillata kan gadonta, ta hau sintiri a ɗakin.

To murna za ta yi ko kuwa jimami, wata zuciyar ta ce “Ke ina ki ka gata jimami, damar da ki ka daɗe ki na jira, Allah ya kawota a sama ki tsaya wani jimami? Yanzu hanya ta miƙe miki fetal, aiki kaɗan ya rage miki”.

Wayarta ta rarumo, sai dai ta rasa wa za ta kira ma, jefar da wayar ta yi, ta janyo akwatinta ta hau shirya kayanta, ko ba ta samu jirgi ba a mota zata koma gida gobe.

A daren ranar babu wanda ya runtsa a iyalin ammi, mussaman ita, da a kunnenta kishiyarta da facalolinta ke jifanta da miyagun maganganu.

Sabir kuwa tuni mama ta aike da shi gidan wata ‘yar garinsu da take aure a kano, matar kamar ƙanwa ce a wurin ammi, dan haka aka kai sabir can, duk surutun da aka din ga yi ba ta faɗi in da sabir yake ba.

Washegari ma haka aka ɗora zaman makokin aisha, samha kuwa tun da sassafe ta taho kano, sai dai ta rasa wani mood yakamata ta shiga, na farinciki ko akasin haka? Duk yadda ta so ta ji lamarin ya ratsata ta kasa, babban fatanta Allah yasa da gaske Aisha ba ta raye.

Sai da ta isa gida ta tarar da tarin mutane, sannan ta tabattar da gaske aisha ta mutu, tun daga waje ta fashe da kukan ƙarya, dan kar a fuskanci wani abu, kai tsaye ta nufi cikin gidan tana kuka kamar gaske.

Nan yan makoki suka din ga rarrahinta suna yi mata nasiha a kan aisha addu’a take buƙata ba wannan kukan da take yi ba.

Abu kamar gaske, Samha ta din ga kuka tana tumami, ana rarrashinta da ƙyar ta yi shiru, ta tafi ɗakin mamanta ta kwanta ta samu bacci.

Sai bayan la’asar sannan Hajiya Asama’u ta shiga ɗakin ta tashi Samha.

Ta dubi Samha ta ce “Ke yanzu Samha dan aishar ta mutu ki ka zauna kina wannan uban kukan kamar ni na muty? Yarinyar da ta hanaku rawar gaban hantsi a wurin mahaifinku, har wani kukan mutuwarta zaki yi?”.

Samha ta ɗan duba bayan mama, ta ji babu almar wani zai shigo, sannan ta dubi mama ta ce “Mama na dole ne, ko ba kowa ba wasu san da cewa ina son Adam, idan har na nuna ban damu ba, wasu ma ai sai su ce ina murna da rasuwarta ne, nima na dole ne kukan, amma mama ya aka yi ta mutu wai? Sannan ina ɗan da ta haifa ɗin?”

Mama ta kwaɓe baki ta ce “Mhmm, su suka san me suka yi mata dai, wai can in da ta tafi karatun a can ta zo haihuwa ta rasu, jiya nan suka zo da jaririn, ammma sun ƙi fito da shi yanzu, tun jiya ake fama amma Giwa taƙi faɗar in da yaron yake sai ɓoye shi take sai ka ce ciwo”.

Samha ta jinjina kai ta ce “Taɓ a nan aka yi mata sutura kenan?”.

“To waye ya ga gawarta, wai a can london ɗin ta mutu aka binneta, haka suka ce fa, ni ko yaushe ta yi cikinma oho, na ga dai tana can tana karatu, to can ya bita yayi mata cikin? Ko kuwa da cikin ta tafi Allah masani, saboda wata lalacewa ma, ita ya turata karatu ƙasar waje, ya zo yana nema ya haikewa iman”.

Samha ta girgiza kai ta ce “Mama ba haka aka yi ba, batun iman wannan wani abu ne da Mummy ta shirya shi, amma yadda abubuwan ne suke wakana, akwai wani abu a ƙasa, amma dai bari na yi wanka na sauya kaya”.

Ta tashi ta ɗau wayarta ta shiga banɗaki, lambar Khalifa ta nemo, ta kira shi, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

Ba sallama ba komai ya ce “Ya akwai labari ne?”

“Eh kusan haka, Allah ya yi wa matar adam rasuwa ne”.

“Na ji labari” ya katseta.

“A ina ka ji?”.

“Kin manta fitacce ne shi? Labarin duk ya karaɗe dandanlin sada zumunta”.

Ta yi ajiyar zuciya ta ce “Haka ne, sai dai an ce a can london wai aka binneta, ba a kawo gawarta ba, sai jaririnta kawai”.

Da sauri khalifa ya ce “What? Jariri kuma? How a wace maƙabartar aka binneta a London ɗin? Suwaye suka halarci jana’izar ta a can?”

“I don’t know, nima abun da na zo na tarar kenan” ta bashi amsa.

Khalifa ya yi dariya ya ce “Shikenan, kin zo mini da labari mai daɗi, wannan ma wani abu ne na yaƙar adam”.

“Amma dai ina fatan ba cutar da shi zaku yi ba, sannan ina son cire hannuna a contract ɗin nan, tun da ma dai wadda ta hanani rawar gaban hantsin ta mutu, ina ga na samu chance”

Khalifa ya ce “Haka ki ke gani?”

“Eh mana, babu abun da yayi saura ai”

“Ba zai yiwu ki saɓa yarjejeniyar mu haka kanki tsaye ba, dole ki kammala mini aikina”.

A fusace samha ta ce “Kai saurara, ba fa ‘yar ka ba ce ni, ka daina yi mini magana da isa kana bani umarni, ka kiyayeni” da haka ta kashe wayarta tana tsaki.

Kwanaki uku aka yi aka watse daga makokin aisha, sai dai adam sam baya hayyacinsa, kana kallonsa ka san a tashin hankali yake, ko abinci baya iya ci, haka yake tafiya gidansa, ya zauna ya saka kayan aisha a gaba yana kallonsu.

Ranar da suka rabu ya tuna, da zai yi tafiya, lokacin kwananta biyu da dawowa tana yi masa magiyar ya barta ta yi tafiya, ya din ga jan kumatunta yana yi mata dariya ya ce “Cikin nan naki ya sanya kumatunki ƙara cika, kuma sun fi daɗin wasa a haka” kwaɓe fuska ta yi za tayi masa kuka ta ce “Dan Allah ka mayar da maganata serious please ka bari na je”.

“Ki bari idan na dawo da kaina zan kai ki, kin ji fulanina”.

Kamar ƙaramar yarinya ta shiga turza ƙafarta za ta yi kuka ta ce “Dan Allah kar ta mutu ban je na dubata ba”.

Ya ɗan tsuke fuska ya ce “Bana son rigima fa, ke ba ki ga yadda cikinki ya tsufa ba, kin san hatsarine ki fita a san kin dawo, a sirri fa na bari ki ka dawo, tun da kin kasa riƙe kanki, sai kin dawo wurin mijinki”

Buɗe baki ta yi ta ce “Ni haka nace maka?”

Dariya yayi mata ya ce “Idan ma baki ce ba, yanayinki ya nuna ai, tun da ki ka dawo ko waje ban leƙa ba, soyayya kala-kala kawai nake sha, ki yi haƙuri jibi zan dawo in sha Allah sai na kai ki”

Idonta ne ya cika da hawaye, amam ya mayar da abun jokes, ya cigaba da ja mata kumatu yana kashe mata ido.

Da ya zo nan a tunaninsa ya durƙushe a kan gwiwoyinsa, yana kallon kujerar dressing mirror da ta zauna, suka yi wannan abu, da washegari ya ga message ɗin ta na ban haƙuri, a kan ba zata iya jiran dawowoarsa ba jikin kakarta ya tsananta da yawa.

Ya dinga zubar da hawaye yana surutai a hankali, wata irin kewarta tana ratsa shi.

Wani abu ne mai kama da bacci ya ɗauke shi, kawai sai ganin rumaisa ya yi a kan kujerar, tana zaune tana ta yi masa dariya, ‘Sarki mai koriyar alkyabba, ka ɗananiba dokinka” tayi  masa maganar tana murmushi, daga bisani ta taso ta nufo shi, tare da miƙa masa hannu, ya miƙa hannunsa zai riƙo nata, kawai yayi firgigit ya farka yana kalle-kalle. Ɗan tsuke fuska ya yi, ya tuna yadda ya din ga fama rumaisa tana yi masa gizo a baya, da ƙyar ya daina ganinta, kwatsam yanzu ma ta cigaba da yi masa gizon, ba dan ya ganta tare da ‘yan gidansu ba, to da babu shakka zai gazgata cewar aljana ce ita.

Kusan kwanaki ukun nan, rumaisa ta ƙi sakin jikinta, kusan kullum cikin kuka take a kan a dawo mata da jaririnta, tun mama tana ta tata har ta gaji ta ƙyaleta, abinci ma sai an yi kamar za a zaneta sannan take ci. ‘yan islamiyyarsu tawaga guda suka yo, har da malamansu suka sake zuwa dubata, amma mirsisi taƙi kulasu, taƙi magana.

Kwanaki huɗu da sallamar su, mama ta ce wa usman yakamata su je gida su yi wa ammi gaisuwar rasuwar aisha.

Mai sunan baba na jin jaka ya ce bai yadda ba, kar su zata wani abun suke nema a wurnsu, tun da sun yi musu gaisuwar a asibiti ya isa.

Mama ta ce “Kai ka san ba zamu je wurinsu domin neman wani abu ba, amma dai-dai gwargwado sun yi ɗawainiya da ƙanwarku, kuma babu laifi dan an bisu gida an kuma yi musu gaisuwa, shi ne abun da yakamata ai, tun da rashi suka yi. Shi dai mai sunan baba ba haka ya so ba, amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya ƙyalesu.

Mama ya shirya ya saka rumaisa ta shirya, ta ce usman da Aliyu suka raka su, ruma sai murna take ko ba komai, zata ga Sabir, sai jin daɗi take yi, ta shirya cikin riga da hijjabi, sannan ta kawo face mask ta saka.

Usman ya ce “Meye kuma na rufe fuska?”.

“Bana son a din ga kallona duk in da na je”

Ya ce “Ko kuma baki da gaskiya ba, ko kin yi wa wani laifi”

“Haba yaya usy, yaushe na dawo da zan nemi maganar ma”.

Yayi murmushi ya ce “Ashe kina sane ki ke neman maganar”

Gyara zaman hijjabinta ta yi, ba tare da ta sake magana ba suka tafi.

Gidan galadima kuwa, ammi ta karɓo sabir, su iman sun kewayeshi suna kallonsa, yaron haƙurinsa har yayi yawa, ba ya kuka sai ya ga dama, sai dai yayi ta bacci.

Babu in da ya bar adam, kamarsa ɗaya sak da adam, an yi masa wanka an shirya shi, nusaiba tana bashi madara a feeder.

Iman ta ce “Allah sarki rayuwa, Allah ya yi wa anty aisha rahama, mun ci buri sosai a kan haihuwar nan, duk da yadda ake ɓoyewa ba a son a san da cikin, amma tayi buri a kan cikin, kusan kullum sai ta turo mini hoton siyayyar da ta yi wa baby”.

Ammi ta ce “Rayuwar duniyar kenan, amma ba zan taɓa manta yadda aisha ta mutu ba, Allah ka kawo mana tsaro a ƙasarmu, ka ƙara kiyaye al’ummar musulmi” suka amsa da amin.

Adam ne ya yi sallama, suka amsa gaba ɗaya, su iman suka shiga gaishe shi, bai iya amsa musu ba sai jinjina musu kai kawai da yake yi.

Ya durƙusa ya gaida ammi. Ammi ta amsa masa tare da tambayarsa ya haƙuri.

Muryarsa a raunane ya ce “Alhamdilillah”

“Allah ya yi mata rahama, Sannan a cigaba da haƙuri duk mai rai mamaci ne”. Ya jinjinawa ammi kai, tare da zura hannunsa a aljihunsa, Saboda vibrating da wayarsa ta fara.

Bai san mai lambar ba, amma ya ɗaga tare da yin sallama.

Aliyu amsa sannan ya ce “Aliyu ne yayan rumaisa, mun zo mu yi maka gaisuwa ne, mun shigo cikin gidan bamu san ina zamu bi ba, a wurin bashir na karɓi lambarka”.

Adam ya ce “Ok babu damuwa, bari na zo gani nan” ya miƙe ya ce “Ammi ina zuwa”.

Rumaisa kuwa riƙe ƙugu tayi tana ƙarewa harabar gidan su takawa kallo, ga motoci gefe guda kuma ga burgar dawakai, ko ina sai manyan bishiyu da ƙanana, sai kalle-kalle take kamar ‘yar ƙauye, ga dogarai suna ta shiga suna fita, suna kaiwa da komowa a harabar.

Rumaisa ce ta fara hango adam ya nufo su, ya rame sai uban wuya, da dogon hanci, idon nan nasa jawur ya ƙaraso in da suke yana yi musu sannu da zuwa.

Risunawa ya yi ya ce “Mama sannu da zuwa, ya gida?”.

Cikin kulawa mama ta ce “Lafiya lau, ya ƙarin haƙuri?”

“Alhamdilillah”

Haka ya bi su usman duk suka gaisa, amma bai kula ruma ba, ita ma ba ya kula shi ba.

Ya ce “mu shiga daga ciki”

Rumaisa dama tun da ya zo yana fara magana, ta wani juya ƙeya, irin ba ta ma san yana wurin ba, sai dai kamar yadda ta ga ya rame, haka shima ya ga tayi rama, ta fi cikowa kwanaki uku baya da aka sallameta daga asibiti.

Yayi musu jagora zuwa ciki, rumaisa ta gwalala ido, ganin kayan alatun da ke falon ammi, ya wuce da su babban falon, ya ratsa da su zuwa falon ammi, wanda bai kai wanda suka baro ba.

Yayi musu iznin su zauna, ya kira ɗaya daga cikin barorin ammi, ya ce a karɓi su rumaisa. Ya ce “Bari na yi wa ammin magana”.

“To ina ɗana yake?” Ta yi maganar ba tare da ita kanta ta yi niyyar maganar ba.

Banza yayi mata bai kulata ba, sai da ya juya zai bar falon, sannan ya ce “Na kai shi koyo yadda ake gaida mutane”

Aliyu ya ce “Ai da abun duka ka samu ka zaneta wallahi, mara kunya kawai”.

Adam yana barin falon, rumaisa ta miƙe tsaye, ta sake zama a kan kujerar ta ce “Wayyo laushi, Innalillahi kujerar nan ta ji katifa yasin, kujerar masu kuɗi daban take, har na tuna wata kujera da na gani a gidansu wata ‘yar ajinmu, kujerar nan duk ƙashi, sai soso duk a waje, na ƙusa ta kusa tsarge mini mazaunai”

Usman ne ya talle mata ƙeya ya ce “Gaisuwa fa muka zo, ki ke yi mana surtu, shashasha” shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa kamar ta Allah.

Mama ta ce “Rumaisa yaushe ki canza halaye zuwa na banza ne? Dama haka na koya miki rashin gaida mutane ko?”

Ta girgiza kai ta ce “A’a ki yi haƙuri”

Aka zo aka din ga jere musu kayan abinci kala-kala, da na sha, ita dai rumaisa burinta ta ga Sabir.

Adam ya je ya tarar da ammi ta aiki su Nusaiba, daga ita sai sabir a ɗakin, ya ce “Ammi kin yi baƙi”.

Ammi ta ce “Suwaye, na ce duk wanda yayi gaisuwa ya tafi ina son hutawa ne”.

Rasa mai zai cewa ammi yayi, dan ko sunan rumaisa ba ya son kamawa, ya ce “Yarinyar nan ce, da mamanta da yayyenta suka zo yi mana gaisuwa”.

Cikin rashin fahimta ammi ta ce “Wace yarinyar kenan?”

“Wannan yarinyar da ta zo da Sabir” Sabir ɗin ma da ya faɗa ji yake kamar ya kwafsa, kasancewar rumaisa ce ta sanya masa sunan.

Cikin fara’a ammi ta miƙe tana faɗin Allah sarki.

Adam ya karɓi Sabir a hannun ammi, da niyyar ya gwanyawa rumaisa, suka fito falon.

Ko ammi ba ta kalla ba, ta miƙe tsaye tana jiran Adam ya ƙaraso ta karɓi Sabir, amma ya canza hanya ya yi wani wurin. Ai ba su ankara ba rumaisa ta bi bayansa da gudu tana “Ka tsaya in ɗauke shi, ka zo ka bani ɗana”.

Da fari bayan bayyanar rumaisa, mama ta zaci ruman nutsuwa ta ɗan ratsata, amma ina sai ta ga akasin abun da ta yi tsammani, halinta yana nan yadda yake, Aliyu na ƙwala mata kira amma ta rufawa takawa baya.

Murmushi ammi ta yi ta ce “Ƙyaleta, shi ma dai neman magana ne ya sanya ya ɗauke shi zai fice, da na san haka zai yi da ban bashi sabir ɗin ba”.

Usman ya ce “Ai gara da ya hanata, ƙin gaishe shi ta yi, sai tambayarsa ina ɗan ta dan ba ta da kunya”

Mama ta girgiza kai ta ce “Rumaisa ai sai fatan Allah ya shirya. Hajiya ina wuni ina gajiya?” Ta yi maganar tana mayar da kallonta ga Ammi

Ammi ta ce “Lafiya lau Alhamdilillah, ya gida ya iyali?”.

“Kowa lafiya ƙalau, ya kuma ƙarin haƙurinmu”.

“Haƙuri mun gode Allah”

Mama ta ce “To Allah ya sa ta huta, Allah ya rahamsheta”

Ammi ta amsa da “amin ya rabb, ya jikin rumaisa kuwa ina fatan ta wartsake gaba ɗaya”

Mama ta ce “Jikinta dai da sauƙi, amma taƙi sakin jiki kullum kuka ita sabir, yau ne ma ta ɗan saki jiki har da hira da ta ji an ce za a zo gaisuwa”.

Ammi ta ce “Allah sarki rumaisa, Allah dai ya bata haƙuri”

Hira suka ɗan shiga taɓawa da mama, har ammi take ɗan gutsura mata kaɗan daga cikin halin da take ciki, na dangane da ƙalubalen rasuwar aisha, daga ita har adam, haka nan ammi take jin yadda da mama a cikin ranta.

Rumaisa kuwa bin adam ta cigaba da yi, tana cewa ya bata ɗan ta, amma yayi banza da ita ya cigaba da tafiya.

“Wallahi idan ba ka tsaya ka bani ɗana ba, sai na yi maka ihu na tara maka mutane” bai ko tsaya ba balle ta sanya ran zai kulata. Kan ta ankara tuni ya sulale ta wata ƙofar ta neme shi ta rasa.

Komawa ta yi falon da ta baro su mama tana kuka.

Duk suka bita da ido, ammi ta ce “Rumaisa lafiya? Menene?”

Cikin kuka ta ce “Ba guduwa yayi da sabir ɗin ba, ina ta roƙonsa yaƙi kulani, ya bi ta wata ƙofa ya gudu”

Ammi ta ce “Subhanallah, takawa fa wasu lokutan ba shi da girma sai na jikinsa, bari kan ku tafi zai zo har nan ya sameni”

Mama ta ce “Rabu da ita, yanzun nan zamu tafi, can gida ina ta baƙi, yan dubiya da jaje”

Ammi ta ce “Allah sarki, na zata zaku wunar mini, baku ci komai ba fa”

“Wallahi karki damu”

Rumaisa ta ce “Dan Allah mama mu ɗan jira ko zai dawo “.

Aliyu ya ce “Ba in da zai dawo, ba dai ke fitsara ba, gara ayi maganinki ai”

Ammi ta yi murmushi ta ce “Yauwwa, dan Allah wata alfarma nake nema, idan Allah ya kaimu jibi, ina son a kawo mini rumaisa, za’a kaita wurin turaki, mahaifin aisha, abun da zai hana a kaita yanzu, haryanzu yana karɓar gaisuwa kuma yana cikin alhini, amma ya buƙaci ya ganta, ko zuwa jibi ne in Allah ya kaimu sai ko turowa na yi a ɗaukota”.

Mama ta ce “Yayyenta za su rakota in Allah ya yarda, babu wata damuwa Allah ya yi mata rahama, ai ko bai nemeta ba ya ci taje ta yi masa gaisuwa “

Ammi ta yi ta yi wa mama godiya, da kanta ta raka su har harabar gidan, rumaisa kuwa sai kuka take yi, ammin tana bata haƙuri, tare da yi mata alwashin hukunta adam.

Ko da suka taho hanya, mita ta cigaba da yi tare da cewa da ta san ba zata ga Sabir ba da wallahi ba zata bi su ba, dan ita saboda sabir ta je.

Su Aliyu ne suka tanka mata, mama kuwa shiru ta yi mata, sai da suka je gida, ta dirar mata da faɗa, faɗan da tun da ta kuɓuta daga hannun yan ta’adda ba ta yi mata irinsa ba, sakamakon rashin hankalin da ta yi wa takawa yau.

Takawa kuwa ya kai awanni uku bai dawo ba, har wayarsa ammi ta din ga kira, yana ɗakinsa ya kulle kansa da shi da sabir, sai da ya daidaici su ruma sun tafi, sannan ya mayarwa da su iman sabir, ya fice ba tare da ya bari ya haɗu da ammi ba dan kar ta yi masa faɗa a kan abun da ya yi.

Yana fita gidansa ya wuce, ya je ya kulle kansa, ya kashe wayoyinsa, dan baya ko son jin motsin wani a kusa da shi.

Rainin hankalin da rumaisa ta yi masa ne ya faɗo masa a rai, taƙi gaishe shi, amma ta biyo shi tana kiran ya bata ɗan ta, wani gajeren tsaki yayi ya nemi wuri ya kwanta tare da lumshe idonsa.

Da magariba mama take bawa su Abdallah labarin yadda suka yi a gidan su takawa da suka je gaisuwa, da abun da rumaisa ta yi, suka yi mata caa suna yi mata faɗa, ita gaba ɗaya faɗan da suka yi mata bai dameta ba kamar takaicin rashin ganin sabir, ji take da zata ga Adam ta shaƙe shi ta huta.

Mai sunan baba da yake jin hirar ta su bai ce komai ba, ya kalli in da rumaisa take ya ga sam hankalinta baya kan faɗan da suke yi mata, baya raba ɗayan biyu ya san ba zai wuce tunanin Sabir take ba.

Gyaran muryar da ya yi ne ya sanya su waiwayowa suna kallonsa.

Cikin kakkausar muryarsa ya ce wa rumaisa “Ki nemo uniform ɗin ki kafin ranar monday in Allah ya kaimu, zan je mu yi magana da shugaban makarantar ku zaki koma makaranta” turus rumaisa ta yi, dan har ga Allah ita ba ta ƙaunar makaranta a ganinta kawai salon uzzurawa rayuwarta ne.

Usman ya ce “Amma mai sunan baba bai yi wuri ba? Yakamata a bari ta gama warwarewa”

“Ba wata warwarewa da zata kuma yi, makaranta za ta koma, daga boko har islamiyya” yadda ya yi maganar very serious, ya sanya kowa jan bakinsa ya tsuke, rumaisa ji ta yi kamar ta fasa ihu, dan ba ta ƙaunar makaranta ko kaɗan.

Daga bisani ta ajiye tunanin komawa makaranta, ta sanya tunanin yadda za ta yi ta ga Sabir a gaba.

Samha ba irin tunanin da ba ta yi, a kan yadda za ta samu burinta ya cika a kan Adam, tun da yanzu dai wadda za ta zame mata matsalar ta kau, so take yi ta samu wata kafa da za ta sanya ace ta maye gurbin aisha a wurin Adam.

Ko da ta je ta yi wa mahaifinsu gaisuwa baya walwalar da zata sanya ta kawo masa zancen abun da yake ranta.

Rashin samun mafita ya sanya ta shirya ta tafi gidansu takawa, wurin babbar aminiyarta Fauziyya.

Bayan da Samha ta gama gaya mata abun da ke ranta, Fauziyya ta ce “Lallai Samha kina da matsala, a wannan yanayin da ake ciki, ana tsaka da jimamin mutuwar zaki ce ga buƙatar ki, ai wannan sai ace ma ke ki ka kasheta”.

“Allah ko? Wallahi na rasa yadda zan yi ne Fauziyya, yadda ki ka san in ɗaura mana auren da kaina, wata dama ce fa da na daɗe ina jira, kawai sonake na yi amfani da ita ko ta yaya”.

Fauziyya ta ce “Aikuwa kwaɓarki za ta yi ruwa, ke kin san yadda mai girma turaki yake ƙaunarta, daga mutuwarta ki zo masa da kina son mijinta, ashe kuwa kin taro aradu da ka”.

Samha ta yi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta ce “Hmm ba dan idon mutane ba, ai mu mutuwarta abun farinciki ce a garemu, ko banza mayi ‘yan ci mu samu ya din ga yi mana kallon ‘ya’yansa mu ma. Yanzu dai ba wannan ba, fauzi meye abun yi?”

“Yanzu ai baki ga ta neman abun yi ba, har sai Allah ya sa an kammala zaman makokin nan, ki ga in da mai girma turaki zai sanya gaba”

“Zan iya jiran nan kuwa Fauziyya, kar na sake rasa wannan damar?”

“Aikuwa idan ba zaki jira ba, zaki jawa kanki magana”

Samha ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Haka ne, yanzu tashi mu je sashin su takawar na ga jaririn dai”.

Fauziyya ta ce “Saboda me, da an so mu ganshi ai ba za a din ga ɓoye shi ba”.

Samha ta riƙo hannunta ta ce “No, kar ki yi mini haka mana, ai duk cikin salo ne shi ma, dan Allah taso”.

Haka Samha ta lallaɓa Fauziyya suka tashi suka nufi part ɗin Ammi.

Hadiman ammin suka tarar suna ta aikace-aikace, Fauziyya ta yi musu umarnin da su yi musu iso a wurin ammi.

Mintuna biyar, sai ga hadimar ta dawo, ta ce su shiga.

Kamar na kirki haka suka shiga a kame, a falon sashin suka tarar da ammin a zaune, suka gaida ammi, suka sake yi mata gaisuwa sannan Fauziyya ta ce “Ammi, dama zuwa muka yi mu ga jaririn, tun da Allah ya sa aka yi rasuwar nan babu wanda ya ganshi”

Ammi ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Akwai dalili ne, bashi da cikakkiyar lafiya shiyasa ba a son kowa ya din ga ɗaukar sa, amma bari in sa a kawo muku shi”.

Wayarta ta ɗauka ta kira iman a waya, ta ce mata ta zo da sabir falonta tana son ganinta.

Daga cikin bedroom ɗin ammi iman ta fito, nusaiba na biye da ita, sai dai kallon da samha ta yi wa iman, ya sanya iman saurin kawar da kanta gefe.

Ta ƙarasa gaban ammi ta ce “Ammi gani”.

“Ina sabir ɗin? Su Fauziyya ne zasu ganshi”.

Iman ta ce “Ammi bacci yake yi, kuma kin san likita ya hana ɗaukarsa, sai dai mu shiga su ganshi a  net

Nusaiba ta ce “A net ɗin ma dan dai su ne, amma ba shi da cikakkiyar lafiya” da ƙyar samha ta danne fushinta, suka bi su iman ɗakin ammi, Sabir yana cikin net ɗin sa sai bacci yake yi, yayi ƙalau da shi.

Samha ta kwaɓe baki, dan haka kurum ta ji ta tsani ɗan, ta ce “Ammi bari mu je, idan ya ji sauƙi sai a bamu mu ɗauka”.

Ammi ta ce “Ku yi haƙuri fa, likita ne ya saka wannan dokar”

Fauziyya ta ce “Bakomai ammi, Allah ya raya shi” da haka suka fito, suna fitowa Fauziyya ta ce “Aikin banza da ki ka takura mu je, gashi nan a wulaƙantamu a banza ai”

“Ke ni ba wannan ba, zuwa na yi da niyyar in nuna nafi kowa ƙaunar yaron, amma ina ganinsa na ji na tsaneshi wallahi, wai meya hana ya bi uwarsa ya mutu ne shi ma?”

“Aikuwa ki ka kuskura aka gane ba kya son yaron nan, ke da Adam har abada” Samha ta ja tsaki ta ce ‘Dole zan daure zuwa lokacin da burina zai cika, shegen yaron kyau kamar ubansa, na so da wani yayi kama ace ɗan shege ne ma, tunda ba wanda ya san ta na da ciki, duniya kowa ya san ciki baya zama a mahafairta kamar rariya haka take”

“To ni dai shawara nake baki, kar ki ɓata rawarki da tsalle, ki iya takunki”

“Ohhh Allah, to shikenan zan bi komai a sannu, amma a wannan karon adam ba zai kuɓuce mini ba”

Bayan fitar su Fauziyya kuwa, bin su iman da kallo ammi ta yi ta ce “Mai ya sa zaku hanasu ɗaukar yaron nan, suma ai ɗansu ne”

Nusaiba ta ce “A’a ammi, ta idonka daban ta bayan idonka daban, dole ayi kaffa-kaffa da sabir, ba kowa ne ma yakamata ya din ga zuwa wai ya zo ganinsa ba, kin san komai ammi”.

Ammi ta jinjina kai ta ce “Haka ne, Allah ya iya mana”

Suka amsa da Amin.

Rumaisa kusan tun da suka dawo daga asibiti, sai ta yi mafarki gata a wurin su sule, ta yi ta zabure-zabure, tana ihu, sai mama ta riƙeta tayi mata adduoi, gashi kullum ta zauna ba ta da zance sai na Sabir ɗin ta.

Duk tsananin surutu irin na rumaisa, ta ƙi sakin jikinta ta bayar da labarin abun da ya faru da ita a hannun ‘yan bindiga, da an fara zancen kuma sai ta yi shiru taƙi magana.

Yau shine ranar da suka yi, za a kai rumaisa wurin turaki, dan tun da safe ammi ta kira wayar mama, maman ta tabattar mata da za a kawo rumaisan.

Da safe bayan ruma ta cakali abinci, mama ta sakata tayi wanka, dan da fari taurin kai ta fara, wai ba zata je ba, sai da mama ta yi da gaske sannan ta shirya.

Mama ta kalleta a tsanake ta ce “Rumaisa” ta ɗago ta kalli mama.

“Gaban babban mutum zaki je, kar ki je ki nuna masa halinki na rashin hankali, tsaf zai saka a zaneki, wurin mahaifin ita mai rasuwar za a kai ki, ya ce yana son ganawa da ke, saura ki je ki yi masa rashin hankalin naki da ki ka saba, ko kuma kina ji ana tambayarki abu, ki ƙi bayar da amsa, ki ka dawo mini gidan nan sai jikinki gaya miki, ki ka kuskura ki ka yi rashin ɗa’a zaki ga yadda zan yi da ke. Usman ka saka mini ido a kanta, duk abun da ta yi na rashin ɗa’a ka zaneta tun a can”

Ya jinjina kai ya ce “In sha Allah” ita dai ba ta ce komai ba, ta tashi ta ɗauko facemask ɗin ta ta saka, usman ya tasata a gaba suka fita.

Duk wanda ya gansu a hanya, sai ya tsaya ya sake jajanta abun da ya samu rumaisa, da masu son bugun cikinta su ji yadda aka yi, duk tayi mirsisi taƙi magana, kai ka ce shiriya ce ta zo mata.

Adam tun safe yana gida, yana jiran zuwansu rumaisa, dan ya kai su wurin turaki, amma ba su zo ba sai azahar.

Suna sanya ƙafa a cikin falon, ƙamshin turarensa ne ya fara dukan hancin rumaisa. A hankali ta ɗaga kai aikuwa ta hango shi a zaune, ya kashingiɗa ya lumshe idanunsa.

Ammi ta faɗaɗa murmushinta, tare da yi musu sannu da zuwa. Sam rumaisa hankalinta ba ya kan su, ko gaida ammi ba ta yi ba, sai waige-waige take yi.

Ammi ta ce “Rumaisa ai kya bari mu gaisa, kan ki fara neman ɗan naki ko?” Rumaisa ta durƙusa ta ce “Ina wuni?”.

Ammi ta ce “Na ga dai hankalinki baya nan, bari yanzu zasu kawo miki shi”.

Rumaisa na jin su suna cigaba da gaggaisawa, amma ta kasa zama, kawai jira take ta ga ta ina za a fito da sabir.

Usman suka gaisa da takawa, yake tambayarsa ya mama ya ce masa tana nan lafiya.

Kamar mai shirin zarewa, suka ga rumaisa ta tashi ta nufi Nusaiba, tana zuwa ta karɓe sabir daga hannunta, nusaiba ta bi rumaisa da kallo, dan ba ta san wacece ba.

Ta rungumo sabir ta zauna da shi a wurin, kawai ta saka kuka “Sabir ɗina, ka ganni, ka gane ni? Ka yi missing ɗina ko? Kullum sai na yi tunaninka, kullum sai na yi mafarkinka, bana iya cin abinci ma kullum ina tunaka mai sunan babana, wallahi ina sonka sosai, ƙwace mini kai aka yi” ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka, da yake bayyanar da tsantsar damuwar da take ciki.

Abun ka da uwa, take jikin ammi ya yi sanyi, ta ji hawaye sun cika mata ido, tausayin rumaisa ya kamata, amma ta dake ta ce “Haba rumaisa, ai kowa ya san Sabir ɗanki ne, babu mai rabaki da shi, ki daina kuka kin ji, nusaiba saka a kawo musu ruwa ma, da abun taɓawa”.

Nusaiba kuwa tsananin mamaki ne ya cikata, yanzu wannan ‘yar yarinyar ce ta yo jigilar jariri har ta kuɓutar da shi, iko sai Allah.

Sabir kuwa ƙura wa rumaisa ido ya yi, ko ɗan ɗauke kai ta yi, sai ya bita da ido kamar zai yi mata magana. Murmushi take yi masa, hawayenta na ɗiga a kan kayansa ta ce “Ka gane ni? Na da muka taho tare daga dajin nan? To nice nan rumaisa mamanka, ka din ga ce mini ko mama, ko umma ka ji ɗan albarka”.

Ɗan lumshe ido sabir yayi kamar zai yi barci, sai kuma ya washe mata bakinsa gaba ɗaya yayi dariya.

Cikin matuƙar farinciki ta ce “Yaya usy, yayi mini dariya wallahi, kalli ka ga ya gane ni”.

Usman ya ce “A’a ba wani ganeki da yayi, bacci zai yi haka jarirai suke bacci”.

Haka aka jere musu kayan abinci, ruma ta koma gefe taƙi cin komai, sai wasa da take yi wa sabir, shi kuwa takawa satar kallonta kawai yake yi, wata ajiyar zuciya da take yi, kai ba ka ce ba ɗan ta bane ba.

Adam ya numfasa ya ce “Ina ga mu tafi, rana na cigaba da yi”.

“Ni dai ku je ku dawo, kan nan na ga sabir sosai”.

Ammi ta ce “Rumaisa, ai zuwan naki ne, ke yake son gani, ki yi haƙuri in Allah ya yarda da kaina zan din ga sawa a kawo miki sabir kin ji”.

Kallonsa ta cigaba da yi tana kuka, Adam kuwa ya taso, yazo kanta ya durƙusa zai ɗau sabir.

Riƙe shi ta yi gam tana kuka, ya saka hannu ya ɗauke sabir ɗin ya bar ta da towel.

Riƙe towel ɗin tayi ta cigaba da kuka, ammi gaba ɗaya ta rasa me zata cewa rumaisa, sai da a ranta ta ji tsoron kar su shiga hakkinta wani ciwon ya kamata saboda ƙwace yaron nan.

Haka nan sai ammi ta ji nauyin rumaisa, ta ma rasa me zata gaya mata ta rarrasheta.

Nusaiba kanta wani irin tausayin ruman ne ya kamata, ta tashi ta bi bayan Adam bedroom ɗin ammi.

Ya dubi nusaiba ya ce “Ku kula da kyau, kar a sake fito da shi, ina iman take?”

Jiki ba ƙwari Nusaiba ta ce “Ta sha maganin mura ne, tana ɗakinta tana bacci”

Ya miƙe mata sabir, sannan ya fito ya dubi usman ya ce “Mu je ko”.

Ammi ta kasa cewa komai, sai riƙo hannun rumaisa, zuwa babban falo, ta ce “Rumaisa, ni dai ina kuma baki haƙuri, na san mu masu laifi ne a wurinki, amma ki yi haƙuri ki mayar da hankali a kan makaranta, in dai sabir ne bamu isa mu rabaki da shi ba, tunda ɗanki ne”

Baba Uwani ce riƙe da tsintsiya a hannunta, ta biyo bayan ammi, ta washe baki ta ce “Uwar ɗakina baƙi ki ka yi haka ne?”

Ammi ta waiwaya ta ce “Eh, dama ina nemanki” ta mayar da idonta kan rumaisa ta ce “Rumaisa, ki gaida mini da mamanki, akwai saƙonki a wurin takawa, ki yi haƙuri ki yi ta addu’a kin ji yarinyar kirki” rumaisa kawai jinjina kai ta kasa, ta bi bayansu takawa.

Usman har cikin ransa yake jin babu daɗi kukan da rumaisan ke yi, adam kuwa jinjinawa azababben ƙarfin halin rumaisa yake yi.

Ba wanda ya kuma juyowa tsakanin shi da usman, sai dai suka fita haraba wurin motar da za su hau, sannan suka waiwaya ba su ganta ba.

Usman ya ce “Kaii, ina yarinyar nan ta tsaya kuma?”.

Adam ya ce “Bari na je na duba, ina zuwa “

Ya ja da baya ya koma in da suka biyo.

A zaune ya tarar da ita, bayan wasu bishiyu, ta cukuikuye a cikin hijjabinta, tana kuka mai ɗan sauti kaɗan.

“Ke!” Ya yi maganar cikin tsawa. Ta zabura ta ɗago ta kalleshi, da sauri ta tashi tsaye.

A ɗan ƙufule ya ce “Meye haka muna tafiya zaki ja ki tsaya? Sauri fa nake bani da lokaci”.

Wani mugun kallo ta yi masa ta ce “To ina ruwana da rashin lokacinka, ni fa ba a son raina na zo ba in gaya maka, kuma wallahi babarku tana son bani sabir, kai ne ka dage ka ƙwace mini ɗa, kuma sai ka bani ɗana ko ba ka so, ko kuma ka ga matakin da zan ɗauka”.

Adam ya ƙare mata kallo ya ce “Idan aka baki shi, gaya mini da me zaki shayar da shi? Kalleki fa”.

“To ai dai na ga ba shayar da shi ake yi ba, madara ake bashi, kuma idan na girma na zama babba sosai zan dinga shayar da shi”.

Ya girgiza kai ya ce “An daina ba shi madara yanzu ai, ni nake shayar da shi, tunda na san nesa ba kusa ba, na fiki abun bashi, tashi ki wuce mu tafi”.

Shiru ta yi ta bishi da ido, tana nazarin maganarsa, ta yaya namiji zai shayar da jariri ita tun da take ba ta taɓa gani ba, ko dai raina mini hankali yake?’ ta tambayi kanta.

“Ki tashi mu tafi ina magana kina kallona” ta ji maganar sa cikin tsawa, da sauri ta tashi ta yi gaba ta wuce shi, ba tare da ta waiwayo in da yake ba ta miƙa ta tafi hanyar harabar gidan.

Usman na ganinta ya ce “Ke kuma ina ki ka tsaya, sai da ki ka saka a koma nemanki, wato dai ba ki ji abun da mama ta gaya miki ba ko?” Ta girgiza kai alamar a’a.

“Ba ki ji ba mana, idan muka koma gida sai na gaya mata” ita dai ta yi shiru ba ta ce uffan ba.

Adam ya ƙaraso ya nufo motar, rumaiss kallonsa take ta ga ƙirjinsa a cike yake yadda zai shayar da yaro, amma ta kasa gane komai, kasancewar dogayen kayane a jikinsa.

Adam ya shiga ya kunna motar, usman ya buɗewa ruma baya ya ce ta shiga, amma ya ga ta tsaya cak, ta zubawa gate ɗin gidan ido.

“Wuce mu je” usman yayi maganar yana tunkuɗata cikin motar.

Cikin motar wani irin sanyi da ƙamshin turaren Adam suka cika mata hanci, sai dai ta din ga jikinta wani iri, kamar wani mara daɗi na tunkaro in da suke.

Adam ya kunna motar, ya nufi gate, sai ga motar Jabir ta shigo, jabir ya tsaya dai-dai in da motar adam take ya ce “Yaa ina zaka kuma? Daga gidanka nake”.

“Eh wani muhimmin abu ne ya taso mini”

Samha ta ce “Barka da rana yaya” ɗaga mata kai kawai yayi ba tare da ya amsa ba, ya ce wa jabir “Ka jirani da daddare, zan nemeka in sha Allah”

“Ok, dama na je na kuma yi wa turaki gaisuwa, Samha ta ce idan nan zan taho zata zo ta sake yi maka gaisuwa”.

“Na gode, zan je na dawo yanzu in sha Allah”.

Tun da samha ta sanya idonta a na rumaisa, ta ji wata mummunar faɗuwar gaba da fargaba, kamar ta san idon rumaisa amma ta manta a ina ta santa, gashi ruman ta rufe fuskarta da facemask, ita kanta ruma ba ta san yadda aka yi ta tsare samha da ido ba, ko ƙiftawa ba ta yi, kamar wani abu mai muhimmanci take son ganowa a tattare da Samhan, amma ta kasa gano ko me take son ganowar. A haka Adam ya ja motar suka bar gidan.

Tun da suka fara tafiya, rumaisa ba ta iya cewa komai ba, ras ba ta manta samha ba, sun taɓa haɗuwa, kenan ‘yar uwar su takawa ce ko kuwa oho?.

Har suka ƙarasa gidan turaki, kasancewa tafiyar ba wata ta azo a gani bace, ruma zancen zuci kawai take yi.

Ko da aka buɗe gate ɗin gidan suka shiga, kamar wadda ta farka daga bacci ruma ta ce “Kai, ai na san wannan gidan”.

Usman ya ce “A ina?”

“Ni da hauwwaliya muka taɓa zuwa gidan, wai akwai ƙawarta ana bikin ƙanin babarsu, wata fiddausi sunanta ko jannatu na manta, har na ga waccan da muka gani a motar ɗazu mai bluen kaya, tana ta hantarar mutane ba ta da mutunci, har muka yi faɗa da ita”.

Adam bai ko nuna ya san mai rumaisa take cewa ba, usman ya juyo, yayi mata inkiyar ta yi shiru, amma ina kamar ya tunzurata “Wasu mutanen dai yan uwansu kaɗan ne masu kirki, duk masifaffu ne, ta din ga yi wa mutane tsawa, na fito kawai muka yi karo da ita, wai ke ba kya gani ne, nace eh bana gani, yo ni za ta yi wa gatse, bana son in ga ana wulaƙanta mutane”

“Ke ya isa rufewa mutane baki” usman ya yi mata maganar cikin tsawa,  jan facemask ɗin ta ta yi, ta buɗe motar ta fita, kasancewar tuni adam yayi parking.

Hadimai na ta risunawa, suna gaishe shi, yana ɗaga musu hannu maimakonsa ya amsa, hakan ya ƙara sanya rumaisa jin haushin takawa, tare da ganin yana wulaƙanta mutane.

Adam ya yi musu jagora, har cikin babban falon gidan, nan ma rumaisa ta sha kallo, gidan ya so yayi shige da na su Adam, sai dai na su ya fi kyau sosai a kan nan.

Adam ya ce wa usman “Ina zuwa, bari na shiga na sanar masa da zuwanmu”.

Usman ya ce “To shikenan”

Adam na barin wurin, ya matsa kusa da rumaisa ya riƙe kunnneta ya yi ƙasa da murya ya ce “Dan ubanki me aka gaya miki a gida, wato ke ba a isa a faɗa miki ki ji ba ko? Ki ke ta zuba kina surutu, kina cewa wata ba ta da mutunci ke mutuncin ne da ke?”

Riƙe kunnen ta yi ta fa ƙoƙarin fara kuka, wata mata ta fito ta ce musu “Bisimillah, an yi muku iznin shiga”

Suka tashi suka bi bayan matar. Subhanallah wani irin ƙaton falo ne, ko ina ya sha kilisai da lallausan carfet, sai ƙamshi yake yi.

Daga nesa ta hango dattijon jawurr da shi a zaune, sanye cikin kayansa masu sauƙin nauyi, sai rawani sai dai ya sauke takunkumin fuskarsa.

Maimakon rumaisa ta nutsu, sai ta yi ta kalle-kalle tana kallon abubuwan gidan sarauta da ba ta taɓa gani ba.

Usman ya ce wa dattijon “Barka da wannan lokaci, fatan mun same ku lafiya?”.

Turaki ya jinjina kai ya ce “Alhamdilillah”.

Usman ya sake duƙawa ya ce “Ya ƙarin haƙuri na wannan rashi, Ubangiji Allah ya jiƙanta da rahama, ya bada haƙurin jure rashin”

Turaki ya amsa da “Amin ‘yan samari, madalla Allah ya yi albarka”

Rumaisa ya kalla da take ta kalle-kalle, usman ya zungureta tayi maza ta kalli turaki ta ce “Ina wuni?” Yayi ƙuri yana kallonta, amma bai amsa ba.

Kallonsa tayi, ta kalli adam sannan ta kalli usman, ta kuma cewa ina wuni.

Adam ya risuna ya ce “Tuba take, ba ta san kan gaisuwar gidan sarauta ba, kamar yadda  na yi maka bayani a baya, wannan ita ce wadda ta zo da jaririn wurin marigayiya”. Adam ya ƙarasa maganar yana yi mata alamar ta sauke facemask ɗin ta.

Harar Adam ta yi, ta sake jan facemask ɗin ta, ta rufe fuskarta.

Turaki ya yi mata ƙuri da ido, tsananin kwarjininsa ya sanyata sunkuyar da kai, ta ji kamar jikinta zai hau rawa, saboda kwarjininsa, sun fi mintuna biyar bai ce komai ba.

Adam ya kuma yi mata nuni da ta sauke facemask ɗin ta, amma taƙi sai da usman ya kalleta, sannan ta cire.

Turaki ya cigaba da kallonta sannan ya ce “Iko, sai Allah yanzu wannan ƙaramar yarinyar ce ta ceto yaron wurin fulani”

“Eh Allah ya baka nasara, ita ta zo da shi”

Ruma a ranta ta ce “Taɓ, wanna wace irin wahala ce, da ban cire facemask ɗin ba, kenan haka zamu yi ta zama ba zai yi magana ba?’.

Turaki ya ce “Bamu labari, ya aka yi aka haɗu da fulani, har aka zo mana da jaririnta?”

Rumaisa ta ɗan waiwaya ta ce “Wace fulani kuma?”

“Aisha” Adam ya bata amsa.

Sai ta yi turus, ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Usman ya ce “Ki yi magana mana”

Ta yi shiru ta shiga wasa da ƙasan rigarta.

Turaki ya ƙura mata ido ya ce “Ke muke sauraro yarinyar kirki” ɗaga idonta ta yi tana kallon adam, da ya murtuke fuska saboda ƙuluwa da ya fara yi, da iskancin da rumaisa ke yi.

“Ko su bamu wuri ne?” Turaki yayi maganar yana nuna su adam.

Ta jinjina masa kai alamar eh, ya ce “To babu laifi, takawa a bamu wuri, kar a damu a bamu wuri mu tattauna”.

Takawa bai taɓa zaton iskancin rumaisa ya kai haka ba, ƙin yarda da shi ta yi masa bayanin abun da ya faru, ya sanya yayi zaton a gaban turaki za ta yi bayani, amma mirsisi taƙi magana sai sai ya fita.

Ganin yadda adam ya harzuƙa, ya sanya turaki yi masa alama da ya kwantar da hankalinsa.

Sai dai ba iya adam ɗin ne ya ƙulu ba, har usman ya ƙule da abun da rumaisan ta yi.

Haka suka tashi suka bar falon.

Turaki ya mayar da kallonsa ga rumaisa ya ce “Matso kusa da ni nan ki yi mini bayani”

Rumaisa ta ɗan ƙara matsawa daf da shi, ta hango hoton aisha a bayansa, ta ƙurawa hoton ido, da har sai da turaki ya waiwaya ya kalli hoton.

Ya ɗauko hoton a hannunsa, ya shafa shi ya ce “Kin ganta nan, a cikin ‘ya’ya na kusan goma sha rayayyu da wanda suka rasu, babu wadda nake jin daɗinta nake zartar da hukunci komai ɗacinsa ta karɓa sai Aisha. Na tafka babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba, Allahn da ya bani ya fi ni son ta, ban so ta mutu a wulaƙance haka ba, sai dai ba zan zargi sirikina ba, ɗana ne shima, kuma ba zai cutara da aisha ba”

Rumaisa da hawaye ya fara zubo mata ta ce “Tabbas anty aisha tana da kirki, kowa cewa yake yi bana jin magana, amma ita ta fara cewa rashin ji na yana burgeta. A makaranta bana gan karatu, amma ta ce mini mai kaifin basira ce ni, ta yi ta kula da ni a hannun ‘yan bindiga kan ta rasu, amma mijinta ne ba shi da kirki ko kaɗan, shiyasa naƙi magana a gabansa”.

Turaki ya yi murmushi ya ce “Tabbas takawa yana da zafin rai, amma mutumin kirki ne sosai”.

“Na san a ƙule yake da ni, yanzu ba dan kai ba tsaf sai ya zaneni a wurin nan, ita rayuwa idan mutum yana son ya ci ribar abu ba haƙuri ake a bishi a sannu ba? Idan haka zai din ga yi komai ya tunkara sai ya faɗi. Kuma dai naga ɗan sanda ne shi, mai ya hana ya kai mana agaji lokacin muna hannun ‘yan bindigar, da bakinsu fa suka ce jami’an tsaro ne suke basu gudunmawa, to yanzu kuma dan Allah me zai yi bayan mai faruwa ta faru”.

Zuba mata ido kawai turaki yayi, yadda take zaro magana, tana arranging ɗin ta, tamakar tana karantowa, kuma ba zaka taɓa cewa yarinya ce mai kamar shekarunta take faɗa ba.

Ya gyara zamansa ya ce “Haka ne, kema kin yi magana mai kyau, amma yanzu dai ina jin ki”.

“Baba”

Ya ce “Na’am yarinyar kirki”

“Amanatun amana, zan gaya maka komai, gani ake ni Yarinya ce amma ina da wayona, ta ƙarfin tsiya fa ya ƙwace mini ɗa, ko tausayina ba ya ji alhalin anty aisha ta ce ta bar mini shi halak malak. Zan gaya maka komai, amma shi ba zan gaya masa ba, kuma wallahi na san abubuwan da shi bai sani ba”.

Duk girman turaki, ruma ta iya kallonsa ta ce masa amanatun amana, tare da yi masa kashedin, kar ya gaya wa kowa abun da za ta gaya masa.

Ƙwarin gwiwar ta, da rashin tsoronta a ƙananun shekarunta ne ya fi bashi mamaki, kuma tsara zancenta da kaifin basirarta ya burge shi.

Ya ce “Kar ki damu, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai ke sai Allah”.

Nan rumaisa ta gyara zama ta fara yi masa bayanin abubuwan da suka faru, duk a hirarta ta ya fuskanci ba komai ta gaya masa ba, amma a hakan ta yi ƙoƙarin yi masa duk wasu bayanai da yakamata ya sani, sai dai kan ta kammala, hawaye ya wanke mata fuska, sai gogewa take da hijjabinta.

Shi kansa turaki kasa jurewa yayi, cikin dabara ya goge hawayen da yake shirin zubo masa, yana jin labarin wai-wai a kafafen watsa labarai, bai taɓa zaton masifa da tashin hankalin ya kai haka ba, kuma ta bakin rumaisa ne idan aka fara haɗawa da ‘ya’yan masu faɗa a ji ana sacewa wataƙila a mayar da hankali a kan maganin abun, kuma abun kunya ne ga jami’an tsaro, ace an sace matar jami’in tsaro kuma an kasa ceto ta har ta rasa ranta.

Uwa uba azabar da rumaisa ta sha kan ta fito da jaririn, shi kansa ya isa abun tausayi duba da ƙananan shekarunta, gashi sai nanatawa take ita fa aisha ta bar mata ɗa, amma adam ya ƙwace mata.

Ya duba gefen sa, ya ɗauko wani handkerchief mai matuƙar kyau da taushi, sai ƙamshi yake yi, ya miƙawa rumaisa ya ce “karɓi nan ki goge hawayenki, kukan ya isa haka”.

Karɓa ta yi, amma ta kasa gogewar, saboda kukan da ya ci ƙarfinta.

Usman kuwa ba ƙaramar mita yayi ba, a kan abun da rumaisa ta yi, tun da suka fito yake mita.

“Ban taɓa ganin yarinya mai azababben taurin kai, na tashin hankali kamar rumaisa ba, gaba ɗaya yarinya kamar wata majanuniya, ita duk wata hanya ta masalaha ba ta santa ba, idan ta akasin masalahar ma aka biyo mata ta fi misbehaving, ba a gane gabanta da bayanta kamar ɗan wake”.

Adam kam azabar takaici, bai bari ya iya tankawa ba, gani yake gaba ɗaya yarinyar ta gama raina masa hankali.

A nutse turaki ya din ga rarrashin rumaisa, yana yi mata nasiha, har sai da ya sanya ta ɗan yi murmushi ta ce “Baba ka iya magana a nutse wallahi, ni yadda kake magana ma daɗi yake yi mini”

Abun da ta faɗa ɗin sai da shi ma ya sanya shi murmushi, ta kai handkerchief ɗin da ya bata fuskarta,

Ta lumshe idonta ta ce “Wayyo ƙamshi, baba ban taɓa jin turare mai daɗin wannan ba, kamar na suma dan daɗi”.

Jan rawaninsa yayi ya rufe fuskarsa, dan dariya rumaisa take neman ta saka shi.

Hadimai ne suka yi sallama, suka shigo masa da kwanukan abinci a kuloli da kuma akushi, aka zo aka jere su a gabansa.

Rumaisa ta dinga kallon fulasai na alfarma.

Turaki ya ce “Ga abinci nan, buɗe a ciki ki zaɓi wanda ki ke so ki ci”.

“A’a na ƙoshi, mama ta hanani cin abinci a waje”.

“To ai nan gidanku ne, ki ci duk abun da ki ke so”.

Ta nuna masa akushi ta ce “Wannan menene?”.

Ya ɗauko akushin ya ajiye a gabanta ya ce “Sunansa akushi”.

“Akushi da rufi, sai sarki, kenan kai ma sarki ne?”

Ya girgiza mata kai ya ce “A’a, ni ba sarki bane ba”.

“To dama ba duk masu rawani ba sunansu sarki ba”

Turaki ya murmusa ya ce “A’a ba kowane mai rawani ne sarki ba, kowa akwai sunan muƙaminsa”

Ruma ta din ga kallon akushin nan, ta saka hannu ta buɗe, ta ga dubulan fal a ciki” tayi iya ƙoƙarinta wurin tuna sunan sa amma ta kasa ta ce “Mmm ya ma, abun da ake kaiwa idan an yi aure mai sugan nan sunan shi kenan”.

Ya kuma miƙo mata wani akushin, ya ce “Gashi nan, duk duba ki ci wanda ki ke so”.

Ta bubbuɗe kulolin nan, wata irin miya ta alfarma, ta sha naman kaza yanka manya manya. Ta ce “Mama ta yi mini kashedi a kan banda rashin ji, kuma idan na yi wani rashin ji, yaya usman ya gaya mata zaneni za su yi”.

Turaki da bai ji ya gaji da surutun rumaisa ba, kuma bai jin zai gajin ya ce “Ki ci ba zan gaya masa ba, ba zata sani ba”.

“Hmm ba ka san halin mama ba, yaya usman sai ya gane, amma dai bari na ci wannan”.

Ta saka hannu ta ɗau dubulan, ta fara ci, dama rumaisa gata mayyar suga, tana ci tana lashe baki.

Kallon rumaisa kawai yake yana murmushi, yarinya ce ƙarama, ita a yanzu babu abun da yake damunta, sai dai ta yi ciye-ciyenta ta faɗi abun da take ji a ƙwaƙwalwarta shi ne dai-dai, sai dai yanayin yarinyar ya nuna ba za ta yi ƙarya ko ha’inci ba, kuma tana da ɗan karen wayo.

Hajiya Sauda ce ta shigo, sai dai ta yi turus, ganin yarinya zaune a gaban turaki tana cin abinci a kwanonsa, duk da ta bawa ƙofa baya, ba ta iya sanin kowacece ba.

“Mai girma turaki wannan kuma wacece? Meyasa take cin abinci a kwaonka, kwanon da ko ‘ya’yan cikinka ba su da wannan damar”.

Ɗan turus rumaisa ta yi, amma ba ta waiwayo ba, ta kuma miƙa hannu, ta ɗauko alkaki, tana taunawa tana jin zaƙin sugan har cikin kunnuwanta.

Turaki ya ɗaga kai ya kalli mama ya ce “Baƙuwata ce?”.

“Baƙuwarka kuma kamar yaya kenan?”

Ya kalli rumaisa ya ce “Yarinyar kirki, je ki ki kirawo mini takawa”

Rumaisa ta miƙe ta ce “To baba”.

Sai a lokacin ta juyo suka yi ido huɗu da mama.

Rumaisa ta wani lumshe ido, ta ce “Ina wuni”. Kallon banza ta yi wa rumaisa, ta ji gaba ɗaya yarinyar ba ta yi mata ba, idonta kawai zaka kalla ka gane tattacciyar mara kunya ce.

Rashin amsawar ta ta bai ɗaɗa ruma da ƙasa ba ta fita falon.

Usman na ganinta ya harareta, sai dai bai tsinke da lamarin rumaisa ba sai da ya ga tana lashe hannu tare da gutsurar wani abu a hannunta.

“Kar dai yarinyar nan ciye-ciye ta je ta zauna ta na yi? Ya tambayi kansa.

“Wai ka zo in ji baba mai rawani” ta yi maganar tana kallon adam ba tare da ta kama sunansa ba.

Bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da danna wayarsa.

“Magana nake maka, ana kiranka”

Still bai amsa mata.

“Takalmawa ake ce maka ko me?, sunanka dai Adamu ba wani Adam ba to ka zo in ji baba mai farin rawani”

Wata irin tsawa aka bugawa rumaisa, wadda sai da ta tsorata, ta kusa faɗuwa!

A razane ta waiwaya tana kallon in da aka yi mata tsawar, wasu dogarai ne su biyu suka shigo suna baza riga, shigowar ta su yayi dai-dai da lokacin da rumaisa ke gatsali da sunan takawa.

“Hattara dai yarinya, hattara ‘yar talakawa, ba a furta wannan sunan hakan babu girmamawa”

Ɗayan ya juya ya kalli Adam ya ce

“gaba salamun baya salamun, takawarka lafiya magajin saraki, basarake ɗan basarake jikan basarake, mai babban suna, takawa magajin takawa, motsawarka lafiya ɗan gidan giwar galadima jikar fulanin gombe, ayi mana izinin bata horon yadda ake girmama wannan suna”.

Adam ya girgiza kai, tare da ɗaga musu hannu, ɗan risuna masa suka yi, sannan suka nufi sashin turaki, dan neman iznin shiga wurinsa.

Rumaisa ta ce “Yau na ga masifa, to naga annabawa ma ana faɗar sunansu, sai sunan wani mutum gama gari ace ba za’a faɗa ba, taɓ kun haɗu da wahala, wai wani ƴar talakawa sai ka ce su masu kuɗi ne”.

Usman ya ce “Dan Allah maiyasa ba ka saka sun ɗagata sun zaneta da bulala ba? Wataƙila a samu hankali ya shigeta”.

“Yaya usy ai ni yanzu na wuce duka yasin, sai dukan ruwa bari na je na gaya wa baba mai rawani ka ce ba zaka zo ba” ta wuce ta koma wurin turakar turaki.

Dogaran nan ta tarar a tsaye, suna jiran iso, amma ta zo ta saka kai zata shige.

“Ke! Ke hattara dai, tsaya a nan ina zaki ba ayi miki iso ba?” Ai ba ta ko tsaya ba, ta daka tsalle ta shige da gudu, ta tsaya tana jiran ko zasu biyota.

“Wallahi tura ta kai bango, abubuwan da ka ke aikatawa sun isa haka, kai ko kunya ma ba ka ji? Ka mayar da ‘ya’yanka ba komai ba, sai guda ɗaya shiyasa Allah ya kasheta a wulaƙance, saboda zaluntar ‘ya’yanka da kake yi, kuma idan ba ka yi wasa ba, kuma ba ka nemi afuwar yaranka ba, kaima a yadda ta mutu haka za ka mutu.

Ka binne wa mutane gaskiya, kun haɗa kai da giwa da ɗanta sai rainawa mutane hankali ku ke yi, tayaya za ace wannan yar yarinyar ce ta dawo da jariri, ta yaya aka tabattar ɗan aisha ne, wataƙila ma wani abun suka ƙulla, ya haihu da wata aka kashe aisha aka kawo yaron a matsayin nata, ba abun da ba zai iya faruwa ba, tun da dai ‘yar ka ce ba tawa ba, matsalar ku ce”

Turus rumaisa ta yi tana bin Hajiya saudat da ido, ta gama zubarta, ta nufo hanyar fita, cikin tsawa ta cewa rumaisa “Ke kuma ban hanya ko na yi gaba da ke” maimakon rumaisa ta matsa, sai ta tsaya tana ƙarewa ƙwayar idon mama kallo, ba tare da tsoro ko shakka ba.

Babu tsammani, rumaisa ta ji an ja ta gefe, an bar hanyar da mama zata wuce.

Hajiya sauda ta yi wa adam wani mugun kallo, ta fice. Rumaisa ta ƙwace hannunta, ta ƙarasa gaban turaki ta ce “Baba, mai ya sa ka tsaya matar nan take maka masifa, kai ba sarki bane ba? Ai ba a ɗagawa sarki murya in ji mama, haka ta ce mini kan mu zo nan”

Turaki ya ce “Yarinyar kirki, sarki a waje yake sarki, amma wani sarkin a gida bawa ya fishi power, kar ki damu zaki gane me nake nufi ” ya kalli Adam ya ce “Takawa, Biliyaminu nan sun kawo saƙon ‘ya ta, ba sai sun ganni ba, na ta ne a kai mini ita har gida, Allah ya yi miki albarka”.

Rumaisa ta ce “To baba dan Allah ka saka baki ya bani ɗana sabir, kaga na gaya maka anty aisha ta bar mini shi wallahi, amma ya ƙwace mini shi, kar na kai shi kotu ne a ga kamar ban kyauta ba, kuma ina ganin girmanku kai da mamansa, amma da wallahi nima kotu zan kai shi wurin alƙali, wata a unguwarmu ta taɓa bawa mama labari wai a kotu an ƙwato mata ɗan ta daga wurin mijinta an bata”

Turaki ya girgiza kai tare da murmushi ya ce “Subhanallah, ba za ayi haka ba, ai mu yanzu mun zama ‘yan uwa, za a duba lamarin in sha Allah, saƙonki yana mota Allah ya tsare”.

Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce “To na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi Allah ya sa ka zama sarki, ka zama shugaban ƙasa baba”

Sunkuyar da kai turaki yayi, yana rife fuskarsa da rawani, dan sha’anin na rumaisa ba ya ƙarewa.

“Wuce mu tafi ina da wurin zuwa” Adam yayi maganar a kausashe.

“Ai ko ba ka ce ba zan tafi, ba sai ka kaɗani kamar wata akuya ba” ta yi maganar tana ficewa waje.

Tun da ta fito usman ke cigaba da aika mata harara ko ta ina, amma ta yi kamar ba ta gani ba, haka suka fita suka hau motar takawa.

Suna tafe a hanya, babu wanda ya kula rumaisa a cikinsu, usman ya ce wa Adam “Ina ga idan muka ƙarasa titi ka ajiyemu, sai mu samu abun hawa mu ƙarasa gida”.

Adam ya girgiza kai ya ce “A’a zan kai ku gida, akwai kaya ma, ba zai yiwu in ajiyeku a hanya ba” daga haka suka ɗan shiga taɓa hira suka cigaba da tafiya.

Tafiyar su takawa babu daɗewa, Samha ta dawo, har ta shiga ɗakinta ta canza kaya ta fito, ba ta ga gilmawar mama ba, dan haka ta bita ɗaki.

Ta iske mama na ta ƙananun maganu, da mita.

“Mama, wai baki san na dawo ba? Ke da waye ki ke ta mita haka ne?”.

“Ba dole na yi mita ba, ubanku na nema ta ƙarfin tuwo ya mayar da ni mahaukaciya”.

“Ohh mama, kullum cikin case da Alhaji, yakamata ku daina zuwa yanzu”.

“Ke dalla rufe mini baki, mai za a fasa? Ai yanzu aka fara ma ba ayi komai ba, na rasa abun da yake shiryawa da shi da adam, sai ɓoye-ɓoye suke yi, da rainin hankali wata shu’umar ‘ya ya kawo masa, wai ita ta dawo ɗan wurin aisha daga hannun ‘yan bindiga”

Cikin rashin fahimta samha ta ce “Yan bindiga kuma, wasu ‘yan bindigar kenan kuma? Ba a can in da take karatun aka ce ta haihu ba? To meya kawo ƴan bindiga ban gane ba”.

Hajiya Sauda ta yi ajiyar zuciya ta ce “Ke, adam wani abun yake shiryawa, aisha ba wani a ƙasar da taje karatu da ta mutu, a hannun’yan bindiga, da suka yi garkuwa da ita, ta haihu ta mutu a wulaƙance ko gawarta ba wanda ya gani, waya sani ko shi ya cinyeta ko ya kashe ta yayi tsafi da gangar jikinta”.

Cikin rashin fahimta samha ta ce “Mama kin yi wa kwanyata dabaibayi da zantukkanki, na gaza fuskantar ko da guda daga ciki, ki yi mini bayani gwari-gwari. Ƴan bindiga ne suka bi ta can suka sace ko kuwa?”.

Nam mama ta fayyacewa samha komai, duk da gargaɗin da turaki yayi mata a kan hakan.

Salati samha ta yi, tare da tafa hannuwa cike da tsananin mamakin sarƙaƙiya da ruɗanin lamarin, a fili ta ce “Oho musu, ko ma dai yaya ne, a wannan karon nasan babu abun da zai hanani mallakar takawa”.

Sheƙeƙe mama ta kalleta ta ce “Wai ke samha wace irin mara zuciya ce ne?, Au ke yanzu duk abun da ya faru da ke a baya, da irin cin kashin da yayi miki baki haƙura da batunsa ba?”

“Dan Allah mama karki ce komai, wallahi ina son sa haryanzu kuma abun da ya faru, ya riga ya wuce, dan Allah kiyi haƙuri ki bani goyon baya a wannan karon na auri adam dan Allah”

“Kin ga tashi ki je, ina da abun yi yanzu”.

Samha ta haɗa hannayenta biyu cikin magiya ta ce “Please mama”.

“Na ji, amma jeki yanzu, ki bari na yi tunanina” Samha ta tashi ta bar ɗakin mama, tana ta nazari da zancen zuci a kan abun da maman ta gaya mata.

Nusaiba ce ke ta bawa iman labarin rumaisa, da abun da ya faru ɗazu da suka zo, zasu je gidan turaki.

Iman ta ce “Allah sarki, na ji ina son ta tun ban ganta ba, ai mu duk mai son waninmu muna son shi”.

Nusaiba ta ce “Ke kin ganta, wallahi yarinya ce sosai, dan ba ta kaimu ba ma ko kaɗan, na yi mamakin yadda ta iya tsira da sabir”.

Iman ta ce “Ai babu mamaki a cikin lamarin Ubangiji, babu abun da bau iya ba”.

“Gaskiya ne, amma wai ya maganar uncle J ne, kun kuma magana da shi?”

Haushi ne ya kama iman ta ce “Dan Allah ki rabu da ni da wani uncle J”

“Dole na yi miki maganarsa, ke ma kin san rasuwar nan ce ta hanashi cigaba da bibiyarki, ina son nema miki mafita ne, idan ya je ya biyo ta saman fa kamar yadda ya gaya miki?”

Iman ta ɗan yi jimmm sannan ta ce “Bakomai, Allah ya fishi, mu bar maganar nan sai wani lokacin*.

Lura da yanayin yadda iman ba ta son zancen, ya sanya Nusaiba jan bakin ta ta tsuke.

Rumaisa kuwa bayan kayan takaicin da ta turawa su usman, suna tafe a mota tana yi musu waƙe-waƙe, tayi wannan waƙar ta saki ta kama wata, gashi galibin waƙoƙin na indiya take yi, sam ba ta san ma me suke faɗa ba, kawai dai tana yi ne, kuma cikin ikon Allah daga usman har takawa ba wanda ya tanka mata har suka ƙarasa gidan rumaisa.

Usman ya kalli Adam ya ce “Mun gode ƙwarai da gaske Allah ya saka da alkhairi”.

Adam ya ce “Bakomai, ni ne da godiya ai”.

“Hmm ai Yakamata in ƙara ma da baka haƙuri, a kan abun da rumaisa ta yi, ka yi haƙuri dan Allah” Adam yayi Murmushin gefen baki ya ce “Kar ka damu, akwai saƙonta a mota amma, bari na buɗe booth ɗin”

Ruma buɗe motar tayi, ta ruga da gudu cikin gida tana kwaɗa sallama.

Kaya ne fal a booth ɗin Adam, da wanda ammi ta bawa rumaisa da wanda turaki ya bayar a bata.

Usman ya ɗauka ya yi wa Adam godiya suka yi sallama ya ce a gaida mama.

Ko da ya shiga gidan, rumaisan ya tarar har ta tuɓe kayanta tayi ɗai-ɗai wai ta gaji.

“Dan ubanki ni bawanki ne? Da zaki bar ni da kwaso miki kaya dan baki da kunya?” Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ganin irin kallon da yake yi wa rumaisa ya sanya sanin cewa akwai abun da rumaisa ta yi.

“Usman, ya aka yi ne? Kun je ɗin?”

“Eh mun je, amma ba ta sauya zani ba, ta yi iya shegen na ta da ta saba”

Mama ta kalli rumaisa ta sake kallon usman ta ce “me ta yi?”

Nan ya gaya mata iskancin da ta din ga yi, mama ta girgiza kai ta ce “Wai rumaisa me bawan Allah nan yayi miki da ki ke yi masa wannan rashin mutuncin? Duk jan kunnen da na yi miki ba ki ji ba kenan?”

“Mama na faɗa komai fa”

Usman ya ce “To amma meye na cewa sai mun fita, a matsayin sa na mijinta yafi kowa buƙatar sanin meyafaru da ita”.

Mama ta ce “Meyasa baka kama mini ita ka zaneta ba”.

Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce “Ai kin san wasu lokutan sa’a ce da ita, daga zuwanmu ta dinga zuba tana yi wa dattijon shishshigi tana ce masa baba,  aikuwa ya dinga biye mata, saboda sakarci har da ci masa abinci a gabansa”

Huzaifa da yake banɗaki yana jin hirarsu, yana fitowa ya ce “Sai ka ce mayya daga zuwa baƙunta ki hau cin abinci”

Aikuwa ta ce “To zigazigi wutar maƙera, mai zuwa lahira da ƙoƙon dambu waya kasa da kai gwanin na iya”.

“Kin rufe mini baki ko sai na taushe shegen bakin naki”

“Wallahi mama ni ban ci abinci ba, wannan abun na kayan gara mai kamar kashin nan da suga shi kawai na ci”.

A fusace mama ta ce “Ni rufe mini baki, bera kawai” haka ta koma ta tura baki tare da jin haushin yadda kowa yake caccakarta.

Adam sai da ya fara biyawa yayi sallar la’asar, yana komawa mota ya tarar da missed calls ɗin Bashir.

Bin kiran yayi, bayan bashir ya ɗaga sun gaisa ya ce masa akwai issue, su haɗu a wani wurin cin abinci bayan sallar isha’i.

Adam ya amsa masa, ya yanke shawarar fara zuwa gida, kan lokacin sallar isha’i sai su haɗu da Bashir.

Ko da ya je gida, Ammi ta din ga tambayarsa yaya suka yi, da fari basarwa yayi, da ammi ta matsa ya gaya mata cewar rumaisa ba ta yi magana a gabansa ba sai da ya fita.

Ammi ta yi shiru ta ce “Wai ni anya Adam babu wani abu a tsakaninka sa yarinyar nan ƴar tsamar da ku ke ta yi yawa, ta rainaka da yawa”.

Ya girgiza kai ya ce “Ni ban santa ba sai a dalilin abun nan da ya faru, dan haka ni babu komai a tsakanina da ita”

“To, amma ina kyautata zaton akwai wani abu mai muhimmanci a bakinta, tun da taƙi faɗa a gabanka”.

“Haka nake tunani nima, amma zan koma wurin turaki, sai mu yi magana”.

“To shikenan, Allah ya yi jagora”

Ya amsa da amin.

Kamar yadda suka shirya, suka haɗu da Bashir a wurin cin abinci, ya tambayi adam mai za a kawo masa ya ce ba ya jin yunwa.

Bashir ya ce “A’a ba zai yiwu ba, sai ka ci abinci ko na koma da labarin da na zo da shi”.

Da ƙyar adam ya yarda a kawo masa chips, bashir ya din ga yi masa hira, tare da gaya masa ya kusa komawa abuja wurin aiki.

Adam dai bai iya tankawa ba, jira yake kawai ya ji me Bashir zai ce masa.

“Wai ni kuwa ya ake ciki da maganar binciken da ka ke yi ne, na mutanen nan mutane hukuma fa suke jira, su ji sakamakon binciken ku, gashi wa’adin da kwamitin da gwamnati ta kafa ya cika ya wuce, amma ba su ce komai ba, kaima kuma kun yi shiru.

Adam yayi ajiyar zuciya ya ce “Bashir, sawun giwa ya take na raƙumi ai, ƙasar da ba ta damu da halin da al’ummarta suke ciki ba, tayaya zan cigaba da wahalar da kaina, a hukumar tamu ma kana gani sun rabu biyu, wasu suna goyan bayanmu wasu ba sa yi, a ƙasa kuwa talakawa ne kawai suke supporting ɗinmu. Ni yanzu hankalina yafi karkata ga binciko wanda suke da hannu wurin sace matata, dan a jikina nake jin na jikina ne”.

“Kenan kana nufin zaka fito ka cewa duniya sace matarka aka yi, bayan an gama jita-jitar a ƙasar waje ta zo haihuwa ta mutu?”

“Bashir dole hakan zan yi mana, ba zan bar mutuwar aisha ta tafi a banza ba, ko da haka yana nufin zubewar kimata ne a idon duniya”.

Bashir ya jinjina kai, ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ya ɗan daddana sannan ya miƙawa adam.

Adam ya karɓa ya fara dubawa, shafin wata jarida mai suna ciki da gaskiya ya buɗe masa.

Yana shiga ya ci karo da hotonsa, tittle ɗin labarin aka rubuta dara ta ci gida.

Shahararren jami’in tsaron nan na farin kaya, mai jagorantar wata tawaga da ta zama babbar barazana ga manya ɓarayin ƙasarmu, ko kuma dai ace, shugabannin da yake yi wa sharrin sata, wato Adam Sharif Galadima. Kwanaki kaɗan bayan kamala zaman makokin mutuwar mai ɗakinsa, An bankaɗo wani babban al’amari game da shi, in da lamarin mutuwar matarsa ya sha ban-ban da abun da aka sanar game da rasuwar ta ta, ashe ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da mai ɗakinsa, har ta haihu a hannunsu, daga ƙarshe ta rasa ranta.

A wata majiyar kuma, aka ce da sanya hannunsa a yin garkuwa da matar ta sa in da ya kasheta yayi tsafi da gangar jikinta, kwatsam wata yarinya ta zo da jariri a zuwan ɗan matarsa ne, duk dan a ɓatar da hankalin mutane, da tunaninsu daga kan zargin shi wannan zaƙaƙurin bawa da yake jin cewa ya fi kowa gaskiya da adalci, masu bibiyarmu ko menene ra’ayinku game da wannan labari?!

Hannun adam har rawa yake yi a lokacin da ya kammala karanta labarin, wani irin wahalallen gumi ya din ga tsatstsafo masa, ya aka yi maganar nan ta fita? Waye ya yi masa wannan yankan bayan?.

Jiki na rawa ya ajiye wayar, ya miƙe tsaye, jin kansa ya fara sarawa, yana neman rasa nustuwarsa, bashir ya tashi zai yi masa magana, amma tuni adam ya sulale ya bar wurin.

Kafin ya cimmasa, ya hau motarsa yayu mata key, ya fice daga restaurant ɗin da gudu.

Gudu yake sosai a kan titi, Bashir ya hau motarsa ya bi bayansa, amma ya kasa cimmasa.

Ko da Adam ya ƙarasa gida, wani irin horn ya din ga yi kamar tashin hankali. A gigice masu tsaron ƙofar suka buɗe masa gate ya shiga da motar, ko da ya fito ko rufeta bai yi ba ya wuce sashin Ammi.

A can cikin gidan kuwa, bayan sallar isha’i, wata hadima ta shiga ta sanar da ammi cewar mummy na son ganinta.

Mamaki ne ya cika ammi, meya kawo mummy a wannan lokacin? Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta tashi ta fita falonta, ta tarar da mummyn tare da autarta ruƙayya.

Ta kalli ammi ta yi murmushi ta ce “Barka da warhaka giwar mata”.

“Barkanki dai, kuna lafiya?”

“Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?”

Ammi ta amsa da “Alhamdilillah”

“To Allah ya jiƙanta da rahama”

“Amin ya rabb”

Mummy ta gyara zamanta ta ce “To, ni dai giwa idan wani abun na yi miki dan Allah ki yafe mini, ban san me na yi miki haka ba, ai ko ban samu shigowa ba, ya kyautu a ce kin aika mini jaririn na gani, nima jiakana ne, amma har su Fauziyya suka zo aka hanasu jaririn, yaran nan ko muna so ko ba ma so tsatsonsu ɗaya fa, wannan abun babu in da zai kaimu, ni dai ki yafe mini, amma a bani yaron na ganshi”

Ammi ta ɗan dubi mummy, kamar ba a wurin zaman makoki suka din ga yi da ita a gabanta suna yasar mata da maganganu ba, ta basar ta ce “Bari a kawo shi ki ganshi” tayi maganar ba tare da ta tanka wancan maganganun da ta yi da fari ba.

Iman ce ta ɗauko sabir, ta kawo wa mummy shi, ta sanya hannu ta karɓe shi, tana wani irin murmushi ta ce “Tubarkallah masha Allah, wannan yayi wayo sosai, sai dai ni kasa gane ma da wa yake kama a tsakanin aishar da takawa”

Ammi kawai ta kalleta ba ta ce komai ba.

“To wane sunan aka saka masa?”

“Mahmud, ana kiransa sabir”.

Da sauri Mummy ta kalli Ammi ta ce “Mahmud kuma? Sunan Mahmud ya ci kenan?”

Ammi ta ce “Eh, sunansa ya mayar masa”

Mummy za ta yi magana, Adam ya faɗo ɗakin kamar wanda ya ƙwato a hannun miyagu.

Tun a falon ya fara ɓalle rigarsa, saboda wani irin gumi da yake yi, ƙafafuwansa kamar ba zasu iya ɗaukarsa ba.

A gigice ammi ta tashi ta bi shi tana kiran sunansa, sai dai bai iya tsayawa ba, Mummy ma tashin ta yi ta bi bayansu, tana tambayar ko lafiya.

Kan gadon ammi ya haye, jikinsa ya fara wannan mazarin, kamar wanda ake bugawa gangi.

A gigice ammi ta ce “Iman, ɗauko maganinsa maza”

Da hanzari iman ta fita ta bar ɗakin, ammi Cikin damuwa ta ce “Takawa meyafaru ne? Meyake damunka?” Bai amsa mata ba, sai runtse idanuwansa da ya yi.

Iman ta dawo da jarkar maganin da ake shafa masa, ta buɗe ta tsiyayo, ta fara ƙoƙarin shafa masa, amma ya juya kansa ya ce “Kar ki shafa mini, a hayyacina nake, jikina zai daina rawar ne, ku lulluɓeni” duk yadda ammi ta so shafa masa ƙin yarda ya yi, sai lulluɓe shi da aka yi.

Bin maganin da kallo Mummy ta din ga yi, sannan ta ce “Wai giwa harzuwa wani lokacin zaki bar yaron nan ya cigaba da rayuwa da wannan larurar ba tare da kin nema masa magani ba?”

“Ina iya ƙoƙarina, Allah ne bai kawo ƙarshen abun ba”

“To kina zaune Allah za kawo ƙarshen lamarin, shi meye wannan ɗin da ake shafa masa?” Ganin ammi ba ta bata amsa ba ya sanya iman cewa “Magani ne”

“Miƙo mini na gani” ta yi maganar tana tsare iman da ido, iman ta ɗauka ta miƙa mata, ta karɓi jarkar ta din ga jujjuyata, tana nazartar meye a ciki, amma ta kasa ganewa, ta ajiye robar ta ce “Shikenan, ga wannan yaron, amma akwai buƙatar ki miƙe tsaye fiye da da, ko kuma ya dauwwama cikin nakasa” kamar dai ɗazu, a yanzun ma ba ta samu amsa daga ammin ba.

Bashir kuwa tun da ya ga Adam ya ɓace masa, ya haƙura ya koma, dan bashi da tabbacin in da zai nufa ya bi adam ɗin, kuma ya kira shi bai ɗaga wayarsa ba.

***

Rumaisa kuwa zazzage kayanta ta yi da aka bata, na wurin Ammi da na turaki. Turmi biyar ammi ta bata na atamfar tare da turare mai ƙamshin gaske.

Turaki kuma ya sanya an cika mata ledoji da kayan dubulan, da uban kilishi fal da soyayyen naman kaza, sai kuma turaruka, ga kuma nono mai kyau kusan galan guda da man shanu. Ruma ta din ga yashe baki tana murna.

Mama ta ce “Eh dole ki yi murna mana, a dalilinsa kin samu iyayensa sun yi miki sha tara ta arziki ke kuma kina yi wa ɗan su rashin mutunci”

Ruma a ranta ta ce “Hmm mama ba zaki gane bane ba, baki san girman laifin da mutumin nan yayi mini ba, sai na tabattar masa da abun da na gaya masa ai” mama ta yi ta mita, amma ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai ma tunanin gobe in Allah ya kaimu za ta koma makaranta abun da ba ta so.

Sai da ta zo kwanciya barcci, sannan wata irin kewar sabir ta sake kamata, ta rungume fulonta, ta rintse idonta, ta din ga hango fuskarsa yana kallonta yana lumshe idonsa.

Kamar an kunnawa zuciyarta wuta, haka ta din ga jin wata irin ƙishirwar son sake ganin sabir, tamkar ta yi tsuntsuwa ta tashi. Ta sake rintse idonta, tana sake tuna yadda take kwana gata sabir a asibiti, ganinsa da ta yi yau ta sake jin du rintsi duk wuya sai an bata ɗan ta.

Haka kurum ta hau kuka, tana sake jin tsana da haushin adam a zuciyarta, a ganinta duk shi ya ƙulla a ƙwace sabir a hanata shi.

Cikin ikon Allah, takawa ya farfaɗo gaba ɗaya, ammi ta saka shi a gaba ta din ga tambayarsa a kan meyafaru har ya shiga wannan yanayin.

Ya ɓoye yaƙi gayawa ammi dalili, ya ce mata bakomai, kamar kullum ta din ga yi masa nasiha tare da fatan Allah ya bashi lafiya da mafita a kan lamuransa.

Washegari da safe rumaisa kamar ta saka kuka, mai sunan baba ya kafa ya tsare, ya sanya rumaisa a gaba ta shirya cikin uniform ɗin ta da suka sha guga, kamar ta fashe saboda takaici, ba ta son makarantar nan, ya sakata a gaba ya tafi kaita makaranta.

A ofishin shugaban makarantar ma, sake jajantawa rumaisa abun da ya sameta malamai suka yi, suka yi mata barka da dawowa tare da fatan Allah ya sanya ta nutsu zamanta a hannun ƴan bindiga ya zame mata darasi.

Gaba daya hankalinta ba ya kansu, tunaninnta kawai yadda za ta ga sabir, mai sunan baba ya gama clearing ɗin abun da yakamata, aka ce ta tafi aji, amma ajin baya zata koma saboda an riga an yi mata nisa a karatu.

“Kaii repeating aka yi mini, kenan ba zan yi candy da wuri ba, taɓ wallahi ba…” Gum ta rufe bakinta ba ta ƙarasa maganar ba, saboda kallon da mai sunan baba yayi mata, tana ji tana gani aka mayar da ita ajin baya.

A ranta ta ce ‘Wallahi ba zan zauna a ajin baya ba, sai a zata ma daƙiƙanci ne ya saka aka yi mata repeating”

Da aka fita break, ƴan ajinsu da suka yi gaba, suka din ga tsalle suna murna, rumaisa ta dawo.

Sam ta ƙi shiga sabgar kowa, ta ɗau littafinta ta din ga zana hoton sabir a bayan litattafan ta. Har aka tashi ba ta san me aka yi ba.

Da ta koma gida mama tana ta murna, tana tambayarta ya aka yi a makarantar?

Rai a ɓace ruma ta ce “saboda tsabar tsanar da mai sunan baba yayi mini, ya sa aka yi mini repeating, wallahi ba zan zauna a ajin nan ba, ni ajin yan candy ma zan koma” ganin rumaisa za ta ɓata rai, ya sanya ta shareta.

Can rumaisa ta kuma cewa “Mama dan Allah in anjima, ki ce yasir ya rakani gidan su hauwwaliya na duba ƙafarta”

Mama ta ce “Kuma kin yi tunani mai kyau, kya je ki gaishe su, su ga kin warware sosai, amma sai gobe in Allah ya kaimu”

“Dan Allah mama in je yau”

“Goben in Allah ya kaimu ma sai na ce ba zaki je ba”

“To ki yi haƙuri, Allah ya kaimu goben”.

Adam kuwa gaba ɗaya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar saƙon ko jabir ya zo, a bashi haƙuri ba zai iya ganin kowa ba.

Ya kulle kansa a ɗaki, ya kunna wayarsa ya hau social media, ya ga yadda labari ya baza ko in, ga tarin kiran waya da saƙonni daga ƴan jarida, mutane sai comments suke kala-kala.

Ganin wayar na neman caza masa kai, ya sanya yayi jifa da wayar, gaba ɗaya ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar da zai sake fuskantar duniya, da ƙudurinsa na son kawo ƙarshen yi wa ƙasa da harkar tsaro ɓarna. Ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar bincikar waɗanda suka yi garkuwa da matarsa.

Sai da Ammi ta yi da gaske, sannan ya buɗe ɗakinsa, har ya samu ya ci abinci, amma bai gaya mata abun da yake faruwa ba, saboda kar ya sake ɗaga mata hankali.

Rumaisa yau ji take yi kamar salla, saboda yau zata kuma zuwa ta gano Sabir, dan a yanzu babu abun da yake faranta mata rai sama da haka.

Yau da rumaisa ta je makaranta, ƙin zama ta yi a ajin da aka kaita, ta tafi ajinsu ta yi zamant, ta ce ba ta ga wanda ya isa yayi mata repeating ba, sai dai a gaji a koreta daga makaranta gaba ɗaya, wanda da za ayi mata haka da shi ta fi so, dan ita ba ƙaunar makarantar take yi ba.

Mai martaba a yau da kansa ya dira a gidan su takawa, wanda hakan ya sa gidan ya cika maƙil da hadimai, da jami’an tsaro, masu kaiwa suna komowa, tun daga farkon titin har cikin gidan.

Bai sauka a ko ina ba, sai a sashen Ammi.

Mummy na jin labarin zuwan mai marataba, ta tarkato yaranta ta bazamo sashin ammi, da sunan zuwa kwasar gaisuwa a wurin mai martaba sarki.

Ƙafa da ƙafa ya zo ya yi wa Adam ta’aziyyar mutuwar aisha, sakamakon baya gari lokacin da abun ya faru.

Mai martaba ya numfasa ya ce “Turaki yayi mana bayanin komai yadda al’amarin ya faru, sai dai bai kamata a ɓoyewa duniya gaskiyar abun da ya faru ba, maƙiya za su iya amfani da wannan damar, wurin cutar da kai, kamar yadda zancen ya fasu har wata gidan jarida suka wallafa, kuma ba zai wuce saboda ƙoƙarin da ake yi wa ƙasa ba, ya sanya miyagu ke ta ƙoƙarin bayyana laifinka, amma ayi haƙuri a daure, a cigaba da abun da ake yi kar a fasa Allah zai shiga lamarin”

Adam ya risuna ya ce “In sha Allah, muna fatan mai martaba ya cigaba da sanya mu a addu’a”.

“Addu’a kullum cikin yi muku ake, kuma ko dan albarkacin mu babu wani abu da wani zai iya yi ya cutar da ku a kan gaskiya a ƙasar nan, a cigaba da ƙoƙari. Ita kuma ‘yar mu Allah ya jiƙanta ya raya mini wannan kyakykyawan jikan nawa” yayi maganar yana shafa kan Sabir da yake hannunsa.

Mummy ta risuna tana “Allah ya taimaki mai martaba, mun gode da wannan karamci, Ubangiji Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara maka lafiya da nisan kwana”

“An gaisheki amaryar Galadima, , ƴar malam kin ƙi halin malam, mai martaba ya amsa kuma yana godiya” wani irin takaici ne ya kama mummy, jin yadda hadimin mai martaba ya amsa mata.

Aka karɓi jaririn aka miƙawa ammi, shamaki ya dubi ammi ya ce “Mai martaba ya bawa jariri gidaje guda biyu, ya bashi dawakai guda uku, sannan mai martaba ya yi umarnin a  gina masallaci sadaka ga mahaifiyarsa. Sannan idan ya shekara uku a duniya mai martaba ya ce a kai shi umara”

Nan dogarai suka ɗauka da “Godiya yake mai martaba, godiya yake Allah ya baka yawan nasara. Mai bayarwa da dama hagu ba ta sani ba”

Takawa ma risinawa yayi, suna yi wa mai martaba godiya.

Dogaransa suka kare shi ya tashi tsaye, har zai fita ya hangi iman a gefe a zaune.

Ya ce “Ahhh giwa, wannan buzuwar ƴar ta ki tana nan dama, ko da yake an ce mini bafullatana ce? ta daina zuwar mana, Allah ya jiƙan mai babban ɗaki, lokacin da muka kai mata ziyara a Saudiyya kan ta rasu, take tambayar ina wannan buzuwar ƴar ta giwar Galadima, a lokacin bamu sani ba ko kuna tare ko kin mayar da ita, mai babban ɗaki tana sonta”

Ammi ta yi murmushi ta ce “A’a muna tare mai martaba, ai tun da kuka saka baki a kan maganar nan, muke tare da ita”

“Allah sarki, baki fuskanci wani abu ba binta, wataƙila albarkacin yarinyar nan ne Allah ya kawo muku yaron nan cikin aminci, Ubangiji Allah ya yi jagora, Allah ya raya mana su baki ɗaya”

Ammi ta amsa da amin mai martaba.

Ba ƙaramin ƙulewa Mummy ta yi ba, yadda mai martaba ya mayar da hankali a kan yaran ammi, har da agola, amma ita ko kanta bai bi ba.

Mai martaba na tafiya, mummy ta fice fuuuuu ta bar sashin ita da su Fauziyya.

Bayan fitar su Ammi ta ce “Iman, mun yi laifi fa daina zuwa gidan mai martaba da ki ka yi, balle ki je gaishe shi,  kin ga har ya magantu, Allah sarki mai babban ɗaki, lokacin kina ƙarama rigingimun da aka yi ta yi a kan ki,  cewa ta yi sai na bata ke, na din ga kuka, ita tsaya mini a kan riƙonki”.

Iman ta ce “Ammi tsoron zuwa gidan nake, fulanin yola ta hana ni zuwa, saboda yarima Hashim, kin san ai abun da aka yi mini su da Mummy”

Ammi ta ce “Na ji, kar ki yi kuka, jikina na bani mijinki mutum ne na gani na faɗa, karki damu autata”

Kunya ce ta kama Iman, Nusaiba ta ce “To ni fa, ko ita kaɗai ake yi wa Addu’a”

“Ke dai nusaiba baki da girma sai na jikinki, kishi ki ke iman ɗin?”

“To shikenan ma, ni na yi zuciya” Nusaiba ta tashi za ta fita, iman ta tashi ta bita da gudu tana yi mata dariya.

Ammi ta mayar da hankali a kan adam, da fuskarsa sam babu walwala, ta dube shi a tsanake ta ce “Mai martaba yake magana a kai ne, na ji yana cewa an yi amfani da gaskiyar abun da ya faru ana sukarka, meyafaru?”

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Wata gidan jarida ne suka yi posting a social media, cewar aisha ta mutu a hannun ‘yan bindiga, ko kuma ni na kasheta na yi tsafi da gangar jikinta tun da ba aga gawarta ba ma”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, adam waye ya aikata wannan abun? Waye ya fitar da wannan zancen har da sharri haka?”

“Nima ban sani ba, ɗazu na ɗauko wayata a mota, kira daban-daban da saƙonni daga ƴan jaridu, suna buƙatar wai na ce wani abu a kan lamarin na kashe wayar ma gaba ɗaya”.

Ammi ta dafe kai, ta rasa me ma za ta ce ko ta yi? Abubuwa kullum sake rikicewa suke yi.

Da la’asar yasir ba dan yana so ba, ya saka rumaisa a gaba zai kaita cikin gari, suna tafe yana mita, sai da suka je titi, sannan rumaisa ta ce “Dan Allah Yasir taimakona zaka yi”

“Taimakon me?”

“Dan Allah gidan su sabir zaka rakani na je na ganshi” wani mugun kallo ya yi mata ya ce “Ba zani ba, yaushe ki ka je ki ka ganshi? Ba zani ba ba nan muka yi da mama ba”.

Riƙe hannunsa ruma ta yi ta fara kuka “Dan Allah yasir, wallahi na kasa bacci jiya, ba zamu daɗe ba dan girman Allah” ganin tana kuka ya sanya jikinsa yin sanyi.

“Kin yarda zaki wanke mini uniform, ki ɗaukar mini jakata zuwa islamiyyar”

Da sauri ta ce “Eh wallahi na yarda”

“Shikenan mu je, saura idan buƙatar ki ta biya, ki yi mini rashin kunya”.

“Ai ba ma zan yi ba”

Ya tarar musu abun hawa, suka hau suka tafi.

Suna tafe yasir yana danna waya, can ya ce “Kaii”

Ruma ta ce “Menene?”

“Wani labari na gani, ke dama baban sabir ɗin nan shi ne Adam Sharif Galadima?”

“Wai wannan mai tona asirin mutanen, ba wani nan ba shi ne ba”

“Dan ubanki ƙarya zan yi miki?”

Rumaisa ta ce “Taɓ, ba shi bane ba, shi wannan yana abun arziki ne?”

Yasir ya ce “Ke ba wannan ba, wani labari aka wallafa wai, ya sayar da matarsa yayi tsafi da gangar jikinta, kuma jaririn da aka ce nasa ne, ƙarya ne rainawa mutane hankali ake”

Wani takaici ne ya turnuƙe rumaisa ta ce “In ji uban wa?”

‘oho, wani gidan jarida ne suka wallafa”

Rumaisa ta ce “To rubuta musu ka ce ƙarya suke yi, wannan yaron nice nan na zo da shi”

Yasir ya ajiye wayar ya ce “A’a ba ruwana”

Rumaisa ta ce “Zan yi waya katsina a kawo mini wayata ni na rubuta, wannan ai sharri ne”

“Ke dalla rufewa mutane baki, zaki saka na ƙi rakakin wallahi”

Ta riƙe bakinta ta ce “Na daina in sha Allah”

Da haka suka ƙarasa gidan su Adam, rumaisa har da ɗan tsalle za su je ta ga Sabir.

Sai dai rumaisa ta yi ta mamakin ganin layin duk kashin dawakai, duk da abun mamaki bane, amma yanayin wurin ya nuna an yi wani sha’ani a wurin.

Yanzu babu wanda yake yi wa rumaisa shamaki da shiga sashen ammi, sai dai ta jira ta ce wurin ammi suka zo, ak shiga da su sashen Ammi.

Ko da ammi ta ga rumaisa sai da mamaki ya kama ta, shekaranjiya rumaisan ta zo, yau ma kuma gata.

Ammi ta ɓoye mamakinta, ta yi musu maraba, a nutse Yasir yake gaida Ammi, rumaisa kuwa ko gaisawar ba ayi ba, ta koma kusa da ammi ta ɗau Sabir.

Shi kansa takawa kallon rumaisan take, wannan nacin na ta ya fara yawa.

“Rumaisa ya mamanki”

“Tana lafiya ƙalau” ta ƙarasa maganar tana jujjuya sabir da yake bacci, wai sai ya tashi ya ganta.

Hakan kuwa aka yi sai da sabir ya buɗe ido yana miƙa, wasa rumaisa ta yi masa, ya geɓare baki ya fara murmushi.

“Laaa kun ga, yayi mini dariya, Yasir kalli yana yi mini dariya, ya gane ni, sabir ummanka ce rumaisa ka gane ni ko?”

Ammi ta ce “Ikon Allah, ko bacci bai fiye dariya ba, lallai ya ganeki, ke ya fara yi wa dariya”.

“Kaii dama kewarsa ce ke damuna, na yi ta mafarkinsa, na cewa mama a rakani mandawari na duba ƴar uwarmu Hauwwaliya, na cewa yasir dan Allah ya rakoni na ga sabir ɗina”

Ammi kallonta take tana murmushi, tana jin daɗin yadda sabir ke yi wa rumaisa murmushi.

“Rumaisa baku gaisa da baban sabir ba” ruma ta ɗago ta kalleshi ta ce “Ni ma bai kulani ba, yauwwa ammi wai da gaske shi yake shayar da shi?”

“Shi wa?”

Rumaisa ta nuna Adam ta ce “Haka ya ce mini, wai idan aka bani sabir bani da abun da zan shayar da shi, na ce masa ana bashi madara, wai ba a bashi madara shine yake bashi abun da ake bawa jarirai wai ni idan an bani sabir me zan bashi?”

Dariya ce ta kuwa kufcewa ammi, ta ce “A’a rumaisa wannan maganar dai taku ce ba tawa ba”

Takawa dai ko kallonta bai yi ba, dan ya fuskanci yarinyar ba ta da kunya sam.

“Amma dai ammi ai ni ban taɓa ganin maza suna shayarwa ba, shi kuma ya ce mini haka, kuma dai na ga shima ƙirjinsa babu komai”

Ammi rasa amsar da za ta bawa rumaisa ta yi, can sai hankalin rumaisa ya ɗauke daga kan maganar.

“Ammi” ta faɗa a hankali.

“Na’am umman sabir”

Rumaisa ta washe baki ta ce “Wayyo daɗi, ammi na ji daɗi, Allah ya amsa dukkanin buƙatinki, na fili da na ɓoye ya biya miki buƙatunki na alkhairi, na ji daɗi da ki ka kirani umman sabir”

“Amin rumaisa, in dai kin ji daɗi, ina son ki din ga saka baban sabir a addu’a, Allah ya biya masa buƙatunsa”.

“To ammi, ai saboda ke zan yi masa addu’a ba dan halinsa ba”

“Subhanallah, meye da halin nasa?”

“Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne”

Wani ƙarfin hali sai rumaisa, mace da ɗan ta, amma tana faɗin ba ta san halinsa ba ne.

Ammi ta ce “Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da shiga sabgar mutane”.

“To ni dai saboda ke zan yi masa addu’a kawai”

“Yauwwa rumaisa, maƙiya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir ba ɗan sa bane ba”

Ruma ta waro ido ta ce “Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala’i, to shi kuma yayi shiru” ta yi maganar tana ƙare masa kallo.

Sai kuma ta sake cewa “To shine yayi kuka da aka faɗi haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?”.

“A’a ba kuka ya yi ba, addu’a dai zaki din ga yi masa”

Ruma ta ce “Taɓ, ammi kin san wani abu?”.

Ammi ta ce “A’a”.

“Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a unguwarmu ce mini ake ƙanwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da ƴan unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faɗa. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko…..

Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa “Bari mu tashi mu tafi”.

Ammi ta girgiza masa kai, ta ce “Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir”

Ta sake gyara zama ta ce “Tun da na fuskanci ƴan unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi mini ba zance na yi ba. Allah kaɗai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa dole ne. Wallahi ammi a kan gaskiyata sai da a kasheni, kin san bala’in da na gani a hannun ‘yan bindiga kuwa? Hmmm ai wallahi idan nice shi, zan kalli duk wanda ya ce na kashe matata na ce na kasheta idan kana da alaƙa da ita ka nemi shaida ka kaini kotu.

Ba dai baba mai farin rawani ne baban Anty Aisha ba, kuma ya ce mini ya san baban sabir ba zai cutar da anty aisha ba, to wallahi sai na kalli uban kowa na ce masa na yi ɗin. Ai su yadda na fuskanci mutane, idan suka yi maka ƙage, ka yi ƙoƙarin kare kanka, to zasu yi ƙoƙarin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaɗai a lokacin da babu wanda zai taya ni ƙwatar ƴancina, sannan na fuskanci abun da yake bani tsoro, aikuwa na ɗauka, ai tunda na gane ƴan unguwa sun gane lagona su kai ƙarata gida mama tayi mini faɗa na fetsare, ka kai ƙarata gobe na yi maka abun ya fi na jiya, idan ka kawo ƙarata aka tambayeni na yi in ce eh, zaɓi ya rage a kasheni ko a barni da rai.

Wallahi ammi idan ya ce wa masu cewa ya kasheta yayi ɗin, ya gani idan za a cigaba da takura masa, duk wanda ya damu ya kai ƙara, ko kuma tun da ɗan sanda ne ya kamosu ya yanke musu hukunci, su faɗi yadda aka yi suka san kasheta ya yi, ko kuma ya kullesu ba rannan wata haka ta yi ba, wannan kwamishiniyar ba aka ce wani ya ɓata suna ba, aka kai su gidan yari, ko decoration of character ko me ake cewa oho dai”.

Duk da damuwar da adam yake ciki, sai da ya tattara hankalinsa yana sauraron rumaisa, duk da ba kallon in da take yake yi ba. Shi wasu lokutan har tsoro take bashi, ta wani fannin maganganunta a kan gaskiya suke, da maganar hankali da shirme haka take kwaɓa kayan ta.

Ammi ta ce “Waii, rumaisa an gaisheki, ban taɓa ganin yarinya irinki ba, ke kuwa ya ƴan bindiga suka iya zama da ke?”

Ruma ta yi murmushi ta ce “Haka suka zauna da ni, amma na ci ubana ba ƙarya ammi. Ni fa tun da ga kano aka ɗaukemu da ƴan bindiga, har kaza suka sai mini da na ce ina jin yunwa, suka nuna mini wata jaka, cike da bullet, har da bindigogi, shugabansu ne fa ya zo in da aka yi garkuwa da mu, ya sakeni ni da sabir, shi wanda ya sai mini kaza, ammi garin da na je, idan ka yi noma ba zaka taɓa ba sai ƴan bindiga sun yi maka izini, ni na je na ɗauki masara aka je aka gayawa mai gari, da nake a gidansa.

Da aka yi garkuwa da ni, baki ji abubuwan da suka faɗa a gabana ba, na ce idan na kuɓuta sai na faɗa suka ce kona faɗa a banza, la’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, na yi ta karanta musu, ba ƙaƙƙautawa sai Allah ya kawo mini anty aisha, daga baya kuma muka kuɓuta ni da sabir”

Ammi ta yi wata irin ajiyar zuciya ta ce “Amma abun da mamaki, wannan wane gari ne haka?”

Rumaisa ta ɗaga kai ta kalli adam, sannan ta ce “Na manta sunan garin”

Adam tambayoyi ne fal a ransa, amma girman kai ya hana ya tambayi rumaisa, gashi ammi ta fara taɓo abubuwa masu muhimmanci, amma rumaisan ta kauce taƙi magana.

Ruma ta yi wa sabir kiss, ta miƙawa ammi shi ta ce “Ammi, bari mu tafi, kar mu yi dare ba mu je gidansu Hauwwaliya ba”.

Ammi ta ce “To madalla, Allah ya tsare dan Allah ku gaida mamanku, ku jira bari na baku kuɗin mota”.

Ruma ta ce “A’a muna da kuɗi, na ga kaya na gode sosai da sosai, baba mai farin rawani ma, ya bani kaya har da kayan gara masu daɗi da zuma da nono, da kilishi na gode sosai”

Ammi ta takura ruma, ta basu dubu biyar suka tafi.

Bayan tafiyarsu ammi ta kalli takawa ta ce “Adam, dan Allah ne ka fuskanta game da yarinyar nan, ji yadda take magana kamar ana karanta mata?”

“Ni banga komai ba sai shirme da rashin nutsuwa a tare da ita”.

Ammi ta ce “No, maganganunta abun dubawa ne, a duk lokacin da duniya ta nemi juya maka baya, ka kama Allah ka nuna musu zaka iya rayuwa kai kaɗai, kar ka yi ƙoƙarin lallai sai an yadda da kai”

Ya numfasa ya ce “Ammi wannan shirmenta ne kawai na ƙuruciya, da rashin sanin ciwon kanta, yaushe ta zo duniyar balle ta san me duniyar ke ciki, tana tunani ne a iya ƴar ƙaramar duniyar ƙwaƙwalwarta, bari na tafi masallaci “.

Ammi ta ce “Shikenan Allah ya taimaka”.

Sai dai maganganun rumaisa suka cigaba sa shiga suna fita a cikin kwanyarsa, kamar maganganun ta na bisa turba.

Rumaisa sai da suka je gidansu Hauwwaliya, ƙafar Hauwwaliya ta yi kyau sosai, suka din ga murna da ganin rumaisa, ana yin sallar magariba, Yasir ya tasata a gaba suka tafi gida.

A hanya yasir ya yi ta yi wa rumaisa faɗa a kan tsinannen surutunta yayi yawa, ko a jikinta tun da muradinta ya cika.

Bayan sallar magariba, Adam da kansa ya je gidansu Jabir, ya tarar da shi da Jamil suna tare.

Jabir ya ce “Ka gama jan ajin ka neme ni kena?”

“Jan ajin me fa?”

“Ai ka fini sani, ka ce zamu haɗu amma na yi ta kiran wayoyinki ka ƙi ɗagawa”

Adam ya ce “Ba ƙin ɗagawa na yi ba, kaɗaici nake buƙata ne, abubuwa sun sha kaina da yawa”.

Jamil ya ce “Ai kai dama yanzu sai ana yi maka uzuri”

“Hmm baku ga abun da yake ta yawo a social media ba, game da mutuwar aisha? Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin yaɗawa a media dan a ɓata mini suna”

Jamil ya ce “Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun ɗazu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?”

“Ba ni da isasshen lokacin da zan ɓata wurin ƙoƙarin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani ƙorafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu” yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya faɗa.

Jabir ya waro ido ya ce “Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da ɓata maka suna?”

“Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da ƙoƙarin wanke kaina, za su cigaba da ƙoƙarin kaini ƙasa, idan na tsaya a kan ƙafata na cigaba da karɓar duk abun da za’a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta”

Jamil ya ce “Amma kana ganin hakan mafita ce adam? Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye”

Adam ya ce “In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni”

Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.

Jabir ya ce “To, bari mu ga zuwa yaushe wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora”

Adam ya amsa da Amin, ya miƙe ya ce “Bari zan shiga gari na ga Bashir, gobe in Allah ya kaimu zai bar gari, ina da muhimman abubuwan da zamu tattauna”.

Jamil ma tashi yayi ya ce “bari nima na gangara gida, na gaida Alhaji, sannan na wuce gida sai sa safenku”.

Jabir ya ce “To Allah ya bamu alkhairi”

Kamar yadda Jamil ya faɗa, gida ya wuce ya je ha gaida mama da turaki, sannan yayi aniyar tafiya gidansa, Samha ce ta bi yo shi, tana kiran sunansa.

Ya tsaya yana jiran isowarta, ko sa ta ƙaraso, hannunsa ta ja ta ce “Mu je motarka mu yi magana” bai musa mata ba suka wuce motarsa, suka shiga.

Shiru ne ya ɗan ratsa, daga bisani ya ɗan numfasa ya ce “Ina jinki”

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce “A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil, mama ta kasa fahimta ta, ban sani ba ko kai zaka fahimceni, domin kuwa kaine dai-dai da zamanin da muke ciki”

Jamil ya ce “Haka ne, ina saurarenki”.

“Yaya jamil game da takawa ne”

Ya dubeta ya ce “Takawa again, me kuma ya faru?”.

“Maganar nan ce dai ta shekarun baya, tun da Aisha ta mutu ina son maye gurbinta, na so na je wurin baba da kaina, amma sai na ga rashin dacewar hakan, ka taimaka yaya kai kaɗai zaka fahimci halin da nake ciki”

“Wai ke samha ba zaki ƙyal adam ba kamar baki da zuciya? Duk cikin tarin samarinki babu wanda zaki fitar ki aura sai shi dai?”

Kamar ta fashe da kuka ta ce “Da zan iya cire shi daga zuciyata da tuni na yi, dan Allah ka taimakeni yaya jamil”

Jamil ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Zan fara yi wa adam ɗin maganar na ji mai zace”

Da sauri ta ce ‘A’a dan Allah kar ka gaya masa yanzu, turaki zaka fara yi wa zancen”

“To amma kin san magana yanzu ba zata yiwu ba, tun da haryanzu ana cikin alhinin mutuwar nan”

“Ohhj God, to sai zuwa yaushe kenan?”

‘dole ki yi haƙuri, lokaci ya ɗan tura kaɗan”

“To shikenan na gode, ina saurarenka ka gaida gida ” ya jinjina mata kai, ita kuma ta buɗe motar ta fita, tana jin a jikinta kamar a wannan karon za ayi nasara.

Kamar wutar daji, haka Zancen mutuwar aisha, ya cigaba da zaga gidan jaridu, da kuma kafafen watsa labarai, yayin da ta ɓangarensa yaƙi cewa kowa komai, kuma yaƙi magana da kowane ɗan jarida.

A yau babu tsammani, mai girma turaki ya karɓi baƙuncin wambai da misalin ƙarfe tara na dare.

Turaki yayi mamakin ganin ɗan uwan nasa a wannan lokacin, amma ya ɓoye mamakinsa, ya karɓe shi.

Wambai ya ce “Na san zaka yi mamakin ganina a wannan lokaci, sai da ba komai ne ya kawoni ba, illa zuwa in sake tabattar da abun da kunnuwana suke jiye mini, kuma ka yi burus, ba ka ce da ni komai ba”

Cikin rashin fahimta, turaki ya ce “Meke nan kake nufi?”

“Maganar rasuwar ƴar wurinka aisha mana, ko kai ba ka jin jita-jitar da ke ta yawo a kan mutuwarta?”

Turaki yayi murmushi ya ce “Alhamdilillah, da kai da kanka ka ce jita-jita ne, nima haka nan na tsinci zancen”

“Turaki na zuwa na yi domin mu yi wasan barkwanci ba, gaskiyar lamari zaka sanar mini, gaba ɗaya mutuncin masarauta na nema ya zube, martaba da kimar gidanmu adam na ta cigaba da rusata sa shi da uwarsa, wannan wane irin abu ne?”

Turaki ya girgiza kai ya ce “Na san mai ɗakina ce ta je ta gaya maka wasu abubuwan, maganar da ke yawo a gari, tabbas aisha ta mutu a hannun ‘yan bindiga, amma ba adam ne sila ba, ko ya kasheta ya sha jininta ba kamar yadda maƙiya ke ta kwarmato, kuma yarinyar da aka tsaresu tare ta zo da yaron wurin aisha”.

“Turaki kana nufin goya masa baya wurin ɓoye laifinsa, dan me za a ce a ƙasar waje ta mutu a ɓoye gaskiya, wannan banzan aikin da yake yi na shishshigi ga manyan ƙasar nan da kawo ƙarshensu, ai gashi shi zasu kawo ƙarshensa, ko iya wannan labarin an yi mana mummunan tambari, a ce an samu babbar zuriya kamar ta mu da ƙarya. Dan haka dole a hukunta adam, sai ya yi wa duniya bayanin yadda matarsa ta mutu domin wanke ahalinmu daga mummunan zargin tsafi da kisan kai, ga uwa uba ayar tambaya a kan yaron da ake ce nasa ne, na baku awanni arba’in da takwas, idan har bai yi abun da na ce ba, matakin da zan ɗauka a kan sa ba zai yi muku daɗi ba.

Kai banda tsabar rashin sanin ciwon kai, kamar ba ƴarka ba wane irin abu ne haka?”

Turaki ya ce “Da Adam da A’isha, duk tsatso ɗaya ne, kuma ƴaƴanmu ne, dukkansu…..

Bai ƙarasa ba, wambai ya ɗaga masa hannu tare da faɗin. “Ba nasiha nake buƙata ko tunatarwa ba, martabar ahalinmu da sarautarmu nake ƙoƙarin karewa, dan haka ayi abun da muka umarta, ko a ga ba dai-dai ba”

Turaki yayi ajiyar zuciya, ya bi wambai da kallo, da ya tashi fuuuu ya fice.

Yayi ajiyar zuciya yana jin wani irin matsanancin tausayin Adam.

Duk wannan kumfar bakin da wambai yayi, ya biyo bayan ziga da kuma famfon da Mummy ta je har gida ta yi masa tare da taimakon hajiya sauda, shi kuma kamar kullum ya hau kai ya zauna ba tare da bincike ba.

Rumaisa har islamiyya ta koma, in da malamai da ɗalibai suka din ga yi mata barka da arziki na kuɓutowa daga hannun ƴan bindiga, sai dai a wannan karon ma, duk yadda ƴan bugun ciki, suka so ta basu labarin abun da ya faru da ita ƙi ta yi, wasu har suna cewa rumaisa ta koma saliha.

Bayan tashi daga islamiyya, ta wuce gidansu habiba, dan tun da ta dawo ba ta je gidan su habiba, suka rungume juna suna tsalle a tsakar gida.

Daga bisani suka zauna suka hau hira, mamansu habiba ta zubo musu ɗan wake, suka kewaye suna ci suna hira.

“Ruma ina yaya Aliyu ne?”

Ruma ta kalleta ta ce “Meyasa ki ke nemansa?”.

“A’a, tun a asibitin nan ban kuma ganinsa ba”

“To meye haɗinki da shi, to idan son sa ki ke yi, zaki dinga sai mini kayan daɗi kina bani”

Waro ido habiba ta yi ta ce “Astagfirullah, dan Allah ruma ki daina yi mini haka, baki san kirkin da ya yi mini ba lokacin da nake zuwa gidanku da ki ka ɓata, mai sunan baba yayi ta hararata, shi yake rarrshina ya dawo da ni gida”.

Ruma ta kwashe da dariya, ta ce “Allah sarki habibata, kamar ba nan muke kwasar dambe da ke ba, ke ni shawara zaki bani ma”

“Shawarar me” habiba ta yi maganar tana suɗe hannunta.

“Mutumin nan da ya ƙwace mini jaririna, wai ya zan yi da shi ne in karɓo ɗana?”

“Wai ƙwace jaririn suka yi gaba ɗaya to saboda me?”

“Saboda wulaƙanci mana, kullum da tunanin yaron nan nake kwana nake tashi, babarsa fa cewa ta yi ta bar mini shi, amma ya ƙwace mini shi. Habiba kin san in da kotu take? Ƙararsa zan je na kai, ba dama an ce zulai ta kai ƙara kotu alƙali ya bata ɗan ta ba, to nima kotu zan kai shi”.

Habiba ta ɗan yi shiru ta ce “Tsoro nake ji ruma, kin san ba a wasa a kotu”

“Na sani, ai ba wasa zamu je ba, ƙara zamu kai”.

Habiba ta ce “To, a unguwar su babanmu akwai kotu, dama za ayi sauka a gidan, sai ki zo mu je”.

Ruma ta yi murmushi ta ce”Amma na ji daɗi habiba, Allah ya kaimu in sha Allah sai an bani ɗa na, bari na tafi gida” ta miƙe suka fita tsakar gida suka wanke hannu, ta yi wa maman Habiba sallama sannan ta tafi gida.

Idan har da wanda za’a zarga a kan mutuwar aisha, to ba kowa bane ba face ni mahaifinta, domin ni na ɓoye ainihin abun da ya faru, adam ba matsafi ba ne, bai kashe aisha ba, kuma bai yi tsafi da gangar jikinta ba, a madadinsa, ina mai baiwa al’umma haƙuri na ɓoye haƙiƙanin gaskiyar abun da ya faru.

Mummy ta yi jifa da wayar hannun ta, bayan kammala karanta abun da turaki ya sanar da ƴan jarida, ya wanke adam.

Masifa mummy take kamar ta ari baki, duk ƙoƙarin da ta yi, amma turaki lokaci ɗaya ya watsa komai.

Takawa ma mamaki ne ya kama shi, da ganin abun da turaki ya ce, ya wanke shi ya ɗau laifin, bai jira komai ba ya tafi gidan turaki.

Bayan an yi masa iso ya shiga sun gaisa da turaki, ya dubi turaki ya ce “Allah ya baka yawan rai,  na ga abun da ka gayawa manema labarai, amma ni yakamata na ɗau wannan laifin na magantu ba kai ba”.

Turaki ya murmusa ya ce “A’a mu ɗin ne dai yakamata, wambai ya zo nan ya nemi mu sanya ka fito duniya ka bayar da haƙuri, a kan abun da ya faru, wai sunan masarauta na neman ɓaci saboda kai, hakan ya sanya ni na bayar da haƙurin, kar ka ji komai”

“Amma Allah ya taimake ka…”

Turaki ya girgiza wa adam kai ya ce “An rufe wannan babin, ina ƴa ta?”

Adam ya ce “Wace ƴar ta ka?”

Turaki yayi murmushi ya ce “Ƴa ta yarinyar da ta kawo jikana, rumaisa”

Adam ya ɗan tsuke fuska ya ce “Tana gidansu”

“Allah sarki, duk lokacin da aka ganta, ace muna gaisuwa, Allah ya ƙara mata lafiya” turaki yayi maganar yana murmushi, yana tuna lokacin da rumaisa ta zauna a gabansa tana ta zuba shirme son ranta.

Haka adam ya tashi ya tafi, yana ta tunani kala-kala a ran sa. Idan har turaki zai fito duniya ya kareshi, zai iya fuskantar duniya ya ce duk mai cigaba da zarginsa idan yana da hujja. Kansa na kashe aisha ya je ya nema mata hakkinta a kotu.

‘kar dai shawarar wannan yarinyar mara kan gado zaka ɗauka, ta kai ka ta baro’ wata zuciyar ta gargaɗe shi, tsaki ya ja ya kawar da wannan tunanin a ransa.

Maganar da turaki ya fito ya yi, ta ƙara yamutsa hazo, kowa da abun da yake faɗa, yayin da hakan ya ƙara tunzura wambai, turaki ya ƙara zubar musu da mutunci ta hanyar kare adam.

Yau kwanaki kusan bakwai rabon rumasa da jaririnta, dan haka ta shiga damuwa ba kaɗan ba, tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. Wata irin ƙishirwar son ganin yaron ke damunta.

Ta gama shirinta tsaf za ta tafi makaranta, ta fito daga gida har ta nufi hanyar makaranta, ta kalli kuɗin makarantarta a hannunta, kawai ta canza hanya, ta nufi titi.

Ta san kuɗin hannunta ba zai kai ta gidansu takawa ba, dan haka ta saɓi hanya da ƙafafuwanta ta dinga tafiya kamar mara hankali.

Tun da sanyin safiya, har rana ta ɗaga ta fara jin zafinta sosai a jikinta. Idan ta gaji ta zauna ta huta, idan ta huta ta tashi ta cigaba. Sai da ta ci fiye da rabin tafiyar sannan ta samu napep ta yi masa magiya ya ɗauke ta, shi ma in da ya ajiyeta da sauran tafiya, ta sauka ta cigaba.

Sai dai da ta ƙarasa, tana zuwa ƙofar gidan, security suka tare ta.

Ta kalli wanda ya sha gabanta ta ce “Wucewa zan yi”

“Ki je ina?” Ya tambayeta.

“Ciki mana wurin ɗana, ko ba ka gane ni ba ne?”.

Ya ce “Na gane ki, sai dai an ce kar mu sake barinki ki shiga idan ki ka zo?”

Cikin mamaki ta kalli securityn ta ce “Waye ya ce kar a sake barina na shiga?”

“Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba”

“Kam bala’i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani ɗana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?”

“Ke da shi ne wannan, matsa daga nan”

Wata irin zuciya ta turnuƙo rumaisa ta ce “Wallahi ba in da zani sai an bani ɗa na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni” ta yi maganar tana tunkarar gate ɗin.

Tare gate ɗin ɗaya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata “Ki ka motsa daga nan sai na harbeki”

“To ka harbenin mana, sai me? Allah sai na shiga”

Gaba ɗaya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.

Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka, ɗaya daga cikin masu gadin ya ce “Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?”

“Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta taɓa zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu”

Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro ƙofar gidan, sanye da ƙanan kaya, kunnensa ɗaya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi ƙiba abunsa, kan ya ƙarasa gate ɗin rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta riƙe rigarsa tana kuka.

Sororo yayi yana kallonta, “Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka karɓe mini yarona? To ka shiga ka ɗauko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba”

Ɗaya daga cikin security zai yi magana, ya ɗaga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce “Wane jaririn ki ke magana a kai?”

Waro ido rumaisa ta yi ta ce “Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na ɗebo maka ƴan sanda, ko kuma tun da kai ma ɗan sanda ne, na san haɗa baki zaku yi, alƙali zam je na gaya wa, kuma ka bani ɗana ba zan sake zuwar muku gida ba”

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Shikenan, mu shiga ki ga ɗan na ki, sakar mini rigata”.

“Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga” ta ƙara riƙe masa riga, suka nufi gate ɗin.

“Ranka ya daɗe, Yallaɓai ya ce kar a sake bari ta shiga”.

“Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?”

Ya girgiza kai, suka buɗe gate ɗin, suka shiga, sai da suka zo ƙofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.

Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.

Turus! Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.

Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.

Ammi ta ce “Rumaisa daga ina haka?”

Ta ƙarasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar ƙafa, ta zauna ta ce “Tun safe nake tahowa, da ƙyar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da ƙanan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan”. Tayi maganar tana kallonsa.

Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta ɗaya, jin ta ce da ƙafa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.

Ammi ta ce “Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?”

“Waye Mahmoud? Ba shi na gani a waje ba kenan?”.

“Ba shi ki ka gani ba” Ammi ta bata amsa.

Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce “Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi haƙuri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.

“Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?”.

“Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wulaƙanta ni a kansa, bakomai wataran sai labari”

Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.

Ammi ta riƙe hannunta ta ce “Rumaisa, babu mai wulaƙantaki a kan sabir, sabir ɗanki ne, ki yi haƙuri zan ɗau hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma”

Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce “A’a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar ƴar maula” tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.

“Kiyi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wulaƙanki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida”.

Ta girgiza kai ta ce “A’a na gode, dama sabir kawai nake son na gani, ban ci wani abun ba balle yayi tunanin ina fakewa da son ganin sabir ina zuwa kwaɗayi”.

Kalaman rumaisa ya tabattarwa da ammi rumaisa ba wauta da ƙuruciya kawai ta iya ba, ta san mutuncin kanta, kuma tana girmama kanta.

Ta ce “Ai na baki haƙuri, kuma na gaya miki zan ɗau mataki a kansa, kuma ko me zai ce ki rabu da shi, abun da ki ka yi masa a rayuwa bai isa ya biyaki ba, ladanki yana wurin Allah, tashi mu je ki sha ruwa ki sake karyawa, wannan tafiyar da ki ka yi na san kin gaji sosai” da ƙyar rumaisa ta amince ta tashi ta bi ammi, dan tana ganin mutuncinta da darajarta, amma ba dan haka ba, sai ta ce ko iskar gidan ba zata shaƙa ba balle ruwa, saboda cin mutuncin da aka yi mata.

Ammi ta kai rumaisa falonta, ta saka a ka kai mata abinci, ta fita ta bata wuri dan ta ci, ta dawo ta tarar da Adam a falo.

Rai a ɓace Ammi ta ce “Ban ji daɗin abun da ka yi ba ƙwarai da gaske, muzanta yarinyar nan da aka yi a waje, a kan me zaka ce kar a sake barinta ta shigo?”

Cikin ladabi Adam ya ce “Tuba nake, ba na yi haka ne domin ɓata miki rai ba, amma yawan zuwanta gidan nan akwai matsala, bana son ta shiga cikin wani hatsari saboda ni ko ayi amfani da ita wurin cutar da waninmu”

Ammi ta ɗan yi shiru ta ce “Ban ƙi ta taka ba, amma a ƙuruciya irin ta ta, da irin ƙaunar da take nunawa gudan jininka bai kamata a ɗauki wannan matakin kai tsaye a kanta ba, ba tare da bin wasu hanyoyi da ba zata ga an wulaƙantata ko cutar da ita ba. Tana da matuƙar wayo da kaifin basira, dan haka abun da ka yi mata dole ta kirashi da wulaƙanci da tozarci, kar ka sake yanke makamancin wannan hukuncin ba tare da izinina ba”.

Ya risuna ya ce “In sha Allah”

“Ka biya ka fara ajiyeta a gida, ka sanar musu halin da ake ciki, don a saka ido sosai a kan ta ta daina missing makaranta, kuma kar ta sake yin wannan doguwar tafiya haka a ƙafa ita kaɗai”

Ya jinjinawa ammi kai.

Rumaisa ta fito, idanun nan sun yi ja ta ce “Ammi zan tafi”.

“Maman Sabir har kin gama, bari ya mayar da ke gida” rumaisa ta kalli Adam sannan ta kalli ammi za ta yi magana, ammi ta girgiza mata kai ta ce “Ba’a jayayya da umarnin giwar galadima” Ammi ta yi mata maganar cikin gargaɗi, haka ya tilastawa rumaisa yin shiru.

Adam ya miƙe yayi gaba, rumaisa ta durƙusa ta sumbaci goshin sabir, sannan ta bi bayan Adam.

Kamar yadda ransa yake a haɗe, haka ita ma ta tsuke ta ta fuskar, babu alamar wasa da yarinta.

“Laa ka ga, bawan Allah” Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa, da gudu ya ga ta nufi jikin bishiyar dabinon da ke tsakiyar harabar gidan. Mahmud ne a tsaye yake waya, amma ya katse wayar ya zubawa rumaisa ido yana jiran ta ƙaraso.

Ta ƙarasa tana ɗan haki ta yi murmushi ta ce “Ashe ba kai ne shi ba?”

Mahmud ya ce “Shi wa?”

Rumaisa ta nuna masa in da Adam yake.

“Na zata shine da na ganka ɗazu, idona ya rufe sosai da ɓacin rai, ga gajiya kuma kuna kama sosai da sosai, dan Allah ka yafe mini na yi maka rashin kunya a gaban mutane”

Yayi murmushi ya ce “Kin ga jaririn naki?”

“Na ganshi, Allah ya saka maka da alkhairi da ban ganshi ba yau, da ina ga mutuwa zan yi. Ɗa na ne fa anty aisha ta bar mini shi, amma ya ƙwace shi kuma wai ya hana ni shigowa gidan nan”

“Wace aishar?”

“Kai baka san ta ba? Kai ba ɗan nan gidan bane?”.

“Eh ɗan nan gidan ne, amma bana ƙasar jiya da daddare na dawo”.

“Au ho, to in gaya maka sace ni aka yi a katsina, sai aka sato anty aisha matarsa, ta haihu ta rasu ta bar mini jaririn na kuɓuto da ƙyar, bayan na yi kwanaki ina wahala, amma ya ƙwace ɗan kuma wai idan na zo kar a sake barina na shigo, dan Allah wannan ba mugunta ba ce ba?”

Mahmud ya yi murmushi ya ce “Bai kyauta miki ba gaskiya”

“To kai baka taɓa zuwa sashin ammi ka ga jaririn ba, au ashe fa ka ce jiya ka dawo, ba ka ga ɗan nawa ba, mai kyau tubarkallah, ai na san ammi zata nuna maka shi ma, tunda a gidan nan ka ke”

“Eh a gidan nan nake, amma ni ba a sashinsu nake ba, ni ɗan Mummy ne”.

“Wacece kuma hakan?” Ta tambayeshi tana ɗan gyatsine fuska.

“Babata ce, ko baki san mata biyu ne a gidan nan ba? Anyway na ga kamar jiranki yake yi, ki je kar ya zo nan wurin ya karairayaki, shi yafi masa komai sauƙi”

Cikin fitsara rumaisa ta ce “Wallahi wuce nan, na gode sosai ba zan taɓa manta taimakon da ka yi mini ba yau, kuma ka na da kirki fiye da wancan mutumin, dan Allah ka je ka ga ɗana a wurin ammi, sunanshi Mahmud ana ce masa sabir” tana maganar ta yi gaba tana murmushi.

Turus Mahmud yayi ya bi rumaisa da kallo, Adam ya sanyawa ɗan sa sunan Mahmud? Ya tambayi kansa, dan abun da mamaki.

Wurin motar adam ta nufa, da tuni ya kunnata, ya fito ya saka ana karkaɗewa motar ƙura.

Ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce “Bawanki ne ni da zaki shanya ni ki tafi yawon surut?”.

Ta kalleshi ta ce “Ba yawon surutu na tafi ba, godiya na je yi masa na bashi haƙuri. Ya nuna mini karamci saboda ni ɗan adam ce bai koreni ba ɗazu da na rasa nutsuwa ta ina kuka ba, ya taimaka mini na samu abun da nake so”. Ta yi maganar irin ko maganar ta yi masa daɗi ko kar ta yi masa bai shafeta ba.

“Tun daga lokacin da ki ka sake shigowa rayuwata, ki ke ta wasu irin halayya da son nuna lallai akwai wani abu a tsakanina da ke, ina ɗaga miki ƙafa albarkacin yaron nan da kuma ƙuruciyarki, idan ki ka cigaba da wannan abubuwan ki ka shiga trap ɗi na zaki sha wahala na gaya miki, and as from today kar ki sake zuwar mana gida, abun da ki ka yi Allah ya baki lada, bana buƙatar sake ganinki a cikin gidan nan da sunan kin zo ganin yaron nan, idan kuma ki ka cigaba da zuwa zan nesanta shi da ke, nisantawa mai tazarar gaske da ba zaki iya cimm masa ba, dan haka idan ma wani abun ne a ranki ya sanya ki ke bibiyarsa, ki saka abun da na gaya miki a ranki. Idan har zaki cigaba da bibiyar yaron nan, za’a iya amfani da ke a cutar da shi, dan haka bana buƙatar sake ganinki a kusa da shi” yayi maganar cikin kashedi.

Cak ta tsaya ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, sai wasu irin hawaye da suke zubowa daga idonta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *