Tafiyar Mu Hausa Novels

Tafiyar Mu Chapter 6

This entry is part 6 of 6 in the series TAFIYAR MU by Suwaiba Muhammad (Mum Fateey)

(6)

Washe gari asabar aikan Juwairiyya ya iso ta aika ƙaninta Walid tashan mota ya je ya karɓo mata. Da yamma ta shirya tare da Sumayya suna jiran ƙannen Hafiz biyu mata da zasu biyo su tafi tare. Ana idar da sallah la’asar suka shigo gidan da sallamarsu, gaishe da Mama kawai suka yi suka fita ƙofar gida inda motar ɗaya daga cikinsu mai suna Hafsat yake fake, dashi kuma zasu je gidan mai jegon.

 Suna tafiya suna hira tsakaninsu har suka iso gidan Salima, Hafsat ta buɗe booth suka fara ciro kaya ita da ƙanwarta Zainab suna ajiyewa a ƙasa. Daɗi ne ya ziyarci zuciyar Juwairiyya ganin irin hidiman da dangin Hafiz suka yiwa mai jego da jaririn, ta sani Hafiz ɗan’uwansu ne amma ita a gurinta sun mata kara ba kaɗan ba.

A jiya da ta samu labarin ta kira ta faɗa musu, Umma mahaifiyar Hafiz har da kukanta, yau gashi sun aiko mata da kaya niƙi-niƙi tare da alƙawarin Umma da sauran family zasu zo ganin jariri daga baya.

Almajirai suka samu a waje suka tayasu shigar da kayan, Salima da wacce take tayata zaman biƙi suka karɓesu hannu bibbiyu, aka kawo musu juice tare da soyayyen naman rago. Su Juwairiyya suka yi godiya sosai akan karamcin da aka musu na sanya sunan marigayi Hafiz da aka yi. Suma su Salima suka yi godiya bisa hidiman da aka musu.

“Tun jiya nake ta zuba ido na ɗauka zaki zo, da naga baki zo ba shine na kira Muhammad nace ya miki albishir da kanshi. Da dai sunan Babana za’a saka amma nace ya mayar da sunan marigayi zaki ji daɗi ba kaɗan ba.” Salima ta ƙarisa maganan hawaye na taruwa a idanunta.

Juwairiyya share fuskarta ta yi dalilin hawayen da ya zubo mata, kana ta dubi jaririn da yake hannunta yaro fari kyakkyawa wai mai sunan Hafiz ɗinta.

“Nagode da wannan karamcin Salima, Allah ne kaɗai ya san daɗin da naji a cikin zuciyata. Kin kyauta mana ba kaɗan ba, Allah Ya bar zumunci Ya kuma raya mana Muhammad Hafiz.”

  Dukkan ƴan ɗakin suka amsa da ‘Ameen’. Basu jima sosai ba suka tashi tafiya aka basu cincin ɗin suna.

“Ni wallahi ku bari zamu hau napep ni da Sumayya, ke kuma Hafsat sai ki sauƙe Zainab a gidanta kar zagayen ya miki yawa.” Faɗin Juwairiyya a lokacin da suka fito waje.

“Ai yanda na ɗaukoki haka zan mayar dake har ƙofar gidan Mama, babu abun da zaki faɗa da zai hanani kai ku.”

“Ke dai kina son wahalar da kanki wallahi, mu je to kar maghriba ya sameku a hanya.”

Bayan sun sauƙesu suka shigo gida, a nan Juwairiyya take labartawa Mama irin karamcin da Salima ta mata, yanda ta sa aka fasa saka sunan Babanta aka saka na Hafiz.”

“Kai Masha Allah ta yi ƙoƙari sosai Allah Ya bar zumuncin da ke tsakaninku.”

“Da bata yi casting mijinta out irin haka ba, yanzu mu mun ɗauka shi yayi niyyar yiwa abokinshi takwara alhali ashe ita ce.”

“Koma yaya ne duk sun yi ƙoƙari amma ba zan taɓa mantawa da Salima ba, ta cika ƙawar amana.”

Mama kallonsu kawai take yi bata sake cewa komai ba, har suka gama hiransu suka watse.

*****

Bayan shekara ɗaya.

 Juwairiyya ce zaune a gaban Mama tana mata faɗa kamar yanda ta saba kullum idan bazawari yayi sallama a waje tace ba zata fita ba.

“Na san kina son mijinki kika rabu dashi amma kin ga rayuwar nan bata da tabbas, yanzu gashi nan rubibinki ake yi amma gaba kaɗan zaki ga yayinki ya wuce an rasa mijin auren. Ki yi amfani da opportunity ɗin da kike dashi a cikin maneman naki ki darje ki zaɓi wanda zuciyarki ta aminta dashi, kiyi aurenki ki rufawa kanki asiri. Juwairiyya baki da ɗa baki da jika aure ba zai baki wahala ba kuma ba zaki rasa kalan mijin da kike so ba, kar kiyi wasa da damanki har ya kuɓuce miki. Zawarawa masu ƴaƴa suke wahala wajen samun mazajen aure domin mazan yanzu basa son ɗawainiyar kowa, wani idan zai samu a riƙe mishi ƴaƴanshi ma zai yarda. Kuma na faɗa miki ba zaki koma makaranta ba muddin kina zaune a cikin gidan nan, wallahi ba zaki janyo mini bakin jama’a ba ana shigowa gidan nan ana ƙirga zawarawan ciki ba.”

Surayya har ta buɗi baki zata yi magana sai kuma ta rufe, da cewa zata yi a littafin Ruwan Zuma haka Ummii wato uwar Laila ta faɗa mata, sai dai da ta tuno irin ɓacin rai da zai biyo baya sai ta gimtse bakinta. Yaushe ma aka bata wayar? Kwata-kwata yau wata biyar ne shine zata ƙara yin wani wawancin? Ba dai ita ba!

“Ina miki magana kin yi shiru.” Mama ta faɗa a hasale.

“Kiyi haƙuri Mama.”

“Ni ba haƙuri zaki bani ba, cewa na yi ki zaɓi miji kiyi aure.”

Shiru Juwairiyya ta yi kanta a ƙasa tana tunanin rayuwarta a gidan mahaifiyarta ya fara zama takura a dalilin maganar aure da ake mata kullum sai dai in ba’a yi sallama a waje ba. Karatun da take son farawa an hanata, sana’ar girke-girken ma Mama ta hanata a cewarta in Juwairiyya ta saba da riƙe ƙuɗi da zaman kanta zata ƙi auren. Yau shekara ɗaya kenan har da wata shida da rasuwar Hafiz, maza kala-kala sun kawo mata cafka, wasu da kyakkyawar niyya wasu kuma da neman banza babu ko kunya a tattare da su.

Duk cikin maneman nata babu wanda ya mata, to ma yaushe ta yarda suka saba har soyayya ta samu shigowa? In Mama ta matsa mata fita waje bata wuce minti biyar da duk wanda ya ziyarcetan zata dawo gida, irin tarɓan da take musu kuma ya jawo da yawa basa dawowa sai ƙalilan masu naci, ciki kuwa har da Ilyas magidanci ɗan unguwarsu. Matarshi ɗaya da ƴaƴansu biyu, ba wani babba bane don ta tabbata zai yi sa’an Hafiz. Sosai yake mata naci har Mama ta san da zamanshi domin ya shigo sau biyu ya gaisheta.

Sannan ga Hussani da yake damunta wanda har tana tunanin kanshi ba ɗaya ba, tun tana lallaminshi su rabu lafiya har ta dawo tana ɗaga mishi murya tare da faɗa mishi baƙaƙen maganganu, sai dai duk da wannan wulaƙancin da take mishi bai sa Hussaini ya nuna ko sau ɗaya ranshi ya ɓaci ba, naci kuwa sai abun da ya karu. (Da alama dai ya karanta Ruwan Zuma kuma yana son ya kwaikwaya).

Sannan ga Muhammad, zuwanshi ya fi na kowa ɓata mata rai. Tana tunawa bayan haihuwar Salima da wata ɗaya ya zo kawo mata shopping ɗin monthly da ya saba ya nemi zai gaisa da Mamanta. Bata kawo komai a cikin ranta ba don haka ta mishi iso kana ta fita a falon ta barsu. Abun da ya bata mamaki shine tsawon lokacin da ya ɗauka yana magana da Mama, me suke cewa? Ta je bakin ƙofar da niyyar gulma suka ci karo a yayin da yake fitowa.

“Sorry.” Ta bashi haƙuri tana jin takaici a ranta domin bata samu ta ji komai ba.

“Ki rakani mota akwai saƙon da zan baki.” Ya ce da ita bayan ya sanya takalmanshi.

“Ka bawa yara su kawo mana.” Ta faɗa tana shiga falon. Sai dai irin muguwar kallon da Mama ta mata yasa ta dawo waje ba shiri ta bi bayanshi.

“Lukuti kawai.” Ta furta a hankali tana ganin yanda ƙeyarshi ta tara tsoka yana kuma tafiya ɗai-ɗai tsabar ƙiba.

A bakin motarshi Juwairiyya ta tsaya wacce tun zamanin samartaka da ita yake yawo wanda a yanzu har ta fara gajiya dashi ta kuma tsufa.

Zama yayi a cikin motar bayan ya ɗan wahala sannan ya dubeta fuskar nan babu annuri ya ce,

“Tun ba yau ba naga kin fara tsayuwa da masu neman aurenki, hakan yasa nima yau na nemi izinin Mamanki don ina son fara neman yardarta kafin in zo gareki. Idan kin amince bana son dogon nema a ɗaura auren ki tare.”

 Sai da ta ɗauki seconds goma maganarshi na yawo a brain ɗinta sannan ta kwashe da dariya. Sosai take yi har masu wucewa suna dubanta, hakan yasa ta tsuguna tare da ɓoye fuskarta a cinyarta taci gaba da yi jikinta na girgiza.

Sai da tayi dariyar mai isarta sannan ta miƙe tsaye tana share hawayen idanunta lokaci ɗaya kuma tana danne wata dariyar da ke son kwace mata. Bai ce mata komai ba amma ya haɗe rai sosai har sai da fuskarshi ta ɗan yi ja.

“Wai idan kin amince…Mwhahahaha….bana son dogon nema…. a ɗaura auren ki tare….Mwhahahaha” Ta ƙara kwashewa da dariya wannan karon har da riƙe ciki.

“Me amsarki?” Kawai ya tambaya yana nazarinta.

Sai da ta saita kanta sannan tace,

“Maza baku da ta ido wallahi. Yanzu ni da nake ƙawar matarka kuma matar abokinka….”

“Late, you should add late.”

Nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke ta dubeshi sama sa ƙasa sannan ta ce,

“Ba sai ka tuna mini cewa baya doron ƙasa ba, tsayawarka a nan tare da ni kaɗai ya isa ya tuna mini cewa mijina ya mutu. Kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan da wannan zancen domin na farko, ni ba butulu ba ce, ina zumunci da matarka ba zan taɓa cin amanarta ba. Na biyu kuma har abada ba zan taɓa auren ɗaya daga cikin abokan Hafiz ba, domin hakan zai zama tamkar cin fuska ne a gareshi, ba zan wulaƙantashi ba. Sannan na uku, Muhammad, wallahi ko na rasa mijin aure ne ba zan aureka ba. Da mutum irina da mutum irinka ba zasu taɓa zama a ƙarƙashin rufi ɗaya ba, in kuma aka kuskura aka haɗasu to sai dai gobara. You hate me, nima kuma na mayar maka da daidai naka. Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shine kar ka kuskura ka nunawa Salima cewa mun yi wannan maganan saboda bana son alaƙar mu ya samu matsala.”

“What if shi ya nemi hakan?” Muhammad ya tambayeta yana kafeta da ido.

“Shi waye ya nemi me?” Ta mayar mishi da tambaya don yayi confusing ɗinta.

“What if Late mijin naki ne yace in nemi aurenki idan ya bar doron ƙasa?”

“Stop saying ‘Late’ i know he is late.” Ta faɗa a harzuƙe.

“Hmm.”

“And you are lying, kai ne ka sakashi ya maka alƙawarin idan ka mutu ya auri matarka Salima kuma ya faɗa mini tun a ranar saboda tsakanina dashi akwai kyakkyawar alaƙa bama ɓoyewa juna komai.”

“To bai faɗa miki duka ba, he asked me to marry you too.”

“Ƙarya ne.”

“Ba zan taɓa yiwa mai rai ƙarya ba balle mamaci, ƙarya bata cikin halayena.” Ya faɗa a hankali kamar ba shi ake yiwa ihu a kansa ba.

Shiru Juwairiyya ta yi domin ba haka ta so ba, ta so ne yayi losing mind ɗinshi ta cire filtern bakinta ta zageshi tatas, amma calm demeanor ɗinshi ya hanata hakan. He is too calm for her liking, kuma hakan na sakata jin baƙin ciki kamar ta kurma ihu.

Ganin ta yi shiru tana cika tana batsewa yasa ya kunna motarshi kana ya ja ƙofar ya rufe ya dubeta ya ce,

“Me kika ce? Zaki aureni?”

“Ko sunana baka taɓa ambato a bakinka ba, ko sunana baka taɓa sauraron harshenka ya furta ba, balle a kai ga so har aure.”

“Ba wannan na tambayeki ba.”

“Ba zan taɓa aurenka ba ko mazan duniya sun ƙare.” Ta bashi amsa a numfashi ɗaya tana hararanshi.

“Shine final say ɗinki ko zaki yi tunani?”

Wani malolon baƙin ciki ne ya zo ya tokare a maƙoshin Juwairiyya ta ji kamar ta fara kuka, wai bai ji abun da ta faɗa bane, meyasa ba zai yi fushi su yi uwaka ubanka ba?

Bakinta har rawa yake yi tsabar ɓacin rai ta ce,

“Har abada.”

“Dama mun yi dashi akan sai kin ƙi amincewa kafin in barki. Allah Ya gani na cika alƙawari, ke kuma kar ki ce ban taya ba. Allah Ya bada sa’an neman mijin aure.” Da haka ya yiwa motarshi giya ya tafi.

Daga ranar bai sake waiwayarta ba, sai dai kuma bai fasa aiko mata shopping kowanne month ba.

Ko da ta dawo cikin gida Mama ta tambayeta me ya faru cewa ta yi ya nemi aurenta tayi declining domin ba zata munafurci Salima ba, Juwairiyya bata ga amfanin yiwa Mama ƙarya ba domin shi da bakinshi ya faɗa mata sun yi maganar da ita.

“Allah Ya kyauta.” Kawai Mama tace, daga nan kuma bata ƙara ɗago mata zancen Muhammad ɗin ba.

A nan Juwairiyya ta dawo daga dogon tunanin da take yi ta dubi Mama da tayi kasaƙe tana kallonta tace,

“Ki bani wata uku zan nemi ɗaya daga cikin zawarawan nawa in aura sai a haɗa aurena da na Sumayya.”

“Ke kika yankewa kanki lokaci ba ni ba, don haka idan lokacin nan ya cika baki fito da mutum ɗaya ba wallahi, wallahi Juwairiyya kin ji na rantse? Ni da kaina zan zaɓi ɗaya daga cikinsu a ɗaura muku aure! In kin ga dama ki bijire a nan ne kuma zaki gane duniya budurwar wawa ce.”

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

(7)

Yau Ilyas ya zo gurin Juwairiyya, abun mamaki yana aikawa kiranta bata ɓata lokaci ba ta fito, sannan ta ƙara bashi mamaki ta hanyar yi mishi sallama tare da ɗaga mishi gaisuwa. Tunani ta yi mai zurfi, duk maneman nata da suka rage Ilyas ne kaɗai ta ga zata iya rayuwa dashi in har ta faɗa son shi. Sauran kam ko tunaninsu bata so kwakwalwarta ta kawo mata.

 Shi kuma Ilyas tsabar murna kasa rufe bakinshi yayi, a jikin motarshi ta jingina yayin da shima ya fito ya tsaya a gefenta. Bayan ƴan gaishe-gaishe su ka ɗan yi shiru na wasu ƴan seconds kafin ya buɗi baki ya fara magana.

“Alamu sun nuna addu’ata ta karɓu, na ɗauka akwai sauran aiki a gabana Hajiya Juwairiyya.”

“Hmm.” Kawai tace don bata san me zata faɗa ba.

  Basu jima ba ta koma cikin gida domin tuni hirar ya gundureta ba don kuma Ilyas bai burgeta ba, a’a haka kawai ta ji bata son su tsawaita hiran. Tun daga ranar suka fara soyayya a hankali har ta kai Juwairiyya na iya hira da shi cikin walwala a nan kuma ta gane ta kamu da son Ilyas. Ita a rayuwarta idan namiji ya iya soyayya nan da nan zai sace zuciyarta, sannan ya dinga martaba mace ya ɗauketa a matsayin abu mai tsada abar tattalawa kamar yanda Hafiz yake cewa. Ta ɗauka ba zata taɓa samun namiji irinshi ba amma sai gashi Allah Ya kawo mata Ilyas duk da cewa bai kai Hafiz ɗinta ba. A hakan ma ta godewa Allah sannan tana ji a jikinta in dai ta aureshi zasu zauna lafiya domin tana da labarin matarshi tana da hankali bata da fitina ko kaɗan, to me ya fi ranta?

Wata ɗaya har da sati biyu da fara soyayyarsu ta ji shiru bai mata maganar aure ba, hakan yasa da aka ƙara sati biyu ya zama saura mata wata ɗaya wa’adinta ya cika ta yanke shawarar mishi magana.

Yau ma ya zo hira kamar kullum tana jingine a jikin motarshi wacce ya mata nacin su dinga shiga ciki suna hira amma ta ƙi. Saboda ko a lokacin da take budurwa bata shiga mota ta yi hira da saurayi, saboda bayan Mama ta haneta ita kanta ta san abun da zai iya faruwa a ciki ba mai kyau bane.

“Ni fa sanyi nake ji a wajen nan, nayi da ke mu shiga mota mu yi hiranmu a ciki amma kin fi son sanyi yayi ta shiga jikinmu.”

Murmusawa kawai Juwairiyya ta yi kana ta fara tunanin ta yaya zata ɗauko mishi zancen tunda in a al’adance ne namiji ne yake fara kawo maganar aure ita kuma ta amsa.

“Bikin Sumayya yanzu saura wata ɗaya.”

“Haka dai muke ta lissafi tare. Allah Ya nuna mana da rai.”

“Ameen Ameen.” Ta amsa sannan ta yi shiru.

“Ya dai naga kamar kina cikin damuwa?” Faɗin Ilyas yana matsowa kusa da ita.

 Idan za’a tambayi Juwairiyya aibun Ilyas abu guda zata furta shine bai ɗauki taɓa macen da ba nashi ba a matsayin zunubi. A farkon zuwanshi yana respecting space ɗinta, amma suna fara sabawa ya nemi ya riƙe hannunta tare da son su shiga cikin mota su yi hira, babu ɓata lokaci ta nuna mishi bata son hakan don bata manta da cewa laifi ne mai girma aikata hakan ba.

“Wallahi Mama ce ta damu wai sai a haɗa aurena da na Sumayya. Na ce mata ni dai har yanzu baka mini maganan ba.”

Shiru Ilyas ya yi, can kuma yace,

“Dama tuntuni ina son mu yi wata magana da ke amma na rasa ta yaya can ɗauko miki ita.”

Jin furucinshi yasa cikin Juwairiyya ya kaɗa, nan da nan kuma ta fara addu’an Allah Ya sa ba cewa zai yi ba zai aureta ba, domin in har ya mata haka ya kassarata. Duk manemanta dama ƙalilan ne suka rage, a hakan ma tana fara soyayya da Ilyas ta koresu don ita tace ba zata yaudaresu ba, ba zata haɗa manema da yawa a lokaci ɗaya ba. Ilyas kuma da niyyar aure ya zo mata domin har bincike ta sa anyi mata a kanshi aka ce bashi da aibu. To me zai faɗa mata?

“Ina jinka.” Kawai ta iya cewa dashi tana sauraronshi.

Gyaran murya ya fara kana ya gyara tsayuwarshi ya fuskanceta tarr yace,

“Juwairiyya ina sonki ina kuma da niyyar aurenki, sai dai a yanzu matata ta samu labarin ina nemanki muna ta fitina a gida. Yanzu abun da nake so dake shine ki yarda mu yi auren sirri tsakaninmu, zan baki sadakinki ba tare da kowa ya sani ba sai mu biyu, da zarar nayi settling ɗin matata sai mu bayyana auren ki zo ki tare.”

Shiru ta yi har na tsawon minti ɗaya kanta a ƙasa tana tunani, shi kuma Ilyas ido ya zuba mata yana ta gyara tsayuwarshi kamar mara gaskiya. Can Juwairiyya ta ɗago kanta da ɗan guntun murmushi a fuskarta tace,

“Shikenan zan yi tunani a kai. Amma yaya batun….?” Ta nuna kanta sannan shima ta nuna shi.

Ƙura mata ido yayi yana son fahimtar me take nufi, kashe mishi ido ɗaya ta yi wanda hakan yasa fuskarshi ta washe hakwaranshi suka bayyana cikin farin ciki.

“Yauwa ƴar gari, wannan ba matsala bace. Nuhu abokina da name baki labarinshi yana da gida a nan cikin New GRA, unguwar ma ba’a gama cika ba kuma gida ne mai kyau. A can zamu dinga zuwa muna rage zafi har lokacin da zamu bayyana auren.”

“To idan nayi ciki kafin nan fa?”

“Zamu yi amfani da protection ko kuma ki sha maganin hana ɗaukan ciki.” Ya faɗa hankali kwance kamar dama ya jima da wannan nazarin.

“Da alama ka jima kana tunanin nan, amma kuma meyasa tun zuwan ka baka faɗa mini hakan ba ai da yanzu an wuce gurin, nima da na samu sauƙi.”

Wata dariya Ilyas ya saka Juwairiyya kuma ta murmusa tana kallonshi.

“Ke ɗin ce an bani labarin kina da zafi, gashi kuma in bakya son abu babu mai sakaki dole. Amma dai nace musu sai dai in ba’a bi dake yanda kike so ba. Kin ganni nan? Bana son na ga ana takurawa mace ko kaɗan, ku mata sai da lallami.”

“Hakane kam. Kuma idan mutum yana son yin zina da mace zai iya shafe har wata biyu yana bibiyarta don buƙatarshi ta biya. Su waɗanda suka faɗa maka ina da zafin sun manta basu faɗa maka cewa ina da ilimin addini ba, sannan ni ba shashasha ba ce.”

Nan take annurin fuskarsa ta ɗauke, domin sai a yanzu ya gane cewa shigo-shigo-ba zurfi ta mishi. Fuskarshi ya tamke don ya san daga yanzu duk wata kalma da zata fito daga bakinta ba lallai bane ta mishi daɗi ba.

“Ilyas ka bani mamaki ka kuma saka na ƙara tsorita da mazan yanzu. Masu hali irin naka sun zo amma da buƙatarsu suke zuwa a tafin hannunsu babu ɓoye-ɓoye, kai kuma sai da ka yaudareni da kyawawan hali har na faɗa sonka. Wallahi ni ba mazinaciya bace Ilyas, sannan na ɗauka zuwa kayi ka rufa mini asiri ashe kai tona mini asiri ka zo yi. Ka yaudareni ka kuma cuceni, Allah Ya saka mini.” Sai a lokacin muryarta ta fara rawa ta nufi cikin gidan su cikin sauri tana share hawayen da ya zubo daga fuskarta.

Bata kai ga shiga ɗaki ba ta ji ya kunna motarshi ya tafi, ta yi tsammanin zai kirata ya ce gwadata yake yi, amma shirunshi har ta shigo ya nuna cewa da gaske yake. Kuma tunda bai samu abun da ya zo nema ba ya tafi.

Baby wanda ya ga shigowar Juwairiyya balle ya ga halin da take ciki, tayi kuka sosai domin ta san in ba mutuwa ba bazata samu kanta a cikin wannan halin ba, da Hafiz ɗinta yana raye da babu wani ɗan iskan garin da zai zo ya nemeta da lalata, ashe an yi gaskiya da aka ce ‘Mutuncin mace ɗakin mijinta’ ashe aurenta ba ƙaramin rufa mata asiri yake yi ba. Yanzu ina zata saka kanta? Ga wa’adin Mama saura wata ɗaya ya cika! Da waye zata haɗata in bata nemo mijin auren ba? Da wannan tunanin Sumayya ta shigo ta sameta, amma ko da ta tambayeta me ya sameta bata iya faɗa mata ba, da haka ta lalatar da zancen.

Sati ɗaya da haka Mama ta lura babu mai zuwa gurin Juwairiyya, hakan yasa ta kirata don a yanzu da biki ya saura sati uku tana son sanin halin da take ciki.

“Mama shima Ilyas yaudarata ya zo yi ba aurena zai yi ba.”

“Ina jinki.” Faɗin Mama tana tsareta da ido.

A nan Juwairiyya ta faɗa mata yanda suka yi wanda ya bawa Mama mamaki kwarai da gaske domin itama ta sa an mata binciken halayenshi da ta lura hankalin ƴar tata ya fi karkata kanshi. Ashe a ɓoye yake iskancinshi shiyasa ba’a gane ba.

“Kina da sauran sati uku, a cikin waɗanda kika koran sai ki kira wani ya dawo ku daidaita.”

“Mama don Allah ki yi haƙuri kar ki mini haka, ki ƙara mini wasu wata ukun wallahi zan zo miki da mijin aure. Duk waɗanda na koresu bani da masaniyar daga ina suke balle kuma in karɓi number wayarsu.”

“Ni dai na faɗa miki kuma na yi rantsuwa ba zaki sakani kaffara ba.” Mama ta mayar mata da amsa kana tayi shigewarta ɗakinta.

 Cikin tashin hankali Juwairiyya ta fice daga falon Mama ta koma nata ɗakin, ta ɗauka idan ta bawa Mama labarin abun da ya faru zata barta tunda ba laifinta bane kuma ba ita ta ƙi auren ba. Ta yarda zata auri Ilyas shiyasa take soyayya dashi wanda ita kanta Maman ta sani tunda tana ganin fitanta in ya zo hira. To me yasa ba za’a mata uzuri ba? Me yasa Mama take son takurawa rayuwarta haka? Me yasa ba zata bari ta nemi mijin cikin kwanciyar hankali ba? Wa ya faɗawa Mama cewa har yanzu ana irin haka? Sai yanzu ta yarda mazan kirki na aure suna wahala.

Tunanin duniyan nan ta yi don neman mafita amma babu solution, don bata da inda zata je ta kai Mama ƙara a bata haƙuri. Ƴan’uwan babanta da basu san cinsu da shansu ba ta sani sun fi kowa ma son tayi aure, domin da yanzu zata je musu da zancen haɗuwa zasu yi da Mama su uzzurata. Dangin Mama kuma babu mai sakata dole saboda duk wani da zata ganshi a matsayin uba ko uwa basa raye, shaƙiƙanta kuma ita ce babbarsu. Kakarsu kuwa wacce suke zaune gida ɗaya da ita da babu duk ɗaya, bata cewa kas balle as. Mace ce mai sanyin hali sosai wanda Juwairiyya take cewa sanyin halinta da haƙurinta ne suka sa tayi tsawon rai. To gurin wa zata je? Bata da kowa sai Allah, domin shi kaɗai ne zai sassauto da zuciyar Mama ko kuma ya sama mata mafita a cikin ƙanƙanin lokacin nan.

A kwana a tashi yau ya rage saura sati ɗaya auren Sumayya da Juwairiyya wacce bata da mijin aure, abun duniya duk ya bi ya dameta domin har tunanin guduwa ta yi amma ina zata je? Bata da kowa sannan ta kasa faɗawa kowa damuwarta balle a bata shawara, Juwairiyya tana da ƙawaye amma ita a gurinta su yi zumunci ne kaɗai ba wai su yi sharing sirrukan juna ba. Wannan dalili ya sa babu wanda ya san halin da take ciki sai ƴan gidansu.

 Abun da Juwairiyya bata sani ba shine tuni Mama ta janye maganarta don har tayi azuminta uku na kaffara saboda ta sani mijin aure ba kamar zani bane da zaka je kasuwa ka siyo ka dawo dashi gida ba. Ta san ta uzzurawa Juwairiyya amma hakan da ta mata shine daidai. Kwata kwata a yanzu shekarun Juwairiyya ashirin da uku ne (23), yarinya ƙarama da ita bai kamata a barta tana zawarci har yayi tsawo ba. Tana da sauran ƙuruciyarta sannan zata samu mijin aure ba tare da an sha wahala ba, shiyasa tun lokacin da maza suka mata rufdugu ta so ta sauraresu har a samu wanda ya burgeta, ta matsa mata ta fita waje amma ta kasa hanata yi musu baƙin halin da suke tafiya basa ƙara waiwayarta. Wannan babban kuskure ne da Juwairiyya ta yi da zai sa gaba ta yi hankalin ba’a korar mai tayin soyayya, a duba a gani kafin a sallami mai tayin. Zata bar Juwairiyya a yanzu, amma ana gama bikin Sumayya zata tayar da zancen kuma ba zata zo mata cikin lallami ba.

 Ana saura sati ɗaya biki ɗaya wata ƙawar Juwairiyya mai suna Halima ta kawo mata ziyara. Tare suka yi secondary school kuma sun yi zumunci sosai har aka yi auren Juwairiyya basu rabu ba, hakan yasa da aka tashi auren Halima itama Juwairiyya ta halarci kowanne event har aka gama Hafiz ne mai kaita yana dawo da ita. Bayan auren mijin Halima ya samu aiki a ƙasar waje inda yayi karatunshi, hakan ya sa ya tattari matarshi suka koma can da zama. Sai dai bayan shekara mahaifiyarta ta rasu wanda hakan yasa suka dawo gida Nigeria, mijin nata sati ɗaya kawai yayi ya koma ita kuma ta zauna kula da Babanta don bayan an watse gida ya rage daga shi sai ita. Matarshi ɗaya ce sannan su biyu ne kaɗai ƴaƴanshi, daga ita sai yayanta namiji wanda yake karatu a ATBU. Wannan kenan.

“I’m sorry to say, amma Juwairiyya kin ƙara ramewa. Ke da Daddy kuna fama wallahi, ban san raɗaɗin rashin masoyi ba amma na san rashin uwa, kuma a hakan naci gaba da rayuwa ban fasa ba. Kun fi kowa sanin ba zasu dawo ba, haka kuma yawan damuwarku ba zai amfanesu da komai ba, zasu so ku nitsu kuma ku cigaba da rayuwa sai ku aika musu da addu’a. Don Allah ki rage yawan damuwa, mutuwa kowa tana jiranshi babu mai zama a doron ƙasa.”

“Hmm, Halima ina cikin wani hali ne mai wuya.” Faɗin Juwairiyya domin yanzu tana son ta buɗe cikinta ko zata samu a bata shawara.

“To Allah Ya yaye miki amma na menene?”

 A man Juwairiyya ta zayyanewa Halima kaff halin da take ciki sannan ta ƙarishe da cewa,

“Wallahi Halima bani da maneman ma yanzu, in kika cire Hussaini babu kowa. To yanzu in ba Hussaini ba wa zata aura mini, wallahi in har aka aura mini Hussaini sai na gudu an rasani.”

“Ya Salam! Juwairiyya kar ki sake faɗin haka, abun bai kai ga haka ba. Shi kuma Hussaini in banda rigima ina shi ina ke? Ya fi kowa daƙiƙanci a aji gashi har yau shi bai ƙaro ilimi ba kuma bai kama sana’ar komai ba.”

“Kuma ni Allah Ya sani ba zan auri sa’ana ba.”

“To ga wani dalilin ma.”

Shiru suka yi na ƴan wasu seconds sannan fuskar Halima ta washe da annuri tace,

“What if na kawo miki miji na gani na faɗa har gida? Mijin da bashi da aibu sannan zai riƙeki amana tamkar ƴar cikinshi? Mijin da zaki zauna a gidanshi daga ke sai shi babu mai takura muku? Mijin da yake da rufin asirin da ba zaki nemi komai ki rasa a gidanshi ba? Kina so!?”

“Halima ina zaki samo mini mijin aure mai duka waɗannan qualities ɗin a ƙanƙanin lokaci haka? Sannan in ma an samu shi zai yarda ya aureni ne daga haɗuwa da ni?”

“Ina ji a jikina za’a yi auren nan shiyasa ƙaddara ta hankaɗoni gidan nan. Wallahi tun last month

mijina yake ta damuna akan in koma Turkey amma hankalina ya ƙi kwanciya da in bar Daddy shi kaɗai a cikin gidan nan, ina nan ma kullum cikin damuwa yake ina ga kuma babu ni? To kwana biyu da suka wuce ya daina ɗaukan wayata Juwairiyya, na san ina cikin fushin Allah kuma ina ɗaukan alhakinshi amma Daddy fa? Ni kaɗai yake gani ya ji sanyi a ranshi saboda Abduljalil tuni ya koma school baya dawowa gida sai ƙarshen semester. Juwairiyya…….” Bata kai ga ƙarisa maganarta ba Juwairiyya ta katseta da hanyar ɗaga mata hannu.

“No, ba zan auri Daddy ba Halima! Wallahi ba zan auri Daddy ba.”

“Juwairiyya….”

“Kai ina! Mu bar maganan nan bana son jin komai.”

“Don Allah ki saurareni in ya so zaki iya yanke duk hukuncin da kika ga dama. Ki saurareni please.”

“Duk abun da zaki faɗa ba zai canja mini ra’ayi ba amma ki faɗa tunda kin kira sunan Allah. Haba Halima Daddy ne fa, Daddyn mu. A ƴa ya ɗaukeni fa.”

“Ki dai saurareni.”

“Ina jinki ai.”

“Juwairiyya wannan aure da nake son haɗawa rufin asirinmu ne. Na farko ni zan samu in koma gurin mijina wanda yake fushi dani, na biyu Daddy zai samu mata wacce zata kula dashi sannan ta taimakeshi wajen ɗauke hankalinshi daga kan Mummy, he is lonely he really need a companion. Sannan na uku Juwairiyya ina zaki samu miji mai kyakkyawan hali kuma mai shirin aurenki a kwana bakwai? Kin san waye Mama zata haɗaki dashi? Bakya son kiyi zaɓinki kafin a haɗaki da wanda bakya so? Ki zauna ki yi tunani wallahi wannan shine kaɗai mafitan da in kin amince kin ceci mutane huɗu ne lokaci ɗaya sannan kema zaki samu kwanciyar hankali domin kin san waye Daddy halinshi na gari duk kin sani. Kiyi haƙuri Juwairiyya ki taimakeni, wallahi hankalina zai fi kwanciya idan na san a hannunki na bar Daddy.”

“Wayyo Allah na! Halima idan na auri Daddy me duniya zata ce da ni? Zasu kirani butulu na auri Baban ƙawata.”

“Da Mummy tana raye ne za’a faɗi haka, amma bata doron ƙasa. Sannan duk wani da zai kawo suka akan auren man ina nan ba zan bari ba wallahi. Ke dai amincewarki kawai nake nema.”

 Shiru Juwairiyya tayi tana aikin tunani, wannan shi ake kira ‘Ga samu ga rashi’. Idan ta ƙi wannan haɗin ita ce a cikin tashin hankali, in kuma ta yarda mutanen duniya ba zasu barta ba. To yaya zata yi?

“Halima ki bani lokaci zan yi tunani amma wallahi ina tsoron bakin mutane, sannan shi Daddy zai amince ya auri ɗiyar cikinshi?”

“Wannan duk ba matsala bace, zan kiraki anjima da dare in ji hukuncin da kika yanke Juwairiyya. Don Allah kar ki manta taimakonmu kike yi dukkaninmu sannan hakan shine kaɗai rufin asirinki.”

“To shikenan Halima.”

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

(8)

Juwairiyya ta kasa yanke hukunci, tun tafiyar Halima da yamma take kai kawo a ɗaki ta kasa samun nitsuwa, ana ƙoƙarin kiran maghrib yara suka yi sallama sun kawo shopping ɗin month. A tsakiyar gida suka jibge suka tafi Surayya da Walid suka fara ɗauka zuwa ɗakin Mama, daidai nan kuma Juwairiyya ta fito ta nufi gurin Mama da ke can cikin ɗakinta don ta bata shawara kan wannan gagarumin matakin rayuwar tata.

Tana shiga ta samu Mama tana waya don haka ta samu guri ta zauna har sai da ta gama,

“Kika ce duk waɗanda suka nemi aurenki kika koresu baki da number su, shi kuma Muhammad fa? Gashi yau ma an ce mini ya yo aika.”

“Mama don Allah mu daina ma ɗauko maganan Muhammad, fisabilillahi ina ni ina auren mijin Salima? Wallahi idan ita ce ba zata taɓa auren nawa mijin ba, sannan in dai na auri mutumin nan ko awa biyu ba zan yi ba zamu rabu. Ya tsaneni, nima kuma na tsaneshi.”

“Kar ki sake cewa kin tsani mutum, akul in sake jin kin furta haka ga ɗan’uwanki musulmi. Kuma don baki da mutunci duk ɗawainiyar da mutumin nan yake yi a kanki bakya gani shine zaki jefeshi da kalmar tsana? Uban me ya miki Juwairiyya? Kasheki ya yi ko bunneki ya yi da ranki? A zamanin nan mutum yana iya mutuwa ya bar ƴaƴa amma kaff cikin abokanshi ba za’a samu mai yiwa yaran nan hidima kamar yanda mutumin nan yake miki ba. Baki haihu da abokinshi ba amma a hakan ya nuna har yanzu ba’a rabu ba. Juwairiyya ki kiyayeni, tukunna ma wa kika fitar don ina son sanar da ƴan’uwan babanku da wuri ba sai an je gurin ɗaurin aure ba.”

“Na samu Mama. Daddyn Halima ne.” Juwairiyya ta faɗa hawaye na taruwa a idanunta.

*****

A can gidan su Halima rigima ce ta kacame tsakaninta da mahaifinta wanda ya ɗauki zancen a matsayin wasan yara da kuma rashin hankali.

“Daddy don Allah ka amince ka aureta, wallahi tana cikin damuwa domin Maman rantsewa tayi akan in har bata fito da miji ba zata aura mata duk wanda ta ga dama. Gashi a cikin waɗanda ta ƙi har da ƴaƴan baffanunta da suke ƙauye, duk da cewa bamu da tabbacin a cikinsu Maman zata zaɓa mata miji.”

“Sau nawa zan faɗa miki bana son ƙara jin zancen nan Halima? In ba zamani da kawomu irin wannan lokacin ba yaushe ɗiya zata nemawa ubanta matar aure har ta dinga tura mishi ra’ayin da baya so?”

“Daddy ka tsaya ka ji mana.”

“A zaune ma nake Halima, a zaune nake.” Ya faɗa yana murmushi yana ganin wautarta a fili.

“Daddy na san idan har na tafi baka yi aure ba wallahi zai yi wuya kayi ɗin, shiyasa na zaɓo maka matar da na san zaka ji daɗin zama da ita sannan zata kula da kai.”

“Gashi dama nace miki ina neman baby sitter ko?”

“Daddy please mana.”

 Shiru yayi yana ganin yanda ta dage ita da gasken-gaske so take yi ya auri ƙawarta. In banda shirme irin na Halima ta yaya zai auri ƴar cikinshi kuma ƙawar ƴarshi?

“To na ji. Ita ta yarda ne zata auri tsohon ƙawarta?”

“A’a tace mini zata yi tunani.” Faɗin Halima tana jin tsoro a ranta kar Juwairiyya ta ƙi yin na’am da zancen.

Daddy buɗe jaridarshi ya yi kana ya ɗaura ƙafarshi ɗaya kan ɗaya ya ce,

“Idan ta amince sai ki mini magana in tura gidansu.” Ya yiwa Halima je-ki-ƙarata.

 Cikin murna Halima ta miƙe tsaye tana cewa,

“I promise you Daddy ba zaka yi dana sanin wannan haɗin ba.” Da haka ta saka kai ta fita daga falon shi kuma ya bita da ido yana karkaɗa kai.

“Yaran yanzu akwai shirme.”

Juwairiyya bata sha wahalan samun yardar Mama ba akan aurenta da Daddy, a farko ta nuna hakan ba zai yiwu ba, amma bayan Juwairiyya ta faɗi positive dalilanta na wannan aure sai Mama ta fara sauƙowa.

“Yanzu Juwairiyya tsoho zaki aura kuma baban Halima?”

“Mama ni tsufarshi bata dameni ba, kuma ke ce kika sa na kawo miki shi, kuma gaskiya Mama da in auri wani gwara na auri Daddy.”

“Na janye wancan maganan, zan ƙara miki wasu watannin Juwairiyya.” Faɗin Mama ganin da gaske ƴar tata ta kafe akan zaɓinta.

Shiru juwairiyya tayi tana tunani, ta sani Mama ba zata ƙara mata lokaci mai yawa ba, to don haka ba taga dalilin da zai sa tayi sake reshe kama ganye ba. Ta sani rayuwarta ta lalace tun ranar da Hafiz ya daina numfashi, jindaɗin da ta samu a baya ba zata taɓa samun irinshi ba a gaba in ba wani ikon Allah ba. Daddy bashi da aibu, yana da kyansa daidai gwargwado ga kuma iya gayu fiye da wasu matasan yanzun. Ɗan boko ne sosai sannan yana da sanin addini ga uwa uba sanyin hali. Sau da dama in ta je gidan su Halima ta ga yanda suke wasa da Daddy sai itama ta ji kewar nata uban, sakin fuskarshi ga ƴaƴanshi bai sa suka ɓaci ba, sai ma kyakkyawar alaƙa da ke tsakaninshi da su.

  Tunda Allah ne Ya kawo mata shi zata aureshi don ta huta da matsalar Mamanta. Ta sani a yanzu ba’a yiwa yara auren dole ko kuma a matsa musu sai sun kawo mijin aure, zata iya yiwa Mama musu amma zuciyarta ba zata barta ta aikata hakan ba. Mama tana sonsu, son da a yanzu duk duniya babu wanda zai musu irinshi, Mama ta musu ƙoƙari tun bayan rasuwar mahaifinsu ita take kula dasu babu mai taimaka mata, a haka har ta aurar da ita ba tare da ta rasa wani necessitys na rayuwa ba. Don yanzu Mama ta matsa mata ta fitar da mijin aure sai ta zama maƙiyyarta? Sai ta bijire mata ta watsa mata ƙasa a ido yanda dangin babanta da ma wasu masu son ganin lalacewarsu su mata dariya? Idan ta bijire mata ta san wani irin bala’i zata tarar a gaba? No! Ta gwammace matsalarta ta tsaya a nan kar ta ƙara yawa. Rasuwar Hafiz kuwa ya sa ta gane duniya ba matabbata bace sannan komai mai wucewa ne. Itama bata da tabbacin ƙara wasu shekaru masu yawa. Wannan kenan.

“Mama idan dai ba wani mugun hali yake dashi ba ki barni in aureshi, da yanzu da nan gaban duk ɗaya ne, duk ni ɗin ce.”

Shiru Mama tayi tana jin tausayin ƴar tata a ranta, ta san ta matsa mata amma hakan shine daidai in ba haka ba zama zata yi ba zata yi auren ba, yarinya ce mai jini a jika, in bata nemi namiji don zama a ƙarƙashinshi ba zata nemeshi don biyan wani buƙata.

“Bashi da mummunan hali, Allah Ya sa hakan shi ya fi miki alkhairi. Amma ban taɓa jin ko sau ɗaya kin ce ya zo gurinki ba.” Faɗin Mama cikin damuwa.

“Sau ɗaya ya zo shine na nuna mishi bana ra’ayi, bai sake zuwa ba sai yau ya aiko Halima.” Juwairiyya ta yi ƙarya.

*****

“Daddy albishirinka?” Faɗin Halima cikin tsantsan farin ciki ga mahaifinta da ke shirin shiga bacci don lokacin har ƙarfe tara ta gota.

“Gobe zaki tafi?” Ya tambayeta yana dakatawa.

“Haha funny you. Ta amince Daddy, gobe ka shirya ka je ka samu baffanunta ku yi magana.”

“Halima wai dama da gaske kike yi?”

 Abun da ya faru a gaba ya jawo ɓacin rai tsakanin Halima da mahaifinta har ta kai tana kuka da idanunta, shi tun farkon zancen bai ɗaukeshi a matsayin maganar hankali ba, shiyasa da ta dameshi ya mata kora da hali. Saboda ya san ƙawar tata ba zata yarda ta auri tsoho mai shekara hamsin da biyu ba (52). Yana son ƴaƴanshi ya kuma sabar musu da su zauna su yi wasa da dariya dashi don haka da ta kawo wannan zancen sai ya ɗaukeshi a matsayin raha, ashe da gaske take yi.

“Daddy kar ka mini haka, wallahi na kwaɗaita mata wannan auren har ta sanar da mahaifiyarta duk sun yarda kai kawai ake jira ka gabatar da kanka. Ka rufa mini asiri kar kasa in ji kunya.” Faɗin Halima tana share hawayen fuskarta.

“Ni da nake matsayin uba a gareki Halima ban miki auren dole ba saboda na san illanshi, amma yau ke kike neman tursasani in yi auren da ban shirya mishi ba? Babu batun aure a gabana Halima, rayuwar auren da nayi da mahaifiyarku ya isa sai kuma Allah ya haɗamu a Aljannah. Ki bata haƙuri, sannan ita ma mahaifiyar tata ki bata haƙuri.”

Kuka cur-cur Halima take yi da idanunta, Daddy na neman wargaza mata plan. Sannan ba zata iya tafiya ta barshi shi kaɗai ba sai dai ta kashe aurenta ta dawo su zauna. Zata iya haƙuri da auren nata don shi ya rayu, ta rasa Mummy ba zata so shima su rasashi ba. Shine kaɗai katangar su and she can do anything don ganin bai tafi ya barsu ba.

“Shikenan Daddy, na san ban isa in maka dole ba amma wallahi ba zan barka kai kaɗai a cikin gidan nan ba. Zan kirashi ya sakeni sai in dawo mu zauna, wallahi na gwammace in kashe aurena da in rasaka ko in barka cikin halin maraici.”

“Kar ki kashe aurenki Halima, ki faɗa mata gobe zan je mu gana da iyayenta.” Shine abun da Daddy ya faɗa kana ya tashi ya shige ɗakinshi zuciyarshi na mishi zafi.

Yasan halin Halima, sosai zata iya kashe aurenta ta dawo su zauna, shi kanshi ya san zamanshi shi kaɗai bashi da amfani, saboda disadvantages ɗinshi ya fi yawa akan advantages ɗin. Amma me yasa ba zasu gane cewa Sadiya ita ce rayuwarshi ba? Sannan tafiyarta ya tafi da duk wani sha’awarshi na aure? Tsabar son da yake mata ya kasa yi mata kishiya, sannan tana haihuwar ƴa mace ya mayar da sunanta don ya nuna mata ta fi kowa a gurinshi. Ba haka ya so ba, amma tunda Halima ta kafe sai yayi auren, da ita da ƙawar tata duk zasu yi regretting daga baya, sannan ita Amaryar da kanta zata nemi saki ba sai ya miƙa mata ba.

“Wai ana kiran Juwairiyya a waje.” Faɗin wani yaro a can bakin ƙofar gidansu.

 Tsaki Juwairiyya ta ja kana tace a ranta an kusa daina mata wannan kiran domin haushi take ji ba kaɗan ba. Amma tunawa da ta yi cewa wataƙila Daddy ne sai ta yi saurin ɗauko hijabinta ta fita domin yau saura kwana huɗu a ɗaura musu aure wanda har gidansu ya fara tara baƙi na nesa amma ita ko ganin idon mijin bata yi ba. Sadakinta kawai aka aiko mata har dubu sittin, sannan Halima tare da wasu ƴan uwan mahaifin nata suka kawo mata ƙuɗi dubu ɗari uku da hamsin na wanda zata sayi sutura da kayan kwalliya.

Tana fita ta ja tunga ta tsaya dalilin ganin motar Muhammad da ta yi, kamar ba zata je ba amma ta ga yanzu ne ya kamata ta mayar mishi da martanin kan addu’a mai  kama da gatse da yayi mata a ranar da zasu rabu. Tana isa bakin motarshi ya fitar da ƙafarshi ɗaya waje ya daidaita zamanshi kana ya ce,

“Na ji labarin zaki yi aure, Allah Ya bada zaman lafiya. Sannan ina tunanin a nan zan dakata da turo miki aika da nake yi tunda zaki koma ƙarƙashin wani.”

“Dama ba ni na sakaka ba.”

“Nima ban ce ke kika sakani ba, kuma ba don ke name yi ba, ina yi ne don abokina.”

“Gori ka zo ka mini kenan?”

Kallon ta yayi wanda in zai iya ƙirgawa yau na goma da tara kenan, murmusawa yayi wanda shi kanshi sai da yayi mamakin hakan. Kuɗi ya ciro a cikin aljuhunshi ya miƙa mata yana cewa,

“Ga gudumawata dubu hamsin, ni ba mai kuɗi bane.”

“Bana buƙata, tukunna me ya kawoka ne?” Faɗin Juwairiyya cikin gajiyawa, domin ƴar tsiwar da take son ta mishi ma ta kasa.

“Na zo miki bankwana ne, sannan in baki gudumawata. Ko kina tunanin akwai abun da zai kawoni?”

Bata amsa ba kuma bata karɓi kuɗin da yake miƙa mata ba har hannunshi ya gaji ya mayar ya ajiye a gefenshi.

“Ki matsa zan tafi.” Yana faɗin hakan ya ja murfin motarshi ya rufe.

Bai ƙara seconds uku ba ya bar ƙofar gidan. Ita kuma Juwairiyya jiki ba kuzari ta koma cikin gida, domin wanda take zato ba shi ne yazo ba, shi kuma Muhammad ta so faɗa mishi magana mai zafi amma bata samu damar yin hakan ba, dalilin yayi sanyi sosai ba kamar yanda ta sanshi ba. A da ko gaisuwarta ba ya amsawa amma yanzu har shi yake mata fatan alkhairi a aurenta? Ta wani gurin tana ganin laifinta domin riƙon nata yayi yawa.

Kwanci tashi asarar mai rai. Biki ya zo domin har an yi walima ranar Jumma’a akan washe gari asabar za’a ɗaura auren. Ƙiri-ƙiri Juwairiyya ta ƙi yin kwalliya balle ta yi shiga na alfarma don waliman, a cewarta ba zata ci zamaninta sannan ta ci ta Sumayya ba. Don ita har yanzu bata gaskata cewa aurenta za’a yi ba dalilin har yau bata ga fuskar mijin ba, hakan ya sa a matsayinta na yayar amarya take shige da fice yanda ya kamata. Mama ta so hanata akan cewa ai itama amarya ce amma Juwairiyya ta kafe dole aka zuba mata ido aka barta.

Washe gari aka ɗaura aurensu wanda Halima ce ta kira Juwairiyya cikin tsantsan farin ciki tana cewa cikin waƙa.

“An ɗaura, an ɗaura. Kin zama matar Daddy Allah na gode ma.”

Jin haka ya sa zuciyar Juwairiyya ya buga da ƙarfi, kenan yau ta zama matar wani ba Hafiz ba? Bata iya cewa komai ba ta kashe wayar hawaye na zuba a idanunta. Ita kuma Halima tsabar murna bata ma gane ba domin tana cikin ƴan’uwansu da suka taru don yin ƙaramin wunin taya Daddy aure.

 Da rana aka zo ɗaukan amarya inda a nan ne Juwairiyya ta ga tijarar Mama.

“Don baki da hankali sai ki fita ba tare da izinin mijinki ba?” Faɗin Mama kenan tana hararar Juwairiyya.

Ihu ne kaɗai Juwairiyya bata kurma ba amma sai da hawaye ya ɗigo mata, juyawa ta yi ta shige banɗaki ta kira Halima don ta tambaya mata Daddy.

“Wannan ba hurumina bane Aunty Juwai, zan turo miki numbernshi ki kirashi ki tambaya da kanki.”

“Halima kar mu yi haka da ke don Allah. Wallahi ba zan iya ba, ban san ta yaya zan fara mishi magana ba.” Faɗin Juwairiyya tana jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaƙe wuyan Halima.

“A haka zaki koya matar Daddy, zan tura miki yanzun nan.” Da haka Halima ta kashe wayarta, itama ta rama.

Juwairiyya tsabar haushi sai da ta naushi gini da ƙafarta, zafin da ta ji yasa ta yi hankali ta sunkuya tana sosa gurin tana wash wash.

Ƙarar shigowar saƙo ta ji a wayarta wanda tana dubawa ta ga numbern Daddy ne kamar yanda Halima ta mata alƙawari. Kamar ba zata kirashi ba amma ta ga in bata kira ba ita ce da asara, ta jima tana burin Allah Ya kawota ranar auren Sumayya ta yi ruwa ta yi tsaki, don haka ta yanke shawarar kiranshi.

Ringing biyu ya ɗauka Juwairiyya ta ɗaga mishi gaisuwa cikin ladabi kamar yanda take gaisheshi idan ta je gidansu Halima a da.

“Daddy dama ina son zuwa kai Amarya ɗakinta ne.”

“Babu komai zaki iya zuwa.”

“Ai idan na faɗawa Mama ka barni ba zata yarda ba, Daddy ko zaka mata magana?”

Sai da yayi ɗan jimm wanda har ta fara tausayin kanta sannan ya ce,

“Ki jirani zan zo na kaiki.”

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

 Suwaiba Muhammad

Marubuciyar Matar Kabila

Fatu A Birni

Ruwan Zuma

Canjin Muhalli

(9)

 Zuciya na lugude Juwairiyya ta koma ɗaki inda ta bar ƙawayenta da suka zo tayata murnar aure ciki kuwa har da Salima. Wasu a cikinsu gulma ce ta kawo su domin basu yarda da cewa wai Daddyn Halima ƙawar tasu ta aura ba, wasu kuma suna ganin hakan haɗine daga Allah kuma sun dace da juna, domin kuwa dukkaninsu sun rasa abokanen rayuwarsu zasu tausayawa juna, kuma zasu fi fahimtar juna.

 A gefen Salima ta zauna wacce take hira da sauran ƙawayen nata cikin sabo domin suna ɗan haɗuwa a gidan Juwairiyya lokacin da Hafiz yake da rai. Taɓa Salima ta yi wacce take bawa Hafiz Junior kunu a feeder ta rankwafo tana tambayarta menene.

“Wai Daddy shi zai zo ya kaini gidan amaryar.”

 Wata shewa Salima tayi wacce ta sa idon sauran ƴan ɗakin ya dawo kansu amma Juwairiyya ta yi saurin raba hankalinsu don kar su tambayi menene ya faru. Cikin dabara kuma tasa suka tafi don ta nuna musu itama zata bi tawagar Amarya Sumayya da za’a kai gidan iyayen mijinta da ke nan bayan gidan Sarki.

 Ɗaki ya rage daga Juwairiyya sai Salima da Hafsat (Ƙanwar Hafiz) waɗanda suma zasu je gidan amaryar. Suna zaune har ƴan tafiya da amarya suka tafi sannan Daddy ya mata text a waya. ‘Ki fito ina waje.’ Shine abun da ya rubuta ta ɗauki mayafinta zuciyarta na bugu wanda bata san dalilinshi ba.

 Kafin ta fita sai da ta faɗawa Mama wacce ta ƙaryatata sai da ta aika aka dubo mata eh lalle shine sannan ta bari suka fita. Ita ta fara isa bakin window ta russuna ta gaisheshi sannan su Salima ma suka rufa mata baya tare da miƙa gaisuwarsu cikin girmamawa domin ya musu kwarjini ba kaɗan ba, dukkansu kuwa sun san ya haifesu. Sanye yake cikin plain white yadi mai tsada da aka yiwa ɗinkin jumfa da gare sai kuma hularshi ita kuma dark blue, sosai yayi kyau kamar ba ɗan shekara hamsin da ɗori ba.

 Daddy cikin sakewar fuska ya amsa musu kana ya dubi Juwairiyya wacce tun fitowarta har lokacin bata kalli fuskarshi ba ya ce,

 “Mu tafi ko?”

“Umm Daddy dama Hafsat tana da mota zamu tafi tare kar mu wahalar da kai.”

“Ba damuwa amma tunda na zo ku shigo in kaiku.”

Juwairiyya bata son musu dashi don dalilin da yasa kenan ɗazu bata ƙara kiranshi ta faɗa mishi cewa akwai mota a hannunsu ba, ita dama buƙatarta ya yiwa Mama magana ne amma kuma sai ya ce zai zo ya kaita.

Juyawa tayi tana kyafta idanu ta kalli su Salima da suke mata dariya ƙasa-ƙasa ta ce,

“Hafsat ki biyomu a motarki, ke kuma Salima ki shigo mu tafi.” Ta faɗi hakan tana karɓan Hafiz Junior daga gurin Mamanshi.

Da haka ta zagaya ta shiga gidan gaba tare da yaron sannan ta rufe marfin motar, tana jiran Salima ta shigo amma sai ta hangota ta mirror ta shiga ta Hafsat. Basu kyauta mata ba da suka barta daga ita sai shi, nan da nan kuma ta ƙara nitsuwa domin numfashin kirki wannan bata yi. Shi kuma Hafiz Junior wasanshi yake yi da agogon hannunta bai damu da cewa mamanshi bata kusa ba, ya saba da Juwairiyya domin tunda ya fara gane mutane Salima take turoshi gurin Juwairiyya tare da mai aikinta yayi awa ɗaya zuwa biyu sai a mayar dashi, sannan ita kanta Saliman tana zuwa gidansu Juwairiyya sa’i da lokaci.

“Da alama ƙawarki ta fi son shiga can. Mu tafi ko?” Juwairiyya ta tsinkayi muryar Daddy wanda yake ƙoƙarin kunna mota.

Gyaɗa kai tayi tamkar yana ganinta kana suka fara tafiya su Hafsat na bin su a baya. Hannun Hafiz Junior ta kama tana wasa dashi don ta rasa me zata yi ɗaya taƙamaimai, duk kuwa da sanyin A.C da yake cikin motar wanda ya haɗu da daddaɗan turaren Daddy bai hanata haɗa zufa kaɗan a goshinta ba. She is nervous, she really is.

 Sai da suka daidaita akan titi sannan ya tambayeta ina zasu yi, a hankali ta dinga mishi kwatance har suka iso wata magana bayan nan bata haɗasu ba. Yana yin parking ta mishi godiya tare da buɗe marfin motar zata fita ya dakatar da ita ta hanyar kama hannun Hafiz Junior.

“Dama kina da ƙaramin yaro ne?” Ya tambayeta wanda sarai ya sani bata taɓa haihuwa ba.

“Ɗan abokin marigayi ne, takwaranshi.”

“Allah Ya mishi rahama. Ga wannan ku yiwa amarya liƙi.” Da haka ya damƙawa Hafiz Junior bundle ƴan naira ɗari yaron ya karɓe da sauri zai tura a bakinshi.

“Daddy da ka barshi kawai.” Faɗin Juwairiyya tana ƙoƙarin kwace kuɗin amma ya damƙe har yana shirin kokawa da ita.

 Bata yi aune ba ta ji sautin dariyar Daddy a hankali domin da alama abun ya ƙayatar dashi.

“Yaro ma ya fiki sanin me ya dace, he meant to say ba’a maida hannun kyauta baya. Sai anjima.” Yana gama faɗin hakan annurin fuskarshi ta ɗauke kamar wanda ya tuna da wani abu.

Ganin haka yasa Juwairiyya saurin fita daga motar har tana cin tuntuɓe, tana matsawa daga jikin motar ya juya a hankali a bar gurin ba tare da ya ƙara kallonta ba. Sai a lokacin ta tuna cewa ba fa auren soyayya suka yi ba, aure ne na rufin asiri kuma wanda aka yi shi cikin gaggawa, aure ne da aka yi tsakanin ruhi biyu wanda suke cikin damuwar rashin masoyansu. Nan take ta ji ta ƙara tausayin kanta akan wanda take yi, ko yaya rayuwarsu zata kasance? Ko a wani matsayi Daddy zai ɗauketa alhali ya saba da ganinta a matsayin ƙawar ƴarshi.

 Bata gama wannan tunanin ba su Salima da suka yi parking a bayansu suka iso suna ɗaga nata signa suna dariya.

“Me kika bashi haka har ya biya da tukuici?” Faɗin Hafsat tana leƙen fuskar Juwairiyya wacce ke ƙoƙarin shanye hawayen idanunta.

“Kun fiye gulma wallahi. Masoyi (Hafiz Junior) ya gani wai ya mishi kyau shine ya bashi.” Ta faɗi hakan tana miƙawa uwarshi kuɗin bayan ta yi nasarar kwacewa daga hannunshi ganin ya fara kaiwa baki.

Kuka Hafiz J ya dalla yana miƙa hannu ga mamanshi da alama ya tuna da ita ne ko kuma don kuɗin ya koma hannunta ne sai Allah. Hakan yasa su Salima suka fasa faɗin abun da yake bakinsu suka dawo rarrashinsa daga baya suka ɗunguma cikin gidan ganin sauran mutanen da suke waje suma sun shige ciki.

 Da la’asar aka saka anko aka yi buɗan kai, zuwa isha kowa ya watse aka bar Amarya da Angonta da kuma halinsu. A daren ranar misalin ƙarfe sha ɗaya na dare Juwairiyya tana zaune a ɗakinta inda zata kwana da mutane biyar waɗanda suka zo biki ta jawo jakarta da nufin ɗauko igiyan charger sai ta ga kuɗi mai yawa har dami biyu. Nan da nan ta gane  Salima ce ta saka mata domin ɗayan babu makawa kuɗin da Daddy ya bata ne ta kasa gida biyu ta ɗauki rabi sannan ta ajiye mata rabi, ɗayan kuma dubu hamsin ɗin da Muhammad ya bata na gudumawa ne ta ƙi karɓa shine ya aiko matarshi dashi.

Samun kanta ta yi da jin sanyi a ranta domin duk yanda ta kai da son riƙe Muhammad a ranta yanzu ta rage, sai yanzu take tambayar kanta dama me ya mata? Da wannan tunanin ta ɗauki wayarta bayan ta jonata a charge ta turawa Salima text ɗin godiya tare da cewa ta miƙa godiyarta ga Muhammad.

Bayan kwana uku gida ya watse ya dawo na masu gidan su kaɗai, ko’ina an wanke an gyara tamkar ba’a yi biki ba sai kuma kewan Sumayya kowa ke yi musamman Iya (Kakarsu) da yake da ita Sumayya take kwana.

 Ba’a ƙara wasu kwana biyun ba Mama ta zauna da Juwairiyya akan maganar tarewarta a gidan Daddy.

“Ina ta jiran ki mini maganan tarewanki amma sai naji shiru, yaushe ya ce zaki tare?”

“Yace duk lokacin da na shirya domin gidanshi ba ya buƙatar wani gyara.”

“To kayanki na yanzu zaki tafi dasu ko kuma wasu zaki canja?” Mama ta tambayeta wanda ta san amsan ko ba’a faɗa mata ba.

“Mama dama tun wancan lokacin na ce miki a sayar ba zan ƙara amfani da su ba, kayan kitchen kaɗai zan ɗauka da sauran ƙananun abubuwa amma banda gado da kujeru.”

“Shikenan, zan yiwa Bala Capenter magana sai ya sayesu a baki sabo, in ma za’a yi ƙari ne sai mu yi. Ana ribibin bikin nan masu hayan gidanki suka yi biya na shekarar gaba, sai ki rubuta ki ajiye, kuɗin kuma yana cikin account ɗina in kina so in turo miki.”

“A’a Mama ki ajiye, idan ina da buƙatar wani abu zan miki magana.” Faɗin Juwairiyya tana jin tsoron Allah da kuma tsoron rayuwa na daɗa shiga jikinta.

Wai yau ita ce mamallakiyar gidan ta da rayu ita da Hafiz a ciki? Bayan gama takabanta aka haɗu don rabiyan gado, a nan aka haɗa dukiyar da Hafiz ya mallaka wanda ya kunshi gidan da suke ciki, babban gona, mota da kuma wasu kuɗade da ke cikin banki. Iyayen Hafiz da suka tashi rabiyan sai basu yiwa Juwairiyya kyashi ba, a maimakon su sayar da komai sai a raba kuɗi kamar yanda wasu suke yi sai suka damƙa mata gidan a matsayin nata gadon sauran babban gona, mota da kudaɗe kuma suka raba tsakanin iyayenshi da ƴan’uwanshi. Bayan an gama rabiyan gado aka damƙawa Juwairiyya takardun gida da kuma makulli, a wancan lokacin tana tunawa itama miƙawa Mama ta yi domin kamar haushin kowa take ji, wai har za’a tsaya ana raba dukiyar Hafiz? Yaushe ma mutuwar ta fita a zuciyarsu? Abun da ta manta shine haka Allah Ya tsara domin gujewa fitina da kuma samun sauƙi ga shi mamacin.

“To sai ku yi magana ku tsaida rana a kaiki a wuce gurin.”

“Mama wallahi sai in dinga ganin kamar bakya sona kin gaji da kallona, kamar zamana a gidan wani abu nake tare miki.” Faɗin Juwairiyya a marairaice kamar zata yi kuka.

“Sonki da nake yi yasa nake son ki shiga inda zaki zama mai mutunci abun mutuntawa. Shekaru aru-aru ina zawarci Juwairiyya, na ga mutane kala-kala a wannan journeyn nawa wanda da ba don ku ba da nima nayi auren na rufawa kaina asiri. Amma na ga bazan iya watsar daku ba, tunaninku kaɗai ba zai barni in yi zaman gidan mijin cikin kwanciyar hankali ba, I just couldn’t. Ke kuma babu ɗa babu jika ga ƙanƙantar shekaru, aure ne kawai ya fi dacewa da ke. Zaki fahimceni komin daren daɗewa Juwairiyya.”

Sati daya da haka aka yiwa Juwairiyya jerenta a gidan Daddy gefen matar gidan ta da, falo ne madaidaici sai ɗakuna uku a ciki wanda ɗaya yake a rufe wanda nan ne ɗakin Mummy na da, ɗayan ɗakin shi aka barwa Juwairiyya yayin da ɗayan kuma yake na baƙi kuma na Halima a da. Gefen maigidan kuma shima falo ne babba mai ɗauke da ɗakin bacci ɗaya da kuma wasu ɗakuna biyu a waje wanda ɗaya na ɗanshi Abduljalil ne ɗayan kuma na baƙi maza.

 Yanayin tsarin gidan sosai ya burge ƴan’uwanta da suka mata jere, bayan sun koma suka faɗa mata har sabon fenti aka yiwa sashen nata. Washe gari kuma Juwairiyya ta shirya tarewa.

Sosai Mama tasa aka mata gyara ciki da waje duk da cewa Juwairiyyan ta ƙi yarda a farko, amma da Mama ta zare mata ido sai ta dawo cikin hayyacinta aka mata gyaran fata, kitso da kuma kunshi mai kyau. Nan da nan ta fara walwali ta fito a Amarya sakk sai dai raman da tayi ne ya kasa ɓuya.

Halima ce tare da wata ƙanwar Daddy wacce zata yi sa’ar Mama suka zo ɗaukanta bayan sallah isha, Juwairiyya kuka take yi kamar yau ne za’a kaita gidanta na fari. Sosai ta bawa Mama tausayi wacce ta kasa magana saboda ta san in dai ta buɗe bakinta itama zata taya ƴar tata kuka, tana ji tana gani aka fitar da ita daga gidan don zuwa bautawa ubangiji.

Waɗanda suka mata rakiya basu jima ba suka tafi bayan sun mata addu’a tare da fatan alkhairi. Salima ce ta ƙarshen tafiya wacce Muhammad ya zo ya ɗauka jimm kaɗan da tafiyan sauran. Juwairiyya ta yi kuka har sai da ta ji kanta ya fara ciwo sannan ta tsagaita, duba agogo ta yi taga ƙarfe goma sha ɗaya na dare, to ina maigidan nata yake?

 Tashi tayi tana kallon tsarin ɗakin irin yanda tace tana so, babu hayaniya domin set ɗin gado ne mai haɗe da mirror da kuma wardrobe, sai ɗan decoration kaɗan a jikin bango don kar ginin ya zama wayam. Banɗakin da ke cikin ɗakin ta shiga nan ma ta sameshi tsaf irin yanda ta hasko a ranta, alwala ta ɗauro sannan ta zo ta tada sallahn shafa’i da witri. Tana idarwa ta ji ana kwankwasa ƙofar ɗakinta ta yi sauri miƙewa tsaye zuciyarta na bugawa ta dubi kanta a madubi, in banda ramar da ta yi babu abun da ya samu fuskarta don ta wanke duk kwalliyan da aka mata kafin a kawota.

 Ƙara kwankwasa ƙofar aka yi wanda hakan yasa ta isa ta buɗe tana mai matsawa gefe. Daddy ne ya shigo ɗauke da wasu ledoji a hannunshi bakinshi ɗauke da sallama amma fuskarshi babu walwala sannan ba’a tsume ba.

Russunawa tayi ta gaisheshi bayan ta zauna a bakin gado shi kuma ya amsa yana mai shiga cikin ɗakin ya tsaya a gefen mirror sannan ya ajiye abun hannunshi akan ƙaramin carper ɗin da yake bakin gadon,

 “Ga abinci kici in kina jin yunwa, in kuma kin koshi ki adanashi.” Ya faɗa yana kalle-kallen ɗakin wanda kwata-kwata ma hankalinshi baya ma kai.

Gyaɗa kai tayi kana ta haɗa ta ‘to’. Daga nan suka yi shiru na wasu seconds goma kana Daddy ya tako zuwa bakin ƙofa zai fita sai kuma ya tsaya ya fara magana ba tare da ya kalli inda take ba,

“Farko zan fara baki haƙuri akan yanda zaki samu gidana, I’m not trying to belittle or humiliate you amma wannan auren bana sonshi Juwairiyya. Kema kuma na san kin yi auren ne don kaucewa wata matsala da ke shirin faruwa dake to kin ga babu batun ɓoye-ɓoye tsakaninmu. Kin samu abun da kike so, ƙawarki ma ta samu abun da take so sannan nima ta wani gurin na samu relief domin babu wanda zai ƙara mini maganan aure da illolin zama ni kaɗai a gida. Zan ƙara baki haƙuri Juwairiyya don ba zan taɓa zama mijin da kika rasa ba haka nima ba zaki iya maye gurbin matata da na rasa ba. Zan yi ƙoƙarin sauƙe duk wani nauyinki da ke kaina na ci, sha da sutura, in kuma kina buƙatar wani abu kar kiyi ƙasa a gwiwa ki sameni ki faɗa mini, I promise in dai bai fi ƙarfina ba zan saya miki ko in mallaka miki. You are free ki je duk inda kike so amma sai kin faɗa mini, sannan Halima ta faɗa mini kina son komawa Jami’a, zan nema miki addmission da zarar shekara ta zagayo kici gaba da karatunki. Sannan abu na ƙarshe ki kiyaye lafiyarki please, ko ciwon kai kike ji ki faɗa mini mu je asibiti. Kin ji?

“Na ji Daddy.” Faɗin Juwairiyya cikin sarƙewar murya kanta a ƙasa.

“Allah Ya bamu haƙurin zama da juna, sai da safe.” Da haka ya sa kai ya fice daga cikin ɗakin ya bar Juwairiyya cikin tausayin kanta da kuma sabon gurin da ta tsinci kanta a ciki.

 Itama ta sani babu soyayya a tsakaninsu amma yanda ya nuna mata da ita da babu duk ɗaya sai ta ji kuka ya kwace mata, minti kaɗan da haka ta share hawayen fuskarta don bata ga dalilin zubarsu ba, ko itama ma bata shiryawa zaman aure ba sai da Mama ta matsa mata sannan ta saduda, to tunda ta samu mai irin tunaninta ai faɗuwa ce ta zo daidai da zama. Zata rayu dashi duk da cewa babu ɗigon sonshi a zuciyarta amma zamansu shine rufin asirinta kuma rufin asirinshi, they are the perfect couple yet far away from perfect.

TAFIYAR MU

 Suwaiba Muhammad

Free page

(10)

  Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah. Yau wata ɗaya har da sati uku da auren Juwairiyya da Daddy, sosai ta dawo da jikinta ta murje tayi kyau. Hutu ta samu a gidan Daddy wanda take samun irinshi a gidan Hafiz, bata aikin komai sai girki domin kuwa tana da mai wanke-wanke da shara da take zuwa kullum tana tayata aiki domin har falon Daddy ita take sharewa ta goge, ita kuma sai ta gyara mishi ɗakinshi idan ya fita Office.

 Juwairiyya bata da damuwan komai sai ta maigidanta da yake treating ɗinta kamar ƴar cikinshi, kullum da safe kafin ya fita aiki zai shigo har sashenta ya dubata ta bashi breakfast ɗinshi a cikin basket ya tafi dashi bayan ya tambayeta ko tana da buƙatar wani abu. Idan tana son fita zai barta baya hanata amma da sharaɗin ta dawo kafin maghrib. Yana dawowa daga aiki da yamma kuwa zai yi wanka ya ci abinci wanda shine na rana kuma na darenshi sannan ya zo ya ƙara dubata ya ji yaya ta wuni sannan ko tana da matsala.

 A yanzu da ta fara sabawa dashi ta sake sosai har tana iya kallonshi cikin ido idan tana mishi magana wani lokaci akan abun da yake son a dafa mishi da yake yana da ciwon Diabetes ko kuma wata magana ta daban. Rayuwarsu ta zama kamar na Boss da employee wanda gaskiya ita Juwairiyya ta fara gajiya.

 Zamanta da Hafiz ya koya mata juriya a fagen auratayya wanda har daga baya itama ta kama hannu ta zama daidai shi, matsalar da take fuskanta a yanzu shine Daddy ko hannunta bai taɓa riƙewa ba balle ya kirata shimfiɗarshi. Gashi ita ba itace bace domin kuwa tana buƙatar ɗa namiji a rayuwarta musamman yanzu da ta samu hutu, cima mai kyau ga kuma kwanciyar hankali. Sai yanzu ta fara gane dalilin da yasa Mama ta matsa mata tayi aure don ita kanta ta fara gajiya da wannan zaman.

 Yau ma video call take da Halima mutanen Turkey wacce tun bayan aurensu da kwana biyu ta koma gurin mijinta.

 “Ya zaman naku dai? Da fatan babu wata matsala?” Faɗin Halima tana kwaɓa batter ɗin cake a kitchen ɗinta yayin da laptop ɗin ke gabanta tana kallon Juwairiyya ta ciki wacce take shan Mango a wani ƙaramin bowl.

“Kullum maganarki kenan, ke bakya gajiya ne ko ke uwamu ce?” Juwairiyya ta bata amsa tana cakan guda ɗaya da fork kana ta kai bakinta tayi rolling ɗin idanunta ga Halima.

“You know you two are my responsibilities, dole ne in dinga bibiyarku don na ga alama kuna da taurin head.”

“Halima baki da kunya, Daddyn ne mai taurin kai?” Ta yi dariya.

“Ni kin ji na kira sunan Daddy?” Itama ta yi dariya ta fara juye batter ɗin cikin baking pan.

“Ohh da ni kike kenan?”

“Ni na isa Aunty Juwai matar Daddy? Amma seriously ya kuke?”

“Wallahi muna zaman lafiya bamu da matsala, bai taɓa ɓata mini rai ba sai dai ban sani ba ko ni na taɓa ɓata mishi.” Ta faɗi iyakar gaskiyanta.

“I’m sorry to ask and I know it’s not my place amma ya batun ‘the do’?”

“Ya Salam Halima! Zan yi kamar ban ji me kika ce ba.” Juwairiyya ta faɗa cike da kunya tana hararan Halima.

“Mu bar maganar wasa Aunty Juwai, da ni da ke duk ba yara bane, kuma mun san yaya aka yi auren nan sannan ciwon ƴa mace na ƴa mace ce. Wallahi burina yanzu bai fi in ga kuna walwala tare ba kamar kowanne normal mata da miji, I’ll love to see that day.”

Shiru Juwairiyya tayi tana tunani domin itama tana son ta samu wani su yi maganan ko za’a bata shawara, har yau kuma har gobe babu wanda ya san yaya aka yi aurenta da Daddy bayan Halima. To wa zata je gurinshi ta buɗe mishi cikinta in ba Haliman ba? Hakan ya sa ta kaɗa baki tace,

“Halima babu wannan batun domin ko yatsata bai taɓa kamawa ba.”

Runtse ido Halima tayi sannan ta buɗe ta isa gaban oven ta saka cake ɗin sannan ta dawo ta zauna kan dogon stool ɗin da ke kusa da kitchen island ɗin. Sai a lokacin dukkan hankalinta ya dawo kan Juwairiyya wacce ta ajiye bowl ɗin Mangon a gefe kamar ya fita a kanta.

“Aunty Juwai wallahi ban yi tsammanin Daddy zai ɗauki wannan lokacin ba tare da ya saisaita tsakaninku ba. Wallahi shi mutum ne mai fara’a da kuma sauƙin kai, tun bayan rasuwan Mummy na lura ya canja sosai but I thought daga baya zai dawo yanda yake ashe I was wrong. Lokaci yayi da zai cire komai a ranshi domin mutuwa tana kan kowa.”

 Juwairiyya bata ce komai ba illa kaɗa kanta da tayi tana aikin tunani, itama tana son Hafiz ya tafi ya barta sannan har yanzu bata mantashi ba balle ta daina sonshi, amma a hakan take son ci gaba da rayuwa kamar kowa tunda mutuwa bata hana walwala.

“Ko kuma ina zaton bai yi tsammanin zaki so ku zauna a matsayin ma’aurata bane domin sai da na mishi barazanar kashe aurena sannan ya yarda.”

“Me kika ce?” Juwairiyya ta faɗa da ƙarfi tana zaro idanunta waje cikin mamaki.

“I’m sorry ban faɗa miki ainihin abun da ya faru ba amma hakan ba hujja bace da zai sa ya ƙi ƙarfafa auratayyanku ba. Ke mace ce Aunty Juwai, kiyi amfani da iliminki da wayonki da kuma young jikinki ki jawo hankalinshi kanki ki nuna mishi kina son a gyara wannan auren. Please try.”

“Mu bar maganan nan kawai Halima. Ya batun cooking classes ɗinki?” Da haka Juwairiyya ta shashantar da zancen ba don ba zata gwada abun da Halima ta faɗa ba sai don tana jin nauyinta domin Daddy da yake uba a gareta.

 Bayan sun gama hiran Juwariyya ta zauna ta fara tsara yanda zata canja musu Tafiyar tasu, bata ce tana mishi so irin na soyayya ba amma kyautatawan da yake mata yasa ta ji tana ƙaunarshi domin kuwa ai zuciya ma tana son mai kyautata mata. To ko a haka aka tafi ta sani zata ji daɗin zama dashi sannan itama zata yi ƙoƙari wajen kyautata mishi da kuma bashi girmanshi.

 Sai da aka yi sallan azahar sannan ta tashi ta ɗaura musu abincin rana wanda zai zarce ya zama na dare kamar yanda suka saba kullum. Kafin la’asar ta gama komai ta sallami mai aikinta kana ta faɗa wanka, cikin lokaci ƙanƙani ta gama shiryawa cikin farar riga mai V neck da baƙin wando wanda yake da adon lace a can ƙafan wandon. Sosai tayi kyau kamar wata ƴar tsana hakan yasa ta dinga juyawa a gaban madubi tana kallon kanta, in ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce ta taɓa aure domin jikinta yana nan da ƙuruciyarsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta nitsu tana ganin suturan da ta saka, yau ne karon farko da zata taɓa saka English wears a gidan Daddy domin kuwa kullum a cikin atampa take watarana har da gyale ko Hijab.

Tana jin ƙarar shigowar motarshi zuciyarta ta buga da ƙarfi amma ta danne kana ta shiga kitchen don kai mishi abinci sashenshi. A da tun kafin ya dawo zata kai ta ajiye shi kuma idan ya ci zai zo ya duba lafiyarta to shikenan sai wata safiyar ko kuma in ya kawo mata abun kwalama da dare.

 Sai da ta bari ya shiga ɗakinshi ya gama abun da zai yi yana fitowa ita kuma ta shigo hannunta ɗauke da tray mai ɗauke da warmers ɗin abincin.

“Daddy sannu da dawowa.” Ta faɗa cikin ladabi har tana russunawa kamar yanda ta saba.

Daddy da bai yi expecting ganinta haka ba sai ya tsaya yana kallonta da alama tafiyar zata yi kyau. Bai amsa ba hakan yasa ta yi gyaran murya ta matso kusa dashi tana kallonshi innocently tace,

“Daddy baka da lafiya ne?”

Firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga sannan ya juyar da kanshi kan dinning table inda ta jera mishi abincin ya ce,

“No, lafiyata kalau. Kina lafiya?”

“Lafiya kalau, sai zaman kaɗaici. Gidan shiru babu kowa watarana har tsoro nake ji.”

“Uhm, zaki saba a hankali Juwairiyya. And ki daina jin tsoro babu abun da zai sameki.”

“To Daddy.” Ta faɗa tana murmushi sai can kuma murmushin nata ya faɗaɗa tayi wani guntun tsalle ta riƙo hannunshi tana cewa, “Daddy albishir!”

Ƙaramin ruɗewa yayi ko kasa numfashi yayi ne bata gane ba amma bai amsa wannan albishir ɗin da wuri ba sai da ta ƙara maimaitawa. Hannunshi kuwa da ta maƙale a ƙirjinta tana bouncing shi Daddy yake kallo sai kuma ya dawo ya kalli fuskarta.

“Goro.” Yayi gyaran murya yana ƙoƙarin zame hannun nashi amma ta ƙi sakinshi.

“Na duba internet na samu dishes irin naku masu diabetes da yawa shine yau na maka kunun acca da cookies sugar free.”

“Sounds amazing, to nagode bari in ci abinci da cookies ɗin sai anjima da dare in sha kunun. Kin ga yau babu shan fruits.”

“To Daddy, bari in ɗauko maka Cookies ɗin.” Da haka ta fita daga falon cikin walwala har ta ɓace masa da gani.

“Ya Allah.” Faɗin Daddy yana takawa zuwa dinning table.

Yana fara zuba abinci a plate Juwairiyya ta dawo hannunta ɗauke da wani kyakkyawan ƙaramin tray da cookies ɗin a ciki, a gefen Daddy ta ajiye sannan ta matso kusa dashi har jikinsu na gogan na juna ta ce,

“Bari in saka maka.” Da haka ta karɓe serving spoon ɗin ta ƙarisa saka mishi ya fara cin abincin jiki a sanyaye.

Abun da ta lura dashi shine kamar ya rage walwala, ko dai da gaske baya son mu’amala da ita. Ji tayi gwiwanta yayi sanyi ta fara waswasi a ranta ko dai bata burgeshi bane? Ko dai tayi zumuɗin yayi yawa ne? No! Bata fara don ta bari ba! Dama ba lokaci ɗaya zata karkato da hankalinshi gareta ba, dole sai ta ɗauki lokaci kuma sai ta jajirce. A ƙarshe tana fatan Allah Ya sa wanka ya biya kuɗin sabulu.

“Abincin yayi daɗi?” Ta tambayeshi bayan ta dawo da walwalar fuskarta sannan ta zauna a gefenshi.

“As always Juwairiyya. Na faɗa miki girkinki yana mini daɗi, nagode.”

Murmushi ta yi wannan karon har cikin ranta wanda yasa kumatunta suka lotsa ciki kana ta miƙe tsaye tana duban agogon hannunta ta ce,

“Bari in barka ka huta, sai anjima Daddy.” Ta haka ta fita daga cikin falon bayan ta ɗauki Cookie ɗaya tana humming waƙa a hankali.

Tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar kana ta jinginu da gini tana gwalalo idanunta waje, lallai ta cancanci a jinjina mata. Daddy da take jin kunyarshi yau shi take ƙoƙarin seducing? But amma bature yace desperate times call for desperate measures, Daddy mijinta ne halalinta ba wani random mutum a waje ba don haka zata iya yin komai don ganin ta inganta wannan zama nasu da bata san yaushe ne ƙarshenshi ba.

A ƙa’idan Daddy idan ya dawo daga office zai zauna a gida har sai an kira maghrib, daga nan kuma in ya fita ba zai dawo ba sai an yi isha. Don haka Juwairiyya tana ganin an yi isha ta yi wanka tare da canja kaya wannan karon zuwa wata doguwar riga ɗinkin bubu da aka yiwa aiki da stones. Sosai take walwali sannan ta yiwa kanta simple kwalliya wanda ba zai sa ace she is trying so hard ba. Da haka ta kallaba ɗauri mai ƙayatarwa kana ta nufi sashen Daddy bayan ta ɗauka mishi kununshi.

Da sallama ta shiga ta samu yana zaune a ƙasan carpet yana karatun Jarida da gilashi a idanunshi, sanye yake cikin jallabiya fara tass wacce ta mishi kyau ba kaɗan ba a fuskar juwairiyya. Ta lura in dai ya dawo gida kayan sakawanshi kenan don yana dasu design kala daban-daban kusan ashirin a wardrobe ɗinshi wanda take gani in ta je mishi gyara.

“Daddy sannu da dawowa. Ga kununka.” Ta faɗa tana ajiye flask ɗin a kan dinning table.

“Sannunki da ɗawainiya, ki sako mini a kofi.”

Da haka ya koma karatun jaridarshi Juwairiyya kuma ta zuba mishi kunun tare da saka mishi irin sugarn su sannan ta gauraya ta tako zata kawo mishi. Da gangan tayi ɗan tuntuɓe kaɗan wanda tayi kamar zata faɗi amma ta tare kanta, Daddy cikin azama ya miƙe yana tambayarta lafiya kana ya yiwo kanta ya kamo hannunta tare da karɓan kofin yana mata sannu.

“Subhanallahi, Juwairiyya garin yaya haka? Ina baki ji ciwo ba kuma kunun bai zuba a jikinki ba?” Ya faɗi hakan yana duba dukkan jikinta har lokacin bai saketa ba.

Marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka cikin shagwaɓa tace,

“Ina tahowa zan kawo maka kunun shine na ji nayi tuntuɓe, amma bai zuba a jikina ba.”

“To Masha Allah, amma ki dinga kula next time Allah Ya tsare na gaba. Ki zo ki zauna na ga kamar kina karkarwa.”

Juwairiyya tana son cewa shine yake karkarwan amma ta kunshe bakinta tayi shiru tana dariya a ranta. Halima ta faɗa mata weakness ɗinshi shine Cuta. Da zarar ya ji ahalinshi basu da lafiya to fa duk wata kulawa ta duniya zai nuna musu, yana tausayawa mai cuta sannan baya raina cuta ko da ciwon kai ne dalilin abun da ya faru da tsohuwar matarshi shiyasa a daren da aka kawo Juwairiyya yace ko ciwon kai ta ji ta faɗa mishi su tafi asibiti.

A kan kujera ya zaunar da ita kana ya ajiye kofin akan center table sannan ya dawo gefenta ya zauna yana kallon yanda take numfashi ɗai-ɗai alamar dai ta tsorita.

“Daddy ka ji har yanzu zuciyata bata daina bugawa ba wallahi.” Da haka ta ɗauki hannunshi ta manna a ƙirjinta saitin zuciyarta.

Daddy dai bai ji bugun zuciyar ba amma ya ji wani abun na daban, cikin dabara ya sauƙe hannun nashi ya ce,

“Na ji, sosai take bugawa. Sannu, ko zaki sha ruwa?”

“A’a, sai dai chocolate.”

 Hararanta yayi cikin wasa ita kuma ta mishi gwalo wanda hakan yasa yayi dariya yana karkaɗa kai.

“Ku yaran nan na rasa gane meyasa kuke da son zaƙi. Ban taɓa jin mutumin da aka yiwa offering ruwa don ya kwantar mishi da hankali ba yace shi sai chocolate sai ke Juwairiyya sweet tooth.”

“Daddy ni ba sweet tooth ba ce.” Ta faɗa a shagwaɓance.

 Bai ce komai ba amma kuma murmushin bai bar fuskarshi ba ya jawo kofin kunun ya kurɓa sannan ya ƙara na biyu.

“Marigayiya tana mini kunun nan kusan kullum, watarana kuma tayi mini na Tamba. Yayi daɗi sosai nagode.”

A gurin wata hakan zai zama kamar ya ɓata musu yanayinsu ne amma a gurin Juwairiyya ta ga hakan ne a matsayin wani babban cigaba domin bai taɓa mata maganar tsohuwar matarshi ba, kenan a hankali ya fara sabawa da ita har yau ya kawo musu hiranta.

“Nima akwai ranar da na zo gidan nan Halima ta kawo mini na sha amma dai da sugarn mu, Mummy bata gane an taɓa mata kununta ba sai daga baya.” Ta ƙarisa maganan tana dariya domin da gaske hakan ya faru, a lokacin suna secondary school aka tashi daga makaranta suka biyo gidansu Halima akan zata ƙarbi wani style ɗin ɗinki amma suka samu ba’a gama abincin rana ba sai kunun Daddy da ya rage, Halima ta sato musu suka sha.

Daddy murmusawa yayi kana ya kaɗa kanshi ya ce,

“Ta faɗa mini hakan ya faru, Halima akwai rigima. Tun tana ƙaramarta tafi Abdul jalil kiriniya, there was a time da ta mari wasu yara a waje…..”

Da haka hiran ya canja salo ya dawo kan Halima, Juwairiyya tayi dariya domin labaran rigiman Halima da Daddy yake bata, ta wani guri kuwa daɗi take ji sosai domin zata iya rantsewa wannan shine karon farko da ya zauna suna hira. Kullum maganarsu bata tsayi amma yau ta ga improvements, kenan nisanta kanta daga gareshi da take yi a da shi yasa shima ya ja baya ko dai menene? Sai da goma ta wuce sannan suka farga dare yayi, Daddy kuwa ya sha kunu har kofi biyu sannan yace a ajiye mishi sauran zai sha da safe. Sallama ta mishi ta tattari kwanukan da zata kai kitchen ta nufi ƙofar fita amma ta ji Daddy ya kira sunanta.

“Juwairiyya.”

Juyowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa.

“Cookies ɗin sun yi daɗi na cinye su duka. Thank you.”

“Aikina nake yi Daddy, in kana buƙatar wani abun ma ka faɗa mini. Good night.”

Murmushi kawai yayi kana ya juya ya fara kashe tv itama ta juya ta tafi sashenta tana jin farin ciki a ranta.

Sati biyu da haka zamansu ya ƙara daɗi domin zasu zauna su yi hira, wani lokaci kuma zasu zauna a falonshi yana karatun jarida ko yana aiki ita kuma tana kallon Korean series ɗinta da ya zame mata jiki. Duk abun da yace ta dafa mishi tana yi hakan yasa yanzu ta san menene favorites ɗinshi da kuma waɗanda baya so. Sai dai abun da ta kasa canjawa shine Daddy baya son taɓa jikinta, sannan ko ita ce ta taɓashi zai yi dabarar da zasu rabu ba tare da yayi hurting feeling ɗinta ba. Ita kuma a yanzu da suke zama su yi hira sai buƙatarta ya fi na da, domin ganinshi kaɗai kan sa ta jita a wani yanayi. Tana buƙatar mijinta amma bata san meyasa har yanzu bai gane ba balle ya bata abunda take so ba.

Yau ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan zama shiyasa tun tashinta da safe tsokanar nata ya fi na kullum, a yanda ta lura ta birkita Daddy ba kaɗan ba don haka da yamma ma da ya dawo ta ƙara akan na safe, wannan karon bai bari maghrib tayi ba ya fita. Bayan isha Juwairiyya ta ci kwalliya kana ta sanya wando three quarter tare da wani cotton riga sky blue mai siririn hannun wanda bata saka komai a ciki ba, hakan yasa albarkatunta suka fito da ainihin siffarsu har in ta sunkuya za’a iya hangosu sarai. Tana jin Daddy ya shigo ta nufi falon nashi da flask a hannunta wanda yake cike da kunun Tamba.

“Welcome Daddy.” Ta faɗa tana mai adanawa kafin ta tsiyaya mishi a kofi ta nufoshi ƙirjinta na rawa.

“Thank you.” Faɗin Daddy yana kallon duk wani motsinta.

Sai da ya kusa shanye kunun sannan ta tashi ta je ta tsaya a bayanshi ta fara massaging kafaɗunshi tana cewa,

“Daddy idan na gama maka nima zaka biyani.”

Murmushi yayi kawai ya kaɗa kanshi kana yace,

“To rigimatu, zan miki.”

Seconds kaɗan da haka ya ajiye kofin kunun yana jin daɗin yanda take matsa mishi kafaɗun nashi yana lumshe ido. Ana cikin hakan ne ta fara haɗawa da kunnenshi da kuma kanshi cikin salo mai rikitarwa ta wani gefen kuma tana manna mishi ƙirjinta wanda ta lura suna ƙara gigitashi ba kaɗan ba. Bata yi aune ba ta ji ya kamo hannunta ya zagayo da ita gabanshi kana ya zuba mata ido ya ce,

“What do you want?”

Shiru ta yi kanta a ƙasa tana jin wata muguwar kunya na lulluɓeta, hakan yasa ta rufe fuskarta da ɗayan hannunta wanda bai riƙe ba ta fara ƙoƙarin zillewa.

“Juwairiyya look at me.” Ya umurceta wanda babu musu ta buɗe fuskar tata tana kallon cikin nashi idon amma bata iya jurewa ba ta sauƙe nata ƙasa tana murmushi.

Bai ƙara cewa komai ba ya tashi tsaye har lokacin hannunta na cikin nashi ya kashe kallon da take yi kana ya jata zuwa ɗakinshi.

Minti goma da haka Daddy ya koma gefe yana kallon yanda Juwairiyya ta gama rikicewa tana buƙatarshi amma ba zai iya biya mata ba.

“Kiyi haƙuri Juwairiyya, ki tashi ki saka kayanki zamu yi magana.”

Waɗanda suka yi payment zasu samu cigaba a weekend, masu jiran free pages kuma mu haɗu ranar monday In shaa Allah.

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad

(11)

Babu musu Juwairiyya ta tashi ta mayar da kayanta sannan ta jawo bargo ta lulluɓe jikinta, duk wannan abun da tayi Daddy na can bakin gado yana dafe da kanshi ya juya mata baya.

“Juwairiyya.” Ya kira sunanta yana mai juyowa gareta.

“Na’am.” Ta amsa can ƙasan maƙoshinta domin har a wannan lokacin baza ma ta iya faɗin a wani hali take ciki ba, tsananin buƙata ne, kunya ce, takaici ne ko zullumi?

“Da farko zan fara da baki haƙuri, I’m so sorry Juwairiyya domin na cuceki na ɓoye miki wani babban al’amari game da ni. Sai dai kuma na yi hakan ne for my selfish reason saboda gudun kar Halima ta nemi saki a gurin mijinta don kawai ta zauna dani. Juwairiyya wannan matsala da kika ganni da ita ba haka nake ba, shekara biyu da suka wuce wannan cuta ta Diabetes ta bayyana a jikina. Bayan an ɗaurani akan magani na fara samun lafiya sai ya kasance bana iya gamsar da iyalina. A lokacin mun yi tunanin ko don rashin lafiyan da nayi ne ya jawo hakan amma da aka shafe watanni har biyar babu sauƙi sai muka tafi asibiti don duba me yake damuna. Marigayiya ita tayi ta yawon zuwa asibiti dani amma sai abu yayi kamar yayi sauƙi sai kuma ya dawo da ƙarfinshi wanda a yau da ni da jaririn da aka haifa duk ɗaya muke. Kina jina?”

Gyaɗa kai Juwairiyya tayi kanta a ƙasa tana sauraron labarin Daddy zuciyarta na bugawa, kenan ba wai itace bata mishi kyau ba kuma ba wai ba ya sha’awarta bane! Dama ya jima da cutar a jikinshi a hakan kuma ya yarda ya aureta?

“Allah Ya yi ni mutum ne mara son magani amma da na samu cuta biyun nan sai na mance ma dalilin da yasa bana son maganin. Marigayiya babu irin maganin da bata kawo mini ciki har da na gargajiya wanda ta tabbatar ba zai taɓa lafiyata ba, amma duk shan da zan musu duk kuma ka’idarsu da zan bi abun yaci tura na rasa ƙarfina na ɗa namiji. A haka muka cigaba da zama tana tare dani tana riƙe da sirrina har ta koma ga mahaliccinta dalilin ciwon kan da tayi na awanni kaɗan. Daga nan kuma na ƙara tsinkewa da rayuwa na ji ba zan sake aure ba har abada amma Halima ta tursasa mini na aureki. Wallahi bana dana sanin aurenki Juwairiyya, zaman da nayi da ke yasa kika shiga zuciyata yanda bakya tsammani amma duk lokacin da na kalleki kika burgeni ko kika bani sha’awa bana jin kaina. Hakan yasa ban nemi mu keɓance ba har sai da na ga da gaske kina buƙatata, Wallahi Juwairiyya ban yi tsammanin zan baki kunya ba, na yi tunanin tunda kina da ƙuruciya wataƙila zan iya performing amma sai abu ya zama haka. Ki yi haƙuri domin na san ko a musulunci wannan auren namu ba zai ɗore ba, sannan na cuceki kiyi haƙuri ki yafe mini.” Ya ƙarisa maganan cikin sanyin murya mai cike da nadama da kuma tausayi.

Kuka Juwairiyya take yi a hankali kanta a ƙasa hawayen na ɗiga kan bargon da ta lulluɓa dashi. Kuka take yi na tausayin Daddy da kuma ita karan kanta domin wannan shi ake kira ga samu ga kwanan yunwa. Ta shigo gidan Daddy ne da niyyar in zaman bai mata daɗi ba zata fita, amma da ta ga kyawawan halayenshi da kuma yanda yake kula da ita sai ta ayyana a ranta cewa babu mai rabata da gidan sai kuma wani ikon Allah. Me yasa ita rayuwarta ba zai tafi daidai ba? Me yasa a kullum jarabawa yake faɗowa kanta? Me yasa wannan karon wahalarta ba zai ƙare ba? Why her?

 Tana jin lokacin da ya miƙe tsaye ya shiga banɗaki har ya fito ya mayar da kayanshi ya dawo gurinta ya zauna bata daina kuka ba.

“Juwairiyya kiyi magana, ban san me yake ranki ba. Wataƙila kin tsaneni ko?”

 Girgiza kanta tayi tana share hawayenta, sannan ta ɗago ta ce,

“A’a Daddy.”

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana shima yayi shiru yana tunani, can ya ƙara dubanta fuskarshi kamar wanda zai yi kuka ya ce,

“Shikenan, ba zan cigaba da cutanki ba Juwairiyya zan sawwaƙe miki sai ki samu…..”

Bai kai ga ƙarisa maganan ba Juwairiyya ta sukwano cikin sauri ta rufe mishi bakinshi tana girgiza kanta tana cewa,

“Ka rufa mini asiri kar ka sakeni. Zamu cigaba da neman magani har Allah ya baka lafiya Daddy. Wallahi zan yi haƙuri har lokacin da Allah zai baka lafiya. Ina son zama da kai kuma ba zan yi gaggawan rabuwa da kai akan ciwon da yake da magani ba. Wallahi zan yi haƙuri, zan tayaka zan kuma yi supporting ɗinka wajen neman maganin.”

“Kayya. Da zan samu lafiya da tun wancan lokacin na samu Juwairiyya. Nima ba zan so rabuwa da ke ba don na saba da ke ina jinki har cikin raina, wallahi rabuwa da ke zai ƙara fame mini wani ciwo a cikin zuciyata. Amma ba zan ƙara cutar da ke ba, wanda na miki a baya ma ya isa kuma ina neman gafararki.”

“Daddy don girman Allah kar ka ƙara kiran rabuwarmu. Ka tsaya ka saurareni.”

Duk da irin raɗaɗin zafin da yake ji a zuciyarshi bai hanashi yin murmushi ba dalilin kalmarta na ƙarshe.

“A zaune ma nake Juwairiyya, a zaune nake.”

“To Daddy. Ka ga bamu jima da yin auren ba, yanzu in aka ji mun rabu ni duniya zata zaga a ce wani mugun halin nake maka ka kasa zama dani. Kuma ba zamu yi gaggawa ba tunda a da ba haka kake ba, rashin lafiya ce kuma kowacce cuta Allah Ya ce tana da maganinta. Don Allah kar ka yanke hukunci ba tare da ka duba yaya rayuwata zata ƙare ba, ka rufa mini asiri. Kuma nima ina son zama da kai bana son rabuwa da kai. I will stay with you in sickness and in health. Mu ɗauki hakan a matsayin jarabawarmu kuma mu roƙi Allah Ya sa mu iya cinta.”

 Juwairiyya bata samu Daddy ya yarda da uzurinta ba sai da suka yi doguwar debate, tun tana kan gado har ta dawo ƙasa ta durƙusa a tsakanin ƙafafunshi sannan ya nisa ya ce,

“Abun da nake so ki fahimta shine ke yarinya ce Juwairiyya, ba lalle bane ki gane cewa wannan auren akwai cuta a ciki ba. Amma ba zan ƙi taki ba, zamu nemi magani Allah kuma Ya bani lafiya. Sai dai in ba’a samu waraka ba kiyi haƙuri da duk hukuncin da zan ɗauka.”

 Cikin murna Juwairiyya ta miƙe tsaye ta rungumeshi tana mishi godiya domin ita a gurinta ba ƙaramin cetonta yayi ba. Da ace ta koma rayuwarta ta zawarci gwanda ta zauna tare da Daddy har Allah Ya bashi lafiya. Wannan kenan.

 Wata huɗu da haka Juwairiyya ce zaune da Daddy a gaban Doctor yana sauraran bayanansu wanda idan Daddy ya faɗi nashi sai Juwairiyya ta ƙarisa, yanda suke magana sosai ya bawa Doctor sha’awa da kuma dariya amma saboda profession ɗinshi ya hanashi nuna waɗannan emotions ɗin sai ya cigaba da gimtse fuskarsa yana jeho musu tambayoyi suna amsawa. Magani ya rubuta musu kamar yanda sauran Doctors ɗin da suka ziyarta a baya suka basu kana ya ƙara musu da shawarwari yanda zasu shawo kan matsalar, yanda Juwairiyya ta maida hankali tana sauraron Doctor tana gyaɗa kai sosai ta bawa Daddy tausayi har yana jin zuciyarshi na mishi nauyi, kar cutar tayi yawa fa.

 Suna fitowa daga asibitin suka nufi gida bayan sun sayi magungunan, a falonshi suka yada zango Daddy ya shige ɗaki don zai yi amfani da banɗaki ita kuma Juwairiyya ta fara rage kayan jikinta sannan ta jawo ledan magungunan tana dubawa don sanin dosage ɗin su. A haka Daddy ya dawo ya sameta zaune a ƙasa daga ita sai leggings da half vest.

“In ba dole ba bazan sha duka waɗannan magungunan ba. Ganinsu kaɗai idan nayi sai in ji zuciyata ta tashi.”

“Ohh Daddy ka fiye tsoron magani wallahi, to ko za’a maka alluransu?” Ta faɗa cikin zolaya tana murmushi.

“No, bani maganin in sha.” Ya amsa yana zama a saman kujera ta fara miƙo mishi yana zubawa a bakinshi yana korawa da ruwa.

Sai da ya shanye sannan ta tattarasu ta zuba a leda kana ta miƙe tsaye don zuwa adanasu Daddy ya riƙo hannunta ya jawota ta tsaya tsakanin ƙafafunshi kana ya ɗaga kanshi yanda zai ga fuskarta ya ce,

“Juwairiyya anya akwai haske a lamarin nan? Anya kuwa zan warke? Aurenmu yanzu wata shida wanda ko sau ɗaya ban taɓa biya miki buƙatarki ba Juwairiyya. Abun yana damuna sosai.”

 Ajiye maganin tayi a kan kujera a gefenshi kana ta tallafo kanshi da hannayenta duka biyu ta kalli fuskarshi wacce take tattare da damuwa ta sumbaci goshinshi kana ta ce,

“Neman magani muke yi wanda dama ba lokaci ɗaya zamu samu waraka ba, dama mutum kan iya shan magunguna kala goma sai a na sha ɗaya yayi dace. To mu ma bamu fara don mu bari ba, da yardar Allah zaka samu lafiya ka daina ma kawo waswasi a ranka. Ka ji Babyna?”

Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana jin sanyi a ranshi domin Juwairiyya ta san yanda zata kwantar mishi da hankali muddin ya furta mata cewa ya karaya ko kuma ya nuna mata alamun hakan.

“Juwairiyya bana son cutar da ke, kullum buƙatarki ƙara ƙaruwa take yi….” Bai kai ga ƙarisa maganan ba ta tari numfashinshi ta ce,

“Mu bar zancen nan, yanzu ba magani aka ɗauraka a kai ba?”

“Hakane.”

“To ka gani. Don’t lose hope. Ka ji?”

“Na ji rigimatu.” Ya faɗa yana dariya.

Itama darawan ta yi kana ta ɗauki ledan da ta ajiyen ta je ta adana kana ta nufi sashenta don ɗaura musu abincin rana dama fitan hantsi suka yi.

 A daren ranar Juwairiyya ce kwance a jikin Daddy a ɗakinshi suna hira kaɗan-kaɗan yana danna wayarshi, can ya dakata da danne-dannen ya ajiye wayar a gefe yana jin yanda Juwairiyya take mutsu-mutsu a jikinshi kamar wacce ma hankalinta baya jikinta. Ji yayi hawaye ya taru a idanunshi amma yayi saurin maidasu domin gudun kar ta gani, a jikinshi kuma bai ji wata alama da zata nuna zai iya taimakonta ba wanda hakan shine abun da ya fi tsoro a yanzu. Hannunshi ya kai wani sashe na jikinta wanda ya sa ta ƙara birkicewa ya ce,

“There, there, let me help you a little.”

Bayan wata ɗaya Daddy ne tsaye a falonshi tare da Juwairiyya wacce take mishi shagwaɓa dalilin tafiyar da zai yi na sati biyu.

“Daddy to ka tafi dani mana.” Ta faɗa tana bubbuga ƙafanta a ƙasa.

“Ke da kika fara zuwa school shine zaki yi tafiyan har sati biyu? A’a kiyi zamanki a gida, next time idan zan yi tafiya kuma kina hutu sai mu tafi tare.”

“Ni dai wallahi ba’a kyauta mini ba, sai da na shiga school sannan zaka yi tafiya mai daɗewa haka?”

“Juwairiyya Rigimatu, to ki barni in tafi kar in yi missing ɗin flight ɗina.”

 Da haka ya mata sallama ya fita harabar gidan inda Abdul Jalil zai tuƙashi zuwa Airpot. Har ya zauna a cikin mota ya rufe sai kuma ya buɗe ya fito ya koma cikin gidan ya samu Juwairiyya tana tattare kan dinning inda ya gama cin abinci. Tana jin shigowarshi ta juyo tana tambayarshi ko ya manta wani abu ne amma bai amsa mata ba ya rungumeta tsamtsam a jikinshi. Murmushi tayi ta fara tsokanarshi ko zai fasa tafiyan ne ya dawo su zauna?

“Duk abun da ya faru ki sani ina sonki Juwairiyya, and please take care of yourself for me. Kin ji?”

“Na ji Daddy kuma Babyn Juwairiyya.”

Da haka ya saketa yayi kissing goshinta kana ya fita cikin sauri ta bishi da addu’a fuskarta ɗauke da murmushi.

A bakin window ta tsaya tana leƙenshi har ya shiga mota suka fita daga gidan sannan ta juya ta cigaba ta aikinta. Tana gama gyaran falo ta koma ɗakinshi nan ma ta fara gyarawa tana tattare kayanshi da ya cire tare da sauran tarkace. Sai da ta gama ta hango wani damin kuɗi mai yawa akan bedside tare da wani paper a ƙasanshi. Murmushi ta yi domin ta san Daddy ya manta ne dasu domin ya tura mata kuɗi cikin Account ɗinta wanda in tana buƙatar wani abu ta saya duk da cewa suna da komai a gidan.

Kuɗin ta matsar gefe sannan ta ɗauki takardar kamar ba zata buɗe ba amma ta buɗe, contents ɗin da yake ciki yasa ta kwala ihu ta zube a gurin tana kama kanta da dukkan hannayenta, nan da nan kuma kuka mai ƙarfi ya kwace mata har numfashinta na ɗaukewa.

“Mugun mutum! Coward! Ka cuceni ka tona mini asiri. Me yasa ba zaka ƙara haƙuri ba?”

Da haka ta tashi ta ɗauki wayarta hannunta na karkarwa har bata ganin me take dannawa, hakan yasa ta goge fuskarta da hannunta sannan ta samu numbern Daddy ta danna kira amma aka ce mata is switch off. Da haka ta nemo na Abdul Jalil ta kirashi ya ɗauka babu ɓata lokaci,

“Aunty Juwai….” Bai kai ga ƙarisawa ba ta katseshi.

“Ina Daddy?”

“Tun ɗazu na sauƙeshi ni kuma ina dawowa gida. Wani abu ne ya faru?”

Wannan tambaya da ya mata shi yasa ta ƙara fashewa da kuka har tana sarƙewa, shi kuma Abdul jalil hankalinshi ne ya tashi ya fara tambayarta me yake faruwa. Da kyar ta saisaita kanta ta ce,

“Daddy ya sakeni, ya raba auren da ke tsakanina dashi Ya Abdul jalil.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Me yasa?”

Bata bashi amsa ba ta jefar da wayar ta ƙara zama a ƙasan ɗakin tana kuka tana tausayin rayuwar da zata fuskanta nan gaba.

“Hafiz mutuwarka tonon asiri ne a gareni, rayuwata tana ta gararamba saboda rashinka. Allah ka kawo mini ɗauki, Allah ka ji tausayina ka taƙaita mini wannan wahalan rayuwar.”

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad

(12)

Kafin Abdul Jalil ya dawo gida Juwairiyya ta kwashi iya abun da zata iya ɗauka na buƙatunta ta bar gidan. Tana shiga ta samu Mama tana gurin aiki sai Nan (Kakarsu) da kuma mai aiki ne kawai a gidan. Babu ɓata lokaci ta buɗe ɗakin da tayi zawarcinta a ciki ta kwanta akan katifa taci gaba da kuka har Nan ta shigo ta sameta a haka.

“Ke ƴar nan ina miki magana kika ƙi kulani sannan kika shigo nan kina kuka? Me ya faru kika bar gidan mijin naki?”

“Don Allah Nan ki barni da abun da yake damuna ki daina mini wasu tambayoyi.” Ta faɗi hakan tana mai juyar da kanta ɗayan gefen inda ba zata ga Nan ba.

“Ki ji mini ja’irar yarinya da rashin kunya, don na tambayeki shine ya zama laifi. To mutuwa aka yi kike kukan?” Ta ƙara wata tambayar don bata haƙura ba.

“Ni nace miki wani ya mutu? Babu wanda ya mutu.”

“To menene ya faru?”

 Daga haka Juwairiyya bata ƙara kulata ba, hakan yasa Nan ta juya ta tafi tana cewa,

“Kici kanki ke ɗaya.”

 Tunda Juwairiyya ta shiga ɗakin bata fito ba har Mama ta dawo daga aiki, Nan tana ganin ta dawo ta bata labarin cewa ga can Juwairiyya a ɗaki ta zo tana kuka. Gaban Mama ne ya faɗi rass wanda sai da ta ga duhu ya wuce lumm ta gabanta sannan ta dafe ƙirjinta ta nufi ɗakin da Juwairiyyan take tana haɗa hanya.

“Menene ya faru kika zo kina kuka Juwairiyya? Ki tashi ki faɗa mini abun da ya faru.” Faɗin Mama tana shiga cikin ɗakin ta tsaya kan Juwairiyya.

A hankali ta miƙe fuskar nan tata ta kumbura idanunta sun yi jajur kamar garwashi sannan sun ƙanƙance duk da girmansu. Hijabin da yake jikinta kuwa ya jiƙe da zufa, hawaye har da guntun majina. Buɗe baki tayi da niyyar magana sai kuma wani kukan ya kwace mata har tana sheshsheƙa.

“Juwairiyya ki faɗa mini abun da yake faruwa domin hankalina ya tashi wallahi. Ki daina kukan nan ki faɗa mini.” Faɗin Mama wacce a yanzu tsoron ya yawaita a zuciyarta.

“Daddy ya sakeni Mama, ya mini saki ɗaya.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Haka tayi ta maimaitawa bayan ta samu guri ta zauna.”Me kika mishi Juwairiyya ya sakeki? Rashin kunya kike mishi ko kuma wani abun?”

“Wallahi Mama babu abun da nake mishi mara daɗi, lafiya kalau muke zaune yau yayi tafiya muka rabu lafiya amma ina shiga ɗakinshi na samu takardar akan bedside. Ko a fuska bai nuna mini ya sakeni ba har muka yi sallama Mama.” Faɗin Juwairiyya tana ƙara jin haushin Daddy a ranta.

Dama ga abun da take gudu domin duk yanda za’a yi babu mai yarda da cewa ba laifi ta mishi ya saketa ba. Kwata-kwata auren nasu yanzu ya cika wata bakwai da ɗori! Me yasa ba zai ƙara haƙuri har su shekara ba kafin ya ɗauki matakin ba?

“Haka kawai ba zai sakeki ba Juwairiyya dole akwai wani dalili. Ki faɗa mini tun wuri sai mu san yanda zamu gyara al’amarin.”

 Ga kuma abun da take tsoro! Wato duk yanda zata kai ga faɗa musu cewa ba laifi tayi mishi ya saketa ba ba zasu yarda ba. Idan kuma ta fito fili ta faɗi gaskiyan al’amarin ta tona mishi asiri ne sannan wasu ba zasu yarda ba zasu ce ƙarya take mishi tana son wulaƙantashi ne a cikin mutane. Ta sani kuma zata iya rantsuwa Mama ma ba zata yarda da ita ba, to me amfanin bayyanawan? A zaman da tayi dashi ya kyautata mata don haka ba zata so ta kwaye mishi zani a kasuwa ba, ta wani gurin kuma Daddy uba yake a gurin Halima ƙawarta. Idan ta fito ta faɗi matsalarshi da wani ido zata ƙara kallon Halima? Zata rufa mishi asiri ko don waɗannan dalilai biyun amma ba zata taɓa daina jin haushin yanda ya saketa ba. Me yasa ba zai iya bata takardarta a hannunta ba sai dai ya ajiye ta je ta ɗauka? Ashe tun kafin ya tafi sunanta sakakka ce a gurinshi bata sani ba! Wannan sakin da yayi mata da kuma salon da yayi amfani dashi wajen sakin zai kasance a cikin zuciyarta har ƙarshen rayuwarta, ba zata taba mantawa dashi ba har abada.

“Wallahi, wallahi babu laifin da nayi mishi.”

Shiru Mama tayi tana zaune a gurin har na tsawon minti biyu tana kallon Juwairiyya sannan ta ce,

“Idan zaman hakan kika zaɓa gaki ga ita Juwairiyya, amma sai dai zan faɗa miki ba lallai bane ta miki daɗi ba. Sannan ba a kanki aka fara yiwa mutuwa ba, hakan da kika yi kin nunawa Allah kenan baki da tawakkali baki san ƙaddara ba. Ga ki ga gidan Juwairiyya, in kuma kina da wayo sai ki san yanda zaki yi mijinki ya mayar da ke gidanshi.” Tana faɗin hakan ta tashi ta koma ɗakinta, abincin ranar yau kuma bai samu ya shiga cikinta ba.

Fitan Mama daga ɗakin yasa Juwairiyya ta ƙara fashewa da kuka domin gashi nan hatta uwar da ta haifeta bata yarda da ita ba, haka kuma duk duniya ita za’a bawa laifi babu wanda zai yi tunanin laifinshi ne. Wannan shine ƙalubalen da Juwairiyya ta fara fuskanta bayan aurenta da Daddy ya ƙare.

****

“Gata can zata tafi makaranta, ka ganta sulum-sulum kamar in ka saka mata yatsa a baki ba zata iya ciza ba amma nan jarababbiya ce.” Faɗin Garbati mai shago da yake can ƙasan layinsu Juwairiyya.

“Cewa aka yi Jarababbiya ce?” Wani baƙon mutumi ya tambaya yana mai kallon lokacin da ta tari mai napep akan titi ta shiga suka tafi.

“Haka dai ake faɗa, wai tsohon tafi ƙarfinshi saboda jarabarta shine da ya ga ba zai iya ba ya sallameta.” Garbati ya amsa mishi yana bawa wani saurayi sigari.

Saurayin yayi caraf ya karɓi zancen yace,

“Ba haka aka faɗa ba fa, cewa aka yi yana zarginta da ɗan cikinshi ne amma bashi da shaida shine ya saketa.”

“To in dai hakane ai abubuwan da aka faɗa da yawa, ni wannan na ɗauka don shi zai fi zama gaskiya. Gaskiya ana mata kyakkyawar shaida zai yi wuya a ce fasiƙanci take yi da ɗanshi, sai dai baka san halin mutum na ɓoye ba amma gaskiya zai yi wuya.”

“Wai menene sauran abun da ake faɗin?” Mutumin ya sake tambaya amma Garbati yayi shiru kamar bai ji ba don ya lura kamar takanas mutumin ya zo domin binciken halin Juwairiyya.

“Ai ka san baban ƙawarta ta aura, to an ce wai ƙawar tata ce bata son auren shine tayi yanda ta rabasu. Wasu sun ce ta rainashi ne, wasu kuma suka ce sata take mishi tana kawowa gidansu….” Saurayi mai sigarin ya fara zayyanowa Garbati yayi saurin katseshi da cewa,

“Wannan kam duk wani mai hankali ma ba zai ɗauka ba, da tana da waɗannan halayen da mutanen unguwan nan ne zasu fara sani. Lukman don Allah kayi tafiyarka kar da sassafen Allah ka ɗauki alhakin ƴar mutane.” Ya bugi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.

 Wannan magana ta sa Lukman ya tafi yana busa sigarinshi shi kuma mutumin yayi jimm kamar ba zai tafi ba, can kuma ya miƙe ya karkaɗe rigarshi ya shiga mota ya tafi.

“Mutane sai shegen gulma da bin diddigi.” Faɗin Garbati bayan ya ga tafiyar mutumin ya manta cewa da shi aka fara kafa chaptern Juwairiyyan.

 Juwairiyya ce zaune a class tana jiran lokaci yayi Lecturer ɗin ya fita don ta samu ta koma gida da wuri. Yana fita ta bi bayanshi ta fita daga makarantar ta tari napep sai gida, a can ta tarar da aikin da yake jiranta na girkin rana da kuma gyaran ɗakin Mama kafin ta dawo daga aiki, domin kuwa Mama ta kori mai aikinsu tace bata ga amfanin zamanta a gidan bata aikin komai ba, duk kuwa da cewa Juwairiyyan tana zuwa makaranta watarana ma a can take wuni amma a haka zata dawo ta samu wasu aikin suna jiranta. Wani abun da ta lura dashi shine ko Surayya ƙanwarta da yanzu take SSS 3 bata kaita tiƙan aiki a gidan ba, kamar Mama tana mata kora da hali ne. Amma wannan bai dameta ba kamar maganar aure da Mama ta fara matsa mata a kai.

Tun bayan mutuwar aurenta Daddy bai nemeta ba haka itama bata sake nemanshi ba sai Halima ce da take yawan kiranta wanda Juwairiyya ta yi blocking ɗinta don bata ga me zata faɗa mata ba. A yanda ta lura Daddy bai faɗawa Halima dalilin rabuwarsu ba sai cewa yayi wai a tambayeta, to kenan ita ce mara rufin asiri mara kunya da zata buɗi baki tace ga matsalar da suka fuskanta har ya kai ga datsewar zaman nasu? Duk irin tambayar duniyar da Mama tayi mata akan dalilin sakinta da aka yi kuwa ta ƙi faɗa mata domin tayi alƙawarin rufawa Daddy asiri har ƙarshen rayuwarta, na biyu kuma ta sani ko ta faɗa Mama ba zata yarda ba zata ce karya take mishi don bata son komawa. To wa ya fita son komawa gidan Daddy? Ita ta ji ta gani zata iya zama dashi duk da lalurar da yake fama da ita amma bai nemi shawararta ba ya saketa, duk hakan bai isheshi ba sai da ya ƙara da kin kiranta har sai da ta gama iddah sannan ya nemeta a waya yana tambayar wai ya take. Kalma ɗaya ta ‘Coward’ ta furta mishi daga nan shima tayi blocking ɗinshi. Ana haka kuma sai gashi wai ya zo ƙofar gidansu, babu yanda ta iya haka ta fita don a gaban Mama aka yi kiran nata.

“Juwairiyya kina lafiya?” Ya tambayeta yana mai mata kallon tausayi domin har ta canja ta ƙara ramewa.

“Kalau. Me ya kawoka ƙofar gidanmu?” Ta tambayeshi kai tsaye domin ta so ta tsigeshi tass amma kwarjininshi da girmanshi sun haɗu sun danne wannan tsiwar tata.

“Na zo ne na dubaki, sai na lura kuma bakya murna da ganina.”

Wannan magana da yayi shi jawo hawayen da Juwairiyya take ta dannewa suka zubo kan fuskarta ta dubeshi duk jikinta a sanyaye ta ce,

“Daddy sakina dai kayi, sakina kayi ka ajiye mini takardar sai da naje na ɗauka na gani sannan na gane ni sakekkiya ce. Bamu yi haka da kai ba sannan ba haka muka yi alƙawari ba, ka mini gaggawa ka datse mini farin cikina ka dawo dani rayuwar da nake gudu. Wallahi baka kyauta mini ba, zuwanka kuma ya ƙara fame mini wani ciwo a zuciyata don Allah kar ka sake zuwa inda nake, zaman da muka yi a baya ma ya isa. Don Allah ka tafi.” Da haka ta juya ta shige cikin gidansu ta barshi tsaye a gurin shima yana jin kamar yayi kukan.

Bata jima da shiga ba yara suka yi sallama suka fara shigowa da kayan masarufi mai yawan gaske, hakan yasa Mama da ta tareta a tsakar gida tana tambayarta dalilin zuwan nashi ta dakata har aka gama shigo da kayan sannan yaro na ƙarshe ya shigo da envelope mai kauri ya miƙa mata wai in ji Alhajin waje.

Tana buɗewa ta ga kuɗine a ciki wanda a baya ya ɗaura mata a kan takardan sakinta wanda zai yi kimanin dubu ɗari biyu, sai kuma wata wasiƙa wacce kamar yanzu ya rubutata. Saboda rashin sanin me ya rubuta a ciki yasa Juwairiyya ta miƙawa Mama kuɗin ita kuma ta shiga da wasiƙar  ɗaki ta fara karantawa kamar haka….

‘Zan fara da ƙara baki haƙuri Juwairiyya duk da nasan yayi kaɗan ya goge laifin da na miki, amma kiyi haƙuri ki kuma yafe mini domin rabuwarmu shine mafi alkhairi kuma ba zan iya cigaba da zama dake ina cutar da ke ba, wallahi ba zan iya ba. Sannan ina sonki ina ƙaunarki zaman da nayi da ke kin shiga zuciyata ba zan taɓa mantawa da ke ba har ƙarshen rayuwata. Kafin ki aureni I’m a broken man, bayan haka kuma ya ƙaru da cewa ba zan iya biya miki buƙatunki ba, you deserve someone better someone who can take care of you. A ƙarshe ina miki fatan alkhairi, Allah Ya miki albarka Ya kuma baki miji nagari wanda zai riƙeki amana don you are a rare gem Juwairiyya, da ina da lafiya wallahi babu abun da zai sa in rabu da ke. Allah Ya miki albarka.

Daddy.’

  Tun daga ranar bata sake jin ɗuriyar Daddy ba haka kuma Halima ma ta daina nemanta don da alama tayi fushi ne, sai dai bata sani ba cewa ba laifinta bane kuma ba zata iya faɗa mata gaskiyan abun da ya faru ba. Mama kuma ta mata faɗa ta mata nasiha amma kullum maganarta shine ‘ba laifina bane ya sakeni’. Labaran da ake faɗa a kanta kuwa duk yana dawowan kunnensu wanda Mama tafi kowa shiga ɓacin rai don ta san ɗiyarta ba zata taɓa neman ɗan mijinta ba ko kuma tayi sata ba. Ire-iren waɗannan ƙalubalen yasa Mama ta fara mata kora da hali wai duk don ta gaji tayi aure. Wannan kenan.

 A yanzu itama Juwairiyya tana son yin auren domin ta huta da faɗan Mama sannan ta huta da tsegumin mutane, hakan yasa wannan karon duk wanda yayi sallama da ita zata fita ba tare da an mata dole ba. Ita kanta mamaki take yi wato idan duniya ta bugeka zaka yi hankali babu wanda ya sani. Sai dai matsalar da aka samu shine duk cikin masu zuwa gurin nata a yanzu ƴan iskan sun fi yawa musamman da suka samu labarin cewa wai ita jarababbiya ce, waɗanda suka zo da niyyar aure kuma tayi rantsuwa da Allah su ba ajin aurenta bane. Duk da cewa tana son auren tayi alƙawarin ba zata auri wanda zata dawo tana dana sanin aurenshi daga baya ba.

 Ana cikin haka Hussaini ya dawo da jarabarshi tare da wani magidanci mai suna Salisu wanda gurin aikinsu ɗaya da Mama sannan Maman ne da kanta ta bashi izinin neman Juwairiyyan. Ranar farko da ya fara zuwa ta nuna bai mata ba don haka kawai ta ji tana jin haushinshi, a zuwanshi na biyu kuwa da ta kalli cikin idanunshi da ya sakawa kwalli sai ta ji wani sashe na hankalinta ya kau, abun bai tsaya a nan ba domin kuwa bayan tafiyanshi duk waɗanda suka zo sai ta koresu kuma abun mamaki Mama ta daina cewa komai, hakan yasa babu mai zuwa gurinta a yanzu sai Hussaini mai baƙar jaraba da kuma Salisu mai kwalli a ido.

Juwairiyya tana shigowa gida ta kai jakanta ɗaki kana ta fito tsakar gida ta ɗaura musu abincin rana wanda shinkafa ce da wake da mai da yaji. Tun da ta dawo Nan bata fito ba hakan yasa bayan ta sauƙe abincin ta gama rabiya ta kai mata nata har ɗakinta ta ajiye ta sameta tana bacci, bata tasheta ba ta fice don zuwa gyaran ɗakin Mama, tana gamawa Maman ta dawo daga aiki wanda kai tsaye ta wuce ɗakin Nan don dubata da yake ta kwana da zazzaɓi. A nan ta tarar da gawar mahaifiyar tata wacce ta mutu cikin baccinta, tana hawaye ta gyara mata kwanciyarta sannan ta lulluɓeta ta fita zuwa ɗakinta ta samu Juwairiyya na adana tsintsiya don ta gama mata sharan.

“Mama me ya faru kike kuka?” Juwairiyya ta tambaya cikin kiɗima don ta jima bata ga mahaifiyarta tana kuka ba.

“Allah Ya yiwa Nan rasuwa, wahalarta ta ƙare. Ki kira kannena a waya ki faɗa musu.” Tana faɗin hakan ta fice ta koma ɗakin Nan ta bar Juwairiyya itama hawayen na zuba a idanunta.

Ya za’a yi Mama ta barta da wannan aikin? Me yasa ita ba zata kirasu ta faɗa musu ba sai ita? Me zata ce musu? Tana tsaye a gurin Mama ta dawo ta ɗauki wayar ta fara kiransu tana faɗa musu don kamar itama ta ga ita ya dace ta kirasu ba Juwairiyya ba. Wannan abincin da ba’a ci shi cikin daɗin rai ba kenan, ana sallar la’asar kuwa aka kai Nan makwancinta na gaskiya.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad

(13)

Bayan rasuwar Nan da sati biyu Mama ta koma bakin aikinta, hakan yasa in zasu fita sai dai su rufe gidan tunda babu kowa a ciki domin Surayya yini take a school sai yamma take dawowa, Walid kuma da Mama ta lura zai fi ƙarfinta sai ta mayar dashi boarding school na wani babban malamin addini da yake can Kano, cikin ikon Allah kuwa ya fara nitsuwa domin bayan karatu da ake koya musu a can har da tarbiyya. Idan kuma Juwairiyya bata da lectures sai ya kasance ita ɗaya za’a bari a gida, wannan tsarin yasa Mama ta tashi haiƙan da cewa Juwairiyya ta zaɓi miji tayi aure bata son zamanta ita kaɗai a gidan.

 Yau Salisu ya kawowa Juwairiyya ziyara wanda da ya aiko yaro cewa yana waje sai da zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske kamar kullum, domin ta lura kamar shakkarshi take ji bata kuma iya mishi musu. Sau da dama sai ta fita da niyyar korarshi sai ta kasa, haka zai gama surutunshi ya tafi tana biye mishi domin kuwa bata son ta ɓata mishi rai.

Fuskarta babu walwala ta fita ta sameshi a cikin motarshi yana zaune, gaisheshi ta yi daga waje ya ƙi amsawa kana ya dubeta a lalace yace,

“Ki shigo motar mu yi hira.”

Girgiza kanta tayi alamar a’a amma kuwa zuciyarta lugude take yi don bata san yanda Salisu zai ɗauki hakan ba. Gimtse fuskarshi yayi sosai ya dubeta a karo na biyu ya gyara zamanshi ya ce,

“Ki shigo bana son musu Juwairiyya. In kuma kina son raina ya ɓaci ne to bismillah.”

Kamar zata yi kuka haka ta shiga cikin motar wanda zata iya rantsuwa bata taɓa shiga motar duk wani mai nemanta ba sai a kanshi. Zuciyarta ta haneta ya fi sau a ƙirga amma kuwa gangan jikinta ya kasa kin aikata abun da aka umurceta a kai ɗin. Suna hiran kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ji ya kamo hannunta ya fara murzawa, wannan abun da ya mata shi yasa ta zabura ta kwace hannun nata tana mai jin tsanarshi a cikin zuciyarta. Zagi da baƙaƙen maganganu kuwa babu irin wanda bai zo cikin zuciyarta ba amma ta kasa furtawa a harshenta, ji tayi hawaye sun taru a idanunta tana jin ta tsani kanta da shi Salisun amma babu yanda ta iya.

“Yaya dai?” Ya tambayeta kamar bai san me yayi ba.

“Don Allah kar ka sake taɓani wallahi bana so.” Ta faɗa a sanyaye kamar mai neman gafara.

“To don na riƙe hannunki shine ya zama laifi? Ba aurenki zan yi ba?” Ya tambayeta kamar mai yin faɗa.

Girgiza kanta tayi sannan ta ɗago fuskarta wacce tayi kalar tausayi ainun ta ce,

“Na sani amma ni bana jin daɗi ana taɓani ne. Kayi haƙuri.”

“To naji ba zan sake ba, amma dai ki barni in riƙe hannun naki one last time. In kin barni na riƙe ba zan ƙara tambayarki ba.” Ya faɗa yana mai ware tafin hannunshi akan ta ɗaura nata a kai.

Miƙar da hannunta tayi don yin abun da ya buƙaceta da yi amma suka ji an kwala mata kira da wata kakkausar murya wacce ta sa hanjin cikinta suka kaɗa.

“Juwairiyya!” Da sauri ta juyo a razane tana ganin mutumin da yayi kiran nata.

Muhammad ne tsaye a bakin window ta gefen Salisu da alama ya ji kuma ya ga duk abun da ya faru. Fuskar nan tashi ta turnuƙe har sai da tayi jaa tsabar ɓacin rai yana tsaye yana kallonsu.

“Ki fito daga motar ɗan iskan nan.” Ya umurceta yana nuna Salisu da yatsa.

Har ta juya da niyyar fita sai kuma ta juyo tana kallon Salisu kamar mai neman izininshi shi kuma Muhammad yake kallo yana mishi wata murmushin mugunta.

“In fita?” Ta tambayi Salisu domin kuwa itama tana son fitan bata son ƙara ko second ɗaya ne a ciki.

Bai amsa ba sai da ya ɗauki seconds talatin suna kallon-kallon tsakaninshi da Muhammad sannan ya gyaɗa mata kai ta fita da sauri ta samu guri ta tsaya tana kallonsu.

Sai a lokacin Muhammad ya dubeta kamar wanda zai daketa ya ce,

“Yanzu ke baki ji kunya ba? Yanzu wannan mutumin ne zai sa ki saɓawa ubangijinki? Ina hankalinki da iliminki yake?”

“Mallam kai waye zaka zo har ƙofar gidansu kana zaginta? Ta sanka ne ko ƙarfin hali ne irin naku na ƴan sa ido?”

“Ba da kai nake yi ba, ka kuma riƙe sauran guntun mutuncinka.” Da haka ya ƙara maida dubanshi kan Juwairiyya wacce ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta amma idanunta na zubar da hawaye.

“Wannan ba halinki bane kar kuma ki bari wani ya zo ya ɓata miki tarbiyyar da aka jima ana baki. This is not you at all! Me yake damunki?”

“Don Allah ka tafi.” Ta samu kanta da faɗi ba tare da ta kalleshi ba.

“Mallam ka ji tace ka tafi.” Faɗin Salisu yana kaɗa kanshi kamar yana jindaɗin draman da suke yi.

Takawa Muhammad yayi da niyyar zuwa gurinta amma tayi saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu tana cewa,

“Just ka tafi, ba ya buƙatar ganinka a nan.”

“Something is wrong with you, this ain’t you! Yaushe kika damu da abun da wani yake so?”

 Wannan magana yasa ta harareshi sannan tace,

“Wato a haka ka ɗaukeni? Muguwa wacce kanta ta sani bata damu da wasu ba?”

Zai yi magana Salisu ya rigashi don ya lura spotlight ɗin ya bar kanshi ya koma kansu, hakan bai mishi daɗi ba don haka yace,

“Juwairiyya ki shiga gida sai gobe idan na dawo.” Yana gama magana ƙafafunta suka fara takawa ta nufi cikin gida.

Muhammad da hakan ya bashi mamaki yayi mata magana na ƙarshe don ya ga reaction ɗinta ya ce,

“Muhammad Hafiz bashi da lafiya suna kwance a asibiti, mamanshi tace tana son ganinki.”

Tsayawa tayi cakk sannan ta juyo fuskarta ɗauke da matuƙar damuwa ta ce,

“Subhanallahi me ya sameshi?”

“Juwairiyya ki koma cikin gida bana son tsayuwarki da wannan mutumin. Ki kirasu a waya ki gaishesu ya isa.” Faɗin Salisu a hasale domin zuwan Muhammad yana ƙoƙarin ɓata mishi shirinshi.

Bata ƙara magana ba ta shige cikin gida da sauri, hakan yasa Muhammad ya juyo ya kalli Salisu wanda shima shi yake kallo irin ‘me zaka yi akai?’ Bai ce komai ba ya shige motarshi ya tafi, ganin haka yasa shima Salisu ya kaɗa tashi motar ya bar unguwar yana ayyanawa a ranshi cewa Juwairiyya ta fara mishi musu ya kamata ya ƙara ɗaukan mataki a kanta.

Da daren ranar aka aiko wani yaro gurin Juwairiyya da wani leda babba tare da wani guntun note a paper wanda ta karanta kamar haka…

 ‘Ina ta duba hanyarki amma baki zo ba, jikin Hafiz har yayi sauƙi an sallamemu. Amma kafin nan sai da muka haɗa maganin da na gida kamar mayu ne suke son tsoritashi. Ga wannan ganyen magarya ne da wasu haɗi da aka yi don kare jikin mutum daga miyagun mutane, its 100% halal and sunnah kuma na karya sihiri ne. Ki tafasa ganyen kiyi wanka dashi sai kuma ki dinga karanta waɗannan addu’o’in a ruwa kina sha.’

Juwairiyya tana gama karantawa ta ɗauko wayarta don ta kira Salima amma ta samu wayarta is switch off, hakan yasa tashi ta je ta tafasa maganin tayi wankan dashi sannan ta karanto Du’a’ul Kanzul Arsh tare da wasu addu’o’i na karya sihiri ta sha ruwan, bata  jima da gamawa ba bacci mai nauyi ya ɗauketa.

Da ta tashi da asuba da ciwon kai ta tashi wanda ta alaƙantashi da kwanciyar da tayi wuyanta ya lankwashe. Tana idar da sallah ta ƙara ɗaukan addu’o’in kamar yanda Salima ta umurceta ta karantasu ta sha a ruwa wani kuma tayi ta shafa a jikinta. Gari na gama wayewa ta gama aikinta ta tafi makaranta akan idan ta dawo tayi abincin rana zata je ta dubo Hafiz Junior, ta ma manta da cewa wani mai suna Salisu ya ce kar ta je.

Bayan ta dawo gida ta ɗaura girki tana yi tana duba wayarta wacce Salisu yake kira akai akai. Tsaki ta ja da taga kiranshi na ashirin da uku tun safiyar yau, ita sai yanzu ma take mamakin yaya aka yi ta iya cigaba da fita tana hira dashi alhali tun farkon zuwanshi bai burgeta ba! Tana gama abinci Mama ta dawo daga aiki take tambayarta me ya samu wayarta Salisu yana ta kiranta bata ɗauka?

“Wallahi haushinshi nake ji Mama, kawai ki bashi haƙuri ba zan aureshi ba. Zan jira har Allah Ya kawo mini wani.” Ta faɗa tana ajiyewa Mama abinci a gabanta.

“Me kika ce? Sai da auren naku ya matso sannan zaki ce ba zaki aureshi ba?” Faɗin Mama tana dafa ƙirjinta kamar wani babban laifi Juwairiyya ta yi.

“Mama ni yaushe nace zan aureshi? Sai dai in da ke yayi maganar amma ni ban taɓa cewa zan aureshi ba wallahi. Shi ya faɗa miki haka?”

“Kar ki yarda ki fara wallahi domin dukkaninmu ranmu zai ɓaci. Ni zaki watsawa ƙasa a ido Juwairiyya? Ni ce nan na tambayeki ko kina sonshi kika amsa mini ehh zaki aureshi shine yanzu zaki ce kin manta?”

Shiru Juwairiyya tayi tana tunani sannan ta tuna lallai an yi hakan. To amma ina hankalinta yake da zata auri mutum irinshi kamar ɗan daudu?

“Sai yanzu na tuna wallahi, amma ni gaskiya na fasa. Ba zan iya auren irinshi ba.”

Shiru Mama tayi tana kallonta kamar mai kallon wata baƙuwar halitta, rainin wayon Juwairiyyan har ya kai haka ko dai barinta da tayi tana karatun ne yasa ta fara haɗuwa da ƙawaye masu hure mata kunne? Me yake damun Juwairiyya?

Abun da Mama bata sani ba shine Juwairiyya na fama da sihirin da Salisu ya mata a zuwanshi na biyu. Malaminshi ya bashi kwalli da zai zizara a idanunshi wanda da zarar ta kalli cikin idon nashi shikenan zata faɗa sonshi sannan zata dinga bin maganarshi kamar raƙumi da akala. Haɗuwan Muhammad da Salisu yasa Muhammad ya gane ba haka banza ya barta ba domin kuwa babu abun da bai sani ba game da rayuwar Juwairiyya. Labarin da ake bashi mara kyau akan Salisu yasa ya yanke hukuncin zuwa ya gani da idanunshi. A nan ya gane lalle Salisu yayi halin nashi don dama an ce yana biye-biyen malamai wasu kuma sun ce yana bin ƴan’uwanshi maza, shi Muhammad wannan ba damuwarshi bane, damuwarshi ita ce rayuwar Juwairiyya yanda zai kareta daga sharrinshi domin ya ɗauki alƙawari mai wuya, alƙawarin da yake wahalar dashi har ya jefashi a wani halin da bai shirya masa ba.

“To wallahi baki isa ba. Ba zaki mayar dani mutumiyar banza ba mai baki biyu. Wato karatun da na barki kici gaba da yi yasa kike son ki gagareni ko? To wallahi ba’a gidan nan ba. Sai ki zaɓa karatunki ko aure! In ba zaki yi auren ba ki zauna a gida kin daina fita zuwa makarantan kenan, don haka daga yau na soke zuwa makarantar.”

A bazata Juwairiyya ta ji furucin Mama wanda ya saka ta zaro idanunta tana kallonta cike da mamaki da kuma tsoro.

“Mama don Allah kar ki ce haka, nan da sati ɗaya fa zamu fara exams na second semester sannan kice ba zan ƙara fita ba? Ya zan yi da exams ɗin?”

“Sai ki bari wata shekara mai zagayowa ki yita idan kin yi aure kenan, in kuma wata shekarar ma ta zagayo baki yi auren ba sai ki bari sai wata. Batun makaranta kam na sokeshi dama mutane sun fara saka miki ido a kanshi.”

Kuka Juwairiyya ta fara wiwi da idanunta don ta lura da gaske Mama ta hanata cigaba da karatun akan wani banza Salisu. To wai ita ina hankalinta yake da ta amince zata auri sakarai irinshi har kuma take fita su yi hira? Tana cikin wannan kukan ne tana bawa Mama haƙuri aka aiko wani yaro wai Salisu yana kiranta a waje, tsabar haushi bata san lokacin da ta fita ta ɗauki takalmi a bakin ƙofa ta jefi yaron dashi ba, Allah Ya taimakeshi ya gani yayi saurin duƙawa takalmin ya wuce ta saman kanshi kana ya fita da gudu bayan ya ɗura mata ashar.

Mama da ta ga komai sai abun ya ƙara ɗaure mata kai game da Juwairiyya, lallai da alama ta fara kufce mata, yaushe ta bari rashin hankalin nata ya kai haka?

“Sannu isheshshiya, nace sannu! Yanzu in takalmin ya bugeshi ya ji ciwo me zaki cewa uwarshi? To wallahi Juwairiyya ki fita a idona in rufe. Karatun na sokeshi sannan idan ba zaki yi auren ba ki fita ki faɗa mishi da bakinki ya daina damuna a office a kan zancenki, wallahi na gaji da fitinarki Juwairiyya. Kullum idan na doso gidan nan na tuna cewa kina ciki kina zawarci sai na ji gabana ya faɗi, na samu kin amince zaki aureshi shine yanzu zaki toɓare? Haba, yarinya ke kaɗai kin hanani kwanciyar hankali? Ke ce wannan gobe ke ce wannan? Kullum maganar da za’a kawo mini a kanki daban nan ma na yarda da tarbiyyar da na baki ne amma ko faɗin bana son in ji ana yi. Da kina gidan mijinki babu wanda zai dinga bin diddiginki shiyasa na gwammace kiyi auren ki huta nima in huta. Haba!” Tana gama faɗin haka ta shige ɗakinta ta bar Juwairiyya na kuka wanda tsananin mamakin kalaman Mama take yi.

Wato ashe ta gaji da kallonta a gidan? Wato gulmarta ake kai mata duk dama bata aikata komai na alfasha ba, in banda riƙe hannunta da Salisu yayi jiya nan ma bata san dalilin da yasa ta yarda har ya shammaceta haka ba. Ai kuwa baƙin cikinta ya ninku ya zo mata har wuyanta ya toshe mata maƙoshi, duk sai ta sauƙesu yau a kan Salisu tunda dama a kanshi ake mata wannan faɗan har aka hanata cigaba da karatunta alhali yanzu shine kaɗai yake ɗebe mata kewa da kuma ɗauke mata hankali kan damuwarta.

 Kamar iska ta figi hijabinta dake bakin ƙofar kitchen ta fita waje ta samu Salisu a cikin motarshi ya harɗe hannunshi ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da waya ya kara a kunnenshi da alama ita yake kira domin yana ganinta ya ajiye wayar yana mai tamke fuskarshi. Tana isa gaban motar ta ja tunga ta tsaya tana huci kamar zata ci babu, tsabar masifar da yake nuƙurƙusarta har ta rasa ta ina ma zata fara azalzalarshi.

“Menene ya faru tun da safe ina kiranki kin ƙi ɗauka? Kin san bana son irin haka, in ma wata damuwa ce nace ki kirani ki faɗa mini ba wai ki barni ina ta wahala ba.”

“Sannu ubana! Na ce sannu ubana Salisu. Kai ka ganka? Wallahi ka kiyayeni don in ba haka ba sai na maka rashin mutuncin da kullum ka tuna da ni sai ka koka. Mugun mutum mai shiga tsakanin uwa da ɗanta kawai. Auren da nace zan yi kuma na fasa, dama ni ban san ina hankalina yake da har na yarda zans aureka ba. Macuci azzalumi ɗan iska mai riƙe matar da ba tashi ba, ashe dama kai ma  ɗan iskan ne ban sani ba? Ashe kaima zuwa kayi ka cuceni ka watsar ko? To wallahi ka ganni nan? Na fi ƙarfinka! Na fi ƙarfi  mutum irinka, kuma in kana da zuciya a ƙirjinka kar ka sake tako ƙofar gidan nan da sunan ka zo gurina.”

“Yauwa, ga Juwairiyyan da na sani.” Faɗin Muhammad yana takowa a hankali yana murmushi mai ƙayatarwa.

Ta juya shima zata masifeshi ya ɗaga hannunshi sama alamar surrender ya ce,

“Na zo tambayar meyasa baki zo kin duba Muhammad Hafiz bane.”

Ai kuwa nan da nan ta sassauto ta matso gurin Muhammad tana cewa,

“Ya jikin nashi? Jiya nayi ta kiran mamanshi wayarta a kashe, dama akan idan na gama aiki zan je na dubasu ne. Kai kuma me kake jira? Ta juyo ga Salisu ta zare mishi ido wanda sai da ya ji ɗarr a ranshi.

Mamaki kuwa yana cikinta tsulum domin har yanzu ya kasa gaskatawa wai Juwairiyya ce take mishi masifa ba! Juwairiyyan da bata mishi musu tana bin umurninshi kamar shi ya haifeta yau shi take yiwa masifa tana zaginshi? Ba dai aikin da Mallam ya mishi ya karye ba? Dama ba wani mai ƙarfi aka yi ba saboda baya son mutane su ankara don a yanzu ma an fara ganoshi. Dubanta yayi a karo na biyu ya ga tana watso mishi harara da alama ba zata daina ba har sai ya bar ƙofar gidan, hakan yasa ya rufe marfin motarshi ya tafi ba tare da ya ce musu komai ba, amma kuwa fuskarshi ta fallasa zuciyarshi wato bai haƙura ba kuma sai ya rama cin mutuncin da Juwairiyya ta mishi.

Dandandandandandan!

“Juwairiyya ina so mu yi magana da ke amma kafin nan ina so ki nitsu ki bani hankalinki.”

Confused take kallonshi don bata san me zai faɗa mata ba.

“Lafiya kam?” Ta tambayeshi tana mishi iso zuwa inuwar katangar gidansu.

“Ba lafiya ba. Aikan da jiya aka ce miki Salima ce ta aiko miki ba ita ba ce, ni ne! Sannan na saka ta kashe wayarta ne don kar ki kira ta faɗa miki ba ita ba ce ki ƙi amfani da maganin.”

“Innalillahi wa inna ilaaihir raji’un! Maganin mallaka ka bani?”

Kallonta yayi kamar wata wawuya yace,

“Kin taɓa ganin an yi maganin mallakar mutum Du’a’ul Kanzul Arsh? Addu’an da yake karya sihirin ne zai zama na sihiri?”

“To na uban me ka bani?”

“Da alama kin samu kanki, da kuma a nan kika tsaya kina kuka wancan wawan ya tasaki a gaba yana miki ihu kina bin umurninshi blindly.” Faɗin Muhammad yana hararta don ya lura she is ungrateful duk da cewa bata san ceton da ya mata ba.

“Wallahi nima sai yanzu abubuwan suke ta dawo mini, na rasa gane meyasa nake bin duk maganarshi kamar wacce ya yiwa asiri.” Ta faɗa tana murza goshinta a hankali tana tunani kanta a ƙasa.

Jin shiru Muhammad bai yi magana ba yasa ta ɗago kanta tana kallonshi. Gyaɗa mata kai yayi wanda nan da nan kwakwalwarta ta fara haɗa mata nan da can!

“No!” Ta faɗa a hankali hawaye na taruwa a idanunta.

“Yes.”

“No!” Hawayen suka zubo ta rufe bakinta da hannunta jikinta ya fara ɓari tana kuka.

“Look at me! Ki daina kukan nan kar ki jawo mana hankalin mutane kanmu.” Faɗin Muhammad yana mata katanga da jikinshi kar masu wucewa su ga halin da take ciki.

Sai da ta ɗan nitsu sannan ta dubeshi tace,

“Ya aka yi ka gane? Sannan kai ka kawo mini maganin da ya karya sihirin?”

“Baki da kunya, kina da raini sannan ba’a sakaki kiyi, da haka na gane.”

In a wani lokaci ne ya faɗa mata haka zata ce zaginta yake yi amma wannan karon godewa Allah ta yi da ya har yasa ya gane cewa wai ba’a hayyacinta take ba.

Godiya ta shiga yi mishi babu ƙaƙƙautawa domin wa zai so akalar rayuwarshi ta zame daga hannunshi ta sauƙa kan hannun wani? Shikenan mutum ya zama kamar mutum mutumi bashi da tunanin kanshi sai abun da wani yace yayi! Akwai baƙar ƙaddarar da ta wuce wannan? Ai sai ta ji ashe a da hankalinta ma a kwance yake, yanzu kuma da ta san me ya faru da ita sai tsoro ya shiga ranta.

“To yanzu ya zan yi? Kar fa ya ƙara mini wani. Wayyo Allah na.” Nan kuma ta sake birkicewa sai da kyar Muhammad ya saitata nan ma sai da ya ɓata rai ya mata tsawa.

“Idan ba zaki nitsu ba sai in yi tafiyata, ina da ayyuka da yawa na bari na zo ina babysitting ɗinki.”

“Why are you helping me? Na ɗauka ka tsaneni.”

Kamar ba zai amsa ba sai can kuma ya tsura mata ido ya ce,

“Saboda abokina Hafiz! Na mishi alƙawari kuma ba zan taɓa karyawa ba duk da cewa you are insufferable. And I don’t hate you, halayenki ne bana so.”

Harara ta watsa mishi kana tace,

“To yanzu ya zan yi kar mutumin nan ya samu galaba a kaina again? Gashi yau ɗin nan Mama ta datse mini farin cikina wai ba zan sake zuwa school ba sai dai in bari ko kuma in yi aure in ci gaba da yi.” Ta nemi shawaran Muhammad wanda a da in aka ce mata zata zo ta kalleshi a matsayin mai bata shawara zata zagi duk wanda ya faɗi hakan.

Kaɗa kafaɗa yayi sannan ya gyara tsayuwarshi domin ya fara gajiya ya ce,

“Ki yawaita addu’a ko kuma kiyi auren, auren kuma shine rufin asirinki domin idan ya ji kin yi zai haƙura sannan zaki samu kici gaba da karatunki, nima kuma na huta da bibiyar rayuwarki don na fara gajiya.”

“Na yarda zan aureka Muhammad. Ka aiko sadakinka gobe a ɗaura mana aure.” Ta faɗa da murmushi a fuskarta domin sai yanzu ta gane ɓullowar Muhammad a rayuwarta kullum ba haka banza bane, they were meant to be together ne. Salima zata fahimceta tana da tabbacin hakan. (Ohh, you don’t!).

“No!” Muhammad ya faɗa da sauri yana ɓata fuskarshi.

“Yes.” Ta ƙara faɗaɗa murmushinta.

Juyawa yayi ya nufi motarshi yana karkaɗa kanshi ta bishi tana cewa,

“Ka turo gobe a ɗaura auren.”

“Ke ki barni fa.”

“But you promised him cewa zaka aureni idan na yarda. You promised Muhammad!”

Wannan magana yasa ya carke ya tsaya kana ya juyo ya dubeta bata daina murmushi ba ya ce,

“You will be the death of me. Ki faɗa musu gobe zan taho da magabatana a ɗaura auren da safe.”

“To maigida.”

Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama’a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne!

 Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. To yaya rayuwar tasu zata ƙaya? Ku biyo Mum Fateey domin yanzu zamu shiga gundarin labarin.

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad

(14)

“Cewa aka yi da ta ji labarin auren suma ta yi.”

“Nima na ji wannan, to amma kuma wasu sun ce ita ce tace ya auri ƙawar tata.”

“Ɗazu kuma na ji wai asiri ta yiwa ƙawar da mijin suke bibiyanta a gindi sun kasa rabuwa da ita, to in ba asiri ba don tana matar aboki kuma abokin ya mutu shekara uku da suka wuce babu ɗa tsakaninsu sai kuma su ci gaba da zumunci da ita? Ni dai wannan cin amanan da tayi yasa na daina kallonta a mutumiyar kirki, dama an ce ba’a shaidan ɗan kuturu sai ya mutu da yatsa.”

“Ku naku duk mai sauƙi ne, ni abun da na ji sai da yasa na ja baya. Wai ashe bibiyar mijin ƙawar take yi har ya mata ciki shine ƙawar ta fahimta tace zata tona musu asiri suka yi gaggawan yin aure don su rufe.”

“Ni dai koma menene gaskiyar ban ji daɗin auren mijin ƙawar tata da tayi ba. Haba ai da kunya da kuma nauyi, suna zumunci sosai har mijinta da ya mutu sai da ƙawar ta sa maigidanta ya mishi takwara. Yanzu duk wannan bai isa ya haneta aurenshi ba?”

“Kuna ta wani cece kuce, kuma duk maganar akan ita macen ce! Shi mijin ba zaku ga laifinshi bane da yake bibiyar ƙawar matarshi? An ce maza sun fi mata hankali to me yasa ba za’a ɗauki laifin kacokam a ɗaurawa namijin ba tun da ya fi hankali? Sai a mata uzuri tunda dama bata da hankali, ba haka mazan suke cewa ba?”

“Ku dai mu bar maganan nan haka, Allah Ya basu zaman lafiya kawai.”

*****

Juwairiyya ce zaune a gaban Mama tana mata nasiha sannan ta ɗauki dubu hamsin ta miƙa mata tana cewa,

“Ga sadakinki nan, Allah Ya baku zaman lafiya Ya kuma sa gidanki ne na har abada Juwairiyya. Allah Ya kaɗe hau Ya kuma haɗa kanku kuyi zaman lafiya.”

“Amin.” Juwairiyya ta amsa kamar ma hankalinta baya gurin.

Da haka Mama ta sallameta ta koma ɗakinta ta samu guri ta zauna tana tunani. Wai shikenan da gaske ta zama matar Muhammad? Mutumin da ta tsana a da har take zaginshi tana kusheshi yau shine mijinta? Bayan wannan yaya zata yi da Salima wacce aka ce suma tayi da ta ji labarin mijin nata yayi aure kuma wai ita Juwairiyya ya aura? Anya bata tafka babban kuskure ba wajen auren Muhammad? Anya kuwa shima ba asirin ya mata ta nemi ya aureta ba? Kai da hankalinta! Don tana tunawa ta gwammace ta zauna da Muhammad akan ta rasa karatunta ko kuma worse Salisu ya mata wani asirin ya ɓatar mata da hankali har ya aureta. Sai dai da akwai wani option da zata samu a wannan lokacin ba Muhammad ba to da shi zata zaɓa. Lallai ta ƙaryata zancenta da take cewa ko mazan duniya sun ƙare ba zata aureshi ba. Gashi yanzu akan gujewa wani namijin ta zaɓi zama dashi don tsoro.

Fatanta Salima ta fahimceta domin ba son mijinta take yi ta aureshi ba, tayi hakan ne don shine only hope ɗinta don gujewa mummunar ƙaddara. Sannan da zarar ta samu ta gama makarantarta ta kama aiki zata nemi ya saketa a lokacin kuma ta san tayi girman da Mama zata barta taci gashin kanta. Da wannan tunanin ta ɗauki waya ta kira Salima amma ta ji wayarta a kashe, ko dai har yanzu bata farfaɗo bane? Tun jiya ta so kiranta fa faɗa mata amma sai ta ji ta gagara, don haka ta barwa Muhammad wannan aikin. Shi kuwa tunda suka gama magana jiya bata sake jin ɗuriyarshi ba sai sadakinshi da aka damƙa mata bayan an ɗaura aurensu da misalin ƙarfe tara na safe. Kwata-kwata mutanen da suka halarci wannan ɗaurin auren mutum goma ne, biyar daga gareshi haka biyar daga fanninta. Wani ƙanin babanta da bai san cinta ko shan ta ba ya buɗi baki yake faɗawa mamanta wai shi fa ya gaji da zuwa ɗaurin aurenta! Wannan magana ya yiwa Juwairiyya zafi da take sauraronsu daga can ɗakinta yayin da su kuma suke tsakar gida. Ta so ta fita ta faɗa mishi baƙar magana amma da ta tuna cewa Mama ba zata goya mata baya ba, kai karshe ma hakan zai jawo musu matsala yasa ta kame kanta amma ta mishi addu’a shima ya ji yanda ta ji. Ai ba yin kanta bane aure-auren, mijinta na farko mutuwa yayi wanda in ba don mutuwa ba babu abun da zai rabasu, na biyu kuma lalura yake dashi ya saketa ba da son ranta ba. Sai kuma wannan na ukun zata yi shi ne na wasu shekaru uku zuwa huɗu tsanani kafin ta samu ƴancin kanta ta kasheshi. Wannan kenan.

Duk ƙoƙarin da Juwairiyya ta kai ga neman Salima bata sameta ba, hakan yasa ta ji shakka ya shiga zuciyarta ba dai tayi fushi da ita bane? Ta ɗauka Saliman zata nemeta saboda tafi kowa sanin yanda ta tsani mijinta, zata tambayeta ba’asin yaya aka yi har hakan ya faru? A nan ita kuma zata mata bayani sannan ta ƙara da bata haƙuri don zata shigo gidanta ne ba da niyyar zama ba sai don ta yada zango kaɗan ta wuce.

Har maghrib tana nemanta amma bata sameta ba, gashi Mama har ta kafa mata doka kamar kwanakin can wai ba zata fita ba sai da izinin Muhammad mijinta. Abun dariya ya so ya bata, wato shi Muhammad ɗan lukutin zata tambaya idan zata fita?

Ganin babu sarki sai Allah yasa Juwairiyya ta danna kiran Muhammad wanda bata ma san ya aka yi ta samu numbernshi ba.

“Don Allah ka zo ina son ganinka.” Shine abun da ta faɗa da ya ɗauki wayan.

“Ba zaki iya jira har ki tare ba kenan?” Ya bata amsa daga cikin wayar.

Sai da tayi jimm sannan ta gane inda maganarshi ta dosa. Kunya da kuma takaici ne ya zo ya rufeta wai yau ita Muhammad yake faɗawa maganar banza? Ko da yake laifinta ne da ta faɗi wannan sentence ɗin don koma waye ne ya ji zai ɗauka wani abun take nufi.

“Dalla ni ba abun da nake nufi ba kenan. Allah Ya sauwaƙe God forbid bad thing. Magana nake son mu yi.” Ta faɗa a hasale tana ɗaga murya.

“Idan kin koyi magana da miji ki kirani sai mu yi maganar a natse.” Da haka ya kashe wayarshi ya bar Juwairiyya da ɗan banzan mamaki a fuskarta. Wai da gaske kashe wayar yayi? Lallai bai san wacece ita ba.

Shiru tana zaune tana tunanin zai kirata amma har aka shafe minti ashirin bai kirata ba, kuka ne kaɗai bata yi amma haushi kam ya kusa kasheta. Ashe dama bai daina wannan halin nashi ba?

Ganin babu Sarki sai Allah yasa ta kirashi ta fara magana a hankali.

“Don Allah magana nake son yi da kai in zaka iya zuwa.”

“Na ji.” Kawai ya faɗa ya ƙara kashe wayarshi.

Wannan karon hanjin cikin Juwairiyya ne ya kaɗa domin da alama ta manta waye Muhammad, ta manta ɗan banzan halinshi da take kushewa kullum a gaban kowa. Ashe bai daina ba? Yanzu ta yaya zata iya zaman auren dashi na shekara huɗun yana gwada mata wannan halin? Lallai watarana zasu yi kokawa, amma da ta tuno siffarshi sai ta girgiza kanta, ba zata fara ba! To yanzu kam yana zuwa ne ko dai?

Bayan wani minti ashirin ɗin ya kira wayarta, tana ɗauka ya faɗa mata yana waje.

Sai da ta faɗawa Mama kafin ta fita ta sameshi a cikin mota yana zaune, ganin ta fito yasa shima ya fito suka tsaya gefe da gefen juna.

“Ina ta neman Salima amma har yau wayarta a kashe. Lafiyanta kam?”

“Shine maganar?” Ya tambayeta da ɗan mamaki a fuskarshi.

“Akwai wasu amma wannan ne farko.”

“Wayarta ce ta fashe.”

“Don Allah yaya ta ɗauki zancen auren nan? Ta yi fushi ko?” Ta tambayeshi cikin zullumi.

“Ba zan iya faɗa miki ba amma dama ta san hakan zai iya faruwa.”

“Ban gane ba.” Ta faɗa cikin ruɗu.

“Sai wanne?”

“Ba zaka fahimtar da ni ba kenan?”

“Eh.”

“Sai kuma batun tarewa ta ina so sai bayan na gama exams kafin nan mutanen da suke cikin gidana sun fita.”

“Me kike nufi kenan?” Ya tambayeta yana ɗaga girarshi ɗaya wanda bata gani ba dalilin duhun dare.

“A can zan zauna.” Ta bashi amsa zuciyarta na bugawa. Dama ta san sai sun kai ruwa rana kafin ya yarda.

“Kina nufin ba zaki zauna a gidana ba kenan ni zan dinga binki gidanki?”

“Ni ban ce ka dinga bina ba, ba lalle sai ka zo inda nake ba.”

“Juwairiyya me kika ɗauki aure ne? Wasan yara ko shiririta?”

“Yau karo na uku kenan kana kiran sunana a rayuwarka.” Ta faɗa duk kuwa da irin taraddadin da take ciki.

“Kar ki canja mana magana. A gidana zaki zauna har lokacin da Allah zai buɗa mini in canja muhalli, but for now a can zamu zauna.”

“Don Allah Muhammad ka rufa mini asiri kar ka kafe akan wannan maganar, aurenka da nayi ma na san Salima zata ji zafinshi shiyasa nake son yin nesa da ita ta yanda ba zata dinga kallona ba balle ranta ya dinga ɓaci. Ka ga kuma gidan ka na zaman mace ɗaya ce ba zai ishemu mu biyu ba. Don Allah ka yi haƙuri.”

“Yanzu bari in tambayeki. Wancan mutumin da kika aura kin faɗa mishi cewa a gidanki zaki zauna?”

Girgiza kanta ta yi don bata san ina maganarshi ta dosa ba.

“Sai nine da kika rainawa arziki zaki nemi tarewa a gidanki? No. Sai kuma wani magana?”

Wani mololon baƙin ciki ne ya zo ya tokarewa Juwairiyya wuya, ji take yi kamar ta ɗauki sanda ta yita zabga mishi tsabar haushin shi da take ji. Zai ɓata mata tsari, ba haka ta tsara ba. Ta so ta tare a can gidanta da marigayi Hafiz ta yanda zata yi nesa da Salima haka kuma Muhammad ba zai dinga damunta ba saboda zata san yanda zata dinga ɓata mishi rai yana nisantarta, a haka tayi ta cin karenta babu babbaka ita ɗaya har ta gama makaranta ta samu aiki ta kashe auren. Duk wannan tsarin da tayi Muhammad na neman wargaza mata shi.

“To na ji ba zaka bini gidana ba amma ai zaka iya kama mini haya a wani guri kafin Allah Ya buɗa maka ɗin.”

“Bani da kuɗin karɓan hayan wani gida alhali ga nawa.”

“Muhammad ka yi haƙuri don Allah, wallahi ko tsugunawa kace in yi zan yi don kar ka haɗamu gida ɗaya.” Ta faɗa da bakinta amma zuciyarta na jin takaicin furucin.

“Ke ma ki yi haƙuri amma ba zan raba muku gida ba, tun farko haka ne tsarina kuma ba zan canja ba.”

Tsabar baƙin ciki komawa ta yi cikin gida ba tare da ta mishi sallama ba. Tana shiga ɗaki kuwa ta ji wayarta na ringing wanda tana dubawa ta ga sunan Salima ce a jiki wanda ta sanya mata ‘Maman Masoyi’. Tsoro ne ko fargaba ya hanata ɗauka sai Allah! A haka ya tsinke can kuma aka sake kira ta ɗauka hannunta na rawa bakinta kuma ya fara rasa yawu.

“Hello.” Ta furta muryarta na rawa kaɗan.

“Amaryar mu! Baban Hafiz yace kina ta nemana a waya baki sameni ba, wallahi jiya ne yace in kashe wayar ban san dalili ba, daga nan kuma na ajiyeta a kan kujera Masoyinki ya jawo ya dokata a ƙasa sai da taci screen. Yanzu aka dawo mini ita daga gurin gyara shine nace bari in kiraki. Kar in cikaki da surutu, Congratulations! Allah Ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna.” Faɗin Salima ta cikin wayar da alama bata da damuwar komai a ranta.

“Ranki bai ɓaci ba da na aure miki miji?” Juwairiyya ta tambayeta tana jin hawaye na taruwa a idanunta.

“Ko bai aureki ba zai auri wata, to na gwammace a kawo mini ke domin na sanki kema kin sanni kuma zamu fi fahimtar juna mu lallaɓa rayuwar mu. Kin san yanda mijin namu yake, yanzu idan nace ma zan ɗaga hankalina sai na  gwammace kiɗa da karatu.”

Hawaye ne ya zubowa Juwairiyya domin da alama ta manta halayen Muhammad, da gaske ta manta. To in ba haka ba sau nawa Salima tana faɗa mata abubuwan da yake mata tana jin haushi a ranta har take jin da tana da iko dashi da sai ta hukuntashi! Yau gashi itama tun kafin aurensu ya kwana ya shirga mata baƙin ciki, kuma babu yanda ta iya dole ta bishi saboda babu yanda zata yi. Duk masifanta ta sani cewa ba zai yi amfani akan Muhammad ba.

“Da gaske baki yi fushi ba?” Ta ƙara tambayarta don sanin zuciyar Salima.

“Na faɗa miki ban ji komai ba, fatana Allah Ya bamu zaman lafiya. Maganganun da yawa amma sai gobe zan kiraki zan je in yiwa Muhammad aiki kar ya dawo ya samu ban yi ba.”

Da haka suka yi sallama Juwairiyya na jinjina haƙuri irin na Salima, ta wani gurin kuma tana tausaya musu dukkansu domin Muhammad ya cika mugun mutum kuma mara tausayi.

Sati ɗaya da haka Juwairiyya ta fara exams wanda Muhammad ya nema mata mai napep da zai dinga kaita yana dawo da ita domin ya ce baya son tana zuwa bakin titi taran abun hawa, sannan shi kuma ba zai iya kaita ba domin yana da ayyuka. A haka taci gaba da rubuta exams ɗinta cikin nitsuwa domin bata da damuwar komai yanzu in ba ta Muhammad ba, yana zuwa dubata kullum sannan ya tambayeta ko tana da wata buƙatar da zai iya biya mata? Idan tana dashi sai ta faɗa ya saya mata, wani lokaci kuma sai ta ƙureshi ta tambayeshi abun da ta san ya fi ƙarfinshi, to a nan ne zasu yi dramansu su rabu. Sai kuma Mama ta daina tsangwamarta, Salima kuma da take tunanin za’a samu matsala da ita sai ta bata mamaki domin kuwa sai ta ga kamar ma sun ƙara shaƙuwa akan yanda suke a da, domin duk gyaran gidanta da ake yi na toshe-toshe tana faɗawa Juwairiyya watarana har ta mata video.

Dama gidan Muhammad ba wani babba bane, da ka buɗe gate ka shigo zaka samu farfajiyar gidan mai ɗan faɗi amma mota ɗaya zata iya ɗauka, ƙofofi biyu zaka gani a jikin ginin gidan wanda na gefen dama ƙofa falon Muhammad ne da kuma ɗakinsa da banɗaki a ciki, a cikin falon kuma akwai wata kofa wacce ita ta raba tsakaninshi da falon Salima, wanda ita nata gefen ɗaki take dashi da kuma kitchen ɗinta wanda yake da ƙofa ta bayan ɗakunan nasu. To wannan ƙofar tsakanin falon Salima da Muhammad ɗin aka toshe, sannan aka yanki wani guri kaɗan a cikin tsakar gidan nasu aka yiwa Juwairiyya ƙaramin kitchen kamar ɗakin maigadi.

 Duk lokacin da Salima ta nuna mata progress ɗin aikin sai tayi tsaki tana jin haushi a ranta sannan sai ta fara kushewa, tana faɗa mata cewa ita ba haka ta so tun farko ba, sannan ga plan ɗinta na zama a gidanta amma Muhammad ya hanata. Wannan kenan.

Tun kafin ta gama exams Mama ta fara bata kayan gyara amma da ta je ɗaki sai ta watsasu bayan wardrobe, ana saura kwana huɗu tarewanta Mama ta kawo mata ci da kaza wanda Juwairiyya tsabar kwaɗayi ta kasa haƙura sai da ta cinye tass ta shanye romon, a cewarta ta karanta Suratul Fatiha a ciki ba zai mata maganin komai ba. Sannan wa ya faɗa musu wani abu zai shiga tsakaninta da Muhammad? Mutumin da zai iya karyata a dawo ana jinyarta!

A ranar da aka mata jere a ranar aka kawo Juwairiyya ɗakinta da daddare wanda tsabar haushi da kuma takaicin ɓata mata plan da Muhammad yayi sai ta samu kanta da zubar da hawaye bayan kowa ya watse. A haka Muhammad ya shigo ya sameta tana zaune a ƙasa tana zubar kwalla.

“Me ya sameki? Baki da lafiya ne?” Ya tambayeta yana ajiye ledan kaza a gabanta.

“Babu ruwanka da ni.” Ta faɗa cikin tsiwa.

“Hakan na nufin lafiyarki kalau kenan.”

Da haka ya fara cire kayan jikinshi wanda yasa Juwairiyya ta ji kunya ta juyar da kanta taci gaba da matsar kwalla. Tana ji yayi wanka ya fito sanye da jallabiya sannan yace ta shiga tayi alwala su yi sallah amma tace ba zata yi ba. Shi yayi sallanshi ya idar ya jawo ledar kaza ya buɗe ƙamshinta ta doki hancin Juwairiyya amma tsabar taurin kai tace ba zata ci ba. Bai ƙara kulata ba ya ci kazarshi ya bar mata saura sannan ya shiga banɗaki ya wanke hannunshi da bakinshi ya fito ya hau kan gado yace,

“Idan kin gama kukan ki zo ina buƙatar matata.”

Dandandandandandan!!!

Wai yaya rayuwarsu zata kasance a rufi daya?

Wai shin salima har cikin zuciyarta take murna da auren Muhammad da Juwairiyya?

Wai kuwa burin Juwairiyya zai cika na datse igiyar aurenta da Muhammad idan ta samu sarari da Yancin kai?

Wai yaya za’a yi wannan zaman ne tsakanin Salima mai sanyin hali, Muhammad Mugu da Juwairiyya Yar rigima?

Jama’a wai ina Daddy yake? Shin ya rabu da Juwairiyya har abada ne ko Akwai sauran rabo?

Ina Salisu mai kwallin sihiri? Ya rabu da Juwairiyya ne ko zai dawo da karfinshi?

Juwairiyya ce zaune a ƙasa tana gyangyaɗi ta ji muryar Muhammad a tsakar kanta wanda hakan yasa tayi firgigit ta farka tana kallonshi. Yana kan gadon har lokacin bai motsa ba sai danna wayarshi yake yi.

“Kina wahalar da kanki, ki tashi a gurin ki zo ki kwanta.”

Har zata buɗi baki tayi mishi tsiwa sai kuma tayi shiru domin ita kanta ta san tana buƙatar baccin bayan wunin da suka yi da baƙi yan tayata murnan tarewa duk da cewa bata gayyaci kowa ba sai family na kusa sosai.

Cikin wardrobe ɗinta ta buɗe tana neman rigar bacci don bata san a ina ƴan jeren suka ajiye mata ba. A cikin wardrobe na biyu ta gansu a jere iri daban daban wanda ta saya lokacin tana seducing ɗin Daddy. Lallai komai zai zo ya wuce domin a yanzu bata buƙatar irinsu saboda bata da niyyar seducing ɗin Muhammad sai dai su gama shan ƙurarsu a gurin.

Da wannan tunanin ta ɗauki pajama riga da wando ta nufi banɗaki tayi wanka sannan ta saka kayan ta fito tana lulluɓe da hijabi. Bargon da aka ajiye a kan gado ta ɗauka tana hararan Muhammad wanda shi kuma binta yake yi da ido da alamun mamaki a fuskarshi. A can ƙasan tiles ta shimfiɗa bargon sannan ta ɗauki pillow ɗaya daga kan gadon ta kwanta abunta.

“Me hakan kenan?” Ta jiyo muryar Muhammad.

“A ina?”

“Me yasa ba zaki zo mu kwanta ba?”

“Nan ya fi mini daɗi, kuma sai in kwanta gado ɗaya da kai? Ka sake tunani.”

“Don me yasa ba zamu kwana kan gado ɗaya ba?”

“Saboda ka tsaneni.”

Murmushi yayi mai sauti kana ya tashi ya kashe wutan ɗakin ya koma ya kwanta ya cigaba da danna wayarshi. Juwairiyya kuma juye-juye ta fara yi a ƙasan domin sai ta ji kamar bata saka komai a ƙasan ba don tiles ɗin har kartan ƙasusuwan haƙarƙarinta yake yi. Minti sha biyar da haka ta miƙe tsaye tare da bargon ta kwanta a gado can nesa da Muhammad bayan ta saka bargon a tsakaninsu.

“What changed your mind?” Ya tambayeta yana ajiye wayar tashi a gefe sannan ya juyo yana fuskantar bayanta dalilin ta juya mishi baya.

“Ai ni ya kamata na kwana akan gadon tunda nawa ne, kai ka koma ƙasa.”

“To dama ni na faɗa miki ina son mu raba makwanci ne?”

Bata kulashi ba, dalilin zuciyarta da take tsananin bugawa tun da ta haura kan gadon saboda muryarshi da take ji kamar a ƙeyarta. Yaushe ya gangaro har bayanta? Ko dai mind ɗinta ne yake tricking ɗinta? Bata yi aune ba ta ji Muhammad ya saƙala hannunshi a cikinta ya kwanto ta bayanta sosai har tana iya feeling kowanne gaɓa na jikinshi ciki kuwa har da wanda ya sakata jin tsoro da kuma mamaki.

“Muhammad don Allah ka sakeni kar ka manta fa ka tsaneni.” Ta faɗa muryarta na rawa sannan ta ƙasa ko motsi gudun kar ta tsakalo wani abun.

“Ni ban tsaneki ba.” Ya bata amsa yana shinshinar wuyanta yayin da hannunshi kuma yake yin sama a hankali tamkar mai tafiyar tsutsa.

Runtse ido Juwairiyya tayi tana fighting da feelings ɗin da take ji domin kuwa jinta kaɗai da tayi a jikin Muhammad ya tayar mata da tsohuwar yunwarta da yayi shekaru yana nuƙurƙusanta. Halayen Muhammad da bata so ta fara tunawa wai duk don ta daina jin abun da take ji amma abun yaci tura domin a yanzu zata iya rantsewa babu abun da bai taɓa ba na jikinta.

Shawara ta yanke akan zata barshi wannan karon amma daga yau ba zata ƙara bari ya taɓata ba, ko ba komai itama tana buƙatar ta samu sassauci. Da wannan tunanin ta biye mishi suka luluƙa duniyar ma’aurata wanda da tafiya tayi nisa sai da Muhammad ya rufe bakinta gudun kar makwabta su jiyo ta.

Duk wannan abun da ya wakana a kunnen Salima wacce ta kasa bacci ta fito ta ƙofar kitchen ɗinta ta je bakin windown su ta tsuguna tana sauraran haɗuwarsu, wanda take ji kamar ruwan dalma ne ake zuba mata a zuciyarta. Daidai saitin zuciyar ta kama hawaye na gudu a fuskarta ta tashi cikin sauri ta bar gurin ta koma ɗakinta.

Da asuba Muhammad ne ya riga tashi ya je yayi wanka sannan ya zo zai tayar da Juwairiyya wacce tun shiganshi banɗaki ta farka, tana tuno abun da ya faru ta ji wani mugun kunya ya dabaibayeta. Wai ita ce ta raya sunnah da Muhammad ɗan lukuti? A da tana mamaki idan ta ga mata ƙarama miji babba don a zatonta ɗaya zai karya ɗaya amma a jiya ta gane cewa Allah ba ya ɗaurawa mutum nauyin da ba zai iya ɗauka ba. (Hahaha).

“Ki tashi ki je kiyi wankan janaba.”

“Ai na sani ba sai ka faɗa mini ba.”

“Na ɗauka baki sani bane saboda jiya ma sai da nace ki rage muryarki.”

Wannan karon rufe fuskarta tayi da tafukan hannayenta ta fara kuka domin ita kanta in ta tuna irin bajintar da tayi sai ta ji kamar ta shaƙe kanta, to da alama Muhammad bai manta komai ba kuma sai ya nuna mata bai manta ɗin ba.

 Kaɗa kanshi yayi yana murmushi kana ya fita daga ɗakin ya je ya kwankwasawa Salima wacce ta kwana bata yi bacci ba, gyara muryarta tayi kamar mai magagin bacci tace mishi ta tashi shi kuma ya wuce masallaci.

Juwairiyya tana jin Muhammad ya fita tayi saurin faɗawa cikin banɗaki tayi wanka, fitowanta kenan ta dubi kan gadon nata ta ga yanda suka wargazashi kamar an yi yaƙi a kai. To wai dama haka lukutaye suke basa jin nauyin jikinsu? Ta ɗauka a cikin maza sune ragwaye ashe bata san komai ba da sauranta. Wannan tunanin yasa ta fara jin wani baƙon yanayi a jikinta don haka tayi saurin canja tunaninta domin ta rantse daga wannan sau ɗayan ba zasu sake yi ba.

Kafin Muhammad ya dawo daga masallaci ta yi sallah sannan ta canja musu bedsheet don ta lura ba za’a ƙara morarshi ba sai an wanke. Yana shigowa ya nufi kan gado ya kwanta ya fara bacci wanda tun shigowarshi bata ɗaga kai ta kalleshi ba balle ta mishi magana.

Tana lazimi itama ta fara jin baccin don haka ta miƙe tsaye don ta kwanta amma ganin Muhammad akan gadon yasa ta ja birki tana kallonshi. Ganin bacci yake yi yasa ta koma can gefenta ta kwanta tana mai ƙudundune jikinta guri ɗaya. Minti biyar da haka ta sake jikinta har da miƙe ƙafafu saboda baccin ya mata daɗi sai kawai ta ji Muhammad a bayanta a karo na biyu daga jiya zuwa yau.

“Ka bari….” Bata kai ga ƙarisa maganan ba ta carke dalilin birkita mata lissafi da yayi, da alama a jiya ya karanci duk wani lungu da saƙo na jikinta wanda har ya gane ina ne lagwanta.

A nan ne kuma Juwairiyya ta ƙara rantsuwa a ranta cewa daga wannan ba za’a sake yin wani ba. Sai dai kafin taran safe ya cika an sake na uku.

 9:12am.

Juwairiyya ce ta fito daga banɗaki ɗaure da towel a jikinta amma ta ɗaura hijabi a kai dalilin Muhammad da yake cikin ɗakin yana saka kaya don ya rigata tashi yayi wanka. Tana sussunne kai kamar wata munafuka ta nufi bakin wardrobe ɗinta don ɗaukan kaya ta jiyo muryar Muhammad na kwaiwayarta yana cewa,

” ‘Allah Ya sauwaƙe, God forbid bad thing’ sai kuma ga bad thing ya sakata surutai.”

Baƙin ciki, takaici, kunya da kuma dana sanine suka bugi Juwairiyya lokaci ɗaya, duk abubuwan da suka faru ba laifinta bane laifin jikinta ne domin yayi betrying ɗinta a lokacin da ta so ta riƙe ragamar emotions ɗinta. Dariya mai sauti ya fara yi ganin ta fara hawaye kanta a ƙasa.

Bai sake cewa komai ba ya fice daga ɗakin zuwa bakin ƙofar falo inda ake kwankwasawa. Tana tsaye a gurin ta jiyo muryar Salima tana sallama tayi saurin ɗaukan kayanta ta saka bayan ta amsa sallamar ta kuma ce mata tana zuwa. Doguwar riga bubu ta saka sannan ta ɗauki wani gyale ta yafa a kanta ba tare da tayi kwalliya ba, sai da ta je bakin ƙofa ta tsaya cakk domin bata san me zata cewa Salima ba in har itama ta jiyo muryarta a jiya da dare ba. Tun bayan ɗaurin auren take nuna mata cewa bata son Muhammad kuma ba zaman daɗi zata yi tare dashi ba, wanda Saliman kuma take bata baki kan cewa in dai ta koyi haƙuri to zata iya zama dashi.

Sai dai duk wannan cika bakin a cikin awa sha biyu da kawota gidan tayi tarayya da Muhammad ɗin ba sau ɗaya ba! Ba kuma sau biyu ba! Sai Sau uku!!! Kuma duk babu wanda ya mata dole ko ya mata fin ƙarfi sai dai in tana son ta mishi ƙarya, amma dai wannan karon ba zata karya alƙawari ba, sau ukun nan sun isa ba za’a ƙara ba har ta bar gidan.

Sai da ta saisaita kanta sannan ta buɗe ƙofar ɗakin ta samu Salima zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon tana riƙe da hannun Hafiz Junior wanda yake ƙoƙarin kwacewa.

“Amarsu an tashi lafiya.” Salima tayi saurin ɗagawa Juwairiyya gaisuwa tana fitowa.

“Maman Masoyi ina kwana? Ya masoyi?” Ta mayar mata da sallamar tana ɗaukan yaron ta zauna tare da ajiyeshi a kan cinyarta.

Ɓangala mata dariya yayi wanda nan take ta ga kamanninshi da Babanshi a lokacin da yake tsokanarta yau da asuba. Saurin kawar da wannan tunanin tayi ta dubi Salima da ta zuba mata ido tana kallonsu da murmushi a fuskarta tace,

“Yanzu kam sai ki daina kiranshi Masoyi saboda kar kisa wani ya yi kishi.”

Wannan furuci ya tayarwa Juwairiyya guntun rashin kunyarta wanda ya haɗu da haushin Muhammad da take ji ta ce,

“Babu mai hanani faɗin haka, Hafiz masoyina ne babu mai maye gurbinshi.” Ta ƙarisa maganar cike da jin kai.

“To ni dai babu ruwana.” Faɗin Salima tana dariya.

Da haka kuwa suka yi shiru wanda Juwairiyya bata taɓa tunanin akwai ranar da magana zai yanke tsakaninta da Salima ba. Lallai ne auren mijin ƙawa ba zai taɓa bari ka cigaba da sake jiki da ita ba, nan ma ita ba wai auren soyayya aka yi ba, aure ne da aka yi in desperate situation.

“Dama na kawo muku breakfast ne amma Baban Hafiz ya karɓi nashi ya tafi office, sannan ya bani kuɗin cefenenki amma nace mishi zan miki girkin kwana ukun. Na hutar da ke.”

“Ohh har ya tafi kenan?” Shine abun da Juwairiyya ta samu kanta da faɗi tana jin babu daɗi a ranta. Duk irin gurzanta da yayi daga jiya zuwa yau shine zai kasa yi mata sallama? Ai ko ba zata amsa ba ko kuma ba zata mishi Allah ya kiyaye ba zai faɗa mata tunda ita matarshi ce. Kwaɓan kanta tayi domin she sound emotional, yaushe ma ta fara kula da wani Muhammad balle wani lousy issue kamar sallama. Da haka ta kori wannan tunanin ta cigaba da wasa da Hafiz junor suna ɗan hira sama sama.

Yunwa ne ya fara damunta domin goma har tayi, sai dai ta kasa tashi ta ɗaura kuma ta kasa tambayar Salima wacce ta faɗa mata ta bawa Muhammad nashi, to ina nata karyawan?

Suna nan har sha ɗaya wanda hiran yawanci Salima ce take yi tana bawa Juwairiyya labarin dangin Muhammad waɗanda bata san labarinsu ba. Sai sha biyu Salima ta mata sallama ta tafi akan zata je ta ɗaura girkin rana, Juwairiyya da ta galabaita da yunwa har tana jin kamar ta yi amai ta yi saurin shiga ɗakinta ta jawo sauran kazar da Muhammad ya rage mata tana yaga tana haɗawa da Exotic ɗin da yake gefen ledan. A haka Muhammad yayi sallama ya shigo ya sameta baki dumu-dumu da maiƙon kaza sai zare idanu take yi kamar mara gaskiya.

“Kaza kam in ana cinta ba’a surutai ko?”

Yana aiki a office amma lokaci-lokaci hankalinshi na komawa kan Amaryarshi da ya raɗa mata suna ‘Masifa’ amma babu wanda ya san da hakan sai shi kaɗai. Murmushi yayi a karo na ba adadi da ya ƙara tuno da abun da ya faru jiya da dare, shi kanshi bai yi zaton hakan zai faru ba domin yayi alƙawarin kama kanshi sai dai ganinta da yayi a ƙarƙashin rufin gidanshi da kuma sunan matarshi ta sunnah sai ya ji ba zai iya haƙuri ba sai ya ɗanɗani zumarta.

 Tunawa yayi da ranar da ya fara ganinta bayan ya raka abokinshi kuma marigayi Hafiz hira gurinta. Sanin halin Hafiz na tara ƴan mata yasa ya ji baya son sabawa da ita gudun kar daga baya Hafiz ɗin ya dawo ya ce mishi sun yi faɗa sun rabu ko kuma ya ji ya daina sonta, ba karya yake yi ba hakan ya faru sau biyu zuwa uku. Sannan kuma a lokacin da Hafiz ya kira sunanshi akan ya zo su gaisa da ita baya jin daɗin jikinshi ne domin kanshi ciwo yake yi kamar zai tsage gida biyu, hakan yasa bai fito suka gaisa ba wai ashe hakan ya ɓata mata rai har ta ɗauki gaba dashi wanda shi a gurinshi ya ɗauki hakan a matsayin shirme da kuma rashin girmama na gaba.

Bayan Hafiz ya roƙeshi akan ya bincika mishi halinta ya bincika, binciken ma mai tsanani. A nan ya samu labarin rayuwarsu har da halayenta masu kyau, ganin ana yabonta yasa ya ƙarfafawa Hafiz gwiwa don ya aureta. Bayan haka ya so ya gyara tsakaninsu ganin tana da hankali sannan da gaske Hafiz ɗin zai aureta amma sai ya lura tayi nisa a fushin, hakan yasa shima ya ɗauke mata wuta domin bai ga abun fushi don ya ƙi zuwa su gaisa ranar ba, shine saurayin nata ko abokinshi Hafiz? Ko kuma shi zata aura?

Ko bayan auren ya ƙi zuwa gidan abokin nashi saboda baya son ta mishi raini don ko ɗaga mishi gaisuwa bata yi, to kenan shi take jira ya gaisheta? Idan ba zata bashi girma a matsayinshi na abokin mijinta ba ai zata bashi girma saboda ya sani ya bata shekara goma zuwa goma sha uku. He deserve some respect.

Bayan auren Hafiz kuwa ya haɗu da Salima wacce ta dace da siffar matar aurenshi, wato mai kunya, mai haƙuri sannan uwa uba submissive! A cikin wata biyu da haɗuwarshi da ita bata kauce maganarshi kuma bata mishi musu sannan ko da wasa bata taɓa mishi rashin kunya ba, hakan yasa bai jima da fara nemanta ba ya aureta gudun kar wani ya rigashi, sannan ko bayan aurensu bata canja hali ba tana mishi biyayya wanda ya so hanata yawan hulɗa da matar abokin nashi gudun kar Saliman ta koyi irin halinta amma sai ya ga tana son zumuncin da ita, wannan dalilin yasa ya barta sannan yasan idan ya hanasu zumunci Hafiz ba zai ji daɗi ba domin kuwa duk da rashin kunyar matar tashi yana sonta sannan ya lura bata yiwa mijin nata sai shi kaɗai da sauran mutanen da ta ƙullata a ranta.

 Sau da dama idan suka haɗu ba zata gaisheshi ba sai Hafiz ya mata magana, hakan yasa shima ko ta gaisheshi baya amsawa don bai ga amfanin amsa gaisuwar da ba’a yi niyyar yinta ba. Wannan dalili yasa ko a ranar da Hafiz ya ɗauketa suka je gaisheshi a asibiti ya ƙi amsawa don ya ga lokacin da Hafiz ɗin ya take ƙafarta sannan yana ganin yanda tayi kicin-kicin da fuska sannan ta ɗaga gaisuwar wanda yayi kamar bai ji ba. Wannan karon ya lura Hafiz ya fara gajiya da halinsu domin bai ƙara tursasata ta gaisheshi ba ya nemi su fita waje su sha iska sai su jira matan nasu a can. A nan ne kuma ya fallasawa abokin nashi sirrin zuciyarshi na cire rai ga rayuwa! Kamar yanda kowanne ɗan Adam yake rashin lafiya sa’i da lokaci a rayuwarshi haka shima Muhammad yana wannan rashin lafiyan wanda in ya sha magani zai ji ya warke a wuce gurin, amma a yanzu baya wuce wata ɗaya zai kwanta rashin lafiya har gadon asibiti, an yi test kala kala don duba me yake damunshi amma sai dai a ce Malaria ce da Typhoid, ƙarshe kuma likitocin suka bashi shawara akan ya rage cin maiƙo sannan ya dinga yin exercise don rage kitse. Wannan dalilin yasa ya fara tunanin ko cutar ajali ce ta fara taɓashi domin shi kaɗai yasan me yake ji a jikinshi.

“Ina so ko bayan mutuwata don Allah ka kula mini da ahalina, sannan zan roƙeka don girman Allah ka mini wani alƙawari guda ɗaya!”

“Ina jinka.” Hafiz ya amsa mishi fuskarshi cike da damuwa.

“Ina so ka mini alƙawarin bayan raina zaka auri Salima.”

Yana tunawa sai da suka kusa yin faɗa da Hafiz sannan ya amince amma bai tsaya a nan ba sai da shima Hafiz ya sa ya mishi alƙawarin zai auri matarshi Juwairiyya. Karkaɗa kanshi yayi cikin sauri ya ce,

“Halin Salima da matarka daban ne, a yanzu ma matarka bata ganin girmana ina ga kuma in baka doron ƙasa? Ni ina da tabbacin Salima zata yarda ta aureka idan ka faɗa mata ni na aikoka, sannan ni ba zan iya aurenta babu jituwa a tsakaninmu ba.”

“Ban san dalilinka na cewa in auri matarka ba amma maganar gaskiya shine if you won’t return the favour nima zan ajiye nawa.” Faɗin Hafiz cikin finality a maganarshi.

Dogon tunani Muhammad yayi domin dalilinshi na son Hafiz ya auri Salima shine she is too soft and submissive! A yau idan baya duniya ta auri wani to ragamar ɗan cikinta zai koma hannun mijin nata ne, hakan na nufin duk hukuncin da ya yanke a kan ɗan shi zata bi saboda bata iya voicing mind ɗinta, he can’t risk that kuma ya sani duk duniya Hafiz ne zai iya riƙe mishi matarshi da ɗanshi cikin amana babu cuta ko cutarwa.

“Kai me yasa kake son in aureta?” Ya tambayi Hafiz.

“Ba zan tambaye ka naka dalilin ba amma ni nawa shine Juwairiyya yarinya ce da zan iya cewa tana da zafi wanda zafin nata  yana sa tayi making rash decisions ba tare da tayi tunanin consequences ɗin ba. Yawanci kuma they backfired, amma hakan duk bai sa ta hankalta ta daina ɗaukan komai da zafi ba. Wallahi mutumiyar kirki ce, ita dai ta ƙi jinin wulaƙanci ne da cin zarafin mutum, kuma kaima in zaka mata adalci zaka faɗi hakan domin abu ka mata wanda ta ɗaukeshi a matsayin wulaƙanci. Amma ba gashi she goes along with your wife ba! Why? Saboda bata da fitina, wulaƙanci ko cin zarafin mutum. Ina tausaya mata idan ta shiga hannun mutum mai mugunta amma kai zaka iya riƙe mini ita amana. Ka kula mini da ita da duk abun da ta haifa in Allah Ya bamu rabo.”

“Na yadda zan aureta amma in har ta nuna bata so I won’t pressure her. But bana ma tunanin hakan zai faru domin ni ne zan mutu Hafiz kafin kai.”

“Ka daina cewa haka, mutuwa tana kan kowa sannan sau nawa mutumin da yake kwance a asibiti rai a hannun Allah ya warke sai wani da yake bacci a kan gadonshi ya tafi ta can? Allah Ya sa mu cika da imani kawai Muhammad.”

Bayan wannan maganar ta su ya samu Salima da maganar a ranar bai bari ya kwana ba ya umurceta da cewa in ya mutu kar ta auri kowa sai Hafiz domin shi kaɗai ne zai riƙeta amana da ɗan cikinta, tana kuka ta amince don ta faranta mishi rai kuma ya sani ba zata tsallake ba saboda ta san Hafiz mutumin kirki ne to me zai hanata amince mishi? Ya ji daɗi a ranshi domin yanzu yana da tabbacin ahalinshi zasu faɗa hannu mai kyau bayan ranshi, abun da bai sani ba shine ashe Hafiz ne zai tafi ba shi ba.

Faɗin irin tashin hankalin da ya shiga ba zai iya faɗuwa ba sannan ganin Juwairiyya da yayi yasa yaji tausayinta matuƙa a zuciyarshi domin Hafiz yana faɗa mishi irin soyayyar da take nuna mishi. Ya sani tana jin mutuwar fiye da yanda take nunawa a fuskarta idan ya shigo da abokansu gurinta don su gaisheta, sannan ganinta kaɗai kan sa ya ji shima kuka na son kwace mishi, domin daga shi har ita sun yi rashi babba a rayuwarsu.

Tun bayan rasuwar ya ɗaukarwa kanshi nauyin kula da ita domin ya sani da Hafiz ne yake da rai zai kula da iyalinshi sai inda ƙarfinshi ya ƙare, to shi me yasa ba zai yi hakan ga nashi ba? Bayan takabanta ya so ya zo mata da batun Hafiz amma kullum sai ya ji shakka ya shigeshi domin bai san yaya zata ɗauki zancen ba, bai san ko Hafiz ya faɗa mata sun yi wannan alƙawarin wa junansu ba. Sannan zai aureta amma ba don yana sonta ba sai don shima ya fara jin tausayin nata domin kamar bata da wayon zama da mutane. A yanda yake mata hidima ya kuma sauƙe duk wani jin kanshi da yake nuna mata a da, ya kamata a ce tana mishi godiya ko kuma ta nuna abun da yake yi yana taimakonta. Tana buƙatar koyon zama da mutane babu tantama.

 Bai taɓa ganinta da wani ba tun bayan rasuwar Hafiz sai ranar da ya kawo mata aika kamar kullum ya ganta tare da wani tsamurarren saurayi wanda nan take ya ji yana taya abokinshi kishi. Amma ganin yaron ya tafi tun kafin ya iso su yasa yayi tsammanin saurayin unguwa ne take tsaye dashi amma ba zai bari a hakan ba sai ya tambayeta.

“I see har kin fara tara zawarawa a ƙofar gidanku.” Ya faɗa don kawai ya ji gaskiyar lamarin.

“Idan wannan ne ya kawoka kayi saurin tafiya don baka da amsa.” Ta bashi amsa cikin tsiwa wanda in da sabo ya ci ace ya saba da hakan.

Ganin ba zai samu amsa ba yasa ya faɗa mata labarin da zata ji daɗinshi ba don komai ba sai don ya faranta mata kamar yanda shima nashi ran ya faranta, domin kuwa Salima tana haihuwa aka faɗa mishi ɗa namiji ta haifa ya raɗawa yaron sunan abokinshi Muhammad Hafiz.

“Salima ta haihu.” Ya fara da haka duk da cewa ya san ta sani.

“Ina sane.”

“Yau suna bikin suna.”

“Shima na sani.”

“Ta haifi yaro ɗa namiji.”

“Haka na ji.” Da haka ta juya da niyyar komawa cikin gida amma sai ya faɗa mata ainihin abun da yake son faɗa mata na farin cikin.

“Na saka mishi sunan abokina Muhammad Hafiz.” Da haka ya juya ya koma motarshi don dama ya gaji da tsayuwar yana buƙatar zama. Ba sai ya tsaya ya ga murnarta ba domin ya sani zata yi.

Bayan nan sai da ya ƙara wata ɗaya sannan yayi niyyar zuwa wajen Juwairiyya da maganar aure kamar yanda ya yiwa abokinshi alƙawari. Sai dai kafin nan sai da ya zanta da mahaifiyarta bai ɓoye mata komai ba yanda suka yi da Hafiz domin ba ya son ta hanata tayi tunanin za’a ci amanar Salima kamar yanda hankalinsu na mata zai basu. Bata yi jayayya ba ta amince hakan yasa ya nemi su fita waje tare da Juwairiyya don ya faɗa mata me ke tafe dashi.

Sai dai bayan ya faɗa mata ta hau dariya wanda nan da nan kuwa ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci domin bai san rashin hankalin Juwairiyyan ya kai haka ba. Ta wani gurin kuwa kunya ce ta kamashi don gabaɗaya sai ya ji ya tsargu, shin akwai wani aibu ne a jikinshi ko a halinshi da ya cancanci wulaƙanci irin haka?

“Wai idan kin amince… Mwhahahaha….bana son dogon nema…. a ɗaura auren ki tare….Mwhahahaha” Ta ƙara kwashewa da dariya wannan karon har da riƙe ciki.

“Me amsarki?” Ya tambayeta yana jin kamar ya rakwashi tsakar kanta ko zata yi hankali.

Ya lura da kyar ta saisaita kanta sannan tace,

“Maza baku da ta ido wallahi. Yanzu ni da nake ƙawar matarka kuma matar abokinka….”

“Late, you should add late.” Yayi saurin katseta domin ba zai taɓa neman matar abokinshi ba idan ya sake matarshi, amma ita fa? Mijinta abokin nashi ya rasu.

Ai kuwa sai ya lura annurin fuskarta ya ɗauke dalilin tuna mata da rasuwar mijinta.

“Ba sai ka tuna mini cewa baya doron ƙasa ba, tsayawarka a nan tare da ni kaɗai ya isa ya tuna mini cewa mijina ya mutu. Kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan da wannan zancen domin na farko, ni ba butulu ba ce, ina zumunci da matarka ba zan taɓa cin amanarta ba. Na biyu kuma har abada ba zan taɓa auren ɗaya daga cikin abokan Hafiz ba, domin hakan zai zama tamkar cin fuska ne a gareshi, ba zan wulaƙantashi ba. Sannan na uku, Muhammad, wallahi ko na rasa mijin aure ne ba zan aureka ba. Da mutum irina da mutum irinka ba zasu taɓa zama a ƙarƙashin rufi ɗaya ba, in kuma aka kuskura aka haɗasu to sai dai gobara. You hate me, nima kuma na mayar maka da daidai naka. Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shine kar ka kuskura ka nunawa Salima cewa mun yi wannan maganan saboda bana son alaƙar mu ya samu matsala.” Ta gama surutunta wanda bai ɗaukesu a maganar hankali ba.

“What if shi ya nemi hakan?” Ya mata tambaya mai ɗauke da amsa duk don ta gane ba yin kanshi bane. Ko dai Hafiz bai faɗa mata alƙawarin da suka yiwa juna bane?

“Shi waye ya nemi me?” Ta mayar mishi da tambaya don kamar she is confused.

“What if Late mijin naki ne yace in nemi aurenki idan ya bar doron ƙasa?” Ya fayyace mata.

“Stop saying ‘Late’ i know he was late.” Ta faɗa a harzuƙe da alama ranta yana ɓaci idan aka mata tuni da mutuwar Hafiz.

“Hmm.” Ya ji ya fara gajiya da halinta

“And you are lying, kai ne ka sakashi ya maka alƙawarin idan ka mutu ya auri matarka Salima kuma ya faɗa mini tun a ranar saboda tsakanina dashi akwai kyakkyawar alaƙa bama ɓoyewa juna komai.”

“To bai faɗa miki duka ba, he asked me to marry you too.” Ya faɗa mata sauran labarin da Hafiz ya boƴe mata.

“Ƙarya ne.” Dama ya sani ba zata yarda da wuri ba.

“Ba zan taɓa yiwa mai rai ƙarya ba balle mamaci, ƙarya bata cikin halayena.” Ya faɗa a hankali kamar ba shi ake yiwa ihu a kansa ba.

Ganin ta yi shiru tana cika tana batsewa yasa ya kunna motarshi kana ya ja ƙofar ya rufe ya dubeta ya ce,

“Me kika ce? Zaki aureni?”

“Ko sunana baka taɓa ambato a bakinka ba, ko sunana baka taɓa sauraron harshenka ya furta ba, balle a kai ga so har aure.” Ta canja akalan maganar nasu wanda yasa ya ƙara yarda da cewa bata da wayo, me kuma ya kawo maganar kiran suna?

“Ba wannan na tambayeki ba.”

“Ba zan taɓa aurenka ba ko mazan duniya sun ƙare.” Ta bashi amsa a numfashi ɗaya tana hararanshi.

“Shine final say ɗinki ko zaki yi tunani?”

A lokacin sai ya lura ranta ya ƙara ɓaci duk ba bai ga abun da ya tunzuratan ba. Bakinta har rawa yake yi tsabar ɓacin rai ta ce.

“Har abada.”

“Dama mun yi dashi akan sai kin ƙi amincewa kafin in barki. Allah Ya gani na cika alƙawari, ke kuma kar ki ce ban taya ba. Allah Ya bada sa’an neman mijin aure.” Ya faɗa yana jin daɗi na ziyartarshi domin kuwa dama bai so ta amince ba, kuma a yanda ya san halayenta da kyar ne dama ta yarda, amma duk da haka yana waswasi. Gudun kar ma ta canja ra’ayinta yasa ya kunna motarshi ya tafi, ai dai ya cika alƙawari.

Daga ranar bai sake waiwayarta ba, sai dai kuma bai fasa aiko mata shopping ɗin da ya ɗaukarwa kanshi nauyin kai mata ba kowanne month.

Ranar kwatsam aka kirashi aka faɗa mishi wai zata ɗaura sure nan da wasu kwanaki kaɗan! Wannan magana tasa ya tashi shi da kanshi ya je ya binciki halin mutumin da zata auran, cikin ikon Allah kuwa ya samu mutumin kirki ne bashi da aibu, hakan yasa hankalinshi ya kwanta don ba zai bari amanar Hafiz ya wulaƙanta ba ko kuma tayi zaɓen tumu na dare ba.

Ko da ya kai mata gudumawa sai ya lura ranar ta kasa mishi tsiwa sannan maganarta na cewa ya zo mata gori ya sakashi dariya har sai da yayi mamakin kanshi, sai dai ya alaƙanta hakan ne da cewa farin cikin da yake ciki ne na cewa nauyinta zai sauƙa a kanshi.

Duk da ta ƙi karɓan gudumar da ya bata bai bari a hakan ba ya aika Salima ta kai mata a lokacin biki, a yanzu baya hana Salima zuwa gurinta duk lokacin da ta tambaya domin ya lura ba zata taɓa canja halayenta don ta ga Juwairiyya tana yi ba. Amma ta wani gurin yana son Salima ta iya tsayawa kanta don a wani gurin sanyin rai ba zai kwace ka ba, haka a wani gurin ma zafin rai ba zai kwace ka ba, mutum dai ya iya duka sannan ya gane wani yanayi ne ya dace yayi zafi sannan a wani yanayi ne zai yi sanyi. Duk wanda yayi mastering wannan zaman duniya da mutanen cikinta ba zai bashi wahala ba, don haka yana son Salima ta koyo wani halin Juwairiyyan Itama Juwairiyyan yana son ta koyi wasu halayen Salima don su yi balancing.

Bayan aurenta yana tunaninta sa’i da lokaci yana mata fatan alkhairi yana kuma zama curious ko dai shima mijin nata tana can tana mishi rasar kunya? Sai dai bai taɓa jin magana ta fito ba har sai da suka yi wata bakwai kwatsam ya ji wai an saketa! Wannan labari ya gigitashi ya kuma ɓata mishi rai tamkar ƙanwarshi aka yiwa haka? Me ta yiwa mijin da har zai saketa a cikin wata bakwai kacal da aurensu? Shima kanshi mai kawo rahoton bai san abun da ya faru ba amma ya faɗa mishi labaran da mutanen unguwa suke faɗa a kai wanda ko ɗaya bai yarda ba saboda ya san Juwairiyya ya san me zata aikata da wanda ba zata iya aikatawa ba ciki kuwa har da sata da kuma bin ɗan mijinta.

 Dama an bar maganar ne a cewa mijin da ta auran ba ya gamsar da ita saboda a wasu lokuta da Hafiz yake da rai yana jin Hafiz ɗin yana tsokanarta a waya akan cewa tayi missing ɗinshi ya dawo ya ƙara bata da makamantansu, ire-iren waɗannan maganganu yasa ya gane cewa abokin nashi da matarshi kamar zomaye suke, basa gajiya da auratayya saɓanin shi da Salima ta take gudunshi a shimfiɗa, idan ya nemeta sau ɗaya to fa ba zata iya na biyu ba. Duk irin biyayya da bin maganarshi da take yi a nan kam ta sha kwana kuma yayi ƙoƙarin koya mata amma ta ƙi koya har ya haƙura ya barta don ba zai mata dole ko fin ƙarfi ba, sannan dama ya sani mutum tara yake bai cika goma ba, kenan duk biyayya da sanyin halin Salima ita kuma buƙatarshi ce ba zata iya biya mishi ba.

Bayan mutuwar auren yayi bincike da kanshi domin har unguwarsu yake zuwa yana jin ra’ayoyin mutane, a wannan binciken ne ya gane gaskiyar magana da wani mutumi yace ya taɓa haɗuwa da mijin nata a gurin wani mutum mai sayar da shayi, ba shayi na madara da lipton ba, a’a shayi ne na ƙarawa maza ƙarfin sha’awa da daɗewa a kan gado, a nan ne kuma yaji cewa shi mijin nata yana cewa a mishi haɗin da ko jariri aka bawa zai iya aiki. A yanda ya lura shi kanshi mutumin bai gane abun da mijin nata yake nufi ba domin sun ɗaukeshi a matsayin raha har ya faɗa mishi cewa dariya kawai suka yi aka wuce gurin. Amma shi Muhammad ya sani Juwairiyya ta auri jaririn ne a cikin naɗi ba tare da ta sani ba, sannan wannan auren nasu ba zai je ko’ina ba domin kuwa ba zata iya zama da mutum mara ƙarfi kamar marigayi Hafiz ba.

Duk mutanen da suke zuwa gurinta yana sane da su amma ya fi jin haushin tsayawarta da wannan ɗan daudun wato Salisu. Labarin da aka bashi a kanshi yasa ya ji ba zai bari ta aureshi ba tunda ya lura ta kori duk zawarawan nata sai shi kaɗai ne yake zuwa da wannan yaron mai suna Hussaini da ko a lissafi ba ya son sakashi don yasan yana da matuƙar wahala Juwairiyya ta aureshi, baƙar nacinshi ne yasa har lokacin bai daina neman soyayyarta ba.

Da labari ya riskeshi cewa Juwairiyya ta rage walwala sannan tayi sanyi sosai yasa ya gane akwai matsala domin kuwa an faɗa mishi Salisu baya barin victims ɗinshi haka banza sai ya musu asiri wanda asiri gaskiya ce tunda ta kama Manzon Allah ma SAW.

Zuwanshi ya tarar ta shiga cikin motar ɗan iskan sannan ya ji wai yana umurtarta da ta taɓa hannunshi! Ya so ya buɗe motar ya jawo kwalar rigar mutumin ya kwaɗa mishi maruka ko zai shiga taitayinshi. Mamakinshi bai tsaya a nan ba sai gani da yayi ta ɗaga hannun nata zata ɗaura akan na ɗan iskan ya kwala kiran sunanta a karon farko a rayuwarsa.

Cece kucen da ya biyo baya ya gane sam ba’a hayyacinta take ba don ya san wacece Juwairiyya! Hakan yasa ya bazama gurin kakanshi malami ya karɓo mata maganin karya asiri na addu’o’i da ayoyin Allah tsarkaka. Cikin dabara ya aika mata kamar Salima ce ta mata aikan sannan ita kuma Salima yasa ta kashe wayarta don kar ta kirata tace ba ita bace. Da yardar Allah kuwa asirin ya karye! Ko da aka faɗa mishi Salisu ya zo ƙofar gidan nasu shima yayi saurin zuwa amma bai tsaya kusa da shi ba yayi parking a can gefe. Sai da ya ga ta fito daga gida sannan ya tako da ƙafa ya saurari masifar da take yiwa ɗan daudun. Bai taɓa tsammanin akwai ranar da zai yi enjoying masifar Juwairiyya ba amma a ranar har wani tinkaho yake yi yana feeling proud of her.

“Yauwa, ga Juwairiyyan da na sani.” Ya faɗa yana takowa a hankali yana murmushin cin nasara da jindaɗin ganin mamaki da kuma tsoron da ke fuskar ɗan daudun.

Ganin ta juyo shima zata masifeshi yasa ya ɗaga hannunshi sama alamar surrender ya ce,

“Na zo tambayar meyasa baki zo kin duba Muhammad Hafiz bane.” Ya sani ɗanshi mai sunan Hafiz shine weak point ɗinta, tana son yaron don haka ya kira mata shi don kar shima a masifeshi. Ai kuwa nan da nan ta sassauto ɗin ta matso kusa dashi tana cewa,

“Ya jikin nashi?”

Da haka suka kori Salisu mai kwalli wanda ya tabbatar bai daddara ba zai sake dawowa da wani shirin nashi.

A nan ya faɗa mata gaskiyar abun da ya faru don ta yawaita yin azkhar domin kariya ga irin waɗannan mutanen. Ya kuma bata shawarar tayi aure ba don ta zaɓeshi ba sai don ta samu ta huta shima ya huta domin bibiyar rayuwarta da yake yana cinye mishi lokaci sannan yana wahalar da shi da aljihunshi. A bazata ya jiyo muryarta tana cewa,

“Na yarda zan aureka Muhammad. Ka aiko sadakinka gobe a ɗaura mana aure.” Ta faɗa da murmushi a fuskarta wanda bai san dalilinshi ba, amma abun da ya sani shine ba murmushin ƙauna bane, murmushi ne na zaka ji a jikinka.

“No!” Ya furta da sauri yana ɓata fuskarshi da ya hasko irin draman da zasu dinga yi kullum saboda banbancin ra’ayinsu.

“Yes.” Ta ƙara faɗaɗa murmushinta wanda yanzu ya gane na mugunta ne.

Juyawa yayi ya nufi motarshi yana karkaɗa kanshi don ya san zamanshi da ita ba zai taɓa yin daɗi ba amma kuma ta bishi tana cewa,

“Ka turo gobe a ɗaura auren.”

“Ke ki barni fa.” Ya samu kanshi da faɗi wanda sai daga baya ya ji kamar mai tsoro.

“But you promised him cewa zaka aureni idan na yarda. You promised Muhammad!” Wannan magana yasa ya carke daga tafiyan da yake yi kana ya juyo ya dubeta bata bar murmushin muguntar ba. Ya yiwa abokinshi alƙawari don haka sai ya cika. Bashi da tabbacin yana sonta ko baya sonta amma dai abun da ya sani shine; yana jin tausayinta matuƙa wanda ba zai so ya ga ta wulaƙanta ba.

“You will be the death of me. Ki faɗa musu gobe zan taho da magabatana a ɗaura auren da safe.”

“To maigida.” Ta faɗa in a mocking voice sannan ta juya ta koma gida ba tare da ta mishi sallama ba, dama bai yi ƙarya ba da yace hankalinta kaɗan ne sannan za’a sha drama a aurensu.

A ranar ya kira waliyyanshi yace ya samu bazawara zai aura gobe, bayan sun tattauna kan dalilin gaggawan auren washegari aka ɗaura mishi aure da Juwairiyya wanda tsabar mamakin wannan al’amarin sai da ya mintsini kanshi don ya ga ko mafarki yake yi ko a’a. Wani abun mamaki kuma shine sai ya samu kanshi da jin farin ciki, sai yake jin kamar an buɗe wani hanya a jikin huhunshi da zai yi numfashi da kyau. He felt light kamar zai iya firewa idan ya saka kanshi.

Sai dai kiran da ta mishi a waya bayan auren bata gaisheshi ba kawai tace tana son ganinshi yasa yaji ya kamata ya fara saitata don ba zai ɗauki raininta ba alhali tana ƙarƙashinshi. Amma sai ya fara zolayarta don she sound desperate kamar mai buƙatarshi.

“Ba zaki iya jira har ki tare ba kenan?”

Kamar bata gane maganar tashi da wuri ba sai da tayi tunani, sai kuma ya ji ta fara magana a hasale.

“Dalla ni ba abun da nake nufi ba kenan. Allah Ya sauwaƙe God forbid bad thing. Magana nake son mu yi.”

“Idan kin koyi magana da miji ki kirani sai mu yi maganar a natse.” Da haka ya kashe wayarshi don ya lura kamar abun nata ƙara gaba yake yi. Da yaso ya bar laifinta na farkon ya wuce amma sai ta ƙara da wani wanda ya fi mishi zafi. Baya son rashin ɗa’a.

Ya san zata nemeshi tunda ita take da buƙatar ganinshi ba shi ba, sannan idan ma bata nemeshi ba ita ta sani. Yana zaune ta ƙara kiranshi a karo na biyu wannan karon ta sassauto da muryarta alamar ta fara kama hanya.

“Don Allah magana nake son yi da kai in zaka iya zuwa.”

“Na ji.” Kawai ya faɗa ya ƙara kashe wayarshi don yanzun ma bata gaisheshi ba.

Bayan wani minti ashirin ya iso ƙofar gidan nasu ya kira wayarta, tana ɗauka ya faɗa mata yana waje sannan ya kashe wayarshi. Tana fitowa ta fara mishi magana babu sallama balle gaisuwa.

“Ina ta neman Salima amma har yau wayarta a kashe. Lafiyanta kam?”

“Shine maganar?” Ya tambayeta don bai yi tsammanin abun da yasa ta kirashi ba kenan.

“Akwai wasu amma wannan ne farko.”

“Wayarta ce ta fashe.” Ya faɗa mata kaɗan daga cikin gaskiyan.

“Don Allah yaya ta ɗauki zancen auren nan? Ta yi fushi ko?” Ta tambayeshi cikin zullumi kamar ma jikinta na rawa.

“Ba zan iya faɗa miki ba amma dama ta san hakan zai iya faruwa.” Saboda tun ranar da suka yiwa juna alƙawari da Hafiz ya sanar da ita bai kuma ɓoye mata cewa shima zai auri Juwairiyya ba idan Hafiz ya mutu. Kuma tana sane da cewa yana yi mata aika kowanne month sannan ya tambayeta ta aureshi kwanaki ta ƙi.

“Ban gane ba.” Ta faɗa cikin ruɗu.

“Sai wanne?” Ya kawar da zancen don ba zai iya faɗa mata cewa Salima da ta ɗauka a matsayin ƙawa ta suma ba da ya labarta mata labarin aurenshi.

“Ba zaka fahimtar da ni ba kenan?”

“Eh.”

“Sai kuma batun tarewa ta ina so sai bayan na gama exams kafin nan mutanen da suke cikin gidana sun fita.”

“Me kike nufi kenan?” Ya tambayeta don yana son ya fahimceta da kyau kar yayi gaggawan magana. Amma in dai abun da yake zato ne lallai zai nuna mata bata da wayo, ba zai bi mace gidanta ba.

“A can zan zauna.” Ta bashi amsa kamar mai jin tsoron amsar da zai fito daga bakinshi. Ai kuwa dole ta ji tsoro don ba zai amince ba.

“Kina nufin ba zaki zauna a gidana ba kenan ni zan dinga binki gidanki?” Ya ƙara tambayarta for clarification.

“Eh.” Ta amsa mishi.

A nan ne ya nuna mata ko da wasa kar da ƙara ɗauko zancen don ba zai amince ba, shi wannan mai lagwanin da ta aura bata ce zata tare a gidanta ba sai shi? Wato ta raina arziƙinshi? Rai dai babu daɗi suka rabu ko kwana ɗaya auren bai yi ba, dama abun da yake gudu kenan.

 Batun karatunta zai barta taci gaba sannan zai bari ta gama exams kafin ta tare tunda shima yana buƙatar yin gyara a gidan nashi. Sai dai ya lura duk ranar da ya zo sai ta ɓata mishi rai wanda da gangan take yi don kawai ya hanata zama a gidanta. Akwai ranar da tace ya bata motarshi a dinga kaita school wai bata son napep! Yayi dariya ya kama hanyarshi ya tafi bai mata sallama ba.

Ya ɗauka Salima zata ɗauki gaba da Juwairiyya amma sai ya ga saɓanin hakan amma yana jiyewa Juwairiyya don zata sha wahala wajen kishi da Salima, tana da wayo da kissa shi kanshi ya sani amma ba zai faɗawa Juwairiyyan ba don zata yi zaton so yake ya raba kansu.

A haka ta tare amma yana shiga ɗakinta ya sameta tana kuka. Abun ya so ya bashi dariya amma ya danne don kar ta fusata, tana bazawara aurenta na ukun ne zata zauna tana kuka? Kukan me take yi? Yace su yi sallah ta ƙi, ta zo su ci kazar amarcin ma ta ƙi. Hakan yasa ya kwanta a gado ya fara danna wayarshi don baya son yayi bacci bata tashi a gurin ba. Shima da zata san yanda zuciyarshi take tsinkewa a lokacin da zai shigo ɗakinta da ta mishi dariya, amma ba zai taɓa faɗa mata ba.

Tana zaune ya lura tana gyangaɗi lokaci lokaci kuwa sai ya ga bakinta yana motsi wanda dimple ɗinta sai sun fito idan sun yi hakan, dimple ɗin yana burgeshi amma baya gani idan tana masifa.

A lokacin ya ji yana sha’awar kaɗaituwa da ita tunda ita halalinshi ce, ya so ya haƙura sai ta yi kamar sati kafin ya bijiro mata da buƙatarshi amma sai ya ji ba zai iya ba. A yanzu ma baya son ta butsare ne da ɗaukanta zai yi kawai ya ajiyeta akan gado, zai mata a hankali yanda itama zata yi participating ba wai ya mata da ƙarfi ba tunda itama Salima ba ya mata da ƙarfi duk da hanashi kanta da take yi.

“Idan kin gama kukan ki zo ina buƙatar matata.” Ya faɗa mata don ta gane lcewa ba zai barta ba.

A nan ne kuma bakinta ya ƙara buɗuwa har take faɗa mishi wai ya tsaneta, shi kuma bai tsaneta ba. Kuma ko ya tsaneta babu ruwanshi zai nemi biyan buƙatarshi tunda matarshi ce.

Yana ji ta shiga banɗaki ta canja kayan da anjima zai ciresu ta zo ta kwanta a ƙasa. Bai mata magana ba don ba zata iya kwana a gurin ba dalilin tiles ɗin ɗakin suna ɗaukar sanyi gashi bargon nata bashi da kauri sosai. Yana danne dannenshi wanda wani abun ma bai san me yake dannawa ba ya ga ta miƙe ta kwanta akan gadon, ai ya san hakan zai faru. Sai da ya bari ta saki jikinta sannan ya kwanto a bayanta wanda hakan da yayi kaɗai sai da numfashinshi ya kusa ɗaukewa, a lokacin ne ya gane lallai yana cikin tsananin buƙata. A hankali ya fara bibiyar duk wata gaɓa ta jikin mace da yake kashe musu jiki aka yi sa’a kuwa itama a hannu take. A ƙarshe da ta bada kai ba ƙaramin farinciki yayi ba domin har kwalla sai da ya taru a idanunshi wanda yayi addu’an Allah Ya sa bata gani ba.

Ta kashe mishi ƙishinshi sannan kuma ta ƙara kunna mishi wani ƙishin amma na jikinta, don haka bayan sallah asuba ya gwada nemanta ta ƙara amince mishi ya kuma ƙarawa da safe. Jin kanshi yake yi kamar jaririn da aka haifa yau domin rashin damuwa, ta wanke mishi zuciyarshi don ta ɗanɗana mishi zumarta mai ɗaɗin lasa, ƙarshe cewa yayi me yasa tun bayan aurensu bai nace mata ta tare ba?

Irin amsar da take bashi a lokacin da suke auratayya shi ya ƙara mishi kwarin gwiwar faranta mata wanda yasa ta kasa rufe bakinta sai da shine ya saka  hannu ya rufe mata, baya son Salima ta jiyosu domin baya son ranta ya ɓaci ko tayi tunanin da gayya ake mata hakan. Tsokanarta yayi tayi yana jin daɗin reaction ɗinta don yasan jikinta ne ya bada ita ba zuciyarta ba, koma menene ba da ƙarfi ya mata ba kuma itama ta samu sassauci.

 Yana shirin Office ya ji Salima tana kwankwasawa ya je ya buɗe mata ta shigo da basket ɗin abinci da kuma Hafiz junior. Karɓan abun hannunta yayi ya ajiye a gefe sannan ya ƙarbi yaronshi yana mishi wasa cikin farin ciki.

“Yau kayi lattin Offices.” Salima ta faɗa mishi amma akwai alamar tambaya a ciki.

“Eh.” Ya bata amsa don bata buƙatar sanin dalili.

Da haka ya juya da niyyar komawa ɗakin Juwairiyya amma ta tsayar dashi ta hanyar cewa,

“Ina son in ka yarda in karɓawa ƙanwar tawa girkin kwana ukun nata, ina son ta huta sai ku ƙara sabawa.”

Bai kawo komai a ranshi ba amma yace,

“Idan ta amince sai ki yi.” Da haka ya bata kuɗin cefenen ya tafi domin yasan Juwairiyya tana canja kaya kar ya shiga ya kasa controlling kanshi.

Ya tafi office ɗin ma amma hankalinshi na kanta, yana kuma buƙatarta. Duba agogo yayi a karo na ba adadi amma sai ya ga lokacin baya tafiya domin sha biyu saura wasu mintuna kuma basa tashi sai biyu. Hakan yasa ya ajiye aikin yana cewa yau kam su mishi uzuri zai koma gida ya ƙara lasan zuma sai dai bai yi tsammanin zai je ya samu mai zumar tana figar kazar amarcinta da tace Allah ya kasheta ba zata ci ba.

“Wato ita kaza kam in ana cinta ba’a surutai ko?” Ya tsokaneta domin nishaɗin da yake ji in yayi hakan.

Mum Fateey 👌

“Kaza kam in ana cinta ba’a surutai ko?” Muhammad ya faɗa cikin tsokana.

“Don Allah ka barni.” Shine abun da Juwairiyya ta faɗa tana mai juya mishi baya don kar ya cigaba da kallonta amma ta ji kunya kam ba kaɗan ba.

Bai sake cewa komai ba ya shige toilet yayi alwala ya fita zuwa masallaci, kafin ya dawo ma har ta gama cin kazarta ta kai ƙasusuwan kitchen, a nan ne ta ga ɗan ƙaramin kitchen ɗin nata Wanda na gidan Hafiz da Daddy ya kai wannan uku ko huɗu.

Tana banɗaki tana alwala ya dawo ya kwanta akan gado yana danna wayarshi, fitowanta ta ganshi ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana shan iskan fankan da ke saman ɗakin. Hararanshi tayi a zuciyarta kuma tana mitan zai lotsa mata gado da nauyinshi.

Bayan ta idar da sallah ta zauna lazimi don a takure take tana son sakewa ita ɗaya amma ta lura Muhammad kamar daɗin gadon nata yake ji. Ta rasa gane me ya dawo dashi gida yanzu saboda Salima tace sai ƙarfe biyu yake dawowa. Har ta gama lazimin bata tashi a gurin ba don ta lura kamar mutumin nata neman wani abu yake yi kuma ba zata bayar ba.

“Har yanzu baki gama sallan bane?” Ta jiyo muryarshi a dodon kunnenta.

“Wani abu ne?” Ta mayar mishi da tambaya.

“Eh, ki zo.”

“In maka me?”

“In kin zo zaki gani.”

“Ni fa bana son baƙar jaraba.” Ta faɗa ƙasa-ƙasa amma ya ji sarai.

Nan da nan annurin da yake fuskarshi ta ɗauke, da haka kuma ya miƙe ya fita daga ɗakin, ƙarshe ta ji ya fitar da motarshi daga gidan gabaɗaya. Nan da nan kuma sai ta ji kamar bata kyauta ba, bai kamata ta furta mishi hakan ba tunda itama a jiyan ta nuna tana son hakan. Minti goma da fitanshi ta ɗauki wayarta ta mishi text kamar haka…

‘Ina jin zafin gurin ne.”

Sai da ta tura ta ji dama bata tura ba, kar ya ɗauka don zafin ne yasa ta ƙi yarda dashi, a’a ita an daina yi ne gabaɗaya. Sannan maganar gaskiya kam tana jin jiki domin ta kai shekara uku rabonta da ɗa namiji, sannan da ta haɗu da Muhammad sai ya gurjeta da kyau wanda hakan yasa ta fara waswasi akan maganar Salima da take faɗa mata wai bashi da ƙarfin sha’awa. To ya aka yi daga zuwanta ko 12 hours bata cika ba ya nemeta sau huɗu? Ko dai don ita amarya ce? Amma a yanda ya nuna mata bajintarshin nan sai ta rasa me zata ɗauka, maganar Salima ko kuma ita abun da ta gani da idanunta ta kuma ji a jikinta?

Da haka ta fara kiran mamanta da kuma ƴan’uwanta da suka kawota tana musu bangajiya, wasu suna haɗawa da tsokana tana basarwa. Tana waya da ƙanwarta Sumayya mai cikin wata bakwai (itama bata samu haihuwar da wuri ba) ta ji shigowar Muhammad amma yana zuwa ya ajiye mata abu a ƙasan sallayar tata ya fita, ibuprofen ne a cikin baƙar leda tare da ruwan gora, sai da ta kashe wayar sannan ta ga text ya shigo mata tun ɗazu.

“Allah Ya baki lafiya.”

Kunya ne ya kamata da ɗan guntun takaici wai yau ita ce take sharing irin wannan Texts ɗin tsakaninta da Muhammad? Sallamar Salima ta jiyo a falo ta amsa kana ta sha maganin cikin sauri sannan ta fita da fara’a a fuskarta tana mata sannu. Abinci ta kawo mata ta ajiye a kan center table tana cewa,

“Don Allah kiyi haƙuri ashe ɗazu na manta ban ɗauko miki abincinki ba muka zauna hira, kinsan hiranmu kullum baya ƙarewa sai dai lokaci ya mana kaɗan.”

“Laa babu komai ai da ina jin yunwar da na miki magana.” Ta yi ƙarya tana murmusawa.

“Ai na faɗa nace ke ba baƙuwar gidan bace, ɗazu wasu ƙannen Baban Hafiz suka zo gaisheku sai nake cewa maigidan yana ciki suka tafi akan sai daga baya zasu dawo ganin ɗakin amarya.” Faɗin Salima tana zama a kan kujera.

Juwairiyya bata ji daɗin hakan ba domin sai take ganin kamar zasu ɗauka wani abun ita da Muhammad ɗin suke yi a ɗaki alhali kwanciyarshi yayi duk da cewa ma abun yake nema bai samu ba.

“Ai da baki hanasu shigowa ba, sallah nayi na jima akan sallayar ina lazimi.” Ta faɗi iyakacin gaskiyarta amma sai ta ga kamar Salima na mata kallon rainin wayo, amma lokaci ɗaya kuma ta daina ta cigaba da murmushi.

“Ayya ai ban sani ba. Ai ko yaya ne ma amarya tana buƙatar hutu, ni da za’a bi ta nawa wallahi in an yi aure ya kamata a bar mata da mijin su huta na sati kafin ƴan ganin ɗakin amarya su fara zuwa. Amma yaushe gajiyar amarci ta bar mutum da har zai fara entertaining baƙi?”

“Nima wallahi ina faɗan hakan saboda wasu mutanen gulma ce take kawosu, in ba gulma ba jiya an gama biki da ku kowa ya gaji wai kuma gobe ku zo ganin ɗaki? Ɗakin guduwa zai yi? Sai ku bari sai an kwana biyu kafin nan kowa ya huta.” Ta faɗi view ɗinta wanda ta jima dama tana faɗan hakan.

“Ai sai a hankali, mutanen ne sun fi son zuwa da wuri don in suka ce sai daga baya to fa zasu yi ta saka rana suna ɗagawa. Ina maigidan ne? Ɗazu naji ya fita ya dawo ya kuma ƙara fita. Ya kamata ya ci abinci don yana da ulcer, ko zaki kirashi ya dawo gida.”

“Ke da kika san yana da ulcer sai ki kirashi, ai shi ba yaro bane ya san yunwar cikinshi.” Juwairiyya ta bata amsa domin ita bata ma son ya dawo ya ƙara takurata.

“Ayya dai, yanzu wallahi in baki kirashi ba sai ranshi ya ɓaci yace ba’a damu da shi ba.”

“To dama nace na damu dashi ne? Allah Ya gani auren nan an yi shi ne kawai amma daga ni har shi bama so, to yaushe kuma zan tuna da yunwar cikinshi? In shi ba zai tuna ba nima ba zan tuna ba, bani da wannan lokacin.”

“To dai kar ki ci sai ya dawo ku ci tare don baya son a ɗibi abinci a bar mishi saura.”

“Ohh Maman Masoyi. Ni ki daina ma faɗa mini irin waɗannan abubuwan don ban damu da abun da bawan Allahn nan yake so da wanda baya so ba. Idan ya ga ba zai iya ba ya san inda ya ɗaukoni. Haƙurin da kike yi dashi ni ba zan iya ba shiyasa tun farko zan fara nuna mishi.”

“To shikenan tunda haka kika ce, kar watarana ki ce ai ni ce ban faɗa miki ba, kuma dama ke ba zai miki wannan faɗan da yake mini ba don kamar yana shakkarki.”

“Mu bar zancen kawai.”

“Bari in je in kirashi a waya ya zo ku ci abincin.” Faɗin Salima tana tashi tsaye zata koma ɗakinta.

Har Juwairiyya zata mata musu sai ta tuna cewa ita Saliman tana son mijinta ba kamar ita ba da tolerating ɗinshi ma bata iyawa.

Salima tana fita itama Juwairiyya ta bi bayanta zuwa kitchen ɗinta ta ɗauko plate da spoon ta dawo falon ta fara ɗiban abincin domin kuwa har lokacin yunwa take ji duk da cewa ta ci sauran kazar jiya. Farar shinkafa ce da aka watsawa karas sai kuma miya da ta ji namomi da kuma yankakken latas da aka mishi ado da tumatur da albasa. Tana ɗiba yawunta sai tsinkewa yake yi don haka tana gamawa ta shige da plate ɗin ɗaki ta fara cin abincin wannan karon ta sakawa ɗakin makulli gudun kar Muhammad ya ƙara dawowa ya sameta irin na ɗazu.

Cikin ikon Allah har ta gama ci bai shigo ba, a nan kuma aka fara kiraye-kirayen sallah la’asar ta shige toilet don yin alwala. Tana fitowa ta sameshi a tsakar ɗakin yana tsaye fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce,

“Ke kika ɗebi abinci?”

“To dama waye zai ɗiba in ba ni ba?” Ta mayar mishi da tambaya mai ɗauke da amsa.

“Na san baki sani ba, amma bana son a ɗibi abinci a bar mini saura. Next time ki saka mini nawa a wani kulan daban.”

“Me yasa?” Ta tambayeshi duk da cewa ba wai ta damu bane, a’a curiosity ne kawai.

Shiru yayi yana kallonta na wasu seconds sannan ya numfasa ya fara magana.

“Akwai wani lokaci da bana tare da mahaifiyata idan za’a bani abinci sai an ci an rage duk da cewa nima ɗan gida ne. So wannan dalili yasa duk lokacin da aka mini hakan sai in ga kamar wulaƙanci ne da kasƙantarwa, to gaskiya bana son hakan. Why are you laughing?” Ya tambayi Juwairiyya wacce take dariyar mugunta tun lokacin da ya fara magana.

“Mallam kace mini kawai kana da PTSD (post traumatic stress disorder). In ba haka ba menene don an ɗibi abinci an bar maka saura sai kake ganinshi kamar wulaƙanci? Hannu aka saka aka jagwalgwala ko yawu aka tofa a ciki.”

“Ki daina faɗin haka.” Ya faɗa yana runtse idanunshi da ƙarfi.

Juwairiyya tsayawa ta yi tana kallonshi kamar wata wawuya, to ko dai an taɓa tsirta mishi yawun ne a cikin abincinshi?

“An taɓa saka maka yawun ne?” Ta sake tambaya wannan karon a fili don sai ta ji duk ta ƙagu ta san me ya faru.

“Kawai bana so, kar ki sake irin haka. In kuma kin yi kawai ki cinye ko ki kyautar kar ki ajiye mini.”

“To ni kuma da jiya ka cinye kaza ka bar mini saura fa? Ni ba wulaƙantani ka yi ba?”

“Cinya ɗaya da ƙirji ɗaya kawai na ci ban cinye duka ba, sannan nace ki zo mu ci kika ƙi ci! Amma da na dawo sai na samu kin kafu a kanta kina yagarta.”

“Ka tafi masallaci ana kiran sallah.” Kawai tace dashi kana ta juya ta ɗauki sallayarta ta shimfiɗa.

Shima yana ganin hakan ya shige banɗaki ya yi alwala ya fita. Kafin ya dawo Juwairiyya ta share ɗakinta da falonta tass ta saka turaren wuta a burner, nan da nan guri ya ɗauki ƙamshi duk dama cewa na jiya bai gama fita ba. Da haka kuma ta fita zuwa side ɗin Salima don tayata aikin abinci in ta fara yi.

Sallama ta fara yi sannan ta kwankwasa ƙofar falon aka amsa mata ta shiga, a falo ta samu Salima na bawa ƴar aikinta mai suna Nanayo aika da zata siyo mata a shago.

“Amarsu ke ce a gurinmu? Sannu da shigowa.” Faɗin Salima bayan ta sallami Nanayo.

“Dama ina ta zaune nace bari in zo in tayaki wani aikin in akwai. Ina Masoyi.”

“Masoyinki yana ɗaki yana bacci, aiki kuma ban sakaki ba, ai ni na hutar da ke don haka babu aikin da zaki yi.”

Da haka suka suka yi shiru wanda  Juwairiyya ta ke jinta a takure, hakan yasa ta mata sallama ta koma ɗakinta ta samu Muhammad ya dawo ya ci abincin ya bar kwanukan duk a gurin. Haushi ne ya kamata ganin har ya zubar da shinkafa a ƙasan carpet, Hafiz ba haka yake mata ba domin shi yana gama cin abinci zai ɗauka ya kai kitchen, shi kuma Daddy ummurni yake bata yace ta kwashe ko kuma ya faɗa mata cewa ya gama, to Muhammad duk ba zai yi ko ɗaya daga ciki ba, kenan bar mata su zai yi a gurin duk lokacin da ta gani ta kwashe.

Tana mita a ranta ta fara tattare gurin ta kai kitchen sannan ta wankesu ta mayarwa Salima wacce ta sameta tana girki da Nanayo a kitchen. Duk yanda ta kai ga son tayasu aikin Salima ta ƙi yarda, haka ta dawo ɗakinta duk jikinta a sanyaye.

Zaman shirun ne ya mata yawa hakan yasa ta ɗauki wayarta ta fara chatting don har lokacin ba’a jona mata kayan kallonta ba, ya kamata in muhammad ya dawo ta faɗa mishi a saita mata su.

Sai bayan magrib Salima ta yi sallama ta shigo mata da abinci ta ajiye, Juwairiyya ta mata godiya kana ta fita. Da haka itama ta fita zuwa kitchen ta ɗauko ƙananan ƙuloli biyu da zata sakawa Muhammad abincinshi amma tana zuwa bakin ƙofa ta canja ra’ayinta ta koma cikin kitchen ɗin tana dariyar mugunta.

Bayan isha Muhammad ya shigo falo Juwairiyya tana jin shi a yayin da take cikin ɗaki tana dariya ƙasa-ƙasa don ta san dole ya zo ya ji dalilin da yasa ta aikata mishi haka. Tana jin lokacin da ya buɗe kulan da ta saka mishi abinci sannan ya rufe ya tako zuwa ɗakinta ranshi a ɓace fuskarshi a murtuƙe kamar wanda ya ji mummunan labari.

“Me yasa kika mini haka?” Shine kawai abun da ya tambaya yana tsaye a kanta ita kuma tana kan gado tana zaune.

“Me na maka?” Ta tambayeshi kamar bata san me ta aikata ba.

“Kin haɗa mini tuwo da miya a kula ɗaya kamar wani almajiri alhali na faɗa miki ko ɗiba aka yi aka bar mini saura bana so. Why? Me na miki da har zaki mini haka?” Wannan karon he sound very hurt.

“Na ga na ɗazu ma ka ci daga baya, dama kawai kana son wahalar da mutane ne yasa kake cewa wai kai baka so.” Ta faɗa cikin rashin nuna damuwa.

“Shikenan.” Yana faɗin hakan ya fice daga ɗakin can kuma ta ji ya buɗe ƙofar falon ya fita.

Yanzu da daren nan ina zai je? Salima ta faɗa mata in dai ya shigo gida bayan isha baya fita sai da babban dalili daga nan kuma sai washegari da safe. Miƙewa tayi cikin sanɗa ta bi bayanshi tana dariya ta leƙa ta window, a daidai nan ta hangoshi ya shiga falon Salima. Nan da nan annurin fuskarta ta ɗauke amma sai ta samu kanta da tsayawa a gurin tana jiran fitowarsa, wataƙila ya je mata sallama ne, ko kuma ya je duba Hafiz Junior. Tana nan tsaye har ta fara gajiya tana gyara tsayuwarta amma bai fito ba, ganin zata wahalar da kanta yasa ta koma ɗaki ta shiga wanka don bata son Muhammad ya ji tana tsami, kwarai da gaske ba zata bari wani abu ya ƙara shiga tsakaninsu ba amma hakan ba zai hanata wanke jikinta ba gudun kar ya rainata ya ɗauketa ƙazama, sannan hakan ma wani salon horon ne da ake cewa ‘nan gani nan bari’ ko kuma ‘kwalele dokin iliya’.

Har ta fito daga wanka ta murje jikinta da humra bai dawo ba, kayan baccinta ta saka doguwar riga mai tsantsi kana ta kwanta bayan ta kashe wutan ɗakinta ta fara kallon wani Korean series a wayarta, a haka bacci ya kwasheta wayar ta faɗi gefenta.

Firgigit ta farka jin motsin mutum a ɗakin, Muhammad ta gani a yayin da yake shiga banɗaki ɗaure da towel a kunkuminshi ya ja ƙofar ya rufe. Wani malolon baƙin ciki ne ya cika mata ciki ya zo nan makwoshinta ya tsaya bayan ta duba lokaci ta ga ƙarfe goma da rabi, uban me yayi a ɗakin Saliman duk waɗannan awannin? Tana zaune sai cika take yi tana batsewa wanda ita kanta ta rasa dalilin ɓacin ran nata sannan can ya fito yana ɗigar ruwa a farar fatarshi lokaci ɗaya kuma yana gyara zaman towel ɗinshi yana kuma furzar da ruwa ta bakinshi wanda ya gangaro ya zo kan laɓɓansa. In ka cire yawan girman jikinshi ba ƙaramin haɗeɗɗen mutum za’a yi ba, wannan faɗin Juwairiyya kenan yayin da take binshi da kallo tana jin wani irin yanayi a jikinta.

Girgiza kanta tayi don tayi rantsuwa kuma ba zata karya ba, sai a lokacin kuma ta tuna ai ranta a ɓace yake! Me ya ɓata mata rai? Yauwa ta tuna kuma sai ta titsiyeshi don bata son rashin adalci.

“Ina ka je tun ɗazu bayan ka dawo daga sallan isha?”

“Ina ɗakin Salima, wani abu ne?” Ya mayar mata da tambaya ba tare da ya ko kalli inda take ba.

“Me ka yi a ɗakinta?” Ta ƙara jeho mishi wata tambayar tana harɗe hannunta kan kirjinta.

Sai a lokacin ya juyo ya dubeta, a nan ne ita kuma ta hango akwati a ƙasan wardrobe ɗinta wanda suke cike da suturunshi.

“Na ci abinci ne sai kuma na ɗebo wasu daga cikin kayana na kawo nan.”

“Mutum dai ya ji tsoron Allah ya yi adalci, amma wannan uban jimawan ba iya cin abinci da ɗebo kaya ya tsaya ba.”

Murmushi yayi kaɗan wanda yana farawa kuma ya daina ya gimtse fuskarshi ya ce,

“Me nayi?”

“Wa ya sani? Ni dai in an zalunceni Allah Ya isa.”

Wannan karon dariya yayi har tana iya jiwo sautin kana ya buɗe wardrobe ya fara jera kayanshi yana cewa,

“Ke da baki damu da ni ba ban yi tsammanin ko na yi rashin adalci zaki ji haushi ba, ni a tunanina ko kwana nayi a can ba zaki damu ba don na lura kamar presence ɗina yana takuraki.”

“Dama wa yace na damu da kai? In ka ga dama daga yau kar ka sake shigowa ɗakin nan dama ni haka nake so. Abun da na faɗa kuma da gangan nake yi don na ɗauka zai ɓata maka rai ne.”

“Wato ɓacin ran nawa kike so? Dalilin da yasa duk abun da bana so shi kike yi ko?”

Bata kulashi ba tayi kwanciyarta tana gunguni, shima bai ƙara kulata ba ya cigaba da abun da yake yi har ya gama ya saka wando three quarter ya kashe musu wutan ɗakin ya kwanta.

“Ɗazu na kawo miki magani.” Ya faɗa yana mai juyawa yanda zai ga doron bayanta.

“Eh.” Ta amsa a taƙaice.

“Kin samu lafiyan ne?”

“Idan na samu lafiyan sai me? Don Allah ka kyaleni, wancan ma ina regretting.”

“Waɗancan zaki ce don suna da yawa. Amma kuma tarayya da ni ɗin ne kike regretting?” Ya tambaya da mamaki a muryarsa.

“Eh.”

Shiru yayi na wani lokaci mai tsawo har tana tunanin ba zai yi magana ba sannan ta jiyo muryarshi yana cewa,

“Na san kin aureni ne ba don kina sona ba, kin aureni ne a matsayin escape route ɗinki. Na san hakan amma ban ƙi aurenki ba a tunanina idan mun yi auren you will give it a chance kamar yadda nima nace zan yi. Sai dai tun kafin mu tare na lura duk abun da zai ɓata mini rai kike so kuma kike yi, na ɗauka idan kin shigo gidana zaki daina amma gashi a cikin awanni kaɗan da shigowanki kin mini abubuwan da suka ɓata mini rai kuma cikin sani wanda dama hakan shine plan ɗinki. Juwairiyya ki bar duk wani grudges da ke tsakaninmu mu rayu a matsayin kowanne mata da miji. Wannan faɗace faɗacen babu inda zai kaimu sai dai ranmu yayi ta ɓaci. This is me waving the white flag, ki manta duk abubuwan da suka faru a bayanmu mu gina rayuwar aurenmu a kan aminci sai ki ga har soyayya ta shigo ciki. Bana son zaluntarki haka kuma bana son cin amanar Hafiz domin aurenki da nayi wani alƙawari ne da na ɗaukar mishi kamar yanda kika sani. Duk abun da ya faru a baya kiyi haƙuri ki barshi a baya.”

“Duk wannan dogon speech ɗin saboda ana neman abu.” Ta faɗa in a mocking voice.

“Haka kika ɗauka? Kenan duk maganan da na faɗa miki kina tunanin saboda biyan buƙatata ce? Gaskiya you think low of me, in ba aure da yake tsakaninmu ba babu abun da zai sa in ganki har in yi sha’awarki. Me amsarki?” A ƙarshe ya sassauto da muryarshi.

“Akan me?” Ta tambaya duk da cewa ta san me yake nufi.

“Akan zaman aurenmu da zamu canja.” Ya amsa ba tare da nuna gajiyawa ba.

“Never! Haka ya fi mini.” Ta faɗa cikin sauri domin ta samu garaɓasa, tunda shi ya bata zaɓi sai wanda take so zata zaɓa.

“Haka kika zaɓa?”

“Eh shi na zaɓa, kuma ka daina mini magana bacci nake ji.”

“Shikenan tunda haka kika zaɓa, sannan ki dinga tunawa cewa I tried to amend our relationship.”

“Na ji.” Ta amsa cikin gajiyawa.

Bai sake cewa komai ya juya mata baya, Juwairiyya tana jin hakan wani daɗi ya ziyarceta domin ta san Muhammad zai riƙe alƙawari wajen ganin tayi rayuwarta babu takurawa, girman kanshi da rashin son raininshi ba zai barshi ya yita bibiyarta ba dole zai kama kanshi hakan kuma na nufin ta samu abun da take so kafin shekarun da zata yi a gidanshi yayi ta fita. Yau cikin farin ciki ta kwanta tana jin sanyi na ratsa zuciyarta.

Mum Fateey 👌

Washe gari ya kama Friday Muhammad yana dawowa daga sallan asuba ya fara shirin fita office bai koma bacci ba, Juwairiyya kuwa tana ganin hakan ta kwanta abunta. Bata farka ba sai takwas da rabi, bata nemi Muhammad ba don ta san ya wuce office, hakan yasa ta gyaran ɗakinta da falonta ta kunna turaren wuta sannan ta shiga banɗaki ta wankeshi tayi wanka ta fito. Sai da ta gama shiryawa sannan ta fita falo don cin abincin da aka ajiye mata, tana buɗewa ta ga ɗumame ne na tuwon jiya, gashi kuma da alama an daɗe da saka ɗumamen a cikin kulan don har ya fara sanyi. Tsaki ta ja ba don bata cin ɗumame ba sai don ita bata son a sakashi a kula ya jima, domin kuwa shi daɗin shi daga tukunya sai kuma cikin plate ne. Cikinta ne yayi ƙugin yunwa tana jin haushin ƴan gidan gabaɗaya, da haka ta koma ɗaki ta ɗauko wayarta tare da kuɗi ta fito tana rubutawa Muhammad text.

‘Zan je shago sayo abun karyawa, kun yi ɗumame ya jima a cikin kula ba zan iya ci ba. Kar ka ce na fita ban faɗa maka ba.’

Bata jira amsarshi ba ta saka kai ta fice zuwa shago mafi kusa dasu wanda dama ta sanshi a da lokacin da take kawowa Salima ziyara. Cartoon ɗin Indomie ta saya da crate ɗin kwai sai gwangwanin madara, milo, sugar, da kuma cereals kala biyu ta dawo gida hannunta niƙi-niƙi da kaya.

Tana shigowa ta ji ƙarar shigowar text a wayarta ta duba ta gani.

‘Kar ki fita ko’ina’

Tsaki ta ja tana ayyanawa a ranta ai aikin gama ya gama. A kitchen ɗinta ta fara yada zango ta ajiye komai inda ya kamata sannan ta ɗaura girkin indomie da kwai, nan da nan kitchen ɗinta ya gauraye da ƙamshi har na waje da yake wucewa zai iya ji, tana ƙoƙarin kwashewa ta ji muryar Salima a bakin kitchen ɗin tana mata magana.

“Ina can zaune a ɗaki na jiyo ƙamshi busss a hancina nace to waye yake girki don nasan makwabtana da muke kusa bana jiyo ƙamshin girkinsu.”

Murmushin yaƙe Juwairiyya tayi kana ta fara juye abincin da ta yishi kaɗan don cikinta ta ce,

“Da yake nayi bacci ban tashi da wuri ba shiyasa na kasa cin ɗumamen nace to bari in sayo abun da zan sakawa bakin salati. Mu isa falo. Ha’ah Masoyi har ka tashi?” Ta ja ƙofar kitchen ɗin ta rufe kana ta musu jagora zuwa falonta.

A tsakiyar carpet ta ajiye musu abincin sannan suka zauna.

“Ni kuma bana iya cin indomie idan na dafa, ƙamshinshi sai ya hau kaina.” Faɗin Salima tana gutsiran kwai ta miƙawa Hafiz J da yake cinyar Juwairiyya.

“Ni kuma abun maiƙo ne yake mini haka.” Juwairiyya ta faɗi nata kana suka fara ci suna hira.

“Bari in bar miki haka kar garin santi in cinye ke da kike jin yunwa.”

“Ah ah haba zai ishemu wallahi. Ni dama ba wani yunwar kirki nake ji ba.” Ta ƙara wata ƙaryar akan wata.

Da haka suka cinye abincin tass Juwairiyya bata kashe yunwarta ba gashi kuwa Salima sai mata hira take yi na abun dariya tana biye mata ba don tana son yin dariyar ba. Ai kuwa kumatunta ya fara zafi dalilin force dariyan kana ta ji kanta na ciwo tana son su tafi su bata guri.

Suna zaune a gurin Hafiz J na wasa da plates ɗin da suka ci abinci suka ji sallamar mutane a tsakar gida.

“Ina tunanin makwabta ne suka shigo miki sannu da zuwa, bari in duba.” Faɗin Salima tana miƙewa tsaye tare da HJ a hannunta suka fita daga falon.

Juwairiyya tana ganin haka ta fara tattare gurin cikin sauri domin HJ ya kucincina kwai ya zubar a kan carpet ga indomie da ake bashi a baki ma ya zubar. Kafin ta gama ta jiyo sallamar mutane a bakin ƙofarta sai ta ƙi amsawa domin bata son ko da wasa su ga ƙazantarta a ranar farko da zuwansu, sai kawai gani tayi Salima ta shigo tana musu iso.

“Ku shigo ga Amaryar tana ciki.”

Da haka suka shigo su bakwai suka samu guri suka zauna Juwairiyya na ƙasa a zaune tana cigaba da tsince dottin tana musu barka da zuwa.

“Ki ce abun daɗi take ci shiyasa ta ƙi amsa sallamar tamu, to gamu nan mun shigo a bamu rabon mu.” Faɗin wata farar mata da zata yi sa’anni da su.

“Kai Maman Hanan, ai ta cinye sai dai a dafa muku wani.” Salima ta amsa tana dariya.

Juwairiyya ta take zaune a ƙasa tayi shiru bata ce komai ba amma tana murmusawa, a ranta kuma cewa take yi babu uban da zai sa ta ƙara yin wani girkin yanzu.

“A’a ba sai ta sake dafawa ba, ai yanzu kam an haɗu guri ɗaya, aje aje watarana sai mun ci girkin nata. Kwanaki ai na taɓa haɗuwa da ita a nan gidan, dama kin ce matar abokin mijinki ce. Da na ji labarin auren nan sai da na girgiza domin wallahi ba kowacce mace ba ce zata ɗauki hakan cikin kwanciyar rai ba, amma da yake ke kina da haƙuri ko a jikinki. To Allah Ya kau da fitina, duk wanda ya zo da baƙi Allah Ya mayar mishi da abun shi.”

Nan ɗakin yayi tsit baka jin sautin komai sai ƙarar standing fan da kuma hayaniyar HJ da yake cakular wata jaririya da ke hannun mamanta. Juwairiyya kuwa kanta na ƙasa zuciyarta na tafarfasa domin ta gane da gayya matar take mata magana haɗe da habaici.

“Ina kwananku?” Salima ta katse wannan shirun ta hanyar ɗaga musu gaisuwa suka amsa, da haka itama Juwairiyya ta gaishesu amma tana lura Maman Hanan bata amsa ba haka kuma tana ta aiko mata da harara.

“Kin san da na shigo wallahi ban ganeta ba kai tsaye sai dana zauna, a da tafi haka ƙiba yanzu kuma duk ta rame.” Faɗin Maman Hanan tana kallon Salima da alama da ita take yi.

“Ayya ai tana zuwa makaranta a nan GSU, kin san karatu yana draining mutum.” Salima ta amsa.

“Da kuma damuwa ko rashin miji, shiyasa tayi wuff da mijinki.” Faɗin Maman Hanan tana dariya don ta nuna wasa take yi amma duk cikin falon babu wacce bata gane da gayya take yi ba.

Wannan karon zuciyar Juwairiyya ya kai ƙololuwar ɓaci domin har ji take yi numfashinta na sarƙewa, gani tayi idan tayi shiru an cuceta duk dama cewa ita ce da laifi ita ta auri mijin ƙawar tata amma ai ita kanta Saliman bata ɗauki abun da zafi ba kamar yanda Maman Hanan ɗin ta ɗauka ba. Ɗago kanta tayi ta kalli matar tarr cikin ido ta ce,

“Kamar magana kike nema Maman Hanan kike ko wa? Idan ba zaki faɗi alkhairi ba kiyi shiru da bakinki ko kuma ki fita mini a ɗaki don ba zan lamunci ki shigo har cikin gidana kina yaɓa mini maganganu ba, bana yarda da wulaƙanci komin ƙanƙantarshi.”

“Sannu masu gida, kin gani ko daga zuwanta har ta fara kiran gidan da sunan nata? Wallahi Salima sanyinki yayi yawa shiyasa ake cin kashi a kanki kina shiru. Ke kuma har kina da bakin magana ne da kika auri mijin ƙawarki? Ai faɗin abun da kika aikata aka yi ba wai zaginki aka yi ba.”

“Don Allah Maman Hanan kiyi shiru, sai da kika mana rantsuwar ba zaki yi magana ba muka taho. Ita wacce aka aure mata mijin ma tayi haƙuri bai kamata ke kuma ki shigo gidansu kina tayar musu da harzoma ba.” Faɗin wata daga cikin matan wacce da alama duk zata girmesu.

Nan ɗakin ya kacame kowa da abun da yake tofawa, Juwairiyya dai bata sake cewa komai ba saboda ta san in ta buɗe bakinta zata iya yin kuka, yau ita ce aka titsiye kamar wacce tayi sata! Shin basu da labarin cewa ba ita ta nemi auren Muhammad ba shi ya fara zuwa mata da zancen? Shin basu san cewa itama bata son auren ba sannan aure ne mai ƙayyadadden lokaci ba?

“Don Allah mu bar maganan nan haka bana so, in kuma abun da ya kawoku kenan ku tafi.” Wannan faɗin Salima kenan don ta sauƙaƙa al’amarin.

Juwairiyya tana ganin haka ta tashi tsam ta shige ɗakinta ta kullo ƙofa, sai da ta tabbatar sun fita hawaye ya fara zuba a fuskarta. Daga inda take kuwa tana jiyo Maman Hanan tana aiko mata da baƙaƙen maganganu amma babu yanda ta iya domin gaskiya suke faɗa tayi butulci da auri abokin mijinta da take ƙawance da matarshi. Ta san idan tace zata yi sa’insa dasu ita zata rasa abun faɗi domin ita ce mara gaskiya a cikin wannan al’amari. Me yasa bata yi tunanin hakan zai faru ba ta yarda ta amince? Kenan haka kowa yake mata kallon mai butulci mara amana? Ashe shekarun da zata yi a gidan ba zai mata daɗi ba domin ta lura yawancin matan suna goyon bayan Salima ce domin ita suka sani sannan suna tayata kishi akan abun da ya faru.

A can bakin gate kuwa Salima ce take gyara riƙon da ta yiwa HJ tana cewa,

“Gaskiya Maman Hanan baki kyauta ba, ba haka muka yi da ke ba. Kin mini alƙawarin ba zaki ce komai ba amma yanzu zata ɗauka ni nace ku mata haka. Yanzu in ta faɗawa Baban Hafiz faɗan kaina zai dawo don shima zai ɗauka duk haɗin baki ne don mu ci zarafin amaryarshi.”

“Ni wallahi yanzu kema kin fara bani haushi, yanda kika ɗauki abun nan cikin sanyin rai ɓata mini rai yake yi. Wallahi da ni ce aka yiwa wannan cin amanar sai na tayar da hankalin kowa an kasa zaman lafiya. Sanyinki da haƙurinki yayi yawa gashi ita waccar shegiyar da alama zuciyarta a bakinta yake bata tsoron fallasashi. Kar dai ki bari ta gane lagonki tayi ta ha’intarki don Allah. Kuma ni da ban yi niyyar magana ba, amma ganin yanda ta wani shantaƙe a falon tana cin indomie da kwai yasa na ji ba zan iya shiru ba sai na amayar da maganan da yake cikina, irin an samu duniyar nan. Allah Ya kareki daga sharrinta.”

“Ɗumame ma muka yi breakfast sai daga baya na shiga gurin nata na ga tana cin indomie da kwai ɗin, wataƙila ita ta saya amma tun da aka fara gyaran gidan nan Baban Hafiz yace mu sarara mishi da irin waɗannan kayan abincin sai ya daidaita komai tukun.” Salima ta ƙarisa maganan a sanyaye tana murmushi alamar babu abunda yake damunta.

“Jar uba! Wai dama kina nufin ba dukka gidan aka ci abincin ba ita kaɗai ta dafa ta ci? Maman Hafiz lafiyanki kuwa? Kai jama’ah don Allah mu tafi kar hawan jini ya kamani, ita ake yiwa amma nine nan baƙin ciki zai kashe.” Fadin Maman Hanan tana fita daga gidan tana mita.

Ganin haka yasa sauran ma suka rufa mata baya dama ita take masifar su basu yi niyyar magana ba amma dai suna tausayin Salima. Mace ɗaya ce kawai abun bai zauna mata ba kuma tana ganin akwai alamun tambaya a kan Salima amma ta kasa gane menene.

Salima tana rufe gate tayi saurin canja yanayin fuskarta zuwa damuwa kana ta shiga falon Juwairiyya tana mata sallama tana kiranta. Juwairiyya da take hawaye tayi saurin shiga banɗaki ba tare da ta amsa ba, a can ta cigaba da kukanta tana sauraron Salima mai mata magiyan ta buɗe ƙofa kar ta illata kanta. To dama tace mata kashe kanta zata yi ne ko menene? Ko dai ta taɓa yin hakan ne da yau ma zata yi tunanin zata sake? To ko dai ta kashe kanta ne kowa ma ya huta?

Salima da take can bakin ƙofar ta fara bubbugawa tana cewa,

“Juwairiyya don Allah ki fito kar ki illata kanki, kuma wallahi ban san zasu miki haka ba da ban bari sun shigo har ɗakinki ba. Don Allah ki buɗe don kin fara bani tsoro, in baki buɗe ba zan kira Baban Hafiz.” Tana faɗin hakan ta koma sashenta ɗauke da ɗanta tilo yana ganin ikon Allah.

A falonta ta yada zango ta zauna a kan kujera kana ta ɗauki abun wasa ta miƙawa ɗanta da yake zillo yana son sauƙowa, yana ganin abun wasa ya wafce ya fara wasanshi daga kan kujerar. Da haka ta fara kyakyatawa da dariya tana rufe bakinta har hawaye na zuba a fuskarta, sai da ta tsagaita da dariyan sannan ta fara magana kamar akwai mai sauraronta.

“Ba mijina kika aura ba? Yanzu kika fara gani domin wallahi ke da kanki zaki saka ƙafa ki fita babu boka babu mallam.”

Da haka ta fara tunanin farkon haɗuwarta da Juwairiyya wacce take matar abokin mijinta. Tun kafin aurenta da Muhammad ta san abokinshi Hafiz sannan ta san Hafiz ɗin yana da mata mai suna Juwairiyya wanda ta lura Muhammad ko sunanta baya son a ambata, cikin kissa da dabara ta tambayeshi dalilin menene ya faru basa shiri ya ce,

“Bata da hankali ne.”

Tun daga ranar itama ta ji bata son Juwairiyya domin Mamanta ta faɗa mata duk abun da mijinta baya so itama ta nuna bata sonshi. Sai dai bayan aurensu ta haɗu da Juwairiyya sai ta gane cewa mutumiyar kirki ce sannan mutumin nata ne ya taɓota ta nuna mishi rashin hankalin. Tun a lokacin suka ƙulla ƙawancen da daga baya zata dawo tana dana sanin shi, ta ƙulla ƙawancen da ita ne don ta ga Juwairiyya tana da fara’a sannan ga saurin sabo da mutum, kuma duk cikin abokan mijinta Muhammad bashi da wani shaƙiƙi irin Hafiz, to me yasa ba zata yi abokantaka da matarshi ba? Don wani lokacin ba zata san wani abu game da mijin nata ba sai ta gurinsu.

Hakan yasa ta yiwa Muhammad musu a karon farko a rayuwar aurensu tace ya barta tayi zumunci da Juwairiyya wanda bai ƙara cewa komai ba ya barta suka cigaba da mutunci. Ba zata ce tana son hulɗa da Juwairiyya ba don tana yawan kushe mata miji, hakan yasa tayi amfani da wannan daman wajen nunawa ita Juwairiyyan cewa Muhammad baya ragar mata sannan yana mata yawan mata faɗa don ta nuna mata da sauran mutanen duniya cewa ita mai ladabi ce da haƙuri, wannan kuma salon kissan da ta koya a gurin mamanta kenan. Domin kuwa hakan zai sa a dinga tausayinta ana ganinta mai sanyin hali, hakan kuma zai sa duk wacce ta ji labarin halin mijinta na faɗa da disga matarshi zata sha kwana, sannan in aka yi nasara wata ta samu ta shigo gidan zata fita da kanta domin kuwa ta sabarwa Muhammad tsantsan biyayya da ba zai iya zama da kowacce mace ba sai mai irin halinta, wanda zai yi wuya a wannan zamanin domin kuwa itama pretending take yi.

Ranar da Muhammad ya zo mata da zancen wai zai iya mutuwa tayi kuka sosai domin jikinta yayi sanyi bata son abun da zai rabata dashi da ɗansu da ke cikinta. Maganarshi ta ƙarshe kuma da yake cewa ta auri Hafiz bayanshi bata yarda ba sai da yayi da gaske sannan ta amince, a ranta bata fatan mijinta ya barta balle har ta kai ga auren Hafiz, sannan in hakan ya faru to babu makawa zata auri Hafiz domin ta san halinshi kaf daga bakin matarshi da kuma abokinshi kuma idan ta shiga babu mai rabata da gidan sai Allah, a hakan kuma zata san yanda zata yi Juwairiyya ta bar mata gidan don bata son zama inuwa ɗaya da kishiya!

Lokacin da Hafiz ya rasu tayi kukan da bayan matarshi da ƴan’uwanshi na kusa babu wanda yayi kuka irin nata. Tayi kuka ne domin tausayin kanta da kanta, sannan tayi kuka ne don tsoron cikar wani alƙawari da zai jawo mata rugujewar farin cikinta. Ta yi kuka ne don canjawar TAFIYAR SU tsakaninta da mijinta Muhammad.

Zumuncin da yake tsakaninta da Juwariyya ta ƙara ƙarfafawa bayan mutuwar Hafiz domin tana tunanin duk sa’ilin da da Muhammad ya je mata da zancen aure zata tuna girman ƙawance da amincin da ke tsakaninsu ta bar mata mijinta. An shafe kusan shekara kafin nan Muhammad ya bata labarin ya je gurin Juwairiyya da zancen amma ta nuna bata so. Wannan abu yasa tayi farin ciki sosai amma bata nuna mishi ba, ƙarshe ta kaɗa kai ta ce,

“Ni da zata yarda ai da ta amince mu zo muyi zaman mu tare tunda ta san halina nima na san nata.”

Muhammad bai ce mata komai ba da haka maganar ta wuce dama ita ta matsa mishi akan duk lokacin da yayi niyyar tunkarar Juwariyya ya faɗa mata amma sai gashi sai da ya je tukun ya faɗa mata, a hakan ma ita ce da godiya.

Lokacin da ta haihu kuwa Muhammad ne da kanshi ya sakawa ɗanshi sunan Hafiz tun ranar da aka haifeshi amma da Juwairiyya ta zo duba jariri tare da danginta da wasu ƙannen Hafiz sai ta nuna dama ita ta roƙi Muhammad ya canja sunan daga babanta zuwa na Hafiz don Juwairiyya ta ji nauyin aura mata miji.

 Kwarai! Me yasa zata yarda ya aureta alhali ta san wacece ita, tana da kyau, tana da ilimi both boko da Arabi sannan ga iya girki, soyayya da kuma jajircewa akan gado abun da ita kuma ta rasa kenan tana kuma neman magani har gobe. Ta rasa gane meyasa take gudun mijinta a shimfiɗa sannan tayi amfani da magunguna da yawa wanda zai bata wannan jajircewan da son tarayya dashi ɗin amma duk a banza. Wannan matsalar kaɗai ya isa yasa ta ji tsoron wata ta shigo mata gida ta sace mata miji.

A ranar da ta samu labarin Juwairiyya tayi aure tayi farin ciki fiye da ita amaryar domin a gurinta wannan jefar da kwallon mangwaro ne a huta da ƙuda. Da ita aka kaita har cikin ɗakinta sannan hankalinta ya kwanta ta bita da addu’ar mutu ka raba. Duk da haka bata daina hulɗa da ita ba domin ta wani gurin tana son zumunci da ita domin kuwa Juwairiyya tana ƙara mata haske akan abun da ta gaza akai wato sirrin kan gado, shima wannan dalili kaɗai ma ya isa yasa ta ƙara riƙeta su ci gaba da mutunci.

Wata bakwai da auren ne ta samu labarin auren ya mutu, tsabar ruɗu sai da ta dinga kewayawa banɗaki, da haka ta kira mamanta ta sanar da ita wannan mummunan labarin.

“Wannan yarinya ta zame miki raƙai, yau na ga ikon Allah. Wai me ya rabata da gidan nata?”

“Wallahi ban sani ba don kwana uku da ya wuce aka mata sakin.”

Bayan Salima ta ji labarai da dama akan musabbabin rabuwar auren sai ta ɗauki wanda take ganin shine gaskiya, wato tsohon da ta aura baya iya biya mata buƙatarta. Wannan labari yasa ta ƙara tsorita domin ta san yanayin Juwairiyya ba zata iya zama haka nan babu mijin aure na tsawon lokaci ba, haka kuma wasu daga cikin zargin da ake mata zai sa ta rasa mijin aure musamman wanda aka ce ta nemi ɗan mijin nata da lalata, hakan na nufin Muhammad ne zai zama last option ɗinta kenan.

Duk da cewa ta ƙara ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninta da Juwairiyya bayan mutuwar aurenta bai hana duk lokacin da take tare da ita ta ji ta kasa nitsuwa ba, wani lokaci sai ta ji kamar ta mata maganan alƙawarin da mazajen nasu suka ƙulla amma sai ta fasa.

Ana haka ne kuma kwatsam Muhammad ya zo mata da mummunan labarin da har ta mutu ba zata taɓa mantawa dashi ba, wai an ɗaura mishi aure da Juwairiyya a safiyar yau. Da gaske ta suma wanda hakan yasa wayarta da ke hannunta ya faɗi ƙasa ya tarwatse! Bayan ta dawo hayyacinta ta gane Muhammad ne ya watsa mata ruwa ta farka, kuka take yi sosai har bata iya jin sautin komai sai nata, hakan yasa duk lallashin da Muhammad yayi mata bata ma sani ba.

“Ka fita ka bani waje.” Haka tace dashi wanda zata iya rantsewa wannan shine karo na farko da ta mishi tsawa.

“Bana son tafiya in barki a cikin wannan halin, kuma kin san auren nan zai iya faruwa Salima ban ɓoye miki ba tun farko. Auren ne kuma ya zo a ƙurarren lokaci domin kuwa jiya da dare ta amsa mini zata aureni.” Ya faɗa cikin kwantar da kai kamar ba shi yake mata tsawa kullum ba.

“Dama dole ta yarda mana tunda kullum kana bibiyarta kana kai mata kayan masarufi. Kaine kullum a ƙofar gidansu duk da cewa ta faɗa maka ba zata aureka ba tun wancan lokacin, ina sane da duk abun da yake faruwa ni ba makahuwa bace. Kuma ai ba akan haka aka ƙulla alƙawarin ba, dama abun da kake so ne ya faru. Don Allah ka fita ka bani guri bana son ganinka.”

Duk yanda ya kai ga son tsayawa bai tsaya ɗin ba domin ya tsorita da halin Salima mai sanyi hali, lallai kishi banzan abu ne don bai taɓa tsammanin akwai ranar da Salima zata ɗaga mishi murya ba ko ta bashi doka ya bi ba. Yana fama da halin da Salima ta tsinci kanta a ciki Juwairiyya ta kirashi har tana tambayar me ya faru wayar Salima bata shiga? Bai faɗa mata ainihin abun da ya faru ba domin baya son ta ɗaga hankalinta itama.

Fitan Muhammad yasa itama Salima ta fice daga gidanta wannan karon ba ta nemi izini ba sai gidansu, a can ta zube a gaban mahaifiyarta tana kuka tana labarta mata abun da ya auku.

Da kyar mahaifiyarta ta lallameta aka kai wayarta gyara sannan ta ƙarfafa mata gwiwa cewa duk da cewa an ɗaura auren ba lallai ne ya daɗe ba. Da wannan huɗuban ta dawo gida ta gyara gidanta da jikinta tsaff sannan ta zauna zaman jiran sabon angon.

Wunin ranar kaff a waje Muhammad yayi sai dare ya koma gida ba tare da ya san me zai tarar ba, anan ne kuma mamaki ya kusan kasheshi domin ya samu Salima ce cikin kwalliya ta tarɓeshi kamar kullum fuskarta a washe kamar babu abun da ya faru ɗazu. Bai gama suncewa da lamarinta ba sai da ta faɗa mishi wai an gyara mata wayarta ta kira Juwairiyya sun fahimci juna za kuma su zauna lafiya. Duk yanda ya kai da son gane me yake yawo a kwalwarta ya gagara, hakan yasa ya bar komai a ranshi domin kuwa yasan duk rintsi Salima ba zata cuceshi ko wani ba.

Salima tana lura da Muhammad ko kaɗan baya kauɗi ko wani rawar kai a wannan auren domin yanda ya saba da rayuwarshi haka yaci gaba da yi. A nan ta gaskata zancen Juwairiyya da take faɗa mata cewa ta aureshi ne don gujewa wani mutum sannan don ta samu tayi exams ta ƙarisa school ɗinta ba tare da Mama ta hanata ba.

Duk da cewa hakan gaskiya ne Salima bata ji sassauci a ranta ba domin bata ga dalilin da zai sa Juwairiyya ta zaɓi mijinta a matsayin escape route ba, duk mazan duniyan nan shi kaɗai ta ga ya dace da hakan? Wannan kuskure ne da tayi kuma zata biya da sanity ɗinta don ta rantse sai ta nemi saki da bakinta tun kafin lokacin fitan nata yayi. Ita kuma wannan ne plan ɗinta.

Ta danne kishinta yanda babu wanda yake ganewa har aka kawo Juwairiyya, a daren ranar ta kasa bacci ta jiyo abun da zai daɗe yana damunta. Tayi kuka har ta fara ji  tsoron kar su jiyota, a haka ta kwana babu bacci domin suyar da zuciyarta take mata. Ashe karya suke mata daga Muhammad ɗin har Juwairiyya? Ko da gaske suke yi basa son junansu to dama sun daɗe da yawo da sha’awar juna in ba haka ba me zai sa a ranar da aka kawota zai nemeta ita kuma ta biye mishi har da surutai?

Saboda wannan hanata baccin da suka yi yasa ta hora Juwairiyya da yunwa cikin dabara, sai da ta tabbatar lokacin fitanshi yayi sannan ta kai mishi abincinshi a basket ya saka a mota ya tafi. Da haka kuma ta ja sukuwar da hira har sai da ta lura yawun bakinta ya kafe sannan ta mata sallama ta tafi akan cewa zata girka abincin rana. Da murna ta koma ɗakinta domin ta horata da yunwa kuma ta horu.

Ƙannen Hafiz mata da suka zo kuwa ita ta hanasu isa ɗakin Juwairiyya.

“Da dai kun bari sai daga baya ku dawo ku ga ɗakin don yanzu ba lallai ne su buɗe ba. Amma in sun fito zan faɗa musu kun zo.” Faɗin Salima tana murmusawa babu ko ɗigon ɓacin rai a tattare da ita.

Haka kuwa aka yi suka tafi da maganar Juwairiyya a bakinsu wai ta shige ɗaki da miji da tsakar rana sun kulle alhali sun san zasu yi baƙi ƴan ganin gida.

Da haka kuma ta gayyato makwabtanta da take mutunci dasu musamman Maman Hanan wacce tun da ta ji labarin auren ta so a bata numbern Juwairiyya wai ta kirata ta zazzageta don ta ci amana. (Mai fushi da fushin wani)

Ta san Maman Hanan ba zata iya shiru ba hakan yasa ko da ta fara habaicinta bata hanata ba sai da abun ya fara yawa. Yanzu kuma da abun ya kacame har Juwairiyya ta shige ɗaki ta kulle sai ta samu damar kiran Muhammada kar Juwairiyya ta rigata a ga kamar laifinta ne.

“Assalamu alaikum. Baban Hafiz don Allah ka dawo gida yanzu, ga Juwairiyya ta rufe kanta a ɗaki ina tsoron kar ta yiwa kanta illah.” Ta faɗa cikin numfashi ɗaya da alamar tsoro a muryarta.

“Me ya faru ta rufe kan nata? Faɗa kuka yi?” Ya tambayeta yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar office ɗin nasu kana ya ɗagawa wanda suke sharing office hannu ya fice cikin sauri.

“Wallahi bamu yi faɗa ba, su Maman Hanan ne suka shigo sai suke mayar da zancen yanda aka yi auren shine bai mata daɗi ba tace su fita a gidan. Suna shirin fita ta tashi ta shige ɗaki ta rufe.”

“Ehen ina jinki.” Ya faɗa yana shiga motarshi ya kunnata.

“Bayan na musu rakiya na dawo in bata haƙuri na samu tayi locking ƙofar kuma bata amsa kiran da nake mata.”

“Gani nan ina zuwa, babu abun da zai faru.”

Mum Fateey 👌

Cikin mintuna kaɗan Muhammad ya iso gidanshi, a waje yayi parking ya samu Salima a tsakar gida tana hawaye ga Hafiz J shima yana kuka duk sun birkice.

“Me ya sameki ke kuma kike kuka?” Ya tambayeta yana karɓan yaron daga hannunta ya ɗaurashi a kafaɗa yana lallashinshi.

“Babu komai.” Ta bashi amsan tana share hawayen fuskar tata.

“Haka kawai zaki fara kuka babu abun da ya sameki?” Ya tsareta da ido yana ɓata rai don baya son yawo da hankali.

“Dama kar ka zo kace ni na sakasu ne ka mini faɗa, wallahi bani na sakasu ba. Kuma da Maman Hanan ɗin ma tace zata yi magana sai da na roƙeta tace ta fasa amma kuma sai da tayi. Kayi haƙuri.” Ta ƙarisa maganan tana kecewa da wani kukan.

“Ni nace zan miki faɗa Salima? Kuma na san halinki ba zaki nuna musu su aikata hakan ba. Yanzu dai ki share hawayenki, hingo karɓi yaron ki je ki kwantar dashi zai yi bacci.” Da haka ya miƙa mata HJ wanda har ya fara gyangyaɗi domin ya gaji da kukan da bashi da dalili.

Da haka Muhammad ya shiga falon Juwairiyya ya isa bakin ƙofar ɗakin nata ya fara bugawa yana kiran sunanta.

“Juwairiyya ki buɗe ƙofar.” Ya cigaba da murɗa handle ɗin yana jijjigawa.

Caraf ya ji ta cire lock ɗin ya buɗe ya shiga yana binta da kallo har ta je ta kwanta a kan gado tana mai kare fuskarta da hannayenta duka.

“Wa ya dafa indomie a gidan nan?” Shine abun da ya fara tambaya yana tsaye a kanta.

Wani irin zabura tayi ta miƙe zaune tana kallonshi fuskarta ɗauke da tsantsan mamaki ta ce,

“An faɗa maka an shigo har cikin gidana an mini rashin mutunci shine ba zaka tambayi wani hali nake ciki ba sai waye ya dafa indomie? Ni ce na dafa da kwai don ba zan iya cin ɗumame ba.”

“Akan bakya cin ɗumamen ne a gidanku?”

“Zagina zaka yi kenan? Kana so kace mu talakawa ne?”

“Tambaya na miki ki bani amsa.”

“Don Allah ka barni, idan abun da ya kawoka kenan ka tafi ka barni in ji da abun da yake damuna.”

“Wato da na hanaki fitan kin fita?”

Galala take kallonshi cike da mamaki, ta ɗauka zai zo ne ya ji ba’asin me ya faru sannan ya samu mazajen shegun matan nan a musu faɗa ko a musu iyaka da gidan amma shine zai zo yana maganar wani indomie?

“Na fita kuma na sayo carton ɗin indomie da crate ɗin kwai da kayan haɗa tea saboda ina so kai kuma baka saya mini ba.” Ta faɗa a harzuƙe don haushinshi take ji sosai kamar ta je ta wanka mishi mari.

“Saboda kina da gajen haƙuri ne, da kinyi haƙuri da kin jira kin ga gudun ruwana. Na farko na hana cin indomie a gidan nan saboda illolin da ke cikinta. Na biyu fitan da kika yi ba da yawun bakina ba na barki da wanda ya bani amanarki har sai kin nemi gafara a gurina. Na uku kuma na haramtawa kowacce matata zuwa shago, in kina da aika ki bawa almajiri in babu ki jira in dawo in sayo miki amma na hana zuwa shago. In kuma kika ga ba zaki iya ba ki tafi gidanku don zan iya jure duk rashin hankalinki amma banda fita ba tare da izinina ba, ba zan lamunci hakan ba ko kaɗan.”

Kallon-kallon suka tsaya yi zuciyoyinsu na tafasa domin kuwa wannan karon ran Muhammad ya ɓaci sosai domin ya tsani ya ga matarshi ta je shago tana sayan abu sai kace a bariki suke, wannan dalili yasa ya hana Salima wacce dama ko a gidansu ita bata fita sai dai su aika masu aiki ko almajiran da suke musu aika. Ya dawo ne don Juwairiyya amana take a gurinshi amma ba wai don yayi tsammanin zata lahanta kanta ba, wannan ba halinta bane sannan a da ta shiga damuwar da ta fi haka amma bai taɓa jin cewa ta yiwa kanta illah ba. Ya dawo kuma ya samu hakan ne wato tana nan lafiyarta kalau, sai dai ya tarar da guntun indomie da aka ci a plate aka bari akan carpet. Kenan Juwairiyya fita tayi ba tare da izininshi ba?

“Na ji. To ka yiwa matan nan iyaka da gidan nan kar su sake shigowa ciki tunda ba gidansu bane.” Ta faɗi hakan cikin ɗaga murya rai duk a ɓace.

“Me suka miki?”

Yanda yayi maganar a sanyaye ya ƙara harzuƙa Juwairiyya domin ta kura bai ma damu da halin da ta ke ciki ba, to uban me ya dawo dashi kenan?

“Sun shigo har cikin gidan nan suna mini haibaici suna faɗa mini baƙaƙen maganganu wai na auri mijin ƙawata.”

“Haƙuri zaki yi dasu, zasu daina idan TAFIYAR MU tayi nisa amma ni ba zan hanasu shiga gidan nan akan laifi ɗaya ba, sai dai zan yiwa mazajensu magana su ja musu kunne kar su sake shigowa gidana su tayar mini da hankalin iyali.”

Hawaye ne ya gangaro kan kuncin Juwairiyya ta goge ta ce,

“Wallahi baka sona.”

“Sai kuma me?” Ya tambayeta yana mai gyara tsayuwarshi.

“Idan Hafiz ne wallahi ba zai bari a shigo har cikin gidanshi a wulaƙantani sannan ya kasa ɗaukan mataki ba, kai na lura ma ba wannan ne damuwarka ba, kuma kamar daɗi kake ji da aka ci mutuncina.”

“Ni ba Hafiz bane. Kuma na faɗa miki irin matakin da zan ɗauka, idan bai miki ba sai ki biye musu kuyi ta hargowa a cikin unguwa tunda ke mijinki ma baki barshi ba.” Yana faɗin hakan ya fice daga ɗakin zuwa waje inda motarshi take ya koma office.

Wani sabon kuka ne ya ƙara kwacewa Juwairiyya don sai tafi jin zafin halin ko in kulan da Muhammad ya nuna mata akan laifin matan ɗazu, kenan shima bayansu zai bi su ci zarafinta ba zai ɗauki mataki ba? Yaushe rayuwarta ta gurgurce haka ta rasa madafa ko ɗaya? Wa zata kaiwa kukanta ya share mata? Babban abun ma shine wa zai fahimceta?

Tana kukan ta jiyo sallamar Salima a falo, wannan karon ta amsa bayan ta saisaita muryarta tace mata tana zuwa. Sai da ta wanke fuskarta sannan ta fito fuskar nan har ta kumbura idanu yayi ja.

“Yau ki ga yanda idanunki suka kumbura! Kiyi haƙuri ban san zasu miki haka ba da ban bari sun zo gaisuwan ba. Nayi zaman mutunci dasu amma ba zai hana in faɗi laifinsu na, basu kyauta ba ko kaɗan. In ma fushi ne ni ya kamata ace nayi fushi amma na ɗauki hakan a matsayin ƙaddarar da ba zan iya kauce mata ba. Kuma na sani Baban Hafiz zai ɗauki mataki ba zai bari ba.”

“Kayya babu abun da zai yi.”

“Ban gane ba.” Salima ta tambaya don tana son sanin me ya faru.

Nan Juwairiyya ta faɗa mata duk yanda suka yi da Muhammad don ta san Salima zata goyi bayanta ta ƙarisa da cewa,

“Dama ya hanaku cin indomie ne kuma ya hanaki fita zuwa shago?”

“Dama ni bana son fita sayan abu, to da ya ce shima baya so sai muka tafi a haka ban yi tsammanin ƙin da yake yiwa fitan ya kai haka ba. Ke dai ki nemi gafarar tashi kamar yanda ya faɗa…”

“Allah Ya sauwaƙe in nemi gafarar mutumin da ko haƙƙina ba zai iya kwato mini ba. Kuma ni ban ga text ɗinshi ba sai da na shigo cikin gidan nan a lokacin ma har na sayo. Amma ki faɗawa wannan Maman Hanan ɗin wallahi ta ƙara shiga sabgata sai na nuna mata kuskurenta, wallahi ba’a mini in share sai na rama.”

“Ai ke kam kina da baki kina iya kwatarwa kanki ƴanci, yanzu ko na mata magana haka zata sakani a gaba da zagi wai bani da zuciya da ire-irensu. Haka muke zaune da su saboda Allah ne Ya haɗaku unguwa ɗaya mutum ba zai ƙi mutunci da su ba. Kema zuwa gaba hakan zai zama tarihi.”

“Babu abun da zai sa in yi hulɗa da su tunda su munafukai ne masu tada tarzoma. Ki bari kawai ba sai kin musu maganan ba kar laifi ya dawo kanki, ki barni da su ni ce zan yi maganinsu.” Faɗin Juwairiyya tana jin wani ƙarfi a zuciyarta domin sai tayi maganinsu ɗaya bayan ɗaya.

“Shi kuma Baban Hafiz bai kamata ya faɗa miki haka ba, tunda ranki ne ya ɓaci sai ya lallasheki tukunna kafin nan ya gindaya miki sharuɗɗan gidanshi.”

Hawaye ne ya taru a idanun Juwairiyya da ta tuno sa’insar da ya faru tsakaninta da Muhammad, shima kuma zata yi maganinshi don ba zata manta ba sai ta rama.

Da haka Salima ta mata sallama ta koma ɗakinta zuciyarta yau ma fari tass, tsabar jin daɗi yau girkin rana favourite ɗin Muhammad ta yi wato fried rice da coslow wanda ya ji hanta, da kuɗinta ta aika kaza guda ɗaya babba ta musu pepper chicken da juice ɗin karas. Tana aiki tana waƙoƙinta daɗi na ratsata har ta gama ta barwa Nanayo gyaran kitchen ɗin.

Kamar kullum da kanta ta kaiwa Juwairiyya nata kana ta tsaya sai da ta fito daga sallah sannan tace,

“Yau nayi favorite ɗin Muhammad, don Allah kar ki kwaɓa mishi guri ɗaya zai ɗauka zaki rama abun da ya miki ɗazu ne.” Ta ƙarisa maganan tana kifta ido kamar bata san me ta shirya ba, tunda tace bata da wayo zata cigaba da ingizata.

“Laa babu komai. Nagode da ɗawainiya Allah Ya saka.” Juwairiyya tayi godiya kana suka yi sallama.

Kamar kullum Salima tana fita itama ta bi bayanta zuwa kitchen ta ɗauko plate da kula ta dawo parlour. Abincin ta buɗe inda ta ga an saka shinkafar a kula madaidaiciya sai pepper chicken shima a kula da coslow a wani bowl mai faɗi an rufeshi da Cling film. Sai da ta ɗibi shinkafar daidai cikinta a plate sannan ta saka coslow tare da naman da take so kana ta kwashi komai ta watsa kan shinkafar ta rufe, bata yiwa Salima alƙawari ba don haka zata rama abun da mijinta ya mata ɗazu duk dama wannan kaɗan ya gani.

Tana cin abinci wannan karon ya shigo, sallaman da yayi ma a bakin ƙofa bata amsa ba, haka kuma ko arziƙin sannu da dawowa bai samu ba. Ta gabanta ya zo ya wuce ɗaki ya rage kayan jikinshi ya bar singlet da dogon wando kana ya dawo falo ya zauna don cin abincin. A lokacin har ta gama cin nata ta miƙe kenan zata kai plate ɗin kitchen ya kira sunanta.

“Juwairiyya.”

“Ya dai?” Ta amsa tana tsayawa a bakin ƙofa tana haɗe fuska kamar bata san me tayi ba.

“Ni da gidana da abincina ba zaki daina mini haka ba? Don na faɗa miki weakness ɗina kwara ɗaya shine zaki dinga amfani dashi wajen ɓata mini rai? Yanzu ke haka aka kawo miki da zaki bani shi haka? Menene laifina? Ko kuma aurenki da nayi mai kama da taimako shi yasa kike wulaƙantani?”

“Ka gama?” Ta tambayeshi tana mai buɗe ƙofa zata fice don aikinta yayi kyau, dama so take yi ranshi ya ɓaci kuma da alama ya kai ƙololuwa.

Bai ce komai ba ya rufe kular yana jin raɗaɗi a zuciyarshi, wai da gaske yau shi mace take yiwa haka amma ya kasa tankwarata? Ji yake yi kamar ya tashi ya lallasata amma baya son dukan mace, ba zai taɓa aikata haka ba. Wani lokacin sai ya ji kamar yace ta koma gida amma idan yayi haka manya zasu ce yayi gajen haƙuri tunda kwata-kwata yau ne kwana biyu da tarewan nasu. A yanzu ma ya fara dana sanin auren ina ga kuma in Tafiyar tayi nisa?

Yana zaune yana wannan tunanin ta dawo kana ta tsaya a kanshi tace,

“Ka kira mai gyara ya saita mini kayan kallona na gaji da zama haka shiru.”

Wani wawan kallo ya watsa mata wanda yasa cikinta sai da ya kaɗa amma ta tsaya kyam bata da niyyar matsawa. Miƙewa yayi da niyyar zai tafi ɗakin Salima ita kuma ta kare fuskarta da hannayenta ta ɗauka dukanta zai yi, zuciyarta na bugawa ya zo ya wuceta ya fita daga falon zuwa na Salima. A nan ne ta sauƙe ajiyar zuciya ta fara dariya a hankali amma dai ta tsorita, a wani gefe na zuciyarta sai ta fara jin tausayinshi domin da gaske ya taimaketa ne da ya aureta. Sannan ya so ya ƙi yarda da auren amma tayi blackmailing ɗinshi da maganar alƙawarin Hafiz ya kuma amince aka yi auren. Tabbas bashi da laifi kuma in ta tuna jiya ya bata haƙuri duk da cewa bata san ko don yana son jikinta ne yayi wannan doguwar sharhin ba. Alƙawari tayi a ranta daga yau zata daina kwaɓa mishi abinci guri ɗaya sai ya mata laifi, da haka ta tattara gurin ta kai kitchen akan in almajiri yayi bara zata bashi domin ta sani Muhammad ya tafi ɗakin Salima ce don ya ci abinci a can wanda ta wani gurin bata so hakan ba.

Muhammad yana shiga falon Salima ya samu ko’ina na tashin ƙamshi ga matar tashi tayi wanka tayi ado sai walwali take yi tare da ɗanta suna kallo.

“Sannu da dawowa Baban Hafiz, ya gurin aikin?” Ta faɗa tana mai russunawa daga zaune.

“Lafiya. Ki kawo mini abinci.” Shine kawai abun da ya faɗa yana mai zama a kan kujera ɗanshi ya tako zuwa gurinshi yana ɓangala mishi dariya.

“Ai na kai muku naku can, kuma yau na faɗa mata favorite ɗinka nayi akan tayi haƙuri kar ta haɗasu guri ɗaya.”

“Ba wannan na tambayeki ba, idan zaki bani abinci ki bani. In kema ba zaki bayar ba in fita waje in saya Allah Ya hore mini kuɗin da zan ciyar da kaina da abincin wajen.” Ya faɗi hakan ranshi na tafarfasa.

“Kayi haƙuri bari in je in kawo maka, Allah Ya huci zuciyarka.” Tana faɗin hakan ta shige kitchen ɗinta tana murmushin jin daɗi.

Abincin da dama ta ajiye dominshi ta kawo mishi a kan tray ta ajiye a kan Dinning table kana ta fara zuba mishi irin yanda yake so. Sai da ta gama ta faɗa mishi ya taso tare da yaron ya miƙa mata shi kuma ya zauna ya fara cin abincin yana ganin lokacin da take saka mishi ruwa a cikin kofi da juice ɗin karas. Nan take ya fara jin son ƙebancewa da ita wanda in dai ya tambayi na farkon zata amince, amma na biyun ne zasu samu matsala. Kawar da wannan tunanin yayi ya cigaba da cin abincinshi amma zuciyarshi na ga Juwairiyya yana neman hanyar da zai gyara mata zama a gidan nashi.

Sama-sama Salima take mishi hira yana amsawa har ya gama cin abincin kana ya zauna a cikin falonta yana wasa HJ. Sai da ya tabbatar yayi awa ɗaya sannan ya koma ɗakin Juwairiyya ya sameta ta cika tayi fam.

“Yau ma cin abincin ne yasa ka daɗe haka?”

Bai kulata ba ya ɗauki rigarsa ya saka kana ya fice gaba ɗaya daga gidan. Tana ganin fitanshi ta ji kamar ta bishi ta masifeshi amma sai ta tuna Salima zata iya jin su kuma zata ɗauka kishi take yi da ita, ita ba kishi take yi ba kawai so take yi idan ta kwaɓa abincin ya ci shi haka nan don ta huce haushi, amma sai ta lura ya samu hanyar zuwa gurin matarshi ce. Wa ya sani ko ba’a cin abincin kawai zuwan nashi yake tsayawa ba? Ba haka ta so ba domin tayi niyyar takura mishi ne sai kuma ya samu hanyar ɓullewa. To dai daga yau zata hana wannan zuwa cin abincin domin ta daina haɗa mishi guri ɗaya ko ta ɗiba ta bar mishi saura.

Wannan karon bata je sashen Salima tayata abinci dare ba domin tasan ba zata bari ta tayata ɗin ba. Tana nan zaune Salima ta kawo mata abinci ta bita da godiya sannan ta ware abincin kamar yanda Muhammad yake so kana ta ci nata ta shiga sallan isha.

Muhammad bai dawo ba sai ƙarfe takwas da rabi, tana daga can ɗakinta tana sauraron shigowarshi falo amma sai ta ji shiru, hakan yasa ta fita zuwa falon don dubawa ko wani abu ne ya faru. Wayam babu shi babu alamunshi amma da ta kasa kunne sai ta ji muryarshi a falon Salima yana wasa da HJ, wani malolon baƙin ciki ne ya zo ya tokare mata a wuya amma ta haɗiye ta koma cikin ɗakinta. Tana danna wayarta ta jiyo sallamar Salima ta amsa kana ta fito da fara’a a fuskarta.

“Baban Hafiz ne yace in yi kiranki zai yi magana da mu.”

“Yana ina?” Ta tambaya duk da cewa ta san ina yake.

“Yana can falona yana wasa da masoyinki.” Salima ta bata amsa tana yi mata jagora itama kuma Juwairiyya ta bita a baya.

Tana shiga ta sameshi zaune a kan kujera itama ta nemi kujeran ta zauna amma sai ta hango Salima zaune a ƙasa can nesa dashi tana sunkuye da kai kamar mai neman tuba. Haushi ne ya turnuƙe Juwairiyya domin ta sani haka Muhammad ya ɗorata a kai amma ita ba zata bi ba, wannan nuna ikon nashi da gadaran ba dai a kanta ba. Ƙarshe gyara zamanta tayi ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana challenging ɗinshi da ido ko zai ce itama ta sauƙa ƙasa. Abun da Juwairiyya bata sani ba shine wannan zama a ƙasan Salima ce ta ɗaurawa kanta wanda shi Muhammad duk da son girmanshi ya ce ta bari amma ta nuna mishi ya fi ƙarfin ya zauna a kan kujera itama ta zauna in har yayi kiranta ne da niyyar mata magana.

Gyaran murya ya fara kana ya ajiye HJ a ƙasa ya tafi gurin mamanshi yace,

“Na so taraku guri ɗaya in yi magana da ku tun ranar da kika tare amma sai Allah bai yi ba, hakan yasa na ɗaga zaman zuwa yau domin gobe ke Salima zaki karɓi girki na gama kwana ukun a ɗakin Juwairiyya. Ba sai na muku magana kan haɗin kai ba saboda na san baku da wannan matsalar, abun da zan faɗa muku shine ku zauna zaman lafiya domin a yanzu da kuke guri ɗaya zaku ga abun da bakwa so game da junanku, domin kuwa bahaushe yace zo mu zo mu saɓa ne. Duk da cewa sa’anni kuke Salima ita ce babba kuma uwargida a gidan nan, ina fatan ke Juwairiyya zaki bata girmanta sannan in ta miki ba daidai ba ki sameta kuyi magana tsakaninku. Haka kema Juwairiyya ina fatan zaki bawa Salima girmanta sannan in ta miki abun da bai miki ba ku sasanta kanku. Sai kuma batun kwana, ku yanke yanda kuke so.”

Duk wannan magana da Muhammad yake yi Juwairiyya ta ɗaukeshi ne a matsayin surutu domin a wani auren wucin gadin ne za’a zo ana wani wai batun haɗin kai da bada girma. Wayarta da yake hannunta ta fara dannawa tana jin lokacin da Salima ta buɗi baki tace,

“Wanne kika zaɓa mana ƴar’uwa? Kwana biyu ko ɗaya?”

“Ni kowanne ma, in kina son duka kwanan ma na bar miki ni bani da matsala.” Ta faɗi hakan tana kallon Muhammad ta wutsiyar ido wanda ta san kalamanta lallai ne ya ɓata mishi rai.

Amma ko hakan ya ɓata mishi rai bai nuna ba domin ko kallonta bai yi ba hankalinshi na kan Salima da take walwali tayi shiga ta alfarma kamar zata je liyafa. Hakan yasa Juwairiyya ta raina kanta domin tun da ta zo gidan Muhammad ta daina kwalliya a cewarta bata ga mijin da zata yiwa ba. Sannan kwalliyan da zata yi zai jawoshi gareta ne kuma ita ba haka ta tsara ba, wannan dalili yasa da ita da Nanayo mai aikin Salima tsafta ce kawai zata rabasu amma ba dai kwalliya ko gayu ba.

“Yau me yayi zafi? A barshi a kwana biyu Allah Ya haɗa kanmu ya ƙara mana zaman lafiya da fahimtar juna.” Faɗin Salima tana murmusawa fuskarta cike da annuri.

“Ameen.” Muhammad ya amsa kana ya dubi Juwairiyya da take jin zaman ya gundureta yace “Zaki iya tafiya.”

“Kai kuma fa?” Ta samu kanta da tambaya ko dai ya manta a ɗakinta yake?

“Idan na gama abun da zan yi zan shigo.” Ya bata amsa yana bin Salima da ido wanda hakan ya ƙara harzuƙa Juwairiyya wato cin amanarta zai yi?

“Idan kayi dare rufe ƙofata zan yi don bana son barinta a buɗe.”

“Babu matsala. Mu kwana lafiya.” Ya faɗi hakan yana dubanta briefly kana ya mayar da dubanshi ga Salima ya ce, “Salima sako mini juice ɗin ɗazun nan.”

Juwairiyya tana jin hakan ta fice daga falon ranta a ɓace wai ita Muhammad zai wulaƙanta don ta nuna mishi kulawa kaɗan? To anyi na farko anyi na ƙarshe, nan gaba ko a bola yace zai zauna babu abun da zai dameta. Amma ta wani gefen hankalinta bai kwanta ba domin ita kanta gayun Salima ya burgeta domin tana ganin lokacin da ta miƙe tana tafiya mazaunanta na juyi Muhammad na bin su da kallo, nan take sai ta raina kanta domin ramar da tayi ya tafi ta kaso mafi tsoka na albarkatun da suke jikinta ga baƙin da ta ƙara yi saboda masifar school. To wai me yasa take haɗa kanta da Salima? Wannan tambaya ne da ta yiwa kanta a lokacin da take kwanciya a kan gado hawaye na taruwa a idaniyarta.

Mum Fateey

Wannan karon Juwairiyya bata yi bacci ba tana jiran dawowan Muhammad har goma ta wuce sannan ya shigo da sallama a bakinshi. Bata amsa ba ta jeho mishi tambaya,

“Sai yanzu?”

“Eh.” Ya bata amsa a taƙaice kana ya fara cire kayanshi wanda yasa Juwairiyya ta kawar da kai don ta lura ba damuwanshi bane wai in ta ganshi haka nan.

Towel ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunshi ya shiga wanka Juwairiyya na kawo tunani kala-kala a ranta na dalilin wankan nashi. Sai da ta daina jin ƙarar ruwa sannan ta kwanta tana neman abun da zata faɗa don ta nuna mishi bata son zamanshi a ɗakin Salima a hakan kuma bata son yayi tunanin ko kishinshi take ji.

Yana fitowa ta runtse idanunta kamar mai bacci har ya gama shiri ya kashe musu wuta ya zo ya kwanta a gefenta. Daga gurin da take tana jin ƙamshin sabulunta da yayi wanka dashi tana jin daɗin shaƙarshi, lallai ya kamata ta hanashi wanka dashi tunda ba sabulun maza bane.

Yau ko danna wayar bai yi ba dalilin bacci da yake ji saboda ya kwaso gajiya daga office gashi zaman da yayi a can ɗakin HJ ya wahalar dasu, don ya ƙi yin bacci sai ɓarna yake yi har ya taho nan Salima na goye dashi tana jijjigashi don yayi baccin. Don haka yana kwanciya bacci yayi awon gaba dashi duk da cewa ya so yayi tarayya da Juwairiyya amma ba zai iya da baƙaƙen maganganunta ba.

Ita kuma tana can gefe tana jin sautin numfashinshi har ya canja alamar yayi bacci, tashi tayi zaune tana leƙen fuskarshi wanda ita kanta bata san dalilin da yasa tayi hakan ba. Baccinshi yake yi bil hakki wanda hakan ya ɓatawa Juwairiyya rai, wato shi bashi da damuwan komai shine daga kwanciyarshi har yayi bacci? Ita awa nawa tayi tana jiranshi? Hannunshi ta bubbuga ya farka.

“Juwairiyya lafiya? Me ya faru?”

“Ka tashi na kasa bacci.” Ta faɗa tana harɗe hannunta akan ƙirjinta.

“To ya za’a yi kenan?”

“Mu yi hira.”

Shiru yayi yana nazarinta, lallai yau ya ƙara tabbatarwa Juwairiyya tana da rigima, in ba rigima ba ita ce jiya ta furta da bakinta akan ya daina shiga harkarta sannan ba zasu yi zaman lafiya ba, sai gashi yau ta tasheshi a bacci wai su yi hira.

“Ina jinki.” Ya faɗa shima yana tashi zaune ya zuba mata idanu.

Inda-inda ta fara yi ta kawar da nata idanun daga barin kallonshi don sai ta ji ba zata iya haɗa ido dashi ba, ta wani gurin kuma jikinta ne yake nemanshi amma Allah Ya kasheta ba zata nuna mishi ba don an yi na ƙarshe.

“Sai da safe.” Tace dashi tana mai kwanciya tare da juya mishi baya.

Shima kwanciyar yayi don bacci yake ji kuma baya son fitinan Juwairiyya da tsakar daren nan. Tana jin ya kwanta ba tare da nuna damuwa ba sai taji duk jikinta yayi sanyi wato dama bai damu da ita ba?

Shi ya tasheta sallan Asuba ya tafi masallaci yana dawowa ya samu tayi salla tana addu’a. Da yake Saturday ne babu aiki sai ya koma ya kwanta, itama Juwairiyya bin shi tayi ta kwanta don bata ga me zata yi ba bayan baccin. Yana wanka a banɗaki ƙarfe goman safe ta farka tana hamma tana miƙa kamar wata macijiya a haka ya fito ya sameta, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kanshi ya cigaba da shiri don zai fita cikin gari sannan zai isa gidansu gaishe da Babanshi.

Har ya gama shiri tana zaune a kan gadon wai jira take yi ya fita gabaɗaya tayi harkokinta, idan kuma ta tuna abunda tayi jiya da dare sai ta ji haushi ya kamata. Ta sani son kasancewa da ɗa namiji ne yake damunta amma in ba haka ba bata ga dalilin da zai sa wai ita ta tashi Muhammad a bacci tace su yi hira ba, sai yanzu da gari ya waye itama hankalinta ya dawo jikinta ta gane katoɓarar da ta aikata.

Yana gamawa ya dubeta sai a lokacin ya ga irin wargajewar da tayi sai dariya ta kamashi amma ya murmusa kawai ya ce,

“Zan fita cikin gari, ina tunanin daga yanzu kuma na miki sallama sai nayi kwana biyu a ɗakin Salima kamar yanda kuka daidaita. Singlets da boxers ɗina ki wankesu don naga sai tarasu kike yi a banɗaki kuma bana son sai sun taru a wanke.”

“Muhammad yau ni zan wanke maka boxers? Lallai ma! Akan cewa baka da hannu ne ko an faɗa maka abun da ya kawoni kenan wato wankau?”

“Na ga kema kina da washing machine so ba zai baki wahala ba, kuma Salima ita take wanke mini.”

“Yauwa gwanda da ka faɗi haka, Salima kace matar da kake so kake zuwa ɗakinta ku yi duniyancinku sai ka ga dama ka zo nan. Ba zan iya wankewa ba.”

“Haka kika zaɓa?”

“Eh.”

“Shikenan.” Yana faɗin hakan ya shiga banɗaki ya kwasosu a cikin bucket bayan watsa musu detergent ya tafi tsakar gida ya kunna famfo zai wanke.

Salima da take ankare dama tana sauraran fitowarshi don ta mishi sallama ta leƙa ta window ta hango mijin nata zai yi wanki, wankin me zai yi to? A ranta kuma tace ko pant ɗin Juwairiyya yake wankewa zata karɓa saboda ta haramta mishi wankin ko handkerchief ne a gidan. Da sauri ta fita dama HJ na bacci ta isa gurinshi ta tsugunna a cikin rana tana cewa,

“Ina kwana Baban Hafiz.”

“Lafiya kalau, ina abokina?”

“Ya koma bacci ɗazun nan, yana ta jiran ka fito har yayi bacci.”

“Yau nima baccin safen nayi domin kwana biyu ina yawan zirga-zirga. Amma zan dawo da wuri ya jirani.” Faɗin Muhammad yana ƙoƙarin tattare hannun rigarshi don fara wankin amma Salima ta dakatar dashi ta hanyar riƙo hannun nashi a hankali.

“Me zaka yi?”

“Wankin boxers ɗina.”

“Ina da rai zaka yi wanki a gidan nan Baban Hafiz? Ashe ba zaka iya kirana ka sakani in yi maka ba alhali ina da lafiyata kuma kullum ni ce nake maka? Ko dai laifi na yi kake son horani da haka?”

Abunka da mai son girma da kuma submissive wife nan ya karkaɗe hannunshi ya matsa gefe kaɗan ya ce,

“Baki mini laifin komai ba. Hasalima so nake yi yau in gwada wankin amma tunda zaki yi gashi nan.” Bai saba da yin ƙarya ba amma yau ya gwada kaɗan don kar ran kowa ya ɓaci.

Ya sani Salima ce mai wankewa amma ya za’a yi a ɗauko na kwanan kishiyarta a bata ta wanke? Baya son rashin adalci da ƙeta kuma ba zai fara tun yanzu ba, amma tunda ta nuna zata yi shikenan ta hutar dashi da kanta ba tare da ya sakata ba.

Da haka ya shiga motarshi ya kunna Salima ta buɗe mishi gate ya fita, tana mishi sallama ya leƙo da kanshi ya ce,

“Allah Ya miki albarka.”

“Ameen.” Ta amsa cikin jin daɗi kana ta rufe gate ta nufi bakin famfon ta ɗauki bucket ta wuce dashi sashenta.

A ranta kuma cewa take yi Juwairiyya ba zata zo ta kwance mata ƙullin da ta daɗe tana yi saboda rashin hankalinta ba, duk abun da ta san zai shafeta zata gyarashi, in tsakaninsu ne can suyi ta fama dama hakan take so. Wannan abu ta tayi ta san ya ƙara mata girma a gurin Muhammad domin ba kasafai yake mata addu’ar ba sai ta burgeshi matuƙa, to gobe ma bata ƙi Juwai uwar raini ta ƙara yin wani abu ita kuma ta gyara a bita da addu’a ba.

Duk abun nan da aka yi a idon Juwairiyya wacce ta ɗan ji haushin Salima na shigarta sabgarta, don me yasa ba zata barshi yayi ba?

“Mu kuma Allah Ya tsine mana ko?” Ta faɗi hakan tana sake labulen windown kana ta koma cikin ɗaki ta faɗa wanka.

A falo ta tarar da karyawanta na soyayyen kwai da bread sai kuma gwangwanin madara da milo har da sugar wanda zai yi kwano ɗaya an saka mata a cikin container mai kyau. To sun san zasu bata don me yasa basu faɗa mata ba ta kashe kuɗinta a banza? Sannan indomie ba zata fasa cin shi ba sai dai su da basa so su daina ci. Tana karyawan Salima ta shigo hannunta ɗauke da bucket tare da HJ wanda ya tashi daga bacci suka gaisa cikin mutunci da fara’a.

“Masoyi gaskiya kayi nauyin baki, wai har yau ka kasa ko kiran sunan mamanka?” Faɗin Juwairiyya tana jawo yaron kan cinyarta.

“Ina tunanin babanshi ya ɗauko don dai nikam nayi magana da wuri.” Salima ta faɗa tana dariya.

Jin an ambaci sunan Muhammad ya rage fara’ar da ke fuskar Juwairiyya wacce ta tuna abun da ya faru a jiya da kuma yau da safe. Hakan yasa ta canja musu hiran ta ce,

“Nikam Maman Masoyi ina zan samu mai aiki ne? Don gaskiya idan na koma makaranta aikin zai mini yawa dole zan buƙaci mai tayani.”

“To gaskiya sai dai in sa Nanayo ta duba miki a cikin unguwa.”

“To shikenan nagode.”

Kamar yanda Muhammad yayi alƙawari yau ya dawo da wuri tun bayan la’asar yana ɗakin Salima sai sallah maghrib ne ya fitar dashi, kafin ya dawo Salima ta gama abinci ta kaiwa Juwairiyya wacce zaman kaɗaicin ya fara damunta, sai a lokacin ta gane shiga da ficen Muhammad a ɗakinta ba ƙaramin ɗebe mata kewa yake yi ba. Ta ɗauka Salima zata tayata hira kaɗan amma sai ta ga ma kamar sauri take yi zata koma gurin mijinta da ɗanta, kenan ta zauna ita ɗaya kamar mayya? Danna wayar har tayi ta gaji gashi ba’a saita mata kayan kallonta ba balle ta fara sana’ar wato kallon Korean series.

Har ta kwanta ta ji ana buga mata ƙofa da yake tun bayan isha ta kulle, tana buɗewa ta ga Muhammad ne tsaye hannunshi ɗauke da baƙar leda ya miƙa mata ya ce,

“To sai da safe. Ko kina buƙatar wani abu?”

Kamar tace ya zo su kwanta domin sautin numfashinshi kaɗai zai rage mata wani kaɗaicin amma ta datse harshenta ta girgiza mishi kai kana ta rufe ƙofar a fuskarshi.

Girgiza kanshi kawai yayi ya koma side ɗin Salima wacce take jiranshi su ci roasted fish ɗin da ya sayo musu, suna ci take bashi labarin Juwairiyya tana neman mai aiki.

“To har zan ce mata ga Nanayo ta dinga mana aikin dukkaninmu tunda gidan namu ƙarami ne amma sai nayi shiru nace sai na faɗa maka tukun.”

“A wannan ɗan gidan ba zamu ɗauki masu aiki biyu ba, kema yanzu aikin ya ragu miki zaki iya yinshi ke kaɗai ba tare da kin nemi taimakon mai aiki ba.” Muhammad ya amsa don ba zai iya biyan masu aiki biyu ba itama ta Nanayon za’a sallameta.

Cikin Salima ne ya kaɗa domin kar garin ɗanawa Juwairiyya tarko ta sanya ƙafarta a ciki, don haka ta marairaice fuska ta ce,

“Ayya Baban Hafiz da dai ka bar mana Nanayon saboda bayan aiki muna aikanta shago da kasuwa idan buƙatan hakan ya taso, wani lokacin kana can office ba zaka samu daman dawowa ka miƙo mana abun da muke buƙata ba, to ka ga ko a nan ta taimaka. A taimaka a duba mana please.”

“Shikenan, amma ba za’a ƙara ɗaukan wata ba, guda ɗayar ta isheku sai a ƙara mata kuɗi tunda aikin ma ya ƙaru.”

“To mun gode Allah Ya kara girma da arziki.” Ta faɗa da murnanta kamar wani babban kyauta ya bata.

Suna gama ci ta kawo mishi roba ɗan babba da ruwa a jug tare da handwash ya wanke hannunshi kana ya shiga ɗaki ya wanko bakinshi a toilet ya dawo falo ya zauna suka cigaba da hira tana kwance da a jikinshi tana tsokanoshi da haka ya biye mata suka wuce aza room.

Juwairiyya tana kwance akan gadonta tana jiran bacci ya kwasheta bayan ta cakali kifin da Muhammad ya kawo mata ta fara jin muryar Salima kamar wacce take wani abu, zumbur ta tashi ta zauna ta kasa kunnenta jikin window wanda yake ta bayan ɗakunansu a nan ne ta sake jin abun da yasa ta ji cikinta ya hautsine kifin da ta ci yana neman dawowa ta bakinta. Da gudu ta miƙe ta nufi banɗaki sai dai kafin ta buɗe toilet seat ɗin har ta fara amai babu ƙaƙƙautawa, kenan abun da suka yi ita da Muhammad shi yake yi da Salima? Wannan tambayar da tayi a zuciyarta shi yasa ta ƙara jin wani aman ya taso a makwogoranta ta cigaba da kelayawa a ƙasa kamar ranta zai fita.

A can ɗakin kuma Muhammad ne ya rufe bakin Salima wacce ta buɗe murya tana sambatu a karo na biyu a daren.

“Ke lafiyanki kuwa? Zaki tayar da yaron nan.”

“Kai ɗinne yau kamar an ƙara maka ƙarfi.”

Murmusawa kawai yayi yana kallon Salima da ke aika mishi da wani shu’umin murmushi mai ƙara mishi kaimi wajen faranta mata. A gurin Salima kuwa fata take yi Juwairiyya ta jiyo su domin ba’a mata bata rama ba kuma don ita tayi hakan.

Tun asuba Muhammad ya kwankwasawa Juwairiyya wacce ta kwana ido biyu dalilin aman da tayi ya galabaitar da ita. Magana tayi mishi akan ta tashi sannan ya wuce masallaci ita kuma ta faɗa banɗaki wanda ta wankeshi tun jiya da daren.

A inda tayi sallah bacci ya kwasheta sai wajen goma na safe ta tashi da wani matsanancin yunwa har jiri na ɗibanta. Da yake ta san falonta a kulle yake sai ta duba bakin ƙofar ko Salima ta ajiye mata abincinta amma wayam bata ga komai ba, hakan yasa ta shige kitchen ɗinta ta haɗo golden morn mai ɗumi ta dawo falo tana sha a hankali kamar yaron goye don kwata kwata bata jin taste ɗinshi a bakinta. Bata iya shanyewa ba ta mayar kitchen ta wanke kulolin da Salima ta saka mata abinci sannan ta koma ɗakinta ta share ta shiga wanka, tana wankan ta jiyo muryar Muhammad a ɗakin yana kiran sunanta. Amsawa tayi daga ciki tace tana fitowa amma sai kawai ta ji ya buɗe ƙofar yana kallonta.

“Zan fita ne ina sauri ba zan iya jiran sai kin gama wankan ba. Akwai abun da kike buƙata?”

Juwairiyya da tayi saurin tsugunnawa tun lokacin da ya buɗe ƙofa tayi saurin cewa,

“Babu.” Tana gama faɗin hakan ya ja ƙofar ya rufe yayi tafiyarshi.

Ta ɗauka zai tsaya yayi ta kallonta kamar yanda Hafiz yake mata amma sai ta lura kamar bai damu da jikin nata ba. Nan da nan ta ji ta raina jikinta da ta tuno siffar Salima, ga fari, ga ƙirji a cike sannan ga manyan cinyoyi. Ita kuma fa? Ƴar baƙa, wacce damuwa yasa ta rame duk ƙiban nata ya tafi da ƙirjin da kuma cinyoyin. Wai me yasa take haɗa kanta da Salima ne? Kuma me yasa take son burge Muhammad da jikinta? Saboda bata son ya rainata ko ya ɗauka bata kai matsayin mace ba! Tana son in zata mishi kwalele ya kasance da jiki mai kyau mai ɗauke hankali zata yi hakan. Kawar da wannan tunanin tayi a ranta domin ta lura idan taci gaba da yi hankalinta ba zai kwanta ba sannan zata ƙarawa kanta damuwa ne kan wanda take ciki.

Wunin ranar ma bata ga idon Muhammad ba har dare yayi, sai can da dare ya kwankwasa mata ƙofa ya mata sai da safe kana ya juya ya koma inda ya fito. Yanzu kam kaɗaicin ya fara damunta domin ta lura Salima bata zuwa mata hira idan Muhammad ne a ɗakinta, ita kuma bata son zuwa gurin da suke gudun kar su yi tunanin tana neman cusa kanta ne a gurinsu kuma abun mamaki babu wanda ya gayyaceta cewa ta zo su yi hira, ita kaɗai ɗinta take zaune a ɗaki kamar mujiya har ta fara marmarin gari ya waye Muhammad ya dawo ɗakinta. Samun kanta tayi tana murmushi ta kwanta tare da yin addu’ar bacci.

Washe gari da fara’arta ta farka ta kimtsa gurinta da wuri kuma bata koma bacci ba, a ranar kuma Muhammad zai tafi Office ya shigo ya mata sallama kana ya miƙo mata kuɗi yana cewa,

“Ga kuɗin cefene idan kina buƙatar wasu kayan abinci kuma akwai a store ɗin Salima ki je ki ɗiba.”

Ɗan guntun annuri da kuma fara’ar da ke fuskar Juwairiyya ya ɗauke ta dubeshi a tsanake ta ce,

“Kana nufin kullum in zan yi girki sai na je gurinta na karɓa?”

“Eh, amma zuwa wani lokaci ne idan na samu sarari zan miki shopping ɗinki ki adana a gurinki.”

Ranta bai so haka ba, hakan yasa ta tuno da cewa ai ranar ma da ya fara kwana a ɗakinta Salima ya bawa kuɗin cefenen nata ta bata, wato ita bata da darajar da zai zo ya miƙa mata da hannunshi?

“Shima kuɗin cefenen ka kai mata zan je in karɓa.”

“Ban gane ba.” Ya tambaya don bai ga dalilin da zai sa ta ƙi karɓa ba alhali gashi nan a hannunshi yana miƙa mata.

“Eh saboda baka san darajata ba, ranar da ka fara kwana a nan ma ita ka bawa ta bani haka tun da na zo sai jiya ta kawo mini kayan tea wanda yau ma gashi kana cewa in je in ɗibi kayan abinci a gurinta. Tunda komai a hannunta yake sai ka bata wannan ɗin ma ba zan karɓa ba.” Ta ƙarisa maganan a harzuƙe.

“Batun kayan tea duk na gidan ne ya ƙare ban saya ba sai shekaran jiya na barshi a mota ta ɗauka ta raba muku da safe. Ranar kuma kina can cikin ɗaki ne ita kuma tana falo na bata ta ajiye miki. Na yau kuma na faɗa miki zuwa gaba ne idan an yi salary zan saya miki naki ki ajiye.”

“Ba zan karɓa ba, ka kai mata.” Tana faɗin hakan ta shige cikin ɗakinta ta barshi a nan tsaye.

Muhammad juyawa yayi da kuɗin a hannunshi ya kaiwa Salima wacce bata yi tsammanin hakan ba, a nan take tambayarshi don meyasa ba zai bawa Juwairiyya a hannunta ba.

“Ita tace a dinga baki.” Ya bata amsa kana ya sa kai ya fice ta bishi ta buɗe mishi gate ya fita.

Da murnarta da rufe gate ɗin sannan ta nufi ɗakin Juwairiyya don neman full story ɗin. Da sallama ta shiga ta samu Juwairiyya ta dawo falo tana zaune tana danna wayarta.

“Wa’alaiku mussalam. Yau kuma ga idon Maman Masoyi a ɗakina, tun da kika samu mijinki kika shareni aka daina zuwa mini hira.” Ta ƙarisa maganan cike da tsokana.

“Ayya kema kin san halin mutumin naki da zarar ya nemi abu bana kusa sai faɗa, shiyasa yau kika ganni cikin farin ciki domin zai dawo gurinki ni kuma zan samu sarari na kwana biyu.” Ta yi ƙaryar banza.

“Ke dai kina tsoron wannan bawan Allahn, ni ban ga abun tsoro da zaki bari yana miki faɗa kullum kamar bakya mishi ƙoƙari ba.” Juwairiyya ta faɗa cikin tausayawa.

“To ya zan yi haka muka fara rayuwa ba zan iya mishi musu ko hargowa ba, amma ke ce daidai shi bakya iya bari.”

“To ban saba da baƙar halin irin nashi ba, duk mazan da na aura masu sanyin hali ne shiyasa ba zan lamunci tsawa ba.”

“Gashi yace in kawo miki kuɗin cefene nace da ya baki da hannunki ai ke matar gida ce.” Ta ɗauko zancen da dama shi yasa ta shigo.

“Kawai na ga kece uwargida komai a hannunki yake shiyasa nace kuɗin cefenen ma ya baki zan dinga ƙarba.” Ta faɗa mata kaɗan daga ciki don tana tunanin in ta faɗa mata dukkan abun da ya faru zata ɗauka kishi take yi da ita tana son matsayinsu yayi ɗaya duk da cewa ita barin gidan zata yi.

“To amma hakan ba zai takuraki ba?”

“Babu komai ai ke ce matar gidan sai yanda kika yi damu.” Juwairiyya ta ƙara tura kanta a rami.

“To shikenan tunda haka kike so, ga kuɗin cefenen anjima Nanayo zata zo ta miki aiki sai ki bata ta sayo miki abun da kike buƙata.”

“Da kin barta sai na samu tawa kawai.”

“Oh bai miki maganan bane? Ai shi yace ta ringa mana mu duka akan ba zai ɗauki masu aiki har biyu a ƙaramin gida irin namu ba.”

“Akan me?” Juwairiyya ta tambaya ranta har ya fara ɓaci shi Muhammad kam komai ɗin shi babu daɗi?

“Wallahi ban sani ba, amma ko biyan kuɗin ne zai mishi yawa sai Allah. Ki tambayeshi dai idan ya dawo.”

“Ki kyaleni dashi Allah Ya dawo dashi lafiya. Idan kuɗin ne ba zai iya biya ba ni zan dinga biyanta ba zai gagara ba.”

“Ni dai kar kuyi sa’insa akan haka ya korar mini Nanayo.” Faɗin Salima tana kyafta idanu, bata ƙi su hau sama su rikito ba akan maganar amma kar dai yayi fushin da zai sa ta rasa Nanayo.

“Kar ki damu ba zai kai haka ba, idan kuma ya nace ba za’a ɗauko mini wata ba sai kici gaba da zama da Nanayon ni na haƙura.”

“To ke meyasa ba zaki bari ta mana ita ɗaya ba?” Salima ta tambaya don ta fara tunanin ko Juwairiyya ta gane shirin da take yi ne in sun haɗa mai aiki ɗaya.

“Bana son mai aiki ɗaya tana zagaye a tsakanin mu don kin san wasu suna da munafurci bana son muna zaman lafiya kuma ya kasance an fara shiga tsakanin mu.”

“Eh to da gaskiyanki, amma dai Nanayo bata da laifi. Tun in amarya muke tare har yau shi kanshi Baban Hafiz yana yabon hankalinta.”

“Mu bari dai ya dawo in mishi magana duk yanda ake ciki zaki ji ni.”

Da haka suka yi sallama Salima ta koma ɗakinta wai zata yi baccin hantsi ita kuma Juwairiyya mood ɗinta ya canja daga farin cikin dawowar Muhammad gurinta zuwa jiranshi da masifa a kan mai aiki.

“Zaka zo ka sameni.” Ta faɗa tana karkaɗa kafanta.

Mum Fateey 👌

Ƙarfe biyu da wasu mintuna Muhammad ya dawo gida ya tasamma ɗakin Salima wacce ita tayi girkin rana, a can ya ci abincinshi har yake bata labarin wani scholarship na ƙarin karatu da zai iya samu amma ta tayashi da addu’a Allah Ya tsaga da rabonshi.

“Allah Ya nufa da rabonka Baban Hafiz. Allah Ya ga kyakkyawar zuciyarka da ƙoƙarinka kan iyalinka Ya baka wannan dama. Allah Ya biya maka dukkan buƙatunka na alkhairi.” Ta cigaba da kwararo mishi addu’a yana amsawa da Ameen yana murmusawa cikin jin daɗi.

Sai yamma liss ya dawo ɗakin Juwairiyya a lokacin tana kitchen tana girkin dare, tana kallon lokacin da ya fito daga ɗakin Salima ya shiga tata amma ko uffan bata ce mishi ba, a zuciyarta kuma tana ta hararo abubuwan da zata faɗa mishi akan wannan mataki da ya ɗauka ba tare da ya shawarce ta ba. An kusa fara kiran sallah maghrib ta gama abincin ta zuba a kulolinta ta kaiwa Salima kamar yanda ta ga Saliman ta mata a cikin kwana biyar ɗin da suka zauna tare.

“Masha Allah yau zamu ci abincin amarya, to mun gode da ƙoƙari ga ƙamshi sai tashi yake yi tun kafin a buɗe kula.” Faɗin Salima kenan tana karɓan tray ɗin daga hannun Juwairiyya ta ajiye a kan dinning table ɗinta.

Kamar wawuya Juwairiyya ta washe baki tana jin daɗin yabon da aka mata kana ta yiwa Salima sallama ta koma kitchen ta ɗauki nasu ita da Muhammad ta kai falonta ta ajiye akan center table da yake ita bata da gurin ajiye dinning table a falon nata. Muhammad ta gani a tsugunne wajen kayan kallonta yana haɗawa wanda hakan yasa zuciyarta ta mata daɗi amma da ta tuno abun da yake gabansu sai ta gimtse fuska ta zo ta wuceshi ta shige ɗaki ta faɗa wanka. Tana cikin wankan ya shigo har cikin banɗakin ya fara alwala a sink ba tare da yace mata komai ba. Ita ce da ta durƙushe a guri ɗaya ta harareshi ta ce,

“Kai baka san menene privacy ba? Yanzu in ka shigo ka samu ina wani abu ne ba wanka ba fa?”

“Sai nayi abun da ya kawoni in fita.”

Don tsabar takaici sai ta kasa cewa komai ta wani gefen kuma daɗi ta ji a zuciyarta da ta lura yana satan kallonta ta wutsiyar ido. Yana gama alwalar a sink ya fice zuwa masallaci ita kuma ta ƙarisa wankanta ta fito ta nemi wata comfortable doguwar riga ta sanya ta shafa mai shikenan ta gama kwalliyar karɓa miji, to Muhammad ɗin da bata son zata yiwa kwalliya?

Tana zaune a falo ya dawo ya shige ɗakinta, minti kaɗan ya fito bayan ya rage kayan jikinshi ya zo ya wuceta ya tafi ɗakin Salima. Sauƙe labulen window tayi bayan ta ga shiganshi, tabbas ya tafi ne cin abinci. To me yasa yau ba zai duba cewa bata jagwalgwala abincin ba? Me yasa kuma in ta jagwalgwalan ba zai ci ba tunda ba dotti ta saka a ciki ba? Tana wannan zancen zucin ne ya dawo ya zauna a kujerar da take kai ya ce,

“Kunna mini TV zan kalli News.”

“Baka da hannu ne? Tukunna ma daga ina kake?”

“Gurin Salima, wani abu ne?” Ya tambayeta yana nazarinta don ya lura kamar yau ma sai sun yi rigima kuma jira yake yi lokaci yayi itama ya saita mata hanya ta bi.

“Na san daga ina kake, me kaje yi a can alhali yau girkina ne? Shekaran jiya da jiya da kake gurinta a ƙofar ɗakina kake tsayawa baka ko shigowa ciki sai ni ce yau zaka tafi ɗakinta ka zauna a can?”

“Da ban san halinki na rigima ba da sai in ce kishina kike yi, amma duk da haka ina mamakin yanda aka yi baki san me na je yi ba. Abinci na je ci a inda ake darajani ake kuma ɗaukana a matsayin mai kawo abincin.”

 Har ta buɗe baki zata ce mishi ta daina jagwalgwala mishi abincin sai kuma ta fasa don kar ya ce neman sulhu take yi dashi. Maganar da ta wuni a kai shi ta ɗauko ta bar na abinci.

“Wai kai kace yarinyar da take mata aiki nima ta zo tana mini?” Ta tuhumeshi kamar wata lauya.

“Ni ne.”

“To gaskiya ni nafi son in ɗauko tawa ni kaɗai, in kuɗin ne ba zaka iya biya ba ni zan dinga biyanta.”

Muhammad yayi shiru yana kallonta da ɗan mamaki a fuskarshi can ya ce,

“Ba zaki biya ba kuma ba za’a ɗauko wata ba.” Da haka ya ci gaba da kallonta yana jiran me zata ce.

Kallonshi take yi itama amma ta lura kamar ranshi bai ɓaci ba ko kaɗan, kamar ya ɗauki hakan ne ma a matsayin funny. Idanunta ne suka ciko da hawaye domin sai a lokacin da gane bata da power na kanta balle gidan, sai a lokacin ta gane ta ɗauki ragamar rayuwarta ce kacokam ta sanya a hannun Muhammad kuma sai yanda ya ga dama yayi da ita. Sai a yanzu ta fara jin tsoron makomar rayuwarta domin ta sani duk wani rashin kunya da take mishi shima jira yake yi a zo gurin da zai yanke hukunci ya nuna mata iyakarta. Kamar ta sassauto da murya ta tambayeshi kamar yanda take yiwa sauran mazajenta amma sai ta ji ina!! Ba zata iya ba! Girman kanta da kuma kin wulaƙancin da zai iya mata idan ta kuskura ta sauƙe kanta take tsoro, ba zata bashi wannan daman ba, aiki kuma zata yi kayanta ba za’a haɗa kamar yanda yake so ɗin ba.

“Ta je ta yiwa Saliman ni na fasa.” Ta ce dashi tana hararanshi.

“To. Dama ina son faɗa miki ina neman wani ƙarin karatu da zan tafi in yi…” Kafin ya ƙarisa ta miƙe tana cewa,

“Wannan ba damuwata bace.” Da haka ta shige ɗakinta ta ja ƙofa gwaram ta rufe da ƙarfi kamar zata ɓallashi, tana shiga kuwa hawaye ya zubo kan kuncinta na baƙin cikin da take tunanin Muhammad ne sila.

Sosai hakan shi kuma ya sosa mishi rai don bai ga abun fushi a ciki ba da har yana mata magana akan abun farin cikin da yake nema tana cewa ba damuwarta ba ce. Shi da kanshi ya je ya kunna kallon ya ɗauki remote da yake cikin drawer ya fara canja channels, yana hakan ne ya ga Juwairiyya ta fito fuuu ta wuce ta fita, da ya saurara sai ya ji ta shiga ɗakin Salima don shi har ya ɗauka waje zata fita a nan ne zai nuna mata abun da ta manta game dashi.

Har aka kira sallan isha tana can ya fita sallah ya dawo yaci gaba da kallonshi lokaci ɗaya kuma yana waya da wani mutumin da yake tayashi neman karatun suna tsara yanda abun zai kasance.

Ita kuma Juwairiyya gani tayi zaman ɗakin ba zai mata daɗi ba kuma idan ta tafi ɗakin Salima ta barshi shi kaɗai hakan zai ƙona mishi rai, wato dai shima ya ji abun da ta ji!

Tana shiga falon Salima ta sameta tana waya amma bata ƙara cewa komai ba ta kashe wayar ta faɗaɗa fara’arta tana cewa,

“Amarsu ke ce?”

“Ni ce, na zo tayaki hira ne tunda kema kina zuwa mini.” Ta zauna a kujera mai fuskantar Salima.

“Ah ah to ina maigidan kika barshi? Baya son zama shi ɗaya, kar ya nemi wani abun bakya kusa a sami matsala.”

“Idan ba zai iya yi da kanshi ba ya bari. Kin san ya hanani ɗauko mai aikin nan?”

“Kai don Allah?” Salima ta faɗa tana gyara zama don sai lokacin ta ji she is interested da zuwan Juwairiyyan sashenta.

“Wallahi kuwa. Wai in bana son haɗin in haƙura, ni kuma nace na haƙuran sai ya gani ko aikin zai kasheni.” Ta faɗa cikin dakewa gata ita mai zuciya.

“Ai na sani da kyar ya yarda don shi ba’a tankwarashi. Kiyi haƙuri dai ta haɗa mana aikin.”

“Ai na rantse na haƙura, ina Masoyin nawa?” Ta tambaya tana kalle-kalle.

“Yau yayi bacci da wuri ina ta tsoron ma kar ya tashi mini da tsakar dare in ya gaji da baccin. Amma ni kam da kin koma wallahi, ba zai ji daɗi ba kin barshi shi kaɗai.”

“Dama ban yi don ya ji daɗi ba, shima ya ji ya ake ji idan ya takura miki.” Ta faɗi hakan kamar wacce ta kwatowa Salima ƴancinta.

Ita ko Salima murmushi kawai tayi kana ta kawar da zancen ta ɗauko musu wata har aka yi kiran sallan isha suka ji Muhammad ya fita, sai da ya dawo sannan Juwairiyya ta koma ɗakinta don gabatar da nata sallan. A bakin ƙofa tayi kiciɓis da Muhammad shi kuma ya taho sai fita, saura kaɗan ta faɗi yayi saurin kamota ta faɗa kan ƙirjinshi ya riƙeta tsam, fuskarshi babu walwala ya dubeta tayi tsuru-tsuru da ido ya ce,

“Ki dinga lura in kina tafiya, yanzu idan kika faɗi kika ji ciwo fa?”

“Ka sakeni.” Kawai tace dashi ta fara mutsul-mutsul zata kwaci kanta don yanda jikinta ya mannu da nashi sosai ya canja mata yanayi ta ji tana son su fi hakan, gudun kar ta bada kanta yasa ta nemi su rabu.

“Ki daina hakan don in na sakeki zaki iya faɗuwa ko ki buge kanki.” Ya ƙara riƙota da kyau don ya lura sam bata da wayon hakan, sannan ta wani gurin kasancewarta a jikinshi ya tayar mishi da tsohuwar yunwarshi da yayi kwana da kwanaki tana addabarshi.

Tsayawa tayi ta daina kokawar don tuni jikinta ya mutu tana jin numfashinta na sama-sama kamar baya isanta sannan idanunta suka yi nauyi ta lumshesu tare da ƙara langwaɓewa a jikinshi. Kamar a mafarki ta ji yana tafiya dasu ta buɗe idonta kaɗan ta ga ya shigo da su falon ya ja ƙofar ya rufe, sai a lokacin ta kalli tashi fuskar, sosai ya mata kyau don dama bata taɓa cewa yana da muni ba, hannunta ta kai kan laɓɓanshi wanda cikekken sajenshi mai taushi ya kewaye ta fara zagayesu da yatsunta biyu.

“Kar ki fara in kin san zaki gujeni daga baya.” Ta ji dakakkiyar muryarshi a saitin kunnenta wanda vibration ɗin muryar ya bi duk ilahirin jikinta ya je ya tsaya can inda ta fi buƙatarshi.

Kaɗa kai tayi don bata tunanin ko tayi magana sautin zai fito, buƙatarta a wannan lokacin shine ya zama babu wani hijab tsakaninsu, tana son kasancewa dashi har tana jin in bata aikata hakan ba zata iya zaucewa.

“Please.” Tace dashi tana tsayawa akan yatsun kafanta ta haɗe bakinsu guri guda.

Kamar jira yake yi ya ɗauketa yayi cikin ɗaki da ita, a wannan daren sai da ya kashe duk wani kishinta da yake dashi. Tana kwance a ƙirjinshi yana shafa kanta tayi wani miƙa ta haye kanshi ta kwanta gabaɗaya domin haka take yiwa Hafiz kuma tana jin daɗin hakan.

“Kina da nauyi fa.” Ya tsokaneta yana jan bargo ya lulluɓesu.

“Na kai ka nauyi ne? Sai an haɗa ukuna kafin a samu irinka ɗaya.”

Dariya yayi a hankali wanda ya zama kamar jijjigata yake yi ta ƙara narkewa a jikinshi ta lumshe ido tana jin bacci mai daɗi na neman fisgarta.

“Ki tashi kiyi wankan janaba kar ki yi bacci.”

“Don Allah ka daina faɗin haka.” Ta muntsineshi a ribs.

“Me ɗin?” Shima ya rama a gadon bayanta wanda bai kai nata zafi ba.

“Ouch, wai…wai…wai wankan J, kawai kace ‘wanka’ shikenan, wancan sounds vulgar.” Tayi maganar kamar a buge take don tsabar baccin da take ji.

Wani dariyan yayi wanda yasa ta ƙara jin baccin yana son fin ƙarfinta.

“Dama kana dariya ne?”

Bai amsa ba ya sauƙeta daga kanshi ya kwantar da ita a gefe kana ya sauƙa daga gadon ya jata zuwa banɗaki tana layi ya buɗe banɗakin ya shigar ita ciki.

“Ki fara wankan J ɗin.” Yana faɗin hakan ya rufe mata banɗakin ya koma ya zauna a bakin gado yana mamakin canjawar Juwairiyya kamar hawainiya.

Tunani ne da yawa suke ta yawo a brain ɗinshi har ta fito, a nan ne ya lura kamar tana avoiding haɗa ido dashi, kenan har ta canja? Bai ce komai ba ya shima ya tashi ya shiga. Kafin ya fito ta gyara musu kan gadon kana ta shimfiɗa sallaya fara sallan ishan da dama shi ta dawo yi mai aukuwa ya auku. Sai da ta idar sannan ta hau gadon ta kwanta a can gefenta ta ƙudundunu kamar mai jin sanyi.

Muhammad da dama ya rigata kwanciya ya sanya hannunshi guda ɗaya ƙasan haƙarƙarinta ya jawota ciɗok ya mannata da jikinshi duk a cikin seconds biyu. Mutsul mutsul ta fara ya matseta sosai yace,

“Stop fighting, ki yi bacci kar sanyi ya shiga jikinki.”

Kamar dama jira take yi yayi magana ta sake jikinta har da gyara kwanciyan yanda zai mata daɗi.

“Good girl.”

Mum Fateey 👌

Tun da Juwairiyya ta tashi sallan asuba ta ke duk wani ƙoƙarinta na ganin bata haɗa ido da Muhammad ba, shi kuma yana son mata magana amma sai ya kyaleta don baya son ya tsokalo tsuliyar dodo ana zaman lafiya.

Tana idar da sallan tayi addu’o’inta ta shafa kana ta tashi ta canja kayan baccin da ke jikinta zuwa wata doguwar Abaya mai taushi ta fice daga ɗakin zuwa kitchen, Muhammad binta yayi da ido kana ya kaɗa kanshi kawai. Sai da ta je ta bugawa Salima ƙofa ta faɗa mata abun da take so sannan ita kuma ta miƙo mata ta koma kitchen ta fara girkin, tana girkin cikin kwarewa komai na tafiya mata yanda take so domin ita tana son yin girki, hakan yasa tun wancan lokacin ta nunawa Hafiz tana son ƙara koya ya kuma sakata a classes ɗin.

Kafin bakwai na safe ta gama komai ta kaiwa Salima tata sannan ta tsaya a kitchen ɗin domin bata san yaya zata yi da na Muhammad ba wanda ta lura tafiya yake yi da nashi office. Shin ta kai mishi nashi gurin Salima ce ko dai ta kai falonta ta ajiye ko kuma ta jirashi a nan har ya fito ta saka mishi a mota? Tana wannan tunanin ne ya fito cikin shiri zai tafi amma sai ta kasa kai mishi abincin, zuciyarta na nauyi tana tsoron kar ta kai mishi ya gwatsaleta.

 Tana tsaye a kitchen ɗin ta ji ya kunna motarshi da ta fara bashi gardama, can kuma ta ji muryar Salima a tsakar gidan tana gaisheshi, cikin sanɗa ta leƙa ta window ta ga lokacin da Salimar take tsugunne tana gaisheshi yana amsawa cikin jin kai.

“Miƙo mini abinci sai ki buɗe mini gate.” Ya bawa Salima umurni yana mai shiga motarshi.

Sai ta lura Salima tayi ɗan jimm kaɗan tana murmushi sannan ta miƙe ta je ta ɗauko abinci a basket, tayi zaton abincin da ta kai mata zata bashi amma sai taga har kulan an canja ta fito da wata mai shegen tsada da ta lura a irin su Salima take sakawa Muhammad abinci. To wani girkin ta mishi ko dai nata aka juye a ciki? Sannan me yasa da ya aiketa ɗauko breakfast ɗin ba zata zo gurinta ta tambayeta inda breakfast ɗin maigidan yake ba?

Tana ganinsu suna magana a hankali wanda bata iya ji dalilin ƙaran motar Muhammad da ya kunna, can kuma ta ga Salima ta buɗe mishi gate ya fita tana ɗaga mishi hannu. Ta sani bata son Muhammad amma ya kamar Salima na neman kwace mata spotlight ɗinta ne duk da cewa bata son haskakawan? Domin da tana so babu uban da ya isa ya hanata ko ya kawo mata cikas saboda ta yarda da kanta ta kuma san wacece ita! Wani gefe na zuciyarta kuma sai ta kwaɓeta da cewa don bata tarairayar Muhammad bai kamata kuma ta hana Salima ba ko ta ji haushi in tana yi ba, saboda Salima tana son mijinta kuma dama haka take mishi tun da.

Kawar da zancen ta yi a ranta kana ta juye abincin Muhammad ɗin a wani kula daban na kowa da kowa domin duk da cewa bata sonshi ta sani ba’a haɗa kulan maigida da kowa. Barin abincin ta yi a kitchen ta fara wanke-wanke ta kimtsa kitchen ɗin nata cikin ƙanƙanin lokaci don ita aiki baya bata wahala.

Tana cire kaya a ɗaki zata shiga wanka ta jiyo sallamar Salima a falonta, da kamar ba zata amsa ba don wanka take son shiga ta gasa jikinta da kyau saboda murjeta da Muhammad yayi jiya ta ji jiki. Jiki duk gajiya ta fito sanye da Hijab dogo yayin da ta ciki kuma zani ne kaɗai.

“Maman Masoyi an tashi lafiya?” Ta samu guri ta zauna ganin Saliman ma ta samu guri ta zauna tare da HJ.

Hannu Juwairiyya ta miƙawa HJ ya je da gudu ya faɗa jikinta ta ɗagashi ta ɗaura a cinyarta tana jin sonshi a ranta.

“Lafiya kalau Alhamdulillah. Tun ɗazu na so zuwa mu gaisa Masoyinki ya tashi sai da na dafa mishi breakfast sannan na samu ya daina mini kuka.”

“Ya Salam! Ba dai ba ya cin pancake da sauce ɗin ba?” Juwairiyya ta yi kamar bata san me ya faru ba.

“Babanshi ne yace mu bashi namu, ni kuma ina jin nauyin zuwa in ce miki ki bamu wani, gashi ƙamshin sai bugan hancina yake yi. Ni zan zo ma ki koya mini pancake ɗin nan don watarana in nayi sai yayi ruwa ko kuma yayi kauri da yawa, ina son yayi irin naki fluffy ɗinnan ya fi kyau.”

“To zan nuna miki yanda nake yi. Ai kuma da kin yi magana akwai wani in baki.” Faɗin Juwairiyya tana tashi tsaye cikin jindaɗin yaba mata da Salima ta yi.

“A’a ki barshi kar mu cinye miki naki.”

“Kar ki damu dama akwai nashi da bai ɗauka ba sai ku ci.” Juwairiyya ta yi katoɓara ba tare da ta sani ba.

Murmushin jindaɗi Salima tayi kana ta gyara zamanta Juwairiyya ta kawo musu breakfast ɗin har tana tambayarsu shayi zasu sha ko cereals.

“Ni kam da zan samu kunun gyaɗa yanzu da shi zan sha amma bani da garin kunun.” Faɗin Salima tana zuba abincin mai yawa a plate.

“Ai ina da garin kunun da na gyaɗa, bari in miki tunda bashi da wahala.” Faɗin Juwairiyya tana ƙara miƙewa.

“Ah’a ki bari kar in sakaki wahala.”

“Ah haba minti nawa ne ma.” Da haka fita zuwa kitchen ta kama dama kunu da ya ke tana da markaɗeɗɗen gyaɗa da kuma garin.

Cikin minti sha biyar ta gama ta kawowa Salima wacce tayi ɗai ɗai a kan kujera tana kallo a Tv ga HJ ya kacancana sauran pancakes ɗin da suka bari.

“Har kin gama? Yanzu nake cewa bari in tashi in gyara inda masoyinki ya ɓata kar ki zo ki sameshi haka.” Ta faɗi hakan tana miƙewa zaune.

“Dama ban yi shara ba, ki bari zan tsincesu. Da haka ta kama tsincewa kana ta kwashe kulolin ta kai kitchen ta dawo ta samu HJ ya ɓarar da rabin kunun da ta dama yanzu. A lokacin ne ranta ya ɗan ɓaci don ita bata son ƙazanta, musamman dotti a kan carpet gashi yau ba dotti ne kaɗai ba har da kunu ya malale.

“Yau kuma ɓarna kake ji dashi ko?” Ta fita zuwa kitchen ta ɗebo ruwa a roba tare da kitchen towel ta ajiye Salima ta sauƙo ƙasa wai zata gyara Juwairiyya ta hanata.

Sai da ta gama ta dawo hira ya ɓarke tsakaninsu, a nan Salima take faɗa mata wata ƙanwar Muhammad ta haihu jiya da dare bayan tafiyanta yin sallah tana jira ta dawo ta faɗa mata sai kuma bata dawo ba.

In ina Juwairiyya ta fara kamar mara gaskiya don ta yaya zata faɗa mata cewa daga komawanta ɗaki ta haɗe da mijinta suka kwana abu ɗaya?

“Ina yin sallah na kwanta bacci don tun muna hira nake jin baccin.”

“Ko kuma kun kwana kuna amarcewa dai.” Ta faɗa cike da zolaya amma a ranta ba zolayar ba ce sai tsantsan kishi domin ta lura kamar sun ƙara wani haɗewan amma bata da tabbacin hakan.

Wannan zargin ne yasa tayi ta sakata aiki don ta huce takaici, ta wani gurin kuma tsoro ne ya shiga ranta akan kar Juwairiyya ko Muhammad su fara son junansu, don in hakan ya faru rabasu zai bata wahala duk da cewa bata karaya ba.

“Ah haba wani amarci kuma? Bacci kawai na yi.” Ta amsa tana kallon ƙasa kamar wacce tayi laifi.

“To tunda kin ce haka shikenan, ki tambaya mana maigidan gobe mu je mu dubo mai jego da baby daga nan kuma sai suna.”

“A’a ke ki tambaya mana shi. Ni da kin bari ma sai suna mu je, don goben nan ina da baƙin da zan yi, Hafsat ƙanwar marigayi ce zata kawo mini ziyara.”

“To shikenan.” Salima ta faɗa tana murmushin mugunta domin ta ga wani kullin da zata kulla, minti biyu da haka ta tashi tsaye ta kama hannun ɗanta suka yiwa Juwairiyya sallama suka fice.

Suna fita Juwairiyya ta sakawa ɗakinta key ta fara gyara daga ɗaki har falo ta kunna turaren wuta sannan ta faɗa wanka, tana fitowa ta saita alarm ya tasheta sha biyun rana domin ta ɗaura girkin dare.

Alarm yana bugawa ta tashi ta shiga kitchen ta girka musu Jollof rice haɗeɗɗiya da pepper meat sai kuma zobo, tana cikin kitchen Salima na bakin ƙofa a zaune wai tana tayata hira da koyon girki. Bata damu ba hasalima ta ji daɗin hakan domin sai aikin ya tafi da wuri ta gamashi cikin ƙanƙanin lokaci ta bawa Salima nata kana ta shigar da nasu falo. Alwala ta fara yi domin har an yi sallah azahar kuma lokacin dawowan Muhammad yayi, har ta idar bai dawo ba hakan yasa ta isa gaban madubi ta kalli kanta for the first time tunda ta zo gidan. Ramarta yana nan amma sai ta ga kamar ta yi haske kaɗan duhun fuskarta ya fara washewa. Murmusawa tayi domin sai take ganin samun nitsuwar da tayi ne ya jawo haka, lallai Muhammad ya taimaka mata. Kamar da wasa ta ɗauki kwalli ta zizara a manyan idanunta nan da nan ta ga ta ƙara kyau. Buɗe drawer ta yi da niyyar shafa powder sai kuma ta fasa, kar Muhammad ya gane ta fara mishi kwalliya ya tsokaneta akan she is trying so hard, tana rufe drawer ta ji ƙarar motarshi a waje wanda ko ba’a faɗa mata ba ta san Salima ce ta buɗe mishi, ita ba zata iya wannan ɗisi da bullin ba.

 Kallon kanta tayi one last time kana ta fita falo don bata son ya shigo rage kaya ya tarar da ita a cikin ɗakin. Tuno da tarayyarsu tayi na jiya ta ji kunya ya rufeta ta wani guri kuma sai take jin kamar a cigaba da yin hakan ko da babu soyayya a tsakaninsu.

Sallama yayi a bakin ƙofa ta amsa a karon farko tun aurensu ya shigo fuskarshi babu yabo babu fallasa don bai san me zai tarar a tattare da matarshi mai halin hawainiya ba. Kallonta yayi na wasu seconds suka haɗa ido amma tayi saurin kawar da kanta tana wasa ta yatsun ƙafarta, sai ya ga ta mishi kyau fiye da sauran ranakun da yake tare da ita, ko dai sha’awarta ce ke ɗawainiya dashi har yake ganin hakan? (Mata a dinga saka kwalli, duk gayunki in bakya saka kwalli baki haɗu ba.)

“Ka dawo?” Ya jiyo siririyar muryarta tana tambayarshi.

“Na dawo.” Shima ya bata amsa yana cike da mamakin yau wai ta gane ya dawo gida, shin wani canjin aka samu kamar jiya ko dai wani abu take nema?

Kaɗa kanshi yayi domin ya sani taurin kan Juwairiyya ba zai barta da sauƙar da kanta don tana neman wani abu a gurinshi ba, duk yanda aka yi canji ne aka samu kuma yana farin ciki da hakan, da haka ya shige ɗaki ya barta a gurin.

Yana shiga Juwairiyya ta sauƙe wata wawuyar ajiyar zuciya wacce bata ma san ta riƙe ba, lallai bakinta na buƙatar farsa, domin bata san lokacin da ta furta mishi tambaya mai kama da tarɓa ba. Tana nan zaune ya fito daga shi dai dogon wando da singlet zai fita, har ya je bakin ƙofa ta tsayar dashi.

“In zaka je?”

“Zan je cin abinci ne.”

“Ga naka a nan.” Ta faɗa don ta gaji da wannan sintirin nashi daga ɗakinta zuwa na Salima da sunan cin abinci, ba kishi take yi ba amma in yana can ya zauna a can, in kuma yana nan ya zauna a nan.

Dawowa yayi yana murmushi ya zauna kusa da ita amma sai ta matsa kaɗan, ya gani amma bai nuna hakan ya dameshi ba ya ce,

“Zuba mini.”

“Baka da hannu ne? Ko sannu da girki ka faɗa mini? In dafa kuma in kawo maka har falo kuma na tausaya maka don ka daina sintiri shine zaka ce in zuba maka?” Ta faɗi hakan a numfashi ɗaya tana harararshi don yana son ya wuce gona da iri, ya samu ma ta tausaya mishi?

“Oh tausayina ashe kika ji? Dama kina tausayin mutane?” Ya tambayeta yana ɗaga gira ɗaya sama yana murmusawa don ya yaudari kanshi ɗazu, ashe tana nan bata canja hali ba.

“Ka ɗibi abincin nima in ɗibi nawa yunwa nake ji.” Ta faɗa tana kallon kulolin da ke kan center table ɗin.

Tausayinta ne shima ya ji ya kamashi haɗe da mamaki amma bai bari ta gane ba, hannu yasa ya jawo center table ɗin ya ɗauki plate ɗaya ya zuba jollof ɗin shinkafar da take ta tashin ƙamshi ya haɗa da pepper meat sannan ya gyara zamanshi ya fara ci.

Baki buɗe Juwairiyya take kallonshi don ta ɗauka ita zai fara miƙawa amma sai ta ga akasin hakan, kwafa tayi ta matso ta fara ɗiban nata sannan ta miƙe ta ɗauko musu zoɓon a fridge tare da glass cup biyu, bata canja guri ba ta dawo kan kujeran da yake zaune ta zauna kana ta tsiyaya a cup ɗaya ta kai bakinta ta sha sannan ta fara cin abincin.

Suna cikin ci ta ga Muhammad ya ɗauki kofin nata ya kwankwaɗe zoɓon duka kana ya ajiye ya cigaba da cin abincinshi, harara ta bishi dashi ya ɗago ido ya kalleta kamar bai san me yayi ba, ɗaga kafaɗarshi yayi irin he has no clue da abun da yayi. Zoɓon ta ƙara tsiyaya ta sha kaɗan ta ajiye ya ƙara ɗauka ya shanye.

“Muhammad ka daina ɗauka mini cup ɗina muna sharing, ga naka nan na kawo maka.”

“Bakya son mu yi sharing ɗinne?” Ya tambayeta.

“Eh.”

“To ai mun yi sharing abun da ya fi cup jiya da dare, ko in tuna miki?” Ya tsareta da ido ta fara inda inda tana sunkuye da kai kamar munafuka.

“Ka bari bana so.”

“Muhammad nan, yes, faster, yes! Shin kin tuna dalilin da yasa kika yi waɗannan furucin?”

Wannan karon ajiye abincin tayi a ƙasa ta ɓoye fuskarta a cinyarta tana jin haushi da kuma tsantsan kunyar wannan bawan Allah. Ita take mishi rashin kunya amma ba zai hana da dare tayi ta mishi sambatu ba.

“Ki tashi ki ci abincinki na daina.” Ya faɗa yana tsiyayan zoɓon ya kurɓi kaɗan ya ajiye yana murmushin mugunta.

Sai da ta ƙara minti ɗaya a haka sannan ta miƙe da ta tabbatar ba zai ƙara cewa komai ba, hararanshi tayi sannan ta ɗauki abincinta ta cigaba da ci, tana ganin ya cinye nashi ya ƙara a ranta tace dole ya zama lukuti mana.

“Abincin yayi daɗi.” Ya samu kanshi da faɗi wanda shi kanshi sai da yayi mamaki domin baya taɓa yabon girkin Salima.

“Shi kaɗai?” Ta tambaya don ai tun jiya ta fara girki su ɗin basu yi daɗi ba kenan?

“Ke ma kin yi daɗi.” Ya faɗa yana binta da mayataccen kallo.

Rufe fuskarta tayi da hannunta ɗaya wanda baya riƙe da plate ɗin cikin tsananin jin kunya ta ce,

“Ni ba haka nake nufi ba, sauran abinci nake nufi, na jiya da safen yau.”

“Oh, suma sun yi daɗi but shinkafar is my favorite da ke.”

“Oh my God! Muhammad stop saying that, will you? Kai baka jin kunya ne?” Ta faɗa embarrassed.

“Me yasa zan ji kunyar matata?” Ya faɗa yana gyara zamanshi a kan kujerar wacce sai da tayi ƙara kiiiiii.

‘Matata’ ta furta a ranta, wato da gaske yanzu ita matar Muhammad ce?! Gashi har sun fara zama suna hira duk wani differences ɗinsu sun ajiyeshi a gefe na wani lokaci. Ashe zasu iya rayuwa ba tare da hantaran juna ba? Shin ko dai ta cigaba da zama dashi ne ba sai ta fita ta sake wani auren ba? Saboda ita kanta in ba ƙaddara ba bata son a dinga irga aurarrakinta. Ko dai zata bashi chance? To ya zata yi da Salima da ta yiwa alƙawarin cewa zata bar mata mijinta da zarar buƙatarta ta biya? Gashi ko sati biyu ba’a cika ba sun fara zama suna hira har tana tunanin zama dashi na har abada? Girgiza kanta ta yi da ta ji muryar Muhammad na mata magana.

“Ki ci abincin nan kar yayi sanyi, in kuma wani abun kike son ci kuma to.” Yayi magana mai harshen damo.

Kamar zata kware da abincin da ta saka a bakinta ta dubeshi, shi kuma yayi kamar bai san me yayi ba yana kallonta innocently.

“Dama haka kake da dirty mind?” Ta tambayeshi bayan ta kawar da kanta don har ga Allah tana jin kunyarshi.

“Baki bani amsa ba.”

“Mu bar maganan kawai.” Da haka taci gaba da cin abincinta wanda har yayi sanyi amma ta daure ta ƙarisashi don bata son barin abinci.

Tattare gurin tayi ta kai kitchen ta kwashe sauran abincin ta saka a robobi ta dawo parlour zata saka a fridge Muhammad ya dakatar da ita.

“Me zaki yi da abincin?”

“Zan ajiye ne watarana in ina jin yunwa in ɗumama ko kuma in nayi baƙi unexpected in ɗuma musu.” Ta mishi bayani.

“Why?” Ya tambayeta kamar wani yaro.

“Saboda hakan ya fi sauƙi kuma baya ɗaukan time, nan da nan mutum zai ga abinci a gabanshi in no time.”

“Hakan yayi, amma ni karki bani.”

“Ba zan baka ba tunda da gaske ka nuna baka so.” Ta ji tausayinshi kaɗan domin ta sani PTSD is real.

Kaɗa kanshi yayi da haka ya ƙara jawo zoɓon zai sha ta tare hannunshi ta ɗauke tana cewa,

“Zaƙin zai maka yawa, ka bari sai anjima da dare.” Ta sanyashi a fridge ta dawo ta zauna a wani kujera daban bayan ta kunna musu kallo.

Samun kanshi yayi da murmusawa yana mamakin yanda aka yi bai ji ranshi ya ɓaci ba, ya sani da Salima ce ta mishi haka da sai ta gane kurenta amma ya kasa fushi ga wannan ƴar rigiman, hakan da tayi nuna kulawa ne and he appreciate.

Daga lokacin basu sake magana ba har aka kira sallan la’asar ya fita yayi sallah ya dawo, tana ɗaki ya dawo ya canja kaya ya ce,

“Zan fita cikin gari wataƙila sai bayan isha zan dawo, kina buƙatar wani abu?”

“Ka taho mini da kankana da kwakwa da dabino.”

“Yanzu ko sai na dawo?” Ya tambaya yana danne murmushin da ke son kwace mishi.

“In ka dawon dai.” Ta faɗa ba tare da ta gane ya canja akalar zancen ba.

“To yaushe zai yi aiki har in samu rabona?”

“Wayyo Allah na! Don Allah Muhammad ka bari.” Ta faɗi hakan tana kife kanta a ƙasa cikin tsananin kunya amma wannan karon sai ta samu kanta da yin murmushi. She loves dirty talk don Hafiz yana mata haka Daddy.

Bai ce komai ba ya fita yana murmushi ya je bakin ƙofar ɗakin Salima ya buɗe ya leƙa ciki ya hangota zaune ta ci ado amma kamar ranta a ɓace yake.

“Sannu da dawowa, ya gurin aiki?” Ta ce dashi tana russunawa amma still yanayin fuskarta bai canja ba.

“Lafiya. Me ya sameki na ga ranki a ɓace?” Ya tambayeta cike da mamaki.

“Babu komai, kawai ina zaune ne ni kaɗai babu abokin hira. Baka zo ka ci abinci ba.” Ta mishi magana mai kamar tuhuma.

“Na ci a can. Zan fita cikin gari zan kai bayan isha, kina buƙatar wani abu ne?” Itama ya tambayeta kamar yanda ya tambayi ƴar’uwarta.

“Babu komai. A dawo lafiya, Allah Ya tsareka.”

“Ameen.” Ya amsa yana jin daɗin addu’arta.

Yana fita Salima ta dafe ƙirji ta ɗauki wayarta ta shige da ita ɗaki tana dannawa, can ta ce,

“Hello Mama.”

Shi kuma Muhammad yana fita ya fara sayan aikan Juwairiyya sannan ya bawa yaro yace ya kai musu kowacce da ledanta, sannan ya ƙara da sauran fruits irin su lemo da Apple. Juwairiyya tana tsakar gida zata ɗaura abinci yaro yayi sallama ya shigo ya miƙa mata tata kana ya wuce ya miƙawa Salima wacce ta ƙi fitowa su yi hira da Juwairiyya.

A kitchen ɗin ta buɗe ledan ta fara ciro kayan ciki tana ware wanda zata yi amfani dasu yanzu, sauran kuma ta kai fridge ta adana. Kankanan ta yankasu a bowl, ta kawo Kwakwa tayi grating ta watsa a ciki, sannan ta ɗauki Dabino ta yankasu ƙanana suma ta watsa, ta ɗauki Ayaba tayi dicing suma ta watsa ta ɗauko gwangwanin madara ta ɗibi cokali uku ta saka sannan ta zuba sugar kaɗan saboda bata da zuma, gaurayasu tayi kana ta koma can cikin ɗakinta ta fara sha a hankali har ta shanye sannan ta dawo taci gaba da aikinta. (Ƴan Ruwan Zuma kun tuna wannan haɗin ko kun kwanta a kai? Lol)

A ranta kuwa cewa take yi in har za’a cigaba da yin harkan zata yi gyara saboda kowa ya ji daidai ba zata so ta kwareshi ba. Kafin maghrib ta gama aikinta ta kaiwa Salima wacce ta mata ƙaryar wai bata jin daɗi, hakan yasa ta ɗauko HJ ta kawoshi sashenta wai mamanshi ta huta kaɗan. Duk wani abun ɓarna sai da ta ɗage kafin ta kunna mishi kallo ta barshi a falo ta shiga wanka mai haɗe da gyare-gyare wa Muhammad.

Yanda ta bar yaron haka ta dawo ta sameshi bai motsa ba yana kallonshi, kallonta da yayi yasa ta ga kamanninshi da mahaifinshi wanda hakan ya sa ta tuna darensu na jiya da suka raya, alwalarta ce ta fara ƙara alamar zata karye tayi saurin ɗage tunanin daga ranta ta koma ɗaki ta shirya cikin atampa ɗinkin riga da siket. Wannan karon ta shafa powder da kwalli daga nan ta bulbuli turare a jikinta ta dawo falo ta fara sallah domin har lokaci ya wuce an fara kiraye-kirayen Sallah Isha.

Tana idar da sallah ta jiyo ƙarar buɗe gate alamar Muhammad ya dawo Salima ta buɗe mishi gate, cikinta ne yayi wani irin murɗawa ba don tsoro ko ɓacin ciki ba sai don sha’awar son kasancewa da shi hakan yasa ta ji kamar abu na zuba a jikinta (Haɗin kankana yayi aiki). Tana zaune a gurin ya shigo ya fara ɗaukan yaronshi yana mishi wasa sannan ya dubeta ya ce,

“Na dawo.”

“Sannu da dawowa, na ga aika nagode.”

“Ok.”

Da haka ta ga ya fice tare da yaron wanda sai ta ji ranta ya ɓaci, to ina zai je? Bai ga abincinshi bane ko bai yarda cewa ba zata jagwalgwala ba? Tana wannan tunanin ya dawo wanda kwata-kwata bai yi minti biyu a can ɗin ba, hakan ne ya tabbatar mata cewa mayar da yaron yayi gurin uwarshi, sai ta ji kunya ya kamata. Zumuɗin me yake yi? Ta nan babu inda zata je.

Ɗaki ya wuce ya shiga wanka ita kuma ta tashi a gurin ta adana abun sallar tata sannan ta zauna ta fara kallo tana kuma danna wayarta har yayi wankan ya fito ya zauna ya jawo abincin ya fara sakawa. Wannan karon ita ya fara bawa kana ya saka nashi ta bishi da murmushi tana jin daɗi a ranta suka fara cin abincin suna magana jefi-jefi wanda yawanci tambaya ne da amsa ba wata doguwar hira ba.

Sai da suka gama cin tuwon ta tattara ta kai kitchen domin gobe ɗumame zata yi musu a matsayin karyawa sai kuma wani abun mai sauƙi. Tana dawowa yace mata ta rufe ƙofa da key.

“To in muka yi baƙi fa?” Ta tambaya tana rufe bakinta don dariya ke son kwace mata, zumuɗinshi yayi yawa.

“Sai su san inda zasu shiga.” Ya amsa ko a kwalarshi.

Da haka ta zo ta zauna a wata kujerar suka cigaba da kallo can ya ce,

“Ni ina nawa?”

“Don Allah ka daina.” Ta faɗa cike da kunya.

“Ni Apple nake nufi, ki bani ɗaya.”

Wannan karon kunyar tata yafi na ɗazu ta tashi jiki duk madara ta nufi fridge ta ɗauko mishi ɗaya dama ta wankesu ta miƙa mishi. Hannunta mai riƙe da Apple ɗin ya riƙe ya jawota jikinshi kana ya ce,

“Har da wancan ma duk zan ci.”

Cikin kunya jiki kuma na mazari Juwairiyya ta biye mishi suka fara soyayya a nan kafin daga baya ya sunkuceta ya shigar da su ɗaki.

Washe gari da safe tana kitchen don yi musu breakfast ya shigo yana tambayarta me zata yi.

“Ɗumame da wani abu amma ban gama shawara ba.”

“Kiyi ɗumamen kawai na hutar da ke, na ga kamar a wahale kike.”

“Bana so Muhammad.” Ta faɗa tana kare fuskarta da hannayenta.

“A ajiye mini Apple na rana.” Ya faɗi hakan yana karɓan basket ɗin hannunta ta bishi da ido tana murmushi a hankali, da haka ya wuce bakin ƙofar Salima ya mata sallama ta fito ta buɗe mishi gate ya fita.

Da wuri ya dawo daga office ya ci Apple har sau biyu sannan ya haƙura gudun kar ruwan jikinshi ya ƙare ba don ya gaji ko ya kosa ba.

Da yamma liss ya bar ɗakin Juwairiyya sai ƙamshin sabulunta yake yi ya koma gurin Salima wacce tuni ta gama shirin tarɓanshi jiki duk madara.

Sai da yayi sallah maghrib sannan ta kawo mishi abinci, sai dai kafin ta zuba mishi kamar kullum ta ga ya jawo plate zai zuba ta dakatar dashi tana cewa,

“Ya ya dai?” Don abun ya ɗaure mata kai.

“Zan zuba ne yau na hutar da ke.”

Wannan magana a maimakon ya yiwa Salima daɗi sai ya sa cikinta ya kulle, bata ce komai ba ta bari ya ɗiba tana jin kamar ta kwace don ba haka suka saba ba, kara suncewa tayi da ya miƙo mata plate ɗin sannan ya fara ɗiban wani wanda ta tabbatar shine na shi. Da haka suka fara cin abincin yayi loma na farko, ya ƙara na biyu ya ce,

“Abincin yayi daɗi ke kuma kin yi kyau.”

A wani zamani a baya Juwairiyya ta ce,

*”Allah Ya haɗaki da wahala, ga rashin lafiya da kuzarin ɗa namiji, ga ci kamar gara sannan ga banzan hali kamar rainon fir’auna. Allah Ya kawo miki sauƙi.”*

 *Abun da Juwairiyya bata sani ba shine sauƙin na zuwa wa Salima, sauƙin ma mai ɗorewa.*

Mum Fateey 👌

Washe gari da hantsi baƙin Juwairiyya suka zo wato su Hafsat da Zainab ƙannen marigayi Hafiz, sun jima a ɗakin Juwairiyya suna hira sannan ta musu jagora zuwa ɗakin Salima don su gaisa. Sai da suka zauna sannan ta fito daga kitchen tana musu sannu da zuwa HJ na maƙale da ƙafarta ɗaya yana mata kuka.

“Masoyi zo nan, me ya sameka yau kake ta bore?” Faɗin Juwairiyya tana miƙa mishi hannu akan ya zo gurinta amma ya maƙe kafaɗa ya ƙara shigewa jikin mamanshi.

“Wallahi yau tun tashinshi yake ta mini hakan, ina zaton ko baya jin daɗi ne.”

“To Allah Ya bashi lafiya.” Suka mishi addu’a kana suka gaisa aka hau hira.

“Kar mu tsareki da surutu na ga kamar daga kitchen kike.” Faɗin Juwairiyya tana ƙoƙarin miƙewa.

“La babu komai, na ɗaura tafashen nama ne ban ma fara girkin ba. Ai tun shekaran jiya take faɗa mini zaku zo muna ta zuba ido shiru.” Salima ta ƙarisa maganar tana kallon Hafsat da alama da ita take yi.

“Wallahi kuwa Allah ne bai yi ba, ta kiramu akan mu ɗaga zuwan sai yau sai ya kasance mu ɗin ma wani uzuri ya taso mana.” Hafsat ta bata amsa tana murmusawa.

“Tana tare da ango ne shiyasa ta ɗaga muku zuwan sai yau.” Ta faɗa cikin zolaya tana ɗagawa Juwairiyya gira wacce mamaki da kuma kunya ne ya kamata tayi murmushi ta kawar da kanta.

“Aunty Juwai dama abun haka ne?” Zainab da bata cika magana ba ta tsokaneta.

“Sharri kawai take mini. Maganar yana ɗakina kuma gaskiya ne, nasan ƙarshenta in kuka zo zaku takura ne shiyasa.”

“Eh to da wannan ma, amma ai Baban Hafiz kam ba baƙonsu bane. Bai fi ya zauna a yi hiran dashi bane.” Faɗin Salima cikin son tura kan Juwairiyya cikin taɓo.

“Ya Muhammad ko a da baya zama mu yi hira dashi, zamu dai gaisa a mutunce a yi magana ɗaya zuwa biyu shikenan.” Hafsat ta kare Juwairiyya don ta ga kamar Salima nema take yi a ga laifinta amma kuma cikin dabara da kissa.

“Ai ina ga in banda Marigayi babu wanda yake iya zama da Muhammad yayi hira mai kyau. Kullum fuskarshi a gimtse ta yaya mutane zasu so su yi wata doguwar hira dashi?” Faɗin Juwairiyya kamar dama jira take yi.

“Shi yasa kowanne mutum kika gani da halinshi mai kyau ko mara kyau da kuma yanda yake mu’amalantar mutane a rayuwarshi, shi kuma sakewa mutane fuska ne baya yi amma bayan haka bashi da wani hali mara kyau.” Wannan karon Zainab ce ta kare Muhammad.

“Ai ina faɗa mata kullum shi haka yake kuma babu mai iya canjashi. Ko ba haka bane?” Salima tayi maganar tana dariya kaɗan yayin da Juwairiyya kuma tayi rolling idanunta.

“Da alama albashin masu kareshi ya iso kanki Zainab.” Faɗin Juwairiyya cikin raha.

Har Salima zata buɗi baki tace wani abu Hafsat ta miƙe ta rigata magana ta ce,

“Bari mu barki ki ƙarisa aikinki.”

Nan suka miƙe dukkansu suka koma ɗakin Juwairiyya ita kuma Salima ta shiga kitchen tana ƙulle-ƙulle a zuciyarta.

“Wannan matan ta cika faɗi ba’a tambayeta ba, yanzu da mu wasu baƙi ne a gurinki sai mu ɗauki maganar can da zafi na canja mana ranar zuwan. Kuma wai sai ta ɗauko gulman sai ta canja zani ki rasa a wani sashe ma take.”

“Wai Salima matar da bata cika wani magana ba? Kawai dai hira take muku.” Wannan karon Juwairiyya ce ta kareta.

“Eh na san bata da magana sosai amma in tayi ɗaya sai ta fi dubu na mai surutu. Kawai ni kiyi hankali da ita don yanayinta bai zauna mini ba wallahi.” Tayi maganar wanda har cikin ranta haka take ji domin bata yarda da Salima ba amma ta kasa ɗaura yatsa akan abun da bata yarda a kanshi ɗin ba.

“To Allah Ya rufa mana asiri, ni yaushe zaku je Ashaka? Ina da aika gurin Yayi?” Da haka Juwairiyya ta canja musu taɗin zuwa na wata Kakarsu da har lokacin take da rai duk tsufanta.

Suna sallah Azahar suka ci abinci suka yi haramar tafiya, Salima ta basu leda mai ɗauke da turaruka biyu wai na su, suka mata godiya itama Juwairiyya ta basu nata. Har waje inda Hafsat tayi parking Juwairiyya ta rakasu kana suka shiga suka tafi. A hanya Hafsat ta kaɗa kai ta ce,

“Gaskiya Aunty Juwai tana da wauta don wallahi na lura kamar matar Ya Muhammad wayo take mata. Ta jata a jiki ita kuma sai ɓarin zance take yi ko wa ya faɗa mata ana kushe miji a gaban kishiya? Ni wallahi tun ranar da muka je bayan haihuwar mai sunan Ya Hafiz da take cewa wai sunan Babanta za’a saka amma tace a fasa a saka na marigayi! Akan yafi ubanta kenan ko me? Sannan in ma hakan ne me yasa zata faɗa mana? Sai a barshi a cewa Ya Muhammad ne ya yiwa abokinshi takwara don son kanshi. Ni sai yanzu ma na ji abun bai zauna mini ba, kai karya ma take yi wallahi.”

“Ikon Allah, kuma fa haka ne!” Faɗin Zainab tana tuna ecounters ɗin nasu duka.

“Gashi yanzu ko an bata shawara ba ɗauka zata yi ba don zata yi tunanin ana son gwara kansu ne za’a hanasu zaman lafiya.”

“Ah haba! Yanda muke da Aunty Juwai ta sani ba zamu mata ƙarya mu munafurceta ba. Ke dai in kin koma gida ki kirata ku yi magana.”

“Ko zan yi magana ma ba yanzu ba don ba zata ɗauka ba. Zan bari sai Tafiyar tasu tayi nisa in itama ta fara hasko wasu abubuwan sai in faɗa mata.”

“Hakan ma yayi.” Da haka suka cigaba da hiran har Hafsat ta sauƙe Zainab a gidanta ita kuma tayi nata gidan.

Muhammad ne zaune a kan Dinning Table yayin da Salima ke tsaye a gefenshi tana zuba mishi abinci suna magana.

“Ɗazu su Hafsat ƙannen marigayi suka kawo mana ziyara.”

“Yayi kyau, suna lafiya?” Ya tambaya yana kai loman farko bakinshi.

“Lafiyansu kalau, ai suna da kirki don har nan ɗakin suka shigo muka yi ta hira. Ashe tun shekaran jiya suka so zuwa amma Juwairiyya tace su bari sai yau, wai kar su takura saboda kai kullum fuskarka a gimtse take baka dariya balle har hira ta shiga tsakaninku.” Ta ƙarishe maganan tana murmushi kamar bata san me tayi ba.

Shiru Muhammad yayi bai ce komai ba amma ta lura kamar bai ji daɗin maganar ba, dama haka take so, don haka da ta tabbatar saƙonta ya isa sai ta canja musu hiran ta ɗauko na batun karatunshi ya biye mata yana faɗa mata cigaban da aka samu.

Washe gari da yamma Juwairiyya ta ƙarbi girki, aiki take yi babu yabo babu fallasa domin yanzu ta fara sabawa da zaman gidan da kuma rayuwar cikinta. Tsakaninta da Muhammad a kwana biyun da yayi a ɗakin Salima duba lafiyarta da safe ne da kuma mata bankwana da dare in zai kwanta shikenan. Shi yasa ko a yanzu da take kwashe abinci a kitchen ta ji shigarshi ɗakinta bata motsa ba haka kuma bata mishi magana ba.

Sai da ta tabbatar ya fita sallah maghrib sannan ta bar kitchen ɗin ta shiga ɗaki domin bata son su haɗu. Wanka ta fara yi sannan ta fito ta samu har ya dawo daga sallah yana falo dalilin ƙaran TV da ta jiyo, jiki a sanyaye tayi sallah kana tayi kwalliya kaɗan wanda iyakarta powder da kwalli shikenan. Fita falo tayi ta sameshi yana waya amma tana fitowa yayi sallama domin dama ya gama, hakan kuwa da yayi sai ya saka zargi a zuciyar Juwairiyya ko dai da budurwa yake waya? Wannan tunani da tayi yasa ta ji wani ɗaci a ranta amma sai ta basar ta zo ta zauna can wata kujerar daban.

“Saka mini abinci.” Shine abun da ya faɗa yana mai ƙara komawa ya zauna a jikin kujerar.

Kamar ba zata yi ba amma da ta tuno bai mata laifin komai ba sai ta tashi ta fara zuba mishi. Kamar kurame haka suka ci abincin wannan karon shima Muhammad bai mata magana ba domin maganar Salima ce take yawo a zuciyarshi ta hanashi sukuni. Ya sani tun ba yau ba Juwairiyya tana cewa yana da ɗaure fuska baya son dariya domin ko a gabanshi ta faɗi hakan, amma a yanzu sai yake ganin sun wuce wannan gurin shi da ita da zata dinga kusheshi a gaban mutane, shin me yasa ba zata gane cewa shi haka yake ba? Sannan me yasa ba zata mishi uzurin cewa ba haka kullum yake ba tunda itama ta ga the other side of him da yake teasing ɗinta? Ko dai bata ɗaukeshi a bakin komai bane? Ko dai kawai ta ɗaukeshi a matsayin escape route ɗinta ne kuma mai biya mata buƙata? Shin ta ɗaukeshi a matsayin mijinta mai daraja kuwa kamar yanda shi ya ɗauketa a matsayin matarshi ahalinshi?

Ita kuma Juwairiya tunaninta daban, ko dai har an ci moriyar ganga ce an yada kaurenta? Kwanaki tayi tunanin rayuwarsu zata iya tafiya kamar na sauran ma’aurata amma kuma yanzu shakku ya shiga ranta. Lallai tayi saurin yanke hukunci domin a yanzu da ta saci kallonshi ma sai ta ga ko murmushin nan da yake mata a da yanzu babu shi, fuskarshi a ɗaure babu fara’a kuma ko kallonta baya yi. Nan jikinta yayi sanyi matuƙa har ta ji abincin ya gundureta ta ajiye tana mai ɗaukan ruwa ta kurɓi kaɗan shima ta ajiye. Tayi tunanin zai tambayeta dalilin da yasa ta kasa cinye abincinta amma sai ta lura hankalinshi ma baya kanta kwata-kwata kamar tunani yake yi. (Shi yasa Communication is good a tsakanin ma’aurata.)

Har ya gama cin abincin ta tattare ta kai kitchen bai mata magana ba, a nan ne kuma aka fara kiran sallah isha ya tashi yana ɗaukan wayarshi da ya sakata a charge yana cewa,

“Zan fita cikin gari zan kai dare. Zaki iya rufe ƙofar ina da key zan buɗe idan na dawo.” Yana faɗin hakan ya fice ba tare da ya saurari amsarta ba.

Ji tayi idanunta sun ciko da kwalla wato hira zai je gurin budurwa a waje ita kam amfaninta ya ƙare ko? Bata ƙara minti biyar ba ta kashe kallon ta shiga sallah, har zata kwanta da wuri sai kuma ta fito ta nufi ɗakin Salima don rage kaɗaici. A can suka yi ta hira Salima na cewa,

“Har yanzu mun kasa zuwa Barkan haihuwar nan gashi sunan saura kwana uku.”

“Ai yanzu kam lokacin barkatu har ya wuce sai batun suna ake yi.”

“To ya zamu yi kenan? Zamu je goben ne ko sai ranar suna?”

Juwairiyya da dama ba wani saninsu na kirki tayi ba ta kaɗa baki ta ce,

“Gaskiya mu bari sai sunan in hakan ya miki.”

“Ni surutunta ne bana so, Iyami tana da faɗa da girman kai. Yanzu in bamu je barkatun ba sai ki ga ya zama abun magana suyi ta ƙananun maganganu.”

“Magana yau aka fara yi a kan mutum? Kuma in bamu je ba Allah ne bai yi ba zamu je ba. Girman kanta kuwa ba damuwata bace, don ni ko kallo ba zata isheni ba balle ya dameni. Ke ce dai kika basu fuska suna ƙannen mijinki amma suna miki abun da suke so.”

“To ya zan yi? Duniyar ma a nawa take? Ni bana damuwa ne ko sun yi sai in ɗauke kai kamar ban san suna yi ba. Ke dai kiyi taka tsantsan da ita ki san irin zaman da zaku yi.” Salima ta ƙarisa maganan tana langaɓar da kai.

“Allah Ya kaimu ranar sunan.”

Da haka suka cigaba da hiransu wanda yawanci Salima ce ke faɗan karya da gaskiya akan dangin Muhammad tana ta cika Juwairiyya tana batsewa tana jin sanyin halin Salimar ce yasa suke mata haka amma ita da zafinta zata je yanda babu wanda zai kawo mata wargi.

Sai tara da kwata ta bar ɗakin ta koma nata kana ta rufe kamar yanda Muhammad ya umurceta, tana kwance amma baccin ya ƙi zuwa sai juye-juye take yi a gado ƙarshe ta tafi can gefen kwanciyarshi ta kwanta, a nan bacci ya saceta ya dawo ya sameta.

Wanka ya fara yi sannan yayi shirin bacci ya zo ya tsaya a kanta yana ganin yanda ta yi ɗaiɗai a kan gadon wanda har hakan yasa rigarta ta kauce ana ganin wani sashe na ƙirjinta. Hannu ya kai ya fara wasa dashi ta motsa kaɗan kana ta riƙe hannun nashi duk a cikin bacci ta ce,

“Bee.”

Tsayawa yayi cakk kamar wanda aka daskarar yana jin wani irin ƙuna a zuciyarshi domin ya san waye take kira da sunan ‘Bee’. Ita kuma a daidai nan ta farka ta buɗe idanunta ta ganshi a kanta ga hannunshi akan ƙirjinta ta kuma riƙe da nata hannun. Cikin sauri ta sakeshi kana ta mirgina can gefenta ta kwanta, shima kwanciyar yayi amma ya kasa runtse idanunshi dalilin muryarta da yake ta ji tana kiran sunan abokinshi marigayi alhali shi yake taɓata. Kasa haƙuri yayi ya mata magana domin zuciyarshi ta kasa gaskata cewa bada saninta tayi hakan ba.

“Kin san me kika furta mini ɗazu da nake taɓaki?” Ya tambayeta cikin duhu duk da cewa sun jima da kwanciya amma ya tabbata bata koma bacci ba.

“Me na furta?” Ta mayar mishi da tambaya.

“Baki tuna ba?”

“Ban tuna ba. Zaginka na yi?”

Ajiyar zuciya ya sauƙe don yanzu ya yarda bata sani ba kawai bakinta ne da ya saba kiran sunanshi a wannan yanayin, don haka ba zai kamata da laifi ba.

“Eh.” Ya amsa domin ya gwammace ta zageshi akan ta kira abokinshi a irin wancan yanayin.

Tashi tayi ta zauna ta dafe ƙirjinta tana mai gwalalo idanunta waje ta ce,

“Da gaske zaginka na yi?”

“Zan miki ƙarya ne?”

“A’a kawai na tambaya ne don baka mini laifin da har zai sa in zageka cikin baccina ba.”

“To yau kin yi.” Ya ƙara ƙarya a karo na biyu.

“To sai kayi haƙuri don Allah ma baya kama mai bacci da laifi.”

“Shi yasa ban buge bakinki ba.”

“Ai da ka buge da ka ga tijara.” Ta ƙarisa maganan tana kwafa irin zai ga bala’in nan.

“Me zaki yi?” Ya tambayeta yana murmusawa kaɗan don har tone ɗinta ya canja ya dawo kalar na masifaffu.

“Ka gwada ka gani.” Ta faɗa tana girgiza ƙafa.

“Dukana zaki yi?”

Dariya tayi kana ta koma ta kwanta ta ce,

“Me zai kaini faɗa da kai? Naushi ɗaya in ka mini ai sai gadon asibiti.”

“To me zaki yi?” Ya ƙara tambaya don he is curious, yana son jin me zata yi.

“Kai dai ka gwada zaka gani.” Ta ƙara jan ranshi da alama dai ba zata faɗa ba don bata da abun da zata yin, kawai kuri ne.

“Ki kawo bakin ki gani.” Ya faɗa yana mai juyowa ya fuskanceta.

Ita kuma uwar neman bala’i har da mirginowa ta kawo mishi bakin tana cewa,

“Ga bakin, ga bakin.”

Jawota yayi jikinshi ya haɗe bakin nasu guri guda ta fara mutsil-mutsil amma ta kasa kwatan kanta, minti ɗaya da haka ta ma mance dalilinta na son kwace kan nata ta cigaba da karban zafafan saƙonni daga gareshi.

Mum Fateey 👌

Ranar suna tun da safe matan Muhammad suka shirya fita tare da shi akan zai ajiyesu a gidan sunan shi kuma ya wuce office. Juwairiyya ce ta fito tsakar gida tana jiransu don sun yi akan bakwai da kwata zasu fita. Tana tsaye tana karkaɗa ƙafa don bata son su ɗauki lokaci basu fito ba tunda sun ce da wuri za’a tafi.

Muhammad ne ya fara fitowa ta ɗauke kai kamar bata ganshi ba domin har lokacin ta kasa koyon gaisheshi ko mishi sannu da zuwa in ya dawo gida. Ta wutsiyar idanunta take ganin lokacin da ya shiga cikin motarshi ya kunnata ana haka ne kuma Salima ta fito riƙe da hannun HJ wanda yake tsala ihu kamar wanda ake yankawa.

“Subhanallahi! Me ya sameshi?” Faɗin Juwairiyya tana takowa zuwa gurinsu bayan ta gyara zaman jakar hannunta da yake kafaɗarta.

“Yau ma dai da boren ya tashi, wai ya tsaya in gama shiryashi ne yake ta wannan ihun.” Faɗin Salima tana ɓanɓare yaron daga jikinta don Juwairiyya ta karɓeshi amma ya ƙi yarda ya ƙara maƙale uwarshi.

“Kai! Kai! Ka rufe mini bakinka a gurin kafin na zo.” Faɗin Muhammad kenan yana fitowa daga cikin motar ranshi a ɓace domin ya gaji da sauraron ihun.

Har gaban Salima ya zo ya riƙo hannun HJ ya rabashi da ita sannan ya nunashi da yatsarshi yana cewa,

“Tun ɗazu kake kuka ana ta rarrashinka amma sai ƙara botsarewa kake yi. Uban me aka maka kake kukan? Oya rufe bakin naka ko in bugeshi.” Da haka ya ɗaga hannunshi da niyyar make bakin yaron amma a maimakon ya ji tsoro sai ya ƙara saka wata ihun.

Ganin haka ya sa Muhammad ya buge bakin nashi wanda zai ji zafi amma ba tare da ya ji ciwo ba, ai kuwa ya ƙara watsa wani ihun domin ba’a taɓa mishi duka irin haka ba. Daga Salima har Juwairiyya ɗauke kai suka yi domin zafin da suke ji a zuciyarsu amma babu wacce ta ce kanzil. Salima kan ma barin gurin tayi ta isa bakin ƙofarta ta ja ta rufe tana maƙala key.

“Oh ba zaka yi shirun ba kenan?” Da haka Muhammad ya ƙara buge bakin nashi wanda wannan karon yaron ya durƙushe a ƙasa ya fara birgima yana riƙe da bakinshi yana kuka.

Juwairiyya ce tayi saurin isa ta ɗaukeshi ta rungumeshi tsam a jikinta yayin da fuskarta kuma ɗauke yake da tsantsan ɓacin rai tana hararar Muhammad ta juya zata bar gurin ya dakatar da ita.

“Ina zaki kai mini ɗa ina mishi hukunci? Na baki izinin ki ɗaukeshi ne?” Ta ji dakakkiyar muryarshi a dodon kunnenta cikin ɓacin rai.

“Haba dukan ya isa haka in ba fasa mishi baki zaka yi ba, ka duba inda ka bugeshi har ya kumbura. He is too young da wannan dukan kwata-kwata shekararshi biyu da rabi ta yaya zai yi shiru idan ka dakeshi?” Itama ta mayar mishi ta amsa tana doka mishi harara tana jin kamar shima ta rufeshi da duka.

“Baki fi ni sanin yawan shekarunshi ba, sannan ni naga dacewan hukuntashi kuma zan hukuntashi yanda nake so. Ki ajiyeshi.” Ya faɗi hakan cikin ɓacin ran da ya fi na ɗazu domin baya son Juwairiyya ta wuce gona da iri, yana haƙuri da halayenta amma ba zai ɗauki wasu ba ciki kuwa har da hanashi hukunta ɗanshi.

Yanda ta ga yayi maganar yana huci kamar zai ci babu yasa cikinta ya kaɗa tsoro ya shiga ranta domin ta sani in ta kaishi maƙura daga shi har ita ba zasu ji daɗin abun da zai biyo baya ba. Kuma akan me? Akan yana hukunta ɗan da nata ba! Ɗan da uwarshi ma kawar da kai tayi bata ko kallon inda suke balle ta nuna abun da ake yi ya dameta. Akan ɗan da shi ya haifeshi a cikin cikinshi ba tare da ta kawo tata gudumawar ba. Juyar da kanta tayi tana kallon Salima wacce take bakin ƙofarta tana kallon gefe kamar bata san me yake faruwa ba, hawaye ne ya taru a idon Juwairiyya na tausayin yaron game da jin haushin Salima da ta kasa kwatan ɗanta da kuma tsanan Muhammad mai buge bakin ɗan shekara biyu da rabi.

“Ki ajiyeshi kar in sake maimaita miki.”

“Gashi nan sai kayi yanda kake so dashi tunda kai muguntar taka har ɗan cikinka ba zaka bari ba.” Ta faɗi hakan cikin hasala.

Wani mugun kallo Muhammad ya watsa mata kana ya gyara tsayuwarshi fuskarshi ta ƙara haɗewa sosai ya dubeta tsam ya ce,

“Me kika ce? Ni ne mugu?”

Shiru Juwairiyya tayi zuciyarta na lugude domin kiranshi da tayi da wannan sunan ita kanta ta san ta haura geji. Ajiye yaron ta yi a ƙasa wanda yana juyawa ya ga ubanshi sai ya ƙanƙame ƙafarta yana ɗaga hannunshi sama wai ta ɗagashi. Wannan ne ya jawo hawaye sintiri a fuskar Juwairiyya amma ta kasa ɗaukan yaron don kar ta ƙara laifi domin ta lura ran Muhammad ya ɓaci fiye da yanda take tunani.

Shi da kanshi ya isa gabanta ya kamo hannun yaron kana ya tsayar da shi a gabanshi ya ce,

“Rufe bakinka ko in ƙara bugeshi?” Ya ɗaga hannunshi alamar zai dakeshi ai nan da nan HJ yayi shirun har da kama bakinshi da hannunshi.

“Idan na sake jin kana kukan banza ba’a maka komai sai na cire bakin naka. Kana ji?” Ya zare mishi ido sosai wanda yasa yaron ya kaɗa kanshi da sauri yana hawaye yana kuma kallon uban nashi.

“Maza tafi gurin mamanka ta goge maka hancinka, kar in ji ko tari ka yi.” Da haka ya sake HJ wanda yayi saurin gudu zuwa gurin mamanshi amma bai yi kukan ba sai hawaye da majina da suke zuba a fuskarshi.

“To kaima ba baka ji ba? Tsaya in goge maka fuskar taka.” Faɗin Salima kenan tana ciro hanky a cikin handbag ɗinta ta fara goge mishi yana ajiyar zuciya.

A nan ne Muhammad ya dawo da kallonshi kan Juwairiyya wacce take share hawayen idanunta ya kira sunanta.

“Juwairiyya.”

Dubanshi tayi tana aika mishi harara amma bai nuna alamun hakan ya dameshi ba ya fara magana cikin murya mai kauri yet a hankali.

“Tun ba yau ba na san a wani matsayi kika ɗaukeni wanda a hakan kika aureni ba tare da kin yi la’akari da halayen da kike jifana da su ba. Bayan aurenmu kuma na baki wani lokaci ba tare da kin sani ba, lokacin da zan dinga shanye duk wasu bullshit ɗinki daga nan kuma in wa’adin ya cika ba zan ƙara ɗaukan rashin hankalin naki ba. Sai dai a yau kin jawo lokacin ya zo da wuri domin na lura ƙara gaba kike yi da rashin kunyarki da kuma rashin ɗa’arki. Kin mini abubuwa da dama amma na yau kawai zan miki magana a kai, kar ki sake ki ƙara kirana da sunan mugu! Kar kuma ki sake saka hannu ki ɗauki ɗana a yayin da nake hukuntashi. Ɗa nawa ne, kuma ina da iko dashi, da uwarshi har da ke duk a ƙarƙashina ku ke. Ya isa haka, daga yau ya isa!” Maganarshi ta ƙarshe da ya yita cikin tsawa sai da ahalin gidan nashi suka razana dukkansu.

Juwairiyya hawaye ne ya cika mata ido har bata iya ganin gabanta, bakinta kuma rawa yake yi ta cijeshi ta ciki domin bayan haushi game da tsanar Muhammad ta take ji sai yanzu kuma ya haɗu da tsoronshi da ya ɗarsu a ranta domin yau ta ga zallan tsagwaron ɓacin ranshi. Tana son yin magana amma bata san me zata faɗa ba sannan ko ta buɗe baki ƙarshenta kuka ne zai biyo baya kuma bata son abun ya girmama ya fi haka. Tana ganinshi ta blurry vision ɗinta ya koma cikin mota Salima tayi saurin sakin hannun HJ ta isa ta buɗe mishi gate ya fitar da motar ya tsaya a waje yana jiransu.

Sai a lokacin Juwairiyya ta bari hawayen suka zubo a kan ƙuncinta tana kallon yanda Salima  ta dawo cikin gidan tana saka lock ɗin gate, a nan ne  ta dubeta fuskarta cike da damuwa ta ce,

“Da baki mishi magana ba, ni baki ga ko kallon gurin bana yi ba?”

“Ba zan iya ba. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Shine kaɗai abun da ta faɗa tana girgiza kanta.

Wani dogon horn suka ji ana danna daga waje Salima tayi azaman ɗaukan handback ɗinta da ke ƙasa kana ta jawo hannun HJ suka nufi gate tana cewa,

“Ki fito in kulle gidan.”

“Ni na fasa zuwa ku je kawai.”

“Don Allah kar ki ce haka zai iya yin abun da ranku zai ɓaci gabaɗaya.”

“Let him do his worst! Ba zan je ba.” Da haka ta juya ta nufi ƙofar ɗakinta da niyyar shiga ciki amma Salima tayi saurin binta gudun kar ta wargaza mata plan ɗin da ta shirya da zata yi a gidan sunan ta ce,

“Kiyi haƙuri mu tafi tare don wallahi yanzu in kika fasa duk wani ɓacin ranshi a kaina da ɗana zai ƙare amma in yana ganinki zai rage wani abun. Ki danne zuciyarki ki zo mu tafi tare ko don Masoyinki.”

Wannan furuci na Salima ya sa Juwairiyya ta dakata sannan ta juyo fuska babu walwala ta ce,

“Wallahi don ku zan je, amma in ba haka ba babu abun da zai sa in zauna guri ɗaya da shi.”

“Ke ma haka zaki koyi haƙurin zama dashi.” Tana rufe bakin aka ƙara danna wani horn ɗin suka nufi gate.

“Wallahi ba zan iya ɗauka ba sai dai da ni da shi kullum mu kasance cikin ɓacin rai.”

Suna fita Salima ta ja ƙofar ta rufe ita kuma Juwairiyya tayi gaba fuu ta buɗe ƙofar baya ta shiga ta zauna sai cika take yi tana batsewa, Muhammad da yake gaba ya nuna kamar ma mutum bai shigo cikin motar ba. A haka Salima ta leƙo ta window tana yiwa Juwairiyya magana.

“Ki dawo gaba ki zauna tunda ke ce amarya.”

“Allah Ya sauwaƙe.” Ta faɗa kamar wacce take kyamar zama kusa dashi.

“Don Allah ki fito…” Salima bata kai ga ƙarisa maganar ba Muhammad ya katseta cikin tsawa.

“Don me yasa zaki tsaya kina roƙonta? Idan ta ga dama ta hau saman motar ina ruwanki?”

Bata ƙara cewa komai ba ta shiga gaban motar ta zauna tana sussunne kai itama fuskarta cike da damuwa amma kuwa cikin ranta daɗi take ji kamar tayi hauka, domin kuwa faɗan da suka yi kuma a gabanta ba ƙaramin ƙarfafa mata gwiwa yayi ba na kawo ƙarshen zamansu. Wannan sa’insa da suka yi tare da musayar kalamai sun bata idea kan yadda zata saka su gunduri junansu su da kansu ba tare da ta shigo cikin haske ba.

Kowa rai babu daɗi Muhammad ya sauƙesu a gidan ƙanwar tashi wacce suke uba ɗaya kuma ta rigashi aure, hakan yasa ta girmi su Juwairiyya da wasu shekaru takwas ko ɗori. Juwairiyya ce ta fara fita kamar wacce aka kora ta je can bakin ƙofar gidan ta tsaya tana mai juya musu baya domin ko kallon Muhammad ɗin bata son yi.

“Ga wannan ku bata, babu hali sosai da na saya muku zannuwa kun bata.” Ya miƙa mata dubu takwas ita da Juwairiyya su raba.

Karɓa tayi ta mishi godiya kana ta fito daga motar ya ja ya tafi. Sai da ta gyara riƙon da ta yiwa HJ sannan ta taka zuwa gurin Juwairiyya kamar zata tuntsire da dariya amma ta saisaita kanta fuska cike da damuwa ta iso tana cewa,

“Don Allah ki gyara fuskarki kar ki shiga haka suyi ta tambayanki abun da ya faru babu daɗi.”

“Sai in faɗa musu banzan halin ɗan’uwansu ne ya jawo hakan.”

“To in kika yi haka zasu faɗa mishi kuma kin ga ba lalle bane ya ji daɗin hakan. Ga dubu huɗu yace a baki ki bawa mai jego.” Ta miƙa mata kuɗin ta karɓa.

“Maman Masoyi mu shiga don kalamanki ma ƙara ɓata mini rai suke yi.”

Kaɗa kai Salima tayi kana ta shige gaba Juwairiyya ta bita a baya fuskarta babu annuri. Ita kuma Salima murmushi ta kwaso ta yaɓawa tata fuskar, suna shiga suka samu ba’a fara taruwa ba sai dangin mai jegon kaɗan da zasu yi girkin abincin suna.

“Ha’ah ya aka yi Goggo Ma’u ta rigani zuwa ni da nace ni zan buɗe gidan mai jegon?” Faɗin Salima ga matan wanda biyun cikinsu ƙannen Muhammad ɗinne da kuma ɗaya daga cikinsu take magana.

“To dai na rigaki zuwa, yanzu ya rage ki binciko dalilin da yasa kika yi latti har na samu na buɗe gidan.” Shema’u Ta mayar mata da amsa cikin raha.

Nan suka ɗan tsokani juna kaɗan kana aka hau gaishe-gaishe wanda sai a nan Juwairiyya ta saka baki ta gaishesu suka amsa fuska babu yabo babu fallasa.

“Ita ce amaryar Ya Muhammad ko?” Wata ta tambaya duk da cewa sun taɓa ganinta da suka je ta’aziyyar marigayi.

“Eh ita ce.” Salima ta amsa musu.

“Ku isa mai jegon tana ciki.”

“To bari mu gaisa sai mu fito da shirin aiki.” Salima ta ƙara faɗi.

“A’a wallahi mun hutacceku, mu kaɗai ma zamu iya yi domin yanda kika yi gayun nan baki yi kala da murhu ba.” Faɗin Shema’u wacce har cikin zuciyarta ba tayi ne da gayya ba, amma sai Juwairiyya ta ji kamar habaici aka mata.

Domin kuwa ko shigen da suka yi a yanzu Salima ta fita cakarewa ta saka lace mai tsada ɗinkin doguwar riga da aka watsawa stones, ga kuma full sarƙa, ɗan kunne, awarwaro, zobe da kuma agogo a hannunta, ɗaurin nan ta kafashi ya mata kyau haka kuma fuskarta ta mishi kwalliya. Ita kuma Juwairiyya simple atampa ce a jikinta na riga da siket sai ɗan kunne da ta saka wanda yake ɗan guntu wai bata son damuwa. Fuskarta babu kwalliya in ka ɗauke hoda da kwallin da suka goge bayan tayi hawaye ɗazu kafin su fito. Idan aka dubesu a wannan lokacin sai a ɗauka Tafiyar su ba ɗaya ba, amma nan wai uwargida ce da amaryarta.

“Dama har ana gane kalan murhu ne? To ni dai sai na yi don ko a da ina yi, yau ma kuma ba zaku hanani ba.” Ta faɗa cikin raha kana ta yi gaba Juwairiyya da ta dawo kurma kuma ƴar kallo ta bita a baya sumui sumui tana jin ɓacin rai a tattare da ita akan wanda ɗan’uwansu ma ya kunsa mata.

 A can ɗakin mai jego suka tarar tayi wanka tana shiryawa yayin da shi kuma jaririn yanzu ake mishi wanka yana ta callara ihu. Juwairiyya ce ta zuba mishi ido tana addu’a a ranta itama Allah Ya nuna mata ranar da zata ɗauki nata haka.

Bayan sun samu guri sun zauna aka fara gaishe-gaishe a nan Iyami mai jego ta kaɗa baki ta ce,

“Matan Ya Muhammadu sai yau ko? Na ɗauka ai zaku zo barkatu.”

“Ai wallahi mun so zuwa sai kuma amaryar tamu ta ce zata yi baƙi, daga nan kuma muka ga har sunan ya gabato shine muka yanke shawarar sai yau kawai mu zo.” Salima ta zayyane musu kamar dama ta jima da haddace hakan.

Shiru mai jegon tayi kamar bata ji me Salima ta faɗa ba ta zubawa Juwairiyya ido tana kallonta alamar ita take son ta amsa. Ita kuma Juwairiyya hankalinta ma na kan jaririn da ake sakawa kaya yana ta mutsil-mutsil da alama yunwa yake ji, fuskarta cike da murmushi take kallonshi domin har ta mance ɓacin ran da ta shiga da safe.

“Amaryar Ya Muhammad ashe ke kika hanaku zuwa?”

Sai a lokacin suka samu hankalin Juwairiyya ta juyo tana murmusawa ta ce,

“Ina na hanamu zuwa?”

“Wai kin ce zaki yi baƙi shi yasa baku zo barkatu ba.”

“Ohh, Wallahi ƙannen marigayi ne zasu kawo mini ziyara sai kuma suka ɗaga zuwan har dai lokaci ya ƙure mana. A mana afuwa, amma jariri nan kyakkyawa ne Tabarakallah Masha Allah.”

“Uhm haka dai ake cewa.” Iyami ta faɗa tana murmusawa a karon farko tun zuwansu.

“In an gama shiryashi a bani in riƙeshi. Me sunan nashi?”

“Ahmad, mai sunan yayan babanshi ne.”

“Ah ki ce ubana ne wannan, shi yasa yayi kyau masha Allah. Allah Ya rayashi akan sunnah.”

Duka ƴan ɗakin suka amsa da ‘Ameen’ musamman Iyami mai jego da ta kasa rufe bakinta domin a take Juwairiyya ta kwanta mata a rai, saɓanin Salima da bata son halinta na shiru tana cewa shirunta ba na Allah da Annabi bane na munafukai ne, hakan ne ya jawo rashin jituwa tsakaninsu duk da cewa ita Saliman ta ƙi ta nuna cewa akwai ƴar tsama tsakaninsu domin bata son yi abokin faɗa a cikin dangin Muhammad, sai dai duk yanda ta kai da cusa kai da wayonta Iyami ta fi ƙarfinta kuma ta ƙi amincewa ta sake jiki da ita.

“Baƙin naki su Hafsat ko? Ai sun taɓa zuwa gidan nan sau ɗaya ina amarya shi marigayi ya kawosu, to da yake ba sa’anni muke ba sai zumuncin namu bai yi nisa ba. Amma dai in an haɗu ana gaisawa cikin mutunci.”

Nan fa hira ya ɓarke tsakanin Iyami da Juwairiyya wanda hakan ba ƙaramin ƙonawa Salima rai yayi ba domin ba haka ta so ba, ta so ne Iyami ta ƙi jinin amaryar tata kamar yanda itama basa jituwa, sai dai hakan bai samu ba. Tashi tayi tana cewa,

“Bari mu isa gurin girki mu kama aiki kar mu taru a nan. Aunty Iyami in kina da fallen zani ki bani in ɗaura kan kayana.”

Da haka Iyami ta miƙa mata zani ta ɗaurashi har ƙirjinta kana ta cire su awarwaronta ta sakasu a jaka irin za’a je a tiƙi aikin nan amma ko kallo bata ishi Iyami ba.

“Mu je ko?” Ta yiwa Juwairiyya magana.

“A’a ki barta yau kam mun hutar da ita tunda yau ta fara shiga dangi, ai ana tare, haihuwa kuwa yanzu muka fara.” Faɗin Iyami ana miƙa mata ɗanta don ta bashi nono.

Wannan magana tamkar ruwan zafi aka watsa a ƙirjin Salima wacce ta lura rashin mutuncin Iyami na yau ya fi na kullum. Ita kuma Juwairiyya bata damu don tayi aikin ba hasalima zata so tayi saboda ta gwada profession ɗinta na girkin mutane masu yawa.

Rai babu daɗi Salima ta fice tare da wata daga cikin ƴan ɗakin, a can ake tambayarta ina kishiyar tata take tace Aunty Iyami ta tsayar da ita da yake babu halin yin ƙarya ko lankwasa maganan ta yanda zasu ga laifinta don ga wacce aka yi komai a gabanta kusa da ita.

Amma a nan ne tayi dabarar sako maganar da suka yi ita da Juwairiyya akan waɗanda suka zo gidan nasu washegarin tarewanta suka tafi ba tare da sun ga ɗakin nata ba.

“Ai baku santa da abun dariya ba, wallahi cewa tayi gulma ce take kawo mutane washe garin tarewar amarya in ba haka ba menene an yi biki jiya da ku sannan yau ku dawo wai ganin ɗaki? Tace wai ɗakin gudu zai yi?” Nan ta kwashe da dariya wasu suka tayata amma ransu bai yi daɗi ba.

“Oh haka ta faɗa? To Allah Ya bata haƙuri ba zamu sake ba.” Shema’u ta faɗa wacce abun ya fi ƙonata kuma bata iya ta ɓoye a fuskarta ba.

“Kar ki ɗauki abun da zafi na san ba da ku take ba, kawai tana maganar ne in general.”

“Koma menene bai kamata ta faɗi haka ba.”

Nan aka yi ta mayar da zance Salima dai ta sunkuyar da kai ƙasa har tana cewa wai da bata kawo maganar ba. A nan ta zage aka yi ta aiki da ita cikin nishaɗi domin duk da cewa bata samu ta ɓata goma ba to dai ta ɓata bakwai kuma Juwairiyya zata gani idan Tafiyar tayi nisa. (Ban hanaku aiki a gidan dangin miji ba, ahh to).

Ita kuma Juwairiyya bata san tarkon da aka haɗa mata ba a can bakin murhu, tana cikin ɗaki riƙe da jariri har ta bada wayarta aka ɗaukesu a hoto, a nan ne kuma ta sanya shakku a zuciyarta game da maganar Salima akan halin Iyami da take cewa tana da girman kai da iyeyi, to ita bata gani ba kuma wannan shine na biyu da maganarta baya zama gaskiya. Na farkon ƙarfin sha’awar Muhammad sai kuma na biyu halin Iyami, da alama tayi kuskure da kuma gaggawa wajen yanke musu hukunci.

Ana sallar la’asar suka koma gida wanda Juwairiyya ta lura wasu daga cikin dangin Muhammad ɗin na mata wani gani gani, itama ta ɗauke musu wuta ta cigaba da hira da wanda suka bata fuska.

Sai da suka tafi Shema’u ta zo gurin yayar tasu wato Iyami take mayar mata da maganan da Juwairiyya tayi akan zuwansu ganin ɗakinta, da alama dai hakan ya ɓata mata rai sosai har kasa haƙuri tana amayarwa.

“Kar ki sha mamaki bata faɗi hakan ba kawai dai haɗa guri ne irin na Salima, yarinyar nan ku ne kuke ganinta haka sumui sumui amma ni na san halinta na munafurci.”

“Ke dai Aunty Iyami jinin ku ne bai haɗu ba amma ai ba zata mata ƙarya ba, don daga jin yanda aka yi maganar kin san ita ce don ko shi Ya Muhammad ɗin aka ce bata barshi ba tana mishi fitsara.”

“Ita ta faɗa muku tana yiwa Ya Muhammad ɗin ma fitsara ko? To koma menene ni da na zauna da ita muka wuni tare ban ga aibunta ba, kuma shi magana da kike gani zarar bunu ce, wataƙila hiransu suke yi na sirri tsakaninsu amma ita ta zo ta bayyana na kishiyar ta ɓoye tata. Abun mamaki kuwa wallahi tun zuwansu har suka tafi ban ji ita Juwairiyyar ta kawo maganar Salima ba, ku kuma da kuke can ashe kun kafe chaptern ta da kishiyarta tana faɗa muku ƙarya da gaskiya.”

“Ke dai Aunty Iyami kullum Salima ce mai laifi a gurinki, mu bar maganar kawai.”

Mum Fateey 👌

Bayan suna da kwana ɗaya Juwairiyya ta karɓi girki, wannan karon ƙin haɗuwanta da Muhammad ya fi na koyaushe domin hatta abincin su da take haɗawa guri ɗaya yau sai ta ware nata ta kai ɗaki ta ajiye tayi zamanta a can. Shi kuma gogan da ya ga haka sai ya kama kanshi ya nuna kamar bai san me take yi ba, hakan yasa har ya shigo ya kwanta bai haɗa ido da ita ba.

Ya san bata yi bacci ba dalilin wayarta da ke hannunta tana dannawa, juyar da kanshi yayi gefenta kana ya sa hannu a jikinta zai jawota jikinshi ta ce,

“Kar ma ka fara, bana so.”

“Ban gane ba, me yasa?” Ya dakata yana zubawa gadon bayanta ido.

“Ni dai na faɗa maka bana so.” Ta ƙara nanatawa cikin ɓacin rai.

“To ni kuma ina so kuma buƙatata zan biya.”

“Sai ka je gurin waɗanda baka musu tsawa ka biya a can.”

Shiru Muhammad yayi wanda hakan ya yiwa Juwairiyya daɗi domin ta sani hakan na nuna ranshi ya ɓaci, in ma ruɓewa yayi ita ba damuwarta bace.

“Zaki dinga guduna kenan duk ranar da aka samu matsala a tsakanin mu? Saboda kin yi laifi na miki faɗa shine zaki hanani kanki?” Ya ƙara mata wasu tambayoyin.

Shiru tayi bata amsa ba, hakan yasa ya ƙara kai hannunshi jikinta don yana da buƙatarta sosai ba zai iya fushi a yanzun ba, sai dai yana taɓata ta fisge ta sauƙa a gadon ta fita a ɗakin gaba ɗaya. In ran Muhammad dubu ne to duk sun ɓaci, ta wani gurin kuma tausayin kanshi ne ya ɗarsu a ranshi domin da alama matan nashi sun samu hanyar horashi da wulaƙantashi ta hanyar da tsawa ko force ba zai mishi amfani ba. Ba zai yiwa mace dole ta kwanta dashi ba, haka kuma ba zai dinga bibiyarta kamar soko don biyan buƙatar tashi ba. Idan haka suka zaɓa zai yi haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai kawo mishi mafita, da wannan tunanin ya runtse idanunshi yana niyya a zuciyarshi zai tashi da azumi gobe da izinin Allah.

Juwairiyya tana isa falo ta kwanta akan three sitter tana jin nishaɗi a ranta domin ta rama abun da Muhammad ya mata, idan shi juninshi tsawa ne da kafa doka kamar hukuma to ita kuma ta san hanyar da zata horashi. Ta sani hakan ba abu ne mai kyau ba, domin kuwa ko a lokacin da take tare da Hafiz ko sun sami matsala in ya nuna yana buƙatarta bata hanashi saboda tana sonshi kuma bata son su tashi a haka, amma wannan Muhammad ne, mutumin da bata so kuma take ajiye da exact date ɗin da zata bar mishi gidanshi. Kwanaki da take tunanin basu chance ta yaudari kanta sannan ta lura giyar son kaɗaituwa da ɗa namiji ne ya sakata wannan banzan tunanin, zasu koma zaman jiya, wato zaman doya da manja zaman kowa tashi ta fishsheshi.

Tana wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita bayan ta wahala dalilin kwanciyar gurin bai mata daɗi ba, ita ce bata farka ba sai da Muhammad ya zo ya tasheta ya wuce masallaci. Tana lazimi ya dawo amma sai ta ji ya zauna a falo bai ƙariso cikin ɗaki ba, murmushin cin nasara tayi domin da alama shima ya ɗauki hannu kuma hakan take so.

Gari yana haske ta tashi ta wuce kitchen sai a lokacin da ga abunda ya tsayar dashi, danne-danne yake yi a laptop ɗin shi wanda tun da ta zo gidan bata taɓa ganin ya buɗe yana amfani da ita ba sai dai ya tafi office da ita ya kuma dawo da ita. Tunani tayi yau ko uwar me yake dannawa haka da sauri-sauri? Ko rubutun littafin Hausa ya fara? Da kuwa an ga riƙaƙƙiyar POV na male character ɗin.

Duk da cewa sun samu matsala ta saka mishi breakfast ɗinshi yanda yake so kana ta kawo bakin falonta ta ciki ta ajiye mishi kana ta zauna a nan ganin shi kuma yana ɗaki yana shiryawa. Haka ya fito ya wuceta babu wanda ya kula juna yayi ficewarshi ba tare da ya ɗauki abincin ba, wannan abu da yayi ya matuƙar ƙona ran Juwairiyya, don me yasa ba zai ɗauka ba? Wato shima yana son rama abun da ta mishi kenan? Don saboda shi ta tashi da safen nan ta ɗaura girki domin in don ta ita ce da Salima zasu iya kaiwa tara zuwa goma basu karya ba. Tana jin ɗaci a ranta ta shige ɗakinta ta kwanta akan gado wanda cikin minti kaɗan bacci yayi awon gaba da ita dalilin cewa kwanciyar da tayi a falo bai mata daɗi ba.

Bata tashi ba sai sha ɗaya da rabi, a gurguje tayi brush ta dawo falo ta samu abincin da ta ajiye mishi yana nan, hakan yasa ta ɗauka ta kai kitchen ta ɗibi wanda zata ci sauran kuma ta saka a roba ta kai fridge tana mita a ranta na wulaƙancin da Muhammad ya mata. Kafin ƙarfe biyu ta cika ta gama girki da share-share har da wanka. Tana  zaune a gaban mirrow ta shafa mai, har ta ɗauko powder da kwalli sai kuma ta fasa ta mayar dasu domin da gaske take yi za’a koma gidan jiya, Muhammad bai isa ta mishi kwalliya ba!

Abincinta ta ɗiba ta fita dashi zuwa sashen Salima wacce ta samu tayi kwalliya ta hakimce a kan kujerarta tana kallon tv ga HJ a ƙasan carpet yana wasa sa motarshi mai waƙa.

“Masoyi in zo a ɗanani a motar ne?” Faɗin Juwairiyya tana kallonshi lovingly.

Girgiza mata kai yayi wanda hakan ya sakasu dariya ita da Salima.

“Yau dai an ji kanku.” Faɗin Salima cikin zolaya.

“Ai na lura tun ranar da Babanshi ya buge mishi baki nima ya ɗauke mini wuta, baka san cewa da na zo kareka nima laifin ya shafeni ba ko?”

“Ai kuma yana zuwa gurin babanshi su yi wasansu kamar da, da alama dai ke ɗin ce ya ɗaurawa laifin gaba ɗaya.” Salima ta faɗi abun da ta san zai sosa ran amaryar tata.

“Ohh abun haka ne Masoyi? To ni meye laifina? Allah Ya baka haƙuri. Ka zo mu ci abinci.”

Nan ma ya maƙe mata kafaɗa ya ci gaba da wasanshi. Gaisawa suka yi da Salima wacce tun safe basu haɗu ba kana ta fara cin abincinta suna hira, sai da aka fara kiran sallan la’asar sannan matan suka farga maigidansu bai dawo ba. Salima ce ta dafe ƙirji cike da tsoro tace,

“Maza ɗauki waya ki kirashi mu ji me ya faru bai dawo ba, yau na shiga uku garin hira na manta da mijina.”

Wani gyatsine Juwairiyya tayi wanda bata bari Salima ta gani ba a ranta kuma haushinta ta ji ganin yanda ta wani ruɗe don kawai mijinta ya ƙara awa ɗaya da rabi a akan lokacin da ya saba dawowa gida.

“Ba zan kirashi ba, ai ya san hanyar gida.” Faɗin Juwairiyya tana mai tattara abubuwan da ta taho da su zata koma ɗakinta.

“Ke ya kamata ki kirashi tunda a ɗakinki ya kwana kuma a nan zai sauƙa ya ci abinci.”

“Ke kiyi, amma ni ba zan yi ba.”

“Kar ki ce ina shiga haƙƙinki ko kuma kiyi tunanin so nake yi in shiga tsakaninku shiyasa bana irin hakan kuma nake cewa kiyi.”

“Bai dameni ba kuma ko a gaba ba zai dameni ba. Miji naki ne kina son kayanki, nima kuma miji ne amma kamar hoto yake a gurina. So na baki daman kiyi duk abun da kike so babu ruwana.” Tana faɗin hakan ta fice bayan ta mata sallama.

Ran Salima fari tass ta ɗauki waya ta shige har cikin ɗaki sannan ta kira Muhammad wanda ringing ɗaya ya ɗauka ta gaisheshi ya amsa.

“Muna ta zuba ido shiru baka dawo ba shine nace bari in kira in ji ko lafiya.” Ta yi maganar cikin sanyi kamar wacce take tsoron dodon kunnenshi zai yi ciwo.

“Ina wani cike-cike ne akan batun karatun nan, Allah Ya yi na samu sai shirin tafiya.”

“Kai Alhamdulillah Masha Allah.” Haka Salima tayi ta godiya ga Allah tare da mishi addu’o’i yana amsawa.

“To yanzu a ina zaka ci abinci? Kar ka zauna da yunwa fa ka san kana da ulcer.”

“Ina azumi. Sai na dawo.” Da haka ya kashe wayarshi ya barta cike da murna tare da taraddadin tafiyarshi wanda hakan ba ƙaramin kewarshi zata yi ba ita da ɗanta.

 A nan kuma ta fara tunanin ya aka yi hiran karatun nashi bai taɓa haɗata da Juwairiyya ba? Ko dai bata sani bane? In dai bata sani ba to zata barta a haka saboda idan tafiyar ya matso ta ji labari ranta zai fi ɓaci in ma daɗi zata ji ita ta jiyo.

Juwairiyya tana nan har goshin maghrib bata ɗaura abincin dare ba don ta lura da gangan Muhammad ya mata haka wato kauracewa abincinta, tana son jin dalilin ƙin dawowarshi amma ta kasa zuwa gurin Salima jin ba’asi. Yanke shawara tayi wannan karon akan ba zata yi abincin daren dashi ba don babu kyau almubazzaranci domin abincin Lunch ɗin ma almajiri ta juyewa bayan yayi bara a bakin gate.

Ganin Salima tana son Indomie amma Muhammad ya hanasu ci yasa ta soya musu shi da kwai ta zuba mata nata a kula kana itama ta kai nata falo ta ajiye ta shiga wanka a lokacin har an idar da sallar maghrib.

“Juwairiyya.” Ta ji Muhammad ya kira sunanta a falo bayan ta fito daga banɗaki ɗaure da towel a ƙirjinta.

Bata amsa ba don bata yi tsammanin ya dawo ba amma dai zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske domin ta sani akwai drama a gabansu.

“Juwairiyya!!” Ya ƙara kwala mata kira wanda wannan karon sai da hanjin cikinta suka yi rawa wanda na tsoro ne da kuma excitement, excitement ne menene? Shine bata sani ba.

“Gani nan. Haba!”

Da haka ta zurma uban hijabi kana ta fita fuska a turnuƙe wai ko zai ga hakan ya sarara mata ko ya ji tsoronta. A falo ta sameshi zaune a kan kujera ga kulan abincinta ya buɗe bai rufe ba.

“Ina abinci na?”

“Shine kake ta kwala mini kira haka har kana bani tsoro?”

“I asked you a question, answer me.”

“Ban yi da kai ba.”

Mamaki ne ya cika a fuskarshi don bai yi zaton hakan ba, ya ɗauka zata ce wannan ne abincinshi amma wai bata ma yi da shi bane! Shi da gidanshi da guminshi?

“Ban gane ba.” Ya tambayeta don ya kasa gaskata abun da ya fito daga bakinta.

“Ban san zaka ci ba shiyasa ban yi da kai ba tunda na ga ba kullum kake cin abincin ba.”

“Ta nan kika ɓullo kuma?” Ya ƙara mata wata tambayar yana mai tashi tsaye.

Bata amsa mishi ba illa hararanshi da tayi ta kawar da kanta gefe, ta yaya zata faɗa mishi cewa she was hurt ne na ƙin ɗaukan breakfast ɗin shi da kuma ƙin dawowa da rana cin lunch? Ta sani she might sound hurt or worse, desperate idan ta faɗa mishi dalilinta na yin hakan.

“Shikenan.” Da haka ya fita zuwa tsakar gida Juwairiyya ta ja tsaki mai sauti kana ta koma cikin ɗakinta.

Muhammad yana shiga falon Salima ya samu tana jera abinci kan dinning table ya isa ya zauna ta miƙo mishi cup ɗin black tea irin yanda yake so, daga nan kuma ta fara zuba mishi abincin wanda fried rice ne da coslow sai kuma chips da aka yiwa wanka da sauce ɗin albasa. Sai da ya fara cin abincin sannan fa fara jan shi da hira amma bai amsa ba, ganin haka yasa ta ƙumshe bakinta don ta lura ranshi ya ɓaci ainun da abun da Juwairiyya ta yi.

Tun lokacin da ya faɗa mata yana azumi ta aika fruits ta mishi fruits salads don yana son sha idan ya zo Iftar, wai akan idan ya dawo zata kai mishi can tunda Juwairiyya ta bata go ahead ta yiwa mijinta hidima ko da kuwa a ɗakinta yake. Sai dai tana ganin maghrib ya ƙarato bata ji motsin Juwairiyya a kitchen ba ta tabbatar bata san yana azumi ba kuma wataƙila ba zata yi girki ƙasaitacce irin wanda mai azumi zai ci ba, da wannan tunanin ta shiga kitchen ta ɗaura mishi abun da yake so, tana girkin Juwairiyya ta kawo mata abincin daren nasu a kula guda ɗaya wanda sai da ta tafi ita kuma ta buɗe ta kwashe da dariya domin yau za’a yi rigima a gidan.

Tana gamawa shi kuma ya yi horn a waje ta fita ta buɗe mishi gate ya shigo, bayan ta gaisheshi tare da mishi sannu da shan ruwa ya wuce ɗakin Juwairiyya ta bi shi da ido tana murmushin mugunta. Daga nan ta koma kitchen ta kwashe abincin wanda ta sani yanzu zai shigo gurinta ai kuwa tana jerasu sai gashi ya shigo kamar wanda aka hankaɗo babu magana babu komai ya zo ya zauna ta fara zuba mishi.

A gefenshi ta zauna sannna ta tuna da fruit salads ɗin ta ɗauko mishi a fridge ta zuba mishi a bowl ta ajiye a gabanshi.

“Ga fruit salads, kana buƙatar wani abun ne?”

Girgiza mata kai yayi yaci gaba da cin abincinshi. Sai da ya kusa cinyewa sannan ya dubeta ya ce,

“Ina Muhammad Hafiz?”

“Yana gidansu Nanayo zan maka girki ne yana ta damuna sai na ce ta ɗaukeshi su tafi.”

“Ya aka yi kika san zan buƙaci abinci?” Ya mata tambayar yana kafeta da ido sai dai bata ga alamun ɓacin ran irin na ɗazu a fuskarshi ba.

“Kawai na ga da rana da nace ta kiraka ta ƙi ni kuma na kira kace mini kana azumi na aika maka fruits ɗin, ɗazu kuma na ga har maghrib ya kusa bata shiga kitchen ba nace duk yanda aka yi bata san kana azumi ba. To da har zan faɗa mata amma na fasa saboda ina gudun kar ta mini masifa don kwanaki tace kar in sake faɗa mata wani abun da kake so da wanda baka so don ba damuwarta ba ce.”

“Haka ta faɗa?” Muhammad ya tambayeta ranshi na ƙuna.

Gyaɗa mishi kai tayi fuskar nan tata kamar zata yi kuka ta ce,

“Don Allah duk abun da yake tsakaninku ku yi solving ku daina irin haka domin ni da nake tsakiyarku bana jin daɗinshi, sannan bana son in ga abun da na ɗaukeshi da girma wata kuma tana wulaƙantawa tana ganin bai isa ba, wallahi bana jin daɗin hakan.” Tana faɗin hakan ta runtse idanunta hawaye ya zubo a fuskarta ta tashi da sauri ta shige ɗakinta irin kuka ya ci ƙarfin tan nan.

Kwala mata kira Muhammad yayi ta amsa ta fito tana goge hawayen fuskarta tana kallon ƙasa.

“Me yasa kike kuka?”

“Babu.” Ta bashi amsa tana share wani hawayen.

“Ki bani amsa ki daina cewa babu.”

“Kawai bana son ta cigaba da treating ɗinka haka, idan ita bata sonka ni kuma ina sonka kuma ba zan iya kallon kana wulaƙanta da wahala ba, irin haka in ta faɗawa wasu kana cin abinci a gurina alhali ita ce da girki sai su ɗauka mallakeka nayi hakan kuma zagi zai jawo mini. Kawai ina son a zauna lafiya ne a daina irin haka.”

“Kar ki damu kin kusa daina ganin hakan, kuma ki daina saka damuwarta a zuciyarki domin ni da take yiwa ma bana damuwa. Maganar mutane kuma kar ya ɗaga miki hankali domin ni nake zaune da ku na san halinku. Allah Ya miki albarka akan faranta mini da kike yi.”

“Ameen. Zan je in yi wanka in yi sallah.” Ta amsa tana matse wani kwallan.

“Ki kira yarinyar nan ta dawo mini da ɗana.”

“To.” Ta amsa tana shiga ɗakinta ta buga tsalle sama ta dawo wanda hakan yasa Muhammad da yake falo ya ji kamar faɗuwa tayi ya tashi da sauri ya nufi ɗakin cikin ruɗewa yana kiran sunanta.

“Salima faɗuwa kika yi.”

Ita har ta tsorita amma ganin bai gane mai ya faru ba sai ta riƙe goshinta ta fara wayyo wayyo, a haka ya shigo ya sameta tana cije baki.

“Me ya faru?”

“Na zo wucewa na buge kaina a gini.”

“Sannu, ɗaga hannun naki in gani.”

Ta ɗaga hannun ya saka tafin hannunshi ya fara mulmulawa tana ash wash, wanda dukkansu basu san cewa Juwairiyya na falon ba tana sauraransu.

“Ki tsaya in mulmula miki da kyau.”

“Da zafi ne, ahhh Baban Hafiz da zafi.”

Wani irin malolon baƙin ciki ne ya zo ya tokare a wuyan Juwairiyya wacce ta ɗauki hakan da wata manufa, saurin fita daga falon tayi hannunta riƙe da na HJ wanda Nanayo ta dawo dashi amma ta ƙi shigar dashi domin Salima ta faɗa mata in dai Muhammad yana ciki kar ta kuskura ta shiga.

“Zo mu tafi, idan sun gama zan dawo da kai.” Ta faɗi hakan tana jin ciwo a ranta, don ɗazu da ta bawa Salima daman ta yiwa mijinta hidima ko da ranar girkinta ne bata ce har da tarayyar aure ba, me yasa bata yi tunanin banda shi ba?

Mum Fateey 👌

Ko da Juwairiyya ta mayar da HJ bayan ta tabbatar iyayenshi sun gama cin amanarta Muhammad bai koma ɗakinta ba sai ƙarfe taran dare ya sameta a kan gado ta kwanta tana bacci. Kallonta kaɗai da yayi sai da zuciyarshi ta ɓaci ya kau da kai ya cire kayanshi ya shiga wanka. Duk da cewa yana wanka kullum da dare in zai kwanta bai hana Juwairiyya tunanin wani wanka zai yi amma ba na soso da sabulu ba, hakan yasa ta ji hawaye ya taru a idanunta ya gangara ya sauƙa a kan pillow. Har ya kwanta ya lura kamar bata yi bacci ba ya kira sunanta.

“Me ne?” Ta amsa a zuciye.

“Na samu zuwa ƙarin karatun.”

“Damuwarku.”

Bai ƙara cewa komai ba domin tun  jiya ya sa a ranshi zai fita daga harkar Juwairiyya har sai tayi hankali idan kuma abun ya ƙi zai haɗata da magabatanta domin bai san a wani matsayi ta ɗauki zaman auren da shi ba, kuma ba zai iya rayuwa da ita a haka ba, ko dai ta canja ko kuma ya aikata wani laifi mai girma da rayuwaka zasu ɓaci.

Washe gari ya tashi jikinshi babu daɗi wanda ya fara tunanin rashin lafiyanshi ne yake ƙoƙarin dawowa, tun kafin ya fita zazzaɓi yake ji hakan yasa bai saurari ko Juwairiyya tayi girki da shi ko bata yi ba ya nufi asibiti. Yana isa kuwa ya zube musu a gurin aka yi emergency da shi, a nan aka ɗaura mishi ruwa, sai da ya fara dawowa hayyacinshi sannan ya kira Salima ya faɗa mata tare da yayanshi wanda yayi ta faɗa akan me yasa zai tafi asibiti shi ɗaya alhali ya san yanayin ciwon nashi.

Salima hankali a tashe ta je ta samu Juwairiyya take faɗa mata halin da ake ciki, a zuciyarta tace Allah ne Ya kamashi da ya ci amanarta jiya amma kuma ta ji tausayinshi kaɗan hakan yasa da suka fito tsakar gida cikin shiri ta dubi Salima ta ce,

“Ko zaki yi gaba in dafa mishi abinci don bai karya ba ya fita.”

Salima ji tayi kamar ta kife Juwairiyya da mari amma ta danne ta ce,

“Shikenan. Ki mishi abu mai ruwa-ruwa, ko kuma kawai ki mishi gwaten dankali amma kar ki saka attarugu don in ulcern ta tashi baya cinta.”

Da haka ta buɗe store Juwairiyya ta ɗibi abun da zata buƙata har da na lunch sannan ta fita cikin sauri riƙe da HJ a ƙugunta, itama kuma ta kwaɓe hijabinta ta faɗa kitchen wanda cikin awa ɗaya ta gama ta kwashe sannan ta saka a basket ta fita waje bayan ta rufe musu gidan.

A can asibiti ta sameshi zaune akan gado yana cin abu kamar gwaten dankali a cikin take away Salima na tsaye a kanshi hannunta riƙe da goran ruwa tana bashi in ya buƙaci hakan. A nan ta tuna da ranar da suka zo tare da mijinta Hafiz a lokacin tana cikin farin ciki bata da damuwar komai, tana tunawa ta zauna akan plastic chair ta ƙi gaishe da Muhammad saboda baƙin halinshi sai gashi yau ta shigo asibitin ba tare da Hafiz ba, ta shigo ne a matsayin matar mai baƙin halin wanda bai ma damu da ita ba.

“Sannu. Ya jikin naka?” Wannan karon ta gaisheshi ba tare da an mata dole ba. Lallai rayuwa juyi-juyi.

Bai amsa ba haka kuma bai ko kalli inda take ba illa abincin da ya ƙara kaiwa bakinshi ya fara taunawa a hankali.

“Ai ban yi tunanin zaki yi da wuri ba shiyasa na bi nan restaurant na saya mishi, amma wannan ɗin ma bai ɓaci ba ki ajiye zai ci da rana.” Salima tayi maganar kamar wata mai bada umurni.

Sumui-sumui Juwairiyya ta ajiye basket ɗin a gefe kana ta samu guri ta zauna akan kujera, sai ta ji kamar she is not welcome a gurin kamar ita ce bare domin hatta Salima bata ƙara mata magana ba har aka shafe kusan minti biyar. Sai a nan ne Muhammad ya buɗe baki yayi magana.

“Ki koma gida.”

“Saboda me yasa?” Tayi maganar a hasale.

“Bana son ku bar gidan babu kowa, sannan nima ba zama zan yi ba zasu sallameni anjima zan dawo gidan. Ki ɗauki yaron ku tafi tare.”

“Da ka barta ko hutawa tayi tunda yanzu zuwanta.” Faɗin Salima kamar abun kirki sai dai ta san abun da ta ɗana.

“Hukuncin da na yanken bai yi ba kenan? Da ƙafarta ta zo ne ba abun hawa ta hau ba?”

“Ya isa ba sai ka zageni ba zan tafi.” Juwairiyya rai a ɓace ta miƙe kana ta ɗauki HJ wanda yake zaune kusa da babanshi akan gadon yana shiru kamar bashi da rigima suka fita tare tana jin ƙunci a ranta.

Ko a gida HJ bai yi bore ba sai dai ya je ƙofar mamanshi sau ɗaya yana bugawa ta zo ta sameshi ta faɗa mishi ta tafi asibiti allura amma zata dawo, haka ta ja shi kitchen ta kwaɓa dough ɗin cookies ta mishi duk a cikin awa ɗaya komai ya kammala. Ai kuwa a nan ta ga fara’arshi domin kasa bari yayi cookies ɗin su yi sanyi, haka ta gutsira mishi a kan plate ta ajiye mishi a ƙasa ita kuma ta ƙara shigewa kitchen ta ɗaura abincin rana.

Ana kiraye-kirayen sallah Azahar ta gama ta kwashe sannan tayi sallah ta fita ta kira mai napep har ƙofar gida ya saka mata abincin a ciki suka ƙara komawa asibiti. A can ta samu ƴan’uwan Muhammad ƴan zuwa dubiya sun kawo mishi abinci har basket huɗu, suka gaisheta tare da mata gaisuwar mai jiki ta amsa tana sunkuyar da kai ƙasa domin a cikinsu akwai yayanshi Adam wanda kamanninsu yake ɗaya kamar an tsaga kara amma shi bashi da kiɓan Muhammad, fari ne tass wanda ta ji an ce uwarsu da ta rasu suka ɗauko domin bafulatana ce ƴar Dukku. Daga shi sai Muhammad sai kuma Iyami autarsu, su kenan su uku a cikin mahaifiyarsu.

Ƴan dubiyan basu ƙara minti biyar ba suka musu sallama suka tafi guri ya rage su kaɗai, Muhammad da yake kwance ya dubi Salima ya ce,

“Ki koma gida nima in dawowa anjima.”

“Da ka bari mu tafi tare tunda anjima zasu sallameka in ruwan ya ƙare, bana son kuma ka nemi a taimaka maka da wani abu bana nan.”

 Haushi ne ya turnuƙe Juwairiyya wato ita ba mutum ba ce kuma ba zata iya taimaka mishi ba? Bata kulasu ba ta ɗauke kanta gefe domin dama tun shigowarta bata gaisheshi ba Salima kawai ta ɗagawa gaisuwa ta tambayeta ya mai jikin shikenan.

“Salima yaushe kika koyi musu da ni ne? Bana son wannan halin, kar ma ki koya.” Yayi magana yana ɗaure fuskarshi sosai.

“Kayi haƙuri bari mu tafi.” Da haka ta tattara abun da zata mayar gida ta sakasu a basket ɗaya sannan ta ɗauki HJ ta musu sallama.

Tun da ta tafi har likita ya sake shigowa ya duba jikinshi awa ɗaya da haka basu kula juna ba, sai dai in ta lura ya tashi zai sha ruwa sai ta ɗauko ta bashi shikenan.

“Idan ruwan ya ƙare zaka iya tafiya gida amma dai ka kiyaye sharuɗɗan da aka gindaya maka sannan ka rage cin maiko musamman da dare da drinks masu gas. Allah Ya sauwaƙe.”

Godiya ya yiwa likitan ya fice ya barsu su kaɗai aka sake wani zaman shirun har ruwan ya ƙare, tana gani ya sa hannu ya zare allurar wanda sai da tsikar jikinta ya tashi ta kawar da kanta gefe tana runtse idanunta. Da haka ya sauƙo daga kan gadon ya dubeta ya ce,

“Ki tattara komai ki koma gida ni zan yi cikin gari.” Yana faɗin hakan ya fice daga ɗakin ya barta baki buɗe.

Tsabar mamaki kasa mishi magana tayi har ya fice, sai a lokacin ta dubi uban kayan da zata kwashe basket ɗin abinci ne biyar har da wanda ta kawo ɗazu wanda ko buɗewa ba’a yi ba balle a ci abincin ciki. Lallai yau ta ƙara tabbatarwa Muhammad mugu ne na ƙin ƙarawa. Ta yaya zata fita da waɗannan abubuwa har bakin ƙofar asibiti? Ji tayi hawaye ya taru a idanunta domin yana mata abun da take gani yana yiwa Salima ce har take mata faɗan cewa ita ta kasa kwatowa kanta kima, ashe ba masifa da faɗa ne zai jawo ya daina haka ba, domin kuwa da hakan ne mafita da tuni ya daina mata halinshi da yake yi. Ashe masifar ba zai kwaceta ba, to me zai kwaceta?

Ganin tana ɓatawa kanta lokaci yasa ta saka baskets ɗin ɗaya kan ɗaya suka dawo biyu kana ta saka kulolin a ciki ta jidesu itama ta fita niƙi-niƙi da kaya a hannunta. Tunani ne ya ɗarsu a ranta kan cewa da Hafiz zai ganta a wannan lokacin ba zai bari ta ƙara taku ɗaya ba sai ƙarɓe duk abun hannunta sannan ya zaunar da ita ya ce ta huta. Wannan tunani yasa ta ji hawaye ya cika a idanunta tana tausayawa rayuwar da take yi babu Hafiz a cikinta. Inama tare suka tafi! Ina ma ita ce ta tafi ta barshi domin ta sani shi namiji ne ba zai sha wahalan da ta sha ba.

Karo tayi da mutum dalilin bata kallon gabanta wanda hakan ya sa duk baskets ɗin suka faɗi ƙasa itama tayi tagal tagal kamar zata faɗi amma ta tsaya. Cikin masifa ta ɗago idanunta da niyyar masife duk wanda ya mata wannan aika-aikan amma sai muryarta ta maƙale a maƙoshinta tana ganin mutumin da yake gabanta in all his glory, kamar kullum ya ci gayu sanye cikin kaya masu tsada da alfarma ya kafa hularshi sai zuba ƙamshi yake yi.

“Daddy.” Ta furta a hankali wasu hawayen na taruwa a idanunta domin har da laifinshi da ta samu kanta a wannan halin.

“Juwairiyya.” Shima ya kirata yayi taku biyu da sauri zai zo gurinta amma ko me ya tuna oho ya ja tunga ya tsaya sannan ya koma da baya wannan karon har taku huɗu.

Kuka ne ya kwace mata ta sunkuya a gurin tana yin mai tsuma zuciya amma bai tako ba illa haƙuri da yake bata yana kuma cewa ta tashi a gurin hankalin mutane na zuwa kanta. Kamar wanda aka yi ruwa aka ɗauke ta tsayar da kukan nata ta tattari baskets ɗin ta fincikesu ta fice Daddy na ƙwala mata kira amma bata amsa ba shi kuma bai bita ba. Tana fita ta samu napep ya kawo wasu mata ta shige ya mayar da ita gida.

Bayan ta koma gida ta kaiwa Salima duk abincin domin a ranar Muhammad zai koma ɗakinta, a nan ne take ce mata.

“Kar kiyi girkin dare dani domin ina da abincin rana da ban ci ba, in baki ji ni ba har dare to sai da safe.”

“Ai da kin tsaya kin ga dawowarshi ki ga yanayin jikin.”

“Da ban san wacece ke ba sai in ce neman maganata kike yi. Sai da safe Maman masoyi.”

Da haka ta juya zuciya a cunkushe ta koma ɗakinta ta rufe ruff tana fatan ina ma ta buɗe idanunta ta ga duk abun da ya faru mafarki take yi Hafiz ɗinta gashi nan a gefenta yana bacci in ta girgizashi zai tashi yana mata murmushi sannan ya jawota jikinshi yana cewa ‘Morning Riya.’ Kwanciya tayi a kan gadonta kana ta rufe idanunta da suke cike taff da hawaye suka zuba kan ƙuncinta da haka wasu suka biyo bayansu, wasu ma suka biyo.

“Hafiz mutuwarka tonon asiri ne a gareni.” Ta furta a hankali tana runtse idanunta.

Tun daga ranar Muhammad ya daina dawowa da rana cin abinci in dai ranar girkinta ne, haka da dare ma ba zai shigo ba sai an yi sallan isha, zai zauna a falo ya ci abinci ya yi hidimar gabanshi har sai ya fara jin bacci sannan zai shiga ɗaki, domin baya son ya shiga baya jin bacci buƙatarshi ta tashi ya nema kuma ta wulaƙantashi. Da safe kuwa yana gama shiri zai fita in ta gama abinci ya ɗauka in bata gama ba ya yi ficewarshi ya saya a waje.

Wata ɗaya da sati ɗaya da aurensu ta nemi izinin zuwa gida wanda ta so tun tana sati biyu ta je amma ta haƙura domin Maman ma tace tayi zamanta a gidanta kar ta zo.

“Ba yau ba.” Shine abun da Muhammad ya faɗa yana shirin fita office.

“Sai yaushe kenan?” Ta tambayeshi tana mai jin ɗaci a ranta.

“Sai ranar da na ga ya dace.”

“Amma kasan ba zaka hanani zuwa gurin mahaifiyata ba ko?”

“Ba zan iya hanaki ba amma ban baki izini ba.” Yana faɗin hakan ya fice ya barta a gurin zuciyarta na tuya domin sai ta ga kamar da gangan ya mata haka bata san cewa Maman ne da kanta ta kirashi ta ce mishi ya barta a gida sai tayi wata biyu ba.

Wani abu da Juwairiyya ta lura a gidan shine kamar Salima ta fara jan baya da ita musamman in Muhammad yana gurin, sannan sai ta ga walwalan gidan ya ragu musamman nama ko kifi da yake sayo musu da dare wanda in yau bai sayo ba gobe zai sayo. Sannan tun zuwanta da yace ta dinga ɗiban abinci a gurin Salima akan in aka yi salary zai sayo mata nata bai yi hakan ba domin kuwa har yau in zata yi girki a can store ɗin Salima zata ɗiba hatta kayan miya da naman miya a fridge ɗinta ake ajiyewa da yake tana da deep freezer babba. Wani wawanci da tayi wanda sai yanzu take jin haushinshi shine batun kuɗin cefenenta wanda shima a gurin Salima zata karɓo wanda ba kullum ma take yin amfani dashi ba, shiyasa watarana in tana da duk ingredients sai ba zata tambayi Salimar ba ita kuma ba zata bata ba wai sai ta tambaya.

Haka kuma ta lura in dai tayi baccin safe bata buɗe ƙofarta ba Salima bata ajiye mata abincin safe sai in tana so ta je ɗakinta ta tambaya a bata kamar almajira, hakan yasa ta daina zuwa kwata kwata in har ba’a ajiye matan ba sai ta ɗauki left overs ɗinta da ke cikin fridge ta ɗumama a microwave ta ci kayanta ko ta dafa indomie ko ta sha cereals.

Sannan duk wani abun buƙata da ya ƙunshi su sabulun wanka, wanki da su omo kayan tea duk a ƙarshen wata ake cefenensu har sai wani watan, idan kuma nata ya  ƙare kafin nan sai dai ta saya a kuɗinta ko kuma wai ta faɗawa Salima ita kuma ta faɗa mishi in ya ga dama ya saya in bai yi niyya ba Salima ta bata haƙuri ta ce mata ana matse ne babu kuɗi sai an yi salary. An yi hakan sau biyu da ta ga zai jawo mata ƙasƙanci sai ta daina tambaya ta cigaba da amfani da kuɗinta.

Ranar Juwairiyya ta gama girkin safe ta tsaya a kitchen kamar kullum domin kuwa ta bar Muhammad a ɗaki yana shiryawa, sai da ya gama ya fito ya ɗauki basket ɗinshi a bakin kitchen ya isa gurin motarshi, anan ta lura kamar Salima jiranshi take yi itama ta fito futt ta tsugunna har ƙasa ta gaisheshi ya amsa yana ɗaure fuska. Da haka ya shiga motarshi ya kunna ta ga sun tsaya suna magana amma bata ji dalilin ta window take hangensu can Salima ta buɗe mishi gate ya fita ta rufe ta tako zuwa gurinta, cikin sauri ta bar bakin window ta fara tattare tattare a haka Salima ta leƙo tana mata sannu da aiki Juwairiyya ta amsa fuska babu yabo babu fallasa domin ta fara gajiya da duk mutanen gidan.

“Yanzu nake tsokanan Baban Hafiz yake mini tsiya.” Ta faɗi hakan tana dariya.

“Wai me ya faru?” Juwairiyya ta tambaya not interested tana mai cigaba da aikinta.

“Wai nace yayi kyau kamar wanda zai je hira shine yake faɗa mini hirar ai zai je idan ya tashi daga office.”

Sai a lokacin Juwairiyya ta juyo ta kalli Salima wacce da alama abun bai dameta amma ita kam ji tayi kamar an saka almakashi ne an tsinke igiyar da take lilo da zuciyarta ta faɗi a cikin cikinta. Ƙirjinta ne ya fara ciwo nan take ta ce,

“Wai da gaske hira yake zuwa gurin ƴan mata?”

“Sai Allah, amma ina lura da take-takenshi kwana biyun nan.” Salima Ta rangaɗa ƙarya.

Juwairiyya juyawa tayi domin sai ta ji hawaye na taruwa a idanunta, wato saboda ita bata da amfani shine ko wata uku basu cika da aure ba ya ke neman ƴan mata a waje? Ita kuma Salima sokuwa har da murnanta kamar ba abun da ya dameta ba?

“Sai dai su ƙare a soyayya amma na sani ba aure zai ƙara ba dalili kuwa ki duba yanda al’mura suka fara ja da baya kwana biyun nan sannan ina zai ajiyeta?” Juwairiyya ta faɗi hakan bayan ta saisaita muryarta.

“Namiji kuma in yana son ƙara aure sai ya tara kuɗi ne? Ai aradu suke tara da ka, kuma sai ki ga da ikon Allah sun samu wadata an yi auren.”

“To ma yaushe aka yi auren namu da zai ƙara wani?” Ta ƙara jeho wata tambaya don bata son a bar zancen ba tare da ta samu tabbacin auren yake son ƙarawa ko a’a ba.

“Ni fa ban ce miki zai ƙara aure ba kawai tsokanan juna muke yi amma dai na faɗa miki zai iya yiwuwa da gaske ne. Bari in barki ki ƙarisa aikinki, miƙo mini abincin namu in tafi dashi.”

Wannan magana da ya shiga tsakanin Juwairiyya da Salima ya sa Juwairiyya ta fara bin diddigin Muhammad musamman da yayi tafiya zuwa Abuja yayi kwana huɗu a can ya dawo. A nan ta fara tunanin ƴar Abujan yake neman aure kuma zuwan da yayi hira ya je, jan baya da kayan buƙatunsu na gida kuma tara kuɗin auren yake yi. Hakan yasa bayan ya dawo in yana danne-dannenshi a waya ko kuma yana call sai ta dinga sintiri daga ɗaki zuwa falo ko zata ji wani abu makamancin soyayya da budurwa, sai dai da ta lura Muhammad ya fara binta da kallo yasa ta haƙura bayan ta ja mishi Allah Ya isa muddin aure yake son ƙarawa.

Wani abu da Juwairiyya bata sani ba shine tafiyar Muhammad ne ya ƙarato zuwa UK ƙarin karatu na PhD da zai ɗaukeshi shekaru uku cuss. Yayi niyyar tafiyar ne nan da wata ɗaya domin zuwanshi Abuja ma ya je ne akan process ɗin Visa ɗinshi.

Bayan ya dawo ne ya barta ta je gidansu tare da dubo ƙanwarta Surayya wacce haihuwarta yau ko gobe. Da ta shiga gidansu sai ta ga kamar ta shekara bata shigo ciki ba, ganin Mama kuma yasa ta ji sanyi a ranta ta je ta rungumeta tana jin hawaye na sauƙa kan ƙuncinta.

Nan hira ya ɓarke tsakanin uwa da ƴar duk dama suna waya kusan kullum, a nan ne take bata labarin zaman gidan nasu wanda ya kasance akwai haɗin kai tsakaninta da Salima. Tana bata labarin zaman nasu Mama tayi kasaƙe tana sauraronta har ta gaji ta dasa aya.

“Kiyi hankali da yarinyar nan don a yanayin maganarki na ga kamar kin yarda da ita fiye da wanda ya ajiyeki a gidan.”

“Haba Mama kema fa kin san halinta tun ba yau ba, ai Salima mutum ce.”

“To Allah Ya tsare amma kishiya kishiya ce, ba kuma ina miki huɗuban ki je kuyi ta faɗa bane amma dai ki san takunki in ba haka ba sai ta gama shiga jikinki sai ta naɗa miki tarkon da ba zaki iya kwace kanki ba. Ki kiyaye.”

A gurin da Mama tayi maganar a gurin Juwairiyya ta watsar dashi domin ta sani Mama bata san halin Salima ba don ba zata taɓa mata mugunta ba, da kuma zata iya yi da a zaman da suka yi na wata biyu da ɗori ta mata sau ɗaya ta gani. (Rashin sani, ya fi dare duhu).

Mum Fateey 👌

Duk shirye shiryen tafiyan Muhammad da ake yi Juwairiyya bata da labari, tun kwanaki dai ta lura walwalarsu ta ragu sannan shiga da ficen Muhammad a gida ya yawaita sannan ya daina fita office da safe. Ba dai koranshi aka yi ba? Ko dai da gaske auren zai yi amma aka bashi hutu tun yanzu? Tana son tambayar Salima ko shi Muhammad ɗin amma ta gagara, haka kuma ko a cikin hiransu da Salima in ta sako zancen Salima bata cewa komai sai dai ta shashantar da zancen ta ɗauko musu wani. Me yake faruwa ne a gidan?

In ba zata yi ƙarya ba abun ya fara damunta domin kamar wareta aka yi suna sha’aninsu su kaɗai. Wani abun ɓacin rai kuma Muhammad ya fita a harkarta kwata kwata kamar ba’a yi tsironta ba, kwanaki don kawai tana son ya mata magana ta kwaɓa mishi abinci amma yana buɗewa ya gani ya rufe bai ce kanzil ba ya tafi ɗakin Salima. Zuciyarta na bugun tsoro game da ɓacin rai domin ba haka ta so ba, ta so ne yayi magana itama ta faɗi abun da yake ranta ko zata samu sassauci.

Washe garin hakan ne kuwa Surayya ta haihu, tsabar tsoron kar Muhammad ya hanata fita ya rama abun da ta mishi jiya sai ta kasa faɗa mishi balle ta je dubo mai jegon. A kwana na biyu ne da Surayya ta dameta da waya ta samu courage ɗin samunshi a tsakar gida zai fita ta faɗa mishi.

“Allah Ya raya Ya yi albarka. Ki je.” Yana faɗin hakan ya kwalawa Salima kira ta fito ita kuma Juwairiyya ta koma cikin ɗakinta amma bata gama shiga ba ta ji yana cewa “Ƙanwarta ta haihu, ki ɗauki dubu uku ki bata na abun hawa in kuma sunan ya zo ki tuna mini.”

Wai maganarta ake yi ne ko dai ta wata? To in maganarta ce me yasa ba za’a kira sunanta ba? Tukunna ma wa yace mishi buƙatar kuɗi ne yasa ta faɗa mishi batun haihuwar da har zai tsaya yana kiran matarshi wai ta bata? Zama tayi a ɗakinta tana jiran Salima ta kawo mata kuɗin amma har awa ɗaya da haka bata zo ba haka kuma bata aiko mata kuɗin ba. Ranta na suya tayi saurin zaran jaka da kuma hijabinta ta fita daga gidan ko sallama bata yiwa Saliman ba, tana son ta nuna musu ba kuɗin ne damuwarta ba. (oh oh).

A can gidan mai jego Muhammad ya kirata yana tambayarta ina take tace tana gidan Surayya.

“Me yasa ba ki yiwa Salima sallama ba? Gashi can ta ɗaga hankalinta wai bata ganki ba, ki kirata ki faɗa mata kin tafi ne.”

Bata ce komai ba ta kashe wayarta zuciyarta na azalzalarta, tunda ya ji ina take me yasa shi ba zai kirata ya faɗa mata ba.

“Aikin banza aikin wofi, ba zan kira ba.” Ta furta tana jefa wayarta jaka.

“Me ya faru?” Mama mai zama tare da mai jego ta tambayeta fuskarta ɗauke da damuwa.

“Na tambayi izinin fita ne shine ya cewa matarshi ta bani kuɗin abun hawa, har awa ɗaya ta wuce bata kawo mini ba shine nayi fitowata kuma wai shine ta kirashi wai hankalinta ya tashi bata ganni ba shine ya ce in kirata in faɗa mata na fita ne.” Tayi maganr cikin numfashi ɗaya.

“To ke me yasa baki je kin karɓa ba tunda a gabanki aka ce ta baki? Ko kuma dai tana shiryawa ne zaku fita tare kika yi gajen haƙuri kika barta?”

“Ba’a gabana bane, jin su nayi. Kuma ita Saliman bata ma san da haihuwar ba sai ɗazun don ban faɗa mata ba.”

“Kun samu matsala ne kika ƙi faɗa mata?” Mama ta ƙara watso mata wata tambayar.

“A’a, kawai ban faɗa mishi bane shiyasa itama ban faɗa mata ba.”

“Juwairiyya wani irin zama kike yi da bayin Allahn nan? A yi haihuwa tun shekaran jiya da dare amma baki sanar da abokiyar zamanki da mijin naku ba sai yau? Na ce bakwa zaman lafiya ne?”

“Muna yi, Mama ba zaki gane bane.” Tayi kicin kicin da fuska don bata son a zurma da yawa Mama ta gane zaman da take yi da Muhammad wanda ta sani har marinta zata iya yi in ta ji.

“Eh ba zan gane ba. Maza kirata ki faɗa mata, yanzu haka wataƙila ita fushi tayi da baki faɗa mata ba alhali kuna zaune a gida ɗaya and you claimed that kuna zaman lafiya. Ki kirata ki ce kina gaggawa ne yasa baki mata sallama ba. Kuma wallahi in kika mini musu sai ranki ya ɓaci.”

Wata mata danginsu da take gefe mai suna Aunty Sahla ta tsoma baki,

“Ai Juwairiyya ba haka ake zama da kishiya ba, duk wani abun farin ciki ko akasinshi da ya sameki zaki faɗa mata saboda a yanzu ko mu ƴan’uwanki bamu kaita kusa da ke ba, sannan ko ba’a zaman lafiya in zaki fita zaki mata sallama ta san bakya gidan haka kuma in kin koma ki ce mata kin dawo.”

“Zamanta ma nake yi.” Faɗin Juwairiyya ciki-ciki amma Mama ta ji ta, ai kuwa ta ɗaka mata duka a cinya wanda yasa ta miƙewa ba shiri ta koma can gefe tana ɓata fuska tana kuma sosa gurin.

“Mama dai dukana kika yi da girmana.”

“Ina girman? Ai ni ban ga girman ba. Da wayonki da hankalinki kina rayuwa cikin mutane amma kamar masu cin naman juna? A miki abun murna ki tsallaketa ki fito baki faɗa mata ba haka kuma baki mata sallama ba? Wannan wani irin banzan ɗabi’a ne? Kuma wallahi wannan ba tarbiyyar da na baki ba kenan.”

Nan sauran ƴan’uwansu biyu da suke ɗakin suma suka saka baki aka yi ta yiwa Juwairiyya faɗa wacce ta cika tayi famm amma tana shiru da bakinta.

“Ya ma za’a yi da wayonki har mijinku ya gane ke ce bakya son zaman lafiya da matarshi? Gashi ita ta miki wayo ta kirashi wai tana cewa hankalinta ya tashi, ai tana da numbernki me yasa ba zata kiraki ba? Saboda ta fiki wayo ta fiki iya bariki, ke kuma da yake sokuwa ce uwar zuciya wai kin fice  babu sallama. Maza kirata yanzu.” Mama ta gama maganar cikin hasala.

 Juwairiyya rai babu daɗi ta ɗauko wayarta ta kira numbern Salima wacce ringing biyu ta ɗauka ta fara magana bayan ta saka a loudspeaker.

“Kai masha Allah, wallahi kin bani tsoro. Yanzu Baban Hafiz ya kirani yake cewa ashe fita kika yi amma zaki kirani shine nace bari in jira kar nima in nemeki ya zama number busy. Ashe Surayya ce ta haihu? Kai Masha Allah na taya murna, me aka samu?”

“Ɗa namiji.”

“To Allah Ya raya ya kuma ɗayyiba, tana kusa ne ki bata in mata barka? Ai ɗazun na aika a ciro kuɗi a POS ne shiyasa da ya faɗa mini ban shigo na miki murnar ba ina jira sai an kawo kuɗin, bayan Nanayo ta dawo kuma na je ƙofar ɗakinki na buga shiru ashe ke har kin fito.”

“Wallahi kuwa, ina sauri ne. Gata nan.” Juwairiyya da take jin kamar ta shaƙe Salima ta miƙawa Surayya wayar ta karɓa.

Sun kai minti biyu Salima na mata addu’a game da bata wasu shawarwari na sabon haihuwa sannan suka yi sallama ta mayarwa Juwairiyya wayar.

“Hello.”

“To tunda kin fita zan aika miki kuɗin ta Bank account ɗinki. Ranar suna kuma zamu zo tare tunda ban samu zuwa barkatun ba.”

“To Allah Ya kaimu.”

Tana ajiye wayar ta ga idanun ƴan ɗakin a kanta suna mata kallon mamaki da kuma wani abu kamar tausayi.

“Lafiya kam?” Ta tambaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

“Lallai kishiyarki mai wayo ce, ke kuma wayonki kaɗan ne. Tirƙashi!” Faɗin Aunty Sahla tana taɓe baki.

“Ita tana miki murnar haihuwar ƙanwarki murya duk farin ciki amma ke kina yi a daddare kamar bakya son amsawa. Idan wani yana kusa da ita ya ji haka sai ya ƙara gaba yace ke ce bakya son zaman lafiya da ita kina mata magana a gadarance.” Itama ɗayar ƴar’uwar tasu ta tofa tata.

“Ni fa laifi aka mini na kuma nuna musu don ni bana iya ɓoye ɓacin raina.” Juwairiyya ta faɗa cikin jin kai.

“To kuwa kina cikin wahala! Allah kuma Ya yaye miki wannan ɗabi’an domin in baki da haƙuri da kuma bin rayuwa a sannu zaki ga abun da ba zai miki daɗi ba. Ba baki nake miki ba gaskiya nake faɗa miki don ki gyara halinki.” Faɗin Mama tana tashi tsaye ta fita daga ɗakin.

Nan ƴan’uwa suka sake yi mata caaaa ita Juwairiyya ta ma kasa gane ina suka dosa, sun ce Salima tana kissa kuma sun ce tana mata kirki sai kuma suka ce tayi hankali da ita sannan suka ƙara cewa wai ta dinga sake mata fuska ta kuma daina saurin fushi idan an mata ba daidai ba. Ita ba zata iya da wannan ciwon kan ba, in za’a yi zaman lafiya a yi, in kuma ba za’a yi ba shikenan. Barikin da suke cewa ta koya ita ba zata iya ba domin ganinshi take yi a matsayin munafurci domin abun da kake yi a bayyane daban a zuciyarka kuma ba haka ba, ita bata son haka. Tana jin su suka gama surutansu duk akan auren da zata kashe nan da wasu shekaru amma ba lallai su san da hakan ba.

Sai yamma liss ta koma gida ta leƙa falon Salima ta faɗa mata ta dawo tayi shigewarta ɗaki, bata jima da shiga ba Nanayo ta kawo mata abincin darenta ta karɓa ta kulle ƙofarta bata sake buɗewa ba sai washe gari da safe kuma a ranar zata karɓi girki.

Yau ma bayan ta gama girki ta shiga wanka sannan ta zo tayi sallan maghrib, babu ko man shafawa a fuskarta ta zura doguwar riga mai taushi wacce zata kwana da ita, daga nan ta samu guri a falo ta saka abinci tana ci tana kallo don ta san Muhammad ba zai dawo ba sai ƙarfe takwas ko tara ɗabi’ar da ya koya muddin ranar girkinta ne, don in ranar girkin Salima ce da yamma yake dawowa kuma yana nan sai sallah ne kaɗai zai fitar dashi.

Har ta gama duk abun da zata yi ta kwanta bai dawo ba domin tana son faɗa mishi batun komawarta makaranta don har an fara registration zasu shiga aji biyu. Bai shigo ba sai ƙarfe goma na dare wanda tana sauraronshi ko abincinta bai buɗe ba ya shigo cikin ɗaki yayi wanka ya zo ya kwanta da alama a gajiye yake.

“Ina so zan fara registration ranar Monday an koma school.”

“Ok, amma gaskiya yanzu bani da kuɗi sai dai ƙarshen wata in an yi salary in baki. Nawa ne kuɗin registration ɗin?”

“Ni ba kuɗin nace ka bani ba kawai na faɗa maka ne don ka sani zan fita. Ko an yi salary ma ka riƙe kayanka ka ƙara kan wanda kake tarawa na ƙarin auren da zaka yi.” Yau dai tayi maganar da yake nuƙurƙsarta kullum.

“Aure? Wa zai yi aure?” Ya tambaya da mamakinshi.

“Wani mai suna Muhammadu, kai ma baka da labari ko?” Tayi maganar cikin izgili.

“Duk wanda ya faɗa miki aure zan yi ƙarya yake yi, batun karatun da bakya son sauraro ne yasa nake tara kuɗin don biyan wasu expenses ɗin da scholarship ba zai mini ba.”

Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Juwairiyya wanda hakan ya bata mamaki domin bata san cewa maganar ƙarin aurenshi wani nauyi ne da take ta yawo dashi ba wanda sai yau Allah Ya yi ta sauƙe. Da murmushi a fuskarta wanda Muhammad ba zai gani ba dalilin bashi baya da tayi tace,

“A ina zaka je karatun?” Yau kam ta nuna mishi she is interested da batun karatun nashi.

“UK.”

Wani wawan zabura tayi ta tashi ta zauna ta dafe ƙirjinta da yake dukan uku uku tace,

“Wani UK? Kuma da gaske kake yi ko wasa?” Tayi tambayoyin da su suka fara zuwa brain ɗinta kafin sauran dubbannin su biyo baya.

“United Kingdom. Kuma ba wasa nake yi ba don tafiyar ma saura kwana goma.”

“Shine sai yau zaka faɗa mini kuma nan ma sai da na tambaya?” Wannan karon tashi tayi daga kan gadon ta kunna musu wuta don tana son ganin fuskarshi a yayin da yake faɗa mata wannan maganar mai kama da almara.

Bai yi magana ba illa tare fuskarshi da yayi da tafukan hannayenshi kana ya juya gefe ya bata baya. Baya son hayaniyarta da tsakar daren nan kuma bacci yake ji.

“Magana nake maka kayi shiru ka kyaleni. To mu ina zamu je? Ya zamu yi rayuwa?” Tayi maganar tana jin zuciyarta na zafi sosai, to ina zata saka ranta in ya tafi ya barta?

“A nan zaku zauna ke da Salima, duk abun da kuke buƙata ba zan fasa sauƙe muku shi ba sai dai wanda ya fi ƙarfina. Rayuwa kuma yanda kuka saba zaku yi sai dai wannan karon ku ƙadai babu ni.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Haka Juwairiyya ta dinga nanatawa tana kallon ƙeyar Muhammad.

“To sai yaushe zaka dawo?” Ta ƙara mishi wata tambayar tana riƙe gashin kanta.

“Sai bayan shekara ɗaya don bani da kuɗin da zan dinga zuwa duk lokacin da nake so.”

“Shekara nawa ne karatun?” Ta ƙara wata tambayar muryarta na rawa kamar tana riƙe kuka.

“Shekara uku.”

Ai yana rufe baki Juwairiyya ta fara kuka mai sauti lokaci ɗaya kuma ta dawo bakin gadon ta zauna tana kallon Muhammad.

“Yanzu fisabilillahi ina matsayin matarka a gidan nan zaka tafi karatu har UK amma bani da labari sai ana saura kwana goma tafiyarka? To ma uban me yasa ba zaka yi karatun a Nigeria ba sai ka fita waje?”

“Sau biyu ina miki maganan kika nuna bakya son sauraro.”

“Wannan ai zalunci ne, ya za’a yi ka tafi can uwa duniya ka barmu mu kaɗai har na shekara uku?”

“Na ɗauka zaki fi kowa murna da wannan tafiyar saboda presence ɗina na damunki, zan miki nisan da zaki yi rayuwarki babu ni babu damuwata. Why are you crying?”

Itama bata san amsar wannan tambayar ba, kwanciya tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana cigaba da jin zafi a ƙirjinta tana kukan, to ta yaya zasu rayu babu shi?

Muhammad tashi yayi tsaye ya kashe wutan da ta kunna kana ya koma ya bata baya yana jin sautin kukanta har bacci ya ɗaukeshi don ya sani tana kuka ne don wanda zata dinga wulaƙantawa tana jin daɗi zai tafi ya barta shi yasa bai nemi ya rarrasheta ko lallai ya ji ba’asi ba, baya son fitina.

Juwairiyya ta jima tana kuka wanda ita kanta bata san dalilin yinshi ba amma abu biyu ta sani shine kawai Muhammad ya bar karatunshi ya dawo su zauna, bata son wannan tafiyar! Na biyu kuma wani irin ƙiyayya yake mata da har zai ɓoye mata tafiyarshi sai da ya saura kwana goma? Dama yaushe yake da niyyar faɗa mata? Sai ranar tafiyar zai zo yace mata ya tafi UK sai bayan shekara ɗaya zai dawo?

Wannan abun da ya faru shine mafarin shigar Juwairiyya damuwa da kuma dana sani mara amfani.

Mum Fateey 👌

Duk yanda Juwairiyya ta so ta ɓoye baƙin cikinta da damuwarta na tafiyan Muhammad ta kasa domin ko da asuba da ya tasheta ƙin kulashi tayi, ya kira sunanta ya fi sau uku wanda sai da ya ji tsoro kaɗan ya zo ya jijjigata ya samu idonta biyu kawai shi ɗin ne ba zata yiwa magana ba. Yana fita itama ta miƙe wasu hawayen na sauƙa a idanunta ta wuce banɗaki. Breakfast ɗin ranar har da hawayenta a ciki, bayan ta gama ta ajiye mishi nashi a falonta amma ita bata ɗibi nata ba don bata jin zata iya cin abinci dalilin  kanta da yake mata ciwo kamar zai tsage ko yayi bindiga. Tun bai gama shirin fita ba ta koma ɗaki ta kwanta akan gado ta duƙunƙune guri ɗaya sannan ta ɗauki bargo ta rufe dukkan jikinta har da kanta. Tana jin shi ya gama shiryawa ya fita wanda tana jin ƙarar rufe ƙofar falonta ta ji wasu hawayen sun gangaro gefen fuskarta, nan take kuwa ta ji zazzaɓi ya fara shiga jikinta.

Tana kwance har tayi bacci ta farka ta duba time ɗin ɗaura abincin rana yayi amma sai ta ji ba zata yi ba. Har aka yi azahar ta tashi ta je tayi sallah ta ƙara komawa ta kwanta, sai can ƙarfe uku saura wasu mintuna Muhammad ya dawo ya shigo ɗakinta.

“Juwairiyya yau baki yi lunch bane?” Faɗin Muhammad yana tsayawa a kanta.

“Eh.”

“Me yasa?”

“Na gaji da zuwa karɓan kuɗin cefene da kayan abinci ana gutsira mini.”

“Idan na tuna da kyau ke kika ce haka kike so.”

“Yanzu kuma nace bana so.”

“Dalilin da yasa kika ƙi yin girki kenan?”

“Eh.”

“Juwairiyya ki tashi ina son yi magana da ke.” Ya faɗi hakan yana gyara tsayuwarshi.

Bata kulashi ba haka kuma bata tashi ba don haushinshi take ji sosai kamar ta tashi ta far mishi da duka, shi bai san laifi ya mata bane? Yana ji jiya tana kuka amma ko a jikinshi ya kwanta yayi bacci irin in mutuwa ma zata yi ta mutu ko? Yau da safe ma ya tashi ko ya tambayi ya ta kwana balle ya nemi kwantar mata da hankali kan tafiyar da zai yi da aka faɗa mata a ƙurarren lokaci. Tunda duk ƴan gidan basu damu da ita ba bata ga abun da zai sa ta tashi ta musu girki ba, ita ba baiwarsu ba ce.

“Na ɗauka idan kin ji zan tafi zaki ɗan rage wani abun amma sai kika ƙara ɓullo da wani sabon salo don ɓata mini rai. Tukunna bari in tambayeki, shin laifin me na miki kwaya ɗaya da na cancanci duk wannan rashin mutuncin da wulaƙancin?”

Shuru tayi kamar yanda yayi tsammani, ya zauna yayi tunani sosai kan yanda zai shawo kanta su yi zaman lafiya amma abun ya gagara. Ya sauƙe kanshi a gabanta kamar wawa wanda a da in aka faɗa mishi zai yi hakan ga ɗiya mace to zai musa har ya haɗa da rantsuwa, to sai gashi yayi kuma ya kasa controlling ɗinta ya kuma kasa gyara tsakaninsu, shi kam Hafiz ya haɗashi da wahala.

Ta wani guri kuma yana ganin Allah ne Ya kamashi akan irin yanda yake treating ɗin Salima wanda a yanzu ya rage yawan mata tsawa musamman a cikin mutane da kuma saurin hasala idan ta mishi laifi, yau gashi ya auro wacce take kelaya mishi rashin ɗa’a amma ya zuba mata ido ya kuma kasa taɓuka komai. Lallai an yi gaskiya da aka ce Mace kiwon Allah ce, ko taurin zaluncinka ya kai na Fir’auna in ka haɗu da wata sai ka sarara mata ka kuma ka kwanta ta taka ka. Yau gashi yana gani a gidanshi ba labari ake bashi ba balle ya ƙaryata.

“Shikenan.” Shine kawai abun da ya faɗa ya fice daga ɗakin.

To me zai yi? Faɗa? Yayi faɗan har ya gaji amma bata canja ba. Zagi? Shi ba ya zagin mace don ko Salima bai taɓa zaginta ba kuma ba zai fara akan Juwairiyya ba. Duka? Ba ya fatan har abada ya sa hannu ya daki macen da aka damƙa amanarta a hannunshi! Me zai yi? Shine ya cigaba da fita harkarta har lokacin tafiyarshi ya zo, kafin shekara ta cika kuwa zai ga yanda Allah zai yi da su.

Juwairiyya tashi tayi zaune tana kallon ƙofar da ya fita domin bata tsammaci haka ba, yanzu ta lura ko faɗan ya daina yi sai dai ya ce ‘shikenan’ ya ƙara gaba. Me hakan yake nufi? Ya fara gajiya da ita ne ko dai ya mayar da ita mahaukaciya ce? Wato ta gama neman maganarta da haukarta ba zai kulata ba? Jiki babu kwari ta tashi tsaye ta nufi banɗaki don yau tun safe bata saka komai a bakinta ba haka kuma bata yi wanka ba. Ga can wanke-wanke da gyaran kitchen na jiranta wanda idan ma ta tuna sai ta ji ba zata iya ba, tana fitowa daga wanka ta shirya ta fita a lokacin ana kiran sallan La’asar ta nufi ɗakin Salima don bata haƙurin girkin da bata yi ba duk da cewa itama da laifinta, tun da kullum tana zuwa karɓa me yasa da yau bata je ba sai ita kuma ta ƙi zuwa dubata? Ai zaman amana bai ce haka ba.

Shiga falon tayi da sallamarta ta samu Muhammad zaune a kan dinning table yana cin abinci Salima na gefenshi ta ɗaura hannunta saman cinyarshi suna dariya. Sallamar da bata ida ba kenan sauran kalmomin suka tsaya a maƙoshinta ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallonsu.

“Amarya ke ce? Sannu da tashi, ki iso mana. Yanzu fa nake da niyyar zuwa dubaki, yau ban ji daɗi bane tun safe jikina zazzaɓi ina kwance. Da fatan kina lafiya?”

“Lafiya kalau, na ga kamar kuna hidima bari in baku guri sai anjima.” Tana faɗin hakan ta juya ta wuce ɗakinta cikin sauri bata iya ganin gabanta dalilin hawayen da ya cika mata ido.

A can cikin ɗakinta tayi masauƙi zuciyarta na suya ta zauna a bakin gado tana mayar da hawayen amma sai ta kasa, ƙarshe dole ta bari suka sauƙo kan kuncinta tayi saurin gogesu kana ta saisaita kanta ta fita falo ta buɗe fridge ta ɗauko sauran left over food da take ajiyewa ta tafi kitchen ta saka a Microwave tana jira ya ɗumama.

A haka Salima ta zo ta sameta ta tsaya a bakin kitchen ɗin fuskarta a marairaice ta ce,

“Na ga kin tafi kamar ranki ya ɓaci, wani abu na miki ko shi maigidan?”

Juwairiyya tana son tace zuwan Muhammad ɗakinta ne bata so alhali ranar kwananta ne amma sai ta kasa furta hakan saboda dalilai biyu. Na farko ita ta jawo hakan ya faru domin da tayi girki Muhammad ba zai taɓa zuwa ɗakin Salima ya zauna suna hira ba, duk rashin jituwar da yake tsakaninsu sai dai ya ƙi dawowa gida da wuri amma ba wai ya tafi ɗakin Salima ya zauna ba. Na biyu ita ta bawa Salima daman kula da mijinta ko da kuwa ranar girkinta ne, hakan na nufin bata isa ta nuna mata hakan ya ɓata mata rai ko ta hana ba. Da wannan tunanin ta buɗe bakinta ta ce,

“A’a, kawai na ga kuna hiranku ne kar in tsayar da ku shiyasa.”

“Kin tabbatar ba ranki ne ya ɓaci ba? Na san kin sani tun ba yau ba yana zuwa cin abinci wanda na so hanashi nace ba zaki ji daɗi ba, hakan kuma zai zama kamar cin amana amma ya mini tsawa ya ce gidanshi ne yana da right ɗin cin abinci a duk inda ya ke so. To kin ga tunda ya faɗi haka ban isa in ce wani abu ba, amma kuma zan so hakan ya daina faruwa don ina jindaɗin kwana biyu ya tafi zan huta sai kuma in ganshi ya dawo bini bini wai yana neman abinci.”

Wannan maganan na ƙarshe ba ƙaramin ɓatawa Juwairiyya rai yayi ba, wato ita ce bata cika mace ba shine har mijinta na bin wata bini bini ita kuma tana son hutawa don ya dameta.

“Ai da sai ki hanashi ki ce babu abincin.”

“Ai kuwa in nayi haka da ni da ke duniya zata zaga a ce matanshi biyu amma ya je waje yana sayan abinci, ko kuma in gidan ƴan’uwa yake zuwa ki ga ana zagawa dangi da mu ana zagi. Gwanda hakan dai asirinki a rufe babu mai sanin babu jituwa tsakaninku, wai me ya faru ne ma wannan karon?”

“Babu komai fa, nima bacci nayi ban tashi da wuri ba. Ki buɗe mini store zan zo in ɗibi abinci anjima.” Faɗin Juwairiyya tana bawa Salima baya don sai ta ji bata son ganinta kwata kwata.

“To shikenan sai kin shigo, ga can masoyinki yana mini bore wai sai in mishi Cookies nace wannan sai expert irin masoyiyarshi.” Ta ƙarisa maganan tana dariya wanda bai kai zuci ba.

“Ayya zan mishi.” Ta bata amsa ba tare da ta juyo ba domin so kawai take yi ta tafi ta bata guri.

Salima tana tafiya Juwairiyya taci gaba da jiran abincinta ya ɗumamu tana saƙe-saƙe a ranta, wanda a yanzu itama Saliman ta fara bata haushi amma ta rasa ya zata yi ta nuna mata yanda ba zata ce kishi take yi da ita ba. Ƙarar Timer ne ya katse mata tunanin ta ciro abincinta tare da ɗaukan Spoon ta fita zuwa falo.

Tana zama ta jawo wayarta da ta maƙala a charge ta buɗe kana ta hau WhatsApp, message ɗin contact na farko ta fara shiga kawai wayarta ta fara ringing wanda tana ganin foreign number ne ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske, Hadiza ce!

Har wayar ta tsinke bata ɗauka ba ta ƙurawa numbern ido kamar mai son haddace su. Me yasa Hadiza take kiranta? In bata manta ba rabonta da ita tun lokacin da Daddy ya mata sakin wulaƙanci ta dawo gida ita kuma Hadizan tayi ta damunta da kira akan me ya haɗata da Daddy suka rabu, ta ƙi faɗa mata ƙarshe ta daina ɗaukar wayarta itama tayi zuciya ta daina gwada kiran nata. Ta san wataƙila tana da labarin tayi aure ko gurin friends ɗinsu zata samu labari. To me yasa take kiranta? Ko dai wani abu ne ya faru da Daddy?

Wayar ce ta ƙara ringing a karo na biyu Juwairiyya ta ɗauka ta ƙara a kunnenta ta ce,

“Hello.”

“Ai nayi zaton ba zaki ɗauka ba don sai da na ganki online a whatsapp na kiraki.” Faɗin Hadiza a ɗayan gefen bayan tayi ajiyar zuciya.

“Hadiza ke ce?”

“Ni ce dai. Kina lafiya?”

Nan suka gaisa tare da tambayan juna bayan rabuwa wanda anan Hadiza take faɗa mata kan cewa ta haihu har Baby Girl ɗin ta yi wata biyu, Juwairiyya tayi mata barka tare da sawa ɗiyar albarka kana Itama ta faɗa mata haihuwar Surayya wanda saura kwanaki kaɗan suna.

“Allah Ya raya mana bisa tafarkin Islama. Yanzu kam saura ke In sha Allah.”

Dariya Juwairiyya tayi a fili, a zuciyarta kuma har ta fara cire rai da haihuwa domin kuwa tayi tunanin haɗuwarta da Muhammad a farkon aurensu zai sa ta ɗauki ciki, wanda in ma hakan ya faru tana so domin ita bata damu don bata son Muhammad kuma ta ƙi son haihuwa da shi ba.

“Shiru har yanzu, muna jiran lokacin da Allah Ya ga dacewan bamu.”

“To Allah Ya kawo mai albarka.”

“Ameen.”

“Baki tambayeni Daddy ba.”

“Hadiza kenan, me yasa kika kirani? Don na san ba haka kawai kika yi kiran ba domin last thing i know shine kin yi fushi wanda har haihuwa kika yi amma ba ki faɗa mini ba, sannan ko a cikin friends ɗin mu babu wacce ta faɗa mini which I know ke ce kika hanasu.”

“Kin yi gaskiya Aunty Juwai. Na yi fushi ne akan rabuwanki da Daddy wanda sai jiya na gane ba laifinki bane hasalima ni ce da laifi da na sa ku ka yi auren cikin gaggawa ba tare da bincike ba. Jiya Daddy ya faɗa mini komai.”

Lomar farko na abincin Juwairiyya ta kai bakinta amma bata saka ba ta ajiye cokalin jikinta na rawa kaɗan tsabar kaɗuwa.

“Me ya faɗa miki?” Ta tambaya tana riƙe ƙirjinta domin har yau da suke waya bata taɓa faɗawa ko wanne mahaluƙi dalilin rabuwarsu ba, hatta Mama har yau bata da masaniya.

“Akan rashin gamsar da ke da ba zai iya ba, kun yi neman magani amma ya ga yana cutar da ke ya rabu da ke ba tare da kun zauna kun yi shawara ba. Kiyi haƙuri ki yafe mini ni da Daddy, dukkaninmu mun yi kuskure kuma mun taɓa miki rayuwa negatively and we are deeply sorry.”

Hawaye ne ya sauƙo a kumatun Juwairiyya tana jin nauyi sosai a zuciyarta domin wannan magana ya ɗaye mata ciwon da ta daɗe tana jinyarshi, tun jiya idanunta basu huta da zubar kwalla ba haka kuwa zuciyarta bata samu hutu daga ciwon da take mata ba. Bata ce komai ba Hadiza taci gaba da magana.

“Tun kwanaki Daddy ya kirani yace kun haɗu a asibiti kina kuka kamar kina cikin damuwa, he asked me to call you in tambayeki me ya faru kike kuka amma na ƙi. Wallahi tun wancan karon yake bina na kafe kan cewa tunda kin kashe aurenki da shi kuma kin ƙi faɗa mini dalili ba zan sake shiga harkarki ba, sai jiya da ya ga da gaske nake ya faɗa mini gaskiyar al’amarin. Wallahi ban san haka zai faru ba da ban haɗaku auren nan ba, bani da masaniyar Daddy yana da matsala Juwairiyya kiyi haƙuri ki yafe mana dukkanmu.”

Ta kai minti ɗaya tana share hawayen fuskar tata tana jan majina sannan ta samu ta iya magana.

“It hurts! Hadiza har yau ina jin zafin sakina da yayi da kuma method ɗin da yayi amfani ya sakenin. Ya faɗa miki yanda ya yi?”

“No.”

“Tafiya zai yi Hadiza, a lokacin kin san ina school sai ya ce ba zai tafi da ni ba kar ya katse mini karatu. Ranar tafiyarshi muna wasa muna dariya ya fita zuwa gurin mota ya dawo ya rungumeni wanda sai yanzu na gane ya mini na ƙarshe ne sannan ya ƙara fita ya barni. Sai da na je ɗakinshi gyara na samu takardar sakin Hadiza, wallahi har yau na tuna wannan abu sai na yi hawaye amma na ɗauki hakan a matsayin ƙaddarata.”

Nan Hadiza tayi ta bata haƙuri tace mata ta haƙura sannan ta ƙara tambayarta dalilin kiran wanda Daddy ne ke son jin me ya faru take kuka a cikin asibiti.

“Rayuwa ce kawai, yau ta zo maka da daɗi gobe kuma akasinshi. To ranar ya sameni ina cikin ɗayan ne amma Alhamdulillah komai ya wuce, it was just a phase.”

“Are you sure babu wani abu?” Hadiza ta ƙara tambaya don tabbatar da zancen.

Juwairiyya ta share hawayen fuskarta ta ce,

“Babu komai. Daddy yayi aure ne?”

Dariya Hadiza tayi sannan tace,

“Ai tun bayan rabuwarku duk wanda ma ya mishi maganar aure sai sun yi faɗa. Wallahi sai yanzu na gane har da sonki yake ɗawainiya da shi, you are an amazing person da duk wanda ya rayu da ke dole ya faɗa son ki.”

“Kayya.” Shine kawai Juwairiyya ta faɗa tana son cewa ta zo gidanta ta duba yanda ake treating ɗinta kamar yarinyar gidan ba matar gida ba, sannan wanda ya zauna da ita ɗin bai faɗa sonta ba sai ma share kashinta da yayi yana soyayya da matarshi wanda har amanarta suke ci idan sun so.

Basu yi wata doguwar hira ba suka yi sallama Juwairiyya ta dubi abincin nata wanda har yayi sanyi ta rufeshi ta mayar kitchen akan in almajiri yayi bara zata bashi. Cornflakes ta haɗa ta dawo falo ta sha kana ta shiga tayi sallah ta ƙara fitowa don ɗaura abincin dare.

Kwana uku da haka Juwairiyya da Salima suka je suna wanda kafin nan Juwairiyya ta sake zuwa dubo mai jegon sau biyu. Juwairiyya ta so kwana a can don washe garin suna su tashi da hidiman bikin amma Muhammad ya hanata wai sai dai su tafi da sassafe, ranta bai so hakan ba ta shirya suka tafi tare ya ajiyesu.

Da yake Salima ta san da yawa daga cikin ƴan’uwan Juwairiyya sai ta saje a cikinsu aka yi ta hira ana aiki da ita. Wasu daga cikin dangin nata har zuwa suke yi su sameta su ce wai ta samu kishiya mai kirki! Bata ce bata da kirki ba amma a yanzu she is not her favorite person anymore, don tana shiga harkarta da Muhammad. Aka yi taro aka watse dangin Juwairiyya na sakawa Salima albarka domin hidiman da tayi a sunan ko ƙanwarta sai haka.

Yau ya saura kwana hudu tafiyan Muhammad wanda sai a lokacin kuma Juwairiyya ta ji labarin wai da Salima zai je Abuja daga nan kuma shi zai wuce ita kuma ta dawo gida. Kanbu! Yana maganan ji take yi kamar ta watsa mishi mari amma babu daman hakan saboda dalilai masu yawa ciki kuwa har da cewa Salima tana gurin tana mata murmushi kamar so take yi ta tayata farin ciki. Da kyar ta ƙaƙalo murmushi zuciyarta na ƙuna ta ce,

“Kai Masha Allah, hakan yayi kyau.”

“Zamu barki da yaron naki, kwana huɗu ne kawai zan juyo.”

A nan Juwairiyya ta lura Salima tayi amfani da sunan Hafiz ba kamar yanda take faɗa ba, wato da sunan ‘Masoyi’. Kenan da gaske tsoron faɗin hakan take yi a gaban Muhammad wai don kar ranshi ya ɓaci. Ai kuwa wannan karon tayi murmushin da ya kai zuci amma kuma na mugunta ta ce,

“Laa babu komai. Gida ya rage daga ni sai masoyina, my knight in shinning armor ai ba zai bari in ji kewa ba.” Ta kalli Muhammad ta wutsiyar ido ta ga he flinched kaɗan ya ƙara haɗe fuska.

“Kullum sai ya mini maganar cookies ɗinki, shiyasa kika ga yanzu yana yawan zuwa ya ce ki mishi don cewa nake yi ni ban iya ba ya je gurinki.”

“Da yake bashi da wahala kuma ko akwai wahalan ma mai sunan Hafiz ya fi ƙarfin ya tambayi abu in ƙi mishi. Mai sunanshi mutum ne da kyawun halinshi kan sa masoyina takwaranshi ya girbi alkhairinshi.”

“Ya isa!” Suka jiyo muryar Muhammad cikin kaushi fuskar nan tashi ta haɗe har tayi jaa tsabar ɓacin rai.

Salima tuni ta sunkuyar da kanta ta fara wasa da yatsunta kamar mara gaskiya ita kuma Juwairiyya ƙara tsayin wuyarta tayi tana jin kanta domin bata ga dalilin da zai sa tayi feeling guilty ko kuma tsoro ba.

“Sunanshi Muhammad Hafiz, idan ba zaki kirashi da haka ba kar ki sake kiranshi da wani suna. Ki kirashi da sunanshi kamar yanda na yanka mishi.” Yana faɗin hakan ya miƙe ya fice daga falon Juwairiyya dama a ɗakinta yake, da yammacin ne ya kira Salima su yi hiran bankwana tare amma mai kaifin harshen ta tarwatsa musu taron.

Yana fita Salima ta ja ajiyar zuciya ta dafe ƙirjinta tana goge gumin goshinta ta ce

“Wallahi na tsorita, sai na ga kamar zai kai mana hannu.”

“Ahh haba ya isa?! Banda hannu kam don mu ba bayi bane ko jahilai, kuma ma menene don na kirashi da sunan? Tun bayan haihuwarshi da sunan nake kiranshi don haka ba zai hanani rana tsaka ba.”

“Dama na faɗa miki ki bi a hankali watarana zai ji kishi.”

“Babu wani kishi tsabar ya takurani ne kuma bai isa ba.”

Nan suka cigaba da hiransu wanda Salima ta fakaici idon Juwairiyya ta turawa Muhammad text kamar haka,

‘Don Allah kayi haƙuri da abun da ya faru, ban san abun zai zama haka ba da ban ɗauko zancen har tayi maganar da zai ɓata maka rai ba. Kayi haƙuri ka yafe mini.’

Tana gama rubutun ta tura mishi wanda ta san ba zai mata reply ba amma dai saƙonta ya isa kuma yau ma tana cikin farin ciki domin tarkon da ta jima da ɗanawa yau ya kama mata Kurciya mai siffar kishiyarta.

Washe gari tun safe ƴan’uwa na jiki suka cika gidan don ganin tafiyar Muhammad, Juwairiyya jiya da dare kasa runtsawa tayi har gari ya waye zuciyarta tsinkewa take yi ta kasa samun sukuni. Ga Muhammad ɗin a gefenta wanda yake mata fushi akan maganarta na jiya amma ta kasa mishi magana balle ta roƙeshi ya fasa tafiyar su yi zamansu tare.

Sai da aka fito da bags ɗinshi tsakar gida Juwairiyya ta ji kamar tana dafe da katanga ne amma katangar na crumbling ta kowanne gefe. Idanunta cike da hawaye itama ta jeru a cikin mutane ga Muhammad shi kuma a tsakiyarsu yana bankwana da kowa one by one. Yana zuwa kanta ta zuba mishi ido shima haka, a nan ne ta kasa daurewa ta fashe da kuka ta nufi ɗakinta cikin sauri ta shige, a hankali ya bi bayanta ya sameta a durƙushe a gaban gado tana kuka kamar ranta zai fita. Me yasa take kukan to? Ya yiwa kanshi tambayar don a yanda take treating ɗinshi kamar ɗan iskan gari bai yi zaton tafiyanshi zai ɗaga mata hankali haka ba.

“Juwairiyya zan tafi.”

“Don Allah ka fasa tafiyan ka zauna a gida.” Ta faɗi hakan ba tare da ta ɗago kanta ba domin fuskarta ya caɓe da majina da kuma hawaye.

“Me yasa?”

“Kawai ka fasa don Allah.”

“Ai ba zai yiwu ba, anjima da rana jirginmu zai tashi zuwa Abuja, jibi kuma zan tafi shikenan kin huta da ganina. Dama ba haka kike so ba?”

Girgiza kanta tayi tana mai cigaba da kukan mai tsuma zuciya.

“Wallahi zan daina maka abun da nake yi ka zauna.”

“Tempting, but no! Shekara uku ne yanzu zaki ga sun cika na dawo cikinku. Ki kula da kanki don Allah ku kare kanku ku zauna lafiya Juwairiyya, a yanzu babu abun da zai fi mini daɗi irin in ji ana zaman lafiya a gidana duk da cewa bana ciki. Ku riƙe amanar junanku sannan ku kiyaye mini kanku na san wannan bani da matsala don dukkanku babu na banza. Juwairiyya ki zauna da kowa lafiya please. Na tafi, Allah Ya sadamu da alkhairi.” Yana gama faɗin hakan ya fice yana goge kwallan da ya taru a gefen idanunshi.

Ita kuma Juwairiyya kwanciya tayi a ƙasa tana wayyo wayyo tana kiran sunanshi amma ta kasa tashi ta bi shi.

“Muhammad don Allah ka dawo. Wayyo Allah na. Ya zan yi rayuwa kai ma in babu kai?”

Mum Fateey 👌

Kiranta sunanta da ƴan’uwan Muhammad ke yi a falo ya sa Juwairiyya ta tashi tsaye ta goge hawayenta ta fita ta samesu suka fara tsokanarta tare da rarrashi. Basu ƙara minti talatin ba suka watse aka barta gida ya rage daga ita sai Hafiz J wanda tun jiya da dare Salima ta kawo mata suturunshi da duk wani abu da zai buƙata. A yanzu gwalantoyi yake mata yana tambayarta ina mamanshi da babanshi, wannan tambaya ya sakata hawaye shi kuma yaron ya saka kuka ta dawo tana rarrashin shi, can kuma ta kama hannunshi suka fita waje tana cewa,

“Mu je kitchen in maka cookies.”

Yana jin haka ya rufe bakinshi ya bita tana jin nauyi a zuciyarta,sai da suka fita tsakar gidan ta ji gidan ya mata faɗi da yawa. Da dare kuma tsoro ne ya shiga ranta ta kulle ko’ina suka kwanta da wuri tun takwas na dare, kafin nan kuwa tayi waya da Salima sau biyu tace mata sun isa lafiya suna hotel wanda ta sani suna can suna abun da ba zata so tayi tunaninshi bane.

Tun da aka yi maganar tafiyar ta gane Muhammad ya zaɓi ya tafi da Saliman ne tunda ita bai ɗauketa a matsayin mace ba, ko tarayyar bankwanan ma bai nema a gurinta ba yayi baccinshi wato yana nufin in ita ta matsu ta nemeshi ko? To kuwa tayi rayuwa a baya babu miji kuma babu abun da ya sameta a yanzu, ya je su cinye kan su da matar tashi, in ya ga dama ya gutsire wani sashe na jikinta ya tafi da shi as Souvenir.

Sai can dare wajen sha ɗaya ta ji wayarta tana ringing ta farka cike da tsoro tayi saurin sakata a silent sannan ta duba waye ne. Sunan ‘Muhammad’ ta gani ɓaro-ɓaro babu wani sakayawa balle inkiya. Kamar ba zata ɗauka ba amma da ta ga ya kusa tsinkewa sai tayi saurin amsawa.

“Juwairiyya.” Ya kira sunanta kamar mai jin tsoron magana.

“Na’am.” Ta amsa, daga nan kuma tayi shiru bata sake cewa komai ba domin zuciyarta ce ke kissima mata cewa ya gama sharholiyarshi da matarshi yanzu kuma ya fito half time shine ya tuna banzar da ya bari a gida yace bari ya kirata.

“Kin rufe ko’ina ko?”

Ta sake jin muryarshi bayan an ɗauki lokaci da ta tabbatar ya ƙai seconds arba’in. Wato ba ma ita ɗin ya kira ya ji ya take ba, damuwarshi gidanshi ne da ɗanshi kar wani ya shigo ya samesu.

“Eh.”

“Ina Muhammad Hafiz?”

“Gashi nan yana bacci.”

“Ke ma kin yi baccin ko?”

“Ƙarfe sha ɗaya me zan jira idan ba bacci ba.”

“Juwairiyya kenan. Sai da safe.”

Bata amsa ba ta kashe wayarta tana jin zafi a ƙirjinta domin ya dawo da ita baya, ɗazu da kyar ta samu tayi bacci dalilin duk lokacin da ta rufe idanunta shi da Salima take hangowa akan gado suna abun da suka ga dama. Ta jima idanunta biyu waɗannan images ɗin na ruɗa game da azalzalar zuciyarta kafin bacci ɓarawo ya saceta shine yanzu ya tasheta ta koma squire one, hawaye ne suka cika mata ido amma ta taune laɓɓanta ta hanasu zuba.  Ta gaji da kukan da kuma tunanin banzan mai baƙanta mata rai, ta gaji.

A gefen Muhammad kuwa tun lokacin da ya samu makarantar ya fara saving kuɗi domin buƙatunshi da scholarship ba zata biya mishi ba sannan ga matan aurenshi da zai tafi ya bari har biyu da yaro. Da yake Salima ta san duk halin da ake ciki na tafiyar da kuma plan ɗin sai ya zo ya samu Juwairiyya ma da maganar amma ta furta mishi maganar da bai mishi daɗi ba wai ‘Damuwarku’! Shi da kanshi yana matsayin mijinta ya kawo mata abun farin ciki amma ta nuna halin ko in kula?

Wannan abu da tayi yasa ya share kashinta ya kuma ƙi faɗa mata duk wani shirye-shirye da ake yi, ita kuma Salima ko bai faɗa mata ba zata tambayeshi sannan tana mishi addu’a wanda hakan ba ƙaramin daɗinshi yake ji ba saɓanin amaryarshi da ko kallo bai isheta ba. Tana cewa bata son mutum mai wulaƙanta mutane amma ita ta kasa ganin wanda take yi mishi shi da yake matsayin mijinta wanda Aljannarta ke ƙarƙashin ƙafarshi. Ana washegarin zasu tafi Abuja ya kira Salima falon Juwairiyya don a yi hira wanda tun da yake bai taɓa yin hakan ba, sai dai yana faɗawa Juwairiyya maganar tafiya da Salima Abuja ya ga fuskarta ta canja, a nan kuma yayi imanin kafin a watse sai ta raba hali, ai kuwa ta ɓata mishi rai domin ya sani tun ba yau ba take kiran ɗanshi da sunan ‘Masoyi’ kuma shigowarta gidanshi bai hanata ba saboda ya sani ba da gayya take haka ba. Amma na yau ya gane habaici take mishi, wato Hafiz marigayi shine mutum shi kuma ba mutum bane? Wa zai so matarshi ta furta wannan kalmar a gareshi ko da kuwa wanda ake comparing ɗin nasu abokinshi ne? Not him! Ba zai so haka ba kuma abun ya sosa mishi zuciya wanda ya hanata abun da bai yi tsammanin zai hanata ba.

Wani abu da bata sani ba shine Salima ita ta biya musu kuɗin jirgin daga Gombe zuwa Abujan akan wai shine gudumawarta, shi ya so ne ya tafi ana gobe jirginsu zai tashi amma Salima ta taho mishi da wannan surprise ɗin ya kuma karɓa da hannu biyu, domin kuwa zai samu ya ƙeɓance da ita kafin ya shiga rayuwar Sexual abstinence a UK.

Da wannan ɓacin ran ya fita ya je gidansu Salima da na su Juwairiyya ya yiwa iyayensu sallama. Daga nan kuma ya nufi gidansu ya yiwa Babanshi da Yadikkonshi sallama wacce har gobe baya ganin girmanta amma saboda matsayinta na matar ubanshi yake tolerating ɗinta. Magana wannan mai tsayi bata shiga tsakaninsu tunda ya girma yayi hankalin kanshi ya gane waye mai sonshi. Tana ɗaya daga cikin dalilin kafuwanshi akan wasu halayenshi musamman akan neman mace mai ɗa’a, ya sani Babanshi bashi da iko da gidanshi shi yasa ta wahalar dashi a ƙuruciyarshi aka kuma kasa kwato mishi haƙƙinshi, hakan ya faru ne bayan an sake mahaifiyarshi suka rayu babu ita har na shekara uku kafin daga baya Baban ya dawo da ita suka cigaba da zama har ta rasu a samartakan shi. Tun daga lokacin ya canja halayenshi da dama ciki kuwa har da rashin sakewa wasu mutane fuska idan ya lura mugaye ne ko munafukai!

Haka ya dawo gida da dare ya samu Juwairiyya har tayi kwanciyarta alaman abun da ta mishi bai dameta ba amma gashi ƴar’uwarta da ba ita tayi laifin ba ta mishi text ɗin ban haƙuri wanda ya ji ya sassauto kaɗan, domin kuwa idan ya tuna yana da mace mai ladabi kamar Saliman sai ya ji zai shanye rashin hankalin Juwairiyya har zuwa lokacin da ita ma zata yi hankali. Ya so a ranar ya karɓi Apple a gurinta amma idan ya tuna wulaƙantashi da zata iya yi sai ya ji ya fasa, zai riƙe sauran girmanshi kafin duk su zube a tafin ƙafarta, da haka kuwa yayi baccinshi ba tare da ya nemetan ba.

Ya zo mata sallama ta gudu ɗaki dalilin kukan da ya kwace mata wanda shima ji yake yi kamar an ƙara ɗaura dutsen da aka ɗage a zuciyarshi bayan an ɗaura mishi aure da ita. Ya so ya je ya rungumeta a jikinshi ya ji ɗuminta one last time amma sai ya kasa zuwa domin in ya isa ba zai iya controlling kanshi ba gashi kuwa mutane na jiranshi a tsakar gida. Sallama kawai ya iya mata ya fice yana jin tausayinta a ranta, a yanzu ya ƙara yarda da batun Hafiz, Juwairiyya bata da wayo, bata san me take so ba haka kuma bata san in tayi fushi na lokaci kaɗan ta bari ba, faɗanta ba ya ƙarewa kamar wata kuturwa.

Suna isa Abuja suka sauƙa a hotel ɗin da Salima ta kama musu na kwana biyu tunda ita sai jibi zata koma a jirgin safe. Tun a lokacin ya fara cire kishin ruwanshi a jikinta ta bashi haɗin kai wannan karon ba tare da ta gujeshi ba in ya nemi ƙari. Bayan haɗuwansu na biyu ne ya fito ƙaramin falon ya barta a ɗaki tana baccin gajiya ya kira Juwairiyya wacce yake ganin fuskarta a yayin da yake tare da Salima, bai yi tsammanin ta shiga ranshi har haka ba.

Ya ɗauka zata mishi sannu da hanya ta tambayeshi ya yake duk da cewa shi ya kirata amma sai ya ji tayi shiru, hakan yasa yayi ta mata wasu tambayoyi wai duk don ta sake su yi hira amma sai a ƙarshe ta faɗa mishi magana mara daɗi kuma ta kashe wayarta. Wai me yake damun yarinyar ne? Kanta kalau kuwa? Ba ɗazu da hantsi take kukan rabuwa dashi ba? Ɗazu yana ji ta kira Salima bayan sun isa ta mata ya hanya amma shi ko text bai gani ba, a hakan bai yi zuciya ba ya kirata amma ta kasa mishi magana mai daɗi ƙarshe ma ta faɗa mishi baƙa ta kashe wayar. To ya isa! Abun ya fara yawa!

Komawa ɗaki yayi ya samu Salima ta farka tana cikin banɗaki ya zauna a bakin gado ya dafe kanshi. Yana zaune a haka ya ji ta kwanto a bayanshi wanda hakan ya ɗauke mishi damuwar da yake ciki ya biye mata don it’s now or after one year.

Sai a airport Salima tayi kukanta ya rungumeta tsam a jikinshi yana rarrashinta yana jin shima kamar yayi hawayen. Babu yanda suka iya suka rabu ya ɗauki jakarshi ya tafi tana ɗaga mishi hannu, in ba don yana nemawa iyalan nashi ƙarin walwalar rayuwa ba da babu abun da zai sa ya rabu da su.

Washe gari Salima ta koma tana jin kewar mijinta a ranta wanda ta wani gurin kuma haushin Juwairiyya ce taff a cikin ranta, domin da babu ita da Muhammad ya kwasheta ita da ɗansu sun tafi tare, ko da kuwa ba zai iya biya musu kuɗin jirgi ba Babanta zai saka hannu kuma zata kanainayeshi ta yanda ba zai ƙi ba. Shigan Juwairiyya cikinsu ba ƙaramin wargaza mata shirin rayuwarta yayi na. A hanyan ne ta kissima a ranta zata hura mata wuta ta bar mata gidanta ta yanda in Muhammad ya dawo next year zai kwashesu su tafi tare. Tana son zamanta kusa da mijinta ta yanda rashinta ba zai sa ya manta da wasu ɗabi’un da ta ɗaurashi a kai ba.

Ko da ta iso Gombe ƙaninta ne ya zo airpot ya ɗauketa ya kaita gidansu, a can ne ta tarar da mahaifiyarta wacce ita kaɗai ce matar babanta tana jiranta ta ƙara mata karatun rayuwa irin tasu sannan ta koma gida da shirin fitar da Juwairiyya ko ta halin ƙaƙa.

*****

“Ai nace mishi Baban Hafiz wannan wayan da muke yawan yin nan zai hanaka karatu fa, ya ce wai in bai kira iyalanshi ba wa zai kira?” Wannan faɗin Salima ce tana tsaye a bakin ƙofar kitchen ɗin Juwairiyya bayan sati uku da tafiyan Muhammad UK.

“Ai gaskiyanshi, yana da waɗanda suka fi ku ne?” Juwairiyya ta bata amsa mai ɗauke da tambaya.

“Hakane kam, iyalin mutum su ne rayuwarshi.”

“To kin gani. Bari in je in sha magani kafin shinkafar ta tsotse.” Juwairiyya ta rage gudun gas cooker ta fito daga kitchen ɗin tana riƙe da kanta da yake sarawa.

“Ayya Allah Ya kawo sauƙi. Kin san stress ɗin makaranta ne ya jawo miki haka.”

“Eh.” Juwairiyya ta amsa tana jin yanzu ko maganar bata son yi.

Tana son faɗawa Salima surutunta ne yake ƙara mata ciwon kai amma ta kasa, tun bayan tafiyar Muhammad da kwana huɗu ta fara zuwa lectures, wanda sati ɗaya da haka Salima ta aika mata dubu talatin a account ɗinta wai in ji mijin nasu ta mayar da kuɗinta da tayi registration da shi, wato ba zai yarda tana ƙarƙashinshi ta biyawa kanta kuɗin makaranta ba.  Text ta tura mishi na godiya kamar haka

 ‘Thanks’

Tun bayan tafiyarshi sau biyu kawai suka yi waya wanda duk shine yake kiranta, na farko ya kirata ya ce mata ga sabon numbernshi sannan na biyu ya kirata yana tambayarta labarin makaranta da ta koma, ita duk wannan ba burgeta yayi ba illah ma haushi da ya bata domin kuwa kafin ya mata kiran farkon sai da ya kira Salima suka yi kusan awa suna waya a gabanta yana bata labarin duk abun da ya faru bayan rabuwarsu a airpot, ita kuma sai can yamma ya kirata yace mata ya isa ga kuma numbernshi tace sannu, shikenan suka yi shiru da ya gaji da shirun ya kashe wayarshi. Kira na biyu kuwa yana tambayar ya school tace lafiya itama ta kashe wayarta, ya mata magana a whatsapp har da ɗaukan hoton ƙaramin ɗakin da ya kama haya ya tura mata, sai ta mayar mishi da reply kamar haka,

‘Anya wannan ƙaramin gadon zai ɗaukeka?’

Shikenan ta tura mishi sai dai da ya buɗe bai yi reply ba har rana mai kamar ta yau. Shiyasa a yanzu da Salima take bata labarin yawan wayar da suke yi ta ji baƙin ciki ya cika mata zuciya, wato ita ce ba zai kira ba.

A maimakon Salima ta bar Juwairiyya ta huta sai ta bita zuwa ɗakinta tana mata hiran da wacce take sauraron ta fara daina gane labarin da ake bata. Zama tayi akan kujera tana dafe da goshinta itama Salima ta zauna HJ ne da yake binsu duk inda suka yi ya ƙi zama ya cigaba da fira jirgin samanshi a sama yana wani ƙara da Salima ta koya mishi wai hakane ƙarar jirgin da Babanshi ya shiga ya tafi.

Da surutun Salima da kuma iface-ifacen HJ su suka ƙarawa Juwairiyya ciwon kai ta ji hawaye na taruwa a idanunta. Babu abun da take so yanzu irin su watse su barta tayi nursing ɗin kan nata amma da alama ba zata samu hakan ba.

Tun tana amsawa Salima da ‘eh’ ‘a’a’ har ta daina magana da baki ta fara amsa mata da hannu domin kanta ma bata iya ɗagawa da kyau balle ta girgizashi. Sai da ta tabbatar shinkafar ta tsotse ta miƙe ta nufi kitchen tana cewa,

“Mu je ina tunanin abincin yayi.”

Da haka suka ɗunguma zuwa kitchen Juwairiyya ta raba musu jollof rice ɗin ta miƙawa Salima ta su ita kuma ta shige da nata ɗaki, tana shiga ta sakawa ƙofar lock ta kashe duk wutan falon ta nufi bedroom ɗinta tana zagin Salima a ranta.

Tun ƙarfe bakwai ta bar gidan ta tafi school ita ce bata dawo ba sai ƙarfe biyu da rabi, tana ajiye jakarta a ɗaki ta fito kitchen ta ɗaura musu abincin rana wanda Salima ta ƙi amincewa da tsarin da Juwairiyya ta kawo don ta samu sauƙi, akan cewa ita Salima ta dinga yin na rana kullum ita kuma zata dinga yin na dare in ta dawo daga school, breakfast kuma kowa ya dinga yin nashi. Wannan tsarin da sun bi kowa zai huta amma Salima tace wai zai raba kansu in sun daina yiwa juna girkin safe. Juwairiyya zaginta ne bata yi ba a wannan lokacin amma ranta ya ɓaci, wani irin maganar banza ce wannan? Dama ta faɗa mata haɗin kanta take nema ne?

To ta ƙi amincewa da wannan tsarin amma a hakan yau tana fara girki ta zo bakin kitchen ɗinta ta jawo kujera ta zauna duk da cewa ta faɗa mata kanta na ciwo a farko. Yanzu kam ba zata fito ba sai dab da maghrib ta ɗaura musu na dare wanda tuwo kawai zata yi tana da miya a fridge.

Salima tana ƙarɓan abincinta ta koma ɗakinta tana murmushin mugunta ta baje a falonta suka ci girkin amarya ita da ɗanta sannan ta zauma jiran Yayan Muhammad da yake zuwa dubasu kowanne sati da kanshi. Tana karkaɗa ƙafa har aka yi sallan la’asar bata tashi a gurin ba don bata sallah, can da yamma liss ta ji ana kwankwasa musu gate ta zari hijabinta da sauri ta fita ta buɗe tana mishi sannu da zuwa ya amsa ya shigo tare da ƴaƴanshi uku wanda babbar ta kai shekara goma da ƙannenta biyu maza.

A tsakar gida ya tsaya kamar kullum suka gaisa da Salima wacce ta tsugunna har ƙasa tana mishi kawaici a matsayinshi na surkinta wato yayan mijinta.

“Ina amaryar taki ko bata dawo daga makaranta bane?”

“Ta dawo tun da rana, tace dai zata kwanta yanzu kam na san ta farka tunda bata iya baccin yamma. Bari in buga mata.”

Da haka ta je bakin ƙofar Juwairiyya ta fara bugawa amma ba’a buɗe ba, ƙarshe ta bar bugawan ta ce,

“Bari in kirata a waya in faɗa mata kai ne kar ta ɗauka takura mata zan yi.”

“To.” Ya amsa yana riƙe da hannun HJ wanda ke wasa da ɗanshi ƙarami.

Bayan ta dawo ta kira Juwairiyya har sau biyu yana ringing ba’a ɗauka har zata kira na ukun ya dakatar da ita da yake handsfree ta ke sakawa ya ce,

“Ki bari kawai wataƙila bacci ta yi. Da fatan dai tana lafiya bata da wata matsala?”

“Lafiyarta kalau. Amma ba bacci take yi ba kawai ta yi zaton ni da HJ ne zamu ƙara mata ciwon kai.” Ta ƙarisa maganan tana dariya kaɗan.

“To Allah Ya kyauta. Idan ta fito ki ce na zo dubaku ban sameta ba. Na barku lafiya.” Da haka ya juya ya fita hannunshi riƙe da na HJ suka je bakin mota ya bawa yaranshi ledoji wanda kaji ne manya guda biyu da kuma biscuits ɗin HJ suka bawa Salima ta karɓa da godiya kana ta sakasu a freezer tana murmushi kamar bakinta zai rabe gida biyu.

Sai gab da maghrib Juwairiyya ta fito wacce tayi bacci dalilin ciwon kanta ta nufi ɗakin Salima don ɗiban shinkafar tuwo, a nan Salimw ke bata labarin Yayan Muhammad ya zo ya kawo musu kaji biyu ta tashi ta miƙo mata ɗaya tana cewa,

“Ga wannan ki ferfesa mana ita mu ci da daren nan, duk da cewa bamu da miji a gari ai ba zamu fasa cin daɗi ba.”

Juwairiyya ta karɓa tana yaƙe domin wannan aikin da Salima ta haɗata dashi ya ɓata mata tsarinta na hutawa,

“Da kin bari dai nayi mana gobe da rana tunda lecture ɗaya nake dashi, don idan na fita seven zan dawo ten In sha Allah.”

“Ayya da kin daure dai kin mana don wallahi tunda ya kawo nake ta jin kwaɗayinta kin san last week da ya kawo mana kifi ban wani ci na kirki ba saboda ni na dafa. Amma tunda kin ce haka shikenan.”

“Babu komai zan dafa mana yanzun.” Juwairiyya ta faɗa tana cije cikin bakinta tsabar ɓacin rai, wai ita Salima kam bata san tana takurata bane?

“Yauwa bari mu je mu tayaki.”

“A’a ku yi zamanku zan gama in no time.” Tayi saurin katseta domin bata son ta bita ta tayar mata da ciwon kan nata.

“To shikenan.” Da haka Salima ta koma kan kujera ta zauna Juwairiyya kuma ta shiga store ta ɗebo abun da take buƙata kana ta fito tana cewa,

“Don Allah gobe in Nanayo ta zo ki faɗa mata zata dinga mini wanke-wanke da gyaran kitchen in ya so ni kuma in ji da shara da girki. Wallahi makaranta ya saka na fara ƙazanta don tun jiya ban share ɗakina ba saboda rashin sukuni da lokaci. Sai ki faɗawa maigidan ya ƙara mata albashi kamar yanda aka tsara kwanaki.”

“Ai kina buƙatar samun mai taimaka miki kam, to zan faɗa musu dukkansu. Ai zaki ji daɗin aikinta, yarinyar akwai hankali.” Faɗin Salima cikin farin ciki kamar ta kurma ihu amma tayi containing kanta har Juwairiyya ta fita.

“Kai Hafiz, zo.” Ta yafuto ɗanta wanda ya zo da gudu ya tsaya a gabanta.

“Har na tuna da cookies ranar kayi ta kuka da ba’a maka ba.”

Yana jin sunan cookies ya bi Juwairiyya da gudu zuwa kitchen ya samu ta ciro kazar a ledarta zata wanke irin yanda aka koya musu a eBook ɗin Ailisco (09123227777) mai ɗauke da sirrikan gyaran su nama, kifi kaza da yanda za’a yi avoiding food poisoning (recommended ga matan da basu taɓa shiga classes ɗin girki ba and ƴan mata masu tasowa ko amaren bana).

“Aunty, Tutis.” Ya faɗa yana mai kama ƙafarta ɗaya wai zai haura kanta ya duba me take yi.

“Ya Salam, Masoyi ba yau ba sai gobe. Yau ina da aiki ba zan iya maka ba.”

“Tutis.” Ya ƙara nanatawa yana ɓata fuska.

“A’a yau babu cookies sai gobe. Maza tafi gurin mamanka ina aiki ne.”

Ai yana jin hakan ya fara kuka da ƙarfinshi domin wanda ya hanashi kukan ya tafi ita kuma Salima uwarshi bata kwaɓarshi.

“Subhanallahi me ya faru?” Salima ta fito tana tambayar ba’asi tana jan yaron jikinta.

“Wallahi duk ihun nan akan cookies ne, nace mishi sai gobe shine ya buɗe baki. Masoyi aiki nake yi sai gobe zan maka.”

“Ai shi kuma bai san lallashi ba ko alƙawari, ka zo mu je in baka biscuits.”

Maƙe kafaɗarshi yayi wanda Juwairiyya tana ganin haka ta sauƙe nannauyan numfashi ta ce,

“Shikenan ka zo in maka.”

Yana jin hakan ya daina kuka ya zo ta ajiye kazar a gefe ta fara ciro kayan cookies Salima kuma ta ƙara jawo kujerarta ta fara zuba mata hiran banza da wofi. Sai ƙarfe tara ta samu ta gama komai ta kai musu nasu ɗakinsu da yake tun da aka gama cookies suka ci suka gyatse suka tafi suka barta.

Kanta na sarawa ta ɗauki nata zuwa nata sashen amma tana loma ɗaya ta ji ba zata iya ci ba ta sakasu a containers ta adana a fridge. Tea kawai ta haɗa mai zafi ta sha tayi wanka ta kwanta bacci mai nauyi.

A can ɗakin Salima kuwa bayan su  ci tuwo da ferfesu suka gyatse ta saka ɗanta yayi bacci sannan ta kira Muhammad wanda kullum ita ce mai kiranshi saboda dalilai biyu, na farko in kiran za’a yi daga Nigeria zuwa can ya fi sauƙi akan in Muhammad ɗinne ya kira yanzu kuɗinshi zai ƙare zuut. Na biyu kuma ta sani shi ba zai iya kiranta kullum wai don su yi hira ba shiyasa ta ɗaukawa kanta nauyin kiranshi kullum sau biyu don tana son ta sakaltashi da haka saboda Juwairiyya da bata kiranshi ya dinga jin haushinta. Sun kai minti ashirin suna waya sannan suka yi sallama ta kashe wayar farin cikin tsantsa a ranta domin duk tarkon da take saitawa yana kama mata kishiyarta.

Muhammad yana gama waya da Salima ya ce yau kam bari ya kira Juwairiyya domin yayanshi ma ya ce yau da ya je dubasu bai samu ya ganta ba wai tana ɗaki ta ƙi buɗewa wanda ya san zata aikata, kuma tunda abun ya tsaya ne akan rufe ƙofa ai da sauƙi saboda ya sani she can do worse than that. Kiranta yayi sau biyu bata yi picking ba ya ji haushi a ranshi domin avoiding ɗin nashi da take yi yayi yawa kamar wanda suke gaba da juna, tsaki ya ja ya kwanta don dama bacci yake yi Salima ta kirashi ya farka.

Mum Fateey 👌

Hello.

Da yawan makaranta suna ta ƙorafin wai halin Juwairiyya na ɓata musu rai har wasu na cewa zasu daina karatun har sai ta yi hankali. Wani abu da kuka manta shine bayan dalilin nishaɗi littafin na ɗauke da faɗakarwa ne mai yawa wanda nake son da ni da ku mu ƙaru da su. Akwai irin Juwairiyya a cikinmu waɗanda in kuka yi duba nan kusa cikin dangi ba za’a rasa irinsu ba, ba lallai ne ace kishiyarsu ce take musu zagwan ƙasa ba, zai iya yiwuwa sune suke zuga kansu ko ƙawaye ko wasu mutane daban. Sannan a kusa da mu akwai irin su Salima waɗanda wasu mun ganesu wasu kuma sai dai mu yi addu’ar Allah Ya karemu daga sharrinsu amma wallahi ba zamu taɓa gane da fuska biyu suke zaune da mu ba saboda basa barin evidence.

Kar surutun yayi yawa, ko a zahiri kafin mutum ya gane irinsu Salima sai ya wahala so please ku bi darussan ciki ku kuma gane tactics ɗin masu halin ba wai ku bi iya daɗin book ba. One Love ❤️

(30)

Kamar yanda Juwairiyya ta nema washegari Nanayo ta fara mata wanke-wanke da gyaran kitchen, hakan yasa ta samu sauƙi a harkokinta na school. Wannan karon ma mai Napep Muhammad ya sama mata wanda zai dinga kaita yana dawo da ita gida sannan kowanne sati yana bawa Salima kuɗi tana bata wai na hidimar school ɗin. Irin wannan hidimar da yake mata ne yasa ta fara sauƙo da kanta ta fara kiranshi in anyi kwana uku zuwa huɗu haka, wanda in ta gaisheshi tace ya school shikenan sai ta mishi sallama ta kashe wayarta babu dogon hira.

Yau watan Muhammad biyu a UK, Juwairiyya tun tana cikin napep zata dawo gida take ta tunaninshi domin tayi kewarshi ba kaɗan ba. A yanzu da suka yi nesa da juna sai ya kasance faɗa wannan bai taɓa shiga tsakaninsu ba, wannan dalili yasa yau take jin in ta koma gida ta ci abinci ta huta zata kirashi a waya su yi hira kaɗan ko da na minti biyar ne.

Tana isa ta samu Nanayo ta mata wanke wanke amma bata gyara mata cikin kitchen ɗin ba wanda hakan ya ƙonawa Juwairiyya rai, dalilin ba yau ta fara mata hakan ba. Tun da ta fara mata aiki yarinyar da ake cewa mai hankali ce ta fara mata guntun rashin kunya wanda in tana aiki Juwairiyya ta ce ki gyara kaza ko ki ƙara goge nan bai yi kyau ba, to sai ba zata ce uffan ba watarana ta gyara a gaban Juwairiyyan wani lokaci kuma ta ƙi yi sai ta gama aikin ta tafi Juwairiyya dawo ta samu bata yi ba.

Sannan wani lokaci kuma zata zo ta yiwa Salima aiki amma sai ta koma gidansu ta ƙi yin na Juwairiyya musamman in Juwairiyyyar ce take da girki, sai ta dawo da rana zata ɗaura musu abinci ta samu kitchen ɗin yanda ta bari ko’ina a wargaje. In ta aika a kirata sai a ce wai kanta ne ke ciwo ko kuma bata da lafiya ne ko kuma wai ta tafi aika wata unguwa. Waɗannan abubuwan yasa Juwairiyya ta fara jin haushin yarinyar tana ɗaure mata fuska bisa jagorancin Salima wacce take faɗa mata wai itama farkon fara aikinsu haka take mata amma da ta zare mata ido sai ta sauƙar da kanta suka zauna lafiya.

Rai na ƙuna wannan karon Juwairiyya ta shiga kitchen ɗin nata ta gyarashi tun kafin ta isa ɗaki, da yake ba girkinta bane sai ta nufi ɗakin Salima don ƙarban abincin ranarta a nan ta samu Nanayo na zaune a falo tana kallo ita da uwarɗakin nata da HJ. Sai da ta fara yiwa Salima ya gida sannan ga dubi Nanayo rai a haɗe ta ce,

“Sannu Nanayo, wato dama tun ɗazu kina nan kina kallo shine kika ƙi mini aiki ko? Yau kuma wace ƙarya zaki mini da ya hanaki aiki tunda na kamaki?”

Sunkuyar da kai yarinyar tayi ta ƙi amsawa wanda hakan ya ƙara ƙular da Juwairiyya domin ta tsani wannan shirun (ashe babu daɗi).

“Magana nake miki kin yi shuru kin kyaleni.”

“Bana jin daɗi ne.” Ta bata amsa a karon farko.

“Ba kya jin daɗi amma kin iya zama kiyi kallo ai ko? Wato rashin jin daɗin bai hana kallo ba. Yanzu kam ya riga da ya wuce ai ba yau kika saba mini haka ba, bari in baki kuɗi ki je shago ki saya mini katon ɗin indomie.”

Sai a lokacin Salima ta saka baki wacce duk draman da ake yi tana hakimce a kujera tana kallonsu.

“Ke dai Nanayo na kasa gane me yasa kuke ta samun matsala ke da Auntyn naki.”

“Ni ba Auntyn ta ba ce, domin da ta ɗaukeni da daraja da ba zata dinga wulaƙantani ba.” Wannan faɗin Juwairiyya kenan tana jin ɗacin na dawowa makwogoranta tana bin Nanayo da harara.

“Kuma fa nace miki zaman lafiya nake yi da ita ban san me yasa ke kuma take miki haka ba.”

“Saboda ta rainani ne, in ba haka ba ba’a kwana biyu masu kyau sai ta mini abun da bana so. Kwanaki har nan na kawo miki Non-Stick frying pan ɗina da ta goge mini shi da soson ƙarfe sannan ta bar mini marafen kuloli a cikin ruwa suka sha ruwa wanda har yau da nake miki magana in an matsa sai ruwan ya ɗigo. Ya kamata a ce shekarun da tayi a ƙarƙashinki tana aiki ta san me ya kamata ta yi da wanda bai kamata ta yi ba. Ni har na gaji da magana ma amma dai ki gyara halinki domin in zamu tafi a haka gaskiya kullum sai mun sami matsala, simple instruction kuma simple task amma a ce kin kasa ɗauka. Bari in je in ɗauko miki kuɗin.”

Tana fita Salima ta kalli Nanayo fuska cike da tausayi ta ce,

“Haƙuri zaki yi da ita don nima haka muke zaune, ai bai kamata ta ce miki kina ƙarya akan rashin lafiyarki ba tunda babu wanda ya fi ƙarfin rashin lafiyar. Ki bar mana aikin na kwana biyu zata yi zuciya tace bata so sai ki dawo mu ci gaba. Aikan kuma ki karɓa ki mata kar ki ce ba zaki je ba don na sanki kema kina da guntun zuciya.” Ta ƙarisa maganar tana dariya irin tana tsokanar Nanayon ne wacce ita kuma da yake bata da wayo kamar ɗayar sai ta faɗa tarkon da aka ɗana mata.

Salima tana rufe baki Juwairiyya ta dawo ta miƙawa Nanayo kuɗin tana cewa,

“Katon ɗaya zaki saya mini na asalin Indomie ba sauran tarkacen ba.” Tana faɗin hakan ta zauna a kan kujera suka fara hira da uwargidan tata wacce ta aika Nanayo ta ɗauko mata abincin ranarta a kitchen ta buɗe ta fara ci.

Suna zaune suna hira aka yi sallama a tsakar gida suka amsa da yake sun gane muryar yaron ƙanin Nanayo ce. Sum sum ya shigo ya miƙawa Salima kuɗi yana cewa,

“Wai gashi in ji Innar mu wai kuyi haƙuri Nanayo ta daina aiki tunda ana ɗaukan rashin lafiyarta ƙarya ne.” Yana faɗin hakan ya juya ya fice da sauri ya bar su baki a buɗe wanda ɗaya na gaskiya ne ɗaya kuma fake.

“Kin ji abun da na ji kuwa?” Juwairiyya ta tambayi Salima tana riƙe bakinta cikin tsantsan mamaki.

“Hmm abun ya bani mamaki, yau da zata bar aikin ai da ta faɗa mana ba wai ta je gida ta faɗawa mamarta ba. Yanzu sai su ɗauka wani mugun halin muke mata.”

“Su faɗa mana, tunda ni nasan ba mugun halin nake mata ba ai ba zai dameni ba. Aiki kuwa zan cigaba da yin kayana dama kuma don makaranta ne yasa na nemi a taimaka mini. Aikin banza aikin wofi.”

Nan Salima ta cigaba da hura Juwairiyya ita kuma ta sake baki tana ta maganganu, sai da aka kira la’asar suka watse a nan ne kuma ta fara tunanin wa zai sayo mata indomie ɗin domin Muhammad ya hanasu fita shago sannan gobe saturday da sunday ba zata fita school ba balle ta bawa mai Napep ɗin nata ya saya mata a hanya in suna dawowa. Almajirai kuma tana tsoron su gudu mata da kuɗinta wanda chances ɗin are 99.7 %. Sai kuma yaran unguwa bata aikansu dalilin bata shiri da iyayensu mata waɗanda suka mata laifi tun tana amarya.

Sai da tayi sallahn la’asar ta kira Muhammad wanda numbern ya ƙi shiga amma bata fasa ba ta ƙara kira bayan wani lokaci ta sameshi.

“Hello.” Ta faɗa a sanyaye domin abun da zata tambayeshi ba lallai ne ya yarda ba amma she wants to try her luck.

“Ya?” Shine kawai abun da ya faɗa kamar ma ranshi a ɓace ne.

“Ya karatu?”

“Lafiya.” Ya amsa a taƙaice.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta fara tunanin me yake damunshi yau da yake amsa mata magana kamar wanda aka hassala?

“Dama ina so ka mini izini ne zan je shago in sayi abu.”

“Ina mai sayo muku take? Me yasa ba zaki bata ba?”

“Wai Nanayo?”

“Eh.”

“Ɗazu mu samu matsala tace ta bar aikin.”

“Ke kam Juwairiyya da waye ne ba zaki matsala ba a rayuwarki? Ke duk inda kika shiga mutane na complain ɗinki an kasa zaman lafiya da ke? Wai wannan wace irin rayuwa kike yi ne? Kuma kina jin daɗinta a haka? Ke ce faɗa da makwabta, ke ce yiwa ƴan’uwana gani-gani kuma ke ce faɗa da masu aiki. To dama kina bashin gaba ma da mijinki waye zaki bari? Ba zaki fita ba kuma na faɗa miki tun ba yau ba na hana cin indomie a gidan nan amma kika yi kunnen uwar shegu kina saya kina ci, in baki sani ba nayi hakane don kare lafiyar kaina da taku iyalina saboda indomie na ɗaya daga cikin abincin da a shekarun baya yake kwantar da ni a asibiti, wanda sai daga baya aka gane na kuma haramta cin shi a gidan.”

“Dama ka saba cin junks ɗinka shine zaka ƙalawa indomie, kuma ai kai ne baka da lafiyan ba mu ba. Ni babu abun da indomie yake mini.” Ta faɗa ciki tsiwa domin maganganunshi sun ɓata mata rai matuƙa.

“To koma menene na hana cin shi daga yau kema kar ki sake saya.”

“Wannan kuma ba huruminka bane saboda ba Kare ko Alade na ce zan ci ba balle ka ce Musulunci ya hana.”

“With that your mindset kika kasa zaman lafiya da kowa kuma zan ƙara nanata miki, daga yau kika ƙara sayan indomie kika kawo gidana ki san inda zaki yi tunda ke rarrashi ko bada baki baya aiki a kanki.”

“Me kake nufi kenan? Sakina zaka yi akan na sayi indomie?” Tayi maganar cike da tsoro da kuma kasa gaskata me kunnenta ya jiyo mata.

“Ki gwada zaki ga me zan yi. Kuma ban amince ki fita ko’ina ba.” Yana faɗin haka ya kashe wayarshi ya bar Juwairiyya da tsantsan mamaki wanda sai daga baya ta ji ashe wai hawaye ne ke sauƙa akan fuskarta.

“Ni za’a saka akan na sayi Indomie?” Tayi tambayar tana nuna kanta da yatsa.

Ashe labarun da ake faɗa na an saki mata akan ridiculous abubuwa kamar su cokali ko ruwa a buta ba ƙarya bane gaskiya ne! Yau gata nan Juwairiyya mai ilimi da wayewa ce ake ƙoƙarin danƙara mata nata wai in har ta sayi indomie, fucking indomie!

Yau sai dai duk abun da zai faru ya faru, shiga ɗaki tayi ta ɗauko hijabinta a zuciye wai zata fita wanda har ta ɗaga ƙafarta ɗaya zata fitar waje sai kuma ta ja tunga ta tsaya. Idan an saketa gida zata koma wanda zaman gidan Muhammad ya fi mata daɗi sau dubu akan gidan Mama wanda makarantar da take yi guda za’a hanata ba wai iya cin indomie ba. Tana da freedom a gidan Muhammad fiye da yanda take dashi a gidan Mama, ta aureshi ne don ta ƙarisa makarantarta don haka in ta biyewa zuciya zata ɓata plan ɗin rayuwarta ne gabaɗaya. Zuciyarta na ƙuna ta koma tana jin kamar ta fasa ihu ko kuma ta tafi UK yanzu ta samu Muhammad ta mishi kaca-kaca.

Da wannan tunanin da ɗauki wayarta ta kirashi ya ɗauka bayan ta kusa tsinkewa ya ce,

“Menene kuma?”

“Ka ci sa’a ka hanani cin indomie amma wallahi…” Bata kai ga ƙarisa maganar ba ya kashe ta ciro wayar daga kunnenta tana kallonta da tsantsan mamaki.

Kiranshi ta sake yi a karo na biyu amma aka ce mata wayar is not reachable kenan blocking ɗinta yayi ko ya saka wayar a flight mode. Ranta na ƙuna ta shiga whatsapp ta nemo numbershi da kyar tunda ba hira take yi da shi a nan ba, missed video calls ɗin da yake kiranta take ƙin ɗauka ne ta fara cin karo da su waɗanda sun kai huɗu. A nan ta fara mishi typing me zafi tana faɗa mishi baƙaƙen maganganu wanda a ciki take ce mishi

 ‘an faɗa maka kowa irin lukutin jikinka yake da shi ne mai riƙe fats da zaka wani hanamu cin indomie? Kuma in banda baƙar zuciya kai an san me kake ci a can ne da mu zaka kafa mana doka akan abinci? Wannan ƙauyenci ne da kuma gidadanci! You have no right ka hanamu cin abun da muke so, kuma don ka hanani kawowa cikin gidanka baka isa ka hanani saya a school ko kuma ka hanani ci idan na je unguwa ba.’

Maganganu marasa daɗi ta cika page har biyu ta tura mishi sannan ta tsaya tana duba ko ya karanta, har ta gaji da jira ta ajiye wayar saboda bai hau online ba, can ta haƙura ta samu guri ta zauna zuciyarta na azalzalarta. Muhammad wawa ne kuma mugu ne! Tsabar ɓacin rai kasa komai tayi kawai ta zauna tana duba wayarta akai akai ko ya karanta, sai can goshin maghrib ta ga two blue lines alamar an karanta amma minti goma da haka ta ga bai mata reply ba ƙarshe ma sauƙa yayi ta daina ganinshi online.

Wannan abu da ya faru ya jawo tangarɗa a relationship ɗin Muhammad da Juwairiyya wacce ta daina kiranshi kwata kwata shima ya daina kiranta wanda yau wata ɗaya kenan da faruwar abun basu sake waya ko exchanging text ba. Sai dai in tana buƙatar fita ta faɗawa Salima ta tambaya mata wani lokaci ya bata izini wani lokaci kuma ya hana. Indomie kuwa bata fasa ci ba tana saya a school ta ci amma bata sake shigowa dashi cikin gidanshi ba saboda ta sani muddin Salima ta gani zata faɗa mishi. Don ta lura kamar in ya tambayeta abu da ya shafesu bata iya mishi ƙarya ko da kuwa hakan itama zai jawo mata faɗa, yanzu ta fara kaffa kaffa da ita bata yin abu a gabanta wanda in Muhammad ya ji zai mata faɗa.

Abunda Juwairiyya bata sani ba shine tun ranar da suka yi faɗa da Nanayo tana komawa ɗakinta ita kuma Salima ta kira Muhammad a take a lokacin ta bashi labarin abun da ya faru ta ƙarisa da cewa,

“To dama ta mana aikin sati biyu shiyasa ma na faɗa maka saboda a bata rabin albashin nata.”

Muhammad da zuciyarshi ke zafi akan rashin haƙurin Juwairiyya ya ce zai tura mata kuɗi ta bata. Ita kam Juwairiyya da waye ne ba zata yi faɗa ba? Yarinya sai kace ƴar sarkin ƴaki? Tun Salima tana amarya take tare da Nanayo wanda a yanzu shekararsu kusan huɗu kenan bai taɓa jin Salima ta kawo ƙararta ko ta ce ga abun da Nanayon ta mata na rashin daɗi ba. Sai zuwan Juwairiyya ce kawai yarinyar zata ce ta bar aiki? Wani irin masifa da baƙin hali take mata? Ko da yake idan ya tuna yanda shima take mishi sai ya ga kowa ma ba zata bari ba.

Ita ce gaba da makwabta wanda ko yaransu bata aika haka kuma bata shiga gidajensu. Ita ce ta faɗawa danginshi magana mara daɗi wanda shi bai san maganar ba har yau amma sun ce mishi basu ji daɗinshi ba, hakan kuwa yasa suka ja baya da ita itama ta ja baya da su, Iyami ƙanwarshi wacce kusan halinsu iri ɗaya ne kaɗai suke mutunci kuma bata ganin laifinta. Ita ce ƙin fitowa su gaisa da yayanshi a wata rana da ya kawo musu ziyara amma daga ranar bata sake yi ba. Yana cikin wannan ɓacin ran ne Juwairiyyan ta kirashi ya nuna mata kamar bai san komai ba daga baya kuma ya buɗe mata wuta suka yi baram-baram.

Ta gefen Salima kuwa haƙanta ne ya cimma ruwa domin ta alama abubuwa zasu tafi yanda take so, a yanzu tayi ƙoƙarin ganin Juwairiyya da Muhammad sun yi faɗa wanda shi bai faɗa mata ba amma da ta nemi sani a gurin sokuwar sai ta zayyane mata komai da yake abun na cinta a rai ta rasa wa zata faɗawa ya bi bayanta. Haƙuri ta bata sannan ta bata shawarar wai ta kirashi ta bashi haƙuri ko ta mishi text wanda hakan ya ƙara tunzura Juwairiyyar tace Allah ya kasheta ba zata yi ba. To yanzu kuma matan unguwa sun ƙara tsanarta domin ta faɗa musu cewa yanzu bata da mai aiki kuma tana tsoron ɗaukar wata itama ta zo su kasa daidaitawa da amaryar tata. Ta gurin Nanayo kuwa har gidansu ta je ta bawa mamanta haƙuri kamar ba ita ce take sa Nanayon tana yiwa Juwairiyya laifuffukan ba, ƙarshe ta musu alƙawarin cigaba da bawa Nanayo kuɗin duk wata ko da bata musu aiki wai saboda tana tausayinsu albashin na taimaka musu ba zata bari su koma gidan jiya ba. Wannan ƙoƙari da tayi yasa makwabta suka ƙara ganin girmanta sannan suka ƙara tsanan Juwairiyya wanda a yanzu da gangan mace zata shigo gidan ta dinga habaici amma Juwairiyya bata isa tayi magana ba sai dai ta shige ɗaki ta barsu Saliman na cewa bata so tana hanasu wai kar su jawo mata laifi gurin Muhammad.

Abun da basu sani ba shine Juwairiyya bata ko waya da Muhammad ɗin balle ta kai ƙararsu kuma ko ta kai ɗin ma ba lallai bane ya ɗauki mataki ba tunda last time ma da hakan ya faru babu abun da yayi. (Please in kina irin wannan halin ki daina, don duk inda munafuki yake wallahi akwai ranar jin kunyarshi ko ba jima ko ba daɗe).

Juwairiyya ta fara First semester exams na aji biyu amma saboda halin da take ciki ta kasa maida hankalinta akai. Duk mutanen da take rayuwa dasu sun juya mata baya kama daga makwabta, ƴan’uwan Muhammad da kuma shi kanshi maigidan da har ta manta yaushe rabon da su yi waya. Wani abun takaici shine yanzu ya hanata zuwa ko’ina, ko ta aika Salima ta tambaya mata zuwa unguwa sai tace mata ya hana. School kaɗai da take zuwa take samun sassauci shima kuma gashi gobe zata gama exams ɗin su dawo zaman gida.

A da tayi rantsuwar ba zata sake tambayarshi zuwa wani guri ba amma ba zata iya ba tana son ganin mamanta wacce yau satinsu uku basu ga juna ba, Surayya ma mijinta ba mai son yawan fita bane don sai tayi wata ma bai bari ta zo gurinta ba.

“Maman Masoyi kira mini wannan Rock ɗin kice mishi ina son zuwa gidan Mama gobe idan na yi last paper.”

“To shikenan.” Faɗin Salima jikinta na rawa ta ɗauki waya ta kira Muhammad ta saka a handsfree.

“Kin san a irin wannan lokacin ina class me yasa zaki kirani?”

“Kayi haƙuri amma amaryarka ce tace in kiraka tana son zuwa gidansu gobe idan tayi last paper.”

“Ba zata je ba. Ta fara gane darajar mutane sannan zan barta ta cigaba da shiga cikinsu.” Yana faɗin hakan ya kashe wayarshi.

Juwairiyya zuciya na zafi ta ɗauko ashar ta danna ta riƙe kunkuminta ta fara girgiza tsabar masifa.

“Har ni zai killace a gida kamar dabba wai sai na fara sanin darajar mutane kafin ya barni in shiga cikinsu? An faɗa mishi uwata irinshi ce mai baƙar zuciya da zata ƙi ni? To wallahi sai na je, bai isa ya rabani da uwata ba tunda a gabanta ya je ya auroni.” Itama tana ƙarisa faɗan hakan ta fice daga ɗakin ta nufi tata.

Salima jiki na zikiri ta turawa Muhammad text,

“Tace fa zata je ko baka bata izini ba, don Allah ka mata magana nikam bana son zama a tsakiyarku kuna irin wannan abun. It hurts my heart.”

Muhammad yana class ya ga text ɗin wanda nan da nan sauran annunrin fuskar tashi ta ɗauke ya nemo number Juwairiyya ya tura mata text,

  ‘Daga yau kika fita zuwa unguwa ba tare da izinina ba a bakin aurenki. Na san kin yi karatu kina da ilimin da bakya amfani dashi, amma kuma kin san girman saki kin kuma san hukunce-hukuncensa.’

Yana rubutawa ya kashe wayarshi zuciyarshi na ƙuna ya bada hankalinshi kan lecture da ake musu amma ya daina fahimtar me ake cewa. Shi kam ya zai yi da yarinyar nan ne? Ya ɗauka in sun yi nisa ba zasu dinga faɗa ba ashe ƙarya ne sai ta nemi duk hanyar da zata yi su yi faɗan.

Juwairiyya tana kaiwa da kawowa a falonta ta ji ƙarar shigowar saƙo ta duba ta gani ai kuwa ta sake hawa tana ta masifa ita ɗaya, a haka Salima ta zo ta sameta take tambayarta me ya faru ta nuna mata saƙon.

“Kai shi kuma ai ba’a faɗawa mace haka, mu mata ba hankali ne da mu ba shi yasa malamai suka ce a daina mana irin haka.”

“To kuwa zai ga rashin hankali, zuwa ne sai na je bai isa ya rabani da uwata ba.”

“Ke dai kiyi haƙuri don kin san saki ba ƙaramin abu bane, yanzu idan kika je automatically kin saku kenan fa ko bai furta ba. Kuma kin ga ana lallaɓa rayuwa bai kamata ku rabu ba.”

“Ai idan na rabu dashi har sadaka sai nayi, in ba ƙaddara ba me zai sa in auri mutum mai mugun hali irinshi?”

Nan dai Salima tayi ta bata haƙuri wanda yake ɗauke da tunzurawa, hakan yasa har ta koma ɗakinta Juwairiyya bata ji sanyi a ranta ba sai ma bushewar da zuciya ta ƙara yi, a nan kuma ta yankewa kanta hukuncin rabuwa da Muhammad ta hanyar da ya bata zaɓi don ta nuna mishi ba wai tana zaune da shi don tana sonshi bane, sannan kuma tana son nuna mishi bata tsoron rabuwa da shi, kuma bata tsoron halin da zata faɗa in ta kashe auren nata.

Mum Fateey 👌

“Idrisa yau gidanmu zaka wuce dani.” Juwairiyya ta bawa mai Napep ɗin nata umurni bayan ta fito daga last exams ɗinta na first semester.

“To Hajiya.” Shine abun da ya faɗa kana ya jasu suka tafi.

Tunda Juwairiyya ta fara maganar ta kasa samun sukuni, ji tayi kamar numfashinta zai ɗauke ta gyara zaman hijabinta da take tunanin shi ya matse mata wuya. Zuciyarta ce ta tsananta bugawa da Idrisa ya ɗauki titin da zai sadashi da Arawa wanda a cikin minti biyar zasu iya isa har ƙofar gidan Mamanta.

“Mu koma gida na fasa, na tuna ashe yanzu ba za’a sameta ba tana Office.”

“To Hajiya.” Da haka Idrisa ya juya dasu suka kama hanyar gidan aurenta.

Wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe, nan take kuma ta ji numfashinta ya daidaita tana yinshi yanda ya dace. Me ribarta idan ta kashe auren rufin asirin a kan zuwa unguwa? Unguwar ma zuwa gidan Mamanta wacce a yau ta ji labarin wai an saketa ne akan fita ba da izinin miji ba sai ta tabbatar tayi regretting hakan. Don me yasa zata biyewa zuciya da kuma saurin fushi? Ta lura yanzu Muhammad ya samu abun da zai dinga tsoritata da shi amma ba zata bari ya wargaza mata plan ba, bata fara don ta bari ba, wannan wani Mantra ne da take faɗawa kanta don tayi focusing kan goal ɗinta ba tare da ta bari ɓacin rai ya lalata mata shi ba. Tana isa gida ta samu Salima a tsakar gida tana kaiwa da kawowa wacce yau ma da safe sai da ta bata haƙuri wai kar ta aikata abun da tace zata yi.

“Juwairiyya kin je gidan naku?” Ta tambayeta fuskarta ɗauke da expectation.

“Ban je ba kuma wallahi don ke ce da kike ta bani baki, kar dai ki ce bana ɗaukan shawarwarinki duk da cewa ana zaman tare.”

“Ohh, to yayi kyau.” Ta faɗa ciki  karaya da kuma baƙin ciki wanda wannan karon ta kasa ɓoyewa a fuskarta.

“Lafiya kam? Na ga kamar ranki ya ɓaci.” Juwairiyya ta tambaya tana nazarinta.

“Nima ɗazu nayi laifi, daga tambayar zan je gidanmu yayi ta faɗa wai fitanmu yayi yawa shi baya son yawo mu killace kanmu a gida.” Ta yi saurin shirga ƙarya don kar a ganeta.

“Mutumin nan daddawa yake son mu zama, ai gashi nan kema mai kareshin bai barki ba. Allah Ya haɗamu da masifa sai addu’a, bari in shiga in kwanta don yanzu ji na nake yi sakayau babu fargaban exams. Ina Masoyina yake?”

“Nanayo ta zo ta ɗaukeshi sun tafi gidansu. Ni kam dai nace kiyi haƙuri ta dawo mana aiki.”

“Ni na koreta ne da sai na yi haƙuri ta dawo? Ita ta kori kanta kuma na faɗa miki in kina so ta dawo ku ci gaba da aikinku kamar da amma nikam bana so na yafe.”

“Shikenan tunda kin kafe akan haka, in ta dawo dashi zan mata magana ta dawo.”

Da haka suka watse kowacce ta shige ɗakinta, Juwairiyya kwanciya tayi don huce gajiya yayin da ita kuma Salima tsabar takaicin da take ji a ranta sai da ta zubar da kwalla. Wannan shi ake kiran ga samu ga kwanan yunwa, a yanda ta rabu da Juwairiyya yau da safe sai da ta tabbatar da fomfata sosai ta yanda zuciyarta ta bushe sai ta aikata abun da Muhammad ya kafa mata sharaɗi a kai. Amma da yake tana da tsoro sai ta kasa aikatawa wai ta ji shawarwarinta! Ƙarya take yi ba wani shawaranta da ta ɗauka tsoro ne kawai ya hanata domin bata son kashe auren ta koma rayuwar zawarci. Rai na ƙuna Salima ta shige ƙuryan ɗakinta ta kira mamanta.

“Ta saku?”

“Ta ji tsoro ta ƙi zuwa Mama.”

“Kash! Amma yarinyar nan tana bamu wahala. Kar ki damu, a dai juri zuwa rafi watarana sai tulu ya fashe. Zan kiraki anjima akwai abun da zan ɗauraki a kai.”

A ranar kuwa da yamma Muhammad ya kira Idrisa suka yi lissafi zai bashi kuɗinshi, a nan ya tambayeshi ko sun bi wani guri duk da cewa ya aika wani unguwarsu ya tsaya ya duba mishi ko ta je.

“A’a bamu bi ko’ina ba, da dai tace mu je gidansu har mun kama hanya tace ta fasa na maida ita gida.”

“To yayi kyau. Zan tura maka kuɗin yanzu, sai kuma an koma school zan sa ta kiraka ka ci gaba da kaita. Nagode Idrisa.”

“Ni ma nagode Yallaɓoi.”

Tunda Juwairiyya ta shiga gida bayan gama exams ɗinta bata sake fita ba har aka kusa komawa school, tana son zuwa ganin Mama amma tsabar taurin kai da zuciya ta kasa tambayar Muhammad ko da kuwa ta hanyar Salima ce.

Zaman da tayi a gida kuwa babu walwala babu mai tayata hira yasa ta fara shiga damuwa domin a yanzu Salima ma bata zuwa ɗakinta kamar da. Ganin haka yasa ita ta fara zuwa amma idan ta je sai Salima ta tsibiri aiki ƙarshe haka zasu watse. Da Juwairiyya ta ga abun ya fara yawa sai itama ta daina shiga ta killace kanta a ɗaki ya zama ko cikin gidan bata fitowa sai in zata yi girki, kayan abinci kuwa za ta karbi duk abun da zata buƙata na kwana biyun saboda bata son sintirinta yayi yawa. A wannan matakin ne Juwairiyya ta fara shiga depression wanda kullum babu abun da take yi sai tunane-tunanen banza da wofi wanda suke ƙara sakata a cikin damuwa. Da ta ga damuwan ya mata yawa sai ta yiwa Muhammad text bayan uban lokacin da ta ɗauka bata yi hakan ba ta tambayeshi wai zata je ziyara, shima text ya mayar mata akan cewa ba zata fita ba sai an koma hutun school. Tun daga lokacin shima ta watsar da kashinshi ya zamana ita kaɗai ɗinta take rayuwa sai in ta ci sa’a tayi baƙi daga ƴan’uwanta ko abokan arziƙi.

Hutun wata ɗaya suka yi wanda tsabar ɗoki a ranar da aka koma school ta nemi izinin Muhammad ta text ya barta duk da cewa basu da lectures kuwa. Ko minti talatin bata yi a cikin school ɗin ba ta fito ta nufi gidan Mama, a can ta samu ta tafi aiki Sumayya kaɗai ta samu da wata ƴar ƙanwar kakarsu da Mama ta ɗauko wai zata tayata zama, yarinya ce yar shekara goma sha ɗaya. Tana hira da Sumayya Mama ta dawo Juwairiyya ta zauna tare da ita suna hira, a nan ta kasa haƙuri ta fara sako hiran zaman gidanta saboda ta gaji! Tana cikin damuwa kuma tana neman ta samu wanda zata faɗawa zuciyarta tayi sanyi tunda Salima abokiyar shawarar tata ta gujeta. Tana neman support da kuma shawara don daidata rayuwarta da ta kasa controlling.

Mama shiru tayi tana kallon Juwairiyya wacce ke bata labarin zaman gidan nata idanunta cike da hawaye.

“Ki fara mini daga farko, a nan zan san komai in baki shawarar da ta dace.” Cewar Mama calmly tana danne ainihin ɓacin ran da ke cikin zuciyarta don ta samu Juwairiyya ta faɗa mata komai ba tare da ta rage wani abun ba.

Juwairiyya ɗaga kanta tayi tana kallon fuskar Mama wacce rashin fushinta ya bata mamaki, shiyasa da ta ga kamar ran Maman bai ɓaci ba kuma da alama zata bi bayanta sai ta buɗe baki ta faɗa mata amma tana rage wasu rashin mutuncin da ta yiwa Muhammad, don ta sani a nan kam Mama ba zata taɓa bata gaskiya ba kuma sai ta gwammace kiɗa da karatu.

“Mama yanzu maganar da nake miki kulleni yayi a gida ba wai ni ce bana son fitan ba kamar yanda na faɗa miki. Wallahi ni kaɗai nake rayuwata a gidan ko ƴan’uwanshi sun zo dubamu gaisuwa kawai zasu mini su tafi ɗakinta su yita hira ina jinsu har lokacin tafiyarsu tayi sai su zo su mini sallama. Mama makwabta ma bama jituwa, kuma na faɗa miki ba laifina bane domin tun ina Amarya da suka shigo suka dinga mini habaice-habaice na rama shikenan aka watse a haka. Mama Muhammad baya kirana, baya ko mini text, ban san me yake faruwa a cikin rayuwarshi ba haka shima bai damu ya san nawa ba. Na rasa yaya zan yi wallahi watarana sai in ji kamar in gudu ma kowa ya huta.”

Wannan maganar ta ƙarshe ita tayi sanadiyyar fashewar Mama wacce dama tun da Juwairiyya ta fara bada labarin take ta kumbura kamar burodi. Faɗa take yi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, domin abun da ya ƙara baƙanta mata rai shine bayan rashin kunyar ƴar tata a maimakon ta faɗa mata halin da take ciki tun kafin abun ya ɓaci haka su yi saurin taroshi amma sai ta kame bakinta ta wargaza komai. Sai ta ta gama zageta tass sannan ta sauƙo ta fara mata magana mai kama da rarrashi da nasiha.

“Da dai ba haka kike ba Juwairiyya, wallahi da ba haka kike ba. Tun da kika yi auren fari na lura kin koyi zuciya bakya kunyar yin masifa a gaban mutane da nuna ɓacin ranki idan an miki laifi. Na rasa gane ko don bana tare da ke ne kike haka ko kuma ƙawaye ke zugaki ashe ke da kanki kike zuga kanki. Yanzu wa gari ya waya? Mutane rahama ne ke kuma baki iya zama da su ba shiyasa kike shan wahala yanzu saboda sun gujeki. Ke je ki zauna kiyi tunani; haka kika ga sauran mutane suke rayuwarsu irin taki? Haka kowa yake mu’amala da mutane babu haƙuri babu kawaici babu dabara? Babban abun kuwa shine haka addini ya koyar da mu? Annabi yayi magana akan haƙuri wanda rayuwarshi kaɗai ma misali ce a garemu. Ya mana warning akan harshenmu wacce in ka biye mata sai ta kaika ga halaka. Ya koyar da mu yanda zamu zauna da mutane cikin aminci, haƙuri, yafiya, kawaici da kuma kyautatawa. Shin ke kina duka waɗannan Juwairiyya? Kina haƙuri idan an miki ba daidai ba? Kina kawar da kai in an ɓata miki? Kina yafiya idan laifi ya wuce? Ko kuma kina mayar da sharri da alkhairi ko kyautatawa? Ki koma gidanki ki yiwa kanki karatun ta nitsu, ki duba duk mutanen da kika sani waye ne mara haƙuri kuma ya ci riba ko kuma ya ji daɗin rayuwarshi? Juwairiyya dole ne a miki ba daidai ba, dole ne a miki abun da zai ɓata miki ko da kuwa shi wanda ya miki hakan ba zai so a mishi kwatankwacinshi ba amma idan kin yi haƙuri kin kawar da kai sai ki ga ke ce da riba a gaba. Sannan ki yawaita addu’a Allah Ya sanyaya miki zuciya Ya baki ilimin da haƙurin zama da mutane, Ya kuma daidaita tsakaninki da mijinki, ki yawaita addu’a da tashin dare in Allah Ya yarda zaki ga canji a rayuwarki.”

Sosai Mama ta yiwa Juwairiyya faɗa mai shiga jiki ta koma gidanta da niyyar gyarawa amma sai dai tana tsoro game da taraddadin yaya zata gyara mu’amalarta da mutanen da tun a baya ta ɓata kuma ba laifinta bane? Ita gaskiya ba zata iya cusa kanta ba saboda bata son su wulaƙantata! Ta zama doormat kowa ya zo ya takata ya wuce ba ya daga cikin abun da zata iya ɗauka ko da kuwa tana son canja musu zamantakewar. Yanzu ta yaya zata fara musamman makwabatansu da wasu dangin Muhammad ɗin da kamar tun farko ma ba laifi ta musu ba haka kawai suka ɗauki karan tsana suka dasa mata? To ya kuma zata yi da Muhammad? Mutumin da ya ɗaga mata white flag don neman sulhu su yi zaman lafiya amma ta ƙi a tunaninta don yana son jikinta ne yayi hakan? Ta yaya zata fara?

Da yake da yamma ta dawo sai ta bari aka yi sallah isha sannan ta shiga gurin Salima wacce itama tayi baya da ita, to wai me suke gani a jikinta ne da suke ƙin mu’amala da ita? Sannan duk ba sa ganin ita ke da gaskiya bata cutan kowa kawai ita bata son a wulaƙantata ne? Why her? Me yasa ba za’a yi zaman lafiya tun farko kowa ya mutunta ɗan’uwanshi kuma ya guji ɓata mishi ba?

“Amarya ke ce?” Faɗin Salima tana bawa HJ abinci a baki.

“Ni ce dai, nace bari in zo da kaina in ji laifin da nayi yasa kika daina zuwa gurina kuma ko ni na zo bama hira kamar da.” Juwairiyya ta samu guri ta zauna da murmushi a fuskarta.

“A’a ni kam babu laifin da kika mini, kawai dai ke kike ganin haka amma ai ina shigowa.”

“Mu dai faɗi gaskiya amma baƙya shigowa sai in abinci kika kawo mini ko kuma mun yi baƙi kin rakosu gurina.”

“To kar mu yi ta musu, zan cigaba da shigowa tunda dama kin ce ina yi ne na daina. Dama ina ta son faɗa miki ana nema mini aiki wai in ji Baban Hafiz zaman kaɗaicin zai mini yawa sannan Babana ya saya mini mota next week zan fara driving lessons. Masoyinki kuma ya girma an saya mishi form zai shiga school next term.”

“Shine duk abubuwan nan baki faɗa mini ba sai yanzu? Zan ƙara tambayarki don Allah laifi na miki?” Wannan karon tayi maganar with hurt in her voice.

“A’a laifi kuma? Ni fa na faɗa miki babu abun da kika mini.” Salima ta bata amsa tana murmusawa wanda Juwairiyya tana ganinshi ta gane forcing ɗin shi take yi. To me ya shiga tsakaninsu ne ta canja mata?

“To shikenan tunda kin ce haka. Na tayaki murnar mota Allah Ya sanya alkhairi, aiki kuma da kike nema Allah Ya sa ki samu. Masoyi kuma Allah Ya sa ya fara karatun a sa’a.”

“Ameen mun gode.” Salima ta amsa tana miƙewa ta ɗauki kwanon abincin ta kai kitchen HJ ya bita da gudu da Juwairiyya ta mishi magana wai ya zo su gaisa.

Sai da Salima ta jima a kitchen ɗin sannan ta dawo kafin nan Juwairiyya ta cika tayi famm, shi yasa Saliman tana zama ita kuma ta miƙe ta mata sallama ta koma ɗakinta zuciyarta na tafarfasa. In ma wani abu zata yi a kitchen ɗin ta faɗa mata mana, sai ta ce ‘wance bari in yi aiki a ciki kar ki ji ni shiru’ amma kawai ta tashi tayi shigewarta kamar wacce ta zo roƙo gurinta. Kuma duk abubuwan alkhairin da ya sameta ta ɓoye mata sai da yanzu da ta taka ta je gurinta ne zata faɗa mata? To uban me ma ta mata da zata fara treating ɗinta haka? Me yasa take samun matsala a mu’amalarta da mutane alhali ita da zuciya ɗaya take zaune da su?

Sai da ta bari zuciyarta tayi sanyi sannan ta ɗauki waya ta kira Muhammad wanda rabon ta yi haka har ta manta. Ta sani wataƙila yanzu yana bacci amma dai ta danna call ɗin wanda har ya gama ringing ba’a ɗauka ba, kira ta sake yi a karo na biyu nan ma ba’a ɗauka ba. A zuciye ta wurgar da wayar tata gefe tana huci ranta na ƙara ɓaci wanda ita kanta har mamakin kanta take yi.

“Mutane babu abun da kuka iya sai wulaƙanci da ɗan banzan girman kai. Ba zan bibiyeku kuna wulaƙantani ba wallahi! Na fasa.”

Tana faɗin hakan ta ɗauko wayar ta ta jefar ta fara yiwa Muhammad text kamar haka.

‘Assalamu alaikum ya karatu? Na ce don Allah batun kayan abinci ka raba mana ka bani nawa, kuɗin cefene ma ka dinga bani a hannuna, sai kuma in zai yiwu ka raba mana girki kowacce ta dinga yin nata. Nagode.’

Tana gama rubuta text ɗin ta tura mishi wanda ta sani shi kam dole zai gani kuma dole zai bata amsa, abun da bata sani ba shine Muhammad yana bacci ta kirashi ya farka, amma da ya ga ita ce sai da zuciyarshi ta tsinke don yana da tabbacin masifarta ce ta tashi ko kuma bata da lafiya. In masifa ce ba zai iya ji yanzu ba saboda zata iya hanashi ƙarisa baccinshi, in kuma rashin lafiya ne ba shi ya kamata ta fara kira ba, ƴar’uwarta da suke zaune gida ɗaya ya kamata ta nema wanda a yanzu ya samu labarin wai ta daina shiga harkarta itama ma.

Yana wannan tunanin ne ya yanke shawarar kiran Salima akan ta je ta dubata sai kawai ya ga text ɗinta. Girgiza kai kawai yayi ya karanta sau uku yana son sanin me ya faru da har ta nemi hakan. Da haka ya danna kiran Salima wacce take jiran rana irin ta yau don wani tarkonta ya kama Juwairiyya.

Mum Fateey 👌

Salima tana kwance a ɗakinta Muhammad ya kirata tayi saurin ɗauka domin ɗazu suka gama waya, ko me ya faru ya kirata yanzu?

“Assalamu alaikum Baban Hafiz, ina wuni?”

“Wa’alaiku mussalam. Me ya haɗaki da ƴar’uwarki?” Ya tambayeta kai tsaye don ya matsu ya ji me yake faruwa da iyalin nashi.

“Subhanallahi, wallahi ni babu abun da ya faru tsakaninmu. Wani abu tace na mata?”

Shiru Muhammad yayi yana nazari sai can ya ce,

“To me ya faru take son a raba muku kayan abinci da kuma girki?”

“To gaskiya sai dai ka tambayeta amma ko ɗazu ta shigo muka yi hira kaɗan har tana tambayata wai me yasa kwana biyu bana shiga mata, dama kuma ni ce mai shiga gurin nata, to da na ga kamar ina takurata sai na rage shiga. Amma tunda hakan take so a yi mu samu zaman lafiya don ni shine burina.”

“Shikenan.”

Yana faɗin haka ya kashe wayarshi ya kira Juwairiyya wacce take kwance amma ta kasa bacci tana ta tunane-tunane. Tana ganin kiran tayi saurin ɗauka ta ce,

“Hello.”

“Me yasa kike son a raba muku girki kowa ya dinga yin nashi?”

“Saboda na lura matarka bata son shiga harkata.”

“Kamar yaya? Me ya faru?”

Shiru Juwairiyya tayi domin sai ta ma rasa me zata ce, don excuses ɗinta nata idan ta furtasu basu kai dalilin da zai sa har a raba girki ba.

“Ta daina shigowa gurina sannan nima idan na shiga sai ta kama wasu ayyuka ta barni ni kaɗai, haka yau da na je tayi shigewarta kitchen ko magana bata mini ba. Sai da ta jima a ciki ta fito.”

“Shine dalilin da yasa kika kirani da tsakar daren nan?” Ya tambayeta cike da mamaki wanda sai daga baya ya daina mamakin da ya tuno wacece ita.

“A’a, dama zamu gaisa ne.”

“Juwairiyya kenan.”

“Ai dama na sani ba lallai ka yarda da maganata ba.” Tayi maganar tana jin zafi a ranta, ita aka yiwa laifi ta kuma faɗi laifin amma sai kamar bai yarda da ita ba ko kuma bai ɗauki hakan a matsayin komai ba.

“Ni ban ce ban yarda da maganarki ba, maganar raba girki da abinci da kike so za’a miki tunda haka kike so. In an miki hakan za’a zauna lafiya ko?” Muhammad ya tambayeta kamar mai magana da yaro ɗan shekara goma.

A yanzu da yake nesa babu abun da ya fi so irin ya ga iyalanshi da suke zaune guri ɗaya sun zauna lafiya ba’a jin kansu. Domin kuwa idan suka ƙi zaman lafiya shi da baya tare da su sai ya fi shiga tashin hankali domin su ɗin amananshi ne kuma abun karewarshi. Da yana gida tare da su ne ba zai yarda a raba girkin ba sai dai zai bawa Juwairiyya kayan amfaninta kamar yanda ya mata alƙawari tun farko bai cika ba. A yanzu ya lura kamar neman faɗa take yi wanda ba zai bata wannan daman ba saboda in ita bata da hankali shi yana dashi.

“Ya kake mini magana kamar irin neman masifan nan nake yi kana wani rarrashina.” Tayi maganar tana jin zuciyarta na cigaba da suya, wai ko bai ji me ta faɗa bane?

“Ko ɗaya.” Yayi ƙarya. “Gobe zan sa ta raba komai gida biyu ta kawo miki naki. Idan kuma wata ta cika ni zan dinga aiko miki kuɗin groceries ɗinki da kaina. Sai da safe.” Yana faɗin haka ya datse kiran ya bar Juwairiyya da mamaki a ranta game da takaici.

Ko da yake ba sonta yake yi ba, don me yasa zai yarda da maganarta akan perfect matarshi wacce take bautawa ƙasar da yake takawa? Rai babu daɗi amma haka ta koma ta kwanta sai dai bacci ya ƙauracewa idanunta.

Washe gari bata jira ta karɓi breakfast ɗinta ba ta fice zuwa school wanda yau ɗin ma lecture ɗaya take dashi amma tana son fita ta bar gidan, tana son kuma zama a makarantar bata son komawa saboda gidan baya mata daɗi, in ta shiga sai ta ji duk ranta ya ɓaci saboda wacce take zaune da itan bata jin daɗin zama da ita, balle uwa uba shi wanda take zaman nashi bai ma damu da ita ba. 

Tana dawowa kuwa ta samu kayan abinci tuli jibgi a bakin kofar kitchen ɗinta wanda a maimakon hakan ya mata daɗi sai ya ɓata mata rai, wato ita za’a yiwa tafi ga tsiyarka? Hakan yasa ta je bakin ƙofar Salima ta kwankwasa Salima ta buɗe tana cewa,

“Ha’a kin dawo ne?”

“Na dawo, amma don Allah me yasa kika je kika jibge mini kayan a bakin kitchen ɗina? Da sai ki bari idan na dawo ki kirani in ɗauka ko kuma ki kawo mini. Gaskiya ban ji daɗin hakan ba, wato irin gashi can matsiyaciya ko?”

“To kiyi haƙuri, ai ban san hakan zai ɓata miki rai ba.”

“Ke ma da kika tsaya kina bata haƙuri ke ce abun haushi wallahi Maman Hafiz. Ni har kishiya zata zo ta titsiyeni tana mini faɗa kamar ita ta haifeni ko ita ta ajiyeni? Wallahi bata isa ba! An ajiye a bakin ƙofar kiyi abun da zaki yi.” Wannan faɗin Maman Hanan kenan makwabciya kuma aminiyar Salima tana mai fitowa daga cikin falon ta tarar da su a waje.

“Malama ba da ke nake yi ba, kuma zan so ki ja tsummar bakinki ki fita a harkan gidanmu saboda mun fi kusa zaman mutum ɗaya muke. Ke fa? Just mere makwabciya wacce bata son ta ga ana zaman lafiya. Abun naki ya fara yawa fa, nan gidana ne baki isa ki shigo ciki kina yaɓa mini magana ina barinki ba. Wallahi kin yi ƙarya.”

“Don Allah Maman Hannan kiyi shiru kar ki ce komai. Ya wuce ai.”  Wannan maganan Salima kenan tana riƙe hannun Maman Hanan wai zata shigar da ita cikin falon.

Hakan da tayi kuwa ba ƙaramin daskarar da Juwairiyya yayi ba, ji tayi kamar an ɗebi ruwan sanyi an watsa mata. Kenan maganar da tayi ya ɓatawa Saliman rai? To me yasa bata faɗa mata ba? Kai ranta ma bai ɓaci ba! To amma me yasa ba zata faɗawa Maman Hanan cewa ranta bai ɓaci ba kawai magana suke yi tsakaninsu?

“Salima sai ki faɗa mata cewa ba wai titsiyeki na zo yi ba haka kuma maganar da nayi bai ɓata miki rai ba, saboda kar ta ɗauki wrong signal ta zauna akan abun da take tsammani.” Wannan karon Juwairiyya tayi maganar a sanyaye tana kallon Salima wacce take sunkuye da kanta ƙasa kamar zata yi kuka.

“Ni na ce wani abu ne? Cewa nayi ai a bar maganar ya isa haka.”

“Ke kika nuna kina tsoronta shi yasa take miki haka. Ya za’a yi ki zo har ƙofar ɗakin mata kina yaɓa mata magana sannan kuma ki ce wai ranta ba zai ɓaci ba?”

“Salima ranki ya ɓaci don na faɗa miki abun da kika yi bai mini daɗi ba?” Juwairiyya ta ƙara tambayar tana jin duk walls ɗinta na crumbling mamaki cike taff a ranta.

“Na ce a bar maganar ko?” Wannan karon ma Salima ta sake faɗa.

“Ko hakan ya isa ya nuna miki cewa bata ji daɗin ba, amma saboda kawaici da haƙuri irin nata sai ba zata iya faɗa miki ba ta gwammace tayi haƙuri saboda kar ran kowa ya ɓaci.” Maman Hanan ta ƙara tsoma musu baki tana hararar Juwairiyya da ta sake baki tana kallon Salima da wani irin duba mai ɗauke da shock da kuma betrayal.

Juwairiyya bata sake cewa komai ba ta juya ta shige ɗakinta ta barsu a gurin Maman Hanan tana ɓaɓatu ita kaɗai. A can ɗaki ta yiwa kanta masauƙi ta zauna a kan gado zuciyarta na bugawa tana jin kwakwalwarta kamar ta jagule bata iya tunani mai kyau. Me hakan yake nufi kenan? Me yasa Salima ba zata iya buɗe bakinta tayi magana ta wanketa daga zargi ba? Me yasa tana ji Maman Hanan tana fassara yanda take ji a zuciyarta ba tare da ta ƙaryatata ba? Me yasa ba zata ce ‘A’a! Ni fa wance raina bai ɓaci ba, abu ne na mata kuma tunda tace bata so shikenan ba za’a ƙara ba’. Me yasa kuma take sunkuyar da kanta ƙasa tana wani abu kamar munafuka kamar tana son yin kuka? Me ta mata? Zaginta tayi ko kuma ta faɗa mata baƙar magana ne? Daga cewa abun da kika mini bai mini daɗi ba shikenan sai ya zama laifi ya zama babban abu? Wai me yake faruwa ne a rayuwarta? Kowa nata ya gujeta! Wai ko dai baƙin halinta ya kai har haka ne bata sani ba? Da wannan tunanin ta wuni sai da ta tabbatar Maman Hanan ta fita sannan ta kwashe abincin ta shigar dashi kitchen. Naman miya kam har ya fara narkewa ruwan ya ɓata mata bakin kitchen ta gyarashi sannan ta kai fridge ta adana. Daga nan ta wanke gurin ta ɗaura girki simple daidai cikinta ta gama ta shige dashi ciki ta rufe ƙofarta.

Bayan sati da haka Juwairiyya ta kira Muhammad kan tana son zuwa gidan Hafsat ta ci sa’a kuwa ya barta, domin a yanzu in tana da buƙata direct zata kirashi ko kuma ta mishi text. Daga school ta wuce gidan Hafsat wacce take zaune ita ɗayanta a gidanta duk da cewa tana da kishiya, yaranta biyu ne mace da namiji.

Sai da ta ci abincin rana suna hira sannan Juwairiyya ta sako zancen Salima tana bawa Hafsat labarin abun da ya faru ranar, wanda tsabar mamakin da yake bata ne ma ta kasa barinshi a ranta ta faɗawa Hafsat ɗin ko zata gane me hakan yake nufi.

“Hafsat ina faɗa miki wallahi kasa magana tayi. Ta buɗi baki kawai ta faɗawa wancan matsiyaciyar kan cewa ita ranta bai ɓaci ba amma ta gagara ta barta tana ta mini hauka. Na rasa gane me yasa tayi haka! Shirunta ne yayi yawa ko kuma rashi son fitinarta? Ai da bata son fitina da tuni ta yi clearing confusion ɗin matar ta kyaleni. Don Allah me kika fahimta a nan? Me yasa tayi haka?”

“Aunty Juwai duk abun da zan faɗa miki ki nitsu ki saurareni kar ki ɗaga hankalinki. Zaki iya?”

Wannan magana kaɗai da tayi sai da hanjin cikin Juwairiyya suka kaɗa tsoro ya shiga zuciyarta nan take.

“Me ya faru? Zan iya! Don Allah faɗa mini kar zuciyata ta buga.” Ta faɗi hakan tana jin gumi na tsarto mata akan goshinta.

“Aunty Juwai, kin ga matar nan da kike zaune da ita da zuciya ɗaya? Wallahi ita ba da haka ta ɗaukeki ba. Salima munafuka ce kuma makira ta gaban kwatance.”

“Ni har kin bani tsoro wallahi, Salima kuma da munafurci? Ta yaya kenan? Wa take yiwa munafurci?”

“Ke!” Hafsat ta bata amsa with a straight face.

“Kai mutane dai basa son zaman lafiya don na san wani ne ya zo ya guntsa miki ƙarya. Amma dai ki faɗa ina jinki.” Ta faɗi hakan tana murmushi alamar bata ɗauki maganar serious ba.

Hafsat tsayawa tayi tana kallonta zuciyarta na tausaya mata domin da gaske har yanzu bata gane da wa take hulɗa ba. Ta jima da ganewa game da jin labarin da ita kanta Juwairiyan bata san dashi ba. Tana zaune ne da green snake under green grass bata sani ba.

“Tun farko Salima ta nunawa dangin Ya Muhammad so da kuma kawaici, hakan yasa suke yabonta kuma ta nuna musu cewa ita bora ce saboda Muhammad yana mata faɗa ko a gabansu, hakan yasa suke tausaya mata suke kuma ganin girmanta. Suna zaune a haka kika shigo cikin rayuwarta wacce a da ke matar abokinta ce wacce kuka yi ƙawance na sosai da sosai har bayan mutuwar mijinki bata rabu da ke ba. Sai da aka yi auren sannan magana ta fara fitowa, na farko ta faɗawa dangi wai ta suma da Ya Muhammad ya bata labarin auren tsabar kaɗuwan da tayi, amma da ta zauna sai ta ga hakan rufin asirinki ne da kuma tata sai ta ji komai ya wanku a zuciyarta ta karɓi auren da hannu biyu. Aunty Juwai wannan abu sai ya ƙara mata daraja a idon dangin nashi, har suke cewa haƙurinta ya wuce misali waye-waye, har wasu na cewa da su ne ƙawarsu ta aure musu miji sai an ga tashin hankali sai kowa ya ji a jikinshi, maganganu dai kala-kala. To gaskiya tun daga nan kika rasa wani kaso na cikin matan dangin nasu waɗanda suke da matuƙar kishi suke kuma taya ita Salima kishi tunda ita bata yi. Na biyu da kika zo maimakon ki jawosu jikinki sai kika fara musu da baƙar magana, kuma nasan zaki iya faɗin hakan amma zai yiwu ba da wata manufa kika faɗa ba ita kuma ta je ta canja zancen.”

“Wai me na faɗa?” Wannan karon zuciyar Juwairiyya ce take bugawa domin ta fara jin ƙamshin gaskiya a wannan zancen, jikinta kuwa tuni yayi sanyi har tana jin tsoron abun da kunnenta zasu jiye mata.

“Su Shema’u da wata ƙanwarsu na manta sunanta suka je ganin ɗakinki washegarin da kika tare sai suka samu ƙofarki a kulle, a nan makirar take faɗa musu wai ko sun kwankwasa ba zaku buɗe musu ba kuna ciki, amma zasu iya dawowa daga baya. To wannan ma sai ya jawo abun magana, sai suka ce kenan da gaske ke da Ya Muhammad kun jima kuna cin amanarta kuna soyayya a ɓoye shiyasa kina tarewa kuka kulle ƙofa kuna kashe arna. Kina ji na?”

“Wallahi auren ya faru ne kawai amma babu batun soyayya tsakanina da shi har yanzu kuwa da muke maganar nan.” Juwairiyya tayi maganar kamar zata yi kuka domin ita weakness ɗinta shine sharri.

Ta tsani a mata sharri a kan abun da bata aikata ba, ta sani tana da masifa da hargowa ko tsiwa, to amma in tayi su aka ce tayi bata musawa kuma ba zata ƙaryata ba, amma cin amana da munafurci ba halinta bane, bata yi ba kuma aka bita da sharrinsu.

“Ina kai ki ke kam! To wai a gidan bikin suna da Iyami ta haihu ke kika ƙule uwar ɗaka kina tare da mai jego, a nan Salima take faɗa musu wai kin ce ke bakya son gulma don meyasa daga tarewa zasu zo wani ganin gida? Gidan gudu zai yi? Kun yi maganar nan ko baku yi ba?”

“Mun yi kuma na faɗi hakan amma wallahi specifically ba da su nake ba, ina magana ne a kan amarya budurwa da ake zuwa musu don a ga yanayin tafiyarsu ko kuma wani gulman. Ni bazawara ina zasu ga canjin tafiya a tattare da ni? Wallahi ba da su nake ba.” Wannan karon hawaye ya taru a idanunta amma ta shanyesu ta dubi Hafsat irin ki ci gaba ɗin nan.

“I’m sorry amma wannan magana ta yayata familynsu ana kiranki ƙidangi a maimakon sodangi. A wayo da dabara take bada labarin zamanku ba tare da sun fahimci cewa gulmarki take kawowa ba, har take cewa wai Muhammad ba ya miki tsawa irin wanda yake mata saboda kina da tsiwa da masifa har ta bada labarin yanda wai kika karɓe ɗanta daga hannunshi da yake dukanshi kuma ya kasa taɓuka komai. To kuma kin san dangin miji basa son su ji mace ta raina ɗan’uwansu ko ta mallakeshi, wannan ma dai ya ƙara miki points kan tsanar da suke miki suna cewa kin fi ƙarfin ɗan’uwansu. Wai kuma kin yi faɗa da mai aikinku wacce ta jima suna tare da Saliman amma zuwanki kuka fara samun matsala har uwarta ta gaji tace ƴarta ta daina aiki a gidanku. Sannan ke da makwabta ba kwa ga maciji, bakya ko shiga gidajensu haka kuma ko gaisuwan yaransu bakya amsawa in kika fita waje kuka haɗu. Maganganu dai wani in yarda wani kuma daga ji ma kin san ƙarya ce haka tayi ta yayatawa duk inda ta zauna cikin ƴan’uwa. To abun mamakin shine har yanzu sun kasa ɗaukanta a matsayin munafuka domin yanda take basu labarin cikin hikima ne irin tasu ta makirai da baza ki gane gulma suke kawowa ba, as in kawai hira ake yi itama ta sako tata shikenan a wuce.”

“Wayyo Allah na!” Wannan karon Juwairiyya ta dafe ƙirjinta tana jin hawaye na sauƙa kan ƙuncinta.

“Sai ki san yanda zaki zauna da ita ki kuma iya takunki domin duk wani abu a kanki faɗa musu take yi Aunty Juwai.”

“Wallahi Tallahi da wani ne ya fara bani labarin nan ba zan yarda ba. Kai! Tun daga farko ma zan dakatar dashi ba zan saurareshi ba, amma ke Hafsat ba zan iya miki haka ba shiyasa na saurareki ashe kuwa zan ji abun da ya girmi hankalina. Kai duniya! Wai Salima ce take mini haka? Saliman da na yarda da ita na ke faɗa mata sirrina? Zamana da Muhammad kaɗan ne bata sani ba wallahi don bana ɓoye mata, zamana a gidanta na bata girmanta a matsayinta na uwargida bana mata katsalandan har ya zamana na bata daman kula da mijinta ko da yana ɗakina ne wanda sai daga baya kuma abun ya zo ya dameni amma har yau ban iya cewa na janye maganar ba. Idan da fuska biyu take zaune dani zan bar mata gidanta don ni ba zan iya zama da munafuki ba wallahi. Kai duniya!”

“To ai in kin bar gidan ta samu abun da take so kenan, ke da nake zaton zaki ce zaki yi iya bakin ƙoƙarinki wajen jawo soyayyar dangin nashi sannan zaki koyi karatun zama da ita kuma sai ki bige da cewa zaki bar mata gida! Ki je ina kenan? Wannan ba magana bane sam!”

“Hafsat ba zaki gane bane. I’m hurting fiye da yanda nake nuna miki a fuskata. I trusted her wallahi, na ɗauketa da muhimmanci fiye da wasu makusantana. She knows too much ta yanda ko nace zan cigaba da zama da ita zata kwareni saboda ta san komai. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Mutum mugun icce!”

“Ki koma gida ki zauna kiyi tunanin yanda zaki shawo kan al’amarin sannan wallahi ki kai ƙararta gurin Allah domin ta riga da ta ɓataki kam a idon mutane, kuma Shi kaɗai ne zai miki maganinta.”

“Hafsat me yasa baki faɗa mini tun da wuri ba? Me yasa kika ɓoye mini? Sannan a ina kika ji?” Juwairiyya ta tambaya wannan karon hurt ɗin ya ninka na da, domin sai take ganin Hafsat ɗin ma bata kyauta mata ba.

“Ina tsoron kar ki ƙi yarda da ni ne a samu tangarɗa a zumuncin mu, ko kuma kiyi tunanin ina son tsoma bakina cikin rayuwarki ne. Amma ko kwanaki da muka je gidanku Saliman tayi ta sakaki magana akan halin Ya Muhammad sai ni nake kareshi, to wallahi wannan maganar ma ya isa kunnensu wai kina ta bada labarin halin mutumin naku a gaban ƙannen mijinki na da, shine suka ce baki da sirri, ba kya rufawa ɗan’uwansu asiri. Wannan labaran kuma daga bakin wata danginsu ce da take auren wani cousin ɗin Babanmu.”

“Hafsat zan tafi gida, kaina juyawa yake yi ina son in kwanta in huta.”

“Are you sure ba wani matsala ba ce babba?” Ta tambayeta with concern a muryarta.

“Kawai kwanciya nake son yi, I want to wrap maganganun nan a kaina.”

“Shikenan, amma dai in kin je karki yi confronting ɗinta, just observe her sai ki sha maganin zama da ita.”

“Nagode Hafsat.”

Da haka suka yi sallama Juwairiyya ta tafi gida duk jikinta a sanyaye, ko da ta dawo bata samu Salima a gida ba dalilin lock da aka sakawa gate ɗinsu ta buɗe da nata key ɗin ta shiga ta kulle. Direct ɗakinta ta shige ta kwanta a kan gado tana mai sauƙe ajiyar zuciya. Wai ashe dama bata san da waye take zaune ba? A nan ta fara tuno duk wasu encounters ɗinsu da zasu zauna su yi magana, tana tunowa duk wani maganan da ya fito daga bakin Salima sai dai ya tunzurata ba dai ta ji sauƙi a zuciyarta ba. Ita ke sakata surutai sai kuma tayi shiru tana sauraronta tana tsintan waɗanda zata kai gaba. Hausawa sun yi gaskiya da suka ce makashinka yana nan tare da kai! To yaya zata yi zama da ita? Ko dai ta bar mata gidan ne don bata ma san yaya zata gyara tsakaninta da mutanen da ta ɓatata a gunsu ba.

Menene mafita? Barin gidan Muhammad ko kuma gyara gurin zaman a gidan nashi?

Mum Fateey 👌

A ranar da Juwairiyya ta gane hali ta kuma san wacece Salima sai ta kasa samun nitsuwa haka kuma sai ta ji duk mutanen duniya kowa ma munafuki ne. Haka ta karisa wunin ranar kwance a ɗaki tana kwancewa da warwarewa, zuciyarta kuma har lokacin ta kasa nitsuwa tana jin yana mata zafi bayan tsoron da yake cike a ciki na taraddadin me kuma Salima ta faɗawa dangin Muhammad bayan wanɗanda ta ji da kunnenta? Sannan wane munafurcin kuma ta shirya mata wanda ta ɓoye su kansu dangin basu sani ba? Babban abun kuwa shine me ta mata da ta cancanci haka daga gareta? Ta ji zafi kuma tana kan jin zafin, domin ita ta sani mutane da yawa sun mata munafurci sun kuma yaɗa karya a kanta musamman lokacin da ta fito daga gidan Daddy, duk da cewa abun ya dameta amma bata ji zafinshi kamar yanda take jin zafin na Salima ba saboda ta yarda da ita! Babu abun da ya fi zafi irin mutumin da ka yarda dashi ne yake munafurtarka yana faɗin ƙarya da gaskiya a kanka don kawai sauran mutane su tsaneka ko su ga aibunka.

Ta sani duk abun da Saliman ta faɗa gaskiya ne, amma menene abun yayatawa? Menene kuma na twisting maganarta tana ɗaurasu a kan ƙarya tana kautar dasu daga ganin gaskiya? Me ta mata? Zagi? No! Duka? No! Takurata? No! Ko dai laifinta don ta aure mata miji? Tabbas shine laifinta! To amma me yasa tun a wancan lokacin bata nuna mata ba, ta yanda zata gane ta kuma zauna da ita yanda ta ɗauketa? Me yasa ta mata rufa-rufa da bogin halaye ta jata a jiki alhali ta san ba haka bane a zuciyarta ba? Kai! Munafuki sam bai yi ba!

Hawayen fuskarta ta goge kana ta tashi ta shiga banɗaki da yake lokacin sallan maghrib yayi tayi alwala ta fito. A nan ta ji ƙaran buɗe gate ɗinsu tare da shigowar mota wanda sai da zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske, ko Muhammad ne? Kai ina! Bashi bane saboda ya sayar da motarshi tun kafin ya tafi. Nan kuwa ta ji kewarshi sosai a ranta domin duk iskanci da rashin kunyar da take mishi bai cika kulata ba sai abun ya ɓata mishi rai sosai. Ji tayi ina ma yana nan! Ina ma bai tafi ya barta ita kaɗai da macijiyar matarshi ba! Ina ma ina ma! Ina ma auren soyayya suka yi ta riƙeshi gam ta yanda zata rama abun da Salima ta mata! Ina ma ina ma!

Amma kash, ba auren soyayya ba ne, aure ne na wucin gadi da ko a da bata tunanin tabbata a cikinshi balle yanzu da ta gane uwargidan nata munafuka ce! Zata bar mata gidanta da zarar lokaci yayi ba sai ta haɗa mata da munafurci ba, lokaci take jira, lokacin da zai yi daidai da shima ya gama makarantarshi ya dawo wato nan da shekara biyu da watanni.

Tana jin hayaniya a tsakar gidan amma tayi zamanta a can ƙuryan ɗaki, yunwa take ji amma ta kasa fita don bata son ta haɗa ido da Salima. Ji tayi bayan shaiɗan duk duniya babu wanda ta ji ta tsana irin Salima, ita bata iya munafurci ba, ta kuma tsani munafuki shiyasa da zarar lokaci yayi zata bar mata gidanta wanda daga nan kuma sun rabu kenan na har abada da yardar Allah.

Ƙarfe goman dare ta fita bayan ta tabbatar sun watse, a farfajiyar gidan nasu inda Muhammad yake ajiye motarshi ta ga mota ƙirar Hyundai Elantra 2012 wacce kuɗinta ya kai five million ko fiye. Ba sabuwa bace dal amma kuma second new ce bata sha jiki ba ko kaɗan, ta sani wannan motan da Salima ta ce Babanta ya saya mata ne. Bata ji baƙin ciki ba haka kuma bata ji murna ko farinciki ba ta shige kitchen ɗinta ta ɗauko plate da spoon sannan ta rarumo microwave ɗinta ta shigar dashi can ɗakinta. Left over ɗin da take ajiyansu a cikin fridge ta darje ta zaɓi jollof rice da guntun pepper chicken ta turasu cikin microwave suka fara dumama.

Kamar kullum kaɗawar Timer ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, abincin ta juye a plate kana ta koma kan gadonta bayan ta jawo ruwa gefenta ta fara ci a hankali amma tana kai loma na biyar ta ji ba zata iya ci ba ta ajiye. Ƙarshenta haka ta mayar dashi cikin roba ta kai falo akan gobe zata bawa almajiri.

Washe gari bata da lectures don haka bata fita ba sai wajen sha biyun na rana, nan ma yunwa ce ta dameta tace bari ta soya ko chips da egg ne ta ci. Tana fitowa ta samu matan unguwansu su biyu suna zaune a ƙofar falon Salima ita ma gata a cikinsu sai hira ake yi, to wai yaushe suka fara zama a waje? Ta tambayi kanta tana mai jin haushin fitowarta a daidai wannan lokacin, ai bata san suna zaune ba da babu abun da zai sa ta fito.

“Amarya kin tashi lafiya? Jiya na fita karɓo mana motarmu shi yasa ban faɗa miki ba saboda ina son miki surprise ne. Gata nan mun samu na zuwa unguwa abun mu.”

“Lafiya kalau. Na tayaki murna Allah Ya sanya alkhairi.” Shine kaɗai abun da Juwairiyya ta faɗa ta shige kitchen.

A can ta gurin su Salima kuwa matan ne suka bi Juwairiyya da ido cike da mamaki suna ayyanawa a ransu hassada take yiwa uwargidan tata.

“Ke kin ga yanda fuskarta ta haɗe kuwa? Kai hassada mugun ciwo! Ke kina cewa kun samu abun arziƙi ke da ita amma ita tana cewa wai ta tayaki murna. Wato tana nufin banda ita!” Wannan faɗin Maman Hanan kenan tana ƙasa da murya.

Salima da bata da masaniyar Juwairiyya ta game halinta sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi irin bata ji daɗin abun ba amma dai ba zata ce komai ba.

“Bayan haka kuma da alama jikinta yayi sanyi ta game ke ɗin ba sa’ar karawanta bane. Da tana ɗaukan kanku ɗaya amma yanzu ta sani ajinki ya fi tata tunda bata da mota kuma bata da uban da zai saya mata. Astagfirullah! Duk da ma dai mutuwa tana kan kowa.” Wannan faɗin Maman Sabir kenan tana dariya tana rufe bakinta Maman Hanan ta dara banda Salima da take sunkuye da kai har lokacin kuma bata ce uffan ba.

“Ai wallahi da ni ce ke, tunda ta kasa mini murna ita da shiga motar nan sai kallo daga nesa. In ba baƙin ciki ba me zai hana ta zo ta kalli motar ta duba cikinta sannan tayi murnan na gaskiya?” Wannan magana na Maman Hanan a kunnen Juwairiyya tass

wacce ta fasa dafa abincin ta ɗauko kayan haɗa shayi ta fito zata koma cikin ɗakinta.

Har tayi kamar ta tsaya ta zagesu sannan ta faɗa musu halin makirar da suke zaune da ita sai kuma ta fasa domin kuwa na farko; Ba za ma su bari ta idar da saƙon nata ba zasu katseta a yi uwaka ubanka. Na biyu ko ta faɗa sun saurareta ba zasu yarda da ita ba saboda tun farko sun tsaneta sai dai ƙarshe abun ya dawo kanta su ce hassadar tata yayi yawa wanda ta rasa ta yaya zata nuna sai ta hanyar ƙalawa Saliman sharrin munafurci. Sannan na uku idan magana ya fita wanda ta sani tabbas sai ya fitan zai ƙara mata baƙin jini ne a gurin mutane a ce bata da halacci, matar da ta riƙeta da amana duk da cewa ta aure mata miji ne take mata ƙazafin munafurci. She can’t risk that, a hakan ma an gama ɓatata ba zata so abun ya fi haka ba. Wannan dalili yasa tayi shigewarta ɗaki ba tare da tace musu uffan ba.

Sai a lokacin Salima tayi magana ta ɗago fuska a marairaice ta ce,

“Ni dai bakwa kyauta mini wallahi, gaskiya na kusa daina gayyatarku cikin gidan nan kamar yanda ta ce a hanaku zuwa kwanaki.”

“Bura uba! Wato har cewa tayi a hanamu shigowa cikin gidan nan? To wallahi ƙaryarta ta sha ƙarya! Tun kafin ta zo muke tare da ke muke shigowa don ita ta zo yanzu bata isa ta hanamu shigowa ba. Idan ke tana cin kashi a kanki to mu mun fi ƙarfinta wallahi. Ke bari ma in faɗa miki, ko ke ce kike ja na waje zaki fitar da ni ba zan fita ba saboda zumunci yanzu ma muka fara babu ƙatuwar da ta isa ta shiga tsakaninmu.” Faɗin Maman Hanan tana ta kumfar baki.

“To Allah Ya hana. Allah kuma Ya bamu zaman lafiya duka har da ita.” Salima ta ƙara tunzurasu suka bita da harara kana suka tashi tsaye wai zasu tafi kar ta kashesu da haushi saboda bata da zuciya. (Allah Ya tsinewa munafuki)

Suna fita Salima da ta musu rakiya bakin gate ta dawo zuwa bakin ɗakin Juwairiyya ta kwankwasa mata. Ita kuma tana falo tana jin maganganunsu zuciyarta na tafasa ta tashi ta buɗe fuskarta a gimtse don bata iya ɓoye fushinta ba haka kuma bata iya makirci ba.

“Ya aka yi?” Ta tambayeta kai tsaye don ko kallonta bata son yi balle ta buɗe baki ta fara zuba mata munafurci.

“Dama naga ba ki kalli cikin motar bane shi yasa nayi tunanin ko don su Maman Hanan suna gurin ne, yanzu kam sun tafi ki zo ki gani.”

Da a da ne Juwairiyya buɗe baki zata yi tayi ta zaginsu tana cewa ta fi ƙarfinsu amma a yanzu sai ta muskuta kaɗan ta ce,

“Salima kenan.” Da haka kuma ta rufe bakinta ta zurawa Saliman kattin idanunta tana kallonta.

Sai a lokacin kuma take ganin zallar makircin da yake rubuce a fuskarta. Ina hankalinta da tunaninta yake da duk tsawon wannan lokacin ta kasa ganewa sai da aka ankarar da ita?

“To ko dai tun wancan laifin da na miki ne baki huce ba, zan ƙara baki haƙuri in hakan zai sa ki sassauta mu ci gaba da zamanmu kamar da.”

“Ko ɗaya, amma batun mu koma kamar da zai yi wuya. Zan so kuma don Allah kiyi harkan gabanki nima in yi nawa har zuwa lokacin da Allah zai rabamu.” Tana faɗin hakan ta rufe ƙofarta ta bar Salima da tsantsan mamaki domin bata yi zaton Juwairiyya zata mata haka a yanzu ba duk da cewa hakan shine goal ɗinta amma kuma ya zo da wuri.

Wannan abu da Juwairiyya tayi kuwa ya zaga dangi wanda bayan kwana uku da haka tana school da hantsi Hafsat ta kirata.

“Aunty Juwai kina ina ne?”

“Ina school, wani abu ne?”

“Magana zamu yi, don Allah ki koma gefe.”

Babu musu Juwairiyya ta matsa daga cikin class mates ɗin nata ta koma can gefe zuciyarta na lugude domin ta sani wani abun Hafsat zata faɗa mata da ya shafi gidanta tunda sa’i da lokaci tana aiko mata da shawarwari da sauransu.

“Ina jinki.” Ta faɗa tana mai jinginuwa da bishiyar don samun support gudun kar ta faɗi idan ta ji abunda ya girmi hankalinta.

“Dama na faɗa miki wannan magana da kika yiwa Salima zata yi amfani dashi kuma zai dawo kanki. Aunty Juwai maganar da nake miki shine yanzu ta shiga cikin family wai har gurin Yayan Ya Muhammad ta je wai a zo a muku sulhu ta rasa gane kanki sannan wai kin buɗi baki kin ce ta fita daga harkanki kowa yayi rayuwarsa shi kaɗai. Ita bata san me ta miki ba, kuma a yanda kuke ai in laifi ta miki ma zaki faɗa mata ba wai ki ce ku raba gari ba. Mijinku baya nan yanzu ya fi buƙatar haɗin kanku ita bata son a tayar mishi da hankali waye waye. Sai kuma maganar ƙarshe da ake cewa haushi kike ji akan ta samu mota wai ko wataƙila kina zaton Muhammad ne ya saya mata aka yi rufa-rufa aka ce Babanta ne. Aunty Juwai na faɗa miki in zaki zauna da matar nan sai kin iya bakinki sannan fushi ko nunashi ba naki bane, magana mai kyau tana juya miki shi ya zama mara kyau ina ga kuma ke kika yi magana mara kyau ɗin? Yanzu ana can ana shawara wai ko zai haɗaku ya muku nasiha ne ko kuma a haɗa da magabatanki su miki magana wataƙila zaki fi ganin girmansu.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Shine abun da Juwairiyya tayi ta maimaitawa kenan tana jin zafi da raɗaɗi a zuciyarta. Ashe gwanda da ta mannu da bishiya domin sai ta ji jiri na son kwasarta ya yaɓa da ƙasa.

To ko dai wannan dalilin ne yasa jiya da ta kira Muhammad su gaisa kamar yanda ta ke kiranshi bayan kowanne kwana uku yake wani cijewa kamar baya son wayar? Har a ƙarshe da ya ji bata yi mishi magana kan motar Saliman ba yace wai ‘Kin ji Baban Salima ya saya mata mota ko? Ana fama da rayuwa shi kuma sai ya sauƙaƙa mata saboda kai Muhammad Hafiz school.’

Wato ya mata hannunka mai sanda ne, ta sani ba fa shi ya saya mata ba, tana tunawa ko kanzil bata ce ba ta mishi sallama ta kashe wayarta don ita a yanzu bata ko son ayi hiran Salima. Ashe ashe hakan ma da tayi zai iya tabbatar mishi da zarginshi ne, idan a da bai yarda ba to yanzu kam ta bashi damar da zai yarda cewa tana yiwa matarshi hassada ne sannan bata son zaman lafiya da ita. Ita kam ya zata yi da rayuwarta ne? Ta yaya zata zauna da wannan makirar?

“Aunty Juwai kina ji na?” Hafsat ta faɗa cike da damuwa da kuma haushi har tana cewa ina ma ita ce Juwairiyyan ta gasawa Salima gyaɗa a hannunta!

“Ni makirci da wannan kissan ƙaryan ne ban iya ba Hafsat, in ina tare da mutum ina tare dashi, in kuma bana tare dashi bana tare dashi. Duk yanda nake jinka a zuciyata haka zan nuna maka a fuskata babu munafurci saboda ka gane ka kuma san da wani alƙibla na ɗaukeka. Ta je tayi duk abun da take so, ni na barta da Allah domin tun farko wallahi ban ɗauketa da zuciya biyu ba. Allah Ya na gani kuma zai mini sakayyan ɓata mini suna da take yi cikin mutane.”

Jikin Hafsat ne yayi sanyi sosai domin ta san wacece Juwairiyya a ɗan zaman da suka yi tare a matsayinta ma matar yayansu. Dukkansu da zuciya ɗaya ta zauna dasu, abun da take yiwa ƙannenta su ma haka take musu duk da cewa su sa’annin juna ne. Tana kuma da son mutane da saurin yarda da su wanda in har tana yinka to fa babu kamarka a gurinta, wannan dalili ya sa take zaune da su har aka rabu babu tashin hankali balle fitina. To amma wannan karon abun ya haɗu da kishiya ne, dole ta koyi wani abun ba don ta mata mugunta ba sai don ta dinga kare kanta da zarar ta ga alamar za’a mata zagwan ƙasa. Idan ta koyi kissan sai tayi amfani dashi ta hanya mai kyau ba wanda zai cutar da kowa ba. A yanzu da hankalin Juwairiyyan yake a tashe ba zata saurareta ko ta ɗauki shawaran da zata bata ba, saboda ta sani har yanzu she is hurting akan zamba cikin amincin da Salima ta mata wanda har yanzu bata gama wrapping kwakwalwarta a kai ba. Zata bata lokaci kafin ta mata magana ba zata fasa ba.

“Shikenan Aunty Juwai, amma ki kame bakinki sannan ki dage da addu’a Allah Ya wanke musu ido su ga wacece ita.”

“In sha Allah Hafsat, nagode sosai.”

Da haka suka yi sallama, daga nan kuma Juwairiyya ta ɗauki jakarta ta fita daga school ɗin domin sai ta ji ba zata iya jiran lectures ɗin da za’a musu ba. Sai da ta fita ta kira Muhammad amma bai ɗauka ba, ƙarshe ya mata text wai yana class. Itama text ta mishi kan cewa tana son zuwa gidan Mama ya bata izini ta kira Idrisa ya zo

ya ɗauketa.

A can ta samu Mama yau bata fita aiki ba, suna cin abincin rana Mama tana lura Juwairiyya ta kasa cin abun kirki sai wasa take yi da cokalinta a cikin plate tana tunani.

“Juwairiyya ya dai? Lafiyanki kam?” Maman ta tambayeta itama tana jin damuwa na shiganta.

Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe kana ta fara bawa Mama labarin tun daga farko har ƙarshe ta ƙarisa da cewa,

“Mama sai in dinga jin kamar mafarki nake yi zan farka in ga Salima ba haka take ba. Wallahi kullum idan na zauna sai in dinga tuna zamanmu da yanda take manipulating ɗina ina ta maganganu wai a tunanina zai tsaya ne tsakaninmu. Mama ina jin zafi a raina saboda na yarda da ita, ina faɗa mata sirrikana fiye da yanda nake faɗa miki ke mahaifiyata, na bata matsayin da ko ƙawayena da na tashi da su muka yi school tare basu samu ba. Mama zan bar mata gidan mijinta tunda a kan na aureshi ne yasa ta canja mini tana munafurtata.”

“Har yanzu baki da hankali Juwairiyya. Zan fara miki da faɗa kafin in baki shawara; kin ga wannan abun da ya faru? Ki ɗaukeshi a matsayin darasi ne Allah Ya aiko miki. Juwairiyya ni na haifeki na san duk wasu hakalayenki ciki kuwa har da wanda kike ɓoye mini na faɗe-faɗe, domin kuwa ke idan ranki ya ɓaci sai kowa ya san ranki ya ɓaci wanda ko kwanaki a gidan Surayya sai da na miki faɗa akan hakan amma baki ji ba. Shi wannan harshe da kike gani zai iya yanka wuyan mutum saboda tsabar kaifinshi, shi yasa Annabi Muhammad SAW ya ce mu kiyayeshi. Na sha miki faɗa amma bakya ɗauka sai Allah Ya nuna miki misali wanda dama an ce in baka ɗauki ta mutane ba duniya zata koya maka hankali. Shi kuma mutum da kike ganinshi kar ki kuskura ki mishi so mai yawa, haka kuma kar ki yiwa mutum ƙi mai yawa don idan Allah Ya so zai iya canja wannan son ko ƙin zuwa kishiyarsu. Juwairiyya ba’a yiwa mutum yarda ɗari bisa ɗari domin shi ɗan adam tara yake bai cika goma ba, kalilan daga cikin mutane ne zaki yarda da su kuma ba zasu watsa miki ƙasa a ido ba. Sannan ki dage da addu’a ina faɗa miki amma ban sani ba ko kina yi, idan kika fawwalawa Allah lamuranki sai ki ga ko ana miki ba ya damunki sannan a je-a je watarana sai Allahn da kike kai kukanki gareshi Ya tona musu asiri ke kuma ya wankeki, amma kafin nan sai kema kin iya bakinki kin yarda da Shi kuma baki bibiyesu da sharri ba. Batun barin aurenki kuma don wannan silly abun bai taso ba kuma kar in sake jin kim ambaci rabuwa da mijinki.”

Sosai Mama ta yiwa Juwairiyya faɗa wanda ciki kuwa har da cewa kar ta kuskura ta nunawa Salima ta ganeta, ko kuma ta yanke hulɗarsu ko kuma itama ta biye mata su dinga yiwa juna munafurci. Duk wannan magana da Mama tayi sun shiga kwakwalwar Juwairiyya amma abun da har yanzu Maman bata gane ba shine har lokacin bata daina jin zafin rikiɗar Salima daga ƙawarta zuwa munafukarta ba, har yanzu bata samu nitsuwa ba domin tana jin raɗaɗin a ranta, betrayal ɗin na cinta sosai da sosai.

Bayan Juwairiyya ta koma gida ta samu wasu ƴan’uwan Salima sun zo mata murnar mota, ta gaishesu a sanyaye kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta shige ɗakinta sulum-sulum babu kwarin jiki ta kwanta. A satin haka suka yi ta baƙi ƴan zuwa murna, tsakaninta da Salima kuma gaisuwa ce sai kuma in an yi baƙin ta kawosu ɗakinta sai su zauna suna hira tsakaninsu amma ita nata ido ne kawai babu Umm balle Uhmm domin kowa kallon munafuki take mishi, gani take yi ko numfashi tayi da ƙarfi zasu iya fassarashi da cewa so take yi ta zuƙe duka iskar su kuma su rasa. Abinci kuwa ya zama sai in yunwa ya addabeta ne zata ci domin sai ta ji duniyan ma gabaɗaya ya fita a kanta da mutanen cikinshi.

Bayan wasu kwanaki Yayan Muhammad da yake zuwa dubasu wannan karon ma ya zo kamar kullum tare da ƴayanshi ya shigo tsakar gidan suka gaisa da Salima sannan ta bugawa Juwairiyya ƙofa itama ta fito ta gaisheshi. A nan yake tambayarsu kamar kullum ko suna da buƙatar abu amma kowacce ta ce babu, sai a lokacin ya fara musu nasiha mai haɗe da lallashi kan zaman lafiya da haɗin kai, da Juwairiyya bata san dalilin hakan ba da sai ta ce kawai yana yi ne don tunatarwa a garesu amma yanzu, she know better.

Tana ganin yanda Salima ta sunkuyar da kai ƙasa wani lokacin har da matsar kwalla irin tana cikin rashin kwanciyar hankalin nan tana neman ɗauki, nan take Juwairiyya ta ji ta fara tausayin kanta domin Salima ta wuce tunaninta, ita ina ta iya wannan makircin da kissa da za’a ce wai ta koyi zama da ita? Ina zata iya da matar da kowa yake mata ganin shiru-shiru mai kawaici, haƙuri da kuma son jama’a! Ina zata iya? Wa kuma zai koya mata?

Yana gama nasiharshi Salima ta buɗi baki ta ce,

“In sha Allahu zamu kasance masu haɗin kai da wasu ma zasu yi koyi da mu. Sannan zamu yi zaman lafiya wanda zai farantawa wanda ya ajiyemu rai, da yardar Allah kuma ba zamu zama sanadiyyar tashin hankalinshi ba alhali yana can wata duniya nesa da mu. Mun gode Baban Fahad, Allah Ya ƙara girma da arziƙi.”

Juwairiyya ji tayi hawaye ya gangaro mata tayi saurin gogewa itama ta fara magana murya na rawa ta ce,

“Zamu kiyaye In sha Allah. Ka tayamu da addu’a Allah Ya kawar da sharrin shaiɗan a tsakaninmu.”

“In Allah Ya yarda. Allah Ya muku albarka.”

Da haka ya ciro dubu biyar biyar ya miƙa musu suka karɓa suna godiya sannan ya zari wasu dubu biyu ya miƙawa HJ yana cewa,

“Gashi Mamanka ta saya maka biscuits yau na manta kuma su Fahad basu tuna mini ba.”

HJ ya karɓe kuɗin yayi gudu ya kaiwa Mamanshi ta cigaba da kwararo addu’a Ya Abdallah yana amsawa da Amin har ya musu sallama ya tafi. Yana tafiya Salima ta cakali Juwairiyya da hira wacce ta kasa cewa komai sai kallonta kawai take yi. A nan ne Saliman ta buɗi baki ta ce,

“Yanzu in ba don Baban Hafiz ya yarda da yayanshi ba ai ba zai bari kowacce sati ya dinga shigowa gurin matanshi ba. Wani mijin yana da kishi da kuma gudun sharrin shaiɗan.”

Murmushin ƙarfin hali Juwairiyya tayi wanda har ta buɗe baki zata ce ‘Allah Ya kyauta’ sai kuma ta rufe kawai ta cigaba da murmusawan. Duk yanda Salima ta kai da sakata surutun banza ta gagara hakan yasa ta dubeta kamar wacce ranta ya ɓaci tace,

“Na ga tun ɗazu ina ta surutu ke kin yi shiru kina jina ko buɗe bakinki bakya yi.”

“Rayuwar ce sai a hankali Salima, mutum yana girma yana ƙara hankali. Yanzu surutun ne bana son yi saboda wasu dalilai. Bari in ɗaura abincin dare kar maghrib ta mini a kitchen.” Ta faɗi hakan tana miƙewa daga kan ɗaya daga cikin plastic chair da suke farfajiyar gidan.

“Laa ga abinci mun yi da yawa in dai don cikinki ne kaɗai zan saka miki.”

“A’a ki barshi, wani abu nake kwaɗayi ba wai abinci ba.”

“Ai kuwa kwana biyu baki yiwa masoyinki cookies ba.”

HJ yana jin an ambaci cookies ya je gurin Juwairiyya yana cewa,

“Tutis, Tutis.”

Murmushin ƙarfin hali wannan karon ma tayi kana ta shafa kanshi kaɗan ta ce,

“Mu je in maka Muhammad Hafiz. Cookies ba zai haɗa faɗa ba.”

Da haka Salima ta ja kujerarta zuwa bakin kitchen ɗin Juwairiyya babu ko kunya ta fara mata labarai har take faɗa mata wai ta fara driving lessons ɗin. Amsar da take samu daga gurin amaryar tata sune ‘Ayya’ ‘Allah sarki’ ‘Sai a hankali’ ko kuma ‘Allah Ya kyauta’. A haka ta musu cookies ita kuma tayi fried couscous mai egg ta basu nasu ta shige da nata ɗaki ta kulle ƙofarta, daga nan bata sake fitowa ba sai safiya.

A bakin ƙofar Salima ta mata sallama ta wuce makaranta, tana dawowa kuma ta ce ta dawo ta kule ɗakinta. Haka rayuwar tasu ta ci gaba da zama wanda wani lokacin sai Salima ta daidaici lokacin da Juwairiyyan take girki sai ta je ta zauna mata wai ta zo tayata hira, sai dai har ta gama soki burutsunta Juwairiyya baza tace uffan ba balle a kaita gaba. A yanda ta lura Salima bata faɗin abun da bai faru ba saboda tana gudun a in ranar bankaɗa ya zo a kamata, a’a maganar da aka yi take murɗawa ta yanda ko an titsiyeta tana da hujja sai dai ta rakuɓe da cewa ita ce bata gane kan zancen ba. Wannan kenan.

Watan Muhammad bakwai da tafiya Salima ta zo ta samu Juwairiyya har cikin falonta tana cewa,

“Dama akwai wani surprise da zan faɗa miki shi yasa na hana kowa faɗa.”

Juwairiyya da she is not interested da duk wani surprise daga bakin Salima ta ce,

“Allah Sarki. Me ya faru?”

“Zan je UK gurin Baban Hafiz zan yi sati uku ko wata ɗaya.”

Dumm gaban Juwairiyya ya buga domin ko ɗazu kuwa sun yi waya da Muhammad ɗin wanda shima a yanzu ya koyi kiranta sai dai idan sun tambayi juna rayuwa basa wani dogon hira zasu yi sallama sai kuma bayan wani kwana ukun ko ma huɗu. Video call kuwa har yanzu ta ƙi yarda su yi musamman yanzu da tayi rama mai muni har ana iya ajiye sabulu a ƙashin wuyarta. Duk kuma lokacin da aka mata maganar ramar sai ta ƙara shiga damuwa musamman in Mama ce tayi maganar, don sai tayi ta mata faɗa wai ta saka damuwa a ranta da sauransu.

Wato ita tana nan cikin damuwa tana ramewa su kuma suna can suna soyayya shine har da biya mata kuɗin jirgi ta je duboshi ko? Ita kuma fa? Ko da yake bata da mamora da farare masu manyan cinyoyi ake yi ba irinta ba.

“Masha Allah. Abu yayi kyau, yaushe zaki tafi?”

“Next week In sha Allah. Hmm kuma kin san me? Baban Hafiz ne ya biya kuɗin jirgin duk da cewa rayuwar tamu sai godiyar Allah.”

“Sai a hankali. To Allah Ya kaimu da rai da lafiya.”

“Ni fa na ɗauka zaki ɓata rai ki ce ban faɗa miki da wuri ba.” Salima tayi suɓul da baka domin ba haka ta so ba.

“Ahh haba dai, wannan ba komai bane akan abubuwan da suka faru a rayuwata. Kar ki damu, na tayaki murna.”

Da haka Salima ta tashi zata tafi, har ta je bakin ƙofa ta dakata ta ce,

“Yauwa zan bar Masoyinki saboda yana school kuma kin san tafiya irin wannan ba’a zuwa da yara.” Da haka ta kwashe da dariya ta fice da bar Juwairiyya zuciyarta na tafarfasa kamar ta bita ta faɗa mata dukkan abun da yake ranta amma ba zata yi ba.

Ta sani da gayya ta mata haka saboda ta jima tana cakalarta tana kuma ƙoƙarin ta sakata magana amma bata samu wannan damar ba shine yanzu zata ɓullo ta nan? Rai na ƙuna ta dannawa ƙofarta lock kana ta shige cikin ɗakinta hawaye na bin ƙuncinta babi babi.

Mum Fateey 👌

Tun lokacin da Juwairiyya ta samu labarin tafiyar Salima UK zuwa gurin Muhammad sai ta kasa kwantar da hankalinta wanda ita ta rasa gane dalilin hakan. Ba matarshi bace? To me yasa don ya zaɓeta sai kuma ta ji haushi ta kasa sukuni? Sai dai duk yanda take ji a zuciyarta ta ƙi nunawa Salima saboda ta sani idan har ta gane ranta ya ɓaci to tabbas zata cigaba da shuna mata tafiyar a fuskarta har sai ta daina numfashi.

Kwana biyar da haka Salima ta kawo mata kayan HJ tare da wasu kayan abinci da zasu iya ɓaci idan ta barsu, a nan take cewa,

“Kin ga tafiyar sai ta zo a daidai kin samu hutun makaranta kun gama aji biyu. Da safe in kin shiryashi ƙanina Salim zai taho da mota ya kaishi, idan kuma an tashi zai je ya ɗaukoshi ya dawo miki dashi. Motar tawa kuma zan barta a gidanmu saboda a samu ana kunnata kar ta jima a zaune, da nayi niyyar bar miki kina fita da ita sai na tuna ashe baki iya mota ba.” Yanda ta faɗi maganar tana dariya kamar mai zolaya sai wani da yake kusa dasu yayi tsammanin duk duniya babu wanda ya kaisu zaman lafiya da fahimtar juna.

Amma Juwairiyya ta fi kowa sanin menene a zuciyar uwargidan tata, hakan yasa tayi ɗan murmushin yaƙe wanda a yanzu itama ta fara koyan wannan halin da tace ba zata koya ba wato kissa. A da in aka ce mata zata iya ɓoye fushinta a zuciyarta ta nuna rashinsa a fuskarta zata ƙaryata mutum, amma bahaushe yayi gaskiya da yace ‘Zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farar kai’. A hankali itama ta fara danne zuciyarta tana haƙuri ba tare da ta nuna gazawarta a idon duniya ba.

“Babu matsala, hakan ma ya yi.” Shine kaɗai abun da ta faɗa ta bar Salima na ɓaɓatunta har tana faɗa mata wai Muhammad yace ji yake yi kamar ya jawo kwana biyun da suka rage su zama yau, wai saboda yana son nuna mata wasu guraren tarihi da na buɗe ido.

Kowanne babba mai hankali ya san idan ta tafi sai an yi kwana uku basu ga hasken rana ba dalilin wata bakwai da yayi babu mace mai ɗumama mishi shimfiɗa. To shine don tsabar rainin wayo da son ƙuntata mata shine zata faɗa mata maganar banza wai yana son nuna mata guraren tarihi? Lallai Salima ta raina mata wayo.

Ranar tafiyar har Airport Juwairiyya ta raka Salima bayan ta matsa mata wanda ƴan’uwan Saliman da suka zo mata rakiyan suma suka saka baki. Bata so hakan ba amma dole ta yarda suka shiga motar Salima ta zauna a gaban mota ita da Salim da HJ a cinyarta wanda bai gama gane cewa wai uwarshi tafiya zata yi ta barshi ba. A bayan mota kuwa Salima ce tare da Mamanta da ƙanwarta guda ɗaya suna ta hira tsakaninsu sun bar Juwairiyya da kallon titi tana wasa da yatsun HJ, har suka isa Airport ɗin Gombe wanda daga nan zata sauƙa a Abuja sai kuma UK ba su mata magana ba. Tun tana ƙaƙalo murmushi har ta ji kanta ya fara sarawa ba zata iya ba ta maida fuskarta neutral.

A nan suka tsaya bankwana tana gefe ita kaɗai domin shi ma HJ ya tafi gurin mamanshi yana riƙe da ƙafarta yana kuka da aka faɗa mishi wai zata shiga jirgi ta tafi.

“To Amarya, ga amanar ɗana da gidana don Allah ki kula da su kafin na dawo. Baban Hafiz kuwa zan ce kina gaisheshi duk da cewa baki faɗa ba kuma baki bada wani aika a kai mishi ba. Allah Ya sadamu da alkhairi.” Faɗin Salima kenan da ta zo gurin Juwairiyya bankwana.

“Amin, Allah Ya kai ku lafiya.” Ta amsa ba tare da tayi murmushin pretending ɗin ba saboda ta gaji.

Da haka Salima ta juya ta tafi ta ƙara komawa cikin ƴan’uwanta ana ta bankwan ƙure haushi wanda wacce ake yi domin nata ta cika tayi fam, amma bata buɗe bakinta tace komai ba illa juyawa da tayi daga barin kallonsu har Salima ta tafi su kuma sauran suka taho.

“Allah Sarki, tafiyar ƴar’uwar taki ce yasa jikinki yayi sanyi ko? Ai in kana zaune da mutum yau aka ce maka ya gusa sai ka ji babu daɗi. Idan ba zaki iya zama ke kaɗai ba ga Salwa sai ta tayaki zama kafin ƴar’uwar taki ta dawo.” Wannan faɗin Maman Salima kenan bayan ta iso gurinta.

Ai da sauri Juwairiyya ta kaɗa kanta sannan ta tuna tana da baki ta ce,

“A’a babu komai. Zamu iya zama mu kaɗai, kuma dama nima akwai ƙanwata da zata zo mini hutu.” Tayi ƙarya domin ta sani ba zata taɓa shiryawa da yarinyar ba don tana da raini. Kuma ƙarya ne gulma ne zai kawota ba wai don ta tayata zama ba, yoo in ma taya zaman ne ita bata da dangi ne?

Maman Saliman tsare Juwairiyya tayi da ido tana murmushi kamar mai karantarta, wanda da wani zai gani ba zai taɓa cewa na mugunta bane amma ita Juwairiyya tana karantarsu tsaff wanda har hakan mamaki yake bata. A nan kuma ta ƙara tabbatarwa kanta cewa Salima ta koyo makircinta ne a gurin uwarta, wannan gaskiya ne da bata ko tsoron kaffara.

“To shikenan, mu tafi gida.” Ta faɗa tana mai shigewa gaba iyalan nata suka rufa mata baya.

Sai da suka fara ajiyeta da HJ a gida wanda yake tsunduma ihu sannan suka tuƙa motar Saliman suka tafi. Dama ita bata taɓa shiga motar ba sai yau da aka matsa mata aka kuma sakata rakiyan dole, to anyi na farko an yi na ƙarshe, an sha ta kuma ta warke.

HJ na kuka ta buɗe musu gate suka shiga gidan, sai ta tuno ranar tafiyar Muhammad da Salima ta mishi rakiya haka ta dawo cikin gidan tana jin tsoro tare da son Salima ta dawo su zauna su biyu, amma a yau sai ta ji gidan ya mata daɗi har wani iska ne yake busawa yana shiga gaɓɓan jikinta. A yanzu kam bata ƙi Saliman tayi ta zamanta a can tare da shi ba amma dai ta tafi da ɗanta, wanda a yanzu yayi hanyar ƙofar uwar tashi yana kuka fuska baja-baja da majina da hawaye.

“Hafiz kalleni nan. Ka daina kukan nan anjima Uncle Salim zai zo ya ɗaukeka ya kai ka gurinta, amma in ka cigaba da kuka zan kirashi in ce kar ya zo saboda baka jin magana.”

Da wayo da dabara ta sakashi yayi shiru kana ta jashi zuwa ɗakinta. Bayan awa biyu da haka Salima ta kirata wai ta isa Abuja lafiya gobe kuma jirginsu zai ɗaga zuwa UK. Juwairiyya ji tayi kamar tayi blocking ɗinta domin ita har ta fara mantawa da ita, sannan ta sani zata yita kiranta ne tana damunta. Amma bata isa tayi hakan ba domin kuwa dole Saliman zata so ta ji lafiyan ɗanta da ta bar mata.

Washe gari da jirginsu ya ɗaga, Muhammad ne ya kirata yace gashi nan ya ɗauko Salima a airpot ta isa lafiya, yanzu suna cikin Taxi da zai kai su masauƙinshi.

“To yayi kyau.” Ta amsa tana jin kamar ranta zai fita domin daga yanda yake magana ta san Salima ta birkitashi domin muryarshi ta canja ba kamar yanda ta saba ji ba.

Bata jira me zai ƙara cewa ba ta kashe wayarta ta mayar da kanta kan pillow don dama har sun kwanta, ga HJ a gefenta yana ta bacci ya daina rigima da kukan banzan tun jiya. Sai dai a maimakon Juwairiyya tayi bacci sai idanunta suka bushe tana ta hasko mijin nata da uwargidanta, zuciya na suya tana kuma tsinkewa haka ta raya daren sai goshin asuba sannan bacci ya sureta.

Alarm ne ya farkar da ita ta duba lokaci ta ga ko baccin awa ɗaya bata yi ba, da haka ta miƙe tayi sallah sannan ta wuce kitchen ta yiwa HJ breakfast tare da wanda za’a saka mishin a lunch box ɗin shi, bayan haka ne ta tasheshi a bacci yana layi suka shiga banɗaki ta mishi wanka da brush sannan ta fito ta shiryashi tsaf sannan suka wuce falo yana cin abinci yana kallon cartoon. Shida da minti arba’in Salim ya danna horn a waje domin baya shigowa gidan haka kuma bashi da numbernta ita ma kuma bata nema ba. Da haka ta fitar da yaron har bakin mota ta buɗe mishi ya shiga, a nan kuma Salim ya gaisheta ta amsa sannan tayi komawarta ciki.

Tana shiga ta kulle gate ɗin har da saka lock saboda baccin da yake idanunta da bata yi ba jiya, gashi kuwa Hj ba zai dawo ba sai ƙarfe biyar na yamma wanda abincin ranarshi ma ita zata yi Salim ya zo ya ɗauka ya kai mishi da azahar. Ta sani sun yi hakan ne don su takura mata saboda in ba haka ba, me yasa ba za’a dinga saka mishi abincin daga gidansu Salima ba tunda Salim ɗin daga can yake? Hakan bai fi musu sauƙi ba? Saboda duk wannan sintirin idan kuma aka tashi daga school ɗin shi zai ƙara fita ya ɗaukoshi ya kawo mata! To amma tunda hakan suka zaɓa a je, domin in sun yi hakan don su takura mata ne suma basu huta ba. Sannan girkin rana tana da leftovers da yawa a fridge da ɗauka kawai zata yi ta ɗumama da ko mutum ya fi shaiɗan sharri ba zai gane cewa daga fridge yake ba, perks of being a chef.

Kwana biyu da haka aka kira Juwairiyya da number UK wanda tana gani ta san Salima ce.

“Amarya nayi sabon number shine nace bari in kiraki kiyi saving ɗinta ba sai mun dinga magana da na Baban Hafiz ba. Kuna lafiya?”

“Allah Sarki. Lafiya kalau. Ya UK?” Sai da ta furta tambayar tayi nadama don a da bata tambayi Salima komai ba ma tana shan takaici balle yanzu da ta nema da kanta.

“UK lafiya kalau amma har yanzu Baban Hafiz bai kaini na ga gidajen tarihin ba wai sai na huta gajiya. Kullum fa ina ɗaki sai yau na samu muka fita ya saya mini sim card muka zaga Campus ɗinsu muka dawo.”

“Ayya.” Juwairiyya ta amsa tana jin kamar tayi amai idan ta haskosu manne da juna.

“To na gaisheki, idan Hafiz ya dawo daga school zan kira mu gaisa. Ohh ga Baban nashi ma ya dawo dama ya ɗan fita ne zai sayo abu. Sai anjima.” Ta kashe wayarta.

“Munafukar banza munafukar wofi.” Juwairiyya ta furta a hankali tana mai ajiye wayar tata a gefe.

Har zata juya ta tafi dama ta saka wayar a charge ne ta ji ta fara ringing ta juyo ta ga sunan Muhammad. Ba yanzu Salima tace ya dawo ba? Me kuma zai sa ya kirata? Kamar ba zata ɗauka ba amma ta tuno maganganun Hafsat da take faɗa mata wai kar ta bari Salima ta gane tana raina Muhammad ko kuma tana faɗa da shi.

“Hello.” Ta faɗa cikin sanyin murya tana jiran ta ji kibiyar da za’a kuma caka mata a ƙirji.

“Kina lafiya?”

“Lafiya kalau. Ya karatu?”

“Alhamdulillah. Yanzu nake ganin wani Apron da chef hat mai kyau sai na tuna ke ce kike sakawa in zaki yi girki. Kina so in saya miki Salima ta kawo miki?”

Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauƙe domin ba haka tayi tsammani ba, ita tuni tayi readying mind ɗinta akan zata ji mara daɗi ashe mai daɗi ne yake zuwa. Idanunta ne suka ciko da kwalla tayi murmushi kaɗan wanda ta ji kamar ana squeezing ɗin zuciyarta ta ce,

“Kana ina?”

“Ina cikin wani ƙaramin store ne. Wani abu ne?”

Girgiza kai tayi kamar yana ganinta tana jin sanyi a ranta ta shanye hawayen da suka taru mata a ido ta ce,

“Babu komai, kawai na ji hayaniya ne.” Wanda da gaske ta ji hayaniyar yanzu na wasu maza suna magana.

“Ohh. Kina so?” Ya sake tambayarta nervously.

“Ina so. Nagode sosai.”

“You are welcome.” Yanda yayi maganar kamar wani baturen England yasa tayi dariya.

“Yaya dai? Me ya baki dariya.” Ya tambayeta da mamaki a muryarshi.

“You sound just like them.”

“Them? Su waye?”

“Turawan England.”

Dariya yayi, one hearty dariya wanda sai ta kasa ko numfashi mai ƙarfi gudun kar bata ji wani sound ɗin ba. Dariya dai Muhammad yake yi kuma wai ita ta sakashi! Rabon da ta ji dariyarshi har ta manta, saboda kullum wayarsu business like ne, ya kike, ya kake, ya karatu, zamu fara exams, yau an yi test da ya bani wahala, zan je gidan wance, ina bukatar kaza nawa ya kare, ya Nigeria, ya London? Haka wayar su take kullum babu wani magana mai ɗauke da affection balle dariya ya shigo ciki.

“Na daɗe ban yi dariya irin haka ba.”

Har zata ce ‘kai da kake da matarka a kusa ai tana sakaka dariya’ sai kuma ta datse harshenta domin she might sound jealous or whiny.

“Sai ka biyani ladan dariyar da na sakakan?”

“Zan biya, amma da wani abu zan biya?”

Ji tayi zuciyarta tayi skipping bugawa domin yanda yayi maganar sosai ya karya mata duk lagon jikinta. Ta sani kuma zata iya rantsuwa ya san me ya yi! Why is he cruel? Gwanda shi yana tare da matarshi amma ita fa? In ba don tashin hankalin da take ciki da fitar da rai da rayuwar duniya ba da wata bakwai ya mata yawa bata nemi mijinta ba. Amma a yanzu yayi awakening wani monster da ya daɗe yana bacci hankalin kowa a kwance.

“Don’t! Please.” Shine kaɗai abun da ta faɗa muryarta na rawa kaɗan.

“Sorry. Sai anjima.” Ya faɗa cikin murya mai sanyi sannan ya datse kiran nasu.

Juwairiyya zama tayi a bakin gado tana jin hawaye na taruwa a idanunta, wannan shi ake kira bitter-sweet phone call.

Duk yanda Juwairiyya ta kai da kaucewa Salima abun ya gagara domin kullum idan suka fita yawon buɗe ido da Muhammad sai ta turo mata pictures ɗinsu ta whatsapp. Nan ya rungumeta, nan ta maƙale wuyanshi, nan kuma yana kallon camera ita kuma tana kallonshi haka dai. Wani guri yana tsume kamar yanda ta sanshi wani guri kuma yayi murmushi, a cikin pictures ɗin ne ta ga inda ya fi ko’ina tsumewa, Salima ce zaune a kan cinyarshi kaɗan yayin da shi kuma yake zaune akan wani irin Side bench da ake ajiyewa a public Sidewalks, yanda take murmushin kai idan ka gani kasan forcing ɗinshi tayi. Ko ba’a faɗa mata ba ta san cewa wannan style ɗin hoton Muhammad bai so shi ba amma ta matsa mishi, kuma a yanda yake lukuti itama lukuta wannan ba irin nasu bane.

Ji tayi dariya na son kwace mata amma ta danne, can ta wangale baki tana ƙyaƙyatawa da dariyan domin ta kasa danneshi, tsabar mugunta har sai hawaye ya zuba a fuskarta. Sai da ta tsagaita da dariyan tayi istigfari domin an ce irin wannan dariyan babu kyau a musulunci. Sai dai tana ƙara kallon hoton ta ƙara kwashewa da wata hatsabibiyar dariyar har tana sauƙa ƙasa ta kifu a kan tiles. Wato duk cikin salon Salima ta bata haushi ne amma ƙarshe ya sakata dariya saboda basu yi kyau ba. Ai Allah ba azzalumin bawan Shi bane, sai dai bawa ya zalunci kanshi.

Tun tana buɗe messages ɗin Salima har ta daina domin abun nata ya fara yawa, bata tunanin ko ƴan’uwanta tana tura musu pictures ɗin da take tura mata. Yanzu kam ba zata iya ba, da tana buɗewa ne don kar Salima ta mata sharri amma sai ta ga koma menene tayi sai an ɗana mata, to me yasa zata yi torturing kanta sannan daga baya ta zo bata tsira ba?

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Salima tayi wata ɗaya ta dawo Nigeria, babu yanda ƴan’uwan Salima basu yi ba wai ta rakasu ɗaukota a airport amma ta ƙi amincewa. HJ dai ta mishi gayu domin kuwa har sabon aski ta kaishi aka mishi ana washe garin Maman nashi zata dawo. Haka suka ɗauki yaron suka barta a gida ta zauna zaman jiran uwargidan tata.

Ta mata abinci har kala uku wanda har cikin zuciyarta ta ji ya cancanta ta mata saboda tafiya tayi kuma gidansu ɗaya ba wai gida daban-daban ba. Tana shigowa kuwa ta je har falonta fuskarta babu yabo babu fallasa ta mata sannu da dawowa sannan ta fita ta basu guri duk da cewa Saliman tace ta zauna su yi hira amma ta ƙi, saboda ta san ko ta zauna ƙarshenta su ƙunduma mata baƙin ciki ne ta kasa bacci.

Sai can Salima ta aiko ƙanwarta Salwa wai ta zo za’a buɗe tsaraba, dariya Juwairiyya tayi a ranta tana jinjina ƙarfin hali irin na Salima.

“Ayya zan ɗaura mana girkin dare ne, ta buɗe kawai zan shigo.”

Tana faɗin haka ta tashi ta shige kitchen ta ɗaura musu tuwo domin na daren ma zata bata haka kuma na gobe da safe, daga nan ne zata yanke bata abincin kowa yayi ta kanshi kamar yanda suka saba tun a baya.

Tana aiki a kitchen ta hango Salima ta window tana zuwa wacce da hasken rana ya dalli fuskarta sai Juwairiyya ta ga kamar ma yalƙi take yi, ta ƙara haske ta ƙara ƙiba in tana tafiya albarkatunta sai jijjiguwa suke yi. Kawar da kai tayi daga barin kallonta har ta iso hannunta ɗauke da ledoji uku tana cewa,

“Tunda kin ƙi zuwa ga tsarabanki, wannan ni na saya miki.” Ta miƙa mata ledan farko ta ƙarɓa ta buɗe ta ga wasu English wears ne wanda daga gani zasu yi tsada sai dai sun mata yawa, a yanzu da ta rame ko ta saka ba kyau zasu mata ba. Ko dai da gangan Saliman tayi haka? Kawar da wannan tunanin tayi a zuciyarta domin in ta cigaba da zargi watarana sai ya kaita kabari.

“Kai Masha Allah. Yayi kyau wallahi, nagode.” Ta faɗa with sincere smile a fuskarta.

“Wannan ma ni na saya miki.” Ta karɓi ledar ta ga Handbag ne mai kyau, wannan karon murmushinta ya fi na ɗazu yawa domin Handbag ɗin ya tafi da imaninta ba kaɗan ba.

“Wow! Gaskiya yayi kyau. Nagode sosai Allah Ya saka.” Ta faɗa cikin murna da farin ciki tana juya jakan.

Salima binta tayi da murmushin mugunta sannan ta miƙa mata ledar ƙarshen ta ce,

“Wannan kuma daga Muhammad ne.”

Juwairiyya na jin an ambaci sunanshi zuciyarta tayi wani sanyi domin ko bata buɗe ba ta san Apron ɗinta ne da Chef hat da ya saya mata. Har zata ajiye ledar ba tare da ta buɗe ba Salima ta dakatar da ita,

“Kin san yanda Apron ɗin nan ya mini kyau? Ni da ya kawo ma na ɗauka ni ya sayawa har ina ta murna sai yace ai ke ya sayawa kuma ya faɗa miki da ya bani. Muka je har Store ɗin da ya saya aka ce ai ba zamu samu irin shi ba saboda Handmade ne irin dai wanda ake yi ba za’a sake yin kalanshi ba. Ni kuma ya shiga raina na faɗa mishi ai zan koma gida mu sasanta tsakaninmu da mutumiyar tawa, ya ce babu ruwanshi mu ne ɗaya.” Ta ƙarisa maganan tana dariya.

Zuciyar Juwairiyya ce ta kasa gaskata zancen domin bata taɓa ganin Salima ta saka Apron ba tun da take da ita da har zata nace lallai tana son wannan. Menene a jikinshi da har ya saka ta kasa haƙuri ta tambayeta ta bata?

“Ikon Allah. Bari mu ga Apron ɗin.”

Da haka Juwairiyya ta saka hannu a ledar ta ciroshi kana ta buɗe tana gani. Ji tayi kunya ya rufeta domin wannan ba Apron ɗin da ake shiga kitchen da shi bane, wannan Apron ne da ake shiga bedroom dashi a tashi kan masu gida masu kawo abinci! Tabbas ko dai Muhammad ya san me yayi ko kuma da gaske kyau kawai ya mishi ya saya mata.

Juwairiyya kasa magana tayi tana juya Apron ɗin sannan ta ciro hulan wanda shima kamar chef hat ne amma da ears ɗin Bunny a sama an rubuta ‘Daddy’s Girl’. Dariya ta ji ya kwace mata tayi saurin rufe bakinta tana kallon Salima wacce ta fara canja yanayinta daga dariya zuwa murmushi can kuma ta haɗe rai.

“Baki ce komai ba.” Ta faɗa tana ƙaƙalo murmushi wanda bai kai idanunta ba.

Har Juwairiyya ta buɗi baki zata ce ‘ki ɗauka’ sai ta ji ƙarar shigowar message wayarta wanda tana juyar da kai ta ga sunan Muhammad ne tayi saurin ɗauka ta buɗe.

‘Ga Apron ɗinki an kawo miki and I hope you like it kamar na so shi. Duk da ma kina mini rowan Apple zan so idan na dawo ki saka ki bani in ci. Please.’

Juwairiyya ji tayi kamar ta nitse ƙasa don tsabar kunya da wani abu da take ji a jikinta, yaushe Muhammad ya san kink irin haka? Zamanshi da turawa ko kuma tun da yana dashi bai taɓa nunawa bane sai yanzu?

“Ke nake jira fa.” Wannan karon Salima tayi maganar cikin ɗaga murya alamar haƙurinta ya fara ƙarewa.

Juwairiyya da har ta manta da tsayuwarta a gurin ta dawo daga naughty duniyar tunanin da ta shiga ta ce,

“Umm, kika ce yaushe zai dawo?”

“Nan da wata huɗu, kenan idan ya cika shekara da tafiya. Me yasa kika tambaya?”

“Babu. Amma kiyi haƙuri, I’m keeping it.”

Wohoho!!!

Mum Fateey 👌

“Babu. Amma kiyi haƙuri, I’m keeping it.”

Wannan magana ta Juwairiyya ba ƙaramin bawa Salima mamaki da kuma baƙin ciki yayi ba. Ba haka ta so ba, bata kuma yi tsammanin zata iya hanata ba shiyasa ta fara bata da tsaraban da ta mata duk da cewa iyakacin English wears ɗin ta saya mata kuma ta sayi oversized ne don tayi mocking ɗinta ta ajiyeshi ba tare da ta saka ba, ta nan kuma zata samu abun faɗi kan cewa ta saya mata tsaraba amma bata taɓa ganin ta saka ba. Hand bag kuma kanta ta sayawa amma ta ɗauka ta bata saboda tana son ta ji kunya gami da nauyin hanata as silly as Apron bayan ita ta kawo mata abubuwan da suka fi shi kuɗi.

Bata san yaushe Muhammad ya sayi Apron ɗin ba haka kuma bata ganshi cikin kayanshi ba har sai da ta fara haɗa kayanta don dawowa ya ɗauko ya bata yace ga aikan Amaryarta. Da tace mishi zata buɗe ta gani bai hanata ba, sai dai tana dubawa ta gane na menene amma mutumin nata bai bata fuskar da zata tsokaneshi ko kuma ta faɗa mishi wani abu ba.

“To ni ina nawa Baban Hafiz?” Yanda tayi maganar kalar tausayi ta san cewa he will feel guilty don ya bata duk da ma ta sani ita ba shiganta zai yi ba.

“Guda ɗaya na gani irin shi amma idan kina so zan duba shagon in saya miki kema.”

Haka aka yi washegari gari suka je tare amma suka duba babu irinshi sai dai ire-irenshi. A nan yace ta zaɓi wanda take so amma ta duba ta ga babu wanda ya mata sai wanda ya sayawa Juwairiyya.

“Ni wancan ɗin ne ya fi mini kyau, ka saya mata wani sai in ɗauki wancan.”

“Ko kin ɗauka ya miki kaɗan Salima, kuma ta san na saya mata da sai in ce ki ɗauka.”

“Kana so ka ce ni ƙatuwa ce ko Baban Hafiz?” Ta yi maganar a shagwaɓance amma nan cikin zuciyarta ji take yi kamar ana hura mata wuta.

“Ki yi sauri ki ɗauka ina da abun yi.” Ya yi maganar fuskarshi a murtuƙe don shi bai ga abun tashin hankali a ciki da zata ja maganar yayi tsayi ba.

Da haka ta rufe bakinta suka dawo gida tana kissima yanda zata raba Juwairiyya da wannan abun domin ta sani shiri suke yi tare na haɗuwarsu shine har da ɗan iskan Apron don ƙarawa haɗuwar tasu armashi. Da wannan tunanin ta dawo Nigeria ta kuma ɗauki jakarta mai tsada da ta sayawa kanta ta bawa Juwairiyya amma ta hanata ɗan banzan Apron ɗin ƴan iska.

“Haba Amarya, yanda na saka rai a abun nan kar ki hanani shi. Don wallahi Baban Hafiz zai mini dariya yace ina faɗin kanmu a haɗe ya ke amma ke kin bada ni.” Ta gyara tsayuwarta domin bata karaya ba.

“To ai ko na baki ba size ɗinki bane ba zai shigeki ba. Kuma dama nima bani da irin shi, amma ga wani zai shigeki bari in baki.” Da haka Juwairiyya ta juya mata baya ta buɗe kitchen cabinet ɗinta na sama ta jawo Apron guda biyar ta mikawa Salima babban cikinsu tana cewa,

“Ga wannan dama ban taɓa sakashi ba saboda ya mini yawa. I hope you will like it.” Ta murmusa wanda murmushin har cikin zuciyarta ce saboda tana cikin nishaɗi musamman idan ta ga Salima tayi yaƙe wanda ya fi kuka ciwo.

“To nagode.” Ta faɗi hakan tana waftan Apron ɗin ko warwareshi bata yi ba ta bar bakin kitchen ɗin ta nufi ɗakinta rai a ɓace.

Tana shiga ta jefar da abun hannun nata a kan kujera ta shige ɗaki duk da kiran da ƴan’uwan nata suke mata amma ta musu banza. Zuciyarta na tuƙuƙin baƙin ciki don Juwairiyya ta ɓata mata plan, na farko ta so ta hanata sakawa ne don kawai Muhammad ya rasa abun da yake so ɗin daga gareta. Na biyu kuma da Juwairiyyan ta bata itama ba sakawa zata yi ba saboda ba zai shigeta ba, ita dai ajiyeshi zata yi kowa ma ya rasa. Na uku kuma ta nan zata haɗawa Juwairiyya wani tuggun domin zata cewa Muhammad ai tana tambaya ya bata saboda ya ga kamar bata ɗauki interest ɗin shi da muhimmanci ba. To duk wannan shirin Juwairiyya ta wargaza mata, sannan wani ƙarin takaicin ga kuma Handbag ɗinta da ta saya mai tsada da kuɗinshi zai kai dubu saba’in in aka canja da kuɗin Nigeria. Rai na suya ta kira mamanta a waya ta ɗauka.

“Mama ina tunanin yarinyar nan ta gane, shi yasa tun kwanaki nace miki shirunta yayi yawa bata ɓarin zance kika ce damuwa ce amma yau ita ce har da faɗa mini baƙar magana sannan ta ƙunsa mini baƙin ciki.”

“Me kuma ya faru daga dawowanki?” Maman ta tambaya hankalinta a tashe.

Nan Salima ta bata labarin abun da ya faru har da cin mutuncin da Juwairiyya ta mata da ta bata wani banzan Apron da ake sayarwa dubu ɗaya ko biyu.

“Idan ta gane sai me? Ai kin mata nisan da ba zata iya ko kamo ƙafarki ba. Don yanzu ne ma zaku yi zaman da zaki fi morarta domin tana ji tana gani zaki canja kowanne labari ta kuma kasa nunawa mutanen duniya gaskiya. Ba kin ce zaki zo gobe ba? Ki bar maganar sai kin zo don na ji kamar Salwa ce ke kiranki.”

“Ita ce, sun ga na shigo rai a ɓace ne shiyasa hankalinsu ya tashi suke ta kwala mini kira.”

“Amma dai ke shashasha ce Salima! Don me yasa zaki nuna mata ranki ya ɓaci? lafiyarki kuwa ko dai kin fara manta karatun mu ne?”

“Ki yi haƙuri Mama.”

“Kar ki sake bari ta gane ranki ya ɓaci, zama kuma na faɗa miki yanzu zaku yi wanda zaku gogi juna, ina son ta shiga damuwa ta ƙare ya zama bata da wani mamora a jikinta, wannan shine sakayyarta na aure miki miji. Ki kuma saka a ranki ba mugunta kika mata ba, a’a kin rama abun da ta miki ne saboda an ce ‘Rama cuta ga macuci ibada’. Sai gobe kawai in kin zo zamu ƙarisa maganan.”

A gefen Juwairiyya kuma sai da ta ga ƙulewar Salima ɗakinta sannan ta tuntsire da dariya kana ta jawo wayarta ta fara yin text.

‘Wannan Apron ɗin akan atampa ko lace zan saka?’

Ta tura mishi don kawai ta tsokaneshi tana dariya ta ajiye wayar ta ci gaba da aikinta.

Har da gama tuwon bata bi ta kan wayar ba, a haka ta ɗauki na Salima ta kai mata ta samu ma ƙannenta har sun tafi da yake magriba tayi.

“Kai mun gode da ɗawainiya fa, sai yanzu na samu na ware Apron ɗin da kika bani, ashe shima yana da kyau kuma size ɗina ne. Wancan kam ina ganin ko nonona ɗaya ba zai rufe ba kin san Allah Ya hore mini su.” Salima tayi dariya kamar ba baƙar magana ta yaɓawa Amaryar tata ba.

Har cikin ranta Juwairiyya ta ji haushi wanda duk iya ƙoƙarinta na ganin ta ɓoye sai ta kasa, kenan tana mocking ɗin jikinta ne? Ai kuwa ta fi kowa sanin cewa jikinta mai kyau ne da bata jin tsoron tsayawa a gaban miji, in ba don yanzu da ta rame ba bata isa tace zata kusheta ba, ta sani ita ba perfect bane amma Allah Ya mata ƙira mai kyau kuma mai janye hankalin duk wanda aka kyallarawa ya gani.

“Gaskiya ne kuma fa, ku kam irinku sai an dangana da company an basu measurement. Bari in je in yi sallah kar lokaci ya ƙure, in baki ganni ba sai da safe kema ki samu ki huta. Hafiz zo mu je mu kwanta.” Ta miƙa hannunta ga yaron da yake maƙe a kan cinyar mamanshi.

Kallonta yayi ya mata dariya sannan ya tashi da niyyar zuwa gurin nata amma Salima ta riƙeshi tana cewa,

“A’a ka bar Aunty Amarya ta wataya ai yau kam zata so ta huta da fitinanka.”

“Ni bai fitineni ba, zamanmu muke yi abun mu muna ɗebewa juna kewa.” Tayi saurin faɗa gudun kar Salima ta je da canja mata magana.

“Ai kuwa.” Salima ta murmusa tana jin kamar ta je ta shaƙe wuyan Juwairiyya.”Yau zamu kwana muna hira da ɗan ɗakin naki ai.” Tayi finalizing zancen akan dai ba zata bar yaron ya kwana gurin Juwairiyya ba.

“Yau dai Mamanka ta mini rowanka, to sai da safe mu kwana lafiya.” Da haka ta fice ta basu guri dama itama ba wai da gaske take yi ba, kara kawai ta mata duk da ma bata cancanci hakan ba.

Sai da tayi sallah ta jawo wayarta wacce tun ɗazu ta lura Muhammad ya mata text amma bata buɗe ba.

‘Bamu yi haka da ke ba, shi kawai nake so.’

Murmusawa kawai Juwairiyya tayi kana taci gaba da harkan gabanta, ƙarfe tara na daren ta kwanta tana danna wayarta ta ga saƙon Muhammad a whatsapp wanda basu cika magana ta nan ba. Kafin ta buɗe kuwa ta ga ya kirata video call wanda rabon da yayi hakan har ta manta dalilin ko sau ɗaya bata taɓa ɗauka ba, shi kuma da yayi ya gaji ya daina.

Wannan karon ta amsa amma sai ta saka yatsarta ta rufe front camera ta yanda ba zai ganta ba, shi kuma ganinshi tayi tass yana kallon screen ɗin fuskarshi babu yabo babu fallasa. Sai ta ga ya ɗan rame kaɗan amma yayi haske ya mata kyau sosai, me sirrin UK ɗin nan ne da kowa ya je sai ya ƙara kyau da walwali?

“Bana ganinki.” Shine abun da ya fara faɗa yana kallon gefe kaɗan. Zaune yake a kan study chair wanda Juwairiyya ke iya hango wani sashe na ɗakin nashi.

“Ka yi haske sannan ka rame kaɗan.” Ta mayar mishi da amsa tana mai ƙura mishi ido kamar yau ta taɓa kallonshi.

Murmusawa yayi, sannan ya shafi kwantaccen sajenshi ya kalli screen ɗin kamar yana ganinta ya ce,

“Weather ɗinsu ne ya ƙara mini haske, dama ni fari ne.”

“Sannu ɗan fari.”

“Yauwa ƴar baƙa.”

“Zagina ka yi?”

“Yaushe in aka faɗi kalar fatar mutum ya zama zagi? In zagi ne ke kika fara, kin kirani da ɗan fari.”

“You are a racist!” Ta yi dariya kaɗan mai sauti.

“Ki buɗe cameran, I want to see you.” Yayi maganar cikin sanyin murya yana mai ƙara ƙurawa screen ɗin ido.

“Bana so ka ganni haka ne, na rame sosai.”

“Me ya same ki? Baki faɗa mini baki da lafiya ba.”

“Lafiyata kalau. Kawai ramar ce ta zo.” Ta ƙara faɗa ba tare da ta buɗen ba.

“Juwairiyya ki buɗe cameran na ce.” Yayi maganar cikin ɗaga murya kaɗan yana gyara zamanshi. Baya son musu da taurin kai don ba’a saba mishi ba.

“I’m sorry, amma ba zan so ka ganni haka ba. Sai da safe.”

Tana ganin lokacin da ya zare ido kaɗan zai yi magana amma tayi saurin katse kiran ta kashe data tare da sanya wayar a flight mode.

Ji tayi zuciyarta tayi mata nauyi don bata kyauta mishi ba, sannan ta sani ranshi ya ɓaci amma ba zata iya bari ya ganta a hargitse sannan a rame haka ba. Idan ta murmure ta dawo hayyacinta zata bari su yi video call ɗin kamar yanda ya buƙata.

Washe gari Juwairiyya ta musu breakfast har da wanda HJ zai tafi da shi school ta kaiwa Salima wacce tuni ta tashi ta gama shiryashi. Ita da kanta ta kai ɗanta school sannan ta dawo gida ta fara shirin zuwa gidansu, tana gamawa ta yiwa Juwairiyya sallama ta ja motarta ta fita da hantsi.

A nan Juwairiyya ta ji gidan ya mata sakayau tayi kwanciyarta tana mai buɗe wayarta da ta manta ta sakata a flight mode tun jiya. Texts ɗin Muhammad guda uku ne suka shigo ta fara karantawa.

‘Ki kunna data sannan ki ɗauki call ɗin da zan miki.’

Daga jin yanda yayi text ɗin ta san umurni ya bata ba wai roƙonta yake yi ba.

‘Ina ta kiranki ba ya shiga, in kin ga message ɗina ki kirani.’

Da alama bai gane cewa kashe wayar tayi ba ya ɗauka matsalar network ne. Na ukun ne da ta karanta ta ji zuciyarta ta cunkushe tare da fargaba kaɗan da ya shiga ranta.

‘Kiyi duk abun da kike so, ni na baki dama shi yasa kika rainani ba kya bin umurnina.’

Ba dai tayi katoɓara babba bata sani ba? Dafe ƙirjinta tayi da yake dukan uku-uku ta ƙara karanta text ɗin a karo na biyar sannan ta ajiye wayar a gefe tana tunanin ya ya zata yi ta bashi haƙuri don da alama ranshi ya ɓaci ba kaɗan ba. Text ta tura mishi,

‘Kayi haƙuri sannan don Allah kar ka ɗauki hakan a matsayin raini ko taurin kai, wallahi bana son ka ganni haka ne don na rame sosai ni kaina bana son ganin kaina a madubi. Kuma lafiyata kalau kawai stress ne ya mini yawa.’

Tun da ta tura message ɗin har aka yi kwana uku Muhammad bai mata reply ba haka kuma bai kirata ba. Tana son zuwa gida ta ƙara mishi text amma bai kulata ba, ƙarshe zuciyarta na suya haɗe da ɓacin rai ta kirashi sai a lokacin ya ɗauka.

“Hello.”

“Baki iya sallama bane?” Ya tambayeta wanda hakan ya ƙara ɓatawa Juwairiyya rai don ta ga da alama zai fara dawo da halinshi.

“Assalamu alaikum.” Ta mishi sallama ya amsa sannan ta gaisheshi.

“Dama ina son zuwa gida ne.”

“Ba yau ba.” Yana faɗin hakan ya kashe wayar ya bar Juwairiyya da ɗan banzan mamaki.

Haka ta ciro wayar daga kunnenta tana kallo cike da takaici tare da dana sani, dama hauka take yi da zata yi tunanin ita da Muhammad zasu iya rayuwa babu faɗa? Ina kuma ta manta halinshi na saurin fushi da gadara? Da wannan tunanin da kuma wanda yake damunta suka ƙara haɗuwa suka jagula mata lissafinta ya zamana kullum ranta a ɓace yake.

Sai da aka yi sati bata kirashi ba shima bai kirata ba sannan ya aiko Salima wai ta je gidan nasu, wannan abu da yayi shi ya ƙara tunzura Juwairiyya domin bata ga dalilin da zai sa ya faɗawa Salima ba alhali yana da numbernta.

“Wallahi da ya faɗi saƙon sai hankalina ya tashi nace duk yanda aka yi kun samu matsala ne, to shi ko na tambayeshi ba faɗa mini zai yi ba shine nace ke kam zaki faɗa mini don in baki shawara, mutumin namu ni na san kanshi.”

Wani wawan kallo Juwairiyya ta bi Salima da shi saboda wannan karon kam ta kasa ɓoye ɓacin ranta don abun ne sun haɗu sun mata yawa. Sannan rashin kunya da makircin Salima ya isheta ba zata iya ɗauka ba.

“Salima kenan. Ki koma ki tambayeshi wataƙila in kin haɗa da halinki zai faɗa miki.”

“Ban gane ba, wani hali kenan?” Salima ta tambayeta kamar bata san me take nufi ba.

Har Juwairiyya zata buɗi baki ta ce ‘Munafurci’ sai kuma ta fasa ta girgiza kanta domin ta sani babu wanda zai bata gaskiya idan Saliman ta kai ƙararta gaba kan cewa ta kirata da sunan Munafuka. Hatta Mama da Hafsat ba zasu so ta faɗi hakan ba sannan ba zasu goya mata baya ba.

“Mu bar maganan.” Ta faɗa a ƙarshe.

“To shikenan Allah Ya daidaita, amma dai zaman aure sai haƙuri musamman in kika samu mai mata wanda ba rainonki bane.”

“Me kike nufi kenan?” Juwairiyya ta tambayeta da mamaki don bata gane inda maganar tata ta dosa ba.

“Dama ina ta son faɗa miki abun murna sai yau nace bari in miki surprise.”

Juwairiyya tana jin haka zuciyarta ta buga da ƙarfi domin ta sani wata baƙar magana ko kuma labari mara daɗi Saliman zata faɗa mata, wallahi ta gaji da surprises ɗinta saboda kowanne idan an furta zai an bar zuciyarta cikin wahala.

Kasa magana tayi ƙarshe Saliman da take murmushin mugunta ta dafa cikinta ta ce,

“Masoyinki ne zai yi ƙani ko ƙanwa. Ina da ciki na wata ɗaya da sati uku kuma tun a can London muka gane. Ni na ɗauka ma ya faɗa miki amma da na ji baki yi maganar ba sai na tambayeshi ya ce wai ya manta ne bai faɗa miki ba.”

Daram! Zuciyarta ta ƙara bugawa a karo na ba adadi wanda har ta fara tsoron kar watarana tayi bindiga a rasata gaba ɗaya. Wai Salima ce take da ciki? To ita fa? Ko dai ita juya ce? Sannan me yasa suka ɓoye mata sai yanzu zasu faɗa mata daga matar har mijin? Ko don saboda basu ɗauketa da daraja bane?

Wata zuciyar ce tayi saurin kwaɓarta da cewa me yasa take ɗaukan kanta da matsayin da Allah bai bata ba? A kul ta sake tunanin Muhammad ko matarshi zasu mu’amalanceta irin yanda take so. Ƙaƙalo murmushi tayi kana ta yiwa Salima fatan alkhairi sannan tayi dabarar da zata yi ta bar mata ɗaki, bata ƙara minti biyar a gidan ba ta fice ta nufi gidan Hafsat domin sai ta ji kamar ana hura mata wuta ne a gidan ta kasa numfashi tana son fita. Zuciya na ƙuna, idanu na tara kwalla ta isa gidan wanda sai a nan zuciyarta ta samu salama bayan Hafsat ɗin ta bata shawarwari tare da kwantar mata da hankali.

“Aunty Juwai ramar takin nan tana ƙara gaba fa, anya kina cin abinci kuwa?”

“Watarana ina ci watarana kuma ina jin yunwa amma ba zan iya saka ko loma ɗaya a bakina ba. Ni wallahi duniyar ma gaba ɗaya ta fita a kaina, Astagfirullah, Allah na tuba Ka yafeni.”

“Gaskiya kar ki ƙara cewa hakan kam domin duk halin da kike ciki baki kai wasu ba amma haka suke rayuwa, kuma wani abun mu muke ƙarawa kanmu damuwa domin idan muka ɗauki abunda yake faruwa a rayuwar tamu da sauƙi to wallahi sai ki ga ba zamu wahala ba. Ki rage damuwa Aunty Juwai domin na san shine number one problem ɗinki.”

Duk yanda aka kai da bawa Juwairiyya shawarwari ta kasa kwantar da hankalinta domin a yanzu kam ma zaman cikin gidan Muhammad ɗinne bata son yi saboda duk lokacin da ta ji motsi ko muryar Salima sai zuciyarta ta cunkushe. Hakan yasa ta tsiri fita kullum bata gida, daga school sai gidan Mama ko Hafsat ko Iyami wacce har lokacin maganar Salima bai taɓa shiga tsakaninsu ba, sai dai su yi hiran duniya su watse.

Tsakaninta da Muhammad kuwa komai ya ja baya domin ya daina kiranta ko mata text ɗin, sai dai ita da yake dole sai ta nemeshi don tambayan izini ko abun buƙatu na rayuwa. A haka aka shafe wata uku har da sati biyu wanda a nan ne kuma aka fara shirye-shiryen dawowan Muhammad. Ita bata san da dawowan ba sai da Salima ta zo gurinta fuska cike da fara’a take faɗa mata wai zasu yi fentin gidan idan tana so a mata na falo da ɗakinta.

“Ai ni paint ɗina babu abun da ya sameshi.”

“Gaskiya kam don naki bai fi shekara da yi ba. Kin san yanzu da zai dawo dole ne mu yi kimtse-kimtse kar ya zo ya ga guri ba irin can da ya saba ba.”

Faɗin irin ɓacin ran da Juwairiyya ta ji a wannan lokacin ma ɓata lokaci ne, tana ji tana gani Salima ta gama surutunta ta tafi wanda take jinsu kamar sukar kibiya a zuciyarta. Me yasa ba zai faɗa mata yana dawowa ba?

An yi sabon fenti na side ɗin Salima, cikin gida da kuma waje ko’ina ya zama sabo amma banda na Juwairiyya. Ana saura kwana biyu ya dawo ta ga an cire kujerun Salima an saka mata sabo sannan sai ta ga ta tafi kunshi da kitso ita kuma tana nan zaune kamar kazar mayun da aka firgita.

Rama kam tayi shi iya rama har bata son yawo babu hijabi idan sun yi baƙi, hakan yasa duk kaya da ta saka bata gani ya mata kyau shi yasa ma bata damu da yin kwalliya ko gaye ba. Haka nan take zaune zuciya cunkushe da damuwa babu mai fahimtarta ko da tayi magana, sai dai a bata haƙuri sannan a ce ta rage yawan tunani da saka damuwa a rai.

Tun kafin ranar dawowan Muhammad ya zo ta san ba ita zata ƙarɓeshi ba hakan yasa ko kunu wannan bata yi a ranar da zai iso Gombe ba. Sannan kuma har wannan lokaci maganar dawowanshi bai shiga tsakaninsu ba, shi bai faɗa mata ba haka itama bata kirashi ta tuhumeshi ba.

A ranar da zai dawo ƴan’uwa na kusa suka zo gidanshi tarɓanshi, gida ya cika da jama’a wannan yasa itama Juwairiyya ta shige cikinsu ana ta hidima da ita da yake a ɗakinta Iyami ta sauƙa.

“Ke kam ban ga kin yi kitso da lallen ba matar Ya Muhammadu, ko sai jibi in zaki karɓi mutanen London ɗin zaki yi naki kafin nan nata ya koɗe?” Ta faɗi hakan cike da zolaya amma nan tana fatan hakan ne ba wai da gaske matar yayan nata ba zata yi gyaran bane.

Iyami tana tuna yanda ta ga Salima a wannan lokaci sai a ɗauka gasar sarauniyar kyau zata je don tsabar gayu da ado, ta sha dilka, kitso, lalle, kaya mai kyau sannan ga ɗan cikinta na wata biyar da ya bulluƙo kaɗan ana ganinshi ta cikin rigarta. Da kazar kazar da kuma hanzarinta take bada order a yi kaza da kaza duk don a burge mijinta da zai dawo amma banda wannan da ta fara yarda da wani abu da aka faɗa mata wanda yake cinta a rai amma ta ƙi mata maganar saboda ba huruminta bane.

“A’a ni kam ba yanzu ba.” Faɗin Juwairiyya tana murmusawa.

“Zan aiko miki wata ƴar ɗakina da take kitso da lalle jibi da safe ta zo ta miki don gaskiya baki isa ki zauna haka ba sai kace ba amarya ba.”

Juwairiyya tana jin nauyin Iyami saboda ta fita sannan tana ganin darajarta hakan yasa ta amince amma ba don tana so ba. Don me yasa zata yi wani ado ga mijin da ma bai damu da ita ba?

“To nagode sai ta zo ɗin.” Tana rufe baki suka jiyo tsayuwar mota a ƙofar gida wanda ko ba’a faɗa ba sun san waye ne ya iso. Zuciyarta ce ta tsinke ta ji cikinta ya murɗa wanda hakan ya sa ta kasa motsin kirki tana sauraron hayaniyar mutane.

Nan gida ya cika da hayaniya mutane na fita ana oyoyo oyoyo amma ita tana zaune ita da Iyami wacce ke kallonta kamar mai nazarinta. Sai da aka yi minti biyar an rage hayaniyar Iyami ta miƙe tare da ɗaukan ɗanta ta ce,

“Mu je ko?”

Wannan karon ma babu musu Juwairiyya ta tashi tare da ɗaukan gyalenta ta yafa kana suka fita tsakar gidan inda Muhammad yake tsaye yana cewa,

“Ina Juwairiyya?”

Yana faɗin hakan ya juyo saitin ɗakinta ya hangota tare da Iyami suna tahowa amma hankalinshi na kanta. Nan da nan annurin fuskarshi ta ɗauke kamar wanda aka faɗawa mummunan labari. Iyami ce ta fara isowa ta gaisheshi ya amsa yana mai kallon Juwairiyya wacce ta kasa ɗaga ido ta kalleshi kanta na ƙasa.

“Sannu da dawowa. Ya hanya?” Ta ce dashi murya ƙasa-ƙasa.

“Juwairiyya me haka? Me yake damunki? Ni da ake cewa kin rame ban san ramar taki ta kai haka ba. Salima me yasa baki faɗa mini abun ya kai har haka ba? Dubi wrist ɗinta fa!” Ya kama hannun Juwairiyya yana nunawa no one in particular fuskarshi sam babu walwala.

Ƙoƙarin kwace hannunta tayi amma bata iya ba domin ƙarfinshi da nata ba ɗaya bane. Kunya da takaici kuwa ta ji shi ba kaɗan ba wanda take jin kamar ta masifeshi amma bata isa ba saboda ga ƴan’uwanshi a gurin waɗanda suka yi cirko cirko suna kallon ikon Allah.

“Idan ma abinci ne ba kya son ci to daga yau a gabana zaki dinga ci sau huɗu a rana har sai kin dawo yanda kike. Salima ina abun da kuka dafa?”

Salima ta take jin baƙin ciki kamar ta mutu dalilin kwace mata spotlight ɗinta da Juwairiyya tayi ta buɗe bakinta wanda take jin kamar yawunshi ya kafe ta ce,

“Yana falona.”

“Je ki saka mana ni da ita, ke kuma dole ki zauna a gabana ki ci don bana son ramar nan ko kaɗan.”

Mum Fateey 👌

Juwairiyya ranar ta ga ikon Allah da kuma taurin ido a gurin Muhammad wanda tun da ya riƙe hannunta ya ƙi sakinta tana tsaye a gefenshi kamar wata mutum mutumi kanta a ƙasa cike da kunya. Ta gefen ido kuma tana ganin yanda wasu dangin Muhammad ɗin suke kallon intertwined hannayensu suna murmusawa yayin da wasu kuma suke hararansu.

Basu ƙara mintuna biyu a wajen ba suka ɗunguma dukkaninsu zuwa falon Salima wanda dama ya fi na Juwairiyya girma. Juwairiyya ta so kwace hannunta da ke cikin na Muhammad amma ya ƙi, ƙarshe a tare suka zauna a three sitter har da Salima wacce ta kasa haƙuri itama ta je ta zauna a ɗayan gefenshi tana murmushin yaƙe. HJ kuwa tun ɗazu a gurin mota da baban nashi ya ɗagashi ya zille yana mishi kallon baƙo, ƙarshe gudu yayi ya shige gida, a yanzu kuma yana rakuɓe a gefen mamanshi duk inda ta saka ƙafarta shima sai ya saka tashi.

Sai dai suna zama ta tuna cewa ya kamata ta kawowa Muhammad ruwa, hakan yasa ta tashi tsaye ta wuce kitchen shi kuma gogan ya bita da ido wanda Juwairiyya ta gani ta kawar da idanunta gefe. Ana ta hira Salima ta kawo mishi ruwa tare juice ɗin da ya fi so wato na carrot, da haka ta zo gabanshi ta durƙusa ta zuba mishi kana ta ɗauki glass cup ɗin ta miƙa mishi.

Kurɓa uku yayi ya ajiye ya ci gaba da magana da ƴan’uwan nashi waɗanda suka fara haramar tafiya akan sai daga baya zasu zo. Sa’i da lokaci Juwairiyya na ƙoƙarin zare hannunta cikin nashi amma ya ƙi sakinta, da ta lura da gaske yake yi sai ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido. Minti biyar da haka ƴan’uwa suka mishi sallama Salima ta tashi ta musu rakiya itama Juwairiyya ta miƙe amma Muhammad ya dawo da ita ta zauna.

“Ki zauna a nan.” Yanda yayi maganar cikin izza ko ita ce uwar raini ba zata iya mishi musu ba, don haka sai ta koma ta zauna tana cewa,

“To ka sake mini hannun.”

“No.”

Sai da kowa ya fice falon ya dawo su biyu sannan ya juyo ya dubeta tarr yana mai ɗago haɓarta yana kallon fuskarta.

“Juwairiyya kin rame da yawa! Me yake damunki?” Ya faɗi hakan yana jan gyalen da ke kanta ya sauƙa kan kafaɗunta yana kallon ƙashin wuyanta.

“Babu komai, stress ne.” Ta bashi amsa tana mai mayar da gyalen nata mazauninshi.

“Stress ɗin me?” Ya ƙara mata wata tambayar muryarshi cike da tausayi kuma ba tare da ya daina kallonta ba.

“School.”

“To lallai zaki daina wannan school ɗin.” Sai a lokacin ya sake mata hannu ya kawar da kanshi yana kallon bakin ƙofa inda Salima ke sallama sannan ta shigo.

“Ba school bane wasa nake maka.” Tayi saurin faɗa gudun kar ya jiƙa mata aiki.

“To menene?”

“Maganar me ake yi ne haka?” Faɗin Salima tana zama a ɗayan gefen nashi gurin zamanta na ɗazu, hannunta riƙe da na ɗanta.

“Ki kawo mana abinci.” Shine amsar da ya bata ita kuma Juwairiyya tayi shiru bata ce komai ba. Ina ruwanta da maganar da suke yi?

Jiki babu kuzari irin na ɗazu ta tashi ta nufi dinning table ta fara ɗauko abincin tana kawowa kan carpet, ganin haka yasa itama Juwairiyya ta miƙe tsaye tana cewa,

“Bari in tayaki.” Da haka suka jera mishi abincin kala-kala a gabanshi ya sauko ƙasa ya zauna.

“Salima me da me kuka yi?” Ya tambayeta.

“Akwai tuwon semo miyar ɗanyan kubewa, akwai kuma fried rice, coslow da pepper chicken, sai masa da miya da kuma snacks, cake, samosa, spring rolls da cinnamon rolls. Akwai kuma fruit salads da juices kala biyu. Ƴan’uwa kuma sun kawo su cakes,  meat pie, soyayyen kaza, soyayyen naman sa, da ruwan gora da drinks.”

“Wanne ya fi saka mutum kiba?” Ya ƙara jeho mata wata tambayar.

“Tuwo da snacks tunda an ce fulawa na saka kiba. Baka son mai saka ƙiban ne?”

“A’a. Juwairiyya ce zata ci, saka mini tuwon.”

Nan gurin yayi tsit dalilin tsayawa da Salima tayi tana kallon Muhammad da wani irin yanayi da yake nuna hurt, shi kuma ko ya san me yayi bai nuna a fuskarshi ba don wayarsa ma ya ɗauka da ke vibrating ya duba ya ajiye kana ya kalleta ya ce,

“Baki ji bane?”

“Ta bani nawa na ci fa.” Juwairiyya tayi saurin tsoma musu baki domin sai ta ji tausayin Saliman kaɗan ya shiga ranta.

Ta sani ko ita aka yiwa haka ba zata ji daɗi ba, don haka tunda bata so zata hanashi saboda kar watarana itama ya mata. Bai kamata matarshi ta kashe kanta ta mishi girki kala-kala ba sannan ya nuna bai damu da duk abun da yake gabanshi ba sai abun da wai ita zata ci tayi ƙiba. To wai wa ya faɗa mishi daga cin abinci ne ƙiban zai zo? Da ci yana kawo ƙiba da tayi kiban kafin ya dawo, domin tun ranar da ta ji labarin wai nan da sati biyu zai dawo a gurin Saliman ta fara ɗurawa kanta abinci wai ko zara murmure kaɗan. Sai dai duk lokacin da ta ganta a madubi sai ta ga kamar ƙara ramewan ma tayi ba ƙiba ba, wannan damuwan ma kaɗai ya isa ya ƙara ramar da ita wanda a hakan ya zo ya sameta duk da cewa bata so ba. Kuma duk abun nan da aka yi Salima ko ɗanɗane bata bata ba, tana gani dai ta bawa baƙi da suka zo wanda har Iyami an aiko mata nata har ɗakinta.

“Zaki ƙara. Kuma musun ya isa.” Yanda yayi maganar yasa kowacce ta shiga taitayinta.

Salima ce ta fara zuba abincin idanunta na tara kwalla amma bata bari suka sauƙa ba, ita kuma Juwairiyya ji take yi kamar ta gudu ta bar musu ɗakin domin ta kasa sakewa ko kaɗan kuma bata son cin wannan abincin. Tuwon malmala uku ta saka a plate sannan ta saka miyan a wani bowl wanda ya ji manyan tsokokin nama da ponmo ga ƙamshin kifi a ciki. Nan Juwairiyya ta ji yawunta ya tsinke musamman da ta ga Salima ta ɗibi man shanu a wani ƙaramin container ta zuba kan miyan.

Ruwa a cikin roba ta ajiyewa Muhammad ya wanke hannunshi sannan ya tura gaban Juwairiyya wacce tayi fiki-fiki da ido tana kalle-kalle dalilin muguwar hararar da uwargidan tata take aiko mata.

“Ki wanke hannunki.” Muhammad ya ƙara bata wani umurnin wanda bata so ba ta sauƙo itama ta wanke hannunta sannan ya miƙawa Salima robar ya ce itama ta wanke hannunta duk tare zasu ci abincin. Sai a lokacin fuskar Saliman ta washe kaɗan kana ta gyara zamanta ta saka musu abincin a tsakiyarsu suka fara ci suna hira ita da shi.

Ita dai Juwairiyya tunda ta kai lomar farko bakinta ta ji miyar bata mata daɗi yanda tayi zato ba, hakan yasa ta kasa kai na biyu don dama ba yunwar take ji ba.

“Juwairiyya ki ci abinci ko in miki ɗure don ba zaki sakani magana biyu ba.” Wannan faɗin Muhammad kenan yana hararanta.

Zare idanunta tayi kaɗan kana ta girgiza kai ta ce,

“Ni yarinya ce da zaka mini ɗure?”

“Ba zan iya bane?”

Kallonshi tayi daga sama har ƙasa sannan ta dubi jikinta sai ta raina kanta domin idan ya so zai mata ɗuren da gaske ba sai ya nemi taimakon matarshi ba. Sannan ita ta gaji da dragging maganar kawai so take yi ta bar falon Saliman don ba gurin zamanta bane.

“Amarya ko ki ci abincin nan ko mu miki ɗure don nima ina bin bayanshi, ramarki tayi yawa har tsoro nake ji kar a ce mugun hali nake miki a gidan nan shi yasa kika lalace haka.” Ta ƙarisa maganan tana dariya alamar zolaya ta yi.

Amma Juwairiyya ta san me tayi domin zaginta tayi cikin magana sannan ta rufe duk wata ƙofa da zai sa Muhammad yayi tunanin da gaske mugun halin ake mata. Idan kuma ta buɗi baki ta ce da gaske mugun halin take mata shikenan zata tarwatsa taro domin Muhammad ba zai taɓa yarda ba ƙarshe dai ita za’a bari da takaici. Abun da ya fi shi tayi; wato rufe bakinta ta murmusa aka kawar da zancen. Da haka kuma ta saka hannu suka cigaba da cin abincin wanda in da wani yace mata zata ci abinci a kwano ɗaya da kishiyarta da mijinsu zata ƙaryata domin ita ganin hakan take yi a matsayin ƙauyenci da iyeyi. Kowa ya sani ba’a son juna to don me za’a zauna ana pretending har da cin abinci tare ana exchanging yawu?

Da haka suka cinye tuwon Salima ta saka musu fried rice da coslow ɗin wanda shima Muhammad ya matsa mata ta ci, da haka sai da suka taɓa duk abubuwan da aka girka tare. Suna gamawa Juwairiyya ta shafi cikinta wanda ya taso tsabar ƙoshi ta mulmulashi tana murmusawa.

“Yanzu ke da kika ji ki a koshe ba ki ji daɗi ba?”

“Ji nake yi kamar zan fashe.” Ta faɗa murmushin bai bar fuskarta ba.

“Gaskiya na yarda cin abinci cikin jama’a na sa mutum ya ci da yawa. Nima ji nake yi kamar ba zan ƙara saka wani abu a bakina ba sai jibi.”

“Kun yi overfeeding ne kuma babu kyau a musulunci.” Wannan maganar Muhammad kenan yana mai tashi daga ƙasan ya koma saman kujera yana haɗe fuska.

Juwairiyya ce ta fara fashewa da dariya itama Salima da take ƙunshe nata ta saka tata don ya basu dariya ba kaɗan ba. Shi ya sakasu ɗuren sannan ya ce wai babu kyau kuma fuskarshi so serious kamar bai san me ya yi ba.

Shi kuma Muhammad tsayawa yayi yana kallonsu wannan karon da sakakkiyar fuska wacce take ɗauke da murmushi domin ya fi son ya gansu haka suna wasa suna dariya tsakaninsu.

“Amma dai na rasa gane alƙiblarka, kai ne ka sakamu ɗuren fa.” Faɗin Juwairiyya tana ɗaukan wani kula ta tashi ta kaishi kitchen ɗin Salima kamar yanda ta ga Saliman ta yi. Sai da suka dawo falon Salima ta ce,

“Ai Baban Hafiz ba zaki iya gane mishi ba.”

“Gulmana kuke yi kenan.” Ya faɗi hakan yana jawo HJ kan cinyarshi wanda har lokacin ya kasa sakewa dashi kuma kallon cartoon ma yake yi a wayar mamanshi. “Muhammad Hafiz har yanzu baka ganeni bane? Duk video call ɗin da muke yi kana cewa in dawo shine na dawon ka nuna baka sanni ba.”

Hira suka ƙara yi na minti goma  kamar babu wani abu a tsakaninsu domin da alama babu wacce take son mijin ya ga kamar ita ce bata son hulɗa da ƴar’uwarta. Da haka Juwairiyya ta miƙe tana cewa zata kwanta domin kar ta shiga hakkin Salima wacce take da surutu don jawo hankalin mijin nata kanta.

“To sai anjimanku, nikam zan shiga in yi bacci.”

Da haka ta musu sallama wanda da kamar zata ɗauki HJ don su wataya da kyau amma sai kishi ya hanata. Tana isa ɗakinta ta kwanta wanda overfeeding ɗin da tayi ya jawo mata kasala mai yawa, ko minti biyar bata yi ba bacci mai nauyi ya kwasheta cike da mafarkan mijinta.

Tana bacci ta ji kamar ana shafa fuskarta amma tana tashi ta ga babu kowa, nan tsoro ya shiga jikinta tayi addu’a kana ta tashi ta shiga toilet don yin alwala lokacin sallan la’asar yayi. Bata gama idar da sallah ba ta ji sallaman Muhammad a falonta wanda ya sa cikinta ya kaɗa irin wanda take ji in ta jiyo muryarshi, da haka ya shigo cikin ɗakin ya zauna a bakin gado yana kallonta har ta idar da sallan.

“Come here.” Shine kaɗai abun da yace da ita yana mai mata alama da hannunshi. Sai a lokacin ta ga alamar yayi wanka sannan ya canja kaya domin jallabiya ce fara tass a jikinshi.

Yanda yayi maganar kaɗai yasa alwalar Juwairiyya ya karye sannan ta ji inama a ɗakinta yake ba can ba. Kamar wacce aka yiwa sammu ta tashi ta je ta tsaya a gefenshi amma ya jawota ta zauna kan cinyarshi ɗaya tana kallon ƙasa ta kasa haɗa ido dashi.

Bata yi aune ba ta ji ya ƙanƙameta a jikinshi sosai har tana jin kamar numfashinta zai iya ɗaukewa, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya rage riƙon da ya mata kana ya zare  hijabin nata ya kwantar da kanshi a kan kirjinta wanda ke bugawa da ƙarfin gaske. Da haka ya saka hannunshi cikin rigarta amma kafin ya isa inda yake so ta riƙe hannun nashi ƙamm ta ce,

“Babu kyau.”

Bai kulata ba ya saka ɗayan hannun nashi ya cire tata wacce ta riƙeshin kana ya isa inda yake son zuwa wanda daga ita har shi wata wawuyar ajiyar zuciya suka sauƙe a tare. Tana son mishi magana amma sai ta kasa saboda nauyin da bakinta yayi dalilin salon da yake bi da jikinta wanda yanzu shekara guda kenan rabon da a mata haka.

Minti biyu da haka ya kwantar da ita akan gadon amma kafin yayi move ɗinshi na gaba tayi saurin mirginawa gefe tana maida numfashi ta ce,

“Zamu shiga haƙƙinta, Allah zai kamamu Muhammad.”

Kallonta yayi ido cikin ido kamar mai son cewa wani abu amma sai ya kasa. Da haka ya gyara tsayuwarshi wanda hakan ya fallasa wani abu a jikinshi wanda Juwairiyya tana gani ta saka dariya har da ƙyaƙyatawa.

“What is funny?” Ya tambayeta yana hararanta yana kuma kare abun da ta gani ɗin.

“Babu…Mwhahahaha…. kawai na ga ka……Hahahaha.” Ta toshe bakinta tana kallon yanda yake son kunshe murmushin da yake yi amma ya kasa.

“Idan na kamaki ba zaki yi wannan dariyan ba.” Wannan karon murmushin mugunta ne a fuskarshi kamar mai hasko abun da yake faɗan a kwayar idanunshi.

“Fasa-fasa ɗan halak!”

“What does that mean.” Ya tambayeta yana mai ɗaga girarshi ɗaya sama.

Bata amsa ba ta sauƙo daga kan gadon ta zo gabanshi ta tsaya wanda har suna shakar numfashin juna kana ta yi ɗagelgel ta tsaya kan yatsun kafafunta ta yanda bakinta zai isa kunnenshi ta ce,

“I dare you!”

Hannunshi ya ware da niyyar cafkota amma da yake bata jin nauyin jikinta tuni ta zille sai a bakin ƙofa ya ganta tana mishi naughty dariya kana da fice falon da sauri da yayi kanta. Da wannan dariyar ta fita zuwa kitchen ɗinta ta zauna a nan domin fitinar da ta hango a kwayar idon Muhammad ko a falo ta tsaya sai sun aikata abun da zasu dawo suna regretting daga baya.

Bai fito ba sai da ya ƙara minti uku wanda Juwairiyya ta sani ya tsaya saisaita kanshi ne gudun kar yara su gani su gudu, (lol). Tana ganinshi ya fito ya wuce ɗakin Salima sannan ta koma ɗakinta ta rufe tana tunanin wannan relationship ɗin nasu mai kama da rawar ƴan mata, sai an yi gaba sai kuma a dawo baya sai kuma a sake yin gaba.

Tana nan zaune ita ɗaya amma sa’i da lokaci tana tunaninshi tana murmusawa, sai dai da zaran ta tuno wai yana can ɗakin Salima ne sai ta ji murmushi ya kau ɓacin rai kuma ya biyo baya. Ganin zata iya yiwa kanta illah da tunanin banza yasa ta kunna TV don ya ɗebe mata kewa, Korean series ɗinta da take gani shi ta saka ta nitsu tana gani. Can anjima ta ji ana kwankwasa mata ƙofa ta ce a buɗe Salima ce ta shigo ta miƙa mata wata leda tana cewa,

“Ga tsarabanki in ji Baban Hafiz.”

“To na gode.” Ta faɗi hakan tana karɓa sannan ta ajiyeshi a gefe ba tare da ta buɗe ba don an yi sealing dinshi sannan da sunanta a jiki.

Gani tayi Salima ta tsaya a kanta kamar ba zata tafi ba, to ko dai so take yi ta buɗe a gabanta? Wannan ne kuma ba zai yiwu ba duk dama ta sani Muhammad ba zai taɓa banbantasu a tsaraban ba.

“Bari in je mu ƙarisa rabiyan kayan, nace mishi a kiraki a raba a gabanki kar ki ga kamar an wareki yace hakan ya ga dama.”

“Laa babu komai, ni kallo ma nake yi don series ɗin nan ya tafi da hankalina bana ko son gusawa.” Ta faɗi iyakar gaskiyanta domin bata son a ƙara wancan zaman da aka yi na cin abincin, an yi na farko kuma an yi na ƙarshe.

Da haka Salima ta tafi wanda Juwairiyya har ta fara tsammanin ko ta rasa abun faɗe ne amma da ta tuna wacece ita sai ta kaɗa kai tace an gama bata na yau ne sai kuma na gobe.

Sai goshin maghrib Muhammad ya fita da motar Salima wanda dawo ba sai goma na dare da yake ya je gidansu sannan an haɗu da abokai an yi hiran yaushe gamo. A  bakin Ƙofar Juwairiyya ya fara yada zango ya kwankwasa mata ta buɗe da yake yau bata yi bacci da wuri ba saboda tun lokacin da ta ji ya fita ta kasa sukuni shi yasa ta zauna har wannan lokacin bata yi bacci ba.

“An wuni lafiya?” Ta fara mishi magana bayan ta buɗe ƙofar.

“Lafiya kalau.” Ya amsa yana miƙa mata leda ɗaya daga cikin guda uku da yake riƙe dasu.

“Nagode.” Ta faɗa tana mai karɓa.

“Bashi ne.” Ya furta a hankali kamar mai raɗa kana ya bar bakin

ƙofar tata.

Sai da ya kusa shiga falon Salima sannan maganarshi ta isa kwakwalwarta ta fito tana cewa,

“In dai haka ne bana so ga kayanka.”

“Too late.” Yana faɗin hakan yayi shigewarshi ya barta cikin wani yanayi da ita kanta ba zata iya fassarashi ba.

Da guntun murmushi a fuskarta ta rufe ƙofarta ta je ta zauna akan kujera dama daga nan take. Tana buɗe ledan ta ga tsire ne mai zafin gaske wanda yasa ta ji yawunta ya tsinke ta ɗauki ɗaya ta kai baki a ranta kuma tana cewa ‘nama dai ba’a gajiya da shi’. Domin suna cin na miya da kuma ferfesu akai akai amma tsiren daren nan ne dai suka yi missing saboda babu mijinsu mai sayo musu.

Washe gari da hantsi Juwairiyya tayi baƙuwa wacce tace Iyami ce ta aikota.

“Ai mun yi da ita sai gobe zaki zo ba yau ba.” Faɗin Juwairiyya tana mai kawo mata ruwa ta ajiye mata a gabanta.

“To ni kuma yau tace in zo, amma in kin fi son sai goben sai mu bari.”

“A’a mu yi kawai.”

Da haka suka fara da lalle ja wanda aka mata a tafin ƙafarta da kuma hannunta da yatsunta. Ana gamawa ta dawo kanta aka fara kitso Juwairiyya dai babu hannu babu ƙafa, ana gama kitson aka fara kiran sallah azahar wanda kuma yayi daidai da shigowar Muhammad da tun safe bai fita ba yana huta gajiya.

“Ina wuni?” Juwairiyya ta gaisheshi tana mai son gyara wuyan rigarta da ya sauƙo kaɗan.

“Lafiya kalau. Lalle da kitso kika yi?” Ya tambaya kamar bashi da ido.

“Eh.”

“An gama kenan?” Ya ƙara tambaya yana kallon kitson kanta.

“Eh.”

“Nawa ne kuɗin?”

“Ban tambayeta. Ilhama kika ce nawa ne kuɗin naki duka?”

“Duk yanda kika bani.” Ta amsa tana mai tattara kayanta don tafiya.

Kafin Juwairiyya ta faɗi wani abu Muhammad ya ciro kuɗi a aljihunshi ya miƙa mata ta ƙarɓa tana godiya sannan ta musu sallama ta tafi. Sai a lokacin Juwairiyya tayi dana sanin barinta ta tafi, domin kuwa Muhammad kama gaban rigarta yayi yana leƙawa. Sai dai kafin ta ce komai ya juya yayi tafiyarshi har ta fara tsammanin ko bai ga abun da ya burgeshi bane?

Minti talatin da haka ta cire lallen sannan tayi alwala tayi sallah, sai a lokacin ta buɗe wani aika da Ilhama ta bata wai in ji Iyami. Tana buɗewa ta ji kunya ya kamata, domin maganine irin tasu ta mata da ta fi buƙata a wannan lokacin wanda tsumi ne tare da dakan gumba da ake sha da madara. Kamar ta kira Iyami ta mata godiya amma sai ta ji kunya ya rufeta ba zata iya ba, hakan yasa ta mata text mai nuna jindaɗinta da aikan.

Washe gari tun kafin Muhammad ya dawo gurinta Juwairiyya ta gama shirye-shiryenta na tarɓanshi har tana mamakin kanta wai ita ce take haka! Yamma liss ya dawo ɗakinta wanda sai da ya gama jagwalgwalata sannan ya nufi masallaci wannan karon ma sai da ya saisaita kanshi.

Yana dawowa kuwa suka ci abinci yana bata labarin London da wasu abubuwan da bata sani ba tunda a yau ta nuna tana son ji. Sai da aka yi isha yayi wanka ya dawo falo ya zauna kusa da ita yace,

“Ina tsaraban da na miki kwanaki?” Ya tambayeta yana mai zuba mata mayun idanunshi.

Juwairiyya tana jin haka hanjin cikinta ya kaɗa domin ko da wasa ba zata so ta saka kayan a yanda take a ramen nan ba don ba zata yi kyau ba.

“Yana nan.” Ta amsa mishi bayan ta haɗiyi yawu mai kauri ta fara zare ido kamar mara gaskiya.

“A saka ina son ganin ko size ɗinki ne.”

“Don Allah Muhammad kayi haƙuri amma ba yanzu ba sai na murmure, ko na saka ba kyau zai mini ba.”

“Kar ki mini musu mu koma gidan jiya please. Ramarki ba zai hanani ganin kyawunki ba haka kuma ba zai hanani sonki ba.”

Daram!!! Zuciyarta ta buga da matsanancin ƙarfi da ta ji maganar da ya fito daga bakinshi. Shin yana nufin abun da ya faɗa ko dai kawai suɓutar kalma ce?

“Kace me?”

“Yaushe?”

“Abun da ka faɗa yanzun nan.”

“Wanda na ce ina sonki?”

Wannan magana kaɗai yasa idanun Juwairiyya suka ciko da kwalla tana jin sanyi a ranta, wai yau Muhammad ne yace mata yana sonta? Dama ya iya furta kalmar so? Ita ɗin dai Juwairiyya?

Jawota yayi jikinshi ta dawo saman cinyarshi ya rungumeta tsam sannan ya ce,

“Ba kullum nake buɗe zuciyata ba amma yau zan so ki sani cewa, idan a da ina miki kallon matata ce kawai to yanzu ina miki kallo ne da matsayi biyu, wato matata da kuma abun da nake so a zuciyata. Juwairiyya kina bani headache sannan kina mini taurin kai amma a hakan na faɗa sonki ba tare da hana kaina ba. I will raise the white flag again, please ki rage raini mu zauna lafiya har abada. Kin ji?”

Kwantar da kanta tayi kan kafaɗarshi tana jin kwatankwacin abun da shima yake ji a tashi zuciyar. Tana sonshi in dai ba zata yi ƙarya ba amma ya zata yi da alƙawarin da ta ɗauka na barin gidanshi? Sannan ta yaya zata iya cigaba da zama da Salima makira wanda ba’a san ranar rabuwan ba? Shin ta mishi adalci kuwa da ta aureshi da niyyar barinshi idan burinta ya cika? Kamar bata kyauta mishi ba amma a yanzu zata bar duk wannan tunanin sai daga baya don ita kanta tana son kasancewa dashi kuma ba iya yau kaɗai ba.

“Eh, na ji.”

“Me amsarki?”

“Sai daga baya.”

“Ina jiranki.”

Ba sai ya ƙara nanatawa ba ta san me yake nufi don haka ta miƙe ta isa gaban fridge ta ɗauko Apple guda ɗaya sannan ta juya tana kallon cikin idanunshi ta yi biting seductively ta ce,

“Bani minti sha biyar zan zo in baka Apple.”

Da haka ta shige ɗakinta ya bita da ido har ta ƙule mishi sannan ya dubi agogo yayi marking lokacin da ya rage mishi yana shafa sajenshi yana murmushi shi kaɗai.

Daidai lokacin da ta faɗa kuwa ta fito sanye da Apron da kuma chef hat ɗinta, a ƙafarta kuwa da ya sha lalle ta saka high heel baƙi wanda ya shige da white Apron ɗin. Fuskarta kuwa ta mishi simple yet seductive make up wanda zata iya rantsewa tunda ta zo gidan Muhammad bata taɓa yin irinshi ba.

Numfashi Muhammad ya ja da ƙafi ya zura mata ido ta tako taf taf taf ta zo ta wuceshi ta isa bakin fridge wanda a nan ne ya ga bayanta da babu komai sai igiyar Apron ɗin.

“Kana tashi no Apple for you.” Ta juyo tana kaɗa mishi hannu kamar ƙaramin yaro.

Bai musa ba ya koma ya zauna saboda he is the one who asked for it amma tun kafin a je ko’ina haƙurinshi ya fara ƙarewa. Ƙara juyawa tayi ta bashi baya kana ta ɗauko Apple ta taho tana mai rangwaɗa wanda tsabar ƙarfin hali take yi amma kunya da kuma tsoro ne a ranta kar ta kwafsa ko kuma tayi abunda ba shi yake so ba.

A kan cinyarshi ta zauna yayi saurin ɗago hannunshi zai taɓata ta hanashi.

“No touching sai na baka ka ci Apple. Ba shi kake so ba?”

Gyaɗa mata kai yayi ta ji kamar ta kwashe da dariya don lallai ne an yi gaskiya ta aka ce Namiji raƙumi ne. A yanzu he is at her mercy sai yanda ta ce amma gobe ba zai hana ya danƙara mata doka ba. Murmusawa tayi kana ta kawar da wannan tunanin ta cigaba da gigitashi wanda a haka ya ci rabin Apple ɗin ba tare da ya ma gane yana cin ba, sai da ta gama kawar mishi da hankali ya jata zuwa ɗaki yana cewa,

“I can’t take it anymore, I need you right now!”

 A can wata unguwa a bayan gari wani mutumi ya kira suna a bakin wani zaure aka amsa mishi ya shiga ya zauna yana mai fuskantar mutum mai kama da malami da kuma boka.

“Yau kuma me ke tafe da kai Salisu?” Boka kuma malamin ya tambayeshi.

“Wata yarinya na gani nake so a mini aiki a kanta ina son aurenta ne cikin gaggawa.”

“Waccar kuma fa?”

“Na haƙura saboda shekararta ɗaya har da wasu watanni da auren nata, na kashe kuɗi an yi aiki har sau uku kace an tura mata aljani da zai dinga saka mata damuwa da ɓacin rai don ta bar gidan amma har yanzu shiru.”

“Dama ina son faɗa maka Aljanin da aka aika ya dawo ya ce a kwanakin nan in ya zauna kusa da ita sai ya ji kamar ana ƙonashi, yace idan ya ci gaba da zama zai iya cutuwa, idan kuma ya cutu gurinka zai dawo ya ɗauki fansa.”

“A’a yau me yayi zafi? Ya barshi kawai na fasa na ga wacce ta fita kyau yanzu ita nake son saka mata sona mu yi aure.”

“A ina take?”

Nan Salisu ya fara bada bayanin next victim ɗin nashi wacce ta kasance ƙawar ƙanwarshi ce boka kuma malamin na gyaɗa kai kana ya fara aikinshi.

Mum Fateey 👌

“Ai tun lokacin da uwargidanta tayi mota ta sakawa kanta damuwa ta fara ramewa, yanzu in kun ganta kamar wacce ta kwanta cuta ta tashi, shi yasa aka ce idan ka ɗaurawa kanka hassada kai zaka mutu a tsaye.”

“Ni wallahi ramar tata ta fara bani tsoro, anya ba cutar AIDS ne ta kwaso a wancan gidan tsohon ta kawo musu ba? Allah na tuba zato zunubi amma dai ku duba.”

“Kai zai yi wahala duk da ma hakan zai iya yiwuwa. Amma ni na fi tsammanin tafiyan da mijinsu yayi ya barsu ta shiga damuwa, saboda ai kafin ya tafi tana nan da mamorarta.”

“Ni kuma gani nake yi uwargidan tata ce take gasa mata gyaɗa a hannun domin wallahi uwarta ma bata da hali mai kyau, ta zauna da kishiyoyi har biyar amma babu wacce ta iya zaman shekara uku da ita duk yanzu babu su sai ita kaɗai, mijin har ya gaji da aure ya haƙura.”

“Zato zunubi nima nayi tunanin nan, ta mata shigo-shigo ne babu zurfi. Yoo in ba haka ba wace mace ce ƙawarta zata aure mata miji sannan tayi saurin karɓan auren babu tashin hankali? Ai kowanne mai hankali idan ya zauna zai ga akwai alamar tambaya a wannan al’amarin.”

“Ni kuma nace ko tunanin haihuwan da bata yi ne ya dameta domin gashi har auren nasu yayi shekara da watanni bata da komai ita kuma kishiyar tata da ta je gurinshi kwanaki har tsaraban ciki tayi. To ko wannan ma ya isa ya saka mata damuwa.”

“To dai koma menene wannan ba huruminku bane da zaku zauna kowa yana kawo theory ɗinshi akan rayuwar mutanen da basu ma san kuna yi ba. Allah Ya rufa mana asiri.”

Wannan shine kaɗan daga cikin abun da mutane suke tunani akan ramar Juwairiyya wanda ciki har da wasu daga cikin dangin Muhammad.

***********

“Apple ɗin bai isheki bane?” Muhammad ya tambayi Juwairiyya yana tsantsane jikinshi da towel wanda fitowanshi daga wanka kenan.

Turo baki Juwairiyya tayi kana ta ƙara jan bargo ta rufe kanta don maganar da zata faɗa zai mata nauyin da zata kasa kallon kwayar idanunshi.

“Kai in ka samu abu baka san ka bar na gobe ba sai ka ƙarisa duka? Yanzu kam kana zuwa gudu zan yi in koma gida in cewa Mama zaka kashe mata ƴarta.” Ta faɗa a kasalance kamar wacce tayi aikin wahala ta gaji.

Dariya yayi wanda har sai da Juwairiyya ta buɗe idonta ɗaya tana leƙenshi itama tana murmushi, ta lura shima yana son irin wannan dirty talk ɗin musamman wanda ake yaba ƙoƙarinshi da wayo.

“Ki tashi ki je kiyi wankan J kar kiyi bacci.” Ya faɗi hakan yana mai jefar da towel ɗinshi a kan gado ya ɗauki boxers ɗin shi yana sakawa.

Juwairiyya kuwa ƙurawa halittarshi ido tayi tana jin wani yanayi a jikinta, amma da ta tuna irin wahalar da ya bata wanda duk jarabarta sai da ta ji ta yafe ta mayar da bargon ta ƙara rufe idon nata.

“Ina ganinki kina kallona, ki kalla son ranki I won’t bite.” Yana faɗin hakan ya ƙariso bakin gadon ya janye bargon da ta lulluɓa ya jefar a ƙasa.

Wani irin ihu kaɗan Juwairiyya tayi kana ta duƙunƙune jikinta guri ɗaya domin bata son ya ganta haka nan babu shamaki. Ko ɗazu da ta saka Apron ɗinta sai ta tayi dabara ta ɗaureshi da kyau yanda ba zai mata ruwa ruwa ba a jikinta, sai da ta tabbatar ta ɗan yi kyau sannan ta rufe ƙashin wuyanta sannan ta ji courage ɗin fita gurinshi. Amma yanzu babu komai a jikinta ba zata so ya ganta haka nan ba.

“Don Allah ka rufeni, I’m not comfortable at all.”

Bai amsa ba sai da ya kashe wutan ɗakin sannan ya ce,

“Ki daina damuwa kina tunanin zan ga wani abu a jikinki in kushe, dukkaninmu we are not perfect, I have my flaws ke ma haka but what matter the most shine yanda muka ɗauki junanmu a zuciyoyinmu. Ko kin manta kirana da kike yi da ɗan lukuti? Hakan bai taɓa damuna ba ko kaɗan because I accept my body na san haka nake ba ƙarya aka yi ba. Ki tashi.”

Babu musu Juwairiyya ta miƙe jikinta duk yayi sanyi da kalamanshi wanda ciki har da kunya da ya tuna mata abun da take kiranshi da shi a da.

Sumui Sumai ta sauƙo daga kan gadon ta nufi banɗaki amma duk da haka sai da ta tsaya ta ɗauki towel sannan ta shiga. Tana banɗakin ta ji muryar Muhammad kamar yana waya, zuciyarta ta buga tana tunanin da waye yake waya da tsakar daren nan? Kasa kunne ta yi amma bata ji ya ƙara magana ba sai ma fita falo da yayi wato saboda ma kar ta ji shi ko?

Ranta na suya ta gama wankan a gurguje sannan ta ɗaura towel ta fito, cikin sanɗa ta buɗe ƙofa ta leƙa cikin falon nan ma babu shi, a nan ne ta ji ranta yayi matuƙar ɓaci don ta sani waya yake yi da budurwa shi yasa ya gudu har waje don kar ta ji. Rai na ƙuna ta koma cikin ɗakinta ta saka kaya tana mai jin haushin saurin yarda da maganarshi da tayi wai yana sonta kuma bai damu da imperfections ɗinta ba.

Ji tayi kamar ta je ta rufe ƙofar falonta in ya ga dama ya kwana a wajen amma sai ta tuna idan har Salima ta gane a kan kishi ta rufe mijin nata a waje to kashinta ya bushe. Haka ta kwanta wanda minti biyu da haka Muhammad ya shigo yana kiran sunanta, tsabar haushi kasa amsa mishi tayi sai kuma tayi kamar tana bacci. Da haka kuma ta ji kamar ya ajiye abu mai nauyi a bayanta kamar wanda ya kwantar da mutum. Hakan yasa ta kasa haƙura ta buɗe idanunta tare da juyawa ta kalli ashe HJ ya kawo ya kwantar.

A nan kuwa zuciyarta ta fara raya mata abubuwa kala-kala wanda ciki har da cewa gurin uwar yaron zai je su raya daren saboda ya gane jikinta ya fi nata kyau. (Zuciya mai raye-rayen banza).

“Juwairiyya kin tashi? Ga yaron nan ku kwana tare zan kai Salima asibiti.” A gaggauce yayi maganar yana mai juyawa zai tafi ta dakatar dashi.

“Subhanallahi, me ya sameta?” Ta tambayeshi tana mai dafa ƙirjinta domin ta san duk abun da zai sa su tafi asibiti a yanzu ba ƙaramin abu bane.

“Bleeding take yi wanda dama tun ranar da na dawo take complain mararta na ciwo.” Ya tsaya a nan ba tare da ya ƙarisa sauran maganar ba na cewa tun da ya dawo bai kusanceta ba saboda yana tsoron kar su ƙara jawo matsala.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. To Allah Ya bata lafiya ya tsayar haka.” Ta faɗa tana mai girgiza kanta cike da jimami.

“Ameen.” Ya amsa kana ya fita cikin sauri ya barta cikin zullumi.

Tashi tayi da sauri ta bi bayanshi zuwa tsakar gida inda a nan ta samu Salima a cikin mota tana haɗa gumi gaɓa ɗaya da ka ganta ka san tana cikin tsoro da kuma wahala.

“Juwairiyya ki rufe gidan idan mun fita.” Faɗin Muhammad kenan bayan ya buɗe gate ya dawo ya shiga mota ya kunnata.

“Allah Ya baki lafiya Ya kuma tsareki da abun cikinki.” Ta yiwa ƴar’uwar tata addu’a zuciyarta na mata nauyi domin duk da da cewa ta tsani halayenta ba zata so wani abu ya samu cikinta ba.

Ɗaga kai kawai Salima tayi bata ko kallonta Muhammad kuma ya ja motar suka fita. Da sauri ta ja gate ɗin gidan ta rufe tare da saka kwaɗo sannan ta koma can cikin ɗakinta inda HJ ke baccinshi ba tare da yasan abun da yake faruwa ba. A gefenshi ta kwanta ta lulluɓe ƙafafunshi kana tayi addu’a ta shafa mishi kamar yanda take yi kwanaki da mamanshi tayi tafiya ta bar su.

Away ɗaya da haka ta kira Muhammad amma bai ɗauka ba, da haka ta sake mishi wani kiran nan ma shiru bai ɗauka ba. Addu’a tayi Allah Ya sa ba wai situation ɗin ne ya zama so serious da har ba zai iya ɗaukan waya ba. Da haka ta ajiye wayar a saman night stand tana jiran in ya samu sarari ya kirata ya faɗa mata halin da ake ciki, minti biyar da haka bacci mai nauyi ya ɗauketa wanda bata tashi farkawa ba sai asuba da aka shiga sallah.

Da sauri ta ɗauki wayarta ta duba missed calls ɗin Muhammad har bakwai, sai a lokacin ta tuna ai tun sallah isha ta saka wayarta a silence kuma bata cire ba. Kiranshi tayi cikin gaggawa amma bai ɗauka ba, kira biyu ta ƙara yi amma har suka gama ringing ba’a amsa ba.

A nan ne ta tashi bayan ta gyarawa HJ kwanciyarshi tayi alwala ta fara sallah. Tana idarwa kuwa wayarta ta fara ringing ta ɗauka cikin sauri ganin sunan Muhammad ne.

“Assalamu alaikum.” Ta faɗa kamar wata mai jin tsoro.

“Wa’alaiku mussalam.” Ya amsa ya kuma yi shiru.

“Jiya da dare na kiraka in ji halin da kuke ciki amma sai baka ɗauka ba.”

“Bani da lokacin ɗaukan wayar ne.”

Muƙut ta haɗiye yawu mai ɗaci sannan ta ce,

“Na ga missed calls ɗinka.”

“Eh ba kin yi bacci ba? A gabanki muka tafi asibiti amma kika yi bacci wanda na dawo nayi ta kiranki ki buɗe mini ƙofa baki ɗauka ba gashi cikin dare ne bana son buge-buge. Yanzu da bani da key ɗin Salima a hannuna sai dai in kwana a waje ko kuma in nemi wani gida. Kin san halin da muke ciki don me yasa zaki yi bacci mai nauyi kamar baki damu da halin da muke ciki ba?”

Shiru Juwairiyya tayi ranta na suya domin bai kyauta mata ba idan ya ga laifinta don tayi bacci, ai ko Allah ne ba ya kama mai bacci da laifi. Sannan ta kirashi ta ji ya suke ciki bai ɗauka ba, to ya yake so tayi? Baccinta ko rashinshi kuma ba shi zai bawa matarshi lafiya ba.

“To yanzu kana ina ne in buɗe maka ƙofar?”

“A gidan na kwana a can ɗakinta, yanzu kuma ina masallaci daga nan hospital ɗin zan koma.” Yana faɗin hakan yayi shiru bai amsa mata ɗayan tambayar ba.

Juwairiyya ta san bai manta da ɗayan tambayar tata ba kamar ma ja mata rai yake yi baya son faɗa, yanda yake magana kuma cikin fushi da ɗaga murya bai mata daɗi ba saboda bata yi laifi ba, Ita a gurinta kenan.

“Ya mai jikin?” Ta sake tambayarshi tana mai danne harshenta da yake son faɗin sauran abubuwan da ke zuciyarta da take ji a lokacin.

Shiru yayi kamar ba zai amsa ba wanda Juwairiyya tayi kamar ta kashe wayar amma ta danne zuciyarta tana sauraronshi.

“Ta haihu…..sun ciro yaran babu rai.” Ya faɗi hakan wanda sai a lokacin Juwairiyya ta gane cewa he was hurting shi yasa yake ta mata wannan attitude ɗin.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah Ya sa masu ceto ne Ya baku haƙurin rashi. I’m sorry. Yara har biyu?”

“Eh. Amin.” Yana amsawa ya kashe wayar wanda Juwairiyya zata iya rantsewa kamar muryarshi ta yi cracking.

Bata koma bacci ba duk da irin ciwon da jikinta yake mata ta wuce kitchen ta fara dafa musu karyawa wanda zata kai asibiti ciki kuwa har da ferfesu. Tana aikin tana jin tausayin Salima a ranta domin ta kwallafa ranta a kan cikin wanda wani lokaci har da shune take mata da wayo, amma ta sani haihuwa na Allah ne kuma damuwarta ba zai bata ba sai Allah Ya so Ya kuma ga dama.

Kafin bakwai na safe Juwairiyya ta gama komai ta tashi HJ ta mishi wanka wanda yau kam ba zai je school ba. Kayan jikinshi ta mayar mishi kana ta kira Muhammad ya ɗauka, sai da ta gaisheshi tare da ƙara mishi ta’aziyya sannan ta faɗa mishi ta gama girki tana son zuwa asibitin amma bata san ina suke ba.

“Ki bari idan an yi jana’izan yaran zan dawo gida in yi wanka sai mu tafi tare.”

“To wai na ga kar su nemi abinci ne ba’a kai musu da wuri ba.”

“A yanda take bana tunanin zata iya saka komai a bakinta, sai na dawo na ce miki.” Ya ƙara kashe wayarshi ya bar Juwairiyya ta mamaki to ita kuma menene laifinta? Komai tayi bata yi daidai ba?

Sai takwas da rabi ya dawo gida ta tarɓeshi tare da ƙara mishi gaisuwa ya amsa yana tambayarta HJ.

“Ɗazu Salim ya zo ya ɗaukeshi suka tafi.”

“Don me yasa zaki basu shi? Ba nace ku jira sai na dawo in kaiku ba.” Ya faɗi hakan cikin tsawa kamar ma jira yake yi.

“To ai baka faɗa mini har da shi ba, nayi zaton ni kaɗai ne. Kuma su da ɗansu ai ban isa in hanasu ɗaukanshi ba.”

“Eh saboda bakya ji ne kina da taurin kai mutum bai isa ya faɗa miki abu ɗaya ki ɗauka ba.”

Da mamaki Juwairiyya take kallonshi kuma baki buɗe don ta fara gajiya da tsawan nashi akan laifin da bata aikata ba. Har ta buɗi baki zata mishi tsawa sai kuma ta ji nauyin hakan, dole ta sassauta muryarta ta fara magana.

“Menene ya faru ne kana ta mini tsawa alhali ban maka laifin komai ba? Idan kuma laifi na maka sai ka faɗa mini ba wai kayi ta faɗa kana fushi ba. Gaskiya bana son haka.” Ta yi maganar cikin ɓacin rai duk da cewa bata ɗaga muryarta ba.

Tana gama maganar yayi shigewarshi ɗaki ya barta a gurin cike da tsantsan mamaki. To laifin me tayi? Don tayi bacci ya dawo gida bata buɗe mishi ba? Shin ba zai yiwa mai bacci uzuri ba?

Sai da ya gama shiryawa ya fito fuska a murtuƙe ya zo ya wuceta yana cewa,

“Ki fito mu tafi.”

Dama ta gama shiryawa tun kafin ma ya dawo, hijabinta kawai ta saka kana ta rufe ƙofar falon ta fito, daga nan kuma ta shiga kitchen ta ɗauko abincin tace ya buɗe mata booth ya buɗe ta jerasu a ciki ta rufe kana ta shiga cikin motar ta zauna. Shiru suka yi na wani lokaci motar na diri shi kuma ya ƙi tafiya yana kuma shiru.

“Wa zai buɗe gate ɗin?”

Da mamaki ta juyo tana kallonshi domin sai a lokacin ta gane dalilin tsayawar tasu. Idan Salima ta sabar mishi da wannan buɗe gate ɗin kamar maigadi ita fa ba zata iya ba, namiji aka sani da wannan aikin ba mace ba. Sai dai a yanzu ko tayi magana ba zai fahimceta ba ƙarshe sai dai duk ransu ya ɓaci a watse a haka, da wannan tunanin ta fita ta buɗe gate ya fitar da motar kana ta mayar ta rufe tare da kullewa ta dawo cikin motar suka tafi asibiti wanda har suka isa magana bai ƙara shiga tsakaninsu ba.

Ita ta ɗauki basket ɗin abincin tana tuna ranar da ya kwanta a asibiti haka ya barta ta wahala wanda har hakan yasa ta haɗu da Daddy da ya nuna mata tsagwaron kulawa yana tambayarta me ya sameta. A hakan bai daddara ba ya aiko ƴar shi wacce ta ƙi aikata abun da yake so sai da ya faɗa mata deepest secret ɗinshi wanda da ita da shi suka ɓoye saboda kar duniya su ji.

Kwalla ne ya taru a idanunta da ta tuna irin yanda Daddy yake sakaltata yana kwashe duk shirmenta a matsayin yarinta, zata iya rantsewa ko sau ɗaya basu taɓa samun saɓani babba ba sai dai misunderstanding wanda shi da kanshi yake zaunar da ita ya fahimtar da ita dalilanshi ko kuma manufarshi akan abun da suka samu banbancin ra’ayin, amma wannan mijin nata na yanzu kamar ma neman laifin yake yi ido a rufe don ya mata faɗa.

Saurin kawar da tunanin tayi kana ta shanye hawayen idanunta ganin sun iso ɗakin da Salima take. Shi ya fara shiga ta bi bayanshi bakinta ɗauke da sallama, aka amsa musu.

Nan guri ya gauraye da gaishe-gaishe wanda Juwairiyya ta gaishe da kowa tare da musu ta’aziyya har da Saliman wacce idanunta suke a kumbure alamar dai ta sha kuka ba kaɗan ba.

“Baban Hafiz ka ci abinci?” Salima ta tambayeshi tana share hawayen da suka gangaro mata kan fuskarta.

Sai a lokacin Juwairiyya ta tuna wai ashe bai ci breakfast ba domin kuwa yana fitowa daga ɗaki ya zo ya wuce ya fita waje ko tsayawa bai yi ba.

“A’a wani abu ne?” Ya tambayeta yana mai gyara tsayuwarshi.

“Don Allah kar ka zauna da yunwa ka san kana da ulcer, mu ɗauki hakan a matsayin ƙaddararmu. Allahn da Ya bamu ya fi mu son su.”

Maman Salima da take gefe ta sunkuyar da kanta ƙasa tana share hawayen fuskarta, dama ita ce take zaune da Saliman da wata ƴar’uwarsu.

“Zan ci anjima.” Shine kawai abun da ya faɗa.

“Amarya ki saka mishi a namu don hankalina ba zai kwanta ba idan bai ci ba.” Ta yi maganar tana kallon Juwairiyya wacce ta tsaya ganin ikon Allah.

“Salima ki bar maganan cin abincina ki kula da kanki, jiya da dare kika haihu bayan wahalan da kika sha. Kin ga kuwa rashin cin abincina ba damuwa bace akan wanda kika shiga ciki har da rasa ƴayanki.”

“Ni kuma kai ne damuwata, shi yasa ba zan bari ka yi wasa da lafiyarka ba don bana son komai ya sameka Baban Hafiz.”

Juwairiyya da tayi kasake tana jin wannan exchanging ɗin maganganunsu tana bin kowa da kallo sai ta ji kamar ta tafa musu amma na takaici. Yanzu duk akan abinci ne ake wannan bankaɗar sirrin zuciyar alhali ga abun da ya samesu ko awa goma ba’a yi da faruwarshi ba?

“Ki saka mishi Amarya.” Ta ƙara jiyo muryar Salima tana bata umurni.

A nan Mamanta tare da ɗaya ƴar’uwar ta su suka miƙe maman na cewa,

“Salima ke dai akwai ki da son mijinki, to Allah Ya barku tare. Bari mu koma gida mu yi wanka zamu dawo yanzu.”

“Amin Mama.” Ta amsa tana mai sunkuyar da kanta ƙasa tana share hawayen fuskarta.

Mamaki taff a zuciyar Juwairiyya ta miƙe daga zaune akan plastic chair ta isa gurin da ta ajiye abincin ta fara sakawa Muhammad kamar yanda aka bata umurni.

“Ya ka koma jiya da dare?” Salima ta tambayi Muhammad wanda ya zauna kusa da ita yana mai gyara zaman drip ɗin da aka saka mata a hannu.

“Na koma na samu sun yi bacci, da yake ina da key ɗin ɗakinki sai na shiga na kwanta a can. Kin samu kin yi bacci kuwa?”

“Ban iya ba, saboda na san kana can hankalinka a tashe sai baccin ya ƙauracewa idanuna.”

Juwairiyya da ta ji abun ya fara yawa ta miƙo mishi plate ɗin abincin tana cewa,

“Zan iya komawa gida yanzu?”

“Eh ki tafi.” Shine amsar da ya bata ya ɗebi abincin wanda gwaten dankali ne ya kai bakin Salima ta buɗe ta ƙarba tana yiwa Juwairiyya wani irin kallo mai wuyar fassara.

Juwairiyya bata iya ko musu sallama ba ta fita daga room ɗin zuciyarta a cunkushe ta ma rasa me yake mata daɗi. Wai me yake faruwa ne? Menene haka? Me yasa suke mata haka?

Mum Fateey 👌

Tunda Juwairiyya ta koma gida bata zauna ba ta shiga kitchen ta ɗaura abincin rana, duk aikin nan da take yi kuwa tunani take yi na saurin canjawar Muhammad da kuma yanda yake mata tsawa wanda ta fi tsanan hakan akan komai. Idan laifi ta mishi me zai hana ya faɗa mata ta bashi haƙuri? Don me yasa zai dinga mata tsawa?

A farko ta ɗauka he was just hurting ne amma da ta ga abun ya ci gaba sannan shi da matarshi sun tasata a gaba suna wasu kalamai cringe worthy sai ta ga kamar akwai wani abu a ƙasa. Ko dai mutumiyar tata ce ta ƙara ɗana mata wani makircin? To gaskiya in dai haka ne zamanta da Muhammad ba zai taɓa musu daɗi ba, don a jiya da dare tana tare dashi wanda har furta mata kalmar so yayi sannan ta bashi jikinta willingly ta faranta mishi irin yanda ya ke so yake kuma haskowa a fantasy ɗinshi.

To menene kuma daga wannan mind blowing encounter ɗin zai dawo yana mata faɗa yana shareta kamar ba’a yi tsironta ba? Me ta mishi? Wani laifi ta yi da ta cancanci haka? Tana gama girki ta kirashi a waya ta faɗa zata kai asibitin.

“A’a ki bari kar gidan ya zama babu kowa. Ina zuwa in karɓa idan na gama abun da nake yi a cikin gari.”

“To shikenan.” Ta amsa mishi a sanyaye domin a yanzu sai ta ji muryarshi babu wannan tsawa da faɗan kamar an yi ruwa an ɗauke.

Tana alwala ya dawo da yake wannan karon bata rufe ƙofar falon ba ya shigo har cikin ɗaki ya kwanta a kan gado. A haka ta fito ta sameshi ya rage kayan jikinshi ya zauna daga shi sai dogon wando da singlet.

“Ka dawo?” Ta tambayeshi tana mai jawo sallayarta ta shimfaɗa.

“Na dawo.” Ya amsa yana bin duk wani motsinta da ido.

Kawar ta kanta tayi kamar bata ma san yana yi ba, ta lura idan jarabarshi ta ciwoshi baya ma tuna me ya yiwa mutum a baya kawai zai nemi buƙatarshi ne babu ko kunya. Tana idar da sallah ko fara addu’a bata yi ba ta ji muryarshi a tsakar kanta.

“Juwairiyya je ki duba na saka lock a ƙofar gida, in ban rufe ba ki yi.”

Babu musu ta tashi ta fita ta je ta samu ma ya saka lock ɗin amma ko ba’a faɗa ba ta sani akwai dalilin da yasa yace ta je ta rufen. A inda ta barshi a nan ta sameshi wannan karon yayi ruf da ciki, tana shigowa ta ce,

“Na duba ka rufe. Ga abincinka a falo ko in kawo maka nan?” Ta faɗi hakan tana cire hijabin jikinta.

“Zo ki matsa mini bayana da kafaɗuna.” Yayi kamar bai ji me ta tambayeshi ba.

Ɗan dakatawa tayi kaɗan ba tare da ta isa gurinshi ba, domin da ita da shi duk sun san me zai faru bayan massage ɗin, sai dai ita tunaninta bata yi wanka ba kuma tayi aikin kitchen ta haɗa gumi kaɗan bata son ya ji akasin ƙamshi a jikinta.

“Ina jiranki, in kuma ba zaki mini ba in tashi.” Wannan karon ma a sanyaye yayi maganar.

A hankali ta isa bakin gadon ta zauna a gefenshi kana ta saka hannayenta ta fara matsa mishi kafaɗun yana nuna mata gurin da yake so a yi da ƙarfi.

“Ki mini na hannayena, suma suna tsami.”

“Me ya faru ne jikinka yake ciwon?” Ta tanbayeshi domin ta san ba wai shagalinsu na jiya ne ya jawo haka ba.

“Da muka isa hospital jiya Salima ta kasa tafiya kuma duk gurin maza ne bana son su taɓata.” Ya tsaya a nan.

“Shine ka sungumeta kenan ka dawo jikinka yana ciwo?” Ta tambayeshi bayan ta dakata daga matsan da take yi.

“Eh. Ki ci gaba.”

Dariya ne ya kwace mata tayi saurin rufe bakinta wanda ita kanta sai da tayi mamakin hakan, she is supposed to be angry ya ɗauki matarshi jikinshi yana ciwo ya zo yana sakata matsa.

“Dariya kike mini?” Ya tambayeta da mamaki a muryarshi.

“Sorry amma kai sakali ne, yanzu duk jikin kan nan don ka ɗauki mace sai ka dawo kana wayyo wayyo?”

“Ni yaushe nace miki wayyo?”

“Ka ce ‘Wash wash’ shi kuma ‘wayyo wayyon’ sai gobe idan hannun ta kwana ta ƙara tsami.”

“Shi yasa ɗazu na bar miki ƙaton basket ɗin ki ɗauka don I’m not feeling my hands. Wanka ma da kyar na iya shafa soso.”

Wannan karon dariya Juwairiyya tayi sannan ta fara haɗawa da mugunta yana ƙara idan ta ɗaki gurin da ya fi ko’ina ciwo. Wani muscle ta kama da ƙarfin gaske yayi siririyar ƙara kana ya fincikota ta sauƙa a bayanshi, da haka ya mirgina da su ya dawo samanta yana mata kallon zaki gane kurenki.

“Why are you wicked?”

“Me na maka?” Ta faɗi hakan tana neman kwacewa amma ya sake mata nauyinshi kaɗan sai ta haƙura ta fara hararanshi cikin wasa.

Bai amsa ba ya canja salon wanda tun tana nuƙu-nuƙu tana faɗa mishi wai bata yi wanka ba tana tsami har ta bada kai wasan ya girmi hankalin yaro.

Sai da komai ya lafa ta ga har ƙarfe ɗaya da rabi tayi, ai da sauri ta sauƙa daga kan gadon ta ja zaninta tana cewa,

“Ka tashi ka kai musu abincin gashi nan har biyu saura kar su zauna da yunwa.”

“Ki kai musu, bacci nake ji.” Ya faɗi hakan yana jaye zanin da ke jikinta ya lulluɓe kanshi tare da juya mata baya.

Juwairiyya ji tayi kamar ta ciji ƙeyarshi tsabar mamaki da guntun takaicin da ya bata.

“Kai fa ka hanani zuwa ɗazu kace baka son a bar gidan babu kowa.”

“Yanzu ina cikin gidan ai. Ki je ki dawo kar ki jima, akwai kuɗi a cikin aljihun wandona ki ɗauka, ina wandon yake? Ko da yake ke kika san inda kika jefar.”

Juwairiyya ƙunshe bakinta tayi da yake son stretching, da kyar ta samu ta tsume kana ta ce,

“Wai da gaske kake yi ni zan fita da tsakar ranan nan?”

“Juwairiyya ki tausaya mini don tun jiya da dare idona biyu har yanzu ban samu na runtsa ba.” Yayi maganar a gajiye kamar ma  baccin ne ke ɗibanshi.

“Shikenan.” Tana faɗin hakan ta jaye zaninta ta rufe jikinta amma ko motsawa bai yi ba alamar he is done fighting bacci kawai yake so.

Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauko ƙaramin bargo mara nauyi ta lulluɓeshi dashi sannan ta tafi falo tana waya.

“Idrisa in kana kusa don Allah ka zo ka kaini asibiti.”

Minti goma da haka ta fita daga gidan ta samu Idrisa mai napep a waje ta shiga suka tafi. Ko da suka iso asibitin bai tafi ba tace ya jirata ba daɗewa zata yi ba, da haka ta shige ciki ta tasamma ɗakin da aka kwantar da Salima.

Da sallama ta shiga ta samu Salima na kwance akan gadon marasa lafiyan, gefenta kuma Mamanta ne da wannan ƴar’uwar tasu sai kuma Iyami da ƙanwarta Shema’u waɗanda suka zo gaisuwa.

Gaishesu tayi ɗaya bayan ɗaya tana haɗawa da ta’aziyya sannan ta isa gaban gadon bayan ta ajiye basket ɗin hannunta ta ce,

“Maman Hafiz ya jiki ya kuma ƙarin haƙuri?”

“Jiki da sauƙi, Alhamdulillah.”

“Ai tun ɗazu ƴar’uwar taki take ta jiran a kawo abinci ta taɓa ta sha maganin rana, to da yake kin kawo na safe sai nace kar a kawo daga gida gudun kar abincin ya taru a rasa mai ci.”

Shiru Juwairiyya tayi domin ta lura ko godiya basu mata ba tun daga na safen da ta kawo da kuma yna yanzu, a hakan kuma shine zata buɗe baki tana complain? Sannan ita ba laifinta bane, don da ta ita ce tun sha biyu abincin zai iso amma mijinsu mai siffar mutum da zuciyar hawainiya sai da yayi yanda zai yi aka kawo musu a makare. To amma me shirunta zai haifar mata idan bata cire kanta daga zargi ba? Don da alama Maman Saliman tana ganin kamar ta sakata a tight spot ne amma bata san cewa zata iya fitar da kanta ba don ba da gangan tayi hakan ba.

“Ayya kuyi haƙuri. Tun sha biyu na gama zan kawo muku maigidan yace in bari zai zo ya ɗauka baya son a bar gidan babu kowa. To da ya dawo kuma sai yace baya jin daɗin jikinshi in fita in kai shi kuma zai kwanta.”

“Subhanallahi, Allah Ya bashi lafiya.” Ƴan ɗakin suka mishi addu’a.

“Shi kuma Baban Hafiz ai da ya barki tun wancan lokacin kin fito tunda ya san shi ba ya jin daɗi.”

“Wannan mijin naku sai wani ya faɗa miki halinshi ne Salima? Na ɗauka kin fi kowa saninshi ta yanda duk abun da kika san zai aikata in aka ce yayi ba zaki musa ba.” Wannan faɗin Iyami kenan wacce ta kare Juwairiyya daga surutu amma bata san cewa tuni tayi hankali ta daina ba.

“Hmm Baban Hafiz sai a hankali, mutane ne basu fahimceshi ba.”

Wata siririyar tsaki Iyami ta ja wanda duk ƴan ɗakin sun ji don ita ta gaji da halin munafukar, ji ta ke yi kamar ta kurma mata ashariya ko ta je ta gwabje bakinta sai ya kawo jini. Saboda yanda tayi maganar sai a ɗauka ba ita ta fara saka mutane a hanyar kusheshi ba.

“Bari in tafi mai napep yana jirana a waje.” Faɗin Juwairiyya kenan tana miƙewa tsaye.

“Mu je ku sauƙeni a gida tunda hanya ne, dama Babansu ne zai zo ya ɗaukeni amma na tuna ina da abun yi a gida.” Itama Iyami ta miƙe tana gyara riƙon da ta yiwa ɗanta.

Da haka suka musu sallama suka bar Shema’u wacce tace ita kam sai daga baya zata koma gida, a cikin napep suna hira har aka iso gidan Iyami sannan ta sauƙa amma sai ta tsaya ta dubi Juwairiyya ta ce,

“Na jima ina son miki magana akan wani abu amma ban yi ba saboda bana son shiga hurumin da ba nawa ba ko kuma abun da ba’a gayyaceni ciki ba, to amma yau na kasa haƙuri zan faɗa miki. Na san ke da Salima ƙawaye ne don tare mu ka ganku kuma na san kin yi trusting ɗinta amma ki kiyayeta, sannan ki rage surutu a gabanta musamman abun da ya shafi mijinku ko ƴan’uwanmu don tana kaiwa gaba. Ki san yanda zaki zauna da ita kuma ni ban yi maganar nan da ke ba balle Ya Muhammadu ya ce ina son gwara kan matanshi.”

“Aunty Iyami nagode sosai, amma tun kwanaki na gane da wa nake zama.”

Ɗan murmushi kaɗan Iyami tayi tana kallon Juwairiyya sannan ta ce,

“Yanzu na ji dahir, don na yi mamakin a ce yanda kike da ilimi da kuma wayewa kina zaune da irinsu baki fahimta ba. Allah Ya sauwaƙe sai anjima ki gaishe mini da Ya Muhammadu”

Muskutawa Juwairiyya tayi kaɗan tana jin kunya a zuciyarta don ba ita ta gane ba sai da aka mata magana. Kenan dai da gaske bata da wayo da kuma ilimin da ake tunanin tana da shi.

Tana isa gida ta samu har lokacin Muhammad yana bacci wanda da alama mai nauyi ne, zuwa tayi kanshi ta zauna a bakin gadon tana kallon ƴar lukutar fukarshi mai kewaye da saje mai taushi. Yanda yake baccin so peaceful kamar innocent mutum amma nan cikin kwakwalwarshi faɗa ne taff da gadara.

Falo ta koma don ta sani in ta kwanta itama baccin zata yi kuma an kusa yin sallan la’asar tana son ta musu abincin dare ta yanda yana tashi daga bacci zai kai musu. Tana danne danne a waya ta ga an sakata a wani group mai suna ‘Talk With Tammy’ a nan ta samu messages fiye da ɗari uku ta fara karantawa. Tana farawa ta riƙe bakinta sannan ta shiga group description ɗin don ganin ƙarin bayani akai, a nan ne ta ga group ne na matan aure zallah da ake ƙara wayar musu da kai kan zaman aure wanda ya ƙunshi self care, yara, gida and uwa uba harkar cikin aza room.

Tana karanta messages ɗin tana starring abubuwan da duk wayewarta itama yau ta ke saninsu, wato gaskiya ne da aka ce ilimi kogi ne, komin saninka wani abun haka zai wuceka idan ba’a faɗa maka ba. A nan ta ga sirrin mintin Tom Tom da yanda ake amfani dashi wajen gigita maigida, ai kuwa da saurinta tayi starring voicenote ɗin tare da alƙawarin in Muhammad ya zama good boy zata gwada mishi.

Sai da ta gama karance-karancenta sannan ta fara tunanin wa ya sakata, a nan ne ta ga Hafsat a ciki wanda ta tabbatar ita ta bada numbernta aka yi adding ɗinta. Ai kuwa dole ta gode mata domin ta ƙaru da abubuwa masu yawa da zata gwadawa ɗan lukutinta. (PC me for more info).

Sai da tayi sallah sannan ta tashi Muhammad wanda da alama baccin bai isheshi ba, yana wanka a banɗaki ta kawo mishi lunch ɗinshi har ɗaki sannan ta fita ta ɗaura musu abincin dare. Cikin awa ɗaya da rabi ta gama ta dawo ta samu Muhammad ya ci abincin amma ya ƙara komawa bacci akan sallaya. Nan ma ta ƙara tashinshi ya farka yana mutsike ido yana cewa,

“An yi maghriba ne?”

“An kusa dai, yanzu ƙarfe biyar da rabi. Ga abincin dare na gama ko zaka kai musu.”

“Ina tunanin ma za’a iya sallamarta yau idan suka duba suka ga babu wata matsala.”

“To Allah Ya bata lafiya. Amma ni kam menene ya jawo pre-mature labour ɗin nata?” Ta tambayeshi don tana son sani amma ta kasa tambaya saboda bata samu fuska ba sai yanzu.

Shiru yayi har ta fara tunanin bazai yi magana ba sannan ya ce,

“Shiga da fice da kuma aikin da tayi da zan dawo ne ya jawo mata haka, wanda Doctors ɗin sun ce she overworked herself ne kuma ta ƙi nitsuwa guri ɗaya. Amma Juwairiyya me yasa baki tayata ba kika bar komai a hannunta alhali kin san tana da ciki?”

“Wannan shine dalilin da yasa yau da asuba ka mini faɗa?” Ta tambayeshi cikin tsananin mamaki domin dama sai da tayi zaton makirar ce ta kulla mata wani abun ashe da gaske ne.

“Baki bani amsa ba.”

“Baka faɗa mini kana dawowa ba saboda kana fushi da ni, ka ɗaukeni kamar ba matarka ba Muhammad. Kuma itama bata sakani a cikin harkokin sai dai kawai in ga anyi abu ba dai ta zo ta ce mini za’a yi ba wai nima in bada shawarata. Idan wannan ne dalilin da yasa ɗazu kake fushi da ni to ka daina don wallahi ban yi hakan da gangan ko don mugunta ba. Ni ce ma ya kamata in ji babu daɗi da kuka wareni a gefe kuna tafiyar da gidanku babu ni a ciki.”

Shiru Muhammad yayi yana tunani sannan ya miƙe ya ce,

“Ki haɗa abincin guri ɗaya, ina zuwa.”

“Na haɗa tun ɗazu. Baka ce komai ba.”

“Na ɗauka da gangan kika bar komai a hannunta, na gane yanzu.”

“Kai ma kasan mugunta baya cikin halina, in ka ce saurin hawa da faɗa na yarda amma banda cutar da wani da gangan.”

“Ni kuma da kike cutata fa?” Yayi maganar yana tashi tsaye ya matso daf da ita ya jawota jikinshi tare da kewayeta da hannayenshi.

“Ni? Yaushe?” Ta tambaya da ɗan mamaki a fuskarta tana murmusawa don ta san ba abun tashin hankali bane.

Magana ya faɗa mata a kunnenta ya barta cike da tsantsan kunya ya shiga banɗaki, kafin ya fito ta gyara kan gadon ta tattare komai. Tana zaune a bakin gado shi kuma yana shiryawa, a nan yake faɗa mata abunda ya faru jiya wanda yana maganan ta ga damuwa ƙarara a fuskarshi wanda hakan ya bata tausayi. Ashe tun kafin su isa hospital labour yayi nisa babu ta yanda za’a hana yaran fitowa, sai dai in sun fito a yi ƙoƙari wajen ganin sun rayu wanda hakan kuma zai yi matuƙar wuya saboda sun yi ƙanƙanta sosai. Ko da aka samu suka fiton babu wanda yayi minti biyar a duniya ya koma.

“Allah Ya baku wasu masu zama Ya kuma baku haƙurin rashi.” Ta mishi addu’a sincerely.

“Amin Amin.”

Bayan tafiyarshi ta koma ta zauna a nan ta fara tuna maganarta da Iyami, lallai mai sonka ne zai ga abun da zai cutar da kai ya faɗa maka. Dole zata ziyarceta ta kuma ƙara ƙarfafa zumuncinsu domin kuwa ita ce ƙanwa ɗaya tilo a gurin Muhammad wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya. Ta lura har yanzu Salima bata daina halinta na kitse-kitse ba, kuma da alama Muhammad yana ɗaukan duk abun da ta bashi labari kuma ba zai yi bincike ba. Yanzu wannan karon ma gani yake yi kamar da gangan ta barwa matarshi aiki wanda ya jawo zubewar cikinta, ai kuwa dole ranshi ya ɓaci amma kuka bai mata adalci ba saboda yayi saurin yanke hukunci haka kuma ya ɗauketa a matsayin muguwa wanda ba halinta bane, da alama har yanzu idanunshi a rufe suke bai san wacece Salima ba.

Sai ƙarfe goman dare ya dawo gida ya samu har ta kwanta amma bata yi bacci ba.

“Sannu da dawowa, ya mai jikin?” Ta tambayeshi tana tashi zaune dama chat take yi a whatsapp a sabon group ɗin da aka sakata ana new chapter tana kwasan ilimi.

“Da sauƙi, sai gobe za’a sallameta. Mu je ki bani abinci.” Ya faɗi hakan yana rage kayan jikinshi.

Babu musu ta tashi suka koma falo ta bashi abinci yana ci suna hira kaɗan kaɗan amma hankalinta na kan wayarta.

“Juwairiyya ki ajiye wayar nan in muna magana.”

“Sorry.” Ta faɗa tana dariya kaɗan.

“Me kike yi a wayar ne kina ta murmushi?”

“Yaushe ka koyi gulma?”

“Yanzu. What are you doing?”

“Babu fa, kawai wani group ne na ƙawayenmu.”

Bai ƙara tambayarta ba ya ƙarisa cin abincinshi ta tattara gurin ta koma kujerarta ta zauna amma wannan karon bata ɗauki wayar ba.

“Kin yi nisa, ki dawo nan.” Ya nuna mata gefenshi.

Kallonshi tayi ta wutsiyar ido ta ga ita yake kallo, da haka ta taso ta zauna kusa dashi yace ta ƙara mishi matsan, amma wannan karon na gaskiya don babu mugunta a ciki. Da suka kwanta kuwa tayi mamakin da bai nemi komai a gurinta ba domin ta gaji kaɗan tana buƙatar hutu, a jikinshi tayi bacci wanda a safiyar yau bata yi tsammanin zasu zauna inuwa ɗaya ba tare da sun ɓatawa juna rai ba.

Washe gari da hantsi aka sallami Salima ta dawo gida, a nan Juwairiyya ta samu labarin wai Salima zata yi jegon sati biyu don haka Muhammad zai yi wannan sati biyun tare da ita! Ji tayi kamar tace bata son hakan domin daga ita har shi lallaɓa juna suke yi gudun kar ɗaya ya fashe a koma gidan jiya wanda ita har ta fara gajiya da wannan rayuwar tana neman canji kafin ta ga abunda Allah zai yi gaba. Sai dai bata ce komai ba, ƙarshe ta karɓi hakan a matsayin wani dama da zai sa ta san waye Muhammad sannan ta nuna mishi itama tana da kyawawan halaye ba wai duk abunda matarshi ta faɗa zai ɗauka ba.

Kwana uku da haka da safe ta tambayeshi akan zata je gidan Iyami da Mama yace ta jira in zai fita su tafi tare, hakan aka yi, misalin sha biyu na rana suka fita ya sauƙeta a gidan Iyami shi kuma ya wuce da motar Salima wanda Juwairiyya ta tabbatar Saliman ce ta bashi ya riƙe tunda ya sayar da tashi kuma ba jimawa zai yi ba zai koma karatunshi.

“Duk da cewa na jima da Salima wallahi ban game ainihin halinta ba sai da aka ɗauki lokaci mai tsawo, da farko ban yarda ba amma da na dinga tuna wasu events na yanda take manupulating harshena sai na yarda. I was hurt, wanda wallahi zan iya ce miki shine ma farkon abun da ya dameni har na fara ramewa. Ni ban iya munafurci ba Aunty Iyami kuma da tun farko ta nuna mini ainihin abun da yake cikin zuciyarta da tuni na san inda dare ya mini.”

“Kina nufin kashe auren zaki yi ki bar mata gidan?” Iyami ta tambayeta cike da mamaki.

Shiru Juwairiyya tayi tana murmusawa kaɗan amma daga ita har Iyami sun san na ƙarfin hali ne.

“Kar ki fara wannan tunanin don Allah balle har ya kai ga ki kin aikata. Ki sa a ranki akwai dalilin da yasa Allah Ya haɗaki da Ya Muhammadu wanda idan kin karanci gidanshi wallahi zaman ciki ba zai baki wahala ba. Ina son zamanku tare don haka zan faɗa miki waye Ya Muhammadu sannan kuma wacece matarshi Salima!”

Mum Fateey 👌

“Kamar yanda kika sani mu uku ne a gurin mahaifiyarmu to hakan ne bamu da wani shaƙiƙi. Kin san an ce ‘ciki mai haife-haife’ to kuwa ba’a yi ƙarya ba domin kuwa kowa da kika gani da halinshi. Ya Muhammadu shi ya fito a cikin mu mai baya son magana komai aka yi sai dai ya bi da ido, amma da an taɓashi ko kuma mu ƙannenshi muka mishi raini ba zai haƙura ba. Mun daku a gurinshi, hakan yasa bayan Maman mu ta bar gidan na wasu shekaru ita kuma Matar Babanmu ta sauƙe duk wani haushinshi da take ji na dukan mata ƴaƴa da yayi. Tana yawan kai ƙararshi gurin Babanmu wanda ko ya kirashi yana mishi faɗa ba zai tambayi me yayi ba sai dai in ma duka ne a dake shi, in ma hukuntashi a yi yana shiru.”

“Akwai wani lokaci da aka taɓa zuba gishiri mai yawa a miyan Baba. Baba ya kira matarshi yana faɗa ta ce miyan gidan lafiyarshi kalau don kowa ya ci ba’a yi complain ba. Baba ya ce ta ɗanɗana in ƙarya yake mata, ta ɗanɗana ta gigice sai da aka bata ruwa ta wanke bakinta sannan ta fashe da kuka wai duk yanda aka yi wani ne yayi amma ita kam ba ita ba ce. Duk gidan kuma mu ne manya saboda Mamanmu ce Uwargida, su Shema’u yara ne da basu da yawon buɗe kula su zuba gishiri sannan su gauraya su rufe ba tare da kowa ya gansu ko kuma sun zubar da gishirin a bakin kula ba. Ƙarshe dai laifi ya dawo kan Ya Muhammadu saboda Ya Abdallah tare suka tafi shago da Baba kuma yanda kika ganshi shiru-shiru yanzu haka yake tun da. Ya Muhammadu kuwa kowa ya san halinshi na taurin kai sannan shi ya samu matsala da ita da safe wanda sai da Baba ya dakeshi kafin ya fita shago. Ko da aka kirashi ya ce bashi bane aka ce ina yake tun ɗazu yace yana tare da ni, kuma wallahi tun da hantsi ya sakani a gaba da tarin wankin kayana akan dole sai nayi saboda bani da uwar da zata tilasta mini in yi ko ta bawa almajirai su mini. Ina kuka ina wankin nan wanda sai da nayi wayo na gane bani nayi wankin ba wallahi shine, don ɗaurayewa ne aikina da kuma ɗebo ruwa a Reservoir don Matar babanmu ta hanamu buɗe na Famfo wai zamu ƙarar da na tankin sama. Juyin duniyar nan ya ce bashi bane kuma shi kaɗai ne ya shiga kitchen ya ɗauko abincinshi ya fita, Juwairiyya ba shi ya aikata ba don ba halinshi bane amma haka Baba ya yarda a cewarshi yayi hakan ne don dukan da ya mishi da safe. Wannan dalili yasa Baba yace zai mishi hukunci mai tsauri ta yanda nan gaba ba zai ƙara wulaƙanta abinci ba, sai da dare Baba ya kirashi yace daga yau bashi da kwano a gidan sai in mun ci abinci mun rage ya ci saura, kuma ko mun cinye akan jagwalgwalon namu za’a ɗaura mishi sabo a bashi.”

“Wayyo Allah.” Juwairiyya ta faɗa tana rufe bakinta zuciyarta na zafi da ta tuno kwaɓa mishi abinci da take yi idan ya ɓata mata rai, wanda ya faɗa mata kaɗan daga cikin dalilin da yasa baya so amma tayi amfani da hakan wajen ƙuntata mishi tare da tuna mishi painful past ɗin shi.

“Wani abu ne?” Iyami ta tambayeta da ɗan mamaki a fuskarta.

“Na taɓa yi mishi haka.” Ta bata amsa ba tare da ta faɗa mata duka ba.

“Saliman ai ta zo tana faɗa wai kina kwaɓa mishi abinci yana zuwa ɗakinta yana ci, ita tana tsoron kar mutane su ce ita ta kitsa mishi, a lokacin ina tunawa na buɗeta na ce idan bata zo ta faɗa ba wa zai sani tunda ba a gidan muke zaune ba? Mu bar wannan maganar don ba shi muke yi yanzu ba.”

Gyaɗa kai kawai Juwairiyya tayi tana jin takaici da baƙin ciki domin ta lura kalar kashinta ne kaɗai dangin Muhammad basu sani ba, saboda hatta abun da bata yi tsammani an yayata ba ta ji shi yau. Salima kam wace irin mutum ce mara rufa asiri? Me yasa take son ganin an tsaneta an ga aibunta? Me yasa kuma ta bari ta mata wayo har ta gama ɓatata a cikin dangin Muhammad ba tare da ta gane ba?

“A farko Ya Muhammadu ya ƙi cin abincin ya fara zama da yunwa, ƙarshe ya fara shiga makwabta idan zasu ci abinci ya ci tare dasu, da ta gane sai ta faɗawa Baba shi kuma ya hanashi shiga ya kuma aika gidajen wai ko ya zo kar a bashi abinci. Hakan kuma aka yi suka daina bashi saboda babu wanda yake son samun matsala da Babanmu don yana mutuntasu suma suna mutuntashi. Da Ya Muhammad ya ga yunwa zata kasheshi sai ya fara ƙarɓan abincin kuma a lokacin ba wani girma yake da shi ba balle ya kama sana’a ko kuma ya je can gurin Mamanmu da take nesa da mu ya ci ba. Ya fi wata huɗu a wannan hali sannan Baba ya ce a bashi kwanonshi, amma hakan bai hana in ya yi mata laifi ta horeshi da hakan ba tunda a baya an mishi hakan ta gani.”

“Rayuwar da yayi a baya yasa ya zama bashi da saurin yarda da mutane, sannan baya son raini da ƙasƙanci ko ƙadan kuma bashi da abokai sai tsohon mijinki da wasu da za’a kirasu da abokan zumunci. Ina faɗa miki haka ne don ki san waye mijinki, a nan kuma zaki gane me zaki iya canjawa game dashi da wanda kuma sai dai kiyi haƙuri ku lallaɓa rayuwarku a haka.”

A nan Iyami ta ƙara da cewa,

“Ya Muhammadu yana son a nuna ana sonshi, yana kuma so a nunawa duniya cewa shi mutum ne mai muhimmanci. Sannan ba ya son musu ko kuma ya ce abu kaza ne, ke kice ba haka bane domin ta wannan hanya ne Salima ta samu kanshi cikin sauƙi ba tare da ta wahala ba. Duk abun da ya sakata tana mishi kuma ko menene ya hanata zata hanu, hakan yasa ta samu damar saka mishi wata banzar akida na cewa shi kowa sai ya bishi irin yanda yake so kuma ba tare da an nuna abun da yake yi ba mai kyau bane. Tun kafin ya ƙara aure na san duk matar da zai ƙara a gaba zata wahala a gurin shi da kuma matarshi.”

“Salima kuma halinta ya fara ne daga can gurin uwarta da ta hana kowacce mace zama a gidanta, idan kin ji labarin irin makirci da kuma wayon da take yi har a saki kishiyoyinta zaki ɗauka tare da shaiɗan suke zaman shawara. Magana wannan ke zaki yita ba da wata manufa ba amma su zasu iya canjata ta dawo babba kuma laifi mai girma. Suna da shiga mutane da nuna halin shiru-shiru, suna kuma nunawa duniya cewa suna son kowa basu da abokin faɗa shi yasa kwanaki da kika ce mata ta daina kulaki kowa yayi harkarshi aka yi ta magana kan cewa ke kike nemanta da faɗa ba kya son zaman lafiya da ita.”

“Idan zaki zauna da Salima itama sai kin koyi tactics ɗin munafurcinta, na farko ko giya kika sha kar ki kuskura ta miki gulman mijinku ko ƴan’uwanmu kema ki tsoma baki. Idan zaki iya ki saurareta don a hakan zaki tsinci wani abu amma ko uffan kar ki furta, daga nan sai ki canja muku taɗi. Na biyu idan zaku zauna kuyi hira ya kasance na rayuwar duniya kuke yi wanda ko ta fi shaiɗan ƙoƙari ba zata iya zuwa ta canja hiran naku ya zama abun magana ba. Na uku don Allah ki cire duk wani abu da yake zuciyarki akan Ya Muhammadu ki kasheshi da biyayya ta nan ne kaɗai zaki faɗi abun da kike so ya miki kuma ku zauna lafiya. Sannan ki nuna mishi so don yana son a so shi, ta haka kuma shima zai nuna miki nashi kalar soyayyar. A ƙarshe idan kin kama mijinki a hannu kuma kin karanci salon Salima sai ki kada ita a wasanta! A’a ban ce ki munafurceta ba amma dole ne ki koyi wasu daga ciki don ta nan ne kaɗai zaki gasa mata gyaɗa a hannu kuma ta kasa jefarwa.”

“Sannan a ƙarshe zan baki wasu shawarwarin da ya danganci ƴan’uwanmu, ki jawo mutane jikinki! Tunda kika shigo baki taɓa zuwa gidajen wasun mu ba wanda dama tun farko a bayan Salima suke suna tayata kishi, daga baya kuma da maganganu suka fara fitowa na halinki sai suka ƙara ɗaurashi akan list ɗin abubuwan ƙin ki. Ke kuma da kika zo maimakon ki sayesu da halaye nagari wanda kike dasu sai kika biyewa zuciya kika share kashinsu ba kya shiga cikinsu. Kamar yanda tayi kema haka zaki yi, ya zama kema kowa naki ne, kar ki bari a ce wannan abokin faɗanki ne ko bakwa shiri. Kin ganni nan? Halina irin naki ne na zuciya da saurin fushi amma duk yanda na kai ga son janye Salima a jikina na gagara, tana da nacin bala’i da kuma tusa kai ta yanda kai mai tureta kai za’a ga laifinka ba nata ba. A ƙarshe kai za’a zaga ba tare da anyi tunanin halinta ne yasa kake gudunta ba, ita kuma sai a ɗauketa a matsayin mai son zumunci amma ana wulaƙantata.”

“Ki fara shiga dangin mahaifiyarmu domin su basu da matsala hasalima su basa ɗaukan maganar Salima don yana musu kamance da irin na Matar babanmu da ta kori mahaifiyar mu a gidanta. Ki san na kusa da na nesa ki ziyarcesu ki kuma ja su a jiki. Dangin Babanmu kuma sai na miki tsinta amma dai suma kar ki ware ki dinga zumunci da su, sannan shaƙiƙaina wanda muke uba ɗaya muna son junanmu sai dai abun da ba’a rasa ba wanda dama dolene a kowanne family, suna da ɓarin zance da son kwaƙulo laifin mutum, hakan yasa da Salima ta fara kawo musu zancenki suka zama tiff da taya don kullum daga bakin Shema’u nake jin labarin zaman gidanku wanda ita ala dole tana son karkato da hankalina ne kan Salima tunda na nuna ita bata gabana. Kiyi zumunci da su daidai misali amma gulma ko halin Ya Muhammadu kar ya shiga tsakaninku don zaki ji shi a gaba.”

“Akwai kuma wani abu da zan ƙara faɗa miki shine kar ki dinga kai ƙararta gurinshi in ba dai ta miki abun da dole sai ya shiga ciki ba. Wani abu da ya burgeni da ke kuma nake so ki ci gaba da yi shine rashin yin maganarta da kowa. Tunda nake da ke baki taɓa cewa ta miki kaza ba, kuma ko hirarta bakya kawowa saɓanin ita da duk inda aka zauna sai ta san yanda zata yi ta faɗi ɗaya wanda za’a ga laifinki a kusheki. Ki barta ku tafi a haka don ance munafurci dodo ya kan ci mai shi, aje aje watarana su masu sauraron nata zasu dawo suna haɗa ɗaya da biyu, a nan ne kuma zasu gane waye munafuki a cikinku. A yanzu daɗin gulmar ne yake ɗibansu amma idan suka fara gajiya zasu dawo kan hanya ita kuma zata sha kunya. Idan kuma maganarta ya shigo cikin hiranku ki yabeta kar ki kusheta wannan ma wani daraja zai ƙara miki a idon mutane.”

“Na san kin san ba’a biyewa miji a shiga haƙƙin kishiya, don idan kika shiga wallahi sai Allah Ya saka mata duk mugun halinta kuwa, ki guji shiga haƙƙinta. Kar ki saka ido akan abun da yake mata ko kuma ki ce ke dole dole sai ya daidaitaku a mu’amala da kuma kula, hakan zai yi wuya amma idan kina haɗawa da Allah komai zai zo miki da sauƙi. Ki sa a ranki dole zaki ga ba daidai ba saboda yana son matarshi ya aurota haka kema, idan kin sakawa ranki haka to ko an yi wani abun don a baƙanta miki ne ke ba zai dameki ba domin dama kin ajiye zai iya faruwa. Wai in ji batura yace ‘expect the worse’ ta yanda idan bad ya zo zaka ji kamar ba komai bane. Ki kuma samu wata sana’a da zaki dinga yi yana kawo miki kuɗi don wani abun in kin gani a tare da ita ba shi ya mata ba gidansu ne suka mata tunda suna da kuɗi.”

“Wallahi sharri suke mini na cewa wai tana yin mota na fara ramewa.” Juwairiyya ta faɗi hakan tana jin zafi a ƙirjinta don ita motar Salima bai tsone mata ido ba.

“Kin ji labarin kenan? To dai ga shawarwari wanda in kin gwada zaman gidan Ya Muhammadu ba zai baki wahala ba don komai zaki dinga ganinshi ne a tafin hannunki. Na faɗa miki waɗannan abubuwan ne don karki zama irina, kwanaki can sai da aurena ya mutu a kan kishiya saboda munafurcinta da wayonta da yake ni kam dama ta haifeni, wahalan duniya yasa nayi hankali amma dai ban koma ba sai da ya raba mana gida. Yanzu tana can ni kuma ina nan amma a hakan wani abun ban tsira ba tana bina. Shi yasa ina fara zama da Salima na gane duk halinsu ɗaya nake kuma tausayawa Ya Muhammadu da Allah Ya bashi makirar mace wacce ta rufe mishi ido bai gane halinta ba har yanzu.”

Wata wawuyar ajiyar zuciya Juwairiyya ta sauƙe tana jin tausayin kanta da kanta, ta yaya zata iya zaman kissa da Salima alhali ita bata iya ba? Iyami kawai faɗa take yi a baki kamar babu wani wahala amma to put it in to practice shine wahalan. Godiya ta yiwa Iyami babu adadi domin ko Mama da ta haifeta bata faɗa mata wasu dabarun haka ba saboda bata zauna da kishiya ba.

Jiki a sanyaye Juwairiyya ta kira Idrisa ya kaita gidan Mama bayan Iyami ta ƙara mata wasu shawarwarin. Tana zuwa gida ta samu Sumayya ma ta leƙo zata yiwa Mama la’asariyya, nan hira ta ɓarke tsakanin ƴan’uwa biyun Mama ta yi kasaƙe tana kallonsu cike da ƙaunar su.

“Ya kuke dai?” Mama ta tambayi Juwairiyya bayan sun keɓance.

“Lafiya kalau Mama, yanzu kam abubuwan da sauƙi sosai don ko ni dashi mun samu fahimtar juna.”

“To Alhamdulillahi. Addu’ata ta karɓu domin tun wancan lokacin da kika faɗa mini halin da kuke ciki na duƙufa da addu’a ina tashin dare akan wannan aure naki Juwairiyya. Don Allah ke ma ki kai zuciya nesa ki dinga haƙuri a zamanku. Allah Ya ƙara rufa muku asiri duniya da lahira.”

“Amin, Amin Mama nagode da jajircewarki a garemu. To gaskiya addu’arki ta karɓu domin ni kaina kwana biyu ji na nake yi kamar ba ni ba. Da haka kawai ina zaune sai in ji raina yana ta ɓaci ba gaira ba dalili, haka kuma da an mini abun da bai gamsheni ba sai in hau fushi, wallahi Mama yanzu kuma jin kaina nake yi kamar an sauƙe mini wani lodi a zuciyata. Allah Ya bar mana ke domin addu’arki ce ta jawo haka.”

Shiru Mama tayi tana kallon Juwairiyya sannan can ta nisa ta ce,

“Juwairiyya kina azkhar da kuma tashin dare da nace ki dinga yi kwanaki don nemawa kanki sauƙi?”

Guri yayi shiru kamar an ɗauke wuta.

“Wato ba kya yi?”

“Mama ina azkhar amma sallar daren ne ban yi ba.”

Irin faɗan da Mama ta yiwa Juwairiyya sai da ta ji dama ƙarya tayi mata, amma faɗan ya shiga jikinta musamman da Maman ta ce,

“Yanzu kika sani ko wani abun ne yake ɗawainiya da ke amma da na duƙufa da addu’a Allah Ya yaye miki? Na sanki da zuciya da kuma faɗa amma na kwanaki yayi yawa har na fara tsammanin mugun halin da suke miki ne yayi yawa kika dawo haka. To wallahi ki riƙe addu’a domin ita ce takobin mumini, wani baki ɗaukeshi a bakin komai ba amma shi ya ɗaukeki a komai kuma zai iya miki mugunta ba tare da ya ji tsoron Allah ba.”

“Kiyi haƙuri Mama in sha Allah zan canja.”

“To Allah Ya sa. Allah Ya kareku daga sharrin masu sharri Ya kuma muku albarka.”

Sai daf da maghrib Muhammad ya kira Juwairiyya wai yana hanya idan an yi sallah zai zo ya ɗauketa. Hakan kuwa aka yi, kafin ya iso Juwairiyya ta gyara fuskarta har da saka turaren Surayya sannan ta fita ta mishi iso ya biyota don ya gaishe da Mama. Suka gaisa cikin mutunci tare da ƴar hira kaɗan sannan suka yi mata sallama suka fita bayan Muhammad ya ajiye mata provision kaɗan a leda.

Suna shiga mota Juwairiyya ta tsaya tana kallonshi domin sai take ganinshi kamar wani sabon halitta, lallai Hafiz yayi gaskiya da yace Muhammad mutumin kirki ne kawai baya son raini ne! Tabbas ta yarda domin idan ta tuna zaman da suka yi a baya duk shiriritar da take mishi baya taɓa mata hukunci mai tsauri, yawanci ma barinta yake yi ya fita a harkarta. Muhammad is a good Man but a little messed up wanda laifin matar babanshi ne da kuma Salima da ta ɗaurashi kan wasu halaye da haka zai yi zato daga kowacce ɗiya mace.

Kunna motar yayi kana ya juyo yana kallonta yana murmusawa ya ce,

“Ya dai?”

“You are a good man Muhammad!”

Zata iya rantsewa ta ga lokacin da ƙirjinshi ta ƙara faɗi da ta faɗi hakan, wannan karon murmushin shi ya fi na koyaushe ya kafeta da ido yana kallonta itama shi take kallo da nata salon murmushin mai cike da so da kuma tausayi.

“Thanks.” Ya faɗa kana ya juya don yin reverse amma Juwairiyya ta dakatar da shi ta hanyar ɗaura yatsunta a kan kumatunshi ta ce,

“And I love you.” Da haka ta haɗe bakinsu guri guda cikin kwarewa ta mantar da shi a wani duniyar yake.

Seconds goma da haka ta janye jikinta a hankali tana mai kallon fuskarshi wacce ta canja yanayi zuwa kasala tare da wani abu da zata iya fassarashi da…..

“And I love you too Jay.”

Ya faɗa da bakinshi ba tare da ya bari ta wahala ba, murmushi ta yi wanda yasa dimple ɗinta ya lotsa sai can kuma ta karkata kanta kaɗan ta ce,

“Da me ka kirani?”

“Jay. Ko bakya son sunan? Jay Masifa.”

Ƙanƙame mishi wuya tayi cike da murna don ita a rayuwarta tana son miji ya saka mata nickname da zai dinga kiranta dashi.

“I love it amma banda masifan. Kuma ban kai ka ba.”

“Ni yanzu ina da masifa?” Ya tambayeta yana mai yin reverse bayan ya tabbatar wannan karon ba za’a yi ambushing ɗinshi da kiss ba.

“Ni ban ce ba, cewa nayi you are my big baby.”

“Ba haka kika faɗa ba. And I don’t mind being your big baby as long as you feed me Apple.” Ya faɗi hakan yana kallonta kaɗan ta wutsiyar ido ba tare da ya daina murmushin ba.

“Zaka canja mana hira ni ba maganar Apple nake ba.” Ta faɗi haka a shagwaɓance wanda har mamakin kanta take yi, amma dai abun da ta sani shine zata canja musu tafiyar tasu don Salima ta kwashi kashinta a hannu, sannan zata canja don Muhammad domin bata son rabuwa dashi, sannan zata canja don wanke mishi ido ya gane wacece Salima.

“Muhammad.” Ta kira sunanshi tana mai dafa cinyarshi.

“Na’am.”

“Tun farkon haɗuwarmu na yi maka abubuwa da dama wanda baka cancancesu ba, har ta kai da muka yi aure ban daina ba. Na maka rasar kunya, na faɗa maka baƙar magana, na fita ba da izininka ba, na hanaka kaina sannan na kasa ganin alkhairanka a gareni. Amma yanzu da TAFIYAR MU tayi nisa sai na gane irin haƙurin da kayi da ni wanda a yanzu ni ce mai waving white flag ɗin. I’m so sorry for all the hurtful words that I said a baya, kuma don Allah ka yafe mini fitan da nayi ba da izininka ba da kuma hanaka kaina da nayi. Ina son canja TAFIYAR MU! Change with me, will you?”

“I’ll try Jay, I will.”

Mum Fateey 👌

Tunda suka kama hanyarsu ta komawa gida basu sake magana ba, shiru ne ya wanzu a cikin motar wanda hakan ya musu daɗi dukkansu domin tunanin juna suke yi duk da cewa kuwa gasu nan kusa da juna. Lokaci-lokaci Juwairiyya na juyowa ta kalleshi tana jin wani irin sonshi na ratsa mata zuciya har tana jin tsoron hakan gudun kar ya canja a dawo gidan jiya.

Shi kuma Muhammad ta wutsiyar ido yake satan kallonta idan ya samu sarari yana jin wani farin ciki a ranshi domin Allah Ya nuna mishi ranar da ya daɗe yana muradi wato ranar da Juwairiyya zata yi admitting daga zuciyarta da kuma bakinta cewa tana dana sani game da neman afuwarshi akan zaman da suka yi a baya.

Tun tafiyarshi UK yake tunaninta akai-akai kamar yanda yake tunanin Salima da kuma ɗanshi tilo Hafiz Junior, sau da yawa sai ya ɗauki waya zai kirata sai ya fasa idan ya tuno ba lallai bane ta biye mishi su yi hira ko kuma ta faɗa mishi abun da zai sanyaya mishi rai ba. Ya so yayi video call da ita kamar yanda yake yi da Salima amma ta ƙi, da ya gwada sau huɗu bata ɗauka ba sai ya haƙura domin ko bai ganta ba ya san tana cikin ƙoshin lafiya saboda Salima tana faɗa mishi haka kuma yayanshi Abdallah da yake zuwa dubasu duk sati yana faɗa mishi. Watanshi shida a can Salima tace tana son zuwa amma ya nuna mata bashi da kuɗin da zai iya biya mata Visa tayi haƙuri zai dawo idan ya cika shekara ɗaya. Bai sani ba Salima ta fara neman Visa wanda sai kiranshi tayi tace an samu, bai so hakan ba domin baya son tana amfani da kuɗinta akan abun da ya shafeshi, idan bashi da shi su haƙura idan kuma yana dashi zai yi.

Ta je har ta dawo, bayan dawowanta ne kuma ya samu matsala da Juwairiyya wacce halin kafiyarta yake ɓata mishi rai sosai ba kaɗan ba, kamar kullum wannan karon ma fita yayi daga harkarta sannan ya hanata fita unguwa ko zata yi hankali, ƙarshe da ya ga ba zata nemeshi ba ya bawa Salima saƙon cewa ta je. Bai faɗa mata dawowarshi bane don hakan ma na ɗaya daga cikin punishment ɗinta, sai dai yayi mamaki sosai da Salima bata sakata a harkan gidan ba wanda har hakan ya jawo mata miscarriage. Ya dawo ne da zumuɗi game da marmarin ganinta, shi yasa da ya ganta a rame ya kasa controlling kanshi ya jawota suka ci abinci tare wanda hakan shine na farko a rayuwar auren nasu wanda zai so ya ci gaba da faruwa saboda ƙara danƙon ƙauna da ke tsakaninsu.

Bai yi zaton Juwairiyya zata yarda da muradinshi ba amma ya lura da ya furta mata kalmar so sai ya ga jikinta yayi sanyi ta ajiye tsiwa da rashin jin magana a gefe ta faranta mishi irin yanda yake so. Me yasa tun da bai gane cewa hakane weakness ɗinta ba? A yanzu da ya gane lagonta sai shima ya fara koyawa kanshi nuna mata soyayya da kuma a baki duk da cewa bai kware ba.

A yau kuma ta bashi mamaki, mamaki na sosai wai Juwairiyya ce take neman afuwarshi tare da faɗin tana son gyara rayuwar aurensu? In da zai bayyana mata yanda yake jindaɗi da farin ciki a cikin zuciyarshi wataƙila zata iya tsorita ko kuma ta mishi dariya har abun ya zama abun tsokana daga baya, amma ya daure ya cigaba da murmusawa sannan daga lokacin bai ƙara cewa komai ba suka zauna a comfortable silence har suka iso gida a lokacin ana kiran sallah isha.

A bakin gate yayi parking ya ga tana ƙoƙarin fita daga motar zata buɗe mishi gate amma ya hanata, domin kuwa ɗazu da ta buɗe mishi da safe ya ga yanda wani mutum mai wucewa ya zura mata ido a lokacin da ta rankwafa zata tura gate ɗin, zuciyarshi tayi zafi amma bai nuna mata ba. Sai a lokacin kuma ya tuna idan Salima ce take buɗewa har rawa mazaunanta suke yi, to ita kuma wani irin kallo ake mata? Don haka daga yau zai hanasu buɗe gate, idan kuma ya koma Salima ta fara fita da motarta zai hanata fita da gyale muddin ta san zata ja gate, ta saka hijabi zai fi suturtata.

“Ki bari.” Shine kawai abun da ya faɗa yana mai buɗe nashi gefen ya fita.

Da ido kawai Juwairiyya ta bishi cike da mamaki domin wannan buɗe gate ɗin na ɗaya daga cikin abunda Salima ta koya mishi ita kuma bata son a ci gaba da yi amma bata san hanyar da zata yi ta hanashi ba, duk da bata da masaniyar cewa an daina yi ne gaba ɗaya bai hanata jin sanyi a ranta ba ko da kuwa na yau ne. Da alama dai yau yana cikin shauƙin soyayya kuma zata yi enjoying every bits of affection da zai gwada mata.

Yana parking ta fito ta wuce bakin ƙofar Salima ta kwankwasa mata aka ce ta shigo ta murɗa handle ɗin ta shiga. Salima ta samu zaune a kan kujera da bowl ɗin fruits a cinyarta tana sha a hankali, gefenta kuma Nanayo ce zaune a ƙasa tana kallo wacce a yanzu ko gaishe da Juwairiyya bata yi amma bata damu ba don ita tama fi son hakan. A ɗayan kujerar kuma Salwa ce ƙanwar Salima itama tana kallon da alama kuma hira suke yi amma shigowanta yasa suka yi shiru.

“Amarsu kin dawo?” Faɗin Salima tana mai murmushin yaƙe sannan ta miƙa bowl ɗin hannunta bayan kujera inda HJ ke wasa ya karɓa, da alama dama abun da yake jira kenan.

“Na dawo. Ya muka barki da jiki?” Juwariyya ta amsa tana mai murmusawa na cin nasara duk da cewa nasaran bai zo ba.

“Jiki Alhamdulillah na wartsake. Ai yanzu muke hira da Salwa nake cewa tunda muke baki taɓa shiga motata ba sai da Baban Hafiz ya dawo sannan kika shiga.” Tayi maganar a daidai lokacin da Muhammad ɗin ya shigo falon domin dubata kamar yanda yake yi kullum a rana sau uku ko sau huɗu kafin ta gama jegon nata na sati biyu.

“Da fatan dai kin faɗa mata cewa baki gayyaceni bane shiyasa ban shiga ba?” Juwairiyya ta mayar mata da amsa mai tambaya har lokacin murmushi bai bar fuskarta ba.

Salima bata amsa ba ta ɗan rankwafa kaɗan daga zaunen ta yiwa Muhammad sannu da zuwa ya amsa sannan ya tambayeta jikinta.

“Da sauƙi Alhamdulillah. Ka ji amaryarka zata min sharri ko? Wai ban taɓa mata tayin shiga mota ba alhali ko da na gayyaceta ta zo ta gani ƙi tayi. Shi yasa na ji tsoron ce mata ta zo ta sha ɗani.” Salima ta faɗa kanta tsaye da alama yanzu ta ƙara kwarin wuya a gaban Juwairiyyan zata fara magana ba wai a bayanta ba.

Juwairiyya sai ta rasa abun faɗe domin idan tace dalilin su Maman Hanan suna gurin ne zai zama bata da hujja, kuma zai iya cewa me yasa daga baya bata je ta gani ba in ma tsoron makwabtan take yi? Salima ta sakata a kwana sannan bata san ya zata fitar da kanta ba. Yanzu ko a da bai yarda tana mata hassada ba to yanzu kam zai yarda tunda gashi a gabanta ta faɗi abun da tayi amma ta kasa kwatar kanta, shi yasa take faɗawa Hafsat da Iyami cewa ita bata iya kissa ba balle ta gwabza da gwanar ba.

Muhammad ne ya fara fita wanda ko kulasu bai yi ba don bai ga dalilin sakashi a cikin maganarsu ba.

“Ai ranar da aka kawo da dare na fito kitchen na gani tun a lokacin, shi yasa da kika mini magana washegari na miki fatan alkhairi kawai.”

“Shikenan yanzu kam magana ya wuce ai tunda yau kin shiga cikinta.” Salima ta faɗa cike da jindaɗin wannan magana da suke yi.

“To sai da safenku.” Faɗin Juwairiyya tana murmusawan dole wanda tana fita ta ɓata fuskarta.

“Mata sai shegen neman laifin mutum!” Ta faɗi hakan a hankali tana mai buɗe ƙofar falonta ta shiga ta samu Muhammad yana ƙoƙarin fitowa don tafiya masallaci.

“Me zamu dafa na dinner?” Juwairiyya ta tambayeshi a sanyaye a ranta kuma fata take yi ina ma ya yarda ta musu reheating ɗin leftover su ci kawai.

“Kiyi duk mai sauƙi.” Ya amsa mata yana mai saka takalminshi da ke bakin ƙofa.

Tura baki tayi don ba haka ta so ba, ta kalleshi ta wutsiyar ido tana jin kamar ta muntsineshi.

“Wa kike turawa baki?” Ya tambayeta yana mai takowa zai zo gurinta ta ja da baya da sauri amma sai ta ga shima ya dakata da kanshi.

“Ya ka tsaya, ka ji tsorona ne?” Ta tambayeshi tana mai ɗaga girarta ɗaya sama.

“Zaki karya mini alwala ne. Ki bar girkin kawai dama bana jin yunwa sosai.”

Murmusawa tayi tana jin zuciyarta na mata nauyi yana kuma swelling domin ta sani ya faɗi haka ne don ya lura kamar bata son yin girkin.

“A’a zan yi, idan ban maka ba wa zan yiwa big baby? Ka tafi kar ka rasa Jam’i.”

Ya kai seconds uku yana kallonta sannan ya juya ya tafi, kaɗa kanta tayi kana ta shiga ɗaki ta cire gyalenta tare da adanashi sannan ta fito zuwa kitchen ɗinta. Couscous ta musu wanda aka yi frying ɗinshi da kwai da veggies, cikin minti talatin ta gama a lokacin har Muhammad ya dawo ta ga shigowanshi.

Sai da ta jera komai kam center table sannan ta jawo mishi gabanshi tana cewa,

“In zuba maka?”

“Sai na yi wanka.” Ya amsa mata yana mai tashi tsaye ya nufi ɗaki ta bishi a baya domin itama wankan zata yi.

“Amma dai na rigaka.”

Suna shiga ta fara cire kayanta cikin sauri ba tare da ta lura shi ya tsaya ne kawai yana kallonta ba, sai da ta gama kwaɓe komai ya rage daga ita sai undies sannan ta gane ita kaɗai take tseren. Kunya ne ya kamata tayi saurin jawo rigarta da ke kasa wai zata rufe jikinta amma bai rufe mata komai ba.

“Striptease ne?” Ya tambayeta looking very amused.

“Allah ka daina kallona ni kam.” Ta faɗa cikin shagwaba tana mai wucewa zata shiga banɗaki ya tare hanya ya jawota.

“Baki gama ba, I want them all gone.”

Yanda yayi maganar sosai ya sakawa Juwairiyya kasala ta kwantar da kanta kan ƙirjinshi da yake bugawa da ƙarfin gaske tayi shiru tana shaƙar ƙamshin jikinshi da a yanzu ya zauna a kwakwalwarta ta yanda duk inda ta ji zata san shine ba waninshi ba.

“I’m waiting.” Ya ƙara faɗa wannan karon a kunnenta hannunshi na yawo a bayanta.

Ɗage kanta tayi tana murmusawa domin duk da cewa bata da confidence na jikinta dalilin ramar da tayi ba zai hana ta ruɗashi ba saboda akwai saura ba komai bane ya tafi. Komawa tayi da baya don bashi the show of his life suka ji ana kwankwasa ƙofar falo tare da jin muryar Salima tana sallama.

Siririyar tsaki ta ji Muhammad ya ja kana ya shige banɗaki da sauri ya barta a gurin tana dariya sosai bayan ta toshe bakinta. Sai da ta saisaita kanta sannan ta jawo wata doguwar riga a wardrobe ta sanya ta fita tana amsa sallamar tare da cewa su buɗe. Salima ce ta shigo hannunta riƙe da HJ, bayanta kuma wasu mata ne biyu wanda daga ganinsu Juwairiyya ta gane danginta ne ƴan zuwa ta’aziyya.

Bayan sun gaisa suka yiwa Juwairiyya ta’aziyya ta amsa kana ta tashi zata ɗauko musu ruwa suka dakatar da ita wai sun gode, daga haka kuma suka musu sallama suka fita amma Salima na nan zaune kamar ba zata tafi ba.

“Yau nace bari in zo mu yi hira tunda mun jima bamu yi ba.” Ta faɗi hakan tana mai gyara zamanta.

Juwairiyya ta ji kamar ta buɗi baki tace ‘ki tafi bana so’ amma bata isa ba, ta sani ta zo ne don ta takurata amma a gurin wani da kuma Muhammad gani zasu yi kamar ta zo ne don ƙarfafa zamantakewarsu. Tana ji tana gani ta zauna suka fara hira wanda wani abun bai ma shafeta ba amma haka ta biye mata, suna hiran ne Muhamamd ya fito daga ɗaki da alama yayi wanka har ya canja kaya zuwa wani jallabiya mai taushi sai zuba ƙamshi yake yi. Dukkansu binshi suka yi da ido har ya samu guri ya zauna inda yake cin abinci kullum kana ya ce,

“Yau kuma hira ne ya tashi? Jay saka mini abinci.”

Juwairiyya ce ta miƙe tana kallon fuskar Salima domin tana son ganin reaction ɗinta akan wannan sabon suna da aka saka mata. Ai kuwa da bata gani ba da ta cutu domin bayan Saliman ta zama confused na wasu seconds sai kuma ta ɓata fuska da abun yayi clicking a brain ɗinta ta gane cewa wai amaryarta ce aka sakawa nickname da harafin ‘J’ wanda in zaka kira sai ya zama kamar ka ce ‘Jay’ ne.

“M.D, da yawa zaka ci ko kaɗan?”

Wannan karon da sauri Salima ta kalleta fuskarta cike da mamaki kan yaushe suka canjawa kansu suna? Da alama sun ruɗata kaɗan domin sai ta kasa cewa komai tana bin su da ido kawai.

“Ɗan daidai kawai, ki saka zan ce ki tsaya idan ya mini.”

“To.” Ta amsa wanda a da ba zata ce komai ba.

Da haka ta fara saka mishi yana kallonta tare da abincin, kaɗan ta saka yace ya isa kana ta miƙa mishi gabanshi sannan ta miƙe ta kawo mishi ruwa da carrot juice wanda ya faɗa mata yana so ta kuma yi mishi mai ɗaɗin gaske.

Duk wannan abun Salima na zaune a gefe ta ƙura musu ido zuciyarta na azalzalarta saboda ta lura akwai abun da ya faru tsakaninsu da ya tsallaketa. Ba dai sun fara son juna har sun bayyana ba? In ba haka ba menene kuma na canja suna Juwairiyya ta zama ‘Jay’ shi kuma Muhammad ya dawo ‘M.D’? Ji tayi zaman falon na neman gagararta domin kuwa satar kallon juna da suke yi suna murmusawa ma kaɗai ya dagula mata lissafi.

Juwairiyya komawa tayi ta zauna ta ɗauko mata hiran school ɗinsu Muhammad na cin abincinshi yana kuma danna waya bai saka musu baki ba. Sai da ya gama sannan Juwairiyya ta tattare gurin ta kai komai kitchen sannan ta dawo ta samu Muhammad na magana da Salima wacce a yanzu fuskarta ta washe kaɗan domin ta samu abunda take so duk da cewa ta samu na ɓacin rai kuwa. Wani tunani Juwairiyya tayi wanda yasa murmushi ya suɓuce a fuskarta ta je bakin fridge ta tsaya sannan ta juyo tana kallon Muhammad bayan ta cire murmushin a fuskarta ta ce,

“M.D a kawo Apple ne?”

Abun da ya fara yi shine gyara zamanshi wanda hakan ya nunawa Juwairiyya tabbas saƙonta ya isa, barin fuskarta tayi neutral irin innocent ɗin nan kamar bata san me tayi ba. Abu na biyu da yayi shine ya ajiye wayarshi a gefe sannan yayi gyaran murya ya ce,

“Sai anjima.”

“To zan shiga wanka, in kana buƙata ka mini magana.” Yanda tayi maganar wani ba zai ɗaukeshi da wata manufa ba ko kaɗan amma da ita da shi duk sun san me suke magana a kai.

Ita kuma Salima murnarta ce ta koma ciki ganin hankalinshi da ta karkato ɗin ya koma kan Juwairiyya wanda kamar ma ruɗashi tayi, to me ya ruɗa shi? Tsabar jaraba ce ko kuma wani abun ta mishi ita bata gani ba.

“Maman Hafiz bari in shiga wanka don in dare yayi ina tsoron shiga banɗaki in ba wai rakani aka yi ba.”

Tana faɗin hakan tayi shigewarta ɗaki zuciyarta fari tass domin ta rama titsiyeta da Salima tayi ɗazu a ɗakinta. Ji tayi dariya na son kwace mata tayi saurin toshe bakinta ta shige banɗaki bayan ta jefa TomTom ɗaya a bakinta wanda take tsotsa a hankali don gigita big baby saboda dama tayi alƙawarin in ya zama good boy zata kai shi cloud nine.

Kafin ta gama wanka ta ji ya shigo ɗakin ya kwanta da yake bata rufe ƙofar da kyau ba, tana gamawa ta fito ta sameshi yana danna waya amma yana ganinta ya ajiye game da ware hannunshi yace,

“Ki zo ki cika alƙawari we are alone now.”

Babu musu ta rage musu wutan ɗakin sannan ta isa gurinshi tana mai tauna saura tomtom ɗin ya narke a bakinta ta mishi magana a kunnenshi wanda ya sa ya ƙara gyara zamanshi a karo na biyu ya lumshe idanunshi ya ce,

“Ina so, and this will be my first.”

 Mamaki ne sosai a zuciyar Juwairiyya amma bata bari ya gane ba, can kuma mamakin ya canja zuwa jindaɗi saboda abun da zata mishi gaba da yace shine na farko a rayuwarshi ba ƙaramin daraja da kuma so zai ƙara mata a idanunshi da kuma zuciyarshi ba.

“Wannan ne na farko, akwai kuma wasu hundreds da zasu biyo baya My Big Baby.” Da haka ta fara mantar da shi abubuwa da yawa ciki kuwa har da sunanshi.

Mum Fateey 👌

“Ni kam ba zaka fasa komawa school ɗin nan ba?” Juwairiyya ta tambayi Muhammad a lokacin da take kwance a gefenshi tayi matashi da damtsenshi.

“Me yasa?” Ya gyara musu kwanciyar suka fuskanci juna.

“In baka nan gidan ba ya mini daɗi ko kaɗan.” Ta tura kanta jikin ƙirjinshi don tana jin nauyin kallon da yake mata.

“Ni da kike mini rowar ganinkin?”

“Ba wannan maganan mu ke yi ba.” Ta faɗa tana mai ɗago idanunta ta harareshi kaɗan cikin wasa.

“Wanne muke yi?”

“Na tafiyarka, ka zauna damu kar ka tafi, please.” Ta faɗi hakan da iyakacin gaskiyarta.

Shiru yayi wanda yasa Juwairiyya ta fara tunanin ko bacci yayi amma da ta ƙara ɗaga idanunta sai ta ga idonshi a buɗe suke sai dai ya faɗa kogin tunani ne.

“Baka ce komai ba.” Ta faɗi hakan a sanyaye tana jin gwiwarta na sanyi duk dama ta san hakan zai yi matuƙar wahala.

“Jay, ina ƙarin karatun nan ne don ku iyalina da kuma karan kaina, rayuwarmu duka nake son ingantawa ta yanda zaku rayu a wadace ba tare da an shiga matsin rayuwa ba duk da cewa Allah ne Mai bayarwa kuma Mai hanawa. Ki yi haƙuri saura shekara biyu in gama in dawo mu zauna kamar yanda kike so ɗin. Kin ji?” Ya ƙarisa maganan yana shafar kanta.

Gyaɗa mishi kai tayi domin in tayi magana zata iya yin kuka, sai take ganin kamar yau ne zai tafi saboda kullum kwanakin da ya ɗaukan raguwa suke yi wanda a yau saura mishi wata ɗaya ciff ya koma. Bata san lokacin da hawaye suka zuba daga cikin idanunta ba suka sauƙa kan hannunshi, shi kuma jin damshi a fatarshi yasa ya ɗago kanta yana ganin yanda wasu masu ɗumin suke sauƙa kan fuskarta.

“Wai kuka kike yi?” Ya tambayeta yana dariya kaɗan ita kuma tana ɓoye fuskarta.

“Dariya kake mini ko?”

“Bakya son rabuwa da Apple ko?” Ya ƙara sautin dariyarshi wanda yasa Juwairiyya ta ji kamar ta nitse ƙasa don kunya.

“Ni ba shi ya sakani kuka ba.” Ta yi saurin kare kanta tana murmusawa sannan tana share hawayen idanunta.

“To menene in ba haka ba? Yarinya daga karɓan Apple sai ki fara kuka wai kar in tafi? Ta yaya ba zan yi tunanin shi bane? Wato dama ba ni ake yiwa kuka ba, gaskiya I’m deeply hurt.” Ya dafa gurin zuciyarshi da hannunshi ɗaya.

“Don Allah ka daina faɗin haka, wallahi kunya kake bani.” Wannan karon rufe fuskarta tayi tana dariya shima yana tayata.

Sai da yayi dariyar mai isarshi sannan ya haƙura wanda a ƙarshe Juwairiyya kasaƙe kawai tayi tana kallonshi don har gobe bata gajiya da kallon Muhammad in yana dariya.

 Tun daga ranar Juwairiyya bata sake kallon ƙeyar Salima a falonta ba da niyyar wai ta zo hira, sai dai ita kuma tana shiga kullum da safe ta tambayi jikinta shikenan sai kuma wata safiyar. School kuma yanzu da Muhammad yake gida shi yake kaita, amma idan an tashi sai ta kira Idrisa ga zo ya ɗauketa. Soyayya da kuma tattalin juna ne tsakaninta da Muhammad wanda sai yanzu ta gane ashe bata san waye shi ba, mutumin kirki ne da in dai za’a bi umurninshi za’a zauna lafiya. Wani abu da ta lura da shi shine ya rage yawan tsawan da yake yiwa Salima a da, ko kuma faɗa da zarar an mishi ba daidai ba. Ta lura ya koyi haƙuri ta yanda ko an ɓata mishi rai sai dai ya faɗa yace kuma a gyara in ba’a gyaran bane za’a ga matsala. Shi yasa da gane haka take kiyaye ɓacin ran nashi, duk abun da ba ya so kama daga tara mishi boxers a banɗaki, kwaɓa mishi abinci ko a ɗiba a rage mishi, fita tsakar gida babu ɗan kwali wanda tana yawan yi amma da ya sakata a gaba ta daina sai aka zauna lafiya.

A yanzu babu mai faɗa mata waye Muhammad domin ta sanshi. Matsalarta yanzu Salima ce wacce ta lura kamar jikinta yayi sanyi amma daga baya da ta ga tana mata wani irin kallo na ‘zaki gani’ sai ta sha jinin jikinta amma bata bari ta gane ba. Satin Muhammad biyu a ɗakinta sannan ya fara haramar komawa ɗakin Salima wacce a cewarta ta gama jegon don har Salwa mai tayata zaman ta koma gida. Sai dai ta lura kamar Muhammad na rawar kai kaɗan wanda hakan yasa ta ji zafi sosai a ranta, ko dai wannan shi ake kira kishi? In dai kishi ne to ta jima da jinshi a zuciyarta wanda a da ta ɗauki hakan a matsayin haushinsu da take ji. Amma yanzu da ta tabbatarwa kanta cewa tana son Muhammad ta fara ware fari da baƙi.

Da zai yi mata sallama da yamma sai duk jikinta a sanyi amma bata san ko bai lura bane saboda bai mata magana ko ya tambayeta me yake damunta ba, wannan abun yasa ana sallar isha ta garƙame ƙofarta ta wuce can cikin ɗaki ta kwanta a gado tana neman abun da zai kawar mata hankali daga tunanin da take yi wato wai mijinta yana gurin wata ba ita ba! Ashe kwanaki jakanci tayi da har ta bari Salima take mishi hidima a kwananta, wanda a yanzu ma ta lura idan Muhammad ɗin ya shiga gurinta yana jimawa wanda in ba don ta san Saliman bata da tsarki ba cewa zata yi cin amanarta suke yi. Ko dai har yanzu Saliman tana riƙe da batun ne? To kuwa zata hana, kuma bata damu duniya su zageta akan cewa tayi amai ta lashe ba.

Ganin tunanin zai iya hanata bacci yasa ta ɗauki wayarta ta shiga WhatsApp a nan ta ga saƙon Hafsat na wasu addu’o’i don biyan buƙata da kuma neman kariya. Bayan ta gama karantawa ta tura mata reply kamar haka:

     ‘Nagode sosai, in Allah Ya yarda zan yi.’

   ‘To Allah Ya yarda. Yau kuma ina maigidan na ganki war haka online?’

  ‘Yana can gurin matarshi.’

   ‘Hahahaha, ki ce kema gauruwa ce irina. Ni tafiya ma suka yi tare Egypt, wai ɗansu na biyu zai yi graduation.’

   ‘To Allah Ya dawo da su lafiya. Nikam dama haka kuke ji idan basa ɗakinku? Wallahi ji nake yi kamar in je can in zazzagesu, shi kuma haushinshi nake ji.’

  Emoji na dariya Hafsat ta tura mata masu yawa wanda yasa Juwairiyya tayi dariya duk da tuƙuƙin kishin da yake cikin zuciyarta. Har ta fara typing ta ga Hafsat na kiranta ta ɗauka suna yiwa juna dariya sun kasa gaisawa.

“Wato kin ji daɗi miji har kin fara kishinshi ko?” Hafsat ta tsokaneta.

“Ke dai bari, wallahi yanzu haushin kowa nake ji kuma ban ƙi ace ya dawo yace ya fasa kwana a can ba.”

“Yanzu ne abun yake damunki, trust me nan gaba har alla alla zaki yi ya tafi saboda ki wataya. But for now ki sa a ranki baya ma gidan yayi tafiya, da haka mata da yawa suke coping da raba kwanan nan. In kuma ba zaki iya zama that delusional ba ki sakawa kanki haƙuri wanda shine best, ki ce yana gurin matarshi ce ta sunnah kamar ki ba karuwa ba, sannan ko ya je zai dawo miki da ke da ita babu wanda ya sameshi dukkanshi. Sai kiyi tunanin in yana ɗakinki itama haka take zama restless, wannan zai sa ki ji sauƙi domin in ana wahala tare raɗaɗin na raguwa.”

“Gaskiya zan ɗauki na biyun domin na sani ko na fara yiwa kaina wannan karyar zuciyata ba zata yarda ba saboda ta san ina yake. I better accept the truth ta yanda ko muryarsu na ji dama na ajiye a raina zan iya ji.”

  Nan suka yi hira kaɗan sannan suka kashe waya suka koma chatting ta WhatsApp, a nan Juwairiyya ta ga Halima ta mata sallama tare da tura mata hoton baby tana cewa,

‘Ga wani yaro ya yiwa yayarshi overtaking ya fito bata gama shan nono ba. Mai sunan Daddy ne Abubakar amma muna kiranshi Sadiq’

 Nan Juwairiyya ta mata barka tare da addu’an Allah Ya rayashi, a nan ne kuma take faɗa mata kwana biyu kenan da haihuwar sai yanzu ta samu kanta shine take faɗawa ƴan’uwa da abokan arziki. Sai goma da rabi ta musu sallama dalilin baccin da yake damunta, wanda tana ajiye wayar hankalinta ya dawo kan haihuwa ta manta da wai Muhammad na gurin Salima, da wannan tunanin bacci ya ɗauketa.

A ranar da Muhammad zai dawo sai ta samu kanta cikin farin ciki, girki ta mishi kala biyu da snack da kuma juice ɗin cucumber mai lemon tsami da ɗanyen citta don kashe maiƙo. Kwalliya tayi wannan karon kamar mai fita biki har da saka flat shoe wanda ya tafi da kayan jikinta na atampa ɗinkin riga da straight siket.

Yamma liss ya dawo ya kalleta daga sama har ƙasa yana murmusawa sannan ya tsaya yana cewa,

“Babu oyoyo ne?”

“Zaka ɓata mini kwalliya. Welcome.” Ta faɗi hakan tana mai tasowa ta karɓi briefcase ɗin hannunshi mai ɗauke da laptop da wasu tarkacenshi.

Har ta juya zata tafi ta ajiye mishi ya rungumota a jikinshi yana mai shaƙar daddaɗan turarenta,

“I missed you.” Ta faɗa mishi tunda ta lura shi ba zai faɗa ba.

“Me too.” Ya ƙara ƙanƙameta wanda yasa tayi ƴar ƙara kaɗan ta fara magana cikin shagwaɓa.

“Zaka karyani don ka ganni ƴar siririya ko? Nima kwanan nan zan yi ƙiba in kai haka.” Ta misalta mishi da hannunta wanda yayi daidai da nashi.

Bai ce komai ba ya zauna akan kujera ita kuma ya zaunar da kan cinyarshi sannan ya ce,

“Bana so, na fi son ki zauna a haka  ta yanda zan ci gaba da juyaki yanda nake so. Ban dai ƙi ki murmure kamar yanda kike a da ba, amma bana son ƙiba, nima na fara zuwa gym, dawowana kuka fara ɗura mini abinci amma daga yau zan rage.”

Sosai Juwairiyya ta ji daɗin maganarshi domin sai ta daina jin kunyar ramarta ta ji confidence ya shigeta, lallai ne miji na sa mace ta tsani jikinta ko kuma ta so shi. Shi yasa wasu matan duk kyansu da gayunsu basu da confidence saboda wanda suke gyara da gayun domin shi yana kushewa, sai wata kucaka can ta fi su jin kai saboda ita nata mijin yana fasa mata kai tana jinta kamar ta fi sauran mata. (be confident da jikinki ko wanne iri ne don maza har yau basu ga perfect mace ba, ko mata goma aka basu kala daban daban ba zai hana in sun ga wata da bata kai waɗancan goman da komai ba su ce bari su gwadata su ji ita kuma ya take. A nan ne self love zai shigo, ki so kanki, ki yabi kanki tun kafin kowa ya miki ta yanda ko ba’a yi ba ke kin san kin isa kin kuma kai.)

“To amma dai ba yau ba, don yau na maka girki masu daɗi har biyu da wasu abubuwan.”

“Dama kullum abincinki mai daɗi ne.” Ya amsa mata mai ɗauke da compliment.

Murmushi Juwairiyya tayi wanda yasa kumatunta suka lotsa Muhammad ya saka yatsarshi a ciki yana kallonta.

“Ban san nayi zaɓen mijin da ya dace da ni ba sai da na fahimci wanene kai, da a wautata har tunanin barinka nake yi amma yanzu ko maganar ban so zuciyata ta kawo mini saboda I got the best husband ever.”

Rungumeta yayi a jikinshi ba tare da yace komai ba amma a yanda ta ga fuskarshi ta washe ya ji daɗin maganar ba kaɗan ba, mayarwan ne yake bashi wahala amma a hankali zata koya mishi duk dama cewa shima ya iya nashi salon.

Washe gari da dare suna zaune a falo suna hira sai ga Salima ta shigo wannan karon ma da HJ. Juwairiyya da take manne da Muhammad yana tayata wani assignment ta ɗan matsa daga jikinshi kaɗan ya bita da ido. Sai da Salima ta zauna sannan ta fara magana cikin kissa.

“Amarsu an saka ranar auren Salwa fa, ke ce ƙirjin biki kuma yayar amarya tare zamu dinga fita kullum har a gama biki.”

Juwairiyya tana jin haka ƙirjinta ya buga domin ta sani wannan ma wani haɗin ne domin Salima ta sani babu jituwa tsaninta da Salwa, gaisuwa ce kaɗai take haɗasu wanda wani lokacin idan an mata gaisuwar sai ta gwammace da zaginta aka yi, saboda fuskar ta aka yi amfani da ita mai ɗauke da raini da kuma nuna ƙanƙanci.

Har ta ɓuɗe baki zata ce ba zata je ba sai ta rufe domin ta fahimci da gangan Salima ta kawo maganar gaban Muhammad, wato idan ta ce ba zata je ba ya mata faɗa ko kuma ya tursasata tunda ai dangin matarshi ce.

“Masha Allah, ashe biki ya zo? To Allah Ya kaimu, In sha Allah da mu za’a yi komai.”

Annurin fuskar Salima ce ta ragu amma Juwairiyya ce ta gane saboda shi Muhammad hankalinshi na kan yi mata assignment.

Nan hira ya ɓarke tsakaninsu wanda da akwai wani a gefe zai gane dukkansu forcing ɗinshi suke yi amma shi wanda ake wannan hayagagar a kanshi bai ma gane ba. Ana tsaka da hiran ne Salima ta karkata baki ta ce,

“In na ganku haka sai in ji sanyi a raina, ba kamar da da kike cewa zaki bar gidan namu idan kin gama makaranta ba kafin nan zaki ci gashin kanki babu mai takura miki.” Tana gama faɗin hakan ta koma jikin kujera ta zauna fuskarta so innocenta ba za’a ɗauka kulli ta kulla ba.

Juwairiyya da dama ta san komin daren daɗewa Salima zata jefeta da wannan magana ta lashi lips ɗinta sannan ta kalli Muhammad da alama wannan karon maganarsu ta ja hankalinshi ta ɗago ta kalli Saliman tarr cikin ido ta ce,

“Maman Hafiz ke kika bani tsoro ta yanda kike faɗin halin ogan namu, amma sai da na shigo na gane he is the perfect gentleman.” A nan ta juya tana kallonshi fuskarta cike da murmushi ta ci gaba da magana “He is loving, honest, charming and a family man da zai iya sadaukar da kanshi don iyalinshi, sannan ga uwa uba ilimi da kyau, me yasa zan bar shi? Muna nan tare har tsufa in sha Allah.” Ta ƙarisa maganan tana murmushi ganin yanda Muhammad yake ta ƙoƙarin tsumewa amma ya kasa sai da ya murmusa kaɗan.

“Wannan yabon duk don ina miki assignment ne?” Ya kwance kullin Salima ba tare da ya sani ba, saboda abun da take son a yi maganar a kai wato na rabuwa da shi kamar bai ji ba.

“Kai ma ka sani ko ka mini ko baka mini ba ina yaba maka, saboda ka kai ne a maka M.D. Ko ba haka ba Maman Hafiz?” Ta juyo tana kallon Salima da fuskarta tayi ja kaɗan amma a hakan take murmushi ta ce,

“Hakane.” Da haka kuma tayi shiru tana jin Muhammad na tambayar Juwairiyya wani abu game da assignment ɗin ta amsa mishi yaci gaba da yi.

Juwairiyya ta lura Salima tana son ƙara magana amma tana tsoro saboda sun yi 1-1, kenan ta nuna mata in kika faɗi laifina ɗaya a wayo da dabara nima zan faɗi naki ana dariya ana tafawa. Yanda Muhammad ya share zancen barin gidanshi haka ya share na Salima da take faɗin halinshi a waje, da alama shiru ya zaɓarwa kanshi yi domin ganin sun zauna lafiya.

 Salima bata ƙara minti biyar ba ta  fice ta basu guri, a nan kuma Muhammad ya gama assignment ɗin ya miƙawa Juwairiyya wacce take gani da farin ciki a fuskarta ta ce,

Mum Fateey 👌

“Dama kina da infection ne?” Wannan shine tambayar da Muhammad ya yiwa Juwairiyya bayan ya koma ɗakin Salima ya dawo gurinta.

Juwairiyya ji tayi cikinta ya hautsine ta ji kamar tana son kewayawa banɗaki, sannan mamaki, takaici, kunya da kuma tsoro suka dira a zuciyarta ta ji kamar bacci take yi zata tashi ta farka daga mafarkin da take yi. Shin wannan wani irin magana ne kuma me ya faru da zai ce haka? Ko dai wari ya shaƙa a gurinta ko kuma tana bacci ya ga tana sosa jikinta? Kai ina ba zai yiwu ba, tana gyara kanta, ko a lokacin da take gida tana kula da martabarta balle yanzu da take da miji! Sannan in mace ta san kanta ko ba don ɗa namiji ba zata tattali wannan gurin. Zuciyarta na bugawa ta dubeshi da kyau bayan ta ajiye briefcase ɗin shi kan kujera ta ce,

“A’a bani dashi, wani abu ka gani a tattare da ni?”

Sai a lokacin ya zauna a kan kujera ita ma ta kwaikwayeshi amma wannan karon sai ta ji ta kasa zama kusa dashi kamar yanda take yi kullum. Haka kawai ta zama self conscious ta fara jin kamar jikinta na ƙaiƙayi.

Shiru Muhammad ya yi wanda a yanzu Juwairiyya ta lura haka yake yi kafin ya furta magana mai nauyi, nan kuma ta ƙara shiga wani yanayi na ruɗewa game da zargi.

“Tun wancan karon da na komawa Salima washegari tace mini tana jin ƙaiƙayi a jikinta, amma daga baya tace ya daina, wannan karon ma da na koma tace ta fara ji amma tana tunanin wataƙila daga ke ce. Da ban yi niyyar faɗa miki ba amma da na yi research a kai sai na ga we both have to treat it saboda ta nan ne zai mutu daga jikinmu duka, in ba haka ba zai dinga tafiya ne yana dawowa.”

Wannan karon takaicin Juwairiyya ne ya ƙaru domin wannan yana ɗaya daga cikin abun da yasa bata son auren mai mata a lokacin da take budurwa saboda wannan issue na infection ɗin. Ta wani gefen kuma kunya ce ta kamata ta ji she is uncomfortable da wannan magana da ke tafiya tsakaninsu.

“Amma ita ta taɓa samun matsala irin haka a zaman ku?” Ta tambayeshi don neman ƙarin bayani.

“Ina tunanin sau ɗaya.” Ya bata amsa.

“Maganar gaskiya ni bani da infection, sai dai ko zaku ƙara bincike wataƙila nata ne ya sake dawowa ko kuma lokacin da tayi miscarriage ta samu dama ana iya raɓa a gurin haihuwa. Ka yi research akai zaka gani.” Ta yi saurin bada reference don kar ya ce tana son ɗaurawa Salima ne.

Ta wani gefen Juwairiyya sai ta fara zargin da gangan Salima ta yi haka amma sai ta kawar da zancen gudun kar komai ya faru ta dinga ɗaura mata, don an ce zato zunubi, ko da kuwa ya kasance gaskiya. Amma dole ne ta ƙare kanta tunda ta sani ba ita ta saka musu ba, yanzu damuwarta ma lafiyarta ce, domin kuwa in dai Salima tana da shi to kuwa dole shi ma Muhammad yana da shi that means itama kenan akwai burbuɗinshi a jikinta. Sai ta ji kamar ma kar su sake cuɗanya ko kuma a yiwa kowacce nata abun daban ta yanda ba zasu yi sharing ɗinshi ba.

“Zan bincika in gani, idan ma dukkanmu ya kamata mu je asibiti sai mu je.”

“To.” Shine abun da Juwairiyya ta amsa dashi don sai ta ji ta ƙagara a daina wannan maganan.

Sai a lokacin kuwa ta gane mood ɗinta gaɓa ɗaya ya canja daga murnar ganinshi zuwa wani abu daban. Kiran sallah maghrib da ake yi yasa ya fita waje wanda shima ta lura kamar jikin nashi a mace yake, wannan wani irin abu ne yake tunkarar rayuwar aurensu?

Muhammad bai dawo ba sai da yayi sallah isha, a nan kuma ya samu Juwairiyya tana sallarta a ɗaki ya shiga wanka sannan ya fito ta zuba mishi abinci ya ci itama ta ɗebi nata.

“Me yasa ba zaki zo mu ci ba?” Ya tambayeta don kwanan nan ta fara koya mishi cin abinci tare da ita.

“Ohh saboda miyar yauƙi ce tana buƙatar mutum ya riƙe plate ɗin kusa da bakinshi gudun ɓata kaya.” Ta faɗi guda ɗaga daga cikin dalilai biyun da yasa ta aikata hakan.

Wannan karon hiran nasu bai yi yawa ba dalilin kowa da abun da yake cikin ranshi musamman Juwairiyya da ta ɗauki maganarshi kamar mari ne a fuska, wai ita ce mai infection! Ta sani mata da yawa suna fama dashi wanda wasu suna samu ne wajen mazajensu, banɗaki mara kyau, gurin haihuwa ko kuma idan sun samu ciki, wasu kuma tsabar ƙazanta ce da kuma cushe-cushen maganin mata da basu san da me aka haɗa ba ya jawo musu wannan cuta. To ita tana iya bakin ƙoƙarinta wajen kare kanta, bata wannan cushe-cushen, sannan bata ƙazanta kuma idan ya kamata dole sai tayi amfani da banɗakin da bata yarda dashi ba bata tsugunawa a ciki, a tsaye take fitsarinta sai ta wanke jikinta da ruwa ta fito. (It’s better akan ki kwaso ƙamayamaya da zai ɗaukeki watanni kina treating. Ga kashe kuɗi ga wahala sannan ga rashin jindaɗin rayuwa da kwanciyar hankali.)

Ko da lokacin baccinsu yayi Muhammad bai nemi ya biya buƙatarshi a jikinta ba, itama kuma bata damu ba domin kwata-kwata bata jin itama zata iya. Sai washe gari da dare da ya tabbatar ba zata nemeshi ba ya jawota ta biye mishi amma ba don tana so ba, ana gamawa kuwa ta nufi banɗaki ta shiga ruwan gishirin da ta tanada don lokaci irin haka. Sai da ta dawo yake tambayarta wai me tayi don ya leƙa ya ganta da ya ga ta jima.

“Just for prevention ne da kuma kashe kwayar cutar in akwaita a jikina.” Ta bashi amsa tana mai tura gashin kanta cikin wig cap ta kwanta. Bai sake cewa komai ba ya jawota jikinshi da haka kuma suka yi bacci.

Washegari tana chatting da Hafsat bayan Muhammad ya fita cikin gari take tambayarta ko sun taɓa battling da infection tunda ita ta daɗe da kishiya.

“Wani abu ne ya faru?” Hafsat ta tambayeta ba tare da ta bata amsa ba.

“Matarshi ce wai ta samu shine take tunanin daga ni ce, ina zaton ma ta je asibiti. Ni gaba ɗaya ma sai nake jin jikina a mace shima kuma na lura haka.”

“Wai har sun koma raya sunna ne? Ba sati biyu kenan ba da yin ɓarin nata? Kai mata akwai jaraba! To Allah Ya sa ba wani abun ta sake yi ba, wai an ce ‘Once bitten, twice shy’. Matsalar zama da munafuki kenan, wallahi ko abun kirki yayi sai ka fara waswasi kana kaffa-kaffa. Mu ma mun taɓa samun haka amma ni ce abun ya dameni na mishi magana tace wai ita ba zata je asibiti da ni ba, abun dariya abun takaici, neman magani ne ba zamu je tare ba amma mu ke sharing abun duniyar tare? Ƙarshe dani da shi  muka je ita kuma ya saya mata irin maganin da aka bani ya bata. Yanzu dai Alhamdulillah bamu sake samun matsalar ba don shi yana da tsoro da yake yana da diabetics, bai yi wasa ba.”

“Yauwa har kin tuno mini da wani abu, ni kam masu diabetics suna fama da rashin ƙarfi ne? As in, su daina performing kwata-kwata?” Juwairiyya ta tambayeta ko itama mijinta ya taɓa samun wannan matsalar, don ana kiran sunan diabetics ɗin Daddy ne ya faɗo ranta. Ko ya warke ko bai warke ba bata sani ba kuma tana jin nauyin tambayar ƴarshi kuma ƙawarta Halima.

“In dai cutar ta sakasu a gaba suna rasawa na wani lokaci, but idan aka ɗaurasu a kan magani kuma aka samu sugarn nasu ya sauƙa sai su dawo normal. Kar ki ce mini Muhammad ne ya samu baƙar cutar nan!”

“A’a wallahi lafiyarshi kalau. Kawai na tambaya ne.”

“Ke dai idan kin san baki dashi kar ki kuskura ki bari ya ɗauka ke kika kawo musu, don zai iya fara jin shakka ko kuma dana sanin tarayya da ke ko kuma ya dinga ganinki kamar ƙazama mai cuta a jiki.”

“Wayyo Allah.” Juwairiyya ta kwashe da dariya don maganar ya mata wani iri.

Hafsat ma dariya tayi kana suka ci gaba da hiransu tare da ƙara wayarwa juna kai.

Tun daga ranar dai Muhammad bai sake yiwa Juwairiyya maganar infection ba, ita kuma tun da aka yi maganar sai ta rage kauɗi tana jin jikinta a mace. Ƙarshe sai da Muhammad ya mata magana yace baya son wannan Juwai mai ko in kula yana son Jay ɗinshi sannan ta sake jiki suka dawo kamar da.

Abun da Juwairiyya bata sani ba amma take zargi shine da gaske Salima munafurci ta haɗa mata, lafiyarta kalau amma ta ɗauki cuta ta laƙabawa kanta ta kuma faɗa mishi wai wataƙila daga jikin matarshi ce amma kar ya faɗa mata ranta zai ɓaci.

“Zan nemi magani kawai har Allah Ya sa in warke, yanzu in ka faɗa mata sai ta fara tunanin ko bata da tsafta ne tun da ƙazanta ma yana kawoshi.” Faɗin Salima kanta a ƙasa cikin sanyin murya.

Shi kuma Muhammad kasa sukuni yayi, shi yasa yana komawa gurin Juwairiyya ya furta mata. Nan kuwa ta wanke kanta sannan ya ƙara saka ido kan tsaftarta ya ga ta ma fi Saliman tsaftar baɗaki da kuma jiki, wannan dalili yasa ya koma ya faɗawa Salima ta je asibiti cutar daga jikinta ce wanda tsabar baƙin ciki ta mishi ƙaryar wai ta je asibiti an ce ba komai bane yana faruwa idan mace ta haihu ko tayi ɓari kuma ba abun tashin hankali bane. Wannan dalili ne yasa hankalinshi ya dawo jikinshi har ya lura Juwairiyya ta ɗan ja baya dashi amma ya mata magana suka dawo yanda suke da.

Yau saura sati ɗaya Muhammad ya koma UK, daga shi har matan nashi sun fara jimamin rabuwa da juna. Juwairiyya kam da ta tuna sai ta fara hawaye, watarana haka zai tasata a gaba yana bata haƙuri sannan tayi shiru, watarana kuma dariya zai mata yana tsokananta wai zata yi missing ɗin Apple ne shi yasa take kuka, a irin haka kuma sai a dawo ana dariya ana tsokanar juna, rayuwar dai da alama tayi musu daɗi. (Zamu gani in zai ɗore.)

Wannan karon shi da kanshi ya biya musu kuɗin jirgi shi da Juwairiyya suka sauƙa a Abuja a wani madaidaicin Hotel mai sauƙin kuɗi. Duk da irin jajircewarta sai da Muhammad ya ƙarar mata da ƙarfi wanda tsabar wahala da ɗingishi ta rakoshi Airpot.

“Wannan tafiya taki Jay ta sa mutane suna ta kallonmu, suna gani zasu gane me ya faru.”

Hararanshi don itama ta lura da hakan kuma ta ji kunya amma ina ruwansu? Ita matarshi ce ta sunnah kuma an yi na bankwana ne so it’s bound to happen.

Sai da ya mata sallamar ƙarshe famfon idanunta suka ɓalle sai kuka har da sheshsheƙa, dole ya sake dawowa ya rarrasheta shima yana jin zafi a zuciyarshi sannan tayi shiru ya tafi ba tare da ya sake waiwayowa ba. Bata ƙara minti biyar ba ta bar airpot ɗin don ba zata iya ganin tashin jirginsu ba gudun kar ta buɗe baki tana kuka mutane su zo su tsaya a kanta.

Washegari itama ta bi flight ta koma Gombe, tana isowa gida kuwa ya kirata da numbershi ta can wai ya isa gashi a ɗakinshi amma har ya fara kewarta.

“Allah kar kasa yanzu ka ganni a bayanka, fiffike zan yi in zo.” Ta faɗi hakan a shagwaɓance.

“In hakan zai yiwu zan fi kowa farin ciki ai, babu ni babu girki sannan ga Apple steady. In da na samu haka ai karatun ma ba zai bani wahala ba.”

Tafiyan Muhammad da sati ɗaya bikin Salwa ya tashi, har cikin falo Salima ta kawowa Juwairiyya katin gayyata wacce ta duba ta ga zasu yi Kamu, Walima sai kuma Ɗaurin aure da buɗan kai. Juwairiyya tayi addu’a amma tana ji a jikinta ba zata ji daɗin zuwan ba.

Ai kuwa ranar da za’a yi Kamu tun da safe suka fita ita da Salima wanda wannan shine karon farko da ta shiga driving ɗinta, a gidan kuwa sai ta zama kamar mayya domin kowa harkar gabanshi yake yi an barta ita kaɗai bata da abokin hira. Da zarar Salima tayi introducing ɗinta a matsayin kishiyarta sai ta ga ana harararta sannan magana da ita kuma ya ƙare. Tun tana danna waya har ta gaji ta ajiye, nan kuma kanta ya fara ciwo ta fara zagin Salima a ranta wacce ta fi awa ɗaya bata ganta ba amma da zarar ta dawo sai ta bata haƙuri wai hidima ne ya mata waye waye.

“Ai ina ga zan tafi gida kawai sai yamma in dawo in an fara Kamun.” Juwairiyya ta faɗawa Salima bayan ta dawo, a lokacin ana kiran sallan azahar.

“A’a don Allah kar ki mini haka, ke da muka zo biki kuma ki koma gida ai bai yi ba.”

Da haka ta shashantar da zancen Juwairiyya zuciya na ƙuna ta zauna ganin ikon Allah, babu mai kulata itama bata kula kowa gashi hatta amaryar da suka haɗu bata gaisheta ba, ƙarshe ma binta tayi da kallon banza wanda yasa ta ji kamar ta gaura mata mari amma bata isa ba.

Sai bayan La’asar aka fara haraman tafiya Kamu, a nan ne Salima ta ja Juwairiyya ɗakin da ake yiwa amarya make up itama Salima ta zauna ana mata. Juwairiyya bata tashi kuncewa ba sai da aka gama mata make up ɗin Salima ta ɗauko wata arniyar lace ta saka wanda anko tayi ita da mamanta da kuma amaryar. Juwairiyya sai ta ji ta raina kanta duk dama cewa itama wannan karon ta cakare ta saka kaya mai kyau ta kuma gyara fuskarta da suka yi sallah.

Aka sha shagalin Kamu Juwairiyya na can baya kan plastic chair kamar wata marainiya, abun haushi kuwa sai Salima tayi ta jawota suna ɗaukan hoto tana ce mata wai zata turawa Muhammad!

Ana tashi daga shagalin tace zata koma gida Salima ta ce,

“Haba Amarya, ba tare zamu koma ba bayan isha?”

“Wallahi kaina ne yake ciwo ina so in je in kwanta.”

Nan dai suka mata addu’a aka taro mata napep Salima na cewa,

“Ai wallahi da kin iya mota da sai in baki nawa ki koma gida ni kuma sai Salim ya dawo dani a motar Mama.”

Yaƙe wanda ya fi kuka ciwo Juwairiyya tayi don maganar ya ɓata mata rai, in banda baƙar magana da ƙaryar banza sai ta ɗauki motarta ta bata wai ta koma gida? Wannan abun shi ya zama cherry kan icing ɗin wanda tana isa gida ta buɗe baki ta ce,

“Wallahi ba zan sake komawa ba, na je sau ɗaya ya isheni.”

Sai dai da Muhammad ya kirata da daren ya tambayeta ya biki ta ce,

“Biki Alhamdulillah, amma gobe ba zan je ba tunda dama itama in ta je ba zata dawo gida ba sai an gama.”

“Ban gane ba.” Ya tambayeta don uzurin nata bai mishi ba.

“Kawai na je sau ɗaya ya isa.” Ta bashi amsa.

“Kar ki fara faɗin haka, zaki je duka events ɗin tunda ta gayyaceki. Bana son kuna zaman lafiya kuma kuyi abun da zai jawo ɗayanku ya ji babu daɗi. Ko baki ji ba?”

“Na ji.” Ta faɗa tana mai tauna cikin bakinta don ta sani in tace zata yi musu dashi sai ransu ya ɓaci duka kuma dole zai tursasata ta je.

Sai dai tana kiran Hafsat ta kwashe da dariya ta ce,

“An miki irin yanda aka mini a bikin ƴarsu sa’ata, ni don wulaƙanci ma ƙawayenta ne suke zuwa kaina su tambayeta wai ko nima ƴarta ce? Sai tace Amaryar Alhaji ce! Su kuma sai su kama baki wasu kuma su bini da kallon tausayi kamar ce musu aka yi auren dole aka mini ba sonshi nake yi ba. Washe gari da zan je aka bani shawara na ɗauko su Zainab da wata cousin ɗina ƙawata, ganinsu yasa basu mini wannan rainin wayon ba sannan ban zauna guri ɗaya shiru ba muna ta hira tsakaninmu no dull moment. Ke ma ki gayyato naki mutanen, kai da ni za’a je ma wallahi, bari ma ya shigo in sanar mishi.”

Ai kuwa washe gari da suka fita da Salima da safen ta lura tana cikin farin ciki, sai dai suna isa Juwairiyya ta dubeta ta ce,

“Ni na manta ma ban faɗa miki ba na gayyaci mutane a matsayina na yayar amarya, anjima su ma zasu zo.” Ta faɗi hakan da ƙayatatcen murmushi a fuskarta.

Annurin fuskar Salima ne ya ragu, hakan kuma ya nunawa Juwairiyya abun da tayi ya taɓata.

“Laa babu komai, su waye ne?”

“Basu da yawa. Hafsat ce sai Sumayya da kuma Surayya.”

“Ke da kike yayar amarya ai mutanen ma sun miki kaɗan.” Salima ta jefa mata mara daɗi.

“Yawan nasu bashi bane damuwa, damuwar shine na ka samu na kwarai, waɗanda suke tare da kai tsakani da Allah babu wata manufa a ransu.”

“Me kike nufi kenan?” Salima ta dubeta kaɗan tana driving wannan karon babu murmushin a fuskarta.

“Ina nufin tara mutane masu yawa a circle ɗinka yana jawo bara gurbi. Ko ba haka bane?” Juwairiyya ta kafeta da ido.

“Eh hakane.” Salima ta amsa can ƙasan makwoshinta.

Daga nan basu sake magana ba har aka iso gidan nasu, minti biyar da haka Hafsat ta diro, can kuma sai ga Surayya da Sumayya da bedsheets masu kyau guda uku wai na amarya. Haka aka cigaba da biki dasu har aka gama basu fasa zuwa ba, a nan ne kuma suka ga kissa domin hidima aka musu sosai kamar wasu mutane masu muhimmaci, ko ba komai dai sun ci sun sha.

Mum Fateey 👌

Wanna page naki ne Umm Raa’if mai AiLisco Venture. Ina sonki Fisabilillahi. ❤️

A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiyawa iyalan gidan Muhammad, yau daɗi gobe rashinsa. Sau da dama Salima na cakalar Juwairiyya da baƙar magana don ta fusata ta faɗi abun da zata kai gaba amma bata samu hakan ba, domin kuwa a hankali itama Juwairiyya ta gane hanya ta daina saurin fushi da kuma ɓarin zance in ranta ya ɓaci.

Abun da ta koya shine, duk lokacin da take tare da Salima ta ɗaukarwa kanta alƙawarin nitsuwa ta yanda duk abun da zai fito daga bakinta sai ta taceshi kafin ta furta. Na biyu kuma idan Salima ta yaɓa mata baƙar magana cikin wasa to sai ta tabbatar maganar da zata mayar mata itama cikin wasa ne ba cikin faɗa ba kafin ta yi, idan kuma ta rasa comeback mai zafi ta gwammace ta rufe bakinta ta bita da murmushi domin hakan ya fi mata alkhairi, saboda an yi hakan sau ba adadi.

A yanzu ta koyi haƙuri da kuma kawar da kai, ba komai aka mata take masifa ba sai in an kaita bango, nan ma kafin a kai ga haka sai ta tabbatar na kawaicin ba zai yi amfani bane, wannan yasa har yau tsakaninta da Salima tuƙawa ake yi bata bari suka rasa hankalinsu aka yi uwaka ubankan ba.

Dangi Muhammad kuwa ta bi su ɗaya bayan ɗaya ta kai musu ziyara tare da ihsani daidai aljihunta, masu yara ta kai musu sweets da chocolates, manyansu marasa ƴaƴa ta bi wasunsu da turare, Omo, sabulun wanka da wanki. Haihuwa ko biki kuwa in dai ya tashi bata ƙiwuya tana zuwa sannan hannunta ma yana isa. Kafin a cika wata bakwai an shafe babin a kafa tanti ana yin gulmarta ko kuma Salima ta kai maganarta su ɗauka. A nan ne kuma Iyami ta faso tana yabon halayen Juwairiyya wanda dama tun da tana ƙoƙarinta amma da yake sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi yasa basa yarda da ita.

“Kullum sai kuyi ta cewa ina bin bayan matar Ya muhammadu ta biyu akan ta farko. Maganar gaskiya ni gulma ne bana so da kuma haɗa guri wanda halin Salima ce, kullum aka zauna sai ta kawo hiran kishiyarta ai tayi kaza ko kuma tace kaza. Kuma in zaku lura wallahi 90% na hiran nata da take kawowa haushi yake baku ko kuma yasa ku ji kun tsaneta. To menene hakan kenan in ba gulma da munafurci ba? Ita kuma ta biyun ko sau ɗari zaki zauna da ita ba zata taɓa kawo miki maganar kishiyar tata ba, sannan ko ke ce kika kawo maganar sai dai ta faɗi alkhairanta ba dai sharrinta ba. In kuma ƙarya ne ku faɗa mini ɗaya.”

Nan guri yayi shiru babu wacce tace wani abu, amma wasu har lokacin da yake basa son gaskiya kuma sun yi nisa basa jin kira sai suka bi Iyami da murmushi irin ‘kanki a ke ji’, wasu kuma suka kaɗa kansu cikin yarda da maganarta.

“To ai abunda take faɗan gaskiya ne ta aikata ba wai sharri ake mata ba.” Faɗin Shema’u da har lokacin bata so ɗaukan gaskiyar ba. (Duk yanda kika kai da kirki da kuma son dangin miji akwai waɗanda ba zaki taɓa burgesu ba, hasalima komai kika yi haushi zaki basu ba don komai ba sai don son zuciyarsu, ki zauna da kowa lafiya wanda kuma ya cuceki ki barshi da Allah zai rama miki tunda suma suna da dangin mijin.)

“A rayuwa kowa yana son rufin asiri saboda dukkanmu muna aikata wasu abubuwa da bama so ya fita waje, to me yasa ita in tayi nata ba za’a rufa mata asiri ba? Kuma rayuwar auren nan da kuka gani kowaccen mu ta san yanda yake, muna samun matsala da kishiya, dangin miji kai har da mazajen namu da suka ajiye mu, to wai me yasa ba zamu yi la’akari da namu ba sai nata? Duk fa matsala ɗaya muke da shi na kishi ko kuma miji! Reactions ɗinmu kuma zai iya zama ɗaya ko kuma na wata ya fi na wata zafi. To me zai sa mu zageta don tayi wani abu da wata daga cikinmu tayi makamancinshi ko ma fiye? Don kawai muna dangin mijinta? Mu ma dai muna da dangin miji sannan zamu aurar da ƴayanmu suma su shiga cikin dangin mijin, idan mun mu’amalanci wanda suka shigo mana da gaskiya da kuma kawar da kai sai mu ma a yiwa namu wannan kawaicin. Sannan ku guji saurin yaɓawa mutum baƙar fenti don wani ya faɗa muku halinshi, sai kun zauna dashi tukunna a nan zaku san halinshi na gaskiya. Allah Ya rufa mana asiri Ya hana mutane kwaye mana zani a cikin kasuwa.”

“Amin amma dai wannan sharhin ko kuɗi ta baki albarka. Maganarki kuma gaskiya ne, ni wallahi duk haɗuwana da ita bata taɓa aibata kishiyar tata ba, sannan tana da son yara wani lokaci idan ta je gidana da su take hira su ma kuma na lura suna sonta har kwanaki suka yi zuga suka tafi wai tace zata musu cookies da Lollies.” Faɗin wata daga cikin ƴar uwar tasu mai suna Umm Raa’if.

“Dama ku iyayen yara haka ake kasheku, da zarar mutum ya so ɗanku shikenan bakwa iya ganin laifinshi.” Shema’u ta ƙara tsoma baki.

“Ya Salam! Shema’u ni kam matar nan ta taɓa miki laifi ne?” Umm Raa’if ta tambaya cike da mamaki tana binta da ido.

“A’a, kawai ku ne ba zaku san halinta ba.”

“Eh lallai! Yanzu kam abun yayi yawa. Kar ki bari abunda waccar take faɗa miki yasa ki kasa ganin alkhairin wannan alhali bata miki laifin komai ba fa.”

Nan dai aka yi ta mayar da zance a nan kuma Shema’u ta raina kanta domin da alama maganar Iyami yasa wasu sun hankalta, wanda a ƙarshe da su ake mata faɗa wai kar ta bari tsanan yayi yawa. (Ke kuma ya kike treating ɗin matan da ƴan’uwanki maza suka kawo cikin zuri’arku? Wai na ce kar ki manta ke ma zuriyar wasu zaki shiga, in baki shiga ba ƴan uwanki zasu shiga ko ma sun shiga, yanda kike so a yi treating ɗinku haka kema ya kamata ki yiwa wasu. Mu sauƙaƙa rayuwar wasu sai mu ma a sauƙaƙa namu da na ƴaƴanmu.)

Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, yau shekara guda kenan da tafiyar Muhammad wanda soyayyar da ke tsakaninshi da Juwairiyya ya ƙara bunƙasa, duk lokacin da ya dawo gida daga Campus in bashi da aikin komai yana tare da Juwairiyya suna video call wanda a yanzu ta murmure ta dawo ƴar duɓurɓur kamar yanda take da, komai ya ciko dalilin kunun Sabaya da ta saka a gaba wanda hatta fatar jikinta sai da ya canja yana kyalli.

In ka ganta a wannan lokacin sai ka ƙara juyawa ka kalleta dalilin kyau da ta ƙara domin bata da damuwar komai, mijinta yana sonta, dangin mijinta suna sonta, tsakaninta da mahaifiyarta da kuma danginta ma bata da matsalan komai, karatunta na tafiya yanda ya kamata nan ma a hakan ta taɓa samun carry over a exams ɗin da tayi a aji biyu lokacin tana cikin depression. Sai a lokacin take tuna irin yanda damuwa ya sakata a gaba a kwanaki wanda take fatan kar Allah Ya ƙara jarabtarta da haka.

Akwai wata rana da Salima ta kasa

haƙuri ta shigo har ɗakinta wai ta zo hira wanda su kan shafe wata ɗaya bata shiga ɗakin ɗaya da sunan hira ba sai dai a gaisa a ga lafiyar juna sai a watse. Amma wannan karon da Salima ta shigo sai Juwairiyya ta ji wani daɗi a ranta domin ita a yanzu bata ƙi su zauna lafiya ba. Sau da dama in aka kwana biyu Salima bata yaɓa mata mara daɗi ba sai tayi tunanin ko ta haƙura ne amma ana ƙara wasu kwana biyun zata fitar da hali sai a cigaba daga inda aka tsaya.

Ana cikin hira wanda wannan karon ya yiwa Juwairiyya daɗi har ta sauƙar da defence ɗinta kaɗan tana dariya sosai akan wani labari da Salima take bata, ana gama wannan labarin Salima ta kaɗa baki ta ce,

“Ni dai kullum ina ta son tambayarki, wane supplement kike sha ko kike shafawa ne da ya sakaki ƙiba kika murmure kuma kike glowing?”

Juwairiyya kuma jin an yabeta kuma gashi bayan an gama hira mai daɗi sai ta buɗe baki ta ce,

“Wallahi babu wani supplement da nake sha, kawai kunun Sabaya ne dama yana gyara jiki sosai.”

“A’a amarsu kar mu yi haka. Tunda na zo da kaina a bani satar amsa don wannan kyan ba kunun sabaya bane kaɗai sirrin.” Ta faɗi hakan tana murmusawa amma zafi take ji a zuciyarta domin ta sani Juwairiyya ta raina mata wayo ne.

“Kin san Allah? Wallahi kunun sabaya kadai nake sha. Ni dai ina jin labarin supplements amma ban taɓa sha ba wataƙila sai gaba don akwai wanda na gani an ce yana da kyau zan saya in gwada.”

Salima shiru tayi tana murmushi don har lokacin bata yarda da maganar Juwairiyya ba, don ita a cewarta ma ta raina mata wayo ne. Hakan kuwa ya mugun ɓata mata rai amma bata bari ya nuna a fuskarta ba sai dai a lokacin ta tuno abunda zata faɗa don ya baƙantawa Juwairiyyan rai itama ta ji abun da ta ji.

“Ya batun zuwanki asibiti ne? Kin fara zuwa ne?” Salima ta tambayeta tana mai gyara zamanta don kallon reaction amaryar tata da kyau.

Ai kuwa nan da nan annurin fuskar Juwairiyya ya ragu ta dubi Salima da take murmushi, a nan ta gane tayi wauta da tayi tunanin wai Salima ta shigo gurinta ne don kawai su yi hira ba don ta faɗa mata abun da zai ɓata mata rai ba.

“Ban je ba. Ai dama na faɗa miki ba zan je ba.” Ta bata amsa tana mai shiga taitayinta.

“To me yasa? Haihuwa fa da ɗadi wallahi don ni ban ƙi a ce mun cika gidan nan da ƴaya ba.”

“In Allah bai baka ba baka isa ka bawa kanka ba. Idan ina da rabon samu zai bani ba sai na je asibiti ba.”

“Eh haka ne amma ai Allah ma Ya ce mu nemi magani. Yanzu ke kina zaune baki sani ba wataƙila wata matsala ce da ke babba, amma idan kin je asibiti sai a baki magani ki warke. Gashi mai gidan namu da son yara kullum maganarshi wai in ya dawo sai ya tabbatar an yiwa masoyinki ƙani ko ƙanwa kafin ya tafi, yana da son yara wallahi, shi yasa ma nake mamaki da bai tilasta miki kika fara zuwa asibitin ba.”

“Sai a hankali. Allah Ya bamu masu albarka.” Juwairiyya ta faɗi abun da zata iya faɗi domin a yanzu bata da wata comeback mai ƙarfi, sannan mood ɗinta gabaɗaya ya canja daga farinciki zuwa baƙin ciki.

Salima ta sani maganar haihuwa na sakata damuwa shi yasa take kawo mata shi duk ranar da ta rasa abun da zata yi amfani dashi wajen sosa mata rai.

“Amarya bari in tafi don yanzu Masoyinki zai dawo daga school.”

Sallama suka yi Salima ta fice ta bar Juwairiyya cikin baƙin ciki domin ko ita da kanta ta haramtawa kanta tunani kan maganar haihuwa, amma a yanzu da ta ji wai Muhammad na faɗawa Salima wai in ya zo zai mata ciki sai ta ji tausayin kanta ya shigeta, wato ita ce juya da in ya zo ba zai yiwa ciki ba. Saboda ko sau ɗaya basu taɓa maganar haihuwa ba duk hiran da zasu yi, kenan ita ya ɗauketa ne a matsayin sex object mai rage mishi ruwa a mara, ita kuma waccar a matsayin uwar garke mai kawo mishi ahalinshi doron duniya!

Duk yanda ta kai ga daina wannan tunanin ta kasa domin ko da Salima ta faɗa mata hakan don ranta ya ɓaci ne to gaskiya ta faɗa, domin Muhammad bai taɓa mata maganar haihuwar ba, kenan bai damu da ta haihu ko kar ta haihu ba tunda matarshi waccar tana yi. Ko dai baya son haihuwa da itane? Domin yana yawan tsokanarta wai tana da masifa kenan baya son ta haifa mishi ƴaƴa masu masifan!

Da wannan tunanin Juwairiyya ta kwanta wanda tayi iya bakin ƙoƙarinta ta daina zargin Muhammad amma ta kasa, ta wani gurin kuma tana jin haushinshi kaɗan wanda ta sani in ba wai sun yi magana ya wanke kanshi ba ba zata daina ji ba.

Kwana uku da haka ya kirata kan cewa dawowanshi ya tabbata zai zo gida nan da sati biyu. Murnar da tayi har ba za’a iya misaltawa ba, tuni kuwa ta mance da wata maganar baya son haihuwa da ita domin irin yanda yake ta kasheta da dirty talks akan in ya dawo sai tayi sati bata iya tafiya da wa ya mutu wa ya dawo!

Nan kuwa ta fara gyara, wanda ya kama na duniya da kuma fatar jikinta. Wanke kai, kunshi, da kitso kuma ta bari sai ana saura kwana biyu ya diro zata yi. Ana saura sati ɗaya ya iso lokacin ta fara tsumuwa da ingantaccen tsumi Salima ta shigo mata falo, Juwairiyya sai ta ji kamar ta kama bakinta ta rufe domin bata son tayi magana ta ɓata mata mood.

“Amarya ana ta shirin dawowar maigida an manta da mu, yau kwana biyu kenan bamu ga idon juna ba.”

“Ayya sai a hankali, amma kuma ai ina zuwa bakin ɗakinki ina miki sallama idan zan tafi school.” Juwairiyya tayi defending kanta.

“Ai ban ce bakya mini sallama ba, cewa nayi kwana biyu rabon da mu ga idon juna.” Salima ta ƙara nanata maganarta.

“Mun wuni lafiya? Ya Hafiz? Kwana biyu bana jin shi ko dai gajiyan school ne ya ladabtar da shi?” Juwairiyya ta kawar musu da zancen don kar musun yayi yawa.

“Lafiya kalau. Wallahi ya tafi gidanmu ne hutu sun samu na mid term.”

“Ayya, yayi kyau.”

“Dama na zo faɗa miki ne na karɓa mana kuɗin gyaranmu a gurin Baban Hafiz. Na faɗa mishi muna son wanke kai, kitso, lalle da kuma abun da ya shafemu na mata shine ya bani. Yanzu ya zamu tsara? Yaushe zamu je wanke kai? Sannan yaushe zamu kira masu lalle da kitso su zo su mana a gida don ni wallahi bana son zuwa gidan su mazajensu su yi ta kallonka.”

Juwairiyya buɗe baki tayi kaɗan ta zubawa Salima ido tana kallonta cikin tsantsar mamaki da kuma takaici, wai da waye zasu je gyaran? Da ita? A kan me? Sai ta zama so confused wanda hakan yasa ta kasa cewa komai kawai taci gaba da kallon uwar ƙarfin halin.

“Yauwa sai kuma wa kika sani mai sayar da abunmu ta mana haɗi mai kyau?”

A nan Juwairiyya ta ji abun ya isheta ta ɗaga hannunta duka biyu sama wanda yasa Salima tayi shiru tana kallonta ta ce,

“Salima kenan! A ina kika taɓa ganin kishiyoyi sun je gyaran jiki tare fisabilillahi har kuma su haɗa wajen sayan maganin mata? Gaskiya abun naki yayi yawa ya kai maƙura yanzu kam. Me haka?” Ta ƙarisa maganan cikin ɗaga murya kaɗan.

“Allah Ya baki haƙuri amma ni a matsayin ƴar’uwa na ɗaukeki ba kishiya ba. Idan hakan bai miki ba shikenan zan turo miki kuɗinki. Sai anjima.” Tana faɗin hakan ta fice ta bata guri.

Tsaki mai ƙarfi Juwairiyya ta ja domin fitinar Salima ya fara isarta, wani irin sabon salo ne kuma ta ɗauko wai su yi gyara guri ɗaya kuma iri ɗaya? Tsabar makirci ne ko kuma fitina da neman tada hayaniya? Ta sani yanzu babu mamaki ta ƙulla mata wani sharri a gurinshi amma ita ba damuwarta bane, wannan haɗin ne ba zata yi ba.

A daren ranar suna waya da Muhammad yake tambayarta.

“Me yasa kika ce ba zaku yi lalle da kitson ke da ƴar’uwarki ba?”

Wannan magana yasa zuciyar Juwairiyya yayi zafi amma sai tayi murmushi mai sanyi ta ce,

“Matan mutum ɗaya basa gyara guri ɗaya kuma iri ɗaya Big Baby. Kyanta kowacce tayi a wani guri saboda ka ga different kyau ba duka ya zama iri ɗaya ba which is boring. Shekara guda baka nan sai kuma ka dawo ka samemu komanmu iri ɗaya babu difference? Me amfanin auren mata biyun in kowacce bata fito da tata kalar kwalliyar da salon daban ba? You deserve more than that M.D, shi yasa nace mata kawai mu yi a guri daban. Amma ina fatan ranta bai ɓaci ba?”

“A’a, ranta bai ɓaci ba kawai dai ta saka rai ne akan zaku yi tare. Kuma dama ba ni zan biya ba don ta tambayeni nace mata bani da kuɗi zuwana ya cinye kuɗi sosai shine ta ce zata biya muku.”

“Allah Sarki ƴar’uwa. Ai da ta faɗa mini ba zan bari ta tambayeka ba saboda na san halin da ake ciki. Zan mata magana ta bar kuɗin nima sai nayi da nawa ka ga kowacce ta samu lada.”

Ɗan dariya kaɗan Muhammad yayi suka cigaba da hiransu wanda yawanci na ɗagawa junansu hankali ne domin su a lissafinsu idan ya dawo a ɗakinta zai sauƙa yayi kwana ɗaya sai ya koma ɗakin salima yayi kwana biyu. Dalili kuwa shine; washegarin da zai tafi a ɗakinta yayi kwana ɗaya, Next day kuma suka tafi Abuja kenan akwai sauran kwananshi ɗaya a ɗakinta.

Washegari da safe Juwairiyya zata tafi school ta bi ɗakin Salima ta shiga har cikin falonta suka gaisa take cewa.

“Jiya muke waya da Baban Hafiz kan batun gyara da zamu yi shine yake faɗa mini yanda kuka yi. Ai ni da kin fara magana da ni ba zamu tambayeshi ba saboda ya kamata mu tausaya mishi ɗawainiyan da yake yi. Yanzu kema na yafe miki ki bar kuɗinki nima ina da wasu canjuna zan yi amfani da su.”

Ko ba’a faɗa ba ran Salima ya ɓaci wanda duk yanda ta kai ga ɓoyewa ta kasa, amma a haka ta buɗe baki ta ce,

“A’a, zan baki tunda ni nayi niyya.” Tayi hakan don Juwairiyya ta ƙule.

Amma sai ta ga saɓanin haka a fuskar Juwairiyya wacce murmushinta ya fi na ɗazu yawa ta ce,

“If you insist babu komai zan  karɓa. Nagode, Allah Ya baki ladan gyara aure da kike ƙoƙarin yi. Bari in wuce school kar in yi latti.” Har ta juya zata tafi Salima ta dakatar da ita da cewa,

“Dama in ya dawo a gurina zai sauƙa ko? Ranar fa sai dai in baki masoyinki ku kwana don ya fara wayo.” Ta faɗi hakan tana murmushin mugunta.

“Kamar kin ɓata lissafi, a gurina zai yi kwana ɗaya sai ya koma miki don kwana ɗaya muka yi washe gari muka tafi Abuja.”

“Anya kuwa? Kema dai ki ƙara lissafi ba haka bane.”

Ganin zasu yi ta musu yasa Juwairiyya ta dakatar da maganar ta ce,

“Shikenan ya sauƙa a gurin naki, Allah Ya dawo dashi lafiya.”

“Ko dai ranki ya ɓaci ne? Ki bari kawai na haƙura ke ya sauƙa a gurinki.”

“Ni nace miki raina ya ɓaci?” Juwairiyya tayi dariya wanda na takaici ne ta ce, “Ko kaɗan. Na ga babu daɗi muna ta jayayya ne kamar wasu ƙananan yara. Sai anjima.” Da haka ta saka kai ta fita zuciyarta na tafarfasa domin tana hango murmushin muguntar da ke fuskar Salima wanda take ji kamar ta share mata shi ta hanyar wanka mata mari mai zafin gaske.

Team SalMoh da Team JuMoh wai kwanan waye? Sannan wa za’a bawa? Mu haɗu a comments. Lol

Mum Fateey 👌

Yinin ranar a school Juwairiyya haushin Salima ce a ranta, idan kuma aka ci sa’a ta manta da ita na wani lokaci dalilin karatu ko kuma hira da course-mates ɗinta to minti kaɗan da haka tunanin zai dawo kwakwalwarta ta ji zafi a zuciyarta. Sai da ta nitsu sannan ta fara jin haushin saurin bar mata kwanan da tayi saboda ta sani nata ne, haƙƙinta ne. Amma ta wani gurin kuma ta jinjinawa kanta tare da ganin ƙoƙarinta da bata biye mata suka yi ta kace nace akan namiji ba wanda shi idan ya ga hakan ma daɗi zai mishi ya ji kanshi na ƙara girma wai ana faɗa akanshi.

A daren ranar tana tsifar kai a can cikin ɗakinta tana kuma karatun wani test da zasu yi Muhammad ya kirata.

“Ina wuni Big baby?” Ta faɗa cikin sanyin murya.

“Lafiya kalau Jay, ya school?”

“Alhamdulillah, ya naka? Ya kuma shirye-shiryen dawowa?”

“I can’t wait to hold you in my arms, in yi ta kallonki ina taɓa dimple ɗinki.”

Dariya Juwairiyya tayi wanda hakan yasa ta manta da wani ɓacin rai da take ciki, a yanzu ji take yi kamar babu kowa a duniyar daga ita sai M.D ɗinta.

“Kar mu yaudari juna Big baby, da ni da kai mun san ba a iya kallon abun zai tsaya ba.” Tayi maganar cikin jan hankali.

“Saura kwana nawa in dawo?” Ya tambayeta duk da cewa ya sani.

“Kwana shida ciff. Umm dama ina son maka wata magana.” Sai a lokacin ta fito daga wancan duniyar daɗin da ta shiga, duniyar da babu kowa sai ita da shi.

“Jay, ki bari sai mun gama maganar nan, ina son faɗa miki yanda na yi missing ɗinki ne.”

“Ai akan hakan zamu yi magana.” Ta faɗa a sanyaye.

“Me ya faru? Ina fatan ba wata matsala ba ce?”

“Dama akan dawowanka ne, Salima tace a gurinta zaka sauƙa.”

“Ban gane ba, ba kwana ɗaya na yi a gurinki muka tafi Abuja ba?” Ya tambaya wannan karon muryarshi ba kamar na ɗazu ba mai cike da shauƙi da wani abun daban.

“Eh hakane, amma dai haka tace. Na ce tayi lissafi tace wai ni ce ban yi nawa daidai ba. Mun gama magana ma don nace mata na bar mata.”

“To ban yarda ba, kar ki kuma sake mini irin haka. Ki je ki sameta ki mata lissafi ku fahimci juna, yanzu ba anjima ba.”

Juwairiyya ji tayi kamar ta yi ihu domin bata so Muhammad ya ƙi yarda ba, ta so a bari a hakan duk dama itace da gaskiya amma menene don an sace mata kwananta ɗaya? Babu abun da zai faru, miji kuma zai zo hannunta tunda idan ya je ɗakin Saliman kwana biyu zai yi ya dawo. To menene abun gaggawa da kuma cece kuce.

“M.D don Allah kar ka ce nayi musu da kai, wallahi ni har zuciyata na bar mata babu abun da zai faru. In ya so daga baya sai mu zauna a tattauna a tsara ta yanda ba wanda zai ƙara ruɗewa.”

“Yanzu ma musun kike yi da ni. Na baki umurni ki je ki sameta ku fahimci juna, idan kuma ban kai in baki umurni ki yi bane sai ki faɗa mini.”

“A’a, Allah Ya huci zuciyarka, abun bai kai haka ba. Zan je.”

Juwairiyya tayi saurin bashi haƙuri da ta ga alamar ranshi ya ɓaci domin hatta muryarshi sai da ta canja. Gone is the gentle Muhammad, har gobe dai halin yana nan bai canja ba.

Bai amsa ba ya datse kiran ta bi wayar da kallo cikin mamaki wanda ko da ta tuna waye shi sai ta shafawa kanta ruwan sanyi. Tufke gashinta tayi a ƙeyarta kana saka hijabi ta fita zuwa ɗakin Salima lokacin ƙarfe takwas har da rabi. Sallama ta fara yi aka amsa mata sannan aka ce ta buɗe ƙofar, da wata sallamar ta kutsa kanta ciki tana yaɓawa fuskarta murmushi don maganar da ya kawota in ba don an mata dole ba wallahi ba zata yi ba. Yaushe zata bi ɗakin kishiya wai tana roƙon a bar mata kwananta da aka sace? In ba don tana tsoron musu da Muhammad ba da sai ta san yanda zata kanainayeshi da magana mai daɗi ya haƙura, amma taurin kai ne da shi kuma ba ya son musu.

“Amarsu ke ce? Ai kuwa yanzu nake cewa zan tashi in rufe ƙofa ashe ina da abokiyar hira tafe.” Faɗin Salima tana miƙawa HJ text book ɗin da take koya mishi homework ya karɓa ya ci gaba bayan ya yiwa Juwairiyya murmushi.

“Wallahi fa, ya kuke ya gida. Mallam Hafiz kana homework ne?” Ta tambayeshi tana mai zama a kujera.

“Eh.” Ya bata amsa a kunyace.

“Baka iya gaisuwa bane?” Salima ta kwaɓeshi.

“Ina kwana?” Ya gaishe da Juwairiyya bayan ya ɓoye fuskarshi a jikin littafinshi.

Dariya Juwairiyya tayi kana ta amsa gaisuwar tashi tana tambayarshi labarin school amma baya amsawa sai doka mata murmushi kawai yake yi. Shi kuma haka yake maganar bai iya yi sosai ba.

“Ai wannan masoyin naki da ƙin magana, wasu cewa suke yi Babanshi ya ɗauko.”

“Allah Sarki.” Juwairiyya ta faɗi abun da ta saba faɗa.

“To ya school? Yanzu kam kun kusa gamawa, zaki riga Baban Hafiz ko?”

“Alhamdulillah. Eh zan rigashi don ni saura mini wata bakwai shi kuma shekara cif cif. Dama ya aikoni ne akan maganar da muka yi ɗazu, ya ce in miki bayani.”

Nan Juwairiyya ta fara zayyano mata yanda suka fara tun daga farko wanda in har aka bi haka to akwai sauran kwana ɗaya da za’a mata kafin ya je gurinta.

“To dai ni nace na haƙura amma yace kar mu ɓata tsarin, yanda muka fara mu tafi a haka.” Juwairiyya ta kai ƙarshe a maganar tata tana kallon fuskar Salima wacce ta hautsine babu annuri ko kaɗan.

“Dama tun ɗazun nima na faɗa miki na yafe amma kika sameshi kuka yi magana, yanzu kin saka yana ganin laifina yana ganin kamar ni ce nake son kwace miki kwananki.”

“A’a kar ki ce haka, bai ga laifinki ba. Kawai yana so ne mu fahimci juna kar wata ta ga ba’a mata ba daidai ba.” Juwairiyya tayi saurin taran numfashinta don ita ba haka tayi tsammanin Salima zata faɗa ba.

Ta ɗauka idan ta gama mata bayanin zata gane ita tayi ɓata sai kowa ya gamsu a rabu lafiya, amma wannan accusing ɗin nata da tayi bai mata daɗi ba. Danne zuciyarta kawai ta yi amma da a da ne yanzu babu wanda zai ji muryar ɗan’uwanshi sai ta tartsawa musu taron.

“Ni kin ganni in ma so kike yi in ƙara miki wasu kwanakin kan ɗayan da kika nace sai an miki ni zan baki babu matsala. Amma ki je kina haɗani da shi ne bana so.” Yau dai da alama Salima ta sha jar kanwa ya tsaya mata a wuya.

“Me kike nufi kenan? Ni ce na nace akan dole sai ya kwana a ɗakina? Magana muke yi nace mishi ba’a gurina zai sauƙa ba kamar yanda yake tunani yace in zo in sameki, an faɗa miki nima na damu ne dole sai ya kwana a ɗakina? Da ya tafi da ke Abuja, kika bishi kuma ya dawo ya sauƙa a ɗakinki ni na ce wani abu ne? Ban ce ba! Binku nayi a haka saboda ban damu ba, tsarin da kuke yi shi zan bi.”

“Eh saboda lokacin baki san daɗin mijin bane.” Salima ta faɗa can ƙasan maƙwoshinta amma Juwairiyya ta ji sarai.

“Excuse me! Me kika ce?” Ta faɗa tana mai karkata kanta tsabar masifar da ke cin ranta da yake son bulluƙowa daga ƙirjinta.

“You heard me.” Salima ta faɗa tana mai murmusawa kaɗan alamar ta samu abun da take so.

Juwairiyya har zata buɗe baki ta fara azalzalarta sai ta lura da wayarta da ke hannunta yana blinking kamar wacce take recording ɗin maganarsu. Takaici, tsoro, fargaba da kuma baƙin ciki ne ya ƙara dabaibaye zuciyar Juwairiyya domin sai yanzu ta gane da gangan Salima ta cakaleta. Shiru tayi tana kallonta tana karanta ‘Lahaula’ a ranta.

“To bari in tafi, mu kwana lafiya Maman Hafiz.” Juwairiyya ta faɗa tana mai murmushi wannan karon har cikin zuciyarta domin bata bawa Salima abun da take nema ba, wannan ma kaɗai ya isa yasa zuciyarta tayi sanyi ta kuma godewa Allah da Ya sa ta ankara da wuri.

Da haka ta juya ta fice mata daga falon ta koma nata. Tana shiga ta kulle ko’ina ta shige can cikin ɗakinta inda take zaune tun ɗazu ta ɗauki wayarta ta kira Muhammad.

“Big baby na.” Ta kirashi bayan ya ɗauka.

“Kin je?” Shine abun da ya fara tambayarta ba tare da ya amsa kiran sunanshi da tayi ba.

Ɗan dariya Juwairiyya tayi kana ta rufe littafin da take karatun ta ce,

“Na je mun fahimci juna, ina tunanin ta gane amma don Allah in ka dawo ka zaunar damu a yi maganar a tsanake.”

“Na ji. Me aka tanadar mini?”

Da haka suka cigaba da hiransu tana ƙarisa tsefe kai har ta gama ba tare da ta sani ba.

Kwana biyu da haka bayan ta tashi daga school ta wuce kasuwa ta yo duk sayayyar da zata yiwa Muhammad na tararshi, daga nan kuma ta nufi saloon aka wanke mata kai sannan ta dawo gida. Sai da ta ajiye komai ɗinta a kitchen sannan ta zo bakin ƙofar Salima ta ce mata ta dawo kana ta wuce ɗakinta wanda jiya ta kakkaɓe cobwebs ta canja zaman kujerun falon sannan tayi duk wasu gyara da ya kamata duk dama ita bata bari datti da ƙazanta a space ɗinta.

Washe gari ana saura kwana biyu Muhammad ya diro Ilhama mai lalle da kitso ta zo ta fara mata lalle, ana kitso Salima ta shigo ta samesu a haka dalilin babu wutan lantarki kuma ana ɗan zafi kaɗan sun bar ƙofar falon a buɗe.

“Ah’ah! Yau kam kin fito a amaryarki sakk! Masha Allah. Amma me yasa baki yi baƙin lalle ba?”

Juwairiyya da take mamakin ƙarfin hali irin na Salima da kuma kishin banza ta ce,

“Ban gama tunanin zan yi ko ba zan yi ba.”

“Ai Baban Hafiz yana son mace tayi baƙin lalle, idan kina so gobe sai in kira miki wata ta miki.” Ta mata ƙarya domin bai cika son baƙin lalle ba kamar Ja.

“A’a nagode, akwai wacce nima na sani tana yi, idan ta ga nayi a wani guri ba zata ji daɗi ba.” Itama ta mayar mata da irin tata duk da cewa bata son tana sakata yin ƙarya.

“Ohh, ni kuma dama mai kitso ne na rasa shine na ce ko wannan mai miki ɗin zata mini.” Sai yanzu ta faɗi ainihin abun da ya kawota.

“Gata nan ai sai ku yi magana, sunanta Ilhama.” Juwairiyya ƙara mata bayani don ita yanzu abun Salima ya so ya daina bata mamaki.

Duk faɗin garin Gombe ta rasa mai kitso sai da tata ta zo wai ita zata mata?

“Ilhama ina wuni ya ƙoƙari.” Salima ta mayar da hankalinta kan mai kitso.

“Lafiya kalau, Alhamdulillah.” Ta amsa babu yabo babu fallasa.

“Zan samu kitso kuwa? Wallahi wacce muka yi alƙawarin zata zo ta mini wai bata da lafiya.”

“Gaskiya kiyi haƙuri ba zaki samu ba, domin a rana kai ɗaya nake yi, gobe kuma zan yi tafiya.”

“Oh ohh, don Allah ki dai duba, yau kam ki gwada kai biyu.”

“Ai mutanen nawa ne ba zasu barni ba, kai ɗaya nake yi.”

Muƙut!! Juwairiyya ta haɗiye yawu cike da tsoro, itama Salima tuni ta shiga taitayinta, ai bata ƙara seconds ashirin ba ta musu sallama ta fice. Nan kuma falo yayi shiru aka cigaba da kitso, sai can Ilhama tayi dariya mai sauti wanda ya kaɗa hantar Juwairiyya da take tsammanin aljanun sun iso ne.

“Aunty kamar kin tsorita fa, wasa nake mata.”

Ajiyar zuciya Juwairiyya ta sake kana itama ta saka dariya tana cewa,

“Wallahi na tsorita kam, na ce ga hannu da ƙafa da lalle kar ki shaƙeni a rasa mai kwatata. Amma me yasa zaki yiwa kanki ƙaryar aljanu?”

“Ina da su amma basa hanani kitso, kawai na faɗa ne.”

Nan murnar Juwairiyya ya koma ciki amma tsoron yanzun da sauƙi, tunda basa hanata kitso ai ba zasu tashi su shaƙeta ba. Nan aka cigaba da kitso aka gama ta zauna jiran lallen yayi ta cire mata don tace kwanaki ta wahala gurin cirewa.

Washe gari Juwairiyya da Surayya a kitchen suka wuni suna haɗa abubuwan da zata buƙata gobe, domin ta gani idan ƴan’uwan Muhammad sun zo suna cin wani abu da aka girkawa wanda ya dawon, don haka ta shirya musu nasu daban da kuma snacks ɗin da zata basu su tafi dashi.

Sai da suka gama duk wani aiki mai wahala ya rage abun da zata yi gobe ba mai yawa bane sannan ta bar Surayya ta tafi wacce ita tafi wahala, domin Juwairiyya tace ba zata wanke abubuwa ba gudun kar lallenta ya koɗe. Da yamma liss Muhammad ya mata waya wai gashi ya sauƙa a Abuja yana gidan wani friend ɗinshi da ya hanashi kama hotel.

“Ni anya ba zan kamo hanya kawai in zo ba? Zan iya isowa da tsakar dare idan na bi motar kasuwa.”

“Ka dai yi haƙuri, gobe da azahar Insha Allah kana cikin gidanka.” Juwairiyya da take mishi dariya ta bashi shawara gudun kar ya jiƙa mata aiki.

Washe gari tun da asuba ta tashi ta fara aiki, ƙarfe bakwai Surayya kuma ta iso tare da wata ƴar makwabtansu wacce zata tayasu aiki. Tuwon shinkafa suka tuƙa mai yawa suka kulla a leda sannan aka saka a cikin kula babba da haka kuma suka ƙarisa sauran aikin nasu wanda kafin sha ɗaya sun gama komai sun gyara kitchen sun yi wanke-wanke, ita dai Juwairiyya nata bada order ne don ta ƙi yarda tayi aiki wai kar ta zama exhausted idan ya dawo.

“Gamu zamu shiga cikin jirgi zamu iso nan da awa ɗaya.” Faɗin Muhamnad yana mai taka matakalar da aka tanada don shiga jirgi.

“Can’t wait to see you My Big Baby.” Juwairiyya ta mayar mishi da martani bayan ta ƙule can cikin ɗakinta gudun kar baƙin da suka zo taryanshi su jiyo ta.

“I love you, sai na iso.” Yana faɗin haka ya kashe wayar ita kuma ta fito falo sai kyalkyali take yi kamar wata amarya.

A nan ta samu Surayya tana sakawa mutane tuwon shinkafa miyar Egusi da ta gajiya da haɗuwa sannan ana bin su da kunun aya da ruwa a gora.

Nan ido ya dawo kanta domin an yi gaskiya da aka ce ‘Black is beautiful’ domin duk da kasancewarta wankan tarwaɗa sai ta zama mai walwali duk inda ta kutsa. Ta sha atampa mai matuƙar kyau da ɗaukan ido, ɗinkinta na doguwar riga shi ya fitar da kyakkyawan shape ɗinta wanda in ta juya tana tafiya mutum zai iya shagala ba tare da ya sani ba. Hannunta da ƙafarta sun sha jan lalle, kanta ya sha kitso ƙanana wanda ake ganin kaɗan ta cikin ɗaurinta, a cike take wanda ba zaka iya cewa kiba ba, a murmure take ta yi dub dub sai walwali take yi kamar wacce aka watsawa glitters, sirrin kuma yana cikin gyaran da take yiwa jikinta tun da ta dawo hayyacinta ta gane wacece ita.

Duk inda ta ratsa ƴan’uwa na tsonkanarta wasu kuma na yaba mata kan kyan da tayi tana murmushi tana musu godiya. Suna gama cin abinci aka tattare plates suna yabon girki sannan su Surayya suka ƙara gyara guri aka banka turaren wuta suka mata sallama suka tafi. A nan ne kuma Ƙanin Muhammad ya tafi airpot ɗaukoshi don an ce ya kusa sauƙowa.

Bayan wani lokaci suka jiyo tsayuwar mota a waje wanda hakan yasa zuciyar Juwairiyya ta buga da ƙarfin gaske, shauƙi da kuma so ya dabaibaye wannan zuciya mai bugawan, sai ma ta rasa me zata yi ɗaya. Tana zaune ƴan’uwa suka fara fita ana cewa ‘ga Ya Muhammadu ya iso’. Amma ita tana zaune.

“Ba zaki je taro mutanen UK bane?” Iyami ta tambayeta tana mai murmusawa.

A kunyace Juwairiyya ta miƙe jikinta har rawa yake yi ta yafa gyalenta ta nufi hanyar fita, har ta je bakin ƙofa ta dawo ta wuce ɗaki Iyami na mata dariya ta gyara ɗaurinta da kuma fuskarta duk da cewa basa buƙatar hakan sannan ta fesa turare kaɗan a wrist ɗinta ta fito tana kare fuskarta ga Iyami wacce itama ta miƙe ta biyota a baya bata daina tsokanarta ba.

“Ina Juwairiyya?” Muhammad ya sake maimaita tarihi.

Sai dai a maimakon ya ganta kamar wancan lokacin wannan karon tafiya tayi da imaninshi saboda kyan da ta mishi. Lallai video call bai mata adalci ba, yanzu ne yake ganinta da kyau yana kuma adana hotonta a kwakwalwarshi. Tana isa gurin da take ta russuna kaɗan kanta a ƙasa ta ce,

“Sannu da dawowa, ya hanya?”

“Hanya lafiya kalau.” Ya amsa yana binta da mayataccen kallo amma sai ta koma gefe tana murmusawa dalilin bata son ko kaɗan ta matsa kusa dashi ya kama hannunta.

Nan aka nufi falonta aka sauƙa a can, a nan ne Muhammad ya jawota ta zauna kusa dashi tare da Salima wacce itama tayi gayu har ta gaji da haɗuwa amma fuskarta yau babu annuri, wanda shine kaɗai ya mata cikas. Nan aka hau gaishe-gaishe tare da ban gajiya, minti talatin da haka ƴan’uwa suka musu Sallama sai dai wannan karon kafin Salima ta tashi Juwairiyya ta miƙe tana mai gyara gyalenta ta musu rakiya har bakin gate, sai da suka tafi sannan ta koma wanda tayi hakan ne don ta bashi lokaci shi da matarshi wacce itama yake satar kallonta idan ya ga kamar bata gani. (Ba zaki taɓa zama ke ce tauraruwarsa kaɗai ba, yana son matarshi kuma duk maganganun da yake miki kar ki sha mamaki itama yana yi da ita, ahh to.)

Sai dai tana shiga falon ta samu babu Salima babu Muhammad, to ina suka yi? Ko dai sun wuce falon Salima ne duk da cewa bata ga wucewarsu ba.

“Juwairiyya!” Ta ji dakakkiyar muryar Muhammad na kiranta daga can cikin ɗakinta.

“Na’am.” Ta amsa cikin siririyar muryar da ita kanta bata san tana da shi ba.

Zuciya na bugu cike da shauƙi da kuma tsantsar farin ciki ta nufi ɗakin ta tura ƙofa ta shiga. A bakin gado ta sameshi ya cire hularshi ya ajiye a gefe ya dafe hannayenshi duka biyu a gefenshi kamar sune kaɗai suke supporting ɗinshi.

“M.D.” Ta kira sunanshi tana mai ƙare mishi kallo sosai wanda na yanzu babu kunyan idon mutane don daga ita sai shi ne.

“Alƙawarinmu.” Shine abun da ya faɗa yana mai gyara zamanshi.

Wata shu’umar murmushi tayi kana ta ciji leɓenta kaɗan ta ce,

“Na me?” Kamar bata sani ba.

“Don’t toy with me Jay, in ba haka ba zaki sha punishment.”

Wannan karon dariya tayi mai sauti tana tsaye a bakin ƙofar bata iso ba, shi kuma tuni idanunshi suka canja kala bata ganin komai sai tsantsar jarabar da ke ciki.

“Abinci fa?” Ta ƙara testing haƙurinshi.

“Juwairiyya! Strip now!”

**********

Bayan awa biyu da haka suka fito falo Muhammad na riƙe da hannun Juwairiyya kamar wacce aka ce mishi zata gudu, yana zama ta nemi kwatan hannun nata amma ya ƙi saketa ƙarshe ya jawota ta faɗa jikinshi tana dariya.

“Zan baka abinci ne?”

“Irin na ɗazu?” Ya faɗa yana cizon kunnenta ta ƙara wata dariyar tana neman kwacewa.

“Na ɗazu ya ƙare, wannan wanda aka dafa ne a tukunya.”

“Too bad! Wanda ba’a dafawan nake so.”

“M.D.” Ta kwaɓeshi tana dukan kafaɗarshi kaɗan.

Sai da ya jagwalgwalata son ranshi sanna ya kawo bakinshi daidai saitin kunnenta ya ce,

“Ki kira Salima ta zo mu ci abinci.”

Sai a lokacin Juwairiyya ta tuna ashe tana da kishiya, a nan kuma ta tuna ai ɗazu suna tare ya aka yi ta tafi basu ci abincin ba? Ƙafarta na rawa kaɗan ta fice zuwa ɗakin uwargidan tata ta sameta a falo fuskar nan ta fi na koyaushe haɗewa.

“Wai in ji shi ki zo mu ci abinci.” Ta faɗi saƙon da aka bata.

“A ƙoshe nake.” Salima ta bata amsa muryarta sam babu fara’ah.

“Kya iya zuwa ki faɗa mishi.” Juwairiyya ta mayar mata da martani don ba zata zama ƴar aikanta ba.

Tana shiga falonta sai ga Salima wannan karon da fara’a amma in ka lura da kyau bai kai idonta ba.

“Ina Muhammad Hafiz?” Muhammad ya tambayeta bayan ta samu guri ta zauna.

“An kai shi Islamiyya. Ai da yace zai zo ya ganka kafin ya tafi na ce kana bacci.” Ta bashi amsa wanda yasa Juwairiyya da take sauƙe abinci kan carpet yin dariya amma bata bari sautin ya fito ba, yau kuma guilt tripping ɗin Muhammad aka yiwa.

“Ok.” Ya amsa mata ko a jikinshi, da alama bai ma san ta yi ba.

Sai da Juwairiyya ta gama sauƙo musu da abincin ta zuba sannan Muhammad ya yiwa Salima tayi tace a ƙoshe take amma yace dole sai ta ci.

Jiki a sanyaye rai kuma babu daɗi ta sauƙo suka fara cin abincin kamar wancan karon da alama dai an ramawa kura aniyarta. Hira suke yi wanda yawanci shine mai maganar da yake bashi da damuwar komai, amma su matan sun san me yake cikin ransu, lokaci lokaci kuwa in sun haɗa ido sai kowacce ta kawar da tata.

Suna gama cin abincin Juwairiyya ta kwaso wanda ƴan’uwa suka kawo mishi tace Salima ta tayata rabawa gida biyu, tace ta kai ɗaya gurinta ɗaya kuma zata ajiye a nata gurin. Wannan abu da tayi ya yiwa Muhammad daɗi wanda ya buɗi baki ya ce,

“Allah Ya miki albarka.”

Salima tana tafiya Muhammad ya ja Juwairiyya ɗaki sai ana kiran Maghrib ya fito cikin shiri ya wuce masallaci, bai dawo ba sai ƙarfe taran dare domin ya je gurin babanshi da yayanshi.

Yana shigowa falon Juwairiyya ya ɗauki waya ya kira Salima yace ta zo yana kiranta. Jim kaɗan sai gata tana walwali amma tana ganin amaryar tata ta gane ba ita kaɗai ce ta iya ado da kwalliya ba, domin canja shiga Juwairiyya tayi, wannan karon Abaya peach colour ta sanya mai adon stones ta ɗaura ɗankwalin nashi kamar hula sai ƙamshi kawai take zubawa.

“Dalilin da yasa na taraku a nan shine; kan maganar rabiyan kwana da kuka ɓata lissafi. Farkon tafiyata a ɗakin Juwairiyya na gama kwana biyu na, washegari akan zaki karɓi girki ke Salima amma baki karɓa ba muka tafi Abuja. Bayan nan kin je har UK muka yi wata ɗaya kika dawo amma da zan dawo sai bamu yi la’akari da duk wannan tafiya da nayi da ke da kuma bina da kika yi ba na sauƙa a gurinki na rama miki kwana biyunki aka cigaba da tafiya haka. Wannan karon kuma kwana ɗaya nayi a ɗakin Juwairiyya sannan washe gari na tafi da ita Abuja kun ga kenan akwai sauran kwananta ɗaya da ya saura wanda yau shine yau zata ƙarisa. Abun duba a nan shine in har nayi tafiya da mace ba zamu ƙirga kwanan da nayi da ita a can wani gari ba, sai wanda muka yi a nan gidanmu. Kowanne gida da irin tsarin da suke so suke yi, after all duk abunda muka haɗu muka magantu a kai shine daidai matuƙar ba’a cuci kowa ba. Wani ƙarin bayani shine a addinance an bani daman idan nayi tafiya in sauƙa a ɗakin da na so amma ni ban ɗauki haka ba, na zaɓi a cigaba da tafiya da kwanan da nake dashi tare da mace. Sannan idan nayi tafiya da mace muka dawo tare to ba’a ɗakinta zan sauƙa ba, zan sauƙa ne a gurin wacce muka bari a gida. Haka kuma in mace ce tayi tafiya ita kaɗai idan ta dawo yau washe gari ni kuma zan dawo ɗakinta. Idan hakan ya muku shikenan sai mu zauna a haka, idan bai muku ba kuna da daman canjawa ba zan hanaku ba, haƙƙinku ne ba zan shiga ba. Kuma zan so ku ma ku tayani yin adalci a tsakaninku kar ku bari in shiga halaka don Allah. Shin hakan ya muku kuma kun fahimta?”

“Eh ya yi, kuma mun fahimta.” Faɗin Salima jiki a sanyaye.

“Eh ya yi. Allah Ya baka ikon yin adalci tsakaninmu.” Itama Juwariyya ta tofa tata.

“To Alhamdulillah.”

Minti biyar da haka Salima ta musu sallama ta fice jikinta gabaɗaya a mace. A nan ne Muhammad ya dubi Juwairiyya da take sauƙo mishi abinci ya dakatar da ita ya ce,

“Bana jin wannan yunwan, wani yunwan nake ji.”

“Apple? Zai maka yawa fa.” Ta faɗa tana dariya.

“Never!”

9:23 am

“Kin mini ƙarya wai kina missing ɗina, amma ji yanda kika tara tsokoki a jikinki ta ko’ina.” Faɗin Muhammad yana taɓa mazaunan Juwairiyya wacce take durƙushe a gaban bags ɗin da ya dawo dasu tana ciro abubuwan ciki.

Dariya tayi kana ta ɗaga ido ta kalli yanda hankalinshi gabaɗaya yake kan abun da yake yi ta kaɗa kanta ta ci gaba da aikinta.

“Ni kuma ban yi tsammanin ramewar taka ta kai haka ba, ka rage ƙiba sosai fa, yanzu zaka iya yin daidai da Yaya Abdallah (Yayanshi).”

Shiru yayi bai amsa ba, Juwairiyya taci gaba da aikinta amma da ta ji shirun yayi yawa sai ta ɗago ido ta kalleshi, girarshi ɗaya a sama yake kallonta da wani expression mai fassarar ‘me kika ce’! A nan ta gane tayi katoɓara ai kuwa ta rufe bakinta da dukkan hannayenta tana dariya amma bata bari sautin ya fito ba.

“Wato idan ya zo kallonshi kike yi har kin gane girman jikinshi ko Juwairiyya?” Yayi maganar a hankali yana bin kowacce kalma ɗai ɗai.

“Wallahi ba haka bane, kar ka mini sharri. Ni kunyar haɗa ido ma dashi nake yi kawai dai yau da gobe ne yasa na gane.” Ta kare kanta tana mai buɗe ɗayan jakan ta fara ciro kayan ciki wanda shima tsaraba ne kowanne da sunan mutum a jiki.

“Gwanda da kika faɗa mini, daga yau ya daina zuwa.”

“Innalillahi M.D kar ka ce haka please. To sai ka ce mishi me? Cewa zaka yi ya daina zuwa gidanka kamar yanda ya saba?” Juwairiyya ta dakata da abun da take yi ta rarrafo ta zo gabanshi ta shige tsakanin ƙafafunshi.

“Kwarai.” Ya bata amsa a taƙaice yana hararanta.

“To idan ya tambayeka dalili me zaka ce?” Juwairiyya ta ƙara gwalalo idanunta tana ƙara shigewa jikinshi ya saka hannunshi ɗaya a ƙirjinta ya dakatar da ita.

“Ki tsaya daga can in ba haka zaki ƙara jin jiki. Sai in ce mishi matana suna kallonka da yawa ne.”

Juwairiyya ta ja numfashi da ƙarfi kana ta rufe bakinta tana dariya don ta san wasa yake yi amma wani gefe na zuciyarta na raya mata zai iya aikatawa.

“Don Allah kayi haƙuri. Wallahi ni bana kallonshi, yayanka ne fa!”

Bai ce komai ba ya cigaba da hararanta ita kuma ta ci gaba da dariyan tana kawar da idanunta gefe in kallon nashi ya mata yawa.

“Big Baby ka ce wani abu.”

“Wani abu.”

Ta ƙara tuntsirewa da dariya tana mai kwantar da kanta kan cinyarshi, amma sai da ta bari ya shagalta ta cijeshi kana tayi saurin matsawa gefe kamar ba ita ta yi ba.

“You bite me!” Ya faɗa yana sosa gurin kamar bai yarda cizonshi tayi ba.

“Saboda you are being ridiculous ne.”

“Ki zo in rama.” Ya yi maganar with finality a muryarshi.

“A’a na yafe.” Ta ƙara matsawa nesa da shi tana jan akwatin tare da ita.

Miƙewa yayi da niyyar ya kamota ta tashi da tsallenta tana dariya ta je bakin ƙofa ta tsaya, Muhammad yana son tsumewa amma ya kasa dalilin ya kasa controlling murmushin da yake yi.

“Ki zo na ce.”

Ta maƙe kafaɗanta tana mai juya mishi ido tana cizon yatsanta.

“Juwairiyya na faɗa miki ina sauri ko? Ki ware naku sannan ki haɗa mini wanda zan fita dashi.” Wannan karon babu wasa yayi maganar kana ya koma ya zauna ya ɗauki wayarshi ya fara dannawa, sannan wannan lokacin fuskarshi ta zama neutral babu ɓacin rai haka kuma babu murmushi.

‘Dodo ya dawo’ Juwairiyya ta faɗa a ranta tana mai jin shakka kaɗan ya shiga ranta, lokaci ɗaya ta shiga taitayinta ta tako jiki a sanyaye ta tsugunna ta fara aikinta, sai da ta gama ta mishi godiya da nata sannan ta kaiwa Salima tata sauran da zai fita dasu kuwa ta haɗasu a manyan leda guda biyu ta ajiye a falo saboda in ya zo fita ya ɗauka.

Tana dawowa ɗaki ta ji an kamota ta faɗa ƙirjinta mutum, wata siriyar ƙara tayi ganin fuskar Muhammad na mata wani murmushin mugunta sannan ya haɗe hannayenta duka biyu ta bayanta ya riƙe da nashi ɗaya. Ta zama helpless don ƙarfinta da nashi ba ɗaya ba.

“Wa na kama?” Ya faɗa a hankali yana shinshinar wuyanta.

Girgiza kai tayi tana ƙunshe dariyarta amma idanunta roƙonshi suke yi kar ya cijeta.

“Oh! Ba zaki yi magana ba?” Ya ƙara damƙe hannun nata wanda is enough ta ji zafi amma ba zai ji mata ciwo ba.

“Ni.” Ta amsa tana jin kamar ta sake fitsari don tsoro da kuma dariyar da yake cinta. (I love love, sorry, let’s continue.)

“Ban ji ba.” Ya faɗa yana mai banƙara ƙirjinta ya ɗaura kanshi a kai.

“Ni ce, wallahi ni ce!”

Da haka ya fara binta da wani irin salo mai wuyar fassara har ta fara mantawa wai kamata aka yi, bakinshi na kan albarkatun ƙirjinta ya yi magana.

“In rama?”

“Allah idan ka cijeni a gurin sai na kai ƙararka.”

“Ina?”

Tayi shiru a nan kuma ta ƙara mance me suke magana a kai tana lumshe idanunta suka ji ana buga ƙofar falo. A nan ta dawo hayyacinta tana kallon Muhammad wanda da alama shima ya manta ramako yake yi amma zafin da ta ji a jikinta yasa ta callara siririyar ƙara ta fara mutsu mutsun kwatar jikinta.

“Gobe ki sake cizona. Kin ji?” Yana faɗin haka ya saketa yana murmushin cin nasara kana ya ɗauki towel ya wuce banɗaƙi.

“Ana zuwa.” Juwairiyya ta ɗaga muryarta tana duba inda ya cijeta ko ya tsinke amma yana nan yanda yake, murmushi ta yi kana ta gyara zaman rigarta sannan ta ɗauki ɗankwali ta fita zuwa falo.

“Ko dai kuna bacci ne?” Faɗin Salima bayan an buɗe mata ta shigo.

“A’a wallahi.” Juwairiyya ta bata amsa tana mai zama a kujera.

“Ina mai gidan? Na zo mishi godiya ne tunda na ga yanzu kika kawo mana na dai tabbata ba bacci zaku koma ba.” Yanda tayi maganar kowa ya ji zai san akwai ɗaci a harshenta.

“Ya shiga wanka yanzu, bari in faɗa mishi kin zo.” Da haka Juwairiyya ta miƙe ta tafi ɗaki, tsabar neman magana sai ta ƙi rufe ƙofar ɗakin ta yanda Salima zata ji ƙarar buɗe ƙofar banɗakin.

Minti ɗaya sai gata ta dawo tana murmusawa ta ce,

“Na faɗa mishi, ki jira ya fito.”

Nan suka yi shiru har na minti uku a nan Salima ta miƙe tana cewa,

“Bari kawai in tafi, anjima zan dawo.”

“To shikenan.”

Minti sha biyar da haka Muhammad ya gama shiryawa cikin white yadi mai taushi ɗinkin half jamfa, sai kuma hularshi da take kalar black and white mai zane mai kyau da kuma takalmi black da ratsi-ratsin white. Sosai yayi kyau wanda hakan yasa  Juwairiyya take bin shi da kallo har ya gama fesa turare a jikinshi amma ta kasa buɗan baki ta yaba mishi gudun kar tayi katoɓara irin na ɗazu, domin da gaske ya rage ƙiba sosai wanda tana sane da hakan saboda suna ganin juna a video call, amma a yanzu da take ganinshi a zahiri sai ta gane distance ɗin da ke tsakaninsu bai mishi adalci ba, domin kuwa tumbinshi da ta ake hangota cikin riga a yanzu ta narke sai ɗan kaɗan domin ya faɗa mata har yanzu da sauran aiki a gabanshi don bai kai inda yake son tsayawa ba.

A falo ta tsaya shi kuma ya fita waje zuwa ɗakin Salima bayan ya saka ledojin a cikin booth ɗin mota, minti uku da haka suka fito tare wanda Juwairiyya da take tsaye a bakin window ta hangosu ta ji ɗaci a ranta dalilin manne mishi da Salima take yi. Futt itama ta fita ta je har bakin motar ta sameshi yana ƙoƙarin shiga mota amma Salima ta yi banke banke ta tare mata shi.

“Excuse me.” Juwairiyya ta faɗa tana mai raɓewa ta gefenta ta isa bakin ƙofar a yayin da yake shiga motar ya zauna.

Hannu ta saka ta gyara mishi zaman hularshi wacce kafin ya fita daga falonta lafiyarta kalau kana ta dubeshi ido cikin ido tana murmusawa ta ce,

“Na gyara maka hulanka ne don na ga ta karkace, yanzu kam ta zauna kamar na ɗazu. And kayi kyau sosai.”

“Thank you.” Ya faɗa a sanyaye amma saƙon ya isa ya marairaice fuska yana mata magana ta ido irin ‘I’m sorry’ ɗin nan.

Gyaɗa kanta tayi a hankali kana ta dubi Salima ta take cewa,

“In buɗe maka gate ɗin ne?”

“A’a bari in kunna motar zan je in buɗe, in ya so in na fita sai ki rufe amma ki je ki saka hijabi.” Ya amsa mata yana mai kunna motar ta fara diri.

“Sai yaushe zaka dawo?” Juwairiyya ta tambayeshi tana mai langaɓar da kanta.

“Bayan azahar, wani abu ne?”

“Ban gaji da kallonka bane.” Ta faɗa a shagwaɓance.

Shiru yayi yana kallonta da murmushi a fuskarshi sannan ya fito daga motar bayan ta matsa mishi ya kalli ƙofar Salima wacce tun da aka ce ta je ta saka hijabi ta tafi, da ya ga bata fito ba sai ya rankwafo ya haɗe bakinsu guri guda wanda cikin seconds huɗu ya janye jikinshi ya ce,

“In kika cigaba da faɗin haka zan zauna a gida, and you know what will follows.” Ya kashe mata ido ɗaya kana ya barta a gurin tana blushing ya buɗe gate sannan ya dawo ya shiga, a lokacin ne kuwa Salima ta dawo sanye da hijabin.

“A dawo lafiya M.D.” Faɗin Juwairiyya bayan ta koma can gefen kitchen ɗinta inda ba za’a hangota daga waje ba.

“Allah Ya tsareka ya dawo da kai lafiya.” Salima ma ta faɗi tata a lokacin da yake jan motar ta fice daga gidan ta ja ƙofar ta rufe.

Tana gama rufe gate ta hango Juwairiyya na takowa taf taf gurinta da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce,

“Kin tuna wani lokaci da nace miki ki mishi hidima ban damu ba?”

“Eh.” Salima ta amsa cautiously tana binta da kallo.

“To na canja ra’ayi, yanzu da na san daɗin mijin sai na ji ya kamata in datse wancan maganar. A daina ba na so.” Tana gama faɗin haka ta juya tana takawa ɗaiɗai ta bar Salima baki buɗe wacce bata san kaurin wuyar Amaryar tata ya kai har haka ba.

Sai bayan azahar Muhammad ya dawo Juwairiyya ta kawo mishi abinci tana saka mishi ya dakatar da ita bayan serving spoon na biyu.

“Haba M.D wannan kam ai babu abun da ka ci.” Ta yi maganar kamar zata yi kuka.

“Zaki ɓata mini work outs ɗin shekara biyu Juwairiyya, haka ya isheni in ba so kike yi in dawo kamar da ba.”

“Ni ko yaya ka dawo ina son mijina amma ka ci abincin da na dafa maka. Allah ina lura jiya ma baka ci wani abincin kirki ba.”

“Ke fa kike kirana ɗan lukuti har da saka mini suna wai Rock.”

“Ya Salam! Wa ya faɗa maka?” Juwairiyya ta kalleshi cike da mamaki tana murmusawa.

“Ina da kunnuwa a gari.”

“Kana da masu kawo maka gulma dai, lokacin ai neman magana nake yi.”

“Juwairiyya kin ji rasar kunya, idan na tuno har mamaki nake yi da ban taɓa kama wannan bakin naki mai tsiwan na murɗeshi ba.”

Dariya tayi bata ce komai ba don bata son a faɗaɗa magana a tuno abu mai girma rai ya ɓaci, shirme da rashin hankali kam tayi amma yanzu ta yi hankali, waɗanda ma suke irin nata zata fara musu addu’an Allah Ya shiryesu.

Da yamma liss ya mata sallama ya tafi ɗakin Salima, tana ji tana gani bata isa ta hanashi ba haka ya fita daga hannunta ya koma na wata. Lallai mata a gaishesu, lallai ya kamata a tausayawa mata domin sun kasance masu haƙuri da juriya akan al’amarin kishi.

Kwananshi biyu a can ya dawo gurinta, suna zaune a falo suna hira Muhammad ya rage volume ɗin TV kana ya ce,

“Faɗi abun da yake ranki.”

“Na me?” Juwairiyya ta tambaya ta mamaki a muryarta.

“Ina lura da ke kamar akwai magana a bakinki.”

Shiru tayi tana sadda kanta a ƙasa wanda hakan yasa Muhammad ya dubeta wannan karon fuskarshi so serious ya ce,

“Juwairiyya menene?”

“Ba wani abu bane fa.” Tayi saurin faɗa don sai ta ji bata son yin maganar ta fasa.

“Kar ki sake mini musu, menene?” Shikenan ya kashe duk wata hanyar inda inda.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta gyara zamanta ta fuskanceshi da kyau ta ce,

“Yanzu kana tunanin ni juya ce?”

“Me ya kawo wannan maganan kuma?” Ya tambayeta yana ɓata fuska.

“Shine maganar da nake son yi da kai ɗin kuma kai ka umurceni in faɗa maka.”

“Right. Me yasa kike wannan tunanin?”

“Shekaru da dama da auren fari na amma har yanzu ko ɓatan wata ban taɓa yi ba. Shine nake tunanin anya ni ba juya bace?”

“Kar ki yanke tsammani da rahamar ubangiji, haihuwa tashi ce kuma Shi yake bawa kowanne bawanshi a lokacin da Ya ke so. Mutane nawa ne kike jin labarin sun shekara da yawa har sun fara tsufa basu samu haihuwa ba amma kwatsam sai ki ga Allah Ya ba su? Suna da yawa Juwairiyya. Sannan ke da sauran ƙuruciyarki, ki cigaba da addu’a Allah zai baki.”

“Amma me yasa baka taɓa mini maganan ba duk tsawon lokacin da nake tare da kai? Ko baka son haihuwa da ni ne?”

“Me yasa ba zan so haihuwa da ke ba?” Shima ya mayar mata da tambaya da alama maganan ya fara ɓata mishi mood.

“Kawai na ga baka taɓa kawo maganan bane.”

“Maganan ne bai zo ba, amma ba zan ƙi haihuwa da ke ba Juwairiyya. Mu bar maganan nan haka.”

Da haka suka canja hira amma can cikin zuciyar Juwairiyya bata gamsu da amsoshinshi ba, sannan bai nuna mata ko ya furta cewa yana son haihuwar da ita ba, kamar ma bashi da plan ɗin haihuwa da ita, kenan da gaske ya ɗauketa ne a matsayin sex object? Ganin zata iya ɓata musu peaceful zamantakewarsu sai bata sake kawo zancen ba har Muhammad ya gama wata ɗaya da sati ɗayanshi ya koma UK ya bar matan nashi da tsantsar kewa.

Kwanci tashi yau wata bakwai ciff da tafiyar Muhammad wanda ake sa ran wata uku na gaba zai dawo ya gama school ɗin gabaɗaya. Ita kuma Juwairiyya yau take cikin tsantsar farin ciki dalilin gama makarantarta, yau suka fito a last paper ƙarfe goma da rabi, da yamma kuma bayan la’asar suna da Departmental party wanda daga nan ne ta gama da GSU wanda har cewa take yi zata dawo yin Masters daga baya.

Sai da ta samu guri a can gefe ta kirashi kamar yanda ya umurceta tun a daren jiya.

“Congratulations graduate. An gama exams lafiya?” Muhammad ya fara faɗa bayan ya ɗauki wayar.

“Lafiya kalau. I can’t believe it wallahi wai yau ni ce graduate.”

“Ikon Allah kenan, na tayaki murna, and sannunki da ƙoƙari.”

“Nagode, kai ma sannunka da ɗawainiyata Allah Ya biyaka da Aljannah nagode.”

“Yiwa kai ne. Albishir!”

“Goro!” Ta saurin faɗa don bai cika yi mata hakan ba.

“In zuwa next week zan muku kwana huɗu in koma.”

Wani ihu Juwairiyya tayi kana tayi saurin toshe bakinta ta ƙara matsawa can gefe ganin mutane sun zuba mata ido ta ce,

“Ka ce wallahi!”

“Baki yarda bane?”

“But how? Why?”

“Wannan abokin nawa da na baki labari Sharafadeen, auren nashi ya tashi shine mu abokanshi da muke tare a nan zai biya mana kuɗin jirgi zuwa Nigeria. Da har na ce ba zan je ba amma daga baya na canja ra’ayi, ko ba komai zamu ci kuɗin gwamnati kuma zan ga iyalina. It’s unexpected for me too, so kar ku faɗawa kowa zan zo tunda ba jimawa zan yi ba. I’m coming home.”

Da jindaɗi biyu Juwairiyya ta koma gida wanda ji take yi kamar a kan gajimare take tafiya tsabar murna da farin cikin da ya dabaibaye zuciyarta da ilahirin jikinta gabaɗaya, tana shiga gida tayi hanyar ɗakin Salima kamar yanda suka sabarwa kansu, kwankwasa mata ƙofa tayi aka mata iso ta kutsa kai ciki.

“Na dawo, na sameku lafiya?”

“Lafiya kalau. Yanzu kam kin gama school ɗin ko?” Salima ta tambayeta tana mai murmusawa.

“Eh wallahi.”

“Na tayaki murna.”

“Nagode. Kin ji wai zai zo next week ko?” Juwairiyya ta kasa ɓoye murnanta.

“Eh, ɗazu yake faɗa mini da safe shine nace wataƙila daga nan zamu yi bankwana da ke.”

“Ban gane bankwana da ni ba.”

“Ba dai har kin manta alƙawarin da kika mini cewa da zarar kin gama school zaki bar mini mijina ba? Ke fa da bakinki kika ce don kar a tsayar miki da karatun ne kika aureshi. Ko dai ni nake imagining komai?”

Shiru Juwairiyya tayi kamar kaska ta ci shirwa, bata taɓa zaton akwai ranar da Salima zata furta mata wannan magana gaba gaɗi haka ba. Ta ɗauka an wuce wannan babin sun zama ɗaya kuma ta gane ba zata tafi ba.

“Kina son tsonaka.” Shine abun da ta faɗa don canja musu yanayin nasu daga tension zuwa sauƙi.

“Alƙawari kika ɗauka ke da bakinki, na kuma bar miki mijin na shekara uku har da watanni. I want my husband back tunda burinki ya cika.”

“Salima kanki ɗaya kuwa? Ko munafurcin naki ya ƙare shiyasa yanzu kika canja salo kika ɓullo ta wannan fannin? To shi ma zaki yi ki gaji, kuma babu inda za ni ina na tare da mijin naki har ƙarshen rayuwata. Wannan shine pay back ɗina akan munafurtata da kike ta yi a baya, ki sha damarar ganin fuskata har tsufanki don it will be a long journey.” Ta ƙarisa maganar zuciyarta na tafarfasa kamar zai ƙona mata ƙirji.

“Ni ce mai munafurci?” Salima ta tambaya tana mai dafe ƙirjinta.

“Ƙarya aka yi? Ko don kin ga ban taɓa faɗi bane kike zaton ban ganeki ba? Na samu labarin duk gulmata da kuma aibatani da kike yi a cikin dangin Muhammad, na barki ne da halinki da kuma Allah da ya halicceki don shine kaɗai zai mini sakayya daidai yanda kika mini, amma na san komai na kuma san wacece ke.”

“Ina ce ni ce munafuka?” Salima ta ƙara nanatawa kamar bata ji sauran bayanan ba.

“An faɗa ke munafuka ce Salima, ki mini abun da zaki mini.” Ta faɗi hakan tana mai ɓoye sauran maganganun a ranta domin ta sani in har furta sai abun ya ɓaci fiye da tsammani.

“Ki fita mini a falo don ba zaki zo kina zagina kina ci mini mutunci ina barin ki ba. Ba zan ɗauka ba.”

“Ko baki faɗa ba zan fita saboda nima ba son zama kusa da ke nake yi ba mace mai fuska biyu kawai.” Juwairiyya tana gama faɗin haka ta fice daga falon zuciyarta na lugude tana jin haushi da kuma takaicin kasa controlling kanta da tayi. Me yake damun Salima ne kuma me yake shirin faruwa? Har ta je bakin ƙofarta tana kiciniyar buɗewa ta ji muryar Salima na cewa,

“Kamar yadda kika ɗauki alƙawari kika kasa cikawa ni zan wuce gaba in cika miki, ki saka a ranki daga yau zuwa ranar da mijina zai dawo zaki bar mini gidana, ni kuma shine alƙawarin da na ɗauka.”

Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama’a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne!

 Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?

Mum Fateey 👌

Wannan page ɗin kuma naku ne manyan mata, Mum Nana, Aunty Mamey, Zulaiha, Reine, Maryam Usman da Aunty Bilkisu yan group 1. Mum Fateey na muku Son so ❤️

Tunda Juwairiyya ta koma falonta sai ta kasa samun sukuni dalilin zuciyarta da take bugawa da ƙarfin gaske ga kuma tsoro da ya shigeta da zarar ta hasko fuskar Salima a kwakwalwarta. Ta rasa gane me zata fassara wannan yanayin amma zata iya rantsuwa har da alƘur’ani da hango tsabar mugunta a idanunta, she look crazed kamar wacce aljanu suka shiga jikinta, sannan a yanda take magana da confidence shi ya ƙara ɗaga mata hankali. Wani abu da take shakka kuwa shine; ko a da Salima bata magana ta bata wahala wanda har hakan yayi sanadiyyar fitarta a cikin hankalinta ta shiga depression, to ina ga kuma yanzu da ta fito da maitarta fili har take faɗa mata wai zata fitar da ita daga gidanta? Tana tsoron munafuki don ita bata iya ba kuma bata fatan ta koya balle ta yiwa wani, yanzu bata san me zata je ta mata ba, tana kuma tsoron kiran Muhammad ta faɗa mishi cewa duk abun da Salima zata faɗa mishi ƙarya ne! Amma zai yarda? A’a hakan zai sa ma ya ƙara gaskata abun da zata faɗa ɗinne ya ce tana son ɓoye laifinta shi yasa ita tayi saurin kawo ƙara. Idan kuma ta bari bata yi magana ba sai Allah ne kaɗai zai kwaceta domin bata san me zata yi mata ba balle ta kare kanta. Da wannan tunani da kuma fargaban abun da zai iya faruwa Juwairiyya ta wuni wanda kafin la’asar ta ji komai ya fice mata a rai, ciki kuwa har da Departmental party da zasu yi a yammacin ranar.

Amma kiran wayarta da course mates ɗinta suke mata yasa ta tashi jiki babu kwari ta shiga wanka, tana sallar la’asar ta fita wannan karon ba tare da ta yiwa Salima sallama ba domin ta gaji da sintirin alhali dukkansu haushin juna suke ji. Idrisa ne ya zo ya ɗauketa ya ajiyeta a school, kai tsaye ta shige New Multipurpose Hall ta samu guri ta zauna a baya bayan ta gaisa da wasu daga cikin ƙawayen nata.

“Lafiya dai na ga kin zo kin zauna a baya? Ga can su Aunty Mamey da Zulaiha sun ajiye miki seat a gaba. Ko dai baki da lafiya ne?” Aunty Balkisu ta tambayi Juwairiyya bayan ta iso wajenta.

“Wallahi ni ɗin ne yau sai a hankali, ga kaina da yake ciwo.”

“Allah Ya baki lafiya, gashi abun na yau ne kaɗai da sai in ce ki koma gida. Idan an rabu yau ba za’a sake haɗuwa duka a guri ɗaya ba.”

“Rayuwar kenan fa, komai yayi farko zai yi ƙarshe, za’a yi kewar juna kam. Ni kin sa na ji ƙwarin gwiwa ma, ga can Mum Nana da Reine suma sun iso mu je gurin nasu.”

Da haka Juwairiyya ta miƙe suka tafi can gurin sauran suka zauna aka fara hidima, sun sha hotona don ajiye tarihi sannan an ci an sha an kuma yi raye-raye amma banda ita, don dama bata iya ba kuma bata ra’ayin rawa cikin jama’a.

Sai ana kiran maghrib ta dawo gida, kai tsaye ɗakinta ta wuce ta fara gabatar da sallah sannan ta kira Mamanta wacce sun yi waya da safe bayan ta fito daga exams ta mata murna.

“Mama kuna lafiya?”

“Lafiya kalau Graduate, ya bikin gama school ɗin kun yi ne?”

“Mun yi, yanzu ma dawowana gida kenan. Mama ki mini addu’a Allah Ya sa duk wanda ya nufeni da sharri kar ya samu nasara.”

“Wani abu ne ya faru Juwairiyya?” Mama ta tambayeta da ɗan tsoro a muryarta.

“Babu komai. Kawai ki mini addu’a Mama.”

“Addu’a kam kullum cikin yi muku nake yi, ya rage gareku ku ma ku dinga ƙarawa a kan nawa. Juwairiyya na san akwai abun da ya faru kika ce haka, ki faɗa mini don hankalina ba zai kwanta ba idan ban sani ba, baki da kowa da zaki faɗawa damuwarki sama da ni Juwairiyya. Faɗa mini menene ya faru? Matsala kika samu da abokiyar zaman taki?”

Juwairiyya shiru tayi domin tana tsoron faɗawa Mama abun da ya faru don ta sani ita zata bawa laifi duk da cewa ta san tayi laifin amma ba zata gane cewa an kaita bango ne yasa ta yi hakan ba. Wai Bahaushe ya ce ‘Abun da aka gasa shi ya ga wuta, tsire labari yake ji’. Duk yanda zata faɗi me aka mata kuma ake kan mata ba zasu ganshi a bakin komai ba saboda ba su suke jin raɗaɗin da take ji a ranta ba, gani zasu yi tayi gajen haƙuri sannan ta kasa controlling bakinta.

“Kin yi shiru.” Mama ta sake nanatawa.

A nan Juwairiyya ta ja numfashi ta fara zayyanewa Mama duk abun da ya faru bata rage komai ba itama ta faɗi laifinta. Sai dai a maimakon ta ji Mama ta fara mata masifa sai ta ji saɓanin haka.

“She knows how to push your button, tayi amfani da haka kin furta mata kalma babba Juwairiyya da ko’ina aka je ke za’a bawa rashin gaskiya. Duk da cewa tana miki munafurcin ba shi zai baki lasisin kiranta da sunan ba, kin yi kuskure babba kuma ina miki addu’a Allah Ya kareki ya kuma sa kar abun ya zama babba.”

“Amin Mama. To yanzu ya zan yi?” Ta tambaya desperately.

“Kiyi addu’a, shine mafita. Don da zan ce ki je ki bata haƙuri ne amma sai na tuna ko me kika yi sai ta yi abunda ta shirya, wannan bada haƙurin ma shi zai yi fueling abun a ce ke da kika yin ma kin san baki kyauta ba kin zo kina bata haƙuri. Amma in zaki iya ki je wataƙila I might be wrong. Ke dai a rayuwa ki guji bakinki, duk lokacin da aka ɓata miki rai ki dinga yin shiru wallahi ya fi miki alkhairi. Allah Ya rufa asiri.”

Da daren ranar Juwairiyya ta yi waya da Muhammad amma har suka yi sallama bai mata magana akan Salima ba haka kuma bata ga canji a yanayin shi ko muryarshi ba, kenan Salima bata faɗa mishi ba ko kuma ta sanar da shi ɗin ya bata haƙuri an wuce wajen. A nan ta samu hankalinta ya kwanta ta fara shirin dawowar nashi duk da cewa bata yi mai yawa ba saboda kwana biyu kadai zai yi a ɗakinta ya koma, hakan yasa tun ana saura kwana biyu ya diro ta gama duk abun da zata yi hatta lalle da kitso da kuma abincin da zata tareshi da shi, ta yi soups har kala huɗu ta saka a fridge. Tsakaninta da Salima kuwa kamar kowaccen su avoiding ƴar’uwarta take yi, saboda a yanzu da Juwairiyya ta daina fita school sai ya kasance bata zuwa ɗakin Salima don mata sallama. Ita kuma Salima dama ko zata fita kai HJ school ko ɗaukoshi bata mata sallama a cewarta ai ba zuwa unguwa bane kuma ko ta tafi bata wuce minti goma a can ta dawo. So sai tayi amfani da wannan daman take ficewanta ba tare da ta yiwa Juwairiyyan sallama ba, hakan yasa har ranar da Muhammad zai iso basu ƙara magana ba.

Wannan karon da yake basu yi gayya ba kuma babu wanda ya san da dawowar tashi Salima ce kaɗai ta je ta ɗaukoshi tare da ɗanta wanda yake murnar dawowan Babanshi. Bayan ta ɗaukoshi suna dawowa gida yake cewa,

“Ina Juwairiyya? Na ɗauka tare zaku zo.”

“Tana gida, kayi haƙuri ban san kana so mu zo tare ba da na mata magana ai.”

“Shikenan.”

Suna dawowa gida ya sauƙa a ɗakin Salima ya zauna a falo yana sauraron inda zai ga Juwairiyya domin ya ɗauka zai ganta a waje ta zo tarɓanshi, amma gashi har ya shigo ya zauna shiru babu ita babu alamarta.

“Juwairiyya bata gida ne? Ko bata san na dawo bane?” Wannan karon yayi maganar kamar ranshi ya ɓaci kaɗan.

“Wallahi ban sani ba.”

“Ki kira mini ita.”

Salima sai da ta gama tsiyaya mishi juice a glass cup ta miƙa mishi ya karɓa sannan ta fita zuwa gurin Juwairiyya wacce ta ji alamun shigowarsu amma tana sallah ne yasa bata fito ba. A tsakar gidan suka yi kiciɓus suka kalli juna kowacce da abun da yake ranta game da ƴar’uwar tata.

“Baban Hafiz yana kiranki.” Faɗin salima tana mai juyawa inda ta fito.

Suna shigowa Juwairiyya tayi locking eyes da Muhammad sai duk suka samu kansu da murmusawa,

“Sannu da dawowa, ya hanya?”

“Lafiya. Baki ji mun shigo bane?” Ya watsa mata tambaya duk da ma cewa ba cikin ɗaga murya bane.

“Wallahi ina sallah ne, ai tun ɗazu da ka faɗa mini ka hau jirgi nayi lissafi akan 20minuntes back zaka iso amma shiru, to lokaci yana ta ƙurewa ne shiyasa na tada sallah. Ka iso lafiya? Ya gajiyan jirgi.”

“Alhamdulillah, ya na sameku?”

“Wallahi lafiya kalau.”

Nan suka hau hira tsakaninsu dukkansu a nan Salima ta sauƙo mishi da abinci ya ci kaɗan wannan karon bai ce su ci tare ba. Ganin ya gama cin abinci yasa Juwairiyya ta musu sallama ta koma inda ta fi wayo domin bata son cigaba da ganin irin kallon da Muhammad ke aikawa Salima. Ta sani matarshi ce kuma ta san abun da zai biyo baya a bayan idanunta amma duk da haka bata fasa jin kishi da zafi ba a zuciyarta. Ta ɗauka ma zasu ce ga HJ su tafi tare amma tana isa falonta ta ji Nanayo ta shigo gidan ta ɗaukeshi zata kaishi Islamiyya. Tana son shiga ɗakinta amma tana tsoron kar kunnenta ya jiyo mata abunda ba zata so ji ba, saboda a yanzu da rana tayi tsakan nan ƙafa ta ɗauke babu mamaki iska ya tattaro mata muryarsu ya kawo mata ɗakinta.

Sai bayan isha Muhammad ya dawo daga masallaci ya aika Salima ta kirata wai su zo su yi hira, bata so hakan ba amma babu yanda ta iya ta je suna hiran ya kallesu dukkansu ya ce.

“Lafiya kam na ga bakwa yiwa juna magana kamar da? Ko dai akwai abun da ya faru bayana ne?”

Girgiza kai suka yi dukkansu domin ta ɓangaren Juwairiyya bata son ma a ɗauko zancen ba don bata da gaskiya ba sai don za’a fi ganin laifinta fiye da na ƴar’uwar tata, sannan bai dace daga dawowanshi yau su tayar mishi da hankali ba. Ita kuma Salima ba yau tayi niyyar yin maganar ba don haka da ya sake tambaya sai suka buɗi baki suka mishi ƙarya wai babu komai, sai dai yanda yake bin su da kallo suka gane bai yarda ba amma dai ya bar su for now.

Washe gari da hantsi Muhammad ya shigo ɗakin Juwairiyya ya sameta a falo ta cakare kamar mai zuwa walima dalilin ta sani zai shigo gurinta da safe. Sai a wannan lokacin ya samu keɓancewa da ita ya ware hannayenshi wai yayi hugging ɗinta ta girgiza mishi kai.

“Ka tuna kwanaki ka yi na nuna bana so? To itama ba zan shiga haƙƙinta ba.”

“Wannan ba hujja ba ce, Annabi ma yana rungumar matanshi ko da ba ranar kwanansu bane.”

“Na shi innocent hug ne wanda bashi da maraba da wanda uwa zara yiwa ɗanta don so da ƙauna, kai fa Big Baby? Seconds biyu yayi yawa zan tsinci hannunka a wani gurin, ko ba haka bane?” Ta tambayeshi tana murmushi mai cike da naughtiness.

“Kin fi ni gaskiya, amma ki sani duk ranar da na kamaki zaki ji a jikinki.”

“I actually don’t mind.” Ta kalli mid section ɗinshi tana cizon yatsarta.

“Jay, you are playing with fire.” Ya faɗa yana mai takowa gurinta amma tayi saurin miƙewa tsaye ta ƙara ratan da ke tsakaninsu tana dariya.

“Babu inda zan je, ina nan ina jiranka. And kayi kyau, sosai, kamar in ƙara aurenka haka nake ji.”

Shiru yayi bai ce komai ba yana kallonta sama da ƙasa, can ya girgiza kanshi ya fice yana murmusawa, da haka ta leƙa window ta ga tare da Salima suka fita, a nan ta tabbatarwa kanta cewa kenan ba zata faɗi abun da ya faru ba ta haƙura ko kuma ta karaya.

Washe gari tun da wuri ta gama shirye-shiryen karɓanshi, sosai ta haɗu ciki da waje, jira kawai take yi yamma liss yayi ya shigo kamar yanda ya sabar musu. Amma tana fitowa daga wanka karfe biyar ta ji wayarta na ƙara tayi saurin ɗauka dalilin sunan mijinta da ta gani. Cikin zumuɗi ta ɗauka duk da cewa ta san yana ɗakin Salima ta ce,

“Assalamu alaikun M.D na.”

“Ki zo ina nemanki.” Yana faɗin hakan ya kashe wayarshi.

Wani irin kaɗawa hanjin cikin Juwairiyya suka yi tsabar tsorita domin yanda yayi maganar da dakakkiyar murya da kuma ɓacin rai yasa ta gane duk yanda aka yi Salima ta faɗa mishi encounter ɗinsu. Hannunta har karkarwa yake yi ta ɗauki doguwar riga ta saka sannan ta yafa gyale ta fita zuwa ɗakin Salima.

30 minutes kafin haka;

Muhammad ne ke zaune a bakin gadon Salima tana haɗa mishi kayanshi yana tayata, sai da suka gama sannan ta zuge zip ɗin jakar ta kai falonta sannan ta dawo ya jawota gefenshi ta zauna domin a yanzu ta fi shi ƙiba sai dai a ce shi namiji ne ya fita faɗin ƙashi da kuma muscles.

“Yanzu haka zan tafi ban moreki ba? Kwanaki kamar na ji an ce akwai maganin da ake sha yana tsayar da jini ai da kin sha tunda na lokaci ɗaya ne.”

“Ni ban ma taɓa jin akwai irinshi ba, amma kuma na baka dama ka je gurinta ka ƙi ai.”

“Akwai dalilai na, ciki kuwa har da cewa bana son a fara yin hakan saboda wasu dalilai again wanda matsalar daga ku ne mata.”

“Umm dama ina son maka wata magana.”

“Na me fa?” Ya tambaya hankalinshi na kanta.

“Ni da ƴar’uwar tawa ce, da gaske ne mun samu matsala shi yasa ka ganmu haka. Kayi haƙuri na maka ƙarya bana son daga dawowarka ne in faɗa maka abun da zai ɓata maka mood. Kuma nayi niyyar yin haƙuri amma wannan karon na kasa domin kalmar da ta jefeni da ita shi yake damuna.” Nan idanunta ya ciko da hawaye amma bata bari sun sauƙa ba.

“Me ya haɗaku?” Ya tambayeta wanda har muryarshi ta canja babu wasa a ciki.

“Dama ka sani tun tafiyarka na farko Juwairiyya ta canja mini wanda a da ba haka muke ba, a da muna zama mu yi hira har mu faɗawa juna damuwarmu mu magance. Amma ban sani ba ko zugata aka fara yi ta fara baya-baya da ni, ƙarshe har take ce mini wai kowa yayi harkan gabanshi kar in sake shiga tsabgarta, in ka tuna har ka aiko Yaya Abdallah ya zo ya mana faɗa. To wallahi tun lokacin har yau da nake maka magana bamu koma kamar da ba, ta nesanta kanta da ni, haka kuma idan na je gurinta bata yarda mu yi hira. A yanda na lura kamar kishi take yi da ni duk da cewa ni ce ya kamata in yi kishi da ita tunda a da ƙawata ce amma ta zo ta aure mini miji.”

“Me ya haɗaku shi na tambayeki ba wannan abun da ya wuce ɗin ba.” Ya dakatar da ita zuciyarshi na mishi ƙuna don baya son ya ji suna samun saɓani tsakaninsu alhali baya ma ƙasar.

“Ka yi haƙuri. Yau ta dawo daga school na mata murnar gamawa shine nake tsokanarta nake cewa yanzu kam mun kusa mu yi bankwana tunda kin ce da kin gama makaranta zaki rabu da mijina, wallahi wasa nake mata amma ita sai ta ɗauka da gaske ne ta fara zagina tana cewa ai an faɗa mata duk abubuwan da nake yi a bayan idanunta wanda ni ban ma san me take magana a kai ba. A nan ne ta buɗi baki ta kirani da munafuka! Wai ni ce munafuka Baban Hafiz! Wannan kalma ta mini zafi saboda munafuki cewa aka yi wutarshi daban take ko a lahira. Na so in haƙura amma na ga ba zan iya ba, duk abubuwan da take mini zan yi haƙuri amma gaskiya banda jifana da mummunan kalma irin wannan.” Da haka ruwan hawayen suka gangaro kan fuskarta ta share wasu ma suka zubo.

“Na san a yanzu ka fi sonta a kan ni, amma don Allah zan roƙeka ka duba darajar ɗan da ke tsakaninmu ka mata magana ta daina kirana da wannan sunan wallahi bana so. Idan wasan ne bata so ba zan sake ba, kuma a da mun saba ne shi yasa ni har yanzu da nake mata kallon ƙawata na faɗa mata, amma na daina daga yau.” Nan ma wasu hawayen suka ƙara zubowa ta fashe da kuka tana mai rufe fuskarta sai ɓari take yi.

Muhammad da ya gama jinta sai yayi jimm yana tunani na wasu mintuna sai kuma ya ɗauki waya ya kira Juwairiyya.

“Ki zo ina nemanki.” Ya faɗa ta cikin wayar ba tare da ya amsa sallamar da take mishi ba.

Yana kashe wayar ya tashi ya fice falo Salima ta biyoshi ta zauna a ƙasa tana sunkuye da kai tana hawaye. A haka Juwairiyya ta zo ta samesu ta samu kan kujera ta zauna don ba zata iya zaman ƙasa ba don yana mijinta, mutumin da gado ma tare suke kwana a kai.

Mum Fateey 👌

Juwairiyya ta muskuta kaɗan kamar wata mara gaskiya sannan ta kalli Salima wacce ke zaune a ƙasa tana share hawayen ƙarya da wofi, da haka kuma ta ɗaga idanunta suka sauƙa kan Muhammad wanda ya turnuƙe fuska kamar bai taɓa dariya ba. Muƙut ta haɗiye yawu mai kauri kana ta buɗe bakinta ta fara magana muryarta na rawa kaɗan.

“Magana ta faɗa mini wanda bai mini daɗi ba, kuma dama ta saba mini irin wannan shine na faɗa mata kalmar da sai daga baya nima na ga bai dace ba.”

“Me ya faru na tambayeki amma kina mini magana in codes. Ta yaya zan gane me kike nufi har in muku shari’a?” Ya tambayeta yana mai ƙara haɗe fuska kamar ba da shi take wasa da dariya ba.

“Na dawo daga school na shigo ɗakinta shine tace mini wai sun kusa mini bankwana, na tambayeta na menene, tace ai na ce idan na gama school zan bar mata mijinta. Sai nace tana son tsokana, amma ta ƙara cewa ai ni na ɗauki alƙawarin da bakina don haka sai in cika tana son in bar mata mijinta tunda burina ya cika. To a nan ne nake tambayarta ko lafiyarta kalau ko dai ta gama  munafurcin nata ta ga bai ɓulle ba shine zata biyo ta wannan hanyar? Shine tace wai ita ce mai munafurci? Nace mata ina sane da duk aibatani da take yi a cikin danginka shine ta ƙara tambayata wai ita ce munafuka? Na ce mata na faɗa ita munafuka ce. Shikenan.”

Nan falo yayi shiru Muhammad na bin ta da kallo yayin da ita kuma Juwairiyya zuciyarta ta bushe babu alamun ko hawaye a idanunta, ita kuma makirar tana gefe ta Ƙara sadda kanta ƙasa sai share hawayen fuskarta take yi.

“Maganan da ta miki ke baki san a cikin wasa ta miki bane?” Shine abun da Muhammad ya fara tambayar Juwairiyya yana cigaba da tsareta da ido.

“In ta faɗa maka cikin wasa tayi mini maganar wallahi ƙarya ne, with a serious face ta faɗa kuma har cikin ranta she mean it.” Juwairiyya ta amsa tana mai jin takaici domin sai yanzu ta gane salon da Salima tayi amfani dashi.

“Shin kin faɗi akan zaki rabu da mijin nata idan kin gama makaranta? Don yau sau biyu ko sau uku kenan ina jin wannan maganar.”

“Na faɗa.” Ta amsa kai tsaye.

“Tambaya na gaba kuma shine munafurcin me ta miki da har kike jefeta da kalmar?”

“Kayi haƙuri da duk abun da zai fito daga bakina amma da gaske ne Salima ta munafurceni. Wallahi a ƴar’uwa na ɗauketa amma tunda na shigo gidan nan ta fara shiga cikin danginku tana lankwasa maganan da nayi da ita ko kuma ta je tayi ta faɗa musu nayi kaza da kaza. Ni duk ina gefe ban sani ba ashe da yawansu haushina suke ji suna mini kallon ganga babu rufi. Farko washe garin tarewana su Shema’u sun zo tace musu muna ciki ba zamu buɗe ba, daga baya da ta je gidan sunan Ahmad ɗin Aunty Iyami sai tace musu ai nace gulma ne ya kawo su, tabbas na faɗi hakan amma wallahi ba dasu nake yi ba. Sai kuma ta ƙara zuwa tana faɗa musu wai na fi ƙarfinka ina maka tsawa wai kana tsoron mini magana, wai kuma ina faɗa da makwabta da mai aikinmu, duk wani abu da ya faru da ni sai ta je ta faɗa musu su kuma suna jin haushina. Daga baya na gane ita take fara ɗauko magana sai ta barni in yi ta surutu ita kuma ta kai gaba, ni kuma a inda muka yi magana  a gurin nake ajiyeta bana kaita ko’ina.” Tana faɗin haka tayi shiru zuciyarta na suya amma ita kanta ta sani furucin da tayi bai yiwa halin da ta shiga adalci ba.

Sannan iya na mutane kawai ta faɗa mishi, bai san irin makircin da tayi ta mata na tunzurata da take yi tana mishi rashin kunya da jin haushinshi ba. Ga kuma ƙaryar da take yi akan halinshi wanda hatta mazantakanshi sai da ta muzanta tace bashi da ƙarfin sha’awa alhali shi jarumi ne ko a cikin maza. Amma ba zata faɗe su saboda laifinta ne da ta ɗauki maganar ta yarda dashi, laifinta ne da ta yarda da duk maganganun da ke fita daga bakinta kuma take tausaya mata tana cewa ana oppressing ɗinta, ita zai yi kallon mara wayo kuma wawuya.

“Last question. Wanene yake faɗa miki ta je cikin dangin nawa tana aibataki ko kuma tana kai maganarki?”

Shiru tayi don ba zata taɓa kiran sunan Hafsat ko Iyami ba, domin in ta kira Hafsat ba zai ji daɗi tana shiga harkan cikin gidanshi ba a matsayinta na bare, in kuma Iyami ta kira zata haɗasu faɗa wataƙila ya iya zuwa gidanta ya mata kaca kaca ko kuma ya kirata ya ja mata kunne. To me amfanin hakan? Mutane biyun da suka fito da ita daga cikin duhu su zata kwayewa baya ta haɗasu faɗa da mijinta? Kai ba zata iya ba! Hakan yasa ta buɗi baki tace,

“Kayi haƙuri amma gaskiya ba zan faɗi waye ba.”

“Juwairiyya.” Muhammad ya kira sunanta bayan an ɗauki lokaci mai tsawo.

“Na’am.” Ta amsa tana mai ɗago kanta tana kallonshi don tun ɗazu itama da sadda kanta ƙasa.

“Tun da nake da Salima har yau da muke zaune ban taɓa jin tayi faɗa da wani ba, kaff danginta da nawa ban taɓa jin an ce ga abokin faɗanta ba sai yau, kuma ke. Na san halin matata, na san abun da zata yi da wanda ba zata yi ba ciki kuwa har da munafurci. Da dai kin ce tana hiranki da su zan yarda saboda kema kina yi da wasu wanda gashi yanzu kin kasa faɗin sunayensu, kin ga kenan duk halinku ɗaya. Kalmar munafuka da kika kirata dashi hatta ni na ji zafinshi saboda ni nasan matata ba munafuka ba ce, kuma da wani ne ya faɗi haka a waje wallahi Juwairiyya sai nayi hukunci dashi. Kin yi kuskure babba, kuma dama ke bakinki ne takobinki sam baki iya wielding ɗinshi ba. Zan mata faɗa ta daina maganarki da su tunda bakya so, kema kuma ki daina maganarta da mutanen naki da baza ki faɗi sunansu ba, sannan a ƙarshe ina so ki bata haƙuri, tare da alƙawarin ba zaki sake jefenta da kalma mummuna irin wannan ba. Salima mutumiyar kirki ce, tana kuma sonki wanda tun da nake da ita har yau bata taɓa nuna mini tana ƙinki ba da har zata so ki bar gidan nan ba.”

“Saboda hakan ma yana ɗaya daga cikin munafurcin nata ne shiyasa ba zaka gani ba. Shin ka saurari duk abun da na faɗa maka kuwa? Zuwa take yi tana twisting maganata tana kai hirana wanda yake sa mutane suna jin haushina suna zagina.” Juwairiyya tayi saurin taran numfashinshi dalilin zuciyarta da take ta tafarfasa tun da ya fara magana kamar ya fi jin zafin abun da ta yiwa Salima akan abunda ita ta mata.

“Na ji, shine na ce miki zan mata faɗa zata daina kema ki daina. Ki bata haƙuri.” Ya ƙarisa maganan yana ƙara haɗe ranshi.

Shiru Juwairiyya tayi tana taune fatar bakinta wanda sai da yayi jini kaɗan tana jin taste ɗin metallic a kan harshenta. Me yasa ita ya mata faɗa a gaban Saliman amma ita Saliman bai mata faɗa a gabanta ba? Me yasa kuma ya yabi halayenta har yana cewa bata da abokin faɗa sai ita? Kenan ita ce mai masifa ita ce mai neman magana? Ko dai bai yarda da maganar da ta faɗa bane?

“Ina sauraronki, we don’t have all day.” Ya ƙara nanata mata da alama yanzu kam patience ɗinshi ya ƙare saura kaɗan.

Wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka, zuciyarta suya take yi har tana jin kamar in aka gwada jininta yanzu za’a samu ya hau can ƙololuwa saboda tsabar ɓacin ran da take ciki.

“Ka yi haƙuri ka barta in ba zata bada haƙurin ba ni dama tuntuni na haƙura. Kalmar ce dai kawai nake roƙon kar ta sake faɗa mini.” Salima ta tsoma musu baki cikin shaƙewar murya irin wacce mutum ya sha kuka ya gaji, har lokacin kuwa bata ɗago kanta ba haka kuma bata daina sharar hawaye ba.

“Dolenta sai ta bada haƙurin in zamana take yi a gidan nan.” Wannan karon Muhammad yayi maganar cikin tsawa yana aikawa Juwairiyya wani irin mugun kallo.

“Ka ga irin munafurcin ko? Ka ga irin yanda take manipulating ɗin ka kana ganinta kamar mutumiyar arziki? Wallahi Salima ke munafuka ce, Allah Ya isa tsakanina da ke kuma sai Allah Ya mini sakayya da irin abubuwan da kike mini.”

“Idan na sake maimaita umurnin da na baki wallahi daga ni har ke sai mun yi dana sanin abun da zai fito daga bakina next. Apologize, now!”

“Kiyi haƙuri.” Ta bada haƙurin da aka ce ta bayar amma a nan ne ta ji zuciyarta ta karye domin ta gane yayi wannan maganan ne don ya tsoritata kuma ta tsorita ta bada haƙurin alhali ita ce ake zalunta.

Hawaye masu zafi suka gangaro kan ƙuncinta da ta ga murmushin da Salima tayi ta gefen bakinta wanda hakan ya ƙara tunzurata ta miƙe zata fice Muhammad ya dakatar da ita.

“Ina zaki je?”

“Ɗakina.” Ta bashi amsa tana ƙara cizon bakinta hawaye na malala kan kumatunta.

“Juwairiyya bana son wannan rainin naki, nace miki na gama da ke ne? Ki zauna.”

Zama tayi zuciyarta na cigaba da ƙuna wanda a yanzu har ji take yi kamar zata iya shiɗewa tsabar ɓacin rai da kuma tausayin kanta, tabbas yanzu ta gama yarda zaman gidan Muhammad zai yi matuƙar bata wahala domin ya yarda da munafukar matarshi ta yanda duk abun da aka faɗa ba zai yarda cewa ta aikata ba, ganinta yake yi a matsayin mace mai shiru-shiru da kawaici kuma mara son fitina. To ita kuma wace shaida ya mata? Mai rashin kunya? Mai masifa? Mai neman magana da faɗa ko kuma mai dogon baki da bata iya controlling ɗin shi ba?

“Da farko zan fara da muku nasiha ku ji tsoron Allah a zamanku, ku saka a ranku da ni da ku duk zaman ibada muke yi saboda sunnar Ma’aiki ce SAW, a wannan zama kuwa duk wanda ya cuci ɗan’uwanshi Allah ba zai barshi ba sai ya saka mishi.”

Kuka ne ya kwacewa Juwairiyya tayi saurin toshe bakinta tare da jan gyalenta ta rufe fuskarta domin maganar da yayi ta ƙarshe da ita yake yi ba kowa ba. Shi a gurinshi ita ke cutar matarshi amma bai san cewa matarshi ce mai cutarta ba kuma sai Allah Ya saka mata kamar yanda ya faɗa.

“Dama an ce ‘zo mu zauna zo mu saɓa’ hakan yasa dole ne a TAFIYAR MU wani ya ɓatawa ɗaya rai, to amma hakan ba zai zama hujja ko dalilin da zai sa ɗaya yana cakalar ɗaya da faɗa ba ko kuma ya faɗawa ɗaya magana mara daɗi ko mai muni ba, mu guji ɓacin ran junanmu, mu guji yiwa juna abun da mu ba zamu so a mana ba.”

Wannan nasihar ba ita da Salima yake yiwa ba, ta sani ta kuma ajiye a ranta tuntuni ita yake yiwa faɗa ba kowa ba.

“A rayuwa kuma idan zaku biyewa gulmar mutane zasu kai ku su baroku, domin wani zaman lafiya ne kawai ba ya son ya ga ana yi, don haka sai ya san yanda zai yi ya haɗaku a samu matsala tsakaninku. A daa ku ƙawaye ne wanda har bayan na aureki ke Juwairiyya baku fasa ƙawancenku ba, to me yasa tun shekarun baya baku taɓa samun matsala ba sai yanzu? Saboda an ganku guri ɗaya kuma kanku a haɗe shine za’a so a gwara muku kai ku fara kishi da juna kuna tayar mini da hankali. Ba zan so haka ba kuma bana fatan a sake samun matsala irin haka.”

Nan ya dubi Salima ya sassauto da muryarshi ganin hawayen da ke ɗiga kan cinyarta ya ci gaba da magana,

“Ke Salima na sanki da sanyin hali amma kema watarana kina da surutu, maganan da kike yi da wasu a kanta daga yau na sokeshi na hana. Ke ce babba don haka ki riƙe girmanki sai ita kuma ta baki respect that you deserve. Ke kuma Juwairiyya na sha faɗa miki bakinki yana da kaifi, kina kuma da surutu da saurin fushi, shawarar da zan baki shine ki iya bakinki sai kuma zan umurceki da kar ki ƙara kiran ƴar’uwar taki da kalmomi marasa daɗi irin haka, na hanaki kema daga yau. Sannan a ƙarshe ina son in roƙeku da ku haɗa kanku ku zauna lafiya kamar daa, hakan shi zai sa hankalina ya kwanta, ku ma zaku fi jin daɗin zaman ku fiye da in kuna hantarar juna. Allah Ya ƙara mana zaman lafiya Ya kuma ƙara mana haƙurin zaman da juna.”

“Ameen, ke ma kiyi haƙuri da wasan da na miki, in sha Allah ba zan sake ba.” Salima ta ce ga Juwairiyya bayan ta ɗago kanta.

Wannan karon Juwairiyya ji tayi kamar numfashinta zai ɗauke, hakan yasa ta ji kamar ta tashi ta tafi amma sai ta kasa ta bar Muhammad na magana wanda shi a gurinshi wai yana so ne ya sakasu su yi hira amma abun ya ci tura, domin ita Salima uffan bata ce ba kanta na ƙasa, ita kuma Juwairiyya hawaye kawai take ɗigarwa ta kuma rufe fuskarta babu mai ganinta. Ganin abun ba zai yiwu ba yasa Muhammad ya karaya kana ya dubi Juwairiyya wacce har lokacin ta ƙi haɗa ido da shi ya ce,

“Shikenan, ki je. Ga bag ɗina kan kujera ki tafi dashi.”

Babu musu ta tashi ta ɗauki jakar yana kallonta amma ta ƙi yarda ta kalli ko inda yake balle su haɗa ido, binta yayi da ido har ta fita riƙe da jakar kana ya dawo da dubanshi kan Salima ya tamke fuska ya ce,

“Me yasa kike kai maganarta cikin ƴan’uwana Salima? Don me yasa ke ba zaki iya bakinki ba? An sha faɗa mini kina da faɗi ba’a tambayeki ba amma ban taɓa yarda ba saboda na sanki, sai dai gaskiya yanzu kin fara saka mini kokonto a raina. Idan ma kina yi ki daina. Kuma da ban san halinki ba da sai in ce da gangan kika nemi faɗa da ita kika kawo mata wannan zancen, amma ban sani ba ko don kishi ne da kika fara yi da ita yanzu. Tun a da baki yi kishi ba kar ki bari mutane su fara zugaki yanzu ki canja halinki da na sanki da shi. Ki riƙe girmanki don ta hakan ne kaɗai nima zan kareki miki shi, amma muddin kika kasa to gaskiya kiyi kuka da kanki don ba zan bi bayan ƙarya ba. Na san Juwairiyya bata da faɗa haka kurum sai an taɓota, don haka kema ki kiyayeta ku zauna lafiya. Ɗauko mini wayata a ɗaki.”

Sum sum ta tashi ta wuce ɗaki ta ɗauko mishi ta kawo mishi ya karɓa kana ya tashi ya fice ba tare da ya ƙara ce mata komai ba. Yana fita ta canja fuskarta daga abun tausayi zuwa ɓacin rai, ba haka ta so ba, ta so ne Juwairiyya ta tafasa fa ƙone ta mishi rashin kunya ya saketa a nan gabanta amma da alama ta fara sanyi duk da ma cewa da sauran turjiya da taurin kanta. Kwafa tayi zuciyarta na suya tana tunanin me kuma zata yi da zata haɗasu faɗa har su rabu tunda wannan bai yi aiki ba!

Muhammad yana shiga falon Juwairiyya ya samu bata nan, kai tsaye ya shige can cikin ɗakinta ya samu jakarshi a kan bedside table sannan ga kayan da ta saka ɗazu ta cire ta shiga wanka. Murmushi yayi yana jin wani irin shauƙi a ranshi kana ya tasamma hanyar banɗaki sai dai kafin ya isa ta fito ɗaure da towel ta zo ta wuceshi ta isa bakin wardrobe ta fara neman kayan da zata saka.

Bin ta yayi domin shi kanshi ya san ranta a ɓace yake amma laifi tayi aka mata faɗa. Tana ƙoƙarin zaro kayanta ta ji ya iso bayanta ya rungumeta tare da sauƙe wani nannauyan ajiyar zuciya kana ya zare towel ɗin nata jefar a ƙasa ya fara yamutsata. Sai dai duk abun nan da yake yi Juwairiyya bata ko motsa ba haka kuma bata nuna mishi abun da yake yi yana affecting ɗinta ba, ƙarshe ma hawaye take yi da ta tuna maganar da suka taɓa yi kwanaki na cewa baya son haihuwa da ita, yanzu kam ta gane jikinta kawai yake so don shi yasa ko a ranar da aka kawota duk da rashin shirinsu ya nemi biyan buƙatarshi har sai da ta gujeshi. Gashi yanzu kuma ya nuna mata ƙiri-ƙiri matarshi ta fita daraja, gaskiya da kuma kyan hali. Wato a kowanne fanni ta fita ita kuma kashe mishi kishin ruwanshi ne ta fi ta? Da gaske kenan ya ɗauketa ne a matsayin Sex object!

Juyo da ita yayi gabanshi da niyyar haɗe bakinsu guri guda ya ga hawayen da ke malala a fuskarta ya dakata da abun da yake yi ya fara magana muryarshi a shaƙe dalilin halin da yake ciki na tsananin buƙata.

“Jay menene? Me ya sameki kike kuka?”

Shiru tayi bata amsa ba illa hannunta da tasa ta kare ƙirjinta tana mai sunkuyar da kanta ƙasa. She feel exposed a gaban mutumin da kwata kwata bai ɗauketa a matsayin abar sonshi ba.

“Na tambayeki kin yi shiru, menene ya faru?” Ya sake nanata mata tambayar yana mai sauƙe hannayen nata ya riƙesu cikin nashi.

Wannan karon ma shirun ta sake yi kana ta zare hannunta ɗaya ta share hawayen fuskarta duka kana ta kalli gefe tana mai cije laɓɓanta. Kamar maye haka ya bi lips ɗin nata da kallo yana tuna taushinsu a kan nashi da kuma wani ɓangare na jikinshi da take gigitashi da su.

“Saboda na miki faɗa akan laifin da kika yi shine kike kuka, kuma kika ƙi nuna mini farin cikinki na ganina Juwairiyya?”

Wani shirun ne ya sake biyo baya hakan yasa ya sake mata hannu ya ja da baya kaɗan ya ce,

“Idan faɗan da na miki ne yasa kike haka to ki ci gaba, kuma ko gobe kika yi laifi zan nuna miki kuskurenki saboda ni ne sama da ke kuma dukkanku amana kuke a hannuna ba zan bari ɗaya ta cuci ɗaya in kasa hukuntata ba. Kuma ki mini magana bana son shirun nan.”

“Kai kace bakina yana da kaifi shi yasa na rufe don ba lallai ne ka ji daɗin abun da zai fito daga ciki ba.” Ta samu kanta da faɗi bayan ta ɗauki towel ɗinta ta rufe jikinta.

“Saboda na taho da buƙatata shine zaki wulaƙantani don na miki faɗa? Da na san abun da zan zo in tarar kenan da ban zo ba, kuma kin bani bani mamaki.” Yana faɗin haka ya shige toilet yayo alwala ya fito Juwairiyya na tsaye a inda ya barta ya fice ko kallonta bai ƙara yi ba.

Itama toilet ɗin ta sake shiga ta ƙara wanka a karo na uku wannan karon har da na tsarki domin abun da ya mata ta haura ƙetare amma shi bai sani ba. Wankanta na biyu kuwa wanke gumi tayi da hawayenta sannan ya taimaka mata wajen jin sanyi a jikinta duk da cewa zuciyarta bata samu wannan gatan ba.

Tana idar da sallah tayi kwalliya kaɗan tare da saka kayan da ta adana don tarɓanshi wanda sabon ɗinki tayi riga da siket da ya matuƙar matseta in the right places ya fito mata da shape ɗinta. Tana zaune a falo tana jiran ko zai dawo amma shiru har aka yi isha itama ta je tayi nata sannan ta dawo falo ta samu ya shigo har ya zuba abinci yana ci. Satan kallonshi tayi kaɗan ta ga ya haɗe rai wanda hakan yasa itama ta ji ta ƙara hawa ta samu guri nesa dashi ta zauna.

Haka suka zauna shiru babu mai magana, ƙarshe da ta gaji da zaman ta tashi ta shige ɗakinta ta cire kayanta ta saka na bacci ta kwanta ta fara danna wayarta wanda lokaci lokaci hankalinta na komawa kan mijinta da ta bari a falo tana jin motsinshi yana God knows what.

Har ƙarfe goma ta gota bai shigo ba ita kuma tuni ta fara gyangyaɗi, adana wayar tayi kan bedside kana ta gyara kwanciyarta bacci yayi awon gaba da ita. Sai dai yana shigowa ƙarfe sha ɗaya ta farka amma bata bari ya gane ba. Tana ji ya shiga wanka ya fito ya zo ya kwanta ya juya mata baya, da haka kuma ya fara juye-juye kamar ko gadon ne bai mishi daɗi ba amma ita ta san menene. Bata hanashi kanta ba amma batun ta nuna mishi bajintarta kamar yanda take mishi kullum ne wannan karon ba zata iya ba, saboda ciwon da zuciyarta yake mata na haushinshi da take ji.

Tana jin shi ya cigaba da juye-juye har bacci ya ɗaukeshi sannan itama ta samu tayi. Asuba shi ya fara farkawa ya fita masallaci amma bai dawo ba har sai da gari yayi haske, a nan kuma ya zo ya sameta tana aiki a kitchen yayi shigewarshi ya je ya kwanta wani baccin yayi awon gaba dashi. Bai tashi farkawa ba sai ƙarfe goma na safe ya samu ta gama breakfast har ta yi wanka tayi ado.

“Ina kwana?” Ta ce dashi bayan ya yi wanka ya fito falo.

“Lafiya.” Ya amsa a taƙaice yana shan mur.

Yana zama ta sauƙo mishi da abinci wanda bai fi loma uku ta saka mishi ba ya dakatar da ita wai ya isa. Ranta na zafi ta bari don abinci kala biyu ta mishi ta buɗe ɗayan kulan zata saka mishi ya ƙara dakatar da ita.

“Wannan kaɗai ya isa.” Da haka ya karɓi plate ɗin ya fara ci.

Komawa tayi gefe ta zauna don ta lura horata yake yi saboda ya sani she loves to cook kuma tana son a ci abincinta. Yana gamawa ya tashi ya fice yana cewa,

“Na fita cikin gari.”

Da haka tayi shiru tana sauraronshi ya shiga ɗakin Salima amma ya kai awa ɗaya a ciki bai fito ba har ta fara tunanin ta je ta ga me suke yi amma ta hana zuciyarta. Ai kuwa ta sake hawa wannan karon ma sai da ta zubar da hawaye tsabar takaici domin bayan rashin gaskiya da ya bata har da ƙarin cin amana zai mata?

Tana zaune ta ji ya fito ta leƙa ta hangoshi yana riƙe da hannun Salima wacce ta bata baya, buɗe mata mota yayi ta shiga abun da bai taɓa mata ba kana ya buɗe musu gate suka fita daga gidan. Rai na suya ta sauƙe labulen ta cire kallabin kanta kana tayi locking ƙofar falon ta shige can cikin ɗakinta ta kwanta. Kenan cin amanan bai tsaya a nan ba sai sun fita waje an je an yi a can?

Sai bayan maghrib suka dawo a lokacin Juwairiyya ta gama cika fam, domin abincin rana da ta mishi haka ta juyewa almajirai kana ta ɗaura na dare wanda tuwo ne kaɗai tayi sai kuma ta ɗumama miyar wake da peppered offal.

“Sannu da dawowa.” Tace dashi ba tare da ta kalleshi ba.

“Yauwa.” Ya amsa yana mai zuba mata ido sai kuma ya wuce ya shige ɗaki yayi wanka ya fito.

Wannan karon ta saka mishi abinci mai yawa ya ci har yace ta ƙara mishi ferfesun, tana gama tattare gurin ta koma ɗaki ta cire kayanta ta kwanta. Can tana kwance ta ji ya fita daga falon amma har aka shafe minti arba’in bai shigo ba, hakan yasa ta ji hawaye na kwaranya a fuskarta, wato tunda ba zai samu nitsuwan a gurinta ba shine ya tafi gurin matarshi? Saurin goge hawayenta tayi kana ta gyara kwanciyarta da ta ji ya shigo falon ya rufe.

Da haka ya kashe su wutan falon da kayan kallo sannan ya tasamma cikin ɗakin. Bayan ya kwanta ya kira sunanta ta ƙi amsawa tayi kamar tana bacci.

“Juwairiyya.” Ya sake kira a karo na uku.

“Na’am.”

“Guduna zaki yi?”

Tayi shiru tana cije leɓenta.

“Bana son shirun nan. Yanzu na zo don in ganku in rage kaɗaici shine zaki fita daga harkata ki ƙi kulani?”

“A’a.” Ta amsa ba tare da ta faɗi dubbannin maganganun da ke bakinta ba. Tana son yin magana amma tana tsoro domin kowa cewa yake yi bakinta yana gudu, kenan dai gaskiya ake faɗa mata.

“To menene na hanani kanki da kike yi?” Ya sake tambayeta yana mai juyowa yana kallon doron bayanta.

“Ni ban hanaka ba.” Ta bashi amsa iyakacin gaskiyarta.

Shiru yayi da alama shima ya gane bata hanashi ba shi yayi zuciya don kanshi ya ƙi nemanta. A hankali ta ji ya motsa ya jawota jikinshi sai dai bata ko ɗaga hannunta ba balle ta tayashi har ya rabata da kayan jikinta. A nan ne kuma ta shaƙi ƙamshin turaren Salima a wuyanshi, wannan yasa ta ji hawaye ya taru a idanunta sun fara gangara kan pillow.

“Me haka ne? Why ain’t you doing nothing?” Ya tambayeta yana mai dakatawa.

Bata amsa ba, da haka ya dago fuskarshi ya ga hawayen da ke zubowa daga idanunta.

“Idan haka kika zaɓa fine.”

Yana gama maganar ya cigaba daga inda ya tsaya har ya samu nitsuwa da ita, da haka ta tashi jikinta na mata zafi ta shige toilet tayi wanka ta fito. Sai dai tana ƙara kwanciya ya sake maimaitawa wanda wannan karon tsabar haushinshi da Juwairiyya ta take ji sai da tayi kokawa dashi amma da yake ya fi ƙarfinta haka ya ci nasara sannan ya rabu da ita bayan ya gamsu.

“Kukan me kike yi kuma yanzu?” Ya tambayeta yana mai kallon yanda take kuka a hankali.

“Dama na sani ba ni kake so ba jikina kake so. Ka ɗaukeni a matsayin sex object wacce her feelings does not matter. Sai yanzu komai yake dawo mini Muhammad, na gane. Ka ɗauki matarka a matsayin wacce bata laifi kuma ita ce uwar ƴaƴanka mai kawo maka ahalinka duniya amma ni ko sau ɗaya baka taɓa min maganar haihuwar ba, da na kawo maganar haka kayi brushing ɗinshi off saboda ba shi bane a gabanka kuma ba so kake yi ba. Ni kuma kalar nawa jarabawar kenan ko’ina na shiga sai na gamu da ƙalubale. You don’t need to pretend anymore na gane.”

“Haka kike tunani? Ni kuma in ce me da tun aurena da kika yi kin sakawa kanki ranar rabuwa da ni? An faɗa miki bana jin baƙin cikin wannan maganan ne? Kin ɗaukeni a matsayin toy wanda da zarar kin gama wasa da ni zaki jefar ki ƙara gaba. Da ke na yiwa haka zaki ji daɗi ne? To don me yasa zan miki maganan haihuwa? Don me yasa zan fara hango future da matar da ke ƙirga adadin da ya rage mata a cikin gidana? Juwairiyya na aureki ne don Hafiz, na kuma yi haƙuri da rashin hankalinki ne don ina tausayawa rayuwar da zaki yi a gidanku a matsayin bazawara amma da yake kina da son kai sai kika kasa ganin laifinki kina kallon nawa. Na yi tunanin mun wuce wannan babin amma sai na ga da saura, kin yi laifi na miki faɗa shine kike fushi da ni har kika sa na aikata abun da ban taɓa yi na wato forcing kaina a gurin mace. Ban ta taɓa haka ba amma wannan will be the last In shaa Allah. Ki tafi gida.” Yana gama faɗin haka ya miƙe ya bar Juwairiyya zuciyarta na lugude.

“Sakina ka yi?” Ta tambayeshi cikin razana muryarta na rawa.

Bai amsa ba ya shige toilet ya barta a gurin hawaye na gangarowa kan fuskarta. Ko da ya fito bai sameta a ɗakin ba, yana kwanciya ta shigo ta wuce toilet. Sai da yayi bacci sannan ta fara haɗa kayanta wanda kafin ya tashi da asuba ta kira Idrisa ya zo da asuban fari ya ɗauketa sai gidan Mama.

Mum Fateey 👌

Wannan page naki ne ƙawata Twinnie na Hajiya Sa’adatu uwar Anwar da Na’im mata a gidan Alhaji Mustapha. Ina miki Son so ❤️

TAFIYAR MU

“Surayya ki kai mata kayan nata ɗakinku, sai ku yi alwala ku yi sallah. Juwairiyya ke kuma ki biyoni.” Faɗin Mama kenan bayan ƴarta ta shigo musu da asuba cikin gida da akwatuna har uku.

Ɗakin Mama suka shiga can kurya Mama ta zauna a bakin gado ita kuma Juwairiyya ta ja kujerar mirror ta zauna tana kallon Maman nata cikin fargaban yanda zata ɗauki wannan magana na sakinta da aka yi. Ta sani zata wahala a gidan kamar yanda zawarcinta na baya ma bata share ba, ita dai yanzu fatanta Mama ta fahimceta ta gane cewa ba laifinta bane ko zata sassauta mata wasu abubuwan.

“Daga ganinki da asubar farin nan kuma da kaya niƙi-niƙi na san matsala kika samu da mijin naki amma ina fata tare da addu’an ba sakinki yayi ba Juwairiyya. Faɗa mini me ya faru?”

“Kin tuna maganar da muka yi last week da na ce miki na kira Salima munafuka? To Mama tunda ya dawo bata faɗa mishi ba har sai da bari zai dawo ɗakina da yamma ta faɗa mishi wai akan ita wasa take mini amma na zageta. Mama a gabanta ya mini faɗa har yana cewa ina da baki ban iya magana ba, wanda a yanzu wallahi ko ke ce zaki mini shaidan na rage faɗe-faɗe kamar yanda nake a baya Mama. Wannan magana ya ƙona mini rai amma ban ce mishi komai ba yace in bata haƙuri wai kuma zai mata faɗa kar ta sake kai maganata gaba kuma kar ta sake mini wasa tunda bana so. To bayan ya dawo gurina bai samu fuska ba shine yace in dawo gida.”

“You are terrible at narrating stories Juwairiyya. Ki faɗa mini labarin daki-daki daga farko kuma kar ki cire komai ki faɗa mini gaskiya.” Mama tayi maganar a hankali tana mai cigaba da kallonta.

Tiryan-tiryan Juwairiyya ta fara bata labarin bata rage maganar kowa ba haka da nata, abubuwan da ta cire shine na kunya da ba zata iya faɗa ba amma dai Mama ta gane komai.

“Mama kullum idan na mishi laifi sai ya dinga mini barazana da rabuwa da ni, saboda yasan hakan shine weakness ɗina tunda zaman zawarcin ba ya mini daɗi. Wallahi wannan dalilin ne ma yasa yanzu yace in tafi gida ya ɗauka zan tsorita in bashi haƙuri tunda bana son tafiyan.”

“Bayan wannan babu abun da ya faru?”

“Wallahi Mama iyakar gaskiya kenan na faɗa miki ban musu ƙarya ba kuma ban cire duk abun da na yi ba.”

“Laifinki shine ƙin bada haƙurin da kika yi har ta samu ta ƙara tunzurashi. Sannan ba ki iya kissan bane Juwairiyya amma da kin iya lafiya kalau zaki fito daga ɗakin nata sai dai ita ki barta da cikin cizon yatsa. Shi kuma ina mishi kallon mutum mai sanyin hali ashe barazana yake miki akan saki? To ya saurara ya ji in zaman gidan naku zai baki wahala, ki kwanta ki huta, ko tsinke ban yarda ki ɗauka a cikin gidan nan da sunan aiki ba. Ba wai bana sonki bane yasa nake son kiyi auren, son ne ya jawo haka amma ban san haka mazan yanzun suka zama ba basu da kara. Idan gari ya waye zan kira Baffanki in faɗa mishi a nemeshi a ji me yake nufi da cewa ki tafi gida, in sakinki yayi shikenan Allah Ya sa hakan Ya zame miki alkhairi, in kuma ba saki bane ya aiko mana ke to ya jira ya ji ko zamu je roƙanshi ya mayar da ke kamar yanda yake tsammani. Tashi ki je kiyi sallah kar kuma ki bari damuwa ta shigeki don gashi nan yanzu kin yi kyau kin murmure bana son ki canja daga haka. Allah Ya kyauta.”

Zuciya fari kal Juwairiyya ta fito daga ɗakin Mama don bata yi zaton haka daga gareta ba, ta ɗauka zata yi ta mata faɗa ne kan cewa me yasa da yace ta tafi gida bata bashi haƙuri ba tayi zaman aurenta? Amma da alama itama bata ji daɗin barazanar da Muhammad ɗin yake mata ba, dama tsakanin uwa da ɗiyanta sai Allah. Duk yanda uwa ta kai ga hantarar ƴaƴanta to da zarar wani ya taɓa mata su za’a ji kansu. Da wannan tunanin Juwairiyya ta koma ɗakin Surayya tayi alwala tayi sallah, tana gama azhkar kuwa ta bingire a gurin dalilin kwanan da tayi bata yi bacci ba, amma a can ƙasan zuciyarta bata son rabuwa da Muhammad domin kuwa tana sonshi kuma ya shiga zuciyarta yanda ba’a tsammani. Sai dai duk abun da ya faru zata ɗaukeshi a matsayin ƙaddara, ta rabu da Hafiz da Daddy bata mutu ba, shi ma kuwa idan ta rabu dashi ba zata fasa numfashi ba.

Bata tashi ba sai ƙarfe goma na safe, miƙa tayi tana hamma sai ta tuno da abun da ya faru a rayuwarta wanda har gata nan cikin ɗakin ƙanwarta. Nan ta ji zuciyarta ta tsinke, fargaba da zafin ran ya dawo mata sabo dal a zuciyarta. Da wannan tunanin tayi wanka Surayya ta kawo mata breakfast har ɗaki na doya da kwai da kuma sauce ɗin kifi.

“Baku yi ɗumame bane?” Juwairiyya ta tambayeta tana jin ba zata iya cin doya ba don dama ba mutuminta bane kuma jiya shi ta musu ita da Muhammad.

“Akwai wani guntu a fridge sai dai in ɗuma miki.”

“A’a ki bari kawai zan ci wannan ɗin. Nagode.”

“Kunun gyaɗa zaki sha ko tea?”

“Kunun gyaɗa.”

“To gashi can a flask a gefenki, bari in kawo miki sugar da cup.” Surayya tana faɗin haka ta fita sai can gata ta dawo ta ajiyewa Juwairiyya abun da zata buƙata sannan ta fice ta bata guri.

Cikin ƙanƙanin lokaci Juwairiyya ta cinye abincin tare da kunun dalilin tun shekaran jiya rabon da ta ci abinci cikin daɗin rai. Tumbinta ta shafa wanda ya taso tsabar koshin da tayi kana tayi gyatsa. Sai da Mama ta dawo daga aiki Juwairiyya ta je ta gaisheta.

“Ɗazu da safe mijinki ya zo yana tambayar ko kin zo aka faɗa mishi ma kina bacci, shine ya bada key ɗin ɗakinki. Ɗazu ina Office na kira baffanki na kuma tura mishi numbern Muhammad ɗin ya kira wai wayar bata shiga amma dai ya ce zai sake kira daga baya.” Faɗin Mama tana cin abinci da alama itama bata ɗaga hankalinta ba kamar kwanaki da in Juwairiyya ta kaso aurenta sai ta shiga damuwa.

“To.” Juwairiyya ta amsa amma tana son sanin me ya faru bayan nan.

“Gari yana haske ya zo ya buga ƙofar gida na aika Surayya ta je ta duba. A nan yake tambayarta wai kin zo ta ce mishi eh. Wai ina kike tace kina bacci, shine ya ɗauko key ya bata wai ta kai miki kuma a ce miki ya koma.” Mama ta ƙara mata bayani don ta lura tana son ji.

Kwafa Juwairiyya tayi kana tayi hira da Maman wacce a ƙarshe ta nanata mata zancenta na ɗazu da asuba.

“Ki ci ki sha, ki kuma yi bacci kar ki bari damuwa ko kaɗan ya shiga ranki har ki kasa walwala. Idan kina buƙatar wani abu ki mini magana a saya miki, idan yana tunanin bama sonki ne muka bashi aurenki sai ya zo ya ganewa idonshi ba ki tagayyara ba.”

Wannan karon ma da murmushi Juwairiyya ta fito daga ɗakin Mama wacce da alama yanzu ta daina ganin laifin ƴar tata sai na Muhammad da yake yiwa ƴar tata barazana da saki, da alama abun ya sosa mata rai shi yasa take ta nanata mata kar ta saka damuwa a ranta.

Washe gari Mama take faɗa mata wai an kirashi yace shi ba sakinta yayi ba kawai ta je gida ne ta huta sai ya dawo ƙasar zai zo a yi magana. Wannan magana ya ƙonawa Juwairiyya rai wacce a gaban Mama bata nuna ba amma tana zuwa ɗaki ta ɗauki wayarta ta rubuta mishi text ta tura mishi da yake har lokacin yana Nigeria amma suna can Lagos wajen auren abokin nasu, ana gamawa kuma zai tattara ya koma.

‘Ban san dalilinka na faɗa musu cewa baka sakeni ba alhali ka nuna mini zaman auren da kake yi da ni kamar alfarma kake mini. Da ni da kai duk mun sani Tafiyar mu an fara shi ne babu tushe mai ƙarfi, kar ka ɓata mana lokaci ka ja abun da dole ne watarana sai ka furta. Ka aiko mini takardata don ba zan koma gidanka ba.’

Tun da ta tura text ɗin har aka cika sati bai amsa mata ba haka kuma itama bata sake tura mishi wani ba. Tana son shi haka kuma bata son rabuwa da shi amma idan hakan zai faru tana son a yi shi tun yanzu ba wai tayi ta zama da igiyarshi a kanta ba. Salima kuwa ko tunata bata son yi amma ko bata furta ba ta barta da Allah, munafurcinta kuma tana fatan Allah Ya nunawa Muhammad ko da kuwa bata gidan ne ya gane da waye ya ke zama.

Yau watan Juwairiyya ɗaya da komawa gida, babu abun da take yi illah ta ci ta kwanta kuma bata fita ko’ina, tuni ta ƙara murmurewa har da yin haske wannan karon da yake babu school kuma babu damuwar Salima da makircinta. Tsakaninta da Muhammad babu text balle waya, sai dai a ƙarshen wata ta ga ya aiko mata kuɗi ta account ɗinta wanda ta ɗaukeshi a matsayin na kula da kanta sai dai ba shine damuwarta, damuwarta yanzu shine NYSC da zata fara wanda tana son fita registration amma Mama ta ce ta kirashi ta tambayeshi, ƙarshe tana ji tana gani aka rufe portal ɗin registration bata yi ba don ta rantse ba zata sake neman shi ba gudun kar ya ɗauka neman komawa gidanshi take yi. Wannan abu yasa ta ƙara jin haushin Muhammad wanda ya mance da kashinta kamar ba’a yi tsironta ba, a nan ne kuma ta sakawa ranta cewa ta rabu da gidanshi kenan har abada don ita ba zata iya rayuwa da mutumin da ba ya sonta ba.

Watanta biyu da sati ɗaya a gida ta tashi da matsanancin ciwon ciki wanda tun da tayi sallan asuba take mutsu-mutsu har ta kasa daurewa ta aika Surayya ta karɓo mata Magani a gurin Mama. Sai dai a maimakon Mama ta bada magani sai ta taho da kanta don duba me yake damun ɗiyar tata.

“Surayya ta ce mini cikinki na ciwo, na period ne ko Ulcer?”

“Na period ne don dama wata uku kenan ban ganshi ba.” Juwairiyya ta amsa tana muƙurƙusu sai cije leɓe take yi.

Shiru Mama tayi tana lissafi sannan can ta ce,

“Wata uku ko biyu? Yaushe rabonki da mijinki?”

Duk da ciwon da Juwairiyya take ji bai hanata jin kunya ba amma ta buɗe baki ta amsa mata.

“Wannan dawowan da yayi ne wata biyu da sati biyu.”

“Kuma kin ce wata uku kenan rabonki da ganin period ɗinki?”

“Ko uku ko huɗu.” Ta ƙara amsawa.

“To ko dai ciki kike da shi Juwairiyya? Amma ko cikin ne you are not supposed to have period cramps a wannan lokacin, it’s too early in dai ba cikin ne yake neman lalacewa ba.”

Ai tana jin haka ta tashi ta zauna zumbur tana kallon Mamanta da mamaki a fuskarta,

“Mama ciki kuma? Ta yaya?”

“Ta yanda ake yi. Amma bari a fara buɗe shaguna in aika a sayo Pregnancy Test Strip mu gani. For now ba zan baki kowanne magani ba sai na tabbatar, in ya so in abun babba ne mu tafi asibiti. Surayya haɗa mata ruwan lipton mai zafi ki bata ta sha. Allah Ya baki lafiya.”

Da haka Mama ta saka kai ta fita ta bar Surayya na haɗawa Juwairiyya lipton, tana gamawa ta miƙa mata ta ƙarɓa ta shanye, ai kuwa a maimakon ta samu sauƙi sai abu ya ci gaba. Tun tana daurewa har ta dawo hawaye na malala a fuskarta tana dafe da mararta wanda yayi tauri.

Ƙarfe takwas Juwairiyya ta aika Surayya ta kira mata Mama wacce ta leƙota sau ɗaya bayan ta dubata na farkon.

“Ya ya dai Juwairiyya? Ko mu tafi asibitin ne?” Mama ta tambayeta cike da tausayi ganin yanda take shan wahala.

“Mu tafi kawai Mama, wallahi ban taɓa jin ciwo irin wannan ba tun da nake, ji nake yi kamar zan yi nishi sai kuma in ji kamar wani abu zai fito daga jikina.”

“Subhanallahi. Juwairiyya kika ce yaushe rabon da kika ga period ɗinki?” Mama ta sake tambaya tana matsowa kusa da ita tare da ɗaga rigarta sama.

“Wata uku ko huɗu.”

“Ki kwanta kiyi rigingine, bari in dubaki. Surayya yi maza ki kira mana mai napep a waje.”

Juwairiyya na yarfe hannu tana hawaye ta kwanta sannan Mama ta kwaye cikinta ta fara taɓawa tana danna gefe da gefe, can kuma ta saka kanta kan cikin ta saurara kaɗan sai kuma ta ɗaga ta cigaba da dannawa.

“Mama me ya sameki kike hawaye kuma kina murmushi?” Juwairiyya da ta ƙara ruɗewa ta tambayeta tana mai jin tsoro na shigarta.

“Ciki kike da shi Juwairiyya full term kuma haihuwa zaki yi yanzu.”

Wani irin miƙewa tayi da sauri cikin razana amma Mama ta ankara da sauri ta danne ƙirjinta ta mayar da ita kwance

“Wayyo Allah Mama wa zai haihu?”

“Ki yi a hankali kar ki jiwa kanki ciwo ko abun cikinki, tashi a hankali, maza ki saka hijabinki mu tafi asibiti ki haihu a can.”

Ai nan Juwairiyya ta sake ruɗewa sai ta ji kamar ta tsula fitsari ta fashe da kuka tana cewa,

“Wallahi Mama ni ba zan je asibiti ba, wallahi ni ba zan haihu ba. Ni bani da ciki, ciwon mara kawai nake yi.”

Ganin ta ruɗe yasa Mama ta miƙar da ita tsaye ruwan ya biyo ƙafarta, ai kuwa ta sake ruɗewa ta fashe da wani kukan tana cewa,

“Wayyo Mama Bladder na ya fashe.”

“Ba fashewa yayi ba, fayanki ne ya fashe. Zo mu tafi.”

Da haka Mama ta saka mata hijabi tana rarrashinta suka fita tana takawa da kyar har suka shiga napep suka wuce asibiti. Suna isa aka shiga labour room da ita wanda Juwairiyya tana karanta sunan ɗakin ta fara turjewa wai ita ba zata shiga ba, sai da Mama ta mata tsawa sannan ta shiga taitayinta ta fara mata magana.

“Ke bana son shashanci da rashin hankali, ki nitsu ki fara addu’a Allah Ya rabaki da abun da ke jikinki lafiya.”

Ai kuwa Juwairiyya ta nitsu amma zuciyarta bugawa take yi da ta ga Mama na ɗaukan handgloves tana sakawa bayan ta cire gyalenta ta ajiye a gefe.

“Metron sannu da zuwa, Juwairiyya ce zata haihu?” Faɗin wata nurse da ta shigo wacce aka faɗa mata an kawo mai labour.

“Eh sister Maryam. But we are dealing with Cryptic pregnancy ne don ita kanta bata san tana da cikin ba, nima watana biyu tare da ita amma ban ga alamunshi ba. The baby is fully developed sannan ya juya kai, contraction yana zuwa 5 minutes apart. Ina buƙarar ki dubata mu ga CM nawa take.”

“Mama me kuma Cryptic pregnancy?” Juwairiyya ta tambayesu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

“Ciki ne da yake ɓuya ba’a ganinshi ko alamarshi har sai ya girma sosai ko kuma mace ta fara labour wanda shine case ɗinki. Now hips up zan cire miki wandonki.” Sister Maryam ta amsa mata.

Babu musu Juwairiyya ta ɗaga hips ɗin nata sister Maryam ta cire mata tana godewa Allah da Ya sa bata barin abu a jikinta da ta ji kunyar Mama wacce a yanzu she is so business like ta koma Nurse Mama ba Mamanta da ta sani ba.

“Ok, abun da zan miki yanzu zaki iya jin zafinshi amma ki sake jikinki, ba zai ɗauki lokaci ba kin ji Juwairiyya. Ki yi ta addu’a kuma.” Faɗin Sister Maryam tana mai mata kallon tausayi tana murmusawa.

“Mama wani addu’a zan yi kuma wai da gaske haihuwa zan yi?”

“Ki dinga cewa Hasbunallahu wa ni’imal wakil. Kuma haihuwa zaki yi Juwairiyya, Allah Ya baki a lokacin da bakya tsammani, ki gode mishi sai ki roƙeshi Ya rabaku lafiya Ya kuma yiwa abun da kika haifa albarka.”

Sai a lokacin Juwairiyya ta ji murna ya dabaibaye zuciyarta akan ɗazu da take cikin ruɗani da kuma tsoro. Murmushi ne ya suɓuce a bakinta ta fara zubar da hawayen murna duk da irin azaban da take ciki.

“Alhamdulillah, Allah na gode maka, Allah na gode, Allah ka rabamu lafiya ka yiwa abun da zan haifa albarka, Allah Ka sa duk abun da na haifa ya zama sanyin idaniyan iyayenshi da addini gaba ɗaya…. Wash da zafi.” Ta faɗa cikin jin azaban abun da sister Maryam ta mata don gwadata.

“Kiyi haƙuri ki sake jikinki yanzu zan cire, sake mini hannu kin ji? Ki yi haƙuri.” Ta faɗa cikin rarrashi tana kallon yanda Juwairiyyan ta tamke hannunta tana girgiza kai tana hawaye.

“Zan mutu.”

“Ba zaki mutu ba, sake mata hannu, yanzu zata gama ba zaki sake jin zafin ba.” Mama ta dawo ta kanta tana mai ɓanɓare hannun daga jikin na Sister Maryam.

“Mama kar ta mini irin na ɗazu.”

“Ba zata miki ba, oya ki ci gaba da addu’an da nace ki yi.”

“To, to, to Hasbunallahu, Mama ina jin nishi….. ahhhhh… Wayyo Allah na.”

“Then do it Juwairiyya! Do it!”

“Ina kayan haihuwan, ga kan baby ya fara fitowa.”

Awa ɗaya da haka Juwairiyya ce zaune akan gadon hutawa bayan an sha wahala, hannunta riƙe da abun da ta haifa da ke cikin showel mai taushi tana kallo sai murmusawa take yi tana shafa fuskar babyn da yatsarta guda.

“Wannan yarinyar babu abun da ta ɗauko naki, kamar ba kya ɗakin aka yi cikinta.” Faɗin Sumayya da ta kasa haƙuri ta zo da aka bata labarin yayarta ta haihu.

Juwairiyya bata kulata ba taci gaba da kallon ƴar tata tana taɓa hancinta da kuma bakinta wanda ke kama da Babanta, fara ce tass mai yalwataccen gashi a kai wanda shine abun da Juwairiyya take tsammanin shine abun da ta ɗauko nata. Kallonta take yi amma tana jin tausayinta domin ba lallai bane babanta ya so ta ba, dalili kuwa baya son haihuwa da ita. Tana tausayinta tana kuma tausayin kanta sannan tana jin ƙarfi da kuma wani abu da ake kira overprotectiveness akan wannan ƴa tilo mai nauyin 3.0kg.

“Kin yi shiru kin ƙi magana ko dai cikin ne har yanzu yake murɗanki?” Sumayya tambayeta tana mai matsowa kusa da ita

“Yana mini amma ba sosai ba, gurin ɗinkin nan ne dai yake mini zafi.”

“Kwana biyu in kina shiga ruwan zafi kina kuma shan magani zaki warke sumul. To ki bani babyn in riƙe mana sau ɗaya dai na riƙeta Adda Juwai.” Sumayya ta ƙarisa maganan tana dariya.

“Gashi, kiyi hankali bacci take yi kar ta tashi.”

Wannan karon buɗe baki Sumayya tayi ta kwashe da dariya wanda ya jawo mata harara daga gurin Juwairiyya ta fasa bata babyn ta ƙara rungumeta a ƙirjinta tana jijjigata a hankali.

“Jarirai idan suna bacci ko girgizan ƙasa ake yi ba zasu tashi ba sai sun ga dama.”

“Ki rage muryarki Sumayya, zan saɓa miki.”

“Mai jego ya jiki? Sannu fa. Me kike ji a jikinki yanzu?” Sister Maryam ta shigo tana murmusawa tana leƙen baby.

“Cikina ne yake ciwo.”

“Kina jin hajijiya?”

“A’a, sai dai bacci da gajiya.”

“It’s normal. Idan Metron ta dawo daga kasuwa zaku iya tafiya gida sai ki samu kiyi wanka ki ci abinci ki sha magani ki kwanta. Allah Ya raya baby girl, gata kyakkyawa Tubarakallah Masha Allah. Gaskiya na yiwa Ra’ees ɗina kamu.”

Nan suka saka dariya Juwairiyya har ta manta da damuwar da ke nuƙurƙusan ranta, a haka Mama ta dawo daga kasuwa ita da Surayya hannu niƙi-niƙi da kaya sauran kuma suna waje sun bada ajiya. Sai a lokacin sister Maryam ta fita ta basu guri Mama ta ajiye abun hannunta ta dubi Juwairiyya ta har lokacin ke riƙe da ƴarta ta hana kowa ta ce,

“Ohh Juwairiyya baza ki basu su riƙe miki babyn bane?”

Kunya ne ya kamata ta miƙawa Sumayya wacce dama tun ɗazu take jira a bata amma ta hanata.

“Kin kira ubanta kin faɗa mishi ne?”

“A’a Mama.” Ta bata amsa zuciyarta na bugawa da ƙarfin gaske ko ya zai karɓi labarin.

“Ji mini shiririta, tun ɗazu me kike jira da baza ki kira ki faɗa mishi ba?”

“Zan kirashi yanzu.”

“To kiyi sauri, bari in nema mana motan da zamu koma gida, kai yanzu kam na ga amfanin mota da ake ta bina in saya na ƙi.” Faɗin Mama tana ficewa tare da Surayya a bayanta.

Juwairiyya ta jawo wayarta da ke gefenta ta nemi numbern Muhammad na Uk wanda tsabar sun daɗe basu yi waya ba cikin contacts ta shiga ta ɗauko amma aka ce mata wayar is switch off. Ajiyar zuciya ta sauƙe domin har ta ƙara wayar a kunnenta bata gama deciding me zata ce mishi ba. A nan ta nemi numbern Iyami ta kira wacce tun a ringing na farko ta ɗauka tana cewa,

“Matar Ya Muhammadu.”

“Aunty Iyami an tashi lafiya ya yara?”

“Lafiya kalau, ya gida ya su Mama?”

“Lafiyansu kalau. Umm nace saƙo nake son in baki ki faɗa mishi please.”

“Hmm, me zai hana shi ki kirashi?”

“Na kira ba ya shiga.”

“Gashi nan kuma yana waya, shi yasa ya ƙi shigan.”

“Ya dawo ne?” Juwairiyya ta tambayeta cike da tsantsar mamaki.

“Ya dawo jiya da dare, yau kuma muke taron tayashi gama makaranta. Yauwa gashi nan ya gama wayar. Ya Muhammadu ana maka magana a waya.”

“Hello.” Ta ji sautin muryarshi wanda tayi kewa sosai ba kaɗan ba.

“Hellooo.” Ya sake nanatawa da ya ji ba’a yi magana ba.

A nan kuma ta ji hawaye ya taru a idanunta sun fara gangara kan ƙuncinta.

“Iyami ba’a magana fa, waye ne?”

“Na haihu ɗazu da hantsi, ka zo ka karɓi ƴarka sannan ka taho mini da takaddata aure zan yi.”

“Juwai…” Bai kai ga ƙarisa maganan ba ta kashe wayar tana mai rufe fuskarta hawaye na gangarowa kan kumatunta.

Minti biyu da haka Mama ta shigo tana waya bakinta a washe kamar wacce aka yiwa albishir da babban kyauta.

“Alhamdulillah…babu wata matsala……duk lafiya suke……Eh, muna asibitin da nake aiki…….to shikenan sai ka zo……Amin Amin babu komai. Ai yiwa kai ne……..To madallah sai ka zo.”

Da haka ta kashe wayar ta dubi Juwairiyya tace,

“Mijinki ne ya kira wai yana zuwa yanzu zai zo ya mayar da ke gida, ashe bashi da kunya wai har tambayata yake yi ƴar da waye take kama.” Mama ta saka dariya da alama tana cikin farinciki bata da damuwar komai.

“Mama ni fa ba zan koma gidanshi ba.” Juwairiyya tayi maganar tana jin haushi a ranta ganin kamar Mama ta manta rashin mutuncin da ya musu.

“To. Idan ya zo sai ki faɗa mishi. Alhamdulillah, Allah na gode maka da baiwarka a gareni.”

Mum Fateey 👌

Kamar yanda kuka sani Tafiyar Mu ba littafi ne da zaki karanta ki ji daɗinshi ki wuce bane, no, littafi ne mai ɗauke da darussan rayuwa wanda wani kin sani wani baki sani ba saboda shi ilimi kogi ne. Ku biya ku shigo group a dama da ku inda zaku samu wasu ƙarin hasken kan rayuwar aure da Mum Fateey ke bawa matan aure kaɗai. A dari biyar zaki samu ilimin zamantakewa da yake daukan mata shekaru da yawa kafin su gane. (Nima ina da masu ƙara mini hasken 😌.)

Muhammad ne ke zaune a cikin jirgi zai koma UK wanda sa’i da lokaci yana jin ina ma da ya aikata wani abu kafin ya bar Gombe, me yasa bai nemi ganin Juwairiyya ya mata sallama ba? Me yasa bai damu ƙanwarta Surayya ta je ta tasheta ya ganta one last time ba? Sai dai duk yanda ya kai ga son mata bankwana ta wani gurin kuma yana ganin hakan shine daidai domin kuwa daga shi har ita suna buƙatar space saboda ransu a ɓace yake, zasu iya aikata ko faɗawa juna abun da zasu zo suna regretting daga baya.

Tunawa yayi tun wancan dawowan nashi na biyu da ya ganta cikin ado da kwalliya sai da ya kasa numfashi na wasu seconds, a take kuma ya ji kishi ya shigeshi da ya tuna wai da wannan kyan fuska da kuma kyan surar take fita school tare da unguwa babu shi. Sai dai ya yarda da ita, bayan yardan kuwa ya kafa mata dokan fita school da Hijab duk da ma cewa ya lura ita saka gyalen bai dame ta ba. Kwana ɗayan da yayi a gurinta sai da ya tabbatar ya rage mishi kishin da ya kwaso na shekara ɗaya a jikinta da ya zame mishi kamar iskan numfashi, bai taɓa zaton mutum yana zama addicted da jikin mace ba sai a kanta, tana ƙoƙari sosai wajen ɗaukan nauyinshi domin a kowanne lokaci ya nemeta, ko wanne lokaci bata gudunshi sannan tana da juriya, wanda har ya fara zaton ko a cikin kalmar ‘JURIYA’ Marigayi Hafiz ya zaƙulo sunan da yake kiranta da shi wato ‘RIYA’ duk da ma cewa akwai kalmar a cikin sunanta.

Yayi kwanakin da ya ɗauka ya koma cike da kewarsu, a nan kuma Juwairiyya ta ƙara canjawa daga mai mishi rasar kunya da fitsara ta dawo mai sonshi, ta zama mai mishi biyayya da bin umurninshi sannan ta zama mai ɗebi mishi kewa da sakashi nishaɗi da irin kalolin dirty texts messages da take mishi wanda ke sakashi shafe awanni da ita suna chatting ba tare da ya gaji ba.

Shi yasa da ya samu opportunity na ganinta ya karɓa duk da cewa yana tsaka da kammala thesis ɗinshi, amma da ya duba ya ga ba zai matsu sosai ba saboda sati ɗaya kawai zasu yi su dawo ya bar komai ya zo. A Abuja suka sauƙa ya bar sauran abokan nashi shi ya gudu Gombe, yana isa ya ga bata zo tarɓanshi ba haka kuma ko da ya isa gida bai ganta a waje ba har ya zauna, ƙarshe sai abun ya ɓata mishi rai ko dai bata murna da ganinshi ne kamar yanda take faɗa mishi a waya? Da ya kasa haƙuri sai ya aika Salima kiranta wacce ta dawo tare da ita seconds kaɗan da fitanta da alama sun yi kiciɓus da Juwairiyyan ne a hanya.

Ganinta kaɗai da yayi sai ya ji ɓacin ran ya kau har bai san lokacin da ya murmusa ba, amma sai da ya tambayeta dalilinta na ƙin zuwa da wuri ta ce mishi tana sallah ne, wani abu da yake ƙara burgeshi da ita kenan wato sallah akan lokaci wanda watarana ita ke tashinshi sallan asuba ya samu jam’i. Wannan karon bai ce su zo su ci abinci tare ba saboda tun farko ma da aka fara don ya ga ramar Juwairiyya yayi yawa ne ya sakata cin abinci a gabanshi, sai kuma wancan karon da ya sauƙa a ɗakinta sai ya ramawa Salima saboda kar ta ga kamar bai mata adalci ba. To a yanzu da aka yi 1-1 ba zai ƙara tursasasu cin abinci tare ba tunda ya lura basa so.

Ya godewa Juwairiyya a ranshi da ta basu guri da Salima wacce bayan ta bawa mai aikinta Hafiz Jnr ta kaishi makaranta take faɗa mishi wai period ɗinta ya dawo jiya amma ta kasa faɗa mishi saboda kar ya ji gwiwarshi ta karye da dawowa gida amma ya je gurin Juwairiyya tunda ita tana da tsarki.

“Bar shi kawai.” Ya faɗa yana jin kamar yayi kuka don ba haka ya so ba, watanshi bakwai rabonshi da ɗiya mace, gashi can cikin farar fata masu buɗe jiki suna tayar mishi da sha’awa duk da kawar da kan da yake ƙoƙarin yi.

“Wallahi har cikin zuciyata na bar mata kwanan nawa duka saboda ko ka zauna a nan ba zaka samu nitsuwa ba, ba zan bari ka cutu ba Baban Hafiz.”

Tausayinta ne ya cike mishi zuciya domin ya sani tana sonshi tana kuma son farin cikinshi da kuma mishi kara, wannan dalili yasa ya ji itama ya kamata ya mata karan don ta ji daɗi.

“Ba don samun nitsuwa kaɗai bane yasa na aureki Salima, har da cewa ina sonki don haka ko ba zan samu komai ba zan zauna a haka. Ke dai ki mini wata dabara in rage zafi.”

Duk yanda ya kai ga nuna mata son a mishi wani salon farantawa miji rai ta kasa koya wanda a ƙarshe ta fito ɓaro ɓaro ta ce mishi ba zata iya ba wai tana jin amai. Sai dai da ya auri Juwairiyya ta gama mishi rasar kunyarta ta yi hankali sai ta gwada mishi abun da ya jima yana mafarkin samu, wanda tsabar farin ciki da kuma nishaɗi sai da ya ji hawaye ya taru a idanunshi. To a yanzu da ya san ba zai samu haka ba sai ta mishi wanda ta iya ya kuma samu nitsuwa har ya kwanta bacci wanda bai tashi ba sai yamma liss.

Tunda ya tarasu da dare ya gane akwai wani abu a tsakaninsu dalilin kowacce ya lura bata yiwa ƴar’uwarta magana in ba ya kama dole ba, ya tambayesu duk suka nuna mishi babu komai amma har cikin ranshi ya san ƙarya suke yi. Sai a ranar da zai komawa Juwairiyya Salima take faɗa mishi abun da ya faru wanda ya ji zafin wannan kalma ta munafuka da ta kirata da shi, da alama bata san waye munafuki ba. Ganin Saliman kuma tana kuka yasa ya gane lalle ba ƙaramin cinta abun yake yi a zuciyarta ba domin kuwa ita tana da kawaici da haƙuri wanda ya sani Iyami bata shiri da ita amma a hakan Saliman take zaune da ita bata nuna mata ɓacin ranta ko kuma ta kawo mishi ƙararta. Wannan karon lallai an kaita maƙura wanda har ta kasa haƙuri ta faɗa mishi.

Ya kira Juwairiyya don ya musu shari’a wacce ya sani ta aikata ɗin don Salima ba zata mata ƙarya ba, ko da ta zo ya tambayeta sai ta gaskata zancen wanda a yanayin maganarta ya gane cewa wasu ke zugata basa son ta zauna lafiya da matarshi duk da cewa tana da sanyin hali da haƙuri. Wannan taurin kan nata shi ya fi tsana domin shi ko ƙannenshi basa mishi balle matrshi, shi yasa da yace ta bata haƙuri ta ƙi har ta ƙara kiranta da sunan munafukar a gabanshi ya ji he had heard enough.

“Idan na sake maimaita umurnin da na baki wallahi daga ni har ke sai mun yi dana sanin abun da zai fito daga bakina next. Apologize, now!” Ya furta yana jin ɓacin rai na ƙara mishi yawa. Ya tsani taurin kai.

Sai a lokacin ta bata haƙuri, ya musu faɗa tare da jansu da hira don su sake jiki amma sai ya lura ba gyara yayi ba, ɓarna yayi mai yawa wanda a yanzu ko kallon juna basa yi ga Juwairiyya ta rufe ido tana hawaye. Ya sallameta sannan ya koma kan Salima ya mata faɗa domin ya lura ita flow ɗinta shine surutu wato faɗi ba’a tambayeka ba. Ya sani zata aikata yin maganar Juwairiyyan tunda shima an faɗa mishi wai tana cewa  tsoronshi take ji tana kuma shakkar mishi laifi, a da ya ɗauki hakan a matsayin isa wanda har ya fara jin kanshi eh shi ya isa da gidanshi, amma da tafiya tayi nisa sai ya ga kamar kowa yana mishi kallon mutum ne mara son mutane da mugunta wanda shi ba haka yake ba. Ya so mata magana ta daina amma ya rasa ta yaya don ba ya son ta ganshi kamar mace wato mai karɓan gulma yana aiki da shi.

Ya tafi ɗakin Juwairiyya da niyyar kashe duk kishin ruwanshi amma sai ya samu tana wanka wanda hakan ma sai ya ƙara tayar mishi da hankali shi yasa ko da ta fito bai iya mata magana ba ya nufeta. Ya sani itama tana cikin shauƙin ganinshi da zata iya mantawa da duk abun da ya faru su farantawa juna in ya so sai daga baya su yi magana ya nuna mata kurenta a natse ta gane kiran mutum da kalma mara daɗi irin haka is not acceptable. Sai dai yana juyo da ita ya ga tana hawaye wanda ya sani tana tuna abun da ya faru ne ɗazu wanda hakan shi ya hanata biye mishi. Ya so tayi magana amma ta ƙi ƙarshe ta mishi habaici da cewa tana tsoron buɗe bakinta ne don ya ce yana da kaifi. Ya fita da ɓacin rai ya zauna a masallaci har aka yi sallah isha sannan ya dawo wai duk don ta gane ranshi ya ɓaci ta yanda in ya dawo zata canja yanayinta su manta da komai. Sai dai yana dawowa ya samu bata ma falon hakan ya ƙara tabbatar mishi cewa bata huce ba, da haka ya ɗebi abinci kaɗan ya fara ci, wanda a haka ta fito daga ɗaki ta samu guri ta zauna ya bita da ido kamar ya bar cin abincin ya bata haƙuri ko da hakan zai jawo mishi raini a gurinta, amma da ya tuna kalar rashin kunyarta musamman in ta samu guri sai ya ƙara ɓata fuskarshi yayi kamar bai ganta ba wanda kuma hakan ƙarya ne, domin kuwa duk lokacin da ta juya ko ta tashi ɗauko abu sai ya bita da mayun idanunshi yana kissima me zai mata ko kuma ita me zata mishi.

Bai san ko gajiya tayi ba ta tafi ɗaki, wato ba zata bashi haƙurin abun da ta mishi ɗazu na hanashi kanta da tayi ba. Wai ko shin bata ga kamar ranshi a ɓace yake ba? Me yasa ba zata tambayeshi laifin da tayi ba kamar yanda Salima take yi wanda in dai bai faɗa mata ba hankalinta ba ya kwanciya ta ringa magiya kenan watarana har da hawaye? Sai da ya ja lokaci ya shiga ɗaki yayi wanka sannan ya zo ya kwanta ya bata baya, amma tun daga inda yake yana jin ƙamshin Humranta mai sanyi da yake jin ɗaɗin shaƙa a ƙofofin hancinshi. A nan kuma ya fara hasko surarta a idanunshi wanda maimakon hakan yasa ya samu sauƙi sai ƙara mishi wahala yayi wanda ya dinga juye juye har yayi bacci mai cike da mafarkanta duk da ma gata nan kusa dashi.

Ya san tana son a ci abincinta shi yasa ya ƙi cin breakfast ɗin da ta mishi ya fita zuwa ɗakin Salima don ya dubata kamar yanda ya sabar musu. A can ya samu tana ciwon ciki duk da ma bai taɓa ganin tana period cramps ɗin ba.

“Salima mu je kawai in kaiki asibiti.” Ya faɗa bayan ya shafe kusan awa a gurin nata yana ganin yanda take wahala har da hawaye yana mata sannu.

Gyaɗa mishi kai tayi ya saka mata hijabi tare da riƙo hannunta suka fito ya buɗe mata mota suka tafi ba tare da ya faɗawa Juwairiyya ba don yana fushi da ita. Magani aka bata a asibiti daga nan kuma ta nemi alfarmar ya kaita gidansu don kar ta koma gida ita ɗaya ta zauna ciwo ya ƙara gaba.

“Ba ga Juwairiyya a gida ba? Don me yasa zaki je har gidanku? Me amfanin zaman naku ku biyu in ba zaku taimakawa juna ba?”

“Kayi haƙuri amma wallahi ba wai ina son musu da kai bane, ka ga jiya ka mana shari’a wanda na lura bata ji daɗinshi ba har ta tafi ko kallon inda nake bata yi. To ta yaya yau kuma zata yarda ta kula da ni bayan tana ganin ni na jawo ka mata faɗa? Amma in baka so ka mayar dani gidan zan je in zauna ni ɗaya babu abun da zai faru da yardar Allah.”

Wannan sanyin halin nata da kuma hangen nesan shi yasa yake respecting ɗinta, tabbas Juwairiyya ba zata kula da ita ba saboda ko shi da ya ajiyeta bata isheshi kallo ba balle matarshi. Hakan yasa ya karya kwana ya kaita gidansu ta wuni a can shima ya ƙi dawowa gida da rana ganin ko sau ɗaya Juwairiyya bata kirashi ko ta mishi text ta ji ya yake ba. Sai bayan isha ya bi gidansu Salima ya gaishe da iyayenta sannan ya ɗaukota suka dawo gida, a nan ne kuma ya fara shiga taitayinshi da ya lura da gaske Juwairiyya ba kulashi zata yi ba har ya tafi, to ina zai kai lodin da ya dawo dashi a mararshi?

Wannan shakkar yasa ya ci abincinta sosai har da yin ƙari amma duk wannan bai sa ta sassauto ba domin yana gama ci ta tattara komai ta mayar kitchen ta tafi ɗaki ta kwanta, wato shi ake yiwa silent treatment? Bai jima ba shima ya fita don yiwa Salima sai da safe tare da duba jikinta amma sai ya samu ciwon cikin nata ya dawo tana kuka wiwiwi, a nan ya ƙara shafe minti arba’in har samu ciwon cikin ya daina da yayi browsing a Internet cewa idan ana matsa musu kunkuminsu suna samun sauƙi, da haka ya sakata ta ɗaura kanta kan wuyanshi ya fara matsa mata har ta daina hawayen tace ta samu sauƙi ya mata addu’a ya koma gurin Juwairiyya wacce ya samu har tayi bacci.

Da tsananin buƙata ya dawo gareta wanda hakan yasa ya cire girman kai ya kira sunanta.

“Juwairiyya.” Amma bata amsa ba sai da ya kira na uku.

“Na’am.”

“Guduna zaki yi?” Yanda yayi maganar shi kanshi sai da ya ji tausayi game da haushin kanshi amma ya ya iya? Dole ita kaɗai ce zata biya mishi buƙata.

Shuru tayi wanda shi ne abun da ya fi tsana, don me yasa zata bari shi yana magana amma ita ba zata mayar mishi da amsa ba.

“Bana son shirun nan. Yanzu na zo don in ganku in rage kaɗaici shine zaki fita daga harkata ki ƙi kulani?” He sound desperate, he knows it amma he is desperate ɗinne.

“A’a.” Ta amsa mishi a taƙaice wanda ba haka ya so ba.

“To menene na hanani kanki da kike yi?” Ya sake tambayeta yana mai juyowa yana kallon doron bayanta don muryanta kaɗai da ya ji yasa ya ƙara manta wani girman kan.

“Ni ban hanaka ba.”

Sai a lokacin ya gane tabbas bata gujeshi ba shi ya yi fushi yana neman ta zo ta bashi haƙuri kafin ya nemi kaɗaicewa da ita, ehh lallai yayi shirme don gashi zuwa safiyan gobe ne kaɗai ya rage mishi ya koma Lagos a fara biki don bai isa yayi missing ɗinshi ba saboda dalilin a kan bikin aka biya mishi kuɗin jirgi kuma Sharafadeen abokinshi ne na sosai da ba zai yi missing aurenshi ba.

Da wannan tunanin ya yanke shawarar kwana yin abu ɗaya da ita don ya sani zata jure, amma a maimakon ta tayashi sai ta kyaleshi wanda hakan bai mishi daɗi ba, don haka ya mata ƙorafi tayi shiru bata amsa ba, a nan ne ya yanke shawarar yin duk abun da ya so har ya samu biyan buƙata. Tayi gaggawan yin wanka shi yasa tana dawowa ya kai mata farmaki a karo na biyu ta nuna zata yi kokawa dashi, a nan ya so koya mata hankali domin bata isa ta hanashi kanta ba alhali yayi wannan doguwar tafiyar ne don ya samu nitsuwa. He forced himself on her wanda sai da komai ya lafa ya fara jin haushin kanshi na sosai da sosai yana jin baƙin ciki a ranshi domin yana ɗaya daga cikin mazan da suke yiwa ƴan’uwansu maza faɗa kan Marital rape duk da ance babu shi a musulunci, amma me yasa zaka yi amfani da karfi wajen yin abun da ake so ya zama so intimate and sacred?

Yana wannan self loathing ɗinne kuma ta kawo mishi wani wawan zance wai jikinta yake so. Kwarai yana son jikinta ba ƙarya bane saboda tana gamsar dashi, amma ba shi kaɗai bane abun da ya jawo hankalinshi gareta ba. Ita kanta abar so ce domin tana da addini, kyau, iya soyayya, iya girki da kuma daɗin hira amma ba zai faɗa mata duk wannan ba saboda haushinta da kanshi da yake ji duka.

Shi yasa shima ya buɗi baki ya faɗa mata abunda ya daɗe yana ci mishi rai wato aurenshi da tayi na wucen gadi!! Shi ɗin Muhammad za’a aura don wata manufa sannan in buƙata ta biya a nemi yayi saki a barshi? Laifin me yayi mata da ya cancanci haka? Riƙon mutum a rantan har ya kai haka? Yana tunawa ba gori ba tunda Hafiz ya rasu yake tausayinta wanda hakan yasa ya dinga taimaka mata tare da bibiyar rayuwarta don yana ganinta a matsayin amanar Hafiz ce da aka danƙa mishi a hannunshi. To amma duk wannan abu ita bata gani balle tayi appreciating ko ta ji nauyin using ɗinshi a matsayin escape route ɗinta. Shi bai ɗauka auren wucen gadi aka yi ba, ya ɗauka aure ne na dindindin shi yasa a ranar da ta tare ya kasa haƙuri ya fara lasar zumarta da ta ɓata mishi kowacce zuma yana jin ita kaɗai ce zai sha ya ji ya ƙoshi har wuya.

Bayan ya faɗa mata insecurities ɗinshi sai ya ƙara da cewa ta tafi gida, yayi hakan ne kuma don ta koma gidan ko zata yi hankali. Sannan idan ya barta a nan tare da Salima wani faɗan zasu sake yi tunda ya lura kamar tana cike da Saliman ta ɗauki fushi mai tsanani. Yayi wanka ya kwanta amma bai yi bacci ba har ta shigo dakin itama ta je tayi wanka, yana jin ta fara haɗa kayanta bai mata magana ba har dare ya tsala, a nan ne kuma bacci mai nauyi ya ɗaukeshi saboda nauyin mararshi da ya sauƙe. Bai tashi farkawa ba sai da aka idar da sallah a masallaci, a nan kuma ya duba ya ga ta tafi babu ko sallama duk da cewa ta san yau zai koma.

Jikinshi a sanyaye ya gama tattare kayanshi ya saka a jaka, kana ya buɗe fridge ɗinta ya kwaso duk abun da zai iya baci a wata ukun da zata yi bata gidan ya bawa Salima wacce har hawaye tayi da ya faɗa mata Juwairiyyan ta tafi gida ne sai ya dawo zata dawo.

“Ni kam don Allah ka bata haƙuri ta dawo mu zauna, yanzu sai a ga kamar ni ce na haɗaku faɗa har ka koreta gida. Ka rufa mini asiri kar ka jawo mini zagin mutane a gari Baban Hafiz.”

“Ki sakani dole in dawo da ita. Idan kuma kina son zaman lafiya da ni kar ki ƙara ɗauko mini maganarta. Ever.”

A nan ya rufe mata ƙofar ɗakinta tare da kitchen ya tafi gidansu ya kai mata key da safe, amma a maimakon ita ta fito sai ta aiko ƙanwarta wai kuma tana bacci saboda bata da damuwar komai. Kenan da gaske bata damu da shi ba sannan kuma burinta ne ya cika na rabuwa da shi a daidai lokacin da ta gama school wanda dama tun farko shi ne plan ɗinta, amma wani abu da bata sani ba shine har abada ba zai taɓa rabuwa da ita ba sai dai tayi ta yawo da igiyarshi a kanta, kafin shi wasu sun lashi zumarta amma da ranshi ba zai bari wani ya samu wannan chance ɗin ba sai dai in mutuwa yayi. Yes, he is that toxic!!!

Da wannan tunanin ya koma Lagos aka yi bikin kwana uku sannan suka koma UK cikin tawagar Amarya da Ango.

Na san wasu basa son jin POV na abunda ya wuce amma hakan dole ne a wannan book ɗin, saboda a nan ne zaku ji abun da dayan yake tunani ya kuma faru dashi sai ku hada daya da biyu ku gane wani lokacin rashin fahimta da kuma magana tsakanin ma’aurata ke jawo rashin jituwa ko kuma a zo a yi ta ganin laifin juna. Sometimes dukkan mu muna da gaskiya amma ba zamu gane ba sai mun zauna mun yi magana mun fahimci juna. Communication is the key.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Ya koma UK da kewarta a ranshi da kuma guntun haushi wanda yayi alƙawari ba zai nemeta ba har sai ta gane kurenta ta bashi haƙuri. Kullum idan ya ɗauki wayarshi sai yayi tsammanin zai ga heart warming ko kuma dirty text ɗin da ta saba tura mishi sai dai har aka yi wata ɗaya bai gani ba. Text ɗaya ta taɓa turo mishi da baya son ko tunashi a lokacin yana Lagos wai ya saketa! She must be joking, da shi da ita sun zamewa juna ƙarfen ƙafa mai wuyar cirewa.

Wata ukun da ya rage mishi bai iya cikawa ba don yana yin graduation ya tattara komai ya dawo gida wanda wannan karon jirgin maghrib suka hau zuwa Gombe don haka yayi isowan dare ba’a yi taron da aka saba ba. Sai dai washe gari da safe yana kwance a ɗaki yana tunanin yanda zai fara bikon Juwairiyya wacce ya gane taurin kanta ba zai barta ta nemeshi ba Salima ta shigo wacce ita kuma ya lura tun asuba da suka tashi bata zauna ba tana ta shiga da fice.

“Baban Hafiz.” Ta kira sunanshi nervously.

“Ya dai?” Ya amsa yana mai juyo da kanshi ya kalleta.

“Anjima kaɗan ƴan’uwa zasu fara zuwa ka tashi ka shirya na haɗa maka surprise Walima.”

Shiru yayi yana kallonta yana jiran ta ƙaryata kanta, amma ganin ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da yatsunta ya gane abun da ta aikata ai kuwa ranshi ya ɓaci ya tashi ya zauna yana faɗin,

“Don me yasa zaki haɗa bayan nace miki bana so? Me yasa ke bakya jin magana ne? Yaushe ma na dawo da zan fara dealing da mutane?”

 Tun yana can UK ta mishi maganar walima ya ce baya so, a cewarshi kowa ya mishi addu’a daga inda yake shi kuma zai yi azumi biyu don nuna godiyarshi ga Allah da Ya bashi wannan daman. Amma sai ta koma baya ta haɗa wanda ya san babu ko sisinshi a ciki, idan ma zai yi waliman ba zai yi yanzu ba sai ya dawo da Juwairiyya domin itama tana da hakki ta kasance a wannan lokacin don tare da ita ya barsu har na tsawon shakaru ukun suna haƙuri da rashinshi. It’s only fair in tana nan, don yanzu idan ta ji yayi walima bata gidan ya san ba zata ji daɗi ba.

Hawayen da Salima take yi yasa ya dawo kuma ya fara rarrashinta don sai ya ji tausayinta, sai da tayi shiru sannan kuma ya fara mita.

“Ai ina da dalilin da yasa na ce ba zan yi yanzun ba, da kin bi yanda na faɗa raina ba zai ɓaci ba, bana son kina mini haka. In nace bana son abu kar ki mini ko da da kuɗinki na, nima ba rashin kuɗi ne ya hanani yi ba, ina jiran time ɗin da ya dace ne.”

“To kayi haƙuri, ba zan sake ba.”

Shi da ya so yau ya kwanta ya huta sai yamma zai fita amma da alama hakan ba zai yiwu ba don ta ɓata mishi plan. Haka ya tashi ba tare da ya ji nauyin jikinshi ba dalilin yanzu ƙarya ne ka ganshi ka kirashi da sunan lukuti, shekara uku na work outs da watching diet ɗinshi ya saka ya dawo giant mutum ƙarfaffa, wannan tsokokin jikin nashi duk sun murɗe sun zama muscles, tumbinshi ya koma sai skin kaɗan da zai dinga workouts ɗin da zai sa shima ya tafi idan ya nace, sai dai ko bai tafi ba Muhammad yayi niyyar zai ɗauki hakan a matsayin trophy da kullum in ya gani zai tabbatarwa kanshi sanin he tried to be healthy. Sai da ya fara zuwa gym ya gane yawan rashin lafiyarshi cin junks ne da kuma rashin exercise, yana tunawa tun bayan rasuwar Hafiz ya hana kanshi ciye-ciyensu sannan ya so ɗaura iyalinshi kan hakan. Tun da ya fara rage ƙiba Salima ta nuna mishi wai ita tafi son ganinshi a lukutinshi wanda hakan ya bashi dariya yace mata itama zata rage nata idan ya dawo gida in tana so.

Rai babu daɗi yayi wanka wanda tun kafin ya fito ƴan’uwa suka fara shigowa wai daga nan za’a wuce BraveRock Park a can za’a yi waliman wanda kawai za’a kirashi get together. Haka kawai ya ji ya ɗinga ɓata time saboda in an je can kar a jima da yawa ya samu ya fita da yamma ya je gurin Juwairiyya su magantu ta dawo ɗakinta.

Shiryawan da ba ya ɗaukanshi minti goma yau sai gashi har awa ɗaya bai gama ba, sai da ya ga kamar Salima ta fara ganeshi sannan ya ƙarisa shirin cikin half jumfa da wando kalan dark blue, wannan karon ma ya saka hula wacce ta shiga da kayan. Da haka ya fita ya fara gaisawa da ƴan’uwa suna mishi barka yana amsawa, a nan ne ya sake fuskarshi suka ɗunguma suka tafi can BraveRock ɗin. An buɗe taro da addu’a tare da yaba mishi da kuma mishi murna sannan aka fara zuba abinci da snacks ana kawowa mutane wanda Salima da Shema’u ne a kan komai, hakan yasa a lokacin da Juwairiyya ta kira Iyami basu sani ba suna can inda ake rabiyan abinci suna bayarwa ana kawowa wasu har sun kusa cinye nasu.

Yana zaune kusa da Iyami aka kirashi ya fara waya, zai iya rantsuwa duk cikin ƴan’uwanshi ya fi shaƙuwa da ita da kuma sonta, amma sai dai abun mamaki sun fi kowa samun matsala don tana da taurin, sau da dama in tayi laifi shi ake kawowa ƙararta ya je har gidanta ya mata kaca kaca ya dawo, sai sun ɗauki lokaci bata nemeshi ba shima bai nemeta ba, sai daga baya ta nemeshi ta bashi haƙuri. Yana gama wayar ya ji Iyami na magana a cikin wayarta.

“Ya dawo jiya da dare, yau kuma muke taron tayashi murnan gama makaranta. Yauwa gashi nan ya gama wayar. Ya Muhammadu ana maka magana a waya.” Ta miƙa mishi wayar ya ƙarba domin an yi irin hakan ya fi sau a ƙirga, domin wataƙila wasu dangin mijinta ne da suke son tayashi murna amma basu da numbernshi.

“Hello.” Ya faɗa wanda sai daga baya ya ga rashin dacewar haka, sallama ya kamata yayi, nan ba da jajayen fata yake magana ba.

“Hellooo.” Ya sake nanatawa don ba zai canja ba don kar a gane yayi laifin da gaske.

“Iyami ba’a magana fa, waye ne?” Ya faɗa ba tare da ya cire wayar a kunnenshi ba, sai dai yana rufe baki ya jiyo muryarta wanda ko bacci yake yi in dai ya ji zai gane nata ne, sai dai sautinta kamar a gajiye take.

“Na haihu ɗazu da hantsi, ka zo ka karɓi ƴarka sannan ka taho mini da takardata, aure zan yi.”

Dudum! Dudum!! Dudum!!!

Ya ji zuciyarshi tayi mugun bugawa da ƙarfi don bai ji alamun wasa a muryarta ba, wani irin haihuwa?

“Juwai…” Bai kai ga ƙarisa maganan ba ta kashe wayarta ta barshi baki buɗe wanda yasa Iyami da take gefenshi ta ja hannunshi suka matsa gefe tana tambayarshi lafiya?

“Juwairiyya ce tace mini ta haihu, dama tana da ciki ne kika ɓoye mini Iyami? Ta yaya?” Yayi maganar yana jin kamar hajijiya na neman jefar da shi ƙasa lokaci ɗaya kuma ya fara gwada kiranta aka ce mishi it’s not reachable.

“Haihuwa kuma? Wallahi ban sani ba, sau uku ina zuwa kamar yanda ka sani amma wallahi ban ga alamun ciki a tattare da ita ba. Ka ƙara kiranta mu ji ko dai ɓari tayi.” Itama ta faɗa cikin ruɗani.

“Wayar bata shiga, kira mini Mamanta.” Ya faɗa yana mai binciko numbern a wayarshi, can ya ce, “Ki bari ma na samu.”

Ringing biyu Maman Juwairiyya ta ɗauki wayar ya mata sallama cikin girmamawa tare da gaisuwa ta amsa mishi babu yabo babu fallasa domin bata mance kora mata ɗiya da yayi daga gidanshi ba.

“Mama me ya faru da Juwairiyya ta kirani ta ce mini ta haihu.” Ya tattaro duk courage ɗin shi ya tambayeta don wani irin shakka da kwarjininta ne ya ɗarsu a ranshi duk da cewa baya ganinta.

“Ta kiraka kenan?” Mama ta tambayeshi.

“Eh ta kirani.” Ya amsa yana mai lashe lips ɗinshi da ya ji sun bushe dalilin numfashin da yake yi ta baki don yana ganin wanda yake shaƙa ta ƙofofin hancinshi are not enough su hanashi losing consciousness ɗinshi.

“Haihuwa tayi ɗazu, ta samu ɗiya mace, da yake Cryptic Pregnancy ne yarinyar bata da girman normal yara da ake haifa a nine months, she is just 3.0kg.”

Yanda tayi maganar kamar wata mai bada labari a gidan television ya gane tana kullace da shi don haka ya ajiye duk wani hargitsin da zuciyarshi take ciki ya fara mata magana bayan ya ƙara sausauto da muryarshi ƙasa.

“Mama na san ban kyauta muku ba da na aiko Juwairiyya gida kuma ban kirata ba duk tsawon wata biyun da nayi, wallahi tallahi ina sonta kuma ba wulaƙanci ko tozarci yasa na mata haka ba illa ƙoƙarin kaucewa wani abu da nake ganin zai iya faruwa tsakaninta da abokiyar zamanta matuƙar na tafi na barsu su kaɗai. Ku yi haƙuri nayi laifi da ban nemeku na ƙara muku bayani ba, dama wallahi niyyata yau zan shigo da yamma mu yi magana da ke, sai mu zauna ga ki ga Juwairiyya in faɗa miki duk abun da take yi ki mata faɗa tunda na lura duk duniya ke ce kaɗai take jin maganarki.”

“Ka dawo kena?” Mama ta tambaya kamar bata ji duk sauran bayananshi ba.

“Eh na dawo jiya da dare.”

“To Allah Ya sanya alkhairi kan karatun da ka yi. Juwairiyya kuma tana jin maganar duk na sama da ita ba ni kaɗai ba ce.”

“A’a wai ina nufin ke kin fi kusa da ita ne zata fi ɗaukan shawaranki.” Yayi saurin gyara zancenshi cikin sanyin murya har hannunshi na gumi tsabar nervousness.

“Eh wannan hakane.”

“To Mama suna lafiya kam? Babu wata matsala ko? Ina Juwairiyyan?” Yayi maganar duk a numfashi ɗaya.

“Lafiyansu kalau, babu wata matsalar komai. Muna asibiti bamu koma gida ba amma dai yanzu zamu tafi.”

“Alhamdulillah, Alhamdullilah. Allah nagode maka.” Haka yayi ta hamdala cikin farin ciki ba tare da ya damu da Mama tana sauraranshi ba.

Sai dai bai sani ba wannan nuna farin cikinshi da yayi shi yasa Mama ta sassauto daga dokin fushin da ta ɗale, nan da nan kuma fara’a ya wanzu a fuskarta har tana murmushi mai tsada.

“Mama nagode da kula mini da iyalina da kika yi, Allah Ya saka miki da aljannah. Nagode, nagode sosai. Amma Mama yarinyar da waye take kama? Ni ko Juwairiyya?” Yayi maganar cikin ɗoki kamar wani yaron da aka ce za’a kaishi amusement park.

Ai kuwa wannan magana yasa Mama ta kwashe da dariya tana jin nishaɗi a zuciyarta ta nufi labour room tana cewa,

“Sai ka ganta zaka tantance.”

Dariya yayi shima kana ya ce,

“Kika ce Juwairiyya tana lafiya ko babu wata matsala?”

“Alhamdulillah, babu wata matsala duk lafiya suke.” A nan ta shigo ɗakin tana kallon Juwairiyya da ke binta da ido cike da tuhuma.

“Kuna asibiti ko?” Ya sake tambaya kamar bai ji na ɗazun ba, so kawai yake yi ya tabbatar.

“Eh, muna asibitin da nake aiki.”

“To ganin nan zuwa kar ku tafi zan zo in kaiku gida.”

“To shikenan sai ka zo.”

“Mama Nagode, Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi da ƙoƙarin da kika yi. Allah kuma Ya ƙara miki haƙuri da girma.”

“Amin Amin babu komai. Ai yiwa kai ne.”

“To sai na zo, gani nan yanzu nan.”

“To madallah sai ka zo.”

Yana kashe wayar ya zurmata a aljihu yana washe baki yana kallon Iyami da itama haka fuskar tata yake,

“Wai da wa yarinyar take kama?” Ta tambayeshi cike da ɗoki itama.

“Ya wuce ni? Kin san ni jinina akwai ƙarfi. Iyami mintsineni don Allah kar fa mafarki nake yi….. Ouch… Baki da kai ko? Mintsinina kika yi fa?” Ya faɗa yana sosa hannunshi wanda tuni har gurin yayi ja abun ka da farin mutum.

Nan ya kai mata duka tayi sauri  kaucewa tana dariya wanda zata iya rantsewa rabon da su yi irin wannan wasan tun tana budurwa kafin a aurar da ita, don tunda tayi aure ta lura yana respecting ɗinta ko dukan wasa ba ya kai mata. Amma fa idan tayi laifi, wayyo, har gidanta zai je ya masifeta ya yi tafiyarshi.

“Allah ne Ya bani da best gift ever na gama school ɗina. Alhamdullilah mu je mu sanar da ƴan’uwa wannan babban labarin. Wallahi har yanzu gani nake yi kamar mafarki nake yi?” Ya faɗi hakan a lokacin da suka doshi inda suka bar sauran ƴan’uwan da suke hangensu sa’i da lokaci suna tunanin me suke tattaunawa kuma har da yin waya?

“Ko dai in ƙara mintsininka?” Iyami ta tambaya cike da tsokana.

“Ki taɓani in koya miki hankali.” In ba don dariyar da yake yi ba da tuni Iyami ta shiga taitayinta amma a yanzu ta gane wasa yake mata.

Da haka suka isa kan manyan carpets ɗin da aka shimfiɗa Muhammad ya kwalawa su Salima kira suka zo suka tsaya hannunta riƙe da abincinshi wanda ta sako mishi.

“Abun murna ne ya faru a yau ɗin nan da mu gabaɗaya.”

Nan kowa hankalinshi ya dawo kanshi ana ta murmusawa wasu har da matsowa kusa don ganin murnar da ke kwance a fuskarshi sun sani ba ƙaramin abu ne ya sameshi ba. Ko dai aiki ya samu mai tsoka daga gama karatun?

“Tun kafin in ji har na fi kowa murna.” Faɗin Salima fuskarta a washe wanda kallo ɗaya Iyami ta kawar da kanta tana murmushi.

“Yanzun nan Juwairiyya ta kirani ta haihu an samu ɗiya mace.”

Nan aka hau mishi murna da addu’a yana amsawa fuskarshi cike da annushuwa, sai dai Salima tana buɗe bakinta komai ya tsaya cak!!

“ƙarya ne! Wallahi ƙarya ne!! Ta yaya zata haihu?” Salima ta faɗi hakan cikin ruɗewa da ta lura da gaske yake maganar ba wai wasa ba.

Nan ido ya koma kanta ana kallonta cike da mamakin yanda lokaci ɗaya ta birkice tana ɗaga murya, plate ɗin hannunta kuwa tuni ya faɗi ƙasa dalilin karkarwa da hannunta yake yi.

“Ban gane ƙarya ba, ke lafiyanki kuwa?” Muhammad ya tambayeta cike da tsoro don ya fara tunanin ko aljanu ne suka shigeta, saboda wannan ba Salima ba ce.

“Me yasa kika ce ƙarya ne?” Iyami ta ɗaga muryarta yanda zata jiyota dalilin kowa a lokacin ya fara magana ana mayar da zance.

“Wata biyu ne kaɗai da tafiyarshi shine har tayi ciki ta haihu? Haba ku duba mana. Son zama da shi ɗin har ya kai su yi ƙaryan haihuwa su saci jaririn wata?” Ta ƙara musu bayani don su ga abunda ita ta hasko a nata kwakwalwan.

“Cryptic Pregnancy ne, idan baki san menene hakan ba shine cikin da yake ɓuya ba’a ganeshi har sai ya girma ko kuma har sai ranar labour mace ta gane wanda shine case ɗin Juwairiyya. Ki daina saurin yanke hukunci idan baki san abu ba, kuma ke kin fi kowa sanin halin Juwairiyya ba zata taɓa abun da kike accusing ɗinta a kai ba, don haka bana son shirme ki kiyayi bakinki.” Faɗin Muhammad calmly don gudun kar shima ya tunzura su tonawa junansu asiri cikin dangi.

Domin a yanda ya ga Salima take magana zata iya sakawa shima ya faɗi mara daɗi a dawo ana yamaɗiɗi da su ana cewa sun yi sa’insa a gaban mutane.

“Ka dai bincika in ba haka ba za’a kawo maka ɗan da ba naka ba.”

Wannan maganar da tayi shi ya ƙara bashi mamaki da kuma haushi, hakan yasa ya yamutsa fuska yana kallonta yana kifta idanunshi akai akai, me yake damunta ne? Me na wannan accusations ɗin?

Ranshi a ɓace ya dubi Yayanshi Abdallah ya ce,

“Yaya bani key ɗinka zan je in ɗaukosu in dawo da su gida.”

“Mu je tare, wannan abun farin cikin kuma a bazata ba zai wucemu ba. And I hope daga asibitin ka dawo da ita gidanta.” Bai jira amsar Muhammad ba ya kira matarshi da ƴaƴanshi uku akan su tafi tare.

Nan sauran ma suka ce suna zuwa idan sun gama cin abinci wanda dukansu mutanen Juwairiyya ne ciki kuwa har da Iyami wacce ta shiga motar wata cousin ɗinsu ta gefen uwa. Minti sha biyar da haka guri ya watse aka bar Salima da muƙarrabanta su Shema’u da wasu matan kalilan. Sai da ta tabbatar su Muhammad sun fita a gurin ta fashe da kuka suka dawo rarrashinta.

“Wallahi cutarshi zasu yi ba ita ta haihu ba, so kawai take yi ta koma amma in ba haka ba wani irin ciki ne wata bakwai ina tare da ita ban ganshi ba balle alamarshi sai kawai a kira a ce ta haihu? Wallahi cutan ɗan’uwanku zasu yi shi kuma da yake yana son haihuwa gashi har ya yarda.”

“Ai dai zasu je su gani da idonsu domin kuwa kammanin zuri’arsu baya ɓuya, duk kamannin uwarsu suka yi, ki dubi ƴaƴan Yaya Abdallah da Iyami da ɗanki Hafiz kamar uwa ɗaya uba ɗaya suke. Ai da sun ganta wata kala su ma zasu sha jinin jikinsu. Kai dolema in je in ganewa idona abunda zai faru.” Faɗin Shema’u tana tattara abubuwanta.

“Gaskiya mu je tare nima in ganewa idona, don tsiya ma wai ƴa mace ta haifa saboda ta ji suna son haifan ɗiya mace tunda Iyami bata da ko ɗaya cikin ƴaƴanta huɗu, shi kuma Yaya Abdallah ɗaya gareshi ku kuma baku samu ba.” Ƙanwar Shema’u mai suna Fauziyya ita ta tsoma bakinta.

“Ku jira nima zan je bari in kirashi  ya bani izini.” Faɗin Salima tana ɗauko wayarta cikin sauri amma ta kirashi sau uku bai ɗauka ba, a nan ta gane ba zai ɗauka ɗin bane kawai.

“Bari mu tafi fa kar a yi banda mu, ke kam ki sha zamanki zamu baki labarin duk abun da ya faru.”

Da haka suma suka tafi aka bar Salima da sauran wanda su kansu basu san wa suke bi ba, amma dai duk inda gulma take suna gurin. Nan kuma suka zuba mata ido suna karantar reaction ɗinta sannan sa’i da lokaci suna kawo mata maganar tana sake layi suna ajiyewa a kwakwalwarsu don su kai gaba. (Idan ka yiwa wani kai ma wallahi ka jira ranar da za’a maka.)

Muhammad gani yake yi tafiyan da Yaya Abdallah yake yi baya sauri hakan yasa ya dubeshi da yake shi yake tuƙasu ya ce,

“Ni kam da gangan kake tafiya a hankali ne ko dai haka kake tafiya kullum?”

“Duka.” Ya amsa yana murmushi wanda hakan yasa shima Muhammad ya murmusa cike da jindaɗi ya ce,

“Wai mace fa ta haifa, kai Alhamdulillah.”

“Nihal ta samu abokiyar shawara. (Ƴar shi babba).”

“Ai kuwa Nihal kin samu ƙawa.” Faɗin matar Abdallah da ke bayan motar tare da ƴaƴanta.

Nan suka hau hiran wannan abun farin ciki da al’ajabin har suka iso asibitin, Muhammad shi ya riga kowa shiga ya samu Mama a  reception  yayi saurin isa gurinta tare da russunawa ya gaisheta ta amsa cikin fara’ah.

“Mu je suna ɗakin hutu.” Ta faɗa kana tayi gaba suka bita a baya dukkansu.

Sai a lokacin zuciyar Muhammad ta kaɗa da ya tuna yanda Juwairiyya zata ƙarɓeshi, sai a lokacin kuma ya tuna wai da ta sanar mishi ta haihu cewa tayi ya zo ya ƙarɓi ƴarshi sannan wai ya taho mata da takardarta, wace takarda kenan? Idan na saki take nufi tana buƙatar resetting.

Mama tana isa bakin ɗakin ta ja tunga ta tsaya tana cewa,

“Ku shiga bari in gama clearance da asibiti.”

Ai kuwa tana rufe baki Yaya Abdallah ya karɓa yana cewa,

“A ina za’a yi biyan kuɗin? Wannan aikinmu ne Mama.”

Murmushin jindaɗi Muhammad ya yi kana ya kutsa kai cikin ɗakin cikin sauri gudun kar wani ya rigashi don ya san yanzu sauran sun kusa isowa cikin asibitin domin ya ji matar Abdallah tana waya da su tana musu kwatancen inda suke. Zuciya cike da shauƙi ya fara hango Juwairiyya a kan gado tana kwance an lulluɓeta da zani da kuma hijabi a jikinta, fuskarta ta kumbura sannan idanunta sun yi ja kamar wacce tayi kuka, ba dai kukan haihuwan tayi ba?

Sallama yayi Surayya da Sumayya suka amsa banda mutumiyar tashi wacce tana ganinshi ta rufe ido kamar tana bacci, ko dai bata san ya ganta bane?

“Baban Baby ka zo ganin Baby ne?” Faɗin Sumayya tana murmusawa wanda in ba don murmushin da take yi ba zai ce magana ta faɗa mishi a fakaice.

“Adda Juwai ga mijinki.” Faɗin Surayya tana taɓa Juwairiyya wacce ta yi banza da ita.

“Ga Babyn.” Da haka Sumayya ta saka mishi ƴar ƙaramar yarinyar a hannunshi ya ƙarɓeta ya manna da ƙirjinshi sannan ya buɗe showel ɗin da aka lulluɓeta da shi yayi revealing fuskarta.

“Ya Salam! So beautiful.” Ya faɗi hakan bakinshi a washe tamkar zai tsage gida biyu wanda su Surayya suka tsaya ganin ikon Allah don tunda suke dashi basu taɓa ganin dariyarshi haka ba.

“Ai na cewa Adda Juwai babu abun da yarinyar ta ɗauko nata.” Sumayya ta amsa mishi.

“Gaskiya kam.” Shima ya mayar mata yana shafa fuskar ƴar tashi wacce ke kama da HJ a lokacin da yake jinjiri. A nan ne ya dubi Juwairiyya wacce har lokacin idanunta a rufe suke ya ce, “Jay na san idonki biyu ki tashi mu gaisa.”

Bata kulashi ba wanda dama ya san hakan ne zai faru, a nan kuma Maman Nihal da sauran ƴan’uwa suka shigo ɗakin wanda dole yasa Juwairiyya ta buɗe ido ta ƙaƙalo murmushi ta shimfiɗa a fuskarta ba tare da ta ko kallin inda Muhammad ya ke ba. Shi kuma binta yayi da ido yana jijjiga ƴarshi a hankali yana jin son iyalin nashi na ƙara shiga ranshi, ya san akwai aiki babba a gabanshi wajen rarrashin wannan amaryar tashi mai taurin kai.

Nan ya fara jinta tana gaisawa da dangi shi kuma ya matsa gefe ya fara kiran sallah a kunnen yarinyar, da haka ya mata addu’a sannan ya miƙata ga dandazon mutanen da suke ta jira ya gama addu’ar su karɓeta. Ganin ɗakin ya cika da mata yasa ya fice bayan ya ƙara kallon Juwairiyya wacce har lokacin bata yarda ta haɗa ido dashi ba.

Minti biyar da haka sai ga su Shema’u sun shigo room ɗin, ko ta kan Juwairiyya bata bi ba ta karɓi jaririyar tana gani ai kuwa sai tayi mutuwar tsaye domin wannan ko Saliman da ta fita ƙin Juwairiyya bata isa ta ce ba ƴar yayanta bane.

“Shema’u daga shigowa sai karɓan Baby wato ƴarku kaɗai kuka sani ko?” Iyami tayi magana mai harshe biyu, ita tun ɗazu ta shigo da Maman Nihal da sauran mutane.

yarinya

“Wannan miracle Babyn ne ta jawo haka, ki ga  fara kal kamar balarabiya, kai amma ta ji kyawun fuska kamar ku.”

“Masha Allah. Masha Allah.” Iyami tayi saurin faɗa tana murmushi.

Nan ta miƙawa Fauziyya itama tana yabon kyan baby har da ɗaukanta a hoto don anjima ta turawa Salima. Sai a lokacin suka yiwa Juwairiyya barka ta amsa tana murmusawa.

“Ai wallahi Matar Ya Muhammadu da kin san da zaman cikin nan da mun ɓata, in ce sau uku ina zuwa gurinki amma baki faɗa mini ba?”

“Wallahi nima ban sani ba kamar yanda na faɗa miki sai da safen nan.” Nan dai ta basu labarin yanda aka yi tana cire wanda bai kamata ba kamar dai yanda mata suke bada labarin labour da haihuwarsu which is normal.

Minti goma da haka suka watse akan sai daga baya zasu zo ganin Baby har gida. Sai a lokacin Muhammad ya shigo ya sameta ita ɗaya tana bawa Babyn nono wacce take kuka duk da ma cewa babu ruwan nonon sai ɗan kaɗan.

“Juwairiyya ya jiki.”

“Alhamdulillah.” Ta amsa tana mai saurin cire nonon a bakin yarinyar don haka kawai ta ji bata son ya ga jikinta.

Sai dai tana cirewa yarinyar ta callara ƙara Muhammad ya iso a sukwane yana tambayar menene.

“Me ya sameta? Ciwo ta ji?”

“An cire ne take kuka.” Ta amsa ciki ciki don ita bata ga dalilin tsayawarshi ba, kuma menene yake ta nuna kamar yana son yarinyar?

“To ai sai ki bata, don me yasa zaki yi abun da zata yi kuka?” Ya faɗi hakan yana mai gyara showel ɗinta ganin ta fitar da hannunta ɗaya.

Wani irin kallo Juwairiyya ta bishi dashi wanda yasa ya sosa kai yana murmusawa sannan ya sassauto da muryarshi ya ce,

“Ki bata nonon please, yunwa take ji.”

Bata amsa mishi ba ta saka yarinyar cikin hijabi amma sai ta kasa bata saboda bata iya ba kuma bakin nonon yayi ƙarami.

“Ka fita.”

“Ba kya son in ga nonon ne? Jay na ga abun da ya fi shi a jikinki.”

“Ka kuma kalli na last ba. Ka fita ko ka karɓeta kai ka bata”

“Nawa jarirai basa sha sai dai maman jarirai.” Ya yi maganar yana kyafta mata ido ɗaya.

Sai dai a maimakon ta yi murmushi sai ya ga ta haɗe ranta hawaye na taruwa a idanunta. Nan kuma ya sha jinin jikinshi yayi shiru yana kallonta ta ciro yarinyar a cikin hijabin ta buɗe nonon ta fara bata. Tana karɓa kuwa tayi shiru ta fara tsotsa hungrily kamar wacce ta fito da yunwa.

“Ya jikin naki? Da fatan babu wata matsala?”

Kai kawai ta gyaɗa mishi kana ta share hawayen fuskarta ta gyarawa yarinyar riƙon nata.

“Har yanzu fushi kike da ni ko? Ki yi haƙuri, idan mun koma gida zamu zauna mu yi magana tsakaninmu.”

“Wani gida kenan?”

“Gidanki, gidana.”

“Gidanka dai da ka koreni a ciki, kuma na faɗa maka ba zan koma ba wallahi. Ina takardata?”

“Ta tsire ko balangu?” Ya tambayeta yana mai ci gaba da kallonta.

“Muhammad don Allah kar ka ɓata mana lokaci don yanzu in ka sakeni bani da iddah ka ga kenan cikin ƙanƙanin lokaci zan samu in yi aurena.”

“Wa zaki aura?”

“Duk wanda Allah Ya kawo mini.” Ta amsa tana hararanshi.

“I missed conversing with you Jay.” Yayi maganar so calm kamar bai ji abunda ta gama faɗa ba.

“Ka bani takardata.”

“No. In kin gama bata nonon ki kirani a waya sai mu tafi. Na gode da kika kawo mini tsatsona duniya. Allah Ya miki albarka Ya kuma bamu ikon tarbiyyantar da ita. Na gode.” Yana faɗin hakan ya manna mata kiss goshinta na seconds uku sannan ya fice.

Juwairiyya kuwa bin shi tayi da ido har ya fice daga ɗakin hawaye na zuba a fuskarta. Da alama zata wahala kafin Muhammad ya saketa, kuma gidanshi da yake cewa ta koma ko sama da kasa ne zasu haɗu ba zata koma ba. Tana wannan tunanin su Sumayya suka dawo ɗakin waɗanda da alama da gangan suka basu privacy.

Baby tana komawa bacci ta zare nonon a hankali ta ga ko motsawa bata yi ba, da haka ta gyara mata riƙon tana jin cikinta na murɗawa wanda tun ɗazu take ji amma take daurewa kar a ga ragwancinta. Minti ɗaya da haka suka fara haramar tafiya aka taimaka mata ta sauƙo a hankali daga kan gadon, jinta take yi kamar a rarike kamar an cire mata wani nauyi, ashe nauyin da take ji a jikinta na Baby ne ta ɗauka kawai tsabar cin abincin da take yi ne ya jawo haka, ashe halittan mutum ne guda a ciki.

Har bakin mota ta taka da ƙafarta sai dai tana ganin motar Yayan Muhammad ne ta tirje ta ce ba zata shiga ba.

“Bana son shashanci Juwairiyya me haka?” Faɗin Mama tana kalle kalle kar ta tara musu jama’a.

“Mama wallahi ba zan koma gidanshi ba.” Ta faɗa tana yarfe hannunta tana jin kamar ta fashe musu da kuka don ta lura kwata kwata Muhammad bai ɗauki abun da ya mata da girma ba, gani yake yi da yace ta koma gidanshi zata taho da gudu ne ta shiga, bai san cewa ta haƙura da zaman gidanshi ba tun watan farko da tafiyarshi.

“Ba gidanshi za’a kaiki ba, gida zamu koma sai an miki shara da gyare-gyare kafin ki koma.” Mama ya bata amsa.

“Mama don girman Allah kar ki mini haka ki rufa mini asiri. Wallahi ba ya sona.”

Yanda tayi maganar sosai ya bawa Mamanta tausayi tayi shiru tana kallon Muhammad da shima jikinshi yayi sanyi wai duk wannan turjiyan saboda bata son komawa gidanshi ne? Wani irin mugun hali ya mata da ya cancanci haka?

“Babu mai miki dole Juwairiyya. Ki zo ki shiga gidanku zan kaiki kuma In shaa Allah ba zan takuraki ki koma ba har sai lokacin da kika huce.”

Magana ta ido Mama ta mata wanda yasa Juwairiyya isa bakin motar aka buɗe mata gefenshi tace bata so, dole Surayya ce ta shiga gaba ita kuma da Mama mai riƙe da baby da kuma Sumayya suka shiga baya, Muhammad jiki a sanyaye ya kunna motar suka fita daga asibitin zuwa gidansu.

Shi da kanshi ya sauƙe musu kayan da Mama ta sayo a kasuwa ya shigar musu cikin gida, a nan ya keɓance da Mama wacce ya nemi ta masa list ɗin abun da ake buƙata ya kawo, tare da kuɗin kayan da ta saya.

“Wanda dai na saya bana buƙatar a biyani saboda Juwairiyya ƴata ce, ita kuma waccar mai farar fuskar na mata alfarma in an kawo kayan aurenta zan cire a ciki.”

Wannan magana yasa ya ɗan sake jikinshi yayi murmushi tare da yiwa Mama godiya wacce tace zata tura mishi list ɗin ta text message, godiya ya mata ya tafi duk da cewa ya so ya ga Juwairiyya, sai dai da ya tuna zai dawo sai ya haƙura.

Ya kuke gani? Shin Juwairiyya zata koma gidan Muhammad kuwa?

Da ina tunanin na kusa gama littafin amma sai na ga akwai sauran Tafiya a gaba don haka ku biyoni a wannan Tafiyar ma’auratan wanda yake tangal tangal babu wanda ya san makomarshi (sai Mum Fateey).

TAFIYARMU

Awa uku Muhammad ya ɗauka ya dawo ƙofar gidansu Juwairiyya booth ɗin mota cike da kaya har da wanda ba’a aikeshi ba, so yake ya burge Juwairiyya ko zata sassauta ta dawo gidanta ba tare da an kai ruwa rana ba. Yara ya samu waje suka shigar mishi da kayayyakin cikin gida, sai da suka gama ya musu ihsani suka tafi suna godiya.

Yana tsaye minti ɗaya sai ga Surayya ta fito wacce dama ya aika a kirata.

“Assalamu alaikum Baban Baby, an ce kana kirana.” Ta faɗa bayan ta iso.

“Wa’alaiku mussalam. Eh, dama zan tambayeki ne ya suke?” Ya fara maganan da haka don zuwa anjima ya nemi ta mishi iso ya shiga.

“Suna nan lafiya kalau, an yiwa Baby wanka itama Adda Juwai tayi wanka har ta ci abinci ta sha magani.” Surayya ta mishi bayani.

Murmushi mai kyau Muhammad yayi domin ya lura zai shirya sosai da Surayya, da alama bata withholding information sannan ya lura tana respecting ɗinshi da kuma son ya kasance tare da yayarta, don a ɗazu da ya shiga ɗakin da suke asibiti ita ce ta girgiza Juwairiyya tana faɗa mata wai ga mijinta. He has a Fan, and he will use her to his advantage.

“To Masha Allah Auntyn Baby, da fatan dai kina kula mini da su?” Ya yi tambayar yana faɗaɗa murmushinshi wanda yasa itama ta ƙara nata kamar masu audition na tallen toothpaste.

“Sosai ma, ni na jidi ruwan zafi na kai banɗaki Mama ta mata wankan jegon.”

He laughed, Surayya kuma tsayawa tayi tana kallonshi kamar mai admiring ɗinshi tana mai cigaba da fara’a.

“Allah Ya sa dai bata yi kukan ruwan zafin ba, kin santa da raki.”

“A’a ai Mama ta barshi yayi lum lum sannan suka yi wankan.” Ta ƙara mishi bayani.

“To hakan yayi, Baby fa?”

“Itama Mama ta mata wanka, sai dai ana farawa ta fara kuka har aka gama bata daina ba. Amma yanzu tana bacci.”

“To ko zaki mini iso ina son shiga in gansu.” Ya faɗi ainihin abun da ya tsayar da shi.

“Eh to yanzu gidan a cike yake da ƴan barka ko zaka bari zuwa bayan isha kafin nan sun watse, in ka shiga yanzu zaka takura.”

Har cikin ranshi Muhammad ya ji daɗin maganarta sannan kuma ya yaba da hankalinta da kuma hangen nesanta. Ashe bayan surutun yarinya ce mai basira.

“Ai kuwa hakan yayi, bani numbernki anjima in sun tafi sai ki kirani.”

“Ai ina da numbernka zan maka flashing idan na shiga gida.” Ta faɗi hakan a kunyace.

“Shine kuma baki taɓa kirana muka gaisa ba? Gaskiya I’m offended.” Ya faɗi hakan yana mamaki sosai a ranshi, ashe ita har numbernshi take da shi.

“Ai baka mana dariya ne shi yasa, amma na ga tunda Adda Juwai ta haihu ka canja kuma kana dariya. Kuma don Allah kar ka yarda ka rabu da ita wallahi tana sonka don watarana har kuka take yi in ta zo bacci ta ɗauka ban sani ba. Kai kaɗai na faɗawa don ko Mama ban taɓa faɗawa ba, kuma please kar ka faɗa mata.”

Muhammad ji yayi wani abu ya zo ya toshe mishi makwoshi sannan ya kasa haɗiyewa, ji yayi kamar ya mayar da hannun agogo baya ya sakewa Surayya fuska domin a baya in banda gaisuwarta magana mai ƙarfi wannan bata haɗasu. He really fucked up!

“This will be our little secret, and In shaa Allah babu abun da zai faru.”

“To Allah Ya sa. Bari in shiga ciki, Mama ta sakani dafa Zabbin da ka kawo na mai jego. A ajiye maka zaka ci?”

Dariya Muhammad yayi yana kallonta sai yake ganinta kamar Juwairiyya amma wannan mai sauƙin kai ce mara masifa.

“Ki ajiye mini amma kaɗan don bana son in dawo luti kamar da, Juwairiyya zata ƙi komawa gidana.”

“Uhm ai ko yaya kake bana tunanin zata damu, kuma ka ƙara kyau yanzu. Sai anjima.” Tana faɗin hakan ta shige cikin gidan cike da kunya shi kuma ya bita da ido yana murmusawa da haka kuwa ya bar ƙofar gidan ya tafi gidan yayanshi kai mishi motarshi.

“Yace ka tafi da motar ka ƙarisa zirga-zirgan shi zai tafi da Kasea ɗinshi. Dama fa in ba family outing ko in zai fita da wasu ba bai cika fita da ita ba.” Faɗin Maman Nihal bayan Muhammad ya dawo da motar gidan yayan nashi.

“To shikenan.”

Da haka ya mata sallama ya tafi yana jindaɗi a ranshi domin ba ƙaramin taimaka mishi yayan nashi yayi ba, saboda a yanzu da ya dawo na ƴar gaɓa ɗaya kuma Salima ta ɓata mishi rai sai ya ji ba ya son fita da motarta kwata kwata. Ba ya son ta mishi gori idan ta ga ya ɗauka zai je gurin Juwairiyya tunda har shegantaka mishi ƴa ta yi, abun da yake bashi mamaki kenan matuƙa har yanzu ya kasa ganewa. Shin ko dai ita ma Saliman ta fara jin zugin mutane ne? In ba haka ba me yasa zata ƙaryata haihuwar Juwairiyya har ta ce wai satan na wata aka yi? Wannan ai banzar magana ce! Ita ta fi kowa sanin halin Juwairiyya ita ya kamata ta mata shaida kyakkyawa in dai a kan haka ne. Shi ko da aka faɗa mishi bai kawo kokonta a ranshi ba ko kaɗan saboda ya san kamun kan Juwairiyya, kuma ko da ƴar bata yi kama da su ba ya sani cikinshi ne kuma jininshi ce.

Salima kuwa tunda aka watse aka barsu ta gama kukanta ta share hawaye ta koma gefe ta kira mamanta ta sanar mata wannan baƙin labarin, Mamanta da mamaki ya kusan kashewa kasa magana tayi sai da ta ɗauki lokaci mai tsawo sannan ta ce,

“Idan kin samu dama kawai ki zo gida wannan ba maganar waya ba ce.”

Tana cire wayar a kunnenta ta ga shigowar saƙo daga gurin Fauziyya wai ta buɗe whatsapp ɗinta ta tura mata saƙo. Jikinta na rawa bakinta na addu’an Allah Ya sa jaririyar wata kala ce ta shiga whatsapp ɗinta ta buɗe hoton. Babyn sakk HJ a lokacin da shima yake jariri! Wani irin duhu ta gani dulummm ya zo ya tare mata ganinta sai can kuma idanunta suka washe zuciyarta kuma ta tsananta bugu kamar zata faso ƙirjinta. Ya aka yi Juwairiyya ta tafi da cikin wata bakwai amma bata sani ba? Wannan wani irin canjin al’amari ne? Kullum sai tayi kamar zata kori Juwairiyya sai kuma ta dawo da ƙarfin gaske! Me yasa ita ta kasa korar kishiyarta kwalli ɗaya takk alhali Mamanta ta kori biyar?

Kuka take son yi amma bata son ta ƙara yi a gaban waɗancan mutanen da suke tatsan information daga gurinta ɗazu, wanda suka ci sa’a a lokacin bata cikin hayyacinta  tayi ta zuba musu zance amma tun kafin a kai ko’ina har ta fara regretting, domin kuwa ta sani sai sun kai gaba. Wannan jazaman ne!

Kiran Muhammad ta sake yi a karo na huɗu wannan sa’in ya ɗauka ta mishi sallama ya amsa murya babu walwala.

“Dama na ga kowa ya watse ne nace ina so ka mini izini zan je gidanmu in kai musu kayan waliman.”

“Ki je.” Shine amsar da ya bata ya kashe wayar.

Salima rai na ƙuna hankali kuma a ɗage aka tayata tattara gurin suka saka a booth ta ɗauki ɗanta tare da sauran mutanen a cikin motarta akan zata ajiyesu a bakin titi ita kuma zata wuce gidansu.

Muhammad sai goshin maghrib ya koma gida ya samu Salima har ta dawo tana girki a cikin kitchen, tana jin shigowarshi ta fito tana mishi sannu da dawowa ya amsa fuska a ɗaure ya shige ɗaki. Alwala kawai yayi ya fita masallaci sannan sai da ya jira aka yi isha sannan ya dawo gida ya sameta ta gama girkin tayi wanka tana jiran dawowarshi.

“Baban Hafiz ga abinci.” Salima tace dashi tana mai miƙewa tsaye daga zaune.

“Sai na dawo zan ci.” Yana faɗin hakan ya shige ɗaki.

Bin shi tayi don ta bashi haƙurin abun da ta aikata yau amma sai ta samu ya shiga wanka, a bakin gado ta zauna tana sauraron motsin HJ da ke falo yana homework.

“Baban Hafiz dama ina son baka….” Salima ta fara magana bayan ya fito amma yayi saurin taran numfashinta ya ce,

“Save it, ba yanzu ba.”

Da haka tayi shiru tana bin shi da kallo har ya gama shiryawa cikin manyan kaya kamar mai zuwa hira, ai kuwa a nan ne cikinta ya murɗe da ta fahimci me yake nufi ɗazu, wato fita zai yi? Ita ta ɗauka yana nufin sai ya dawo falon ne zai ci abincin ashe ba haka yake nufi ba. Ai kuwa nan ta ji zuciyarta na Ƙara mata zafi tana jin numfashinta kamar zai ɗauke sannan huɗuban mamanta na neman kuɓuce mata domin a yanzu kishi da azaban da take ji a zuciyarta ya hanata tuna karatun.

“Ina zaka je?” Ta tambayeshi wannan karon babu wannan sanyin muryar.

“Gidansu Juwairiyya.” Ya bata amsa a taƙaice yana fesa turare a jikinshi.

“Nima zan je.” Ta faɗa don kawai ta je a yi komai a gabanta.

“Me yasa ɗazu baki je ba?”

“Na kiraka baka ɗauka ba.”

“Daga baya da kika kirani na ɗaga fa? Me yasa baki tambayi zaki je ba amma kika iya kika tambayi zuwa gidanku? Wato har yanzu kina kan bakanki ƴar ba tawa ba ce ko? Wallahi kin bani mamaki, da wani ne ya faɗa mini ke kika furta waɗanɗan kalmomin a kanta da ba zan yarda ba, ashe da ke da ita ɗin duk baku iya bakinku ba. Na ki sai ya fi nata muni da kika jefeta da ƙazafin satan ƴaƴan mutane. Wallahi I’m disappointed.”

“Wallahi…” Ta fara magana ya ƙara dakatar da ita.

“Ba zan saurareki ba sai na dawo.”  Yana faɗin hakan ya nufi ƙofa ta biyoshi zuwa falo.

“Ki canjawa yaron kaya zamu tafi tare, ya sameni a waje.”

“To ni fa?” Ta ƙara tambayarshi kamar zata yi kuka.

“Gobe ki je.” Ya fice ya bar Salima hawaye na kwaranya a fuskarta.

Sai yanzu take jin baƙin cikin me yasa ita bata koya mishi masifa ba? Ai da wallahi ko sama da ƙasa ne zasu haɗu ba zata bari ya tafi ba balle ya ɗaukan mata ɗa su je hira. Amma ita ta koya mishi sanyin hali dolenta ta ja HJ wanda tun da ya ji an ce a canja mishi kaya ya daina abun da yake yi yana kallonta expectantly kuma cikin zumuɗi.

A garin shiryashi yake tambayarta wai ina zasu je ta shareshi sai kuma ya ci gaba da damunta har bata san lokacin da ta gaura mishi mari ba sai da ya kife ƙasa, daidai nan kuma Muhammad ya shigo kenan ganin sun jima daga canja kaya kawai ya ga wannan ɗanyen aikin da Salima tayi wanda ko shi uban zuciya bai taɓa marin yaron haka ba.

“Ke baki da hankali ne?” Ya faɗi hakan cikin ƙaraji sannan ya taho a sukwane ya kwashi yaron a hannunshi wanda yayi wata ƙara sau ɗaya sai kuma yayi shiru kamar wanda ya suma.

Jijjigashi ya fara yi yana kiran sunanshi yana tsayar da fuskar yaron wacce take tangal tangal kamar ta ƙarye tsoro da fargaba cike taff a cikin ranshi.

“Hafiz, Hafiz, kai buɗe idanunka.” Ya faɗi hakan yana fita da shi falo Salima ma da ta kiɗime ta tsorita da yanayin yaron ta biyosu tana neman karɓanshi Muhammad ya danna mata wata muguwar kallo ya ce,

“Wallahi kika sake kika taɓashi sai na miki abun da ya fi wanda kika mishi.” Da haka kuma ya mayar da dubanshi kan yaron wanda yake ajiyar zuciya lokaci ɗaya kuma ya fashe da gigitaccen ihu dama ya iya balle na yanzu mai dalili.

“Wayyo Allah na.” Ya faɗa yana riƙe ƙuncin da aka mareshi Muhammad na rarrashinshi yana kuma jijjigashi.

Ita kuma Salima kuka take yi wanda ta fara tun ɗazu tana daga can gefe tana kallonsu tana bawa Muhammad haƙuri.

“Wallahi ban yi niyyan marin yayi ƙarfi haka ba, don Allah kayi haƙuri. Ka bani shi in dubashi.”

Bai kulata ba ya fice daga falon har waje inda ya ajiye mota ya saka HJ wanda ya daina ihun sai kuka kawai yake yi har ya ɓata gaban rigarshi da hawaye da kuma majina. Da haka Muhammad ya ja motar suka bar Salima a bakin gate tana bashi haƙuri amma bai saurareta ba.

Sai da suka hau titi ya faka a gefe ya zari tissue ya fara goge mishi fuskarshi yana kuma bashi haƙuri, wai me yake damun Salima yau? Gaɓaɗaya ta canja sai fito da hali daban daban take yi. Kishin nata har ya kai ta kashe ɗan cikinta? Wannan marin ko babba aka yiwa sai ya gigice balle yaro ƙarami irin HJ. Ashe zata iya aikata halaye irin wanda ta nuna yau? Wai ita ce kuwa?

Da wannan tunanin ya isa gurin sayar da Ice cream ya sayawa HJ wanda sai a lokacin ya ga yanda yatsun Salima suka kwanta akan ƴar ƙaramar fuskarshi yayi jaaa sosai har yayi kamar zai yi maroon. Ranshi na ƙuna ya isa inda ake sayar da tsiren da Juwairiyya ta fi so, a nan ya sayi mai yawa ya kama hanyar gidan da HJ a gefenshi wanda ya bar kuka yana shan ice cream yana kuma ajiyar zuciya akai akai.

Yana isa ya kira Surayya wacce tun ɗazu ta mishi flashing ɗin ya ga numbernta sannan ya aika mata da katin dubu biyu. Ta kirashi tana godiya ya ce babu komai.

Sai da ta fito ta gaisheshi sannan ta mishi iso wanda ya ɗauka falon Mama za’a sauƙar dashi amma sai ya ga an wuce da shi wani ɗaki da yake tsammanin nan ne na Juwairiyya.

A bakin gado ya sameta tana shan kunu a kofi wanda ganinshi da tayi a kanta yasa ta kware ta fara tari tana kallonshi kamar bata gaskata shi take gani ba. A nan ne ya gane Surayya bata faɗa mata yana zuwa ba, and he will thank her for that.

“Ina ta sallama baki amsa ba.” Ya ce da ita yana mai zama a kan 2sitter ɗaya da ke cikin ɗakin ya jawo HJ ma gefenshi ya zauna. Kallon ɗakin yayi sai ya bashi sha’awa domin babu tarkace ko kaɗan ko’ina tsaftsaf sai tashin turaren wuta kawai yake yi ga can kuma ƴar shi cikin Baby mosquito net da alama baccinta take yi.

“Wa’alaiku mussalam.” Ta amsa ciki-ciki tana hararan Surayya da ke ajiye mishi tray a gabanshi mai ɗauke da kula ɗaya da plate sai ruwan gora da cup.

“Ga ferfesun na ƙara ɗuma maka.” Ta ce dashi kamar shi ya ce tayi hakan.

“Ina zan sa kaina in babu Surayya a gidan nan? To nagode kwarai. Ga wannan ki kaiwa Mama.” Ya miƙa mata ledojin hannun nashi ta ƙarɓa tana godiya ta fita bakinta har kunne.

Da ido kawai Juwairiyya ta bi Surayya a ranta kuma tana cewa ‘Traitor’ don yanda take kauɗi kamar saurayinta ne ya zo. Sai a lokacin ta dubi HJ da yake gefen Babanshi ta miƙa mishi hannun alamar ya zo sannan ta ce,

“Ina wuni.”

“Lafiya kalau. Ya jiki? Kuma ya baby?”

“Alhamdulillah. Mallam Hafiz zo mu gaisa mana.”

Sai a lokacin ya taso ya zo gurinta yana ɗan murmusawa kaɗan.

“Subhanallahi, me ya sameshi haka a fuskarshi?” Juwairiyya ta faɗa tana mai dubawa da kyau hankalinta har ya tashi.

A nan ta ga yatsu guda huɗu wanda babu tantama ta san Muhammad ne, baƙin ciki da kuma tsoro ne ya shiga ranta da ta tuna wai itama haka zai daki ƴarta wata rana. Har ta buɗi baki zata fara azalzalarshi ya ce,

“Mamanshi ne ta mareshi.”

Wannan yasa ta kame bakinta kana ta kalli Muhammad ɗin wannan karon cikin ido, a nan shi kuma ya gane kamar bata yarda da abunda ya faɗa ba, hakan yasa ya ji babu daɗi a ranshi amma sai ya buɗi baki ya ce,

“Muhammad Hafiz wa ya mareka?”

“Mummy ne.” Ya bada amsa hawaye na taruwa a idanunshi.

“Me ka mata haka Hafiz? Baka jin magana ko?” Juwairiyya ta tambayeshi tana mai jin kamar ta zubar mishi da hawaye.

Girgiza kai yayi hawaye na sauƙowa kan ƙuncinshi yace,

“Ina ta tambayanta ina zamu je da Daddy ta mareni.”

“Kayi haƙuri ka ji? Sorry.” Ta ce dashi cike da tausayawa sannan ta zaunar dashi a gefenta kana ta buɗe net ɗin baby ta cirot ta ɗaura mishi kan hannunshi ta ce,

“Ka zama big brother, ga ƙanwarka nan.” Ta faɗa cheerfully Muhammad na gefe ya zuba musu ido kawai yana ganinsu.

Na so page din ya fi haka tsayi amma dare yayi. Ku yi manage.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

“Me sunanta.” HJ ya tambaya yana washe bakinshi har kunne, da alama sosai ya ji daɗin da aka ce ya samu ƙanwa.

“Sunanta Baby for now, amma gaba za’a saka mata suna.”

“A saka mata irin sunana.” Ya faɗa a kunyace yana kallon fuskar yarinyar wacce baccinta kawai take yi abunta.

Dariya Juwairiyya ta yi sannan ta ƙarɓeta ta miƙawa Muhammad wanda ya taso ya zo kansu sannan ya koma kan kujera ya zauna yana dubanta tare da gyara bargon da aka lulluɓeta da shi.

“To ai kai sunan maza aka saka maka, ita kuma mace ce, sunan mata za’a saka mata.”

Gyaɗa kai yayi bai ce komai ba ya koma gurin Babanshi ya tsaya a kanshi yana kallon Baby da alama bai gaji da riƙonta ba aka karɓeta.

“Wani suna kike so a saka mata?” Juwairiyya ta jiyo tambayar Muhammad a bazata wanda yasa ta ɗago ido ta kalleshi ta ga shima ita yake kallo.

“Duk wanda kayi niyya.” Ta bashi amsa tana mai kawar da idanunta gefe.

“Zaɓi na baki. Ki zaɓi kowanne suna in dai mai ma’ana ne zan saka mata.” Ya faɗi hakan sincerely wanda hakan ya bawa Juwairiyya mamaki ya kuma sa ta ji daɗi har cikin ranta.

“Ka mayar da sunan Mamanku.”

Shiru ta ji Muhammad yayi wanda hakan yasa ta ɗago idanunta ta kalleshi, murna, farin ciki da kuma gratitude ne kwance a fuskarshi tare da wani abu mai kama da so, in bata yi ƙarya ba kenan.

“Are you sure? A saka mata Aisha?” Ya tambayeta kamar wanda yake tsoron anjima zata canja ra’ayinta.

“Eh.”

“To nagode da wannan karamcin da kika mini. Allah Ya sa ta ɗauko halin mai sunanta kyawawa.”

“Ameen.” Ta amsa tana mai wasa da yatsunta.

“Ɗaukemu a hoto.” Ya miƙa mata wayarshi sannan ya jawo HJ gefenshi suka dubi camera suna murmushi.

Juwairiyya da hannunta yake rawa kaɗan ta ɗaukesu a hotuna uku sannan HJ ya matsa gefe Muhammad yayi shi da Baby kaɗai sannan ya ce,

“Ke ma ki zo mu yi.”

Girgiza kai Juwairiyya tayi kana ta miƙawa mishi wayarshi ta koma ta zauna a hankali, sai a lokacin Muhammad ya lura da yanayin tafiyarta wanda ya tuna mishi da wani tafiyarsu Abuja ya ce,

“Kin samu tear ne?”

“Eh.”

“I’m so sorry, Allah Ya baki lafiya.” Ya faɗa cikin tausayawa.

Sai a lokacin Muhammad ya yiwa Baby huɗuba tare da kira mata sunanta a cikin kunnenta kamar yanda sunnah ta koyar sannan ya miƙata ga Juwairiyya wacce ta mayar da iya cikin net ta rufe.

A nan kuma Surayya ta musu sallama ta shigo hannunta ɗauke da Plate cike da tsire sai tiriri yake yi yana ƙamshi da toothpick a ciki. Sai kuma wani bowl cike da fruits kala uku na kankana, ayaba da kuma lemo.

“Adda Juwai wai gashi in ji Mama wanda Baban Baby ya kawo.”

“Ba yanzu zan ci ba.”

“Bani zan bata.” Muhammad ya miƙa hannunshi Surayya ta danƙa mishi plates ɗin ta fice.

“Don Allah duk fushinki da ni idan na kawo miki abu kar ki ce ba zaki yi amfani da shi ba Juwairiyya, haƙƙinki ne kuma nayi.”

Shiru tayi na wasu seconds wanda har cikin ranta tana son ci ɗin amma bata son yi a gabanshi ne, sannan ba wai fushin da take mishi ne yasa ba zata ci ba.

“Bani.” Ta miƙa hannunta ya bata su ta ajiye a gefenta sannan ta yafuto HJ ya zo suka fara ci tare.

“Kin koyi rowa, ni ba za’a mini tayin bane?” Muhammad ya tambayeta yana mai komawa jikin kujera ya lafe yana kallonta.

Ita kuma Juwairiyya a takure take jinta dalilin zuba mata idanunshi da yayi yana kallon duk motsinta, every bite, every swallow kamar mai ɗaukan hoton haka a kwakwalwarshi, Allah Ya taimaketa naman yana da taushi sosai don haka bata kokawa da shi balle ta ji kunya.

Bata kulashi ba don ta san tsokanarta yake yi ta jawo musu bowl ɗin fruits suka fara sha. Shi kuma Muhammad wayarshi ya ɗauko ya fara dannawa har suka gama sannan ya duba ya ga tara da rabi ya ce zasu tafi. Juwairiyya ta kira Surayya akan ta zo ta wankewa HJ bakinshi, da haka kuwa ta ja hannunshi suka fita tare. Sai a nan Muhammad ya taso ya zo ya zauna kusa da ita a kan gadon amma ta tashi da niyyar barin gurin yayi saurin riƙota ta zauna a hankali.

“Don Allah don’t make this harder than it already is. Please.” Ta faɗi hakan tana kawar da kanta gefe hawaye na taruwa a idanunta.

Shiru yayi yana riƙe da hannunta bai ce komai ba, sai da ya ji motsin su HJ suna shigowa sannan ya miƙe tsaye yana cewa,

“Me na miki kika tsaneni Juwairiyya? Me kuma zan yi ki haƙura ki koma gidanki?”

Har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta fasa ganin su Surayya na sallama a bakin ƙofa, shi ya amsa musu suka shigo kana ya ɗauki kulan ferfesu ya bawa HJ a hannu yana cewa,

“Auntyn Baby zan tafi da kulan ferfesun gida in sha a can. Juwairiyya sai da safe, Allah Ya baki lafiya.”

“Amin.” Ta amsa a hankali sannan ta yiwa HJ bankwana suka fita Surayya ta karɓi kulan hannunshi ta rakasu har bakin mota suka tafi.

Juwairiyya sai da ta tabbatar sun fice daga gidan sannan ta bari hawayen idanunta suka sauƙo kan ƙuncinta, bata san tana son Muhammad mai tsanani ba sai da ya zauna kusa da ita, ji tayi kamar ta riƙeshi kar ya tafi ya zauna tare da ita har abada, sai dai wannan tunanin ne ya ankarar da ita ta gane cewa muddin ta bari ya shawo kanta to dolene ta koma gidanshi, hakan kuma na nufin ta koma zama da Salima da shi karan kanshi wanda yake ganin matar tashi a matsayin wacce bata taɓa yin laifi. Zamansu ba zai yiwu ba, za’a yi ta kwaranta ne ita ta sani balle yanzu da Saliman ta fitar da maitanta a fili, shi kuma ko kwana dubu zata yi tana faɗa mishi halin matar tashi ba zai yarda ba saboda ya yarda da ita. Abun da ya fi zama musu alkhairi shine su rabu ba tare da ɗayansu ya cutu ba.

Tausayin ƴarta ce ya ɗarsu a ranta da ta kalleta, shikenan haka zata rayu tare da mamanta, kuma ba tare da babanta ba? Da ire-iren wannan tunanin ta tashi ta shiga banɗaki ta yo brush ta kama ruwa sannan ta fito ta samu Surayya ta kwashe duk abun da suka ɓata sannan ga Mama na zaune tana jiranta.

“Juwairiyya ya jikin dai?” Mama ta tambayeta.

“Alhamdulillah yanzu ko zafin gurin bana ji.” Ta amsa mata tana mai zama a bakin gadon.

“To Allah Ya ƙara miki lafiya. Kun yi magana ne dashi?”

Girgiza kai kawai tayi Mama ta bita da ido tana kallonta cike da tausayawa, ko da wasa ba zata so ƴarta ta rabu da mijinta ba amma tana jiye mata zaman auren da zata yi babu kwanciyar hankali kuma mai cike da munafurce-munafurce. Kuma da shi mijin ya gane halin matarshi za’a samu sauƙi saboda duk abun da ya faru gaba zai yi bincike sosai ba zai yi shari’a base on halayyan matanshi da yake tunanin ya sani ba.

“Kar ki nemi saki a gurinshi Juwairiyya don abun bai kai haka ba, mata da dama suna zaune da kishiyoyi waɗanda suka fi taki iya makirci amma basu raba aurensu ba. Idan zai yiwu ki lallaɓashi ya raba muku gida wanda yin hakan zai rage kaso mai yawa na samun matsalarku saboda baku haɗu ba ma balle tace kin yi mata laifi. Ni dai har cikin raina ina son zamanku tare duk da cewa shima da laifinshi, amma mazan ne duk haka suka zama kowa da matsalarshi sai an yi haƙuri an kai zuciya nesa sannan za’a iya zama da su. Na lura kina son mijinki shima yana sonki, a yanzu da yake marmarinki yana lallaɓaki ki samu ki zauna dashi ku fahimci juna ki faɗa mishi duk abun da bakya jindaɗinshi da yake yi ko matarshi. Ki bi komai a hankali kuma cikin wayo da dabara in Allah Ya yarda zaki samu canji.”

“To Mama.” Shine kaɗai abun da Juwairiyya ta faɗa amma canjawan Muhammad sai ƙarfin ikon Allah domin Salima ta gama ɓatashi ta yanda da ta nemi canjashi zai ce tana da taurin kai ne da kuma rashin haƙuri. Da alama su sun manta duk abun da ya faru ne amma ita tana sane da every detail da kuma emotion na rayuwarta a gidan Muhammad tare da kishiyarta Salima.

“Kika ce ba zaku koma ɗakina ku kwana ba ko? Kar ta tashi da dare tayi ta kuka fa, don kin san wasu yaran haka suke da kukan dare.” Mama ta tambayeta tana mai tashi tsaye.

“Zamu biyoki kawai don in ta fara kuka ban san ya zan yi ba.”

Da haka Mama ta ɗauki baby Surayya ta bita da net ɗinta aka bar Juwairiyya na ɗaukan abun da zasu buƙata a cikin daren kamar su sutura, diapers, da kuma wipes. Cikin ikon Allah har aka wayi gari baby bata yi kukan dare ba sai tashi shan nono da tayi sau biyu.

Washe gari da hantsi Juwairiyya na ɗakin Mama suna hira Salima ta shigo gidan da sallamarta fuska ɗauke da fara’a kamar ita aka yiwa haihuwar. Surayya da take tsakar gida tana aiki a kitchen tana ganinta ta sha murr ta amsa mata sallamar.

“Surayya ƴan mata, yanzu kam saura kema ki shige daga ciki, kin gama makaranta ko?”

“Eh.” Ta bata amsa.

“Ina mai jegon take? Kai na ƙagu in ga sabuwar babynmu.” Ta faɗa tana mai gyara zama jakarta.

“Tana ɗakin Mama, mu je.” Da haka Surayya tayi gaba Salima ta bita a baya har falon Mama sannan tayi hanyar shiga ɗakin ta ga Saliman ma ta biyota ta dakata ta ce,

“Ki tsaya a falo bari in kirata.” Tana faɗin haka ta shige ta bar Salima wacce tana bata baya ta danna mata harara kana ta samu guri ta zauna.

A cikin ɗaki kuwa tun sallamar Salima na farko da Juwairiyya ta ji sai da zuciyarta ta tsinke ta kalli Mama wacce Itama ta yi kasaƙe tana saurara.

“Mama me ya kawota? Don munafurci ina gidan namu ma baza ta barni ba sai ta zo inda nake? Tunda na bar mata gidan nata uban me kuma zata zo ta mini?” Juwairiyya ta faɗi hakan a fusace da alama ranta ya ɓaci ba kaɗan ba.

“Ɗaɗina da ke kenan, bakya bin abu a hankali, ki nitsu ki saurareni. Ki cire duk wani ɓacin rai ki tarɓeta ku rabu lafiya, dama done ne ta zo tunda haihuwa kika yi kuma ba rabuwa da mijin naku kika yi ba. Kina ji na?”

Gyaɗa kai Juwairiyya tayi kana ta ɗauki ɗankwalinta ta kafa a nan kuma Surayya ta shigo tana cewa,

“Adda Juwai ga kishiyarki a falo ta zo ganin Baby.”

“Ki ce mata ina zuwa.” Ta bata amsa tana mai tsayawa gaban mirrow tana adjusting rigarta har da shafa vaseline a baki.

Duban kanta tayi ta ga ta haɗu musamman yanzu da take jego sai ƙirjinta ya ƙara cikowa, tumbi kuma babu shi kamar ba haihuwa tayi ba. Da haka ta fice ta bar Mama na canjawa Baby Diaper.

Tana ɗaga labule ta sanyawa fuskarta murmushi tana ganin yanda Salima ta bita da kallo daga sama har ƙasa mask ɗin fuskarta kuwa yana slipping kaɗan daga murmushi zuwa mamaki da haushi. Da alama bata so ganinta cikin ƙoshin lafiya haka ba, ta so ne ta ganta a rame a ƙanjale kamar kwanaki da depression ya sakata a gaba.

“A’ahh Maman Hafiz ke ce? Ai har nayi fushi da ban ganki tun jiya ba.” Faɗin Juwairiyya tana mai neman gurin zama ta zauna.

Yaƙe Salima tayi sannan ta buɗe bakinta ta ce,

“Ai jiya da kika kira batun haihuwar muna can gurin Waliman gama makarantarshi to sai aka barni a gurin da tattare kaya. Ina babyn take?”

“Ayya to na miki uzuri. Baby ana canja mata diaper. Kun zo lafiya?”

Nan suka gaisa sai kuma ga Mama ta fito da jaririya, Salima tana ganinta ta sauƙo daga kan kujerar ta gaisheta Mama ta amsa cikin fara’a har da saka mata albarka sannan ta miƙa mata baby ta fice tsakar gida don ganin girkin da Surayya ta ɗaura.

“Kai Masha Allah. Baby kyakkyawa kamar babanta.” Faɗin Salima tana mai kallon yarinyar.

“Ai kuwa ta ɗauko kyau, har nake tsokananshi na ce kai kam ka mana wayo, yara duk sunyi kamanninka.”

Wannan magana yasa murmushin Salima ya suɓuce ta dubi Juwairiyya da kyau kamar bata gaskata zancenta ba. Sai can kuma ta ƙaƙalo murmushi ta ce,

“Na ɗauka ai tunda ya dawo zaki dawo gida kema, gashi yanzu kuma kin haihu maimakon ki je kiyi jegon a can sai kika zauna a nan kina wahalar da Mama.”

“Ai ko na koma zan dawo wankan jego, to wannan zuwa da dawowan ne naga zai yi yawa.”

“Wallahi da bakya nan gidan babu daɗi kullum sai nayi niyyar in kiraki sai in ce kar ki ce gulma ne yasa haka.”

“Gulma kuma na menene?” Juwairiyya ta tambayeta kamar bata san me take magana a kai ba.

“To dai bana son zurfafa maganan ne amma ai mun san dawowanki gida ba haka banza ba akwai abun da ya faru tsakaninku.”

“Shi ya faɗa miki mun samu matsala?” Juwairiyya ta ƙara mata wata tambayar tana mai gyara zamanta don ta lura Salima ƙarfi da yaji take son ta tunzurata amma bata san yanzu ta wuce wannan level ɗin ba.

“A’a kawai na lura da hakan ne, don kin fita da sassafe babu sallama sannan da na mishi maganan ya hau ni da faɗa wai kar in sake kawo mishi maganarki.”

Dariya Juwairiyya tayi har da rufe baki kana ta tsagaita ta ce.

“Oh maza! Abun da ya faɗa miki daban abun da ya faru daban.”

Wannan magana ya jawo curiosity ɗin Salima wacce ta matso gaba kamar zata zamo daga kan kujerar har Juwairiyya ta fara damuwa kar ta jefar mata da ƴa ta ce,

“Me ya faru don Allah, don ni gaba ɗaya kun sakani a ruɗani na rasa gane me yake faruwa.”

“Yoo ni na isa in yi magana in ƙaryatashi? Ai duk abun da ya faɗa miki ki ɗaukeshi shine gaskiya, babu ruwana nikam.” Juwairiyya ta faɗi hakan tana darawa kamar bata da damuwar komai a duniya. Da alama tana jin daɗin wasa da hankalin Salima.

Shuru Salima tayi tana murmushin da bai kai zuci ba, a nan kuma ta fara nemo abunda zata faɗa, sai can ta ce,

“Jiya kuwa yace mu zo tare na ce mishi sai yau, ai ya fi in zo da rana akan da dare.”

“Da kin yi zuwa biyu ai, kai da naka! Hafiz kuma ya zo da shatin mari a fuskarshi, ni na ɗauka ma wani mai aikin dako ne ya mareshi sai yace wai ke ce da ya dameki da tambayar ina zai je da Babanshi kika mareshi. Nace to duk yanda aka yi a lokacin ranki a ɓace yake don na san baki da saurin hannun bakya kuma son dukan yaro haka banza. Nace mishi kar ya ƙara tunzuraki idan ranki ya ɓaci.” Duk wannan magana da Juwairiyya tayi idanunta na cikin na Salima wacce a kowanne second murmushin fuskarta na raguwa kamar ana sace baloon.

“Uhm, an ɗan ɓata mini rai ne wallahi sai da na dokeshi nima na ga yayi yawa.”

“Ai yara sai ana kai zuciya nesa, in rai kuma a ɓace yake ba’a hukuntasu in ba haka ba za’a dawo ana regretting daga baya.” Juwairiyya ta ƙara yaɓa mata magana mai harshe biyu.

“Bari in koma gida zan je in ɗaura girkin rana kar maigidan ya zo ya samu ba’a gama ba.” Faɗin Salima tana mai miƙewa tsaye ta isa gaban Juwairiyya ta bata baby.

“Haba daga zuwa sai tafiya? Ni fa na ɗauka yini zamu yi.”

“A’ah wallahi, sai dai wani jiƙon.”

“To Allah Ya kaimu, muna zuba ido. Ki gaishe mini da Mallam Hafiz, ko da yake ma ashe anjima zai rako Babanshi kallon Baby.”

Da haka suka yi sallama Salima ta basu ledan da ta kawo mai ɗauke da onesies guda biyar da diaper da wipes, Juwairiyya ta mata godiya ta musu sallama ta fice daga gidan rai na ƙuna.

“Juwairiyya yaushe kika koyi bariki haka?” Mama ta kwashe da dariya da Juwairiyyan take bata labarin yanda suka yi.

“Wallahi gani nayi in ba haka na mata ba ni zata kashe da haushi, wallahi in ni ce ita ba zan zo har gidan mutane ina musu makirci ba, ita na lura ko kunya bata ji balle tsoron Allah.”

“To dai ni ƙaryan nan ne bana sonshi, kar garin neman gira a rasa ido. In abu bai faru ba kar ki ce ya faru ko da ba abun ƙi bane, ki iya takunki domin kuwa ko da zallar gaskiya zaki iya beating ɗinta at her own game.”

“Wallahi abun nata ne yana yawa shi yasa.”

“Ni dai na faɗa miki bana son ƙarya. Wannan yarinyar na rasa a ina ta koyi wannan hali nata.”

“An ce daga gurin Mamanta ne, ta kori kishiyoyi biyar. To yanzu ina ganin Baban nata ya gaji da aure-auren ne don har yanzu ita kaɗai ce a gidanta.”

“Kai mutane kuma akwai su da zuzuta abu, wataƙila kuma shi mijin ne ba ya shiryawa da matan shi yasa suke rabuwa aka ƙaƙabawa matarshi.”

“Mama in ba don ke Mamata ba ce wallahi sai in ce goya musu baya kike yi.” Faɗin Juwairiyya tana turo baki kaɗan don gwatsaleta da ake yi yayi yawa.

“Hakan shi ake kira da kyakkyawan zato ga kowanne bawa, ta yanda in an maka abu na alkhairi ba zaka yi saurin condemning ɗinshi ba hakan kuma zai sa zuciyarka ta kasance at peace saboda baka bin kowa da negetive thoughts untill proven otherwise.”

Yau ma da dare Muhammad ya zo hira wannan karon shi ɗaya, bai jima ba ya tafi domin bai samu fuskar Juwairiyya kamar na jiya ba. Haka washe gari ma ya sake dawowa daga gaisuwa bata ƙara mishi magana sai dai in ya tambayeta abu game da lafiyarta ko ta baby shi ne zata bashi amsa amma hira ne bai samu ba balle wasa da dariya ko nuna soyayya.

A hakan bai daddara ba har aka yi kwana huɗu da haihuwa wannan karon ya zo da HJ tunda ya lura idan ya zo da shi Juwairiyya na sakewa tayi hira dashi, shi kuma yana gefe riƙe da baby yana kallonsu.

“Saura kwana uku bikin suna kuma baki ce komai ba.” Faɗin Muhammad minti biyar da zuwanshi.

“Ba zan yi sunan ba ne.”

“Me yasa ba za’a yi taron sunan ba?”

“Kawai na ga ɗawainiyan ya maka yawa ne.”

Murmushi yayi mai ƙayatarwa kana ya ce,

“Ni na ce miki ba zan iya ba? Ki faɗa mini duk abun da kuke buƙata zan yi iya ƙarfina.”

Da haka suka rabu akan zata yi list ta tura mishi. Washe gari tun da rana ya aiko Iyami da kayayyakin tare da kayan mai jego da baby a cikin akwati babba. Juwairiyya tana gani ta gane cewa Muhammad ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba nan ma a hakan bata saka wasu abubuwan ba akan zata yi da kanta don ta rage mishi ɗawainiyan.

Tun ranar da Salima ta je sau ɗaya bata sake zuwa ba har ana gobe suna, hakan kuma ya samu asali ne da Muhammad ya hanata zuwa ya ce sai suna akan wasu dalilanshi da bai faɗa mata ba. Haka kuma ta so ta samu ƙarin bayani a gurinshi kan tafiyar Juwairiyya gida amma duk kissarta haka ta haƙura ta barshi don ya ƙi faɗa mata komai.

Ranar suna yarinya ta ci sunan Maman Babanta wato Aisha, wanda hakan ya yiwa su Iyami da sauran dangin Muhammad na gurin uwa daɗi matuƙa.

Juwairiyya ta sha kyau a ranar, domin kuwa mai make up guda aka ɗauko ta mata simple yet elegant kwalliya, kaya kuwa har kala uku ta ɗinka na alfarma don bikin suna ita da take cewa baza tayi ba.

Da hantsi Muhammad ya kirata wai in ta gama shiryawa ana zuwa a ɗaukesu a hoto ta nuna bata so, bai ƙara minti talatin da maganar tasu ba ya taho tare da photographer ɗin suka ɗauki guda uku tare dashi da ita da kuma BabyAisha, sannan ya tafi ya barta ana mata da sauran ƴan’uwa da abokan arziƙi. Sai azahar Salima ta iso wanda hakan ya bawa Juwairiyya mamaki matuƙa amma bata ce mata komai da rashin zuwan nata da wuri ba. Haka aka yi shagalin suna cikin walwala da da wadata, an ci mai kyau an sha har da masu guziri domin itama Juwairiyya sake bakin aljihunta tayi ta ƙara ƙayatar da bikin ɗiyarta da take ta addu’a Allah Ya bata. Haka kuma har aka watse daga ita har Salima babu wacce ya cakali ɗaya da maganar banza, sai dai ta lura kamar akwai wani abu da ya faru don ta ga mutumiyar tata jikinta a sanyaye kamar akwai damuwa a tatttare da ita.

Da daren sunan Muhammad bai zo hira ba kamar yanda ya saba saboda ya san Juwairiyya ta gaji kuma babu mamaki a samu sauran ƴan biki da basu tafi ba. Hakan yasa washe gari tun bayan maghrib ya ɗauko HJ suka kamo hanyar gidan, a nan ne kuma ya tsaya gurin mai sayar da fruit don ya saya mata HJ ya mishi tambayar da ya tono garma.

“Daddy me suke ci a can?” Ya nuna wani ɗan rumfar Mai shayi inda maza ke zaune a ciki suna cin indomie da kwai.

“Indomie suke ci da kuma shayi.” Ya bashi amsa yana mai ƙarɓan ledan da mai fruit yake miƙa mishi.

“Irin wanda Uncle Salim yake sayowa Mummy?” Ya sake tambayar uban a lokacin da suke tafiya zasu shiga mota.

“Shayin ake sayo mata?” Shima ya mayar mishi da tambaya cikin mamaki yau wani irin kwaɗayi take ji da zata sayi shayi a waje.

“A’a indomie dai. Ana saka egg da cabbage muna ci. Kullum idan na cewa Mama ta dafa mana sai ta ce ka hanamu kuma kar in faɗa maka muna ci.”

Shiru Muhammad yayi kwakwalwarshi na juyawa domin yanzu abubuwan sun fara mishi yawa, daga haihuwan Juwairiyya zuwa yanzu ya ga kuma ya ji abubuwa da yawa game da Salima wanda suke bashi matuƙar ciwon kai. Har sun shiga mota sun fara tafiya ya juya ya koma gurin mai Indomie ya tambayi HJ ta yaya ake musu ya faɗa, a nan ya gane soyeta a ke yi da kwai. Minti kaɗan da haka aka gama aka saka mishi a leda HJ ya karɓa yana jindaɗi suka nufi gidansu Juwairiyya ana kiran sallahn isha. Muhammad bai iya shiga ba ya kira Surayya ya bata fruits ɗin tare da saƙo kan a faɗa mata ba zai shigo yau ba yana sauri zai je wani guri.

Da haka ya karya kwana suka koma gida ya bar motar yayan nashi a waje suka shigo tare da HJ mai riƙe da ledan Indomie bakinshi a washe. A falo suka zauna Salima ta mishi sannu da dawowa fuskarta cike da mamakin dawowarsu da wuri.

“Lafiya kam yau na ga kun dawo da wuri?” Ta tambayi Muhammad cikin son jin me ya wakana.

“Mun tsaya zamu sayi fruits Muhammad Hafiz ya ga gurin da ake sayan Indomie ya ce irin wanda Salim yake sayo miki ne, shine na tsaya na saya muku.” Yayi maganar yana kafeta da ido domin so yake yi ya ga reaction ɗinta ba tare da wani alama ya wuceshi ba.

A nan kuwa ya ga tsoro, fargaba, da kuma tashin hankali duk a fuskarta lokaci ɗaya kuma ta fara zare idanu tana inda-inda can kuma ta ƙaryata ta ce basa saya.

“Kwanan nan kamar canjaki aka yi Salima. Wasu halayen da ban sanki da su ba sai fito mini da su kike yi ɗaya bayan ɗaya. Tambaya ɗaya zan miki kuma ina so ki bani amsa bana son ƙarya, da gaske kina aikan Salim ya sayo miki?”

Girgiza kai tayi hawaye na taruwa a idanunta, sai dai kallon da Muhammad yake mata yasa ta canja amsa ta ce,

“Wallahi bai fi sau uku bane.”

“Ki ɗauko plate ki juye muku ku ci. Zan fita unguwa.” Yana faɗin hakan ya tashi ya nufi bakin ƙofa Salima na bashi haƙuri amma bai saurareta ba.

Har ya je bakin ƙofa ya juyo ya ce,

“Kuma kar ki kuskura ki taɓa mini ɗa wallahi.”

Yana fita ya shiga mota sai ya rasa ina zai je haka kuma sai ya rasa wani tunani zai yi, maganganun mutane ne suke ta yawo a kwakwalwarshi game da halayen Salima da yake gani kamar ƙarya ake mata, amma a yanzu ya fara kokwanto tare da waswasi a ranshi. Parking yayi a bakin hanya ta ɗauki wayarshi ya kira the only person da ya yarda da ita a yanzu wato ƙanwarshi Iyami.

“Yau maigidanki yana tare da ku ne?” Ya tambayeta bayan ta amsa kiran.

“A’a, yana wancan gidan.”

“Gani nan zuwa zan zo mu yi wata magana ne.” Yana faɗin haka ya kashe wayar ya kunna mota sai gidan Iyami domin ya lura ita ce kaɗai ba zata mishi ƙarya game da abun da ya shafi gidanshi ba duk da cewa kwanaki yace kar ta sake shiga harkan gidan nashi da ta taɓa ce mishi Salima tana da fuska biyu.

“Ki faɗa mini komai da kika sani game da Salima, duk wani abun da ya kamata in sani kar ki cire komai har da na kwanaki da kike faɗa mini tana munafurtan Juwairiyya amma ban saurareki na. Tell me everything Iyami.”

Mum Fateey 👌

“Cewa aka yi ita ta saka mijin nasu ya kori amaryar tata. Ashe tun farkon zamansu shigo-shigo take mata babu zurfi, shi yasa duk inda ta zauna sai ta aibata kishiyar tata.”

“To ai gashi da ya koretan bai hanashi bibiyarta ba daga baya. Ni abun da yake kashe ni da mamaki shine yanda aka ce tayi ƙaramin hauka a gurin walimar gama makarantarshi da aka kira aka bashi labarin waccar ta haihu. Cewa aka yi watsi ta dinga yi da abinci tana ihu wai ƙarya ake mishi cikin ba nashi bane satowa suka yi.”

“Ai wannan furuci ya bani takaici domin na ji ance yayi ta kyafta maga idanu don ta hankalta tayi shiru kar ta tozartasu cikin jama’a amma haka taci gaba da sambatu har da kuka. Shi da yake ya san shi yayi cikin ko gezau bai yi ba balle ya kawo kwakanto a ranshi ya bawa ƴan’uwa labarin haihuwar.”

“Ai a ƙarshe da ya kasa danne zuciyarshi tafiya yayi ya bar mata waliman da ta shirya ɗin ya tafi gurin matarshi da ƴarshi, aka ce yarinyar kyakkyawa fara mai kama da shi sakk kamar yayi kaki ya tofar.”

“Ni fa dama tun kwanaki da take da kawo maganar mijin nata akan ya fiye matsa mata sannan tana tsoronshi nace wannan ba matar rufin asiri bane, don mijinki ya fiye hargowa da baƙin hali shine ba zaki rufa mishi asiri ba sai dai ki zo kiyi ta yayatawa jama’a? Kuma a hakan ki ce kina sonshi?”

“Koma dai menene yanzu kam ta tonawa kanta asiri a idon jama’a, an yi walkiya an ganta! Ita kuma waccar idan tana da wayo sai ta kame mijinta ta koma ɗakinta ta ci gaba da haƙuri da su duka.”

“Ni kwanaki nake jin labari kan uwarta, aka ce kishiyoyinta da suka fito su biyar in suna baka labarin makircin da ta musu a lokacin da suke tare sai kun zubar musu da hawaye.”

“Ohh dama ashe haka abun yake? Ni fa na ɗauka auri saki ne da uban nata, ashe da muguwar hali take korar mishi mata.”

“Zato zanubi amma haka kishiyoyin suke faɗa, kuma dai kun san ba zasu haɗa baki su mata ƙarya ba indai matsalar daga mijin ne ba ita ba.”

“Hakane, wannan shi ake kira barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Sai dai wannan ƴar barewar bata gwanance a makircin ba tunda ta kasa korar guda ɗaya da ta zame mata ƙarfen ƙafa.”

“Ai komin gwanancewanta idan Allah bai so ƙarewar wannan auren ba ba zata iya ƙarar da shi ba. Ai Ɗan Adam yana laifine Allah yana kallonshi, duk ranar da kuma Ya tashi kamashi haka zai nemi wayo da dabaran da yake tunanin yana da su ya rasa. Allah dai ya kiyashemu da annamimanci da munafurci.”

“Kai Ameen, ni har kun sa jikina yayi sanyi wallahi. Kuka ce yanzu nawa ake sayar da kwanon sugar?”

********

Ɗan muskutawa kaɗan Iyami tayi kamar mara gaskiya ta tsaya tana kallon yayan nata wanda he looked dejected kamar wanda aka ce his favorite toy ya ɓata.

“Ya Muhammad wani abu ne ya faru?” Ta tambayeshi ba tare da ta bashi amsa ba.

“Ni na zo gidanki na miki tambaya don haka ki amsa mini sai ki tambayeni dalili daga baya. Ki yi sauri dare yana yi bana son in jima a gidanki.”

“Duka zan faɗa maka ko major topics ɗin?”

“Wato da yawa ne?” Yayi dry dariya mai ɗauke da takaici.

Gyaɗa kai Iyami tayi tana binshi da kallon tausayi, sai dai a wani gefe na zuciyarta tayi murna ba kaɗan ba da Allah Ya sa idonshi ya buɗe ya gane halinta matarshi tun kafin ya rabu da Juwairiyya ya tafka babban asara.

“Tell me everything.”

Haka kuma aka yi, duk abun da zata iya tunawa ta faɗa mishi, bata bar komai ba; yanda Salima ta dinga faɗan zafin halinshi ana mata kallon abun tausayi, da kuma yanda take manipulating Juwairiyya tana sake zance ita kuma tana kaiwa gaba, da yanda Juwairiyyan ta gane ta shiga depression ta rame har ta nemi kashe auren nata amma shi Muhammad ɗin ya tsamota daga wannan halin suka cigaba da rayuwa. Bata bar komai ba ta sanar dashi har da yanda aka yi ta tunzura Juwairiyyan ta kirata munafuka wanda sai a yanzu ya gane dalilinta na kiranta da munafukar, ashe ba ƙarya tayi ba, kawai bakinta bai iya riƙewa ba ya furzar.

“Ban taɓa sanin haka take ba wallahi, I trusted her, I….” Kasa ƙarisa maganan yayi ya shafi kanshi da yake sarawa kana ya tashi zumbur yana cewa, “Dare yayi bari in tafi gida.”

Iyami ta duba agogo ta ga ƙarfe tara har da rabi ta rakashi har bakin gate ɗin gidan nata tana bashi baki sannan ta ƙara da cewa,

“Don Allah kar kayi hukunci cikin fushi Ya Muhammadu, ka bari sai ka nitsu sai ka ɗauki mataki.”

“Ni ba yaro bane Iyami.” Shine abun da ya faɗa kana ya mata sallama ya shiga mota ya tafi.

Yana cikin mota ya doshi gidansu Juwairiyya duk da cewa dare yayi amma ya kamashi dole ne yana buƙatar abu a gurinta. Sai da ya kusa isowa ya kirata yace gashi nan zuwa ta fito mishi da key ɗin ɗakinta.

“Me zaka yi da shi?” Ta tambayeshi cike da mamaki domin ɗazu tayi mamakin da bai shigo ba wai yana sauri ya aiko fruits aka kawo mata. Ko dai har ya gaji da bibikon ne?

“Ki fito mini dashi gani nan na kusa zuwa, kuma kar ki bawa Surayya ko wani.” Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.

Minti biyar da haka ya isa gidan ya kirata a waya sai dai bata ɗauka ba, seconds goma da haka sai gata ta fito sanye da hijabi fuskarta a ɗaure. Sallama ta fara mishi sannan ta haɗa da gaisuwa ya amsa fuskarshi babu yabo babu fallasa a nan ne kuma Juwairiyya ta gane something is wrong, ko dai da gaske ya gaji ne ya fara neman hanyar rabuwa da ita kamar yanda ta tambaya? A nan ta ji tsoro da fargaba ya shiga cikin zuciyarta duk da cewa idan ya saketan ita ta tambaya Kuma shine alkhairi a gareta.

“Gashi. Akwai kayana a ciki idan lokaci yayi zan aiko a zo a kwashe mini.”

“Sai a kaisu ina?” Ya tambayeta fuskarshi babu wannan wasa ko murmushin da ta saba gani dashi kwanan nan.

“A dawo mini da su gidan mu.” Ta bashi amsa tana mai cigaba da miƙa mishi key ɗin wanda ya ƙi karɓa.

“Har yanzu kina kan bakanki na neman ki rabu da ni ko?”

Yanda yayi maganar so painful kamar da gaske baya son rabuwa da ita, to amma shi bai san abun da take gudu ba, ko kuma a ce ita bata san me ya sani a yanzu ba.

“Eh. It’s for the best.”

“Haka kike so? Haka kika zaɓa Juwairiyya? You won’t fight for us or even try?”

Shiru tayi kanta a gefe tana cije leɓenta dalilin hawayen da yake ƙoƙarin zubowa kan fuskarta, bata son ya gane she is weak when it comes to rabuwa da shi.

“Bari in miki wata tambaya and I want you to answer honestly. Zaki iya?”

“In zan iya zan yi.” Ta amsa mishi zuciyarta na tsananta bugawa.

“An taɓa betraying ɗinki? Irin kin yarda da mutum amma daga baya kika gane cutar da ke yake yi a bayan idanunki? Ya kika ji?”

Kallonshi tayi cikin ido wannan karon cike da curiosity kan me yasa ya mata wannan tambayar don ba shi tayi tsammani ba, she anticipated questions kamar me yasa bata son komawa gidanshi ko wani makamancinshi, but not this! Sai dai zata amsa mishi don har gobe tana jin ɗaci a harshenta idan ta tuna experience ɗinta.

“Farko na zama cikin denial sai ina ganin kamar ba gaskiya bane. Sai dai daga baya da na fara tuna wasu events sai komai ya fara clicking, a nan na yarda fully wannan mutum ɗin cutata yake yi a bayan idona bayan ni kuma na yarda shi 100%. Kafin in gane zan iya taking bullet for that person amma a yanzu bana tunanin zan iya. Na shiga damuwa sosai kullum cikin tunani nake yi na duk abubuwan da suka faru tsakaninmu ina tuna duk laifina ina kuma dana sani mara amfani. A lokacin sai na fara yiwa mutane kallon munafukai ya zama ban yarda da kowa ba sai dai kawai a yi sha’ani a watse amma sai in ga kamar anjima shi ma zai iya betraying ɗina. Ba zan iya faɗa maka ainihin yanda ake ji ba amma feeling ɗin bashi da daɗi ko kaɗan don in mutum bai yi wasa ba zai iya rasa kanshi, wannan events guda ɗayan kan sa ya canja mu’amalarshi da mutane mai kyau ko mara kyau. Why do you ask?”

“Ina rubuta article ne kan haka shine nake jin ta bakin mutane kala-kala. Thank you.” Ya amsa mata mechanically yana kallon gefe kamar wanda baya ma tare da ita a gurin.

“Ga key ɗin zan shiga gida dare yayi.” Ta faɗi hakan tana miƙa mishi, wannan karon Muhammad ya ƙarba ya saka a aljihunshi ya sake mata wata tambayar kafin ta juya.

“Kika ce ba zaki koma gidana ba? Me yasa?”

“Saboda hakan shi zai fi mana.”

“Baki bani amsa ba.”

“Saboda wasu obstacles da suke cikin auren namu da komin yanda muke son zama da juna ba zasu bari ba.” Ta yi magana in codes irin wanda yace ba ya so.

“Wasu obstacles kenan?”

“I can’t say, amma we have different views a kansu, don haka kullum zamu kasance ne wajen disagreeing da juna.”

“Me yasa baza ki faɗa mini ba?” Ya tambayeta yana zuba mata ido.

“Saboda ba zaka taɓa yarda ba. I’m always the impatience one, remember? Ko yanzu na faɗa maka you will judge me ne da rashin haƙurina da taurin kaina.” Ta yi maganar emotionally.

“Try me Jay, may be this time around zan fahimceki fiye da yanda kike tsammani. Please try me.”

“I can’t! Ka taimaka mana ka daina jan wannan abun da komin daren daɗewa zai zo ɗin. Ba rabuwan faɗa zamu yi ba, rabuwan fahimtar juna ne ta yanda ko ba’a tare ba zamu dinga sukar juna ba saboda an yi zaman mutunci kawai wasu abubuwan ne ba za’a iya cigaba da ɗauka ba.”

Shiru Muhammad yayi yana tunani sai can ya ce,

“Shikenan. Sai da safe.”

A maimakon hakan ya yiwa Juwairiyya ɗaɗi sai ta ji hanjin cikinta ya kaɗa tsoro ya dira a zuciyarta. Ba dai shikenan tayi convincing ɗinshi ya yarda zai saketa ba. Ita ta nema amma kuma bata son hakan ya faru, me yasa? Saboda tana sonshi har gobe har kuma ƙarshen rayuwarta ba zata taɓa mantawa dashi ba. Bata iya ƙara ce mishi komai ba ta juya ta shige cikin gida, tana shiga ɗaki ta ɗauki wayarta ko har ya tura mata sakin amma bata ga komai ba da wannan damuwan tare da fargaban ta kwanta wanda da kyar bacci ya ɗauketa.

Muhammad daga gidansu Juwairiyya gidanshi ya koma yayi parking ɗin motar a cikin gida yayin da na Salima kuma ake ajiyeshi a gidan makwabtansu da suke da parking space babba sannan ita bata fita da motar akai akai kamar shi. Yana fita daga motan ya wuce side ɗin Juwairiyya ya buɗe yana jin wani irin ɗaci a zuciyarshi, shikenan shi kam ba zai taɓa sa’an samun mata masu son shi ba? A cikinsu daga mai son rabuwa dashi sai kuma mai munafurtarshi a bayan idanunshi. Shi kuma wannan ne ƙaddaranshi sai dai yana addu’an Allah Ya sa ya cinye ba tare da ya zauce ba, domin a yanda Juwairiyya ta faɗa mishi stages ɗin wanda aka yi betraying shi yanzu yana cikin kowanne stage ne, wato yana cikin denial, yana kuma haɗa one da two suna making sense, sannan a yanzu gani yake yi kowa ma munafuki ne  sannan babu mai sonshi da gaskiya duk duniya.

Duk da ma windows a rufe suke bai hana ɗaki da falon yin ƙura ba, hakan yasa Muhammad ya hau yin kakkaɓe kakkaɓe yana jin Salima na kwankwasa ƙofar falon amma bai mata magana ba balle ya ɓuɗe mata. Yana son nesanta kanshi da ita ne wanda dawowanshi ɗakin Juwairiyya shine farko.

Lokacin da yake karatu a UK ya koyi gyaran gida har da girki shi yasa a yanzu cikin ƙanƙanin lokaci ya gyara komai har da wanke banɗaki. Yana gamawa ya shiga wanka sannan ya fito ya ɗauko jallabiya daga cikin wardrobe ɗin Juwairiyya ya saka. A nan ya tuna bai ci abincin dare ba amma bai damu ba, zai iya kwana a haka don baya ma jin zai iya ci ɗin.

Sai a lokacin ya ɗauki wayarshi ya ga missed calls ɗin Salima da yawa har da texts messages ya bi yana karantawa, a text na ƙarshe take cewa wai hankalinta ya tashi idan bai buɗe ba zata kira Yayanshi ta faɗa mishi halin da ake ciki. Dariya yayi wanda ya fi kuka ciwo, sai ya tuna irin wanda ta yiwa Juwairiyya can da jimawa ta kirashi ya dawo daga office, yau kuma abun a kanshi ya sauƙa?

Kiran Yayan nashi yayi ya ɗauka babu ɓata lokaci yana cewa,

“Lafiya kam Matarka ta kira hankalinta a tashe tana cewa ka shiga ɗaki ka rufe tana kiranka ka ƙi amsawa kuma ka ƙi ɗaukan wayarta.”

“Babu abun da ya faru neman abu nake yi.”

“Ok shikenan. Sai da safe.”

Yana kashe wayar kira Salima ranshi na ƙuna ya ce,

“Bayan duk abun da kika yi har kina da guts ɗin ɗaukan waya ki kira yayana kina faɗa mishi maganar banza? Ni yaro ne da in na shiga guri na rufe zaki yi ta nemana har ki kira wani da bai san me yake faruwa ba ki faɗa mishi? Dama ashe haka kike baki da rufin asiri baki san me ya dace ba? Ki kiyayeni, ki kuma kama kanki in ba haka zan mugun baki mamaki.”

Da wannan furucin ya kashe wayarshi bai bari ko tari tayi ba. A nan ya kwanta zuciyarshi na zafi game da azalzakarshi kan wannan abu da yake faruwa da iyalin nashi wanda ko’ina ya juya babu sauƙi, shi yasa yanzu yayi isolating kanshi don ya zauna shi ɗaya ya nemawa kanshi mafita kafin komai ya lalace mishi.

Kaina na ciwo, iya abun da zan iya yi kenan. A mini addu’a please.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Yau sati uku kenan da faruwar wani al’amari da ya girgiza kwakwalwar Muhammad ya kuma sakashi cikin waswasi game da halayen mutanen da yake rayuwa da su na yau da kullum. Ya ƙauracewa Salima ta yanda gaisuwarta na safe kaɗai yake amsawa idan ya fito daga ɗakin Juwairiyya zai fita cikin gari, daga nan kuma sai dare idan ya dawo zai sameta a tsakar gida tana jiranshi watarana riƙe da tray ɗin abinci, a nan zata mishi sannu da dawowa ya ɗaga mata hannu ko kai shikenan sai ya shige ciki ya barta tana magiya game da roƙonshi ya faɗa mata laifin da tayi ya ƙaurace mata ko kuma ya karɓi abincinta ya ci. Sai dai Muhammad bai taɓa tsayawa ya mata magana ba, so yake yi ta horu ta yanda duk ranar da ya zaunar da ita ya tuhumeta zata faɗi gaskiya ba zata mishi ƙarya ba, domin kuwa ya gane da ƙaryata abunda tayi take dodging duk wani laifukanta.

Tsakaninshi da Juwairiyya kuwa su ma sai godiyar Allah, domin wannan shiga gidansu da yake yi ya zauna kullum ɗin ya daina, sabon tsarin da ya ɗauka shine idan ya zo yau to gobe ba zai zo ba, haka kuma ya daina shiga har cikin gidan sai dai ya kira Juwairiyyan ta fito ta bashi ƴarshi ya ganta, minti biyar kuwa yana cika zai tafi sai kuma an ƙara kwana ɗaya. Ita kuma ya mata hakane don ya ƙara mata lokaci da  space don ta huce kuma tayi tunani mai zurfi game da wannan magana da take yi na rabuwa dashi, idan tsoronta halin Salima ce to ya gane, sai dai ba zai nuna mata ba saboda wasu dalilai nashi.

A daren ranar da ya cika sati ukun ya yanke shawarar tuhumar Salima, yana dawowa ya sameta a tsakar gida tana jiranshi wannan karon hawaye take yi sosai tana gogewa. A maimakon ya nufi ɗakin Juwairiyya kamar yanda ya saba sai ya tasamma falonta hakan yasa ta gwalalo idanunta waje ta bi bayanshi har tana tuntuɓe. A kan kujera ya zauna inda HJ ke bacci a kai ya gyara mishi kwanciyar sannan ya dubi Salima wacce ta zauna a ƙasa tana kallonshi kamar in ya ce ta shiga wuta yanzu zata iya shiga babu musu balle tambayan dalili.

“Tambaya zan miki kuma ina son ki faɗa mini gaskiya, kar ki ce zaki mini ƙarya saboda na san duk abun da yake wakana kawai so nake yi in ji daga bakinki.”

“Wallahi zan faɗa maka gaskiya. Don wallahi zan iya ƙirga maka sau nawa muka ci indomie ɗin.”

Har Muhammad ya buɗe baki da niyyar magana sai kuma ya rufe ya tsaya yana kallonta, domin maganar ba na Indomie ne kaɗai ba, a’a it’s much more than that saboda shi maganar Indomie zai ɗaukeshi ne a matsayin incident ɗin da ya buɗe mishi ido. To amma me zai ce? Cewa zai yi me yasa kike munafurci ko kuma me yasa kike shiga cikin mutane kina haɗasu faɗa da matata, ko me?

“Salima me yasa kike cewa ina da mugun hali ina takura miki bana tausayinki?” Ya fara mata tambayar yana mai kafeta da ido.

Shiru tayi tana kallonshi fuskarta ɗauke da mamaki, da alama ba wannan tambayan ta hasaso za’a mata ba. Ta kai seconds goma bata amsa ba sannan ta buɗe baki ta fara magana,

“Ni wallahi ban taɓa faɗawa kowanne mahaluƙi kana da mugun hali ko baka jin tausayina ba, sannan duk wanda ya faɗa maka ka kirashi, gani ga shi ya faɗi ranar da na furta waɗannan kalmomin.”

Wannan shi ake kira ‘in baka iya kama ɓarayo ba shi zai kamaka’. Tabbas bata taɓa furta waɗannan kalmomin a kanshi ba amma yanayin maganganunta ne ke indicating hakan, kamar ta bayar da haruffan ne ga mutane su kuma suka haɗa suka furta kalmomin. Da alama wayon nata da yawa yake kuma sai yayi da gaske kafin ya kamata da laifin da yake tuhumarta da shi.

“Ai nima ban ce kin je kin faɗa ba, maganganun da kike amfani da su ne suka saka har mutane suka bani wannan title ɗin. Shin kin taɓa jin ni na fita ina cewa kin mini laifi ko makamancinshi?”

Girgiza kai tayi tana mai tara hawaye a idanunta wanda Muhammad yana gani ya ji haushi ya turnuƙeshi, shi aka yiwa laifi amma ta zo tana mishi kuka?

“Bana son koke-koken nan, idan za ki nitsu mu yi magana in ba za ki nitsu ba in tafi.”

“A’a wallahi na daina.” Ta faɗa tana goge idanun nata.

Sai a lokacin Muhammad ya ji duk abubuwan da aka faɗa mishi a kanta yana yawo a kanshi ya ji ba zai iya wannan diplomatic approach ɗin ba.

“Salima na samu labarin duk abun da kike yi a kaina da kuma Juwairiyya.”

Kafin ya kai ga ƙara faɗin wata kalma ta tari numfashinshi ta fara magana kamar zata yi kuka.

“Wallahi sharri take mini tana so dama ta rabani da kai ta rabani da gidan aurena da ɗana. Tun da ta fara jin zugin mutane watarana ta sameni tana cewa wai sai ta saka na bar mata gidan. Ashe wannan dalilin ne yasa kake fushi da ni ka kaurace mini Baban Hafiz? Shikenan ta samu nasara a kaina don kawai ta ƙirƙiri labarin ƙarya ta faɗa maka?” Sai hawaye kuwa suka gangaro kan fuskarta.

Tsura mata ido Muhammad yayi yana ganin ƙarfin halin Salima, idan a da yana kwokwanto yana tunanin sharri Iyami take mata to yanzu kam ya daina domin kuwa ya san gaskiya, sannan wacce take iƙirarin ita ta faɗa mishi ba ita ba ce. Me yasa ta ɗauki ƙarya abun faɗinta kullum?

“Kina tunanin Juwairiyya ce ta faɗa mini? Ba ita ba ce Salima. Hasalima ita har yau ta ƙi faɗin duk laifinki a kanta saboda tana tsoron ba zan yarda ba, kuma gaskiyanta, ko ta faɗa ɗin ba zan yarda ba saboda zan yi tunanin kishi ne ko kuma wani halinku ne na mata yasa ta faɗi hakan.”

“Aunty Iyami ce ko? Baban Hafiz kai ma kasan bata so na, komai nayi ita a gurinta laifi ne bata kuma jin nauyin faɗa mini magana mara daɗi a gaban kowa.”

Muhammad cigaba yayi da kallonta yana mai ƙara jin mamaki a ranshi, shi ya kirata ya zaunar da ita don ya tuhumeta amma sai tayi dabaran da zata yi aka dawo shi yake bata amsa ba the other way round ba.

“Interrogating ɗina zaki yi kenan? Akan ki nitsu in faɗa miki laifinki ki gyara shine kike ta faɗe-faɗe wai wane ya tsaneki wane kuma ya ce zai rabaki da gidanki? Ashe dama haka kike? To Iyami bata tsaneki ba Salima sai dai ta tsani halayenki kamar yanda nima a yanzu na tsanesu. Kuma muddin kina son mu ci gaba da zama tare dole ne ki canja Tafiyarki, wannan ƙarya, faɗe-faɗe, manipulating mutane da pretending ɗin da kike yi ki daina. Ranar da Juwairiyya ta gama makaranta da gangan kika tsokaneta ta kiraki da munafuka ko kuma wasa kike mata kamar yanda kika faɗa mini? Kuma kar ki kuskura ki mini ƙarya.”

Ɗago ido Salima tayi ta kalleshi tana ganin yanda ya murtuƙe fuska sai ta shiga taitayinta, sunkuyar da kan nata tayi kana ta ce.

“Da gangan ne.”

“Why?” Yanda yayi maganar sai yayi sounding so hurt kamar ba amsa yake nema ba kawai ya faɗa ne.

“Saboda ita ce ta mini alƙawarin zata bar gidan da zarar ta gama school. Amma da na lura bata da niyyar tafiya shine na ɗauko mata maganar.”

“Don ta tunzura?” Ya sake yin wata tambayar yana yin tagumi.

“Eh.”

“Why?”

Shiru tayi bata amsa ba tana murza ƴan yatsunta a hankali.

“You planned all that?”

Gyaɗa kai tayi alamar ‘eh’ wanda ta ƙara sakawa Muhammad mamaki da kuma tausayin kanshi da ma Juwairiyya. She played them all! Ta karancesu duka sannan tayi amfani da wannan sanin halayen nasu ta haɗasu faɗa har ya kori waccar gida. Duk da ma abun da ya faru tsakaninsu ba ita ta tsara hakan ba amma haushin laifin da Juwairiyya tayi mata ne ya haɗu da laifinta da ta mishi yasa ya ce ta tafi gida. In bai manta ba ko a wancan lokacin Juwairiyyan ta so faɗa mishi halin matarshi amma sai ya ajiye hakan a matsayin neman fitina, ƙarya da kuma tozarci. Shi yasa ko da ya gama musu faɗa ya ƙi lallaɓata domin laifi tayi aka mata faɗa ba wani abu ba. Kuma ba zai yi hukunci sannan ya dawo yana sauƙar da murya a gaban mace kamar bai isa da gidanshi ba, hakan zai sa gaba in sun ƙara laifi ya musu faɗa su jirashi ya zo ya basu haƙuri in private, abun da ba zai iya ɗaukawa kanshi ba kenan.

“Ban san ko tun da haka kike ba amma wannan sabon halin naki da na sani yanzu yasa na daina kallonki a yanda na sanki. Wallahi kin ɓata trust ɗin da ke tsakanina da ke Salima, wanda a yanzu har na fara kwakwaton so da kulawan da kike nuna mini, shin su ma ƙarya ne ko?”

Saurin girgiza kai tayi kana ta ɗago kanta tana cewa,

“Wallahi ba ƙarya bane Baban Hafiz.”

A nan ya fara ƙirgo mata duk abubuwan da aka ce tayi, wasu ta ƙaryata wasu kuma ta amsa. Sai da ya gama jin komai sannan ya nisa ya ce,

“Kin bani mamaki Salima, ban taɓa expecting haka daga gareki ba. I thought halinki daban ne, I don’t even know who you are anymore.”

“Ka yi haƙuri don Allah.” Ta faɗi hakan tana hawaye caɓe caɓe.

“Why all these? Me yasa?” Ya tambayeta domin har lokacin bai ga kwakkwaran dalilinta na yin hakan ba.

“Saboda ina sonka ne bana son rabuwa da kai?”

“Bullshit! Kina sona ba kya son rabuwa da ni ne yasa kike badmouthing ɗina a waje kina nunawa ni mai mugun hali ne? Is that love Salima?”

Shiru tayi tana goge hawayenta da tun ɗazu yace mata baya son ya ga tana zubarwa don haushi suke ƙara bashi.

“Abun da kika yi bai kai in rabu da ke ba shi yasa zan cigaba da zama da ke, amma ki sani you tainted your image a zuciyata har ƙarshen rayuwata wanda hakan shine hukuncin laifin da kika aikata. Ki sani ba zan sake ganinki a yanda nake ganinki a da ba, you already scratched that. Abun da ya faru kuma ko da wasa kar in ji kin kai gaba ko gurin ƴan’uwana ko naki.”

Yana faɗin hakan ya tashi zai fita Salima tayi saurin binshi tana kiran sunanshi ya amsa ya dakata.

“Na san nayi laifi amma kayi haƙuri ka yafe mini kuma wallahi na maka alƙawarin ba zan sake ba. Kuma don Allah ina neman alfarma a gurinka da ka dawo mu ci gaba da rayuwa tare, komawanka can ganin shi nake yi kamar mari ne a fuskata.”

“Idan har haka kike gani then kwalliya ta biya kuɗin sabulu, dama ban yi don ki ji daɗi ba. Dawowa kuma zan dawo amma sai na gama hucewa.”

“To ko abincina ka dinga ci tunda ka tuhumeni kuma na amsa laifina. Please.”

Shiru yayi kamar mai shawara da zuciyarshi sannan ya gyaɗa kai ya fice ita kuma tayi saurin shiga kitchen ta ɗauko tray tare da saka  kulolin da ke kan dinning table a kai kana ta kai mishi falon Juwairiyya bayan ta gyara fuskarta.

Sallama tayi ya amsa ta sameshi a zaune babu abun da yake yi, a kan center table ta ajiye mishi kamar yanda ta ga Juwairiyya tana yi sannan ta koma gefe ta tsaya, ita bata zauna ba ita kuma bata tafi ba.

Minti ɗaya da haka ya ɗaga ido ya mata wani irin kallo ai kuwa babu shiri ta fice ta bashi guri. Sai a lokacin Muhammad yayi ajiyar zuciya yana jin komai ma ya fita a kanshi, damuwar kuma tana ta yawaita. Ko’ina yayi babu ɗaɗi daga gurin Salima har gurin Juwairiyya kowacce da gagarumin matsalarta. Ya jima zaune a haka yana tunani sannan ya ɗebi abincin kaɗan ya ci ya rufe ƙofar falon sannan ya shige cikin bedroom inda yake mishi ƙamshin humran Juwairiyya da yake watsawa akan bedsheet don kawai ya dinga jin ƙamshinta a kusa da shi. A nan kuma yayi niyyar zuwa gurinta gobe su yi finalizing maganarsu domin ya sani ta kusa yin arba’in, its either ta dawo gidanta ko kuma su aikata abun da shi kanshi baya ma son tunawa.

Duk wannan bidiri da aka yi kuma ake kan yi Juwairiyya bata da masaniya domin kuwa Iyami bata sanar da ita cewa Muhammad ya gane halin Salima ba. Abun da ta sani shine Muhammad ya daina zuwa gurinta yana wannan lallaɓata tare da mata magiyar ta koma gidanshi. A da kullum yake zuwa amma a yanzu ya dawo yana tsallaken kwanaki ta yanda in yau ya zo to gobe ba zai zo ba, kuma ya daina shigowa cikin gida sai dai ya tsaya a waje ta fito ya ga ƴar shi ya tafi. Kenan har ya gaji da bibikon? Wannan tunanin da Juwairiyya take yi kenan a lokacin da take yiwa Muhibbat (Aisha) wankan safe Mama na gefenta tana mata gyara idan ta kwafsa. Sai da suka gama wankan sannan Mama ta karɓeta tana tsantsane mata jiki tana cewa,

“Yanzu kam saura kaɗan ki gama iyawa ta yanda ko kun koma gidanku ba zaki nemi mai miki ba.”

Juwairiyya tana jin haka zuciyarta ta buga da ƙarfi domin ta lura zancen Mama kullum kenan a yanzu, a kan da tayi arba’in ta tattara ta koma gidanta. Bata ko lura da cewa wanda za’a koma gidan nashi he stopped trying ba. Mama na shirya Muhibbat itama ta shiga wanka ta fito a nan kuma ta samu Halima zaune da ƴaƴanta biyu a kan gado tana riƙe da Muhibbat.

“Halima?!!” Juwairiyya ta kira sunanta da ƙarfi tana zaro ido tana kuma washe baki.

“Your one and only! Dama haka yarinyar nan take da kyau Masha Allah? Gaskiya hoto bai mata adalci ba.”

“Ni ina murnan ganinki ke kuma kina gushing over a baby? Yaushe rabon da mu ga juna amma ke ko kallo ban isheki ba ko?” Juwairiyya ta faɗa tana murmusawa kana ta zauna gaban mirror tana tsantsame jikinta.

“Ke na sanki amma ita ban santa ba.”

“Bayan haka kuma kin mini bazata. Yaushe kuka shigo? Ko last week fa mun yi magana da ke a whatsapp amma baki faɗa mini zaki shigo Nigeria ba.”

“Surprise ne, kwananmu uku a gari kuma mun zo biki ne.”

“Kai Masha Allah. Sannunku da zuwa mutanen Turkey. Ƴan yarana ku zo mu gaisa mana, ko basa jin hausa?” Faɗin Juwairiyya tana miƙawa babbar hannu don ƙaramin mai sunan Daddy yaro ne yana gefen mamanshi.

“Suna ji amma ba sosai ba, sun dai fi jin English da Turkish.”

“Merhaba.” Faɗin Juwairiyya tana ɗaga musu hannu.

Dariya Halima ta saka har da rufe baki tana kallon Juwairiyya da ke hararanta ta ce,

“Suna jin Hausa fiye da kowanne language don a can babu mai musu sai mu. Bamu bari suka taso haka ba saboda da zaran sun shiga school English da Turkish ɗin kaɗai za’a koya musu. Kyiwa ce kawai suke dashi sannan ba su saba ganin baƙaƙen mutane ba.” Halima ta ƙara kwashewa da dariya da ta ga Juwairiyya na aiko mata da harara.

“Sannu fara.”

“Sannun mu fa. I missed messing with you wallahi ke kuma uwar zuciya kiyi ta hawa kamar flour da aka sakawa yeast. Mun sameku lafiya? Ya gida ya kuma bayan rabuwa?”

Nan suka hau gaishe-gaishe har Juwairiyya ta gama shiryawa ta ƙara attempting ɗaukan yaran Haliman amma suka saka kuka ta koma gefe tana ganin ikon Allah.

“Halima ni kaɗai ce suke yiwa haka ko dai kowa da kowa ne?”

“Wallahi kowa ne, Yaya Abduljalil da Daddy ne kaɗai suke yarda da su don muna yawan video call suna ganinsu. Amma anjima kaɗan zasu sake.”

“To Masha Allah don har na fara zaton ke kika musu huɗuba kan cewa zaku zo gurin wata baƙar mata kar su je gurinta.” Ta faɗi hakan tana dariya tana karɓan Muhibbat wacce take bacci zata kwantar da ita.

A nan kuma hira ya ɓarke tsakaninsu bayan Surayya ta zo ta kwashi yaran Halima wanda ya bawa kowa mamakin ganin basu mata kyiwa ba. Sai a lokacin ne kuma Juwairiyya ta ji musabbabin zuwansu, wai Daddy ne zai yi aure!

“Daddy yayi neman magani na asibiti har da na gargajiya, ƙarshe dai aka haɗa da addu’o’i wani Malami ya bashi maganin karya asiri da ya ga kamar da saka hannu a ciki. Wallahi sati ɗaya da amfani da maganin ya dawo da lafiyarshi, ashe tun wancan lokacin jifa aka mishi.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Wa zai iya yiwa ɗan’uwanshi haka kuma don me yasa?” Juwairiyya ta faɗa tana dafe ƙirji cike da mamaki da tsoro.

“Wa ya sani? Ya wuce zawarawan da suke bibiyarshi ya auresu amma ya ƙi, don shi yace ba zai taɓa yiwa Mamanmu kishiya ba, kuma yana faɗawa mata masu son shi hakan. To wataƙila don haushin wannan furucin yasa wata ta mishi aiki don kowa ma ya rasa, sai dai ta ɗauki alhakinshi domin magunguna da yayi ta ɗurawa cikinshi tun daga na asibiti har na gargajiya da yawa suke, Allah Ya kare mishi kidney ɗin shi kawai.”

“Ameen.” Juwairiyya ta amsa mamaki cike taff a ranta.

A nan kuma ta fara jin haushin kanta me yasa basu nemi na Islamic ba? Saboda dukkansu sun ɗauka Diabetics ɗin shi ne ya jawo mishi.

“To ya batun Diabetics ɗin?” Juwairiyya ta tambayi Halima.

“Yana nan amma yayi sauƙi sosai.”

“Kai Allah Ya rabamu da duk sharrin mai sharri.” Juwairiyya tayi addu’ar tana tuna wanda Salisu ya mata ya rufe mata baki tana jin tsoronshi kuma bata iya musu da shi.

“Amma dai babu wanda ya san wannan maganar ko?”

“Duk duniya daga Daddy sai ke sai ni ne muka sani, oh sai kuma Doctors ɗin da yake zuwa gurinsu neman magani. In a nutshell dai ko Yaya Abdul jalil ma bai sani ba.”

“Masha Allah. Allah Ya basu zaman lafiya.” Juwairiyya tayi addu’a tana jin wani irin babu daɗi a ranta. Yanzu shikenan Daddy har ya manta da ita zai ƙara aure?

“Ameen. Da fatan dai za ki zo don wannan karon ma ni na nemo mishi mata na haɗa auren.”

“A’a nikam ban miki alƙawari ba.” Juwairiyya ta amsa tana girgiza kai, yoo ko giyar wake ta sha zata je ne? A matsayinta na me? Tsohuwar matarshi da ya aura ya kasa biya mata buƙata ko sau ɗaya ko me?

“Dama na sani. Daddy ya ce yana gaisheki kuma yana miki addu’a Allah Ya raya miki ƴarki. Ga kuma kaya mun saya ni dashi na Baby da Mamanta.” Da haka ta tura mata ƙatuwar ledar da ta taho dashi wanda yake cike da kaya sai kace su aka yiwa haihuwar.

A nan Juwairiyya ta ɗauka tana ciro kayan ciki tana murmusawa, lace da atampa ne masu tsada guda biyu sai rigunan baby guda biyar da su pampers wipes tare da headbands da tarkacen kayan kwalliyan ƴaƴa mata.

“Wannan kaya yayi yawa Halima.”

“You deserve more than that Aunty Juwai.”

Sai yamma Halima ta tattari ƴaƴanta suka tafi akan next week za’a ɗaura auren Daddy da wata bazawara mai shekara talatin da biyar. Ƴayanta guda biyu ne mata masu shekara goma da bakwai, kuma mijinta ne ya rasu shekara biyar da ya wuce ya barta dasu. A wani group na kasuwanci Halima ta haɗu da ita, wanda tausayinta da kuma ganin kyawawan halayenta yasa Haliman tayi bincike a kanta ta kuma nemawa Daddy aurenta, babu musu ta amince bayan Daddy ya je sun ga juna. A cewar Halima tunda tana da yara gidan zai zama lively kuma Daddy ma zai fi jin daɗin gidan da hayaniyarsu kafin shima in Allah Ya yi ta haifo mishi nashi.

Bayan maghrib Juwairiyya tana sallah wayarta ta fara ringing, sai da ta idar ta duba ta ga Muhammad ne ta kirashi tana mamakin kiran nashi domin jiya ya zo.

“Assalamu alaikum.” Ta mishi sallama ya amsa.

“Gani a waje na zo.”

“Ba jiya ka zo ba?” Ta mishi tambayar da ta kasa haƙurin riƙewa.

“Sai aka ce ƙa’ida ne idan na zo jiya yau ba zan zo ba?”

“A’a. Na ga haka ka mayar da tsarin ne. Bari in bawa Surayya ta kawo maka ita zan yi nafila ne.”

“Kin gama wankan jegon kenan?”

Kasa bashi amsa tayi domin tsoro ne ya shiga zuciyarta, kar maitarshi ta tashi ya rufe ido ya kasa ganin abun da take hanga musu duka. Muƙut ta haɗiye yawu mai kauri kana tace,

“A’a.”

“Bana son ƙarya, ko a da bana son ƙarya balle yanzu.”

“Na yi.”

“Ki bar nafilan tunda dama ba dole bane, sannan ke na zo gani ba Mamana ba (sunan da yake kiran Muhibbat da shi).”

Jiki na rawa Juwairiyya ta kashe wayarta tana jin kamar ta kurma ihu, tabbas ta tsokanoshi daga cewa kawai tayi wanka. Shi idan yana tunanin kaɗaituwa da mace ta lura ba ya tunani mai kyau. Dama fitowanta daga wankan yamma kenan aka kira maghrib don haka mai kawai ta shafa da humra ta fita ko powder bata shafawa fuskarta ba.

A cikin mota ta sameshi ta kwankwasa mishi glass ya ɗago yana kallonta lazily ya ce,

“Ki shigo.”

“Ni bana shiga mota a waje.”

“Wannan motar mijinki ne, in kuma zaki yi musu da ni ne to.”

Ta kai minti ɗaya tsaye tana kallon gefe ko zai haƙura shi ya fito amma shiru bata ga alamar hakan ba, jiki babu kwari ta buɗe gaban motar ta shiga amma ƙafarta ɗaya na waje ta kuma ƙi rufe ƙofar.

“Me haka? Cinyeki zan yi ne?” Ya faɗi hakan yana kallonta da mamaki a fuskarshi.

“Hakan nake so don zafi nake ji.” Ta yi ƙarya.

“Bana son ƙaryan nan.”

“To kawai bana son rufewa ne a yi tunanin wani abun mu ke yi a ciki.”

“Idan ma mun yi wani abun zunubi muka aikata? Ko ke ba matata ba ce?”

Shiru tayi, don wannan tambayar ba ita zata amsa mishi ba tunda shima ya sani.

“Ki rufe ƙofar na kunna A.C.” Ya faɗi hakan bayan ya yi abun da ya faɗa ɗin.

Zuciya na luguɗe baki a ɗane a sama Juwairiyya ta saka ƙafar tata kana ta rufe motar tana harɗe hannayenta a saman ƙirjinta wanda hakan yasa albarkatunta suka bulluƙo ta sama duk dama cewa Hijabi ne a jikinta. Muhammad kamar maye haka ya bi gurin da kallo kana ya lashe lips ɗinshi tare da kaɗa kanshi ya ce,

“Yaushe zaki koma gida? Don kin ga yau kwana talatin da biyu kenan da haihuwar taki, yanzu saura miki kwana takwas.”

“Ni fa ba zan koma gidanka ba.” Ta faɗi hakan a sanyaye.

“Me yasa?” Ya tambayeta kamar yanda yake mata kullum kuma take bashi amsa iri ɗaya.

“Saboda Tafiyar Mu ba zata mana daɗi ba.”

“In ji waye?”

Wannan tambaya da yayi yasa Juwairiyya ta gane har yanzu bai ɗauki maganarta a ta masu hankali ba, domin idan Muhammad ya fara silly and head-butt worthy questions to bai ɗauki duk maganar da ake yi da muhimmanci ba. Hakan yasa ranta ya ɓaci ta buɗi baki ta fara mishi maganan da ta rantse ba zata mishi ba.

“Saboda halinka da kuma halin matarka. Kai ka ɗauki kanka da wani irin muhimmaci ta yanda baka taɓa yin laifi, kuma ko ka yi laifin ka gane baka iya lallashin mace balle ka bata haƙuri ko kuma ka yi wani abu da zai sa ta gane cewa eh, ita mace ce abar tausayawa kuma abar a yiwa lallashi. Kana da saurin judging mutum base on halayenshi da ka sansu da shi, babu ruwanka kuma da duk bayanin da mutum ya maka ba zaka yarda shi ba sai abun da zuciyarka ta saƙa maka. Kai baka san cewa mutum kan iya canjawa bane? Ko kuma baka san cewa ba kullum shi mai masifa da hayaniya yake da laifi ba? Ka tuna lokacin da kake yaro, kullum ne laifin da ake tuhumarka dashi ake kuma hukuntaka a kai ka aikata?”

Duk wannan bayanan da Juwairiyya take yi Muhammad binta yake yi da ido yana murmusawa, amma kalmarta ta ƙarshe yasa ya tamke fuska ya juyar da kanshi gefe. Hakan yasa ta gane she hits a nerve ta ci gaba da magana.

“Sannan zan faɗa maka gaskiya sai dai in ƙara wani laifin matarka tana munafurtata tana aibatani cikin mutane, yanda ka san manomi mai ɗana tarko a cikin gonarshi don ya kama Rodents masu mishi ɓarna haka matarka take ɗana mini tarko ina faɗawa ɗaya bayan ɗaya, wanda sai daga baya na gane na kuma hankalta na koyi dodging amma duk da haka wani tarkon nata ya fi ƙarfin hankalina haka nake faɗawa cikin fushi ba tare da na iya haƙurin tsallakewa cikin hankalina ba.”

Shiru tayi tana kallon fuskarshi wannan karon ya kama haɓarshi da hannunshi guda ɗaya yana kuma karkaɗa ƙafarshi ɗaya. Ita tayi mamaki ma da ya barta tana ta magana bai katseta ya ƙaryatata ba ko kuma ya mata tsawa kan wani abu da bai yarda da shi ba.

“Kin gama maganar?” Ya tambayeta yana mai juyowa suka haɗa ido wanda sai da zuciyarta ta buga don tsabar kwarjinin da ya mata nan take.

Sunkuyar da kanta tayi ƙasa kana tace,

“Sannan baka so na. Wallahi baka sona jikina kake so shi yasa duk abun da ya faru tsakaninmu baka damuwa da emotion ɗina kai dai kawai ka samu ka biya buƙatarka shine damuwarka.”

A nan ne kuma hawaye ya sauƙo kan ƙuncinta tayi saurin sharewa tana cije bakinta.

“Da farko dai ni namiji ne ina sama da ke, to don na ɗauki kaina da wannan matsayin bai kamata a ce ya dameki ba Juwairiyya. Na biyu ina lallashinshi, sai dai dama an ce mutum kan manta da alkhairi ya tuna sharri. Ko rantsuwa zan yi ina kwatanta miki wannan lallashin ko da kowa ba kullum bane and I respect you. Batun matata kuma baku fahimci juna bane kuma nima nima ban fahimta ba, amma yanzu komai zai zo da sauƙi. Kullum sai kiyi ta cewa ina son jikinki, Juwairiyya in nace bana so na miki ƙarya amma da ke ɗin dukkanki, your personality da jikin naki duk ina son su. Kuma ke ɗin ce kike driving ɗina crazy shi yasa bana iya tunani mai kyau muddin na kyallara ido na ganki.” Da haka yayi shiru yana kallonta yana murmusawa.

“Is that all? Abun da zaka iya cewa kenan?”

“Eh, yaushe zaki dawo gidanki?”

“Ba zan koma ba.” Tayi saurin bashi amsa tana haɗe ranta sosai.

“What?!” Ya tambayeta yana mai gyara zamanshi kamar bai gaskata abunda kunnenshi ya jiyo mishi ba.

Shiru tayi tana kallon window tana mai cigaba da cije bakinta wanda har ta fasa yayi jini, domin kuwa kuka take son yi amma take da dannewa.

“To yanzu me kike so mu yi?”

“Ka sakeni.”

Baki buɗe Muhammad ke kallonta bayan ta furta wannan kalmomi biyun yana mata kallon kamar bata da hankali. Amma ko me ya gani a fuskarta yasa ya sha jinin jikinshi ya sassauto da murya ya fara magana.

“Yanzu ke da gaske kike yi kina son rabuwa da ni? Ko tunanin Muhibbat ba kya ji ta taso iyayenta basa tare? Kuma ke kenan kullum a yi ta ƙirga miki aurarrakinki? Haba Juwairiyya!”

“Ban damu da ko aure nawa zan yi ba.” Ta faɗa cike da tsiwa don maganarshi na ƙarshen ya ɓata mata rai.

“Haka kika zaɓa?” Ya tambayeta shima yana mai ɗaure fuskarshi.

“Eh.”

“Rabuwan dama kike so tuntuni ko?” Ya ƙara mata wata tambayar.

“Eh.” Tayi ƙarya.

Tana furta hakan ya fara kokawar  buɗe Glove compartment wanda sai da Juwairiyya ta matsar da ƙafarta sannan ya samu ya buɗe ya ciro wata Memo kana ya cigaba da bincike.

“Babu pen, ki shiga ki dubo ko akwai a cikin gidanku.”

Sai a lokacin Juwairiyya ta gane me yake nufi ai kuwa cikinta ya murɗe ta fara jin numfashinta na neman ɗaukewa, shikenan abun da take neman zai faru yau gashi har ana cewa ta je ta nemo Biro.

“Kiyi sauri kar in rasa jam’i za’a shiga sallan isha.” Ya faɗi hakan ba tare da ya kalli fuskarta ba, and he sound hurt.

Jiki na rawa, zuciya cike da tsoro Juwairiyya ta buɗe marfin motar ta fita da kyar har tana cin tuntuɓe da wani ƙaramin dutse da ke bakin motar ta nufi cikin gidansu tana haɗa hanya. A tsakar gida ta tsaya ta dafe ƙirjinta da ke dukan uku-uku kana ta lallaɓa ta shiga ɗakinta inda ta bar Surayya na mata gadin Muhibbat.

“Surayya bani biro.”

Yanda tayi maganar yasa Surayya ta sha jinin jikinta itama ta ji cikinta ya murɗa, fuska cike da tsoro ta ce,

“Me…me za kiyi da shi?”

“Babu ruwanki, ki bani biro na ce.” Juwairiyya ta faɗa tana mai doka mata harara.

“Ni bani da biro.”

Kwafa Juwairiyya tayi ta nufi drawern da Surayya take ajiyan littafanta da take zuwa Islamiyya da su ta fara bincikawa.

“Adda Juwai ki daina wargaza mini guri na ce miki bani da biro.”

Tana gama maganar Juwairiyya ta hango biro ta ɗauko kana ta nuna mata tana cewa,

“Gashi na samu.” Sai kuma tayi hanyar fita Surayya tayi saurin kwantar da Muhibbat ta daka tsalle ta isa gurinta ta kamo hijabinta tana girgiza mata kai hawaye na taruwa a idanunta.

“Don Allah kar ki nemi rabuwa da shi wallahi yana sonki.”

“Sake mini hijabi bana wasa da ke.” Faɗin Juwairiyya ranta a ɓace.

“Wallahi kika rabu dashi ni sai na aureshi.”

“Good luck because you will need it. In dai kan wannan matar tashi za’a kaiki zaki gane kurenki don nima ta ci ubana kuma ban share ba.”

Da haka Juwairiyya ta kwace hijabinta kana ta fita tana jin Surayya na kwalawa Mama kira bayan ta sungumi Muhibbat da take bacci bata san wainar da ake toyawa ba. Da sauri ta fice daga gidan ganin Surayya ta fito ta nufi ɗakin Mama.

Wannan karon Juwairiyya bata shiga motar ba ta zagaya ta gefen Muhammad ta tsaya a bakin window ta miƙa mishi biron ya ƙarba sannan ya yagi paper ɗaya ya ɗaura kan babban memon ya fara rubutu.

Wani kuka ne ya nemi kwace mata amma tayi saurin rufe bakinta ta juyar da kanta gefe duk dama bata ganin komai dalilin hawayen da ya cika mata idanu.

“Me full name ɗinki?” Ta jiyo muryar Muhammad na tambayarta babu ko ɗigon emotion a tattare da shi.

Shiru tayi bata amsa ba har na wasu seconds biyar, sai a lokacin ya ɗago ya dubeta ya ce,

“Kina ɓata mini lokaci kuma na faɗa miki bana son rasa jam’i.”

“Juwairiyya Ahmad.” Ta faɗa cikin dakewar zuciya ba tare da ta kalleshi ba.

Seconds goma da haka ya gama rubutun ya miƙo mata ta ƙarba kana ta shige cikin gidansu tana kuka mai tsuma zuciya.

What the!!!!

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Juwairiyya tana shiga cikin gidan ta samu Mama tsaye a bakin ɗakinta ranta a ɓace sosai, gefenta kuma Surayya ce goye da Muhibbat tana doka mata harara amma bata damu ba domin mugun kallon da Mama take binta dashi shi ya ɗaga mata hankali ta tako ta zo ta tsaya kusa da su tana sunkuye da kai hawaye na zuba a fuskarta.

“Ashe baki da hankali kuma baki da godiyar Allah ko? Ashe haka kike da taurin kai da rashin amfani da iliminki? Shikenan ya sakekin ko?” Wannan tambayoyin da Mama ta mata kenan cikin ɓacin rai matuƙa wanda har Juwairiyya na da tabbacin zata iya jin saukan mari ko duka gaba kaɗan.

Hakan yasa ta kasa amsawa domin tsoro, sai ta fara inda-inda wanda babu ma mai gane maganar da take yi.

“Zaki buɗe baki ki mini maganan da zan gane ko kuma sai na duma miki duka a bayanki?” Mama tayi maganar cikin hasala.

“Shi ya ce in ɗauko mishi biro.” Sai yanzu ta yi maganar da za’a gane.

“Da kika matsa mishi ya sakeki ko?” Ta sake mata wata tambayar.

“Ni ban ɗauka zai yi da gaske ba wallahi.” Juwairiyya ta faɗa wasu hawaye masu ɗumi suna gangarowa kan ƙuncinta.

“Ke kika sani, idan hakan kika zaɓarwa kanki shikenan. Saki nawa ya miki?” Mama tayi tambayar wannan karon cike da karaya domin mai aukuwa ya auku, faɗa da tashin hankali ba zai yi maganin komai ba sannan mutum ba ya wuce ƙaddararshi.

Sai a lokacin Juwairiyya ta miƙa mata takardar da tayi squeezing ɗinshi a hannunta ya zama ball. Rai na ƙuna Mama ta ƙarba ta warware sannan ta fara karanta abunda yake ciki, tana gamawa ta miƙa mata tana cewa,

“Sai ki je ki adana, Allah Ya sa hakan shi ya fi muku alkhairi.” Ta miƙa mata takardan kana ta juya zata koma ɗakinta Juwairiyya ta dakatar da ita.

“Mama saki nawa yayi?”

“Don uwarki ba ki iya karatu bane?” Ta doka mata harara ta shige ta barsu.

Sum sum Juwairiyya ta wuce ɗakinta tana jin takardan sakin nata kamar nauyin dutse ne a hannunta. A bakin gado ta zauna tana dana sanin wannan katoɓaran da tayi, yanzu shikenan ta ƙara zama sakakka? Shikenan kuma ta rabu da Muhammad? Me yasa bata nemi ya raba musu gida ba ta nemi kawai ya saketa? Shin ta yiwa kanta zaɓi mai kyau kuwa? Yaya rayuwarta da ta Muhibbat zata kasance? Tana zaune tana wannan tunanin har aka shiga sallah aka idar, a nan ne kuma Surayya ta kawo mata Muhibbat wacce ta tashi tana kuka ta karɓeta tana bata nono.

“Adda Juwai kin duba ne?” Surayya ta tambayeta tana doka tagumi hawaye na taruwa a idanunta.

“A’a ban duba ba, Mama ta faɗa miki saki nawa ne?” Itama ta mayar mata da tambaya.

“Ta ƙi kulani don rufe ɗakinta tayi ta barmu a falo.”

Juwairiyya tana jin hakan ta gane lallai abun ya girmama, ba dai har saki uku ya mata ba? Tana gama bawa Muhibbat nono ta tashi ta kabbara sallah don tana da alwala, tana gamawa kuwa ta haɗa da shafa’i da witri sannan ta zauna zaman addu’a. Sai da ta gama ta naɗe sallaya ta adana kana ta dubi Surayya wacce tun ɗazu take ta binta da ido ta ce,

“Me haka kin zo kin tasani a gaba kina kallona?”

“Yanzu ke bakya jin kin yi babban kuskure kin rasa wani sashe na jikinki?”

“Don Allah ki barni da abun da yake damuna Surayya. In zaki fita ki kashe mini wuta bacci zan yi.”

“Baki ci abincin dare ba.”

“Bana jin yunwa.”

“Zan faɗawa Mama.”

“In kin ga dama ki faɗawa Nan (kakarsu da ta rasu).”

Wani matsiyacin kallo Surayya ta aika mata wanda ya ƙara tunzura Juwairiyya ta ɗauki ledan wipes ɗin Muhibbat da ke gefenta ta wurgeta da shi amma tayi saurin gocewa ta fice a ɗakin da gudu.

“Wato rainin naki har ya kai haka ko Surayya? To ki kiyayi ranar da zan riƙeki a gidan nan kar ki ga tsayinmu yayi ɗaya.”

Kwafa Juwairiyya tayi kana ta isa ta rufe ƙofar ɗakin ta dawo ta saka Muhibbat cikin net ɗinta kana ta ɗauko takardar sakin amma ta kasa buɗewa, tana sallah babu irin tunanin da bata yi ba, ciki kuwa har da cewa ta kira Halima ta ce mata aurenta ya mutu ko Daddy zai fasa auren waccar matar, ko kuma ya haɗasu duka ya aura amma da sharaɗin zai raba musu gida domin kuwa duk auren da zata ƙara yi a gaba ba zata yarda ta zauna gida ɗaya da kishiya ba. Ta kuma yi tunanin ta zauna a haka babu aure har ƙarshen rayuwarta domin ta gaji da sampling mazan duniyan, dama kuma aure ba dole bane tunda ga Mama ma da ta doshi shekaru masu yawa babu auren kuma bata da niyyar yi. Ko kuma kawai ta ɗauki ƴarta ta gudu inda babu wanda ya sansu su yi rayuwarsu su kaɗai, sai dai bata ɗauki hakan a matsayin option ba saboda how terrible and stupid it sounds.

“Allah Ka sa hakan shi ya fi mana alkhairi.” Ta furta tana mai warware takardar ta fara karantawa.

  ‘Assalamu alaikum uwar taurin kai. Ni Muhammad Dawood ina tare da matata Juwairiyya Ahmad har ƙarshen rayuwarmu. Idan ta yarda da irin soyayyar da nake mata ta shirya next week Friday zamu tafi Abuja, daga nan kuma in ta samu Visa ta bini zuwa UK don attending wani event.’

“Bura uba!!” Shine abun da Juwairiyya ta furta da ƙarfi tana tashi zaune ta juya bayan takardar ta ga babu wani rubutu sai wannan da ta karanta ɗin.

Dafe ƙirjinta tayi da ke bugu da sauri sauri kana ta samu kanta da kasa believing me ta gani, ai kuwa sai ta sauƙo daga kan gadon ta fice daga ɗakin gaba ɗaya ta nufi ɗakin Mama don ta tabbatar mata me ta karanta, ko dai idanunta ne suke mata ƙarya?

A falo ta tarar da Mama da Surayya suna cin abinci hankalinsu a kwance suna kallon Tv, guri ta samu ta zauna bayan sun amsa sallamarta kana ta dubi Maman ta wutsiyar ido wacce tana ganinta ta haɗe rai ta kuma cigaba da cin abincinta.

“Mama na karanta sau da yawa kamar ba saki bane yayi.”

“Ban iya karatu bane?”

“A’a ina nufin ɗazu kika ce Allah Ya sa hakan shi ya fi mana alkhairi.”

“Uwa ba zata yiwa ɗanta addu’a ba kenan a duk halin da ya tsinci kanshi mai kyau ko mara kyau?” Mama ta ƙara watso mata tambaya har lokacin bata kalleta ba.

“A’a, to Mama ba saki yayi ba kenan?” Ƙarin bayani take so don ta gaskata abun da ta karanta ba wai Mama tayi ta mata shaguɓe ba.

“Gashi ai kin gani.”

“Mama ki yiwa Surayya magana don me yasa zata tasani a gaba tana mini dariya?” Juwairiyya tayi maganar tana mai hararan ƙanwar tata da ke mata dariya har hawaye na zuba a idanunta.

“Saboda baki da hankali ne.” Mama ta bata amsa tana mai cire hannunta daga plate ɗin da take cin tuwon shinkafa da miyar taushe.

“Allah Mama baki ga yanda ɗazu take ta salloli tana rafkanuwa ba.” Surayya ta ƙara kwashewa da dariya wannan karon dukkansu suka bita da harara.

“Bana son raini Surayya, kar ki ga na barki ɗazu ki ce zaki rainata. Ke kuma da wa kika bar jaririyar?”

Sai a lokacin Juwairiyya ta tuno da cewa ta bar Muhibbat ita ɗaya a ɗaki ta miƙe tsaye tana cewa,

“To Mama ya zan yi?”

Sai a lokacin Mama ta kalleta a karon farko tun shigowarta ɗakin, nan ta gane ƴar tata is lost tana neman guidance ɗinta ne. A nan kuma ta ji zuciyarta ta sassauto ta dubi Surayya ta ce,

“Ɗauki abincinki ki je ki zauna da yarinyar.”

Babu musu Surayya ta fice ta basu guri kana Mama ta sa Juwairiyya ta zauna suka fuskanci juna.

“Da farko zan faɗa miki kin ɓata mini rai matuƙa da kika nemi saki a gurin mijinki ba tare da na sani ba, yanzu wataƙila yana can yana tunanin nima na san da zancen yana mana kallon ƙananun mutane da basu da haƙuri da sanin ya kamata. Sannan yanzu ke abun alfahari ne a gurinki mijinki ya miki shaidar taurin kai har ya rubuta a rubuce? Haba Juwairiyya! Yanzu ke duk ƙoƙarin mutumin nan baki gani ba kuma bai sa kika sassauto daga dokin zuciya ba? Sau nawa ana koro mata gidan iyayensu wasu har da saki amma daga baya a zo a fahimci juna a koma zaman auren? Ke kanki kin sani wani abun ba laifinshi kaɗai bane har da na matarshi da ta rufe mishi idanu ba ya ganin laifinta, don me yasa ke ba zaki yi ƙoƙarinki na wajen ya gane hakan ko kuma kin yi avoiding sharrinta ba? Maimakon ki nemi ya raba muku gida ku samu sauƙin fitinarta sai kika nemi kawai ya sakeki tunda ke kin zama wawuya. Ina zaki kai ƴar taki? Kin tunanin zai barki da ita ne? Idan kuma ya karɓeta gurin wa zai kaita ta riƙeta in ba matar tashi da kika gujewa ba?” Nan Mama tayi shiru tana kallon Juwairiyya da abubuwan da aka faɗa mata suna yawo a kwakwalwarta.

“Mama to ba sai mu tafi kotu ba,  tunda ko a addini ni ce ke da right ɗin karɓanta?”

Girgiza kai Mama tayi cike da takaici kana ta ce,

“Eh kina da right amma me kuma hakan zai haifar a tsakaninku? Gaba ko rashin jituwa mai tsanani? Yaya kuma ƴar taku zata taso tsakanin iyayenta ana ƴar tsama? Juwairiyya duk ba kya wannan tunanin ne? Me yasa in zaki yi abu ba kya tunanin outcomes ɗin sai dai kawai immediate effect ɗin? You are a mother yanzu, hakan na nufin duk wani tunani da za kiyi ki dinga haɗawa da ƴaƴanki a ciki, idan kin yi kaza me zai haifar miki da su gaba ɗaya. A nan ne sai ki zaɓi solution ɗin da ba zai taɓa rayuwarku ba, ko kuma wanda ke da sauƙi ko da kuwa ba’a son shi. Shin ba kya son mijinki ne?”

“Ina yi.”

“To me yasa don an samu bump a Tafiyar Ku sai ki nemi tsayar da ku gabaɗaya? Shin baki san ko waɗanne ma’aurata suna fama da battles ɗin su bane? Shin akwai waɗanda haka suke zaune babu mai ɓatawa ɗaya rai sannan ba’a samun tangarɗa a tafiyarsu? Juwairiyya kowa, ina nufin kowa na fuskantar matsala a gidan aurensu, ko da kuwa hakan na nufin sun yi mastering zaman rayuwa har suna bawa wasu shawaran yanda zasu tafiyar da nasu auren. Bumps a rayuwar aure ki sa a ranki dole ne sai dai in an kasa controling cuta tayi yawa sannan za’a nemi rabuwa. Yanzu ke menene matsalarki da shi?”

“Mama bai san halin munafurcin matarshi ba, duk abun da ya faru ni yake bawa laifi ba ita ba.”

“To ke a ganinki ta yaya zaku magance wannan matsalar?”

“Ko na faɗa mishi ba yarda zai yi ba Mama.” Juwairiyya ta faɗa cikin karayar zuciya.

“To a nan zan baki shawaran tunda ke kin san halinta sai ki sha maganin zama da ita! A da baki sani bane kika wahala amma a yanzu da kika san tactics ɗinta sai ki dinga dodging kina kuma ƙoƙarin fahimtar da shi ta yanda ba zai gane ƙararta kike kawowa ba, and don’t make it a habit domin zai gaji yace kina yawan kawo ƙararta ko maganarta.”

Gyaɗa kai Juwairiyya tayi tana dana sani a zuciyarta domin tayi wasa da damarta amma yanzu ma wataƙika da sauran chance tunda ta lura Muhammad ba zai iya sakinta da garaje ba. Sai yanzu kuma take tunawa duk da irin tarin laifukan da take mishi da kuma munafurcin Salima a kanta bai saka ko sau ɗaya ya nuna mata yayi dana sanin aurenta ko kuma yana son rabuwa da ita ba. To me yasa ita ta kafe sai an rabu ta ƙi basu another chance?

“Ki koma gidanki Juwairiyya ki ci gaba da haƙuri tunda mijinki yana sonki ba ya kuma wulaƙantaki ko tauye miki haƙƙinki. Sai ki duba a yanayin zaman naku jindaɗin da yake ciki shi ya fi yawa ko rashinsa? To a nan ne zaki gane ba kullum ake gudu ba, watarana taran aradu ake da ka sai a haɗa da addu’a don a samu sauƙin impact ɗinta. Ki je kiyi tunani akan maganganun da na faɗa miki gobe zamu ƙarisa, ina fatan dai har yau kina amfani da ganyen magarya da gabaruwan da ke butan ƙarfen?”

A kunyace Juwairiyya ta ɗagawa Mama kai wacce ko a jikinta ta ce,

“Eh.”

“Good. Zan sa a miki tsumi da dakan su aya sai ki haɗa da su. Allah Ya haɗa kanku ya kau da fitina.”

“Ameen.” Juwairiyya ta amsa sannan ta yiwa Mama sallama ta koma ɗakinta ta samu Surayya na magana a waya, kuma wai wayarta!

“Ke da waye kike magana? Sumayya ce?” Juwairiyya ta samu guri a bakin gado ta zauna tana cire ɗan kwalin kanta kana ta duba Muhibbat da ke motsi a hankali kamar tana son farkawa.

“Ai kullum cikin bacci take da cin abinci shi yasa take ta kumatu tana ƙiba. Ga Adda Juwai ɗin ta dawo.” Faɗin Surayya tana dariya.

Da haka ta miƙawa Juwairiyya wayar ta karɓa ta ga waye Surayya take waya da shi. Muhammad ne kuma sun yi minti bakwai suna magana! Me take faɗa mishi ko kuma shi me yake faɗa mata har na tsawon wannan lokacin? Harara ta dannawa Surayyan wacce ta fice ta bata guri don bata manta da rashin kunyar da ta mata ɗazu ba, gashi kuma yanzu ta ƙara da wani laifin, don wataƙila ta faɗa mishi abun da ya faru.

“Adda Juwai ɗinmu mai kuka.” Shine abun da Muhammad ya fara faɗa bayan ta saka wayar a kunneta.

“You tricked me! Ita kuma sai na karyata.” Ta faɗa tana jin kunya, relief da kuma haushi duk a lokaci ɗaya.

“Ke da Mama idan kika karya mata ƴarta.”

Shiru Juwairiyya tayi tana numfashi a hankali don bata san me kuma zata faɗa mishi ba.

“Kin yi shiru.” Ya ce da ita a hankali kamar ba shi ba.

“Why?” Ta tambayeshi.

“Why? A kan me?” Shima ya mayar mata da tambaya.

“Me yasa baka sakeni ba?”

“Saboda ba zan iya ba. Wannan abun da ya faru tsakanin mu yayi kaɗan da ya jawo saki Juwairiyya.”

“To ya zamu yi Tafiyar Mu tayi kyau alhali muna da banbanci ra’ayi akan abubuwa da yawa? Baka tunanin kullum zamu kasance cikin disagreeing da juna?”

“A hakan zamu lallaɓa rayuwar kamar yanda kowa ke lallaɓa nasu. Ban miki alƙawarin ba zan taɓa ɓata miki rai ba amma ki sani daga yau idan zan yi hukunci sai nayi bincike sosai akan abun, I promise you that.”

“Matarka fa?”

“Me ta yi?”

“Ina son ka raba mana gida don haka ne zai sa mu samu kwanciyar hankali babu faɗa tsakaninmu. Zama guri ɗayan shi ke jawo duk wasu ƙananun maganganu da zai jawo rashin jituwa da fahimta tsakaninmu.”

“For now ina so ki cigaba da haƙuri Juwairiyya har Allah Ya buɗa mini in rabaku, dama gidan da muke ciki na zaman mace ɗaya ce. Ki tayani da addu’a Allah Ya sa in samu abun da nake nema.”

Ajiyar zuciya Juwairiyya ta yi domin bata tsammaci zai yarda da raba musu gida cikin sauƙi haka ba. Ko dai yana lallamata da daɗin baki ne sai ta koma ta ga ba haka ba? Sai dai wani abu da zata yiwa Muhammad shaida shine yana da cika alƙawari sannan ba ya ƙarya don ya burge kowa. Hakan yasa ta ji ƙarfi ya shiga zuciyarta tare da alƙawarin jajircewa har Allah Ya sa ya samu abun da yake neman ya rabata da wannan matar tashi.

“Allah Ya baka sa’a Ya kuma sa alkhairi ne a gareka.” Ta mishi addu’ar da yake so tana mai jin kamar an ɗauke mata wani dutse mai nauyi a kanta.

“Ameen Maman Mamana. Gobe ki shirya ƙarfe goma zamu tafi Immigration office mu miki passport, in kin samu Visa sai ki rakani UK, in baki samu ba sai ki yi tsayawarki a Abuja har in je in dawo.” Yanda yayi maganar so cheerfully ya sa ta ji ba zata iya gwatsaleshi ba ko ta ja mishi aji ba.

Da haka ya dinga janta da hira tana amsawa a hankali har ta ɗan sake sannan suka yi sallama, abun da ya bata mamaki shine ko sau ɗaya bai mata wata magana da zai nuna yana son kaɗaicewa da ita ba  ko makamancinsa, sai dai a maimakon hakan ya mata daɗi tunda kullum accusing ɗinshi take yi da cewa yana son jikinta sai ta zama so worried. Ko dai maganar da ta faɗa ɗin yasa ya daina jin sha’awar tata ya barta da jikinta? Da kuwa ta kwafsa ta cakawa kanta wuƙa da hannunta!

Washe gari tun ƙarfe tara da rabi na safe ta gama shiryawa cikin lace mai kyau ɗinkin riga da siket da ya bi curves ɗin jikinta ya zauna ɗamas. Muhibbat kuwa wacce a yanzu ta cika tayi kumatu sai walwali take yi a cikin shiga ta alfarma da aka mata tana hannun Surayya wacce tace da ita za’a yi tafiyar amma Juwairiyya ta ce ba zata je ba.

“Shi ya kirani jiya da dare yace in shirya zamu je tare fa.”

“To baza ki je ba tunda ba mijinki bane.”

Nuƙu nuƙu ta fara ta fice don kaiwa Mama ƙara a nan kuma Muhammad ya kira Juwairiyya akan ya kamo hanya tace mishi sun gama shiri tun ɗazu. Yana isowa ta karɓi ƴarta da ke hannun Surayya Mama na mata magana,

“To ku je tare mana tunda shi ya ce zata je?”

“Mama ki kyaleta raini take ji dashi, wai har tana ce mini a