Kurkun Kaddara Hausa Novels

Kurkukun Kaddara Chapter 1

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Boss Bature ✍️*

Dedicated to Aunty Kubra❤ _Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata’ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al’ummar Annabi ba.✍️_

*E1*

Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfin gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, jikinsa na sanye da singlet da gajeran wando fari, aƙalla ya kai shekaru 40 a duniya. A launin fata kuwa wankan tarwaɗa ne, da ƙyar yake iya ware manyan idanuwansa a kan katafaren gadonsa kafin a hankali ya mayar da ƙwayar idonsa kan agogon bangon, tafin hannunsa ya kai tare da shafa fuskarsa cikin sanyin murya ya ambaci sunanta, “Angel!”

Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar, cike da mamakin wane ne yake kiran shi a irin wannan lokaci? Anya kuwa Lafiya?

Lokacin da ya kalli screen ɗin wayar sunan Aminina ne ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da ɗaga kiran ya manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, “Aminina!” Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,”Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare.”

A firgice ya dakatar da shi, “Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?”

“Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu…” Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse.

A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa’a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, “Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka.” Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.

Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, “No, no!” Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.

Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon ya zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake  yi masa daɗi duniyar nan.

Yana cikin wannan halin ha’ula’in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, “Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku.” Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel.

A matuƙar ruɗe ya miƙe, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key ɗin motarsa ya ɗauko saboda tsabar ruɗu wardrobe ya dosa zai buɗe a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin ƙofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiɗime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko’ina ba sai ɗakin Angel, bugu ɗaya ya yi ma ƙofar ta buɗe, ko’ina duhu, kunna hasken ɗakin ya yi, nan take haske ya gauraye ko’ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke ƙunshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, “Angel, Angle my daughter!Azeezaty!” Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaɗarsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar Range Rover, back seat ya buɗe ya kwantar da Angel tukunna ya buɗe driver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin, kafin ya koma cikin motar  ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci kusan su shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka da gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror ɗin motar, hakan yasa shi ƙara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La’ila’ha’illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheƙar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.

A ruɗe take furta,”Daddy…What’s happening, where are u going in this darkness night?”

Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.

“Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba.” Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheƙar kuka ta kuma cewa, “Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daɗi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.

Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruɗe ya yi parking ɗin motar ya fito ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya ɗauko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yayi cikin dajin da ita yayin da take sa6e a saman kafaɗarshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare da ya ankara ba, ya ɗaura kafarsa saman wani ƙarfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin ƙasa, kaifinsa tamkar na wuƙa, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin ƙafar ya 6ulo ta sama, wani irin raɗaɗin azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke ƙafarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, “Innalallahi wa’inna ilaihir raji’un.” Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, “Dad let’s go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?” Ta yi tambayar still tana shassheƙar kuka.

Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, “Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne.” Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, “Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji.” Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,

A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin da ya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan da ta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.

Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.

Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi a mace.

A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.

Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.

Guntun tsaki ɗaya daga cikinsu ya ja, “Mala’ika ya riga mu ɗaukar ransa, ba haka na so ba.”

Na gefensa ya ce, “Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir.”

Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, “Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter.” A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.

“Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abu ne mai sauƙi.” Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.

Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.

Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus

*Boss Bature ✍️*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *