Kurkun Kaddara Hausa Novels

Kurkukun Kaddara Chapter 3

*Boss Bature*

Cigaban Labari

Bayan sun samu natsuwa, Aneelerh ta basu shawarar su ta fi asibiti don ta duba lafiyar babyn, Ta kuma Yi mata injections ɗin da ake yiwa kowani yaro da zarar an haifeshi, domin bashi kariya

Atare suka tafi asibitin wanda Ya kasance Mallakin Aneelerh ne, Ƙaramin privet hospital acan aka duba Lafiyar babyn, tana da ƙoshin Lafiya bayan dawowarsu gida Aneelarh taso ta shayar da babyn Amma Taj ya hana saboda gudun kada Ya haramtawa ƴarshi auren ɗansu,wanda burinsu ne shi da Uzair, su haɗa Ya’yan su aure, duk da ita aneelerhn har yanzu shiru,

A ƙarshe sai dai ƙanwar maigadin gidansa  ce Inna kuluwa Take shayar da ita, dama Tana Cikin shayar da jikanta da mahaifiyarshi ta rasu tabar mata, watan shi shida a duniya  shima yabi mahaifiyarshi, baba maigadi ne ya bashi shawarar ya bata Babyn ta shayar da ita, baiyi gaddama ba ya amince, a ranar tazo daga ƙauyen su, Sai da aneelarh taje da ita asibitin su aka duba lafiyar jikinta tukunna aka bata Rainon Babyn, Acikin gidan taj ya ware mata haɗaɗɗen bedroon ɗin da zata zauna,

Ranar suna Yarinya taci sunanta *UNAISAH* shine sunan da mahaifinta ya naɗa mata Amma Yana kiranta da  *ANGEL* a matsayin Nickname dinta, Bayan kammala sallar juma’a akayi naɗin sunan,

Tun ana saura kwana Biyu suna, Mutanan Buzaye suka zo, daga Ciki hada Mahaifiyar tajuddeen Yahanasu ta tsufa tukuf tare da mahaifinshi malam zahiru, hada kakarsu deeeje suka zo, tare da wasu daga Cikin danginshi, a daren ranar da suka ƙaraso, kowa Ya soma tunanin ina Uwar yarinyar take ne, sai a lokacin yake sanar dasu game da guduwar benazir da ta tafi tabarshi da yarinyar, Ran danginshi ba ƙaramin 6aci yayi ba, sunji haushin Abunda Matarshi tayi, dama tun fil azal basu so ya auri bare ba, sun so ace cikin dangi ya samu mata ya aura, don ba yadda zasuyi ne ƙaddara ta riga fata,

A 6angaren Taj kuwa yaso ace uncle abdallah ƙanin mahaifinshi, yana nan a ka yi sunan sai dai kash, tunda jimawa sukayi tafiya zuwa South korea, da ya ke acen kasuwancinshi yafi ƙarfi, duk da haka Sunyi waya dashi, Har video call suka kira shi don ya nuna masu babynsu, aikuwa sunsha ruwan mamakin ganin kyakkyawar ɗiyar tajuddeen, Don ita Hajiya Adama matar Uncle din, cewa tayi da zarar sun dawo nigeria zata ɗauke ɗiyarta, saboda ta raineta ko alokacin Taj bai sanar da su game da Abunda ya faru tsakaninshi da benazir ba, don baiso ya tashi hankalinsu ya bari ne sai Sun dawo tukunna Suji komai,

Alhamdulillah An kammala taron suna Lafiya, ƴan uwa da abokanan arziki sunci sun sha sun shaida Zuwan *UNAISA*  duniya, aranar Tajuddeen kamar yayi hauka saboda tsabar farin ciki, domin kuwa ya samu alheri sosai awurin abokananshi, da kuma masoyanshi don hada key ɗin mota ya samu, ga kuma kayayyakin da suka dinga haɗawa ƴarsa, manya manyan akwatina na kayan baby, shi kanshi ya samu kyautar shaddoji a daren ranar sunan Tare da Uzair suka shiga ɗakinshi suna ƙirga kyaututtukan daya samu, A kalla ya samu kuɗi Sama da 3m, baya ga kayayyakin da ya samu har hawaye saida taj ya zubar, dama shanun da aka yanka ranar sunan bai ƙarasa biyan kuɗinshi ba, bashinsa yaci har uzair na gargaɗin shi akan karya ɗauki abunda yafi ƙarfinshi Ya siya masu rago kawai ya wadatar, Amma yace ina ƴar shi tafi ƙarfin rago sai dai sa.sai gashi Allah Ya rufa mashi asiri,

Sai da su Deeje sukayi Wata ɗaya Cuf tukunna suka shirya komawa Buzaye, Sunyi tunanin taj zai bar masu yarinyar ne su tafi da ita can ƙauyansu buzaye kafin  Ya samu matar aure, Amma ina koda Su ka zo mashi da maganar tafiya da babynshi, Sai ya juya masu ƙeya, alamar bazai bayar ba,don dole suka haƙura, dama deejen ce ta matsa su tafi da ita,amma mahaifiyarshi Yahanasu sam bata ayyana hakan aranta ba, musamman da ta ga yadda Inna kuluwa ƙanwar baba maigadi take kula da ita Sai hankalinta ya kwanta,

Ba ƙaramin alheri taj yayi masu ba lokacin da zasu tafi, kusan abunda ya samu ya kasa uku, ya basu kashi ɗaya,Kashi ɗaya kuma yaba Uzair amininsa, Amma yaƙi kar6a saima ya ƙara mashi sunyi rabuwar arziƙi da iyayenshi Sunata sanya mashi albarka har kwalla saidaya zubar bayan tafiyarsu Allah sarki rayuwa kenan

A 6angaren inna kuluwa kuwa babyn Tana samun kyakkyawan kulawa a wurinta, duk da ba’a tare suke yini ba kuma ba a tare suke kwana ba, saboda taj da kullum yana manne da ita, sai dai fa duk lokacin da  tafara tsala kukan yunwa, dakan shi yake daukar ta yakai ma inna kulu aɗakinta, Yaƙi yarda yabar mata Yarinyar Saboda ya mutu akan sonta, kona seconds baisan rabuwa da ita zuwa aikine kawai yayi mashi cikas, ba ƙaramin abu ke rabashi da babynshi ba, ko aiki yaje yana dawowa jiki na rawa ya ke zuwa ɗakin inna kuluwa ya ɗauketa, idan dare yayi kuwa dama atare da ita yake kwana, Saman kirjinshi yake kwantar da ita Su sha baccinsu,

A daren ranar wata Alhamis ne Yana zaune saman Sofa Yana danne danne acikin Laptop ɗinshi, Ya jiyo sautin dirar motoci a lokacin angel tana a hannun inna kulu, bai kaiga zuwa ya ɗaukota ba, Yana jira ya kammala aikinsa ne kafin ya Amsota don su kwanta,

Zugudum yayi yana jiran ganin wanene Ya kawo mashi ziyara a irin wannan Lokacin Kusan ƙarfe 9 na dare,

Daga wajen Falon yaji anyi mashi sallama, muryar babban mutum,

Da sauri ya kalli agogon dake manne a bango, kusan ƙarfe tara na dare, duk a tunaninshi uzairne don bai ɗauki murya ba,

hakan yasa shi ɗan ɗaga murya tare da cewa”Come In”

Turo ƙopar akayi, a hankali Ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,

Da mamaki akan fuskar taj yake kallonshi,

Babban mutunne yana sanye Cikin kaya na mutunci na hausawa, Shadda tare da malun malun mutun mai cikar kamala,

 fuskarshi ɗauke da murmushi,

Bakowa bane face Alhaji Ubaid Mahaifin Benazir Kaka Ga Angel,

Fuskar taj ɗauke da murmushi ya miƙe tsaye Yana kallonshi, kowannan su da abunda yake saƙawa aranshi,

“Taj nasan ban kyauta ba, wlh naji kunyar haɗa ido dakai,” cikin sanyin murya yayi maganar, da sauri uzair ya qarasa inda yake a tsaye, ya miƙa mashi hannnu don su gaisa,girgiza kai yayi tare da cewa,

“Bana jin zan iya haɗa hannu dakai don bancancanta ba”

Tausayinshi ne ya kama Uzair, cikin sanyin murya yace”kada ka sanya damuwa aranka komai ya wuce,”

Damuwace ƙarara akan fuskarshi”ɗane ka haifeshi baka haifi halinshi ba,”

Murmushi taj ya ɗan saki, kafin ya ruƙo hannunshi zuwa cikin Falon, Suka zauna saman Sofa suna fuskantar Juna,

“Baba yaushe kuka dawo ƙasar bansani ba? ya kuma Jikin naku”?

“Jiya muka dawo, Jiki yayi kyau Alhamdulillah,wlh taj naso nazo tun lokacin da ka kirani waya ka sanar dani rashin Hankalin da benazir tayi maka, Naji takaicin abun nan ƙiris Ya rage in kwashe mata albarka” yakai ƙarshen maganar fuskarshi duk a hautsine, bawan Allah da alama Yaji jiki, tun lokacin da Taj ya haɗu da benazir kafin auransu mahaifinta baya qasar saboda lalurar da ya ke fama da ita, Na ciwon ƙafa mai raɗaɗin gaske,

Alhaji ubaid tsohon gomna ne, bai jima da hawa mulkin ba, Shekara ɗaya kacal Lalurar ta sameshi,Ba ƙaramar wahala yaci ba, Don kowa yayi tunanin bazai rayu ba kullum Ciwon nashi ba sauƙi,ƙara gaba yakeyi,Gashi mutane suna matuƙar sonshi,Yana da farin Jini sosai, adalin shugaba ne mutumin kirki Mai son talakawa, Ga kyautata masu dayawa suna tunanin Abokan hamayyarsa ne suka Yi mashi Asiri, wanda hakan yasa shi ajiye shugabancin, kuma tun daga lokacin zama Nigeria ya gagares hi,da zarar yabar ƙasar Sai yaji sauƙi, da zarar ya dawo sai ciwon nashi ya dawo sabo,tun daga nan ne yabar ƙasar gaba ɗaya tare da Iyalinshi ya koma Dubai da zama, benazir kaɗai Ya bari anan saboda auran da tayi,

“Allah ya ƙara Lafiya, Allah kuma ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada,”

“Ameen ameen tajo, ae ina ganin saƙon gaisuwarka da kake turamun kullum ta waya, Inajin dadi sosai,” shiru suka ɗanyi kafin Alhaji ubaid yaci gaba da magana”Abu biyu ya kawoni wurinka, Na farko ina mai baka hakuri game da abunda Benazir ta aikata mata, yanzu haka maganar da nake yi maka, Na yafeta acikin zuri’ata Saboda bata jin maganata, tafi karfina……”tunkan yakai ƙarshen maganar, taj yayi saurin katse mashi hanzarinshi”kada ayi haka baba, Ayi mata uziri, dukkan mu nan babu wanda yasan dalilin dayasa benazir ta gudu tabar jaririyar ta, Kowa yasan tsakanin Uwa da ɗanta akwai soyayya mai karfi, Ni nasan ba hakanan benazir ta tafi ba, Dole akwai wani abu da yayi silar tafiyarta,

Girgiza kai Alhaji ubaid yayi”bakasan halinta ba ne, ni da na haifeta ni nasan halin kayana, Tagagari kowa, halinta sak dana jatumarta,dama ƙaddara ce tasa na aurota,

Murmushi taj ya ɗan saki”Adaiyi hakuri baba,”.

 “Bazan bari ayi 6arna ina kallo ba, Benazir so take tajamun zagi a idon jama’a, tana so ta zubarmun da mutuncina da kuma ƙimata,sai kace ita ta haifi kanta? Babban abunda yafi damuna, bansan a ina take rayuwa ba,Gaba ɗaya ta kashe layinkan wayarta, nasa A binciko mun ita amma an nemeta ƙasa ko sama babu, Ita kaɗai tasan uwa duniyar data shiga,”dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,

Mu haɗu a Next Page, yanzu wasan ya fara gaba ɗaya book one  Introduction ne wannan story ɗin cakwakiyar dake acikin shi, is hardly to make a prediction about what wll happen next😂 ……………….

*Boss Bature ✍️                       

Taj kuwa tuni jikin shi yayi san yi, duk da ba su yi zaman lafiya da benazir ba, hakan bai sauya komai ba na daga son da yake Yi mata, Yana jinta sosai acikin ranshi, kusan tun ranar da ta gudu, kullum sai ya jaraba kira layin ta da daddare ko Allah zaisa ta buɗe shi, Amma kullum a kashe yake samun shi,

Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mashi tunaninshi”Ka sawwaƙe mata kawai, da ta je tayi ta aikata zunubi da auran ka akanta, don nasan ba dawowa zata yi ba,”

Girgiza kai taj yayi “baba bazan Iya ba, zan jira ta ne har ranar da Allah zai dawo mun da ita nasan zata dawo ne duk mun daran daɗewa”

Gyaɗa kai Alhaji ubaid yayi”Abunda nake fata kenan Yanzu ina jikar tawa take ne? Inaso na ganta,’

“Tana hannun Inna kulu, Ƙanwar matar maigadina ce, itace ke shayar da ita”

“Allah sarki Amma naji daɗi sosai, ka ɗauko mun Jikata na ganta kafin na tafi da yake bani kadai nazo ba akwai escorts dina dake awaje suna jirana”

Amsa ma shi ya yi da toh, kafin ya miƙe da sauri Ya nufi corridor ɗin da zata sada shi da ɗakin inna kuluwa Lokacin daya ƙarasa a kwance ya samu inna kuluwa tana bacci angel kuma na kwance gefen ta an sanya mata kayan sanyi ajikinta, sai  faman tsotar yatsanta take yi, Murmu shi ya saki tare da kai hannu ya ɗauketa Ya fito da ita,

Ƙarasa wa yayi tare da miƙa ma alhaji ubaid ita Wani irin farin Ciki ne akan fuskar shi “Tabarakallahu ahsanul khalikin Taj kaga ikon Allah, Yarinya ƴar kyakkyawa sai kace rainon turai wannan idan ta girma ae zata iya ciyo mana gasar miss world,

Murmushi taj ya saki yana kallonshi addu’o’i ya shiga karanto wa yana tofa mata Taj na amsa ma shi da ameen ameen har ya kammala yi mata addu’ar, Fira sosai su ka yi da surukin nashi, har lokacin Angel na a hannunshi Sai da ya ta shi tafiya ne tukunna ya miƙa ma Taj ita

“In sha Allah zan dinga zuwa akai akai ina duba jikata, Yanzu ka tura mun account number dinka In sha Allah zakaga saƙona”

“Ngde ssae Allah ya kiyaye hanya, idan Anji wani labari game da benazir dan Allah a sanar min”

“Kada ka damu suriki na, duk inda take nasan tana sane da ƴarta da ta bari, kodan saboda ita zata dawo ne”

Har wajen da su ka yi parking na motocin su guda uku, Taj ya rako shi da sauri wani bodyguard Ya buɗe mashi mota ya shiga A jere motocin suka fuce,

Fitar su ke da Wuya, ba zato ba tsammani Sai ga alert na Miliyan 20 ya shigo wayarshi, Ya yi farin Ciki sosai da kuɗinnan dama yana ta tunanin yadda zai tafiyar da rayuwar shi da kuma rayuwar ƴar shi, ga kuma Iyayen shi da yake taimakama wa ga kuma albashin baba mai gadi, Salary ɗin shi basu isa ya dunga ɗaukar duk wani responsibilities nasu, A ranar yayi kwanan farin Ciki,

Bayan Wani Lokaci

Alamu sun nuna cewa Angel ba ƙaramar fitinanniya bace, don tun bayan wata ɗaya da aka haifeta, Taj ya yi ban kwana da yin Bacci cikin kwanciyar hankali, Saboda tsabar kukan ta, da ya ke a ɗaki ɗaya ya ke kwana da ita saboda tsabar son da ya ke yi mata, Kona seconds baison rabuwa da ita,sai suna bacci Idan ta tsala ihu tamkar wadda za’a zare ranta, har asibiti ya mayar da ita don aduba Lafiyarta, Still binci ke ya nuna tana da ƙoshin Lafiya,

Inna kuluwa kuwa da ke shayar da ita lokacin da ta fara Haƙora biyu agaba, Ba ƙaramar azaba take sha ba gartsa mata Cizo take Yi,baiwar Allah Ba ta ta6a sanar da taj halin da ake ciki ba, kullum sai tayi zazza6i duk da tana samun kulawa a wurinshi, Duk wani nauyi nasu ya ɗauke masu shi, Hatta Abincin da take ci wanda ke gina lafiyar jikinta Aneelarh ce ta rubuta masu komai, taj ya siya mata

Lokacin da baby ta fara rarrafe A wata na shida, Tayi 6arna kamar zata haukata masu gidan, da rarrafe take 6aro da kaya su zube kasa ta kacaccalasu akwai ranar da Ta samu wasu mahimman takaddu na Taj, Ta kekketasu into pieces, Ranar Har zazza6i yayi saboda muhimmancinsu kuma idan tayi 6arna taga ya zabga tagumi Yana kallonta Sai ta 6a6aka dariya kamar babban mutun haka sautin dariyarta yake, a lokacin da takai shekara ɗaya da rabi,

Da kanta ta daina shan nono, hakan yasa inna kuluwa ta yaye ta, a washe garin ranar da ta yaye ta, ta sanar da taj maganar komawarta ƙauyen su, ya yi mamakin jin zata tafi duk da irin rayuwar hutun da take yi agidan, Ba don yaso ba ya sallameta, kuma Yayi mata alheri sosai baiwar Allah ita kanta ba don taso ba, tabar gidan sai don zargin wani abu da take yi, Game da Ƴarshi to fah

Bayan tafiyarta kamar an ƙarama yarinyar rashin ji, har tsoro take ba taj saboda ƙarfin halinta, a kwai wani lokaci da ta addabe shi da 6arna, Sai ya dinga ɗaurata Saman Freezer dake ajiye A falo, sam ba ta so Yana ɗaura ta a sama, tun tana mashi kuka a karshe Sai gashi Idan ya daura ta da zarar Ya bar wurin sai ta faɗo kasa, Taci gaba da 6arna Abun Ya ɗaure mashi kai Yarinya sai kace aljana ranar da ta ƙure shi Keji yasa akayi mashi mai girma hada mukullin rufewa Ya sakata acikin kejin Yasa mukulli Ya rufe A tsakar falo ya ajiyeta, shi kuma Ya koma saman Sofa ya kwanta yana kallonta ranta Ya 6aci sosai tun tana gwarancin ta har takai ga fashe mashi da kuka, tausayinta Ya kamashi har baisan lokacin daya  fiddo da ita daga cikin kejin ba, Ya rungumeta yana lallashin ta har ya samu tayi bacci, A daren ranar daga zuwa Yin sallar isha’e, Ya dawo ya taras Ta 6alla mashi Laptop dinshi da yake aiki da ita, idanuwan shi sukayi jawur ga shi bai iya koda yi mata tsawa ne balle aje ga bugu, A fusace ya ɗauke ta ya nufi gidan su aneelerh da ita ya kai ma Su, Yace ya basu kyauta su ruƙe ta awurin su,ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba, hannu biyu suka kar6eta ashe xaune bata ƙare ba A tunanin shi Ya samu hutu Daren Ranar bayan yayi wanka ya zura kayan baccin shi Ya kwanta cike da farin Cikin Yau zaiyi bacci hada minshari,

Wuraren ƙarfe 12:30 na dare, Can Cikin bacci Ya dinga Jin mutsu mutsun mutun ajikinshi, hakan yasa shi farkawa daga bacci, Yakai hannu ya kunna fitilar gefen gadon,

Kamar ance Ya dago karaf idanuwan shi suka sauka akan  baby Angel dake kwance ajikin shi ta ƙanƙameshi, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, a firgice Yake kallonta Har wani murmu shi take sakar mashi, yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniya ba, Abun yayi mugun ɗaure mashi kai taya akai har ta yi wayon da zata iya Kamo hanya daga gidan Taj dake a jikin  gidan shi ta dawo gida ƙarfe 12 da rabi na dare batare da jin tsoro ba,

Jiki a sanyaye Ya shiga yi mata addu’a yana tofa mata asaman kanta, Wai koda shaidanun aljanune suka shafe ta, sae faman lumshe ido takeyi alamar bacci zata Yi,

Babu yadda ya iya haka ya ƙanƙame ta a kirjinshi Yana shafa sumar kanta, Sae gashi bacci Ya ɗauketa bada jima wa ba shima bacci Yayi awon gaba dashi.

Wuraren Sallar asuba, Uzair da aneelarh suka buga uban sammako, Hankalinsu atashe Yarinya ta 6ace, Duk sun ruɗe Suna shiga falon Gidan Suka ci karo da Taj tare da Angel  zaune saman Dining Chairs Hannun shi ruƙe da Kofin tea yana bata abaki tana sha,

A ruɗe suka kalli Juna, saboda tsabar mamaki kafin ma Taj yayi masu bayani Uxair Ya rufe shi da faɗa yana cewa ‘Don me zaije Ya ɗauki yarinya batare daya faɗa masu ba, Yasa duk sun tashi hankalinsu,’sai da ya Kammala zazzaga mashi masifa,

  Tukunna Taj yace”Wlh bani na daukota ba,dakanta ta dawo,

A sukwane Aneelarh tace”Wai dagske ita tadawo da kanta”?

 Kafin taj ya basu amsa angel tariga shi cewa”Eh da ƙafafuna na dawo, kuma ma baba maigadi bashi ya buɗe mun ƙopa ba, ni na buɗe dakaina” tana magana tana cije le6e kamar ƴar daba,

  Tashin hankalin da ba’a sama shi date! cike da tsantsar mamaki suke kallonta, Taya akai har ta iya buɗe ƙopar da ake rufewa da key?

  Girgiza kai Taj yay “Lamarin Baby sai addu’a, Ina kwance jiya wuraren karfe sha biyu  da rabi na dare naji motsin mutun ajikina a she itace ta dawo Ba ƙaramin tsorata Nayi ba”

Tabbas sun fara zargin Yarinyar tana da aljanu shiru kawai sukayi batare da sun sanar ma Taj abunda suke hasashe ba,

A daren Ranar Alhaji Ubaid Ya ƙara kawo masu ziraya, Kamar yadda ya saba duk in yana ƙasar sai ya zo, kuma duk in yazo sai ya kashe ma angel kuɗi kamar hauka kafin ya tafi,

A washe garin ranar da safe Ba zato ba tsammani Sai ga text message an tura mashi da baƙuwar Number, Benazir ce tayi saƙon Bakomai ta rubuta ba face Tana neman Saki a wurin Taj, kuma kada yayi tunanin zata dawo ta tafi kenan har abada abunda yasa ya yi farin Ciki da saƙon sanin cewa tana araye, Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba, Har bibiyar Number da ta tura saƙon yayi amma a kashe ya sameta, Yaji takaici sosai tun yana sa ran dawowar benazir cikin rayuwar shi harya fidda rai, ba don yaso ba ya tura mata da text ta number yasan wata rana dole ta buɗe ta gani, Saki ɗaya yayi mata acikin saƙon daya rubuta mata….,……

A ranar  Uncle abdallah ya dawo Nigeria, Uzair ne da kan shi ya ɗaukosu a Airport zuwa gidansu, tsabar farin Ciki a wurinsu bakinsu kasa rufuwa ya yi musamman Taj, hajiya adama tayi murnar ganin su Cikin ƙoshin lafiya Ranar yini tayi da angel awurinta, tun dawowar su Angel awurun su take kwana, Bakomai yafi ba Taj mamaki ba face irin yadda yarinyar  take natsuwa agaban mutane, Amma idan shi da itane tadinga 6arna kenan kamar 6eran gida,

****Boss Bature******

A kwana atashi. Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea, Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya, duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure rabuwa da ita, Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi, Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki, ko 6ari bata ta6a yi ba a bun ya dame ta sosai, Shi kan shi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa, har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu, Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi, Lokacine baiyi ba ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalin su harya basu Labarin Iyayen shi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa, Tunda suka ji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu,

A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji, Ashe Yanzu wasan Ya fara,

Tun tana da shekara Uku Ya sanyata  nursery, hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata, rana ta farko da ta fara zuwa makaranta, ta samu ƴa’ƴan mutane ta dinga gartsa masu Cizo, Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta, saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta Saboda baza su Iya Control ɗinta ba, ga shi ya hana a dukar mashi ƴa ko tsawa Baiso Ayi mata sai dai bayan idonshi.

Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa’ƴan mutane, tun da yayi mata faɗa abunda bai ta6a Yi mata ba a ranar har fushi tayi taƙi cin abinci, daƙyar Ya lallashe ta ya samu suka shirya da ita,

Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece, tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado, a tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba, bayan fitarshi Da rabin awa ta farka tana Jin yunwa gashi Sam bata da juriyar Yunwa,

Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar Ɗaura girki, Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din, Dama tasan Yadda yake kunneshi Saboda wasu lokuttan a tare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki, To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta.

Yana Wurin aiki Aka kira shi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi, Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan.

Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi, Duk yabi ya ruɗe babban tashin hankalin shi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta, da gudun gaske Ya fada Ciki gidan, Su uzair suka bi bayan shi dama sunzo hada aneelarh, A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo, Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi,

Sai da suka gama shan wahalar nemanta, Ba zato ba tsammani suka same ta a cikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha.

Da gudu suka nufe ta gaba ɗaya suka rungumeta, kowa ya na faman sauke ajiyar Zuciya,

Abunda Ya faru  a she bayan ta kunna gass, ta sauko daga saman Chair ɗin, Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha, Sam ta manta da tabar gass a kunne, duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita ba ta ji ba, Baba maigadi ne Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Ciki  don yaga me ke faruwa, koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi, Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman a gaji,

Angel tasha fada awurin Taj kuma duk da laifin da tayi ma shi ko dungurin ta bai yi ba, kadan daga Cikin munanan halin angel shine, Bata barinbshi yayi bacci muddin ta farka, to shima dole ya farka baccinshi Ya qare, Idan suka fita Yawan shakatawa komai ta gani tana so, koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi idan ba haka ba hmmm xa’aga tashin Hankali, Bayan wannan Ta iya jan faɗa idan suka Je anguwa, komai ta gani saita dauka ta jefar, Ayita nema tana ji bata faɗin ita ta dauka.

duk duniya babu wanda bata Jin tausayin shi Irin mahaifinta, azabtar da shi take Yi, Shi kuma Ya mutu akan sonta Bai iya rabuwa da ita ga shi ta tsani taga yana karatul Alqur’ani, da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun, kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba idan uziri ya hana shi zuwa masallaci, Kamar shaiɗaniya haka take, har malami aka dauko yayi mata addu’a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu, tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta, ta dinga buge mashi hannu tana faɗin dama ya daina wahalar dakanshi, Ita lafiyarta qalou

Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya, Ta sace takalmanshi ƴan madina, sai da ya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗauke su, su ka yi ta nema kasa ko sama babu su, bayan tafiyarshi ta fiddo takalman da ta 6oye a ƙarƙashin gadonsu taba Taj, wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta, haushi kamar Ya rufeta da bugu, yaji kunyar abun nan haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abun sa,

Babban abunda zai baka mamaki da ita sam bata da tsoro, yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon har ta Iya kunna kallo, tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta,

Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radion su, Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe, Tasa key ta rufeshi, dalilin da ya sa Ta yi ma shi haka shi ne, Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair, Ita kuma bata son zuwa gidan tafi son duk inda zai je ya tafi da ita, Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakin shi bayan ya shiga wanka, Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai, Ta murɗa mashi key ta datse ɗakin Ƙarfin Hali,

Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga  uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,

Saboda bala’in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daɗi, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa,

Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,

Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini,

Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi “Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,”

Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya  yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace”Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata” Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje”Kije ki nemi wani uban”

Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama’a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin “Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa”Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa’yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba

Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.

Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,

A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,

Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya’yan mutane,

A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,

Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.

Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,

Har kiran Angel a kayi daga  office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.

Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,

Ba’a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.

Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin “Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin,”

  Copral ne Ya bata amsa da cewa”Ana zargin su da sace Ƴa’ƴan mutane suna amfani da su”

  Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace

  “Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba…..”bata kai ƙarshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta”Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu,”

  Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin, Cikin sanyin murya ta furta”where’s the evidence”?

Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office ɗin shi

A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,

Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baƙin zalunci,” yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen,

Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami”You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce,” muryarta a disashe takai ƙarshen maganar,

“Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi,” acewar dpo,

Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel,

  “Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne,”

  Da buɗe bakin angel sai cewa”Ni ƙarya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae”

Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa”You are under arrest” ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa

Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa”Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani.

  Girgiza kai Dpo yayi”Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne”

  Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution”

 Jinjina kai dpo “Good idea Copral”Dpo ne ya kira sunan shi

  “Yes sir” ya amsa mashi.

  “Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku,”

  “Consider it done sir” Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi,

A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel,

Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men ɗin akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,

Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi,

Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,

Bin shi da kallo kawai aneelerh  tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta ƙalou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou “

Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba, da yake suna waya dashi kusan kullum ne sai sun kira su kosu su kirasu, A ƙarshe suka koma gida da yin jinya, Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu jin Abunda ya faru da shi, Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba, kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane, ya yi hakan ne saboda sanin halin su na ƴan jarida, yanzu ka ji labari a social media,

Bawan Allah Taj kullum yana kwance saman gado, Wanka da sallah ne kaɗai suke tada shi Wani sa’in yana ɗangya shi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet, Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba sai in tana jin yunwa ne zata addabe shi wai ya tashi yayi masu girki, in ba haka ba zata je ta daura da kanta,

In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar  dashi, dama Cikin ƴan kwanakin nan mai aikin su Uzair hada Su taj take girka ma abinci duk in za ta yi, bisa umarnin Uzair ɗin,

Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko’ina Yana gida, Wuraren ƙarfe biyar na marece, ya fitowa daga wanka jikin shi sanye da short baƙi, saman Gado ya haye bacci mai daɗi ya ɗauke shi Yayi nisa acikin Baccin shi, Yadinga Jin  Hayaniya acikin gidan jiki a mace Ya miƙe daga saman gadon ya nufi ƙopar ɗakin, Leƙawa yayi don yaga  su wanene

Waro ido waje ya yi ganin mutane maƙil Cike da falon, Kasa kunne ya yi yana sauraran me suke cewa

  “Allah ya jiƙan shi, Taj mutumin kirki halinshi na gari Ya bishi,”

 Can kuma yaji wani yace”A ina ne za’ayi jana’izar ta shi”?

 Wani ya ba shi amsa da cewa”Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji,”

  Shiru yayi la6e bakin ƙopar Ya kasa fitowa, Jikin shi duk yayi sanyi, tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu? dama akwai wani taj ne bayan shi”? sam bai da mu da rashin ganin angel ba yasan bata wuce Gidan su Uzair.

Komawa Cikin ɗakin yayi Jikin shi duk ya mutu, Wayarshi Ya ɗauka da ke a jiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs, Nan yaga missed Calls sunyi ɗari uku na mutune, abun ya ɗaure mashi kai,

Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira, Tana fara ringing uzair Ya ɗaga,

  “Assalamu alaikum” batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa”Uzair kana ina ne”?

  On the other hand Uzair yace”Gida mana”

  Cike da damuwa yace”Uzair na shiga Uku, Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana, Na kuma taras da missed calls a wayata Ya yi ɗari uku na mutane wai meke faruwa ne”?

Muryar uzair da ɗan ruɗi yace”Kodai angel tayi wani abu ne? bata jima da shigowa Gidan mu ba, Take sanar dani cewa Ta ɗauki wayarka kana bacci, Ta sanya yatsan ka ta buɗe ta “tunkafin Uzair yakai ƙarshen maganar ta shi, Taj Yayi rejecting call ɗin, Ya shiga laluban wayar shi, Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appearing, Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi, A hanzarce Ya shiga facebook dinshi, a nan Yaga hoton shi dana angel ta ɗauka yana bacci tayi share ɗinshi a facebook, a ƙasa ta rubuta RIJF, Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawan su sunyi tunanin ko matarshi ce Tayi amfani da wayar shi donta sanar masu mutuwar shi, Shine suka kwaso ƙafafuwansu zuwa Gidan don a yi jana’ixa da su.

jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasar shi, lalla6awa ya yi tare da samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha, Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta, da kuma abunda zai yi silar bari na duniya ashe ƴar Cikina ce, Laifin me nayi mata ne da ta tsane ni? sai ka ce ba mahaifin ta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta wayyo Allah na,

sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF, a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta’aziyar shi, daga ƙasan hoton shi aka Sanya RIJF, Rest In jannatul firdaus, shine take tambayar shi wai me yake nufi, da yake ta iya tambaya kamar yar jarida, Bai yi tunanin komai ba ya sanar da ita ma’anar hakan, Shine tayi mashi aika aika.

Kiran Uzair Ne ya shigo wayar shi, A sukwane ya ɗaga Kiran a nan yake sanar da shi abunda ta aikata mashi, Uzair yasha ruwan mamaki

A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba, Yana a raye mistake aka samu wurin Yin posting din, ƙin tafiya sukayi Har sai da suka ga Taj da ƙafafun shi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah ya kyauta, A falo suka zauna gaba ɗayan su, Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine,

  “Yanzu menene mafita”? taj ne ya yi maganar yana kallonsu,

  “Lamarin Angel Yafi ƙarfin mutun sai dai Allah, ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruƙiya ta sace takalman shi, tun daga nan Jikina Yayi sanyi,” acewar Uxair,

  “Benazir ta tafi tabarmun bala’e” tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,. 

  “Me zai hana ka jaraba Bugunta”? a ɗan firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar,

 Cigaba da magana tayi”Idan har ba za ka iya bugunta ba shawarar da zan bada shine, Kasan mafi a kasarin ƙananun yara akwai abunda suke tsoro, Ni ina ganin a jaraba samo Mage ko kare ko kuma ƙadangare, Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu, Sai adinga Yi mata Baraza na da shi, Koya kuka Gani”? tayi tambayar tana kallon Taj, wanda ya yi zugudum yana kallonta, yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare, Taya zata Ji tsoron waɗannan halittun, Acikin zuciyarshi ne yayi maganar,

 Jinjina kai Uxair yayi”Good idea idan na fita Yanzu xansa Almajirai su ɗauko mun ƙadangare a fara jarabata dashi, inyaso gobe sai a kawo karen Nasan dole asamu wanda take matuƙar tsoro acikinsu,”

  “Allah yasa dana fi kowa Farin Ciki” acewar Taj,

Sun jima suna tattaunawa kafin Su ka yi ma shi Sallama, Atare suka bar gidan,

Duk dabbobin da aka kawo gidan don angel ta tsorata amma abun ya ba su mamaki bata tsoron su, illa ma ita dabbar da aka kawo taji tsoronta, yarinyar ta zarce tunanin mai tunanin ga karfi Allah Ya yi mata, Ranar da taj yasa aka kawo mage agidan Sai da ya yi dana sani,

A lokacin Yana kwance yana bacci Ya barta a falo ita da magen da ta sanya ma suna Chu chu, suka soma kokawa tana kiciniyar kamata,  magen ta watsa aguje tana kuka, tabi bayanta da gudu suka shiga zagaye palourn, Sune har cikin kitchen, Magen ta haye saman Dish racks, inda Jerin Plates na tangaran suke, Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din, Suka tarwatse kasa duk suka faffashe, Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran, Ruƙo ƙafar magen Angel ta yi, Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse, Kubce mata magen tayi da gudu  ta sauko ta nufi Store da kopar shigar shi ke anan cikin kitchen ɗin, Aguje angel tabi bayanta, Suka shiga yin yar tseral, Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su, A ƙalla sunyi crates goma sha biyu, Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe, hayewa sama magen ta yi inda aka jera Sunƙi sunƙin bready, Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja, Ta haye samanta Ta cakumo wuyan magen, jarkar da ta hau saman kanta ce ta Karkace da ita da magen Da jarkar man, Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa, Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa, bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi, tamkar Bola, uk Ta hargitsa komai ba,

Da ta ga Ta yi 6arna sosai, saita Saki Cucu, Ta ruga da gudu ta nufi gate, A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib, Ya hangota ta nufo shi,

Tunkafin ta ƙaraso Take nuna mashi gate ya buɗe mata, Sanin Tsiwarta yasa Ya buɗe mata ƙopar jikin gate ɗin ta fuce, Sai gidansu Aneerlerh lokacin da ta shiga Gidan, A bedroom ta samu aneerlerh ta kabbara Sallah, Saman Gadonsu ta haye Taja bargo ta kuɗunɗu ne, Bayan aneelerh ta kammala Yin sallar,t ana daga zaune saman darduma ta kalleta”Angel Lafiyar ki kuwa”

Kasa ƙasa da murya tace”Zazza6i nake yi”

“kin sha magani”

“Eh nasha, daddy ne yace inzo wurin ki kiyi mun wanka,i n ya dawo daga masallaci zaizo ya dauke ni”

Mikewa aneerlah tayi, bayan ta cire hijabin ta tura a wardrobe,

“Tashi muje nayi maki wankan”

Yaye bargon tayi ta sauko daga saman Gadon, rigar jikinta duk ta cukuikuye, hada manjan daya gogu agaban rigar,

  “A haka kika hau mun gadona? Ina kika samu manja ajikinki”

  Ashagwa6e tace” nace maki bana lafiya, Ni bana iya magana sosai”

  Sam aneelerh ba ta yarda da ita ba ta ƙyale ta ne kawai,

Within minutes ta yo mata wankan, suka fito daga cikin toilet, ta shafe ma ta jikinta da mai, canza mata kaya tayi, dama Saboda Ita ta sayi kayan Yara dai dai Size dinta, saboda sun ɗauke ta tamkar ɗiyarsu, pink gown ta sanya mata,ta kuma ɗaure mata sumar kanta da ribbom,ba ƙaramin kyau tayi ba, hada light make up aneelerh tayi mata,

“Aunty aneelerh,Z an koma saman gadon in kwanta, dan Allah ki hadamun fura, A sanya kwakwa da yogurt aciki da ƙanƙara”

Jinjina kai aneerlah tayi fuskarta dauke da murmushi tace”Okey My daughter in law, je ki kwanta,”da gudu taje ta haye saman gadon,

Bayan Aneerlerh ta hado mata furar a cikin Cup ta kawo mata Nan ta zauna tasha ta ƙoshi, kafin ta koma ta kwanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,

A 6angaren Taj kuwa, Lokacin daya tashi toilet ya shiga, ya dauro alwala ya dawo Cikin ɗakin Ya dauko Jallabiya Cikin Closet din shi Ya zura ajikinshi, Fitowa ya yi daga ɗakin yana ta faman sauri Ya fuce zuwa masallaci,

Bai tashi sanin aika aikar da Angel tayi mashi ba, Sai daya Dawo daga masallaci, wata irin yunwa ta farmasa, ba arxiƙi Ya nufi kitchen shigar shi keda Wuya Tun abakin ƙopar yaci karo da Fasassun kwanukan da angel ta 6aro, A razane ya dago yana kallon cikin kitchen ɗin, har wani haya ki yake ganin cikin idon shi saboda tsabar 6acin rai, ashe bai ga komai ba sai daya Shiga Cikin store, Hannu ya ɗaura akai yana ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Nashiga Uku! Na bani!

Ya Allah laifin me nayi aka jarrabceni da Angel? wani zunubi na aikata, dafe baki yayi da sauri jin sabon da ya yi yana mai fadin astagfurullah…..” yana cikin sambatun nan yaji kukan Mage, Aikuwa a harzuƙe ya juya ya kalli magen dake a bakin kopar store ɗin, Shaƙo wuyanta yayi tare da jijjigata Yace”Ke da ubanwa ku ka yi wannan”?

    Ƙura mashi ido magen tayi tana Cigaba da yin kukan Yunwar da take yi, wurgi yayi da ita, tare da naɗe hannun rigar shi Ya fuce daga gidan, kaitsaye Ya shiga Gidan Uxair, tun a bakin gate mai gadin Gidan Ya soma tambayar shi”Yalla6ai Lafiya”

Baiko tanka mashi ba Idonshi Ya rufe, Angel kawai Yake nema Ko sallama bai tsaya Yi ba Ya faɗa Cikin Falon Gidan, Ganin bakowa Yasa shi fara kwala mata Kira”Angel!Angel!Angel!!’ tamkar makoshin shi zai 6allo,

Da gudun gaske Aneelerh ta fito daga bedroom ɗinta Jin muryar Taj Cikin tashin hankali,

“Me ya faru ne”?tayi tambayar tana kallon shi,

  “Where is Angel”?

 “Ɗazu ta shigo bata Jin dadin jikinta, yanzu haka bacci take yi adakin”bata kai ƙarshen maganar ta ba, Ya wuce ta a fusace Ya faɗa dakin, Can ya hangota saman gado a kudundune tana ta sharar bacci,”

Hannu biyu yasa ya Cakumeta, da sauri aneerlerh ta biyo bayan shi Tana tambayar shi Meya faru ne,

Da budar bakinshi sai cewa yayi”kashe ta zanyi,”

Yana faɗin  hakan  ya nufi hanyar fita da ita, gida Ya koma da ita a dakin su Ya jefar da ita saman gado, sai lokacin ta farka tana kallon shi da manyan idanuwanta,

  “Daddy what”?

“Zaki Ci ubanki ne” ya faɗi hakan tare da Janyo pillow Ya hau saman gadon Ya turmushi fuskarta dashi, Mutsu mutsu ta shiga yi, tana kokawar fitar da numfashinta, sae faman harba ƙafafunta take Yi, tana neman Ceto,Amma Taj sam Babu alamar zai sarara Mata, Saboda Baya acikin Hayyacinshi Dagasken kasheta Zai yi,

Faɗowa ɗakin aneelerh tayi ko takalma babu a ƙafafuwanta, Anan ta same shi Saman Gadon Ya danne angel Da pillow, A gigice ta fasa ƙara, Tare da yin kukan kura Ta haye saman Gadon, Da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta cakumi wuyan jallabiyar jikin Taj tare da Yin Wurgi dashi gefe guda Ya faɗa  saman mattress din,

Cikin shessheƙar kuka take fadin”Taj ban sanka da haka ba, meyasa zaka yanke hukunci Cikin fushi ne? Meye ribar ka idan ka kashe Angel?yarinyar da ba ta wuci 7years ba, idan ka yi hakuri Wata rana zata daina ne,

“Wlh bazan ƙyaleta ba Kafin ta kashe ni, Ni zan fara kashe ta,” ya ambaci hakan tare da yunƙurawa Ya miƙe Yana ƙoƙarin Cakumar Wuyan angel da ta sume, da sauri Aneelerh Ta sanya hannu ta ɗauketa, tana ƙokarin sauko wa da ita daga saman gadon, A ƙokarin Ya damƙo angel Ya janyo wuyan rigar Aneelerh gaba ɗaya aneelerh tayi baya ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi, Angel kuma ta yi gefe ɗaya saman gadon,

Karo na farko da jikinta ya fara ta6a namijin da ba muharraminta ba, shi kan shi bai yi tsammani hakan zata faru ba, saboda ba ita yayi niyar Janyo ba, Angel da ke a hannunta Yaso Ya damƙo, hatta mayafin da aneelerh ta rufe kanta dashi ya warware sumar kanta mai tarin yawa ta sauka har saman kafadarta, wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarci kowan nan su, ƙoƙarin miƙewa aneelerh ta yi sai dai ina wani magnet ne ya ruketa, Runtse idanuwanta tayi da karfi ta soma ambaton a’uzubillahi minasshaiɗanirrajim, tun da ta ambaci hakan sai ga shi ta samu ƙwarin guiwar Raba jikinta daga Na taj, aikuwa A gaggauce ta hanzarta sauka daga saman gadon, ko mayafin ta bata tsaya ɗauka ba ta watsa da gudu tabar ɗakin,

A hankali taj ya lumshe idanuwan shi, ya yin da hancin shi ke shaƙar mashi ƙamshin turaren Jikin aneelerh daya gauraye Jikinshi, bakomai Ya tuna ba face Matarshi da ta gudu tabar shi, maca ce mai matuƙar son ƙamshi, shima kuma  ma’abocinsa ne, baisan Ya akai ba Ya tsinci kanshi da tariyo yarda Aneelerh ta faɗo saman ƙirjinshi, da kuma yadda yalwataccen gashin kanta Ya zubo har a jikinshi,da kuma daddaɗan ƙamshin turaren ta,

Ganin Zuciyar shi na ƙokarin Zayyana irin kyawun surarta ne yasa shi saurin Ambaton A uzu billahi minasshaiɗanirrajim, Astagfurullah Ya Allah,

Miƙe wa Ya yi zaune Duk kasala Ta rufe shi, saukowa yayi daga saman gadon ya fito palour, babu kowa Hakan ya tabbatar mashi da cewa Neelerh ta gudu, frigde ya buɗe ya dauko Swan Mai sanyi ya dawo bedroom din shi, daga gefen gadon Ya zauna, buɗe murfin yayi ya tarfa ruwan a hannunshi Ya watsa ma angel asaman fuskarta, nan take Taja dogon numshi,

Slowly ta buɗe idanuwanta akan fuskar shi, Suna hada ido ta fashe da matsanancin kuka,

Natsuwa yayi yana kallonta ko kusa baiji tausayin kukan nata ba, tun da ya lura Ba son shi take Yi ba,

Cikin shessheƙar kuka tace “You want to kill me because you don’t love me, yanzu da na mutu Allah zai kamani, so kake in shiga wuta ko? ta yi tambayar tana kallonshi, har lokacin idanuwanshi na akanta baice uffan ba,

  “Kana Jina ka share ni ko”

Gyaran murya ya ɗanyi can kasan makoshin shi ya furta”Dama kina tsoran Mutuwa”!

 A tsiwace tace “Eh mana,malamin mu ya karanta mana wani hadithi wanda ke magana akan mai munana ma iyayensa ba zai shiga aljanna ba, A wuta za’a babbaka shi……”

Ƙiris Ya rage taj ya ɗan murmusa”So you know that but u keep hurting me ko”?

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan, Ganin tasha Jinin jikinta sosai yasa shi kwantowa Yayi mata rumfa da faffadan kirjinshi, cikin sanyin murya ya soma magana Yayin da idanuwan su ke kallon Cikin na Juna,

“Angel, zan sanar dake wani abun da baki sani ba ba ki da wanda yafi ni a duniyar nan, ba ki ta6a tambayata mahaifiyarki ba, Bansani ba ko kina tunanin Namiji yana iya haihuwa ne, Shiyasa kike ganin kamar ni na haife ki, Baki da abun wulaƙantawa Irin mahaifin ki,” shiru ya ɗanyi yana nazarin wani abu, ita kuwa ta kasa kunne tana sauraronshi,

Cigaba da magana yayi”Angel, mahaifiyarki a wulakance ta haife ki, Cikin bathtub tabar min ke, Cikin Jini kina ta kuka, Ni ina bacci kukan ki ne Ya tashe ni haka naje na sameki, Na ɗauke ki na rungume ki ajikina, duk da jinin da ke ajikin ki, Ni ban gudu nabar ki ba, kuma ban bari kin wulaƙanta ba, Sai da na tsaya akan ki angel da taimakon Allah har kika kai wannan lokacin, Tun da ki ke ƙuntatamun dai dai da na rana ɗaya ban ta6a Tunanin na tafi nabarki ba, kuma ban ta6a tunanin in sanya hannuna wurin ta6a lafiyar jikin ba amma angel……”kasa ƙarasa maganar Ya yi jin yadda ta rushe da kuka kamar ranta zai fita, ɗagowa Ya yi zaune yana kallonta.

Hannu ta ɗaura akai tana faɗin “Wayyo Allah na nashiga Uku,Na bani Na lalace!” hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,njin yadda babyn shi take Kuka,

Lallashinta ya soma ƙokarin”Am really sorry daughter, I don’t mean to hurt u darling, Na faɗa maki ne don ki ɗauke ni da muhimmanci, don ki san cewa Ina sonki, kuma ina buƙatar tausayawa daga gare ki,” bata tsaya sauraronshi ba, Ta sauko daga saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe,

A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta, tura ƙopar yayi ya ji tayi Locking dinta,

Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta”My angel am sorry, kada hakan Ya ta6a zuciyarki, kinsan ina sonki, banason zubar hawayen ki”

Daga Cikin toilet ɗin yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faɗin”I hate my self daddy, cikin toilet aka haife ni, kuma ta gudu tabar ni saboda bata sona……”

  Runtse idanuwan shi Yayi tare da ɗan Cizon lips ɗinshi Calmly ya kira sunanta”Angel pls forget about it, Tunda kina da ni don me zaki damu kanki? Ni ne mom dinki kuma daddyn ki,

  Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar, yana ji aran shi cewa tana zaune a gaban ƙopar, tsit ya ji ta daina kukan

  “Pls say something to me, ko naji sanyi acikin zuciyata”

   Shiru bata tanka mashi ba,

  “Ki buɗa mun ƙopar”

 Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa”daddy inaso na mutu, kodan saboda nadaina 6ata maka rai”

  Cikin matsananciyar damuwa Yace”idan kika mutu angel shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima, saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa,”

Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin, don Yaji daɗin Jin muryarta

 “I made a mistake daddy, I won’t hurt you anymore,”

Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya ɗan  dago da kanshi, yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne,

“I love u daddy” ya kuma Jin ta furta mashi aruɗe yace”Repeat it  pls”

  “I love u daddy”

“sake maimaita mun naji”fuskar shi ɗauke da murmushi Ya yi maganar,

 Sake maimaitawa ta yi kamar yarda ya nuna yana son ta yi ma shi,

“I love U daddy, Bani da tamkarka a duniyar nan”

Wani irin ihu ya saki, Irin wanda Ƴan kwallo ke yi idan sunci nasara akan wasan su,

A ƙagare Yace”Come out pls, ina so naji ɗumin ki a jikina”

Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar kamar jira yake yi, tana ƙarasa buɗe wa Ya janyo ta Jikin shi yayi hugging ɗinta very tight, hannun shi na acikin sumarta, Wani irin farin Ciki ne Ya lullu6e shi kamar wanda a ka yi ma Albishir da gidan Aljanna,’ dole Taj ya yi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana son shi a  mtsayina mahaifinta, Ya ji tausayinta sosai, bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau, da ta ji cewa mahaifiyar ta ta gudu ta barta, Jikinta ya yi sanyi, da yasan da haka da tuni ya faɗa mata, da duk wannan abun bai faru ba,

daukarta Yayi asaman bayanshi, yakaita Cikin motarshi, atare da ita suka je masallaci, Ya barta acikin mota, Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant, komai take so shiyasa aka kawo masu, sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Suka dawo gida, A palour suka zauna saman Sofa tana rungume ajikin shi, Suna kallon tashar Mbs 3, dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon, tafi sha’awar kallon Cartoon da kuma zombie,

Tuni bacci ya dauketa ajikinshi, asaman kafaɗar shi ya ɗauke ta Ya nufi bedroom dinsu, don ya kwantar da ita, a hankali Ya tura kopar ɗakin Ya shige, A saman gado Ya kwantar da ita, Sai da ya fara daukar wayar shi dake ajiye agaban mirror, Tukunna Ya haye saman gadon ya janyo ta a jikinshi, Yana shafa sumar kanta, cikin magagin bacci ya ji tana fadin”I luv u daddy” murmushi ya ɗan saki, Tare da manna mata kiss a gefen fuskarta

 “Luv u too My own daughter”

Number Uzair Ya kira, tana fara ringing Uzair ya ɗauka,

 “Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikin ka”

  “Na hutasshe ka ba sai kazo ba, Jiki ya yi sauƙi Alhamdulillah”

  “Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe ƴarka, Ae ni har na yi shirin zuwa ɗaukar rahoto”

  Fashewa Taj yayi da dariya”Ta

6atamin raine, ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba,”

  “Yanzu Ina virus ɗin taka take”?a cewar uzair, don tun ranar da ta Sa ƴan sanda su ka kama su akan ƙazafin da ta yi masu na cewa su ƴan yankar kai ne, tun daga ranar Yake kiran ta da Virus,

Murmushi Taj yayi, tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel, Virus ta yi bacci, Mutumina ka ta ya ni farin Ciki,”

 Uzair yace”Meya faru”?

  Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakanin shi da angel ya sanar mashi,”

 Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi,

  “Ja’irar taji ƙamshin mutuwa, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ce tazo, Amma fa nayi farin Ciki,

“Ameen mutumina”

Shiru suka ɗanyi,yana so ya tambaye shi aneelerh amma ya kasa,

 “Muyi video call mana”acewar uzair,

Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call, A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu, ya dan tada kan shi saman pillow, jikin shi na sanye da kayan Bacci,

 “Show me her face” murmushi taj ya yi tare da haska mashi fuskar angel, ta sa ki baki da hanci tana ta sharar bacci,

  Dariya uzair yayi”waya ga  mashasha, wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a, a haka zata zama surukar mu,”

 Fuskar Uzair ɗauke da murmu shi yace”cin mutuncin ya isa haka aminina, kai ka sani Wlh angel koda kuɗin mutun saida rabon shi, koda rabon shi sai in Allah ya nufa”

 Jinjina kai Uzair Yayi tare da ɗan yatsina fuska yace”Virus ɗin”?

Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani, adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet, Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya, Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakin shi baya, wanda hakan yasa har Taj ya iya hango fitowarta,

Baisan ya a kai ba Ya tsinci kanshi da satar kallonta, Ya bar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daɗi, gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel,

“Me kake tunani ne”? a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair, muryar shi na inda inda yace”Bakomai zan kwanta mutumina, Sae Allah yakaimu,” da sauri ya yi rejecting kiran tunkafin ma uzair ya yi mashi sallama,

Lumshe idanuwan shi ya yi zuciyar shi a cunkushe, duk yadda yaso Ya hana kan shi tunanin abunda ya faru tsakanin shi da aneelerh abun ya faskara, daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba da shi,

Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba, koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakanin su, mutu ka raba takalmin kaza, tabbas Angel taba kowa mamaki, irin yadda take son mahaifinta, tarairayarshi take yi, biyayya take yi mashi sau da ƙafa, Xaman Lafiya ya wanzu a tsakanin su.

A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki,  dawowar shi ke nan daga masallaci, ya ɗan tsaya sauraron wa’azi,  jikin shi na a sanye da jallabiya ash colour, da sauri ya nufi bedroom ɗinsa, Da sallama a bakin shi ya shiga, tunkafin ya ƙarasa shiga ya same ta a kwance tsakiyar gado tana ta sharar baccin ta hada minshari, Agogo ya kalla shida ta kusa, ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin ya yi a gefen gadon ya zauna, tare da ɗan juyo wa yana kallonta, tayi ɗai ɗai a saman gadon, Kayan baccin da ya sanya mata jiya sune a jikinta riga da wando blue sky, curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe,

a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancin ta, yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba,

  “Wake up My lovely daughter” Cikin kunne yayi mata raɗa,

  Buɗe gray eyes ɗinta ta ɗanyi slowly tana kallon fuskar shi biji biji,

  “Nauyin bacci ko? Oya wake up, kada muyi late, ki tashi inyi maki wanka, in girka maki abinci mu ci mu ƙoshi, kafin na sauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina

Jin tayi shiru ba ta ce komai ba, yasa shi fara Yi mata cakulkulo, lokaci guda ta 6a66ake da dariya, white teeth ɗinta kamar gonar auduga, saboda tsabar kyau, kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda hasken su,

Sosai ya sanya ta nishaɗi, a ƙarshe Ya ɗauke ta saman kafadar shi Ya nufi toilet da ita, almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayan shi, Ya ɗaura mata towel ajikinta,

A saman  mirror chair  ya zaunar da ita, Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin, Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu, runtse ido tayi tana dariya mirmishi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura, zura hannun shi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da gashin, Bayan Ya kammala ya kashe dryer din, ya mayar da ita inda ya ɗaukota, ya kuma ɗauko Comb,Ya shiga sharce mata gashin, Sai faman sakin murmushi take yi, A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci?

ta cikin mirror taj ke kallonta, ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu ta ke tunani, Man gashin ta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata, Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta da ke a jiye gaban mirror din, Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta, Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse, Yawan gashi ne da ita ga tsayi, don a yanzu gashin ta ya kai mid back ɗinta, sai da taj yayi da gaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi,

   “Daddy ni da kai wa ya fi kyau” ta yi tambayar tana sakar ma mirmishi

  Dungurin kanta yayi”Kinfi kowa sani ae” ya yi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu, Hannu yasa ya buɗe murfin, Jerin kayan sawan shi ne da kayanta, Uniform ɗinta Ya ɗauko mata riga fara sai mini skirt red colour, Abaya fara ƴar short, a yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta, ga wayau da Allah ya yi mata uwa dila agari,

bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare, Ya zaunar da ita gefen gado”Am coming now” ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta, madara ce me sanyi Acikin roba, tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips,

    Ajiye mata yayi a gefen gadon, Shaf shaf ya shige toilet Yayi wanka, Ya fito sanye da short, zuba mashi ido ta yi tana kallon shi,. 

  Harara ya ɗan jefa mata”Zansa kaya”

 ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi, tamkar bata ji me yace ba,

  Gyaran murya yayi mata”Can’t u hear me? Ki koma Falo inaso zan shirya”.

 Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace”Amma ae ni har wanka ka ke yi mun, kuma kana ganina ba kaya, Amma ni kullum sai ka kore ni in zaka sanya kaya’

Tashin Sense, zaro ido waje ya yi yana kallon ta Cike da mamaki, Ya ma rasa gane wai me take nufi, sai lokacin ya gane kuskuran sa na rashin ɗaukar mai aikin da zata dinga kular ma shi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin,

“Angel don’t waste my time, Oya hold ur basket, ki jira ni a falo,”

Ganin ya ɗaure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket ɗinta ta fuce falo, Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa, Bayan ya kammala shiryawa cikin suit,  Ya fito daga ɗakin Ya nufe ta, Hannunta ya kama suka fito daga falon,

Baba maigadi ya samu, A harabar ajiye motocinshi, Yana goge ma shi motar da zai fita da ita,

Tunkafin su ƙarasa baba maigadi ke ta faman washe ma angel baki, ita kuwa ta tsuke fuska, Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san ta yi kyau, Daƙyar ta ke ma mutane magana,

Suna ƙarasowa bakin motar, Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa, kafin Ya kalli angel”Ƴan mata makaranta za’a tafi”?

Ɗaga mashi kai tayi alamar eh”

  “Allah ya bada sa’a Angelata”maƙe mashi kafaɗa ta yi”Ni ta daddy ce”dariya su ka yi gaba ɗayansu,

Taj yace”Bari mu wuce kada mu makara” baba maigadi yace “Allah ya tsare adawo lpy” ya amsa ma shi da ameen kafin ya buɗe mata motar ta shiga ciki, ya zagaya ta left hand, ya buɗe ya zauna a driver seat,

A tsanake Yayi ma motar key, tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin, da sauri baba mai gadi Ya riga shi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin, Ya fuce daga gidan,

A hankali yake driving, Ta wutsiyar idonshi ya kalleta, Ta natsu ta kame kanta,

  “Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa”

  “Ba bacci nake ba,Ina tunani ne”

“Daddy wlh ni banaso mu rabu, dama ka dinga tafiya dani wurin aikin ku”

  Murmushi ya ɗan saki”Karatun naki fa”?y ayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana,

   Shiru bata amsa mashi ba,

“Ni inaso ki yi karatu angel, sai da ilmi ita kanta rayuwa ta ke yin kyau, ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane za su yi alfahari dake”?

“Inaso” ta amshi amsa a takaice,

“To faɗamun me kikeso ki zama”?

Da buɗar bakin ta sai cewa tayi”house wife” ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba, zuba ma shi ido ta yi tana kallonshi, fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske ta yi maganar,

  “Daddy why are u laughing? did i say something wrong”?

 Girgiza kai yayi”a’a,May be u did’nt understand my question, Ina nufin wani aiki ki ke son Yi idan kika girma, a aikin gomnati? ya yi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar, Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin, A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar,

  Fitowa yayi tare da zagayawa Ya buɗe mata murfin motar “baki amsa mun tambayata ba”?

   Ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi

 “Daddy my answer is the same, I wanna be a house wife” Sakin baki yayi galala yana kallonta, Ya rasa taya ya akai tafara tunanin zama house wife, dududu fa primary school ta ke,

  Gudun kada ya makarar da ita,Yasa shi yin shiru bai ƙara tanka mata ba, Ɗauko mata food basket ɗinta ya yi  kafin ya ruƙe hannunta suka nufi Cikin makarantar, kamar kullum har Cikin class ɗin su Ya kai ta, English teacher ɗinsu ya taras a jin Mrs favour,Cikin harshen turanci suka gaisa da shi, ya damƙa mata angel kafin Ya fito daga class ɗinsu Ya nufi motar shi, Zuciyar shi a cunkushe duk ya rasa sukuni, tunani ya shiga yi taya za’ae ya canza mata ra’ayinta na zama matar aure? don wannan ba ƙaramar matsala bace agare shi, ƴar ƙaramar yarinya tana tunanin zama matar aure,

Karasa shige wa Cikin motar yayi a tsanake Yayi mata key, Ya nufi gate ɗin makarantar mai gadi ya buɗe mashi ya fuce,

Harya haura saman titi, Hankalin shi na akan Kalaman angel, shi da yake da burin ta zama babbar ma’aikaciyar gomnati, ashe ita sam Ba wannan bane agaban ta, A ƙarshe dai ya yanke shawarar idan ya ta shi daga aiki ya ɗaukota suka koma gida, Zai zaunar da ita ya yi mata karatun ta natsu, Ko ya samu ya canza mata ra’ayinta,

Wuraren ƙarfe biyu na rana, Ya tashi daga aiki,Sai daya fara zuwa masallaci Yayi sallah cikin jam’i, tukunna Ya nufi school ɗinsu, Lokacin daya karasa makarantar, tunkafin ya fito daga cikin motar, maigadi ya sanar dashi cewa Dr tazo ta dauketa,

Ba ƙaramin daɗi yaji ba, kaitsaye 6atare da 6ata lokaci ba, yaci gaba da da driving, har ya ƙarasa Gida Tun a bakin gate ya tambayi baba maigadi ko aneelerh ta kawo angel, Yace mashi a’a, hakan na nufin tana a gidan su,

Bayan ya ajiye motar Ya nufi Cikin gidan, Bedroom ɗinsa ya shiga, Shaf shaf Ya rage kayan Jikin shi Ya fada toilet don ya yi wanka, ko yaji daɗin jikin shi,

Adai dai wannan Lokacin Aneelerh ta shigo Cikin gidan, ɗauke da angel da alama ta yi bacci, lokacin da ta shigo falo tana ta kwala sallama ba’a amsa mata ba, kawai sai ranta ya bata cewar ko bai kaiga dawowa gidan bane, don bata lura da motar shi da ke ajiye ba, hakan yasa ta nufi bedroom ɗin shi kai tsaye, ta tura ƙopar kafin tasa kai Cikin ɗakin, Asaman gadon shi ta kwantar da angel, short gown ce ajikinta daga gani hada wanka aneelerh tayi mata ta kuma canza mata kayanta,ranƙwafawa ta ɗanyi daga tsaye tana shafa sumar kanta,

Jin motsin ƙopa yasa Aneelerh tayi saurin ɗagowa tare da juyawa bayanta don taga wanene, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Taj dake fitowa daga Cikin toilet,daga shi sai short a jikin shi,

Burki yaci lokacin da yayi arba da ita, duk tabi ta ruɗe a gigice ta watsa da gudu zata fuce daga ɗakin, Unfortunately ta take rigarta dake jan ƙasa, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da hanzari Taj Yayi ƙwaƙƙwaran Taku Ya ruƙota, ta dawo jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya, taji tsoran faɗuwa ƙasa don ba ƙaramin buguwa za ta yi ba.

Sam ta manta Jikin wa take, ta ƙaƙameshi sosai, har sai da ya ɗanyi gyaran murya tukunna ta dawo hayyacinta, ta yi saurin raba jikinta daga na shi, duk kunya ta rufe kowannan su,

Daƙyar ya iya buɗe baki yayi mata magana

  “Sai ka ce kin ga dodo, kawai daga gani na kin zabura zaki gudu, yanzu da kinji ciwo fa? so kike uzair Yasa a ɗaure ni ko”?

  Murmushi ta ɗan saki ba tare da ta ce uffan ba, idanuwanta na akan yatsun hannunta,

  “Thank u so much aneelerh, kina ɗawainiya da angel ɗina, tamkar mahaifiyarta, naso ace benazir tana da kyakkyawan hali irin naki sai dai kash ni ban yi sa’ar mata ba,”

  Juyawa ta ɗanyi jiki a sanyaye ta soma tafiya tana tunkarar ƙopar ɗakin sai da takusa fita tukunna ta ɗan dakata da yin tafiyar, A tsanake ta soma magana,

  “Zan ta ya ka addu’a Allah ya baka mace ta gari wadda ta fini” tana kai ƙarshen maganarta, da sauri ta fuce daga ɗakin,

Murmushi taj ya ɗan saki, tare dakai hannu ya shafa sumar kanshi, juyawa ya yi tare da koma wa gaban mirror,  lokaci guda kasala ta baibaye shi, ƙamshin turaren aneelerh ne, Ya cika mashi hancin shi, ita koda yaushe Cikin ƙamshi take, Zama ya yi a saman chair din gaban mirror, Ya kura ido yana kallon fuskar shi ta cikin mirror,

A 6angaren aneelerh kuwa, Da sauri ta fuce daga Cikin gidan, Tana shiga falon gidanta, A saman sofa ta zauna tana faman mayar da nunfashi kamar wadda tasha gudu, tarasa dalilin dayasa a ƴan kwanakin nan take jin faduwar gaba aduk lokacin da ta ci karo da taj,

A tsanake Ya kammala Shirya kanshi Cikin farar t shirt,tare da jeans ya feshe jikinsa da turare mai kamshi,

Yasan aneelerh bazata bar angel da yunwa ba, Shiyasa ma baiyi tunanin shiga kitchen ba,

Wayarshi ce ta soma ringing, da sauri yakai hannu ya dauke ta daga saman drawer,

  Kallon screen ɗin wayar yayi sunan Aminina ne ya bayyana akai, murmu shi ya ɗan saki tare da yin picking call ɗin ya manna wayar a kunnanshi”Assalamu alaikum, ɗan uwana rabin raina”

  On the other hand Uzair yace”Ka koma gida lafiya”?

 “Lafiya lou, Yanzu na fito daga wanka ma”

 “Ka ci abinci”?

 Dariya taj yayi sosai, jin irin tambayoyin da yake yi mashi sai kace wani ƙaramin yaro,

  “Meyasa ka ke mun dariya? yau nafara tambayarka hakan”?

 Tamkar yana agaban shi Ya girgiza kanshi”Nop, just naji abun wani irine, kana tunamun rayuwar mu agidan Uncle”

    Muryar shi ya jiyo da sautin murmushi “Unforgettable momeries, Allah Yabar ƙauna aminina, Zan shiga stadio Sai mun haɗe anjima”

  Taj yace”Okey, take care of ur self for me pls”

  Uzair yace”U too”  fuskarshi ɗauke da murmushi ya yi rejecting call ɗin,

Yana ajiya wayar saman drawer, Yajiyo muryar baba maigadi daga Can cikin falo, Yana kwala sallama,

A hanzarce Ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, Yayin da yake amsa mashi sallamar”Wa’alaikum Salam”

Cikin falon Ya nufa, A bakin entry ɗin ya same shi a tsaye, ƙarasawa Ya yi yana kallon shi,

  “Barka yalla6ai”ya amsa mashi da “yawwa barka”

 “Dama baƙo ne ka yi”

Da ɗan mamaki akan fuskar taj yace”baƙo kuma”? yayi tambayar ne don shi a iya sanin shi, ba su yi da kowa  zai zo gidansa ba,

 “yalla6ai, Wannan malamin ne daya ta6a zuwa yi ma angel ruƙiya?’ cike da son fahimtar da shi baba maigadi ya yi maganar,

  “Kana nufin maisalati”?

Da sauri baba mai gadi yace”kwarai kuwa shi ne”

  “Okey, Ka ce ma shi ya shigo”

 “To yalla6ai,” Yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar falon,

Tajo na atsaye Yana jiran ƙarasowar malamin Ya ji sallamar shi, Fuskar nan dauke da murmushi, Jikin shi na sanye da jallabiya wadda tsayinta bai kai idon ƙafar shi ba, Hannunshi na ruke da cazbaha Kanshi yasha uban rawani, Wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,

Sakar ma shi fuska taj ya yi tare da miƙa mashi hannu cikin girmamawa suka soma gaisawa

  “Allah ya gafarta malam, barka da rana Ya iyali ya jama’a ya ƙoƙari, Allah yataimaka, Allah Ya kara ɗaukaka”

 “Ameen ameen tajo, Fatan na sameka lafiya ya aiki, ya kuma ɗiyar mu”

Taj yace”Alhamdulillah, Duk muna lafiya Mu shiga daga Ciki,” ya ruƙo hannunshi, suka nufi sofa ɗin falon, maisalati ya zauna asaman 2 seater, Sae faman sakin murmushi yake yi, Dama shi haka yake kullum fuskar nan a washe, Da wuya kaga bakin shi a ƙulle.

“Bari na kawo maka ruwa” da sauri Malam maisalati ya dakatar dashi”samu wuri  ka zauna tajo, Magana ce mai mahimmanci ce ta kawo ni,”

Tunda Taj yaji hakan, Sai ya zauna saman 1 seater ya tattara kwandon hankalin shi a kan maisalati yana sauraron shi’

“Game da ƴarka injila” da sauri taj yace”Angel sunan ya ke”

  “Oh toh, eh ita ɗin dai” shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara yi ma shi jawabi.

  Taj kuwa ya tsare shi da ido, Jikin shi har tsuma yake yi, don a ƙagare ya ke ya ji me angel ɗin ta yi,

Gyaran murya malam maisalati Ya yi kafin ya soma magana a tsanake,

  “ranar da aka kirani Inyi mata ruƙiya, nayi wani laifi laifin kuwa shine bansanar dakai wani abu da nake hasashe akan yarinyar ka ba, bama hasashe bane inanda tabbaci kan shi,”

  Tunda taj yaji hakan,nGabannshi ya faɗi rass aruɗe yace”malam wani abu kenan”?

  Numfashi ya ɗanja kafin yaci gaba da kora mashi jawabi tiryan tiryan

  “Akwai abunda na gani a tattare da yar wurin ka, A lokacin da nake yi mata ruƙiya, Sai dai tsoro da firgici ya hana in faɗa maka, gaskia yana da matuƙar daure kai saboda ba ƙaramar sarqaqiya bace a cikin lamarin kuma ni kaina na kasa tantance sihiri ne a jikinta ko kuwa saboda gaskiya abunda nagani a jikinta babbar al’amari,

  Tuni jikin taj ya soma kakarwa, muryar shi na kerma yace”Malam dan Allah ka yi mun bayani, hankalina a tashe Yake wlh”

Cigaba da magana malamin ya yi”Kaitsaye bazan Iya ce maka ga abunda nagani atattare da ita ba, Amma ina da tabbacin akwai wani abu dake faruwa da ita a jikinta …….”,

  Muryarshi na ɗan rawa yace”am..amma malam ni inaga kamar lafiyarta ƙalau, yanzu haka da nake maka magana mun samu sasanci a tsakanina da ita, Tana sona ina sonta ba kamar lokacin baya ba”

Murmushi maisalati ya yi dama yasan zaiyi wuya taj ya fahimce shi, jinjina kai yayi tare da cewa”Shin ka ta6a tunanin ka zauna da ita ka tambaye ta game da abubuwan da take yi maka a baya gamon kanta ne ko kuwa? kuma bata ƴan gane gane haka”?

Shiru taj ya ɗanyi, Shi kaɗai yasan halin da zuciyar shi ta ke aciki, duk da yana kokwanto akan kalaman malamin amma kuma yana tsoron Zancen shi ya zama gaskiya,” girgiza kai yayi alamar aah, gyara zama ya yi to gaskia abinda ya kamata kayi kenan dan musan Mike faru da ita ta hakane xamu samo bakin zaren”

  “Shikenan malam in sha Allah zan tambayeta,”

Maisalati yace”Yawwa ko kaifa, Sannan kuma shawarar da nake so na baka, Ka tabbatar kana Yi mata addu’o’i akai akai, idan bata iya ba ka koya mata, hada azhkar na safe dana marece, ka kuma koya mata addu’ar shiga toilet, idan zata kwanta da dare ka yi mata addu’oi’in neman tsari, kuma a koda yaushe ta kasance kanta akwai ɗankwali, ka lullu6e mata gashin kanta, Hatta kaya idan zaka sanya mata ka yi mata addu’o’a, Daso samu ne ma duk in zaka kwanta bacci ka kunna maku karatun al’qur’ani mai girma ku kwana da shi,” sosai malam maisalati ya ba shi shawarwari a ƙarshe yace”Idan Allah yasa ƙarshen wahalar ta kenan sai kaga Allah ya yaye mata, Amma dai ina ƙara gargaɗinka kada kayi sakaci wurin Yi mata addu’a akoda yaushe, na manta ma ban tambayeka ba, Tana zuwa islamiyya”?

Dakyar ya iya buɗe baki yace”Eh amma ta jima ba ta je ba,

Girgiza kai maisalati yayi”Banso haka ba tajo, kanaso ka yi mana buƙulin samun Hafizar al’qur’ani, wadda zata yiwa addini hidima nan gaba, kamar yadda nake fata, Allah ya baka yarinya mai wayo tubarkalla, ga hali kamar na manyan mutane, bai kamata kayi wasa da wannan damar ba, Gaskiya ina mai baka shawara ka hanzarta mayar da ita makaranta, idan da hali harma tahfeez ka sanyata,”

Ajiyar zuciya taj ya dan sauke”in sha Allah zanyi hakan, Nagode sosai malam, Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka, Allah ne kaɗai zai iya biyanka, Allah dai yasa ka maku da alkhairi,” sosai taj ya yi ma shi godiya, Koda ya miƙe zai tafi saibda taj ya ƙara tambayar shi ya kawo mashi ruwan sha,

  Yace a’a, Shi dai burin shi ya yi ƙokari wurin ceto rayuwar ƴar shi, Shi ma kuma zai taimaka mata da addu’o’i shida ɗalibansa,daga haka su ka yi sallama dashi Yabar gidan,

Tofa, Bayan tafiyar malam maisalati, kasa zama taj ya yi saboda ruɗanin da zuciyar shi ta shiga, Zarya ya shiga yi a falon, Zuciyarnshi a cunku she take, wani irin faduwar gaba yake ji, tabbas yanyi kuskure sosai akan angle wurin rashin maida hankali ya yi bincike sosai lokacin da take cikin wannan halin”

A hanzarce Ya juya ya nufi bedroom ɗinnshi, tunkafin Ya ƙarasa shiga Ya hango angel zaune saman gadon Ta jingina bayanta jikin headboard(kan gadon)

Ƙura mata ido ya yi yana kallonta, ganin ta lumshe i danuwanta, tamkar mai tunanin wani abu,

Shiga cikin ɗakin yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna yana fuskantar ta,

 “My daugher” da buɗar bakin ta sai cewa tayi”Daddy, Malam mai dogon gemu yazo ya cika ka da surutu kamar radiyo mai jini ko” idanuwan ta a rufe ta yi maganar,

Da mamaki akan fuskarshi yace”Taya akai kikasan yazo ke da kinke acikin ɗaki”?

Bude idanuwanta ta yi a hankali,

“Tun dazu nafarka daddy, har leƙa ku nayi,”

“Kinji me muka tattauna dashi” girgiza kai tayi”ae ka hanani yi maka la6e, shiyasa ban tsaya ba, nadawo na zauna”

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, Kafin ya kuma cewa wani abu ta riga shi cewa”aunty aneelerh ce ta kawoni gida”? ɗaga mata kai ya yi alamar eh,

 “ta kawomin uniform ɗina da kuma bag dina”?ta kuma jefa mashi tambaya,

  “A’a,zanje na kar6o maki su anjima”

Jinjina mashi kai kawai tayi,

Shiru sukayi na dan wani lokaci,kafin ya ruƙo hannunta cikin na shi,

“My daughter”!

Ware ma shi manyan idanuwanta tayi”na’am daddy”

Murmushi ya ɗanbsaki, ya rasa ta ina zai taro zancen, kamar maijin tsoron ta,

Can dai ya daure Ya soma yi mata magana antsanake”Nasan kina sona sosai,bkuma kina kyautatamun, koba haka ba?

Da sauri tace”Hakane daddy”

Jinjina kai yayi”um..Yanzu kina sona,nba kamar lokacin baya ba da kika ɗauramun karan tsana tamkar ni ba daddyn ki ba ne, Pls inaso na tambaye ki, a wannan lokacin ke ki ke ƙuntata mun da kan ki ko kuwa akwai wani ɗan mutun mutumi dake sanya ki kina yi mun”?

Cikin rashin fahimta tace”daddy i don’t understand me ka ke nufi”?

“Ina nufin, A time ɗin da kike 6ata mun rai, Wake sanya ki kina yi mun,i know there must be a reason, babu yadda za’ae ki tsani mahaifinki lokaci ɗaya,”

Wurga eye balls ɗinta sama ta yi tana kallon ceilling, ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana kallon ceilling ɗin yasa shima ya ɗaga kai yana kallon shi, wai ko zaiga abunda take gani,

Ganin bata da niyar daina kallon ceilling ɗin yasa shi dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Pls explain to me kin ji babyna”

Mayar da idanuwanta kan shi ta yi taɗan turo baki irin na shagwa6a66u,

“Nidai bansani ba, Amma bani nake yi ba, kamar ana ce mun inyi kaza ni kuma sai inyi” takai ƙarshen maganar tana ƙyafƙyafta mashi ido,

“Magana a ke yi maki acikin kan ki ko kuwa”? ya kuma tambayarta,

“Daddy nifa bana ganewa”

“Angel kina mafarki”? ya kuma tambayarta, bubbuga hannuwanta ta yi saman Mattress ɗin”Wlh daddy ni ka yi disturbing ɗina, kana rikita ni”

Lallashinta ya shiga yi”Am sorry, wannan ce tambaya ta karshe, idan ki ka bani amsa, Zan ba ki wayata, kiyi game,” yasanta mayyar wayace, aikuwa da sauri ta soma kora ma shi jawabi

  “Daddy, ko yanzu dana kwanta,na yi mafarki kuma kullum ina yin mafarki,”

  “Faɗamun meke faruwa acikin mafarkin”?a ƙagare ya yi maganar,

Angel tace”Ina ganina a cikin wani ƙurmin daji mai duhun gaske mai ban tsoro, kuma idan nayi mafarkin ina ganina Acikin wasu mutane masu sanye da baƙaken kaya, Bana iya ganin fuskar su, hannunsu zako zako da akaifa, Ni kuma Ina sanye Cikin jajayen kaya, riga da wando,kuma bani kadai bace hada wasu ƴan yara, Kuma suma red uniform ne a jikinsu,Daddy akwai tsorofa mafarkin Kuma babu alkairi a cikinsa”

Tunda ta soma magana zuciyar taj tashiga harbawa da ƙarfi da karfi, tamkar zata faso daga kirjinshi,

“Amma kinsan kina irin wannan bad dream ɗin shi ne baki  ta6a sanar mun ba”?

“Banaso na tayar maka da hankaline, Aunty aneelerh tace in dinga faranta maka rai, kada na 6ata maka rai, Zaka Iya mutuwa ni kuma banso na rasa ka, sometimes ma in nayi yinqurin fada maka sai wani abu ya daukemin hankali na manta” fashewa tayi da matsanancin kuka,

Da sauri Ya janyota jikinshi sosai ya rungumeta, baisan lokacin da hawaye suka soma sauka akan fuskar shi ba, yana jin kukanta har cikin zuciyarsa

“In sha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na ceci rayuwarki, Bi’iznillahi duk wani mai nufinki da sharri zai koma masa ne, Tabbas akwai wani maison shiga tsakanina dake, akwai wanda yake Yi mun maƙarƙashiya, Bansan wanene ba!!Amma Allah ya sani, Kuma zai bayyanar mun dashi ne, duk mun daren daɗewa”!

Yayi maganar ne don yasan Yana da maƙiya a wurin aikin shi, masu yi mashi hassada saboda ɗaukakar daya samu, kuma har akan idon shi suna nuna mashi ƙiyayya, shiyasa ya yi zargin kodai wanine keson ya 6ullo mashi ta bayan fage, shine a kayi amfani da ita wurin cutar dashi,

Sun jima a wannan yanayin manne da juna shi da ita, sai da aka fara kire kirayen sallar la’asar, tukunna Ya ɗago da ita daga Jikin shi, Ganin ta fara bacci Ya dan jijjigata,  firgit ta farka”time din sallah yayi daga yanzu bana so kina wasa da sallah, kinji ko’?

Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ya kuma cewa”Addu’ar shiga toilet kin iya”?ɗaga mashi kai tayi”Eh”yace to karantamun, nan ta shiga karanto mashi, ya kuma tambayarta addu’ar kafin a kwanta bacci da kuma in an ta shi daga bacci duk ta karanto mashi Yace”masha Allah, haka nake son ji My daughter, Sannan kuma zan koya maki azhkar da zaki dinga yi na safe dana marece, pls ki bani haɗin kai, ki dage kin ji indai bakyaso a rabani dake”da sauri tace” zanyi daddy,”yace that’s good, yanzu tashi ki shiga toilet kiyi alwala ina jiranki”

Amsa mashi tayi”toh” da sauri ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, harta kusa shiga ya dakatar da ita”wait” ta tsaya tare da waiwayowa tana kallon shi, saukowa daga saman gadon ya yi ya nufi can cikin ɗakin wurin closet ɗinsu, buɗewa yayi tare da kai hannu ya ɗauko hijabi da mayafi, asaman gadon ya ajiye mata hijabin shi kuma mayafin ya taka zuwa inda take ya ɗaura mata shi a kanta, sosai ya lullu6e mata gashinta”yawwa daga yanzu haka nake so gashin kanki ya kasance a lullu6e, sannan kuma idan kin kammala sallah, ki dinga karanta surorin da nake koya maki” amsa mashi tayi”toh”kafin ta bude toilet ɗin ta shige ciki,”

Tsayawa ya yi har saida ta fito tukunna ya sanya mata hijabin,kafin ya wuce cikin toilet, lokacin daya fito salla ya same ta tana yi, baisan lokacin daya saki murmushi ba,yaji daɗi har acikin ran shi,

Da sauri ya fuce zuwa masallaci, a bakin gate suka ci karo da Uzair yana ƙoƙorin shigowa ciki, dama biyo ma shi yayi don su tafi masallaci atare,

Bayan tafiyarshi, Angel ta kammala sallah ta zauna tana karanta surorin daya koya mata irin su falaki da nasi, su ta yi ta biyawa, duk don saboda yace tadinga yi indai bataso  a rabasu, Tana cikin yin ƙira’ar, Wayar shi daya manta saman gadon su ta soma ringing,

Zumbur ta miƙe takai hannu ta ɗauke ta, Sunan Uncle ne Ya bayyana, Kafin ta ɗaga kiran ya katse, ganin wayar babu finger print din daya ke sanya mata, dama tun lokacin da suka shirya da ita ya cire security din wayar shi, Zama saman gadon ta yi ta dinga buga game na spider man,

Sai da ta yi mai i sarta tukunna ta shiga contact dinshi, Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira, wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya, Har ya katse kiran, ta kuma haɗa wasu numbobin ba’a ɗaga ba, kusan number waya biyar ta kira ma shi wasu ba’a ɗaga ba, Sai na ƙarshene a ka ɗaga kiran,

Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana, shiru taji ba’ace mata uffan ba, kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karaɗe kunnuwanta”who is on the line”?

Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace”Angel ce,”

Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta”kinsan dawa kike magana”?

Girgiza kai ta yi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace”a’a,”

“Ur age”? ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinya ce ƙarama,

“7yrs” voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita”7yrs? ina mai wayar yake’?

“Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya”

“Can i call u video”?

Da sauri tace eh,

Nan take ya mayar da kiran Video call, ɗago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan ta yi picking, Bata ga komai ba a screen ɗin sai duhu sosai, Amma shi wanda  take wayar dashi da alama yana kallonta,

“I can’t see u” ta yi maganar tana faman gwale ido,

Shiru ta ji baya magana, saukowa ta yi daga saman gadon, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, Tana Cikin zagaye palour Tajiyo Sallamar daddyn ta,

A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers ɗin data kira, tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci,

Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna,

“Ban fada maka bane kawai, Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana da  aljanu, zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta same su tunda a nan Benazir ta haifeta, kuma kaga shi toilet madaddalar su ce,”acewar uzair,

Jinjina kai Taj ya yi”Yanzu menene mafita”?

Uzair yace”Mu tayata da addu’a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za’a dace ne,”

Taj yace”Allah Ya yarda, duk na damu wlh,”

Uzair yace”ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah zamu San abun yi,

Sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa tare da uzair kafin ya yi mashi sallama ya tafi gida,

Tundaga wannan Lokacin, bai ƙara yin sakaci wurin kula da ita ba har tahfeez ya sanya ta, ya ci wahala kafin ya samu tafara zama Makarantar islamiyyar, da yake a kusa dasu makarantar take, idan ya kai ta yana barin makarantar take kamo hanya ta dawo gida, Kowa ya yi mamakin yadda a kai ta ke guduwa daga makaranta, dakyar ya samu tafara zama, tun tana yi ma shi kukan ba ta so harta haƙura ta zauna, bai ta6a bari ta zauna tana shiririta ba, Kullum sai ya tasa ta gaba tana maimaita karatun haddar da aka bata, babu abunda bai siya mata ba, Wanda ya danganci karatun addini, Cikin ikon Allah sai ga shi tafara sanya naci tana yin karatun tunkafin ma yace mata ta yi take yi, wani lokacin ko bacci take yi ta dinga sambatu kenan tana Bitar karatun da a ka koya mata, Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yi mashi ba, Uzair da aneelerh ba ƙaramar rawa suka taka ba, wurin taimaka ma taj akan angel, dama sun ɗauketa tamkar ƴar su, Allah ya bata kaifin basira,wani irin ƙoƙari gare ne ita duka boko da islamiyya ko’ina yabon ta su ke yi, Kowa sonta yake yi, duk wani Competition da za’ayi Tsakanin makarantu, ita ke ciyo ma school ɗinsu, shiyasa su kansu malaman Ji su ke da ita, duk in tayi fashi bata zo school ba, Sai sun kira taj a waya sunji dalili, sometimes har gidan suke zuwa ganinta,

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah  Angel ta shiga Cikin shekarata Goma, a wannan Lokacin suka Shirya Mata Party na taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tun ana saura kwana biyu, Aneelerh ta kai ta wurin Saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyan gaske, tare da ƙunshi na jan lalle, da ya rage saura kwana ɗaya birthday ɗin nata, gaba ɗaya suka shirya don zuwa yi mata siyayya A shopping Mall,

Kaya sosai suka siya mata a kasuwar, sai da suka gama kashe mata kuɗi, Tasa masu rigima akan Tana son a siya mata Piano da kuma drawing materials, A lokacin sunyi ƙarƙaf, sun gama kashe ƴan canjin da suka rage masu, Lallashinta su ka soma yi akan tayi haƙuri next time idan suka ta shi dawowa zasu siya mata, Ƙin yadda ta yi a ƙarshe ma ta  rushe masu da kuka tana fadin ita dai su siya mata su take so, ko kuma amaida sauran kayan da aka siya mata don kuɗin su isa a siya mata Piano, sosai Angel ta sanya masu rigima, tun mutane basu lura ba, har hankalin kowa ya dawo kansu, Ganin Yadda yarinyar take ta ruskar kuka, Aneelerh taso ta siya mata, Taj ne ya hanata saboda yasan ba isassun kuɗi gareta ba.

A haka suka koma gida, Sosai ya yi mata faɗa akan ta daina yi ma shi rigima Cikin mutane, tunda yace mata ba shi da kuɗi meyasa zata takura shi, so take ta kunya ta shi a idon jama’a, daga ƙarshe yace mata ta yi hakuri idan ya samu kuɗi zai siya mata komai take so, shi kan shi baiji dadin yadda ya gaza siya mata Abubuwan da takeso ba, Don ta ƙwallafa rai a kan su sosai,

A washe garin ranar ya kasance Juma’a, ranar birthday ɗin ta, Gagarumin party suka haɗa mata, tun bayan sallar asuba aka soma shagali don a wannan lokacin ne Angel tazo duniya, Ƴan uwa da a bokan arziƙi duk sun hallara don tayata murnar birthday ɗinta, Kaya kala Uku ta sanya aranar, aneelerh ce ta shiryata ta yi mata kwalliya, Musamman aka ɗauko photographers, Su ka yi masu hotuna, taro yayi albarka Anyi kulu washrabu hani’an, Kowa ya shaida ya nishanɗantu

Angel ta samu Kyaututtuka masu yawan gaske daga wurin a bokanan aikin shi, Wasu gifts ɗinma baisan su wanene suka aiko mata dasu ba, baba mai gadi ake aikowa daga waje,ya kawo mata su cikin gidan, bakomai ya fi Ba shi mamaki ba, face wata kyuatar bazata da a kayi ma angel, Abun ya ɗaure mashi kai, Abunda angel ta kwallafa rai akan shi ne Aka samu wani ya siya mata su, piano da kuma kayan zane da ta sa masu rigima a shopping mall, Ya yi mamaki sosai har baba mai gadi ya tambaya waye ya aiko mata da gift ɗin don shi ya miƙo su Cikin gidan, Baba maigadi yace ma shi bazai Iya shaida fuskar wanda ya kawo ba, Matashin saurayi ne dai kuma ya sanya facemask a fuskar shi, Sannan kuma Acikin mota ya zo, har tambayar baba maigadi ya yi kobya lura da kofato a ƙafar mutumin daya kawo su? Baba gadi ya yi dariya Tare da cewa Bazai iya tantance  ƙafafune ko kofato ba,tunda ya sanya takalma,

jikin taj dai yayi sanyi sosai, ko angel bai bari taga kayan ba, Ya 6oye su a ɗaya daga Cikin ɗakunnan gidan, Kafin a kammala shagalin sun ke6e da Uxair ya sanar da shi game da kayan da aka siya ma angel, shima ya yi mamakin jin hakan, Amma sai yace mashi  Ya kwantar da hankalin shi, Shi yafi tunanin Cikin mutanan dake kallonsu A mall ɗinne lokacin da angel tasa rigima akan su siya mata kayan, Shine aka samu wani na Allah ya siya mata su, don haka ya cire damuwa aranshi Ya bata kayanta, kada ya hanata yin amfani da su, Iya ka ci dai kafin tafara amfani da su, Ya tofe su da addu’a, kuma kada Ya dinga barinta tana yawan yin kiɗa, ko ƴan zane zane sai ya dinga lura, Sosai Uzair ya ba shi shawara, Har saida yaga hankalin shi Ya kwanta,

Bayan kwana ɗaya da yin Birthday ɗin nata, Sai ga ɗan saƙo an aiko daga wurin Alhaji ubaid, Gift ne Ya aikoma jikarshi, danƙareriyar waya ƙirar i phone tare da Laptop, Bayan ya kar6esu daga hannun ɗan saƙon,Yakaisu ɗakinshi ba zato ba tsammani Sai ga alert na 1.5m ya shigo wayarshi, again daga alhaji ubaid, Ba ƙaramin farin Ciki ya yi ba, Yana ƙara Jin ƙaunar mutumin kodan saboda kyautatawar da yake yi ma ƴar shi, shi kaɗai ya damu da ita duk cikin family ɗin benazir babu wanda ya ta6a tuntu6ar shi koda a waya ne ya tambayi ya angel ta kwana, duk da yasan halin su ko lokacin auran shi da benazir dayawansu basu so ya aure ta ba, saboda arziƙin shi bai kai ya mallake ta ba, shiyasa sam babu ruwansu da abun da ya shafi tajudden, Alhaji ubaid ɗin kaɗai ne ya damu da su, kusan kullum sai ya kira don yaji ya lafiyar jikar shi,

har uzair ya tuntu6a Don su yi shawara da shi game da Kuɗin da alhaji ubaid Ya turo mashi,Yace mashi Yayi amfani da su,Wurin Gyara mata bedroom ɗinta, Inda zata koma da kwana, ya sanya mata kayan wasanni da zasu dinga ɗebe mata kewa, Sauran kuɗin Kuma Akwai hidindimu masu Zuwa, ya ajiye mata su, Duk yadda taj yaso ya ɗauki wani a bu daga Cikin kuɗin yaƙi kar6a, Sai da ƙyar ya samu ya kar6i dubu ɗari,

a tare da aneelerh suka tsara mata komai na bedroom dinta, Wani haɗaɗɗen gado suka sanya mata, Headboard ɗinshi Sak Jikin butterfly ne, Komai na bedroom ɗinta Pink Colour ne, Ba abunda ba’a sanya mata ba, Yaci wahala kafin ya samu angel ta koma kwana dakinta,Saboda sabon da su ka yi da juna, sai ya bari bacci ya ɗauketa tukunna yake kaita ɗakin ta, idan tafarka ko ƙarfe nawa ne na dare saita sauko daga Upstairs ta dawo ɗakinshi da yake ya dawo downstairs bayan sun raba daki, Sai dai kawai yaji ta Kwance ajikin shi,

sai da yabi komai asannu tukunna ya samu Tafara sabawa da kwana a ɗakinta, yanzu da kanta take yin wanka ta sanya kaya har ma tayi kwalliya, har lokacin angel batasan an bata gift din piano da Kayan zane ba, Saboda ya 6oyesu Laptop kaɗai ya bata, wayar kuma da aka bata shi yaci gaba da amfani da ita, don bazai bari ta ruƙe waya ba, Saboda wayon dake gareta, kuma zata iya  ɗauke mata hankalinta daga yin karatu,

Acikin waɗannan kwanakin taj yaso yaje buzaye wurin Dangin shi, Amma Uzair ya dakatar da shi, Akan ya bari Su uncle su dawo Nigeria, in ya so sai su ɗunguma su tafi a tare, ba don yaso ba Ya amince ma shi,

Tuni angel ta kammala primary school ɗinta a yanzu haka tana a Jss 3 Sunyi Exam na first term, tunda suka samu hutu ba  inda take zuwa Kullum tana gida bata zuwa ko’ina, taj Ya damƙa mata Piano ɗinta, Idan ta zauna ta soma yi masu kiɗa ko gajiya ba ta yi, Sai in Lokacin Karatunta ya yi ko sallah take tashi, sam ya hanata Yin kallo In ba cartoon ba, Shima cartoon ɗin Sai ya tabbatar Baida wani abu da zai 6ata mashi yarinya tukunna yake barinta ta kalla, Ya sanya mata ido sosai, duk wani motsinta a tafin hannun shi, idan zai tafi wurin aiki, Gidan su Aneelerh yake turata, koda basa nan mai aikin gidansu Ana tana nan, A wurinta take zama kafin su dawo 

Wannan kenan,

a gajiye ya ke driving a daidai bakin gate, ya soma dannawa mai gadi hon, Da hanzari baba mai gadi Ya fito daga ɗakinsa, ya buɗe ma shi gate ya shigo da motar Jikin gidan, Fitowa daga Cikin motar ya yi, Jikin shi na sanye da Shadda green Colour ba ƙaramin kyau tayi ma shi ba, Sai daya fara tsayawa suka gaisa da baba maigadi tukunna Ya nufi Cikin gidan,

Tunda yayi sallama a palour Yaji shiru ba’a amsa mashi ba, ran shi ya ba shi cewar Ko bata dawo gida bane, yanke shawarar zuwa bedroom ɗinta Yayi, walking slowly Ya nufi stairs ɗin ya haye, a tsanake ya ke tattaka steps ɗin benan harya samu Ya haye sama, Kaitsaye Ya nufi inda ɗakinta yake, Da sallama a bakin shi ya tura ƙopar ɗakin, Yana shiga idanuwanshi suka sauka akan gadon, wayam baiganta ba, Hakan na nufin bata dawo ba, tana agidansu aneelerh, Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da juyawa zai bar ɗakin, Karaf idanuwan shi suka sauka akan Zanen fuskar shi da angel ta yi a jikin bangon ɗakinta, Cike da mamaki Yaci burki tare da nufar Bangon yana kallon Zanunnukan da ta yi, da kuma rubuce rubucen da ta yi duk a jikin bangon,

Motsa lips ɗinsa ya soma yi yana karanta abunda ta rubuta a jikin bangon

_To my biggest hero_

_There’s no better role model than you,_

_There’s no one I’d rather look up to than you._

_I’m so proud to be your daughter_

_You’re my one and only dad,  and you’ll always have a special place in my heart._

_Dad, you’ve made all my favorite memories._

_Dad, you’ve always been my hero._

_I’m so lucky to have your love and guidance in my life_

ya ma rasa mi zai ce lokacin daya kammala karanta Rubuce rubucen da ta yi ma shi, Wani irin tsantsar farin Cikine Ya bayyana akan Fuskar shi, Tuni hawaye su ka wanke ma shi fuskar shi, slowly ya zube saman gwiwowinsa, a yayin da hawayen ke cigaba da bin kuncin shi, kalamanta ba ƙaramin faranta ma shi rai su ka yi ba, maimakon Ya ji haushin 6ata bangon ɗakin da tayi sai ma yaji ya ƙara sonta a cikin zuciyar shi,

Haƙiƙa angel ta ba shi mamaki, ta san ya shi farin Cikin da bazai ta6a mantawa ba,

Da sauri Ya juya ya kalli ƙopar ɗakin Jin motsin mutun, Bakowa bace face angel

Jikinta na sanye da jallabiya, daidai tsayinta, Tayi rolling mayafi akanta,

“Daddy sannu da dawowa Nayi missing ɗinka sosai” ta ambaci hakan fuskarta ɗauke da murmu shi, buɗe mata hannayen shi ya yi alamar tazo gare shi, da gudu ta ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan kirjin shi, Ya sanya dukkan hannayenshi Ya rungumeta sosai, Yana faɗin”kin sani farin Cikin da bazan ta6a mantawa ba angel, I luv u so much, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin bayyana maki irin ƙaunar da nake yi maki, Allah yabarnmin ke angel, Allah ya kare mun ke daga sharrin maƙiya da mahassada, Allah ya yi maki albarka”

   Amsa ma shi tadinga yi da ameen daddy, kusan mintuna goma suna manne da juna, batare daya raba jikin shi daga nata ba, wani irin yanayi yake ji attare da shi, sam baya son yana tuna mutuwa, Saboda yasan ita kaɗaice zata Iya raba shi da angel, ko yana so ko bai so, dolene bayan ita kuma sai wata ƙaddarar rayuwar wadda baya fata,

Ɗagowa tayi daga Jikin shi ta sanya hannu tana goge mashi tears ɗin dake sauka akan fuskar shi”daddy kadaina pls, banason ganin hawayen ka na zuba”

Kallonta ya yi da runannun idanuwan shi waɗanda su ka yi jawur da su, sam ya kasa furta mata komai,

Huggin ɗinshi ta ƙarayi tana shafa sumar kanshi, bacci ya soma Ji hakan yasa shi miƙewa Ya lalla6a ya haye saman gadonta, ya kwanta duk da ya yi mashi ƙanƙanta,

  Gefen gadon ta zauna tana kallon shi, jikinta duk ya yi sanyi tace”daddy baka lafiya”?

Eyes ɗinshi arufe yace”kinci abinci”?

“Naci a wurin aunty aneelerh, Ko inje in kar6o maka naka” girgiza mata kai yayi”a’a,Bana jin yunwa, kizo mu kwanta muyi bacci”

Ƙarasa hawa saman gadon ta yi a gefen shi ta kwanta, Ya sanya hannu ya janyo ta jikin shi, Cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da su,

Wuraren ƙarfe 4 ya farka daga Baccin, Lokacin a nata kiraye kirayen sallar la’asar, saukowa daga saman gadon yai tare da nufar toilet ɗin ɗakin ta Ya shiga ciki,

After some minutes ya fito yana share ruwan alwalar dake a fuskarshi, Kafin ya nufi inda angel take a kwance tana bacci,

Cikin sanyin murya ya soma kiran sunanta”My angel!”shiru bata motsa ba, hannu yasa tare da ɗan bubbuga ƙafarta, nan take ta farka tana mutsu mutsun bude idanuwanta,

“Lokacin Sallah yayi, Ki ta shi kije ki yi alwala, ni zan tafi masallaci”

Muryarta a disashe tace mashi”a dawo lpy daddy,”

Bayan tafiyar shi, ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,

Jim kaɗan tafito ɗaure da alwala, ta ɗauko carpet ta shimfiɗa, Ta zura hijab ajikinta a tsanake ta soma Yin sallah,

Lokacin data idar da sallar zama tayi saman dardumar tana karatun alqur’ani mai girma daga cikin kanta,

Tana cikin yin qira’ar, Ya dawo daga masallaci, murmushi yasaki Yayin da ya ke shigowa  Cikin ɗakin, Ba ƙaramin daɗi yake ji ba aduk lokacin daya sameta, Saman darduma tana Yin sallah ko tana yin karatun al’qur’ani mai girma,

Sai da takai ƙarshen ayar da ta janyo tukunna ta juyo ta kalleshi”daddy sannu da dawowo”

“Yawwa daughter, Kin daiyi mana addu’a ko”? jinjina mashi kai tayi”eh,Ae kullum sai nayi”

“Haka nakeson ji, My daughter”

Shiru ya ɗanyi kafin Yace”Zamu fita tare da daddy uzair ɗinki, Zaki zauna a gida ko In kai ki wurin aneelerh”?

“Daddy bazaka tafi dani ba” aɗan shagwa6e tayi maganar,

“Am sorry, Ba cikin gari bane bazan iya yin tafiya mai nisa dake ba,”

Tuni idonta sun Ciko tab da kwalla sam bataso yana tafiya yana barinta a gida, musamman yanzu da babu school, islamiyace kaɗai yau kuma Alhamis ne basa zuwa da juma’a,

“Dan Allah daddy…….”tunkafin ta ƙarasa yayi saurin katse mata hanzarinta”yi mun shiru nace maki ba cikin gari bane,”

Shiru tayi Ƴar kwallar da take 6oyewa ta soma gangarowa akan fuskarta,

Ƙarasawa Yayi tare da sanya hannayen shi gaba ɗaya ya ɗauketa, yana ɗan bubbuga bayanta”Idan kikayi mun kuka Allah zan fasa zuwa buzaye dake ne”

 Cikin shessheƙar tace”bazanyi ba”

 “Haka nakeson ji my angel”

Sauke ta ƙasa ya yi tare da ruƙo hanunta, suka fito daga ɗakin ya ja ƙofar ta rufe, Kaitsaye suka nufi gidansu aneelerh, lokacin da suka shiga falon gidan a tsaye suka gansu shida Aneelerh, Ya kammala shirin shi cikin boyel, aneelerh kuma na sanye cikin Turkish dress, Riga da wando blue, ta ɗaure kanta da mayafin kayan.

Gaisawa suka fara yi da aneelerh kafin Ya damƙa mata angel,

Batare da 6ata lokaci ba, su ka yi mata sallama atare a cikin motar Uzair suka tafi,

Saman Sofa suka zauna ita da aneeleerh,

  “Kina jin yunwa”? ɗaga mata kai tayi alamar eh,

 “Hawayen menene akan fuskarki”?tayi tambayar tana kallon fuskarta,

   “Daddy inata roƙon shi ya tafi dani amma ya ƙiya”

Murmushi aneelerh tayi”Shine kike kuka? idan ki ka yi haƙuri ae ba kwana zasuyi ba,” ta ambaci hakan tare da miƙewa ta nufi kitchen,

Kishingiɗawa angel tayi tana jiran dawowarta, fitowa aneelerh tayi daga Cikin kitchen ɗin hannunta ɗauke da plate, mai ɗauke da farfesun naman Kaza, da alama ba’ajima da kammalashi ba, don sai huci ke tashi ga ƙamshi,

A saman table ta ɗaura plate ɗin,tare da samun wuri gefen angel ta zauna,

  Jin ƙamshi Yasa angel mikewa ta gyara zamanta,

   “Aunty aneelerh,duk ke kikayi wannan”?

  “A’a bani nayi ba, Ana ce ta yi shi”

 Yatsina fuska angel tayi”wannan matar kamar munafuka,Ni ban yadda da ita ba Allah, Kullum tana aɗaki kunshe, Ita bata fitowa sai zata yi girki ko gyaran gida,

  Dariya sosai Aneelerh tayi”Zaki fara tsegumin naki ko”?

  Ta6e baki ta ɗanyi, tare da zura hannu cikin plate din tana ɗan tsakurar naman, Har wani jinjina kai take yi saboda daɗin da ya kai mata karo, zuba mata ido aneelerh tayi tana kallonta,

  “Aunty aneelerh,”

 “Menene”?

 “Mutane dayawa suna cewa Ni matar Manyace, irin matan masu kuɗinnan, Allah idan na girma mai kuɗi zan aura, inda zanje in huta, Bani aikin komai sai dai Ƴan aiki  suyi mun ina daga kwance,”

  Tunda ta soma zuba, Aneelerh ta ƙura mata ido tana kallonta,Wato Zuzuta kyanta da mutane suke yi suna cewa ita matar manya ce, Shine ta haddace maganarsu acikin kanta, har tafara sawa ranta aure inda zata huta,

  “Bakya son talaka”baneelerh ce ta jefa mata tambayar,

  Yatsina fuskata tayi”ae annabima yace mu nemi tsari da talauci,”

Murmushi Aneelerh tasaki, tasan halin angel da gaddama, shiyasa bata ja zancen da tsayi ba,

  “kinga daddy yaƙi yin aure, Da a lama sai na fara haifa mashi ƴan jikoki” takai karshen maganar tana sakin ƴar dariya,

  Murmushi aneelerh tasa ki a ranta tana mamakin yadda take maganar aure har da haihuwa ko kunya babu halin angle sai ita kafin tace”mai zai hana kisa ma shi matar aure”

  ɗan zaro ido tayi bakinta cunkushe da naman data tura, ahaka tace”Tab, salon tazo ta mallake mun daddyna, Ƙwara yayi ta zaman shi a haka babu auran,”dariya sosai aneelerh tayi”Angel kenan mai abun ban mamaki” ta ambaci hakan tare da mikewa tace”zan shiga daga ciki inaso na kwanta, Idan kin kammala ci, Ki kai plate ɗin a kitchen, kizo ki same ni a ɗaki muyi karatun haddar da aka baki islamiyya”

Ta amsa mata da toh”sai da angel ta kammala shan farfesun tukunna ta miƙe ta nufi kitchen, Bayan ta ajiye plate din,ta fito ta nufi ɗakin aneelerh

***          ***        ***        ***      ***   **

A 6angaransu taj kuwa, gidan wani abokinsu suka fara zuwa kai mashi ziyara, sun jima a gidan bayan sun baro gidan abokin nasu, Suka Nufi gidan Gonar uncle abdallah, da niyar suje su duba yadda komai ke tafiya, Kafin su dawo gida,

Gidan Gonar acan bayan gari yake cikin daji, lokacin da motar su ta ƙarasa Cikin dajin, Adai dai bakin Gidan gonar uzair ya yi parking ɗin motar, Wani tsohone daga waje saman benci yana sauraron radio da a lama shine ke kula da gidan Gonar,

Tunkafin Suyi parking ɗin motar, Ya miƙe yana ta faman washe baki don ya gane motar uzair ce,

At same time suka fito daga Cikin motar, A hanzar ce suka ƙarasa inda yake a tsaye, Jikin shi na sanye da riga da wando na yadi, Zariyar wandon har kasa kamar wani ta6a66e, Gashin kanshi duk hurhurace, Fari ne sol kanshi da rawani irin na buzaye,

“A’a wa nake gani kamar Tajo?’ cike da mamaki ya yi maganar yana kallon tajuddeen, miƙa mashi hannu taj yayi fuskar shi ɗauke da fara’a yace”Nine mana, baba buzu ashe kana a raye” ya yi maganar da zolaya,

  “Amana batace haka ba tajo,Yaushe rabon da in sanyaka a idanuwana tun kana ɗan matashi,”

   “Yau dai gani nazo, kuma bada wuri zamu tafi ba, har sai ka gaji da gani na,” yakai ƙarshen maganar yana dariya, shima dariyar ya yi”wuni kuka zo mun kenan aikuwa har masara zan gasa mana muci muna fira,

   Kafin taj ya yi magana uzair yace

  “Fatan mun same ku cikin koshin lafiya, Ya komai ke tafiya”

  Tsohon yace”alhamdulillah, Ku ƙaraso mu zagaya cikin gonakin mana,” Gaba ya yi su ka bi bayan shi, suna ɗan tattauna fira atsakaninsu”

Sunjima suna kewaye gonakin har cikin gidan gonar suka shiga, koda aka fara kiran sallar Magrib, atare da baba buzu su ka yi sallar Acikin gidan gonar, ba su tashi tafiya ba, sai bayan da akayi sallar Isha’e, tukunna su ka yi sallama da shi,

Taj ne ya kar6i driving ɗin, Uzair na gefen shi, motar su na haurawa saman titi, wasu dankara dankaran motoci masu black tinted suka shararo da gudun gaske kusan su shida, A jere suka Kurɗaɗa cikin dajin,

Duk akan idonsu tajuddeen, Da mamaki akan fuskar Uzair yace”kosu wanene a cikin motocin can? Kuma ina zasu dosa ne? Ni dai a iya sanina babu wani gida dake acikin dajin nan,”

Taj yace”May be ko wani party ne za su yi, ba abun mamaki bane”

“That’s impossible, Party kuma arasa inda za’ayi shi duk faɗin garin mu sai cikin dajin nan, Gaskiya ni ban yadda ba Allah, tabbas inaso nasan me zasu yi a cikin dajin can, Ka juya motar mubi bayan su”acewar uzair,

Taj yace”Ni bazan bi su ba, kawai daga ganin motoci sun shiga daji sai kace mubi su, for what reason?

“Nidai kawai kayi a bunda nace maka, Kada ka manta mu fa ƴan jarida ne,

rai a ɗan 6ace taj yace”Mu ƴan jarida ne, Ba jami’an sirri ba, Don haka ni bazan bisu ba, Gida zamu koma”

Yana ƙoƙarin juya sitiyarin Uzair ya damƙi hannun shi, juyowa yayi suka haɗa ido,

  “Ka yi abunda nace maka, In ba so ka ke in sauka daga Cikin motar nan ba, in bayansu da ƙafafuna”

Sanin kafiyar Uzair ne, Yasa Taj Juya motar Ya nufi Cikin dajin, Zuciyar shi duk a jagule don ba ƙaramin takura shi uzair yayi ba,

“Ka rage gudun motar” acewar uzair, a takure taj ya rage gudun motar, yayin da yake kurɗaɗawa cikin dajin  har Allah ya kawo shi wurin da waɗannan danƙara danƙaran motocin su ka yi parking, A jere su shida a bakin wata ƙorama,

Daga nesa dasu taj yayi parking ɗin motarsu, tare da kashe hasken motar su, don kada su gansu, Amma su suna iya hangensu saboda sunbar nasu hasken motocin su a kunne,

Natsuwa su ka yi suna jiran ganin Su wanene zasu fito daga Cikin motocin,

Kusan ƴan mintuna, kafin a buɗe motocin, kamar a shirin film suka fito a tare, Kowannansu Na sanye da suits ajikin shi black colour, fuskokinsu na sanye da mask, daga ganin bodyguards ne, At same suka buɗe murfin Back seat na motocin,

Wasu Manyan mutanene suka soma saukowa daga Cikin motocin, kowannan su na sanye Cikin shigar hausawa, Daga ganinsu dattawane sun kwan biyu aduniya,

Kallon juna taj da uzair sukayi a lokaci ɗaya kafin suka mayar da hankalinsu kan abunda suke kallo,

Bayan Alhazawan sun kammala fitowa daga Cikin motar, Ɗaya daga Cikin bodyguards ɗin Ya zagaya bayan motar ƙarshe, Ya buɗe boot ɗinta, Hannu ya sanya ciki tare da danƙo rigar Wani bawan Allah dake naɗe cikin boot ɗin, Ya wurgo shi waje, Gaba ɗaya mutumin ya kife ƙasa, Rawanin dake naɗe a kan shi Ya warware, Jikin shi sai kerma yake yi, kamar wanda sanyi ya kama, daga ganin shi dai Malami ne, duba da irin shigar shi,Jallabiyace ga kuma rawanin shi, hada cazbaha a hannun shi lokacin daya ɗago, La66an shi nata kerma Yana ambaton”Innallahi wa’inna ilaihirraji’in, La’ila ha’illah anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin,’duk yabi ya susuce,

Cike da taku irin na majiya karfi, Bodyguard ɗin ya kuma takawa Zuwa mota ta biyun ƙarshe Ya buɗeta,

Wasu ƙananun Yara ne guda biyu, Gwanin ban tausa yi sun ƙankame junansu mace da namiji, Sun cunkushe acikin boot ɗin,Yadda kasan irin kifin gwangwanin nan,

Damƙo wuyan rigunan jikinsu yayi tare da ɗago dasu Ya wurgo dasu ƙasa, Gaba ɗaya suka kife saman Ciyayin dake a wurin,Sautin kukansu ya ƙarade wurin, Miƙewa Yaran su ka yi da gudun gaske suka nufi wannan malamin daga gani ubansu ne, Rungumesu ya yi a jikinshi sunata kuka, A ƙalla macen bazata wuce shekara Takwas ba, Namijin kuma goma,

Tsananin tsoro ne Bayyane akan fuskokin su, Hankalinsu amatuƙar tashe yake, Daga gani bada shiri aka ɗaukosu ba, Saboda kayan dake a jikin yaran duk na bacci ne, Ita macen ko kalli babu a kanta, ɗan kitson Shukkun da akayi matane, ƙafafuwansu ko takalma babu,

Ƙawanya waɗannan Alhazawan Sukayi masu, Suka sanya su a tsakiya, Yayin da bodyguard ɗin ke a bayansu,

Wani irin kallo suke binsu dashi, kafin daga bisani wani dattijo daga cikin alhazawan Ya soma magana”Malam wa kake da suna”?muryar na kerma Malamin yace”Jazuli”

Jinjina kai dattijon yayi”sau nawa ina jan kunnanka”?

“Sau biyu” cikin shessheƙar kuka ya yi maganar,

“Okey,Saboda kafiya da taurin kai irin naka Baka daddaraba ka sake shiga hurumina ko? Meyasa ka tsananta bincike akaina? Ka sanni ne? ko ina da wata alaƙa dakai ne?ya yi tambayar idonshi akan malamin

Shiru Malam Jazuli yayi, yana ta faman mazurai, Hannunshi bibbiyu ya tallabe ƴa’ƴan shi,

“Koda zaku cutar dani, Ina roƙan alfarma ɗaya a wurinku, dan Allah kada ku ta6a ƴa’ƴana,”

Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayan su, mai sautin gaske,

Taj da uzair dake la6e acikin mota suna kallonsu, Tuni sunsha jinin jikinsu, buɗe murfin motar su uzair ya yi da niyar ya fita, da sauri taj ya ruƙo Hannnunshi murya ƙasa ƙasa yace”baka da hankali ne, Idan suka kama mu fa”

  Uzair yace”bana jin abunda suke cewa, dole na fita” ya zame hannunshi daga ruƙon da taj yayi mashi, yasa kai ya fuce daga Cikin motar, kasa zama Cikin motar ya yi ya ƙwammace yabi bayan uzair komai zai faru ya faru, Buɗe motar ya yi tare da fitowa Yabi bayan Uzair Cikin sanɗa suke tafiya har suka ƙaraso gab da su, a bayan wata gabjejiyar bishiya, suka la6e suna kallon su,ɗan Jarida da kasada,

 “Nifa inaga,Yakamata mu tafi uzair”acewar Taj,

  Girgiza kai uzair yayi”Kaɗan jira muga Mai zasuyi ma shi, bari ma na ɗauki video,”yana ƙokarin zaro waya, Taj ya buge hannunshi”ashe baka da hankali, So kake hasken camera ya tona mana asiri, ba don yaso ba Ya haƙura da ɗaukar video ɗin,

Suna Cikin yin Maganar nan, Su ka ji wani irin gurnani mai matuƙar tsoratarwa, A ruɗe suka ɗago suna kallon su,

Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take yazama wata irin halitta mai matuƙar tsoratarwa,Ya shiga girgiza jikinshi Yana wani irin gurnani,

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *