Kwai Cikin Kaya Chapter 1

This entry is part 1 of 3 in the series Kwai cikin kaya by Bilyn Abdul

        WAI CIKIN AYA!!

Bilyn Abdull ce

Da s觼nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai.

Ya rabbi ka bani ikon faar abinda zai amfanar da al’ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka tsare harshena da alalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.唐

Ya ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al’ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama, ALLAH ka kawo mana arshen wannan annoba ta corona virus (covid-19), domin rahamarka garemu唐.

Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin anantarta, inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba對.

Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum), alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da kuke har gadon barci.

_____________________________________

BOOK ONE

Shafi na aya

_____________________________________

………..Ko wacce kafar yaa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine sace shahararren mai arziin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*.

A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin sauka da tashi na babban birnin asar. Abu mafi aure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da mutumin da yay garkuwa da shi ya wamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi aya da Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama’a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ぐan jarida guda biyu a filin jirgin da har suka auki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar da aya a masu gadinsa ya bue masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake bue masa ofa dan ya fita sai yace ku aukeni inda kuka ajiye, a taaice dai Alhaji Sadi kokino yayi atan dabo a hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa.

Zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da bue kunnuwa da idanu ko za’aji wani abu da ga bakin wannan mai wamushe da ba’a san ta yanda yay siddabarun sace Alhaji kokino ba…

*____________________________________*

A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruaen labari suma talakawa ぐan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu ALLAH ya ara suke faa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke aryata lamarin da dangantashi da farfaganda irinta manyan asa ce kawai, ilama yana can kwance a gidansa lafiyar ALLAH.

Daga masu aryatawa har waanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda wamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami’an tsaro da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana.

Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan.

*___________________________________*

Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan anja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa.

Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai oari da jajircewa a aikinsa kallo aya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da unbin kasalar dake tattare da shi.

Tsayuwar motar da bue murfin da akayine ya tilasta masa bue lumsassun idanunsa kaan tare da ago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke aure a tsintsiyar hannun, kaan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaan kafin ya sauke hannun da maida dubansa ga ofar motar da aka bue.

Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baar rigar sanyinsa jibgegiya dake gefe ya zura kafafunsa waje.

Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya bue ofar yay azamar kai hannu zai amshi rigar sanyin yana sake amewa alamar girmamawa.

Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaayansa yana tura aramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando.

Idanunsa da ke jajir ya ago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka ame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinule kawai yay gaba ba tare da suma yace musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba.

Cikin nutsuwarsa ya iso wajen da ake buatar ganinsa, da ganin yanayin akin zaka fahimci wajene keantacce na jami’an tsaro da sukan tattauna akan wani case ko shawarwarinsu idan sun tado musamman ta fuskar tsaro.

Ba tare da yay magana da kowa ba ya samu waje ya zauna, suma sauran waanda suka shigo tare wajen zama suka samu. akin yayi tsit, bakajin komai sai arar AC da na fitar numfashi, sai kuma an motsin da baza’a rasaba.

Wanda ke tsaye jikin allon bangon yana wani ぐan zane-zane ya ago fuskarsa a matukar murtuke yana kallonsu.

“Nasan kowa zaiyi mamakin wannan taron na gaggawa da muka kira, duk da dai dukkan tunaninmu zai iya tsayawa a waje aya game da abinda muka wayi gari da shi na sace babban mutum irin Alhaji Sadi Kokino. Kamar yanda muka sani tun a daren jiya wasu a cikin jami’anmu suna a wajen domin binciko ainahin abinda ya faru, a yanzu hakama daga can muka tado aya da ga cikinsu domin ya bamu bayanai dangane da lamarin, sannan musan mataki na gaba da zamu auka kuma, dan yanzu dai ga agogo ya nuna arfe 7:19am, na tabbata duk inda 8am tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami’ai na farko da kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama’ar gari zuwa ぐan jarida da iyalansa dama jama’ar dunaya baki aya”.

A tare suka shiga jinjina kai alamar gamsuwa da bayaninsa.

Cikin gyara tsayuwa ya ke kallonsu, ya sauke idanunsa akansa da har yanzu hannunsa ke dafe da kansa, *”Jawaad!”*.

Jin sunansa da aka ambatane ya sakashi janye hannunsa tare da ago manyan idanunsa da ke a jajur ya sauke akan ogan nasa, cikin dakewar murya da ke tabbatar da shiin jarumine ma’abocin nutsuwa ya amsa da “Yes sir” tare da miewa tsaye yana amewa.

Gaban allon ogan ya nuna masa da biron dake hannunsa.

Cike da kasala mai tare da nauyin jiki ya taka zuwa wajen, ya maido kallonsa gaba aya zuwa ga sauran jami’an tsaron dake cikin akin taron.

Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara fain, “Duk abinda zan faa game da wannan lamarin a taaice zai iya zama gaggawa, dan har zuwa yanzu da na baro filina jirgin da gidan Alhaji Kokino babu wani bakin zare da muka samu a kai sai surutai marasa makama, a cctv cemaras na Airport kuma lafiya lau Alhaji Sadi ya shiga mota tare da masu tsaron lafiyarsa. A an nazarina ta wannan gaar ya nuna lallai mai satar yanada matuar wayo, kuma wararrene mai aiki da wawalwa…”

Kowa jin jina kai ya shiga yi alamar gamsuwa da bayanin Jawaad da ke rie da kansa da ke ara arfin sarawa na ciwo.

Wanine cikin waanda ke zaune a kujeru na musamman, alamun shima babbane yay gyaran murya tare da gyara abin maganar dake gabansa. “Wato bayanan JAY abin dubawa ne kam tabbas, amma ku wace shawara ce da ku a kan hakan?”.

Wani ne da ga can rukunin kujerun da Jawaad ya taso ya aga hannu, damar magana aka bashi. Bayan ya mie ya ame sannan ya fara magana cike da girmamawa, “Yallaai warai maganar jay gaskiya ce, sannan ya kamata muma muyi shiri na musamman akan wanann case in, dan inhar muka kuutar da Alhaji kokino ba aramin daraja hukumar ぐan sanda zata sake samuba a idon jama’a”.

Tafa masa sukai, wanima ya sake aga hannu aka bashi dama, shima goyon bayansa ya nuna akan maganar Jawaad. Bayan shi mutane biyu sun sake yin mubayi’a kafin wani ya tashi shikuma bayan an bashi izini, fuska a aure yana wani hura hanci da fesar da iska yace, “Sam wannan shawarar tasa bata kan tsari, ya kamata ama alubalancesa, tun a daren jiya bayan faruwar abin da mintunan da basufi goma ba aka turashi wajen shida wasu jami’an tsaro, amma ace babu wani bayani na cigaba da aka samu, bayan a ぐan mintunan da sukaje wajen bai kai nisan da za’ace shi mai wamishen yayi nisa ba, kawai shi dai yace bazai iyaba sai a nema wanda zai iya kawai, inba hakaba ta silar wannan case in to lallai hukumar ぐan sada tana tare da babbar barazana ta zubewar kima da sake saka shakku a zukatan al’umma a kanmu”.

Kowa kallonsa yake kawai, yayinda manyan suke jinjina masa kai da wasu a tsirarun sauran jami’an.

Jawaad kam ko motsi baiyiba balle ya kalli wanda ya gama bayanin, sai dai ya saki wani asaitaccen murmushi da ya bayyana loar kumatunsa guda biyu kawai.

Ba karamin sukar zuciyar Qaseem Ali murmushin Jawaad yayi ba, amma ta wani angaren ya anji sanyi a ransa ganin maganarsa taso kawo ruani, dan sai ya zam kawunan jami’an tsaron yana neman rabuwa, wasu suna bin bayan Jawaad Abdul’aziz yusuf, wasu kuma suna bin bayan maganar Qaseem Ali.

Dan danan cece kuce ya fara yawaita a akin taron har sai da aka tsawatar.

Murmushi Qaseem Ali ya saki ganin Jawaad ya dafe kai, sannan fuskarsa ta kuma aurewa alamar ransa ya sosu, dama babban burinsa kenan.

Sai dai kuma sam tunaninsa bai sanar masa gaskiya ba, dan shi Jawaad surutun da akin taron ya kaure da shine ya kuma saka kansa arfin bugun ciwon da yakeyi sakamakon rashin samun isashshen barci da yay a daren jiya, ga ruwan sama da yay musu dukan tsiya jiyan da daddare, bayan dama ya koma gida a urarren lokaci ne jiyan kafin ayi kiransa akan maganar sace kokino.

Tsitt akin yayi bayan tsawatarwar da akayi, yanzu ma aya daga cikin shugabannin ne yay magana.

“Duk wani kace nace bama buatarsa anan, kowa yasan wanene JAY akan wazon aiki, ba wannan ne na farko ba da aka bashi irin wannan damar kuma ya magance ta, sai dai ko wanne irin case da ruanin da yake zuwa da shi, dan haka a wannan gaar mun naa Jawaad Abdul’aziz yusif matsayin wanda zai kula da wannan case in, sannan mun saka Qaseem Ali matsayin mataimakinsa, kuna da damar haa rundinar jami’ai 30 da zasu taimaka muku, muna fatan zaku bamu gudunmawa ta haia wajen fiddamu kunya ku kuutar da Alhaji Sadi cikin lokaci ankani da baza’a ga rauninmu ko gazawa ba”.

Tunda ya fara magana Qaseem yaji sunansa matsayin mataimakin JAY fara’ar fuskarsa ta ace at, hakama magoya bayansa. Ga Jawaad kam bai ko ago kaiba balle musan yanayin da yake ciki.

Sun an cigaba da tattaunawa kusan na awa aya, wandda acikin awa ayarnan ba aramin a takure Jawaad ya tsinci kansa ba, ana kammalawa ya nema izinin zuwa gida ya an huta koda na awa uku ne.

Babu wani jan zance aka bashi dama, dan yanayinsa ya nuna buatuwa sosai na san hutun…..

*___________________________________*

Tunda Gimba yay fakin motar a harabar gidan ya bue idanunsa da suka sake masa nauyi da yar, ba tare da ya jira Gimba ya bue masa murfinba ya bue da kansa ya fice, rigar sanyinsa ce kawai a hannunsa sai bindiga da aramar wayarsa da ya fita da ita kawai.

A yanda ya shigo ya ga falon jiya yauma haka ya sameshi, yaja siririn tsaki yana haiye wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maoshi, zuciyarsa a matuar cinkushe ya arasa sama inda nanne akin barcinsa yake.

Kallo aya yayma falonsa ya auke kai, dan hatta da kofin da ya sha shayi a daren jiya yana a inda ya barsa, sam shi baima san wace irin mace ya aura ba, azama ko ballagaza?. Takaici bai nemi shake numfashinsa ba sai da ya arasa haaen bedroom insa ya sauke dubansa a kan lafiyayyen gadonsa da har yanzu take kwance, ta wani udundune cikin lallausan bargonsa tana shaar barci. Tuni idanunsa sun sake kaawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka sake fitowa raa-raa, yasan ko rantsuwa yay baza a bisa bashin kaffara ba akan Shuhudah batai sallar asuba ba.

Bai sake kallon gadonba ya jefa rigar sanyin akan sofa tare da zube wayarsa da bindigar saman tabirin dake shakanin kujerar da gado.

Duk da wani jiri-jiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa hakan bai hanashi nufar bayi ba dan ya samu ya watsa ruwa ko zai samo kan jikinsa……………

Series NavigationKwai Cikin Kaya Chapter 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *