Kwai cikin kaya Book 2

Kwai Cikin Kaya Chapter 2

[11/4, 6:29 PM] El~hajj✨: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Alhmdllh inama kowa fatan alkairi, nakumaji daɗin wannan tarba, naso ace zan iya jurewa na biku ɗai-ɗai na amsama kowa Comments ɗinsa, sai dai nace kuyi haƙuri, kamar yanda matsalan ido ta dakatar dani da typing dolene yanzuma na ringa lallaɓawa saboda kunada ɗunbin yawa, akwai group insha ALLAHU da aka buɗe a shafin manhajar Telegram, masu amfani da wannan shafi su maza su garzaya idan suna buƙata, domin canne zai zama dandalin tattaunawa akan littfin ƙwai cikin ƙaya da sada zuminci, duk mai karatu yana buƙatar dandali na tattaunawa akan littafi, dan da yawanmu hakan na bamu nishaɗi da sake fahimtar da mu abinda bamu fahimtaba, kuma yana ƙarama writer ƙarfin gwiwar typing koda batai niyyar hakanba, ku maza kar a baku labari. Zakuna samuna koda yaushe a can domin ku tabbatar ina tare daku, masoyan bily kuma na isar da saƙonku gareta akan ta daina tsoron jay😂, masoyan Shahudah tana miƙo muku gaisuwa itama🤓.

Wannan shine link ɗin group namu mai suna MASARAUTAR BILYN ABDULL A manhajar Telegram😘😘.

2

…………..Koda na fito daga ɗakin saida na huta a falon saboda yanda zuciyata ke mutsu-mutsu a cikin ƙirjina, ina matuƙar mamakin wannan al’amari dake yawan faruwa tsakanina da mutumin nan, na kuma rasa wazan tunkara da maganar halin da nake tsintar kaina akansa kozan samu fashin baƙin saɓanin wanda zuciyata ke kissima min, nidai nasan ba tsoronsa nakeba, to minene dalili? Wannan amsar nake neman mai bani.

Gwiwa a sage naja ƙafafuna na fice daga sashen zuwa harabar gidan. Yanzunma dai ban sami ko ɗaya daga cikin su aunty Aamilah ba, gashi banida Number kowa a cikinsu. Dole na sake nemar guri na zauna inda babu yawan hayaniyar mutane, sai jefi-jefi nakan ɗanga sun gittani.

★★★★★

Yanda Jawaad ya nuna halin ko in kula da ganin na Bilkisu bazaka taɓa tunanin yama santaba, sai dai harta fice daga ɗakin yana kallontane ta wutsiyar ido, acan ƙasan zuciyarsa na raya masa “Ita kuma miya kawota nan?” sai dai a fili bazaka taɓa fahimtar komaiba.

Zama yay a saman ƴar dirowar dake farkon shigowa ɗakin, cikin girmamawa ya gaisa da iyayensa, sukai masa gaisuwar ta’aziyyah tare da jero addu’ar neman gafara ga mamacin, har suka cigaba da ɗan tattaunawa akan rasuwar wadda ta jasu tunowa da rasuwar mahaifin Jawaad ɗin shima da ɓatan mahaifiyarsa.

Haɗiyar zuciya kawai Jawaad yake famanyi, amma bakinsa ya kasa furta komai, daga ƙarshema saiya miƙe yana faɗa musu zaije ya ɗan kwanta, gimba zai kawo musu abincin da zasu ci.

Basu hanashi tafiyaba, dan yanayinsa ya nuna yana buƙatar hutun sosai.

★..::..★

Sai kusan ƙarfe biyar na hangi Mom suna gaisawa da wasu gungun baƙi da sukazo musu gaisuwa, da sauri na miƙe na nufeta karta sake ɓacemin, dan matuƙar gajiya na gaji da zaman ni kaɗai, danma naɗanyi cheating dasu Rebecca ne a group ɗin da muka buɗe iya mu biyar kawai na rage kaɗaici. Daga gefe na tsaya harta gama gaisuwa da mutanen suka tafi kafin na ƙaraso gareta, gaidata na farayi a ɗarare, tunda nasan bani da wata fawa a gareta, amma a mamakina sai naji ta amsa harda tambayata ina na shiga tun ɗazun bata ganniba? wani sanyi ya ratsa zuciyata, kasancewata marainiya ina matuƙar buƙatar kulawar mahaifiya koda kaɗanne, rashin samu kuma na sakani a ƙunci sosai, sai dai ina ƙoƙarin shanyewa ba kowa ke fahimtar hakanba. Cikin girmamawa na bata amsar tambayarta, saita bani umarni akan muje ciki naci abinci.

Ban sake sakashi a idonaba har zuwa dare bayan sallar isha’i da muka fito domin tafiya gida, ƙiri da muzu Aamilah da aunty Shahudah suketa ƙoƙarin zamewa haɗa tafiya dani, duk da basu fito fili sun faɗaba na fahimci haka da kaina, dan kafin nagama kimtsawa harsun fice daga sashen na Mama Atika, sai tare muka fito da Mom, sai muka iske harsun tafi wai tare da Yah Salman.

Banji haushiba, saima murmushi da nayi kawai, driver ne zai tafi da Mom, dan haka nima su zanbi dole. Mom ta tsaya gaisuwa da wasu mata da suma zasu tafi, ƴan gayune sosai da kallo ɗaya zakai musu ka fahimci naira ta zauna musu, nidai bayan na gaishesu jikin mota na koma na jingina kawai ina kallonsu da mamakin yanda naga Mom ta sake dasu sosai, yanda na santa da wulaƙanci, koda yake masu iya magana kance wata gaban tafi gaban raini ai.

Zuciyata ta motsa da ƙarfi a cikin ƙirjina, hakan ya saka tsoro ziyartar raina, koban faɗaba nasan hakan na nufin Dodona ya kusanto wajen koma yana wajen, zuwa yanzu nafara sabawa da wannan SABON AL’AMARIN namu.

Ilai kuwa ina ɗago idanu akansa na sauke, tsaye yake ɗan nesa damu kaɗan, hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ɗayan kuma ya riƙe waya dake kunnensa, wadda ke nuna alamar yana magana da wanine, ɗan taku yake ɗaya biyu cike da nutsuwa da cikar haiba, ba kayan ɗazun bane a jikinsa, daga wando har rigar jikinsa na yanzu duk fararene tas, gefe wando na duka ƙafar biyu akwai ratsin dogon zare jaa daga sama har ƙasa, sai agaban rigar shima anyi rubutu da ja, hasken dake ƙwanyar a tsakar gidanne ya sani ganin abinda aka rubuta, sai silifas fari shima, sosai kayan sukai masa ƙyau, har na iya kasa janye idona a kansa dukda wutsilniyar da zuciyata keyi kuwa.

Haka kawai Jawaad dake waya da Jabeer yaji a jikinsa kallonsa akeyi, kallon kuma irinna wanda keda kaifin gani da baiwar ƙarfin kwarjinin idanu, duk yanda yaso basarwa tamkar yanda ya saba hakan sai ya gagara, dole ya fara wulƙita nasa fararen idanun kozai samu nasarar cafko wannan mayen idon dake neman saukar masa da gajiya. Karaf kuwa idanunsa suka sauka akanta, shima ƙirjinsa ya motsa alamar harbawar zuciyarsa. Tabbas yaji a ransa itace ke kallonsa, amma a mamakinsa sam idanunta da hankalinta basa kansa, karon farko da miskilancin yarinyarnan ya motsa zuciyarsa, tun ganinsa da ita na farko a airport ya fahimci miskilace ta bugawa a jarida, kasancewar ALLAH ya azurtashi da ilimin karantar hallayyar ɗan adam cikin lokaci ƙanƙani, zuwa yanzu mamakin ganinta yabar ransa, dan ya kula akwai alaƙa tsakaninta da Qaseem…….

“Hello…hello…” Da Jabeer keta ambatane ya sakashi dawowa hayyacinsa, dan tuni ya saki wayar da suke ya kama sabgar bilkisu, abinda bayayi sam a rayuwarsa (wato shiga abinda bai shafesa ba), yaja siririn tsaki yana murza goshinsa da hannunsa daya ciro daga cikin aljihu.

Dai-dai lokacin da Bilkisu ta buɗe gaban mota ta shiga ta zauna, dan Mom harta shige baya itama.

Wani irin harɗaɗɗen numfashi ya sauke har Jabeer na tambayarsa “ko lafiya?”.

Gutun tsaki yaja yana yanke wayar batare daya bashi amsaba, yakuma jan wani tsakin har sau biyu yana takaicin kansa da shiga hurumin da ba nasaba.

_______________________________

Washe gari ban biyosuba, dan inama barci suka fice, babu wanda yace a tasoni, nima koda na tashi kuku ke sanarmin sun tafi banji komaiba a raina saima daɗi, tunda nasan zuwana bazai ƙara komaiba koya hana, hasalima banason gamuwa da Dodona.

Bayan na karya ɗaki na koma nai wanka, nai shiri cikin doguwar riga ta atanfa data samu zaunannen ɗinki, bawata kwalliya naiba, nasaka turare sama-sama na fito bayan na yafa ƙarmin gyale.

Kai tsaye gate na nufa wajen baba maigadi dake zaune shida mai bayin filawar gidan suna hira, suna ganina suka shiga gaisheni cikin girmamawa, sam banason hakan da sukemin, dan kuwa niba kowa bace a gidan face maicin alfarma, sannan duk sun girmeni, baba maigadi ma a haife ya haifeni, shima mai bayin fulawar kobai haifi kamata ba nasan yanada manyan ƴaƴa…..

“Hajiya fita zakiyine?”.

Baba mai gadi ya katsemin tunanina, kaina na girgiza masa ina murmushi. “A’a baba ba fita zanyiba, hasalima wajenka nazo muyi magana idan ban takura makaba dan ALLAH”.

Da sauri yace, “Haba wace takura kuma” yay maganar yana miƙewa da sauri, babu jimawa sai gashi da farar kujera, ajiyemin yay gefensu alamar na zauna, mai bayin fulawa kuwa yay mana sallama akan zaije gida yakai cefane.

Sake gaisawa mukai da baba maigadi, yay min ta’aziyyar rasuwar da akayi, nako amsa masa tare da tambayar lafiyar iyalansa, bayan amsamin da yay muka ɗanyi shiru, tunani nake ta ina zan fara abinda ya kawoni garesa?. Zuwa wasu ƴan mintuna sai dabara ta faɗomin, nai murmushi ina sake maida hankalina gareshi da kunna voice recorder dan na samu damar kwashe dukkan abinda zamu tattauna nayi nazari a tsanake a kansu.

“Uhm… Baba dan ALLAH niko wata tambayace dani?”.

Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “ALLAH Yasa na sani hajiya”.

Murmushi naɗan masa, nace, “Insha ALLAHU inada tabbacin kama sani ɗin”.

Baice komaiba sai hankalinsa daya maido kaina baki ɗaya, nima sai na sake nutsuwa sosai.

“Baba dan ALLAH ko zaka iya tuna ranar da abinnan ya faru da Amina a gidannan da wanda ba’asan ko waneneba?”.

A bazata maganar tazo masa, dan haka kawai saiya hau tari babu shiri. A rikice na shiga masa sannu, na jawo ruwan dana fito dashi daga ciki na miƙa masa da sauri bayan na ɓalle murfin, amsa yay har hannunsa na rawa ya kafa goran a baki ya ɓaɓɓaka, saida yasha kusan rabi kafin ya sauke, idanunsa harsun kaɗa sunyi jajur, sai naji tausayinsa ya kamani, koda ya dawo dai-dai shiru nai ban sake masa tambayarba har tsawon wasu mintuna.

Na sake jeho masa tambayar a karo na biyu, yanzunkam a mamakinawa shiru yay bai tanka minba, sai dai yanata ƴan kalle-kalle tamkar mai tsoron a ganmu ko wani ya jimu. Jin bashi da niyyar bani amsa ya sakani kallonsa, a karo na uku na sake maimaita masa tambayar da sigar kwantar da kai………

“Ɗi!! Ɗi!!! Ɗi!!…” mukaji horn ɗin mota daga waje, hakanne ya sakashi tashi da sauri ya nufi gate ɗin, na tabbatar dama hanyar da zai gudu yake nema, sai kawai na samu kaina da ƙura masa idanu ganin yanda har yanzu jikinsa ke mazarin rawa.

Hancin motar Dad ne ya danno kai cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya ina miƙewa tsaye, saboda tsayawar da driver yayi a saitin da nake zaune, shi kuma Dad ya sauke glass ɗin ɓangarensa yana mani murmushi.

Nima murmushin nake masa ina miƙewa na nufesa, da hannu yaymin nuni nazo, dole nabi motar da direba yaja zuwa ciki inda zaiyi fakin.

Tare da Dad muka shige cikin falo yana tambayata miyyasa banbi su Mom ba can gida?, cikin girmamawa na bashi amsa akan sun wucene ina barci lokacin. Nayi zaton zaiyi faɗa, amma sai naji kawai yay ƙaramar dariya. Mun yada zango a falon ƙasa, ya bani Umarnin naje nasa kuku ya haɗa masa abinci mara nauyi yunwa ya keji, ya fita bai karyabane.

Koda naje kicin ɗin sai ban fitoba na zauna mukayi abu mai sauƙi wa Dad ɗin ni da kuku, dan zuwa yanzunkam Alhmdllh hannuna yay masifar faɗawa akan girki kala-kala na zamani, na gargajiya kuwa dama bani da matsala a kansa, innata tarigada tayi min wannan horon tun ban gama fahimtar muhimmancin girki ga ɗiya mace ba.

Bayan mun kammala nice da kaina na kawoma Dad, lokacin yana waya, na ɗora tiren bisa tebir ɗin tsakkiyar falon na jasa gabansa, buɗe masa komai nayi tare da tsiyaya masa ruwa a kofi sannan na koma gefe na zauna, a haka ya faracin abincin yana cigaba da wayarsa data jashi tsayin lokaci, sai yazam yanacin abincinne kawai a shiririce. Dan harya kammala wayar baici ko kashi ɗayaba bisa uku, ya ajiye wayar yana maido hankalinsa gareni, “Taso muci mana ɗiyata”.

“Lah Dad nakane, ni ban daɗema da karyawaba fa”.

Cike da kulawa yacemin, “Da gaske?”.

Na langaɓe kai gefe ina ɗagawa alamar eh. Murmushi yayi ya cigaba dacin abincinasa yana mani hirar data bani mamaki, dan kuwa akan kasuwancinsane ya ɗakkomin hira, yana faɗamin alkairi da kullum kamfaninsa ke samu da yanda kuɗaɗe ke shigo masa babu ƙaƙƙautawa. Banda masha ALLAH da ALLAH ya ƙara sanya albarka babu abinda nake iya cewa, danni kam dai ban fahimci dalilin mani labarinba, tunda a ganina ai sirrinsane wannan, ko a cikin ƴaƴa kuwa a ganina sai wanda ka aminta da amanarsa.

Kamar kuwa ya karanci mike raina, sai cewa yay, “Kinji inata baki labarin abinda bai shafekiba ko?”.

Murmushin yaƙe naɗanyi ina gyaɗa kaina, shima ya murmusa yana mai kai cokalin romon farfesun daya ɗobo a bakinsa.

“Karkiji komai a ranki Bilkisu, na yarda da kene kawai shiyyasa, dan na fahimci keɗin yarinyace mai hankali da tarin nutsuwa, sannan sam baki da yawan surutu, waɗanan halayyar taki na ƙaramin ƙaunarki sosai”.

Murmushi yanzunkam nayi har haƙorana na bayyana, nace, “Nagode Daddy”.

Ƙaramar dariya yay yana miƙewa bayan ya ajiye kofin da yasha ruwa, “Kinga bara naje naɗan kwanta na huta, zuwa yamma saimu tafi gidan rasuwar muma”.

Kaina na jinjina masa kawai, dan nima tuni nake buƙatar keɓancewa, inason yin nazari akan halinda mai gadi ya shiga akan tambayar danai masa ɗazun kafin zuwansu Dad daya gaza amsa mani.

Koda Yammar bamuje ko inaba, dan banga Dad ba sai bayan la’asar lokacin da yah Salim ke dawowa gidan. Harare-hararen da yaketayine ya sakani tashi na barmusu falon na koma ɗaki.

★..★…:::::…★..★

Washe gari litinin kowa yasan tushen aiki, hakanne ya sakani shiri tun a farar safiya, lokacin dana fito babu wanda ya fito a mutanen gidan, tea kawai nasha driver ya ɗaukeni zuwa station ɗinmu kamar yanda a yanzu da Yah Qaseem bayanan kullum shine ke kaini.

Nayi mamakin rashin ganinsa yauma a office, bayan nasan ya dawo, daga baya sai nayi tunanin kodan dai rasuwarcan ne da bansan minene alaƙarsa da mamacinba, dan har yanzu ina mamakin ganinsa a gidan su Mom ɗin, dukda wani sashe na zuciyata na rayamin shima ɗan uwansune ƙila sunje gaisuwane.

Daga haka ban daɗaba ban ragaba har lokacin tashi yayi muka tashi.

Tare muka tafi a motar Ummie, dan ita Dadyn ta ya bata mota ƴar ƙarama tun fara aikinmu, tun tafiyar Yah Qaseem sai yazam direba na kawoni da safe, ita kuma mutafi tare idan mun tashi sai ta ajiyeni gida ta wuce nasu gidan.

Kiran da Nazifa tai minne a waya muke amsawa tare da Ummie dake tuƙi, dan a amsa kuwwa (Hans free)na saka wayar yanda itama zataji, munzo dai-dai shataletalen (roundabout) ɗin da zamu ɗauki hanyar gida danja (traffic light) ta tsaidamu, sai kwasar dariyar labarin da Nazifa ke bamu mukeyi.

Kusan minti goma muna a haka, saina fahimci sam motocin basa motsawa ma, buɗe motar nai na leƙa, hayaniyar mutane sosai ke tashi, dan motocin dake tahowa a dukkannin titinan huɗune suka cure waje guda, watama ta mugun bugama wata, sun saka jami’i mai bada hannu a tsakkiya sunata zabga masa masifa. Mamaki ya sake kamani, nadai dawo na zauna, mun cigaba da hira kusan ta minti ɗaya nadai sake jin abin bai zaunamin a raiba, dan wannan go slow ɗin yafi kama da wanda aka haɗa da gangan, gashi motoci sai sake taruwa sukeyi titin na sake cinkushewa. Ummie na bama Nazifa amsa ni kuma na maida kallona ga mirror ɗin waje, har yanzu dai babu alamar motsin motocin a dukkanin titinan huɗu da suka raba kansu, sai naɗan kalli Ummie ina yamutsa fuska, dan na lura har yanzu ita bama ta fahimci halin da ake cikiba.

“Ummie akwai matsalafa, tabbas wannan cinkosan haɗashi akayi akan sani”.

Da sauri ta katse wayar tana cema Nazifa muna zuwa.

Kashe motar tai duk muka fita a hanzarce, tabbas an haɗashine da gayya, hakkanne ya sakamu fara ƴan dube-dube muna kutsawa tsakanin motoci domin san isa ainahin wajen da danjar take.

Gaba ɗaya wajen ya hargitse, sai hayaniya ke sake tashi, duk yanda mai bada hannun keson dai-daita komai hakan ya gagara, ga waɗanda motarsu ta gogi junama sun fara faɗa na shirin danbe. babu yanda za’ai muyi magana muma wani ya sauraremu, dan abin yafi karfinmu.

Kalle-kalle na maida hankalina wajenyi sosai kozan samo bakin zaren,

Idona ya kasa barin wata baƙar mota mai baƙin gilashi {tinted glass}, na wuceta yafi sau uku ina sake dawowa gareta, dan sai buga azababben horn mai motar yake nason a bashi hanya ya wuce tamkar shi kaɗaine yafi kowa buƙatar titin kosan tafiya.

Glass ɗin na ƙwanƙwasa, dan na tabbata koma wanene a ciki shi yana kallon na waje ai, ba’a saukeba na sake bugawa, dan haka kawai nakejin wata irin jarumta da ƙarfin zuciya da bansan daga ina tazo minba……..

A fusace aka bugo mirfin motar ya bugeni, kafin na dawo daga jin zafin da nayi kawai naji ƙarar harbin bindiga har sau biyu.

Take wajen ya hargitse da ihu, nima na toshe kunnena ina mai duƙewa ƙasa, mutane sai fita suke daga mota suna gudu, masu dabara kuma na kwanciya a ƙasa, tuni jama’ar dasuka taru suna hayaniya kowa ya kama gabansa, wasu sai son jan ababen hawansu baya suke suna komawa da baya-baya domin ƙoƙarin barin wajen.

Cikin tunanin da yazomin daga UBANGIJINA ya sani fahimtar akwai matsala.

Murfin motar da bai gama buɗuwaba aka ziro hannu ahaka aka ƙara wani harbin na kalla, da ƙafa na turashi ya bigi motar, hakan yasaka hannun da yay harbin ya matse sosai, ƙara ya saki yana sakin bindigar itama ta faɗi ƙasa.

Jan motar sukai da wani irin ƙarfi, dukda motsocin dake gabansu bila adadin, tuni wajen ya sake ruɗewa, jikake garraaam!! Kaccaam!! Na haɗewar motoci, wata na bugar wata, gilasai sai fashewa suke famanyi, waɗanda suke a motocin basu fitaba sunata ihu na firgita.

Saura kaɗan su takemin ƙafa, nai azamar sunkuyawa na ɗauki bindigarsa data faɗi, banyi zato ko tsammanin zan iya abinda nake yunƙuriba, amma cikin amincin UBANGIJI koda na harba sai harsashin ya sauka akan tayar motar ta baya.

Tangal-tangal motar ta fara, hakan kuma ya sake hargitse wajen da ihun mutane. Kuma harbin ɗayar tayar nayi, hakan ya saka motocin dake gefenta, sukuma suka bigi fitilar dake a tsakkiyar titi ta tsaya cak.

Gaba ɗayansu suka fito kuma lokaci ɗaya, dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya, gaba ɗayansu bindigace a hannayensu, hatta da wanda na bugama hannu da ƙofa na ɗauka tashi yana tare da wata, hannunsa dana buga sai faman jale-jale yake tabbacin na jimasa ciwo…….

Da ƙarfi naji an fisgi hannuna, dai-dai shigar ihun Ummie cikin kunnena tana faɗin “Bily!!! harsashi!!”………………✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *