Rayuwa da gibi hausa novels

Rayuwa da Gibi Chapter 1

RAYUWA DA GIƁI

Batul Mamman💖

Bismillahir Rahmanir Rahim

In loving memory of Aisha Aminu Balbalo (mai lalurar numfashi da take sayen cylinder ɗin oxygen wadda aka fi sani da Carofee). Allah Ya jiƙanta Ya gafarta mata. Amin

*

Wanki take a tsakar gida tana sauraron hirar mahaifiyarta da ƙanwarta Zee. Ba ta saka musu baki saboda tun ainihinta ba mai son hayaniya bace. Sai murmushi kawai idan sun yi abin dariya.

“Wannan wankin naki zai sami shanya kuwa Hamdi?”

Sararin samaniyar da Yaya ta kalla ita da Zee su ka zuba wa ido. Ga dai rana ana gani tana haska ko ina. Amma idan mutum ya miƙar da ganinsa zai yi tozali da baƙin hadarin da yake ta gangami daga nesa. Tunanin taƙaita wankin ta soma yi yadda wanda ta gama za su sami wuri akan ƙofofin ɗakunan gidan su ka ji sallamar wasu mata.

Da farinciki Yaya ta tashi daga kan tabarmar da take zaune ta nufi zaure tana cangala ƙafarta ta hagu wadda shan inna (polio) ya cinye. Da alama baƙin da aka kwana aka wuni ana zancen zuwansu ne su ka ƙaraso.

“Maraba lale da Altine.”

Shewar Yaya da baƙuwar su ka ji daga zauren da taje ta taro su kafin su dawo tsakar gidan hannun da baƙuwar a kafaɗarta.

“Oh ni jikar mutum huɗu. Ashe rai kan ga rai Jinjin? Ya bayan rabuwa?” Matar ta jero mata tambayoyi su na daga tsaye.

“Sai alkhairi. Rayuwar nan sai godiyar Allah.” Su ka sake rungumar juna su na dariya.

Ƴan matan da baƙuwar tasu mai suna Altine ta zo dasu da kuma Hamdi da Zee sai su ka tsaya kallon abin al’ajabi. Labaran da su ke ji game da juna ashe gaskiya ne don ga zahiri sun gani. Iyayen nasu sun yi zumunci sosai kafin a haifesu lokacin suna zaman Agege a Lagos. Abubuwa da dama sun faru waɗanda su ka yi sanadiyar dawowar su Jinjin garin haihuwarsu Kano. Ƙarancin hanyoyin sadarwa da faɗi tashin yau da gobe ya dakusar da wannan zumunta ta makwabtakar gidan haya ɗaya. Shekara bakwai kenan da dawowar su Altine Kano su ma amma basu taɓa haɗuwa ba sai da Allah Ya haɗa mazansu da wani da ya san duk su biyun. A wurinsa su ka sami labari harma da lambobin wayar juna.

Altine kakkaurar mata ce mai fara’a kamar gonar auduga. Mijinta Maje mahauci ne yana sana’arsa ta fawa. Da yake kakanninsu ɗaya duk su na da billensu na gadon sana’ar a kuncinsu. Akwai ta da kazar kazar don in tana abu sai ka rantse wannan jikin ba nata bane. Da wannan yanayin nata ta ja Jinjin a jiki duk da farkon zuwanta saboda yanayin mijinta da lalurarta bata sakewa da kowa. A gidan nasu na iyali goma sha biyu ƴan ka zo na zo aka taso ta a gaba da tsokana. Don ma maigidan nata ba ƙyalle bane. Bakinsa kaɗai ya ishe su ƙwatar kai. Idan ya fita ne dai ko banɗaki ta fito zagawa an dinga dariyar tafiyarta kenan. Sai da Altine ta gama lura da ita ta gane tsoron ƴan gidan da su ke duk hausawa take yi. Sai ta zame mata baki harma da hannuwa. Don idan abin bawa hammata iska ya kama dukan tsiya take yiwa mace la’ada waje. Ɗan Altine ɗaya lokacin ita kuma Jinjin da ciki su ka rabu.

“Ina Baballe kuwa?” Cewar Yaya cikin yanayi na kewa.

Da jindaɗi Altine wadda ƴaƴanta su ke kira Iyaa (kamar yadda Yarbawa su ke jan sunan) ta bata amsa.

“Ya tafi bautar ƙasa Binuwe (Benue)”

“Allah Sarki. Shekara kwana. Yaron da na tafi na bari yana tatata”

Dariya su ka yi farinciki da jindaɗinsu ba zai kwatantu ba. Duk wannan abin da su ke yi Hamdi da babbar cikin ƴan matan Iyaa kallon gane juna su ke yi. Ganewa mai cike da tsoro da fargaba a ɓangaren kowacce bisa dalilai daban daban. Kamar iyayen sun sani kuwa su ka zaɓi wannan lokacin wurin gabatarwa juna ƴaƴan nasu.

“Kina nufin da cikin Hamdi ku ka taho?”

“A’a, yayarsu dai Sajida. Tsiranta da Hamdi ma ya kai shekara biyar. Bata nan ne. Ta tafi Abuja gidan ƴar yayata da ta haihu.”

Iyaa ta murmusa “Allah Sarki” ta nuna babbar ƴar “Sajidan ce sakuwar Ummi kenan, don baku jima da tafiya ba na haifeta.”

Yayinda Yaya take da ƴaƴa huɗu, Sajida, Hamdiyya, Zinatu (Zee) da Halifa, na Altine uku ne. Baballe, Ummi da Siyama.

Sai da su ka nutsu da gaishe gaishen Yaya ta aiki Zee.

“Maza jeki gidan Lami ki ce ta baki lemukan da na bata ajiya.” Ta yiwa Iyaa bayanin sace musu transformer da aka yi kusan wata uku babu wuta sannan ta fuskanci Hamdi “ke kuma ki je wajen babanku ki faɗa masa Altinen Maje ta iso.”

Iyaa ta sanar da ita ai babansu Ummi na sauke su a ƙofar gidan ya yi waya da maigidan nata.

“Ina jin ya kwatanta masa wurin sana’ar tasa don ya ce can zai je sai su taho tare.”

Cigaba da hirarsu su ka yi wanda hakan ya bawa Ummi damar yiwa Hamdi inkiya da su tashi tana son magana da ita. Ita kuwa sai ta ɗauke kai kamar bata gani ba. Hakan ya tunzura Ummi matuƙa sai kawai ta miƙe tsaye ta ce tana son shiga banɗaki. Hamdi na jin haka ta san kwanan zancen. Cikin ɗakinsu ta gayyato ta ba don ta so ba. Duk da gidansu mai tsakar gida ne amma kowanne ɗaki da banɗakinsa a ciki. Wannan tsarin babansu ne da ya ce baya so ace komai dare, ruwa ko iska sai an fito tsakar gida idan za a zaga.

Shigarsu ɗakin ke da wuya Ummi ta juyo fuskarta a murtuke.

“Zan faɗawa Iyaa makarantarmu ɗaya amma kada ki kuskura ƙaiƙayin baki yasa ki faɗawa kowa sirrin rayuwata a makaranta”

“To” ta iya cewa don hankalinta a tashe yake. Yau ruwa ya ƙarewa ɗan kada. Sirrin ɓoye zai fito fili.

Rai a ɓace Ummi ta bangaji kwalarta yadda ta saba cin zalin ƴaƴan mutane a makaranta.

“Bar ganin nan gidanku ne kin dai san an kusa komawa makaranta. Kin kuma san ko ni wace ce ba sai an faɗa miki ba.”

Ficewa kawai Hamdi tayi daga ɗakin wani abu na hawa da sauka a ƙirjinta. Barazanar Ummi ba ita bace damuwarta kamar yadda zuwanta gidan yake nufin tonuwar asirinta. Gudun rana irin wannan da wata ƴar makarantarsu za ta zo gidansu yasa ta zaɓi makarantar kwana. A can ɗin ma bata da ƙwaƙƙwarar ƙawa ko ɗaya. Tsakaninta da kowa mutumcin gaisuwa ne da kuma taimakon da take yi musu na ƙarin haske akan karatu. Allah Ya yi mata baiwar ɗaukar darasi da zarar an koyar. Bata taɓa tsallake matakin ukun farko ba tun shigarta. Sau biyu makaranta na neman iyayenta domin a karramata a gabansu tana daƙilewa. Na farko ta ce mahaifinta ya yi tafiya. Na biyu kuma ta ce yana kwance tun kafin ta taho ya yi hatsari ya karye. Da taga alamun za a bishi gida gayyatar Yaya ta nuna ai maman ke jinyarsa. Malamin ajinsu da kansa ya gane akwai abin da take ɓoyewa sai ya sanar da hukuma kada a matsa mata. Sun riga sun saba ganin abubuwa marasa daɗi game da dangin ɗalibai. Tunda dai ba karatu aka hanata ba sannan duk dawowa daga hutu da kuɗin makarantarta take zuwa ya ce a ƙyaleta kawai. Daga lokacin sai dai idan an yi taron ta taho da kyautarta gida. Bata tsoron duniya ta ga lalurar Yaya amma mahaifinta da shi ya ɗorawa kansa bata son ana alaƙanta su a waje. Sau tari ita da ƴan uwanta su kan zauna su kwashewa wanda ya haɗa auren mamansu da mutum irin mahaifinsu duk kirkinsa albarka.

Fitowarta tayi daidai da dawowar Zee. Ta ajiye ledar hannunta ta tafi ɗauko tray za ta ɗora musu. Sai ga Ummi ta fito ta dubi Hamdi tana murmushi kamar gaske.

“Don Allah ba ke ce Hamdiyya Habib ta Rumfa Hostel ba?”

Murmushin dole Hamdi tayi ganin iyayen nasu sun dawo da hankali garesu.

“Ni ce. Kema kamar na gane ki.”

“Ummi ce, Ummi Maje. A ‘F class’ nake shi yasa ba lallai ki sanni ba.”

Iyaa ta hau murmushi wanda kuma da wuri ya koma shan kunu da ta gane me hakan yake nufi.

“Kin dai ji kunya wallahi. Karatu kamar cin ƙwan makauniya. Ƙanwar bayanki ma ajinku ɗaya?”

Ta gyara zama ta yiwa Yaya ƙarin bayanin asalin daƙiƙanci irin na Ummi wanda ya janyo ake ta yi mata repeating. Wannan shekarar ma don an riga an saka ranarta ne babansu ya roƙi alfarma aka kaita aji shida saboda ta gama a aurar da ita. Basu san rashin ƙoƙari ba shi kaɗai ne matsalarta ba kamar yadda Hamdi ta sani. Idan kana neman irin ɗaliban nan da ko bayan shekara ashirin in ka tambayi abokan karatunsu game dasu sai dai su bi su da ‘Allah Ya isa’ ko ka ji ana cewa ‘a dai yi shiru’ idan mutum ya riga ya mutu to Ummi Maje ce. Bully ce lamba ɗaya!

*

Lokaci guda rana ta ɗauke, hadarin ya sake duhu ga iska mai ƙarfi tana kaɗawa. Babu shiri hirar ta koma cikin falo. Zee ta ƙarasa shanya wa Hamdi kayanta ita kuma ta shiga kitchen ta haɗa salad bisa umarnin Yaya. Abu ɗaya hakan yake nufi. Abbansu yana tafe da abinci kuma tabbas a yau Ummi za ta sami makamin cutar da ita. A baya ko kallo basu ishi juna ba tunda duk jarabar mutum dole ya haƙura indai Hamdi ce. Bata shiga sabgar kowa balle a kai ga yin faɗa da ita.

Tsananin faɗuwar gaban da taji lokacin da aka yi sallama daga zauren gidan yasa ta sharɓe hannu wurin yankan albasa. Yayyafin da aka soma bai hana kowa jin sallamar mace ba. Yaya da Iyaa su ka amsa da fara’a yayinda Ummi ta ƙagu ta ga wace baƙuwar akayi mai zaƙin murya haka.

“Za mu shigo da Alh. Maje” su ka ji muryar ta faɗi. Sai kuma dariya ta biyo baya inda Baba Maje yake cewa “ai ka rigani indai amsa sunan Alhaji ne.”

Kan Ummi da Siyama ya ɗaure. Zee kuwa duk abinta na rashin damuwa yaƙe ta kama yi da taga yanayin fuskokinsu. A kitchen kuma numfashin Hamdi ya kusa ɗaukewa da Yaya tayi musu izinin shigowa.

Abbansu ne a gaba. Sanye yake da jallabiya yana tafe jiki na rangaji irin na riƙaƙƙun mata. Ga hula zanna bukar da ta ɗan sha jiki ya kafa a karkace. Shigarsa dai da ta sani ta yau da gobe. A bayansa wani mutum ne mai jiki wanda da alama shi ne baban su Ummi.

Suna shiga falon ta leƙa ta tagar kitchen ta hango yadda yake magana yana tafa hannuwan mamaki yadda mata su ke yi harda riƙe haɓa.

“Altine kece haka? Ikon Allah.” Ya zauna a kujerar kusa da matarsa. “Gaskiya rabuwar zumunci bata yi ba ko kaɗan.”

Fuskar Iyaa wasai ta amsa gaisuwarsa sannan ta mannawa yaran nata harara. Ba shiri kowacce ta miƙa gaisuwa da girmamawar dole. Ga mamaki ƙarara bayyane a fuskokinsu.

Namiji har namiji Ummi ta ayyana a ranta. Dogo ne don sai yau ta raina tsayin babanta. Jikinsa babu rama amma yadda yake karairaya shi yasa babu mai cewa jikin namiji ne da ya amsa sunansa. Fatar nan dabbara dabbara alamun an sha bleaching a shekarun baya. Yana buɗe baki kuwa haƙoran Makka ne na azurfa a sama har biyu suna maraba da baƙi.

“Kan uban can…ƊANDAUDU ne?”

Ta yiwa kanta tambayar a zuci ba don tana neman ƙarin bayani akan zahirin da idanuwanta su ke gani ba.

Abba kuwa da zafin nama ya fita shigo da kulolin abinci ita kuma gwanar ta ɗauko ƴar wayarta tamkar mai duba wani abu ta soma yi masa hoto a fakaice. Sautin wayar ma a silent ta saka don kada kowa ya gane. Siyama ce kaɗai ta kula kuma a take jikinta ya yi sanyi don ta sani babu ko tantama irin murmushin fuskar yayarta a lokacin na nufin abin da take yi ba na alkhairi bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *