Rayuwa da gibi hausa novels

Rayuwa da Gibi Chapter 2

This entry is part 2 of 3 in the series Rayuwa da gibi by Batul Mamman

RAYUWA DA GIƁI 2

Batul Mamman💖

Banda hotuna har sautin muryarsa Ummi ta ɗauka daidai inda yake kiran Hamdi ta kawo salad. Tana jin kiran ba amma saboda tsoron yanayin da za ta tarar da fuskar Ummi na farincikin samun lagonta sai ta kasa amsawa.

“Abba bari na kira ta.” Zee ta miƙe tsaye.

“Matso mu su da plates bari naje.”

Tashi ya yi ya tattare gefen jallabiyarsa ya riƙe da hannu ɗaya ya fita. Ya samu ta gama haɗa komai ta lulluɓe da clig (farar leda ta rufe abinci) kamar yadda ya koya mu su. Haɗin ya yi kyau gwanin ban sha’awa. Ya murmusa cikin jindaɗi yana ɗaukan tray ɗin. Ko ƙanƙani bai san wani abu girman kai ba musamman a tare da iyalinsa.

“Allah Ya yi albarka Hamdi. Mu je a ci abinci.”

Jingina tayi da sink ta juya masa baya kamar wani abu za ta wanke ta gyaɗa kai. Amsawa da baki zai iya ankarar dashi kukan dake barazanar ɓalle mata.

Shi kuwa kamar ya sani ya ajiye tray ɗin ya juyo da kafaɗunta.
“Hamdi?”

Ai suna haɗa ido sai kawai ta fashe da kuka. Zuciyarta tamkar ta fashe saboda baƙincikin da take ji. Wani abu mai masifar ɗaci ya dinga kai komo a cikin ƙirjinta. Duk gidan tana da yaƙinin tafi kowa takaicin fita tsatson bawan Allahn nan. Ranta yana ƙyamarsa. Albarkacin karatun addini yasa ta daina danganta shi da munanan kalmomi da fata a zuci kamar yadda take yi a baya. Asalin da mutane ke tutiya dashi Yaya ta janyo sun rasa ta da haifesu tare da tubabben Ɗandaudu. Mutumin da har yau idan aka yi rashin sa’ar gamuwa da tsofaffin abokansa sai kaji ana kiransa Simagade.

Hankalinsa tashi yayi da ganin hawayenta ya dinga tambayarta damuwarta. Da bata ce komai ba ya yi yunƙurin rungumeta domin rarrashi amma sai ta banƙare jiki ta ja baya. Dama can ta saba yi masa haka don shi tarairayar yara sai dai wani ya koya a wurinsa. Na yau ne da ya sanya masa shakku tunda ya san ta kan bari sai dai ta zare jiki da wuri. Kallon tuhuma ya bita da shi sai ta wayance ta ɗago hannun da ta yanke ta nuna masa.

“Ya Salam” ya ce da ƙaramar muryarsa “Sannu. Jeki falo ki jira ni.”

Tray ɗin salad ɗin ya ajiye ya fita cikin ruwan nan mai ƙarfi ya shiga ɗakinsa. Haƙƙin iyaye da a kullum shi ne jigon dake hanata fito masa da zahirin abin da take ji game da shi yasa ta ɗauki tray ɗin. Idonta da na Ummi su ka haɗu taga abin da take gudu muraran a tare da ita. Jikinta ya sake yin sanyi.

Sallamar Abba ta dawo da ita duniyar mutane. Ya zauna akan hannun kujera ya ce ta kawo hannunta. Ɗan akwati gare shi irin na gidan ƴan boko da ya adana magunguna da kayan taimakon gaggawa. Ya umarci Zee da zubawa kowa abinci shi kuma ya zauna bawa ƴarsa kulawa. Spirit ya dangwala a jikin auduga ya goge ciwon. Ga azabar zafi saboda ba ƙaramar yanka bace amma ko uhumm ta kasa cewa. Allah Ya sani zafin da take ji a zuciyarta yafi raɗaɗin ciwon. Saboda yadda ta ƙyamaci rayuwar mahaifinta bata ƙaunar gabaɗaya abokan sana’arsa. A son ranta namiji ko ruwan zafi aka ce ya dafa ya dawo ya ce ya ƙone saboda rashin iyawa. Namiji mai shiga kitchen ba zai taɓa yi mata kwarjini ba balle har taga ƙimarsa.

Dressing sosai ya yi mata ya kawo auduga ya ɗora ya manne ta da plaster. Gwani ne sosai ta wannan fannin wurin son ganin komai ya tafi daidai kamar wani bature. Ire iren abubuwan nan harda Abban da yasa su ke kiransa kamar ba talakawa ba duk bata so. Cikakken namiji bahaushe a wajenta ai Baba ake kiransa ba wani iyayin Abba ko Daddy ba.

Kowa sannu yake mata tana amsawa da ka. Da kuma wannan damar ta samu ta gudu ɗaki ta kwanta. Ba ita ta sake fitowa ba har sai da baƙin su ka tafi bayan Iyaa da su Ummi sun leƙo sun mata sallama.

*

“This is crazy Taj. Waye yake tattara duka ƙwansa ya sanya a kwando guda?”

Wata kamilalliyar dattijuwa sanye da doguwar rigar bacci da ƴar hula ta furta da takaici. Huci take cikin ɓacin rai tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune yana murmushi kamar abin da take faɗi da wani take a talabijin ba shi ba.

“Tajuddin!” Ta kira shi da ƙarfi da gargaɗi.

“Yes Ma” ya miƙe tsaye gami da sara mata. Ta sake tamke fuska.

Shi ma da alama ya gama shirin bacci ne don wandon jikinsa three quarter da singileti basu yi kama da kayan mai shirin fita ba.

“Ina wasa da kai ne?”

Ya girgiza kai.

Abin da ta san za ta yi ya dawo da hankalinsa gareta yadda take so ta aikata.

“Ko don kaga ba ni na haifeka ba? Shi yasa ban isa…”

“Amma gorin haihuwa kuma za ki min. Has it realy come to that?” Ya yi ƙwalƙwal da ido.

Jikin Amma a take ya yi sanyi. Taj ya yi wani ɗan banzan murmushi a bayan idonta sannan ya cigaba da magana.

“Idan baki aminta da abin da nake so ba ai ina ganin ba sai kin tuna min cewa ni ba ɗanki bane.”

“Ba haka nake nufi ba. Kai ma ka sani.”

Marairaice mata fuska ya yi sosai ta yadda ya san hankalinta zai tashi. Ya kuwa yi nasara don faɗan da ta ɗauko da gaske sai ya koma laluma.

“Taj bana son kayi abin da zai zama ganganci. Bayan duk irin abubuwan da ka jure a baya kada wannan step ɗin ya bada ƙofar da za a yi maka dariya.”

“Amma da Happiness mu ke komai. Mun yi survey na yadda malls su ke saurin dakushewa…”

“Durƙushewa dai ko?” Ta ci gyaransa ba tare da ta ɓoye takaicinta ba.

“Yeah, durƙushewa. So after the survey mun gano wasu reasons da suke kawo failure na business ɗin.”

Zama tayi bayan ta gama sauraronsa tayi ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa take guje masa wanda idan ba ɗan fito dasu tayi ba da wuya ya gane inda ta dosa.

“Shekararka nawa a ƙasar nan Taj?”

“10 years” ya amsa kai tsaye.

“And for those years you have been working non-stop kana tara kuɗi. Cikin ikon Allah kuma ka sami nasarar cin gasar nan ka sami maƙudan kuɗaɗe da sponsorship. Sai kawai na yarda da shawarar gina ƙaton mall irin wannan lokaci ɗaya da duka kuɗin? Kai baka hango ganganci a cikin yin haka ba?” Ta nuna zanen ƙayataccen ginin da yake kan laptop ɗinsa wanda nuna mata da ya yi ne ya kawo rigimar.

Marairaice fuska yayi “Tafiya ce ba kya so nayi ko Amma? Nayi miki alƙawarin zama har ki yi ritaya.”

“Bani da son kan da zan yi amfani da gudun zaman kaɗaici na daƙile maka rayuwa.”

Bakinta kawai ya kalla ya yi murmushi. Wata hausar idan ta ɗauko duk nacinsa sai ya tsinci kansa da rashin ganewa. Laptop ɗin ya rufe ya fuskanceta.

“Yanzu me kike so nayi?”

“Ka fara da restaurant ɗin mana. Idan kaga riba sai ayi planning for expansion.”

Tana gama magana ya sake buɗe laptop ɗin ya nuna mata sakamakon bincikensu. Tabbas akwai ƴan kasuwa da yawa a Kano. Tada ginin mall ba wani abu bane a wajensu. Kuma yana samun karɓuwa sosai. Ayi ta tururuwa ana zuwa. To amma fa bayan lokaci ƙanƙani yawanci da wuya ka sami motoci biyu sun ziyarci wurin. Wasu ma kayansu har ƙura su ke suna expiring saboda rashin zuwa. Da wannan su ka haɗa bayanai wurin yin abin da ya saɓawa wanda mutanen su ka saba dashi.

“Kinga na farko zamu yi shi a wurin da bai yi nisa da talaka da mai kuɗi ba.”

Bata ce komai ba. Ya ƙura mata ido sai ta gyaɗa kai don ya cigaba.

“Dole zamu dinga canjawa with current trend. Idan ban yi shi da girma ba chanjin zai dinga bani wahala. Maybe wani ya saye space ɗin kusa dani in rasa hanyar expansion. Sannan yin babba da zan iya bada hayar shops for diverse businesses zai taimaka. Idan mutum bai je don cin abinci ba maybe yaje wurin tailors, grocery shopping, wasan yara and the likes.”

Taƙaita masa bayanin tayi ta hanyar nuna masa ta gane. Yana son yi mall mai ɗauke da shaguna daban daban amma na brands da suka yi suna. A haka nasa ɓangaren wato wurin abinci ko bai yi kasuwa sosai ba zai dinga samun kuɗin haya daga waɗanda suke ciki. Burinsa talaka da maikuɗi kowa ya ɗanɗana ababen more rayuwa a ƙasarsa cikin jindaɗi. Goyon baya ta bashi amma ta yi masa hannunka mai sanda akan tsoron da take ji da kuma ƴan gyare gyare.

“Kamal jininka ne. Kuma na san irin shaƙuwar dake tsakaninku. Amma kada ka manta mutane irinmu da yawa living in diaspora (ƙasar waje) muna fuskantar matsala guda. Sai mu tura kuɗi gida domin wani aiki musamman gini. Idan mun koma mu tarar babu aikin babu kuɗi. Kuma family su nuna basu yarda muyi ƙarar wanda ya cucemu ba.”

Da rashin jindaɗi ya ce “Amma Happiness ne fa.”

“Shi ɗin fa. Ka tafi gida ayi komai a gabanka. Sayen fili, kafa foundation da dukkan wani abu da ya dace ka sani. Daga cikin abubuwan da su ke durƙusar da business harda rashin kulawar wanda ya samar da shi. An bar komai a hannun ma’aikata. Sai abu ya lalace a zo ana complain.”

Sai kuma ta bashi shawarar maimakon mall ita dai tafi son ya yi ƙaton restaurant tunda da girki ya yi fice. Idan an gina sai ya ware wurin wasan yara domin janyo mutane. A ɓangare guda ya yi wurin da masu gashin nama ko tsire zasu iya haya. Da kuma inda masu kayan fulawa kamar cake da su meatpie zasu yi nasu. Maimakon mall indai akwai wurin da aka keɓe domin yara to fa tabbas iyaye za su zo. A ƙarshe ta ce ya tabbatar wurin an yi shi yadda zai burge mai kuɗi sannan bai yiwa talaka tsadar zuwa ba.

Sosai yaji daɗin shawararta. Ya ce zai sa a sake yi masa wani zanen. Amma fa dole zai samarwa Happiness wurin da zai kafa nasa shagon. Addu’a tayi masa da fatan Allah Ya ɗorar da zumuncinsu shi da yayan nasa. Sai da su ka tabbatar sun daddale komai ya ce,

“Ni fa nafi son mu tafi tare.”

“Ya kamata kaje gida uwayenka su ganka haka nan.”

Tashi tayi ta juya masa baya amma bata tafi ba.

“Tajuddin ka sani cewa if your intension is not honourable (idan niyarka ba mai kyau bace). Ina nufin in kana son fara business ɗin nan ne kawai domin ka nunawa Yaya Hayatu cewa kayi nasara duk da yadda ya nuna ƙiyayyar sana’arka, to lallai Allah zai kunyataka. Domin Ya karrama darajar iyaye. Saɓanin fahimta da rashin goyon baya daga garesu ba dalili bane da zai sa mu nuna musu raini.”

“Korata fa ya yi” jijiyar kansa da idanu su ka firfito a lokacin da yake maganar.

“Shi kuma Allah Ya zaɓa maka a matsayin uban. Ya kuma rayata haƙoƙin junanku a kan ku. Idan ya take nasa kada ka kuskura kayi nufin binsa da ƙulli. Wallahi duk wahalarka ta shekarun nan sai ta tashi a banza.”

“Amma…”

“Ka tsaftace niyarka Taj. Everything will just fall into place. Goodnight”

Juyowa tayi ta sumbaci goshinsa sannan ta ɗauki wayarta ta shige ɗaki ta bar shi a tsaye yana kai gwauro da mari. Maganarta a kullum umarni ce a gareshi. Ta san yana yi mata biyayya gwargwadon iyawarsa. Me yasa bayan tsayin lokacin nan don zai tsaya da ƙafarsa za ta ce ya tafi gida?

Series Navigation<< Rayuwa da Gibi Chapter 1Rayuwa da Gibi Chapter 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *