Tafiyar Mu Hausa Novels

Tafiyar Mu Chapter 1

Bismillahir Rahmanir Rahim

  (1)

4:00pm

    Ruwa ne yake ke sauƙa daga sararin samaniya a garin Gombe, hakan yasa baza ka ji sautin komai ba sai ƙaran ruwan dake dukan rufin gidajen mutane dalilin kowa ya shige cikin gidansa. A wannan daddaɗan yanayin kuma a wata unguwa da ake kira Tumfure wasu ma’aurata ke zaune a wani babban falo akan kujera ɗaya, manne suke da juna a lulluɓe da wani ƙaramin bargo suna magana jefi-jefi dalilin kallon TV da suke yi bai bari sun samu hankalin junansu ba, ana gama film ɗin da suke kallo suka ja ajiyar zuciya a tare kana suka dubi juna suna murmushi.

 Mijin ne ya gyarawa matarsa zaman bargon ganin ƙafarta ɗaya ta fita daga ciki, bayan yayi na’am da aikinshi sai ya dubeta da tsantsar soyayyarta a kwayar idanunshi.

 “Riya kin koya mini kallo, and the worst part of it shine wai Korean Series nake zama ina kalla ni Hafiz.” Ya nuna kanshi da yatsa don emphasizing maganarshi.

  Wacce ya kira da Riyan ta kama yatsar tashi tayi saurin kaiwa bakinta ta ciza wanda hakan yasa Hafiz ya janye cikin jin zafin cizon yana dubawa yana kuma ƙoƙarin tsumewa amma yanayinshi ya fallasashi, wato murmushin da yake yi har yanzu bai bar fuskarshi ba.

 “Sorry.” Ta furta tana kama kunnenta ɗaya tana dariya ƙasa-ƙasa.

 “Kin ɗauki bashi kuma zan rama a lokacin da baki yi tsammani ba, I swear.” Ya ƙarisa maganan yana ɗanɗana yatsarshi a harshenshi alamar rantsuwa.

 Murmusawa tayi wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana gefen kumatunta ɗaya kuma ya lotsa.

 “You look childish idan kayi wannan abun. Amma Bee ba nace kayi haƙuri ba?” Ta zumburo baki cikin shagwaɓa wanda hakan yasa Hafiz ya girgiza kanshi.

 “Duk maganar da zaki faɗa ki faɗa amma ba zan haƙura ba sai na rama, shiyasa na rantse. Oya ki tashi mu yi sallah mu je gaishe da Muhammad, bana son har a sallameshi baki je ba.” Ya miƙe tsaye tare da miƙa mata hannunshi ɗaya ta kama kana ta tashi suka fuskanci juna bayan ta yaye bargon daga jikinta gaba ɗata ta ajiye a gefe.

 Ido ta tsura mishi tana kallon surarshi dake burgeta tun mafarin haɗuwarsu. Hafiz baƙi ne mai tsantsar kyau a idanunta, ba kuma irin wanda ake faɗa a littafin Hausa da za’a ce ya zarce tunanin mai tunani ba, a’a, shi Hafiz ɗinta daidai ne wanda bata son a ƙara mishi komai haka kuma bata son a rageshi da komai. A gurinta Hafiz shine perfect example na namijin duniya da kowacce mace zata yi farin cikin samu. Dalilin tsayinshi yafi nata yasa dole sai da tayi ɗagelgel ta tsaya kan yatsun ƙafafunta kafin ta samu damar kissing ɗin bakinshi mai faɗi game da duhu.

  Idanunshi ya lumshe yayi saurin zagayeta da hannayenshi wanda hakan yasa ta mannu da jikinshi har tana dafa ƙirjinshi a yayin da itama take rufe nata idanun. Sun kai minti ɗaya a haka suna exploring jikin juna kafin Hafiz ya sunkuceta duk da nauyinta yayi ɗaki da ita.

  A kan gado ya direta yana ƙoƙarin cire singlet ɗin jikinshi ta tashi zaune tare da mishi farii da ido tace,

 “Bee kace zamu je asibiti gaisuwa fa!”

  Hafiz da kashi casa’in na hankalinshi na ga abun da yake muradin yi ya hayo kan gadon yana cewa,

 “That could wait, but for now let’s make love.”

  Wani shu’umin murmushi tayi domin tun farko ƙudurinta kenan na hanasu fitan, babu wani dogon bayani ta biye mishi suka yada zango a sansanin ma’aurata.

 Awanni biyu da haka ruwan saman ya tsaya wanda hakan kuma yayi daidai da ƙarfe shida na yammacin asabar, Hafiz da matarshi ce suka fito daga cikin gidansu sun yi wanka sun shirya tana kulle ƙofa tana zumbura baki. Hankali kwance kuma cikin jindaɗin yanayin daminar Hafiz ya shiga cikin motarsa ta gani ta faɗa a gari da ke harabar gidan ya kunnata, maigadinsu na jin ƙarar motar ya fito daga ɗakinsa ya fara ƙoƙarin buɗe musu gate.

  Second biyar da haka itama buɗe gaban motar ta shiga tana kallon window fuskarta a kwaye. Briefly Hafiz ya dubeta a yayin da yake yin reverse zai fita daga gidan, murmushi yayi bai ce komai ba har suka fita daga gidan ya ɗagawa maigadin nasu hannu bayan ya aiko mishi da gaisuwa. Sai da suka fara tafiya ya ɗaura hannunshi ɗaya kan cinyarta yana mata tafiyan tsutsa yana kuma ƙara yin gaba wanda hakan ya fara canja mata yanayinta cikin ƙanƙanin lokaci.

  Ture hannun nashi tayi tana ƙara zumburo bakinta ita ala dole tayi fushi amma shi bai bar murmusawa ba, a ƙarshe ma mayar da hannunshi yayi yana mai cigaba da tsokanarta.

 “Allah ka bari bana so.”

 “Allah ka bari bana so.” Ya kwaikwayi muryarta yana dariya kaɗan har Adam apple ɗinshi yana sama yana ƙasa.

 “This is not funny.” Ta faɗa tana fuskantarshi a karo na farko tun shiganta cikin motar, harara ta dalla mishi wanda ya mayar mata da martanin alamar kiss har da hurawa a gareta.

  Kwafa tayi ta harɗe hannayenta saman ƙirjinta ta ƙara juyar da kanta ga window tana kallon gidajen da suke wucewa har suka hau titi tafiyarsu ta daidaita.

 “Seriously me yasa bakya son zuwa gaisheshi? Mutum ya kwanta bashi da lafiya har kwana uku kuma kina ƙawance da matarshi amma kice baza kije ki gaisheshi ba? Ranar da aka kwantar dashi nace ki kirashi kika ƙi, jiya nace muje in kaiki amma kika ce kanki na ciwo, yau kuma kika shammaceni na kwashi gara wai duk don kar mu je amma baki san na gane wayon naki ba and here we are, mun kashe arna kuma mun fito gaisuwan. Yanzu ki faɗa mini dalilinki na tsanarshi Juwairiyya, wallahi wani lokaci har kunya nake ji idan naga kina mishi wasu halayen, ke ko kunyar matarshi bakya yi?” Ya ƙarisa maganan fuskarshi babu yabo babu fallasa domin tun ba yau ba yake sane da rashin jituwan da ke tsakanin matarsa da babban abokinsa.

  First impression ɗin Muhammad a gurin Juwairiyya shi ya jawo duk wannan bashin gaban, faɗan da Hafiz ya yiwa Muhammad yasa yayi ƙoƙarin gyarawa amma ko da ya nuna sakin fuskarsa ga Juwairiyya wacce take cike da haushinshi sai ta basar ta nuna bata san yana yi ba.

  Hafiz ya so tankwara matarsa amma abun ya garara domin ta kafu ne a kan dalilanta na wasu halayyar Muhammad ɗin wanɗanda shi haka ya tashi da

su babu mai canjashi kamar yanda itama tana da wasu halayen da mutane basa so kuma ba zata canja ba.

 “He is always grumpy kullum mutum a tsume kamar kashi, ga ɗan banzan wulakanci ana gaisheshi ba zai amsawa mutum da murya babba ba sai kace shi mace ce. Na rasa yaya aka yi ka iya abokantaka da wannan mutumin for all these years. You are nothing like him, kana da sakin fuska shi kuma kullum a tsume yake, kana da son mutane amma shi wulakanta mutane yake yi wanda har matarshi bai bari ba. Kana da son taimako shi kuma idan ya ga mutum na neman taimako baya ko tsayawa zai yi wucewarsa.”

  Murmusawa kawai Hafiz yayi hankalinshi na kan titi ya

ce,

 “First of all, thanks for the compliments. Wasu abubuwan da kika faɗa a kanshi haka ne wasu kuma ba haka bane, yana da wasa da dariya da kuma son mutane wanda ya ga sun dace da shiga circle ɗinshi. Batun taimako kuma sau nawa zan faɗa miki ki daina judging mutum akan laifi ɗaya? Don kawai bai miki taimako sau ɗaya ba a rayuwarki bashi zai sa kice kullum haka yake ko kuma haka yake da kowa ba. I know he is different kuma ba kamar ni yake ba, but that’s how he is! And ba zai yiwu a canjashi ya zama yanda ake so ba don bakwa son halayenshi. And idan kika yi haƙuri sai kiga ya sake miki fuska ku zauna ana raha tare.”

 “Allah ya sauwaƙe. Kuma dama kai kullum cikin karesa kake yi kamar biyanka yake. Ni nafi tausayawa matarshi da Allah ya haɗata da Rock irinsa.” Faɗin Juwairiyya tana dunƙule hannunta guri guda don misalta yanda yake.

  Wannan karon dariya Hafiz yayi yana kaɗa kanshi yace,

 “Wallahi duk ranar da ya ji kina kiranshi da sunan Rock ɓatawarku zata fi na yanzu.”

  Itama Juwairiyya dariya tayi a karon farko tana hasashen yanda lukutar fuskar Muhammad zata turnuƙe idan ya ji. Ai kuwa nan take ta ayyana a ranta watarana sai ta faɗa ɗin yaji, domin idan hakan zai ɓata mishi rai ita daɗi zata ji. Tuni ta manta da wani ɓacin rai na tilastata da Hafiz yayi kan zuwa gaisuwan suka cigaba da hiransu gwanin ban sha’awa har suka tsaya a bakin hanya suka sayi fruits suka wuce asibitin FTH (Federal teaching hospital).

   Hafiz ne ya musu jagora hannunshi ɗauke da ledan da suka sayi fruits ɗin yayin da ɗayan hannunsa yake riƙe da na Juwairiyya wacce ke fatan Allah yasa an sallami Muhammad ba sai sun haɗu dashi ba. Male ward suka shiga daga nan kuma suka kutsa kai cikin side room B inda suka samu Salima matar Muhammad tana tattare kayansu tana sakawa a wani babban leda, shi kuma mara lafiyan yana kwance akan gado ya kuma ɗaura hannunshi daya a kanshi alamar yana tunani.

  Shigowar Hafiz da Juwairiyya yasa Salima ta dakata daga tattaren kana ta faɗaɗa fara’arta tana musu barka da zuwa.

 “Ya jikin naka?” Faɗin Hafiz yana isa bakin gadon ya miƙawa abokin nashi hannu suka yi musabaha bayan ya tashi ya zauna.

 “Da sauƙi sun sallamemu, yanzu tafiya gida zamu yi.” Muhammad ya bashi amsa yana duban Salima wacce ta tsaya magana da Juwairiyya ta daina aikin da take yi.

 “To Allah ya ƙara sauƙi. Kace da mun ƙara minti kaɗan baza mu zo mu sameku ba.”

 “Kai ma rigima ce tasa ka dawo, ɗazu da safe kafin ka tafi office ka zo mun gaisa. Da mun tafi kam, don wannan mai nawar ta kasa gama kimtsa kayan ne amma da tuni mun isa gida.” Yayi maganar da ƙarfi yanda Salima zata ji yana kuma aika mata wani mugun kallo.

  Ai kuwa tana juyowa ta haɗa idanu dashi ta bar gefen Juwairiyya ta koma bakin aikinta ba tare da ta ƙara cewa komai ba. A hankali Hafiz ya take ƙafar Juwairiyya wacce tun shigowarsu ta samu plastic chair ta zauna bata ko kalli in da Muhammad ɗin yake ba, ɗago kanta tayi suka haɗa ido yayi mata nuni da mara lafiyan da bakinshi. Ɓata fuska tayi sannan ta dubi sashen da mara lafiyan yake tace,

 “Ya jikin?”

  Bai amsa ba illa kawar da kanshi da yayi bayan itama ya aika mata mummunan kallon irin wanda ya yiwa matarsa ɗazu. Kwafa Juwairiyya tayi a ranta tana jin haushin wulakantata da yake yi tun ba yau ba, a ranta kuma zaginshi take yi tare da Hafiz ɗin da ya matsa mata tilas sai ta zo nan.

 “Ana gaisheka.” Faɗin Hafiz ga Muhammad ganin bashi da niyyar amsa gaisuwar tata.

 “A ina?” Yayi tambayar kamar da gaske bai ji ba.

  Hafiz yayi ajiyar zuciya cikin gajiyawa da halinsu kana ya miƙawa Salima fruits ɗin yana cewa,

 “You know what? Ya wuce. Salima ga fruits and idan kin gama tattaren ku samemu a waje mu mayar da ku gida. Kai kuma ka tashi mu fita kasha iska kafin su fito.”

 “Hafiz na kira Abbati zai taho da motata nasan yana hanya ko ma ya iso.” Muhammad ya bashi amsa yana sauƙowa daga kan gadon sai ƙara take yi dalilin nauyin shi.

  Juwairiyya ce tayi siririyar tsaki tana ayyanawa a ranta cewa lukutancinshi kaɗai ma ta isa tasa cututtuka su dameshi tun da ba’a iya wata biyu sai ya kwanta rashin lafiya. Suna fita Salima ta dakata da abun da take yi tana murmushi tace,

 “Sorry fa ƙawata, yau laifina ya shafeki gashi ko gaisuwarki ba’a amsa ba.”

 Tsaki Juwairiyya ta ja wannan karon ba tare da ta ɓoye sautinsa ba ta dubi Salima tace,

 “Kina haƙuri da wannan mutumin, amma gaskiya ko sau ɗaya ne ya kamata ki nuna mishi bakya tsoronshi kuma ke mutum ce. He should stop ordering you around da kakkausar murya cikin bainar jama’a saboda hakan bashi da daɗi kuma girmanki yake zubarwa.”

  Salima tana jin Juwairiyya ta fara faɗan data saba muddin tayi witnessing Muhammad yana treating ɗinta irin haka sai kawai taci gaba da aikinta wanda dama ta kusa gamawa.

 “Hmm, ba zaki gane bane. Mu tafi kar suyi ta jiran mu bamu fito ba mu ƙara yin wani laifin.” Ta faɗi hakan tana ɗaukar ƙatuwar ledan tare da wani mini trolley wanda Juwairiyya ta tabbatar suturun Muhammad ne a ciki.

 “Ai komin rashin lafiyarsa bai kamata ya bar miki duk wannan kayan ki ɗauka ba, he had to atleast take the mini trolley tunda janshi zai yi yana da taya, ke kuma sai ki ɗauki ledan.” Faɗin Juwairiyya tana tuna yanda Hafiz baya barin ta ɗauki komai idan sun je shopping ko kuma zasu fito daga gida. Cewa yake yi zai yi spoiling ɗinta saboda ita ɗin abar tattalawarshi ce.

 Salima ta kalli kayan hannunta cikin confusion don ita bata ga laifin hakan ba, ai shine mara lafiya bai kamata ma tun farko ta barshi ya ɗauki kaya ba, da haka suka fita daga ɗakin tana cewa,

 “Ni kuma dai bana ganin laifinshu, don sau da dama in ya mini faɗa to laifi nayi, kawai don Hafiz ya sakaltaki ne yana miki duk abun da kike so shiyasa kike ganin kamar ni a takure nake. But rayuwarku tana burgeni saboda yana nuna miki so da kulawa a duk inda kuke baya gajiyawa, ni kuma gogan nawa soyayyar ce bai iya ba kuma na kasa koya mishi.”

 “Alhamdulillah Hafiz is good to me, but I really hope one day kema a nuna miki so kamar yanda yake nuna mini, wallahi daga ranar zaki gane zaman da kike yi da Muhammad akwai takura da kwara a ciki. Allah kuma ya ƙara miki haƙuri akan wanda kike yi shi kuma ya shiryeshi. Ni na manta ne ma nayi magana, don na lura daga ke har Hafiz bakwa son laifinsa ko kaɗan sannan kullum cikin karesa kuke kamar wanda ya muku asiri.” Ta ƙarisa maganan cikin raha ganin Salima ta fara shiga damuwa akan maganar da take yi wanda har ga Allah ba wai kusheshi take yi don ta ji zafi ba, a’a ita ta ƙi jinin ta ga ana cin zarafin mutum ne kuma yana shiru ya kasa taɓuka komai. Halinta na rashin ɗaukan wulaƙancin mutane yasa wasu suke cewa tana da rashin kunya da kuma masifa.

  Da haka ta canja musu hirar sannan ta karɓi ledan hannun Saliman suka fita daga building ɗin zuwa waje inda Hafiz yayi parking. Wayam babu su babu alamarsu sai wasu tsiraran motoci da kuma Keke Napeps da suke ficewa da mutane daga asibitin tunda lokacin visiting patients ɗin ya wuce. Juwairiyya ce ta ɗauko wayarta ta danna kiran Hafiz tana cewa,

 “To ina suka yi?”

 Hafiz yana ɗaukan wayar ya fara magana,”Riya dama yanzu nake da niyyar kiranki wani abu ne ya taso mana cikin gaggawa muka tafi amma ga Abbati yana zuwa zai mayar da ku gida. Ina fatan hakan ya miki?” Yayi maganan cikin sanyin murya kamar yaron da yayi laifi yana neman tuba.

 Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Juwairiyya tana tunanin ta yaya zata iya fushi mai tsawo da mutum kamar Hafiz? Mutumin da yake treating ɗinta kamar ita ce kaɗai mace a duniya kuma baya son fushinta?

 “Babu komai Bee, zamu ƙarisa gidan Saliman idan ka gama abun da kake yi sai ka biyo ka ɗaukeni mu koma gida.”

 “Good girl. Sai na dawo.”

 Kafin ya kashe wayar tayi saurin dakatar dashi da cewa,”Bee, ya naji muryarka wani iri, lafiya kam?”

 Tana saurara yayi ajiyar zuciya kana yayi murmushi mai sauti ya ce,

 “Har na daina mamakin yanda kike gane canji a tattare dani daga sauraran muryata kaɗai. I’m fine sai na dawo zamu yi magana.”

 Bata musa mishi lallai sai ta ji me yake damunshi ba saboda ta lura kamar ma driving yake yi, sannan ta san ba zai ta6a ɓoye mata damuwarshi ba kuma kamar yanda yayi alƙawari, yana dawowa gida zai faɗa mata kuma da shi da ita zasu zauna su magance matsalarsu ba tare da kowa ya sani ba. Sallama suka yi ta juyo tana kallon Salima wacce ke waya har tana rage tsayinta idan tana magana, hakan yasa Juwairiyya ta gane cewa da Muhammad ne domin shi kaɗai take bawa wannan girman kamar zata nitse cikin ƙasa.

 Salima tana gama wayar ta mayar da ita cikin jakarta ta dubi Juwairiyya da ke waige-waigen ta ina zata hango mai ɗaukan nasu domin zaman asibitin har ya fara gundararta.

 “Zamu ƙara minti kaɗan domin Muhammad ya aikeshi kasuwa zai sayo karkashi zan mishi tuwo.” Faɗin Salima tana gyara tsayuwarta.

Wani takaici Juwairiyya ta ji domin ta lura Muhammad sam baya tausayin Salima, tunda ya kwanta rashin lafiya tare dashi take kwana kuma a hakan da safe zata koma gida ta mishi karyawa ta bayar a aiko mishi kafin nan ƙaninshi zai zauna dashi, da azahar zata dawo da abincin rana har dana dare wanda wai shi gogan baya cin abinci iri ɗaya sau biyu a rana. To idan ta zo tun azahar ɗin shine baza ta koma ba sai washe gari da safe, kuma ko ta koma gidan ba hutawa zata yi ba abinci zata dafa ta ƙara dawowa dashi.

  To duk wannan ɗawainiyar da tayi mishi meyasa yau ba zai iya mata haƙuri ya barta ta huta ba? Anya mutumin nan yana da tausayi kuwa? Har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta rufe domin yawan maganar ma bashi da daɗi, domin ita Saliman zata ga kamar faɗa take son haɗasu, sannan ita ta ganshi tace tana so kuma take son zama dashi a haka ba tare da ta yi ƙoƙarin canja musu Tafiyar tasu ba. Sannan Juwairiyyan ta sani idan ta yawaita magana da kusheshi wataƙila Saliman zata ji haushinta saboda har ga Allah ita ma baza ta so taji wani yana aibata Hafiz ɗinta ba.

 Wannan karon Salima ce ta canja musu hiran ta kawo musu hiran cikinta da ya shiga wata na uku amma tana nan garau babu rashin lafiya babu laulayi kamar ba ciki ne da ita ba. Ai kuwa ta taɓowa Juwairiyya gurin da yake mata ƙaiƙayi domin tana son duk wata hira da za’a sako maganar yara a ciki saboda tana son haihuwa, gashi yanzu shekarar aurensu ɗaya kenan da Hafiz amma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Salima kuma sun shiga wata na shida kenan amma gata da ciki har na wata uku, ko dai ita juya ce bata haihuwa? Tana yawan yiwa kanta wannan tambayar wanda har ta kai bata ɓoyewa Hafiz damuwarta ba, shi kuma as usual kwantar mata da hankali yayi har yana tsokanarta da cewa dama bai gama moreta ba ta ƙara wasu watannin kafin ta ɗauki ciki. Ire-Iren wannan barkwancin Hafiz ɗin yasa ta rage nuna mishi damuwarta tana kuma addu’ar Allah yasa ta samu ciki ta riƙe ƴaƴanta a hannunta itama.

  Minti goma da haka Abbati ƙanin Muhammad yayi parking a gefensu ya fito ya ƙarɓi abun hannunsu ya shigar cikin booth kana ya shiga motar suka wuce gidan Saliman kamar yanda suka tsara.

  Wani gida madaidaici da ke unguwar Jekadafari  suka shiga wanda nan ne gidan Salima da Muhammad, Abbati ne ya fita ya buɗe musu gate kana ya dawo cikin motar ya shigar da su harabar gidan mai ɗaukan mota ɗaya. Suna tsayawa wata budurwa mai taya Salima aiki mai suna Nanayo ta fito daga cikin gidan ta musu sannu da zuwa tare da karɓan kayan abincin daga hannun Abbati ta shige dasu ciki bayan Salima ta umurceta da ta yanka karkashin ta kuma ɗaura mata ruwan tuwo. Sallama tare da godiya suka yiwa Abbati wanda ya ƙara fita da motar domin kaiwa mai ita.

 A falon Salima daya gaji da haɗuwa suka sauƙa wanda yake cikin tsafta ga ƙamshi sai tashi yake yi a ciki, tuni Juwairiyya ta cire gyalenta ta ajiye a gefe tana sauƙe ajiyar zuciya irin ta gajiya.

 “Wash Allah na.”

 “Oh mutum sai sakalci. Tsakaninki da Allah aikin me kika yi yau da har kike cewa kin gaji?” Faɗin Salima tana ciro kayan cikin ledan tana ware wanda zata shigar kitchen da kuma wanda zata kai ɗakinsu a gefe.

  Dariya Juwairiyya ta yi. “Baza ki gane ba. Amma in kina da miji kamar Hafiz kullum a gajiye zaki dinga jinki.”

  Shewa Salima tayi har da tafa cinya tana dariya. “Da alama ku bakwa gajiya da wannan harkan. Mu sai mu yi sati biyu ma wallahi wani abun bai shiga tsakaninmu ba musamman in ya kwanta rashin lafiyar nan. Wani lokaci ina so amma sai inyi shiru gudun kar in 6ata mishi rai idan na nema.”

  Fara’ar da ke fuskar Juwairiyya ce ta ɗauke domin ta tsani ta ga ana kwara ko cutar mutum alhali babu yanda ta iya. Ta lura duk hiran da zasu yi da Salima matuƙar maganan Muhammad ta shigo ciki sai ranta ya ɓaci saboda halinsa kaff da yake gwadawa matarsa babu na ɗauka. Tana kuma jin tausayin Saliman domin ta lura har da sonshi yake ɗawainiya da ita, wanda har ta kai bata iya ganin laifinsa.

 “Kin san kowa da halittarsa, wataƙila shi ba mai son yawan sex bane.” Cewar Juwairiyyah wanda zata iya rantsewa wannan shine karo na farko data taɓa kare Muhammad bata kusheshi ba idan an gwada mata halinsa.

 To yaya zata yi? Yawan kusheshi a gaban matarsa zai iya jawo wani matsala tsakaninsu don haka tun suna asibiti ta yiwa kanta alƙawarin daina hakan tunda ita wacce take cikin rayuwar bai dameta ba, kuma a hakan suke zaman auren ba tare data nuna mishi bata son hakan ba.

 Murmushi Salima tayi tana cigaba da ware kayan. “Shima haka ya faɗa, yace inyi haƙuri da yanda na sameshi ba yin kanshi bane.”

 “Ohh dama har wani haƙuri yake baki? Wallahi na ɗauka bai taɓa furta kalmar haƙuri ga kowa ba tun da yake. Ikon Allah, ashe idan kuka keɓance soyayya yake nuna miki mu kuma kin bar mu da jin tausayin ana takura miki.” Juwairiyya ta ƙarisa maganan cikin mamaki tana murmusawa don har wani relief ta ji a zuciyarta.

 “Shiyasa kika ga ba komai ya mini nake ɓata rai ba, sometimes ya kan nuna mini kulawa sannan babu abun dana nema na rasa a gidan nan, shi dai ki barshi da saurin hawa idan aka yi abunda baya so.”

 “Dama tsakanin mata da miji sai Allah, wanda kuma ya shiga tsakaninsu shi zai ji kunya.” Juwairiyya ta furta ba tare data daina murmushin ba.

 Suna hiransu har Salima ta gama aikin nata ta sunkuci trolley ɗin tare da sauran tarkacen ta nufi ɗakin Muhammad sannan ta fito suka kwashi na kaiwa kitchen suka yada zango a can suna hira Juwairiyya na tayata girkin. Sune basu gama tuwon ba sai da aka kira sallan isha suka yi sallah sannan suka ci tuwon, bayan sun gama suka fara kallo Juwairiyya na recommending wa Salima wasu zafafan Korean series akan ta nema zata ji daɗin su.

  Takwas da rabi suka ji ƙarar buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo wanda suka ayyana a ransu mazajensu ne suka dawo, tun kafin a kashe motar wayar Salima tayi ƙara tayi saurin ɗauka tare da yin ƙasa da murya ta fara gaishe da wanda yayi kiran nata.

 “Ya jikin naka? Da fatan baka jin komai?”

 “Ki zo ki haɗa mini ruwan wanka.” Ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar tata ba, kafin ta amsa ma ya kashe wayar.

  Juwairiyya ma wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka cikin ɗoki da kuma murmushi a fuskarta tace,

 “Bee.”

 “Awanni kaɗan da rabuwa da ke amma nayi kewarki. Gani a waje ki fito mu tafi gida.”

 Lumshe idanunta tayi cike da annushuwan yanda yake nuna mata ƙauna a fili babu 6oye-6oye.

 “I missed you too. Bari in fito yanzu.” Da haka ta kashe wayar ta dubi Salima dake jiranta ta gama wayar don ta mata magana.

 “Ba dai tafiya zaku yi ba?” Ta tambaya tana riƙe ƙugunta wanda yin hakan ya fallasa tumbi da kuma manyan hips ɗinta, da yake Salima irin matan nan ne chubby, farare kuma kyawawa masu jikin hutu don iyayenta suna da wadata, sai gashi kuma data tashi aure Allah Ya haɗata da ɗan lukuti irinta duk da cewa bata kaishi ƙiba da tumbi ba.

 “Wallahi tafiyan ne. Allah ya bashi lafiya sai kuma gani na gaba.” Faɗin Juwairiyya tana yafa gyalenta kana ta ɗauki wayarta.

“Ina son miki rakiya har waje amma Muhammad ya sakani aiki kar yayi ta jirana ban mishi ba. Kiyi haƙuri don Allah.” Ta ƙarisa maganar tana marairaice fuska.

 “Wallahi kar ki damu babu komai I understand. Sai anjima kar shima ya gaji da jirana.”

 Da haka suka yi sallama Juwairiyya ta fita daga gidan ta samu Hafiz a waje a cikin motarshi. Tana shiga ya jawota jikinshi ya fara kissing ɗinta tana dariya tana kaucewa.

 “Laaa me haka? Irin wannan ambush kamar kayi shekara baka ganni ba.” Ta sa hannu ta riƙe kanshi da yake kwantarwa kan ƙirjinta.

 “Ina gwada miki irin kalar kewarki da nayi ne. Ya kike?” Ya zuba mata mayun idanunshi da suka canja kala dalilin abun da ya faru tsakanin su, duk da cewa cikin motar akwai duhu kaɗan bai hana Juwairiyya gano fitina a kwayar idanunshi ba.

 “Lafiya kalau.” Kawai ta iya cewa dashi domin itama tuni ya canja mata yanayi saboda ta zama rainon Hafiz don ya mayar da ita kalarsa tuntuni.

 “Mu tafi?” Ya tambayeta cikin sarƙewar murya.

 “Yes Bee.”

 Nan take ya tayar da motar suka fita daga unguwar suka fara tafiya akan babban titi zuwa unguwarsu.

 “Zan mana take away me zaki ci?” Ya faɗa yana ƙoƙarin karya kwana zai shiga wani restaurant da ke nan bakin hanya.

 “A koshe nake domin naci tuwo a can, da yake miyar karkashi suka yi shiyasa ban ɗauko maka ba saboda baka ci.”

 Gyaɗa kai Hafiz yayi kana yayi parking ya fita zuwa cikin restaurant ɗin Juwairiyya ta bishi da ido cike da wani zazzafan sonshi dake fisgarta. Tafiyarshi ma kaɗai abun kallo ne domin bayan kyan sura da yake dashi, Hafiz ya san wankan da ya dace da shi.

  Tana zaune a cikin motar tana kwatanta irin son da take mishi ya dawo ya miƙa mata ledojin hannunsa ta kar6a ta ajiyesu a seat ɗin baya.

 “Na saya miki ice cream ki sha yanzu kar ya narke.” Ya tayar da motar ya fita daga harabar restaurant ɗin, ita kuma cikin murna ta ɗauko ice cream ɗin tare da mishi godiya ta fara sha suna hira har suka iso gida.

 Yana gama cin abincin ya jawota jikinshi suka fara hira har lokacin baccinsu yayi suka kwanta. Kanta dake kan damatsanshi ta ɗaga kaɗan tana duban fuskarshi tace,

 “Bee menene ya faru da kai ɗazu? Kace idan ka dawo zamu yi magana.”

  “Juwairiyya akwai maganar da nake so mu yi da ke amma bana son ki d’aukeshi da zafi ko kuma ki mini mummunan fassara don girman Allah. Kina ji na?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *