Tafiyar Mu Hausa Novels

Tafiyar Mu Chapter 2

This entry is part 2 of 6 in the series TAFIYAR MU by Suwaiba Muhammad (Mum Fateey)

2

(2)

Hafiz Isma’il shine ɗa na huɗu a cikin mahaifiyarsa wacce ta kasance mace tilo wajen babanshi, sai ƙannenshi uku mata da duk sun yi aure suna ɗakin mazajensu, yayunshi uku kuma duk maza ne kowanne da iyalinsa.

  Hafiz mutum ne mai ilimin addini da kuma boko sannan yana da kyawawan halayen da yasa mutane su ke son hulɗa dashi. Yana gama NYSC ya samu aikin gwamnati inda ake biyanshi salary mai tsoka wanda cikin ikon Allah ya tara ya sayi fili yayunshi suka dafa mishi yayi gini mai kyau na gani na faɗa.

  Hafiz ya haɗu da Juwairiyya Ahmad ne wata rana da ya raka childhood friend ɗinshi Muhammad wani unguwa. Yana zaune shi kaɗai a cikin mota yana jin waƙa yana kuma danna wayarsa ya ɗago fuskarsa don ya gani ko Muhammad ya fito daga gidan da ya shiga amma bai ganshi ba, juya kanshi da zai yi gefen hagu ya hango wasu ƴan mata huɗu sun fito daga wani gida suna hira suna dariya, hankalinsa ne ya koma kan wata budurwa chocolate colored wacce ita ce ta ƙarshen fitowa daga gidan tana gyara hijabinta tana cewa ƙawayen nata su jirata ta musu rakiya zuwa bakin titi. Hakan ya tabbatar mishi cewa nan ne gidansu, kenan ziyara suka kawo mata.

  Har suka zo suka wuceshi idanunshi na kan oval face ɗinta wanda yake cike da annuri ta kasa daina murmushi. Sai da suka ɓace mishi da gani ya rufe idanunshi yana hasko fuskarta mai ɗauke da manyan idanu irin nashi da kuma hanci daidai fuskarta, abun da ya fi ɗauke mishi hankali shi ne lips ɗinta da suke full ta shafa musu lip gloss sai sheƙi suke yi har yana jin ina ma ita ɗin tashi ce.

Yana zaune a cikin motar ta dawo ita ɗaya ta shige cikin gidan tare da kulle ƙofar ba tare da ta gane cewa ana kallonta ba.

  Shiganta ke da wuya Muhammad ya fito ya shiga motar suka kama hanyar gida yana yiwa Hafiz hira wanda shi hankalinshi na kan yarinyar daya gani wanda zai iya rantsewa ya kamu da sonta ne at first sight.

 “Lafiyanka kam? Ina ta magana ka yi shiru ka shareni.” Faɗin Muhammad cikin hasala.

 “Wata yarinya na gani ta burgeni matuƙa kuma wallahi in har na bincika na ji tana da hali mai kyau zan aureta.”

 “Su kuma ƴan matan da kake waya kana chat dasu fa?” Ya harareshi ta gefen ido.

  Dariya Hafiz yayi ya sosa kai ya ce,

 “Duk cikin su babu matar aure sai budurwar soyayya. Zamu yi soyayya kam tsantsa amma ni nasan ba aurensu zan yi ba saboda bana son mace mara kamun kai da rashin aji. Amma ka ga yarinyar nan dana gani? Ina kallon fuskarta na gane ba shashasha bace she is a wife material. Yanzu dai kai zaka shige mini gaba tun da naga alamar ka san makwabtan gidansu yarinyar ka tambaya mini halinta.”

 “Babu wanda zan je in tambaya wani abu, kuma gidan da kaga na shiga gidan wani distant relative ɗin Babanmu ne ya aikeni gurinsa nima ban ta6a zuwa ba sai yau.”

 “Don Allah kar mu yi haka da kai mana.” Hafiz yayi saurin faɗa cikin kwayewar fuska yana kallon Muhammad.

“Mallam ka kalli gabanka kar ka juyemu a cikin kwalbati. Zan yi tunani a kai.”

  Washe gari da yamma sakaliya Hafiz da abokin nashi suka isa ƙofar gidan su Juwairiyya suka aika yaro yayi kiranta bayan Muhammad ya faɗa mishi sunanta a binciken da yayi na dole.

  Tana fitowa ta samu Hafiz a tsaye suka gaisa ya gabatar da kanshi tare da faɗa mata dalilin zuwanshi babu ɓata lokaci domin shi aurenta yake son yi. Bayan ta ja mishi aji akan cewa bata tsayawa da samari sannan ya roƙeta da girman Allah kan ta bashi number wayarta kafin ya gabatar da kanshi gurin iyayenta. Kamar bata so ta bashi numbern, a nan yake faɗa mata tare da abokinshi yake wanda suna hangoshi a cikin mota a gaba dasu amma ko sau ɗaya bai waiwaya ba. Hafiz ne ya kwala mishi kira Muhammad ya juyo rai a 6ace kamar an mishi dole.

 “Ka zo ku gaisa mana.” Hafiz ya faɗa yana roƙanshi ta cikin ido don kar ya kwafsa mishi.

 “No I’m good.” Faɗin Muhammad flatly kana ya juyar da kanshi.

  Hafiz haushi da kuma kunya ce ta cikasa wanda bai ƙara minti biyu ba Juwairiyya ta mishi sallama ta shige gida akan cewa mamanta zata mata faɗa idan ta ga ta jima.

  A mota Hafiz yayiwa abokin nashi tatas kan cewa ya wulaƙantashi shi dai Muhammad yana shiru bai ce komai ba, ƙarshe da yaga Hafiz ya fusata da gaske sai ya bashi haƙuri yace zai gaisheta idan suka sake haɗuwa.

   Abun da basu sani ba shine ita Juwairiyya tun a lokacin ta ji ta tsani Muhammad domin bata son duk wani abu da ya danganci wulaƙanta mutum. Daga ganin suturun jikinsu da kuma motar da suka zo dashi ta gane suna da wadata in dai ba arowa suka yi ba, amma hakan bashi zai sa abokinsa ya wulaƙantata ba don bata kai su kuɗi ba. Duk da cewa Hafiz ya burgeta amma halin abokinsa yasa ta ji baza ta iya kulashi ba, hakan yasa da dare da yayi ta kiranta ta ƙi ɗauka har ya gaji ya daina.

  Washe gari da safe ta fito daga gidansu zata tafi islamiyya, da yake ta gama secondary school wata uku da suka wuce kuma mamanta ta hanata cigaba da karatu wai aure zata mata ta samu Hafiz rakuɓe a katangar gidansu da alama ita yake jira da fito. Yana ganinta ya sha gabanta fuskarshi abun tausayi da alama ko wanka bai yi ba ya fito.

 “Laifi ne na miki kika ƙi ɗaukan wayata?”

  Tsabar mamaki kasa magana ta yi domin wannan abun da yayi a littafin Hausa ne kaɗai ta ji ana yi wato saurayi ya kasa runtsawa har sai ya shawo hankalin buduwarsa.

 “Ko dai ban miki bane tun farko sai ki faɗa mini ba wai ki bani numbernki sannan ki ƙi kulani ba.”

  Ganin ana wucewa ana kallonsu ga kuma uwa uba hakan da yayi na nuna damuwarsa a kanta yayi matuƙar burgeta, domin ita tana son a nuna mata kulawa da soyayya don haka ta buɗi baki ta ce,

 “Na yi bacci da wuri ne. Sorry.”

  Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya dafa ƙirjinshi saitin zuciyarshi ya ce,

 “Har na ji sanyi a zuciyata, we cool?”

 Murmushi ta yi don ta lura yana yawan saka turanci a maganarsa wanda ba forcing ɗinshi yake yi ba irin ta gane ya iya turanci, a’a ta tabbatar haka ya saba domin ko sau ɗaya bata ta6a kamashi da murɗewar harshe grammatical error ba.

 “Yeah, we are cool. Bye.” Ta faɗa tana ratsewa ta gefeshi don kar ya sakata latti a sakata wanke banɗaki.

  Bata yi taku biyar ba ta ji wayarta na ƙara ta zaro daga cikin jakarta domin tasan babu mai kiranta a wannan lokacin sai mahaifiyarta hala tayi mantuwa ne a gida zata kai mata asibiti inda take aiki, amma ganin numbern Hafiz wanda bata yi saving ba yasa ta juyo ta dubeshi yana tsaye a inda ta barshi da waya a kunnenshi alamar shi ɗin ne dai ya kirata.

  Murmushi yayi ganin ta tsaya tana kallonshi kana ya mata nuni da wayar hannunta wanda hakan yasa ta farfaɗo ta amsa wayar gami da karawa a kunnenta, muryarshi ta fara ji yana cewa,

 “I know ko nace ki zo ki shiga mota in kaiki school ɗin baza ki yarda ba saboda it seems your parents raised you right, so Allah ya kiyaye hanya Ya kuma baki ilimi mai albarka. Take care.”

Yana gama faɗin hakan ya kashe wayarsa kana ya shige motarsa ya tafi ya barta a gurin zuciyarta na bugawa da ƙarfi ba don tsoronshi ba sai don a take a wannan lokacin ya sace zuciyarta ya tafi da ita.

  A ranar Hafiz ya zo da yamma bayan ta amince mishi amma bai zo tare da Muhammad ba, gefe guda kuma yasa an mishi binciken halayenta aka kuma sanar mishi cewa tana da hankali da nitsuwa kamar yanda yayi tsammani. Bai yi wasa ba ya turo iyayensa gurin dangin Babanta aka bashi izinin hira har aka musu baiko.

  Tun rana ta farko da Hafiz yazo da Muhammad bai ƙara zuwa dashi ba har aka saka ranar aurensa da Juwairiyya wacce ta kaucewa duk samarinta tace shi zata aura. Sai ana ribibin auren nasu ne suka haɗu wanda shi Muhammad ɗin ne ya ɗaga mata gaisuwa amma tayi kamar bata ji shi ba.

  Da yake tana yawan jin labarin shi gurin Hafiz yasa ta gane shi ɗin abokinshi ne na ƙut da ƙut, sannan ta fahimci yana da girman kai amma ita neman abu ta yi a gurinshi da zai wulaƙantata? Har aka yi bikin tsakaninta da Muhammad babu jituwa, sannan ko bayan auren bai je gidansu ba sai da suka yi wata biyu wanda ta lura Hafiz ne ya matsa mishi suka zo nan ma bai ci komai a gidan ba ya tafi.

  Juwairiyya Ahmad ita kuma ƴa ce ta farko a gurin mahaifiyarta sai sauran kannenta mata biyu da namiji ɗaya. Babansu ya rasu tun suna yara hakan yasa mahaifiyarsu ta zauna a cikin gidan mijin nata tare da ƴaƴanta ba tare da ta sake aure ba, kuma ta ɗauko mahaifiyarta tsohuwa da take ƙauye suna zama tare da yake ita ma mijin nata ya rasu. Cin su da shan su duk a kan mahaifiyarsu yake wacce take Nurse a wani Maternity wanda jajircewarta da kuma jimawanta tana aiki yasa aka bata matsayin Matron na asibitin gaba ɗaya. Hakan yasa ta samu ƙarin albashi ta kuma cigaba da kula da ƴayanta har ta aurar da Juwairiyya.

  Wata shida da aurensu suna zaman lafiya da nunawa juna so Muhammad ya tayar da maganar auren da zai yi. Ko da Hafiz ya nunawa Juwairiyya hoton matar da Muhammad ɗin zai aura sai ta buɗi baki ta ce,

 “Dama shi lukuti ai sai lukuta ce zata iya dashi. Wannan idan aka aura mishi yarinya ƙarama rana ɗaya zai karya musu ƴa da nauyinsa.”

 “Riya baki da kunya fa, me ya kai tunaninki har can daga nuna hoto kawai?” Faɗin Hafiz yana harararta da gaske.

 “Sorry na taɓo rabin ranka.” Ta mishi gwalo kana ta tashi ta shige kitchen don ɗaura musu abincin dare.

 Bayan auren Muhammad da matarshi Salima su Hafiz suka je gidan amaren a satin farko bayan Hafiz ya tilastawa Juwairiyya zuwa. Tar6an da Salima ta musu yasa Juwairiyya ta sassauto domin ta yi zaton itama Saliman zata yi girman kai ne irin mijinta, ai kuwa kafin su tafi hira suke yi sosai har suka yi musayar number a kan zasu dinga ziyartar juna akai-akai.

 Hafiz ya ji daɗin wannan ƙawancen nasu yayin da Muhammad kuma ya nunawa matarsa baya son hulɗarta da Juwairiyya yayi yawa, bisa la’akari da ya yi na cewa tana da raina mutane da kuma rashin da’a. Sai dai duk da cewa Salima na bin umurninshi amma wannan karon bai samu damar rabata da Juwairiyya ba, ƙarshe haƙuri yayi ya barsu sai dai Cold War da ke tsakaninshi da ita bai ragu ba sai ma gaba da yake yi.

 Tun bayan aurensu Muhammad ya fara kwanciya rashin lafiya domin Ulcer da Typhoid da suka mishi rufdugu, Hafiz na yawan bashi shawarar ya rage cin junk foods da suke sakashi ƙiba suke kuma ƙara mishi cuta amma baya ji, da yake haka ya taso a gidansu suna cin duk abun da suke so babu mai hana su. Wannan kenan.

  Present

 Juwairiyya ce ta gyara kanta data kwantar a kan damtsen Hafiz ta ce,

 “Ina jinka.”

 Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sannan ya fara magana a hankali kamar mai raɗa.

 “Kin tuna ɗazu na faɗa miki abun gaggawa ya taso shiyasa muka tafi bamu jiraku ba?”

 Gyaɗa kai ta yi tana haɗiye wani yawu mai kauri don zuciyarta bugawa ta fara yi haka kurum ta kasa nitsuwa dalilin Hafiz bai ta6a cewa zasu yi magana sannan yayi using wannan tone ɗin ba.

 “Bayan mun fito ne na ga jikin Muhammad a sanyaye na tambayeshi me yake damunshi tun da na lura ba rashin lafiyar ce matsalar shi ba a lokacin. Riya ashe muna tafiya da mutumin nan ne amma shi har ya cire rai da tsawon kwana yana ganin lokacinshi ya kusa, hawayen da naga yana yi ne yasa nace mu shiga mota kar mutane su yi ta kallonshi babu daɗi ana magana. A nan ya nemi mu bar asibitin mu je wani guri zai yi magana da ni, bayan mun fita muka samu wani guri muka tsaya. A nan yake faɗa mini wata magana wacce har yanzu na rasa yaya zan ɗauketa.”

  Shiru ta yi tana jiransa ya ƙarisa maganan lokaci ɗaya kuma zuciyarta ta sassauto ganin akan Muhammad za’a yi maganar ba wai a kan Hafiz ba.

 “A nan ya sanar dani cire rai da yayi da rayuwa wanda bai bari muka rabu ba sai da yasa na yarda da wani alƙawarin da yace in ɗaukar mishi.”

 “Alƙawrin menene?” Ta samu kanta da tambaya don a take zuciyarta ta dawo da saurin bugawar da take yi ɗazu.

  Tunani kala-kala kuwa babu wanda bata yi ba kwakwalwarta na bata wild ideas na wannan alƙawarin da mijin nata ya ɗauka ciki kuwa har da cewa idan matarshi ta haihu Hafiz ya riƙe mishi ɗan kar a barwa Salima saboda mugunta.

 Ya saka na mishi alƙawarin duk ranar da ya mutu in auri matarsa Salima in kuma riƙe mishi duk abun da zata haifa kar yayi agolanci a wani gida.”

  Cikin azama juwairiyya ta tashi zaune har tana buge bakin Hafiz da kanta ba tare da ta sani ba, sosai ya ji zafi har ya ɗanɗani jini a bakinshi amma yayi shiru bai nuna mata ba saboda abun da yake gabansu yafi ƙarfin zogin ciwonsa.

 “Wannan wace irin banzar magana ce?!” Ta tambaya tana aikawa Hafiz wani mugun kallo wanda har lokacin yana kwance bai ko motsa ba yana ganin yanda fuskarta ta rikiɗa lokaci guda da tsantsan kishi, ɓacin rai da kuma wani abu kamar tsoro a kwayar idanunta.

 “I swear Juwairiyya ban san me yasa yayi wannan maganar ba, kuma kukan da yake tayi kamar ƙaramin yaro yasa na ɗauki wannan alƙawarin ba don na taɓa kawo hakan a cikin raina ba. Sannan gani nayi cuta ba mutuwa bace, don yana yawan rashin lafiya bashi zai sa ya gane mutuwa zai yi ba saboda wani yana kwance ma a gadonshi lafiyarshi kalau za’a zare ransa idan lokacinsa yayi. Wani yana tafiya yake faɗi ya mutu yayin da wani abinci ma yake ci zai yi lomarsa ta ƙarshe ya kwanta ya mutu. Na amsa mishi ne don ya daina kukan da yake yi kuma ya bani tsoro ne saboda ban ta6a ganin yana kuka cur-cur da idanuwanshi irin haka ba, ko lokacin da mahaifiyarsa ta rasu bai yi kukan da yayi yau ba. Juwairiyyah tsakanina dake babu 6oye-6oye, shiyasa nake faɗa miki duk abun da ya shafeni bana son na 6oye miki daga baya ki ji ranki ya 6aci kiyi zaton ban ɗaukeki da muhimmanci ba.”

  Shiru Juwairiyya ta yi amma tuni idanunta sun fara tara kwalla, wani irin tsana Muhammad yake mata da tun kafin ya mutu zai bada wasiyyar a ƙuntata mata ta hanyar mijinta ya auri matarsa wacce ta kasance ƙawa a gareta? Shanye hawayen idanun nata tayi ta hanyar kallon saman ɗakin ta buɗe bakinta a hankali tana jan numfashi ta nan tana kuma furzarwa. Sai da ta daidaita kanta sannan ta dubeshi har lokacin zuciyarta bai daina bugu ba wannan karon tambaya zata mishi wanda take tsoron amsar da zai bayar.

 “What if in ya mutun? Zaka cika alƙawarin ne ka auri Salima?”

 Ƙura mishi ido tayi tana ganin ruɗu a fuskarsa wanda ko bai faɗa ba ta gane amsarta.

 “Juwairiyya ki bar maganan nan haka, shima da yayi maganar bana tunanin yana cikin hankalinshi ne sannan who does that for God sake? Ki ɗauki abun tamkar ba’a yi ba, don ni wallahi har na fara dana sanin faɗa miki saboda ban yi tsammanin zaki ɗauki abun da zafi har haka ba. I thought zaki ɗauki hakan ne a matsayin shirme mu wuce gurin.”

 “Zaka aureta ko ba zaka aureta ba?” Ta share duk zancensa ta ƙara mishi tambayar a karo na biyu.

  Sai a lokacin Hafiz ya gane da gaske ta ɗauki maganar da zafi ya tashi zaune ya kai hannu zai jawota jikinshi ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu tace,

 “Just answer me.”

 “Riya I told you….”

 “Hafiz don Allah ka amsa mini. Please.” Ta yi saurin katseshi muryarta har ɓari take yi wanda har sunanshi da bata iya kira a gabanshi yau sai da ta kira.

  Sunkuyar da kanshi yayi ƙasa  kana ya ɗago a hankali yace,

 “He made me promised tare da rantsuwa da Allah akan zan nemi aurenta sai dai in ita ce ta ƙi amincewa sannan zan haƙura, and I know itama ba zata yarda ba saboda ƙawancen da yake tsakaninku.”

 “Baka sani ba dai, babu macen da zaka je mata da zancen aure ta ƙi amincewa da kai Hafiz. Kana da qualities ɗin da mace baza ta iya bari ka wuceta ba.”

  Sai a lokacin kafaɗun Juwairiyya suka sauƙa alamar defeat domin a yanda take faɗawa Salima labarin kyawawan halayen Hafiz zai yi wuya idan ya je mata da zancen ta gujeshi sai dai in ta ji kunyarta ne ta ƙi amincewa.

 Kwanciya ta yi nesa da Hafiz wanda yana ganin hakan yaji babu daɗi a ranshi domin bai ga abun tashin hankali a cikin wannan zancen ba, shi wanda ya kawo maganar ma yayi imanin tsoron mutuwa ce tasa yayi maganar amma ba don zai mutun ba duk da cewa cikinsu babu wanda yake da guarantee ɗin kai tsufa.

 “This is all stupid, da maganar da reaction ɗinki da kuma fushin da kike son ki mini Juwairiyya. But I will let you sleep on it zuwa gobe mu ga ko kema zaki yi tunani irin nawa. Sai da safe.” Yana faɗin hakan shima ya kwanta zuciyarsa a cunkushe bayan ya kashe musu wutan ɗakin.

Series Navigation<< Tafiyar Mu Chapter 1Tafiyar Mu Chapter 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *