(4)
Hafiz ne zaune cikin motarshi a yayin da yake tuƙi ya nufi gidanshi, lokaci-lokaci yana murmusawa in ya tuna surprise ɗin da zai nunawa Juwairiyya. Yana gama parking ya fito ya nufi ƙofar falon ya sanya key ya buɗe ya shiga da sallama a bakinshi.
Shiru ya ji babu kowa a falon don haka ya tasamma cikin bedroom ɗinsu inda ya tabbatar zai samu Juwairiyya. Yana shiga ya samu nan ma bata ciki amma da alamar wanka take yi domin yana iya jiyo ƙaran ruwa a banɗaki. Buɗe ƙofar banɗakin yayi kana ya tura kanshi yana kallon yanda take wanka hankalinta kwance.
“Yau kam dai ba zaka firgitani ba, na ji shigowar motarka.” Faɗin juwairiyya tana mishi gwalo lokaci guda kuwa tana cigaba da wankanta.
Shiru yayi bai yi magana ba sai ma tsayawa da yayi yana kallonta kamar yau ne karon farko da ya taɓa kallonta haka.
Seconds kaɗan da haka Juwairiyya ta watso masa ruwa a bazata wanda ya jiƙa mishi fuska har da gaban rigarsa, ai kuwa ta kyalkyale da dariyar cin nasara domin ta jima tana son watarana ta kama shi off guard kamar yanda ya sha yi mata. Shima dariyar yake yi ya juya cikin ɗaki yana cire rigar yana cewa,
“Eh lallai kin koya, ina ni kika watsawa ruwa kika jiƙa mini shadda mai tsada?”
“Maganin pervets kenan. Kuma ba zan iya ƙirga sau nawa ka mini haka ba, yau kuma Allah Ya yi na rama.” Juwairiyya ta amsa tana fitowa daga banɗakin ɗaure da towel a ƙirjinta fuskarta cike da annishuwa.
“Magana ta ƙare ai, tunda kin koyi wannan zan canja salo.”
“Bring it on pervert. Sannu da dawowa, you are early today.” Ta ƙarisa maganan tana isa gaban mirrow don tsantsane jikinta.
“Ki gama shiryawa ki sameni a palour, ina jin yunwa sosai ba zan iya jira har sai kin gama shiryawan ba.”
“Okay, shikenan. Akwai salads a cikin fridge ka fitar please.”
“To Hajiya.” Da haka ya sa kai ya fice daga shi sai singlet da boxers a jikinshi.
Yana tsaka da cin abinci ya jiwo ihun Juwairiyya wacce ta fito tana tsalle-tsalle ta rungumeshi ta baya sai jijjigashi take yi duk a cikin murna.
“Riya zaki sa in amayar da abun da na ci da wannan jijjigan naki.” Ya faɗi hakan yana mai kamo hannayenta ya ɓanɓaresu daga jikinshi.
“Bee, wayyo Bee. A cikin aljihunka na gani. Wayyo nagode, nagode.” Ta koma gefe tana karanta papers ɗin da ke hannunta bakinta har kunne.
Zuba mata ido kawai yayi yana ganin tsantsar farin cikin da take ciki, she appreciate duk abun da ya mata komin ƙanƙantarshi kuma sai ta nuna farin cikinta ƙarara, hakan ya sa duk lokacin da ya samu dama yake faranta mata da gifts don kawai ya ga wannan murnar a fuskarta.
Sai da ta gama karance duk wasu details na cikin papers ɗin sannan ta matso ta zauna kusa dashi fuska a washe tana cewa,
“Suka ce nan da kwana uku zamu fara zuwa classes ɗin. Bee ka mini bazata ka kuma faranta mini. This is my dream coming true. Nagode, Allah Ya faranta maka kamar yanda nima kake faranta mini.”
Hafiz da tun ɗazu ya koma ga cin abincinshi yanzu kuma tauna ƙashi yake yi yace,
“Ameen. Har yanzu dai na kasa fahimtan bayan kin iya girki amma kuma kina son ƙara koyan wani. A gurina abincinki ya fi mini na kowa daɗi.”
“Bee, shi girki da ka gani yana da sirrika kala-kala wanda yasa wasu experts suka koyi iliminshi sannan suke koyar da mutane. Ba lalle ne in mace ta iya girki ana ci da daɗin rai ya zama ita ta san sirrikan ba, sau nawa ne zaka ga macen ta ake yabon girkinta watarana a kasa cin abun da ta girka musamman in ta haɗa spices ɗin da ba’a son tarayyarsu? Ko kuma ta yi girki amma nama, kayan ciki, kifi ko kaza suna wari duk da kayan ƙamshin da aka saka musu? Ko kuma ka ga an ci abinci lafiya kalau amma daga baya ya zama food poisoning a dawo ana gudawa daga baya? To wannan ilimin sai an koyar da mutum kafin ya sani. Shiyasa nake son shiga catering class ɗin in koya sannan in koyi sauran dishes ɗin da ban iya ba.”
“Umm da gaskiyanki amma babu abun da na gane har yanzu.” Ya faɗa yana dariya.
Da paper ɗin hannunta ta kwaɗe kanshi a hankali wanda kafin ta ankara ya kamo hannun ya riƙe kana ya fara mintsininta a hankali wanda is enough ta ɗan ji zafi kaɗan.
“Bee da zafi fa!” Ta faɗa tana mutsu-mutsun kwatan kanta tana dariya.
“Wai ki ji yanda nake ji ne.” Da haka ya saketa yana dariyar mugunta.
A ranar da dare Juwairiyya ce kwance akan cinyar Hafiz tana chat a wayarta yayin da shi kuma yake danne-danne a laptop ɗinshi suna hira jefi-jefi.
“Bee, yanzu na faɗawa Salima ka sakani a classes ɗin catering, itama tace tana so zata tambayi Muhammad ya sakata, Allah Ya sa dai kar ya hanata kaga sai mu dinga zuwa tare.”
“To ke wa yace ki faɗa mata har ta saka rai?”
“Wallahi muna hiranmu ne nake faɗa mata zan fara zuwa koyan girki shine tace itama tana so akan bari ta tambayi mijinta.”
“Ku dai kuka sani.”
Juwairiyya ta yi dariya kana ta cigaba da danna wayarta can ta ja dogon tsaki ta ce,
“Dama jikina ya bani zai hanata wallahi, wannan mutumin ba’a abun kirki da shi. Don Allah Bee ka mishi magana ya barta.”
“Riya kenan! Yanzu sai in je in sameshi ince ya bar matarshi ta je koyan girki? Ni zata yiwa girkin ko ni na aureta? Duk friendship ɗin mu bama shiga harkan gidajen juna, kowa yana tafiyar da gidanshi ne yanda yake so. Bama yiwa juna shishshigi a al’amura irin haka.”
Juwairiyya dai turo baki tayi gaba kana ta cigaba da chatting da Salima inda take bata haƙuri har da alƙawarin duk abun da ta koyo zata koya mata.
Kwana uku da haka ta fara zuwa koyon girki a Ailisco Catering Class da ke nan cikin Gombe. Kwana biyu da farawarta ta bi gidan Salima daga can gurin koyon girkin, mai aikin Salima ce ta buɗe mata ƙofa ta gaisheta sannan ta faɗa mata matar gidan tana cikin ɗakinta. Kai tsaye Juwairiyya ta isa ɗakin ta yi knocking aka yarje mata ta shiga.
A kan gado ta samu Salima ta kwanta amma fuskarta babu walwala kamar na kullum.
“Hajiya me yake damunki, ko dai baby ne?” Juwairiyya ta tambayeta tana zare gyalen jikinta ta ajiye a gefe kana ta zauna tana fuskantarta.
“Yau kuma na yi laifin da har a gaban cousins ɗinshi
ya mini faɗa, ni wallahi faɗan bai dameni ba ma kamar a kan laifin.”
“Hmm, yau kuma me ya faru?”
“Girki na yiwa wasu ƴan’uwanshi da suka kawo mishi ziyara daga Dukku, na musu shinkafa da miya amma suka gagara cin naman miyan don hamami da yake yi. Wallahi ba zan wulaƙantashi da gangan ba, sannan ban san hakan zai faru ba da nayi wata dabarar.” Salima ta ƙarisa maganan kamar zata yi kuka.
“Wai cewa ya yi kin wulaƙantashi?”
“Mai sauƙin ma na faɗa miki.”
“Kiyi haƙuri Salima sannan ki ci gaba da addu’a Allah Ya sanyaya zuciyarshi. Amma batun naman yau aka mana lecture a kanshi wallahi, don ita mai koyar mana ta yi eBook ga masu son gyara abincisu ba tare da sun shiga classes ɗin ba. Kwanan nan zata yi launching eBook ɗin wanda in ka biya da wuri ₦1000 ne, in aka yi launching ɗin kuma zai dawo ₦3000. Ga number ɗinta ki mata magana a whatsapp sai kiyi payment. 09123227777 AiLisco Venture.”
“Tunda ban samu shiga classes ɗin ba wanna ma will help wallahi, amma iyakacin abun da zata koyar kenan?”
“Gaskiya ban san adadin abubuwan da zata koyar ba amma ina recommending wa amaren bana or teenager da basu da experience na girki. Basu iya gyara nama ba har yayi causing food poisoning, ta ce akwai su knife skills, cutting techniques, methods da kuma pro tips. In taƙaice miki da duk wani basic knowledge na kitchen wanda ya kamata mu sani.”
“Nagode ƙawata, Allah Ya bar mini ke.”
“Amin Amin, dama abun da muka girka yau na kawo miki don na san masu ciki da kwaɗayi.”
Nan da nan fuskar Salima ta washe ta jawo take aways ɗin tana buɗewa, ganinta cikin farin ciki ya sa Juwairiyya jindaɗi da kuma jin tausayinta. Salima deserve someone da ba zai yi taking ɗin haƙurinta for granted ba. Bata bar gidan ba sai yamma liss Hafiz ya zo ya ɗauketa suka koma gida.
Bayan kwanaki da haka ta gama classes ɗin wanda ta koyi komai da aka koya musu sai dai AiLisco tace su cigaba da yin meals ɗin akai akai musamman snacks don hannunsu ya faɗa, don bature ya ce practice makes perfect.
Yau ya kama ranar Friday Juwairiyya ce a kitchen tana haɗa breakfast Hafiz kuma yana can bedroom yana shirin tafiya office. Yana gamawa ya fito ya sameta tana juya pancakes ɗin da ke kan frying pan.
“Ni dai tunda aka koyo girkin nan ban sake cin tuwo a gidan nan ba.”
“Are you complaining?” Ta faɗa tana mai bashi plate cike da pancake wanda aka zubawa pure zuma yayi puff dashi yayi kyau.
“Wane ni? Kawai na yi missing ɗin tuwon ne, and I love every bits of abun da kike girka mini.”
“Bee ɗan siyasa, kana da wayo wallahi. To yau zan yi tuwon da rana, zaka dawo ka samu yana jiranka.” Ta faɗa tana kashe gas cooker sannan suka koma dinning table da ke cikin falon suka zauna suna cin abincin suna hira. Yana gamawa ya miƙe ya tafi ta rakashi har bakin motarshi sannan ta dawo ta cigaba da cin nata tana danna waya.
Ƙarfe biyu da wasu mintuna Hafiz ya dawo Juwairiyya ta tarɓeshi amma sai ta ga kamar baya jin daɗi.
“Bee lafiya na ga jikinka a sanyaye?”
“Kai na ne yake ciwo tun ɗazu a office. Na sha magani amma yanzu kam na san bacci nake buƙata. Gashi ɗazu Muhammad ba lafiya na rakashi asibiti, amma dai basu bashi gado ba.”
“To Allah Ya baka lafiya Bee. Ka je ka kwanta ko zuwa la’asar ne zan tasheka.” Ta faɗi hakan tana mai karɓan abubuwan hannunsa kana ta yi gaba yana binta a baya.
Bata ankara ba ta ji an make mazaunanta ta juyo tana hararanshi, shi kuma da yayi aika-aikan dariya yake yi.
“Nace miki bani da lafiya shine kika yi gaba kina nuna mini abubuwa ko?”
“Mutum mara lafiyan ne idonshi zai je can? Dama sakalcinka ne ya tashi kake son baccin rana.”
“Na ji.” Kawai ya faɗa yana taɓa wani sashe na jikinta.
“Bee.” Ta furta a lokacin da suke shiga ɗaki.
“Na bari, amma ina tashi zan baki saƙo.” Ya ƙarisa maganan yana kashe mata ido ɗaya.
Murmushi kawai ta bishi dashi kana ta taimaka mishi ya cire kayan jikinshi sannan ya kwanta ita kuma ta koma falo don bata jin bacci. Wayarta ta ɗauka ta kira Salima tana tambayarta jikin Muhammad don a yanzu bata son ko da wasa ta ji bashi da lafiya.
“Jiki da sauƙi za’a ce, gashi can dai a ɗaki ya kwanta.”
Dariya Juwairiyya ta saka wanda daga ita har Salima sun yi mamakin hakan.
“I’m sorry, amma wallahi ba dariyar rashin lafiyarshi nake yi ba, ɗazu Hafiz ya dawo shima wai kanshi yana ciwo ya kwanta yana bacci. Shine na yi picturing ɗin mu a matsayin Nannies abun ya bani dariya.”
Wannan karon itama Salima ta dara kana suka yi sallama. Da haka Juwairiyya ta cigaba da danna wayarta wanda karatun littafin Hausa take yi, lokaci-lokaci tana murmushi idan aka zo gurin soyayya wanda sai take ganin kamar ita ce da Hafiz ɗinta.
Tana nan zaune har aka kira sallan la’asar aka shiga sallah sannan ta tashi don ta gabatar da nata kuma ta tashi Hafiz.
“Bee ka tashi lokacin sallah ya yi.” Ta faɗi hakan a yayin da take shiga banɗaki.
Bayan ta gama alwala ta fito ta samu ko motsawa Hafiz bai yi ba, hakan yasa ta saɗaɗa a hankali zata watsa mishi ruwan hannunta sai ta sameshi idonshi a rufe yana murmushi.
“Allah Ya taimakeka domin na tuno baka da lafiya. Ka tashi mu yi sallah.”
Shiru bai amsa mata ba, hakan yasa ta watsa mishi ruwan kaɗan a fuskarshi amma ko firgita bai yi ba haka kuma bai motsa ba. Nan take ta ji wani tsoro ya ɗarsu a zuciyarta ta sa hannu ta fara jijjigashi amma kamar bashi da rai.
“Wayyo Allah na, Hafiz! Ka tashi bana son wannan wasan wallahi. Ka bari, ka bari, ka bari.” Tana faɗan hakan tana jijjigashi amma babu alamar rai a tattare dashi.
Ihu ta kwala mai ƙarfin gaske nan take kuma jikinta ya fara rawa ta kamo kafaɗunshi don ta miƙar dashi zaune amma ya fita nauyi sai ta gagara yin hakan.
Wani ihun ta sake kwalawa kamar wacce ta zauce kana ta fara kiran sunan Allah.
“Allah ka rufa mini asiri, Allah kar ka mini haka. Wayyo Allah na!!”
Fita tayi da gudu zuwa gurin maigadi wanda tun ihunta na farko ya jiyota amma bai je ba, sai dai ya tsaya on alert, ihunta na biyu kuwa yasa ya zo bakin ƙofar falon ya fara kwankwasawa yana kiran sunan ubangidan nashi tunda yana gida. Tana buɗe ƙofar ta kamo hannunshi tana nuna mishi ɗaki tana cewa,
“Baba… Hafiz… yana ciki baya motsi. Hafiz ya mutu.”
Kwace hannunsa yayi ya shiga ɗakin da gudu ita kuma tsabar ruɗewa ta ɗauki wayarta ta kira Salima wacce ringing ɗaya ta ɗauka amma kafin ta yi magana Juwairiyya ta rigata tace,
“Ki tayar da Muhammad ya zo ya kai Hafiz asibiti baya motsi, don Allah ya zo da sauri kar ya mutu.”
Tana gama faɗin hakan ta shiga ɗakin inda ta samu Baba a durƙushe a gaban gadon inda kan Hafiz yake yana kallonshi with so much pain on his face.
“Baba ya mutu ko?” Ta tambaya tana jin zuciyarta kamar ana toye mata shi, idanunta kuwa tuni suka fara zubar da hawaye babi-babi.
“Ki kira yayunshi su zo su kaishi asibiti likita zai dubashi.”
Wayarta da ke hannunta ta duba ta kira babban yayanshi wanda dama a unguwar Tumfuren yake bashi da nisa da su. Yana ɗaukan wayar ta fara magana,
“Yaya Aminu ka zo ka kai Hafiz asibiti bashi da lafiya kuma baya motsi.”
“Subhanallahi. Me ya sameshi?”
“Bayan sallah Jumma’ah ya dawo yace mini kanshi na ciwo shine ya kwanta ya daina motsi, ni da Baba maigadi kuma baza mu iya ɗagashi ba.” Ta ƙarishe maganan tana jan majina tana goge fuskarta da ɗan kwalinta.
“Bani wayar in mishi magana.” Faɗin maigadin yana miƙa hannunshi ta bashi babu musu.
“Alhaji sai dai haƙuri, amma Hafizu ya rigamu gidan gaskiya.” Ya faɗa a hankali amma Juwairiyya ta ji sarai.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Shine abun da Juwairiyya ta yi ta maimaitawa bayan ta durƙushe a gurin da take. Nan take kanta ya fara juyawa tana jin tamkar itama jan ranta ake yi dalilin mutane da ta fara kallo biyu-biyu zuwa uku, can kuma suka fara yawa har bata iya ƙirgasu. Can ta ji kamar ana saka mata hijabi zuwa can ta ji koke-koke kamar Umma ce mahaifiyar
Hafiz.
Daga nan kuma ta ji an ɗagata daga durƙushen an kaita ɗakinta bayan an lulluɓe fuskar Hafiz da mayafin da ta lulluɓeshi da zai kwanta bacci ɗazu.