Tafiyar Mu Hausa Novels

Tafiyar Mu Chapter 3

This entry is part 3 of 6 in the series TAFIYAR MU by Suwaiba Muhammad (Mum Fateey)

(3)

Washegari da safe Hafiz da Juwairiyya suka tashi dukkanninsu jiki a sanyaye. Ƙarfe goma na safen lahadin ta gama musu breakfast suna ci cikin silence kamar ba su ba, lokaci-lokaci tana satar kallonshi tana ganin yanda yake juya taliya da sauce ɗin a jikin fork wanda sai ya yi kusan minti ɗaya kafin ya kai bakinsa, bai gama cin abincin ba ya tashi ya kai plate ɗin kitchen ya fito yana cewa,

 “Zan je gidanmu, daga nan kuma akwai wani abokina da ya shigo gari zamu haɗu. Zan dawo bayan la’asar, akwai abun da kike buƙata ko kike so in dawo miki dashi?”

 “Babu komai. Allah Ya dawo da kai lafiya.” Kawai ta faɗa tana kallonshi cikin ido tana jin zaman nasu a haka har ya gundureta.

 “Ameen. Take care, sai na dawo.” Da haka ya sa kai ya fice.

  Ajiye fork ɗin hannunta tayi tana sauraran duk motsinsa a farfajiyar gidan, bayan ya kunna mota yayi warming ɗinta na wasu mintuna sannan maigadi ya buɗe mishi gate ya fita daga gidan. Tana jin ƙarar rufe gate ɗin idanunta suka ciko da hawaye kana suka silalo kan ƙuncinta. Wai me yake damunta ne? Cewa aka yi Hafiz zai yi aure ko kuma ta ga Muhammad ɗin ya mutu? Sannan ta yaya ma Salima zata yarda ta auri Hafiz alhali suna ƙawance da ita? Menene laifin Hafiz? Shin ta mishi adalci ko kuma tayi aiki da hankalinta wajen auna wannan zancen? Me amfanin wannan cold shoulder da take bashi? Shi yayi laifin ne ko Muhammad? Bata kyauta masa ba, idan tayi haka bata mishi adalci ba, sannan hakan da tayi zai sa a gaba ya 6oye mata damuwarsa saboda tana amfani da emotions ɗinta ba kwakwalwarta ba. Babu mai laifi kuma mugu irin Muhammad da ya nemi a yi mata kishiya, sai yanzu ta ƙara tabbatarwa tsanan da yake mata ya wuce yanda take tsammani. While Hafiz did not deserve any of this!

  Wannan duk tunani ne da Juwairiyya take yi a cikin zuciyarta tana jin tausayi tare da ƙaunar mijinta na ƙara shiga zuciyarta, ta wani gurin kuma tsanar Muhammad ne ya yawaita har tana jin da zata ganshi da ta kwaɗeshi da mari. Sannan ko mutuwa Muhammad ɗin yayi ba zata yarda Salima ta aure mata miji ba, kai Muhammad ɗin ma ba zai mutu ba, daga yau zata fara sakashi a addu’a Allah Ya bashi lafiya Ya ƙara mishi tsawon rai. Ita kuma wannan shine alƙawarinta.

  Kafin la’asar Juwairiyya ta gama girki ta gyara gidanta ko’ina sai tashin ƙamshin yake yi tana jiran a kira sallah ta shiga wanka, ana fara kiraye-kirayen sallah kuwa ta shiga banɗaki ta sillo wanka sannan ta yi sallah ta zauna a gaban mirror ta fara ƙawata fuskarta.

Jim kaɗan da haka ta gama tsara kwalliyar ta sanya Atamfa riga da siket ɗinkin Borno Style da yayi matuƙar karɓan jikinta mai kyawun shape. Falo ta koma ta nemi kujera ɗaya ta haye ta ƙame tana jiran maigidanta Hafiz.

  Ƙarfe huɗu da rabi Hafiz ya dawo ya tarar da Juwairiyya ta kunna kallo a falo tana zaman jiranshi. Ajiyar zuciya ya sauƙe domin ganinta kaɗai kan tafiyar da wani kaso mai tsoka na damuwarshi da kuma gajiyarshi.

 Da murmushi a fuskarshi ya mata sallama ta amsa cikin fara’a kamar yanda kullum ta saba sannan ya shigo ya ajiye abun hannunshi a kan center table dake tsakiyar falon yana cewa,

 “Da ba don ina kishinki ba da na kai ki inda ake zaɓen sarauniyar kyau ta duniya, amma ni ɗaya nake son ganin wannan kyau da kwalliyan.”

 Murmushi tayi mai ƙayatarwa har kumatunta na lotsawa don ba ƙaramin daɗi take ji idan Hafiz ya furta kalamai irin haka a gareta ba, ko ba komai bata yi asaran zama a gaban mirror tana shafe-shafen ba, domin kuwa wanda aka yi kwalliyar domin shi ya gani kuma ya yaba.

 “Bee kana ƙara zugani.” Ta faɗi hakan don bata gaji da jin kalaman yabon daga gareshi ba.

 “Babu zugi Riya, shin kina kallon kanki a madubi kuwa? Da kina ganin me nake gani da baki kawo kokwanto a ranki ba, you are the most beautiful woman I have ever seen and you are mine, mine alone.” Da haka ya miƙar da ita tsaye ya jawota jikinshi kana ya sumbaci goshinta affectionately.

 Irin wannan soyayyar da Hafiz yake nuna mata yasa Juwairiyya bata iya dogon fushi dashi sannan take toshe duk wata ƙofa da zai sa ranshi ya ɓaci balle har wani rashin fahimta ya jawo su nisanci juna. Gashi dai ita ce ta mishi laifi jiya da dare da safe kuma ya fita da ɓacin rai amma da ya dawo gareta sai ya nuna tamkar babu wani abu da ya faru tsakaninsu, haka rayuwarsu ta fara tun farko basa yarda fushi ko ɓacin rai ya yi tsawo har a ɗauki lokaci ana zaman doya da manja, basu iya ba kuma bata fata su fara irin hakan.

 Hafiz ɗinta mutum ne mai haƙuri da kuma sanin darajar ƴa mace, sannan zata iya rantsewa cewa Hafiz yana ɗaya daga cikin few mutanen da suka karanci halayyar mace suka kuma san yanda zasu bi da ita. Sauƙin halinshi yasa itama ta zama mai sauƙar da kai a gareshi da mishi biyayya ba tare da ta nuna gazawa ba.

 “I’m sorry da abun da ya faru jiya, I know it’s not your fault amma zafin kishi yasa na kasa fahimtarka har ina ɗaga maka murya. I’m sorry Bee, I’m so sorry.” Ta faɗi hakan bayan ta ɗago da kanta da yake manne a faffaɗan ƙirjinshi cikin sanyin murya da kuma nuna tsantsar nadamar laifin da ta yi.

 “Ya wuce Riya, na san son da kike mini ne yasa kika kasa ɓoye kishinki kuma kika kasa fahimtata, ko don wannan soyayyar da kike nuna mini ya isa yasa in miki uzuri. Kin yi hakan ne don kina sona and I should thank you for that.”

“Shikenan ka daina fushi kuma ka yi haƙuri?”

“Dama ni ban yi fushi ba, haƙuri kuma na yi tun a jiya kafin in kwanta bacci. Mu bar maganan haka, feed me.”

“Right away Sir. Amma kafin nan ka rage kayan jikinka sai ka ci abincin da kyau.”

“Jiya kuwa na ji wani wa’azi a kan mu maza mu daina zama da singlets da boxers a gida saboda matanmu suna so mu dinga yi musu kwalliya a gida ba wai sai zamu fita ba, to gashi yanzu ke kuma kina cewa in je in rage kayan jikina ba kya son ganin kwalliyan nawa ne?”

“To ai kayi da safe na gani kuma na yaba, yanzu kuma ka dawo cikin gidanka ka fi buƙatar ka samu sarari ka sha iska, but amma I would’nt mind watarana ka mini kwalliyar ka zauna a gida inyi ta kallonka.” Ta ƙarishe maganan tana kashe mishi ido ɗaya.

“Lallai bakya son a ci abincin nan da wuri.” Hafiz ya faɗa yana jin kasala na shiga jikinshi.

“Wani abinci ɗaya?” Ta tambayeshi innocently har tana kyafta idanunta cikin jan hankali.

“Riya, you are driving me crazy. Mu je in baki saƙo a ɗaki the cooked food can wait.”

“Yes Sir.”

  Bayan kwana biyar da haka Juwairiyya ce kwance a kan gadon da ke cikin ɗakinta tana danne-danne a wayarta ta jiyo ƙarar doorbell ɗin falonta. Ta dakata kaɗan tana saurara ta sake jin an danna, hakan ya tabbatar mata baƙi ta yi kuma close one’s domin in baƙi ne wanda maigadinsu bai sani ba baya buɗe musu har sai sun kirata a waya ta mishi magana.

 Babu tunanin komai ta miƙe tsaye kana ta zurma hijabi a kan riga da wandon da ke jikinta ta fita falon tana cewa, ‘Ana zuwa’ ganin wanda yake bakin ƙofar ya sake dannawa. Tana isa bakin ƙofar ta leƙa ta peekhole domin ta hango wanda ya ke bakin ƙofar.

  Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi da ta hango Salima tsaye tana danna wayarta daga bisani ta kara a kunnenta wanda hakan yasa Juwairiyya ta tabbatar ita take kira, gashi abun haushi ta yi magana wanda ta san Saliman ta jiyota da ba zata buɗe ƙofar ba, cikin seconds uku wayarta da ke ɗaki ta fara ringing ta ji kamar ta kwaɗata da ƙasa tsabar haushi.

 Tun ranar da Hafiz ya zo mata da wannan mummunan zancen ta ji bata son ta ci gaba da hulɗa da Salima don haushinta take ji duk da cewa bata mata laifin komai ba, kuma wataƙila ma ita bata da masaniya akan shirmen da mijinta yayi. Ta san tabbas Saliman ta zo jin ba’asi ne domin kuwa ta daina yi mata reply a WhatsApp, haka kuma ko ta yi tagging ɗinta a wani social media a irin post ɗin ƙaruwa ko kuma na ban dariya bata reply. Jiya kuma ta mata missed calls biyar bata ɗauka ba to gashi yau ta tako da ƙafarta don ta ji me yake faruwa.

 Kamar ta yi ihu haka ta buɗe ƙofar Salima ta shigo tana kallonta sama da ƙasa. Da kyar ta ƙaƙalo murmushin dole ta mannawa bakinta sannan ta matsa gefe kana ta maida ƙofar ta rufe tana cewa,

“Sannu da zuwa. Mu isa.”

“To ai ko baki ce in isa ba zan isa.” Faɗin Saliman tana ratseta ta wuce cikin falon ta sami guri ta zauna kan ta cire hijabinta ta ajiye a gefe.

“Kunna mini A.c don wallahi zafi nake ji na haɗa gumi.”

Juwairiyya da take jin kamar ta shaƙeta ta isa gurin A.c ta kunna da remote sannan ta kunna musu tv da dawo ta zauna tana ganin yanda Saliman take fifita da hannunta don rigarta har ta fara jiƙewa da zufa, ‘ƙattin banza kawai’ Juwairiyya ta faɗa a zuciyarta tana nufin Salima da Muhammad.

“Kafin in faɗi abun da yake raina zan miki tambaya ɗaya don Allah, shin na miki laifi ne?”

  Yanda Salima ta yi maganar ya bawa Juwairiyya tausayi ainun nan da nan kuma ta ji kunya ya rufeta domin ta aikata abun da bata son mutane su dinga yiwa wani wato wulaƙanci. Laifi bana kowa bane sai Muhammad, amma zafin kishi yasa ta hukunta Hafiz sannan gashi Salima ma ta samu rabonta, me yasa ta kasa haƙuri har ta bari laifin wani ya shafi innocent souls irin waɗannan mutane biyun?

“Me kike gani?” Ta mayar mata da tambayan ba don bata san amsar ba.

“Kin sani ba sai na faɗa miki ba, kawai ki bani amsa.”

“Babu abun da kika mini wallahi.” Juwairiyya ta faɗi iyakan gaskiyarta cikin nadama.

“To meyasa kika daina mini reply a social media kuma ina ganinki online, sannan jiya na kiraki duk baki ɗauka ba kuma baki biyo baya ba. Ko dai rakiyar da ban miki bane last time da kika je gidana ya ɓata miki rai?”

 Sai da Juwairiyya ta yi dogon tunani sannan ta tuna cewa ranar da ta je gidan Salima bata mata rakiya zuwa bakin ƙofa ba saboda Muhammad ya kira ya sakata aiki.

“Ya Salam! Gaskiya you think low of me. Yanzu fisabilillahi akan hakan ne zan share ki?”

“Kin yarda kenan kin share nin? To me na miki bayan nan? Saboda lafiya muka rabu da ke, ko dai Muhammad ne ya ɓata miki rai?”

Ajiyar zuciya Juwairiyya ta yi sannan ta dubi Salima ta buɗe bakinta zata fara magana sai kuma ta fasa. Me zata ce mata? Tana tsoron mijinta ya rasu ta aure mata nata mijin? Ba zata faɗa mata ba ma balle har ta je tayi tunani a kai ta ajiye a ranta cewa in Muhammad ya mutu zata auri Hafiz! In tayi haka ta zama sakarya. Abun da ya kamata ta yi shine ta ƙara ƙarfafa zumuncinta da Saliman ta yanda ko mijinta ya mutu zata ji kunyar aure mata miji sannan duk wanda ma ya bata wannan shawarar zata iya ɓatawa dashi.

“You can say that amma ya wuce kuma ba laifinki bane. Ki yi haƙuri kaina bisa wuyata.” Ta ƙarisa maganan tana murmushi har kumatunta na lotsawa ciki.

“Don dai ke ce zan yi haƙuri amma wallahi da wata ce da tuni nima na fita a harkarta.” Faɗin Salima tana hararar Juwairiyya cikin wasa.

Da haka suka ɓarke da hira tamkar babu abun da ya taɓa giftawa tsakaninsu, a nan ne Salima take bata labarin cewa har Muhammad ta saka ya kira Hafiz don ta zaci ko bata da lafiya ne, a nan ya sanar da su lafiyarta kalau. Hakan ya sa Salima ta nemi izini a gurin Muhammad kan cewa tana son zuwa yace ba zata je ba.

“Kin san Allah ban taɓa mishi musu ba sai jiya, rufe ido na yi nace mishi ina mishi biyayya amma this time around kar ya mini haka. Ina tunanin ya ji tausayina ne shiyasa yau da safe ya ce in shirya in zo.”

 Juwairiyya kaɗa kai kawai ta yi tana murmusawa domin ta san ba ƙaramin so Salima take mata ba da har zata yi musu da Muhammad a kanta ba wanda idan ya ajiye kara bata iya tsallakewa. To ta yaya zata iya cin amanarta ta aure mata mijin da take so? Salima baza ta taɓa iyawa ba, tana da kawaici da kuma haƙuri.

“Ni dai har gobe ina baki haƙuri ba zan gaji ba.”

“Trust me ya wuce. Amma nan gaba kika sake mini haka zaki ga the other side of me.”

  Da haka suka kwashe da dariya dukkansu aka shiga wata hirar ta daban. Sai yamma liss Salima ta koma gidanta don Muhammad ya kirata ya ce ta dawo gida ta ɗaura musu girki ya fasa barinta sai dare kamar yanda ya faɗa da safe. Tana fita Juwairiyya ta kaɗa baki ta ce,

“Allah Ya haɗaki da wahala, ga rashin lafiya da kuzarin ɗa namiji, ga ci kamar gara sannan ga banzan hali kamar rainon fir’auna. Allah Ya kawo miki sauƙi.”

 Abun da Juwairiyya bata sani ba shine sauƙin na zuwa wa Salima, sauƙin ma mai ɗorewa.

Series Navigation<< Tafiyar Mu Chapter 2Tafiyar Mu Chapter 4 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *