Ameenatou Hausa Novel Part 2

Ameenatou Part 1

This entry is part 1 of 3 in the series Ameenatou na Mamuhgee

AMEENATOU
Mamuhgee

ZafafaBiyar

BlackMoneyLove

Littafin da labarin Ameenatou Wanda ni mamuhgee na rubuta gabaki dayansa sadaukarwa ne ga irreplaceable Besty na AMEENAH ABDULMALEEK (Meenal Maleek)🤍💋

1
BismillahirRahmanirRaheem.

Kaman yanda yake a tabbacen zance Salati baya hana ɗaukar rai, Hakama Ƙasar kabari bata shuka sedai ta binne binnanne,
Itadai ƙaddara yashi ce ko an dunƙulata bata dunƙuluwa,
Rayuwa da kaddara a tare suke tafiya tamkar Yan uwa Daya sbd haka kowace rayuwa take tafe da tata kalar kaddara duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya.

**Cikin tsananin sauri da rawar jiki me tsananin gaske dattijuwar dadahnsu ta fito daga dakin da suke ba tareda ta damu da tsananin ruwan saman da akeyiba masu karfin gaske da iska ga Kuma duhu me.

Runfar madafarsu ta girki ta nufa tareda Saka hannuwanta duka biyu ta share ruwan Dake sauka kan fuskarta sbd ta Gani da kyau.

Madafar data gama jiqewa tsaf ta zubawa idanuwanta da sukai jajir cikin nauyin zuciya da tashin hankali Amma Kuma halinda suke ciki a yanzu ya wuce taji radadin baqin ciki ko wanne iri Dan haka ta qarasa inda murhun wutarsu yake ta fara kokarin gyara Yan sauran itatuwan Dake gurin tana hada kansu Dan hura wuta kota Yaya duk da ruwa da iskan da ake zubawa me karfin.

Motsi taji a bayanta sedai Bata iya juyowa ba sbd kokarin hada wutar cikin sauri dan tasan ba kowa bane face babbah mahaifin ‘yayan nata mijinta.

Zagayowa yayi ta gefenta Shima a jiqe  kayansa na tsiyayar ruwa sosai  hakama rawanin Daya zagaye kansa dashi sbd ruwan Shima ya jiqe sosai Yana tsiyayar ruwa.

Duk ruwan Nan da akeyi akansa aka farasu Yana tsaye kofar dakin da suke Tin safiyar ranar har zuwa yamman sallah kawai ke matsar dashi daga kofar dakin har hadarin ya Hadu Yana tsaye duk karfin iskan da aka fara aka fara ruwan Yana tsaye a gefen dakin Yana jiran tsammani ya zauna ya tashi tsaye,yaje farkon Bango ya dawo Babu abinda yake fata Se Allah ya kawo musu wannan lamarin a cikin sauki ko Dan jarabawa da kaddarorin da suka ringa haduwa dasu a rayuwar Nan.

Tayata hada kan itatuwa gurin da hura wutar yafara kokarin yi Yana Dan rife idanuwansa dasuka manyanta sosai tsufa yafara saukar musu sbd ruwan Dake shiga cikinsu,
Ita kanta dada kokarin kunna ashana takeyi amma ruwa da iska Baya bari Amma takasa Dena kokarin kunnawar hannuwanta na kakkarwan sanyi da mutuwar jikin damuwan Dake dabaibaiye da ita Mai hade da tsananin tsoro.

Shi kansa babba dayake tayata kare iska da ruwan da hannuwansa Dan ta kunna wutar yasan wura wuta a wannan lokacin ba abune da zai taba yiyuwa ba har abada sbd ita kanta ashanar tsiyayar ruwa takeyi Amma dukkaninsu sun kasa yarda da sallamawa sbd Babu Wanda zuciyarta take a daidai da tinanin nutsuwa a cikinsu abu Daya ne a ransa shine bazasu iya rayuwa ba idan wani abin ya samu wadda ke cikin dakin gurin haihuwar abinda yake cikinta,

Itace duk wani karfin zuciya da karfin halin dasuke dashi na ci gaba da rayuwa bayan masifun dasuka ringa shiga,
Babba shine shugaban gidan Kuma gatansu Wanda ya kasance jigonsu,shikuma babba itace hasken zuciyarta Kuma nasa jigon Dan idan Babu ita baida jarumtar cigaba da zama shugaba a cikin Iyalin nasa.

Hannuwansa Dake Dan rawa Shima ya miqa ya karbi ashanar hannun nata yafara kokarin tayarwa Amma kwalin ashanar narkewa ma kawai yafara yi a tafin hannunsa sbd ruwan Daya gama jiqasa..

Qurawa tafin hannunsa idanuwansa dasukai jajir yayi Yana kasa motsawa bare cewa komai zuciyarsa na daukan wani irin nauyi da dumi a lokaci Daya.

Dadah ma da jikinta ke mutuwa dagowa tayi da jajayen idanuwanta ta kallesa zuciyarta na yankewa da ganin yanayinsa,
Yanda yake tsananin son mahaifiyar Ameenatou da Ameenatou haka take tsananin sonsa Dan haka bazata bari ya sake dandana radadin rashin da yayi a Baya ba na rashin ganawa da Rabin jikinsa Dan haka jikinta na rawa ta juya ta nufi inda tasan akwai wata ashanar ta dauko tafara kokarin wura wutar da idan har gawar Dake Rami zata fito tayi magana to tabbas tashin wuta a wannan lokacin zai yiyu.

Ahankali babba ya Bude idanuwansa dake rintse ya Kalli dadah Daketa aikin abinda bame yiyu bane Amma taqi denawa Se qarawa takeyi kaman batasan ruwane ke tsiyayar daga shanar ba.

Hannu ya miqa ya karbi ashanar ahankali tareda saikinta qasa ya kamo dadan suka bar gurin zuwa kofar dakin da ake komai a ciki sedai kafin su iso matar Dake ciki ta fito dakin gabaki dayanta itama a jiqe da zufa jikinta duk a sake.

Zuba musu idanuwanta tayi kaman yanda suma zuba mata nasu idanuwan suka zuba mata kafin babba ya dauke kallansa daga kan matar ya mayar kan kofar dakin Yana kalla cikin sanyi da wani irin zuciya dayaji Yana saukar masa Yana barinsu.

Dadah ce ta iya samun karfin halin Bude Baki cikin sanyi tace

“Ameenatou ta….??? Kasa qarasawa tayi sbd batasan amsar da Za’a bata ba idan ta qarasa tambayar.

Numfashi matar ta sauke ahankali tareda kallansu su biyun cikin nutsuwa da kaucewa matsala tace,

“Bazan iya ba dole ayi gaggawar kai ta asibiti kafin wata babbar matsalar data fi wannan ta biyo baya.”

Shiru dukkaninsu sukayi jin abinda ta fada,
Ruwan dake sauka kansu kawu ya kalla Dan baisan tayaya zaa fita da mara lafiya a cikin wannan ruwan me karfi ba zuwa asibiti yanzu yanzu ba.

Dadah data kasa cewa komai dakin kawai ta shige tana hadiye hawayen dasuke ciko idanuwanta Dan gano ‘yarsu.
Babba Kuwa juyawa yayi Shima batareda yace komaiba Dan Nemo abin hawan tafiya asibitin cikin gaggawa duk da Samun abin Hawa acikin ruwa me qarfi irin wannan tamkar shige ruwa neman allura.

Tsayuwar dadah akanta bayan shigowa dakin yayi daidai da fara jijjigarta Dan haka take jikin dadah yadauki rawar discon da Bata shirya ba,murya rikice a karye ta kwada kiran Hafsatu datake wajen tana kamo ‘yarta jikinta tana rokon kada Allah ya dauki ranta a yanzu yabarsu da ita.

Hafsatu data shigo dakin a rikice idanuwanta na dauka akan yanayin ta qaraso a cikin sabon rikicewa tana cewa,

“Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Shikenan, shikenan, innalillahi wainna ilaihirrajiun..””

Dadah da kunnuwanta suka dauke ji a take dago jajayen idanuwanta tayi tana kallan Hafsatu kaman wawuya takasa furta komai sbd Jin komai na ‘yarta ya tsaya cak a jikinta.

MAFARI
SHEKARUN BAYA!!!!!!

SEELAH’S shine karbabben sunan Aminai biyar da suka taso tamkar uwa Daya ne Uba Daya ya haifesu,
Kauna,shaquwa,AMINCI,yarda,hakuri da tsananin son juna da sukeyi shine ya samar da sunan SEELAH a tsakaninsu Wanda yake dauke da maanar karfin daukaka.

A farko su din bayi ne da suka taso cikin wahala da bauta tareda leburanci a babbar taskar gino danyen zinarin gwal.,

A rayuwar Gina ramukan Nemo zinari suka taso suka girma har Suma suka gada ‘yayansu ma suka gada daga garesu,
Basada lokacin iyalansu sbd wasu lokutan idan suka shiga ramin da tsawonsa da zurfinsa tareda duhunsa da azababben zafin da yake kashe wasu da dama aciki sukanyi kwanaki da Basu fito ba.

Ahaka suke rayuwa wadda babu ranar da baa samun mutuwa a cikin ramin Dan kuwa ginar zinari Yana tafiya ne da ginar kabarin binne wainda jininsu yake tafiya a cikinsa.

MAMMAN SEELAH,OMER SEELAH,LAMEENU SEELAH,KASIM SEELAH da JAMIL SEELAH sune Aminai biyar da suka taso a tare cikin tsananin shaquwa da tsananin hadin Kai tamkar iyayensu da suka taso a Hakan tare tin kuruciya har girma har suka rasu Daya bayan Daya duka a harkar zinari Dan haka suka a tare suka taso tamkar iyayensu dauke da sunan SEELAH Wanda aka shedasu da shi gabaki Daya kauyensu da zagayenta.

Da farko su din sun banbanta da iyayensu sbd halayensu dasuke a Dan banbance tareda raayoyi Amma duk da Hakan kusan su kansu sun shedan da Babu wata kauna ko shaquwa bayan tasu shiyasa da yawa baa San ba iyayensu dayaba a idanuwan mutane su din yayane na uwa Daya Uba Daya.

MAMUH

BLACK MONEY

BEST LOVE STORY

ZAFIN KAI

JAMAAL JEEY SEELAH

DEEP

AMEENATOU

2024ROMANCE

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!! Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

Join our WhatsApp group here

Series NavigationAmeenatou Part 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *