Ameenatou Hausa Novel Part 2

Ameenatou Part 3

This entry is part 3 of 3 in the series Ameenatou na Mamuhgee

34
Maryama gaba Daya ta cire tsammani daga rayuwa Dan haka cikin rawar murya da tashin hankalin da Bata taba Shiga ba ta fashe Da kuka zata fara rokonsu karsu kasheta BB ya sakar mata wani mugun marin bayan hannu Saida bakinta ya fashe Da jini sosai ya sake cakumo wuyanta Yana Dora wuqar kafin yace komai Baki na jini tace

“Koda ranar tazo tana daukeda tsohon ciki wata Tara……

Wani mummunan zufa da sarawan Kai tareda bugawan zuciya ne ya saukarwa Lameenu da Mam lokaci Daya,
Lameenu yayi saurin kallan Mam zuciyarsa na wani irin bugawa da karfi da tsalle sbd baitaba tinanin Jin Hakan ba,
Da gasken kenan dai Omar nada magajinsa,
Magajin dukiyar da baimasan Yaya zeyi da ita ba,
Gadon dukiyar tin suna samari suke dakonta cikin ransu,
Dukiyar da suka zama abinda su kansu basuyi tinanin zama ba ko a mafarki Amma daga karshe ace share fage ne kawai sukaiwa abinda Omar ze Haifa.

Mam kasa motsawa yayi bare juyawa ya kalla Lameenu sedai zuciyarsa kusan tafi ta Lameenun shiga mafi girman tashin hankali da firgici.

Shi kansa BB wani irin zufan tashin hankalin ne ya jiqasa Dan haka ya sake danna wuyanta Yana jiran sauran bayanan
Cikin rawar murya da ficewa hayyaci taci gaba da cewa

“Bata rasu ba a Daren sai bayan data haife cikin dayake jikinta,
Sir Omar yasan ta haihu sbd da kansa ma ya karbi abinda ta Haifa,
Oga Ahmed ma yasan ta haihu a daren….”

Kukanta karuwa yayi muryanta ya tsinkewa sbd tsoro numfashinta na Neman daukewa tsaban tashin hankali da tsoron wuqar Dake wuyanta tanajin kaifinta.

Lam da duka jikinsa ke rawa da zufa kasa hakuri yayi cikin zafi da matsuwa yace

“Me ta Haifa a Daren?
Waye Wanda kuke tareda shi a gidan wannan Daren?
Ina abinda aka haifa din yake?
Waye ya tafi dashi?

Wani sabon mari BB ya falla mata cikin rashin tausayi bare Imani Yana cewa

“Koro bayanin amsosin abinda aka tambayeki kafin na ratsa wuqar Nan cikin makoshinki”

Bakinta da duka jikinta na rikicewa da jijjiga Hawaye da majina duk sun cakude a fuskanta cikin matsanancin tsoron rayuwarta tace,

“Banda tabbacin abinda ta Haifa sbd a dare duka muna cikin tsoro da tashin hankali daga sir Omar Se oga Ahmed da ‘yayan Hajiya Ameenatu din ne kadai suka San Menene aka Haifa tsakanin mace ko namiji…
A Daren yayanta yazo daga gombe gurinta Kuma shine ya tafi da babyn”

Wata sabuwar zufa ce ta tsiyayowa kowannensu Dan kuwa abin yazo a yanda basuyi tsammaninsa ba.

Sake danne wuyanta BB yayi tafara jero musu bayanin komai Daya bayan Daya har address din gidan Babbah dake gombe da yanda suka tsare da Kuma yanda Taga girman son dayake wa yar uwarsa da abinda ta Haifa din tabar masa.

Abu dayane ta boye shine cewan tasan mace ce aka Haifa sbd tsaban rufewa da shiga tashin hankali kwata kwata ta manta mema aka Haifa din.

Tana gama fadan kalamanta na karshe Mam ya miqe tsaye Yana ficewa daga dakin zuciyarsa Babu inda Bata tafasa da daukan nauyi.

Lameenu kuwa bayan ya miqe BB ya kalla da idanuwansa tareda yi masa kallan dayasan me yake nufi kafin Shima ya fice Yana Jin ihun Maryama din datai so Daya Bata Kara ba aka rufe bakinta.

Mota suka suka nufa da sauri BB ya qaraso ya budewa Mam driver Kuma ya budewa lameenu suka shiga Kai tsaye aka rufe driver ya shiga da sauri ya tayar da motar BB na musu a sauka lafiya suka bar gurin.

Tinda suka kama hanya Babu me cewa komai sbd kowa da Saka da warwaran da yakeyi a zuciyarsa cikin tinanin Neman mafita data inda zasu fara Neman Dan uwan matar Omar Wanda a yanzu sukeda cikakkiyar tabbacin ‘dan Omar Yana hannunsa.

Lameenu da hankalinsa yafi na Mam tashi sbd yanada labarin project dinsu ba lallai yakai labari ba Dan kuwa komai Baya tafiya yanda akeso,
Idan Mam yaji Hakan abun sake lalacewa zeyi Dan shi Kam ya gaji da Mam Yana sake bawa Haroon Daman shikuma Yana sake rusa su sbd bazai taba zaba me amfanin da sukeso ba Babu amfanin basa damammakin da ake basa,

Shi a nasa son su cire Haroon daga komai nasu Dan baida amfani kawai su bazama Neman magajin Omar Dan kuwa Babu abinda zasuyi yanzu dukiyar ta dawo yanda take koma fiye da yanda suke tsammani bayan su mallaki dukiyarsu ta Omar Dake ransu tin shekara da shekaru.

Mam ma a cikin ransa kusan tinanin ne a ransa Dan kuwa idan ba bazama sukai suka haukace gurin Neman magajin Omar ba faduwansu zai Sakasa yiwa dansa abinda baitaba tsammata yi din ba Dan kuwa ya tabbatarda Haroon yafi kowanne ‘da rashin amfani,
Ya rasa wane irin Kai ne dashi gashi tsaban rashin basira ya kasa roko ko rarrashin Jamaal ya dawo musu,

Ba komai ya sakashi sakar masa pressure da nuna masa hantara da rashin kauna ba sai Dan ya rufe ido ya dage ya Saka Jamaal dawowa garesu ba Dan yasan duk duniya Haroon ne kadai zai iya Saka Haroon dawo musu Dan kuwa duk Wanda yasansa yasan Haroon ne abinda yafi komai so da kauna fiyeda komai bayan mahaifiyarsa Dan haka suke zafafawa Haroon komai Dan Jamaal ya dawo musu Amma Haroon din kaman kansa Babu komai a ciki Se iska,

Duk maganin da suka Saka masa a drink suna susuta kwakwalwansa Dan ya zama abin tausayin da zai Saka Jamaal ya dawo garesa abin ya gagara sbd yasan duk abinda Haroon zai koma bazai taba zabar barinsaba Koda Jamaal da mum dinsa sunso daukesa bazai taba binsu ba Dan haka yakeda tabbacin Jamaal zai dawo sbd Dan uwansa.

Suna Isa gida kowa mansion dinsa ya shige batareda tsayawa office nasu Dan tattaunawa ba Dan kowannensu Yana buqatan kadaicewa Dan dawowa daidai.

Mum Atee na ganinsa da yanayinsa bayan shigowansa tasan akwai damuwa me girma Dan haka tabarwa Ayesha zaban kayan datakeyi a waya ta bisa zuwa sama tana fatan ba matsalar Haroon bane da itama zuwa yanzu lamarinsa yafara isarta Dan itace kullum me zuba maganin da suke basa a drink dinsa na cin abinci sai kuma ta tabbatarda yasha cikin kulawa da dadin Baki Wanda ahankali ahankali yake yiwa kwakwalwansa illa harma da kuzarinsa batareda sanin Dad dinba Dan abinda yasaka ta ringa basa daban da abinda take basa din.

****Barr Haroon seelah a yanzu ba zaman Nasarawa ne ke basa nutsuwa da farin ciki ba ganin Ameenatou ne da rayuwar ahalinta da yanzu ya zamar musu tamkar Dan uwa,

Ayanzu Daya sabu da zamanta a cikin zuciyarsa Babu ranar da Baya zuwa gidan duk yanda zai gaji da ayyuka kuwa saiyaje gidan da daddare acan yake fira cikinsu sai dare sosai yake komawa masauki.

Babbah da dukkaninsu har zuciyarsu sun basa matsayi me kyau da kauna me sanyi kallansa sukeyi a Dan uwa duk da tsananin tazarar datake tsakaninsu Dan kuwa idan ya zauna cikinsu kaman saika wanke hannu zaka tabasa Dan yanda yake fita daban kaman wata acikin taurari.

Ameenatou sosai suka shaku cikin qanqanin lokaci Kuma a bayyane yake yanzu tsananin son dayake mata duk da itama tana sonsa sosai sedai hakanan wasu lokutan sai takejin kaman irin son datakewa su Yaya Hafiz take masa Amma Kuma tace bazata auri kowa ba sai shi Dan Hakan ne ma yakejin samunta a rayuwarsa zai samu nutsuwa da Kwanciyar hankalin Daya rasa tareda kadaicin rayuwar dayake ciki.

Bai taba sanin wannan son dayake a cikin kirjinsa yanzu ba shine abinda Dan uwansa Jamaal yake ji a lokacinda fadilansa tana raye ba,
Baitaba dauka zaiso mace irin son da Jamaal yayiwa fadila ba sai yanzu dayake Jin Ameenatou har cikin jininsa da ruhinsa Dan kuwa akanta ne yafara Jin Koda Dad dinsa zai yafesa idan har zata zama cikin rayuwarsa zai iya fuskantar Hakan.

Dukkaninsu Babbah sun San so me tsanani yakewa Ameenatoun Dan haka yake sake matsayi sosai a zuciyoyinsu musamman Hafiz dayake Jin farin cikin Ameenatoun zata samu rayuwar da zata zufafa iliminta Dan sunada burin tayi karatu me zurfin da zata dogara da kanta tinda bazata zauna karkashinsuba har abada.

Aikin Daya kawosa fara lalacewa yayi matsaloli suka fara bayyana sbd gabaki Daya hankalinsa da nutsuwan dayake samu a gurin Ameenatou suna can,
Idan ciwonsa yafara tasowa na damuwa Baya gane komai Baya ganin komai idan ba gidansu Ameenatou ya taho ba ya zauna ya zuba mata idanuwansa tana magana yana sauraronta Kokuma Idan tana tareda su Babbah tana zuba sangartanta son ranta batareda damuwa da Yana gurinba Dan matiqar tana taredasu Bata duba kowa duk abinda takeso zatayi Abinta shi Kuma Hakan yake sake kashesa akanta musamman idan tana fadan shi kadai ne zai zama mijinta Babbah zai aura masa ita.

Wannan kalman itace kalman da ayanzu take fin komai Sakasa farin cikin Da bayada shi kwata kwata a rayuwarsa.

Siddeeq hankalinsa yafara tashi sosai da irin son da Haroon yakewa Ameenatou Dan karfinsa yafara Sakasa shakkar lafiyansa ga Kuma bangare Daya aikin dayake gabansu fa Babu haske ko kadan kullum sabuwar matsala ake samu Dan haka yake cikin tashin hankalin.

Ranar dasu Dad suka zauna da turawan da suke cikin aikin suka fara samun barazanar janyewa daga hadin gwiwan kwata kwata jinin Mam Hawa yayi sosai Saida aka kira likitoci gida suka dubasa aka basa magani hadda su ruwa.

Mum Atee hankalinta tashi yayi Dan haka ta dagawa Haroon hankali da kuka Saida ya dawo Lagos a ranar cikin mummunan tashin hankalin abinda ya samu Dad dinsa.

Dad Lameenu kuwa kusan zaucewa yafara kokarin yi Dan ganin Mam a halinda yake ciki yasan balain Da yakai Mam kwance ba qaramin balain da zai kawo karshensu ba kwata kwata ne ba Dan haka ya kira BB ya Bude musu wuta akan tsananta bincikensu ko Wanda ya taba sanin dangin Aminatu ne aka samu a kamosa a kawosa.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

35
Tinda Haroon ya dawo Dad dinsa ya Hanasa ganinsa Dan Baya buqatan ganin ko fuskan Haroon din.

Mum Atee ce ta ringa lallaba Haroon din da duk inda hankalinsa yake ya tashi da wannan hukuncin na Dad dinsa.

Kusan Shima kwantawa yayi ciwon sbd hukuncin Dad dinsa na qin barin ya gansa.

Da wannan damar mum Atee tayi amfani ta ringa shayar dashi kwayar da suke Banka masa Dan haka sai yafara rikicewa ahankali ahankali sbd fushin Dad din da Kuma kansa da suke Neman juyar masa.

Siddeeq Daya fahimci yanayin Haroon din ya sauya sosai ya fara tsananta sosai daukesa yayi suka koma Nasarawa Koda lamarin zaiyi sauki idan Yana ganin Ameenatou wadda itama kullum take cikeda kewansa da damun su Babbah akan kada fa yaje ya auri wata acan Lagos yabarta anan ita tana jiransa.

Dawowansu Nasarawa ciwonsa tsananta yayi gashi basa ganin likita a bayyane a boye suke Gani sbd kada Yan jarida su ji Barr Haroon seelah magajin SEELAHs yana fama da matsalar data shafi damuwa da kwakwalwa.

Su Babbah Jin baida lafiya sosai suka shiga damuwa da tausaya masa sbd kaunar da suke masa ta wuce ta ogan Hafiz da Kuma Mai son Ameenatou.

Babbah da Yaya Abdul da kansu suka takurawa Haroon din da siddeeq suka Kaisa asibiti da kansu suna zuwa aka basa gado a dakin da Babu Wanda zaisan waye a asibitin.

Kwanciyarsa asibiti ya Sakasa sake tabbatarda bazai iya rayuwa Babu Ameenatou ba Dan kuwa kauna da kulawan da Bai taba tinanin ana samu daga ahali ba sune ya samu Dan kuwa Hafiz ne ma kusan yake kwana ya tashi dashi a asibitin babbah da Abdul ma kullum anan suke kusan wuni dadah da Heartbeat dinsa kuwa kullum sai sunzo da daddare su koma tareda su Babbah gaba dayansu.

Ameenatou duk narkewa tayi ganin yanda ciwon kwana biyu ya mayar dashi Dan haka tausayinsa ya Saka sonsa Data kasa ganewa da tantancewa cike dukkanin zuciyarta.

Kwanansa biyu aka sallamesa batareda ance musu komaiba kawai dai wai ciwon Kai da bp dinsa ne ya hau sbd damuwa da stress na aiki.

Bayan an sallamosa da kwana Daya Lagos ya tafi Dan sake dubo Dad dinsa Wanda har lokacin ko wayarsa Baya dauka.

Bayan isarsa Lagos Shima siddeeq gida ya koma Dan dubo umman fadila da yanzu Alhmdlh ta rungume kaddara tana rayuwarta cikin Kwanciyar hankali da Kuma kulawa me tsananin datake samu da kauna sosai daga siddeeq din Daya inganta rayuwarta sosai Babu abinda ta rasa saima Jin dadinta datakeyi.

****Tsayuwa Haroon yayi jikinsa na sanyi ganin Dad dinsa zaune a kan dining din cin abincinsu na dare bayan baiyi tsammanin ganinsa ba a gurin Dan kwata kwata ya Dena barin Yana ganinsa.

Mum Atee ce tayi saurin tasowa daga inda take zaune kusa da Dad din Yana washe Baki cikin kulawa da kauna sosai ta nufosa tana cewa

“Zo ka zauna yau tareda Dad Dinka zakaci abinci Inshallah duk komai ya wuce”

Kallan Dad din yayi Yana qarasowa jiki a Sanyaye zuciyarsa na sanyi hakama jikinsa na sake mutuwa sosai.

Mum Atee ce tayi saurin ja masa kujeran kusa da Dad tana cewa ya zauna ai Dad dinma yayi kewansa.

Zama yayi batareda ya dago ya Kalli Dad dinba Shima Dad din Bai kallesaba ba Saida gurin ya dauki shiru tsawon mintina kafin Haroon din ya dago ya Kalli Dad dinsa da idanuwansa dasukai wani irin ja da sanyi cikin sanyi da nutsuwa yace

“Dad barka da fitowa,
Yaya jikin?
Allah ya karo Maka afuwa da sauki.”

Numfashi mata sauti Dan dumi Dad din ya sauke kafin ya amsa Kai tsaye Babu Jin dadi ko kadan a muryansa Dan kuwa ganin Haroon din kadai tafasa zuciyarsa yakeyi Dan gap yake da yafesa gwara yasan baida ‘da ko Daya a gabansa Saiya fanjama mummunan aikinsa dakyau kawai ayi me yiyuwa.

Ayeesha Dake table din itama cikin kulawa ta gaida Dad din tana masa ya jiki ya amsa Yana gyada mata Kai kafin Suka fara cin abinci Babu me cewa komai.

Suna gama cin abincin mum Atee sai sake zuba masa juice din data hada masa da kanta takeyi cikin kulawa da tattalinsa kaman Dan data haifa.

Suna gama cin abincin kafin kowa ya tashi Dad sai lokacin ya dago ya Kalli Haroon cikin kamewa Babu sakewa ko kadan yace

“Ka hada komai na SSl project ka ajiye za’a rufesa gaba Daya Wanda kasan me Hakan ke nufi ai ko?”

Wani mugun zufa ne ya fara tsiyayowa daga cikin rigar Haroon ya dago idanuwansa ya Kalli Dad din cikin tsananin kwantar da Kai yace

“Dad Ina rokon ka karamin time na cike time din da aka dibarmin tin farko akan aikin nayi alkawarin zan cika Maka alkawarin dana dauka akan aikin,
Dad please Karkayi saurin rufe komai wlh Ina iya kokarina fiyeda yanda kake tsammani,
Ko yanzu rashin lfy nayi kwana biyun shiyasa aka fara samun durkushewa Amma wlh Dad nayi Maka alkawarin komai zaizo gabanka yanda kakeso….

Daga masa hannu Dad din yayi zuciyarsa na wani irin ciwo da radadi Dan har lokacin Jin yakeyi zuciyarsa Bata warkeba.

Jajir idanuwan Haroon din sukai kaman yanda na Dad din sukai jajir yanajin baisan me zai kama ba yabar Daya tsakanin ‘dansa da dukiyarsu dasuke Neman rasawa.

Mum Atee datai shiru Dan muskutawa tayi tana rokon Dad din akan ya sake bawa Haroon din dama.

Ayeesha kuwa shiru tayi dukkanin jikinta yayi sanyi da tausayin Haroon Daya rasa komai akan Dad dinsa Amma Babu Wanda ya taba appreciating nasa ko kadan.

Shiru Haroon yayi zuciyarsa na nauyi me tsanani tareda nauyin Kai shima me tsananin Yana sauraran yanda mum Atee ke rokon Dad din kafin ya amince masa da sharadin ana samun matsala zai tattara ya koma Poland Shima gurin mahaifiyarsa.

Dagowa yayi da jajayen idanuwansa ya kalli Dad din tareda masa godiya kafin ya miqe jiki a mace yabar dining din Shima Dad miqewa yayi yabar dining din.

Koda ya koma dakinsa juyawa kansa yafara yi masa tin a palonsa ya zube Yana dafa Bango kaman ganinsa zai dauke Yana Jin kansa kaman zai tarwatse.

Daqyar yakai kansa dakinsa ya Isa gaban mirror Yana Neman maganinsa Amma Bai gansa ba.

Raffowa yayi Yana barin duk abinda ya fadawa harya Isa gefen gadonsa yafara janyo drawers hannuwansa na wata irin rawa Yana yamutsa kayan ciki gurin Neman maganinsa Amma kwata kwata ya kasa ganinsa.

Buga kansa yafara yi a jikin gadonsa Yana wata irin rawar jiki.

Wayarsa Dake gefen gadon ajiye ce tafara ringing Amma Sam baima San meyake ji ba bare yaji Kiran.

Ameenatou Dake kiransa Dan Jin muryansa sake Saka Kiran Tayi tana matsuwa Daya dauka Dan haka kawai zuciyarta keson jinsa Dan yanzu zuciyarta ta gama yin naam da karban sonsa fiyeda yanda tayi tinanin tana son nasa.

Cigaba da Kiran datake masa ya Sakasa dago idanuwansa da sukai wani irin mugun jajir ya Kalli wayar.

HB ya Gani rubuce kan wayar yaga itace.

Hannuwansa Dake wata irin rawa ya dago suna jijjiga ya Dora akan wayar ya dauko tareda daga wayar ya Saka handsfree ya ajiye Yana Jinta acikin dadaddiyar muryanta me sanyi da nutsuwa tana magana.

Yana jinta Amma kwata kwata Baya iya magana saima Juyewan dayake Jin kaman kansa zeyi da azabbiyar ciwo da nauyi hakama jikinsa rawa yake qarawa sosai Yana hada zufan dayake sake tsatsafo masa Tako ina har cikin tafin hannuwansa da kansa.

Sunansa ta sake kira cikin damuwan jinsa shiru tana narke masa a wayan.

Wasu hawayen azabbiyar Sonta da tausayin kansa masu tsananin zafin gaske suka gangaro masa ya rufe idanuwansa harta gama magana yanaji ta kashe wayar batareda ta sake Kiran ba.

Kuka me zafi ne ya kufce masa Yana buga kansa a jikin gadonsa da karfi har lokacin jikinsa rawa yakeyi sosai musamman hannayensa.

Ya Dade acikin wannan azabar tsawon lokaci kafin ya Dan samu sassauci ya rarrafawa ya sake dudduba maganinsa ya gansa a Palo ya dauka da sauri hannuwansa na kakkarwa ya Bude roban ya zubo guda biyu ya jefa bakinsa tareda Isa inda ruwa suke da sauri ya dauka ya shanye maganin yana sake hada zufa me yawa kafin ya silale a palon ya zauna Yana rintse idanuwansa Yana jingina bayansa jikin bayan Daya daga cikin tsadaddun kujerun palon.

Yayi mintina sosai ahakan kafin ya dawo daidai ya sauke numfashi da ajiyan zuciya tareda miqewa tsaye ya nufi bedroom dinsa gurin wayarsa Kai tsaye ya nufa ya dauka Yana kallan time yasan zuwa lokacin Ameenatou tayi bacci Dan haka Hafiz ya kira ya tambayesa ya sanar mace tayi bacci.

Sallama sukai batareda ya kirata ba Dan kaman yanda su Babbah ke lallabata haka Shima yake lallabata kaman zuciyarsa Dan haka bazai iya tadata bacci da wayarsa ba.

Ajiye wayar yayi ya miqe ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa yayo wanka ya fito daure da towel ya shirya cikin kayan bacci marasa nauyi ya kwanta Yana rufe idanuwansa jikinsa har lokacin a Sanyaye.

Washe gari tinda safe breakfast kawai yayi dasu Dad yayi musu sallama suka nufi airport suka bar Lagos din shida siddeeq.

Bayan tafiyarsa Dad Lameenu ya Saka aka bisa Dan Saka masa ido sosai akan lamarinsa kowanne irin motsinsa da komai Dan shi Kam bazai yadda suna kallo su wayi gari basuda komaiba.

MAMUH

JAMAAL JEEY

HAROON SEELAH

AMEENATOU

IDENTICAL TWINS

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

36
Ameenatou na islamiya ya dawo Dan haka bayan yayi Sallah abinci yaci ya kwanta Dan samun baccin da tinda yake Lagos harya baro Bai wani samuba.
Shima siddeeq hutun ya kwanta ya samu kafin yamma.

Karfe Biyar da mintina ya tashi daga babbacin na awa Daya da Yan mintina San Saida yayi laasar ya kwanta.

Wanka kawai yayi ya shirya ya karbi ke din mota daga hannun siddeeq da kansa yaja ya nufi makarantarsu Ameenatou Kai tsaye.

Yana Isa ana tayar dasu Kuma Hafiz ma Yana Isa daukota Dan haka Koda ta fito cikin doguwar hijabinta akansa idanuwanta suka fara sauka Yana tsaye jikin motarsa Yana waya ahankali kaman mara lafiya kyakkyawar fuskansa ta fada kadan gaba Daya ya juyo hankali da idanuwan duk Wanda ya fito makarantar dama masu wucewa akansa sbd ganin bature tsaye bakin makarantar tasu.

Waya yakeyi Amma Shima tinda ta fito idanuwansa na kanta yanajin jikinsa na mutuwa zuciyarsama sanyi tayi Dan baisan wane irin so ne yakewa Ameenatun ba.

Ganinsa itama ya Sakata sakin kyakkyawar murmushi tana Dan dauke idanuwanta daga kansa Dan kuwa Jin tayi ganinsa ma gaba Daya ya Sakata Jin wani farin ciki me yawa gashi tana son tayi murna sosai a fili Amma batason Yan makarantar Susan shi zata aura su fara kalle mata shi Dan gulmansu.

Nufosu tayi zata Bude Baki tayi magana Hafiz ya jefa mata wani kallan Daya sakata nutsuwa tana hadiye zancen Daya fadawa Haroon na kewan datai masa me tsanani.

Kashe wayarsa yayi Yana kallanta fuskansa daukeda murmushi Mai bayyanarda farin ciki yace

“Barka da fitowa Budurwan Babbah”

Wani sabon farin ciki taji ya rufeta sedai narke fuska tayi tana qasa qasa da murya kada Hafiz yaji tace masa

“Yanzu ba budurwan Babbah bace ai na sauya suna”

Mota ya Bude mata ya shiga ya rufe mata Saida ya zagaya ya shiga ya zauna Hafiz ma ya shigo kafin ya kalleta Yana tayar da motan yace

“Yanzu yar budurwan Barrister ce ko??

Wani sabon dadin taji Yana hararan Hafiz da Shima ita yaketa harara kaman idanuwansa zasu fado Amma taqi kallansa bare taga kwabar dayake mata ya ido sbd sakarcin Data Saba yi musu hadda Haroon din kada tayi a gaban makarantar cikin bainar jamaa.

A hanya kafin su Isa gida guri uku tana sakawa ana biyawa sbd siyan wani littafinta na islamiya da zata dashi gobe kafin suka Isa gida anata kokarin shiga sallan magrib Dan haka Haroon din Bai shiga ba alwala kawai sukai a waje suka wuce masallaci ita Kuma ta shige gida.

Saida sukai ishai suka shigo gidan anan Haroon yaci abincin Dare tareda su Babbah na tambayar yanda ya baro mutanen gida.

Irin son dayake mata itama take masa basa buqatan ma wai saisun kebe sbd a jininsu suke jinsa shiyasa duk firar da sukeyi anan dai tareda kowa tsakar gida ake yinta Kuma ahakan suke soyewansu a gaban su Babbah Dan shi Kam idanuwansa ne basa iya kaucewa daga kallanta matiqar tana gurinda yake ita kanta kallansa shine ke sake sakawa duk tana sake shagwabe masa ko agaban su Babbah ne kuwa sai idan Hafiz ya gaji da sakarcin ya dinga fada kenan Yana hararta idan Haroon din ya tafi.

Washe gari ne zaa tafi da Ameenatou Abuja gurin rubuta jamb nata Daman hadda shi ne ya Saka Haroon din dawowa da wuri Kuma kaman yanda yaso university na Lagos aka cika Mata Dan haka tin 6 da mintina ya iso gidan da motarsa Daman Abdul tini ya shirya itama duk rigimarta Saida aka lallabata tayi wanka tin asuba ta shirya dadah ta shirya mata abincin karyawa da wuri Babbah ma sai addua yake binta da ita Yana cewa saita cinye har marking din Daya wuce Wanda akeso.

Abuja zatai jamb din Dan haka Babu Bata time suka fito itada Yaya Abdul da Haroon din suka kama hanyar Abuja idanuwan Haroon na cikin mirror Yana kallanta itama shi take kalla suna jifan juna da murmushi tana masa magana kadan kadan kaja Yaya Abdul din yaji Mai take fada masa batasan Yana ganinta ba yayi mata banza sbd yasan ma maganar idan yayi Bata bakinsa zaiyi Dan haka yayi kaman ma baisan me sukeyi ba fatansu dai kar Haroon din ya jefar dasu gurin wannan mayen kallan nasa da kullum sai Babbah yace tsoron yakeyi Haroon din ya cinye masa ita da ido ta rame kafin a tashi auren.

Sai 3 suka dawo gida a gajiye budurwan gidan ta dawo harma da zazzabi sbd kaf rayuwarta Bata taba Shan wahalan tafiya ko wata yar gwagwarmayar ba sai yau duk da komai na gata Akai mata Dan kuwa ko Rana Haroon dinta Bai bari ta shiga ba Saida zata shiga exams din ta fito mota hakama bayan fitowanta lafiyayyar tsadaddiyar restaurant yakaisu sukaci abinci Amma Sam Bata iya cin wani abincin ba sbd gajiya gida kawai takeso karshe ma haka suka koma daga shi har Abdul din suna lallabata har aka iso gidan.

Haroon ajiyesu kawai yayi ya wuce Shima Dan haka wanka dadah ta taimaka mata Tayo ta zo ta kwanta take bacci ya dauketa sedai Koda yamma tayi zazzabi sosaine ya rufeta Dan haka hankalin dadah ya Dan tashi zuwa dare Saida aka Kaita chemist kafin su dawo zazzabin ya Dan saketa Se zuwa dare ya sake dawowa.

Koda gari ya waye Haroon Bai Isa gurin aikinsa ba Jin rashin lafiyanta Kai tsaye gidan ya taho karshe dai asibiti aka kwasa aka Kaita duk da narkewanta ne yake Saka ciwon zama wani babba.

Suna zuwa haka aka kwantar da ita sbd ganin yanda hankalin duka ahalin ya tashi hakama Haroon seelah din.

Kwananta Daya a asibitin aka sallameta bayan Haroon yagama lalacewa akanta tareda mantawa da aikin dayake gabansa Wanda duk iya kokari da sadaukarwan siddeeq gurin ganin project din ya tafi daidai ko kadan ne Hakan Bai faru ba Dan haka yake cikin tashin hankali da rashin nutsuwa.

Aikuwa Haroon na dawowa hayyacinsa ya nutsu ya fahimci gagarumar tashin hankalin Dake gabansa take ya shiga firgici Shima Dan tini ma sbd sakacinsu aka sace plans da komai da komai na project din.

Wannan mummunan tashin hankalin ya kusan Sakasa zaucewa Dan kuwa Yanke jiki yayi ya Fadi Saida siddeeq da sauran ma’aikatan suka taresa sedai gaba Daya Jin yayi Yana fita hayyacinsa kansa na Neman Juyewa hannuwansa na rawa.

Gaggawan mayar dashi hotel siddeeq yayi Shima nasa hankalin baa kwance ba Dan kuwa yasan ko Dad yaji wannan zancen sake samun hawan jini zeyi gashi Babu ya yanda zata yiyu cikin qanqanin lokaci su hada sabuwar plan din dazata sakasu Kai labarin wannan project da aka fara.

Haroon Neman zaucewa yafara yi zuciyarta na tsananta bugun Daya wuce misali hakama baisan ta inda zai fara ba.

****Dad Lameenu Dake zaune tareda Mam a palonsu na office suna magana wayarsa ce tayi ringing Ya juya ahankali ya Kalli sunan me Kiran yaga BB ne Dan haka Kai tsaye ya dauka tareda Kai wayar kunnensa Yana cewa

“Yes BB”

Bayanin komai daki daki BB ya fara korowa tin daga kan sunayen ahalin gidan Babbah da Kuma yanda Haroon gaba Daya rayuwarsa ta mace akan yarinyar gidan da Baya gane komai ba a yanzu idan ba abinda ya shafeta ba harma da bautawan dayake musu da gagarumar tsautsayi da aka samu akan project din….

Dad Lameenu Bai gama Jin karshen zancen ba wata mummunan zufa ta tsinke masa Yana cewa

“What???
Yaushe wannan babban balain ya samu??
Ina Haroon din yake yanzu??

Mam na Jin Hakan ya ajiye wayar hannunsa Daya karanta wani article da aka rubuta gameda rushewan da SEELAHs keyi a boye batareda sun bari duniya ta saniba.

Ajiye wayar yayi Yana Dan rintse idanuwansa da suka fara sauyawa Dan kuwa Yana fatan ba abinda zuciyarsa ke Saka masa bane zaiji daga Lameenun.

Cikin tashin hankali lameenu ya buqaci ganin BB yanzu yanzu Dan zuciyarsa bugawa zatai idan Yana sauraron wannan mummunan tashin hankalin ta waya.

Kashe wayar yayi Yana kasa kallan Mam da shima ya kasa tambayar Lameenun komai BB din yake Jira yaji komai Dalla dalla daga bakinsa.

Kafin BB ya iso daga Mam har lameenu da jininsa ya Dade da Hawa Dan tini aka kirawo likita Yana cikin auna BP dinsa BB ya iso take ya sallami likitan akan saisun gama magana.

iPad din hannun BB ya fara kamo hotunansu Hafiz da Yan gidan kaf ya ajiye ipad din gabansu bayan ya kamo hoton Ameenatou datake sanye cikin hijab dinta na islamiya tana murmushi asalin kyanta da kuruciyarta a bayyane tana kallan gefe Dan kuwa batasan ana daukanta hoton bama.

Bayani Daya bayan Daya a tsanake BB yafara jerowa Wanda yayi mugun girgiza su musamman Mam Dan kuwa Bai taba tinanin Shima Haroon zai fada irin kaddarar Dan uwansa ba ta yiwa mace son da Bai kamata ba adaidai lokacinda suke buqatan nutsuwansa da hankalinsa tareda sadaukarwansa fiyeda komai a duniya yanzu.

Ameenatou dukkaninsu suka zubawa idanuwansu da sukai jajir,

Tayaya Haroon zai bari zuciyarsa ta mutu akan mace bayan yasan Menene a gabansu,
Tayaya Haroon zai bari mace ta shiga zuciyarsa,
Tayaya zasu iya samun yanda suke so daga zuciyar Daya mutu akan mace.

Kenan shi tasa mummunan kaddarar akan matan da yayansa suke so ne ko me?
Shima Haroon macen ce zata shiga tsakaninsa da ita?
Ta Ina zai fara karban wannan kaddarar ta Haroon bayan haryanxu Bai fito daga baqin ciki da radadin ta Jamaal ba.

Wani nauyi kirjinsa yayi Yana tafasa da wani irin zafi da radadin da baisan mezaiyiba akan Haroon din Daya kashesu da ransu a Rana tsaka.

Lameenu da tini jininsa ya sake hayewa akan babban tashin hankalin da Basu Saka masa Rana ba da sauri aka sake dawo da likita.

Da sauri likita ya dawo Yana cewa a kwantar masa dashi flat.

Mam tsaban tafasa da qunan da zuciyarsa keyi Jin yayi Haroon baida sauran amfani a garesa ko kadan Dan haka take ya Bada umarnin a Siya masa ticket a ranar zashi Nasarawan.

Lameenu na Jin Hakan yaso wartsakewa su tafi Amma Ina hawan jinin ya sharbesa da kyau Dan haka Yana ji Yana Gani Mam din ya tafi.

MAMUH

DR JEEY

AMEENATOU

MAM SEELAH

BABBAH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

37
Motoci ne na alfamar guda biyu harda securities suka dauko Alh Mam seelah daga airport.

Wayarsa Dake gefensa ya dauka tareda kasheta gabaki dayanta Dan kuwa Baya buqatan Kiran kowa sbd har lokacin zuciyarsa a cikin wani matsanancin zafi da radadin take Mai tsanani.

Daga Haroon har sauran ma’aikatansu manya da abokan huldan Babu Wanda yasan da zuwansa a ranar Kuma aaukan dare sukai Dan haka Kai tsaye masaukinsa Dake cikin Abuja aka nufa dashi Saida safe zai fuskanci Haroon, Haroon dinma ya fuskacesa.

Bayan samun nutsuwa da komai cikin Daren kasa tintsawa yayi ya shiga tinani masu zurfi da sakawa da warwaran ta Ina zai bullowa wannan masifu haka wani bayan wani,

Idan har Haroon na son wannan yarinyar sosai Yana buqatan sauya ha yar handling na abubuwan ta wata hanyar ba irin hanyar dayayi ta farko ba ta rabasa da Jamaal a daidai lokacin dayafi buqatansa da sonsa a kusa fiyeda komai dayake buqata a duniya Dan ko dukiyar Omar da sukeso idan basuda tasu dukiyar tayaya zasu karbeta?

Dole Yana buqatan sauya takun kammala komai cikin hanya mafi sanyi da karfin gaske Amma kwata kwata Babu maganar yabar Haroon yin auren wannan auren a yanzu Dan baima gama zama me amfanin dasuke buqatan ya zama ba ya moru bare idan yayi auren gaba Daya qarasa zama mara amfanin zeyi Kuma sai yanda mace tayi dashi Wanda baqin cikin haka zai iya sakashi yafesa ko illatasa Dan haka bazai taba barin ayi Hakan ba a yanzu saiyaga sauyin Haroon din.

**Har washe gari Haroon Baya cikin cikakkiyar lafiyan hankalinsa Dan shock da tsoron da zuciyarsa take ciki tareda mummunan firgici da tashin hankali ya Hanasa dawowa daidai duk da maganin Daya kwana Yana Sha a cikinsa Wanda harya wuce kaidarsa.

Ya boye kansa bayan siddeeq Babu Wanda yake iya ganinsa duk da ma’aikatansu da yawa dakeson ganinsa da masu zuwa da masu bugo waya duk ya kasa ganin kowa sbd state din dayake ciki bamai dubuwa bane hakama siddeeq din kansa duk ya dage sosai da kokarin hada mafitar gagurumar matsalar shiyasa Shima kansa Baya guri Daya.

Duk daqiqa Daya Dake wucewa sai Haroon ya Tina mahaifinsa da abinda zai iya biyo bayan wannan mummunan aikin kaddarar Daya samesa Dan haka hankalinsa ke sake tashi.

Tinda safe ya samu labarin Dad dinsa na Abuja daga bakin siddeeq Dan haka cikin sabon rikicewa duk da halin dayake ciki ya shirya ya fita aiki Dan Neman mafita koman kankantarta akan aikin kafin Dad ya iso Nasarawan.

Hafiz da siddeeq ganin Halinda yake ciki yana aiki gaba Daya cikin ficewa hayyacinsa riqesa sukai tareda zaunar dashi sai a lokacin idanuwansa suka ciko da wasu irin hawaye masu radadin gaske.

Kallan Hafiz siddeeq yayi tareda cewa ya tafi aikinsa kawai inshallah zaa samu mafita.

Dayake duk ma’aikatansu manya da wainda sukeda kusanci sosai irin Hafiz sunsan ansamu gagarumar matsala Amma bayansu Babu Wanda ya sani shiyasa Hafiz yake cikin damuwa sosai na ganin Halinda Haroon ya shiga akan Hakan.

Kasa aikin yayi ya taho gida Shima bayan siddeeq ya sauke Haroon din sunbar site gaba Daya Dan ciwonsa Daya tashi gadan gadan a gurin tin kafin kowa ya fahimci wani abu ko a gane musamman Hafiz da bazasu so yagani ko ya san ciwon Haroon din ba.

Yana Isa gida jikinsa duk a mace zuciyarsa ba dadi,
Bai boyewa su Babbah ba ya sanar dashi damuwa me tsananin da Haroon yake ciki take Babbah ya daga wayarsa ya Saka Kiran Haroon din Dan basa kwarin gwiwa da adduar samun mafita da nasara a duk inda take Amma wayar Haroon din a kashe Bata shiga kwata kwata.

Ameenatou ma Kiran nasa ta Saka kaman zatai kuka Jin halinda yake ciki Amma kayinsa Baya shiga kwata kwata.
Yaya Abdul ma ya gwada Kiran da tasa wayar duk dai Bata shiga.

Dadah da tashiga damuwar itama kallan Abdul tayi bayan sunkai har kusan rana Ana kiransa baa samu tace

“Bara na sauke abinci saina hada masa nasa kwando ka Kai masa saika dubo mana lafiyar tasa tinda Kiran ya kasa samuwa”

Ameenatou na Jin Hakan ta marairaice fuska akan zata bisa
Dadah ta girgiza mata Kai tana cewa

“Kul na haneki da wanna tinanin Dan Babu inda Zaki….

Karbe zancen Abdul yayi da cewa

“Har sai kin fada? Ni hauka nakeyi zanje da ita gurinsa”

Tana Jin Hakan ta Bata fuska tana komawa jikin dadah din ta kwanta tana kokarin fara Hawaye Hafiz Dake gefen Babbah Yana rubuta text yace

“Kina tsiyayo Hawaye a gurin Nan saina fasa ruwan idonki Daya muga karshen hawayen rainin wayo.”

Katsesa babba yayi da cewa

“Ba zataiba ta fasa”
Maida kallansa yayi kan Ameenatoun Yana cewa

“Mayar da abinki yar budurwan gidan Babbah tare zamu dubosa idan naje ai kaman kinje ne ko??”

Gyada Kai tayi tana mayar da hawayenta tana hararan inda Hafiz yake zaune Yana jifanta da tasa hararar me zafi Shima.

Saida sukai sallah sukaci abinci dayake Babbah baida gurin zuwa ranar sai suka fita tareda Abdul din Dan dubo Haroon din.

****Isarsu yayi daidai da isowan Alh Mam seelah Wanda tin a masaukin Haroon din ya tabbatarda Haroon Baya cikin cikakkiyar hankalinsa me amfani Dan kuwa duk kyau da tsananin tsadan hotel din ganin yayi ‘dan cikinsa jinin Seelahs yafi karfin zama yayi rayuwa a gurin Amma sbd ba shine ya kawosa ba abinda ya kawosa yafi wannan mahimmanci a yanzu.

Babban abinda yasa yake fatan ganawar gaske suyi budaddiyar wasika da Haroon din shine yasan Lameenu akan lamari na faduwa bayada hakuri,
Bayason abinda zai Saka Lameenu ya kasa hakurin dazai iya aikata wani abin batareda saninsu ba Dan idan har zaisa abibiya lamuran Haroon din batareda saninsa ba zai iya rashin hakurin yin wani abun batareda saninsa ba haka zalika alkawarinsu ne dayake yawo a jininsu Dan zuciyarsu kowa ya shiga hanyar shiga tsakaninsu da arzikinsu ciresa sukeyi daga hanyar kwata kwata Dan haka yake buqatan Saka hankali acikin tosashiyar kwakwalwan Haroon din idan ba Hakan ba zai barwa lameenu kulawa da komai Wanda yasan me Hakan ke nufi.

Su babbah ne suka Riga Mam din isowa Dan haka ko ganinsa Basu samu yi ba Yana bedroom dinsa Dayake suite ne yake rayuwa a ciki saiga shigowan siddeeq a gaba Alh Mam seelah din da securities dinsa duk a tsaye bakin Kofar dakin ya shigo siddeeq ya rufe kofar Yana biyo bayansa cikin tsananin girmamawa.

Yaya Abdul na ganin Hakan ya miqe a natse daga inda yake zaune Shima cikin nuna girmamawa Yana masa barka da zuwa cikeda nutsuwa.

Babbah ma miqewan yayi Yanawa mahaifin Haroon din barka da zuwa a mutunce suna kallan juna sbd kowannensu sai fuskan tayi masa kama da Wanda ya sani Amma sbd kada su kure juna da kallo sai kowannensu ya Dan dauke kallansa Dad din Yana amsa gaisuwan a mutunce Shima Dan Daman shi mutum ne Daya iya taku da mu’amalantar mutane shiyasa SEELAHs sukeda mutunci sosai a idanuwan mutane sbd iya tafiyan da lamuransa.

Yanda suka gaisa a mutunce Babu girman Kai ko nuna musu banbanci ya Saka su Babbah din sukai masa sallama suka tafiyarsu Dan Basu guri da ‘dansa batareda Haroon din ya fito ba Dan abinda Basu saniba Haroon din Yana jinsu Amma bazai iya fitowa a halinda yake ciki ba su gansa.

Saida suka fice siddeeq yaje rakasu kafin Haroon din ya fito hannuwansa na tsananin rawa kansa a qasa idanuwansa jajir Babu kyan Gani hakama a jiqe yake da zufa Mai tsananin gaske,

Babu inda yakejin azaba me tsananin gaske kaman a tsakiyar kansa da kirjinsa,

Jin muryan Dad dinsa a dakin ya karasa karya dukkanin Wani karfin halinsa shiyasa ya kasa fitowa Saida su Babbah suka fice Dan ganinsa a wannan halin na mafi Munin rauni zai karya zuciyoyinsu akansa gameda Basu auren macen da bayajin zai iya rayuwar Nan Babu ita su kuwa Ayanda suke tsananin kaunar Ameenatunsu bayajin zasu taba bawa Wanda bazai iya tsayuwa a gaban mahaifinsa bama ya dago kansa aurenta sbd tinanin bazai iya Bata kariya ba ko kare martabarta.

Hannuwansa Dake rawa sosai kaman zasu qanqame yayi Baya dasu Yana kasa dagowa har lokacin kansa Juyewa yake Neman yi.

Zuba masa nasa jajayen idanuwan Mam yaji Yana kallansa sbd baisan ma me zai fara dashi ba sbd baqin ciki da damuwa me tsananin gaske Dan Shima Yana tsaka me wuyar da baisan ta inda zai fara bullowa zancen ba.

Tsadaddiyar wayarsa Daya ajiye gefensa bayan ya zauna ya miqa hannu ya dauka tareda kunnawa ya Nemo hoton Ameenatou ya ajiyewa Haroon din kan centr table Dake gabansa batareda yace komai ba tukuna.

Haroon Daya kasa motsawa bare magana dago jajayen idanuwansa yayi ya Kalli wayar da Dad din ya ajiye masa idanuwan suka sauka akan hoton Ameenatou Dake bayyane a ciki tana murmushi sanye da hijab din islamiya.

Mummunan bugawa kirjinsa yayi ya dago idanuwan da sauri sai alokacin ya Kalli Dad din da Shima shi yake kalla Yana kokarin karantar yanayinsa.

Hannuwansa Dake tsananin rawa ya sake kankamewa Yana sake kallan Dad din da kyau kafin ya Bude bakinsa Dake rawa da muryan Dake bayyanarda tashin hankalin dayafi wanda yake ciki yace

“Dad Kayi hakuri na…..

Katsesa Dad din yayi da cewa

“Ka manta mace ce ta Raba Dan uwanka da mahaifinsa rabuwa ta har abada?
Ka manta matsalolin rayuwar da muke cikinsu duka ayanzu duk sbd macen da Dan uwanka ya so ne fiyeda kansa da ni mahaifinsa?

Wasu Hawaye ne masu tsananin zafi da radadi suka gangarowa Haroon Dan Bai taba tinanin samun kansa a cikin irin yanayin da Jamaal ya samu kansa ba,
Gwara kaddarar Jamaal sbd shi yanada jarumta da karfin zuciyarsa fuskantar duk Wanda zai shiga tsakaninsa da farin cikinsa matars wadda ya tsayawa har ranar karshenta harma a bayan ranta ya tsayawa macen dayake so da dukkanin zuciyarsa.

Wasu zafafan hawayen ne suka sake gangaro masa Yana rintse idanuwansa sbd Yana fatan inama wannan jarumtar zata shigesa ya tsaya akan macen dayakewa mugun son dayakejin yafi Wanda Dan uwansa yayiwa tasa macen.

Hawayen Dake zubawa daga idanuwan Haroon dinne masu bayyanarda tsananin radadin da zuciyarsa take ciki ya Saka Dad zubawa masa idanuwansa hankalinsa na Neman tashi Dan kuwa duk tsananin quncin da rayuwar Haroon din take ciki Bai taba zubar da Hawaye ba sai yanxu.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

38
Ahankali Haroon din yayi qasa sbd kasa riqe jikinsa Dake kakkarwa sosai da yayi har lokacin idanuwansa na kan hoton Ameenatou Dake kan wayar Dad din Yana tsoron me Dad zeyi da hoton nata.

Zuciyar Dad Dake tsallen tafasa tana quna sosai akan abinda idanuwansa ke gane masa na azabbiyar Son yarinyar dayake hangowa a idanuwa da hawayen ‘dansa kwalli Daya daya rage a hannunsa.

Cikin sanyi da tattara nutsuwansa dan fahimtar komai yanda zai fishesa ya Kalli wayarsa shima tareda zubawa hoton Ameenatou idanuwansa zuciyarsa na shiga shakka da rarrabar tinani akan Aminta da ita ko sabanin Hakan sbd bazaiso tarihi ya Kuma maimaita kansa ba.

Dawo da kallansa yayi akan Haroon Yana dauke wayarsa daga kan table din yace

“Sbd itane ka tattarawa dukkanin nutsuwansa kayi Watsi da ita daga aikin dayake gabanka na cika mun alkawarin dakai na sakani alfahari dakai??
Kasan wane yaqin ne a gabanmu akan wannan masifar daka jefamu akan mace?

Muryansa na kasa fitowa sosai yafara kokarin magana Amma zuwa lokacin ran Dad din ya gama tafasa Dan haka ko sauraronsa beyiba ya miqe tsaye Yana cewa

“Ka shirya a yau din zaka bar Nasarawa ban aminta da zamanka ananba bare sake ziyartar Nan din,

Kasan me zai faru daga lokacin da na sake samun labarin ko ‘dan uwan yarinyar Nan Daya ka sake muamala dashi???

Zasu bata ne gabaki dayansu danginta bazaka sake samun ko labarin Wanda ya taba saninsu ba bare sanin duniyar da suka tafi…

Qarasa zubewa yayi gaban Dad din Yana fashewa da wani irin kuka Mai tsananin tausayi da tashin hankali tareda Neman ficewa hayyaci Yana bawa Dad din hakuri jikinsa da hannuwansa na tsananta rawar Daya fara bawa Dad din mamaki da tsoro ya janye kafafunsa da karfi cikin zafi zaiyi magana Haroon din ya sake rarrafowa wannan Karan Yana rokonsa da cewa

“Dad Dan Allah kayi hakuri kada ka hanani Ameenatou,
Itace ke bawa zuciyata karfin hali da zuciyan da Banda shi,
Dad nayi Maka alkawarin wanna Karan wlh zan cika dukkanin buri da abinda kakeso idan ka barni da ita,
Dan Allah Dad ban taba tambayarka komai ba sai ayau din Ina rokon ka barni na aureta nikuma nayi Maka alkawarin zama duka abinda kakeso na zama,
Ka bani Daman karshe Dad zan gyara dukkanin matsalan da aka samu a wannan aikin nayi alkawarin Hakan please Dad.

Tafasa zuciyar Dad din ke karawa yanajin kaman ya shaqe Haroon din da kansa ya qarasashi Amma Kuma zuciyarsa na yaqi da Hakan Dan bayason rasa Dan Daya rage masa.

Rikicewa Haroon yayi ganin Dad din baida niyar sauraronsa hakama yasan kaman yanda Dad din ya fada batar dasu Ameenatou Abu ne me saukin gaske duk da Baya tinanin kashesu zaai ko makamancin hakan Amma dai koma Menene rabasa da Ameenatou kaman rabasa da dukkanin sauran Dan hankalin Daya rage masa ne Dan haka yaji Yana Neman zaucewa gaba Daya Yana tino yanda Jamaal ya rasa fadila har abada sai kawai yaji kansa ya kasa dauka ya sake rarrafowa Yana biyo Dad din cikin matsanancin fita hayyaci daidai Nan siddeeq ya shigo sedai kafin ya karasa gurin Haroon din tini yafara wani irin jijjiga Yana buga kansa da kasa Yana ambatar sunan Dad din Dana Ameenatou batareda ma yasan meyakeyiba.

Jini hancinsa da goshinsa suka fara fitarwa harma da bakinsa Yana wani irin fizga take hankalin Dad din yayi mummunan tashin da baitaba tinanin zaishiga ba ya dawo da sauri Yana Kiran sunan Haroon din da sauri sedai tini ya fice hayyacinsa dukkanin jikinsa na qara jijjiga sosai.

Siddeeq ma cikin matsanancin tashin hankali ya kamo Haroon din Yana janyo pillow na kujera ya Saka masa Akai tareda birkitasa Yana hanasa bubbuga kansa a tiles da jininsa ke fita sosai.

Rasa abinyi Dad yai Yana shiga sabon tashin hankali da mamakin Menene yake faruwa da rayuwar Haroon din,

Badai shi Kuma haukacewa zaiyiba akan mace ba,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun”

Meke faruwa da yayansa?
Innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Duk yanda Dad yake tsammanin lamarin ya wuce Nan sbd Haroon take ya koma tamkar me cikakkiyar tabin kwakwalwa duk tsananin zafi da bacin ran dayazo dashi jin yayi kansa Shima Yana daukan matsanancin zafi.

Siddeeq drawers ya nufa na gado da gaban mirror Yana yamutsa hankali tashe Yana Neman maganinsa Amma kwata kwata ya kasa Gani.

Cikin daga sauti da kidima Dad yake cewa

“Meyake faruwa dashi ne?
Menene Hakan nake Gani?
Ciwon hauka ya kamasa ne kokuwa?
Menene wannan din???

Duk a jere ciki daga murya da tashin hankali yake jero tambayoyi Yana kamo Haroon din Wanda yake jijjiga har lokacin.

A karkarshi pillow siddeeq ya sami maganin bayan ya haukata dakin cikin tashin hankali da mintinan da Basu Fi biyu ba ya iso da sauri yana Bude maganin ya kamo kan Haroon ya Saka masa
Tsaban rudewa Dad dinne da kansa ya dauko ruwa ya miqawa siddeeq ya basa rabi na shiga bakinsa Rabi na zubewa harya hadiye maganin.

Sakewa jikinsa yayi Dad yayi gaggawan Bada umarnin a fito dashi zuwa asibiti shi kansa siddeeq a daidai wannan lokacin yasan likitocin gaske Haroon yake buqata Dan haka ba Bata lokaci aka kwashi Haroon din sai asibiti.

Suna zuwa aka karbesa sbd duka jikinsa ya Dena rawa ko wani abin sai kawai aka miqasa da cewan faduwa yayi.

Dayake Mam yasan abinda zai iya faruwa na zuwan Yan jarida take ya Bada izinin securities kada su bar yan jarida zuwa ko sanin komai.

Har yamma sosai suna asibitin Haroon Bai farfado ba,
Dad magana yayi da siddeeq sosai yaji komai gameda ciwon Haroon da lokacinda ya fara take ya fahimci ba karamar illa maganinsu keyi masa ba Ashe Dan haka take ya sake shiga tashin hankali da damuwan kada Yan jarida ko kadan Susan dansa Barr Haroon seelah na fama da tabin kwakwalwa.

A Daren suka koma Abuja dashi sbd hankalin Dad Bai kwanta ba anan din.

Su Babbah da suka samu labarin anbar Nasarawan da Haroon hankalinsu tashi yayi Dan kuwa ciwonsa kenan yayi tsananin gaske haka suka ringa Kila mintina bayan mintina Dan Jin lafiyansa.

A cikin kwana da wunin Dad yayi sakawa da warwaran datafi dari da hamshin hakama Dad Lameenu ma hakanan ya lallabo ya taho sbd yasan Mam din na cikin damuwa da matsanancin hali Dan haka ya taho su fuskanci lamarin tare duk da Shima ya kasa warware sbd Bai dawo daidaiba idan ba Jin yayi sun samu mafitan warwara ba.

A cikin kwana da wuni Dad ya tabbatarda irin tsananin so da kwallafa Rai da Haroon yayi akan AMEENATOU sunan Daya riqe Kai tsaye sbd Tinanin dasuketa yawo akansa.

A karon farko da zai sauya raayinsa zuwa wani raayin Dan cimma burinsa cikin sauri da samun mafita biyu,tasa data rasa ‘dansa.

Shi kansa Dad Lameenu yashiga firgicin tarihin dayake Neman maimaita kansa,
Idan sun rasa Jamaal sun tabarbare haka to Haroon dinma dasuke ganin baida amfani suna rasasa karasa tabarbarewa zasuyi komai yazo karshe shikenan.

Farfadowan Haroon Saida ya bawa dukkaninsu tausayi sbd yanajin jikin sosai Dan wanna Karan maganin ya Riga yayi masa illa sosai da Babu wani abinda zaa iya yi sai ikon Allah.

Su Dad kasa barin kowa yaji zancen sukai sbd a nasu tinanin maganinsu ne yayi masa wannan mummunan illar.

Duk tsananin halin dayake ciki kallan Dad dinsa yayi har lokacin yanajin raunin batawa su Dad din Rai dayayi da asarar da shi kansa baisan ta inda zai fara gyara ba.

Rokonsa gafara da sake basa Dama shine abi farko Daya furta Yana rintse idanuwansa.

numfashi Dad din ya sauke tareda Gyara zamansa Yana kallansa cikin nutsuwa yace

“Zan sake baka Daman karshen Amma ba iya akan aikin kadai ba,
Zan nema Maka auren Ameenatou Amma sai idan ka cika alkawarinka ka gyara mummunan Barna da Tsaka me wuyan daka Saka SEELAHs gaba Dayanta aciki idan ba Hakan ba ka manta da maganar aurenta Dan kuwa har abada bazaka auretaba idan ba Hakan ne ya faru ba”

Rintse idanuwansa yayi hawayen ciki masu dumi suna gangarowa ya gyada kansa cikin wani irin sanyin jikin da mutuwar jikin batareda ya iya cewa komaiba sai tsananin tsoro da shakkan Dayake mamayesa.

Dad Lameenu da Baice komaiba gyara zama yayi Yana kallan Haroon din cikin nutsuwa Shima ya Bude Baki yace

“Haroon nayi Maka alkawarin bazamu bar garin Nan ba ayau sai munje munyi gaisuwar iyaye da iyayenta sbd Neman Maka aurenta idan har zaka nutsuwa ka fuskanci nauyin dayake kanka sbd Kaine kaidai zaka iya gyara wannan Barnar data riskemu sbd kafi kowa sanin halinda muke Neman fadawa idan bamu farfado ba.

Tinda suke magana idanuwansa a rufe suka Hawaye masu zafi na gangarowa a acikinsu Saida Dad Lameenu yayi masa alkawarin nema masa auren ya Bude idanuwan ahankali ya kallesa Yana sauke Kai kasa.

Dad dinsa ma Jin yayi yayi Naam da Hakan Dan shine maslaharsu ayanzu kada su maimaita kuskuren Baya gwara su nema masa auren su juyasa akan abinda sukeso tinda zai iya komai akanta din.

Duk yanda wani zai samu Daman sanin matsalar ciwon Haroon Saida Dad ya tabbatarda Bata fita ba hatta siddeeq Bai bari likitocin sun bari yasan duk wani abinda aka bincika aka Gano ba har suka sake kwana biyu a garin Akai sallamarsa a ranar suka kwasa zuwa Nasarawa Dan Kai gaisuwan Neman auren.

MAMUH.

39
**Su babbah da suka samu labarin zuwan da Dad din zasuyi gaisuwa tini aka gyara koina hatta kofar gidansa Saida aka share har kofar gidan makota aka shirya tsaf Dan tarbonsu da Aminansa guda biyu da zasu tayasa karban gaisuwan.

Dayake ranar su Dad din zasu koma da wuri suka iso guraren karfe daya na Rana Dan haka su Babbah suka tarbesu da girmamawa da mutuntawa sosai har cikin fara isowan gidan babban suka zauna a babbar dadduman da aka shimfida musu me kyau.

Dad Lameenu Dayake amsa gaisuwansu cikin girmamawa da kulawa sosai Shima tareda farin ciki me tsananin da tin anan aka fara farin cikin Samun Sirikai irinsu da duk kudi da matsayinsu sunsan mutuncin mutane da iya mu’amalantarsu.

Babbah Dad Lameenu yayi kallan tsaf Mintina Yana tantance kamannin nasa da son tabbatarda idan shine Wanda yake tinanin shi dinne.

Ganin irin kallan da Alh Lameenu kewa Babbah ya sakashi sai farin ciki yake sake shiga Yana sake musu barka da zuwa kafin ya tambaya jikin Haroon cikin kulawa sosai Yana dorawa da cewa sai anjima su Abdul su shiga dubasa Inshallah.

Abinda ya tarasu suka shiga gabatarwa Babu wani Bata lokaci suka gabatar da kansu da Neman auren Ameenatou da suka zo nemawa dansu Haroon Wanda su Babbah sun sanshi kuma sunsan aikinsa da halayensa daidai gwargwado.

Naam su Babbah sukai kafin suka suka sake gabatar da kansu da shi babban amatsayin mahaifin Ameenatou wadda shine ya haifa abarsa da cikinsa Kuma yayi na’am da Hakan ya Kuma bawa Haroon aurenta.

Farin ciki da hamdala suka ringa miqawa ana sake taya juna murna Dad Lameenu ya cire kudin Neman auren Naira dubu dari biyar ya bayar kafin suka sake miqa godiyarsu har lokacin zuciyar lameenu wani tsalle takeyi cikin rudewa da rikicewa Dan kuwa ya sake tabbatarda Babbah ne suka tana Gani asibiti gurin Omar a lokacinda aka taba Kai masa attack idan Bai mantaba Kuma ya sake dubawa ya tabbata Babbah ne ya Gani Wlh.

Abdul da shine babban yayan Ameenatou Kuma dashi Akai zaman Neman auren Alh Lameenu ya kalla cikin kulawa Yana tambayarsa Aikinsa da karatunsa.

Cikin nutsuwa da ladabi Abdul din ya amsa masa matsayin karatunsa da aikin dayake yi.

Take Alh Lameenun ya nuna raayinsa na Taimkawa yace Abdul din ya hada takardunsa zai Aiko a karba a aika masa Lagos.

Godiya Abdul din yayi su Babbah dasu Alh sabi’u makocin Babbah godiya sukai suna sake nuna Jin dadinsu kafin su Dad suka saki jiki sosai sukai fira da maganganu dasu babban anan ma sukai sallah azahar kafin suka Shirin tafiya su Babbah suka rakosu har waje inda motocinsu da securities dinsu suke suka shiga take aka bar gurin dasu.

Suna barin gurin Dad Lameenu zufan dayake hadawa tin acan yana shanye abinsa a jikinsa ya zari tissue ya goge kafin ya Ciro wayarsa.

Hotunan da BB ya turo musu nasu babban ya Nemo hannuwansa na Dan rawa ya Nemo na Babbah ya zuba masa idanuwansa.

Mam da zuciyarsa kwata kwata Bata cikin dadi Baida energy din tambayar abinda yake faruwa sbd bayajin zai taba barin ya hada zuria dasu Babbah
Ya nema auren ne sbd yana buqatan Haroon din sbd ya Jamaal ya dawo garesa Amma Badan Hakan ba bayajin zai tana yadda ya Kai kansa Neman auren.

Lameenu Daya sake goge zufansa miqewa Mam wayar yayi Yana cewa

“Wannan shine fitilar da zata kaimu ga sanin duk inda dangin matar Omar suke sbd samun Magajinsa”

Kallan wayar Mam yayi kansa na tsananin sarawa da nauyi Amma Jin Abinda Lameenu ya fada ya sakashi cire hannunsa daga goshinsa Daya dafe idanuwansa a lumshe.

Kallan Lameenu din yayi bayan ya Kalli Babbah a wayar Yana jiran bayaninsa.

Cikin nutsuwa lameenu ya tinatar dashi ganin da sukaiwa Babbah a asibiti tareda Omar shekarun Baya.

A saninsu wancan lokacin daga kauyensu Omar yace musu babban yake Amma basusan Menene alaqarsa dashi ba Dan haka dole babba yasan waye yayan matar Omar Kuma bazasu rasa sanin komai ta hanyar Saba Daman a bagiren Neman ko mutum Daya daga kauyen suke amma tsawon shekaru ankasa samu.

Wani sanyayyan sanyi ne ya ciked zuciyar Mam take yaji nauyin zuciyarsa na rayuwa sedai bayajin zasu samu yanda suke so idan suna nesa dasu Babbah din.

Lameenu Dayasan dalilinsa Daman kenan na buqatan daukan Abdul aiki take ya Saka kira yace a tanadarwa Abdul din aiki me kyau da gidan zama a Lagos inda zai dauko iyayensa ya dawo dasu.

*Su Babbah kuwa A nasa bangaren sunan jeden da Omar yake amfani dashi shine ya hanasa sanin shima Omar din seelahs ne Dan haka farin cikinsu kawai sukeyi.

Da daddare da kansa shi da su Abdul sukaje suka dubo Haroon din Wanda ya danne ya nuna musu karfin hali duk da Yana cikin tsananin tashin hankali da Tsaka me wuya sbd sanin Neman auren bashine aurenba indai Bai cika alkawarin Daya daukanwa Dad dinsaba,

Bayan tafiyarsu da daddare tsananta damuwansa tayi sbd gwara ace baa nema aure ba zai iya runawa ya hakura da Ameenatou Koda zai rasa ransa Dan kawai yabarsu su ta tsira Amma a yanzu da aka nema masa aurenta yasan ba janyewa sedai Kuma irin kaddarar fadila da Dan uwansa yake guje musu.

A cikin Daren siddeeq ya koma Abuja Bai kwana ba Saida ya samu report na komai da akaiwa Haroon ya turawa JEEY Wanda sakonsu ya isar masa a daren daidai lokacinda ya fito wanka daure da towel dinsa gabaki Daya jikinsa wata irin sheqi takeyi kaman Bai taba Shiga rana ba.

Hannunsa yakai ahankali ya dauki wayar Yana ganin report din ya Bude sakon Kai tsaye Yana karantawa.

Tsayar da fararen idanuwansa masu gigita Wanda suka kalla yayi akan report din idanuwan na sauya ahankali zuwa ja zuciyarsa na daukan wani nauyi take.

Shigowan kira ne ya sakashi rintse idanuwan ya budesu ahankali akan sunan Haroon daya bayyana kan screen din wayar.

Iska me dumi ya sake fitarwa daga bakinsa kafin ya daga Kiran batareda yace komaiba ya Dora wayar a kunnensa Wanda yayi daidai da Haroon din na kasa riqe kansa daga zubar da hawayen radadi da kuncin dayake cin zuciyarsa da rubabbiyar rayuwarsa gaba Daya.

Shiru Jamaal din yayi har lokacin Bai furta komaiba sbd wannan shine Karan farko da Dan uwansa ya bayyanar da tsananin kunci da baqin cikin rayuwar dayake ciki garesa,

Bai taba fada musu rayuwar wulaqanta da qasqantar dayakeyi a hannun su Dad ba,
Bai taba barin sun sani ba,
Bai taba nuna musu ba
Ya shanye komai ya hadiyewa kansa baqin ciki da radadin shi kadai Amma ayau dayake cikin tsananin hali ya kasa danne zuciyarsa daga Neman taimakon Dan uwansa Dan idan ya rasa Ameenatou zai iya rasa rayuwarsa gaba Daya batareda yasan rayuwar tasa tana cikin mummunan hadarin tsaka me wuyar da kowane lokaci komai zai iya faruwa ba.

Kasa magana JEEY yayi sbd sautin fitar kukan Dan uwansa dayake tarwatsa zuciyarsa Yana Kona jinin dayake yawo a jikinsa kawai kashe wayar yayi tareda Saka Kiran Siddeeq wadda Kiran na shiga ya daga cikeda girmamawa.

Magana yayi da siddeeq Yana gamawa ya kashe wayar gabaki dayanta tareda jefar da ita.

****Ameenatou gabaki Daya ta daga hankalin mutanen gidan sbd kwanakin Haroon kusan shida bata samun wayarsa Kuma ya Dena fita koina ko Hafiz yace kwata kwata ya dena fitowa aiki,
Yaya Abdul yaje dubosa harso biyu Amma Sam Baya samunsa hakama siddeeq Sam baa samunsa.

Daga hankalinsu Babbah tayi dadah batada aiki saina rarrashinta Hafiz ma kusan sosai suka damu gurin aiki Amma dai Sir siddeeq yace musu Yana hutawa ne sbd rashin lfy da yayi.

Babbah da kansa yaje dubo Haroon din Amma dai kaman duka kwanakin Bai samu ganinsa ba hotel din sunce Yana Abuja.

Ranarda ya cika sati Hafiz na Isa gurin aiki da safe sunfara aiki kenan lafiyayyar sabuwar motar Haroon Daya sauya batareda sun saniba tayi parking bakin site din.

Siddeeq ne ya tuqo motar Dan haka shine ya fara fitowa kafin aka Bude Dayan bangaren Haroon ya fito sanye cikin black Armani’s da sunglasses Daya masifar fitarda hasken fatarsa dayake wani irin kyallin Daya Saka dukkanin ma’aikatan gurin ajiye aikinsu suna kallansa sbd kwarjininsa na yau din daban yake Dan duk Wanda yake gurin saida kwarjininsa ya cika idanuwansa hakama hasken Daya Kara a kwanakin Dan hutun Daya samu ya bayyana fiyeda mamaki.

Manyan ma’aikatansu da sauran manyan Dake cikin project din tasowa sukai dukkaninsu suna tahowa gurinsa Dan ganin sauyi sosai a fuskansa na Babu sakewa ko kadan Dan Kuma kamewa.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

40
Takowa yayi ahankali Yana nufar cikin site din Kai tsaye dukkanin sauran abokan aikin na biyo bayansa.

Siddeeq Dake gefensa umbrella yafara kokarin Bude masa Amma ya girgiza Kai ahankali batareda ya juyoba yana kallan site din da gaba Daya ma kusan aikin Daya bari bama ko kusa dashi ne ake kan yiba.

Hafiz Daya aje aikinsa Yana goge hannuwansa ya nufi ruwa ya wanke hannun zai nufi inda su Haroon din suke saiyaga sunzo sun wuce ya inda yake tsaye Yana murmushin Jin dadin ganin Haroon din da lafiyar Daya samu wadda ta sauya musu shi gabaki Daya Dan shi kansa Jin yayi gabansa Yana faduwa da ganinsa tsaban cika ido da wani irin sauyawan da yayi Dan har gashin kansa dayake kwance kaman na mace tsaban gyara ya sake sauya musu shi,

Wucesa sukai batareda Haroon ya Kalli inda yake ba sedai Dan gyada Kai da yakeyi a natse cikin wata irin class da kamewa idan sun gaidasa tareda masa barka da dawowa.

Dukkanin Wanda yake gurin kusan mamakinsu a bayyane yake Dan ganinsa sedai Kuma ganin hadda sauyin rashin sakewa a halayyan nasa ya Sakasu shiga taitayinsu harya shige tent din da Akai masa a site sbd aiki da meeting da sauran manyan Dake cikin project din.

Suna shiga sauran ma’aikatan suka tsaya waje shi Kuma da sauran suka shiga Kai tsaye kujeran zama siddeeq ya gyara masa Yana Bude takardun Dake zube a table din Yana dauko wasu Dake gefe Yana Bude masa Suma Yana fara yimasa bayani shi Kuma Yana bin takardun da idanuwansa dasuke farare tas.

Dukkanin sauran Manyan Dake sauraron bayanin siddeeq dayake karantowa shiru sukai suna sauraron bayanin hakama hancinsu na shaqar iskan gurin Daya sauya gaba Daya da qamshin da suka tabbatarda daga jikin Haroon din yake fitowa Dan haka saiyi sukeyi suna kallansa gashi baice komaiba har lokacin sauraron bayaninsu yakeyi Daya bayan Daya kowa na gabatar da nasa bayanin Wanda yake tabbatarda Taron marasa amfanin da aka Tara ne ya Saka aikin duka ya lalace yaqi zuwa koina.

Sun dauki mintina masu yawa anata gabatar da sabbin bayanan Yana sauraronsu kafin suka gama yayi shiru tsawon lokaci kafin ya karbi takardun hannun siddeeq din Kai tsaye ya zuba su cikin takardun da basuda amfani kwata kwata kafin ya dago idanuwansa ya kallesu yace ya bawa kowa hutun kwana uku suje kawai Nan da 3 days za’a gabatar da sabon tsarin project din.

Shiru sukai tareda dagowa suka kallesa sedai Sabon Haroon seelah suke Gani a gabansu ba Wanda suka sani a Baya ba Dan haka cikin girmamawa suka amsa umarninsa suka fito Daya bayan Daya suna son juyawa su saci kallansa Amma ba dama sbd ba fuska hakama kwata kwata ba alaman wasa yakeyi a zancen.

Suna fita rufe idanuwansa yayi ahankali tareda budesu Yana Dan duba time din Tsadaddiyar Rolex din hannunsa kafin ya kalli siddeeq a taqaice yace

“A sanar da dukkanin sauran ma’aikatan da leburas 3days hutun da zaayi Ina buqatan kwanakin”

Cikin girmamawa da yar sakewa siddeeq yace

“Anan ma kana buqatan a tanadi sabon masaukin ne??

Girgiza Kai yayi sbd kwata kwata bazai iya zama anan din na Abuja zai koma daga can zai ringa zuwa.

Fitowa siddeeq yayi ya Tara duka ma’aikatan ya sanar musu hutun da aka samu na kwana uku take suka fara murna da farin ciki Dan haka suka fara hada ayyukansu Dan kammalawa su tafi gida.

Dawowa ciki siddeeq yake kokarin yi Hafiz ya karaso Yana murmushi da sakewa yace

“Oga siddeeq barka da Rana,
Kasan ko yau da safe Saida nayi Kiran wayar Barr Bata shiga Kuma kaima na kira taka itama Bata shiga ba”

Murmushi siddeeq ya sake Yana kallan Hafiz din yace

“Network ne da Kuma Kila sbd inda kan hanya,
Yasu Babbah da Dadah??

“Duk suna lafiya,mutuniyar dai ce Kam ta Hana tsoffin gidan zaman lafiya akan rashin Jin Barr”

Wani murmushin siddeeq ya sake Yana cewa

“Ai yanayin jikin nasa ne Amma inshallah ai yanzu yaji sauki ayyuka dai ne Kam gasunan sun tarar masa Amma dai nasan zai samu time din zuwa”

Suna cikin maganar ya fito daga ciki Yana Amsa waya a kunnensa cikin nutsuwa har lokacin sunglasses dinsa suna fuskansa.

Qamshinsa ne ya fara sauya iskan gurin Hafiz ya zubawa hannuwansa Dake riqe da wayar dayake amsawa cikin wani turancin da kwata kwata Baya gane kalma ko Daya Daya fada duk da Yana Jin turancin daidai gwargwado,
Yatsun hannuwansa da kaman Basu taba shiga Rana ko taba komai ba yake kalla cikin mamakin tayaya mutum zai sauya acikin kwanaki kalilan haka.

Akan fuskarsa dake wani irin kwarjini me kyau da Asalin kyau da Hutu ya zubawa idanuwansa hakama kunnuwansa na sauraron sautin muryansa Dake magana kamanma wani yaren daban yakejin turancin Dan haka Saiya samu kansa da kasa karasawa gurin Haroon din ya tsaya gurin siddeeq Dayake jansa da zancen harya jasa suka bar gurin Yana cewa su barsa yagama waya tukuna.

Waiwayowa kadan yayi ya sake Satan kallan Haroon din Yana tafiya zuciyarsa na shiga shakkar Anya basuyi gaggawan karban maganar auren Haroon akan Ameenatou ba sbd yafi karfinsu sosai da sosai duk Bai lura da Hakan ba sai yanzu dayake Jin Yama kasa kallan cikin idanuwansa tsabar cika masa nasa dayakeyi.

Fira siddeeq yajasa sosai suna tafiya har suka fice gaba Daya daga site din ya fada masa sunanan tafe daga Nan zasu taho gida.

Sallama sukai Hafiz ya wuce gida Kai tsaye Jin suna Nan tafe Dan yasan yau budurwan gidan zata barsu su huta da rigimar rashinsa ba kunya ba tsoron Allah.

Yana wucewa siddeeq ya dawo har lokacin waya yakeyi sedai baima gama ba ya wuce ya nufi mota ya shige siddeeq ya shiga yaja suka bar gurin.

Budurwan Babbah Jin Haroon ya dawo farin cikine ya cike ranta Dan haka ranar ko islamiya qin zuwa tayi tai wanka ta shirya jiransa gashi har lokacin wayarsa Bata shiga Dan haka ta San bazai kwana ba Saiya taho ya ganta.

Su dadah ma Kwanciya hankalinsu yayi musamman Babbah da farko harya shiga damuwa Dan ya dauka rawa maganar auren take kokarin farawa shiyasa ma da Abdul aka kirasa Lagos maganar aikinsa dayaje Babbah ya Sakasa yayi masa bincike sosai akan Seelahs din Kuma suka samu yabo a gurin mutane da Dan abinda aka sani akansu Dan haka yaji ya sake samun nutsuwa da auren kodan yanda Ameenatou ya kwallafa son Haroon din a ranta.

A ranar Dasu Dad suka koma a washe gari aka buqaci zuwan Abdul Wanda hatta ticket din jirgi Siya masa Akai daga Abuja yabi jirgi zuwa Lagos acan ma cikin mutuntawa da girmamawa aka aika mota ta daukosa daga airport bar masaukinsa saida ya kwana ya wuni ya huta da kyau aka Kaisa SEELAHs CPN acan dinma Koda ya Isa anriga an samar da aikinsa Wanda zai fara a matsayin sabon secretary din Alh Lameenu na musamman.

Yayi godiya yayi farin ciki sosai hakama ya yaba Dan kuwa table dinsa ko a bankin da yayi aikin security sai manager ne yakeda irinsa.

Bai gama shiga shock da sabon farin ciki ba Saida aka basa gurin zaman da zai tattaro iyayensa ya dawo dasu sbd karatun Ameenatou da zata fara a Lagos din da Kuma saukin sha’anin aurenta.

Sosai ya Nuna farin cikinsa da yabawa tareda alkawarin yin duk iya kokarinsa da ladabinsa akan aikin harma da girmamawan gaske.

Saida ya Kara kwana biyu a Lagos din kafin ya dawo tukuna daga baya yayi Shirin komawa su Babbah sai daga baya zasu bisa.

Duk tsananin qiyayyar da sunan Lagos da Babbah Baya ko kaunar a fada hakanan ya danne a cikin ransa ya boye sbd farin cikin Ameenatoun Dake murna sosai akan karatunta da Kuma zama da zatai kusa da Haroon Koda yabar Nasarawan.

Ita kanta Dadah dayake sun Dade da dannewa da rufe Babin Omar gaba Daya kwata kwata rayuwarsu Bata nuna komaiba Dan ‘yarsu dai tayi girman da zasu iya Bata kariya daga kowa barshi uban nata da basusan ma Yana raye ko mace ba.

**Har yamma Haroon din Baizoba Dan haka Ameenatou tafara Bata fuska tana shiga fushi musamman da yaqi kiranta bayan Hafiz ya tabbatar mata Daya dawo.

Shigewanta tayi daki taqi fitowa kwata kwata a dakin take komai har dare tana fushi Babbah nata aikin rarrashi da Dadah.

Hafiz dai baima da lokacinda harkokin gabansa yakeyi sbd alamu sun nuna Haroon din ya sauya Kila sbd ciwon da yayi da Kuma Maida hankalinsa dayakeson yayi akan gaggawan kawo sauyi da mafita akan illar data rusa aikinsu gaba Daya.

Washe gari da safe tana tashi kashe wayarta tayi gaba Daya sbd ko Haroon din ya kira karya samu

Fitowa tayi sanye da doguwar rigar atampar A shape data zauna daidai jikinta hula data kasa rufe cikakkiyar gashinta me tsayi ce akanta tana son kunna wayar Amma tana Hana kanta.

Gurin Dadah ta nufa tace

“Dadah kisa Yaya Hafiz ya kaini gurin wanke kan fa ni kitso nakeso zafin kaina nakeji sosa”

Dadah datasan a fushi Ameenatoun take cikin kulawa da lallabawa ta kalleta tana gyara mata zaman hular kanta yanda ta sake mata kyau duk da gashin Bai rufe duka ba Yana daure a cikin hulan tace

“Dauko wayata na kirasa yazo yakaiki yanzun Nan”

Juyawa tayi ta nufi dakin dadahn ta dauko wayar ta fito ta Bata tana sake narke fuska kadan take Jira ta fara Hawaye.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

41

Suka kammala ganin komai. Jikin Ashir da Bappah Auwalu sukayi sanyi. Baki daya sun shiga cikin dimuwa.

Alhaji Garbosai ya ce da su,

“To kunga yadda komai ya kasance. Bayan lokacin daya diba ma bai kawo dinnan ba kasancewar halayen sa na kwarai yasa nayi tafiyata ma waje nasan ba damuwa ko da aka sanar mun rasuwar sa nace to shaidun suzo su Fadi akwai nauyi ko ince alkawarin a kansa dake bukatar saukewa. Amman abari na dawo ba damuwa kar a dimauta iyalan sa suna cikin alhini. Hakann kuwa akayi bayan na dawo na Kara bada lokaci Mai tsawo sosai sannan nazo yanzu. “

“Mashaa Allahu. To yanzu Alhaji akan me kazo kenan. Don yanzu sai abunda kace. Tunda Wanda kukayi maganar nan da Kai Allah ya karbu abunsa. Kuma bamuda masaaniyar komai akai”

“Hakane kam Allah ya gafarta masa. Magana daya ce zuwa biyu. Na farko dai idan da akwai kudaden abiyasu kawai acire dubu dari biyar din Kai na yafe wallahi. Akarbu takardun gidan nan. Idan Kuma babu to gaskia zai yi wuya a idan baa karbu gidan ba baki daya Ina nufin kadarar zata maye gurbin kudin da ya karba duk kuwa ma da sai yayi ciko amman na yafe”

“Mashaa Allahu Allah ya saka maka da alkhairi Amin. To yanzu Alhaji ba wata hanya ta daban da zaka bayar. Allah bamuda dalilin biyan ka kudaden daka ambata, Kuma bansan gidan nan nasu ya tafi don shi kadai suka mallaka gaba daya wallahi Alhaji”

“Sai dai muyi hakuri don wallahi a halin da ake ciki nima banida rufin asirin da zan iya hakura da kudaden nan Allah shine sheda”

“To Alhaji yanzu kamar shekara nawa zaa bayar don mu samu mu maido da kudin?”

“Ai bawan Allah baa cewa kawai. Dan wallahi kudaden nan kaga Dan uwana Nan. Rabi nasa ne rabi nawa. Daga baya na bukaci kudin ya ranta mun rabin. Don haka wallahi dama da an biya kudaden Nan to shi zan basa don nasa ne. Haka zalika idan kudin bai samu ba. To lalle wannan gidan zai zama mallakin sa. Sai dai kuyi hakuri. Batun Kara baku lokaci wallahi an baku Kuma Kun sani”

“Munsani ranka ya dade Dan Allah kayi hakuri ni yayan mahaifin su ne. Da Marigayi junaidu da ni uwar mu daya uban mu daya ranka ya dade. Bamu da kadarar da zamu maye gurbin kudaden da kake bi. Kuma wallahi bamaso gidan nan ya salwanta agrare mu. “

“Kuyi hakuri don wallah an Kara muku lokaci an rage kudin ma. shima Kuma Yana bukatar gidan wallahi. Kuyi hakuri”

“To Alhaji kamar yaushe zasu bar gidan kenan? Don nagaya maka shine rufin ashirin su damu baki daya”

“Gaskia gaskia karshen gaskia daga wannan satin da zamu shiga shine karshen kuyi hakuri”

Ashir ya mike da sauri Yana dafe bango Bai jira Mai zasu sake cewa ba ya bi bango Yana dafe dashi ya koma cikin gidah bandaki ya shige cikin sa ya kada saboda tsabar tashin hankali Nan da Nan kuya yafara zawo kamad ruwa..

Daga karshe bappah ne yaji musu sallama suka ja motar suka tafi shi kuma ya shiga cikin gidan inda ya tarar Ashir din a kwance akan kujera ya rufe fuskar sa da littafi.

Jikin yaran duk a sanyaye suna jiyo komai tun dazu da fari har aka kammala. da kawu Auwalu ya rakazu, kowanne fuskar sa duake da damuwa.

Ya dan kwantar musu da hankali ya musu sallama shima ya koma gidan sa dauke da damuwa. Dik kowane danuwan su ya kira su ko zasu temaka kowanne yace bashi da hali. Don bakin ciki har kuka yayi bappah Auwalu.

Haka Kwanakin sukayi ta ja. Mutanen Alhaji Garbosai sai zuwa suke suna bin notice, Ashir yaje gwangwan ya Kira masu saye suka sayi kayan kallon su da firjin su da katifar dakin mahaifan su da suka rasu da drawer su nawrah da kujeru Banda babba daya 3 sitter baki daya ya sayar da komai harda labulaye sai biyu ya rage. Komai da komai ya sayar , Amman kudin da suka samu kwantan kwatan kwantan kwatankwacin rabin rabin rabin rabin abunda ake bi basu hada ba. Haka ya hakura ya sanya kudin a asusu kawai gab daya.

Ranar wata talata da safe kanin Alhaji Garbosai yazo yace lalls su tashi su zubar masa gidah na zuwa da yamma. Suka karasa komai nasu tun da safe Ashir ya zuciya suka fita daga gidan

Bappah Auwalu ya ce suje gidan su. Su koma gidan sa baki daya da zama shi bai wulakanta yayan Yan uwan sa ba. …… Ya kwankwasa.

42
Kayan baccin Avves masu santsi da tsadan gaske ya Saka sedai baima rufe gaban riganba ya fito lafaffiyar cikinsa dake fidda murdewan jikinsa sbd motsa jiki ya sauko kasa sbd Yana buqatan ruwa da drinks sbd aikin da zai kwana yanayi sallah Kuma Daman kafin su baro Nasarawa sunyi ishai ma kafin su shigo gidan sunyi.

Siddeeq ma tini yayi wanka ya shirya cikin gajerun kayan baccin da sukaiwa jikinsa kyau Shima Dan Shima Yana motsa jikinsa sosai Dan hakane ma yafi Haroon budaddiyar jiki kaman ubangidansa.

Shima fitowansa kenan yaji saukowan JEEY da kamshinsa Dan haka ya dakata harsaida ya sauko kallo Daya yayi masa ya dauke idanuwansa sbd JEEY SEELAH ko namiji Dan uwansa yake kallansa zai iya kamuwa da sonsa bare mata Danma Baya mu’amalantar inda mata suka yawaita da baasan irin matan dazai samu masu jiransa ba, har mamakin yanda JEEY din ya kamu da son fadila yakeyi da yanda zuciyarsa take riqe da iya ita kadai yakeyi.

Ruwa Jamaal din ya buqata da E-Bull energy drink dinsa.

Daukowa siddeeq yayi ya kawo masa ya ajiye a gefe hakama already tarin manyan takardun abinda zasuyi suna gurin zube.

Kafin ya fara aikin bayan ya zauna dago fararen idanuwansa yayi ya Kalli siddeeq ya Bude Baki a natse yace

“Zamu bi morning flight zuwa Lagos ka duba mana idan akwai”

Dagowa siddeeq yayi ya Kalli JAMAAL din cikin mamakin ta yanda zasu fuskanci juna da Dad dinsa batareda ya gane shi bane,
Hakama shi kansa Jamaal bazai iya kwantar musu da Kai ba komai tsanani kaman yanda Haroon kansa bayama dagowa a gabansu saita Baci.

Cikin nutsuwa da tinani siddeeq ya sake kallansa Yana cewa

“Dr ko zan kira Dad din na sanar masa wani uzurin dazai daga tafiyar gobe zuwa jibi idan Barr da Mum din sun iso”

Girgiza Kai yayi a natse Yana cewa

“Ba buqatan Hakan,zangansa da kaina”

Sake shiga fargaba Siddeeq yayi duk da yasan idan Jamaal din ya fada ta zauna Amma a gaban Dad Kam Abu ne me wuyan gaske idan baa take zai sheda Jamaal ne gabansa ba ba Haroon dinba ko daga kamshinsa da Baya boyewa kowa da Kuma fatansa data banbanta data Haroon duk da idan suna rarrabe baka ganesu Se Wanda yayi da gaske gaske idanma kayi musu farin sani kenan hakama izzar Jamaal har abada ba Daya take data Haroon dinba.,
Tayaya Jamaal zai iya tsayuwa a gaban Dad dinsa batareda yayi masa kallan dazai Saka Dad din take Ji ajikinsa Jamaal ne.

Jamaal Daya miqa hannunsa a natse ya dauki drink din gefensa ya Bude yakai bakinsa yasha kusan Rabi ajiyewa yayi Yana Bude laptop din Dake gabansa ya kunna kafin ya fara janyo takardun Yana budewa tareda jerawa a gabansa sbd acikin kankanin lokacinda bazai ci masa time din komawa rayuwarsa ba yakeson kammala dukkanin aikin project din sabo da zaiwa Dan uwansa ya tattara ya koma bama tareda wani yasan ya shigo qasar ya fice ba.

Shima siddeeq tattara hankalinsa yayi sbd nutsuwa ga aikin da Jamaal zasuyi.

Nutsuwa yayi sosai Yana aikin cikin kwarewa da tabbatarda komai ya tafi daidai,Shima siddeeq mayarda hankali yana Wanda zaiyi a cikin aikin.

Har kusan hudu saura na guraren asuba suna aikin kafin suka ajiye suka nufi dakunansu.

Jamaal na shiga bedroom dinsa Kai tsaye toilet ya nufa yayo alwala ya fito ya Dora gatuwar jacket akan kayan jikinsa na bacci ya rufe batiran rigarsa Dake Bude ya Saka qaramar hulan sallah fara akansa ya tayarda sallan nafila.

Yana gama sallolin nafilansa ya miqe Dan sallahn asuba da Akai kira har ana kokarin tayarwa daga masallatan nesa Dayake jiyowa.

Bayan gama adhkar da adduoinsa miqewa yayi ya cire hulan da jacket din ya nufi gadonsa ya haye tareda kashe komai tin daga kan wayoyinsu da wutan dakin ya shige bargo a nitse Yana lumshe idanuwansa.

Bacci sosai yayi ya samu hutun jikinsa Dana kansa harma Dana zuciya kafin ya tashi guraren 10 da wani abu.

Toilet ya nufa Kai tsaye yayi brush da sauransu tukuna yayo wanka ya fito daure da towel ya nufi inda wayoyinsa suke ya miqa hannu ya kunnasu kafin ya wuce gaban mirror Dan shiryawa.

Bai wani dauki time ba ya shirya ya fito cikin Ash kaftan din Tsadaddiyar yadin cashmere data tsananin sake sauya kamanninsa zuwa wani bakon baturen bahaushe hakama hulan Daya Saka ya rufe gashinsa Daya sake banbantasa Dana Haroon ta qara masa kyau sosai.

A Karan farko rayuwarsa dayayi amfani da wani turaren daba nasa ba Dan haka yakejin Baya wani Jin dadin iskan Daya bayarwa a jikinsa duk da Wanda yayi amfanin dashi Shima mugun designer ne sedai qamshinsa Daya Saba dashi daban yake a gurinsa.

Siddeeq da tini yayi musu booking tickets din 12 Dan haka Shima ya shirya tsaf cikin kaftans din Shima sai Jakar takardun aikinsu Dan laptop din dasuke hannunsa.

Jamaal na saukowa cikin girmamawa ya masa barka da saukowa kafin ya biyosa suka fito tare Jamaal din suna magana.

Siddeeq ne me tuqin Dan Jamaal Kam bayajin zaiyi tuqi harya gama ya tafiyarsa inda ya fito.

Kai tsaye office din dazai fara gabatar da aikin anan Abuja ya nufa ya zauna dasu ya gabatar musu da sauyin aikin dayayi tareda sababbin plans din dasuka matiqar Basu mamaki da sakasu farin ciki me tsananin gaske Dan kuwa tini suka fara Shirin gabatar da takardun soke aikin kwata kwata tareda raba hannunsu Dana Seelahs,

Hannu suka miqa masa cikin Jin dadi tareda taya junansu murnan sake samun damar aiki a tare Shima hannun ya miqa musu Yana sake gabatar da kansa BARR HAROON SEELAH.

Cikin farin ciki suka sake amsar tayin aiki da juna take akai hotuna da sabon Saka hannu akan new project din dazai maye wancan.

Sai guraren 11:20 suka baro Kai tsaye daga Nan office din airport suka nufa suna Isa suka ajiye motar anan airport suka shige jirgi sbd sunma iso kusan late.

A cikin jirgin yayi breakfast dinsa hankinsa kwance da nutsuwa sabanin siddeeq Daya kasa samun nutsuwa ko Kwanciyar hankalin sbd abinda zai iya faruwa idan aka samu matsalan Dad suka gane.

Suna sauka Lagos drivern Dad dinne yazo airport daukansu sbd shi Jamaal din da kansa Daya turawa Dad text din azo a daukesa daga airport Nan da awanni.

Da farko kaman Bai gane ba Saida ya sake karantawa ya tabbatarda Haroon dinne yayi masa sakon A tura driver ya daukosa daga airport.

Numfashi ya sauke ahankali Yana jinjina lallai Haroon din yafara samun karfin zuciya tinda ya iya masa sakon Kai tsayen Nan Mai kama Dana Bada order.

Driver na Isa airport Kai tsaye siddeeq ne ya budewa Jamaal kofa ya shige bayan kafin Shima ya zagayo ya shiga gaban motar driver Dake Satan kallan Jamaal din ta mirror cikin girmamawa yace

“Barka da dawowa Sir Haroon”

Gyada masa Kai kawai Jamaal yayi sbd hankalinsa na kan sakwannin asibitin Haroon da aka turo na can Poland Yana karantawa.

Suna isowa mansion din Jamaal ya hadiye wani abu Daya danne maqoshinsa Yana kashe wayarsa gaba idanuwansa na Neman sauyawa Amma ya Hana hakan sbd dawowa ko shigowa mansion din seelahs wani abune dabai taba tinanin zai sake ba har abada idan ba yanzu da Dan uwansa Dake tsananin buqatansa ba.

Sedai abinda Basu saniba shine kaman yanda yayi alkawarin duk ranar Daya Sako kafarsa ya dawo musu Saiya tabbatarda sun rasa komai to tabbas tinda ya Sako kafarsa ayau din ya dawo Saiya gyara musu komai sbd Haroon kafin suna kallo ya rabasu da komai daga ranar Daya tabbatarda Haroon ya mallaki macen dayake so fiyeda komai ayanzu.

Kai tsaye bangaren Haroon ya nufa Yana amsa sannu da zuwan da securities din gidan ke masa cikin tsananin girmamawa da mamaki me girma na sauyin Haroon din.

Yana shiga palon Haroon Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ya shige toilet alwala yayi ya fito yayi Sallah Yana idarwa wayar Dad na shigowa wayar Dake gefensa.

Kallan wayar yayi tareda dagawa cikin nutsuwa yayiwa Dad din gaisuwan Data Saka kirjinsa mummunan bugawa Saida yayi shiru ya sake sauraron muryan da kyau yaji sai yaji Yana Neman rudewa sai kawai yayi Watsi da abinda yaji Kai tsaye ya Bude Baki yace

“Ka sameni yanzu a office din cikin mansion din.”

“Ok” kadai Jamaal yace tareda rigan Dad kashe wayan Wanda ya sake Saka Dad din mamakin halayen da Haroon ya fara sauyawa.

Saida yaci abincin da siddeeq yayi masa ordernsa daga tsadaddiyar restaurant ya koshi kafin ya shirya ya fito tareda siddeeq Wanda shine yake nuna masa hanyar da office din yake tinda Bai saniba.

Suna kaiwa kofar office din siddeeq ya tsaya daga waje Jamaal Kuma Kai tsaye ya Bude kofar a natse zai shiga sako ya shigo wayar Haroon Dake hannunsa Kuma Kai tsaye yasan Haroon dinne Dan haka ya dakata tareda duba sakon Daya bayyana akan screen din wayar inda ya rubutu masa tini tareda rokonsa akan yayi masa alkawarin ganin aurensa da Ameenatou ya tabbata kaman yanda tin farko yayi masa wannan alkawarin zai tabbatarda shi din Bai rasa macen da itace farin cikinsa ba kaman yanda shi Bai samu tasa farin cikin ba.
Lumshe fararen idanuwansa yayi da suka fara sauyawa Yana sake Tina alkawarin da yayiwa Haroon din zai tabbatarda su Dad da hannunsu sun aura masa Ameenatou kafin yabar kasar idan har auren Bai tabbataba to Allah ne yayi su din ba ma’auratan bane Kokuma Idan dayansu Baya raye wannan shine abinda mum dinsu ta roka daga Jamaal din sbd bazata so Shima Haroon dinta ya dandani irin radadin da Jamaal ke cikinsa haryanxu ba na Rasa Macen da ita kadai ya bawa zuciyarsa.

Numfashi me sanyi ya sauke ahankali mara sauti kafin Kai tsaye ya shiga batareda knocking ba kaman yanda Haroon yakeyi kafin shigan.

Yana shigowa Dad Lameenu dayake facing kofar ne ya zuba masa idanuwansa Yana kallo cikin Dan mamaki kafin Shima Dad din ya dago Yana kallansa Dan dukkanin idanuwansa mamakinsa a bayyane,

Dad Lameenu Daya rasa abin fada cikin yar rikicewa yace

“Da Jamaal Yana kasar Nan da babu abinda zai hanani tinanin shine a gabanmu,
Haroon hankalinka kuwa kake mayarwa akan aikin gabanka kokuwa gyaran fata ka mayarda hankali Akai sbd mace??

Dad da har lokacin idanuwansa na kan Jamaal din Yana Jin zuciyarsa na kokarin dawo masa da kewan Jamaal da tsananin buqatansa dayakeyi Kuma sai zuciyar ke Jin kaman ta samu Jamaal a gabansa Amma Kuma yasan abune da bazai taba yiyuwaba Dan Koda Jamaal Yana Nigeria ya shigo bazai taba Sako kafarsa SEELAHs ba Dan haka duk yanda idanuwansa ke nuna masa kaman Jamaal ne gabansa bazai yiyuba Dan haka ya dauke idanuwansa daga Jamaal din Yana sauke numfashi ahankali Shima Jamaal din sai alokacin ya ya dago ya zuba musu idanuwansa da suka sauya sosai sedai Bai furta komai ba Dan maganarsa a lokacin zata bayyanarda radadin ganinsu kawai Dake cin zuciyarsa Dan haka ya zabi yin shiru kaman yanda Haroon keyi a gabansu.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

43
A cikin murya me nutsuwa Kai tsaye ya gaidasu Dad din acikin jam’i batareda ya Bada amsar maganarda Dad Lameenu ya jefesa da ita ba ta farko.

Dayake dukkaninsu kowa da abinda yake bakinsa na maganar Dake cinsu Basu tantance sauyin muryanba Wanda Daman Shima Haroon idan jikinsa na Sanyaye muryansa a natse da sanyi take fita Dan haka Babu Wanda ya tsaya amsa gaisuwan bare tambayar ya jikinsa Kai tsaye Dad dayaji Baya iya kallansa Dan yau din cika masa ido Haroon keyi sbd kamanninsa da Jamaal sun tsananta ayau dayake ganinsa kaman Jamaal Dan haka batareda y kallesa ba murya a daure da bacin ran abinda yayi yace

“Ko zaka bani dalilanka Daya Saka bawa project dinmu da ma’aikatan aikinsa Hutu harna kwana uku batareda sanar damu meyake faruwa ba??

Numfashi me sanyi ya sauke Yana dauke idanuwansa daga kallansu kafin ya Tako ahankali dukkaninsu sukai saurin kallansa ganin ya tinkarosu Yana kallansu Dad Lameenu ne yayi saurin cewa

“Amsar abinda yake faruwa muke buqatan Dani sbd Haroon Banga alamar zaka cika alkawarin daka dauka ba na sakamu alfahari dakai,
Aikin Nan fa duka duka sauran sati uku ne a time dinsa ya cika,.

Dad kallansa ya sake yi Yana Jin zuciyarsa na son shiga tinani daban daban Amma ya watsar Yana cewa

“Karka manta nutsuwanka akan aikin Nan shine tabbatan aurenka Dan Neman aure ba shine aurenba Karka manta da Hakan Dan nakai maquran rashin nutsuwan Nan taka,

A Hakan kake Neman mutuwa sbd mace kanason kayi aure batareda kasan ciwon kanka ba bare tinanin tsayuwa ka zama abin alfahari ga iyayenka ba tayaya zaka tsayu ka zama abinda matarka ko yayanka zasuyi alfahi dashi….

Dakatawa Jamaal yayi daga inda yake tsaye tareda dago idanuwansa da sukai ja ya Kalli Dad din dashi ma shi ya Dan kalla Yana cewa

“Yes, Haroon haryanxu ka kasa sakani farin cikin Da kowannen Uba yake shiga akan yayansa da alfahari dasu,
Alkawari nayi Maka akan idan kasakani farin ciki akan wannan aikin zan nema Maka auren da kakeso Amma……

Katsesa Jamaal yayi Dan bazai iya tsayawa sauraron wainnan maganganun akan Dan uwansa ba komai zai iya faruwa Dan zai iya bayyanarda kansa Dan haka wayarsa ya daga ya kira siddeeq take siddeeq ya shigo da takardun komai dasuka gama a yau din ya karba daga hannun siddeeq ya ajiye gaban Dad din Yana kallansa yace

“Gashinan Alkawarin zan cika Maka acikin kwanakin da bazasu kai na cikan kwanakin ba Amma Kuma a ranar da komai ya tabbata a yanda kakesonsa a ranar nakeson a daura mun auren da yarinyar…..”

Daga dad har Dad Lameenu sakin Baki suke kokarin yi gurin kallansa da mamaki hankalinsu na rabuwa biyu daga abinda ya fada da Kuma karanta takardun Daya zuba a gabansu suna karantawa cikin tsananin mamakin sabuwar project din data dawo musu Da cikakkiyar damansu a hannunsu.

Dad Lameenu Daya kasa Kai karshen takardan cikin farin cikinsa Daya mantar dashi mamakin dasuka shiga yace

“Nayi Maka alkawarin daura Maka auren Ameenatou a washe garin ranar da Akai bikin Budewa duniya wannan aikin project dinnan Haroon idan abinda nake Gani da suna SEELAHs a jikin takardan Nan ya bayyana.

Dad ma mamakin ne yayi mugun kashesa kafin idanuwansa su sauka kan signature din jamaal Dake karshe wayarsa tayi ringing daga turawansu na Abujan ne Yana dauke idonsa Akai siddeeq ya matso Yana rufe file din tareda amsar masa cikin girmamawa Dan basa Daman amsa wayan wadda ta Saka Dad Lameenu washe dukkanin bakinsa cikin tsananin farin ciki Yana sake tabbatarwa da Haroon zuwa wani sati zai tabbatarda Abdul yayo parking da familynsa sun iso Lagos din gaba Daya.

Wayar da Dad keyi ta sakashi Shima dukkanin farin cikinsa bayyana Yana washe Baki Yana wayar cikin turanci Dan nutsuwa Yana Kuma Basu tabbacin wannan Karan Inshallah komai zai tafi daidai Nan da 3 zuwa 4 weeks komai ya zama cikin Shirin bikin qaddamarwa.

Dad na gama wayar Haroon din ya kalla cikeda farin ciki yace

“For the first time da yau nake alfahari dakai Son”

Kalman zafafa zuciyar JAMAAL tayi Dan haka baice komaiba sai sake fuska da yayi ya amshi zancen Dan kawai da zargi.

Buga kofar Akai kafin aka Bude tareda shigowa
BB ne Wanda duk kwakwalwansa take Neman Juyewa sbd ba dare ba Rana a bincike da yawon garuruwa suke da kauyuka gurin Neman da haryanxu Babu me baccin arziki akansa tsakanin shi dasu Mam din.

Tinda yake a rayuwansa wannan shine aiki mafi wahalan dayakesha mara sauko ko kadan a duk shekarun Nan,
Shi kansa sbd baqar wahalan dasuke Sha a wannan aikin yakejin bazai taba samun nutsuwa ko Kwanciyar hankali ba matiqar ba Gano abinda suke Neman sukaiba kaman yanda yasan har abada uwayen gidan nasa bazasu taba samun baccin nutsuwa da Kwanciyar hankali ba idan ba burinsu na shekarun cika yayi ba.

Cikin girmamawa yace

“Sir Haroon barka da dawowa”

Batareda Jamaal ya amsa ba Dad Lameenu ya Kalli siddeeq Wanda Shima Kai tsaye ya juya daga office din ya fice tareda Turo musu kofar.

iPad din hannunsa ya ajiye gabansu tareda bayanan daya samo akan bincikensu ya fara da cewa

“Ranka ya Dade na samu tabbacin ‘yayan matar sir Omar Daya gudu da abinda ta haifa a daren yanada nasa ‘yayan guda biyu Kuma dukkaninsu Maza ne sedai Kuma matarsa an bani tabbacin kafin barinsu gombe a wancan lokacin ta haihu Wanda nakeda tabbacin ba haihuwa tayi ba babyn sir Omar dinne”

Cikin zaquwa Dad Lameenu yace

“Bayanin inda suke shine babban abinda muke buqatan Jin idan an samo”

Hakama Menene asalin abinda aka haifa din?
Mace ne ko namiji??
Hakurina da bugawan zuciya akan wannan lamarin ya kusa kamani BB a gaggauta samo mana inda suke sbd tashin aikinmu yau da aka samu shi kadai bazai riqe mana matsayinmu da tsagwaran dukiyar da muka rasa ba muna tsananin buqatan dukiyarmu Dake hannun Omar.

Dad da Shima abinda yake ransa kenan ya Kalli Haroon dayake tsaye har lokacin gabansu Yana kallan fuskokinsu da bakinsu yace

“Haroon ya qara muku kudin Daya kamata banason aurensa yazo duk tsanani duk wuya batareda an samo mana inda suke ba,
Idan Kuma bamu samo Hakan ba to tabbas lokacin zuwansa garemu yayi Dan bazai taba yiyuwaba ayi auren ‘dana dayake matsayin dansa batareda yazo ba,

Zuwansa Nigeria kuwa ba abune da zai taba yiyuwaba yazo ya tafi batareda ya kaiwa abinda ya Haifa da cikinsa ziyara ba Wanda shi da kansa zai kaimu ga Magajinsa batareda ya saniba.

Kallan Haroon ya sake yi Yana sake cewa

“Ka Basu duk adadin kudaden da suke buqata kaje ka fara Shirin aurenka Dan daga lokacinda Omar ya sauka a Nigeria dukkanin motsinsa a tafin hannunmu zai zama.”

Gyara Kai Jamaal yayi Yana kallan BB dayakejin bazai iya barinsa ya sake ahakan iskan yanci ko Daya ba Amma Kuma Yana buqatan sanin abinda yake faruwa kafin komai Dan kuwa zantukansu sun Saka kansa daukan zafi.

Gyada Kai BB yayi Yana Jin nutsuwa da farin cikin Suma wahalallen burinsu ze Kai karshe sbd a saukake ma auren Haroon din zai kawo Omar har gida Kuma zuwansa kaman bayyanar abinda yake boye ne.

Maganganun sauran ayyukansu dasu BB din keyi ne suka fara Kai tsaye tareda tambayan huldan datake hannun BB din da yaransa ya tabbatar musu da komai Yana tafiya lafiya kalau duk da an kama wasu yaransa Amma ya tura yaronsa Daya Daya bari aka kamasa aka Saka cikinsu Sbd ya hanasu fadan komai sedai aka wayi gari sun rasu dukansu su biyu sai shi Dayan yaron nasa sun fito dashi Dan haka Babu matsala Tako ina.

Juyawa Jamaal yayi ya fito idanuwansa basa ganin gabansa sosai sbd Ja da tashin hankalin Daya tsinci kunnuwansa daji batareda ya tsaya jin sauran abubuwan da hankalinsa yake Neman kasa dauka duk da ya Dade da sanin ba imani a lamarinsu Dad bare tausayi sbd abinda sukaiwa fadila da har yanzu baida sheda ko tabbacin sune sukai Amma ayau da kunnuwansa Yana Jin abubuwan da baisan tayaya ma zaace sune suke aikatawanba,

Haroon ya San dukkanin wannan abin dayake faruwa kenan ya boye masa tinda gashi suna maganar a gabansa batareda sanin ba Haroon dinne ba.

Yana fitowa Kai tsaye mota ya nufa Yana miqawa siddeeq hannu ya basa key batareda ya Juyaba,
Kirjinsa yake Jin ya toshe masa Babu iska ko kadan Babu abinda yake buqatan so kaman ya fita daga Mansion din.

Siddeeq na ganin Hakan ya miqa masa key din motar Haroon Daya fito dashi Dan fitarsu idan sun gama.

Saida siddeeq ya nuna masa motar ya nufi inda take tin kafin ya Isa ya Budeta Yana Isa shiga kawai yayi ya tayar da reverse ya fice daga Mansion din Yana saukar da duka glasses din motar sbd iska ta shigesa.

Yana ficewa siddeeq ya Ciro wayarsa Yana shakkar abinda ya faru daga cikin office din Amma dai koma Menene Haroon Yana buqatan sani Dan dawowa sbd ansamu matsala ga dukkanin alama.

Su Dad kuwa farin ciki da zaquwan auren ne gaban Daya ya mamayesu sbd ga dukkanin alama sanadiyar auren zasu samu abubuwa da dama dasuke so suke fata,
Haroon ya fara zama abin Alfaharin da zai sake fitar da sunan seelahs da tsayuwarsu hakama dawowan Omar dasuke fata ta sanadin auren da dole zaizo ko Dan Yan jarida dazasu yada maganar auren koina da rashin zuwansa auren ‘dan farko da zaayi a Seelahs din tinda na Jamaal kaman auren boye ne da ba kowa ya saniba Amma wannan da kansu zasu Kai masa gayyata ta musamman da matsayin zamansa wakilin ango da zai karba auren da hannunsa.

****Haroon dayake tareda mahaifiyarsa tana jinyarsa cikin tsananin so da kauna da kulawa tareda tattali Jin yayi zuciyarsa ta karaya Da yanda tin farko ya zabi mahaifinsa akan mahaifiyarsa,

Bata taba nuna masa banbanci tsakaninsa da Jamaal ba sedai shine Karan kansa ya zabi mahaifinsa akanta sbd sonsa dayakeji cikin ransa fiyeda komai.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

44
Mum Aleena datake Jin batason sake rabuwa da ‘danta sbd halinda yake ciki na tsananin buqatan kulawansu dan sai sunyi da gaske zasu iya rabasa da depression din Daya kamasa,

Drug kuwa da suka samu a jininsa Basu sanar masa ba itada Jamaal sbd sunason tantance shine yake Sha da kansa kokuwa sbd sun kasa yadda ko sanin tayaya zai zama Yana Shan kwayoyi irin wainnan.

Siddeeq Kuma ya tabbatar musu da Babu kwayoyi mayen ko makamancin Hakan da Haroon yake Sha Amma Kuma duba da depression dayake ciki da tsananin matsi a Hannunsu Dad zai iya samun kansa da Shan kwayoyin Dan samun fita hayyaci ya Dena Jin komai.

Tin daga ranar da Haroon din ya taho aranar ya ringa yiwa mum din kuka kaman karamin yaro cikin ciwo da tsananin buqatan again Dan uwansa akan bayason rasa Ameenatou kaman yanda ya rasa fadila,
Shi a yanzu ba yabon mahaifinsa yake nema ba Ameenatou kawai yakeso a rayuwarsa.

A gaban Mahaifiyarsu Jamaal ya Sakasa sukaiwa juna alkawari.

Idan Haroon yayi masa alkawarin dawowa ga mahaifiyarsa Dan samun lafiyansa da rayuwar nutsuwa da Kwanciyar tare Kuma da cika burin Mum dinsu na ganin yayanta duka biyu a tareda ita to shi Kuma yayi alkawarin zuwa ya gyaro dukkanin abinda Haroon yakeso Dan samun yabo daga Dad dinsa da Kuma zama abin alfaharinsa tareda tabbatar da aurensa da yarinyar Amma ana daura auren zasu taho tare.

A daidai wanna gaban Babu abinda Haroon bazai iya yiba akan samun Ameenatou da samun nutsuwan zuciyansa data Dan uwansa da mum Dan haka ya amince da dawowa cikinsu gaba Daya bayan auren take mum ta rungumesa cikin farin ciki da Jin dadi sosai tana Jin kaman tinda ta haifesa sai yanzu ne zata samu zaman datakeson yi da ‘danta hakama zata kaman yanda ta kaunaci fadila take taji tana kaunan Ameenatou har cikin ranta duk da Bata taba ganinta ba Amma tayi masa alkawarin inshallah da ita zaayi aurensa.

Daman ba wani zama zasuyi a Poland dinba Nigeria zasu taho sbd bikin auren Da Haroon din kwata kwata yaji Baya son a dauko lokaci ayi kawai ya tahowansa kusada mahaifiyansa Dan haka sauki kawai sukeson ya Dan samu su taho saiga Kiran siddeeq Wanda ya sakashi shiga fargaba da tsoron abinda Jamaal yaji Dan haka shine ya dagawa mum hankalin komawansa baima jirata ba washe garin ranar ya Siya ticket dinsa ya tahowansa Dan bayason abinda zai janyo fushin Jamaal ya lalata masa komai adaidai lokacinda ake gap da samun abinda yakeso.

Jamaal kuwa a ranar Bai kwana a Lagos ba ya wuce Abuja tareda siddeeq ko su Dad din Basu saniba Dan idan Yana ganinsu zuciyarsa kasa riqe koshi waye din takeyi gwara ya tafi ya Jira zuwan Haroon Daya San duk inda yake idan har baida gaskia Yana hanyar dawowa.

Kwana Daya saiga Haroon din ya diro Amma Bai yadda ya Hadu da Jamaal din ba Kai tsaye Nasarawa ya wuce sbd bayason suyi hayaniya Kuma baisan Menene yaji bama tukuna bare yasan ta inda zai fara.

Da yamma sosai ya iso Dan haka wanka da sallah kawai yayi Bai tsaye komaiba ya wuce gidan Babbah.

Zaune suke a tsakar gidan sai lallabata dadah keyi sbd taqi Shan magani daga ciwon Kai zazzabi ya maqale kwana biyu anata fama da ita.

Zuwansa ya Saka Abdul sakin ajiyan zuciya hakama Hafiz Babbah Baya Nan
cikin sakewan fuska da nutsuwa ya qaraso Hafiz na janyo masa kujeran zama Yana masa barka da zuwa.

Yaya Abdul ya fara bawa hannu suka gaisa cikin tsananin kulawa Yana tambayarsa kwana biyu ko numbernta Baya shiga.

Murmushi ya sake Yana cewa aikin dayake gabansa ne ya sakashi kashe dukkanin wayoyinsa sbd aikin ya koma babba fiyeda yanda suke tsammani.

Gurin dadah ya Maida kallansa Yana gaidata cikeda girmamawa da kulawa kafin idanuwansa suka koma kan Ameenatoun Dake zaune sanye da Riga da wando na bacci ko hula Babu a kanta ko inda yake Bata juyo ta kalla ba maganinta take kokarin Sha tana kasawa sbd batason magani ko kadan.

Hafiz Dayafi kowa shiga damuwan bayan Ameenatou tambayarsa siddeeq yayi suna sake shiga wata firar Amma gaba Daya hankalinsa na kan Ameenatou da yayi magana tayi masa shiru kaman Bata ji ba Kuma kowa yasan ta jisa Daman sun San sai anyi Hakan.

Dadah ce ta Dan rarrasheta tana cewa

“Budurwa bakiji ana Miki ya jiki bane?
Duka fushin bana rashin kiransa da zuwan bane gashinan ai ya taho saiki sauko,
Yi masa hakuri kinji¿

Maganin ta daga duka ta Saka a bakinta tareda binsa da ruwa ta shanye batareda ma tasan tayi Hakan ba sbd fushin Daya taso mata.

Tinda ta fara zazzabin ko ruwa Se ta Saka anbata ko hulan kanta Bata iya sakawa sai an Saka mata sai gashi ta miqe tsaye da kanta ta wuce dakinta tana cewa bacci zatayi.

Hafiz ne ya Bude Baki yace

“Ke meye haka wai?
Inace Wanda ake fushi da ciwon akansa gashinan yazo,Kuma Ashe Zaki iya tashi da kanki kika ringa wahalar Dani da Dadah tin jiya ko bacci na fara saita kirani na kawo mata ruwa Ashe tsaban rashin tausayi ne to Zaki San dawa kikai.”

Tana jinsa Bata ce komaiba saima hararan kofar datai tana Jin zafin abinda yayi mata ranar Yana dawo mata.

Dadah murmushi ta sake tana sake tambayarsa nasa jikin ya amsa mata sbd yasan halin mutuniyar sarai basai an tsaya basa hakurin abinda tayin ba,
Abdul ma sake tambayar jikin da aikinsa yayi kafin suka fada firar tafiyansa Lagos gobe zuwa nxt week Kuma su dadah ma zasu taho duk da ba zuwan kenan ba zadai suje suga inda Allah ya Kaisa dasu.

Duk firar dayaketa yi hankalinsa na kan kofan dakinta Amma Sam taqi yadda ko motsi tayi yaji dadi Bare fitowa.

Sallan magrib suka fita sukayo suka dawo gidan tareda Babbah daya masa ya jikin da fadan rashin Kiran tinda koyayane Daya samu ko mintina bibbiyu a wuni ya ware ya kira din zasuji dadi itama me fushin da bataiba.
Gashi tanata fushi da maimaita shariyan dayayi mata.

Hakuri ya bawa Babbah har suka shiga wata firar inda Babbah din ya sanar masa su Alh Lameenu sun kira akan maganar auren sukeson ta taso ayita kusa tinda dai ba amfanin jiran ko tsaiko.

Har cikin ransa yaji farin ciki Yana mamayesa sedai Kuma fushin da Ameenatou keyi me zafi akansa Yana cin zuciyarsa sbd yasan Jamaal ne yayi mata koma Menene Dan haka Shima take yaji Yana buqatan ganinsa Dan haka anan yayi sallar ishai yaci abinci suna gamawa harya fito Bata fito a dakinba Kuma babbah ya Hana kowa takurata fitowa saita huce da kanta taji ta hakura tukuna.

Yana fitowa da wayar hannunsa ya kira layinsa dayake hannun jamaal Amma Jamaal din yaqi dauka sbd Shima Yana sane da Haroon din ya dawo guje masa yayi.

Kiran dayake yi Jamaal yaqi dagawa ya Sakasa dawowa hayyacinsa akan abinda yake jiransa Dan haka dole ya shirya tinda safe ya nufi Abuja.

Koda ya Isa Jamaal din Yana bacci Dan haka siddeeq na ganinsa ya saki murmushi Mai hade da sakewa Yana masa barka da dawowa.

Kallan hanyar stairs na Hawa sama yayi kafin ya dawo da kallansa kan siddeeq din fuskansa a sake Shima Yana amsawa ya ajiye keys din hannunsa da wayarsa Daya ya nufi dining da aka cikesa tsaf da breakfast din Jamaal din ko zama baiyiba Yana Isa dining din Jamaal ya sauko daga saman sanyeda silk pyjamas farare Kal sai slippers dinsa masu shegen tsada da taushi a qafa kallo Daya yayiwa Haroon ya matse fuskansa datake sheqi kaman ba bacci ya taso ba Yana qarasowa ko zama beyiba Haroon ma ya Dan matse tasa sbd kada Jamaal din yayi masa fada a gaban siddeeq yace

“Meyasa nake Kiran wayanka baka dagawa tin jiya fa da daddare bayan isowana?”

Sai alokacin Jamaal ya juyo ya kallesa da idanuwansa da suka Sakasa Jin kunyar Dan uwan nasa na Abinda ya boye masa duk da haryanxu Yana shakkar idan gaskiyar abinda su Dad keyi ne yaji sbd da bazai zauna haka calm ba.

Ciki muryan dayake kokarin danne bacin ransa yace

“Ka taho ne sbd ban dauka Kiran ba kokuwa sbd kana son sanin abinda na sani gameda ainihin abinda kuke aikatawa a boye?”

Maganar tasa ta Saka Haroon kallansa Yana cewa

“A boye Kuma?
Me kenan??
Me kaji?
Kuma daga bakin wa?

“Daga bakin manyanka,Amma koma Menene baka buqatan sani
kaman yanda ka iya boye sirrinsu bana son sanin komai daga bakinka Amma dai ka fada musu taba Dad jeden shine babban Barna da kuskuren da zasu tafka sbd jinin wani karfi ne dashi baa zubar dashi a sake zama lafiya,
Wannan shawara ce da zaka sanar da daddies Dinka.”

Yana fadar Hakan ya taba sa ya wuce zuwa dining din sbd yin breakfast.

Kasa motsawa Haroon yayi sbd Baisan me zai fada ba.

Yana gurin tsaye Jamaal ya gama breakfast dinsa ya koma sama yayi wanka ya shirya ya fito a shirye qamshinsa na cika iskar gidan ya fice shida siddeeq sbd sosai yake aikin dayake gabansa Dan kasar gaba Daya Jin yayi fita ransa tafiyansa yakeson yi batareda yabar Haroon din ba Koda me zaayi kuwa,
Aikin kawai yake son gamawa ayi auren su tafi Babu ranar dawowa.

A gidan suka bar Haroon yanata sakawa da kuncewa har sai dare suka shigowa gidan ya fice Dan a matse yake dayake ya duba Ameenatou tinda yanzu Kam baida aikin yi bayan zama guri Daya harsai jamaal ya dawo.

Yauma kwata kwata Bata saukoba duk rarrashinta da duka gidan suka taru sunai mata haka ya gama ya koma Amma dai gwara yau din ta zauna Bata shige dakinta ba.

****Jamaal gaba Daya Jin yakeyi kaman ana konasa aqasar Dan haka ya toshe dukkanin hanyar da zata Bata lokacinsa akan abinda ya kawosa ya dukufa sosai akan aikin Wanda tini ya dauki hanyar kammaluwa sbd sosai ake Aiko na masu zallan ilimi gadan gadan ba wasa ba shirme.

Hafiz dayake ganin sauyi sosai a Haroon din dayake Gani Gurin Aiki da safe da Kuma Wanda yake Gani gidansu da daddare sai ya Saka Hakan akan gurin aiki daban da gida Shima Saiya janye daga nuna kusancinsu da Haroon din gurin aiki saisun hade gida suke fira da gaisawa yanda ya kamata.

Jamaal kansa mamakin Haroon din yakeyi sbd yanda zuciyansa ta gama mutuwa akan yarinyar bayaji Baya Gani Baya gane komai idan bana Yarinyar ba da har lokacin shi Yama kasa tsayawa ya riqe sunan.

Fahimtar irin son dayakewa yarinyar ya Saka Jamaal din Jin bazai iya barin Haroon ya rasata ba.

Ta bangaren su Dad kuwa duk lokacinda ya buqaci ganin Haroon Jamaal ne yake zuwa sbd bayason Haroon ya sake tsayuwa a gabansu Dan kada su lalata masa aikin treatment Daya basa shida mum akan lafiyansa da suketa kokarin ganin samunta Dan kuwa shiyasa suka buqaci komawansa tareda sakashi alkawarin komawan acan Dan kuwa abinda yake Sha Wanda Basu gane Menene ba yayi masa Mummunan illan da basason ma ya sani kwata kwata.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

45
Ranar da Abdul ya cike kwana hudu a Lagos Dan fara aiki a ranar su Dad Lameenu suka sake dawowa nasarawa maganar tsayar da aure hadda Abdul din aka taho Wanda Dad Lameenu ya jasa a jikinsa sosai yana masa kallan kaman ‘dansu duk Dan sbd ya sake dasu sosai ya samu aminta dasu har zuci ya yanda komai zai taho a sauki.

Sun sake zama anyi magana an tsayar da ranar auren sati uku hudu masu Wanda daqyar dai su Babbah suka aminta da Hakan sbd kwanakin sun musu kadan duk da ba wani biki sosai akace zaayiba Tinda a Lagos zaayi komai Amma hakama sun buqaci yafiyan duk wani abu da amarya zata buqata Amma Babbah ya nuna amincewa da Hakan gaskia sbd duk fafutikan rayuwar dasukeyi shi da su Abdul na inganta rayuwarta ne su Bata gata Dan haka dole zasu wadata ta da dukiyan aure kaman kowace ‘ya yar asali yar gata daidai karfinsu.

Su Dad din Basu wani ja da Hakan ba Daya dage Dan haka take suka gabatar da komai aka Yanke sukai Godia Suma su Babbah sukai godiya.

Wannan Karan harda dadah aka kirawo musu suka gaisa da ita da Ameenatou din wadda take sanye cikin doguwar Riga maroon sai veil data doro Akai.

Sun nuna yabawansu da nutsuwanta a fili sosai suka ringa sake yiwa Babbah godiya Wanda tini ya sake Jin hankalinsa ya kwanta dasu da mutuncin da suke dashi hakama Abdul ya sake tabbatar masa da mutuncin dasuke dashi harma agurin mutane Dan haka yake sake godewa Allah akan zabin da yayiwa Ameenatou dinsa Dayake ta addua da fata.

Da farko babbah baida niyar zaman Lagos din Amma a yanzu da Aure yakai ‘yar budurwansa yaji bazai iya zama a nesa da inda take ba tinda harsuna da inda zasu zauna din agidan Abdul Dan haka ya aminta da komawa Lagos din gashi Daman Hafiz ma Lagos din zaibi Haroon kaman yanda yayi masa alkawarin dashi zai koma Koda aikin site ya kammalu acan zai basa aiki a kamfaninsu.

Tsayar da ranar auren ya Saka Haroon shiga lokutan farin cikin rayuwarsa Dan haka ya sake nutsuwa sosai Yana mayarda hankali cikin aikin project din da Jamaal ya tsayu akansa Dan kammalawa ya tafiyansa Dan kullum Jin yake Yana sake matsuwa da barin kasar.

Haroon ganin irin kulawa da kaunan da mahaifinsa yake nuna masa ayanzu Dayake alfahari dashi dakuma ganin abubuwa nata dawowa kan hanya sai yaji soyayyar Dad dinsa na kashe masa jiki kaman bazai iya tafiya ya barsa ba Amma Bai bar Jamaal ya fahimci Hakan ba Dan Jamaal kwata kwata ya Dena bayyana a gaban su dad din sbd yanzu kauna zalla sosai Dad yake nunawa Haroon Dan haka yabarsa ya samu kaunar dabai samu daga Dad dinba Wadda yake tsananin so da burin samu.

***Su Babbah kuwa A nasu bangaren sosai hidiman tayi musu yawa sbd ga hidiman Shirin biki gata tashinsu duk da ba siyar da gidansa zaiyiba Yan haya aka Nemo zaa Saka Dan haka suketa shirye shiryen tafiya da siyarda abinda ba dashi zaa tafin ba.
Su mum Atee ma da zasu taho kawo kayan aure su lefe da masu gyaran amarya Babbah cewa Yayi su barshi acan tinda suma a satin zasu iso Daman sun zabi yin auren acan ne sbd kawowa kowa sauki dangin angon masu zuwa da Jamaar seelahs din da duka manyan mutane ne da manyan qasa hakama da Yan kasashen qetare sbd sosai Mam ya fito ya nunawa duniya auren dansa zaayi Kuma aure na alfarma na Manyan masu abin duniya Dan haka aketa shiri da Kuma miqa gayyatansa ga abokanan huldansu da manyan masu kudin da suke tare harma da gwamnoni.

Ita kanta amaryan Haroon Kuma budurwan Babbah farin cikinta kusan kullum Baya boyuwa sbd a kwanakin Dan kullum auren yake matsowa cikin tsakiyar ranta take sake Jin tsananin kauna da son Haroon Wanda ya tsayu tsayin daka ya tabbatarda ya dawo da sonsa sabo fil cikin ranta.

Daga shi har ita Hafiz yace ya rasa wanne yafi rawan kafar aurenba ita dai bata tanka Hafiz din sbd ta shirya masa duk abinda Bai zata ba bayan auren tinda a karkashin mijinta zaiyi aiki.

Duk hidiman auren da akeyi Jamaal Bai shiga ko dayaba sbd baida time ko kadan na batawa aiki yakeyi gadan gadan ba dare ba Rana Kuma Hakan saka su dad farin ciki yakeyi.

Ranar dasu Babbah suka gama parking zasu wuce Lagos Kuma jirgi zasubi dukkaninsu sbd murna Ameenatou har fita tayi yau ita kadai a Karan farko rayuwanta taje gidan kawarta Aminiyarta Khadija Tayo mata bankwana itama Khadijan satin zaa fara bikinta shiyasa bazata samu binsu ba ayi bikin da ita Dan haka suka hakura dole da samun bikin juna.

Fitowa sukai tareda Khadija din ta rakota har kusan Rabi kafin ta koma ita Kuma ta wuce.

Dayake hanyar site ne gidansu Khadijan tana kawowa gurin hanyar site din ya hango motar Haroon ta tsaya a bakin hanyar da zatabi ta wuce bakin shago batareda an Budeba.

Glass ya saukan aka miqo masa Abu daga shagon Wanda take kyautata zaton ruwa ne sbd bayan motarsa aka Saka masa.

Wani kyakkyawar murmushi me sanyi ya sauke daga fuskanta tana kallan motar ta tabbatarda shine a ciki bayan yanzu da sukai magana cemata yayi Yana Abuja.

Motan ta nufo tana daga wayarta Dan Saka Kiransa taji me zai fada mata yanzu Kuma.

Tana isowa motar ta miqa hannunta Daya akan mabudin kofan Baya Dan tasan anan yake zama siddeeq ne me jan motar
Tana budewa daidai Yana dagowa daga abinda yake Karantawa daga iPad din hannunsa ya kalli kofan motar da aka Bude Idanuwansu suka shiga cikin na juna
Shikuma a Karan farko Daya Kalli idon wata ‘ya mace rayuwansa bayan rasuwan matarsa.

Itama nata idanuwan kusan shine karanta na farko kallan cikim idan mutum Dan haka ta dauke fararen idanuwan nata tana sake wata fitinanniyar murmushi tareda shiga ta zauna Kai tsaye tana juyowa suka fuskanci juna qamshinsa na shigan hancinta Kai tsaye zuwa zuciyanta murmushinta Bai daukeba sedai yau din ta kasa kallansa sbd kunyar takusa zama matansa Kila yau takeji da wani shagwabbiyan murya ta dago ta zuba masa idanuwanta tace

“Shine kacemun kana Abuja sbd kada muyi bankwana kafin na wuce ko??”

Siddeeq Daya rasa ta inda zai fara gyaran matsalan Dake kokarin faruwa fitowa yayi da sauri daga motan ya zagayo ya rufe mata kofar Data shigo ya sake dawowa mazaunin driver da sauri ya zauna sai alokacin ya juyo ahankali ya saci kallan JEEY Daya zuba mata fararen idanuwansa Yana kallanta cikeda mamaki da shakkar ko tanada matsala ne Dan baisanta ba baima taba ganinta ba yake ganin.

Hadiye numfashi siddeeq yayi cikin Dan daidaita murya ya riqa JEEY din magana Yana washe Baki da nuna kulawa yace

“AMEENATOU,
barka da fitowa,yau ke kadai kika fita ne??

Hakan daya fada ya fada ne Dan JEEY yasan wacece din shiyasa ya ambaci sunan nata Kai tsaye Yana tada motar yaja ahankali suka bar gurin Yana juyawa Dan maidata gida.

Dauke idanuwansa JEEY yayi akanta tareda rufe iPad dinsa daidai lokacin ta sake motsowa kusa dashi tanason fada masa maganar da batason siddeeq yaji sedai tana motsowa da fuskanta Dan fada mata din Yana juyowa da tasa fuskan kadan ya rage fuskokinsu ya Hadu tayi saurin yin bayan kirjinta na bugawa ta dago ido ta kallesa Shi kuwa Kai tsaye ya Bude Baki yace siddeeq ya ajiyesa site.

Kasa magana tayi sbd kirjinta Dake bugawa har lokacin shiyasa har motan ta tsaya Bata iya cewa komaiba harya Bude motan ya fice yabarta zaune tana kallan inda ya tashi da ido fuskansa da numfashinsa Daya bugu fuskanta na dawo mata.

Gida siddeeq ya wuce ya ajiyeta Yana mata zancen aikin Dake gabansa ne duk suka Saka kansa daukan zafi shiyasa Baya cikin mood kwata kwata yau din.

Bata iya cewa komaiba ta Bude motan ta ficewanta tareda shigewa gida.

Mota ta musamman ce tazo ta daukesu guraren 2 na Rana tayi Abuja dasu daga can suna Isa airport ba Bata lokaci jirginsu ya daga zuwa Lagos.

Suna sauka Lagos Abdul ne da kansa yaje da motan Aliyah ‘yar Alh Lameenu wadda tinda Taga Abdul din taji yayi mata sbd batason namiji me kudin da shine zai juyata tafison Wanda itace me kudin Kuma yar me kudin dazata ringa yanda takeso baya hanata bare ma Saka ido Dan Bata wani zama kasar itama kullum tana yawo karatun ma duk ta kasa tsayawa tayi sai yawon kasashe.

Dayake Dad ne yace yaje da motan ya daukosu shiyasa ya taho da motan ya daukosu.

Gidan Abdul din a kusa da tsadaddiyar anguwan masu shi da mansions din seelah din suke yake Dan haka daga gurin mum Atey driver ya kawo musu abinci bayan isowan nasu.

Gida ne me maana Wanda ya bawa Babbah da Hafiz mamaki sosai sbd ace anbawa sabon ma’aikaci gida irin wannan me Dan yalwa da kyau da tsari Kuma komai akwai a aciki gaskia sedai Dan zasu hada zuria ne Amma tinda a cikin kudin aikin Abdul din akace kamfani zai ringa cire kudin haya sai sukafi Jin nutsuwa da Kwanciyar hankalin sakewa da Hakan.

Daki uku ne a gidan sai Palo biyu da kitchen sai back door da store sai kowanne daki da toilet dinsa.

Kowa daki Daya ya dauka Abdul Daya,Hafiz Daya sai su Babbah Daya sbd Ameenatou tafiyanta zatai gidanta Nan da kwanaki Dan haka baa Raba dakin da ita ba Amma dai na Hafiz itace a ciki da komai nata shikuma yana kwana Palo kafin ayi bikin Amma kayansa suna dakin Yaya Abdul Wanda nasa dakin na daga gefensa daban nasu Babbah ma Yana daga gefe daban na Ameenatou dinne a tsakiya.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

46
Haroon yanason dawowa Lagos Amma sbd kada ya zama ana ganinsa a Lagos Kuma ana ganin Jamaal a site yasakashi hakura ya zauna tareda Jamaal din Wanda Shima yafara kokarin Maida hankali ya gyara career dinsa data watse ta matsayinsa na lawyer.

A bangaren su Dad kuwa tsarin katin gayyatar Omar na musamman ne,

Duk tsawon shekarun Nan da basa tare bawai sun yanke muamala ne kwata kwata ba aa Suna waya da sauran gaisuwa a waya batareda kowannensu ya nunawa Dan uwansa komaiba,
Shi Bai taba yi musu wata maganar bare nuna wani abin daban kaman yanda suka Basu taba cewa komaiba bare nuna shakka fargaban yasan wani abin kawai dai kowa na nesa da Dan uwansa duk dubaru da nuna kaunarsu Bai Bata zuwa inda suke ba kaman yanda ya toshe hanyarsu ta zuwa inda yake iya Hulda da zumuntar waya sukeyi tareda nunawa juna kauna da kulawa a iya wayar sai yanzu da wannan kyakkyawar Daman ta taho musu wadda baida kowanne uzuri ko dalilin Badawa na qin zuwa auren Haroon Wanda sune ma ya kamata ace sinje Neman auren nasa batareda anje dashi Mam dinba Dan shine iyayensa.

***Ta bangarensu Amarya Ameenatou kuwa suna fama da kadaici da bakuntar sabon guri Amma irin rayuwar da suka samu kansu a ciki ta wadata ta Saka bakuntar zuwan musu da sauki ga Kuma hidiman da aketa kokarin farawa gadan gadan.

Su mum Atee dasu mummy Sarat da jamaarsu sun kawo lefen auren Wanda ya amsa sunan lefen gaske na auren masu abun duniya Dan kuwa sosai dadah da umman fadila datazo tarbon lefen sbd Jamaal da siddeeq harma da Haroon din suka girgiza da tarin kayan da aka kawo din tareda wasu mahaukatan sarkokin Dalma(zinari/gwal/gold).

Da dadah da umman fadila sai Jamaar amanar dadah biyu da suka taho bikin Tim daga Nasarawa Dan lasa arzikin Suma da Kuma tabbatarda amanarsu Dan idan Basu taho auren budurwan gidan Babbah ba yar gaban goshin dadah dasu Hafiz ai basuyi komaiba.

Duk da basuda wani karfi Saida Babbah ya fidda kudi masu Dan kauri a Dan abinda suke Tarawa na bikin ya Bada tukuicin da sedai masu aikin da sukai shigo da kayan ne suka karba Amma mum Atee Sam kin karba sukai suna nuna ai ba komai bazasu karba tukuicin ba bayan a cikin ransu dukkaninsu qyanqyamin taba kudin ma sukeyi sbd Yan dari biyar biyar ne a hade dubu hamsin cif.

Su umma anan duka wuni sunata duba kayan har dare suna sake Saka albarka da adduar fatan farin ciki me dorewa a auren.

Washe gari masu gyara na musamman aka turowa Ameenatou wadda za’a fara gyarawa Tin daga satin har satin auren Wanda ya rage saura sati biyu cif.

Ranar farko da aka fara yimata gyaran ta fara sauyawa abinta sbd fatarta irin me santsin Nan ce dake karban komai da wuri,

Farin ciki da dokin datake ciki itada Haroon ya wuce duk inda ake tinani sbd karfi da yaji duk yanda Babbah da Dadah suka Kai basa ganin laifi ko illan komai datakeyi Saida suka ringa Jin kunya da mamakin irin son datake wa Haroon Wanda ya Sakasu shiga tsoro da duqufa da adduar Allah yasa irin girman son dayake mata ya tabbata a rayuwar auren nasu yakuma barsu tare har karshen rayuwarsu.

Haroon a wannan lokacin yana cikin kwanakin farin cikin rayuwarsa me tsananin gaske da Bai taba samun kansa a cikinsu ba Wanda Hakan ya sanyaya zuciyar ‘dan uwansa da mahaifiyarsa akansa wadda Bata isoba har lokacin Amma ta sheda farin cikin Da Haroon dinta yake ciki Wanda takejin a matsayinta na uwa a garesa tayi missing Daman basa wannan farin cikin dasuke Gani tareda shi sedai tana Jin dadi har ranta daya samesa sanadin macen dayakeson.

Jamaal tausayin dan uwan nasa ne ya Sanyaya zuciyarsa bata cikin farin ciki ko walwala kwata kwata Dan Bai taba ganinsa a irin wanna kyakkyawar yanayinba tsawon rayuwarsu Dan haka yake tayasa farin cikin Samun abinda shi Bai samuba Dan kuwa a nasa labarin Bai taba samun farin soyayya a tareda wadda yaso din ba, duk lokacinda suka dauka a tare lafiyanta koyaushe itace abinda take gaban soyayyarsu Dan haka har suka rabu Basu taba samun kansu a cikin irin wannan farin cikin ba Dan haka baisan Menene yanayinba da yanda ake samun Kai acikinsa.

Koda yaushe a waya suke maqale da juna suna magana tana nuna masa duk abinda akai mata na gyaran Amarya Wanda kullum take sake sauyawa sosai tana fita budurwan datake cikin Hutu da gyara sosai Dan tinda suka taho Lagos din Bata sake fita ko gate ba daga gyara sai Hutu da AC datake Sha da lafiyayyar abinci me gyara jiki take ci.

Har lokacin Bai dawo ba Haroon din Yana Nasarawa n Abuja aikinsu gap yake da kammaluwa Wanda yake Jin kaman Yana Neman rasa kansa kafin gama aikin ya koma Lagos din.

****Su Dad so biyu suna turawa Omar jeden gayyatarsa a matsayin Wanda zai karbanwa Haroon din auren Amma Yana toshe buqatansu ta Hakan sai gashi hankalinsu Yana Neman tashi da Hakan Dan haka Kai tsaye Mam yayi masa maganar Amma still dai ayyukan gabansa bazasu basa Daman zuwan ba ya sake Bada uzurinsa sbd Koda suke maganar ba Baya Nan Yana Japan Dan haka Kai tsaye ya Saka Ahmed ya tura musu zunzurutun kudi a matsayin gudunmawarsa data Saka su Dad din shiga mamaki da baqin gaske me tsanani.

Tsaban kudin suka kalla suna sake shiga qyashin gaske da bakin cikin irin yanda ya debo kudi irin wannan me yawa ya Basu kusan 500m as gudunmawarsa.

Shiru Dad Lameenu yayi lokacinda suke cikin tinanin abinyi gameda baqin cikin da Omar yake Neman sakasu Dan kuwa idan har zaayi auren Nan Bai tahoba tabbas Babu amfanin yin auren babba a garesu Dan duka kudi da dukiya me yawan da aketa zubarwa ana Shirin auren da akeson duniya ta sheda auren SEELAHs duk Dan sbd Omar din yazo ne Amma Kuma komai Yana Neman lalacewa a daidai lokacinda Babu time na Neman mafita ko gyara.

Mam da hankalinsa ya rabu biyu a yanzu akan yanda komai na ayyukansu ke tafiya daidai da Kuma sauyin Haroon Daya fara Sakasa Jin so da kaunan Dan nasa me tsanani na cikeda sedai Kuma Yana shakkar Shima yazo yayi auren mace ta sauya masa shi yazo Kuma baida abinda zaiyi masa barazana dashi Dan tankwarasa Dan haka gaskia gwara ya kama dukiyan dayake son kamawa Koda yayansa sun juya masa Baya yanada abinda bazai taba Jin zafi ba.

Lameenu wani numfashi ya sake Yana dagowa ya Kalli Mam da Shima yake Nisa cikin nasa tinanin ya sauke numfashi Yana ajiye wayar hannunsa daya gama da BB akan a Turo Yan jarida gidan Babbah zasu tafi Kai masa ziyara Yana son a yada abinda ya hadasu din sbd Omar yaga abinda sukeson ya Gani.

Mam da Baisan me Lameenu ke nufi ba yace

“Kayi duk yanda zakayi Omar yazo kasar nikuma wanna Karan nayi alkawarin cike aikin komai da hannuna batareda matsala ko dayaba wannan alkawarina ne.”

Murmushin Daya tsaya iya fuska lameenu ya sake Yana Jin dadin Hakan Dan yasan aikin da Mam yasaka hannunsa da kansa aciki kaman cikan alkwarine Da Baya tashi cikar wannan aikin Dan haka ya sake murmusawa Dan shi a nasa bangaren ya gama yadda da indai akwai abinda Babbah ya sani gameda Omar da abinda ya Haifa to tabbas Omar Saiya taho wannan auren idan yaga Babbah a tareda su din.

**Da yamma a gidan Babbah Dad Lameenu yayi Sallah tareda su a masallaci bayan sun Dade suna tattauna maganar daurin auren ya bawa Ameenatou kyautan motan da ita aka taho gidan wadda ta tareda katin gayyatan da aka bugo na musamman me tsadan gaske.

Yan jaridan da BB ya turo sun dauko bayanan da yiwa motar hotuna da Kuma yiwa Babbah da Alh Lameenu din hotunan da suka fito da kyau.

Babbah Bai karbi motan ba ya Saka aka mayar akan bayan auren idan Ameenatou ta dawo hannunsu an Bata acan.

Dayake ba damuwa Daman sukai da lamarin ba Yana dawowa da ita aka ajiye kawai sedai a Daren aka hada labarin dasukeson a hada dauke da hoton Babbah Dana Dad Lameenu suna dariya cikin farin ciki dayake nuna shakuwansu da kusanci sosai.

Washe gari bayan Dad Lameenu din ya gama karantawa kallan fuskanta Babbah yayi wadda ta fito da kyau akan

“mahaifin Sirikitar Seelahs Mal Nuhu babbah ya nuna farin cikinsa da Jin dadinsa ga kyautan motar da sirikansa da kansu suka kawiwa yarsa har gida amatsayin tukuicin auren dansu”

Kai tsaye tareda invitation dinsu na musamman na auren da hoton dayake dauke da wainnan bayanan ya Saka aka yada kafin kace me labarin ya fara yaduwa har inda basa zato.


Greece

Dattijo ne Dan zaka zama confused akan shekarunsa and Hutu da wayayyar ilimin data gama ratsa rayuwansa Tako wanne Sako ya koma half bature kwatakwata.

Zaune yake a cikin lafiyayyar balcony din gidansa Mai tsananin yalwa da tsari irin na masu kudin gaske dayake Shan iska Yana sanye da farin glass Daya qarawa farar fuskansa kyau sosai da qara fitarda sirrin kyau da Kwanciyar hankalin da Allah ya wadacesa dashi yana karanta mahimman bayanai a Apple iPad datake hannunsa kafarsa Daya na kan Daya hakama gabansa table ne da laptop take Akai a Bude da alama itama wani sakon ya karanta kafin daga gefe qaramin tea cup ne Daya Sha coffee yabari a gurin.

Ahmed ne da Shima ya sauya sosai kaman wani lafiyayyan dattijon bakin bature Shima Hutu da kudi sun ratsashi ya iso gurinsa Kai tsaye da tasa iPad Shima a hannunsa.

Yana isowa kafin yace komai iPad din ya jiye a gaban Omar jeden Kai tsaye Yana cewa

“Ya kamata kaga abinda yake faruwa” ya nuna masa screen din iPad din.

Idanuwa Omar ya juya akan iPad din yana zare farin Glass din idanuwansa idonsa Kai tsaye akan fuskan Babbah da suketa azaban nema ya sauka a tareda Lameenu a gefensa suna dariya cikin farin ciki da shaquwa.

Hannuwansa Dake rawa ahankali yakai ya dauki iPad din a hannunsa Yana kafe hoton da ido kafin idanuwansa suka gangara akan abinda yake rubuce Wanda shine yake Saka Ahmed zufa da motsawan zuciya cikin tashin hankalin da Bai taba tinanin samun kansa ba.

Alh Omar Dayake Neman kasa gane komai saurin miqa hannu yayi Yana Neman ruwan Sha sbd yawunsa da suka qafe take.

**
SEELAHs sun shiga satin farin cikinsu Dan aikin project ya kammala an kaddamar
Fadan farin cikinsu Baya yiyuwa musamman Dad Lameenu dayake ganin sun tsallake rijiya da Baya Dan haka sune cikin farin ciki sosai.

Haroon sosai ya samu lambar yabo da karramawa tareda burge abokan huldodinsu da yawa ciki hadda turawa da yawa da suka yaba da aikin Dan haka take SEELAHs suka ringa samun manyan proposals masu zafin gaske Daya Saka su Jin duniya ta sake dawowa hannunsu Kuma a cikin satin suka samu sabuwar babbar Hulda daga Ashalawa wadda ta sake Saka kan Lameenu gigicewa shi Kuwa Mam a yanzu alfaharin gaske yakeyi da Haroon Wanda yake cikin farin ciki Shima sosai ya ringa Jin kaunar Dan uwansa na sake kere dukkanin abinda yakeso a rayuwarsa.

Dan haka a Lagos aka shirya hadaddiyar lafiyayyar dinner da aka barar da mahaukatan kudin gaske ta kammaluwan aikin.

Kusan duk wani babba dayaci ya tayar da Kai dayake mu’amalantar seelah ko sanatayya ya halarci dinner din wadda aka sakawa matakan tsaro da securities sosai.
Karfe goma Sha biyu da kusan Rabi aka gama dinner din wadda tsarinta yake na asalin Yan boko da masu kudin da muqami sai business tycoons kowa ya watse.

A daidai wannan lokacin da aka gama dinner din seelahs a wannan lokacin ne jirgin Omar jeden ya sauka a Abuja Nigeria.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

47
Sabon drivern da suke tareda shi tin Baya Wanda dashi kadai Ahmed ya yadda yayi contacting Tin kafin zuwansu ayau din aka tanadi lafiyayyar motan da zata daukosu daga airport har Mansion dinsa Dayake jere Dana Yan uwan nasa.

Babu amfani ko kadan ga gujewa zama gidansa dayake hade da masu tinda abinda yafi so da kauna duniyarsa fiyeda komai ta riga ta shiga hannunsu Dan haka ya yanke shawaran tinkaransu kaman yanda suka tinkaresa Dan yasan Nemansa ne sukeyi Kai tsaye shiyasa suka bayyanawa duniya fuskan Babbah Dan ya Gani duk da baida tabbacin sun gane asalin waye ‘yarinyar da suke Shirin aurawa dansu din Hakan yake son tabbatarwa Dan baida ikon kowanne irin motsin da zai Saka babynsa a hadarin da zai illata masa ita sbd a yanda aka kawo sauran kwanaki ne kadai suka ragewa auren bayajin Babbah zai fahimci abinda yake son ya fahimta Amma dai Kuma bayajin har abada zai iya bayarwa ko barin ‘yarsa da ita kadaice jininsa Kuma Jaden daya data rage ta shiga hannunsu Mamman.

A cikin Daren su dukkanin iyalan seelahs da suka dawo suka tararda koina na wutar mansion din Jden a kunne ta haskaka koina na zagayen gidan Wanda Hakan ya tabbatar musu da an kunna switch na wutan gidan gaba Daya dayake kashe hakama securities ne na musamman koina zagaye da gidan Wanda Koda suka fita hidiman bikin Babu ko Daya a mansion din.

Babban abinda ya sake raya mansion din shine matar Ahmed da yayansa biyu dasuke tareda su duka a cikin gidan Dayake kusan tsarin Mansion dinsa na can Greece Dan haka a cikin Daren ma’aikatan da duka aka Riga aka tanadar musu suka iso gidan cikin abinda Bai wuce awanni ba aka hau aikin gyaran gidan kafin su iso shiyasa Koda suka iso komai tsaf Babu abinda yake tashi sai kamshin freshners dana manyan humidifiers dana burners dayake tashi a duk inda ka Saka kafafunka da sanyin ACs da Suma suke aiki.

Ma’aikatan kusan guda biyar ne aka kawo dukkaninsu mata sai namiji Daya da shikuma harabar Mansion din itace tasa.

Mum Noor matar Omar da har lokacin ta riga ta rasa cikakkiyar lafiyanta akan abinda ya faru Bata Gani sosai hakama Bata iya tafiya sai akan wheelchair itama hakanan suka taho sbd yazo da niyar zama ya fuskanci wainda suke son fuskantarsa Amma zuwan na yarsa ne Daya danne dukkanin abinda yake ji akanta tsawon shekarun ya nesanta da ita sbd Bata kariya da rayuwar Kwanciyar hankali batareda tsoro ko fuskantar hatsarin dayake tattareda wata dukiyar ba,

Taimako da kyakkyawar rayuwar dayaso Basu itada su Babbah duk ya danne kansa ya janye daga garesu sbd koma huldan dazaiyi dasu a boye su Mam zasu iya bibiyan Hakan su mata illa.

Yayan Ahmed ba wani shekaru ne dasu ba sbd ya Dade sosai sosai baiyi aureba har Saida ya fara manyanta ma Dan haka suke Yara daidai kusan Ameenatou din Amma tama girmesu da shekaru biyu zuwa uku haka Dan babbar kenan sai namijin Wanda duka duka yanzu yakeda 10yrs zuwa 11 Dan haka masu aiki tini suka fara kokarin kaisu dakinsu Dan taimaka musu dasu wanka da sauransu.

Mai aikin da itace kaman babba a cikinsu sunanta Zahida itace ta Kai kayan kowannensu dakinsa ta fito ta nufi dakin yar budurwan wadda batasan sunanta ba Saida taji mom dinta ta ambaci sunanta da Fatmah kafin ta kama itama.

Abincin alfarma marasa nauyi irin Wanda sukasan zasu iya ci ne dayake dukkanin masu aikin kwararri ne aka dauko wainda albashinsu ma na musamman ne suka jere a makeken dining din Wanda Babu abin buqatan ci da Sha da baa jere ba cikin tsari.

Alh Omar ne a sama gaba Daya da mum Noor
A qasa Kuma Dayan bangaren Ahmed da nasa Iyalin ne dakin Fatmah daban hakama dakin Arfat daban.

Dukkaninsu Babu Wanda zai iya cin wani abinci a Daren sbd gajiyan dasuke tattare da ita,basa wani Jin yunwa sbd sunci snacks dasu tea da sai sauransu a jirgi so basa wani Jin yunwa Hutu kawai suke buqata.

Arfat da Bai Saba da koina ba hasalima shi Bai taba zuwa Nigeria ba tinda aka haifesa Dan haka kwata kwata qin yadda masu aikin su kusantosa yayi wanka yayi abinda ya shirya cikin kayan bacci ya fito ya nufi dakin Fatmah ya kwanta tareda ita itama duk da Bata san Kwanciya dashi Amma sbd bakuntan gidan ya Sakata kyalesa bayan sunyi sallah tea me zafi ta buqata daga masu aikin kawai Tasha ta kwanta.

Duk yanda Mam suka shiga mamakin abinda yake faruwa Basu nemesa ba sbd dare yayi Suma Kuma a matiqar buqatan hutun suke sbd hidiman da aka Sha Dan haka suka bari zuwa da safe Dan tabbatarda idan Omar jden dinne ya sauka Nigeria.

****Washe garin ranar da mamaki kowa ya wayi gari da ganin dawowan Wanda baa taba tinanin Gani ko yaddar zai dawo din ba wato Alh Omar jeden seelah wadda tini labarin ya fara yaduwa.

Mam da Lameenu da kansu suka taho yi masa barka da sauka cikeda farin ciki Mai tsananin gaske da nuna yabawarsu batareda nuna komai a fuska ba,
Shima Bai nuna komaiba cikin farin ciki da nuna kewan juna ya bayyana farin cikin ganinsu.

Fira suka zauna sosai cikin kewa da murnan kasancewansu tare da juna a yau din bayan tsawon lokaci sun Hadu a matsayin brothers da aka Sansu.

Mum Noor Bata nuna komai ba sbd ba komai ma ta sani ba Dan haka sosai aka Hadu anata murna da farin ciki musamman dasu mum Atey suka shigo hakama su mummy Sarat ma duk sun shigo hadda su Aliyah anata murna harma da matar Ahmed Aunt Didi Wanda take wayayyar mace sosai Kuma ta waye ga ilimi Dan haka ta saki jikinta ta sake acikinsu.

A tare duka ahalin sukai breakfast qatuwar dining din gidan Dad Omar ana sake tattauna bayan rabuwa da Kuma murnan auren Haroon Daya sake hada auren.

Bayan breakfast shigewa su Dad suka sake yi Babu Wanda yake jinsu suna palonsa anata maganganu.

Su mum Atee ma sun jima sosai kusan a gidan aka wuni gaba Daya sai daga baya kowa ya koma masu fita Kuma irinsu Aliya tini ta qara gaba duk da Dad Omar tana yinsa sbd Yana kaunarsu sosai hakama wasu lokutan idan ta Kalli tazarar dukiya Dan rayuwan dayake da shi da ‘yannansa su Dad dinta sai take Jin inama shine ya haifeta gashi a waye fiyeda Dad dinda da ilimin da kallansa kadai zakai kasan ya gama shigarsa Tako ina.

Sai dare Jamaar gidan suka samu Hutu da gidan yayi tsit sukaci abinci gaba dayansu a dining kafin kowa ya shige dakinsa yayi wanka ya kwanta Dan samun hutawa.

Washe gari Haroon ne da Bai samu zuwa ba jiyan ya taho yayiwa Dad din sannu da zuwa cikin farin ciki sosai.

Zuba masa idanuwa Dad Omar din yayi Yana karantarsa cikin nutsuwa da kulawa a matsayinsa n Wanda zai auri yarsa ta cikinsa.

Haroon sosai yake kauna da girmama Dad Omar shima Amma Kuma kusanci da kaunan Dake tsakanin Jamaal da Dad Omar din Babu Wanda zai iya shiga ko samun irinta Dan haka Shima Omar yake kaunar Haroon har ransa sbd kaunar dayakewa Jamaal da Dr Aleena Amma Badan mahaifinsa ba.

Haroon ya Jima a gidan Shima kafin ya fito Kai tsaye ya nufi ganin amaryansa.

A Daren Ahmed da Omar suka fita sedai Bai nufi gidan Babbah Kai tsaye ba Wanda suka samu bayanin komai nasa da gidansa,
Zuwa gidansa Kai tsaye yanada hadari Dan haka masallacin da babban yake sallah ya nufa Dan yin sallan ishai acan.

Babbah tareda Abdul da Hafiz suka fito daga gida suka nufi masallaci kowanne da sauran ruwan alwala a fuskansa Hafiz na latsa wayarsa Babbah na masa maganar meyasa yake zuwa da waya masallaci Hakan baida amfani tinda ba dadewa zaiyiba a masallacin.

Shiga masallacin sukai Babbah ne a gaba kafin su a bayansa suna shiga suka shiga sahu
Ana kokarin tayarwa Ahmed da Dad Omar suka shigo masallacin Kai tsaye gefen Babbah Omar ya tsaya Yana gyara tsayuwansa Dan tayarda sallan Ahmed ma gefen Omar din ya tsaya Yana gyara nasa tsayuwar.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

48


Babbah da baisan waye a gefensa ba sbd ya riga ya tayar da sallansa Dan haka hankali kwance da nutsuwa yake sallan hakama suma kowa ya natsu a cikin jam’in.

Dun Yana sallah ne Babu filin tinanin komai a zuciyarsa Amma dai Kuma ya tabbatarda ko waye a gefensa bako ne a masallacin Kokuma babban mutum ne sosai Dan qamshinsa me sanyi da nutsuwa ya tabbatarda Hakan kusan a duka sahun Babu Wanda qamshin me sanyi Baya shiga hancinsa.

Ana sallame sallar Babbah yana juyowa zai gyara zamansa idanuwansa suka sauka akan fuskan Wanda yake kusa dashi din take salatin daya debo daga bakinsa ya bace masa bat.

Juyawa gefensa Daya dasu abdul suke zaune yayi yaga hankalinsu Baya kansa adhkar kawai sukey,
Juyawa yayi bayasan yaga kowa abinda yake gabansa yakeyi da sauri ya sake dawo da kallansa gefen nasa ya sake kallan fuskan Omar ya kasa yadda da idanuwansa Gani sukeyi daidai Dan haka ya ambaci sunan Hafiz a hankali cikin nutsuwa yace

“Wannan bawan Allahn Dake gefena ka taba ganinsa a kuwa??”

Kallan Omar Dake zaune hankalinsa kwance Yana addua yayi yaga kwata kwata idanuwansa basa kansu hakama da alama lafiyayyan Mai abin duniya ne dan daga nutsuwansa da motsin jikinsa kadai zaka gane Hakan.

Girgiza Kai Hafiz yayi ahankali Yana dauke kallansa daga kan Dad Omar din Daya Burgesa Kai tsaye sbd wani sanyayyan kwarjininsa Daya cike idanuwansa dama duk Wanda ke kallansa Dan kaman kusan yakusa zama bature Dan fari ne sosai farin ma na Hutu.

Numfashi me dumi Babbah ya sake saukewa a karo na kusan biyar kafin ya juyo idanuwansa da suka sauya take ya Kalli Omar din baice komaiba Shima Omar din baice komaiba sai hannu Daya miqawa babban Yana Dan sake fuska da muryansa me Kamala yace

“Assalam alkm”

Cikin karfin hali babban ya miqa masa hannun Yana amsa sallamar Kai tsaye batareda ya kallesa ba kafin ya miqe tsaye Yana wucewa yabar masallacin.

Su Abdul cikin girmamawa sosai suka gaida Dad Omar din Wanda ya miqa musu hannu Shima Daya bayan Daya sukai musabaha Yana kallansu cikeda kauna da kulawa kafin suka bi bayan Babbah sedai suna fita suka tarar da ya bace musu da alama ya kama hanyar gida.

Hanyar gidan suka kama Hafiz na fidda wayarsa daga aljihu Dan Saka kira Abdul kuwa Kai tsaye hanyar gidan ya kama sbd zai fita da Dadah siyayyar turarukan wutan da zasuje yi itada umman fadila na MEERAH B PALACE masu fitinanniyar kamshin da duk amaryan datai amfani dashi Babu ta yanda bazata Hana zuciyar duk Wanda ya shaqa zaman lafiya ba Dan qamshine da a iya gurinta ne kadai ake iya samunsa.

Dayake washe gari ne kadai bazaa daura auren ba Dan haka Gyaran da akewa Ameenatou din ya koma so Daya a wuni maimakon so biyu sbd sauyin datai yayi yawa gaba Daya bazaka taba ganinta Kai tsaye ka dauka budurwan Babbah bace.

Babbah daga cikin masallacin Kai tsaye wani gurin ya nufa yaqi nufar gidansa Dan Bayaso abinda zai Kai Omar gidansa Kokuma abinda zai Saka a gansa da Omar ko a mafarkinsa kuwa Dan har abada baida alaqa dashi,
Alaqan Dake tsakaninsu sun Riga sun yanketa sbd shine kadai abinda ya Saka Ameenatou dinsu take raye,

Aurenta shine abinda zai sake Bata tabbatacciyar tsari daga mahaifinta da masu bibiyansa sbd zatai aure gidan arzikin da zasu Bata kariyan da duk take buqata Dan haka yaji Inama gobe ne daurin auren…

Aurenta kadai zai Hana Omar amsarta daga hannunsa duk da Shima Koda Babu auren bazai taba basa ita ba sedai bayan ransa kuwa Dan haka yaji tsananin dadin Daya kasance auren ya raba musu gardaman yaqin da zasuyi akanta.

Mema ya dawo dashi bayan tsawon shekarun da sukai Basu San inda yake ba baisan inda suke ba kowa na tasa rayuwar?
Tayaya Ameenatou zatasan bashine asalin mahaifin Daya haifetaba?bama zata San wannan gaskiyar me rugusa farin cikinta ba a yanzu datake cikin tsananin farin cikin aurenta da Wanda take mutuwan so.

Tafiya yakeyi batareda ma yasan inda yake jefa kafafunsa ba sbd tinani da tashin hankali harma da tsananin bacin ran dayake Jin Yana tasowa Yana rufe dukkanin zuciyansa na bayyanar Omar gabansa.

Tafiya Mai Nisan gaske yayi batareda yasan yayi ba har Saida yaji kafafunsa suna Neman kasawa kafin ya tsaya Yana duba inda ya kawo kansa Bai saniba.,
Kafin ya sauke numfashin zafin zuciyar Dake cinsa lafiyayyar motan dake daukan idanuwansa ta tsaya gabansa Batareda an sauke glass ba Ahmed ya Bude motar ya fito ya Bude kofar Baya inda Omar yake zaune Yana kallan Babbahn Ahmed yace

“Bismillah”

Jajir idanuwan Babbah sukai Yana yiwa Omar wani kallo abinda ya danne shekara da shekaru Yana taso masa Mai tsananin zafi da radadin gaske harma ciwo me nauyi.,

Shima Omar Babbah din yake kallan gashi anguwar tsit Babu mutane sosai Kuma akwai duhu Dan haka Babu Wanda zaisan waye suka tsaya dauka.

Ahmed ne ya sake kallan babban Kai tsaye yace

“Ko zaa taimaka Maka ne gurin shigan??”

Maganar Ahmed ta Saka Babbah dagowa ya kallesa Jan idanuwansa na karuwa sbd yasan me Hakan ke nufi,

Ahmed shine Wanda ya kawo sakon yafe Ameenatou da Omar yayi tin tana kwana Daya da haihuwa a duniya Dan haka tsana da zafin Omar Dayake ji daidai yakejinsu akan Ahmed.

Shima Ahmed a nasa bangaren zuciyarsa a shirye take da duka dangin Omar dana matarsa sbd Bai yadda da kowa ba akan Omar hakama zai iya taka kowa Babu ruwansa akansa,
Idan rayuwar Omar sukeso to tabbas saisun shirya daukanta Dan ba sauki ya shirya musu.

Abinda yake ji a zuciyarsa tsananta ta yanda ko numfashin iskan da Omar yake gurin Bazai iya shaqaba,
Hakama tayaya zasu fuskanci juna da Omar din?
Me zasu tattauna?
Meye a tsakaninsu?
Ameenatu ce Kuma ta rasu Dan haka ba sauran abinda ya rage Dan wannan Ameenatou din ya yanzu tasa ce Babu abinda zaisa ya tsaya ya sauraresa, idan ma zasuyi magana to yabari sai bayan daurin aurenta.

Takawa yayi a raba gefen Ahmed ya wuce Yana Jin kirjinsa na tsananta nauyi kaman numfashinsa ma zai toshe.

Motsawa Ahmed yayi zai bisa Omar ya dakatar dashi sbd Shima tasa zuciyar datai nauyi.

Tayarda motar sukai suka bar gurin sbd ganin kaman wata motar tafe Wanda Sam bayason asan Yama San Babbah sbd abinda ya lura ya karanta a tsakanin zuwansa zuwa yanzu shine su mamman basusan Ameenatoun itace Ameenatou Jden ba da suke tsananin nema Dan haka yanada Daman Hana auren ko dauketa kafin sanin nasu Wanda kowanne time zasu iya sanin Hakan sbd yasan sarai ana biye da takunsa da lamuransa shiyasa bayason bayyanarda sanayyarsa da Babbah.

Suna wucewa Babbah ya Nemi guri ya zauna Yana rintse idanuwansa sbd zufan Daya jiqasa me zafi,
Baisan ta inda zai fara barin Ameenatou tasan ba sune suka haifeta ba,
Idan ta sani kwata kwata bayason duniya tasan ita ‘yar Omar Jaden ce sbd hatsarin da rayuwarta zata shiga me girma,
Ba Dan bayason Omar ya Hadu da ‘yar tasa ne ba sai Dan barin su Hadu din asan yarsace komai zai iya lalacewa,
Ameenatou zata iya shiga hadari sbd ko bayan aurenta zata iya shiga hadarin duk da acikin masu arziki sosai zatai auren Amma Shima Omar din me kudin gasken gasken ne Amma aka tafi har cikin gidansa aka kashe Ameenatunsu tana cikin nakuda ba Dan Allah yasa Ameenatou rabo bace da yanxu baisan a wane matsayi rayuwarsa take ba Babu Ameenatunsa Babu abinda ta Haifa.

Ya jima a gurin zaune cikin tsananin damuwa da tashin hankalin da Bai Saka masa Rana ba Dan kuwa duk Jin yayi Lagos din fitar masa a Rai hankalinsa ya fara tashi matiqa.

Daqyar ya dawo da kansa gida sbd kirjinsa dayake wani irin ciwo da nauyi hakama zufa yake hadawa sosai ya kasa denawa.

Yana isowa gida ya shige daki batareda kowa yaga halinda yake ciki ba Dan sunacan sunata hayaniyar bikin da zaayi gobe Wanda Seelahs suka hada.

Omar ma yana komawa gida kusan damuwan tabasa tayi Saida likita yazo ya Danyi checking BP dinsa kafin ya shige cikeda damuwa Dan bayason nunawa Babbah karfinsa yanason ya aminta dashi suyi maganan Daya kamata kafin lokaci ya kure sbd idan ya nuna masa power kaman yaci mutuncinsa ne bayan Tsananin gata da son dayasan Yanawa ‘yarsa fiyeda yanda yake son nasa yayan na cikinsa.

Ahmed dayaji shikam baida hakuri ko lokacin batawa akan lamarin Yanke shawaransa yayi Babbah dole ya saurare abinda ake son fada masa Dan Jin Wanda akeson aji daga garesa.

A cikin Daren jirgi ya sauke Jamaal tareda siddeeq a Lagos batareda sanin kowa ba Kuma a Daren yayi magana da Ahmed Wanda basusan Jamaal na qasar ba Shima Dan haka da safe siddeeq ne yaje mansion din Mam seelah ya dauko Haroon Wanda a ranar yake cikin farin cikin dayafi na kullum sbd daga ranar sai ranar daurin aurensa da mutanensa da yawa Shima suna Lagos Dan halarta daurin auren goben.

Wata lafiyayyar tsadaddiyar Lodge din da Jamaal yake siddeeq ya Kaisa Yana shiga Jamaal dayake jiransa ya fito tareda siddeeq din suka barsa acan sbd Jamaal din na buqatan ganin Dad Jden.

A rumfar hutawan Dake bayan mansion din ta gurin garden suke wadda ta hada kofofin gidajensu uku batareda saika zagayo ya gate ba kake shiga tanan Dan haka yasa familys din suke kaman a gida gade guri daga daga baya Baya gaban mansions din ba.
dukkaninsu ne a zaune su uku sai Ahmed na hudu suna zaune cikin Hutu da nutsuwan Wainda arziki da Hutu ya ratsa fira sukeyi Hakama table dayake gabansu tea ne kusan kala hudu a different tea set masu kyau da tsada sai healthy snacks na Manyan mutane sai wayoyinsu da Kuma jaridan yau.

A Jden mansion baa yadda motar kowa nene ta shigo gidan ba iya ta masu gidan ce kadai take shiga ta Kuma fita Dan haka siddeeq baima nufi gidan Kai tsaye ba mansion din Dad ya shige sbd securities ma na ganin motar Haroon ce ta dawo suka wangale gate din ya shige da ita yayi parking.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

49


Fitowa Jamaal yayi daga motan sanye da sweatset ash na Ralph Lauren wandon mara tsayi da kadan ya sauka gwiwansa kafarsa sanye da sneakers na Louis Vuitton Ash fuskansa sanyeda fcap da glass na Versace Kai tsaye hanyar garden din ya nufa sbd siddeeq Daya sanar masa securities since su Dad na can garden din gidan Sir Jden.

Cikin nutsuwa ya nufosu Kai tsaye idanuwansa na kallan irin zaman Hutu da bayyanarda kusanci,so da shaquwan da sukai Amma abin baqin cikin dukkaninsu ba Hakan ne a cikin ransu ba Dan haka yaji tausayi da tsananin son Dad Jden na sake shigan zuciyansa sbd mutum ne dayake da tabbacin Babu tsatsa a zuciyansa.

Dad Lameenu ne yafara Ankara da tahowansa ya gyara zamansa Yana zuba masa idanuwansa da Shima suke cikin farin glasses Yana kallan fatan kafafunsa Dake bayyane sbd wandon Dake jikinsa sai daukan ido takeyi a fili karara sirkin bature da Nigeria.

Mam ma juyawa yayi ahankali ya Kalli Jamaal din Yana sake fuskan Dan yanzu Haroon ya zama hasken idanuwansa,
Sedai murmushin nasa Neman sauyawa yayi sbd idanuwansa Jamaal suke nuna masa Dan kuwa tafiyan da class da kamewan duk na Jamaal ne yake Gani Amma ya kasa yadda da abinda idanuwansa ke nuna masa da sauri ya juya ya kalli inda lameenu yake shima Lameenu din shi ya kalla kafin suka Kalli Omar a tare Wanda idan Jamaal ne sun tabbatarda zai fisu ganewa sbd shine ya taso Dashi a gabansa har girma Kuma sun tabbatarda suna tare haryanxu din,
Idan har Omar zaizo auren Haroon sun tabbatarda Jamaal ma duk inda yake Yana cikin Nigeria Kokuma Yana hanyar sauka cikinta ayau din tinda gobe ne daurin auren.

Omar da kallo Daya yayiwa Jamaal ya gane waye ke tahowa a natse cikin kulawa da bayyanarda kauna ya saki fuska murmushinsa me kyau Yana fitowa idanuwansa akan Jamaal din Wanda Shima shi yake kalla murmushinsa daya kusan Saka shayin Lameenu biyowa ta hancinsa Ya saki ahankali da nutsuwa..

Yana isowa gurin Omar ya ajiye cup din hannunsa tareda miqewa tsaye ya ware masa hannuwansa suka rungume juna.

Qamshin Jamaal din Mam ya shaqa da kyau yaji bana Jamaal din bane sbd yasan Babu wani qamshi da a duniya zai Saka Jamaal sauya nasa.
Lameenu ma qamshin Haroon Daya shaqa din ya Saka zuciyarsa Dake tsallen rawa Dan daidaita Yana miqa hannu ya zari tissue din gabansa ya Dan goge goshinsa Yana kallan Mam Wanda yake a natse hankali kwance sedai tasa zuciyar aciki tafi ta lameenu shiga wani irin firgita da karyewa Dan ya dauka Jamaal ne ya bayyana gabansa.

Cikin nutsuwa Jamaal Daya dago yana kallan Dad Omar bayan sun saki juna da sauti mara karaje ko sauri yace

“Dad Omar barka da dawowa”

Muryan ya Saka Dad Omar sake kallansa sbd Haroon ne da sauran yayansu ke kiransa Dad Omar Amma Jamaal Dad J kadai yake ambatarsa dashi.

Yanda Jamaal ya fuske bayan maganar Yana rungume Ahmed Wanda ya miqe cikeda farin cikin ganinsa da kaunan dayake masa Shima Mai tsananin gaske Yana cewa

“JAMAAL my man”

Murmushi Jamaal din yayi Yana Dan janyewa yace

“Haroon ne, JEEY Bai isoba tukuna Banda tabbacin ma idan zaizo din”

Dad Omar dayake kallan fuskansa wani murmushi me kyau ya sake Yana dauke kallansa daga Jamaal din Yana cewa

“Haroon Yaya hidiman?farko daya iso Nima na duka Jamaal dinne sai daga baya na gane,
Kamannin nasu nata sake rudarwa haryanxu dai.”

Ahmed ma Yana zaunawa yace

“Ni haryanxu bana banbance su,
Barr Yaya hidiman?
Inshallah zaka samu farin ciki da zaman lafiya da Kwanciyar hankali me dorewa bayan auren,my wishes kenan.

Murmushi Jamaal yakeyi Yana cewa “thank you, thank you”

Bai tsammanin tararda su Dad tareda Dad j dinba Dan haka dole ya sake Yana murmushi da sakewa sosai kaman yanda Haroon yakeyi sbd har lokacin Daya gaida su Dad din idanuwansu dai a kansa suke sun kasa tantance mema suke Gani ko ciki,
Dad Lameenu idan ya shiga wani hali Baya iya boyewa da wuri ake gane Hakan a tareda dashi sbd tinda jamaal din ya taho gurin duk da sun shiga shock a farko Amma ganin dai da gaske Haroon dinne Amma kwata kwata ya kasa Dena hada zufa karshe dai haka ya ringa Neman rikicewa a zance.

Mam kuwa hankalinsa kwance yake ci gaba da maganarsa suna tattauna ci gaban da Haroon din yake samu sosai ayanzu akan manyan ayyukan dayake handling da yanda zai karbi babban nauyi akansa bayan auren.

Sun jima sosai a gurin kowa da abinda yake zuciya da cikinsa hakama kowa a tsananin mace yake Daya tashi yaje ya tattauna abinda yake ransa Amma hakanan kowa ya fuske suke cigaba da fira cikin walwala da farin ciki.

Sallan azahar ne ya rabasu bayan sunyi sallah kowa ya wuce Dan hutawa a gida.

Suna rabuwa Mam da lameenu office suka nufa,

Suna shiga Dad Haroon ya kira a waya Kai tsaye yace masa

“Menene Dayan alkawarin daka mun bayan na project????

Haroon dayake zaune a dakin Jamaal Yana cin abincin dayayi order Yana Jin tambayar yasan me Hakan ke nufi Dad Yana zargin Haroon din dayake gabansa Dan haka Kai tsaye yace

“Alkawarin Nemo Maka duk inda Magajin Dad Omar yake Kokuma bayanin da zai nuna mana inda yake”

Numfashi Dad din ya sauke kafin yace

“Kazo yanzu Nan Ina office ka sameni Kuma ka zo da takardun aikinsu Chris  Jeremy.”

Kashe wayar yayi Yan kallan kofa sbd ya ji abinda yakeson ji Amma Kuma idan har da gaske ne zai gane idan Haroon din ya shigo.

Haroon na kashe wayar siddeeq yafara kira ya sanar masa inda takardun suke ya dauko Kai tsaye yakaiwa Jamaal Daya fito sallan tareda Dad Omar sunason magana Amma dai dama Dan haka address kawai Ahmed ya bawa Jamaal Kai tsaye ta waya da time a yau din zuwa dare.

Haroon Kiran Jamaal din yayi hankalinsa tashe tsoro na ciked zuciyarsa ya sanar dashi abinda sukai magana da Dad din a waya kafin Jamaal din ya nufi office din Dad din.

Koda ya shiga Dad Lameenu Yana tsaye Yana Kaida kawo sbd haduwan Jamaal da Omar su nasu yazo karshe Dan Basu iya da Omar dinba shi kadai bare Jamaal da kaman ma su da suke iyayen sune suke tsoronsa sbd zai iya ruguzasu tinda yasan hanyoyin yin qasa dasu.

Mam kuwa Jamaal din na shigowa ya miqa masa hannu Yana kallansa yace

“Takardun Menene wannan din?

“Chris Jeremy’s” ya Bada amsa Kai tsaye Kansa a kasa.

Dad na Jin Hakan ya jefar da takardun kan table Yana fuskantar Jamaal din yace

“Menene kake Jira haryanxu akan alkawarin daka dauka?
Kana ganin Dan gobe ne daurin auren Nan bazan iya dagasa fa har Sai abinda mukeso ya tabbata”

Dagowa Jamaal yai ya Kalli Dad din Kai tsaye Shima yace

“Ni nafara cika nawa farkon alkawarin komai ya tafi daidai sauran alkawarin da kayi na tabbatarda ka auramun yarinyar a gobe…….

Wuta Mam ya dauke Dad Lameenu kuwa dakatawa yayi daga Kaida kawon dayakeyi cikin rudewan zuciya da Kai Daya dauki zafi ya dawo gaban Jamaal din ya tsaya ya juya ya kalli mam dayake Jin kansa Shima Yana daukan wuta kafin ya sake dawo da kallansa Kam Jamaal kafin yayi magana cikin tsananin zafi da bacin Rai daya rufe Mam idanuwansa na rufewa zaiyi magana Lameenu yayi saurin taresa da cewa

“Ba lokacin fada bane muna tsananin buqatan sanin wani abu gameda magajin Omar ko yayane Kamun gobe a daura auren Nan,

Ana daura auren Nan zai juya ya tafiyarsa yabarmu batareda mun sani sani akan abinda ya sakamu tilasta masa zuwan na,

Jinina tafasa yakeyi Kuma bazai daina tafasa ba zuciyata bazata daina bugawan tashin hankali da baqin ciki ba idan bamu samu sanin abinda mukai shekarun Nan ba muna bibiyan son sani,

Rayukan da aka kashe duka an kashesu a banza,
Har matar Omar din dana yanka cikinta aka kashe duka an kashe a banza,
Hakama su kasim da jamilu da muka kashe da hannuwanmu duk da zamansu jini da Rabin jikinmu tin farko duk anyi a banza,
Duka a banza idan har daga karshen Nan bamu samu sanin abinda Omar ya haifaba da inda yake muka hadasa da Omar din muka kawar dukiyan ta shigo hannunmu,
Duka wannan komai da komai zai tashi a banza idan dukiyar Nan Bata dawo tamu ba,

Zamu rasa komai,zamu koma Asalin zero agaban Omar…..”

Maganganun cikin tsananin zafi da radadi tareda tafasar zuciyar yake fadansu idanuwansa jajir Dan kuwa an daura auren kaman yanda suka samu labari Haroon kasar zai bari Dan su BB sun kawo masa tabbacin Haroon din yakai Ameenatou anyi mata passport ba tareda saninsu ba bayan sun San ko garin Lagos Haroon Baya bari Saida izininsu.

Jin wannan maganar a bakin Lameenu ya Saka Mam Jin kansa ya qarasa daukan zafi Shima zuciyarsa wani zafi takeyi a quntace ya kalli Jamaal da idanuwansa sukai wani irin mugun jajir hannuwansa na wata irin rawa ya dunqule hannuwan sbd rawan da sukeyi tayi yawan dayake Jin zai iya raba Dad Lameenu Kamanninsa na asalin mutum Dan haka juyawa yayi kirjinsa na nauyin da Saida yayi saurin dafesa Yana dafa table din gabansa sbd wani mummunan jiran Daya dubasa kansa ma Neman kasa daukan abinda kunnuwansa suka ji masa yakeyi sbd sunayen dayaji suna ambatar sun kashe da hannuwansu,

Mutuwan granny dinsa Dayake matiqar kauna yaji a bakin Lameenu cewan Dad ne……wani irin sarewa kafafunsa sukai take ya durqushe a Gurin Yana riqe hannuwansa Dake tsananta rawa da zufa me tsananin gaske amma har lokacin Babu Wanda ya tsaya lura da yanayinsa sbd a rikice  suke Suma da tashin hankalin Dan sun tabbata Jamaal na tafe wlh.

Lameenu ne yafara tahowa gurin Jamaal din da sauri Yana cewa

“Ka tashi kaje kaman yanda ayau ka rudar dashi da kamannin Jamaal kaje ayau a matsayin Jamaal ka tabbatarda kaji wani abu gameda inda ‘dansa yake…

Mam Dayake kasa kallansa sbd baqin cikin halayen Haroon din wasu lokutan yace

“Alaqarsa da Babbah nakeson fara sani komai rintsi a Daren Nan kafin daurin auren gobe sbd kada mu daura aure da Wanda bamusan me muka Saka kanmu a ciki ba Dan Omar din Shima zai iya komai Dan ganinmu a qasa Dan haka a yau ka tabbatarda kasan alaqar Babbah da Omar idan ba haka ba wlh bazan daura Maka auren Nan gobe ba”

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

50


Jamaal take yaji Yana Neman samun attack na zuciya sbd bugawan datakeyi Daya wuce kaida da sauri ya miqe sbd iska datai masa karanci
Saiga BB ya shigo office din Yana kallan Mam yace

“Ranka ya Dade P.A din Chris Jeremy ne ya iso karban Sako gurin Barr” ya qarasa fada Yana kallan Jamaal Dake kokari da yaqin Neman iskan Data kasa wucewa cikinsa.

Cikin zafi da bacin ran dayake cinsu ya fizgo takardun Daya zubar a table dazu ya miqawa Jamaal Kai tsaye yace

“Yi signing ka miqa masa ya basa”

Siddeeq Daya shigo office din Shima a lokacin shine ya karbi takardun cikeda girmamawa daga hannun Dad din ya kawo gaban Jamaal Wanda dakyar ya iya riqe pen din da aka basa yayi signing ya fice daga office din.

Miqawa BB file din takardun yayi yace yayi yace yayi scanning nasu a tura masa copy din ta email dinsa ko na Lameenu.

Karba BB yayi Shima ya fice daga office din ya Satan kallan jamaal Daya fice zuciyarsa na shiga shakku Dan kuwa shidai yau JAMAAL idanuwansa suka nuna masa ayau din ba Haroon ba Dan haka ya shiga shakka da tsinkewan zuciya Dan wancan Karan a abinda Bai wuce daqiqa nawa ba ya kakasu prison din da aka gana masu azabar da take tayi kusan sanadin rayukan yaransa biyu.

Bayan ficewansu Dad Lameenu da sauri ya dauki wayarsa Yana sake hada gumi ya kira likitansa Dan Jin yakeyi kaman hawan jini zai sake kama sa.

Mam kuwa zaunawa yayi Babu abinda yake tafasa zuciyarsa da sake cike ta da baqin ciki da zafi sai murmushi da nutsuwan dayake cikeda rayuwan Omar tareda Kwanciyar hankali Dan sun tabbatarda ko crisis na business Baya samu idanma ya samu a take Ahmed ke handling nasu batareda da Omar y samu ciwon Kai ko damuwa ba a wuce gurin.

Amma su gasunan gaba Daya rayuwarsu kullum cikin tashin hankali da fargaba suke da shakka da baqin ciki duk da suna cikin arzikin Amma kwata kwata basuda nutsuwan zuciya Dana fili Dana boye musamman shi Baya tareda ‘dansa dayake cikin zuciyarsa fiyeda komai.

***Jamaal na fitowa siddeeq ne ya taimaka masa ya Isa mota yana shiga ya rufe masa ya zagaya da sauri yaja motar suka fice daga Mansion din cikin mugun speed siddeeq na saukan masa da dukkanin glss din motar sbd ganin yanda idanuwansa da sukai wani mugun ja ya rintse su numfashinsa na fita ba adaidaiba.

Suna isa Haroon da tinda Dad ya kira hankalinsa ya kasa Kwanciya Yana ganin Jamaal yaji gaba Daya gashin jikinsa ya tashi da tsananin tashin hankali sedai Jamaal kwata kwata Baya son komai face shiga dakinsa ya fasa abinda yakejin ya tsaya masa a kirji sbd yau yaji abinda ya jijjiga jarumtarsa da karfin halinsa.

Rufe kansa yayi a daki Wanda ya Saka Haroon juyowa da Sauri ya Kalli siddeeq kafin yayi magana siddeeq din ya girgiza masa Kai Kai tsaye alaman baisan komaiba tukuna.

Sake tashi hankalin Haroon yayi ya Isa kofan da Jamaal din yake ciki yayi knocking Yana Kiran sunansa cikin tsananin kulawa da fargaba.

Ganin ba alaman sauki ya Saka Haroon din karban key dinsa motarsa hannun siddeeq ya fito Kai tsaye gida ya ko zai fahimci wani abin.

Koda ya Isa gidan duka a hargitse da Yan biki da hayaniya sbd evening event din da zaayi a ranar mutane sun halarto manyan motoci Tako ina da securities Dan haka baima yi cikin gidan ba da Ayeesha ya Hadu ta sanar masa Dad Baya Nan duka matane cikeda da gidan anata Shirin tafiya event din wadda aka kashewa kudi bana wasa ba dan ita kanta amaryan kayan da zata Saka a ranar daga Dubai mum Atee Tayo odansa da duk abinda zaka Saka a event din hakama masu makeup dinma professionals aka aika na musamman Dan shirinta.

****Dad Baya gidan ya fita Dad Lameenu kuwa Yana samansa Yana hutawa sbd jininsa daya Dan hau likita ya basa shawaran hutawa jinin ya daidaita.

Hakan ya Saka Haroon komawa side dinsa Yana sakawa da warwara cikin matsuwa da kaguwan dawowan Dad ga mum dinsa ma ta kirasa Bata samu s
Jirgi ba aranar sai washe gari zata iso kusan ma ba zata samu aurenba Dan Koda zata iso kilama amaryan ta tare.

Bangaren Jamaal dayafi na Haroon din girma sosai aka gyara tareda zuba komai na Jin dadin rayuwa masu kudi sabo a cikinsa Nan amarya zata tare su umman fadila ne suka taho suka sake gyara komai tareda Saka abinda suka kawo na turarukan wuta da duka abubuwan da aka Siyawa Ameenatou din suna gamawa suka koma Dan nasu Shirin na tafiya bikin ranar.

Har lokacin event yayi Dad Bai dawo ba Dan haka dole Haroon ya fita yabar gidan Dan zuwa dubo Ameenatou wadda tana can ana shirinta Kuma ladies event ne kawai Dan haka tace saiyazo yaga kwalliyanta kafin kowa ya Gani.

Yana barin gidan Dad na dawowa lokacin duka an tafi bikin Babu kowa a gidan sai masu aiki Dan haka abinci kawai yaci a dining din palonsa ya huta sosai kafin ya fito ya nufi office dinsu Dan Kiran duba sakon da Chris Jeremy yace ya turo ta email ayi gaggawan dubawa.

Yana shiga office din BB ya shigo ya sanar masa tin jiya suke bibiyan Omar Kuma tabbas sungano alaman magana yakeson yi da Babbah sbd a masallacin anguwan babban yayi sallan magrib Dan ishai jiyan hakama yau acan yayi azahar da laasar yanzu ma daga can suke.

Mam na Jin hakan ya dago idanuwansa ya zubawa BB din Yana Jin kansa na shiga tinani.

Wayarsa ya dauka ya Saka Kiran Lameenu Wanda Shima ya gama hutawan zaune yake Yan amsa wayoyi saiga kiran Mam din ya dauka Yana Jin Abinda Mam yace ya kashe wayar tareda miqewa tsaye ya fito sanyeda jallabiya fara qal da wayarsa a hannunsa sai farin glass dinsa Dake fuskansa.

Mam na shigowa kafin yace komai Kiran Chris Jeremy ya sake shigowa wayar Mam Dan haka iPad dinsa ya dauka Dake kan table ya kunna Ya shiga duba sakon.

Abinda yagani je ya sakashi ajiye iPad din gefe ya miqawa BB hannu ya dauko masa glass dinsa na qara Gani dakyau ya miqa masa ya karba ya goge da tissue da kyau kafin ya Saka ya sake daukan iPad din ya sake dubawa dakyau.

Numfashi ya sauke ahankali tareda rintse idanuwansa ya Bude fes akan iPad din hannunsa zufa na tsatsafowa daga goshinsa Wanda Hakan ya Saka Lameenu daga Kai sama ya shaqi iska me zafi sbd ganin abinda ya Saka Mam zufa daga gashi to ba qaramin balbalin balai bane Dan haka hannuwansa suka jiqewa da zufa Yana zuba dukkanin idanuwansa da Kunnuwansa akan Mam din Yana jiran Jin Abinda zai fada.

Mam dago jajayen idanuwansa dasukai jajir din a take ya Kalli BB yace bani copies na takardun file din Chris Jeremy.

Da sauri BB ya juya ya nufi locker dinsu ta takardun sirri ya Saka pin ya Budeta cikin sauri ya Nemo takardun Daman sune a sama Dan shine ya ajiyesu bayan yayi scanning da photocopy dinsu.

Yana kawowa Mam da sauri ya karba hannuwansa na rawa ya budesu zufansa na karuwa ya jefa idanuwansa a inda signature din Jamaal take wadda tabbas tabbas da gangan Daman Jamaal yake Saka signature dinsa a duka aiyukan masu mahimmanci sbd signature din Haroon daban tasa daban Dan haka aiki bazai taba yiyuwaba Saida Wanda Saka hannunsa yake ciki shikuma Baya Nan Dan haka sunaji suna Gani zasu ringa rugejewa Daya bayan Daya.

Sakin file din Mam yayi da sauri Yana miqewa ya nufi locker din da kansa ya fizgo dukkanin files dinsu dake ciki na aikin miliyoyin da biliyoyin kudin da zaayi bayan auren dansa
Hannuwansa na wata irin rawa da jijjiga ya ringa budesu Daya bayan Daya Yana duba signing din dayake cikinsu duk na Jamaal Seelah ne ba Haroon seelah ba……..

Kasa tsayuwa yayi ya zube a kujeran datake gurin zufansa na tsiyaya kaman ya hadiye kunama da ranta.

Lameenu dayake tsaye Yana kallan Mam zufansa Tama Fi ta Mam din Dan kaman ana gobara a cikin jikinsa haka yakeji dakyar ya iya tattara yawu ya hadiyewa makoshinsa Daya Bushe yace

“Jamaal ne ko??
Jamaal ne ba Haroon ba,
Signatures din duka na JAMAAL ne ko??
Shine yake tareda mu duk tsawon lokacin Nan?
Shine yake tsaye a gabanmu da bakinmu mum sanar dashi har abinda Haroon Bai saniba ayau din sbd Haroon baisan dukkanin wainnan da na lissafo ayau mune da hannuwanmu muka kashesu ba…….

JAMAAL me mukai Maka??
Wane balai da masifa ne wannan?
Wace masifa Haroon ya sakamu bayan tarin wadda take gabanmu…

BB ma da tini zufan ta katse masa cikin fargaba da shakkar abinda zai iya biyowa Baya kallan Mam yai Wanda zuciyarsa ke Neman bugawa sbd zufa yakeyi sosai hakama zuciyarsa Bata bugawa daidai.,

Lameenu kujeran datake kusa dashi yayi saurin zaunawa Yana cewa

“BB yi sauri kirawo likita ya dawo bana Gani zuciyata Bugawa zatai jinina ya mummunan hawan da baa so yi sauri kirawosa”

Daga Mam din har Lameenu jininsu mummunan Hawa yayi dole Akai gaggawan Kiran Dr Koda yazo Lameenu yafi Dad shiga Mummunan hali Dan haka shi aka fara dubawa kafin Dad Wanda shi zuciyarsa bugawa take Neman yi kawai.

Dr na fita Haroon da BB ya sanar da Dad na Nemansa Yana shigowa BB ya rufe kofar.

Haroon dayake kallan Dad Lameenu dayake numfashi ahankali ahankali alaman ba cikakkiyar lafiya mayar da kallansa yayi gurin Dad dinsa Wanda ya dago jajayen idanuwansa yayi masa kallo Daya na tsaftan gaske ya tabbatarda Haroon ne a gabansa take ya daga hannu ya sauke masa wani mahaukacin Marin Daya Saka gefen bakin Haroon din fashewa da jini.

Dagowa yayi bakinsa na jinin ya Kalli Dad din sedai wani Marin Dad ya sake saukar masa Mai zafin dayafi na farko.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

51
Radadin Marin Kai tsaye a zuciyarsa yake sauka wadda take tarwatsewa aduk lokacinda mahaifinsa ya Saka masa hannu duk shekarun dayake dasu Wanda da yayi auren wuri da tini ya Tara Yara biyu ko uku.

Jajir idanuwansa sukai a karo na farkon dayaji zuciyansa na tabbatar masa da shidin ba komai bane a Gurin Dad Kuma har abada bazai taba zama komai ba a gurinsu,

A zero yake gabansu Kuma a haka zaici gaba da zama..

Yanda zuciyarsa ke radadi da qunan dayake tafasa jininsa haka ta Dad dinsa ke tafasa ya kallesa da jajayen idanuwansa yace

“Ayau nayi baqin kasancewa Wanda ya haifeka,
Nayi baqin ciki da Dana sanin barinka a qarqashin inuwata sbd har abada bazaka taba zama me amfani ba,
A yanda Aleena ta haifeka ba komai cikin kanka haka ka girma Babu komai a cikin kan naka dayekeda amfani ko buga Maka lissafi Mai amfani……..

Tsananin ‘dacin maganganun ya Saka Haroon rintse idanuwansa dasuke tsananin radadi sbd Jan da suke qarawa hannuwansa na rawa kansa na sarawa ahankali ahankali Yana qara qarfi.

Dad Lameenu da ayau tsaban shock baida karfi ko kadan a zaune yake Yana Jan numfashin wahala da ‘dacin zuciya Bude Baki yayi yace

“Ban taba daukan karshenmu a hannunka zai faro ba Haroon sai ayau din,
Ban taba sanin jinin kafiran dayake yawo a jininku na mahaifiyarku zai taba aiki a kanku ba wataran sai yau,
Haroon Ashe bakada Imani bakada ha nkali???
Tin yaushe ne Jamaal yake acikinmu batareda mun saniba???
Tin tsawon yaushe muke kirari muna dabawa kanmu wuqa a gabansa batareda mun saniba??
Jamaal da yayi alkawarin saiya mayar damu mabarata kafin ya San sirrinmu kenan yanzu Daya San hatta yanda muke kalan numfashinmu kana tinanin a mabaratan zai barmu yanzu???
Wlh Jamaal Saiya tabbatarda ko Baran idan munyi bazaa bamu sadakar ba….. innalillahi wainna ilaihirrajiun,. innalillahi wainna ilaihirrajiun,

Kallan Mam yayi jininsa na sake hayewa a rikice yace

“Wlh mamman Jamaal bazai rasa hada kwararan shedu akanmuba,
Bazai rasa recording na wasu maganganunmu ba……

Kirjinsa ne ke Neman rikewa Dan haka BB Dake tsaye Yana jiquwa da zufan Shima yowa kan Lameenu Yana masa fifita duk da sanyin AC Daya cike office din tsaf Amma dukkaninsu a jiqe suke da zufa.

Mam dayakeji zuciyarsa na tinkudo masa baqin cikin duniya da bacin Rai kallan Haroon yayi Wanda jikinsa keta tsananin rawan Dayake nuna da ciwonsa yafara tasowa Daman gashi tinda ya dawo mum Atee ta Dora daga inda ta tsaya.

“Haroon kaman yanda ka ha’ince ni kabi shawaran Dan uwanka da mahaifiyarsa kuka sakani wannan baqin cikin wlh saina nin ka masa Wanda yafisa Dan bazaka auri wannan yarinyarba wallahi indai nine na haifeka,
Bazaka samu farin cikin dakake tinanin zaka samu ba idan ma ka gujeni ka komawa mahaifuyarka,

Kaman yanda kuka rusamu wlh dakai zamu dawwama acikin wannan baqin cikin da rashin Dan kuwa idan baka sani ba ka sani wannan ciwon haukan Daya kwakwalwanka Babu inda zan zaka Daya wuce na tattara ka na aikaka asibitin mahaukata Koda kanka zai Bude,

Idan har lissafina ya buga daidai Dan uwanka yanda yake kwararren likita na tabbata ya karanci yanayinka Kuma bazai rasa bincike akan abinda ya fahimta tareda Kai ba Dan haka zuwa yanzu yasan mummunan Nisan da qwaqwalwanka yayiba a Juyewa Dan haka ka Saka aranka Babu maganar aurenka gobe wlh….

Dad Lameenu dayake cikin mawuyacin hali har lokacin dagowa yayi yace

“Yanda Babbah ke son ‘yarsa har abada bazai tabawa me tabin kwakwalwa auren yarsa ba kome zaayi kuwa Dan Haka takardun asibitinka kawai zamu basa a Daren ba sai gobe ba,
Maza ma ka fice ni ko ganinka Haroon a yanzu banason yi qaramin hawan jini yakeyi,
Ka cucemu Kaci amanar mu Kaci amanar kaunar da mahaifinka yake Maka.

Zuwa lokacin Haroon ba iya hannuwansa kadai ne suke rawa ba dukkanin jikinsa jijjiga yakeyi sosai hakama kansa tini yayi wani irin mugun nauyi Yana Neman inda zai fara bugasa bakinsa yakeson budewa Yayi magana Amma Dad Shima ko ganinsa bayason yi a lokacin sbd zai iya masa Baki idan Bai bar gurinba Dan haka Dad dinne ya fice Kai tsaye ko gabansa Baya Gani sbd Shima jininsa yayi mugun hawan Daya wuce misali.

Daqyar yakai kansa cikin gida yayi samansa ya shige bedroom dinsa Dan har lokacin Babu kowa a gidan Yan biki suna gurin bikin.

Dad Lameenu ma BB ne ya taimaka masa ya fice.

BB ne ya dawo office din ya kama Haroon daya qanqame gabaki Daya Yana rawan jiki sosai yakaisa har palonsa ya dawo ya rufe office din ya fice daga Mansion din.

Haroon rarrafawa yafara yi idanuwansa na ganin duhu da haske yafara kokarin Kai kansa bedroom Amma ya kasa sbd wani kifewa da yayi akan console mirror dayake hanyar bedroom din ya fado masa ya fashe.

Bugawa kansa keyi sosai hakama hannuwansa rawarsu ta tsananta sosai har tayi muni hakanan ya sake dafawa ya tashi cikin glass din Yana dafa Bango ya Isa kofar dakinsa yana shiga ya zube qasa Yana buga kansa sosai a tiles idanuwansa Dake rufe suna sake birkicewa.

Siddeeq kaman yasan abinda yake faruwa a mansion din ya dawo daukan Haroon sbd acanma Haroon jikinsa ya rikice zazzabi Mai karfin gaske da Bai taba yin irinsa ba ya rufesa Wanda ya bawa siddeeq tsoro hakama mum datake Kiran yayan nata Babu me dauka siddeeq din ta kira tanajin Jamaal ba lafiya taji hankalinta ya tashi Amma Kuma wannan Karan rashin daukan wayar Haroon yafi daga hankalinta fiyeda ciwon Jamaal Dan haka tace siddeeq ya dubo mata mansion din zuciyarta takasa samun nutsuwa.

Koda siddeeq ya Isa halinda ya samu Haroon yayi mugun girgizasa Dan Bai taba ganinsa a irin wannan mugun halinba duk tsananin ciwonsa kuwa.

Da gudun gaske ya qaraso inda yake ya tallafosa sedai Haroon din yayiwa kansa mummunan rauni jini Tako ina Dan haka a haukace ya daukosu gaba Dayansa ya fito dashi Bai tsaya wata wata ya Saka mota sbd ba qaramin munu lamarin yayi ba ya fice dashi zuwa asibitin SEELAHs din da gudun gaske.

Yana Isa aka karbi Haroon din da gaggawa Dan tini ya fice hayyacinsa Wani jijjiga kawai yakeyi sosai kaman me wani ciwon daban.

Fadan tashin hankalin da siddeeq ya shiga a wannan lokacin bamai yiyu bane sbd ya shiga tsoro Mai girma wannan Karan da ciwon Haroon din ga Jamaal a kwance ba lafiyan Shima.

Haroon sosai ya wahala cikin azaban ciwonsa Babu uwa Babu Uba Babu wani nasa sai siddeeq Wanda ya tsayu akansa har Saida ya dawo daidai sbd cikin qanqanin lokaci Allah ya mayar dashi kaman ba shine angon da zaa daurawa gobe ba.

Duk karfin zuciyarsa siddeeq sai dayaji tausayin Haroon ya karyasa sbd bayan dawowansa daidai Hawaye ne masu tsananin zafi da radadin zuciyan gaske suke gangaro masa batareda yace komaiba.

Sallan magrib siddeeq yake yaji daga can ya koma hotel ua dubo yanayin Jamaal Wanda ya Riga ya miqe haryayi wanka yayi Sallah
Siddeeq din na zuwa ya sanarwa da Jamaal halinda Haroon yake ciki.

Karban key Jamaal yayi shi kadai ya nufi asibitin gurin Dan uwansa.

Zuwansa asibitin Haroon na ganinsa hawayen tsananin kaunar Dan uwansa daya tabbatarda duk duniya ko mum dinsa Kila Baya kaunarsa yanda Jamaal din yake sonsa ne suka ciko idanuwansa suna gangarowa.

Jamaal Daya kasa masa maganar abinda ya faru ayau din sbd ganin yanayinsa daukansa yayi suka baro asibitin Babu me magana shiru kowa da abinda yake tinanin Amma dai shi Haroon zuciyarsa da jikinsa gaba Daya a Sanyaye suke sbd rayuwarsa yasan daga yau ta dena moruwa ne sbd aurensa dayasan har abada Dad bazasu taba barin ayi aurenba,

Rasa Ameenatou garesa tamkar zare control na tabin kwakwalwansa ne kaman yanda su Dad suka fada Dan haka idan har tabbas gobe ya tabbata ya rasa Ameenatou to ya cire Rai daga komawa daidai,
Yasan Jamaal da mahaifiyarsu zasu shiga tsananin qunci da baqin ciki akan Hakan Amma Shima kansa a yanzu yasan ko da auren Ameenatou ko Babu tabbas tabin kwakwalwa ne a tattare dashi me tashi Kuma me tsananin gaske.

Rintse idanuwansa yayi ahankali maganganun Dad da fushinsa da Bai taba Ganin irinsaba suna dawo masa a kunnuwansa take yaji ciwonsa na Neman sake dawowa ya dago jajayen idanuwansa ya Kalli Jamaal dayake tuqi a natse Shima zuciya da kansa duka a jagule da lissafi kala kala.

Cikin wata murya me sanyin gaske data Saka zuciyar JAMAAL sanyi akan fushi da bacin ran dayake ciki akansa
yace

“Jamaal,
Kayi mun alkawarin ganin na auri macen danake so matiqar ba Allah yariga yayi cewan ba matata bace,
Ko ban auri AMEENATOU a gobe ba Kai inason ka sheda itace macen danake so fiyeda komai a duniya bayan Kai da mum,
Son AMEENATOU wata jarabtace da Allah ya jarabceni da ita,
AMEENATOU itace macen da zanso har karshen rayuwata Kuma itace mace Daya da bayan ita Babu macen da Nima zan iya so.

Ko ban auri AMEENATOU ba bazan iya rabuwa da ita ba Dan haka Dan Allah Jamaal Karka bari su dadi su hanani samun farin cikin aurenta,

Aurenta shine Abu na karshe da zanzo kafin rayuwata tabar duniya…….

Shiru Jamaal yayi masa har suka Isa mansion ya shigo dashi har cikin harabar gidan wannan Karan shine da kansa ya fito motan tareda Dan uwansa dukkanin securities din gidan da sauran Jamaar dasuka dawo event suna harabar gidan mutuwar tsaye sukai ganin su biyun a tare Kuma kusan kamannin Babu Wanda zai iya banbancewa bayan raunikan Dake fuskan Haroon sai Kuma haske da jamaal yafisa sosai.

Mam da lameenu wainda suka Fito masallaci sallan ishai daqyar sbd radadin da zuciyoyinsu suke ciki mutuwar tsaye sukai lokacinda suka kawo su Jamaal dinma sun kawo cak kowannensu ya tsaya Mam ganin ‘yayan nasa a gabansa tare sai yaji zuciyarsa na narkewa da tsananin kauna da kewan kasancewa inuwa Daya dasu.

Lameenu kuwa kallo daya yayiwa jamaal yaji jininsa na son Hawa da sauri yai gaba
Shima Dad kafin kowannensu ya motsa ya gaidasa gaba yayi batareda ya waiwayosu ba ganin Haroon kawai Yana tafasa ransa.

Jamaal ajiye Haroon kawai yayi ya juya yabar gidan Kai tsaye gidan da zai Hadu da Dad Omar a daren ya wuce Yana kallan time.

Suma acan bangaren tin ana sallan ishai Yana fitowa masallaci Ahmed yayiwa Babbah abinda baisoba waton nuna masa power Kai tsaye sojoji ne suka daukesa daga kofar gidansa suka wuce dashi shi kuwa Haroon da Jamaal na ajiyesa ko zama baiyiba Shima ya fice gidan yayi gidansu Ameenatou Kai tsaye Yana Isa motar na wucewa da Babbah Dan haka ko gidan Bai shiga ba Shima yabi bayansu.

Sun isa da Babbah motar Jamaal ma na Isa Dan haka kusan da Ahmed din da Babbah dayake kallan Jamaal da dukkanin Idanuwansa da tsoro da shakka harma da fargaba tare suka shigo palon da Dad Omar din yake zaune.

Dayake bayason asan da Yana gurin ko makamancin Hakan ko securities Babu a gurin sbd guri ne da bazata taba tinanin samunsa agurin ba bare a biyosa.

Su kansu su BB Dake bibiyar Babbah ganin sojojine suka daukesa sai basuyi gangancin binsu ba sbd yanzu a ankare suke tinda Jamaal ya bayyana komai zai iya faruwa juyawa sukai Dan sanarda dasu Mam.

Haroon da Shima ya shigo da motarsa gurin yayi parking Yana ganin motar Dad Omar data Jamaal a gurin bayan Kuma yaga lokacinda sojojin suka ajiye babba suka fice take kirjinsa ya sake daukan nauyi Yana bugawa Dan haka Kai tsaye ya wuto ciki Shima.

Babba ne yafara maganarsa Kai tsaye da cewa

“Meyasa ka gayyato Haroon anan??
Kanason yasan ko Kai din wanene?
Kanason yasan kaine asalin mahaifin AMEENATOU wadda ka tsallake ka bari ranar da aka haifeta????

Cak Haroon ya tsaya bakin Kofar batareda ya qasara shigowa ba sbd gagaruman kalaman Babbah da suka shiga kunnuwansa.

MAMUH

DR JEEY SEELAH

AMEENATOU SEELAH

UNEXPECTED

CRAXYLOVE

ROMANCE

DEEP

LA HOT

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

52
Dip yaji jinsa Dan ganinsa na Neman daukewa sbd tsananin girgiza da rikewan abinda kunnuwansa suka ji.

Hannunsa Daya iya dagowa da kyar ya bubbuga kunnensa Dan Jinsa Daya dauke take ya dawo idanuwansa da Basu koma daidai ba suna sake rikidewa Dan Bai taba jinsa cikin mummunan tashin hankalin dayake Jin kansa a daidai wannan lokacin ba idan har AMEENATOU dinsa itace jinin Dad Omar din dasu Dad da shi kansa suka ringa dakon nema a tsawon shekarun Nan.

Babbah kuwa da zuciyarsa har lokacin radadin gaske takeyi kallan Omar din yayi Yana cigaba da cewa

“Me kace akan Ameenatou din?
Zaka Nisanta damu sbd Bata kariya
To meyasa ka dawo?
Shin ka manta irin masifar da kusancin naka da ita zai iya jawowa?

Sanyi muryansa tayi jikinsa da bakinsa na rawa cikin mutuwar jiki yace

“Ameenatou itace hasken zuciyata da idaniyata,
Ameenatou itace walwala da farin cikin rayuwata data iyalina,
Ameenatou ita kadaice jinin jinina Danake Gani,
Ameenatou itace nake kallan tawa Ameenatu din a cikinta meyasa zaka dawo Omar?
Meyasa zaka dawo daidai lokacinda take gap da samun farin cikin rayuwarta?
Omar na rokeka da Allah ka koma inda ka fito batareda kowa yasan alaqar da muke da ita dakai ba,
Ameenatou batasan tayaya zata fara karban cewan ga mahaifinta ba a tsaye gabanta wani ne ba ni ba….

Su kansu sirikanta Babu ta yanda Rana tsaka a ranar daurin auren kawai ace musu wani ne mahaifinta ba Wanda suke tinanin sun karba auren a hannunsa ba,

Hakama sanar dasu Hakan dole muna buqatan yimusu qarin bayanin yanda Akai tabar hannun mahaifinta ta dawo nawa hannun,
A wannan gabar me zamu ce musu?
Me zamu sanar musu?
Cewa zamuyi anyiwa mahaifiyarta kisan gilla a gaban idanuwanmu aka yanka cikinta da cikin wata Tara a jikinta????
Ce musu zamuyi a hannuna jininta ya tsayaye Ina kallo ta sadaukar da rayuwarta ta haife cikin jikinta bayan yankan wuqar daya Huda cikinta da kirjinta???
Ce musu zamuyi a wannan ranar da aka haifeta ka tsallake ta ka barta duk akan ana bibiyar rayuwarka zaa hallaka ka??

Jamaal Da kusan Shima mutuwar tsayen yayi sbd shock da tarin mamaki da hada sauran bayanan dayaji a bakinsu Dad da bakinsu ayau din komai Yana haduwa acikin kansa Amma Jin irin kisan da Akaiwa Aminatu a bakin babban ya Sakasa rintse idanuwansa Yana Jin kaman jiri zai daukesa,

Meyake faruwa a duniyar Nan da suke ciki ne?
Wane irin buri ne da son duniya ya Saka su Dad shiga wannan mummunan qazamiyar kaddarar ta kashe kashe irin na zallan rashin Imani????
Bayan irin kisan da sukaiwa Aminatu matar Omar din mahaifiyar Ameenatoun ahakan suke sake bibiyan rayuwarta Baji ba Gani Dan su qarasa aikin da Basu qarasaba shekaru….. innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun?

Omar shiru yayiwa Babbahn idanuwansa jajir Yana Jin zantukansa na shigarsa suna dawo masa da komai tareda yanka zuciyarsa.

Ahmed ne ya katse babban cikin radadin zuciya da kasa dannewa da cewa

“Duk wannan abin da kake fada akan rabuwarsa da gujewansa tareda bawa Ameenatou kariyan da Kai da tasa sadaukarwan zasu tashi duka ne a banza Dan da hannuwanka gasunan zaka miqawa wainda ke bibiyan rayuwar tasa da tata ita a bainar jamaa gobe..
Da kanka zakai kirari ka dabawa kanka wuqa sbd su sirikan da kake magana sune jinin Omar din Kuma sune masu Neman jinin nasa.

Wani kallo Babbah ya juyo Yana yiwa Ahmed kafin ya mayar da kallansa kan Jamaal da Daya kasa kallan kowannensu Idanuwansa jajir Yana rintse su sbd kunyar abinda duk ake fada ana magana ne akan rashin Imani da Barnar mahaifin Daya haifesa.

Kan Omar Babbah ya mayar da kallansa Yana Jin zufa na tsiyayowa har ta cikin kansa da kunnuwansa Dan haka ya zare hular kansa yayi wurgi da ita Yana cewa

“Omar me nake ji?
Me yake faruwa?
Menene yake Kuma Shirin faruwa?
Shin balain ne ya dawo da masifar kokuwa wace balain ce take Shirin dawowa??
Meye hadinka da SEELAHs???

Kallansu yakeyi Daya bayan Daya a rude Yana Neman Karin bayani Dan kansa Neman Juyewa yakeyi da tashin hankali da tsoron abinda zai iya faruwa idan wani abu ya samu Ameenatou dinsa.

Omar ne ya dago tareda tashi tsaye Yana fuskantar babban idanuwansa jajir yace

“SEELAHs shine Nima nawa asalin sunan ba Jden ba?
Mamman seelah, Lameenu seelah, Omar seelah da Yan uwanmu biyu da suka rasu kasim da jamilu seelah Yan uwan jini muke,
Dukiya itace ta lalata jinin dayake yawo a jikin kowannenmu na alkawarin tsira tare mu mutu tare,

jinin yan uwanmu ne Daya zuba akan dukiyar ya gurbata dukiyar ta Saka mu samun Kanmu a mummunan halinda muke ciki a yanzu na bibiyan rayuwar Yan uwanmu Amma ka sani har abada bazan iya rabuwa da yata ba a yanzu kaman yanda nayi alkawarin Bata kariyar da ban samu bawa mahaifiyarta ba,

Ameenatou a yanzu itace babban abinda duk wani maqiyana yake Neman samu,
Ameenatou itace mukullin dayake riqe da duk wani abinda Dana mallaka,
Ameenatou itace mamallakiyar dukkanin tarin dukiyar Jden a rubuce Dan haka samunta a shine mafi farin cikin cikan burinsu,
Sanin wacece Ameenatou shine babbar hatsari da tashin hankalin da dukkaninmu zamu fuskanta Dan haka Babu maganar aurenta a goben Dan har abada bazasu taba Dena Neman ba har sai ranarda suka samu sanin waye magajin dukiyar jdens gaba dayanta.

A rubuce dukkanin dukiyata da abinda na mallaka nata ne,
Ahmed ya sani ayau Kai da Jamaal inason Kuma ku sheda Hakan sedai ku sani barin asan wacece ita shine karshen komai.

Kallan babbah Daya gama jiqewa da zufan gaske hankali tashi yayi kafin ya Kalli Ahmed ya zaune dashi ahankali ya fara zayyano masa asalin tarihinsu da komai tin daga barowansu gaban iyayensu har zuwa yanzu da suke maganar.

Kuka wiwiwi Babbah keyi dukkanin jikinsa na rawa sbd shiga tashin hankali da tsoron rayuwar dasuka samu kansu dumi dumi aciki ta masifar da Bai taba ji ba…

Jamaal ma kusan silalewa yayi kan kujera wannan Karan da hannuwansa biyu ya Saka Yana rintse idanuwansa sbd kansa Dake Neman bugawa tareda zuciyarsa….

Ahmed ma da tinda yake da Omar din baisan asalin asalin mafarin komaiba sai yau din sbd kaf duniya yanzu Babu Wanda yasan ba uwa Daya Uba Daya SEELAHs suke ba sai yau din,
Ko Jamaal da Haroon dasuke yayan cikinsu da matayensu Basu taba sanin wannan sirrin ba sai yau din da Omar yake fada musu da bakinsa cewan ba uwa Daya Uba Daya suke ba…

Dukkaninsu Dake palon silalewa sukai qasa kowa kafafunsu na kasa daukansu,

Duk tsananin jarumta da karfin halin Jamaal Hawaye ne suka ciko jajayen idanuwansa yanajin wani abu me nauyin gaske ya tsaya ya tokare kirjinsa sbd baqin ciki da radadi tareda kunyar abinda ake fada mahaifinsa na ciki,

Makashi ne ya haifesa?
Makashin Yan uwansa da wainda Basu da hakkinsu na komai shine mahaifin Daya haifesa,
Mahaifinsa shine makashin kakanninsa da macen da harya mutu bazai taba Dena Sonta ba…..
innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun

Babbah kuka yakeyi sosai hankalinsa da gashin jikinsa duka suna tashi,

Shi kansa Omar da sai yaune ya Bude Baki ya iya furta abinda yake ransa qunshe tsawon shekarun Nan Bai taba maganar dayake cin zuciyarsa Yana saukar masa da radadi mafi ciwo na yanda shi da Yan uwansa suka kasance,
Tin suna Shan nonon iyayensu suke tareda juna a guri Daya aka haifesu suka taso tare batareda ko a takalman sakawa iyayensu sun banbantasu sbd kauna junan datake yawo a jininsu tin
A iyayensu take acan ta samo asalinta har a nasu jinin,
Sun tashi da kauna me karfin gaske a tsakaninsu Amma yau rayuwar junansu suke nema,

Wannan abin ne yake Saka Omar baqin cikin Daya zauna zuciyarsa yake cinsa akowace daqiqan rayuwarsa Dan haka yau Daya samu furta sirrinsu hawayen ne suka gangaro masa a Karan farko sbd a yanzu bayan su ukun dasuke gabansa Babu Wanda ya yadda dashi Akan yarsa,

Su uku sune wainda yasan zasu tayasa bata kariya da rayuwarsu Dan haka ya juyo da idanuwansa akan Jamaal Wanda shi kadai ne Seelah Daya dayake Jinsa har cikin ransa Kuma ya yadda dashi fiyeda rayuwarsa kaman Ahmed a Sanyaye yace

“My son Ina tsananin baqin cikin hanawa Dan uwansa wannan auren sbd ba Kai bane,
Kai kadai ne namijin dana yarda na bawa aurenta na jefata cikin SEELAHs batareda naji shakka ko tsoron Hakan ba,
Kaine Wanda zan bawa amanarta ko Bada aure ba Amma kwata kwata zuciyata Bazata taba samun nutsuwa ko Kwanciyar hankalin bawa Haroon aurenta ba Badan komai sai Dan rauninsa ga mahaifinsa Wanda ba ita kadaina akanta shi kansa tasa rayuwar a hadari take…..

Dago jajayen idanuwansa Jamaal yayi ya zubawa Dad Omar din tareda girgiza masa Kai bakinsa na sake daukan nauyi sbd tsananin son da Dan uwansa yakewa Ameenatou din idan aka rabasa da ita matsalar ciwonsa zata iya Maidasa cikakken mahaukacin dayake tsananin tsoron ya koma,
Bazai iya kallan Rabin jikinsa Haroon din ya koma Hakan ba,
Zai iya sadaukar da rayuwarsa akan lafiyan Haroon da Kuma samar masa macen dayake so fiyeda nasa ran Dan haka ya Bude Baki bakin cikin muryansa Daya shaqe sbd tsananin tashin hankali da baqin ciki harma da shock yace

“Dad Dan Allah Karka Hana Haroon auren Ameenatou,
Ameenatou itace farin Daya Kuma nutsuwa Daya rak Datake riqe da rayuwar Haroon,
Hana masa aurenta tamkar rabasa da lafiyarsa ne gaba Daya,.
Haroon Yana yimata tsananin son da bazai taba barin komai ya faru da ita ba Koda hakan na nufin zai gitta tasa rayuwar”.

Kuka Babbah ya sake fashewa dashi sbd gano gaba Daya su rayuwarsu acikin seelahs din da aurenma gaba Daya a duhu suke Babu Abu Daya dayake gaskia sai soyayyar da Ameenatou dinsa takewa Haroon sbd Jamaal da Haroon dai mutum biyu n mabambamta da suka ringa wasa da zuciyar Ameenatoun,

Tayaya zai bari Ameenatou tayi aure a cikin wainnan mutanen da yanzu ma tsoro suke tsananin basa bayan Omar din da Ahmed sai Jamaal din Wanda yaji yamafi samun nutsuwa dashi.

“Bazan taba bawa Haroon ko Daya daga cikin zuriar seelahs din auren Ameenatou ba gaba Daya har abada” babban ya fada Yana dagowa jajayen idanuwansa Yana kasa kallan Jamaal Daya cike masa ido har lokacin Hawaye ne ke zubowa daga idanuwansa…..

MAMUH
THE SEELAHS
THE JDENS
LOVERS
MARRIAGE
AMEENATOU JDEN SEELAH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

53
Maimaicin fasa aura masa Ameenatou da akeyi ne ya Saka kansa kasa dauka hannuwansa suka fara rawa hakama kafafunsa,

Toshewa kirjinsa yakeyi Yana Jin kaman bazai iya Jan numfashi ba ga idanuwansa da suka fara ganin babbiyu Dan haka yafara bin Bango Baya Gani sosai ya juya Yana dafe gefen kansa da hannu Daya Yana kokarin Bude idanuwansa dakyau da basa Gani sosai bayan gasu a buden.

Tsananta rawa jikinsa yakeyi sosai,
Mummunan faduwa yayi Yana gap da Isa motarsa sbd tsananin da jikinsa yayi Dan haka da rarrafe ya nufi kofar ficewa ya fice yabar Motarsa a gurin Yana rarrafawa duhun gaske Yana qara rufe idanuwansa.

BB dayake nesa sosai daga gidan sbd bayan ya koma Mam sakashi dawowa yayi akan ya tabbatarda ya riqe tsawon lokacin da suka dauka a tare Dan haka ya dawo batareda ya tabbatarda su waye da waye a cikin gidan ba gashi Kuma Yana shakkar Isa gurin sosai ko shiga a samu matsala Dan baisan takun Jamaal ba.

Idanuwansa akan gidan da duk motsin dazai fito cikinsa yake Dan haka Yana hango motsi ya fito daga maboyarsa ahankali tareda Dan biyu duhun ya iso gurin daidai lokacinda Haroon yake fara buga kansa a Kan titin dayake tsit Babu kowa ko motsin komai..

Tareda yayi da sauri tareda rufe masa Baki ya janyesa da sauri daga gurin yayi cikin duhu dashi Yana Jin kirjinsa na harbawa Yana leqa hanyar gidan baiga ko motsin kowaba dazai fito daga ciki.

Sunkutar Haroon yayi gaba Dayansa duk girmansa sbd shi kansa BB din ba qaramin Mai qarfin gaske bane sbd a Bude yake kaman basamude.

Gurin motarsa Dake nesa da gidan ya nufa dashi ya Bude ya Sakasa ciki tareda rufe motar yana juyawa yaga har lokacin Babu kowa yaja motar yabar gurin da sauri sbd Baya buqatan cigaba da jiran indai Haroon daga ciki yake tareda su Omar din yasan me zai masa duk abinda suka tattauno zasuji koma Menene adaren Nan.

**Jamaal irin roko da tabbaci tareda alkawarin da yayiwa Dad da Babbah akan auren ya Saka jikinsu sanyi Jin irin halinda Haroon yake ciki da ciwon dayake cin kansa batareda shi kansa ya sani ba,

Sanar dasu yayi alkwarine ya dauka ana auren zai tafi tareda Haroon din da Ameenatou gurin mum dinsu acan zasu zauna duk wannan yaqin batareda ko dayansu cikin su biyun ba zaayisa wanna alkwarine yayi musu.

Kallansa Dad Omar da idanuwansa sukai jajir yayi sbd Babu abinda Jamaal zai rokesa a rayuwarsa yaji bazai iya basa ba Amma kuma yanzu ana magana ne akan ‘yarsa da Bai hadata da kowaba hakama tafi komai na duniyar Nan Daya mallaka mahimmanci da daraja Mai girman gaske a zuciyarsa.

Babbah a nasa bangaren farin cikin Ameenatou ne kadai abinda yake tsaye a ransa,
Tsananin Son da Ameenatou kewa Haroon shine babbar matsalar Dake tayar da hankalinsa Dan kuwa Babu wani abu komai girmansa da zai ciresa daga zuciyarta…

Omar kuwa Jamaal Dayake cikin tsaka me wuyar gaske akan Dan uwansa ya kalla Yana Jin abubuwa da yawa a zuciyarsa gameda auren Wanda zaifi farin ciki da Jin dadin tareda samun cikakkiyar nutsuwa ko bayan mutuwa ace Jamaal ne igiyoyin auren ‘yarsa suke hannunsa,

Auren Ameenatou tamkar wani babban nauyin da mutum baisan dashine ba zai dauka Dan kuwa dukiyarta gaba Daya nauyinta akansa zasu sauka,
Haroon bazai taba iyawaba sedai Kuma so yayi gaggawan shiga lamarin nasa da Ameenatou Amma Kuma aurenta ba abune Mai saukin gaske ba garesa,

“Jamaal kayi mun alkawarin zaka tsaya ka tsayu ka zama kariya ga ‘yata?
Ka mun alkawarin zaka Hana duk wani cuta tarwatsa rayuwanta?
Kamun alkwarin ko Dan uwanka zaka tsayu gabansa ka zama katangar karfenta idan ya kasa Bata kariya da tsaron Daya kamata,
Idan na bawa Haroon auren ‘yata ka sani shi auren na basa Amma Kaine na bawa Amanarta ta har abada,
Ni amatsayin mahaifin Daya haifeta Kaine na bawa aurenta da kaina kaikuma ka karbanwa Dan uwanka Dan haka idan har ka Aminta shi ka bawa auren tabbas bazan Hanaka ba sedai Kasani har abada ni Amanar ‘yata na baka Kaine ka aura mata Dan uwan naka.

Jajayen idanuwan Jamaal ya dago Babbah ya fara kalla Wanda Shima shi yake kalla zuciyarsa na rawa hakama jikinsa amsarsa suke Jira Dan dai shi Kam Babbah bayajin zai aminta da auren sedai kafin yayi magana Jamaal ya fadawa Dad maganganun da suka hatta jikin Babbah yin sanyi baisan lokacinda Hawaye suka sake gangaro masa ba sbd yanajin tabbas Shima ya amince a aurawa Haroon din Ameenatou sbd Jamaal ya kashe musu jiki da alkawarin Daya dauka tareda Amanar Ameenatou Daya tabbatarwa dad din idan har su Dad dinsa sun samu damar taba ko suturar jikin Ameenatou da dukiyarta to bayan ransa ne Inshallah.

Ahmed Daya kasa riqe kansa akan tsananin kaunar dayakewa Jamaal rungumesa yayi sbd Daman yasan Jamaal namijin gaske ne ko Dad Omar baice komaiba jininsa yafi karfin ganin cutatarwa indai Jamaal Yana sane,
Kaunar datake tsakanin Jamaal da Omar kaunace irin ta asalin ‘da da uban da suka hada jini,
Yanda yake Jin Dad Omar ko mahaifinsa Baya jinsa a cikin ransa Hakan,
Shi kansa Omar yanda yakejin Jamaal ko ransa ko cewa Yayi yaje da kansa ya sanarwa su Mamman waye yarsa zaiyi sbd yasan bazasu iya komai Dan itaba.

Rungumesa Ahmed yayi Yana Jin nauyin dayake zuciya da kansa sun rage na alkwarin bawa Omar da ‘yarsa kariya Koda da rayuwarsa ne.

Har lokacin Jamaal zuciyarsa wani irin nauyi da daci ne danne da ita Dan haka Dad Omar ma dayake Jin nauyi da tsananin dacin zuciya rungumesa yayi sai alokacin hawayen Jamaal din suka gangaro daga idanuwansa Shima Dad Omar sai alokacin nasa suka gangaro Dan Bai taba zubda Hawaye ga rabuwarsa da Yan uwansa ba sai yau din Badan abin Baya cin zuciya da ruhinsa ba sai Dan baisamu Wanda daidai irin radadin ne aransaba sai yau din Dan yasan radadin dayake ransa shine yake ran Jamaal.

A cikin daren Omar ya sanar dashi komai daya Dade a rubuce na sunan AMEENATOU dayake kan komai na Abinda ya mallaka Dan haka Babbah yaji hankalinsa ya sake tashi Dan kaman sun sake nutso ne shida iyalansu da Ameenatou din cikin wutar qaddarar da zata kona kowa Dan haka take yaji zazzabi da ciwon kirji na rufesa,

Jamaal ma ciwon kan ne tareda zazzabin gaske ya rufesa sbd kirjinsa Daya toshe Dan haka cikin karfin hali ya fito kusan su babban da Dad Omar na bayansa suka fito gurin sedai babban tashin hankalin da suka tarar a wajen ne ya Saka jiri diban Dad Omar da Jamaal lokaci Daya sbd tabbatarda motar Haroon ce a gurin pake.

Ahmed ma dayake cikin shock saurin tare Omar yayi Yana kallan motar da tashin hankali yace

“Haroon Yana gurin Nan??

Babbah na Jin Hakan jiri ya zubar dashi jikin motar Omar Dake gurin Yana ambatar “Qalu innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Jamaal Daya ji kansa na sake daukan masifaffiyar zafi da sauri ya nufi motar yaganta a rufe

Ahmed da Shima cikin tashin hankalin ya zagaya Baya ya zagayo koina gidan baiga Haroon dinba ya dawo saiga key din motarsa a kasa gurin yashe.

Babbah na ganin Hakan yayi zaman Yan bori a gurin Yana cewa

“Shikenan haukarsa ta motsa zaije ya sanar WA mahaifinsa”

Zabura yayi da sauri ya nufi Omar Yana cewa

“Wallahi tinda baida cikakkiyar lafiya tsaf zai iya sanarwa ubansa,ku yi wani abu Akai ko wlh tallahi a cikin Daren Nan na tattara iyalina ku nememu ku rasa wlh ko zaka sake ganina sai qiyama idan mun hadu gaban Allah.”

Dad Omar da Baya ma gane me Babbahn ke fada motarsa ya nufa Dan sauri Shima Jamaal tasa ya nufa Ahmed ne yasamu karfin halin Jan Babbah ya jefa mota ya rufe suka tayarda motacinsu kaman masu wasan tsere cikin mugun gudun Daya Saka Babbah sake shiga tashin hankali suka hau titi su sukai kudi shi yayi arewa kowannensu Yana Saka Kiran wayar Haroon din ba kakkautawa.

Jamaal kaman zai tashi sama haka ya figi motar Yana Saka Kiran Haroon din idanuwansa na rikidewa gaba Daya Dan kuwa kowannensu tsoronsa kada Haroon din ya nufi su Dad Dan haka tabbas yaji wani abu shiyasa ya bar gurin a halinda basuda tabbacinsa tinda ga key din motarsa yashe a gurin.

MAMUH

JAMAAL JEEY SEELAH

AMEENATOU JDEN SEELAH

OMAR JDEN SEELAH

MAM SEEELAH

LAMS SEELAH

THE SEELAHS

WAR

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

AMEENATOU
Mamuhgee

54
BB kuwa Kai tsaye gidansa ya nufa Dan Haroon din Kuma harya Isa Bai Hadu da wata matsala ta jamian tsaro ba Dan haka Yana Isa yayi parking motarsa a harabar gidansa ya Bude ya fito ya zagayo ya Bude motar ya dauko Haroon din Wanda ciwonsa yakai kololuwan tashi sai fizga yakeyi Yana jijjiga kansa Yana buga kan a jikin hannuwansa idanuwansa a rintse.

Kai tsaye Dayan dakinsa yakaisa ya zubar a kasa tareda juyawa ya fice daga dakin Yana Ciro wayarsa ya Saka Kiran babban yaransa.

Yana daukan wayar Kai tsaye BB yace

“Killer ka kawomin Ps biyu yanzun Nan”

“Yes oga” killer ya fada daga bangarensa Yana kashe wayar tareda ture macen datake kansa tana lashesa kaman sweet har Saida kanta ya bugu da Bango ko a jikinsa ya miqe tsaye Yana kama dadar kansa datake a watse ya Saka Roba ya daureta tsakiyar Kai Yana nufar toilet ya wanko jikinsa ya fito,
Underwear yafara sakawa kafin ya Saka Jean Akai ya Saka shirt ya dauki wayarsa da key din motarsa yafice bayan ya shiga dayar dakinsa da mugayen kwayoyin rayuwa suke ciki ya dauko wadda ogan ya buqata.

Koda killer ya iso gidan BB ya tube yayo wanka dagashi sai underwear Wanda kusan Babu abinda na jikinsa da baka Gani.

Dakin suka nufa Yana miqawa killer hannu ya amsa fitinanniyar kwayar wadda take hade da ruwan alluran ta,

Tsananin karfi da balain dayake tattareda ita uku ake tanata asha Daya alluran Kuma tafi komai balai da masifa Dan hadda tsananin azabar gaske ne da ita Dan haka suna shiga dakin ya daga allurar Bai tsaya wata wata ba ya kama wuyan Haroon ya soka masa ita tareda dure masa ruwanta gabaki Daya Wanda yayi daidai da budewan idanuwansa cikin tsananin azabar da Bai taba samun kansa aciki ba take ya qame kaman Sanda kafin jikinsa ya saki gaba Daya Hawaye na gangaro gefen Idanuwansa da sukai duhu gaba Daya Baya ganin komai.

Sakin kansa BB yayi gaba Daya ya yanke jiki agurin ya zube kansa na bugawa da bakin table Dake gurin gashinsa na fashewa jini na fitowa ahankali ya lumshe idanuwansa Yana Jin jijiyan jikinsa kaman suna tsinkewan hakama jinin dayake jikinsa yana konewa cikin wata sanyayyar azaba Mai radadin gaske ga  ganinsa gaba Daya ya dauke Baya ganin komai Baya Jin komai.

Dad Lameenu ne da BB ya kira tin Yana hanya ya shigo dakin bayan BB ya Bude masa kofar Yana kallansa tareda basa tabbacin Haroon din bayaji Baya ganin Komai.

Tsayuwa Dad Lameenu din yayi akansa tareda kallan BB Wanda Shima killer ya kalla aka Ciro kwayar killer na kokarin rabawa uku BB yace ya basa a Hakan.

Cikin tsananin firgici da tashin hankali killer din duk rashin imaninsa ya Kalli BB din sbd ko ukun idan aka ranata akasha  ba qaramin Neman kashe mutum takeyiba bare duka Kuma har gida biyu.

Karban kwayoyin Yan kanana dasu BB yayi baiyi wata wata ba ya Bude bakin Haroon dayake kwance kaman gawan data rasa gatan suturtawa ya zuba masa su duka tareda karban ruwan da Alh Lameenu yake miqa masa ya zuba masa take suka wuce maqoshinsa.

Suna shiga kafin ma su fara aiki BB ya bari fuskansa da karfi tareda tayar dashi zaune duk da jikinsa asake yake Babu abinda yake Aiko a jikinsa.

Cikin tsananin mawuyacin halin da ko mara Imani Saiya zubar masa da Hawaye ya Bude bakinsa kansa na masa wani hayaqin masifa da balai yafara jijjiga Yana cewa

“Ameenatou itace ‘yarka Dad Omar, Dad Omar ka auramun Ameenatou sbd mutuwa zanyi idan na rasata, Ameenatou bazan taba barin kowa yasan itace ‘yar da ake nemaba ko da Hakan zaiyi sanadin Raina Dad Omar,
Babbah ku bani Ameenatou,
Jamaal ku bani Ameenatou,
Dad Omar ka taimakeni ka cika mun burin auren Ameenatou…….””

Sakinsa BB yayi tareda ja Baya da tsananin karfi jikinsa na daukan wani rawa da tashin hankalin da Bai taba tinanin shiga ba sbd Jin Abinda Haroon ke fada,

Shi kansa Lameenu Baya yayi da sauri Saida killer ya tarosa sbd firgici da shock din abinda yaji din.

Haroon kuwa sanqarewa yakeyi jini na fitowa bakinsa da hancinsa sosai sedai Bai Dena magana ba hakama jikinsa Bai Dena jijjiga ba.

Da sauri cikin masifaffen tashin hankali da tsoron abinda yake Gani da Wanda yaji Dad Lameenu ya Kalli BB Yana cewa suyi sauri su gogewa Haroon din jinin su mayar dashi inda zaa samesa kada ya mutu a hannunsu.

Suma Dake cikin tashin hankali sake shiga sabon tashin hankalin sukai sbd sanin waye Mam idan ‘dansa ya mutu a hannunsu Dan haka ba Bata lokaci suka daukesa suka Kai mota
Kusan motarsu data Lameenu a tare suka fice su sukabi wata hanyar Shima yabi wata.

Tafiya sukeyi suna gudu sosai suna kallan Haroon din Wanda yake zubarda jini sosai har lokacin cikin mafi tsananin azabar rayuwarsa da Bai taba jiba.

Tafiya me tsayi sukai kafin suka Isa inda BB din ya daukosa suka ajiyesa agurin suka gudu batareda kowa ya gansu ba.

Suna barin gurin motar siddeeq da shima ya shiga layin masu tsananin Neman Haroon din sbd zautuwan da Jamaal ke Neman yi gurin Nemansa Yana Sako Kai a layin Dan sake dubawa sai gashi kuwa yayi mummunan Gani Dan halinda ya samu Haroon din saura kadan ya buga zuciyarsa,

Bazai iya barin Jamaal ya gansa a wannan mummunan halinba Dan haka hankali tashe ya daukesa tsaban shiga rikici Kai tsaye Mansion din ya nufa dashi sedai Yan Isa ganin abin yayi muni Dad ya nema Kai tsaye sbd shi kansa jijjiga jikinsa yakeyi tsaban tashin hankali.

Mam na fitowa kallo Daya yayiwa Haroon ya Yanke jiki ya Fadi sbd zuciyarsa data buga irin bugun da zai iya kamuwa da shanyewan Rabin jiki mum Atee ce tayi saurin rikesa itama jikinta na daukan rawar tsoro da firgita sbd ganin abinda yafi karfin nata rashin Imanin.

Daukansa Akai aka nufi ciki dashi Kai tsaye bangarensa Akai dashi zuwa lokacin jikinsa sake sanqarewa yakeyi Dan haka suna Isa Kai tsaye toilet siddeeq ya wuce dashi ya Saka a bathtub din dayake cike da ruwan sanyi.

Dad kasa tsayuwa yayi ya qarasa gurin Haroon din dayake sanqare acikin ruwan jini har lokacin Yana fitowa ta hancinsa.

Wani irin kukan da baisan yanada shi bane ya fashewa Dad din Yana ihun ambatar Haroon din daidai Nan Lameenu yashigo Shima kafafunsa na rawar tashin hankali da tsoron abinda zai iya biyo Baya.

Kamo Haroon din yayi Shima Yana ambatar sunansa sedai Haroon Babu abinda yake ji a lokacin.

Sosai jinin yake sake gudu Wanda ya Saka siddeeq kasa riqe kansa ya kira Jamaal Wanda yaketa bulayi a titin Lagos Yana Neman Haroon din Yanajin abinda siddeeq ya fada Kai tsaye ya juyo motarsa kaman zai tashi sama yayo mansion din.

Isowansa yayi daidai da wani tarin jinin gaske da Haroon ya feso daga bakinsa Mai yawa jikinsa na qarasa sakewa gaba Daya a jikin Dad Wanda yake rungume da Haroon din qamqam Yana Jin Abinda Bai taba ji ba na ganin zaka rasa Wanda kake tsananin so da dukkanin rayuwarka.

Ganin Dan uwansa ya Saka Jamaal karasawa kafafunsa na Neman sarewa hakama zuciyarsa koina yankewa yaji tana yi.

Dad Lameenu da sauri ya janye daga Haroon din ya bawa Jamaal guri.

Hannuwansa duka biyu yakai cikin ruwan ya kamo Dan uwansa Yana fitowa dashi sbd gaba Daya jikinsa ya lalace da jini
Bai tsaya komaiba ficewa yayi dashi daga dakin ya fita dashi Dad Wanda ya kasa motsawa daga inda yake tsaban mutuwan dayakejin duka jikinsa yayi Babu inda ke motsuwa mum Atee ce ta kamasa suka fito suma suka marawa Jamaal din Baya.

Asibiti Jamaal ya nufa dashi cikin gaggawa aka karbesa sedai hadda Jamaal din aka shiga sbd samun damun tsayar da jininsa da ya zube sosai Dan take jininsa ya fara yin qasa.

Dayake da yawan manyan doctors din asibitin sunsan Dr Jamaal Seelah din baa hanasa shigaba Dan shine ya tsayar da jinin sedai ana buqatan jinin sakawa Jamaal din da gaggawa take ya kwanta aka fara diban nasa ana sakawa haroon din Wanda ya koma daidai sedai Babu inda yake motsi a jikinsa yayi fari fayau a cikin kankanin lokaci ya koma abin tausayin da zaka dauka shekarunsa ashirin a kwance.

A waje kuwa Dad da mum Atee da siddeeq ne sai Dad Lameenu da mummy Sarat duka tsit gurin ya dauka bayan Kaida kawo Babu abinda siddeeq keyi su kuwa Dad aketa Neman Kiran likita ya dubasa sbd jininsa yayi mummunan hawan dayake buqatan maganin gaggawa Shima.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

AMEENATOUH
Mamuhgee

ZafafaBoyar

55

Dad Omar ma tin kafin a ga Haroon din jininsa yahau Shima har yana Naman zubewa dole Ahmed ya dawo dashi gida Shima aka Nemo likita.

Babbah ma a gida likitan aka Nemo sbd take ya rafke zuciya na ciwo sosai hankalin nasa Iyalin yayi mummunan tashi.

A cikin Daren abubuwa da yawa sun faru marasa dadi da tashin hankali tareda Saka hawan jinin mutane da dama,

Sai guraren asuba Haroon ya farka sedai cikin yanayin Daya Sakasa tsiyayo da Hawaye masu zafin gaske Yana kallan Dan uwansa Dake gabansa zaune Yana kallansa idanuwansa jajir
Ko baa fada ba yasan irin radadin dayake zuciyar JAMAAL bamai faduwa ne ba,

Wani numfashi Mai dumi ya sauke ahankali hawayen cikin idonsa na gangarowa yanason magana Amma ya kasa sbd baisan me zai fada ba,

Abu uku zuciyarsa a yanzu kadai take so sbd samun sanyin da sassaucin azaban dayake ji na cin jininsa,

Ganin mahaifiyarsa,ganin Ameenatou da Kuma Jamaal din Wanda shi gashinan a gabansa.

Ahankali ya Bude bakinsa cikin sanyi da karfin hali yace

“Nagode”

Sukan Jamaal kalmar tayi Dan haka ya miqe tsaye Yana kokarin danne tausayi da tsinkewan da zuciyarsa keyi tareda nauyin dayake ji a kirjinsa yace

“Ka manta yau daurin aurenka???

Murmushi Haroon din yayi Mai sanyi kafin yace

“Ban manta ba shiyasa nayi Maka Godia.

Magana yakeson yi Amma bazai iya ba sbd hakanan zuciyarsa da bakinsa basa son furta komai bayan idanuwansa Daya zubawa Jamaal din Yana kallansa jikinsa na mutuwa hakama idanuwansa sunyi jajir.

Shima Jamaal Jin yayi bakinsa da zuciyarsa sunyi nauyi sosai bazai iya cewa komaiba bayan yin shiru suna sauraron numfashin junansu.

***Mam a cikin Daren Lameenu daya kasa zama ya kasa tsayi yasaka BB ya kawo musu rahoton abinda yake Neman zautashi tinda yaji a bakin Haroon.

BB a cikin asibitin ya sanar da Mam wacece ‘yar Omar Jaden da Kuma alaqarsa da Babbah akan cewa shine da kunnensa yaji lokacinda ya bisu.

BB na gama fada Lameenu ya sauke ajiyan zuciyarsa Dake cikin balai da masifa tinda yaji zancen shi kadai,

Maganar da farko kaman a mafarki Mam ya jita Saida ya dago idanuwansa da sukai jajir ya Kalli BB
BB din ya jinjin masa Kai alamar haka zancen yake.

Da hannu Mam yayi musu alama dasu kira masa likita numfashinsa tsayawa zaiyi.

Da sauri BB ya fice ya kirawo likita Wanda y dawo dakin tareda Mum Atee da itama tana asibitin Taki tafiya.

Tsaban tashin hankalin firgitan da Mam yayi Saida aka Saka masa oxygen na wucen gadi daqyar yakai asuba sbd tinane tinane da sakawa da warwarewa.

Asubar fari yaji dukkanin ciwonsa dayake ji a jikinsa ya warke,
Bai taba sanin Kowane ‘da da baiwar da Allah yayi masa ba da kalan arzikinsa sai yanzu,

Haroon ayau ya tabbatar masa da Hakan sbd zai basa abinda yayi shekaru Yana nema tin kafin ya Saka ran haihuwarsuba,
Bai taba Saka ran duk wannan tashin hankalin da sukaita fama dashina karshen dukiyar Omar a gidansa zata dawo,
Wannan auren shine babbar taskar arzikinsa Daya Dade Yana kashe kashe gurin mallaka,
Wannan auren da yace bazaiyiba ayau Yana tabbatarwa kansa idan baayi auren Nan ba to shine Baya raye Amma wallahi tallahi Babu Wanda zai Hana auren Nan dauruwa ayau kaman yanda ayau din Omar Zai bar duniyar dukiyar tashiga hannunsa da dalili….

Lameenu da Mam din ya Sakasa zuwa asibiti gurinsa tin asubar fari gama tattaunawa sukai inda kansa ya shiga wani zafi da duhu ya shiga lissafin abinda zai faru Idan auren ya tabbata.

Wannan auren idan anyi sa Ameenatou Jden ta zama matar Haroon sirikar Mam ayau Kuma idan Omar ya mutu gadonta na dukiyarsa gaba Daya zata zama a karkashin mijinta wanda dukiyar gaban dayanta zata koma ne akan yanzu gadon sirikar Mam ce ba tasu ba da zasu mallake su Raba tsakaninsu.

Jin yayi kansa na Neman kuncewa da lissafi Amma Kuma ko yayane su Raba Omar din da duniyar tukuna zasu fuskanci juna shida Mam din akan dukiyar sbd tabbas dole kasonsu me tsoka Yana cikinta.

Mam ne ya shiga dakin da Haroon yake kwance sedai idanuwansa biyu har lokacin shida Jamaal Babu me magana sai da Dad din ya shigo Jamaal ya fice ya basu guri dad din ya Kalli Haroon Wanda Shima Haroon din shi ya kalla Yana Jin tausayin mahaifin nasa akan rayuwar Daya samu kansa Dan haka yake Jin inama zai iya sauya Dad din dayayi Hakan.

Sunansa Dad ya ambata cikeda kulawa da farin ciki shimfide a fuskansa Yace

“Haroon Allah ya albarkaci rayuwar da zaka fara daga yau dinnan har ranar tashin qiyama,
Allah ya haskaka zuciyarka yanda ka haskaka tawa,
Allah yayi Maka kyakkyawar karshe ya albarkaci zuriar da zaka Haifa.”

Hawaye ne kawai suka silalo daga idanuwan Haroon sbd Bai taba samun wannan kyakkyawar adduar Mai dadin sauraro daga mahaifin nasa ba Dan haka ya rintse idanuwansa jikinsa gaba Daya na yin sanyi da mutuwa ahankali ya Bude bakinsa cikin kaunar Dad dinsa da har lokacin yakeji yace

“Amin Dad nagode Allah ya Saka da Khairan,
Allah ya tsarkake Maka zuciyarka ya wanketa Dad ya Kuma baka ikon gyarawa da tubar masa”

Shima Dad din cikin farin ciki da tsananin kaunar dansa yace “Ameen Haroon”

Jamaal ne ya dawo dakin daukeda takardun Haroon din Daya karbo dasu zai tafi akwai binciken da zaiyi akansu.

Duk da rashin karfi dayake jikin Haroon din hakanan Jamaal ya daukesa daga asibiti sbd bazai taba barin a daga daurin auren ba daga ranar sbd hakanan a yanzu zuciyarsa tafi ta Haroon cika da tsoron Da baisan na Menene ba Idan ba ganin yayi igiyan auren Haroon din sun rataya akan Ameenatou ba.

Dad ma bayajin akwai abinda zai Hana wannan auren ayanzu Dan haka gida suka dawo kowa na kokarin fara Shirin daurin auren Wanda zaayi da karfe goma Sha Daya na rana.

Dad Omar ma hankalinsa kwantawa yayi Daya samu tabbacin su Mam Basu ma samu damar magana da Haroon ba tin jiyan Dan haka yasan sirrinsu Bai fita ba Dan haka ya kira Babbah Wanda Shima yake a tsinke tini ya sake yafara Shirin daurin auren shi dasu Hafiz da zuciyoyinsu suke cikin farin ciki Mai tsananin gaske.

Amarya Ameenatou kuwa da batai waya da Haroon ba sai da safen Jin tayi kaman yayi mata caji Dan haka ta sake daga sanyin jikin datake fama dashi yin jiyan zuciyarta da kirjinta na nauyi.
Dan haka ta sake Wainda suka taho shirinta ta Basu Daman shigowa inda take Dan fara shiryata sbd daurin auren ma ya kusa ga gidan nasu a cike yake sosai da Yan bikin gashi Babbah yace bayan daurin auren zai sanar da ita abinda Bai taba sanar da ita ba Mai tsananin mahimmanci Dan haka duk ta sake zaquwa da ayi daurin auren ta zama ta Haroon ya zama nata.
Wannan tinanin kadai sake narkar da zuciyarta yakeji cikin farin ciki Mai sanyin gaske.

****A yanzu kusan dukkanin seelah Babu Wanda tin daga zuciyarsa yake cikin tsananin farin ciki da wannan auren ba Dan haka sosai ake cikin annuwan gaske Dan haka tini suka kammala nufinsu da komai akan Omar Wanda Shima yake cikin nutsuwa da farin ciki Dan ana daura auren zasu tafiyarsu hadda Haroon din da Ameenatou da Jamaal shiyasa ma suka dakatar da Dr Aleena daga zuwan tinda Nan zasu taho.

Ahmed ma Yana cikin farin cikin gaske Jamaal ne kadai yake Jin kirjinsa da zuciyarsa cikin nauyin Daya hanasa ko numfashin daidai.

Karfe goma saura kusan kowa ya gama Shirin daurin auren,

Haroon Wanda Jamaal ne ya tayasa shiryawa cikin kyakkyawar farar shaddar datai masa wani irin kyau haskensa da Bai taba sanin yana dashiba bayyana sosai.

Ayau hatta turare iri Daya sukai amfani dashi sbd komai dayake jikinsu iri dayane babu banbanci abinda Basu taba yiba kenan tin suna kanana har girmansu sai yau din.

Time Haroon ya kalla yaji jikinsa ya mutu da farin cikin wannan ranar Dan haka ya Ciro wayarsa ya Saka Kiran Ameenatou wadda itama kusan ankusa gama shirinta tana dauka ajiyar zuciya kawai ya fara saukewa kafin ya ambaci sunanta Yana ce mata Yana Sonta kawai ya kashe.

Murmushi kawai tayi tana damqe wayar a hannunta tareda cigaba da shiryawa.

Jamaal tsayuwa yayi bakin window ranar aurensa na dawowa sabuwa acikin zuciyarsa Dan haka nauyin kirjinsa yake sake karuwa Yana sakashi shiga yanayin tashin tsikar jikinsa idanuwansa na Neman sauya Amma ya kasa Hana zuciyarsa shiga wani irin tsoro duk jarumtarsa.

Matsowa Haroon yayi Yana kallan time da yayi yace

“Muje ko time yayi”

Juyowa Jamaal yayi ahankali ya zuba masa idanuwansa da suka sauya sedai Bai iya cewa komaiba.

Tsoro yakeji sosai Dan haka ya Dan dauke idanuwansa daga Haroon yanayin gaba Haroon din ya biyosa yana gyara zaman babbar rigar jikinsa.

Motar Mam da securities dinsa ce ta fara barin gidan ya wuce daurin auren zuciyarsa fes,

Fitowan su Jamaal yayi daidai da fitowan Dad Omar tareda Ahmed zasu shiga mota Dan haka Kai tsaye ya kofar harabar Daya hada gidajen suna nufa suka Isa gurinsa idanuwansa na kansu Yana kallansu a tare zuciyarsa na cika da farin ganin auren yarsa Dan haka Kai tsaye rungume Jamaal yayi kafin ya rungume Haroon da yau Shima yake cikawa kowa idanuwa da kwarjini Mai sanyi.

Cikin kulawa da kauna Dad Omar ya kallo Haroon yace su shiga motarsa suje daurin auren tare.

Cikin farin cikin Hakan Haroon ya juyo ya kallo Jamaal zaice da Dan uwansa yake son zuwa daurin aurensa sai Jamaal din Wanda ya kasa samun nutsuwa ya girgiza masa Kai Yana kallan fuskansa Yace yabi Dad din kawai.

Murmushi me sanyi Haroon yayi tareda gyada Kai kaman qaramin yaro yabi dad da Ahmed dukkaninsu suna murmushi suka shige mota.

Jamaal na kallo suka tada motar suka bar harabar gidan Shima ya juya yabar harabar gidan.

Dayake sun Dade da fita kafin ya fita Kai tsaye biyawa sukai suka dauki Babbah sbd Shi Daman da Omar zasu tafi daurin auren sai gashi Kuma sunzo da Haroon sai Hakan yayiwa Babbah dadi sbd zaiso ya sake bawa Haroon amanar Ameenatou
Babbah na shiga suka tada motar suka bar gurin.

Jamaal na kama hanyar zuwa gurin daurin auren siddeeq ya kirasa kaman bazai daukaba Saiya Isa sai kuma ya dauka
Abinda siddeeq din ke sanar masa yaji Yanzu daga bakin Lameenu da BB a Mansion shine ya sakashi juya kan motarsa ya kama hanyar gidansu Ameenatou sbd bazai taba barin wani abu ya samu matar Haroon ba aranar aurensu kaman yanda Shima ranar auren ya rasa tasa matar.

Wayar Dad Omar yake kira cikin gaggawa Amma Sam Bata shiga,
Ta Ahmed ya koma kira kwata kwata Bata shiga itama,
Ta Haroon ya kira ita Kuma Saiya jita a cikin motar dayake din Dan haka yayi wurgi da wayar seat din gefensa tareda qarawa motar tsananin gudu yana nufar gidan.

Yana Isa kofar gidan Hafiz da Abdul sun fito kenan cikin Shirin wucewa ko kashe motar baiyiba ya fito da sauri Yana kallan Abdul yace

“Yi sauri karbi bayansu Dad da Babbah ka sanar musu kada su bi ta Aneyam nzki road,
Ka tabbatarda Basu bi hanyar ba yi sauri, yi sauri…

Abdul na Jin Hakan da Kuma ganin yanda Jamaal din yake a zafafe ya sakashi fadawa motar Hafiz ma ya fada suka bi bayan su Haroon din da mugun gudun gaske.

Shikuwa Kai tsaye harabar gidan ya shiga daidai fitowan Ameenatou din zata bawa Hafiz agogonsa Daya manta gurin sauri cikin mahaukacin navy blue tsadaddiyar lace din Daya fidda kayanta da kuruciyarta akansa idanuwanta akansa suka sauka ta tsaya cak daga inda take tana masa kallan Daya Sakasa qin kallan fuskanta bare gane kamanninta.

Takowa tafara yi ahankali tana nufosa cikin sanyin da duka jikinta kawai taji yayi hakama kirjinta nauyi yayi mata take me tsananin.

Gap take da isowa gurinsa wayar hannunta tayi ringing daidai Nan tasa wayar Shima tayi ringing itace ta fara daukan tata tareda kaiwa kunnenta tareda tsayawa cak daga inda take.

Daga nasa Kiran yayi da siddeeq yayi masa sedai baima gama Jin Abinda yafara fada masa ba Ameenatou ta Yanke jiki ta zube a jikinsa kaman matacciya Shima Neman zubewan yakeyi siddeeq daya iso bakin gate din gidan a haukace sbd mummunan tashin hankalin da baa Saka masa Rana ba ya shigo da mugun gudu.ya taresu gaba dayansu.

MAMUH

AMEENATOUH
Mamuhgee

ZafadaBiyar

56
A jikin Jamaal gaba Dayanta Ameenatou din ta zube Dan haka baida zabin Daya wuce riqeta da hannuwansa Shima nasa kafafun na gagararsa daukansa.

Siddeeq da idanuwansa ke rikice da wani mugun ja riqesa Shima yayi Yana Kasa kallan fuskarsa data fara gaba Daya.

Umman fadila ce tareda anti zulaihat cikin mutanen dadah da suka taho daga Nasarawa biki ne suka fito daukan kaya a harabar gidan suka tarar da wanna tashin hankalin da sauri siddeeq yace umman tazo ta dauke Ameenatou daga jikin Jamaal din.

Da sauri suka qaraso tare umman ta tattaro Ameenatou din daga jikinsa tana tambayar lafiya a rude Tana raba idanuwa a tsakanin Ameenatou din da Jamaal da Kuma siddeeq din.

Siddeeq Bai iya cewa komai bayan cewan suyi ciki da Ameenatou din shikuma ya kama Jamaal Wanda har lokacin kaman jiri yake Gani suka fito daga harabar gidan Kai tsaye motar da Jamaal din yazo da ita suka nufa shi siddeeq din yabar wadda yazo da ita a gurin.

Saida ya zaunar da Jamaal din a mota kafin ya zagaya da sauri ya shiga motar zai tayar Jamaal ya dago jajayen idanuwansa ya kallesa daqyar ya iya Bude Baki yace

“Bani key ni zanje na dubo Kai ka Jira anan din Sbd A,dole Ina buqatan barin wani anan din incase.

Siddeeq kallansa yayi da nasa jajayen idanuwan Shima Yana girgiza Kai sbd bazai iya barinsa yayi tuqi ba a lokacin da kansa.

Bude motar Jamaal yayi tareda fitowa ya zagayo ko gabansa Baya Gani dakyau wani irin wuta da radadin azabar nauyi yake ji a kirjinsa Babu abinda yakeso kaman ganinsa gurin da ake maganar.

Karban key din yayi Bai tsaya komaiba ya fada motar Yana rufewa ya tayar Kai tsaye yayi mata wani irin mugun ja yabar gurin siddeeq na bin bayan motar da kallo hankalinsa na mummunan sake tashi sbd kaman zata tashi sama tsaban mugun gudun da Jamaal din keyi.

Jamaal na barin gurin yayi cikin harabar gidan Yana fiddo wayarsa aljihu Yana rasa a cikin wainda suka tafin waye zai kira tinda Babu me lafiyan dauka Kila.

Jamaal kuwa tuqin yakeyi idanuwansa na Neman rufewa Amma karfin hali Dana zuciyarsa Basu bar hakanba Saida ya hau titin da zai Kaisa Aneyam nzki road Wanda yake kaman bypass Babu mutune sosai.

Yana Jin Nisa sosai a kan titin
Tin daga nesa yafara hango mutane da Jamaan tsaro sun rufe titin hakama hadda masu daukan hotuna da wata katuwar mota a gurin datake kokarin kamawa da wuta anata ihu da hayaniya.

Tin anan Kunnuwansa sukai masa wani irin dim suna kokarin dauke jinsu,
Idanuwansa kuwa wani dishi dishi suke son fara masa Amma ya rintse su da karfi tareda budewa Yana budewa motarsa da sauri ya fito batareda ya kasheta ba hakama wani parking din tsakiyar Titi yayi Yana qarasowa gurin da gudun gaske ganin motar Dad Omar data Abdul sun hade guri Daya kaman kayan wankin da aka hada aka matse cikin mafi muni da tashin hankalin kallo a kusan karkashin babbar motar wadda da alama itace tayi musu hawan tela.

Daukewa ganinsa yafara yi da gaske hakama kunnuwansa Dan haka take yafara Neman kasa karasawa sbd jiri da rashin Gani,
Daidai lokacin Mam ya iso gurin da drivernsa tareda Lameenu cikin matsanancin tashin hankalin da Bai taba Shiga ba Shima nasa ganin da Jin kusan daukewa yayi can sama sama yakejin maganganun mutane da iska suna kadawa hakama gabansa Baya Gani sosai Yana Sako Kai inda police din gurin janye masa shida Jamaal daidai lokacinda aka shimfide gawar Haroon da aka samu cirowa a gabansu cikin fararen kayansa da suka sauya take Babu ko dogon haskensu koina jininsa ne ya sauya kalar kayan gabaki dayanta.

Daga Jamaal har Dad lokaci Daya kafafuwansu suka sare a gaban gaban gawar suna zubewa Jamaal take ya qarasa zubewa qasa Yana rarrafowa gaban Haroon din Dan cetan ransa sbd Bai yadda da wani abin ya Riga ya faru ba da Haroon dinsa, Dad kuwa zubawa gawar idanuwansa yayi hannuwansa na wata irin rawar tashin hankali bakinsa na rawa yace

“Kuyi sauri ku kawo mota muje asibiti Dan uwansa likita ne kwararre gashinan zai taimaka masa kuyi sauri,
A kawo mota,
Me kuke Jira?
A kawo mota da sauri ‘dana Yana buqatan taimakon gaggawa,
Yaro na Yana buqatan Isa asibiti,
Lameenuuuu a yi gaggawan kawo mota Dan Allah karku bari yarona ya mutu a Haka yanada raunin zuciyaa, HAROON,HAROON,
HAROON my boy,
Yarona ‘dan Albarka Karka tafi ka barni Kai kadai nake dashi a cikin abinda nake tsananin so a duniyar Nan,
Haroon,Haroon…… innalillahi wainna ilaihirrajiun….

Dukkanin maganganun da Dad din keyi Baya hayyacinsa sbd Bai yadda da Babu Rai a jikin Haroon ba sbd jamaal ma kwata kwata ya kasa yadda da Babu Rai a jikin Dan uwansa Dan haka yaketa kokarin dawo da numfashi a jikinsa ya hanyar dubarunsu na likitoci hannuwansa na wani irin tsananin rawa hakama nasa fararen kayan tini sukai kaca kaca da jinin Yana rungumo Haroon din idanuwansa na qanqancewa Yana ihun su kawo ambulance Shima.

Lameenu rudewa yayi Shima yafara cewa a kawo ambulance Maza Maza daga SEELAHs hospital Yana Jin tsananin tashin hankali da tausayin halin da yaga Mam a ciki yau harma da tsoro da fargaba duk ya shiga sbd dukkaninsu Basu taba kawo tinanin Haroon zai shiga motar Omar ba,to mema ya shigar dashi,

Babban tsoro da tashin hankali da mugun firgicin dayake ciki shine bayan wucewansu Omar din tareda Haroon Saida ya Jira Jamaal ya gama wayoyinsa tukuna ya fice kafin ya fidda wayarsa ya kira Lameenu din Kuma daidai wannan lokacin ne siddeeq ya shigo mansion din Bai dauka su Jamaal din sun wuce ba sbd yanata Kiran wayarsa busy yake.

BB ya sanar da Lameenu cewan Haroon fa yabi motar Sir Omar a dakatar da aikin kokuwa a qaddamar dashi yanda aka tsara sbd Haroon na ciki,

Kai tsaye Lameenu Bada umarnin yayi ayi aikin kaman yanda aka tsara sbd Ameenatou bazata taba zama sirikar Mam ba ta yanda zai fisa Iko ko mallakar dukiyar gaba dayanta bayan wuyar da suka shawo akanta Dan haka gwara Bata zama sirikar tasaba tin farko suna gamawa da Omar itama su gama da ita shikenan sune magada tinda sune ake kallan uwa Daya Uba Daya dashi Kuma kada a kuskura duk tsanani bayan aiki a cewa Mam an sani su tsaya akan Basu San Haroon yabi motar ba.

Hakan da siddeeq yaji ne ya sakashi Kiran Jamaal Wanda ya gama wayarsa harya fara Nisa a hanya ya fada masa take shikuma ya sauya hanya yabi zuwa gidansu Ameenatou Dan cimma su Dad din da bawa Ameenatou kariya kafin ya samu a dauro auren a dawo yasan Dan uwansa ya samu mallakar macen zuciyarsa.

Wuto babbar motar ta fara ci dashi Dan haka Akai saurin Bude ambulance din data iso aka fara dauke gawar Haroon aka Saka kafin ta Abdul wadda itama kallo Daya zakai masa ka fashewa gawar da kuka sbd daidai lokacinda su Abdul din suka iso gap da motar su Dad sun musu magana kenan babbar motar data taho da mugun gudun ta haye kansu gaba Daya cikin rashin tausayi kuma Yana hayewa kansu da motar sedai kafin ayi wata wata drivern ya Bude motarsa yana kokarin guduwa a raunane Dan Shima ya raunana sosai

Sedai Yana fitowa motan zai gudu yaran BB Dake gurin a rarrabe suka taso suna rufesa da dukan mutuwa suna cewa ya kashe mutane zai gudu
Take mutane da Jamaar gurin suka tayasu aka rufesa da dukan da take aka kashesa a gurin Shima duk yanda Yan Sanda suka so samunsa da Rai tini Rai yayi halinsa cikeda baqin ciki suka dauki gawarsa Shima aka jefa wata motar daban.

Dad Omar da Babbah sune Basu rasu ba Amma sunfi wainda suka rasu kakkaryewa sosai tareda wahalalliyar azaba hakama gabaki Daya sun sauya daga mutanen da aka Sansu Dan Babu Wanda ake gane ko fuskansa sunyi mummunan raunana Tako ina Dan haka a cikinsu Babu ma Wanda alamun sauran Rai yake a jikinsa amma dai an duba suna raye din Dan haka Akai gaggawan daukansu zuwa asibiti,
Sai Ahmed da Hafiz da Suma sukai Mummunan kariya ta hannuwa da kafa hakama sun raunana sosai sedai su suna hayyacinsu sedai rikitacciyar azaba Da jininsu Dake zuba kaman ba daga jikinsu yake fitowa ba.

Suma kwasansu Akai zuwa asibiti gaba Daya,

Jamaal har acikin ambulance din rungume yake da gawar Dan uwansa ya kasa sakonsa duka jikinsa rawa yakeyi sosai kaman zai jijjige Haroon din Dan haka koda aka Isa asibitinma da qyar aka bambare gawar daga jikinsa Akai ciki da ita.

Dad Koda ya iso Lameenu na biye dashi sbd kada ya Fadi hakama su Mum Atee tini suka qaraso asibitin
Hakama su Aunt Didi matar Ahmed da Fatmah duk sun iso
Mum Nur kuwa Kuka kawai takeyi sbd tsoron dataji duk ya dabaibaiyeta.

Siddeeq Daya kasa hakuri wayoyin kowa kira yakeyi gashi itama Ameenatou din taqi farfadowan sai ruwa ake zuba mata Dan haka ya daukosu tareda dadah cikin sabon tashin hankali sukayo asibitin da ita.

Suna isowa itama aka karbeta sedai samun ahalin seelahs kaf a asibitin ya Saka su dadah cikin masifaffen tashin hankali kafin dukkaninsu su motsa daga inda dukansu suke tsaye Dr zayyan ya fito daga dakin emergency din da suke ciki da duka su Omar da Haroon din bayan fama da taqaddamar da sukasha da Jamaal kafin ya yadda Allah ya karbi ran ‘dan uwansa ya koma garesa Dan haka kallansu Dr zayyan din yayi idanuwansa jajir hakama Shima hannuwansa yar rawa sukeyi idanuwansa na cikowa da kwallan Daya kasa riqewa ya kasa kallan Dad dake tsaye shi yake jiran abinda zai fada,mum Atee da Dad Lameenu na gefensa kowa Dr zayyan din yake kalla,
Su mum Sarat da Dadah ma duk a tsinke suke,
Sai su mum Nur da kukanta ya tsaya cak suna kallo bakin Dr zayyan din ya Bude cikin sauti me tsananin sanyin gaske yace

“Sai hakuri,sai hakuri, Haroon seelah da AbdulRasheed Allah ya Riga ya dauki ransu lokaci yariga yayi Babu abinda zamu iya sai hakuri da rungumar hukuncin ubangiji”

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

AMEENATOUH
Mamuhgee

ZafafaBiyar

57
Ahankali Dad ya daga hannunsa da yayi masa wani irin mugun nauyi ya Dora a kirjinsa inda yaji wani abu ya tsaya masa Yana hanasa Jan numfashi kwata kwata kafin ma ya sake kokarin Jan numfashin ya yanke jiki a gurin Yana kokawa da numfashin Daya Yanke daga kirjinsa gabaki Daya idanuwansa na tsiyayo wasu zafafan hawayen masu radadi ahankali.

Mum Atee da Dad Lameenu ne suka durkushe gabansa suna ambatar sunansa cikin tsananin tashin hankali da rikicewa.

Dr zayyan ma cikin tashin hankalin me tsanani ya kira nurses da masu daukansa tini aka daukesa Akai ciki dashi Dr zayyan na cewa cikin sauri a kawo oxygen da gaggawa kafin numfashin nasa ya yanke.

Dadah kuwa da Karan farko Bata gane Abdul dinta ake nufi ba saida umman fadila ta rungumeta tana fashewa da kuka sbd dawo mata sabuwa da ranar rasuwar Taya ‘yar tayi a wannan asibitin itama ranar aurenta.

Dadah sai alokacin ta fahimci me ake nufi Dan haka ta silale qasa tana Neman numfashin itama sbd kukan ma mantawa tayi da ana yinsa a duniya iskan numfashi kawai take nema a kirjinta kafin ayi yunqurin Kiran likita ya some a gurin gaba Daya jikin umma.

Mum Nur dasu Aunt Didi kukan baqin cikin rasuwar Haroon din dana farin cikin mazajensu dake raye suka sake lokaci Daya tareda tausayinsu.
Fatmah ma kukan takeyi sbd ta dauka zaace Dad dinta da Dad Omar sun rasu suma sun barsu.

Mummy Sarat ma dasu Aliyah kuka sukeyi sosai musamman Ayeesha datafi kowa shakuwa dashi Kuma ita kadaice yakeda kauna mara sirki daga zuciya a tsakaninsa da ita duk cikin family Dan haka ta zube a gurin kasa tana fasa kukan Daya Saka gaba Daya gurin daukan shiru tana Kiran sunan Haroon din.

Emergency Akai gaggawan shigewa da Dad sbd oxygen din Neman gagararsa ja ma yakeyi Dan haka hankalin likitocin ya fara tashi Dan hak suka Taru akansa ana yaqin cetan numfashin nasa hankali tashe.

Su Lameenu Dake waje ma hankalinsu tashi yayi Dan haka kusan asibitin tayi tsit ba dogon motsi bare hayaniya sbd masu asibitin ne da kansu cikinta a mafi wahalan yanayi da tashin hankalin dasuke ganin Basu taba shigarsaba.

JAMAAL Babu Wanda yagansa har lokacin sbd Yana ciki inda gawar Haroon din take tareda ta Abdul a gefensa,
Gawar Haroon itace gawar datafi masa rayuwar duka Wanda yake duniyarma yake Gani,
Gawar Haroon itace abinda ya kasa dauke idanuwansa daka kansa,
Rabin jikinsa ya tafi yabarsa,
Haroon yasha wahala da baqin cikin rayuwa fiyeda komai,
Bai samu farin ciki ba tinda ya taso harya komawa ubangijinsa,
Yaso samun sauyin rayuwa a tareda Dan uwansa da mahaifiyarsa Dan matarsa bayan auren sedai Allah baiyi zaiga hakanba,

Meyasa suka kasance acikin zuria da jinin marasa imanin duk duniya da rashin tausayi?

Kasa riqe kansa yayi daidai lokacinda ya Tina maganar Dan uwan nasa ta karshe akan farin cikin dayake ciki a yau din sbd zai auri farin cikin rayuwarsa…..

Wani irin kuka Mai tsananin radadin zuciya ne ya fashe dashi Yana Dora goshinsa gefen kan gawar Haroon din duka jikinsa na rawa da jijjigan kukan da yakeyi Mai ciwo da baqin cikin ya rabu kenan da Dan uwansa shikenan.

“Innalillahi wainna ilaihirrajiun”

Kukansa ne sosai ya Saka siddeeq kasa riqe nasa kukan tausayin Haroon da irin rayuwar rashin kaunar da ake nuna masa Daya gudanar tareda wahalan ciwo Daya ringa fama dashi batareda kowa ya sani ba daga karshe ya tafiyarsa yabar duniyar da Babu komai a cikinta sai son zuciya da azaba a gurinsa.

Dadah da Akai gaggawan taimakawa tana farfadowa wani kuka Mai ratsa zuciyan duk uwar Datake da ‘yaya ne da uban dayake da yayane ta fasa tana Jin kirjinta Yana kasa daukan radadin Datake Jin kanta acikinsa,

Rashin ‘dan ta Babba tareda mummunan halinda mijinta yake ciki na tsakanin Rai ko mutuwa baa San wanne zai faru ba da Kuma Hafiz da Shima aketa kokarin ganin an ceta rayuwarsa sbd jininsa da kusan ya tsiyaye da kariyar datafi nawa a jikinsa.

Mum Nur ma da Aunt Didi lokacinda suka samu bayanin halinda su Dad Omar suke ciki mum Nur kasa dauka tayi dole Akai gaggawan mayar da ita gida tinda itama lafiyar tata sai ahankali,

Dadah tin tana iya kuka Dan idanuwanta har lamarin yaci karfina ta sake rikicewa jikinta ya rikice gaba Daya dole dai itama akai gaggawan Bata kulawa aka mayar da ita baccin dole da wahala sbd zuciyarta Dake Neman samun matsala sbd BP dinta yayi mummunan hawan daya fara Sakata kaman zatai jijjiga.

Daidai wannan lokacin ne Ameenatou ta farfado sedai umma kasa barinta tayi tasan meyake faruwa ta dawo gida da ita a taxi sedai Koda suka Isa gida gaba Daya gidan anyi cirko cirko kowa idanuwansa jajir masu kuka sunyi masu shiga tsananin damuwa da tashin hankali duk suna ciki Dan kuwa labarin wannan mummunan ranar ta ahalin SEELAHs ya isarwa kowa.

Duk yanda akaso taimakon Dad abin yaci tura sai da kyar suka samu damar daidaita numfashinsa sedai Kuma Bai San inda kansa yake ba Dan a cikin qanqanin lokaci Allah ya mayar dashi abin tausayi kaman Wanda yayi watanni a kwance take ya jeme.

Lameenu ma cikin tashin hankalin da jemewan yake sbd bazai taba son ya rasa Mam ba tinda a yanzu shi kadai ne yake dashi a rayuwarsa,
Idan ya rasa Mam bazai taba iya komai na rayuwarsa shi Daya ba Babu Dan uwan nasa,

Sun rasa sauran Yan uwansu Badan basa sonsu ba sai Dan son zuciya da shedan tareda muguwar zuciya datake rinjayarsu,
A yanzu tashin Mam da ganin lafiyansa shine abinda yake cikeda zuciyarsa ya Sanyaya jikinsa Dan haka gaba Daya ya koma Kalan jemewan Shima yana cikin tsaka me wuya.

***Hudu bayan la’asar aka iso da gawar Haroon da Abdul mansion din Dad Omar sbd jamaal Daya Bada umarnin anan zaayi janazah dinsu wadda tini mutane masu yawan gaske suka fara halarta sbd daurin auren da sukai Niya tafiya shine ya koma janazah din Dan haka manyan mutane da Jamaa Tako ina.

Saida aka gama suturtasu siddeeq yaje gida ya dauko Ameenatou wadda take gida ta rikice musu gaba Daya Babbah da Yaya Abdul da Yaya Hafiz kawai take ambata sbd wayarta ce numbern da aka fara kira a wayar Babbah cewan sun samu mummunan accident wanda Dayan police din Kuma numbern Jamaal ya kira da wayar Dad Omar.

Zuwan siddeeq gidan ya tararda sauyawan lokaci Daya da Ameenatou din tayi sbd duk abinda yake jikinta na adon auren da Akai mata ta ciresa ko Dan kunne Bata bari ba daga ita sai doguwar Riga mara nauyi da mayafi ya fito ko gabanta Bata Gani Saida umma ta riqeta suka shiga motar datake jin kirjinta na sake toshewa tana Jan numfashi kaman me asthma.

Suna isowa har cikin harabar Mansion din gidan tana fitowa mota kafafunsa suka sare ta kasa daukan kanta sbd ganin tarin mutane Tako ina.

Umma da Aliyah data fito ne suka kamata har cikin palon farko na mansion din Wanda gawar biyu suke a shimfide fuskan Abdul an Riga anrufe ta Haroon ce ake kokarin rufewa ta iso gurin idanuwanta akan fuskan ta fara sauka kafin ta kyafta idanuwata suka sauka akan dadah Dake gaban dayar gawar zaune kaman mutum mutumi take numfashinta yayi sama Yana Neman fita daga kirjinta jikin tsananin tashin hankalin da Bata taba shiga ba da mummunan shock kafin suyi yunqurin tarota tafara kokawa da numfashinta Wanda yake kokarin ficewa…..

Umma datai saurin Kiran sunanta Bata ma gama rufe Baki ba kwakwalwan Ameenatou din ta juye gaba Daya sbd rashin Babbah da Haroon shine abu na karshe da kanta zai iya dauka Yanke jiki tayi a jikin umma ta zube qasa umma na binta kasan tana Kiran sunanta da tsananin tsoro da tashin hankali sbd wannan yanayin nata ya banbanta matiqar gaske Dana farko data Suma.

Daukanta Akai akayi ciki da ita sedai ko qarasa shigewa da ita baayi ba aka dauke gawar Dan yi musu sallah aka fice dasu.

Ficewan da Akai dasu yayi daidai da sake Saka dadah mummunan halin Daya Saka ita Kam dole asibiti Akai da ita.

Daga gurin janazah din suna dawowa wayar Jamaal ta samu mummunan sakon Daya Saka kansa sake ciki fitinanniyar tashin hankali sbd mum dinsu data yanke jiki kasamakon Jin rasuwar ‘danta Kuma likitan ya tabbatar masa data samu paralyze suke tinanin Amma dai Bata farfadoba Dan haka suna tsananin buqatansa da gaggawa kafin ta farfado din.

Wannan mummunan labarin sabon tashin hankalin ya kusan Saka zuciyar JAMAAL bugawa take yafara kokarin tafiya sedai Kuma hankalinsa na rabuwa biyu da barin Ameenatou baa hannun kowaba,.

Babu Haroon,Babu Babbah,Babu Dad Omar,Babu Abdul Babu Hafiz bare Ahmed Dan haka barinta a daidai wannan lokacin kaman barin nama ne a tsakiyar damisoshi.

Babbar tashin hankalin sabo shine Ameenatou din gaba Daya anyi anyi taqi farfadowa dole Akai asibiti da ita itama aka jere su kowa da dakinsa Babu Wanda yasan inda kansa yake tsakanin ita da Dad da Dadah ga su Babbah da sai yanda hali yayi Suma.

Ahmed Daya Dan samu kansa cikin karfin hali ya sanar da Aunt Didi ayi gaggawan shirin fitar da Omar zuwa gurin dangin Didi din Dake Angola sbd jinyarsu acan tinda shi baida lafiyan basa kariya ko jinyarsa Dan haka su tattara su tafi can hankalinsa zaifi Kwanciya sbd zaa iya tinanin qarasa Omar din daga Nan tinda Yariga ya shige coma shi da Babbah sai yanda Allah yayi dasu.

Mum Nur Daman Batada niyar barin mijinta a Nigeria din ayi jinyarsa sbd ko zai tashi dukkaninsu sunsan ba yanzu ba ko duba da yanayin niqan da mota tai masa Dan haka a take washe garin ranar suka hada komai suka bar Lagos zuwa Abuja sbd acan zaa tashi.

Kaman abin da ake Jira qanqanin lokaci aka rufe mansion din suka tafiyarsu batareda sun tafi da Babbah ba kaman yanda Ahmed yaso sedai Shima ba qaramin Jin jiki yakeyiba tinda ya Bada umarnin tafiyar Bai sake sanin inda kansa yake ba shima har suka bar qasar.

Jamaal Neman haukacewa yakeyi a Nigeria din sbd duk yanda yaso wucewa yabar qasar da Ameenatou lamarin ya gagara sbd Babu abinda take dashi na barin qasar hakama acan kiransa akeyi mahaifiyarsa na tsananin buqatansa da gaggawa sbd tsoron sukeyi wani abu ya faru Jamaal din Baya kusa sunsan bazai taba yafewa kowa ba..Dan haka Jamaal din yake cikin tsananin mawuyacin hali da Neman mafitan yanda zai Hana su Dad taba ko farcen Ameenatou din Tako ina.

Washe gari da wucewansu JDENS Dad dinsa ya farfado Dan haka ya sake Jin kansa ya dauki zafin da Bai taba dauka ba Dan haka Kai tsaye karfe biyun Rana ana fitowa sallahn azahar aka daura Aurensa da Ameenatou wadda ita Kuma karfe biyu da rabi ta farka sedai abinda bai taba tinanin zaiwa wani ba a rayuwarsa shine juyar Maka da hankali shine abinda yasan kadai mafita a garesa kafin yaje ya dawo ya tafi din sbd matiqar tana cikin cikakkiyar hankalinta Koda igiyoyin aurensa Dake kanta bazasu Bata cikakkiyar tsira daga su Dad da Lameenu ba sai Hakan,

Kasancewanta mara cikakkiyar hankali a yanzu shine kadai zai Hanasu mallakar ko tsintsiya daga dukiyar Omar kaf datake kasar duka sun bari daga gareta,

Babu maganar kudi ko wani gado tinda Omar yana raye ayanzu Amma sbd tsoron Omar din zai iya rasa rayuwarsa daga can ya sakashi yin Hakan sbd alluran duka duka wata Daya zatayi tana mata aiki zata dawo daidai Wanda yake Saka ran kafin can ya dawo gareta.

Siddeeq kuka yakeyi sosai jikinsa na cira sbd tausayin kansa,Dana Ameenatou din Dana Jamaal din Wanda ya kasance a tsaka me wuyar gaske gashi ya kasa yadda da kowa akan Ameenatou tinda wainda ya yadda dasu gasucan a kwance asibiti Babu Wanda yasan ranar tashinsu.

Hankalin lameenu tashi yayi mummunan yi da samun labarin juyewan kan Ameenatoun Daya fara Jin farin ciki da tsananin Jin dadin an tafi anbarta a hannunsu sune iyayenta sune sukeda cikakkiyar ikonta da dukiyarta.

Bai shiga Mummunan tashin hankalin Daya Sakasa faduwa ba Saida akayo asibitin dashi Shima Saida yaji AN DAURA AUREN JAMAAL DIN DA ITA,
AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH DIN A YANZU CIKAKKIYAR MATAR JAMAAL SEELAH DINCE HALAK MALAK…… Innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Dad ma da farfafowansa kenan zancen girgiza yayi har Saida Shima jikin ya sake Neman rikicewa.

Sunaji suna Gani Jamaal ya dauke Ameenatou din ya Kaita wani tsadaddiyar asibitin masu matsalan kwakwalwa na wani abokin aikinsa acan Poland kwararre Shima ya Bada Amanarta gasu da wani irin tsananin tsaron gaske a asibitin wanda acan ne kadai zai samu nutsuwan barinta,
Hakama radadi da tashin hankalin da zatai ta shiga akan rasuwarsu Haroon da Babbah datake tinanin shine ya rasu bazasu taba dawo mata ba sbd bazata taba tinawa ba sai ta dawo daidai zasuyi mata saukin gaske.

Da zai tafi haka ta zaune a dakinta da Babu abinda ya rasa tana kallonsa da fararen idanuwanta da suka rame lokaci Daya harya fice aka rufe mata dakin.

A ranar jirginsa yabar kasar bayan yabarwa siddeeq komai da zai kula dasu Babbah da Hafiz harma da Dadah da umma ke dawainiya da ita.

END OF PART 1
DAN ALLAH DUK INDA NAHI KUSKURE A DAUKESA A MANTUWA KO AJIZANCI,
Insha Allah bayan sallah zamu Dora part 2
Allah ya bamu ikon ibada cikin aminci da yardar Allah
Allah Kuma ya nuna mana kaman yanda mukaje hutun Nan ayau lafiya mun dawo lafiya.

MAMUH
AMEENATOU JDEN SEELAH
JAMAAL SEELAH
BABY ARFAT SEELAH
LOVE
DEEP
ROMANCE
THE SELAHS
WARISCOMING
ZAFAFA BIYAR

ZAFAFA BIYAR

1 Ameenatou!!
Mamuhgee

2 Tsutsar Nama!!
Billyn Abdull

3 Gudun Kaddara!!
Safiya huguma

4 Kwankwason Jimina!!
Miss xoxo.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

Series Navigation<< Ameenatou Part 2
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *