Kwankwason Jimina Part 3

https://chat.whatsapp.com/Gbut9ibvwWM8JPk0qoMEiZ

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

29

:::::::::

Motar na fakawa… Ma’aikatan wajen suka tattaso… Dr bintu ta zuge glass tana daga musu hannu. Suka shiga gayshe da ita daya bayan daya kasancewar sun san mai dakin mai gidan su..Wani lokacin yakan zo da motar da tazo da ita ma.

“Akwai Kaya ko?”

“Akwai hajia”

“Mota fa?”

“Itama akwai. Aciki za’a kai miki kayayyakin?”

“Eh… “

“Tohm hajia me da me akeso?” Cewar wani daga cikin su don shine in charge na maaikatan wajen.

“Inason buhun shinkafa ta tuwo data dafawa, buhu daya daya kowanne.. Inason taliya cartons uku. Macaroni cartons uku. Indomie cartons uku. Sai garin tuwo buhu biyu. Akwai mai ko sun kare?”

“Akwai ranki ya dade.”

“Okay inason 25 litres na man gyada da manja kowanne jarka daya daya. “

“Tohm hajia bari a saka miki a motar. “

“Godia nake”

Ta fada tana zuge glass din zuwa sama. Maaikatan suka sassaka mata kayyakin a daya daga cikin motocin da ake delivery na kayan abincin idan customers sun saya suna son dispatch.

“Hajia gidah zaa kai?”

“Aa yabiyo motar mu. Naduka zone zamu shiga”

“Tohm shikenan bari ya biyo ku a baya”

“Nagode”

“Munda fa godia hajia. Allah ya saka da alkhairi ya biya bukatu”

“Aaameen”

Baki daya a atsora ce take. Gabanta ya shigaa bugawa fat fat alokacin da direban ya gangara da motar zuwa kofar gidan marigayiya Hindu.

“Hajia min karaso”

“Ta jiyo muryar sa ta daki dodon kunnenta”

“Okay…” Fita tayi ahankali tana gyara zaman mayafin jikin ta

Yayinda motar data dakko kayan abincin itama tayi parking a bayan tasu,

“Hajia ya za’ai da su?” Direban motar kayan ya tambaya

“Ku shiga dasu nan gidan”

“Okay tohm”

Ya fita daga cikin motar shi da direban motar tata suka fara kama kama da buhunhuna na shinkafar da kayan abincin cikin gidan na Bappah junaidu.

Alokacin duk suna parlor a zaune. Bappah Auwalu, Bappah junaidu, Nusaiba, Ashir, Ashfeef, Nawraah, Layla, Ahmad da kuma Amnah.

Suka jiyo bakuwar sallamar su direbobin,

“Waalykm Salam. Suwaye?”

“Aiko mu akai aina zamu saka kayan nan?” Cewar daya daga cikin direban

Ashfeef daya amsa musu ya juya yana kallon mahaifin sa yace da su,

“Anya ba batan kai kukai ba.? Ba nan gidan bane”

“Ba manne gidan marigayiya Hindu ba?”

“Eh nanne. ” Ashfeef ya amsa su

“Kai suwaye ne?”

“Bappah wasu ne suka kawo kayan abinci nace ba gidan nan bane shine suka ce bananne gidan marigayiya ummy ba?”

Bappah Auwalu ya mike Kafin ya taka ya tafi tuni nusaiba ta wuce da sauri ta isa wajen su tana kikkifta idanu sai hucin iskar tafiyar ta yaji ta kunnen sa😂

“Nan ne ku shigo da su” ta amsa su tana bin kayan da kallo

Suka sauke suka sake komawa.

“Nusaiba menene hakan wai! Ya haka kawai bamu san mutane ba zaki ce musu eh nanne su ajiye ke meyasa ne har yanzu … Ya kasa karasawa kawai ya girgiza kai hadi da sakin tsaki. ..”

“Kayan abincin zasu mayar da su muna nema?”

Tsabar bakin cikin kalamanta wai”suna nema” tamkar kayan abincin su aka kawowa ba gidan na Bappah junaidu ba. Bappah Auwalu baki daya halayen Nusaiba sun dai na bashi mamaki..

Suka shigaa kawo kayayyakin suna ajiyewa har suka kammala suka koma suna gayawa Dr bintu sun Kai musu kayan .

Nusaiba sai leken su take tana sake daga kafafunta don hango su sosai. Tun daga tafukan kafafun ta ta shiga kallon ta cikin kayan ta masu matukar tsada ya zuwa fuskar ta data sanya facemask .

Takawa tafara yi har ya zuwa kofar gidan da zaka shiga ta rangada sallama,

“Shigo ciki yar uwata”😂 cewar nusaiba tana dashare baki taga kalar masu kudi da suke burgeta.

Dr bintu ta dan kalleta tana kakaro murmushi itama ta facemask ta zare takalman ta ta shiga parlorn

Sallama ta sakeyi. Suka amsa baki daya aka nuna mata wajen zama ta zauna,

“Uwar dakinta ce ko? Hajian Naduka crescent ?” Nusaiba ta tanbayeta tana kallon fatar dr bintu dake shekin masu kudi.

“Eh yar uwar ta ce ni, Amma ba ita bace. Hajia qibdiyya kike nufi ita suna kasar waje basu dawo ba. Ta haihu dan ba rai sai Kuma ta hadu da rashin lafiya. Shine suka sake daga dawowar tasu zuwa wani lokacin a gaba “

“Okay ko kece wadda takewa abinci ta biyu bayan tafiyar h..

“Nusaiba haba. Ki dakata mana tayi magana da kanta” bappah Auwalu ya tsawatar mata.

Dr bintu da dama nusaiba ta isheta da magana tayi hamdala kasan zuciyar ta. Ta gayshe da su suka amsa kananan Kuma suka gayshe da ita ta amsa musu,

“Ya Karin hakurin mu? Ashe Hindu lokaci yayi? Toh Allah ya jikanta da rahama ya gafarta mata.”

“Aamin… Aamin” suka amsa baki daya.

“Wallahi bamu sani ba. Mai gidah nama Yana muku taaziya yace zai zo inshaa Allah abubuwa ne suka rike shi. Yace ga kayan abinci nan ba yawa dan Allah adafawa iyali su ci. “

“Allah sarki angode kwarai”

“A ranar da muka zo ni da ummyn mu…. Lokacin data ce na taho gidah ta koma ciki bansan meya faru ba. A tsorace take dai. Kikace lalle ta dama muku kunu Kafin ta taho.. A ranar aka bige ummy a mota ta rasu a hanyar ta dawowa daga gidan ku”

Kofofin kunnuwan Dr bintu suka jiyo mata kalaman muryar Nawraah data karashe zancen tana sake nanatawa da,

“Ba kece Dr bintu ba inda ummy ke miiki aikin abinci da rana. A ranar kikace taje da yammaci?”

Nusaiba ta juya ta dubeta tana kallonta da Karin bayani. Bappah Auwalu ya dan zunguri kafar bappah Junaid dake kusa da Nawraah, daya kishingida kansa Yana kallon sama. Baki daya tunda ummyn ta rasu ya dawo tamkar ba shi ba ya zama shiru shiru baya magana gaba daya sai ta kama. .

“Nawraah… Menene haka?” Bappah junaid yace da ita yana kallon ta

Dr. Bintu gabanta ya tsananta bugawa tayi hanzarin seseta kanta. Bappah Auwalu yace,

“Nawrah ya Isa. Ai da yardar Allah Hindu yar aljanna ce. Lokacinta ne yayi. Kuma wannan koma wanene kowacece da sukayi aika aiken nan sai dai muce ubangiji Allah ya saka mana ya biya mana hakkin mu a madakata. Allah Kuma ya bayyana mana su tin a duniya. Hajiya kiyi hakuri kinsan yarinta. Nawraah, Tunda akace a titin nan haka ta rasu kinsan tare ranar suka fita. To abun ya tabata sosai ne wallahi” bappah Auwalu ya ce da dr bintu cikin tabbatarwa

Tayi murmushi tana kallon Nawraah tace,

“Nawraah Allah ya gafartawa mahaifiyar ku kinji? Wallahi banida masaaniyar mutuwar ta ma sai da yar uwata kawata hajia qibdiyya uwar dakinta ta farko ta kirani take gayamun dazu. Wallahi sai na kasa zaune na wuce ofishin mai gidan nake sanar masa. Abubuwa sun masa yawa shi Kuma. Shine fa yace na kawo kayan abincin Kafin yazo. Kuma wallahi nima inata Kiran wayar ta a kashe don nayi mamaki ma da hajia qibdiyya tacemun ta samu wayar Hindu nan take sanar mun ai Hindu ta rasu Kuma accident nema muka kiyasata ranar da tazo gidah na ne ai . Wallahi na shiga dimuwa fiyeda yadda baki zai furta. Don kudin aikinta na wannan watan ma wallahi bata karba ba. Yana waje na, Gasu ma nace bari na kawo . Allah ya jikan Hindu ya gafarta mata”

“Ah kin kyauta. Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa .. Amin”

“Allahumma Aameen. Ni zan tafi sai mai gidan na wa yazo inshaa Allahu, Nima zan sake waiwayowa. Allah ya baku hakurin rashin ta”

“Ko ruwa baa kawo miki ba” nusaiba ta fada tana mikewa tsaye itama

Dr bintu tace da ita,

“A koshe nake karki damu. Nagode. To sai anjiman ku”

“Sai anjima, Allah yabada ladan “

Ficewa tayi da sauri nusaiba tabi bayanta tana cewa da ita,

“Angode sosai… Sai da safe.”

Dr bintu ta daga mata hannu kawai alamar bye bye, ta shiga bayan mota da sauri driver yaja suka tafi. Ta saka hannunta akan kirjinta saboda yadda yake mata duka.

Tiryan tiryan maganganun Nawraah suka shiga mata yawo a kwakwalwa, Wannan wace iriyar yarinyar ce ne? Bata mantuwa? To me take tunani kenan! ? Lalle wannan yarinyar sai anyi dagaske akanta kar ta ballo musu ruwa

Duk kuwa da yadda ac din motar ke turarawa hakan bai hana tashin hankalin da Dr bintu ke ciki ba jikewa jagab da ruwan gumi tamkar tayi wanka da kayanta a jike..

Har suka koma gidah bata daina nazari akan maganar da Nawraah tayi ba…

Tirk’ashi!

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

31

:::::::::

To haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa, Yau da dadi gobe babu sai hamdala kawai.

Nawrah ta gama zana jarabawar gama sakandire baki daya. Ashir ya sanyata a wani lesson school na marasa karfi nan kusa da su. Nusaiba ma dataga hankalin ta ta tursasa bappah Auwalu a dole ya nemo kudi ya saka Layla…

Ashir tun daya kammala sakandire Yayi national diploma bai sake cigaba ba. Malama Hindu nata ciku cikun kan zata fara tarun kudi sosai ta turashi babbar jamia yayi karatun acan Allah beyi ba ta rasu.

Ashfeef Kuma daga sakandire bai sake cigaba ba shi bayason karatun sosai. Don haka bappah Junaid ya ce a kyale shi ya huta, Nan gaba dole ya zabi daya ko karatu ko shiga kasuwa…

Amnah ce kawai bata fara zuwa makaranta kasancewar karancin shekarun ta da kuma yawan lalura da take da ita, Amman duk da haka Nawraah na zama da ita ta koya mata karatun dai dai shekarun ta..

Haka zalika bangaren gidan bappah Auwalu ma Layla tare suka gama sakandire da Nawraah. Ahmad yayan Layla, Bai cigaba ba tun da yakare sakandire daman ajin su daya da ashfeef shima yaki karatun wai yan buga kwallo yake so yayi shi da ashfeef din.

::::::::::

Dawowar su daga lesson kenan ta hango yayyun nata acikin kewayen da suke toya awara.

Kifta idanunta tayi ta sake gogesu da tafukan hannayen ta. Ba gizo bane, Yan uwan nata tagani suna kokarin hada murhun yin awara

Rabon su da yin awarar tun mahaifiyar su malama Hindu na da rai

Wasu hawaye suka ziraro mata da hanzari ta goge tana nufar su.

“Hamma…”

“Ah Nawraah kin dawo?”

“Na dawo Hamma ..”

“Toh maza aje a sauya kayaki yi aikin da aka baku na karatu na gaya, Miki jarabawar jamb dinku na dada karatowa sai ki dage sosai da addua da yin karatu”

“Inshaa Allah Hamma. Amma bari nazo na taya ku awarar za’ayi?”

“Eh awara zamu cigaba da yi Nawraah. Kakki damu Ashfeef ma nace masa ya barshi ni zan toya ta tunda batada yawa yaki.” Ya karasa fada yana bin Ashfeef da kallo yana grigiza Kai

Ashfeef dake gefe yayi murmushi Yana gyara itatuwan yace,

“Haba Hamma abubuwan suna maka yawa ai. Badan yunwa ta dawo da ni bama ai kullum sai dai na dawo na tarar ka kammala komai. Dan dai yau Ina gidah na tayaka. ? Inshaa Allah tun da dai zaa cigaba da yi zan dinga zama da rana zuwa sanda zamu karasa inshaa Allah” Ashfeef ya fada cikin tabbatarwa…

Hamma Ashir yayi dariya, Yana cewa,

“Gayu agaban murhu? Aa fa jeka cigaba da abubuwan ka bros. Aini nayi niya ba wani ne ya saka ni ba.”,

“Aa nima inason na samu lada Hamma, Nawraah Kafin nazo fa naga ya gama komai har awarar ya yanka ya daka yaji ya sayo ledojin yayi komai ya hada wutar murhu daya zai hada wannan wadda nake yi yanzu sai gani nayi saurin karba na fara hadata”

“Wallahi Hamma Ashfeef haka Hamma yake kullum baya gajiyawa. Fatan mu Allah ya shi masa albarka kawai.”

“Haba Nawraah gajiyawa? Da ku Yan uwan nawa? Yo idan ban muku ba wa zan wa eh? Ai kune priority dina. Allah yasa mu dace”

“Aamin Hamma. Amma dan Allah kayi hakuri Zan zo na dinga zuzzubawa a leda idan an saya… “

“Shikenan tunda kikace Allah ai roko ya kare.”

Shigewa cikin gidah tayi da sauri. Cikin kankanin lokaci ta sauya kayanta zuwa wata riga marar nauyi ta yafa wadataccen nayafi na ummy nema, Ta lullube kafafuwan Amnah dake bacci akan kujera , ta futa tsakar gidan inda suke hada aikin awarar ta janyo kujera ta zauna.

Nan da Nan kuwa mutane suka fara turuwar zuwa sayan awarar. Ba kadan ba daman sunyi kewar rashin yin awarar da ba ayi, Duk da sunsan iyalin suna alhini rashin mahaifiyar su ne……..

To haka rayuwar ta su ta cigaba da garawa, dare ya zama safiya, safiya ta zama Rana, Rana ta zama yammaci . Yammaci ya koma dare. Lalle Allah buwayi ne gagara misali…

Nawrah sun zana jarabawar su ta jamb sun Kuma ci inda suka rubuta gurbin jami’oi biyu da polytechnic daya na:

Jami’ar Al-Haramein Naduka mai zaman kanta da ke Naduka crescent (apple island)

Jami’ar gwamnatim tarayya ta Naduka

Da Kuma makarantar polytechnic ta koyan jinya Wanda ke cikin babban asibitin na Naduka..

Cikin ikon Allah Kuma sun samu gurbin karatu a jami’ar Al-Haramein Naduka mai zaman kanta dake Naduka crescent apple island…….

Jami’ar da yayan masu farcinan Susa ne sike zuwa da manyan kusoshin gwamnati da yayan Yan siyasa Dana Yan kasuwa da manyan malamai da masu sarauta. Kai harda ma dalibai na ketare dake halartar karatun a jami’ar . Saboda tsananin kyawunta da Kuma gogayya ta yayan masu kudi. Don babu talakawa sai dai ko Yan scholarship shima tuni an dai na dauka saboda yaran masu kudin daga cikin su since basu San gogayyar rayuwa da yaran talakawa a daina kawo musu su.. abunka da masu fada aji, Nan da Nan kuwa aka dena daukar daliban tallafin ya zama sai yayan wance da wane.. who is who?!!!

Ko da Nawraah taga sakamakon inda gurbin karatun su ya fito.. tuni jikinta yayi sanyi don tasan abune da bazai taba yiwuwa ba inde ba Allah ne ya amince da faruwar hakan ba. Basuda kudin da Za’a iya kaita gurbin karatu a makarantar..

Ta kalli second choice dinsu itama jamia ce ta kasa . To idan ma ai abbiey ba zai iya biya mata ba..

Ta daga kasan kayanta kawai ta saka takardar ta cigaba da harkarta…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

32

:::::::::

….

GIDAN ALH. SAMBASO

  Yana daga kasan carpet a zaune rike da waya a hannun sa yana daddannawa…

Dr. Bintu na gefen sa ta rike kofin shayi a hannun ta tana sha ta dube shi,

“Kaje kuwa?”

“Ina fa?”

“Maganar me nake maka naci constantly?”

Ya dubeta yana dan daga kansa sama alaman tunani,

“Maganar zuwa Texas da kikace ?”

“Alhaji! Dan Allah ka dai na dodging idan muganar nan sarai kasan me nake nufi”

“Sanar da ni, ganar da ni”,

“Ina maganar zuwan ka gidan marigayiya Hindu.”

“Ah ba nasaka a sake tura musu kayan abincin ba me suke bukata Kuma?”

“Haba Alhaji, kaje ka musu gaisuwar ta’aziyya mana”

“Ai lokaci ya kure”

“Gaisuwa bata rub’a ai… Ko shekara nawa ne kaje ka musu gaisuwa ai bata tsufa zasuji dadi, sannan kin zuwan da kake ne zargi zai shiga tsakani. Na gaya maka ai abunda yarinyar tasu Nawraah tace. Ita wadda suka zo ranar da marigayiyar ta rasu”

“Zanje kakki damu”

“Haka kake fada sau ba adadi

“Jibi inshaa Allahu zaa muje”

“Toh shikenan . Allah ya Kai mu”

“Aameen.”

       :::::::::::::::::::::::::

Ranar talata bayan sallar magriba. Alhaji Sambaso da mai dakin sa Dr bintu suka je gidan na Bappah junaidu.

Suka shiga tamkaar wasu mutanen kwarai musamnan Alhaji Sambaso da harda hawayen makirci wai na tausayin iyalin data bari.

Su bappah junaidu suma sun karbe su hannu biyu. Bayan ya tashi zasu tafi ya dakko kudi ya bawa Amnah .

Inda yake ta mamakin ai bai ma san Bappah junaidu mijin marigayiya Hindu bane kasancewar a kamfanin sa yake aiki na kera makeri na gidaje aluminium da sauran su…

Ya sake dakko wani kati ya mikawa bappah junaidu yace da shi ya Kira wannan number yazo zai bashi wani aikin dayafi wanda yake yi..

Suka shiga yi musu godiya Alhaji Sambaso yanata kada mukullin hannun sa na mota yace,

“Zamu shiga cikin case din zamu gano Wanda yayi wannan aika aikan . Amman Kafin sannan ku kwantar da hankulan ku ku bar mana komai a hannun mu. Ni zan samu dakarin farin kaya na tsaro na kasa zamuyi magana sosai zaa zurfafa bincike inshaa Allah”

“To shikenan angode Allah ya saka da alkhairi”

“Aaameen Alhaji. Angode kwarai” Cewar bappah Auwalu.

Suka musu rakiya har kofar gidah bappah Auwalu yanata kambama mutincin su.

Alhaji Sambaso ya ja motar suka koma gidah zuciyar su fari fat ya dubi dr bintu yace,

“Kinga ai na wanke su. Nan gaba kadan ma zan sake zuwa na yi musu wani hidimar”

“Ka debi a hankali Alhaji ba damuwa.”

“Ai ni banida masaniyar mai gidan ta. Ai a karkashi na yake aiki a kamfanin yankin dalla. Zan bashi babban aiki gaskia”

“Yauwa hakan ya yi..”

::;;;

  To haka rayuwar ta cigaba da garawa.

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

33

:::::::::

Amnah yau lafiya gobe babu. Sunata zuryar asibiti duk kudaden hannuwan su suka kare.

An mata tasa tasai an gani tanada ciwon tonsils shi ke sakata amai da yunkurin aman. Sannan typhoid ta mata illa..

Bappah junaidu bayasan bin mutane ko yan uwan sa yana cewa su temaka masa. Don haka ya saka gidan su jingina bada masaniyar kowa ba ya karbu kudin aka yiwa Amnah aiki da shi aka kwantar da su a asibiti sukayi jinya sosai.

Sai bayan da aka sallamo su ne bappah junaidu ya shirya ya tafi ofishin da Alhaji sambaso ya bashi katin.

Ya nufi unguwar har kamfanin akace ya shiga. Ya nufi ofishin zai shiga ya ja ya tsaya jin da akwai mutane aciki suna magana.

Har zai juya yaji an ambaci sunan sa da na matar sa. Sai kuma ya jiyo suna maganar tarin dukiyar dr Abubakar dollars dayake so ta zama mallakin sa har ya saka hannu. Can kuma yake gayawa mutumin, Tsautsayin daya same shi na niyyar illata Malama Hindu sai kuma ya kasheta har lahira. Kafafun Bappah junaid suka gaza daukar sa. Ya sanya hannu a baki ya toshe saboda wani abu daya taho masa. Kafafun sa suka gaza daukar sa. Ya nemi jikin kofar ya jingina saboda wani yanayi na tashin hankali daya samu kansa aciki.

Alhaji sambaso suka gama magana da mutumin na ciki sukayi sallama. Mutumin ya tashi ya nufi kofa zai tafi.

Laptop din Alhaji sambaso ta fara karan shigowar waya ta app ya dauka yana murmushi kasancewar video call ne…

Alhaji ateeks na daga masa hannu yana bude kofar sai ga Bappah junaidu fuskar sa shabe shabe da hawaye. Alhaji ateeks ya dube shi ya wuce dan baisan waye ba ma.

Alhaji sambaso ya ja hannun sa ciki yana rufe ofishin. Ga video call din nata tafiya. Na ciki yanata ‘hello hello’ yana duban sa.

“Meyasa ka kashe mana Hindu? Me ta maka?”

Alhaji sambaso ya bude baki yana shafo keyar sa yana hura iskar bakin sa mai zafi yace…

“Bangane me kake nufi akai ba. Hankalin ka daya kuwa kasan me kake cewa?”

“Na sani mana, da hankali na duk na ji dukkanin abubuwan da kuke fada, Kai da abokin ka. Kun hada kai kun kwato duniyar Dr abubakhr dollars ta karfin dole. Kun kashe Hindu meta muku? Shin akan wani dalili kuka kashe mana hindu? Ashe kai ka bigeta a mota ka kasheta Alhaji? Yanzu duk wadannan kayan abinci da kake aika mana da sauran su dama duk toshiyar baki ne? To Allah ya tona asiirin ku wallahi Allah kuwa daga yau zaka kwashe kashin ka a hannu”

Ya saka hannu akan mabudin kofa da niyyar murzawa ya fita Alhaji Sambaso yayi hanzarin riko hannun nasa yana duban sa sosai,

“Ka tsaya muyi magana ta hankali ba abunda kake tunani bane”

“Babu abunda zanji. Kuka samu kanku gaban hukuma zakuyi bayani, yanzu a yau zan bankada dukkanin kofofin sharrin ku. Mugaye kawai. Allah ya yi wadai da halayen ka”

Ya sake kai hannu zai fita Alhaji Sambaso ya tare hanyar ya riko shi yana duban cikin idanun sa yace,

“Kasan wanane ni kuwa! ? Na ga alamar ba hankalin ka kake ba, wannan zantukan, Idan kudi kuke bukata zan baka ishasshe yanzu. Dan naga alamar rashin su ya fara taba maka kwakwalwa kake ta surutun magana da sambatu acikn ta”

“Wai ka dauka kudi na sayan mutane? Ka dauka dukiya itace kwanciyar hankali? Ka dauka dukiya itace maganin damuwa? To ka bude kunne ka kaji. Daga yau kwanan ka a doren duniya cikin gidan ka babu kai babu kwanciyar hankali. Inshaa Allahkashin ka ya bushe. Police station zan tafi wallahi wallahi ” ya fada yana duban sa cikin tsantsar tsana.

Alhaji Sambaso yayi hanzarin riko kafadunsa. Bappah junaidu ya fuzge. Alhaji ya sake riko shi. Suka shiga kici kici har zuwa wajen wata baranda. Bappah junaidu ya jinga a jikin bango yana magana cikin fushi

Jiyuwar nan da Bappah Junaid yayi Alhaji Sambaso ya hada shi da karfen baranda yana dukan cikin sa.

Ya daga hannu cikin tsantsar tashin hankali da tsana ya shararawa masa mari

Alhaji Sambaso ya rike kuncinsa, Yana duban bappah Junaid daya sake daga hannu zai kauda masa wani , Alhaji Sambaso ya jinginar da shi a jikin baranda, bappah junaid ma ya tattake ya buga shi da kofar.

Alhaji Sambaso cikin hazalar fushi ya cakumi wuyan bappah junaid ya hankada shi da karfunan barandar.

“Kashe ni zakai? Nima ka mar yadda ka kashe matata?”

Alhaji Sambaso ya saka hannu, Yana rufe bakin bappah Junaid dayaki ya sake cakumar sa. Alhaji Sambaso ma ya riko tasa yana sake cakomar rigar sa yace,

“Shashasha”

“Kai ne shashasha, Mugu, Azzalumi….”

Garin riko shi zai naushe shi ya hankada shi. Bappah junaidu ya fada kasa ji kake ‘Timmmmm

Kamar kara ya fada, Take kansa ya fashe bai shura ba ya mutu awajen alokacin….

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

34

:::::::::

Rufe bakinsa yayi da sauri, yana zare idanuwa jin muryoyi suna kururuwa daga waje lalle da alama mutumin ya mutu….

Tun sanda mutumin ya shigo dama yayi hanzarin danna recording kiran na video call da sukeyi….

Alhaji Sambaso ya saka hannunsa ya shafo kasan keyar sa, Yana rufe bakinsa da tafin hannun sa….

“Naga kaman labarai kake kalla ko? Bari na kashe na sake kira yanzu nima zanyi abune?”

Ya jiyo murya daga cikin laptop. Dama bai katse video call din ba? Ai baki daya ya manta.

Ya dafa teburin yana kallon sa ta cikin system din yace

“Dama baka kashe ba? Me kake nufi da labarai? Ka saurari maganganun da nake fada ne?” Alhaji Sambaso ya tambaye shi cikin tsananin tashin hankali

Ya girgiza kansa yana bashi amsa da

“No da naga Jana kallon labarai ne kome. Magana sama sama sai na tashi na shiga bandaki fitowata kenan kuma naga kaman da kanta ma muna waya”

“Ka tabbatar abunda ka sani kenan?”

“Eh mana… “Ya kakaro daria ya sake cewa,

“Futsari na tashi nayo ma sai na tsaya na karba parcel dina da aka kawo yanzu”

“Oh okay. To shikenan zamuyi magana, yanzu zamu shiga meeting ne ” ya katse kiran yana rufe laptop din baki daya..

Zagayawa yayi ta kofar baya emergency exit dinsa wanda ba kowa bane ya sani a kamfanin ya fita ta ciki ya koma kasa…

Nan da nan maaikatan wajen suka fara taruwa akan gawar bappah junaidu….

Da sauri wasu maaikatan suka nufi ofishin nasa suka bude baya ciki. Aka dudduba bayan ko’ina

Nan suka shiga fara kiraye kirayen wayar sa. … Ya fito daga cikin wani guri a kasan kanfanin da suke kira da lodge .

Daki ne da parlor da bandaki inda manyan maaikatan suke shiga su huta.

Nan ya futo daga ciki yana mitssika idanu,

“Ah ranka ya dade ashe baka cikin ofishin na ka?” Cewar wani leburan kamfanin daya nufe shi yan yana tambayar sa. Duk sauran maaikatan suka yayyabe su.

Alhaji Sambaso ya saka hannu yana rufe bakinsa alaman hamma ce tataho,

“Alhaji ayi hakuri amaana afuwa, Ashe hutawa ma kake”

“Wallahi kuwa bansamu bacci bane gaba daya nache bari na dan huta. Bayan tafiyar Alhaji ateeks”

“Ranka ya dade wani mummunan labarin ne ya faru”

“SubhanAllah Allah yasa muji alkhairi meya faru kuma?”

“Wani ne ya fadi daga barandar ofishin ka…

Kafin su karasa maganar da suke. Alhaji Sambaso ya katse su cikin buda baki yace,

“Ba dai junaidu ba da yazo duba gyaran da zaa mun a barandar”

“Allahu Akbar kabiran. To shine… Bawan Allahn nan yazo dazo yake tambayar mu wajen ka muka nuna masa ofishin ka . Dama bakuwar fuska ne kam. Amman daya nuna katin ka dinnan nasan babban bako ne shysa ma muka kyale shi ya shiga. Ashe ashe ajalinsa ne ke kiran sa. Kuma akwai tsani fa a bayan kofar bai duba ba kenan ya taka karfen dama karfen ai girgidi yake”

Alhaji Sambaso farin ciki ya taho masa ya danne don kar su gane. Ba kadan ba yaji dadi da daya ji daya a cikin maaikatan yace dama karfunan barandar suna girgidi..

Wucewa yayi gaba tamkar Wanda yake cikin tsananin tashin hankali .mutanen suka rufu akansa sam ba dadin ganin gawar ma ta bappah junaid. Aka dakko kyalle aka rufe shi.

Alhaji Sambaso ya sanya aka kirawo ambulance nan da tazo aka fara wucewa aasibiti aka gyara shi sannan aka kira gidah da number Ashir dake cikin wayar ta bappah junaidu.

Nan ake sanar dashi zaa kawo gawar mahaifin su ya fado daga benen barandar me tsananin tsayi ya rasa rayuwar sa yanzu ma gasunan akan hanyar motar kwana kwana sun biya ta asibuti an gwada gwaje likitoci sun tabbatar ya rasa ransa..

Ashir baki daya dama suna zazzaune a parlor ne. Ya na tsaye wayar ta fadi daga kunnen sa yana salati

“Menene Ashir? Menene ?”

“Hamma menene?”

“Ashir Ashir menene?” Bappah Auwalu ya shiga girgiza kafadun Ashir. Ashir yana zubar da hawaye duk tsananin dauriyar sa jikin sa na rawa yace,

“Abbiey ne…”

“Abbieey din. Meya same shi meya samu junaidun?”

“Bappah…. Abbiey ya ra su… Abbiey ya rasu bappah “

“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…….

Bappah junaidu ya ambatada da karfi gwiwoyin sa sun gaza daukar sa ya zube awajen ya fara kuka sosai tamkar karamun yaro …

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

35

:::::::::

Nawraah na sama ta sakko rike da bokiti a hannun ta da kaya aciki. Tana murmushi tana taka kafafun benen tana sakkowa tace,

“Hamma! Yau ni ma na rigaka Ina son na samu lada…. Na wanke kayan abbiey daya cire jiya. Yana dawowa zan gaya masa”

Tana sakkowa ta tsaya tana duban su. Yadda sukai cirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi.

“Menene?” Ta tambaye su jikinta a sanyaye ..

Duk sukayi shiru suna kuka sosai. Ta karasa kusada da Layla ta dafa kafadarta,

“Meya faru ? Eh? Menene? Wane ne ba lafiya ko wani abun ne na daban?”

Layla ta daga fuskarta sharkaf da hawaye ta saukar ta akan Nawraah tace,

“Bappah ne?”

“Bappah sani Bappah salisu ko bappah Auwalu? Meya same su bappahn?”

Layla ta sake girgiza mata kai tache,

“Bappah junaidu?”

“Bashida lafiya? Wani abun ne ko? Daman yadda kwana biyu abbiey yake yi nasan bashida lafiya. Me akace ya same shi?”

“Nawraah. Abbieyn ku Allah ya masa rasuwa”

“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…” Ta fada da karfi ta zube awajen a sume.

Sukai kanta da sauri. Bappah Auwalu ya saka aka kawo ruwa aka yayyafa mata. Ta farfado da kyar tana wani irin sauke numfashi mai nauyi tamkar zata shide..

“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un… Bappah Auwalu ku tasheni daga baccin da nake.. wai abbiey ya rasu? Abbiey fa kukace? Abbiey ya rasu fa kukace? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un. Wannan wane irin wasa ne? Layla meyasa zaki ce abbiey ya rasu akan wane dalilin abbiey zai rasu eh?” Ya karasa fada tana sakin dariya harda tafa hannuwa tamkar sabuwar marar hankali, can kuma ta saki kara mai razana ta fashe da wani irin kuka tana birgima.

“Wayyo Allah na. Abbiey. Wayyo Allah na! Wayyo Allah na Ummy. Wai abbiey shima shikenan ya rasu ya bar mu? Abbiey ya tafi shima? Ummy ma tarasu fa? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un. Waya kashe mana abbiey? Kashe abbiey sukai. “

“Kiyi hakuri Nawraah babu Wanda ya kashe junaidu kinji. Lokacin sa ne yayi. Kinaji daga wajen aiki ne wai a karfen baranfa ya taka shine ya fado rai yayi halinsa sun akai shi asibiti ma ance ya cika. Yanzu sun taho kawo shi gidah. ” Ya karasa fada mata shima yana sake barkewa da wani kukan

Baki daya sai suka bude shafukan kuka. Nusaiba daga can gefe tayi shiru itama kanta a kasa. Hakika mutuwar kanin mijin nata junaidu ta razananta kwarai matuka. Agubi agubi anyi musu mutuwa biyu kenan ajere ba daukar lokaci.

“Shikenan Hamma bamuda iyaye? Abbiey da ummy sun rasu? Shikenan bamuda sauran gata ko Hamma? ” Ashfeef ya fada yana girgiza kai.

Ashir ya katse hancinsa Yana goge hawayen fuskar sa yace,

“Ga mota can inaga sune…”

Dunguma sukai suka fita wajen …ambulance ce ta kawo shi har kofar gidan suka shigar dashi gidan bisa jagorancin maaikatan..

Daya daga cikin leburan dake kamfanin na Alhaji Sambaso yace,

“Ina wunin ku? Kuyi hakuri fa. Allah ubangiji ya gafarta masa.ya kyautata namu zuwan Allah Kuma ya baku hakurin rashinsa…wallahi Yana gyaran wani bangare ne dake babbar barandar ofishin mai gidan mu. Ashe bai hau tsaani ba sai yahau karafunan barandar a haka ya taka. Su Kuma dama rawa sukeyi shine ya fado Allah yayi masa rasuwa. Domin kwanyar kansa ma afashe take… Inshaa Allahu aljanna makoma ce agareta shi. Yanzu zamu jira a gama wanke shi sai mu sallah shi mu Kai shi gidan gaskia baki daya daku iyalan sa…”

Bappah Auwalu ya fara kiraye kirayen dangi na kusa dana nesa Yana sanar musu rasuwar junaidu. Auta daga iyalan yafendo. Dangin Hamidniyya Lebanon.. Hakika kowannen su mutuwar ta dake shi .

Alkalani yayi kadan wajen bayyana adadin alhini da dangin suka shiga baki dayan su. Musanman iyalan sa na cikin sa sun shiga cikin dimuwa marar misaltuwa.

Haka aka yi masa wanka. Anayi jini na fita daga jikinsa har da guda guda. Haka aka nannade shi duk da hakan jinin yaki tsayawa.

Aka Kira iyalan sa daya bayan daya suka yi masa sallama. Kowanne da koke koke aka futar da shi.

Aka dauke gawar junaidu aka sanya a makara aka sallace shi aka kai shi gidan sa na gaskiyar wato makabarta.

Allahu Akbar wata bishiya ce ta raba tsakanin kabarin marigayi Bappah junaidu da mai dakin sa marigayiya malama Hindu. Allah ya jikan su ya gafarta musu ya musu rahama..

Hakika junaidu ya samu sheda daga bakunan iyalan sa na cikin sa, dangin sa su bappah Auwalu bappah sani da matayen su baki daya dai dangin hamidniyya Lebanon. Sannan mutanen wajen aikin sa dama yan unguwar baki daya sun yabe shi. Ya Kuma samu mutane sosai da suka sallace shi suka kai shi makabarta.

A farfajiyar gidan aka shinfida tabarma aka fara makoki dukkuwa da ahalin Hamidniyya Lebanon basa zaman makoki, Amma mutane na zuwa yi musu ta’azyiya wasu tundaga birnin bunza na kusa dana nesa…

Suma yan yankin bunza sosai sun yi alhini da jimamin rashin junaidu. Domin yanada halaye na kwarai bai taba fada da wani ba .. kowa nasa ne ga temako .

Yanzu zamu sake tsunduma cikin labarin:
KWANKWASON JIMINA MAI WUYAR SHAFAWA… Ayi hakuri da yadda rubutun yake zuwa… Labarin na gaba In shaa’Allah

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

36

:::::::::

Anyi shela anyi cikiyar wadanda ke bin junaidu kudi ko wani na ajiya suyi magana a basu. Yawanci ma anfi samun wadanda shi yake binsu bashin basu biya shi ba.. duk wadanda suke binshi bashin da yawan su wasu sun yay’yaafe. Wasu kuma sun karbi wani kaso na cikin kudin sunce sun bar sauran..

Sai wani mutumi daya tashi ya taba kafadar na gefen sa suka mike. Suka ce hakika ana bin Junaidu zunzurutun kudade masu matukar yawa.

Hakan ta faru ne kuma alokacin da daya daga cikin yaran sa babu lafiya. Aka tambaye su adadin kudin sukace ai wannan magana ba tasu bace. Domin suma shedu ne na mutumin da junaidu ya karbi bashin agaban su. Kamar jingina yayi ya karbi tarin kudi…

Aka nemi ganin mutumin don sanin waye shi da yadda zaa biya da sanin ma shin nawa ne adadjn kudin daya karba? akace daya mutumin yayi tafiya sai ya waiwayo gidah nigeria tukunna.

Daya daga cikin su ya karkare magana da

“Abunda ya saka muka fada ma saboda hali ne irin rayuwa kada abar mamaci da tarin bashi akan sa. Duk kuwa da kadarar sa ya jinginar ya karbu kudin. Amman dai mun ga yakamata fadar shi yafi alkhairi Allah yasa mu dace”

“Ko zamu iya sanin kadarar daya bayar ya karbu kudin a hannun sa?” Bappah salisu ya tambayi mutumin

Mutumin ya girgiza kai sannan yace,

“Wannan batu baki daya sai an kawo takardar da faifan bidiyo da sukai yarjejeniyar ya sanya hannu tukunna shi mamacin. Kafin shima Alhajin ya rattaba nasa hannun”

“Toh Allah ya rufa asiri. Allah ya dawo dashi lafiya. Shi Kuma wannan Dan uwan namu Allah ya jikan sa ya gafarta masa Allahumma Aameen”

Suka amsa da aameen baki daya. Aka shiga yiwa bappah junaidu addu’oin samun rahamar Allah da nasarar amsa tambayoyin kabari.

::::::::;;;;;;

Sannu ahankali haka mutane suka fara darewa, kowanne yanzo daa irin kyawun halayen da yake fada game da manacin.

Hakika bappah junaidu ya samu yabo sosai daga bakunan abokanan sa, Yan unguwa, Yan wajen aikin su, makotan su, Yan unguwar baki daya dama dangi na kusa dana nesa.

An kakkawo musu kayayyakin abinci na tallafawa marayun. Saboda kallo daya zakai musu su baka matukar tausayi marar misaltuwa. Dubada duk ba wani kawo girma sukai sosai ba har shi Ashir din. Be Kai shekarun da zaa ce zai hade kawunan Yan uwan na sa ba.

Amman dake yanada zuciyar tashi ya nemi na kansa don kare daraja da martabar yan uwan nasa. Hakan bai hanashi kutsawa nan da can ba don ganin ya rufa musu asiri…wannan kenan

Haka aka nannade makoki. Akabi mamacin da addua. Hadi da dangana da hakuri da iyalan sa zasuyi. Kowa ya watse na kusa dana nesa

Idan ka tsame dangi mafi kusantana marigayin ba. Wato su Bappah Auwalu da su Bappah sani…

A parlorn Bappah Auwalu suka hallara baki daya iya yan dakin su. Sai nusaiba da tayi kanai kanai taki tashi suna magana tana tsoma baki..

Ba wanu abu ya bari da yaran zasu mori ba illa dubu biyu da dari uku dake aljihun sa Kafin rasuwar sa, sai Kuma wayar torchlight dinsa . Da wasu dari takwas dake drawer dinsa.

Toh su aka harhada dai aka gangada dai da sauran abubuwan sa aka raba gado aka baiwa yaran sa.

Wasu daga cikin kayan sawar sa bayan yaran sa maza sun dauka suna so. Sai Yan uwansa wasu ma suka dauki wasu. ragowar Kuma aka kyautar sadaka duk Wanda yazo karba sai ache masa yayiwa mamaci addua..

Baki daya a zazzaune suke suna kallon kuna. Suna magana,nusaiba na daga saman kujera tana jin abubuwan da suke fada. Wani ta saka baki baki wani tayi shiru..

Ashir ya taho daga gidan su zuwa gidan bappah Auwalu zai gayshe da bappanin na su kamar ko da yaushe yanata sauri ya karasa kofar gidan. Ya saka hannu zai murza kofar ya jiyo su suna magana haka sama sama tamkar masu rigima ko fada, Bappah Auwalu na cewa….


Assalamu alaikum… HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafawa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata Mai abarka…

idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo tarauni dake unguwar Kano sai akira number opay dincan dake sama

zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki..

kofa a bude take da dik Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin.

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

37

°°°°°°
“Dukkanin mu nan uwar mu daya uban mu daya… Ba bare acikin mu idan kuka tsame Nusaiba…”

“Nima ba bare bace Auwalu . Auro ni fa kayi ka cire ni daga cikin dangi na ka dawo da ni naku. Kana da bakin cewar wani ni ce bare?” Nusaiba ta fada tana gatsine.

Yakumbo Aminatu ta tabo ta tana girgiza kai tace,

“Kash ba da wani abun ya fada ba Nusaiba. Dan Allah tashi ki koma daki. Idan muka gama kyaji duk yadda mukayi. “

Mikewa tayi tana zunburar baki hadi da kananun mita ta shige cikin daki. Ko da ta shiga ma d’age labule tayi ta kasa kunnuwanta tana jiyo abunda suke fada…

“Bappah sani, bappah Auwalu, Bappah salisu, Yakumbo Aminatu … Kamar yadda yaran nan ke fada dukkanin su baki daya ciki harda yaran mu. Basuda wasu da suka fi mu ko suka kamo kafar mu. Mune uwar su mune uban su yanzu. Wallahi Allah sai ya tambaye mu idan bamu kula da yaran nan ba … Bari na sake nanatawa. Acikin mu da muka rage mu hudu dinnan. Kowanne zai iya daukar yaran nan baki daya ya rike su ba wani abun bane. Zumunci ne. Naka shine naka. Ido biyun duk sun tsiyaye musu, sun rasa uwa da uba cikin kankanin lokaci baki daya ba jimawa. Zan sake nanatawa, Salisu, Sani, Ameenatou. Dukkanin ku kunfini karfi Kuma kowannen ku zai iya rike fiye da yawan yaran nan ma akarkashin sa. Allah ya hore muku. Yaran nan suna bukatar danshin iyaye atare da su. Ku temaka yanzu acikin ku wanene zai dauki yaran nan baki daya? Kuna ganin abunda mutanen nan sukazo sukace ma akan junaidu yayi jingina ya karbi kudi. Bayaga haka nace muku junaidu nima ya rantomun kudade nayi gyaran gidah har yacemun kyauta da fari nace masa wallahi bazan karba ba bashi nake so… Kunsan dai halin dan uwan mu da rufawa nasa asiri? Sam bayasan wani na waje yaji barakar mu. Zai iya salwantar da komai nasa don ganin ya sanya mu acikin farin ciki. Dan Allah kada mu bari yaran nan suyi maraicin iyayen su. Kada mu bari yaran nan su Gane Cewar bamuda hadin Kai a tsakanin mu ba zamu iya rufawa dan uwan mu asiri ba. Wanda dukkanin mu nan kowannen mu junaidu yayi masa da aljihun sa, da jikin sa da gumin sa. Bai taba gajiyawa ba….. Shin wa zai karbi rikon yaran nan su dawo hannun sa? Su hudu ne kawai, Ashir, Ashfeef, Nawraah sai Kuma auta Amnah… Wallahi summa tallahi da inada halin da zan rike yaran nan wallahi zan rike su, Amman banda shi. Junaidun dai ke rike damu duka har ni ya rasu. Dan kuwa komai na rayuwa wallahi shi yake mun ya dauke mun komai . Ba abunda zance da shi sai fatan Allah ya masa rahama yasa ya cika da kyau da imani amin “

“Aameen ” suka amsa baki daya

“Sani zaka rike su?”

Bappah sani ya grigiza Kai Yana duban agogon hannun sa yace,

“Kasan halin da nake ciki yanzu. Wallahi Idan na ce zan rike yaran nan zan takura bazan iya ba wallahi.”

Bappah Auwalu ya kada Kai ya dubu Bappah salisu yace dashi,

“Salisu kaifa! Nasan dai ba zaka ki ba. Kusan a bunza junaidu yafi shakuwa da Kai ma”

Bappah salisu yayi hanzarin girgiza kai yace,

“Bazan iya rike su ba gaskia. Abubuwan sai ahankali yaran gaba na kadai ma sun ishemu. Bazan iya hadawa da yaran nan ba saboda banida karfin hakan”

Bappaah Auwalu ya kada Kai cike da takaici . Ya dubu gwaggo Ameenatu yace,

“Ke fa? Aminatu ke fa? Zaki rike su ko? Nasan ke bazaki ki amincewa ba ba zaki ki tallafar ahalin junaidu ba. Ni na sani”

Gwaggo ameenatou ta sauke katuwar bahaguwar zuciya tace,

“Ba wai naki bane. Amman Auwalu a situation din da ake ciki Allah mai gidan ma baze bari na dauke su duka ba. Kaga expenses din sunyi yawa. Amma dai ni Ina son abani Amnah zan riketa. A shirye nake na tafi da Amnah. Idan yaso su Ashir, Ashfeef da Nawraah sai asan yadda zaa kula da su. Ko a rarraba su. Ni na dau Amnah, Kai salisu ka dau Ashfeef da Nawraah, sani Kai Kuma ka rike Ashir dakin nan na wajen gidan ka ku bashi ya zauna aciki ya muku tsaro ma tunda namiji ne Kuma babba, Ko duk wata wata zamu dinga harhadawa yan kudi ana kula dasu. Kowannen acikin mu sai a bashi ya kula da dan dake gaban sa yana ragewa. “

Ashir ya girgiza kai din takaici har hawayen bakin ciki yayi. Wato da iyayen su na raye bappanin nasu kamar su cinye su suna nuna suna kaunar su. Amman yau dan ba ran bappah junaidu da su ke uwa daya uba daya shine autan su Kuma ‘yayan sa na cikin sa. Amma kowanne yaki amincewa ya karbe su.

Cikin zafin nama ya bude kofar ya shiga yana goge hawayen sa yana kallon su yace,

“Yakumbo ba zaki dau Amnah ba, ba Wanda zai dau kowa… Ku barshi kuje ku zauna da iyalan ku na cikin ku. Ni zan rike kanne na. Zan kula da cin su, Shan su, tufatar da su da yi musu komai Wanda mahaifi da mahaifiyar su zasuyi musu. Zan share musu kukan su. Da yardar Allah ba zasuyi na damar kukan rashin iyayen su ba a kusa. Barkan mu da rana dama gayshe mu nazo yi. Ku huta lafiya…”

Ya juya ya fice cikin zafi nama. Ransa na matukar Susa. Ya rakube a jikin wani gini Yana kuka sosai. Dama haka Yan uwantakar take? Wato idan kana raye ne akeyi da Kai da iyalan ka idan ka rasu baya ake juya musu ana kyamatar su haka? Lalle sunyi rashin bango majingina.

“Yaa Allah…. Ka dubi maraicin mu ka kawo mana dauki Aaameen.” Ya fada Yana goge hawayen sa yayi hanyar gidan su jiri nata dibar sa.

Jijiyar kansa ta tashi radau ransa amatukar javula haka ya seseta kansa ya shiga gidan na su. Kai tsaye ya wuce dakin su. Ashfeef baya nan. Ya nemi katifar su ya kwanta Yana rufe fuskar sa da tafin hannun sa..

Hawaye masu matukar dumi suka shiga kwarara daga idanun sa…

‘K’J
(M/W/S)

✍️:MX

38

:::::::::

Bappah Auwalu ya mike tsaye yana nuni da kofar da Ashir ya futa hawaye na gangara a fuskar sa yace,

“Kun gani ko? Tun ba’aje ko’ina ba. Kun fito kun nunawa iyalan sa na cikin sa ba kaunar su kuke ba. Haba haba haba wallahil azim kunban kunya. Wallahi summa tallahi da inada halin da zan rike yaran nan wallahi zan rike su.. Amman tir da halayen ku, kun yanke amanar zumuncta Allah kyauta”

“Ni dai na gaya maka uzuri na. Ai wata kusan tafi wata kusa. Har ga Allah banga ma abunda akayi anan ba. Yaran dai dama yanada tinkaho ne kawai amman me akayi anan ko salisu?”

“Gaskia nima sani banga abunda akayi ba. Magana ce fa aketa gaskia domin Allah. Magana ce ta dindinin abunda zaka dore. Ai bakyau mutum ya dau a abinda ba zai iya cigaba da shi ba. Mun fito mun fadi uzurin mu shin menene matsalar anan? Me mukayi ni gaskia banga wani aibu da akai anan ba kai ma Auwalu da son kakaro mana lefi. “

“Hmm bare ni dana amince zan rike daya daga cikin su. Ni menene aibuna? Na amince zan karbeta na riketa. Ba shikenan ba? Amman yaci ace yaron nan yazo tsakiyar mu manyan sa, da uban sa yace zai gasa mana maganganu har haka? ” Yakunbo Aminatu ta karasa fada tana jan dogon tsaki…

Bappah Auwalu ya ja tsaki akaro na uku yana karkada hannu Yana nuni da ceiling dinsa yace,

“Wannan ceiling din da sabun kofofin nan/kyaurukan nan. Marigayi ne ya kawo mun kudin wallahi kyauta ma yace ya bani shi zai biya su. Nace aa wallahi bazan amince ba nafi kaunar ni na biya da Kai na idan na samu. Domin junaidu adadin bashikan da yaron nan ya biyamun Allah ba zasu fadi ba. Cin mu , suturar mu, komai namu wallahi Allah shine shahidi. Junaidu yana matukar kokari ganin ya mana dai dai gwargwadon ikon sa. Haka ma matar sa wallahi batada bakin hali kwata kwata. Hakama yaran nasu baki dayan su wallah kowanne sai sam barka. Amman tin da ga kowanne acikin ku uzurin daya kawo bazan takura muku ba. Allah ya kyauta. Ni naji na amince zan rike su”

Nusaiba ta fito daga cikin dakin da take labe. Ta daga hannu tayi guda ta nana a cinyarta tace,

“Katarar ubancan. Lalle ma Auwalu, mu sai yan hakora. Da jiki duk qashi muna tafiya da kwana acikin talauci. Kache zaka rakito mana wasu rayikan har hudu su tare awurin mu. ? Shin Ina zamu saka su acikin wannan gidan naka mai ukubar rayuwa eh? To ahir dinka. Wallahi ahir dinka. Narantse da uban da ya haifeni ban amince ba”

“Gaskia babu babbar butulu a duniya irin kiba nusaiba. Babu Allah. Menene a duniya Wanda mamatannan basu Miki ba su da yaran su.? Junaidu daki sukutum ya dauka ya baki kika saka kiwon da kike. Banda tarin alkhairin da yake mana mu da yaran mu kullum. Marigayiya Hindu baiwar Allah nan ba abunda ta rage Miki ta dauke ki tamkar kanwarta bata Miki kallon faccala dede da second daya. Duk sanda tayi awarar data fara ta sayarwa har Allah ya karbu ranta kullum yaumin sai ta aiko mana, karewarta ma ranar da zata rasu sai data shigo muka gaysa tace daman wajen ki tazo ma tamiki fada . Yaran nan wataran wajen ki zasu dawo ki rike su ma ke zaki aurar da su. Wai Amman duk wasiyyar da take bar miki din kuwa wasiyya ce dai dai da kwayar zarra baki taba ajiyar ta ba a…

“Ya Isa dakata da wannan wa’azin kurman da kake don ba saurara nake ba. Da fari kana magana yo wancen akurkin dakin ai sai da ya tabbatar dan Adam ba zai iya kwana aciki ba ko da kuwa rai daya ne bare yace zai moriyar sa shine ya jefe ni da shi. Su kansu kiwon dakyar suke nunfashi saboda azabar zafi da duhu ba ai wundo ba a dakin haba haba dan Allah… Kana maganar awara awarar banza awarar wofi Allah ya kwashewa waken soya ma albarka Auwalu, . Kana maganar suna kyautata mana to ba dole su kyautata ba kudin yafendo ne data bayar ya handame don kuwa sata yayi yasa tayi masa kyautar dole. Dake Kai zakara ne sai da tsaba ya saye ka da kananun kashin kudin da yake maka ya rufe maka baki baka iya ganin lefin sa . Wannan kai ya dama. Na fada na sake fada ba yaran da zai zauna mun agidah wallahi. Muna karime Karime to abincin da zamu ci kullum na rai hudu dakyar zaka karo mana wasu hudun? Tukun nama aina zasu kwana? Wannan gidan Mai kama da turken agwagwi. Muma bai ishe mu ba bare Karin wasu mutanen Na gama magana Allah . Ba dan da yar da zasu zauna mun ” tana karasa maganar ta shiga daki ta bugo kofar.

Bappah Auwalu yayi shiru ya kasa cewa komai. Babban abunda yafi daure masa kai da Yan uwan sa uwa daya uba daya ke wajen basu tanka sun tsawatar mata ba, Amman ba wani abun mamaki bane tunda sun ki amincewa su rike yayan kanin su uwa daya uba daya .

“Allah ya kiyaye hanya idan kun tafi. Na bar ku lafiya Allah yabada ladan taaziyya mungode”

Ya saka kansa ya fuce ya bar su zaune… Suka gama maganar da zasu yiyyi suka hada Yan kudin hannun su suka zura a takardar envelope suka saka masa a bayan kujerar da ya tashi
.
Daya bayan daya suka dare suma batare da sunji kunyar abunda suka aikata ba na kin daukar ‘ya’yan kanin su uwa daya uba daya…

Ashir yana kallon kowannen su ya shiga motar sa ya tafi, ta cikin windon dakin sa.. yakumbo aminatu ma direban ta yazo daukar ta ta shiga mota tatafi.

Rayuwa kenan dama wasu dangin basayi da iyalin ka sai kana raye idan ka rasu kabar iyalan kama juya musu baya suke..

Lalle bango majingina ya fadi. Allah ya jikan Bappah junaidu da malama Hindu. Ya Kuma raya musu yaran da suka bari, Ashir, Ashfeef , Nawraah da auta Amnah.

Sabon shafin rayuwa suka bude mai ban tausayi da ban tu’ajjabi….

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

39

:::::::::

:::

**Dawowar sa kenan daga bakin tashar motar unguwar su ta Naduka zone. Ya shiga gidah bakin sa dauke da sallama. A matukar gajiye yake baki daya jikin sa ciwo yake tamkar ana kwankwatsar kashin sa.

Ya bude parlorn ya shiga yana doka sallama. Amnah ce zaune akan kujera dauke da kofi a hannun ta.

Ta amsa sallamar tana murmushi. Kasancewar akwai shakuwa sosai tsakanin ta dashi. Kusan shi ya reneta tun tana zanin goyo har girman ta.

“Amnah nah”

“Hamma” Ta kira sunan sa tana murmushi.

“Sai ke kadai? Suna Ina?”

“Adda Nawraah ta na kitchen hamma Ashfeef kuma baya nan”

“Me kike sha ne baki rage mun ba?”

‘kunu ne Hamma. Gashi na rage maka” ta mika masa kofin

Ya girgiza kai yana komawa kusa da ita ya zauna yana kai hannun sa kan goshin ta,

“Ya jikin naki?”

“Da sauki hamma”

“Toh sannu kinji? Allah yabaki lafiya mai dorewa Amnah”

“Aamin Hamma”

Bakar ledar dake aljihun gefen rigar sa ya janyo ya sunceta. Yana dubanta yace,

“Kinci abinci?”

“Na koshi Hamma”

“Ah ai bazeyiwu ba. Jeki ce Adda nawrah tabaki plate. To zakici biredi?”

Nanma ta grigiza kai tana mikewa tsaye tace,

‘ga kunu nasha. Na koshi”

“Toh jeki kice ta baki plate”

Tayi hanyar kitchen zata kira Nawraah sai ga fitowar nawraahn “

“Ah hamma yaushe ka dawo?”

“Ba dadewa kenan na shigo. “

“Sannu da dawowa hamma. A kawo abinci?”

“Aa barbabincin nan cikina ya cushe ban dai ruwa kawai, ki taho da plate”

“Tohm Hamma”

Kitchen ta koma tana yan zikirinta labbannata na motsawa ahankali . Ta dakko plate da ruwa ta kawo masa ta durkusa ta mika masa ya karba,

“Allah ya shi miki albarka”

“Aamin Hamma. Wa iyyakum”

Ya karasa shan ruwan kenan sai ga shigar Ashfeef parlorn ya dawo daga filin ball.

Ya tsaya suka gaysa da Hamman na su sai Kuma ya wuce bandaki. Wanka yayi ya sauya kayan sa zuwa na gidah ya koma parlor ya zauna shima

Ashir ya nannade takardar naman ya zazzage naman akan tray. Ba wani mai yawa can bane. Amman yankan su nada girma ya debi manyan tsoka da yawa ya mikawa Amnah

‘kin dora akan abinci. A Zuba Miki ko da biredi zakici uhm?”

“Zanxi da bread”

“Yauwa Ashfeef Miko mata bread idan da akwai”

“Suaran sa kenan dazu na cinye Kafin na gama abinci wallahi.” Nawraah ta amsa shi tana langabar da Kai

‘okau ba damuwa Ashfeef huta ka karno bread anan shagon naga Yan majalisa fal dawowata dana aika Nawraah,

“Ah zan karbo Hamma. Ai ban gaji sosai ba”

“Rike ungo ban naka ne. Nawraah kema ungo naki.” Ya daddanka musu nasu kasan naman yana karkade hannun sa

“Hamma Kai fa?” Nawraah ta tambaye shi cike da tausayin sa

Ya girgiza kai yana kauda shi yace,

“Yana yankawa Ina ci. Kaki damu” ya bata amsa da haka

Sarai tasan bawani naman dayaci sanda ana yankawa. Wannan dabiar tasa ba zai taba sauyawaba. Kusan kullum hakane ke faruwa. Ko abinci ne bai Isa ba zai ce su cinye shi a koshe yake..

Ganin irin kallon da suke masa su ukun yasa ya kakaro murmushi don tabbatar da su yace,

“Gyaran wata mota mukai babba. Ta gyaru sosai shine mutumin da aka gyarawa dayazo karba yaji dadin gyaran sai yayi mana alkhairi”

“Allah sarki Hamma. Allah ya kara daga ku ya inganta ku”

“Aameen. Jam’an”

Ashfeef ya fita ya sayo biredi. Haka suka gaggand’a da abinci suka ci. Dare yaja suka kwanta..

Ashir na tsaye tsayin daka akan su. Kwata kwata baya samun hutu ko na minti. Kullum Yana aikin da zai rufawa kansa dana Yan uwan sa asiri.

Idan yaga ana gini zai cire kayan sa. Yaje ya musu lebura ya debo musu ruwa su biya shi ko bulo, Idan yaga gidan Mai yayi datti ya shiga ya share a biya shi.

Yaje gareji nanma yayi gyaran mota ya Kuma wanke ta a biya shi. Ahakan Kuma duk da haka idan fenti aikinsa ya taso yana zuwa yayi shi da Ashfeef

Ya yinda Nawraah ke kula da gidan tana dawainiya da kanwar ta su marar cikakkiyar lafiya wato Amnah…

Nawraah tana yin kitso akan mutane daya daya haka. Da haka suke hada yan kudaden su rufawa junan su asiri mashaa Allah…

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

40
Assalamu alaikum… HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me naira hamsin me naira dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka…

idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama

zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki..

kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin..

:::::::::

…. Suna zazzaune baki dayan su a parlorn su. Nawraah na koyawa Amnah karatun alqur’ani tana kara mata ayoyi biyu kamar ko da yaushe na daga surar da suke…

Domin Amnan kasancewar batada cikakkiyar lafiya. Kullum a kwance take. Hakan yasanya baa sata a makarantar ba tun da ran mahaifan su…

Ashir na zura yan ashirin ashirin da goma goma na dari takwas din daya samu awajen wankin mota. Yana ta cusa su acikin asusu yace taru zasuyi sosai da azumi sai afasa inshaa Allah ayiwa yaran kayan sallah da abincin sallah.

Ashfeef Kuma Yana gefe da yar wayar sa rakani Kashi a hannu Yana latsawa.

Bubbuga kofar gidan na su aka fara yi da karfi kamar zaa ballo kofar baki daya. Ashfeef ya mike ya fita .

mutane ne guda biyu suka zo acikin wata zungureriyar mota. Sun fakata a daidai kofar gidan tamkar zasu shigar da ita aciki saboda yadda tayi dab da dab motar da kofar shiga gidan.

Sallama yayi musu suka amsa masaa gayshe su yayi Yana bin su da kallon Karin bayani.

Manyan mutane ne Wanda kallo daya zakai musu kasan masu kudi ne.. dubada motar da suka zo da ita da kayan dake jikin su ma na manyan attajirai ne.

“Kai dan gidan marigayi junaidu me ko?”

“Eh Dan sa ne”

“Eh ga kamar Nan” daya daga ciki ya fada

“Kai ne babban Dan sa?”

“Aa akwai Hamma Yana ciki”

“Kira mana shi yanzu “

“Tohm. Amma su waye zaa ce?”

“Kache magana zaai da shi”

“Tohm” ya fada Yana komawa cikin gidan ya shiga Yana sallama suka amsa Ashir ya daga Kai Yana kallon sa yace

“Su waye?”

“Wasu ne gasunan da motar su. Suke tanbayan ni dan abbiey ne? Ni ne babban nace aa akwai Hamman mu shine sukace na Kira ka wai magana zasuyi da Kai”

“Toh Allah yasa lafiya” ya mike Yana gyara zaman rigar jikin sa

Fita yayi ya basu hannu sukayi musabaha ya gayshe da su bayan hannun da yabasu cike da girmamawa,

“Kai ne babban da ga marigayi junaidu ko?”

“Eh ni ne…”

“Mashaa Allah. To ya Karin hakurin mu?”

“Alhamdulillah da godia”

“Toh Allah ya gafarta masa”

“Allahumma Aameen”

“Sunana Alhaji Garbosai . Kuma ni munyi zaman mutinci da mahaifin ku. Ba sa’a na bane na kere shi a shekaru. Amman saboda ganin daraja da kimar sa ta mutane da mutanta kowa yasa aka zama tamkar Yan uwa. Wato abunda ya faru shine duk kuwa dai da anyi zancen ai lokacin rasuwar ko kan wani Yana binsa kudi akwai shedu ma da sheda ko?”

“Eh anyi haka”

“Toh mashaa Allah .. Ni ne Wanda ya bawa Marigayi junaidu kudade. Ya bada jinginar kadarar sa. Ya karbi kudi masu tarin yawa alokacin yazo mun da maganar rashin lafiyar yarinyar karama na daga cikin iyalin sa. Yazo cikin wani yanayi na tashin hankali da ban tausayi. Na debo kudin na bashi yace ba zasu Isa ba Amman ya gode. Na temaka dai na ranta masa kudi masu tarin yawa kimanin naira miliyan d….. Yace ga jinginar kadarar sa kaza ana kammala aikin asibutin yarinyar zai kawo kudin ya karbi takardun kadarar tasa… Lokacin daya diba har ya shude ma. Don magana ta Allah kudin Dana bashi ma yafi jinginar daya bayar tsada bama zaa taba hadawa ba. Amman dai na bashi saboda tausayi. Lokacin daua diba da mukai rubuce rubuce sheda ga sanda zai dawo dasu ya karbi takardun sa, ni Kuma daga baya na tafi Johannesburg wani uzuri ya taso mun….. To Kuma sai ake sanar mun da rasuwar sa. Shedu nama sun zo nan din sunyi magna. “

“Kwarai anyi haka sun zo. Kuma abbiey din tabbas ya dau dawainiyar kanwar mu da batada lafiya aka yiyyi mata aiki sosai…”

“Allahs sarki ya jikin nata?”

“Da sauki Alhamdulillahi… “

“To Allah yakara sauki Amin… Ga shedar faifan bidiyo da Wanda akayi a rubuce ma. Bari a dakko komai”

“Okay bari nasa a Kira bappan mu yayan mahaifin mu ne. Nan gaba kadanne gidan sa a compound daya muke”

“To shikenan ba matsala”

“Ashfeef”

“Naam Hamma”

“Dan kira Bappah Auwalu kace ana iso da shi muna tsaye da su”

“To shikenan”

Ashfeef ya zagaya ta kofar baya ya nufi gidan bappah ya gaya masa atare suka taho

Bappah Auwalu yasa aka dakko tabarma suka zazzauna sannan suka gaysa sosai.

Alhaji Garbosai ya dakko file da takardar shedar take. Ya Kuma budd wayar sa Yana kunna musu faifan bidiyo tar tar tar. Suka karasa kalla.

Ya bude paper nanma ga rubutun bappah junaidu nan ya saka hannu ya karbi kudi ya bada jinginar gidan sa da suke ciki kan idan ya samu kudin zai mayar karshen watan ya karbi kadarar sa ta gidan sa daya bda papers din ginin da komai da komai na court …..

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

41

:::::::::..

Suka kammala ganin komai. Jikin Ashir da Bappah Auwalu sukayi sanyi. Baki daya sun shiga cikin dimuwa.

Alhaji Garbosai ya ce da su,

“To kunga yadda komai ya kasance. Bayan lokacin daya diba ma bai kawo dinnan ba kasancewar halayen sa na kwarai yasa nayi tafiyata ma waje nasan ba damuwa ko da aka sanar mun rasuwar sa nace to shaidun suzo su Fadi akwai nauyi ko ince alkawarin a kansa dake bukatar saukewa. Amman abari na dawo ba damuwa kar a dimauta iyalan sa suna cikin alhini. Hakann kuwa akayi bayan na dawo na Kara bada lokaci Mai tsawo sosai sannan nazo yanzu. “

“Mashaa Allahu. To yanzu Alhaji akan me kazo kenan. Don yanzu sai abunda kace. Tunda Wanda kukayi maganar nan da Kai Allah ya karbu abunsa. Kuma bamuda masaaniyar komai akai”

“Hakane kam Allah ya gafarta masa. Magana daya ce zuwa biyu. Na farko dai idan da akwai kudaden abiyasu kawai acire dubu dari biyar din Kai na yafe wallahi. Akarbu takardun gidan nan. Idan Kuma babu to gaskia zai yi wuya a idan baa karbu gidan ba baki daya Ina nufin kadarar zata maye gurbin kudin da ya karba duk kuwa ma da sai yayi ciko amman na yafe”

“Mashaa Allahu Allah ya saka maka da alkhairi Amin. To yanzu Alhaji ba wata hanya ta daban da zaka bayar. Allah bamuda dalilin biyan ka kudaden daka ambata, Kuma bansan gidan nan nasu ya tafi don shi kadai suka mallaka gaba daya wallahi Alhaji”

“Sai dai muyi hakuri don wallahi a halin da ake ciki nima banida rufin asirin da zan iya hakura da kudaden nan Allah shine sheda”

“To Alhaji yanzu kamar shekara nawa zaa bayar don mu samu mu maido da kudin?”

“Ai bawan Allah baa cewa kawai. Dan wallahi kudaden nan kaga Dan uwana Nan. Rabi nasa ne rabi nawa. Daga baya na bukaci kudin ya ranta mun rabin. Don haka wallahi dama da an biya kudaden Nan to shi zan basa don nasa ne. Haka zalika idan kudin bai samu ba. To lalle wannan gidan zai zama mallakin sa. Sai dai kuyi hakuri. Batun Kara baku lokaci wallahi an baku Kuma Kun sani”

“Munsani ranka ya dade Dan Allah kayi hakuri ni yayan mahaifin su ne. Da Marigayi junaidu da ni uwar mu daya uban mu daya ranka ya dade. Bamu da kadarar da zamu maye gurbin kudaden da kake bi. Kuma wallahi bamaso gidan nan ya salwanta agrare mu. “

“Kuyi hakuri don wallah an Kara muku lokaci an rage kudin ma. shima Kuma Yana bukatar gidan wallahi. Kuyi hakuri”

“To Alhaji kamar yaushe zasu bar gidan kenan? Don nagaya maka shine rufin ashirin su damu baki daya”

“Gaskia gaskia karshen gaskia daga wannan satin da zamu shiga shine karshen kuyi hakuri”

Ashir ya mike da sauri Yana dafe bango Bai jira Mai zasu sake cewa ba ya bi bango Yana dafe dashi ya koma cikin gidah bandaki ya shige cikin sa ya kada saboda tsabar tashin hankali Nan da Nan kuya yafara zawo kamad ruwa..

Daga karshe bappah ne yaji musu sallama suka ja motar suka tafi shi kuma ya shiga cikin gidan inda ya tarar Ashir din a kwance akan kujera ya rufe fuskar sa da littafi.

Jikin yaran duk a sanyaye suna jiyo komai tun dazu da fari har aka kammala. da kawu Auwalu ya rakazu, kowanne fuskar sa duake da damuwa.

Ya dan kwantar musu da hankali ya musu sallama shima ya koma gidan sa dauke da damuwa. Dik kowane danuwan su ya kira su ko zasu temaka kowanne yace bashi da hali. Don bakin ciki har kuka yayi bappah Auwalu.

Haka Kwanakin sukayi ta ja. Mutanen Alhaji Garbosai sai zuwa suke suna bin notice, Ashir yaje gwangwan ya Kira masu saye suka sayi kayan kallon su da firjin su da katifar dakin mahaifan su da suka rasu da drawer su nawrah da kujeru Banda babba daya 3 sitter baki daya ya sayar da komai harda labulaye sai biyu ya rage. Komai da komai ya sayar , Amman kudin da suka samu kwantan kwatan kwantan kwatankwacin rabin rabin rabin rabin abunda ake bi basu hada ba. Haka ya hakura ya sanya kudin a asusu kawai gab daya.

Ranar wata talata da safe kanin Alhaji Garbosai yazo yace lalls su tashi su zubar masa gidah na zuwa da yamma. Suka karasa komai nasu tun da safe Ashir ya zuciya suka fita daga gidan

Bappah Auwalu ya ce suje gidan su. Su koma gidan sa baki daya da zama shi bai wulakanta yayan Yan uwan sa ba. …… Ya kwankwasa

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

42

:::::

°°°°°

Ya sake kai hannun sa ya kwankwasa a karo na biyu. Yana riko hannun Amnah acikin nasa.

Nusaiba dake zaune a kujera taja tsaki ta mike tana mita,

“Auwalu kenan. Kawai saboda kasan yanzu Ina hutawa ne. Zaka dinga wani bugo kofa don na tashi lalle na bude? To gaskia ba komai agidan gwara ka shigo mana da biredi ka koma Layla ta kwanta Kuma na san yunwa ce. ” Ta fada tana bubbuga kofar itama

Bappah Auwalu yaja tsaki cike da takaici yace,

“Bude mana. Ba ni kadai bane”

Nusaiba ta gyara zaman dankwalin ta. Ta dauka bako yayi ko zai basu dan kudi su samu suyi abinci.

Ta gudu ta shiga dakin Layla ta tasota,

“Tashi dan uban ki. Inaga mutumin rannan abokin baban ku ne yazo. Je parlor ki zauna idan kin gayshe shima karki tashi nasan idan suka gama hirar su kamar rannan. Zai baki ko yar dubu biyu ce”

Layla ta tashi tana murza idanu saboda baccin dake kanta tashiga bandaki ta dauraye bakin ta,

“Ba Zaki sauri ba. Wane irin wulakanci ne?”

“Umma yanzu zan tafi ai”

Nusaiba ta zauna a kujera. Alokacin bappah Auwalu ya cika yayi fam. Layla ta saka hannu ta bude kofar tana cewa,

“Ina wuni?”

“Lafiya. Ke Kuma wa kika dauka? Akace kinyi bacci. ? Nusaiba wane irin wulakanci ne wannan tun dazu saboda Allah nake cewa ki bude mana Amman shine kika ki sai da kika taso ta tazo ta bude. Wato ban Isa kizo ki bude mana kofar ba kenan ba ko?” Bappah Auwalu ya karasa fada yana jan tsaki.”

Nusaiba ta mike har tana ball da kofin ruwa agabanta tana mai nuni da su Ashfeef da kowanne ke rike da akwatin sa a hannu tace,

“Bangane ba. Wadannan nan Ina zasu? Wanne bappanin ne ya amince ya rike su? Bappah salisu ko sani ko kuwa Gwaggo Aminatu ce? Ko gidan aikatau dinne suka ce zasu karbe su?”

Tsaki yaja dogo yana nuni da yan kujerun parlorn na su yace

“Ku zauna Nawrah”

“Ka wayar mun da Kai mana Auwalu. Ga ka ga yara rabe rabe kowanne da kayan akwatin sa dashi. Shin wani gidan suka sauya da yafi wannan? Hmm to Auwalu ai gwara Kai ma kasan abunda ke maka ciwo kullum jiya iya yau. Sai dai kache wanin ka. Ba zaka tashi ka nemi na kanka ba.”

Bappah Auwalu ya grigiza Kai Yana yatsina fuska yace,

“Dan Allah ya isheki haka. Yi shiru. Haba sai magana kiketa ratattakawa. Meye haka eh? Haba banason irin wadannan abubuwan wallahi ,yara dan kin gansu acikin gidan nan ai yaya nane suma ko kin ki ko kin so inda kara kema ai baki ne. Bayaga haka. Tun ba yau na gaya miki. Ba Kuma wai amincewar ki ko kin amincewar ki zan bi ba. Wadannan Yara da uban su da ni uwar mu daya uban mu daya. Don haka na dawo dasu gidah na da zama baki daya har zuwa sanda Allah zai warware mana matsalolin mu.”

Nusaiba ta saka hannu a baki taja guda tana watsa hannu sama cike da bakar masifa tace

“Ah lalle. Nace mekace a karshen zancen ka! Ka san ba kasafai maganganun ka suke ratsa kunne na ba”

“Nace Yara sun dawo gidan nan. Ba na neman amincewar ki ko kin amincewar ki”

“Kan babban balastin. A wannan kungun gidan Mai kama da ramin cinnaka zaka ce zamu zauna da yara zagada zagada har hudu? Wallahi summa tallahi bazan yarda ba. Bazan amince ba. Wallahi kaji rantsuwar musulmai kenan.”

“Gidan ki ko nawa? Ni Kuma nace yara sun dawo nan gidan da zama kiyi abunda Zaki. Ku zauna Ashir bari a kawo muku ruwa”

Kitchen ya nufa. Nusaiba tabi bayan sa tana ife ife tamkar zata rusa gidan hannunta daya akan kofar kitchen tana kwaso rantsuwa tana bubbuga hannunta cike da tsantsar masifa tace…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

43

:::::::::

“Wallahi summa tallahi yaran nan bazasu dawo mun gidah da zama ba. Aina zasu zauna rai hudu? Zagada zagada, dakuna biyu ne kawai jallin jal. Daya muna ciki. Daya Layla . Ahmad kuwa a parlor yake kwana saboda babu wajen kwana. To akan mu kakeson wannan rai hudun sun kwana ko meye? Sannan munada halin ciyar dasu ne eh? Muma da Yaya muke samun abincin da zamu saka acikin mu hudu ballantana ka karo rai hudu? Kanzo zaa jika a basu ko menene? Duk acikin Yan uwan ka Kai ne koma baya. Kowanne yafi ka hali nesa ba kusa ba. Amman sika kekashe idanun su. Suka bada musu kasa kowanne yace shi ba zai iya daukar su ba da dawainiyar su saboda halin rayuwa. Amman sai Kai uban dan sarkin son birgewa ba kada ko sisi kana tafe tamkar iska zata hure ka saboda yunwa har Kaine zaka je ka jajibi mana rayuka uku saboda San asani da nuna birgewa aljihu ba ko sisi. To narantse da Allah bazan rike yaro ko daya ba. Kuma babu yaron da zai zauna mun agidah. Wallahi” nusaiba ta fada tana kururuwa tamkar zata hau kansa da duka.

Bappah Auwalu da maganganunta duk sun cika shi ga kunya daya dabaibaye shi yadda take gasa masa magana agaban yayan sa na cikin sa. Duk da sun saba ji su da su nawrah din Amman dai da kunya. Don haukanta na ranar yafi na ko yaushe…

Hannunta Yaja ya shigar da ita ciki ya rufe da mukulli. Suka shiga fadan kache nache tamkar zasu cinye juna don masifa musanman nusaiba dake masa tsiwa tamkar zata rufe shi da duka

“Hamma daman su bappah ca sukai suma na zasu rike mu ba kenan?” Ashfeef ya tambaye Hamma Ashir da kansa ke a sunkuye idanun sa sun kada sunyi jazir

“Hamma wai hakane? Su bappah fa da Gwaggo Aminatu ko ba ka sani ba Hamma?”

Ashir ya saka hannu ya goge hawayen dake zuba a Idon sa Yana Jan majina. Sam bai gayawa Yan uwan nasa bappanin su sinki daukar su ba saboda bayasan suji haushin su saboda zumunci. Amman tunda sun rigada sunji da kunnen su yanzu. Bashida wani dabarar da zai ce baai haka ba. Don idan ya karyata ma yayi kuskure don haka ya kada yai Yana sharce idanun nasa yace

“Abune ya fadamun a idanu na. Anyi haka. Amma ba da wani abu suka fada ba. Kunsan rayuwar yanzu tayi tsada ne gashi muna da yawa. Ku tashi mu tafi. Yan kudaden nan da aka sayarwa gwangwan kayan mu ya Isa mu kama ko da dakine da parlor awani wajen mu koma. ” Mikewa yayi Yana goya jakar Amnah a bayan sa.

Suna shirin buda kofa su fita sai jin muryar bappah Auwalu ya kira sunayen su daya bayan daya,

“Ashir Ashfeef, Nawraah, Amnah Ina zuwa ? Ku dawo ku zauna mana ga ruwan”

“Ai bappah daka basshi wallahi. Zamu je inda zamu samu wajen kwana ne Kafin mu nemi wuri sosai akwai kudin awaje na”

“Ah karmuyi haka da ku ahsir Dan Allah. Kada ku bari maganganun wannan sakaryar suyi muku tasiri a kwakwalen ku gidah dai nawane don haka nike da iko da gadara akan sa. “

“Ita nusaiba da Layla su kwanta akatifa daya. A dakko babbar katifar can dakin a sakata aciki Nawraah da Amnah su kwana tare da su. Dakin Layla Kuma sai Kai da Ashfeef da Ahmad kub dinga kwana aciki. Ni kaga kujerar nan ta bayan ka ta ishenuli daman wani lokacin ma akanta nake kwanciya har safe iska parlorn ga dadin bacci”.

Ashir yayi murmushi yana grigiza Kai yace,

“Dan Allah kayi hakuri bappah Amman wallahi bazan iya dawowa gidan nan da zama ba tabbas gaskiyar Aunty yayi mana kadan”

“Yauwa Ashir kaji yace gaskiyar ta. Yo mu kanmu Ina gidan nan zai dauke mu bakidayan mu”

“Zan mugun saba miki nusaiba Allah kuwa. Ashir….

Kafin bappah Auwalu ya karasa maganar dazai Ashir ya katse shi ta hanyar zube gwaiwoyin sa akassa yace,

“Dan Allah kayi hakuri bappah. Ka dubi girman Allah ka saurari abunda Zan fada. Kuma dan Allah ka amince da abunda Zan fada din. “

“Inasauraron ka Ashir”

“Bappsh gidan nan wallahi ba zai dauke mu ba yayi kadan wallahi Anty tayi gaskia. Na biyu dama wallahi bada niyyar zaman agidan nan muka biyo ka ba yau din. Dama akwai tsare tsare. Da nake akai na.kayi hakuri yau din na amince akan dare yaja zamu kwana anan, Amman daga gobe inshaa Allah ba zamu sake kwana ba. Zamu samu waje kusaa da nan din. Idan Allah ya amince na mun samu kudaden da zamu biya wancen mutumin shikenan sai mu karbi gidan bappah mu biya shi. Dan Allah karma ka ki amincewa bappah. Idan kaki amincewa akwai matsala. Dan Allah Kai ne mahaifin mu albarkar ka muke nema” ya rike kafafun bappah Auwalu ya faraa hawaye dumin su na diga a kafar bappah Auwalu.

Sunkuyawa bappa Auwalun yayi ya riko hannuwan Ashir yace dashi,

“Shikenan na amince Ashir. Amman sai idan inda aka samu din anan zagayen layin yake ko nan yankin idan baa samu ba to gaskia ban amince ba. Haka zaku dawo nan mu cigaba da rayuwa tare watarana ma duk mutuwa zamuyi ashir. Dan Allah Nima Ina rokon wannan alfarmar kaji?”

“Shikenan bappah. Na amince”

“Yauwa ko kaifa Allah yayi muku albarka kaji? “

“Aaameen bappah wa iyyakum”

Nusaiba sai Harare hararare take bappah Auwalu yasa ta dakko zannuwan gado Ashir da su Ahmad sukayi shimfida a parlor suka kwanta.

Nawrah da Amnah da Layla Kuma suka kwanta a adakin layla. A haka sukayi bacci kowanne da abunda zuciyar sa ke saka masa….

Ashir da asubah ya futa tunda akayi sallah Bai dawo gidah ba. Ya sayi biredi wajen takwas na safe da madara da sukari ya Kai musu duka gidan suka ci

Nan ya shiga neman gidan haya kain dana in anan yankin.. Amma Allah cikin ikon sa baa dace ba. Gashi Ashir bayason ketare maganar manya don haka ya cewa bappah baa samu ba . Ya Kuma nemi gafarar sa daya barsu su nema a unguwar kusa da su. Bappah Auwalu yace sai nan gaba amman ba yanzu ba.

Tunda nusaiba ta jiyo su ta fara hauka kamar sabuwar tabi. Har da fashe fashe na kofuna tana nanawa kanta wuka zata kashe kanta kan lalle Auwalu ya zabi daya ko ita ko su.

Ganin haka yasa Ashir yace da kannen nasa su tashi su dakko kayan su duka suka fito. Bappah Auwalu ya biyo su Yana hawaye,

“Dan Allah Ashir karku yanke mana zumuntar mu ku nake kalla naga kamar junaidu don Allah . Kayi hakuri ka janye maganar ka ni ku na zaba ba ita ba. Ita tamkar riga ce da zan cire na sako wata haka take awaje na. Aurota nayi ,Dan haka iya rabuwa da ita na auro wata ku kuwa Yaya na ne bazan iya taba yanke zumuntar mu ba har gaban abadan. Jini ya wuce gaban komai”

Ashir Ya goge hawayen sa Yana rasa Mai zace Duk suna tsaye cirko cirko da akwatinan su a hannu…

‘K’J
(M/W/S)

✍️:MX

44

:::::::::

Zamu iya kwana nan Bappah…” Ashir ya fada yana nuni da dan dakin da Bappan su ya bawa nusaiba take zuba kiwon ta . Tamkar akurkin kaji.

‘ah haba ahsir. Ya za’ai rai na dan Adam ya iya zama nan? Ai ba zeyiwu ba”

“Allah Bappah zai yiwu. Zamu zauna har ya zuwa sanda zaa samu dan waje na kamawa anan yankin. Idan har zuwa nan da yan lokacin dana bari ya cika bamu samu ba. To kayi hakuri ko da awani unguwar ne zamu kana waje mu koma. Kuma zumuncin mu har aljanna inshaa Allah. Haka na dai yanke bappah .. Daurewa zai ayi”

“Ashir ka kalli dakin nan kuwa.”

Nusaiba dake binsu dadi fam ranta ta nufesu tana murmushi,

“Kalau daki yake. Tumakan kawai zaa janye. Kajin Kuma a mayar da kejin su gefen can haka daga ciki ai yayi”

Bappah Auwalu ji yake tamkar ya Kai mata gula aciki ya hanbare ta baki daya. Cike da takaici yace,

“Bar nan nusaiba”

“Naje Ina? Ko ka manta mallaki na ne nan din? Ai na wa ne”

“Mahaifin su ne dai ya baki kada ki manta. Ke butuluce wallahi Allah”

“To daya banu yanzun ai nawa ne ko na baka ta rabaka da kayan ka. Allah na tuba nan din dan ya bani har wani abun birgewa ne…

“Da kata anty.ya isa hakaa. Kada ki tabo abbiey ko ummy. Maganar ta tsaya akan mu please.” Ashir ya katseta Yana kada Kai.

Bappah Auwalu ya juya ya dankara mata harara,

“Ai ga irin ta Nmnan” ya fada Yana Jan dogon tsaki ya dubi Ashir yace,

“Amma da sharadin zaayi gyara sosai acikin sa da sauran su. Don daii ka hadamu da babban bango ne kace Allah bazan iya musu ba. Amman kasani har cikin raina banji dadin kasancewar ku anan dakin ba wallahi Allah ne sheda. Dakinda ake saka kiwon tumaki da kaji daa harda zomaye ma ace dan Adam ne zasu kwana acikin sa?”

“Bakomai bappah Allah. Mungode hakan ma ta mana kokarin”

“Kokarin me bayan mahaifin ku nema ya bata ba wai kudi ta saka ta saya ba”

“Kuma dai ai ba roka nayi ba da zaka ce haka. Allah na tuba dakin da kiwon da duk mutuwa suka dinga y kamar an canfa shi. Ni dai ga daki nan nace su zauna aciki ba Kuma kyauta na bayar ba ban amince Kuma ayi wani fàshe fashe ko gine gine acikin sa ba batare da izini na ba gaskia. “

Tana gama magana ta koma ciki kamar Zata tashi garin,

“Kifi ruwa gudu ma nusaiba. Aikin kawai” bappah Auwalu ya fada Yana hararo bayanta data tafi

Ashir yayi gaba Yan uwan na biye da shi abaya aka bude dakin. Ba lefi Yana da Dan girman sa. Sai dai kofa ce kawai babu window a dakin. Sai kashin tumaki Dana kaji da kazanta dai sosai.

Ashir ya kade hannunsa yana duban nawrah yace,

“Muje keda Amnah . Idan muka gama zamu kira ku. Sai anyi gyara sosai”

“Hamma zan tayaku”..

“Aa jeki zauna da amnah”

“Toh shikenan Hamma Allah ya bada sa’a”

“Aamin”

Tafiya tayi … Ashir da Ashfeef da Ahmad da b. Auwalun suka fara kaude kauden kayan wajen zasu gyara nusaiba ta leko tana kiran Ahmad.

Tunda ta kiraa shi bappah Auwalu ya girgiza kai kawai don ya tabbatar Kiran sa tayi ta hana shi aikin.

Ai kuwa suna fita ta rufe shi da fada,

“Dan uban ka a wannan kurar,wannan shekararren akurkin dakin da ba bil adama ke kwana aciki ba kaje ka baje hanci kana tayasu aiki. Wuce muje gidah. Kuma wallahi ka sake ka fito sai na ci haka kaza ta uban ka”

“Kai umma”

“Zakaa wuce ko sai na sharara maka Mari”

Ciki ya nufa,Yana kananun mita. Ta shiga ta rufe kofar harda mukulli ganin haka yasa nawrah rike hannun Amnah suka koma can gefen famfo suka zauna.

Sannu ahankali suka fara gyara dakin suka wanke shi. Ya bushe suka saka katifun da suka rage akayan da basu sayar ba.

Suka raba dakin biyu da labule. Rabi daya na Ashir da Ashfeef. Dayan Kuma Nawrah da Amnah sai yama tamkar ciki da parlor don sai ka daga labulen zaka Isa wajen su Amnan.

Suka jajjera Yan abubuwan su da suka taho dasu. Suka jinginar da akwatunan su a gefe .

Ashir ya kunna karatun alqur’ani awayar ummyn su dake wajen sa tun da suka fara aikin har safiya sai da wayar ta kare karaf sannan ya kashe…

Haka rayuwar tasu ta cigaba da garawa. Da safe zai sayo biredi ya Kai gidan bappah auwalu suci gaba daya. Da Rana ma Dan kudin da suka samu da Ashfeef zasu auno taliya yar aune ko shinkafa su bawa nusaiba ta dafa…

Dare ya zama safjya, safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci yammaci ya koma dare lalle Allah buwayi ne gagara misali.


Zaune suke baki daya a parlorn su bappah Auwalu wasu a akasan kujera wasu Kuma akan kujerar.

Tun ba su yarda suna zuwa ba. Har dai suka saba saboda takurawar da bappan nasu yake musu kan lalle su je su zauna ayi hira.

Duk abunda ake cewa nusaiba sai dai
ta yamutsa fuska. Tana jinsu. Sai data mula ta sha iska tace…

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

45

:::::::::

::::

“Rayuwar nan da muke gaskia ba zata yiwu ba … Haka zamu cigaba da tafiya kwan gaba Kwan baya shi kenan mu kowa Yana ci gaba amman mu rayuwar mu na sake tabarbarewa. Haba ga nauyi ya sake hawa kan mu. Wutar nepa ma yau da yan nepa suka zo baku ga rokon dana dinga musu ba kar su yanke” Ta karasa fada tana hararo Ashir dake gefe yana jan carbin dake hannun sa.

Bappah Auwalu na hankalce da ita sai da ya bari ta Kai karshe sannan yace,

“Me kike nufi kenan? Duk kokarin nan da yaran nan suke bakya gani kenan? Allah ya jikan Hindu da rahama ba futa take tana aikatau ba tana nemowa iyalin ta? Ke meya hana ki tashi ki nemo Kya dinga biyan nepar ai dake akeshan wutan kusan kinfi kowa amfana da wutar ma. Kullu yaumin wayar ki na makale a socket”

“Lalle ma Auwalu. Ku ba kune mazan ba. Itama Hindu ai junaidu Allah ya jikan rai ba zaman banza yake ba ya tashi tsaya yana nemowa iyalin sa abinci. Kai bakaji kunyar amsar da ka bani ba saboda Allah ? Ai ko a musulunce ca akai uba ya nemo ya kawo. Kuma kaine mijin ba ni ce mijin ba. Don haka kai zaka nemo bani ba. “

“Ni ma ai ba a zaune nake ba haka kawai. Ina tashi Ina nemowa iyakacin karfi na. Wutar ai ba dole bace a yanke ta”

“To ai kuwa ba zai yiwuwa ba ne. Da maza zagada zagada kamar Ashir ace zaa yanke mana wuta. “

“Kinata famfamin magana shin acikin gidan nan suke a zaune? Yaran da duk kwanan Allah sai ya kawo biredi da safe da kayan shayi baya gajiyawa da rana kuma shi da Ashfeef su hada kudi su kawo taliya ko shinkafa ko garin tuwo ayi ajiya kika basu? Ko sassaka su kikayi? Haba dan Allah ki dinga magana kina aunawa a mizanin hankali da tunani mana. Yaran nan dakin da suke ma babu wuta baa jawa dakin wuta ba haka sike kwana sike tashi chajin waya sai dai su kai wajen chaji saboda masifa irin taki. Kai Kai Kai Nusaiba Allah ya kyauta “

“To ai gaskia ne. Tunda dai da su ake girkawa aci ai dole su kawo nasu tagomashin. Maganar wuta ma kuwa ai sukan kawo nan din a saka musu. To bayaga haka ma ai arziki suke ci s…

“Ya Isa haka dakata nan. Ke wataran dama idan kika fara magana wallahi ko Amnah ba zatayi ban sam ba Kai. Arzikin me suke ci? Yadda Ahmad yake anan gidan haka suma suke. Wadannan yaran arzikin su muke ce, Domin mahaifin su abubuwan da yayi mun har na koma ga Allah ba zan dai na godiya da neman rahamar Allah agare shi ba. Badan junaidu ba da yanzu kwanon gidan nan ya rufta. Ba dan junaidu ba da yanzu kofofin gidan nan sai dai ajingine su. Badan junaidu ba da kowacce damanina sai mun fitar da kayan gidan nan saboda ruwa sai ya cinye komai. Ke ba dan junaidu ba wallahi da ni Auwalu ba zan samu matsugunin zama a Naduka ba bari kiji Ina gaya miki tunda naga ke manta alkhairi ne da ke. Alkhairan da marigayin nan ya mun wallahi ko iyayena sai haka. Don haka arzikin mahaifin su muke ci don kuwa fata nake Allah ya hore. Mun na biya kudin da ya ranto mun nayi gyaran gidan nan da shi. Nayi tambayar nayi cikiyar nayi nayi nayi tun da rasuwar tasa har bayan rasuwar sa dik wanda na tambaya sai yace junaidu bai ranci kudi kimanin haka wajen sa ba. Na gama tabbatarwa na sa ne ya bani kamar yadda da fari yace ba rance yabaniba naki. Don haka sai ya ce mun to ranto mun yayi din amman na bayar a duk sanda na samu babu takura …. Saboda haka dana samu kudi Allah kudin junaidu zan bawa iyalin sa gasunan arzikin su muke ci wallahi. Har gobe “

Nusaiba taja tsaki tana karkada kafa tace,

“Ni dai na gama magana ai, dole kowanne ya sake zage dantse ya nemo abincin da zaa ci da kudi. Nawraah ki duba acikin gidajen aikin da marigayiya Hindu tayi aikatu kema ki samu inda zakuyi mu rage wasu abun”

“Wace nawrahn Anty? Nawraah karatu zata cigaba…. Gaskia ba zatayi aikatau ba” Ashir ya fada yana kada Kai cikin tabbatarwa.

Bappah Auwalu ya dubeta ya zabga mata harara cike da takaici da yaki kololuwar mizani yace….

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX).

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

46

:::::::::

:::::

“Nusaiba dan Allah tashi ki bar nan wajen. Don wallahi yadda zuciyata ke tafarfasa ta ke kuna akan maganganun ki da girman Allah zan iya hanbare ki na sumar da Ke yanzu…”

“Ni dai na gama magana…. Idan Kuma baa daiku mataki ba zan dauka da Kai na”.

Mtsceww…” Allah wadaran hali irin na ki nusaiba” bappah Auwalu ya fada Yana grigiza Kai

“Aa karka sake tanka ni wallahi. Magana ce ta gaskia nayi. ” Ta shiga daki ta dakko pillow ta dora akan kujera,

“Ka kwana a parlor banason hayaniya yau” Ta shige daki ta bugo kofa tana murza mata mukulli.

Yaran duk suna saukar da idanun su kasa. Kunya ta dabaibaye shi. Nusaiba ta gama renashi yarasa yadda zai yi da ita.

Ashir ya mike yana kara waya a kunnen sa ya fice. Ashfeef ma yabu bayan sa. Can daga baya Nawraah ta ja hannun Amnah sukayiwa bappan sai da safe suka fita.

Dakin su suka koma. Ashir yasa suka dakko katifar su shida Ashfeef suka shimfida awaje saboda zafi sika nada net. Sai aka yaye labulen su Nawraah su kuma saboda iska ta dinga shigar musu. ..

Haka suka cigaba da rayuwar su gwanin ban tausayi. Lalle iyaye bango ne kuma fukafukai ne dake lullube yaran su

Wai yau yayan bappah junaidu ne da malama Hindu suke kwana a dakin ajiyar tumaki da kaji. Ba wuta a dakin ba bandaki. Ba wajen girki da ga su sai yan kayan su gwanin ban tausayi. Ko window babu a dakin, Wata iriyar rayuwa sukeyi, Mai ban tu’ajjabi Wanda dole Mai Imani sai ya tausaya musu da hawayen tausayi .

Amman duk da haka basu karaya ba. Ashir zai fita tasha da safe yayi lodi yana saka matafiya a mota. Kuma Yana zuwa wajen wanke mota dake tsallaken tashar nanma yana taya maaikatan wajen wanke mota suna bashi dan wani abun…

Sannan duk inda ake gini zai shiga ya musu leburanci ya daukar musu bulo ya ebo musu ruwa idan suka bukata ya kwashe baraguzai na gini…

Sannan idan sun samu aikin yin fenti na wani gidan ko wata ma’aikatar suna zuwa suyi shi da Ashfeef. Ta haka suke samu su rufawa junan su asiri.

Ashir na tsaye tsayin daka akan yan uwan nasa. Duk dai burin sa bai wuce ya wayi gari yaga farin ciki lullube a fuskokin yan uwan nasa ba shakikai da suke uwa daya uba daya ..

Ahakan Kuma kullum sai Ashir ya sayo biredi da kudin daya samu ya Kai wa nusaiba sunyi karyawar safe dashi kullum ba gajiyawa wata rana harda madara ma Yana hadawa idan ya samu faraaga… Idan Bai samu ba Kuma Yana sayo biredi da sukari da lipton daya, su sha ruwan bunu.

Amman duk da wannan wahalhalin buga bugar da suke suna kawo cefane ana abinci. Nusaiba Bata gani idan Bata ga dama bama sai tace abincin ya kare ko tace ya kone ta zubar ta hanasu abinci ta bawa yaranta kadai..

°°°°°

Ashir da Ashfeef a yanzu sun dawo kwanan waje gaba daya sun barwa su Nawraah dakin. Net suke kafawa su saka katifa su kwanta.

Da rana kuma su dan zauna suyi hira ko suyi karatu Ashir Yana kara musu duk asubah. Da safe Kuma Nawraah ta koyawa Amnah dai dai hizb din da take.

Ashir ya kurbi ruwan dake cikin kofi Yana duban Nawraah dake kalabewa Amnah Kai yace,

“Ina takardar makarantar da kika samu? Dakko mun muga”

“Hamma kakka damu wallahi ni baki daya karatu yabar Kai na. Allah kuwa”

“Banason musu dakko mun. Akwai lissafin da nake acikin Kai na”

“Tohm Hamma Yi hakuri”

mikewa tayi ta nufi akwatinta ta daga kayanta daga can kasa ta zaro paper ta Mika masa da hannu biyu ya karba yana karantawa…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX).

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

47

:::::::::

:::

“First choice Jami’ar Al-Haramein Naduka mai zaman kanta da ke Naduka crescent (apple island) dinnan? Second choice jami’ar gwamnatim tarayya ta Naduka dake baya, Third choice Kuma makarantar polytechnic ta koyan jinya ta cikin babban asibitin na Naduka.. mashaa Allah. Allahumma barik”

“Nagode sosai Hamma. Amma dagaske ni banason zuwa wata jamiaa Allah kuwa”

“Kede kita addua Nawraah. Da yardar Allah Zaki karatu a jami’ar nan ta farko kamar yayan kowa. Inshaa Allah Zaki karatu Nawraah. Burin ki da kokarin ki ba zasu salwanta ba inshaa Allah. Fatana dai Allah ya shige mana gaba ya zama gatan mu a dukkanin lamuran mu Allahumma Aameen”

“Aameen Aameen Hamma.”

“Aameen Hamma. Allah ya amince” Ashfeef ma ya amsa.

“Eh abunda nake so dake kawai ki cigaba da addua kuma inshaa Allah muna tayaku . Kowane tsanani Yana tare da sauki Nawraah komai daren dadewa. Rayuwar biyu shi akwai gidan duniya da lahira. Allah ba zai bar mu haka ba. Inshaa Allah wannan kaddarar tamu sai ta zama tarihi agaba Nawraah. Ki rubuta ki ajiye. Ko da rai yayi halin sa Nawraah ba zaku wulakan ta ba ni na sani. Ina Kuma da hope akan ki kinji ko?”

“Ina sauraron ka Hamma. Amma ka dena fadan haka don Allah Ina jin wani iri Hamma. Inshaa Allah dukkanin mu zamu rayu har ya zuwa lokacin da zamu samu sauki acikin wannan matsatsi da muke ciki. Zakayi aure ka hayayyafa ka tara iyalin da yawa Kai ma Hamma”

Murmushi yayi Yana kada Kai yace,

“Ba Wanda yasan gobe sai Allah Nawraah. Kuma dan ku ai ba zaa barni ba. Hakama dan ni ai ba zaa bar ku ba. Kawai dai Ina magana ta ne. Zance ne ya shigo cikin zance. Kita addua kede kada ki karaya. Inshaa Allah sai kin zama cikakkiyar babbar maaikaciyar a fadin kasarar nan sai an dinga kwatance dake ana yaban kyawawan halayen ki da temakawa mabukata da Zaki dingayi masu karamin karfi. Hakama Ashfeef Kai ma Allah zai cika maka naka burin ka zama babban dan ball Wanda kasa da ketare zasu yi alfahari da kasancewar sa gwarzo jajirtacce. Sai kayi fice ana nuna ka sai kere su messi su Ronaldo inshaa Allahu. “

“Hamma ni fa?”

Amnah ta tambaye shi tana mitstsika idanu zatai kuka. Duk ta sake ramewa gwanin ban tausayi daman ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba kullum a kwance. Itama har biscuits da cheese balls Ashir ya saya mata ya ajiye ake bata kullum . Ashfeef Kuma ya saya mata bobo guda goma shima tana sha sosai.

Ashir ya riko hannunta ya taso da ita ya zaunar da ita akan cinyar sa. Ya saka hannunsa yana tallabo habarta yace,

“Ke?…. Amnah ta ai ke babbar maaikaciyar lafiya zaai. Babbar likita Zaki zama inshaa Allah ki dinga temakwa marasa lafiya kina basu kulawa ta musanman cike da tausayin su da kyautata musu kinji.? Allah ya muku albarka gaba daya Allah ya tsare gaban ku da bayan ku Allah ya shiga lamuran ku ya iya muku a dukkanin komai. Allah Kuma ya kare ku daga sharrin masu sharri. Allah ya muku katangar karfe da azzalumai. Allah ya daga darajar ku duniya tasan muhimmanci ku, Ta Kuma yi alfahari da kasancewar ku acikin, Al’ummar ta. “

“Aameen Hamma, Amma dan Allah ka dena irin wannan maganganun” Nawraah tace dashi tana hawaye sosai.

Bude baki yayi Yana murmushi ya dubi Ashfeef yace,

“Kaga? Jaruma ce fa ke Nawraah bansan ki da laushi ba. Banason wannan emotional yanayin naki Allah. Ki jajirce ki tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata. I count all my hopes n you Nawraah. Ke din KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA….”

“Ai kuwa dai Hamma gaya mata. Wannan idan ta fara kuka samari da alama kowanne sai ya sakata kuka Allah kuwa. ” Ashfeef ya fada Yana Kai mata rankwashi ta goce tana dariya.

Suka saka dariya baki daya ciki harda Amnah dake kyakyatawa. Ashir ya dube su daya bayan daya Yana goge hawayen fuskar sa dake tsiyaya yace,

‘haka nake son ku kasance ko da yaushe cikin farin ciki . Da dariya dauke a fuskokin ku. Allah ya dawwamar daku cikin farin ciki ya yaye muku dukkanin damuwa ya nisanta ku da damuwar dake cin ku ya lullube ku da rahamar sa allahumma Aameen”

“Aameen Hamma tare da Kai.”

“Eh mana hamma ka dena cire kanka dan Allah”

Murmushi yayi Yana gyara Kai yace,

“Ai idan kuka kasance cikin farin ciki ku kadai ma ya wadatar. Ni kune nawa farin cikin. Farin cikin ku shine nawa, ganin ku cikin farin ciki shi ke faranta rai na da zuciyata da gangar jiki na. Yan uwana, Ashfeef , Nawraah da Amnah kune farin cikina,. Da ke sanyaya ya Kuma lullube zuciya da ran Hamman ku Ashir a Koda yaushe. Allah ya jikan iyayen mu da rahama Allah ya gafarta musu Allah yasa aljanna makoma ce agare su”

“Allahumma Aameen Hamma”

“Inshaa Allah Hamma”

“Aameen”

Yauwa Amnah ta. Ya ce da Amnah Yana lakutar kumatun ta.

“Zaki Sha alawa?”

“Eh” ta fada tana tafa hannuwan ta.

“Nawraah jeku sayo alawa please. Ungo ki taho da omo da sabulu zan mana wanki sun taru. Kowa ya curo nasa”

“Tohm Amma dan Allah Hamma ka bari muyi kowa yayi nasa”

“Aa ban amince ba. Illa dai Ashfeef zakayi dauraya ka shanya. Ke Kuma ku zauna da amnah idan Kun dawo daga sayo alawar ki koya mata karatu”

“Tohm Hamma inshaa Allah. Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa”

“Aameen Yaa Rabbi jam’an…”

Mikewa yayi ya shiga hada kayan su da sukai datti Yana kaiwa wajen rariya zai wanke. Ashfeef ma ya dakko bokitai ya fara ebo ruwa Yana tarawa a babban baho Wanda zasuyi wankin dashii….

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

48

:::::::::

::::

Rufe kofar gidan tayi ahankali, Ta shirya tsaf cikin riga da zani na atamfa ta yafa mayafin ta ta rike yar jaka. Ta sauka daga yar matattakalar da ake haurawa ahau gidan nasu

Da sauri ta wuce har tana tuntube ta rankwafa kasa dataje wajen dakin su Amnah ta durkusa ta wuce da sauri tana saye fuska.

Dan adaidaita ta tare ta shiga ciki . Bata mance da kwatancen gidan data karba ba awajen direban daya kawo wa su Ashir kayan abinci kwanakin bayan tun da ran bappah junaidu.

Har kofar gidan ya kaita ta sauka ta lalubo kudin sa a jaka tana kallon darin biyun ta dan adaidaita, ya wafce da karfi ganin taki bashi, ta tsirawa wa kudin idanu. Alokacin Kuma Nusaiba tunani take dama bata zo ba da ta kafa ta daba don tanason ta saka data ta hau duniyar online.

Baki ta wangame alokacin data Isa kofar gidan tana yaba tsaruwa irin tasa tamkar a gidajen da ake nunawa a talabijin na masu kudi.

Ta nufi gate din tanata sauri masu gadin suka tareta.

“Ya ke Ina Zaki?”

“Wajen hajiya nazo.”

“Wacace? Bantaba ganin ki ba anan gidan”

“Tabbas bakuwar fuska ce kam, Bana kasar ne”

Nusaiba ta dashare baki tana sosa kasan keyarta ta sake cewa,

“Kawatace matar gidan”

daya daga cikin masu gadin ya bushe da daria har yana rike ciki ya kalleta tun daga kasan kafarta zuwa fuskar ta . Gaba daya ko alamar daukar kalar ire iren kawayen hajiyar tasu batai ba. Don haka ya grigiza Kai hana tabe baki yace,

“Ba nan gidan bane Ina tunanin kinyi batan Kai”

“Banyi ba fa. Gidan Dr bintu mana. Zan maka karya ne”

“Kirata awaya ” ya fada yana rera fito.

Nusaiba ta zaro idanu tana janyo wayarta ta fara latse latsen karya ta danna wajen kira ta kara a kunnenta,

“Eh nazo bintu. Okay bari na shigo. Ai masu gadin nan naki ki canza su basuda kirki. Na gidah na kin manta korarsu nayi alokacin da suka hana hadiza shiga? Okay gani nan”

Ta nufi kofar kantar kantar zata shiga Mai gadin ya tare kofar da hannun sa yana hura hanci yace,

“Aa… Duk munsan ire iren ku. Ba wata hajia da kika kirawo dan Allah malama ki kama kafa ki koma inda kika fito”

Nusaiba ta saka hannu tana mai nuni da shi tace,

“Ka bude mun na shiga… Ya sunan ka ne?”

“Sunana Naziru gidah Kuma nace ba Zaki shiga ba don bansanki ba bakuwar fuska ce, na biyu Kuma ba wata hajia da kikai waya da ita. Yadda kika zo baki a abude tamkar Zaki handame mu ma kina kallon gidan kowa yasan bakuwa ce ke kuma marar karfi iri na. Don haka ki koma inda kika fito kada kisa na saka miki shocking wallahi” ya karasa fada Yana daga shocking din hannunsa. Wata waya Mai karafuna ajiki tanata hartsatsi

“Naziru ko? Ka kyauta ko? Zan nuna maka wacece ni a kasar nan”

“Mtsc” Yaja tsaki yana komawa kan kujerar sa Yana rera baitin wata waka,

Cikin ikon Allah sai ga fitowar motar direban rannan data gani. Ta dashare baki tana daga masa hannu. Ya yi murmushi shima yace,

“Ina wuni? Hajia ta…?”

“Kwarai ta Naduka…. “

“Tasan Zaki zo ne?”

“Munyi waya ai tana ciki”

“Eh tana nan. Ya haka nazman ka barta a tsaye ko wani abun kake?”

Naziru ya dube shi yana kallon nusaiba yace,

“Ka Santa ne?”

“Na kakkai su hajia gidan ………..

Ta katse shi da sauri tana murmushi tace,

“Bai sanni ba ne na masa uzuri. Bari na shiga”

Ta kutsa Kai ta gaban Naziru Mai gadi ta shiga ciki. Ba yadda ya iya ya koma wajen zaman sa ya zauna. Shi Kuma direban ya wuce tsalallaken titi wajen masu kankana…

Ko data shiga bata San kan gidan ba sai da sata Mai aiki ta nuna nata kofar da zata shiga.

Ta shiga ciki bakinta dauke da sallama. Kai tsaye ta shiga parlorn ta hakimce ta zauna ba kowa aciki

Sai daga baya Dr bintu ta sakko tana gyara dankwalin ta. Ta dubeta tana kallonta sama sama,

“Wacece wannan din?”

“Ah hajia ni ce fa. Matar bappan su nawrah “

“Oh” ta fada tana dubanta shekeke. Dake Itama Dr bintu akwai jin Kai

“Baki iya gaisuwa bane? ” Ta sake tambayar ta tana mata kallon tara saura kwata ganin yadda ta babbake akan kujera ta harde kafafu..

“Oh Ina kwana?”

“Lafiya. Meke tafe dake?”

“Dama zuwa nayi akan kayan abincin da kuke bayarwa kwana biyu shiru. “

“Ajiya kuka bamu ne? Na dauka niyyace da temakon musulunci mukayi iyayinmu ko dolen ku akan mu take?”

“Hajia kwantar da hankalin ki ni bada wani abun na ce haka ba. Kuma ni a bayan ki nake wallahi”

“Bangane me kike nufi ba malama”

“Ina nufin rannan ba Nawraah na fadin wasu maganganu ba da kukazo? nufina ki kwantar da hankalin ki nasan komai Kuma bazan bar wani abu ya taso ba muddin kika bani bukatin da nake nema”

Dr bintu tayi shiru gabanta na bugawa tasan komai? Kenan tasan Alhaji Sambaso mijinta shi yake kashe malama Hindu

‘kjnsan komai fa kikace .?”

“Kwarai na sani harda wani abun da ke bakida masaniya ma akansa” Nusaiba ta kara da qarya tana karya Kai bayan ba abunda ta sani

Dr bintu ta gyada kai tana gyara zamanta tace,

“Me kike bukata?”

“Kudi… Kayan abinci.., sutura irin ta ku ta manya. Kuma ba su Nawraah zaa kaiwa ba gidana zaa kawo. Sannan suma su Nawraah ki kawo kudi a basu. Idan kika dore akan haka to shikenan Ina Mai tabbatar Miki komai ya wuce. “

Dr bintu ta gyada Kai. Ta mike ta dakko jakarta hannunta na rawa. Ta ciro check dinta ta dakko biro ta rubuta kudi masu yawa ta mikawa nusaiba.

“Ki dauki rabi ki basu rabi su nawrahn.”

“Bakida damuwa ai awajena ma suke agidana ni nake dawainiya dasu ta komai daga abinci zuwa sutura”

“Allah sarki. “

“Kayan abincin fa?”

“Zan aiko a kawo miki inshaa Allah. Zaki iya tafiya yanzu Ina da abubuwa ne agabana”

Nusaiba ta gyara zaman ta ta dakko wayarta ta rike tana gyara mayafi tace.

“Dan daukeni da wayar ki a haka sai ki tura mun dan Allah”😂

Ba abun Dr bintu tayi, Ba musu ta dauki wayarta ta dau hotunan nusaiba ta tura mata a lokacin

Sannan nusaiba ta mike ta futa sukayi sallama. Ta tsaya a gate ta gaggasawa Mai gadin magana yayi banza da ita yana Jin rediyo harda Mai dakuwa ta Zagi.

Tana tafe tana addu’ar Allah yasa kar Dr bintu ta gane batasan komai ba. Wani bangaren na zuciyar ta Kuma na mamaki hadi da tabbacin lallai akwai wani boyayyen lamari da suke boyewa. Kuma koma menene Nawraah tasan wani kaso daga ciki…

Gidah ta koma ranta fes. Ta boye kudin har nasu Nawraah ta hanasu taki basu. Taki Kuma gayawa kowa kudin data samu da inda taje. Tace wai neman aiki taje a Naduka crescent. Matar ta bata dubu goma tace tayi cefane. Ranar dai abinci har da nama akai kowa yanata mamaki.

Dr bintu na lekan nusaiba ta taafi. Jikinta na rawa ta nufi parlorn Mai gidan nata Yana zaune yana karanta jarida ta zauna akusa da shi tana yarfe hannu tace,

“Nusaiba dinnan tazo komai tac har abunda bansani ba ta sani…

A firgice ya juya ya dubeta bai San sanda ya furta Cewar,

“Tasan ni na tunkuda junaidu Mai gidan Hindu ta baranda ya mutu ma kenan.”

Dr bintu ta mike tana zaro idanu tana girgiza kai tace,

“Alhaji…. Kana nufin kace shima kashe shi kayi? Kacemun ya fado bai taka tsani ba ya rasu. Ashe ashe Alhaji Kai ka kashe shi?. Ka kashe matar sa shima din kaje ka kashe shi. Alhaji wace iriyar rayuwa ce. Kisa fa? Kamai da rai tamkar kiyashi Alhaji? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un. Wallahi tallahi nagaji. Yanzu kenan tunda itama ta sani zaka bita ka kasheta kenan?”

Alhaji Sambaso ya girgiza kai yana harde hannuwa ban roko yace,

“Wallahi bada sani na kashe shi ba. Fada muke na turashi ya Fadi ya mutu. Ki yarda Dani bintu. Zancen gaskia kenan. Ita kuma bansan a inda taji ba Allah”

“To magana ta gaskia Alhaji na tsame hannuwanaa akan ka. Maganar Hindu na rufa maka asiri kace kuskure ne na bar maganar. Amman ka sake kashe musu mahaifiy saboda Allah. Wato kenan itama wannan kasheta zakai ko? Daman tazo tana bukatar kudi da kayan abinci da sutura idan baa bataba ba zaa samu matsala. Saboda tana cewa ita kadai ce tasan yadda zatai da Nawraah komai ya wuce “

“Karki damu duk abunda takeso zaa mata. Allah zaa yi. Kome tameso. Ni ki yafemun kinji?”

“Wace bintu ce zata yafe maka? Ka nemi yafiyar Allah dai ka Kuma roki gafarar iyalin su. Ba ruwana acikin Allah kuwa.”

“Trust me baa abunda zanwa matar nan Allah shima shi ya takalo ni Yana gayamun maganganu Yana marina kinga abunda ya faru kenan”

“Alhaji koma meyake maka sai kayi enduring ka kashe masa mata,shi tunda acikin bacin rai yake. Idan ya huce sai ka gyara amma ka kashe shi?”

“Tasu ta kare ne su. Ya za’ai da wannan matar. “

“Yanzu dai inada aiki asibiti idan na gama cikin week dinnan zanyi tunani”

“Yauwa bintu na Allah ya miki albarka.”

Mikewa tayi ta fice ta nufi asibutin tah dake bayan unguwar, gabanta nata faduwa . Ko da direba ya sauketa ma ta dade Bata futa daga mota ba saboda tunanin data tafi

:;;;

Kwanaki suka shude. Alokacin Ashir har ya fara hada kudade sosai na Sanya Nawraah a jamia.

Ranar wata laraba da yammaci Dr bintu taje gidan na nusaiba ta Sha mamaki dataga gidan dama aciki suke rayuwa

Ta zauna tana kyamatar ko’ina. Aka kawo mata ruwa ma taki Sha. Suka gaysa da nusaiban ta tambayi nusaiban abinda take so.

Nusaiban tace yaran su sun samu gurbi a jami’ar Al-Haramein. Amman ba kudin da zasu shiga. Kuma an dena daukar daliban tallafi.

Dr bintu tace ba damuwa. Satin sama zaa biga musu admission letter. Makarantar harda share din mai gidan ta Dana hajja qibdiyya. Don haka zaa basu scholarship khauta su nawa ne. Nusaiba tace su hudu ne . Layla, Nawraah, Ashfeef da Kuma Ahmad.

Dr bintu tace ba damuwa zaa basu gurbin karatu. Itama yayanta biyu daya zata fara daga kevel one . Dayan Kuma a babban gurbi yake zai karaa karatu ne . ..

Hakan kuwa akayi ana shiga satin aka bugo admission letters aka Aiko dasu akace nanda sati biyu suzo su fara daukar darasi a jami’ar Al-Haramein dake Naduka crescent.

Hakika su Nawraah sunyi murna. Musamman Ashir daya kasa boye farin cikin sa. Ashfeef da Nawraah ma harda su a gurbin karatun.

Wani bangare na zuciyar Nawraah Kuma na kokonto akan amincin Dr bintu da Nusaiba. Don haka ta zuba musu Ido kawai tana nazartar su….

:;;

Ashir na zaune akan kujera… Ya sayo second fairly used din waya dake hannun sa..

Ya ciccire komai na wayar ya mayar kan second din daya saya. Ya kuma bar su akan ta ainhin. Recordings din wakokin Nawraah data yiyyi ya ajiye mata su ya Kuma tura wasu a wadda ya sayo ..

Daya bayan daya ya shiga danna wakokin larabawa yana saurara duk Wanda batai masa ba ya goge akan wayar daya sayo yayinda dayar Kuma ya ajiye don Nawraah yake son ya barwa duka tunda yanzu ta shiga jamia tana bukatar browsing assignment da sauran su. Tasa Kuma sai Ashfeef ya dinga amfani da ita.

Yaje kan wani recording na wakar Maher Zain. Har zai goge sai Kuma ya cigaba da saurara jin tanada dadi. Maganganu ya fara ju suna fitowa daga wayar yayinda recording din wayar baa jinsa sai can daga kasa.

Kamar zai goge sai Kuma ya cigaba da saurara Yana ji….jikinsa ya dau rawa jin maganar da macen da mijin keyi. Da sanda ummy take basu hakuri tana bataji komai ba.

Mikewa yayi a tsaye . Whatsapp dinsa ne yayi kara. Ya duba wayar dake hannun sa. Ganin fefen bidiyo ne aka tura Masa da wata number ta waje. Yana budewa hankalin sa ya tashi na daga abunda ya gani

Jikinsa na bari ya tura budiyon daya wayar daya barwa Nawraah . Ya sake dubawa zai kira number data turo yaga ta bace bat bata kan WhatsApp gaba daya idan ya kirama sai ace batakan network

Fita yayi ransa na zugi. Har zai fuce baki daya sai Kuma ya kwaso shanyar da Nawraah tayi ya Kai mata dakin ya koma ya gyara ko’ina ya shigar musu da takalman su da kayan wasan Amnah daki ganin garin da hadari.

Ya koma ciki ya dakko Dan balangun daya sayo musu basanan ya dora akan katifar su ya fita

Yana rufo kofar sai ga Nawraah ta dawo rike da hannun Amnah

“Hamma Ina zaka?”

“Ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo inshaa Allah. Ungo rike wayar nan taki ce. Ki dinga browsing na assignment da itaa idan kin fara jamia..duk rintsi duk wuya kada ki bari wayar nan fa subule daga hannun ki. Kar ki bawa kowa, Na roke ki da girman Allah kuma recordings din wayar nan kada ki jisu har sai kin shig aji na biyu zaki shiga na uku, sai na hudun kammala jamia kinji ko? . Allah yabada saa”

“Hamma meye haka kamar Wanda zaiyi tafiya ba dawowa? Nagode Allah ya saka da alkhairi Amin”

“Aameen ya Hayyu waayum. Sai na dawo. “

Ficewa yayi dasauri bayan ya yiwa Amnah wasa Yana lakuce mata kumatu

Kai tsaye ya nufi ofishin Alhaji Sambaso ya ci sa’a kuwa yana nan. Akayi masa iso ya shiga

Yana shiga dama Alhaji Sambaso shi kadai ne. Ashir cikin zafin nama ya cikumi wuyan sa yana kunna masa recording din wayar nan.

‘kai ka kashe ummy…. Kuma ka kashe abbiey…” Ya karasa fada Yana daga wayar sa.

“Kaga komai nan evidence ne cikin nan. Inshaa Allah rayuwar ka sai ta tagayyara sai ka zama abun tausayi. Zakasha mamaki”

“Ka tsaya muyi magana yaro”

“Magana? Hahaha zakayi magana aagaban hukuma da gaban Allah ranar gobe kiyama”

Ficewa yayi. Alhaji Sambaso ya saka hannu ya shafo habar sa Yana furzar da iskar bakinsa Mai zafi . Wayar sa ya dauka ya rubuta sako ya koma ya zauna Yana shafe kansa.

Ba jimawa can wayar sa tayi haske …ya dauka yana dubawa hamdala yayi ya kwantar da kansa akan kujera Yana sauke ajiyar zuciya..

°°°°°

Zaune suke baki daya sai ga waya akan kira number Ashfeef ance suje asibitin Naduka na gwamnati bangaren yan accident da quna.

Suna zuwa suka tarar da wata leda an nannade da kyalle. Tamkar an Kona takarda ta yayyanke dinnan tayi baki tayi toka.

“Menene wannan din?” Ashfeef ya tanbayan bakinsa bude ..

Sauran kuwa suka kasa magana.

Daya daga cikin maaikatan wajen yace,

” sunyi hatsari ne da wata tankar mai sun kone baki daya. Su bama a gane komai nasu. Kai ma dakyar aka samu wani dan area ku ya bada number ka …. “

“Bangane ba ‘da na. Me yake faruwa? Konuwar me? . Motar mai kuma?” bappah Auwalu ya tambaya baki daya kamar mahaukaci yama rasa mai zai ce.

Gaban Nawraah ya tsananta bugawa tammar zai zullo ya fado,

Maaikacin yace.

“Bayan dogon binciike da mukai.Sunan sa Ashir junaidu. Ko daga Naduka zone.. Allah ya masa rasuwa”

Diiiiim komai ya dauke. Tamkar duniyar ta tsaya chak.baki daya haka suka zama tamkar mutum mutumi dukkanin su aka rasa mai cewa komai.

Idanuwa na zubar da hawaye. Hanci na tsiyayar majina ta tashin hankali. Yayinda fitsari ya cika marar su. Kafafuwa sun gaza daukar nauyin su. Hannuwan su na lankwasar tashin hankali, Ya yinda sassan jikin su baki daya suka yi laushi..

“Allah ya jikan ka da rahama… Hamma Ashir.”

Suka jiyo muryar Amnah daga gefe ta kwanta akan ledar da aka sanya shi namansa sun kone kurmus kamar babbakakken kan rago gaba daya shine sanye acikin ledar sai gutsattarin naman jikin sa kamar an soya su sun babbake sun kone. Yayinda sauran rassan jikin nasa kuwa ma babu sun nike a titi sun kone da mai. Wasu kuma bazasu ganu ba. Kasancewar direban motar. Da shi Ashir din da yaran motar tirelan man duk sun mutu…

🥴🤐Acigaba da bin littafin KWANKWASON JIMINA MAI WUYAR SHAFAWA…… A kuma yi hakuri, bana labarin haka yazo 🙏🤭

RICH VS POOR
ANEES
MARWAAN
NAWRAH…..
LIFEPARTNERS
AL HUB HAYAT

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

HIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX).

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *